DR TAHEER CHAPTER 5 BY UMMU ASHRAF

DR TAHEER CHAPTER 5 BY UMMU ASHRAF

             WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 

Nafisa suna gama waya da umma..ta ja Layla suka shiga daki…tana kallonta da kyau tace”Layla mgn ce nake sonyi dake..inaso ki tsaya ki fahimceni da kyau..snn don Allah kar ki bamu kunya”…Layla na daga Kai tace”InshaAllah Mami”…Nafisa tayi shiru tana jinjina mgnr da zata fada matan…bata San ya Layla zata dauki wnn mgnr ba…a hankali tace”Layla Taheer ne dama yake sonki…snn mu munaso mu hada aurenku.. yanxu ma zaa Kira daga Dutse a tambayeki”..Layla ta dan bude ido tace”waye wnn Kuma mai sunan daddy Mami..Ni ban taba sanin wani mai suna irin nashi ba..a Ina ya sanni toh”…Nafisa ta dafa goshi cikeda takaici…wato ma bata fahimci Taheer din da ake nufi ba knn…Saida ta kamo hanun Layla snn tace”kinga Layla..ai daddyn naki ake mgn…kindai San ba muharraminki bane Layla akwai aure a tsakninku..sbd haka a matsayina na mahaifiyarki Ina rokonki don Allah..don Annabi Layla ki ceci rayuwar bawan Allahn nn..Taheer yana sonki fiyeda yanda kike tunani Layla..Kuma ba laifi bane idan ya soki.. kema kice musu kin amince…nasan in Allah ya yadda zakiga riban auren a gaba”…Layla ta mike tsaye a gigice tace”Mami wlh ban gane abinda kike nufi bafa..wani daddyn wai kike mgn akai..ba dai daddyna ba koh?…Nafisa itama tamike tsaye tareda kamo kafadan Layla ta rike gam…tana kallon idanunta tace”shi nake nufi

Layla…Taheer dai da kika sani namu..Wanda yake kiranki baby kice daddy..Taheer dai da kike bearing da sunanshi Layla…shidin nedai wanda yake maki sonda ko ni dana haifeki da kyar idan Ina maki irinshi…ki gane Layla..Taheer irin son da yake maki ba irin wanda ke kike tunani bane…shi so irin na au…bata karasaba sakamakon wani Kara da Layla ta saki tareda kwace jikinta daga rikon da tayi Mata…Nanda nan hawaye ya shiga bin kuncinta ta shiga girgiza Kai tace”Mami how could you say such a thing…how on Earth will daddy say he loves me bayan duk matan dake duniyan nn…Mami ko kin manta ne…daddy na nefa..he’s like a father to me Mami so why zakice wai Yana Sona yanxu…why plss”…ta karasa tareda durkushewa nan inda take ta sake sakin wani kukan…a hankali Nafisa ta karaso inda take ta kamata suka koma gefen gado…ta shiga goge Mata tears din a hankali tace”nasan dole zakiji mgnr nn wani iri Layla..but that’s the fact…Taheer is madly in love with you…he loves fiyeda yanda kike tunani”…Layla ta fada jikinta tana sakin wani kukan…wnn love word din jinshi take tamkar saukan aradu a kanta…zuwa yanxu ta tabbatar gsky Mami ta fada amma how..how could daddy do this to her…meyasa Saida ta daukeshi matsayin uba snn zaice Yana sonta…Nafisa ta shiga shafa kanta a hankali cikin sanyin murya tace”nasan yanxu zasu Kira Layla as I have told you ana so aji ta bakinki ne…and if as your mother akwai favour da ya kamata kimin to wnn ne Layla..inaso kiyi accepting Taheer nasan InshaAllah nan gaba sai kinfi kowa yin farin ciki da haka”…Layla dai kukanta takeyi kmr ba gobe…ta maimaita”how”yafi a irga…ita har yanxu gani take kmr a mafarki.+

After like 30 mins aka Kira Nafisa..da sauri ta mikama Layla dake kuka har yanxu…cikin muryanta da baya fita sosae kawai tace tayi accepting snn ta mikama Nafisa wayan…ba bata lokaci ita Kuma ta Kira umma ta sanar da ita sunyi kmr yanda takeso…umma taita suburbuda musu albarka kuwa…har wani sauke numfashi tayi da taji Laylan tayi accepting…kuka kuwa dama tasan dole zaayi haka…dama ya aka cika Layla da kuka bare yanxu da ta samu dalilin yin kukan..tasan InshaAllah nan da wani dan lokaci zata hakura and tanada yakinin zataso Taheer itama ko don sbd kaunar da yake Mata..she prays Allah ya tabbatar da alkhairi snn ya kade dukkanin fitina.

Around 5pm umma da ummi na zaune a parlor…ummi na kokarin Kiran Nafisa taji meya hanasu dawowa har yanxu kawai sai ga Kira ya shigo…kmr bazata sauka ba ganin uncle din Taheer don tasan mgnr da zaiyi Mata..sai Kuma dai ta Kai zuciyarta nesa snn tayi picking…bayan sun gaisa sai tayi shiru tana sauraron abinda yake fada…sai Kuma ta saki wani salati tareda sakin wayan ya Fadi nan kasa…lokaci daya saiga hawaye a idon ummi which is very Hardly kaga abinda zai Sata kuka..da sauri umma ta karaso gareta hankali tashe take fadin”innalillahi wainna ilaihi rajiun..lfy Yaya menene ya faru”…ummi tai banza da ita tana cigaba da hawayenta…umma da duk a rikice take..ta sunkuya tareda dauko wayan umma dake nan kasa..ta shiga duba call logs wai ko zata fahimci dalilin kukan nata amma bataga komai ba..sai kawai ta fice zuwa part din Taheer don ta lura ummi ba kulata zatayi ba..

Ta sameshi kwance kan gado..yayi nisa cikin tunani..tana zama kusa dashi kafin takai ga yimai mgn wayanshi ya shiga ringing..ya bude idanunshi da sauri snn ya tashi zaune..yana kallon umma yace”umma ban San kin shigoba wlh”…yana fadan haka yayi picking wayar tashi…a daya bangaren uncle dinshi yace”kana jina Taheer”…yace”inaji uncle”..Alh Adam yaci gaba”Congratulations..yanxu aka daurama aure da Layla”…Taheer ya zare ido sosae…not believing his ears snn yace”uncle ban ganeba plss..an dauramin aure Kuma”…uncle din yace”yes..nazo garin ne gaisuwa..shine kakan nata yace kawai a tambayeta in har ta amince sai a daura muku aure..in yaso sati mai zuwa idan an daura wancan auren…sai ayi biki tare snn a Kai makasu gaba daya”…tsittt Taheer yai kmr ruwa ya cinyeshi…bai San lokacinda ya saki wayan ba snn ya risina kawai ya shiga jero sujud…umma na gefe tana kallon ikon rabbi…to me ya samu yaron nn haka…Saida ya jero sujud kusan goma snn ya mike da sauri ya isa inda umma ke zaune tana kallonshi…ya rungumeta gam gam harda hawayen farin ciki yace”umma I can’t believe what my uncle told me…umma am married…married to baby umma..yanxun uncle ke fadamin sun daura Mana aure…umma am the happiest man on Earth.. Alhamdulillah ya Allah… Alhamdulillah…i can’t thank u enough umma cox kece sila…umma badan keba da bansan ya zanyi ba…I love you so much ummata…Allah ya saka maki da mafificin alkhairi…Allah ya faranta miki fiyeda yanda kika faranta min ummah”…hannu umma tasa ta dagashi daga jikinta..tana kallonshi da kyau tace”ban ganeba Taheer.. explain your self plss”…ba musu Taheer ya Mata duk bayaninda uncle dinshi ya mai yanxun…umma ma ta saki hamdala tareda kamo hanun Taheer din dake kallonta shima Yana murmushi…sai Kuma ya mike kmr an zungureshi ya nufi bathroom yana fadin..”I have to pray umma..I can’t thank Allah enough… Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!

Umma ma kallonshi kawai takeyi da murmushi har ya shige bathroom din..itama ta mike ta fita… cikeda tunanin wnn al’amari…yanxu ta gano dalilin kukan ummi…tana shiga parlon su Nafisa ma suka shigo…da gudu Layla ta fada jikin ummi dake kuka itama ta fashe da kukan…ummi ta rungumeta a jikinta suka shiga rera kuka tare… Al’ameen na kallon mamanshi yace”Mami meke damunsu…basuda lfy ne”…a fusace ummi ta dago tana dubanshi tace”asibiti ne a kanmu ba rashin lfy ba….dan banzan yaro kawai”…da sauri Nafisa ta sunkuyar da kanta tana kokarin danne dariyar dake son kufce Mata…ita kanta umma kauda kanta gefe tayi tana murmushi…duk Wanda yaga yanda suka hada Kai suna kukan dole ma abun ya bashi dariya…ummi ce ta fara mikewa snn ta kama hanun Layla ta mikar da ita itama..snn suka nufi dakinta…su umma suka bisu da kallo suna danne dariyarsu.

STORY CONTINUES BELOW

Da daddare Taheer ya shigo dakin ummi as a result of kiranshi da tayi…ya nemi wuri ya zauna kanshi kasa…ummi na mai mugun kallo tace”Ni dai kayima haka koh Taheer…nida na tsugunna na haifeka ban isa ince kar kayi abu ka Bari ba knn…sbd tsabar son Kai Taheer kaje ka hada baki da mutane…saura yan kwanaki bikinka…kasa suka shiga suka fita Saida sukasa aka baka auren ‘yar nan..yanxu Dan Allah bakaji kunyaba Taheer..ace ‘yar cikinka zaka aura.. Layla cefa Taheer..wai meya hau kanka ne these days…to Bari kaji in fada maka..idan ma kana tunanin ni zan dauki Layla in baka wai a matsayin Matarka you are mistaken wlh…yadda kasa aka daura maka aure da ita bada sanina ba..itama bada saninta..haka zan sanya ka saketa ko kanaso ko bakaso…Bari a gama bikin naka ka gani…zakusha mamaki na wlh”…Saida ummi tayi shiru snn a hankali Taheer yace”wlh ummi Ni kaina I have no idea of daurin auren nn da akayi..ban San komai akai ba wlh ummi.. believe me..kawai kirana uncle yayi yace an daura Mana aure but wallahi bani na nemi ayi hakan ba…dn Allah ummi kiyi hakuri ki dena fushi Dani..duk abinda kikeso zanyi amma ummi dn Allah kar kice zaki rabani da baby…I can endure duk wani punishment daga gareki just don’t seperate the two of us plss..I beg you”…tsaki ummi taja tana hararanshi ta nuna mai kofa tace”tashi ka barmin daki malan…bani da lokacinka yanxu..ka Bari a gama bikin nn..sai na baka mamaki wlh”…bai sake cewa uffan ba ya mike ya fita daga dakin hoping he can see Layla ko sau dayane…Amma har ya fita ko motsinta baiji ba…yasan yanxu tana can hankalinta a tashe…maybe ma duk duniya babu wanda ta tsana kmr shi..he is suppose to be happy Layla is now he’s but he is not happy with how things are going at all..he really wants to see situation din da take ciki a yanxu…yasan for sure tana can tana kuka and da kyar idan batayi developing fever ba zuwa gobe…on the other hand Kuma Yana tunanin aurenshi da Sameera…yasan for sure idan ya aureta bazata tabajin dadinshi ba cox baida interest a kanta..that aside ma duk duniya baijin akwai macen da zai hadata da Layla Kuma yayi tunanin yin adalci a tsakaninsu…he can’t…son da yake mata is different..dole ya nemi way out kafin lokaci ya kure mashi and he has only one way out..

Washegari…

Karfe 4 daidai yayi sallama parlon ummi…uncle dinshi ne zaune a parlon..sai umma da ummi…kallo daya zakai musu kagano tsantsar bacin ran dake shimfide kan fuskokinsu…a hankali ya karasa ya zauna..bai yadda ya hada ido da kowa ba…ummi ta mike ta iso inda ya zauna din…ta daga hannu kawai sai ji yai ta wankeshi da Mari…cikin hawaye ta fara mgn”mu zaka wulakanta Taheer…ka nuna ma duniya bamu isa dakai ba…meya shiga cikin kanka da zaka aikata abunda kayi…sbd bakada kunya Taheer ka taka kaje har gidan su matar da zaka aura…kayi sallama da mahaifinta Taheer ka kalli tsabar idonshi kace mai ka fasa auren ‘yarsa..sbd kawai kana takama an aura maka yarinya karama da bama sonka takeyi ba…yaushe ka zama mutum mai son Kai haka…yaushe ka zama mara Imani ban saniba”…Taheer dake dafe da kuncinshi da ummi ta wanke da mari…yai tsitt…dama yasan hakan zata iya faruwa so he’s not shocked…uncle dinshi na kallonshi yace”ba mgn akeyi maka ba kayima mutane shiru”…Taheer da kanshi ke kasa har yanxu yace”don Allah kuyi hakuri uncle…Ni banyi haka don in bata muku rai ba…ko na aureta uncle ba dadin zama Dani zataji ba tunda bana sonta…Kuma ni gsky Ina gujema daukan alhakinta ne…babu macen da zan iya hadata da Layla Kuma ince zan iya adalci tsakaninsu…Allah ya sani nasan bazan iya adalcin ba shiyasa naje kawai na sanar da mahaifinta… snn ubangiji ma da yace mu auri mace fiyeda daya Saida yace idan mun San zamuyi adalci..ni Kuma nasan I can not shiyasa naga it’s better a fasa auren kan in aureta Kuma inzo Ina daukan alhakinta”…har Taheer yai shiru binshi kawai suke da kallon mamaki…uncle dinshi na gyada Kai yace”wonderful..ka aikata abinda kake so Taheer muma kuma yanxu zamuyi abinda mukeso…you deserve punishment kan abinda ka aikata..and do you know punishment daya kamace ka?..a hankali Taheer ya girgiza Kai alaman he don’t know…uncle dinshi ya sake sakin smile yace”badai takamarka ka samu Wadda kake so shiyasa kace ka fasa auren waccan ba…to ita wnn da kakeson ai karamar yarinyace dama..don haka bazaa baka ita ta tare matsayin Matarka ba har sai ta kammala karatunta”….a firgice ya dago Kai Yana duban uncle din nashi…sai Kuma ya shiga girgiza Kai idonshi har ya kawo kwalla yace”uncle don’t do this to me plss…wlh mutuwa z…bai karasa ba ummi ta bige mai baki…ya matsa daga kusa da ita da sauri yace”don Allah kar kumin haka uncle…ku tausayamin plss”…uncle dinshi dake kallonshi Yana murmushi yace”ai na gama mgn Taheer..ba dai mu kaje ka kunyata a idon iyayen yarinyar nn ba?…da sauri Taheer yace”na fasa uncle..wlh na hakura..zanje in samu dad din nata in bashi hakuri..Kuma kuyi hakuri plss”…ba Wanda yace mai kala…ya sake karya murya yace”uncle medicine zata karanta fa…for how long zanyita jiranta uncle har saita kammala karatu”…cikeda takaici ummi ta cillo mai pillow dake gefenta tace”tashi kaba mutane wuri fitsararren banza da wofi…har wani for how long kake tambayan mu sbd bakada nutsuwa”…Taheer ya mike zai fita sai ya kalli umma wai ko zata sa baki..amma sai yaga ta dauke kanta gefe…jikinshi a sanyaye ya fita…yasan tunda tai haka bazatai mgn ba knn…yasan itama bataji dadin abinda ya aikata ba…shi da kanshi yasan what he did was wrong Amma to ya zaiyi.

Daren nn ko runtsawa Taheer baiyi ba…sai kullawa yake Yana kuncewa…gaba daya abubuwan sunzo mai a baibai…yanxu tsakani da Allah for how many years zaiyita zaman jira idan akace Layla sai ta gama karatu… medicine fa…ya zama dole ya nemawa kanshi mafita if not yana zaune wankin hula zai kaishi dare…umma is his only hope…itama Kuma yaga alaman bataji dadin abinda ya aikata ba..but it’s not his fault..harga Allah shi yana gujewa kanshi azabar da ubangiji ya tanada wa mazan da suke banbanci tsakanin matansu ne…snn itama yana guje mata bacin ran miji ya fifita kishiya a kanta…yasan shi ba adali bane when it comes to baby shiyasa ya aikata abinda ya aikata din…amma haka nn zaiyi folding hands yana gani su hanshi matarshi..Anya zai iya kuwa?The following day Layla ta tashida zazzabi mai zafi…ummi duk ta rikice ta rasa yanda zatayi da ita…dama duk take rashin lfy to Taheer ne mai jinya…shi zaiyi Mata komai ita ummi saidai dan abinda baa rasaba…gashi sai kuka take Mata anyi anyi tayi shiru taki…dama shi kadai ne ya iya handling dinta gashi kuma yanxu wnn abun ya shigo tsakani…tun dare take ayyana ko kiranshi zatayi ya dubata sai wata zuciyar Kuma ta hanata…ganin dashi ta kwana ummi ta yanke hukunci suje asibiti kawai…ta riko hanun Layla suka fito daga dakinta…Nafisa na tsaye tana jiransu…hanunta rikeda car key..sai umma dake parlor itama tana jiransu…ummi na rikeda ita suka fita daga parlon.. Mama hawwa kadai suka Bari a gidan zata kulada yara…+

Suna fita Taheer na fitowa daga part dinshi…ya bisu da kallo ganin zasu shiga mota..cikin ranshi yana tunanin Ina zasuje haka…bai San lokacinda ya nufi inda suke da sauri ba har Yana dan hadawa da gudu…ganin yanda ummi ke rikeda Layla kadai ya san cewa something is wrong…daidai ummi ta sata a mota..tana kokarin shiga itama kawai ta ganshi a gabanta…yana shafa kai yace”am…umm..me..me yake…damunta..ummi?…wani kallo ummi ta zabga mai tareda jan tsaki tace”bani wuri in wuce”…ya rausayar da kai tamkar zai Mata kuka yace”ummi don Allah me yake damunta…kawai fadamin zakiyi sai in baki drugs ki bata”…ummi murmushin takaici ta saki tana kallonshi tace”you have some nerves…bazaka bani wuri in wuce ba saina gaura maka mari a wurin…waye ya ja Mata ciwon idan ba Kai ba..ka saurari haduwa na dakai  bazaiyi maka kyau ba wlh…now bani hanya in wuce”…a hankali ya sake cewa”ummi to at least ko hijabi a bata tasa mana..bai kamata taje wani wurin da wadan nn kayan ba”…ganin kallonda ummin kemai bai sake cewa komai ba ya matsa Mata ta bude motan ta shiga…Yana tsaye yana kallo Nafisa taja motar suka fita daga gidan…da sauri ya nufi tashi motar shima ya shiga..yai Mata key snn ya bi bayansu.

A hankali yake tafiya don baiso sugane yana binsu…gaba daya he’s worried about her..meyasa ummi zata hanashi dubata…snn meyasa zaa barta ta fita da mayafi kadai..ko hula fa babu a kanta..almost rabin gashinta duk a waje.

Tafiyan almost 13 mins sukayi yaga sun shiga wani private hospital…yai kasake kawai Yana kallon motarsu daya shiga ciki…yanzu ummi ta gwammace ta kawota wani katon banza ya dubata a kan shi ya dubata…laifi ne don yace yanson Layla ko laifinshi ne don an daura musu aure bata saniba…gaba daya he’s becoming more angry than before…bai shiga da motan ciki ba yai parking nan waje snn ya fita ya shiga cikin clinic din…ya sauke ajiyar zuciya daya tuna mai clinic din is his colleague..so at least zai nemi alfarmar a barshi ya dubata and zai samu.

Suna shiga reception ummi ta nemi wuri ta zauna tareda rike Layla a jikinta…umma da Nafisa Kuma suka tafi don bude Mata file…Taheer kam cikin wasu mutane da yaga zasu shiga ciki ya shiga..Yana tsakiyarsu suka shiga wurin…Allah ya taimaka dai ba Wanda ya ganshi a cikinsu… Kai tsaye ya wuce office din abokin nashi…yana kokarin yin knocking sai ga abokin nashi ya fito daga office din…ya wara ido yana kallon Taheer din yace”what a suprise..yau Dr.Taheer ne a clinic dina”… Taheer yai murmushi yace”wlh nine Dr.Umar…wani alfarma nake nema wurinka plss”…Dr.Umar yace”ok mu shiga daga ciki”..

Saida suka shiga suka zauna snn Taheer yace”you know..matata ce aka kawota clinic din nn yanzu..batada lfy and ummi na fushi dani..taki bari in dubata..shine nakeso plss ka Bari in dubata da kaina”…Dr.umar ya daga Kai snn yace”bakada problem Dr…yanzu dama fita zanyi so In na fita zan turo maka ita..saika dubata a nan”…da sauri Taheer yace”yawwa friend…na gode sosae”…Dr.Umar na murmushi ya fita daga office din….ya samu su ummi a reception ko file din ma basu bude ba yace”ummi kece a clinic Dina yau”…ummi na kallonshi tace”wlh nice Dan nn..kaga yarinyace ba lfy wlh”…Dr.umar yace”ba matsala ummi taje office dina ta jirani..yanxu zan dawo sai in dubata…abokin Taheer ne ni ai”…ummi na murmushi tace”Allah sarki..bari muje office din toh”..da sauri dr.umar yace”No ummi ita kadai zataje ai…kinsan yanda yanayin aikin namu yake..in ana bukatar wani abu sai a kiraki”…ummi ba don taso ba ta koma ta zauna snn tace”to shknn”..dr.umar na murmushi ya kalli Layla yace”yawwa baby muje koh”…ba musu Layla ta shiga gaba yana binta a baya..da kyar take tafiya..saida sukaje har kofar office dinshi snn yace”ki shiga ciki ki jirani..ynxu zan dawo”…ba tareda ta kawo komai a ranta ba bude kofar ta shiga…tana cin karo da Taheer ta juya a rikice ta shiga kokarin bude kofar zata fita…ya karaso inda take da sauri yasama kofar key…sai ta durkushe a wurin tareda sakin kuka…Taheer ya risina ya kamota da sauri…yasa hanu ya toshe Mata bakin…ganin zata tara mai jama’a…ta runtse idanunta gam..kirjinta sai sama da kasa yakeyi…Taheer yai tsai yana kallon yanda ta zabura daga ganinshi…duk sai yaji he hates himself daya furta cewar yana sonta…da bai fadaba duk da bazaayi hakan ba…ya kama hanunta a hankali ya zaunar da ita kan kujera…shima ya zauna Yana kallonta da kyau yace”baby am very sorry plss…ki yafemin dn Allah..nasan I was too selfish but wlh sonda nake maki ne duk ya janyo haka…kiyi hakuri ki dena kukan nn..I promise zan sawwake maki tunda baki Sona…i don’t want to be seeing you like this…don Allah stop crying and tell me abunda ke damunki”…Layla dai bata bar kukan da takeyi ba..Kuma bata bude idanunta ba…yana kallon gashinta da rabinshi ke waje yace”why did you come out like this…Ina hijab dinki”…Layla kukanta kawai take batace komai ba…a hankali ya durkusa nan gabanta..ya kamo hannayenta ya rike cikin nashi…murya a raunane yace”zaki fasamin zuciya baby…don Allah ki dena kuka…you are making me feel guilty”…ta tsaida kukan nata tareda zare hanunta dake cikin nashi…ta goge tears din dake idonta Kuma har yanxu bata bude idon ba…Taheer ya mike tareda komawa inda yake ya zauna idonshi a kanta yace”yanxu Ina ke maki ciwo”…”Kai na”ta fada a takaice…yace”bayanshi Kuma sai me”…ta sake cewa”zazzabi”…Taheer yai shiru kawai…Yana kallon yanda take mgn without looking at him…bai taba tunanin akwai rana da zatazo..wai baby taji batason ganinshi ba…lokaci daya zuciyarshi ta sake karyewa…sai yaji kmr ya rushe da kuka…itama da yake so kmr zai mutu ba sonshi takeyi ba..inaga su ummi Kuma..shi dama yasan wnn abune mai kmr wuya…he thinks he’s going to divorce her kawai if that will make he r happy…he always wants to see her happy…ya daure ya kakalo murmushi snn yace”shknn inda ke maki ciwo”…ta daga mai Kai kawai…yace”alright don Allah ki jirani a nan..zanje in siyo drugs in kawo maki”…ta sake daga kai…shi Kuma ya juya ya fita..Saida yai locking dinta ta waje snn ya tafi..don bai yadda da itaba…Yana zuwa pharmacy ya siya drugs din da yakeso snn ya koma office din a gaggauce…ya bude kofar ya shiga…tana nn zaune inda ya barta..ko idanun bata bude ba..da gaske ko ganinshi bata sonyi…jiki a sanyaye ya karasa tareda daukan pen kan table…ya zana Mata prescription na drugs din a jiki snn a hankali ya Mika Mata ledan yace”take”…ta miko hannu ya Dora Mata ledan a Kai snn ta mike tsaye…har takai bakin kofa taji yace”don Allah kar ki cema ummi ni na dubaki…and kar ki kara fita without wearing hijab pls “…ta daga Kai kawai alaman toh snn ta fice daga office din…Taheer ya koma ya zauna tareda dafa kanshi da hannayenshi…wnn shi ake Kira tsaka mai wuya…gaba daya duniyar yaji ta fice mai a rai…komai ya denajin dadinshi.

STORY CONTINUES BELOW

Ummi na ganin Layla ta dawo..ta mike da sauri tareda rikota..ta amsa ledan hanunta tace”wnn meye Kuma”…da kyar Layla tace”magunguna ne”…ummi ta kama hanunta suka nufi hanyar fita snn tace”inace rubutawa zaiyi sai ya bamu katin mu siya..shine zai siya da kanshi Kuma”…itadai Layla batace koma ba…suna isa bakin mota Nafisa ta bude ta shiga..umma ma ta shiga front seat..Layla da ummi Kuma suka shiga back seat.

Dr.Umar ya shigo office din ya samu Taheer zaune…yana dariyar shakiyanci yace”Dr.ashe baby ta zama Matarka Kuma…ka tuna me kake fada Mana a school idan mukace son yarinyar nn kake”…Taheer yai shiru ya rasa abun cewa…shaf ya mance dr.umar din ya San lbrin Layla a wurinshi…bazai manta ba lokacin suna school daidaikun mutane ne basu sanshi da baby ba…wani lokacin kafin a gama lectures zai gudu..idan aka tambayeshi sai yace”baby naje na gani”…ya sauke ajiyar zuciya wato tun tana tsumma yake sonta ganewa ne kawai baiyi ba sai yanxu.

Bayan kwana biyu…

Nafisa da yaranta nata shirye shiryen komawa gobe…ummi tace tunda an fasa bikin ya kamata su koma gida haka nn…ta hadama Layla kayanta.. don tace tareda ita zasu tafi…Nafisa dai kmr tace bai kamata su tafi da Layla ba tunda yanzu she’s married..sai Kuma tayi shiru…tasan tana fadar mgnr nn to ummi ta inda ta shiga ba ta nan zata fita ba..sai taja bakinta ta tsuke tareda zubama sarautar Allah ido.

A bangaren Taheer kuwa..duk Wanda ya sanshi a baya..idan ya kalleshi yanxu zaiyi tunanin yayi wata da watanni a kwance ba lfy sbd tsabar ramewan da yayi…tako Ina bugashi kawai akeyi…ya zamana ba inda zaije yaji sanyi…yayi regretting fadama umma yanason baby tunda gashi fadan baiyi amfani ba…gaba daya yanzu ko shiga part dinsu baiyi…da safe dai kafin ya fita zaije ya gaishesu Wanda umma ce kadai ke amsawa…idan ya fita Kuma bai dawowa gidan sai dare…umma ce kadai ke aiko da abinci a kawo mai..dukda baci yakeba..ita Kuma bata tambayeshi meyasa baici ba..yasan she’s very mad at him..and ya zama dole ya bata hakuri don hakurinshi na gab da karewa…tunanin yanda Layla ta mai dashi tamkar dodo ma kadai ya isheshi kafin ma azo kan mgnr ummi.

Daren ranar har ya kwanta yaga ba iya baccin zaiyi ba..sai ya mike zuwa part din ummi…ganin parlon ba kowa sai ya nufi dakin umma…tana kwance kan gado amma ba bacci takeyi ba…ya karasa ya zauna kusada ita sai ya kasa cewa komai…he really don’t know from where to start…umma Sarai taji shigowanshi amma tayi kmr bataji ba…a hankali ya matso dab da ita..yasa hannu ya kamo hanunta ya rike gam cikin nashi…hawaye na sauka kan fuskanshi ya fara mgn”umma don Allah kiyi hakuri ki dena fushin nn Dani..I know I have wronged all of you amma umma it’s not my fault…umma ke shedace na irin sonda nake ma baby…ko nace zanyi adalci tsakaninta da Sameera wlh ba iyawa zanyi ba…bazan taba iya daidaita son da nake Mata dana wata mace a duniyar nn ba umma…shiyasa nayi haka amma dn Allah ki tausayamin kiyi hakuri plss”…sai ya kife kanshi kan hanunta dake cikin nashi ya shiga kuka a hankali…umma ta mike zaune…jikinta duk yayi sanyi..Allah ya sani dama ba karamin tausaya mishi takeyi ba…yanxu daya zauna gabanta yana kuka sai ya sake bata tausayi…ta zare hanunta daya rike snn a hankali ta shiga goge mai tears din tana girgiza mai Kai alaman yayi shiru…Taheer ya sake rike hannayenta yace”umma don Allah kiyi hakuri”…ta Dora kanshi a kafadanta tace”meya sa ka aikata haka Taheer…meyasa bakayi shawara daniba kafin kayi…Saida kasa aka sanar da kowa Taheer lokaci daya kaje kace musu ka fasa auren ‘yarsu…meyasa ka aikata haka Taheer”…tana rufe baki Taheer yace”sbd bazan iya adalci a tsakaninsu ba umma…bazan iya hada sonda nakema baby dana kowa ba…Ina gudun kar in daukan ma kaina alhakinta shiyasa umma amm…bai karasa ba umma ta rufe mai bakin da hanunta jin yanda muryanshi ke rawa…tana shafa kanshi tace”na hakura Taheer…kasan bazan dawwama Ina fushi da Kai ba…but nan gaba kar ka sake yanke irin wnn decision din ba tareda reasoning ba kanaji na koh”…da sauri yace”naji umma…in Allah ya yadda bazan karaba…thank you so much umma I love you”…umma na murmushi tace”I love you too…yanxu let me get you something to eat…nasan yanzu duk ba wani abincin kirki kake ci ba”..ya bude baki zaice ya koshi umma ta rufe mai bakin tana cewa”shshsshh..kar ma ka fara cemin you are full don nasan you are not”…Taheer murmushi kawai ya saki…Yana kallonta ta fita daga dakin…ya sauke ajiyar zuciya tareda kwanciya kan gadon..at least ya samu saukin kuncin da yake ciki.

Few minutes later umma ta shigo da plate cikeda cookies sai tea…ta karasa ta zauna gefen gadon ta Mika mai mug din hanunta tace”oya tashi kasha tea…baiyi musu ba ya mike zaune tareda amsan mug din hanun nata…ta Dora mai plate din cookies din kan laps dinshi tace”gashi nn”…a hankali Taheer ya shiga Shan tea din Yana hadawa da cookies..gskyn ummi ne rabonshi da wani abincin kirki shi kanshi ya manta…Saida ya shanye tea din gaba daya snn ya Mika Mata mug da sauran cookies din yace”thank u so much ummah”…umma na murmushi tace”you are always welcomed my son…yanxu kaje ka kwanta kayi bacci..da safe sai mu karasa mgn”…Saida ya mike snn yace”to umma Saida safe”…tana daga mishi Kai tace”Allah ya tashemu lfy”…tana binshi da kallo har ya fita daga dakin…ta sauke ajiyar zuciya…tasan baisan ummi na Shirin tura Layla porthacourt ba…bata San ya zaiyi ba idan yaji wnn mgnr.Karfe 9 duk sun gama shiryawa don flight din 10 zasubi…su Al’ameen nata fita da kayansu cikin mota…Layla ta fito daga dakin ummi sanyeda  riga da skirt na atampa..ta daura dankwalin kayan a kanta snn ta kawo mayafi ta yafashi a kafada…hanunta rikeda wayarta…fuskan nn nata fiyau..da gani ba karamin kuka taci ba.

Da sallama Taheer ya shigo parlon…ya shiga binta da kallo kawai… ganin yanda tayi kyau cikin shigan da tayi…he feel like hugging her right now..ko kadan bai kawo da ita zaa tafi ba..sai Kuma ya kalli su Nafisa duk sun gama shiryawa suma…ya karasa kusa dasu…ya gaida ummi ta amsa a takaice…snn ya gaida umma…yana Shirin barin wurin Nafisa tace”inason yin mgn dakai bro”…ya dakata nn inda yake…ta karaso kusa dashi tace”mu danje daga waje”…ba musu ya shiga gaba tabishi a baya…a balcony suka tsaya…Nafisa na kallonshi tace”nasan bakasan tareda Layla zamu tafi ba..ummi tace mu tafi da ita and kar mu kuskura mu bari ta dawo har  sai tace mu dawo da ita da bakinta”…a gigice Taheer ke kallonta yace”I don’t get you…u mean tareda baby zaku tafi wai”…Nafisa ta daga Kai alaman eh…ya firzar da iska a bakinshi tareda zira hannayenshi cikin aljihun wandonshi murya a raunane yace”but how could ummi do this to me…why zaace zaku tafi da ita… u know am not used to living without seeing her around..in Ina ganinta at least zan samu sauki unlike ace bata gari gaba daya…I don’t know why ummi ke punishing Dina haka…tasan babu abinda zatamin inji ciwonshi kmr wnn…wlh Nafisa idan baby ta bar gidan nn bansan ya zanyi ba”…shiru kawai Nafisa tayi tana kallonshi cikeda tausayi…ya mance da duk wani zancen kunya at this point…iyakan gskyrshi yake fada mata…a hankali tace”wlh na sani bro…nasani ba karamin sabawa kayi da itaba..Amma ba yanda zamuyi da ummi…nasan bacin raine yake sata aikata komai…and InshaAllah da zaran ta huce everything will be back to normal again..so kar ka damu kanka plss…anytime you feel like seeing her sai kazo ka ganta…ba Wanda zai hanaka wnn..after all Matarka ce…snn zaka iya kiranta a waya duk kaso yin mgn da ita…da sauri Taheer yace”she won’t pick my calls I know…she hates me to the extent that ko ganina bata sonyi…this whole thing is killing me…ban San ya rayuwa zai cigaba without seeing baby ba…ban San ya zanyi da raina ba”…Nafisa da taji hawaye na ciko idonta tace”don Allah take it easy on your self bro…kar wani ciwon ya kamaka”…Taheer na kakalo murmushi yace”do me one favour plss…kar ki ringa bari tana fita anyhow…snn duk zata fita make sure tasa hijab da zaiyi covering dinta complete…kar ki bari ta fita ba tareda hijab ba plss”…Nafisa na daga Kai tace”InshaAllah I will bro…just take it easy…I promise zanyi iya bakin kokarina inga tayi accepting dinka as hubby…duk wnn abun da takeyi a yanxu nasan she’s shocked ne.. InshaAllah bazata dawwama a haka ba…zata soka da izinin Allah”…wani murmushi yai escaping lips dinshi…shi sai yanxu ma ya tuna da wa yake mgn…idanunshi sun rufe that ko gane me yake cewa ma baiyi ba…Nafisa data lura kmr kunyar abinda ya fada yaji…sai tayi murmushi tace”bari muzo mu wuce bro…nace mu jira ka kaimu ummi tace driver yayi dropping dinmu kawai”…ya daga Kai yace”ba matsala zan biyoku a baya”…Nafisa tace”to shknn…snn ta juya ta koma ciki…cikin ranta tana tunanin wane irin so Taheer kema Layla haka…dubi yanda ya fita hayyacinshi kawai sbd zata bar kusa dashi…tausayinshi sosae ya kamata…ta kumayi alkawarin zata taimaka wajen fahimtar da Layla faidan auren Taheer din da ita.+

Shiko Taheer binta kawai yai da kallo yana shafa Kai…he wonders abunda ya hau kanshi har ya saki maganganu a gabanta haka…yanxu shknn bai kara ganin baby…ummi knows exactly how to deal with him…ko a haka ta barshi ma is enough…yana ganin it’s the worst punishment of his entire life…babu abinda zai wahalar dashi fiyeda rashin ganin nata.

STORY CONTINUES BELOW

Yana nn tsaye suka fito gaba dayansu…suka shiga mota driver yaja motar suka fita…shima ya karasa tashi motar ya shiga snn yai Mata key ya fita daga gidan.

Suna tafe Yana binsu a baya har suka isa airport..bayan anyi parking duk suka fiffito daga motan…ya fito daga nashi motan shima ya karasa inda suke…ya shiga bama yaran hannu suna musabiha snn yai pecking dinsu kowa a forehead…tun kafin yazo kan Layla dama ta juya tareda barin wurin da suke…ya bita da kallo kawai…Nafisa ta karaso kusa dashi tace”to mu zamu tafi bro Allah ya saukaka al’amura”…yana kokarin murmushi yace”Ameen..Allah ya saukeku lfy”…ta amsa mai da Ameen snn tace”Bari in turo maka ita kuyi sallama”…yai murmushi kawai tareda komawa cikin mota…ita Kuma ta wuce inda yaran suke…ta turo Layla wurinshi kmr yanda ta fada…ta taho tana turo baki..idonta har sun kawo kwalla…tana isa jikin motar yasa hannu ya bude mota kofar daga ciki…ba musu ta shiga kafafunta a waje…ko rufe motar batai ba…ya saki murmushin takaici yana kallonta…inshort dai juya mai baya ma tayi…bata son ganinshi…Saida yai gathering courage snn yace”nasan yanxu ba Wanda kika tsana a duniya kmr ni..and as I have told you zan sawwake maki if hakan will make u happy..kiyi hakuri”…banza tai dashi taki kuma juyawa ta kalleshi…ya sake sakin smile snn yace”u can go..Allah ya kiyaye hanya”…kmr jira take ta shiga kokarin sauka daga motan…ya kamo hanunta da sauri..hawaye na kokarin saukowa kan fuskanshi yace”won’t you miss me baby..you are eager to leave me right?…lumshe idanu Layla tayi hawaye na sake wanke mata fuska…a hankali yai kokarin maida nashi hawayen shima snn ya saki hanunta…ya koma ya gyara zamanshi snn yace”am sorry”…bata ce komai din ba tabude motar ta fita..har tana hadawa da gudu…Taheer ya lumshe ido allowing tears din da suka cika mai ido suka saukan kan fuskarshi…ya zaro handky a aljihunshi ya goge snn ya rufe motar tareda dora kanshi ka starring…bai bar airport dinba Saida jirginsu ya tashi.

Kai tsaye clinic dinshi ya wuce don baison komawa gida kwata kwata…yai kokarin yakice damuwarshi snn ya fara duba patients kmr ba abunda ke damunshi…she’s trying his best ya boye abunda ke cikin ranshi but ya kasa mantawa dashi.

Around 3 Yusuf yazo office din nashi…bayan ya shigo ya zauna ko gaisawa basuyi ba yace”man I’ve heard abunda ka aikata..baka kyauta ba gsky..bakayima Sameera adalci ba”…Taheer dafa kanshi yai don ya gaji dajin mgnr nn…a hankali yace”Ni banyi haka don cutarta ba…nayine sbd in tseratar da kaina snn in tseratar da ita itama”… Yusuf ya daga kafada snn yace”shknn Allah kiyaye gaba…yanxu fadamin…Ina amaryar taka…Taheer Ibraheem Jakada angon Maryam Taheer Jakada..what a couple!!!…Taheer yaja tsaki snn yace”ban son irin wnn wasan ka sani”…da sauri Yusuf ya tsaida dariyar da yake snn yace”sorry ango..bazaa Kara ba..yanxu ya amaryar taka”…Dan tabe baki Taheer yai snn yace”sun tafi porthacourt”… Yusuf ya zaro idanu yace”ban gane ta tafi porthacourt ba..don’t tell me iyayenta sun kwace kayarsu ne”…wani dogon tsaki Taheer ya sake yi snn yace”Kai matsalana dakai watarn bakada hankali Yusuf…like how on Earth zakamayi wnn tunanin”… Yusuf ya daga hannaye yace”easy doctor…bani fa na kar zomon ba…naji kace ta tafi porthacourt ne so ban gane me kke nufi ba”…Taheer ya sauke ajiyar zuciya snn yace”ummi ce wlh..kasan har yanxu bata bada consent dinta a auren ba..shine kawai ta hada Mata kaya wai su tafi da ita sai tace a dawo da ita zata dawo”… Taheer ya danyi shiru for some secs snn yace”do you know the worst part of al’amarin nn?…Yusuf na girgiza Kai yace”No”…Taheer yace”wai uncle cewa yai bazasu bani ita ta tare gidana ba har sai lokacinda ta kammala karatu..kaji wani mgn fa don Allah Yusuf.. medicine fa take Shirin karanta..for how many years sukeso inyita zama Ina jiranta tsakani da Allah…kawai don sunga Ina sonta shine suketa bani wahala haka”…

Yusuf da mgnr Taheer din ya bashi abu biyu..wato tausayi da Kuma dariya..sai ya zabi yai dariyarsa kawai don bazai iya rikewa ba…Taheer yai shiru yana kallon yanda ya dage Yana mai dariya..ranshi ba karamin baci yai ba… there’s no point in talking to wnn Dan iskan wlh… Yusuf ya tsaida dariyar snn yace”like yanxu knn da Kai da tuzuru Wanda bashida aure matsayinku daya knn..gsky su ummi basu kyauta maka ba..just when kake shirye shiryen angoncewa zasu yanke ma danyen hukunci irin haka”sai ya sake fashewa da dariya…Saida yai me isarsa snn ya sake cewa”Ni har na fara lissafin nan da 9 month ku haifo mana junior doctor ko junior baby ashe haukan banza na nakeyi ma”…Taheer bai tanka shi ba..ya shiga duba files din dake gabanshi… Yusuf don kanshi ya gama snn yace”gsky am not happy da wnn hukuncin nasu ummi..like suna son suce maka kayita jira har nanda 6 or 7 years nan gaba..inaaa..gsky da sake..haka sukeso kayita zama kana Kara tuzurewa a gida..no..ya kamata mu samu solution..ga shawara zan baka”…ba tareda Taheer ya dago ya kalleshi ba yace”inajinka”… Yusuf hadda gyara zama snn yace”kawai idan sun dawo da ita nan din ka tubure musu…ka nuna kaifa kana bukatar Matarka a kusa dakai.. don haka kosu baka ita..ko Kuma suga danyen aiki”…wani wawan tsaki Taheer ya saki tareda mikewa ya shige bathroom…baiga amfanin mgn da Yusuf ba wlh..gaba daya ya sake lalata mai zuciya…wani wai ya tubure idan basu bashi itaba suga danyen aiki…shi duk ba wnn ne a gabanshi ba yanxu…yanaso ya fara yaki da tsoro da Kuma kiyayyar da yaga suna kokarin rabashi da babynshi…then ya dawo kan ummi itama yayi duk abinda zai iya don ta sauko ta dena fushi dashi…daga nn Kuma yasan karban matarshi zaifi zuwa da sauki don idan ummi ta amince tanayima uncle dinshi mgn yasan zai amince…Allah ya bashi ikon accomplishing wnn plan din nashi🙏🏻(Ameen daddy😥)

Bayan Sati biyu…

Tsakanin ummi da Taheer dai zaace babu abinda ya sauya…har yanxu gaisuwa kadai ke hadashi da ita..shima Kuma da kyar take amsawa…ya zamana Taheer ba inda yake samun sauki sai a wurin ummah…gaba daya zaman gidan bai mishi dadi..at times sai Yana zaune sai yaga kmr Layla ta fito daga dakinta…cikin sati biyun nn Kuma ko waya bai samu yayi da ita ba..yasan ko ya kirata she won’t pick so baima taba attempting Kiran nata ba..

Yau dai ya kudiri niyyan bazai kwanta ba sai yaji muryanta…sai ya mike zuwa dakin ummah…bai ganta a dakinba..yasan kuma bazata wuce bathroom ba..don haka ya nemi wuri ya zauna…umma na fitowa ta ganshi zaune…ta karasa itama ta zauna tana kallonshi tace”yaushe ka dawo”…a hankali yace”yanxun nn umma…umma pls inaso ki Kira baby ne a wayarki..sai kisa a speaker kuyi mgn inaso ne kawai inji muryanta”…cikeda tausayinshi umma tace”nasan wnn abun ka Sanya a rai yaketa damunka Taheer…wato bazaka saukakama kanka ba koh”…da sauri Taheer yace”ba haka bane ummah…a hakan ma am really trying…umma kinsan dai tun da nake da baby bata taba tafiyan sati ta bar gidan nn ba..and ban taba spending two whole days without seeing her ko without talking to her ba…amma yanxu gashi nayi…yau satina biyu umma ko voice dinta banji ba..and hakan na damuna umma..zuwa yanxu Kuma hakuri na ya kare..kiramin ita kawai zakiyi inajin voice dinta shknn”…umma da tayi zuru tana sauraron shi ta girgiza Kai kawai snn ta dakko wayarta…zuwa yanxu har ta gaji da rarrashin Taheer…ta gaji da bashi baki kan yayi hakuri…she’s now out of words so batasan me zata fada mai ba…don haka kawai sai tayi dialing number din Nafisa tareda sawa a speaker kmr yanda yace…tana shiga tayi picking…bayan sun gaisa umma tace”idan Layla na kusa bata muyi mgn”…Nafisa tace toh snn ta mikama Layla wayar tace”ga umma zakuyi mgn”…Layla ta taso daga inda ta amsa wayan ta Kara a kunne…a nutse tace”umma Ina yini”…umma dake kallon Taheer tanason ganin reaction dinshi tace”lfy Lou Layla…ya porthacourt din”…Layla tace”akwai dadi wlh umma…sai naji kmr kar in dawo Abuja”…daramm Taheer yaji kirjinshi ya buga jin abinda ta fada…umma tace”bakida  hankali ai dole kice haka dama”…Layla ta Dan shagwabe murya tace”umma banida hankali kuma”Taheer Saida yasa hannu ya dafa bango don jiri yaji kmr zai daukeshi…he missed her like crazy and bai tabbatar da yayi missing din nataba sai da yakejin muryanta yanzun…he really missed shagwaban nn nata..he missed every single thing about her…umma dake kallonshi kafin tayi mgn Layla tace”umma ya kowa da kowa”…umma tace”duk kowa lfy Lou…baki tambayi daddynki ba”…diff Layla tayi kmr bataji me ta fada ba…Taheer dai yai shiru shima Yana sauraron su…umma tace”ba mgn nayi maki bane Layla kikai min shiru”…a daya bangaren Layla tace”umma ni bansan me zance ba ai”…tun kafin ta rufe baki umma tace”zanci mutunchinki wlh..Taheer din kikema wnn iskancin Layla..wato kin manta duk…bata karasaba Taheer ya mike da sauri ya kwace wayar daga hanunta…yai hanging call din yana kokarin dora murmushi kan fuskanshi yace”umma Mana…ya zakiyi mata fada Kuma…kinga yanxu am happy naji voice dinta idan kikace Zaki Mata fada Kuma spoiling mood din nawa zakiyi ai”…ganin yanda umman tayi shiru tana kallonshi sai ya riko hanunta yace”umma why the blank look?…nidai ko nan gaba don Allah kar kice zakiyi Mata fada a kaina ummah…bazanji dadi ba..Kuma tanada right din jin haushina umma ai kinga ban kyauta Mata ba…so plss kiyi hakuri”…umma kallonshi kawai take totally speechless…cikin ranta tana girmama soyayyan da Taheer ke Mata..tayi imanin ba namijin da zaiso Layla kmr yanda Taheer din ke sonta…ganin ba mgn umma zatayi ba sai kawai ya mike yana fadin”umma Saida safe”…still dai bata iya cewa komai ba ta shiga binshi da kallo har ya fita daga dakin.Porthacourt…

+

farkon zuwansu Layla ba wani sakewa tayi a gidan ba…don ba wai tana zuwa sosae bane tinda su suna yawan zuwa Abuja…ga Kuma batun ta da Taheer da har yanxu take fatan wataran a tasheta ace mafarki tayi…amma daga baya ganin yanda duk suke kula da ita..kowa naji da ita…Mami..Abba..da siblings din nata..sai ta ware…ta shiga sabgoginta kmr ba abunda ya faru..dukda mgnr na nn cikin ranta but  ta dena bari ya dameta yanxu.

Idan tace bata missing Taheer kam tayi karya…she is really missing him and taki tayi admitting tana missing din nashi…tunda suke dashi bata taba tafiyan sati ba…snn ko ita tayi tafiyan ko shi yayi..always suna kan waya dashi..Amma yanxu 2 whole weeks ko massage babu daga gareshi…duk yanda suke nan nan da ita..gani take ba wani kulawa suke bata sosae ba…duk ba Wanda ya iya kula da ita kmr daddynta…shi kadai ne ya iya kula da ita sosae…duk dare haka zatazo ta samu Nafisa tace”Mami don Allah kimin addu’a zanyi bacci”..and Nafisa will be like”ke adduan ne baki iya da kanki ba dole sai anyi maki…ko kannenki ba Wanda bai iyama kanshi addu’a ba sai ke…tsabar sangarta”…Layla saidai ta turo baki kawai…ita ba haka daddy yake Mata ba..

Yau ma sun dawo daga outing gaba dayansu…kmr yanda suka saba duk weekend idan abbansu na gida…to zaice duk su shirya zasu fita yawo…yau ma tun safe suka fita sai yanxu suke dawowa.

Da dare bayan sun gama dinner Layla ta samu abbansu a parlor tace”Abba ni inaso in dawo nan da zama gaba daya…don Allah ka Kira ummi kawai kace mata ba sai na koma Abuja ba zanci gaba da zamana a nan”…abban nasu na kallonta da mamaki yace”meyasa kikace haka Layla…meyasa bakison zama dasu yanxu”…Layla ta turo baki tace”Abba ni kawai banason komawa ne”…abban yace”bazai yiwu ba..karatunki Kuma ya zaai dashi”..da sauri tace”Abba to ba sai a nema min wani school din in farayi a nn ba..ai bamu riga mun fara lectures ba dama”… strictly yace”kar in sakeji kinyi wnn mgr Layla…ko da da bakida aure bamu da ikon da zamu dakko ki muce ki dawo nan da zama…bare Kuma yanxu da kike matar aure..wnn ba hurumin mu bane”…Layla har ta fara hawaye tace”Abba to ba kune kuka haifeni b…bata karasa ba Nafisa dake zaune kusada minjin nata tana kallonsu ta make Mata bakin…tana Mata mugun kallo tace”kika sake cewa mune Muka haifeki sai naci ubanki wlh..wato duk mgnr da nake fada maki bakiji koh…Taheer din da babu abinda baiyi mikiba a rayuwa shi kikema wnn Wulakancin…sbd kinga Yana sonki koh”…Layla da har ta fara hawaye tace”Mami wai ya zaayi ace daddy ne zai aureni..wlh Mami ni ban tabamai kallon komai ba face mahaifi..ya zaai ace inyi zaman aure dashi bayan ni ba kallon haka nake mai ba”…Nafisa zatai mgn abbansu yace”kyaleta…tashi kije Layla kar Kuma in sakejin wnn mgnr a bakinki”…Layla bata sake mgn ba ta mike tareda barin parlon…Saida ta fita ya dubi Nafisa snn yace”bai zama lallai ta fahimci abunda kike nufi ba yanxu tunda ranta a bace yake..ki ringa binta a hankali kina Mata nasiha.. InshaAllah zata hakura..amma a yanxu tana bukatar space”…ajiyar zuciya kawai Nafisa ta sauke..tana tausayawa Dan uwantane sosae.

Abuja..

Tun da Taheer yazo office yau bai samu hutawa ba…kasancewar Monday ne so sunada lots of patients…yana zaune akai knocking office dinshi…a hankali yace”come in”…Sameera ta turo kofan ta shigo idonta a kanshi…Taheer na kallonta da mamaki yace”Sameera..meya kawoki office dina Kuma”… Sameera ta nemi wuri ta zauna tareda ajiye bag dinta kan table dake gabanshi tace”saboda Ina sonka doctor…bazan iya hakura da Kai ba wlh..Ina sonka har yanxu”…mamaki sosae ya sake kama Taheer still idonshi a kanta yace”amma na fada maki na riga nayi aure Sameera…bazan iya sake wani auren ba shiyasa ma nace na fasa aurenki”..yana rufe baki Sameera tace”meyasa bazaka iya Kara auren ba doctor..Haram ne idan ka auri Mata biyu”…Taheer ya dafe goshi..bai San ya zaiyi Mata bayani ta fahimta ba…ta sake cewa”mgn nakeyi fa doctor”…ya dago yana kallonta yace”sbd bazan iya adalci tsakininki da itaba shiyasa…koda na aureki Sameera bazakiji dadin zama dani ba tunda zuciyata ita takeso bake ba”…Sameera taji wani kishi ya lullubeta..idonta har sun ciko hawaye tace”wacece ita doctor..wace macen da kakeyima irin wnn so haka..me tafini dashi da bazaka iya daidaita soyayyata da tata ba”…Taheer ya runtse ido yanajin yanda tausayinta ke ratsashi..bazai ce yasan me takeji game dashi ba but yasan me akeji idan kanason mutum shi Kuma wnn mutumin baya sonka…Sameera ta taso daga inda take tareda durkusawa nan gabanshi…tana hawaye tace”na rokeka da girman Allah ka taimaka ka aureni doctor..can’t you understand..I love you with all my heart”…da sauri Taheer ya mike itama ya kamata ya mikar da ita tsaye…idanunshi cikin nata yace”don Allah Sameera kiyi hakuri..mgnr so tsakanina dake a barta..kona aureki Sameera bazaki tabajin dadin zama Dani ba..kiyi hakuri idan mgnr Dana fada ya bata maki rai..akwai maza da yawa a duniya Sameera..Zaki iya auran duk Wanda kike so Amma Ni”…ya shiga girgiza Kai snn yace”kiyi hakuri kawai..I can’t”…Sameera ta share tears dinta snn ta dauki bag dinta tana kallonshi tace”shknn doctor..na gode sosae”…bata jira jin abinda zai fadaba ta fice a office din tareda banging kofar…cikin ranta ta kudira koma wacece yakeso haka..bazata bari su zauna lfy ba..yanda yace bazai iya auranta ba to duk duniya babu macen da ta isa ta zauna dashi…dole tayi bincike ta tabbatar da matar daya aura din..zasu gane shayi ma ruwa ne.

STORY CONTINUES BELOW

Shi Kuma Taheer da kyar ya koma ya zauna bayan fitarta daga office din…ba karamin tausayi ta bashi ba…ta zubar da duk wani qima da ego irin nasu na Mata..ta durkusa har kasa tana rokonshi ya aureta..yasan ba karamin so take mai ba amma shi ko kadan bai tabajin yana sonta ba…bama itaba shi duk duniya mace daya yakeso itace Layla and baya tunanin zai qara son wata macen a duniya bayan ita…wnn tunanin dashi ya karasa yini..har ya koma gida bai bar jinjina al’amarin ba.

Da dare ya shigo dakin umma don ta Kira Layla suyi mgn shi Kuma yaji muryanta as Always…umma na dariya tace”yaufa bazan Kira maka itaba Taheer..ka kirata da kanka mana ka gani idan batai picking dinba sai in kirata”…ya rausaya Kai yace”umma nasan ba dagawa zatayi ba wlh…nidai kawai ki kirata ai ba mgn zanyi sa itaba muryanta kadai nake so naji”…umma ta girgiza Kai tace”Allah bazan kirata ba Taheer..ka dauki wayarta ka Kira nace..idan taki dagawa sai in kirata”…bai sake cewa komai ba jin ta riga ta rantse..don haka ya zaro wayarshi a aljihu tareda lalubo contact dinta..ya zubama wayar ido kawai Yana kallo zuciyarshi na bugawa…umma ta fizge wayan daga hanunshi tayi dialing number din daya zubama idanu…yanajin Kiran ya shiga ya runtse idanu Yana karanto duk addu’ar dayazo bakinshi…bai san yaushe ya farajin tsoron Layla ba wlh…har ta gama ringing baa dagaba…umma ta sake dialing a karo na biyu…har yanxu Taheer bai bude idonshi ba..kmr daga sama yaji tayi picking tareda cewa”hello”…ya bude idon da sauri…umma ta Mika mai wayar tana murmushi…ya rike wayar hanu bibbiyu Yana sauke ajiyar zuciya…a daya bangaren Layla ta dan turo baki jin baayi mgn ba ta sake cewa”hello”…yana stammering yace”he..hel..lo ba..by”..tace”Ina yini”…Taheer ya lumshe ido ya bude..yanajin wani extraordinary farin ciki na lullubeshi…wnn ma kadai is a progress…a hankali yace”lfy Lou baby..how are you”…a hankali itama tace”am fine”…sai sukai shiru kowa Yana jiran Dan uwanshi yayi mgn…Taheer da murna ta cikashi yace”dama I just called to say hii..good night”…ta amsa da”toh”snn ta katse Kiran…Taheer yabi wayar da kallo snn ya kalli umma Yana murmushi yace”am happy she picked my call…umma do you think tayi accepting Dina knn”…umma ta kamo hannayenshi tace”InshaAllah son…kaidai kaci gaba da addu’a kaji koh”…ya daga Mata Kai Yana murmushi…he’s super happy Layla batayi ignoring call dinshi ba…dukda ba wani long hira sukai ba sai yaji he’s ok…idan abubuwa zasu cigaba da tafiya haka then he have nothing to worry about…yasan in Allah ya yadda with time zata soshi.

Yau tun safe Ramla tazo gidan…yarinyarta tayi girma sosae…suna zaune parlor gaba dayansu umma na duban ummi tace”Yaya mgnr tafiyata fa wnn satin ne”…da sauri ummi tace”yanzu Aisha bamu gama da mgnr nn ba dama…tun yaushe nake binki kan kiyi hakuri da Kanon nn kici gaba da zamanki nn amma kinki…idan kin koma Kanon ma me zakiyi”…umma tayi yar dariya snn tace”babu abinda zanyi Yaya..kawai gani nai tunda ba bikin ai ya kamata in koma..ko dazu da mukai mgn da Sadiq tambaya na yake ko na koma”..(note:Sadiq shine second son din umma..shi yakebin Nafisa and yana abroad shida wife dinshi da da daya)…ummi ta shiga girgiza Kai tace”don girman Allah Aisha mgnr nn a barta kawai…ke ba miji ba..ke ba ‘ya’ya ba..haka nn ki dage sai kin koma kano…dagani sai ke fa iyayenmu suka Haifa..ko don wnn bai kamata kiyi hakuri muyi zaman mu tareba..shima Kuma Sadiq din sai naci ubanshi wlh..kan meye zai wani ringa damunki ki koma kano shida baya ma qasar gaba daya”…ummi na rufe baki  Ramla tace”Dan Allah umma kawai kiyi hakuri kici gaba da zamanki a nn…Ni kainda Banga abinda kikeyi idan kin koma Kanon ba”…Taheer ma da shigowanshi knn yaji suna mgnr yace”gsky suka fada umma..mudai munfiso kicigaba da zamanki a nn plss”…da sauri ummi tace”to ai yanxu sai ki hakura tunda ‘ya’yanki sun sa baki”…Ramla na dariya tace”ummi mu ba ‘ya’yanki bane knn”…ummi tadan harareta snn tace”ga dai uwarku nan a zaune…ni tawa ‘yar tana porthacourt”…dariya kawai sukayi gaba dayansu…umma tace”to shknn..Allah sa hakan shi yafi alkhairi”…Taheer ya mike ya karasa kusada umma tareda manna mata peck a right cheek dinta snn yace”you shall live long ummatah”… murmushi kawai umma tayi tana girgiza Kai…ummi ta danja tsaki tareda kauda Kai gefe…a hankali ya matsa kusa da ita…ba zato ba tsammani kawai taji ya manna Mata peck din itama a left cheek…yana gamawa ya fice daga parlon gaba daya…ummi data saki baki tana bin bayanshi da kallo sai ta girgiza Kai kawai tareda kallon umma tace”ki gaya masa duk ya kuskura ya shigo hanuna bazaiji da dadi ba wlh..aini ba abokiyar wasanshi bace..ko don yaga nayi shiru kwana biyu yana tunanin na manta da abubuwan daya aikata ne…zai dawo har gidan nn ya sameni”… murmushi kawai umma tayi bata dai ce komai ba.

Da dare bayan Ramla ta tafi..Taheer yaje ya lallabo umma wai suje ta fadama ummi ya kamata Layla ta dawo sbd sun fara registration…tana kokarin barin parlon sai gasu sun shigo…bayan sun zauna umma tace”Yaya wai yaushe Layla zata dawo ne…Ashe har sun fara registration a makaranta”…ummi ta kalleta snn ta kalli Taheer da kanshi ke sunkuye kmr Wanda ke gaban sirika tace”Dan nakine ya turoki knn”…umma tace”to tsoron fada maki yake Yaya..duk kin mai dashi kmr stranger a gidan nn”…Saida ummi ta maida idonta ga tv dake aiki snn tace”ko ma me nayi masa ai shiya siya da kudinsa..kuma muddin yarinyar nn bata amince ba ki gaya masa dole sai ya saketa wlh”…umma ta dan kalli Taheer snn tayi murmushi tace”naji yaya in Allah ya yadda zan fada mai..yanxu yaushe Laylan zata dawo”…ummi ta kalli Taheer fuskarta a daure snn tace”yaushe aka fara registration din”…batareda ya dago kan nashi ba yace”yau kwana Hudu knn”…a takaice ta sake cewa”yaushe ne closing date”…shima a takaicen yace”this month end…on 25″…ummi ta mike tareda kama hanyar dakinta snn tace”zuwa month end din sai ta dawo kafin ayi closing”…a tare umma da Taheer suka hada ido snn suka bita da kallo har ta shiga dakinta…Taheer ya wani rausaya kai yace”umma kiji me take fada don Allah…ya kamata ta dawo da wuri…bamusan time din da zaiyi taking dinta kafin ta gama komai ba”…umma ta sauke ajiyar zuciya snn tace”kar ka damu…zan sakeyin mgn da ita.. InshaAllah ko zuwa next week ne sai ta dawo”…Saida ya mike snn yace”to umma Saida safe”…ta mike itama tana fadin”Allah ya tashemu lfy”..daga haka ta shige daki ta kwanta…shima ya wuce part dinshi.

Washegari da safe ummi ta Kira Nafisa a waya..bayan sun gaisa tace”kinaji Nafee…inaso ku bincika idan zaa samu available flight Layla ta dawo cikin satin nn…Ashe har sun fara registration a makaranta”…Nafisa da ba karamin dadin mgnr ummi taji ba tace”to zaa bincika InshaAllah ummi..duk yadda akai zan Kira sai in fada miki”…ummi tace”to shknn..ki gaida yaran gaba daya”…Nafisa ta amsada”zasuji”snn sukai sallama…tana ajiye wayan ta saki wani ajiyar zuciya..Allah ya sani dama tafi son Layla ta koma can…ko ba komai idan Taheer din na ganinta zai Dan samu sauki..snn ita kanta Laylan saita fi accepting dinshi tunda suna tare…matsalarta daya shine yanda Layla bata iya komai ba daya shafi harkan gida…banda gyaran daki babu abinda zatace Layla tayishi ba tareda anyi Mata gyara ba…ko kirgi nn kusan kullum cikin nuna Mata take sbd batason a kaita gidan miji haka..amma kullum da kuka take barin kitchen din..gaba daya Taheer ya gama sangarta ta..babu abinda yake Bari a koya Mata tun tuni…ta mike zuwa dakinda Laylan take don tasan tanacan tana aikin bacci ko kallo..dole ta fito su shiga kitchen din yanxu..Kuma ko kukan jini zatai yau sai tayi musu stew a gidan nn(lallai zakuga stew kuwa😆)

Daidai wnn lokacin Taheer na office…haka nan yaji yana son ganinta yanzu…ya dauka wayarshi dake kan table tareda kunna data hoping ya samu Nafisa online sai suyi video call…luckily Kuma ya sameta online din…aiko ba bata lokaci ya kirata video call…lokacin suna kitchen tareda Layla daketa faman tsalle wai kar miya ya digan mata a hannu…tana ganin shi yake kira ta dauki wayan tareda komawa parlor…Saida ta zauna snn tayi picking call din…tana mai murmushi tace”barka da safiya yallabai”…Taheer ya Dan shafa kanshi snn yace”barkda dai..ya gida ya yara”…Nafisa ta Dan wara ido tace”ya yara zakace ko Kuma ya baby”…Saida ya koma ya jingina jikin kujeran da yake Kai snn yace”nidai ya yara kikaji nace”..tace”to yara duk suna nn lfy..sun tafi school…ita Kuma babyn gata can a kitchen”…Taheer ya zare ido tareda mikewa zaune yace”kitchen Kuma..me takeyi a kitchen”… Nafisa ta danyi dariya ganin yanda ya wani zaro idanu snn tace”aiki Mana bro…zan zauna Ina kallonta ne inyita aiki ni kadai Kuma in gama in bata taci..no..it’s not possible”Taheer dake kallonta da mamaki yace”meyasa Zaki wani turata kitchen sbd Allah..ba girki fa ta sabayi ba konewa kawai zatayi a banza a wofi..don Allah ki kirata ta fito kije ki karasa girkinki da kanki”…kafin Nafisa tayi mgn Layla ta kwala wani uban ihu daga kitchen din…lokaci daya Taheer ya rikice yace”you see..na fada maki ba saba yin girki tayi ba…jeki duba meya sameta”…Nafisa na murmushi ta mike zuwa kitchen din…dariya yake bata wlh…tana shiga ta iske Layla dake tsaye tana zubda hawaye…ta karasa kusada ita tana dubanta snn tace”lafiya kika cika ma mutane gida da ihu haka”…Layla dake kuka kmr Wanda akama dukan tsiya ta shiga nuna Mata finger dinta tace”kingani mai ne ya zubomin a hannu na”…Nafisa taja tsaki ta ajiye wayar kan cabinet snn ta karasa ta kashe gas dinta…tana kallon Layla fuska a tsuke tace”zanyi maganinki ne”…Layla ta sunkuyar da Kai tana hawaye… Nafisa ta karasa tareda daukan wayanta..tana kokarin fita daga kitchen din Taheer da duk yaji abunda suke fada yace”meyasa zakiyi Mata fada plss…tace maki ta kone ko hanun nata baki dubaba kina kokarin tafiya ki barta Kuma”…mamaki sosae ya sake kama Nafisa… Laylan sai kace wata karamar yarinya…kafin tayi mgn ya sake cewa”bata wayan muyi mgn”…Nafisa ta mikama Layla wayar kawai snn ta fita daga kitchen din…Layla ta janyo stool ta zauna tareda share hawayenta snn ta kalli screen din..lokaci daya Kuma tayi kasa da kanta tace”daddy Ina yini”…Taheer dake aikin kallonta ya koma ya zauna..yanajin farin ciki na lullubeshi kafin yace”muga wurin da kika kone din”…ba musu ta dago dan yatsan tana nuna mai…ya girgiza kai ya sake cewa”sorry kinji…nayi Mata mgn bazata kara cewa ki shiga kitchen kiyi Mata aiki ba”…yana rufe baki Layla tace”na kusa barin gidan ma”…ya Dan bude ido yace”Ina zakije”…”Abuja”..ta fada a hankali…Taheer ya sake bude idon nashi da kyau snn yace”u mean kin kusa dawowa gida knn”…ta daga mai kai a hankali…ya saki wani murmushi yana shafa gemu kafin yace”alright kai Mata wayan zamuyi mgn”…da sauri ta mike zata fita daga kitchen din taji a hankali yace”I can’t wait to see you”…ta sake yin kasa da kanta ba tareda cewa komai ba ta fita daga kitchen din…ta samu Nafisa a parlor ta Mika Mata wayan snn ta bar wurin…Nafisa na amsan wayan yace”da gaske baby ta kusa dawowa gida”…Nafisa na daga Kai tace”eh mana..ummi bata fada maka ba”…daga kan shima yayi yana fadin”she never told me”…tace”aikam dai da an samu available flight zata taho..zuwa gobe ko jibi”…yai murmushi yana cewa”thank God she’s leaving..bazaki barni da fargaban kina can kina turata kitchen kina sa tana konewa ba”…Saida ta girgiza kai snn tace”wai don Allah idan Layla bata koyi wnn abubuwan yanxu ba sai yaushe kke so ta koya..kafi son ayita biye Mata duk abinda takeso shi zaayi Mata knn”…tana rufe baki yace”eh nafison ayita biye matan..babu ruwanku”… murmushi kawai Nafisa ta saki tana mamakin wnn al’amari…ace mace bazaa koya Mata girki ba idan sunje gidan nasu zata ha idan shi zai hakura da aikin ya ringa yanayi musu girkin a gida..sai yanzu ma take tunanin wani irin zama zaai duk randa akace ta tare gidanshi ai abubuwanta Kara lalacewa zasuyi…wnn sangartawa har Ina.+

Taheer na ajiye waya bayan sunyi sallama da Nafee ya shiga murmusawa shi kadai..he’s super happy baby ta kusa dawowa gida..Allah sa a samu available flight din gobe kawai ta biyo ta taho..he can’t wait to see her..he missed her like crazy.

Bayan kwana biyu…

Tun safe Taheer ya gama shiri don zuwa dauko Layla a airport…ko aiki yace bai zuwa yau..zai zauna a gida kawai yayita kallonta…duk saiya fanshe kwanakin da tayi ba tare dashi ba..

Ya mike daga dinnig bayan ya gama  breakfast..ko abincin kirki baici ba sbd he’s eager yaje ya ganta…ya kalli wirst watch dake hanunshi yaga it’s 10:30…yai deciding gara yaje ya jirata a can kawai tunda by 12 flight dinsu zaiyi landing…sukaci karo da umma a parlor tana kallonshi with smile tace”wnn kwalliyan Taheer duk na Laylan ne haka”… murmushi kawai yai tareda shafa kanshi baice komai ba…Saida umma ta nemi wuri ta zauna snn tace”ba dai tun yanxu zaka tafi airport din ba”…Taheer yace”yanzu zan tafi mana umma..i can’t wait to see her you know..gra inje in jirata a can”…umma tai murmushi tana gyada kai tace”to a dawo lfy son”…Yana murmushin shima yace”Ameen Umma..na tafi”…har ya juya za fita ummi da fitowanta knn taji conversation din nasu tace”Kai tsaya”..ba musu Taheer ya dakatar da tafiyar da yakeyi tareda juyowa gareta…tana binshi da kallon from head to toe tace”where do u think you are going”…a takaice yace daita”airport”…sai ta shiga girgiza kai tana fadin”kar ka soma..yaushe kaji nace kaje ka daukota..na riga na tura driver yana can yana jiranta..sbd haka kar ka kuskura ka daukota a motarka kaji na fada maka”…da mamaki sosae Taheer ke bin ummi da kallo..wnn wane irin Abu ne for God sake matarshi ta sunna ummi ke cewa bazaije daukota ba sai kace guduwa zaiyi da ita…ba tareda yace komai ba yasa kanshi kawai ya fice daga parlon..ranshi ba karamin baci yai ba wlh..like how on earth ma ummi zata wani tura driver yai picking matarshi bayan he’s around…Kai tsaye Inda motarshi ya karasa..ya shiga tareda yi Mata key ya fita daga gidan…ya dauki hanyan airport direct..idan tasan wata ai bata San wataba..

STORY CONTINUES BELOW

In few minutes time ya isa airport..ya samu driver din da ummi ta tura yana jiranta a can shima…Kai tsaye ya isa inda yake..drivern ya fito daga mota da sauri yana cewa”sannu da zuwa yallabai”…Taheer yai Dan murmushi yace”yawwa sannu Manu..don Allah inaso ne ka biyoni a baya..zan dauketa in yaso da mun kusa zuwa gida sai ka karasa da ita ciki..snn kar ka sanar da hajiya cewa bakai kayi picking dinta ba”…Manu na gyada kai yace”InshaAllah yallabai”…Taheer ya zaro kudi a aljihu ya Mika mai snn ya koma inda motarshi ya bude ya shiga ciki.

Yana nan zaune jirginsu ya sauka…ya bude mota sauri ya fita yanata baza ido yaga ta inda zata bullo… passengers na fara fitowa yai tozali da ita..tana sanye cikin abaya sky blue…tayi veiling da mayafin rigan shima sky blue…side bag dinta rataye a right shoulder dinta..sai dayan hanun kuma janye da trolley…wani irin kyau na musamman yaga ta karayi masa…baisan lokacinda ya sauke nannauyan ajiyar zuciya ba..sai Kuma ya fara murmushi shi kadai kmr mara hankali…kasa hakura yai ta karaso inda yake..don gani yake kmr ba tafiya takeyi ba…ya nufi inda take da sauri idanunshi kyam a kanta…ita kuwa Layla bata lura dashi ba..tanadai ta dube duben inda zata ga motar gidansu…kmr daga sama taji anyi mata wata kyakykyawar runguma…ta bude idanunta sosae..ko baa fadaba tasan it’s him…sbd a jikinshi kadai takejin kamshin perfume din nn…ta lumshe ido tai lamo a jikinshi don ita kanta bata Isa tace batai missing dinshi ba…ta daga hanu zatai hugging dinshi back..sai Kuma tamaida hannayen ta ajiyesu kasa..kmr dai Wanda ta tuno da wani abun…Taheer kam yana jinta a jikinshi yaji duk wani damuwa da kunci daya shiga tsahon kwanaki sun yaye..gaba daya suka tsere suka barshi da tsananin shauki da kuma begenta…gaba daya ya manta da inda suke burinshi kawai taci gaba da kasancewa a jikinshi har Allah ya dauki rayuwarshi…gaba daya yayi nisan da ko tunanin zataji zafi baiyi ba..don ba karamin riko yai Mata ba…a hankali Layla ta shiga kokarin kwace jikinta a nashi don ji takeyi tamkar kasusuwan jikinta zasu karye..ba karamin force yai applying a hug din ba…daidai saitin kunnenshi tace”let go of me daddy plss..it hurts”…da sauri ya saketa yana kalle kallen wurin kmr dai Wanda baa cikin hayyacinshi yake ba ya dawo hayyacin nashi…ganin idanunta har sun dan canza ya kama hanunta a hankali yace”am sorry plss..kiyi hakuri”… murmushi kawai tayi snn ta gyda mai Kai…yasa hannu ya dauki trolley dinta dake gefe snn a hankali yace”muje”…ba musu ta bishi suka karasa inda motarshi ke ajiye..Saida ya bude back seat yasa kayan nata a ciki snn ya zagayo tareda bude Mata..ta taka a hankali ta shiga..shi Kuma ya rufe Mata kofar snn ya zaga shima ya shiga driver seat..yaima motar key suka tafi.

Saida suka kan titi snn ta Dan kalleshi ta gefen ido tace”Ina yini daddy”…ya juyo shima ya kalleta yana smiling yace”lfy Lou baby..how was the trip”…a hankali tace”it was fine”…ya jinjina kai kawai yana ci gaba da tukinshi…baya minti biyu bai kuyo ya kalleta ba..tayi mai kyau ne fiyeda tunanin mai karatu..on the other hand Kuma yanajin kishin yanda ta taho a haka tun daga porthacourt..ya sauke ajiyar zuciya..Allah kadai yasan adadin mazan da suka kalle mai ita…sai Kuma ya kauda wnn tunanin da sauri don baiso yayi spoiling mood din da yake ciki…

Saida sukazo gab da layinsu ya samu wuri yai parking motar…ta mirror ya duba yaga driver din yayi parking shima a bayansu…Layla dake mamakin dalilinda ya tsayar dasu a nn kmr zata tambayeshi sai Kuma ta fasa…Taheer ya zuba mata narkakkun idanunshi da suka koma red yasa hanu tareda kamo nata hannayen ya shiga murzasu a cikin nashi…yanata kokarin hada ido da ita amma taki bashi Daman hakan..sai ya saki dan gajeren murmushi murya can kasa kmr me yin rada yace”baby I missed you so much…nayi missing dinki kaman inyi hauka..am sorry for hugging you in public daxu..it’s just that I can’t control myself…am sorry plss…pardon my manners”…Layla da kanta ke kasa tanajin tamkar kasa ya tsage ta boye kanta ciki don kunya…ga wani irin bugu da kirjinta keyi kmr wadda tayi race…Saida ta tattaro nutsuwarta tana kakalo murmushi tace mai”it’s nothing daddy..bakayimin laifin komai ba”…idanun Taheer a kanta ya dan dage gira yace”Really”…ta daga mai ka da sauri tace”yea”… murmushi ya saki tareda ka hannayenta da har yanxu ke cikin nashi..yai manna musu peck snn ya sake Mata hanun yace”driver zai karasa dake gida..ni zan shigo daga baya..ummi batasan ni nayi picking dinki ba..so karki fada Mata plss”…tana daga Kai tace”I won’t”snn ta bude motar ta fita…fitowa yai shima ya dau kayanta ya maida waccan motar…da kanshi ya bude Mata back seat ta shiga..ya rufe motan..Saida yaga sun tafi snn ya sauke ajiyar zuciya tareda komawa tashi motar…wani irin farin ciki ya tsinci kanshi a ciki…he wish Yana zuwa gida kawai ummi tace”dauki Matarka ku tafi..ohh da baisan inda zaisa kanshi ba don dadi.

STORY CONTINUES BELOW

Layla suna karasawa gida ko kayanta bata tsaya dauka ba ta nufi cikin gidan da sauri…tana zuwa ta fada jikin ummi tana fadin”nayi missing dinki sosae ummi”…ummi ta janyeta a jikinta tana murmushi tace”nayi missing dinki sosae Nima”…peck Layla tayi Mata a forehead snn ta mike zuwa wurin umma tai hugging dinta itama snn tayi mata peck din tana fadin”duk nayi missing dinku wlh”…ummi na girgiza Kai tace”duk dabi’un Taheer ba wanda kika manta baki dauka ba..da ba haka kike da rungume rungume da yima mutane kiss ba wlh..duk shine ya bata ki da wnn abubuwan”… murmushi kawai Layla tayi batace komai ba…driver yai sallama parlon tareda shigo da kanta ciki…umma tace”sai a fito Mana da tsarabar mu mu gani”…Layla ta saki dariya tana cewa”Ni ba tsaraban da nayo fa umma..nida ko fita ma banayi”..ummi ta tare ido tace”kiji tsoron Allah Layla..Nafee tacemin duk weekend sai Awwal ya fita daku gaba daya..sbd tsinannen rowa shine zaki cemana wani wai ba fita kikeyi ba”…dariya kawai Layla tayi kafin ta dauki kayan nata tace”to Bari inje daki..yanxu zan fitoma kowa da nashi tsaraban”…tana gama fadan haka ta wuce dakinta da sauri..cikin ranta tunanin ya zama zai kasance take tsakaninta da Taheer…a yanda ta fahimta shifa da gaske son nata yakeyi…ita Kuma yanzu harga Allah bawai bata sonshi bane..kawai batasan yaushe Allah ya Dora Mata wani irin kunya da Kuma tsananin tsoronshi ba…har yanxu rungumar da yai Mata dazu ta kasa mancewa dashi..she don’t know why.

Taheer kuwa yawo ya shigayi kawai Yana zaga gari ba tareda yasan inda ya nufa ba..baison komawa gidan ne yanzu sbd ummi zata iya zargin wani abu…Saida ya shafe almost an hour yana gantali a titi daga wnn layin ya shiga can…daga karshe dai ya shiga wani store ya siya mata uban chocolates masu yawan gaske…dukda bai sonta da Shan chocolate din amma haka ya siya kmr ba gobe…baima San me ya kamata yayi don ya faranta mata rai ba…ana gama ma packaging ya dauka snn ya koma mota…Kai tsaye gida ya nufa don yasan zuwa yanxu dai ummi bazatayi tunanin komai ba.

Yana isa gidan bayan yayi parking ya fito daga motan..ya bar chocolates din nan cikin mota snn ya nufi cikin gidan…gaba dayansu suna dinning suna Shirin fara lunch ya shigo…ya karasa dinning din shima yaja kujeran dake next to umma ya zauna snn ya karyar da murya Yana kallon umma yace”serve me pls”…umma na murmushi ta mike tai serving dinshi snn ta koma ta zauna… Taheer ya shiga cin abincinshi hankali kwance..yanayi Yana Satan kallon Layla..ita kuwa Yana zuwa wurin taji gabanta ya Fadi…haka nan taji wani kunya ya lullubeta..tama kasa cin abincin dake gabanta..batasan wane irin al’amari bane wnn bayan da ba haka take ba…ta ajiye spoon dake hanunta a hankali snn ta mike zata bar wurin…umma na kallonta tace”Ina Kuma zakije”…tace”umma daki zan koma..na koshi”…kafin umma ta sake mgn ummi tace”yi tafiyarki kinji..idan ma baki koshi ba zan kawo maki daki sai ki karasa ci”… Layla namurnushi tace”yawwa my ummi”snn tabar dinning din da sauri…Taheer shima duk sai yaji abincin ya fice daga ranshi…ko baa fada ba yasan sbd shi tabar wurin..to meyasa..badai yarinyar nan tsoronshi ta faraji ba Kuma..no ko zaiyi tolerating komai bayajin zai iya tolerating wnn gudun da takeyi sbd shi..don Allah ya sani cutar dashi zatayi…a haka dai har suka gama cin abincin yanata tunane tunane…suka koma parlor suka zazzauna..still Taheer yaki tafiya don yana tunanin zata fito ya ganta amma shiru…har yaje sallahn asr ya dawo nan ma babuta ba alamarta… inshort haka Taheer yaita zaman parlor wai ko zata dito ya ganta amma har dare lokacin kwanciya bacci yayi bata fitoba..ranshi ba karamin baci yai ba…ya ringa Satan kallon kofar dakinta yasan dai ko giyar wake yasha bai isa ya doshi hanyar dakin bama don ummi saita tara mai jama’a…haka ba don yaso ba ya tafi part dinshi bayan duk sun tafi sun kwanta suma…ko cikin dare yanata tunanin ko zuwa zaiyi ya sameta yanxu tunda yasan kowa na bacci amma tsoron abunda zai biyo idan ummi tai ram dashi yasa baijeba…haka ya kwana wnn daren ranshi bace..zuciya cikeda tunani kala kala.

Washegari ma same thing happens…tun safe Taheer ke parlorn ummi amma ko keyarta bai ganiba…gaba daya ranshi ya gama baci…Sam bazai dauki wnn halin ba wlh..dole ya nema mafita..

2 nayi ya koma part dinshi don yin shrin tafiya aiki…har ya gama shrin ya fito ya sake komawa yai sallama dasu umma bai ganta tafito ba…ya wuce ya tafi clinic kawai..amma yasa a ranshi yau duk abunda zai faru sai dai ya faru..amma bazai kwanta bacci ba sai ya sanyata a idonshi..sai kuma ta fada mai dalilinda yasa take tserewa daga gareshi…gaba daya yinin yau cikin kunci yayishi har dare.

9pm ya baro clinic…bai karasa gidaba sai around 10…bayan yayi duk abubuwan daya saba before going to bed..sai yai zamanshi nan part din nashi yaki zuwa can..yasan ko yaje dinma ba ganinta zaiyi ba so it’s better yai zamanshi.

Saida ya tabbatar da kowa ya kwanta snn ya mike ya nufi part dinsu..lokacin 12 ya wuce…bai samu kowa parlor ba as he expected..gaba daya bulbs din parlon ma kashe suke…a hankali ya taka zuwa dakinta..ya bude kofar ya shiga…sai yaga ba kowa a ciki..baiyi mamaki ba ya juya ya fito don dama Saida yai tunanin hakan.

A hankali ya tura kofar dakin ummi ya shiga ciki…suna kwance su biyu a kan gadon…ummi na daga farko..ita Kuma Layla na ciki..yabar kofar a bude snn ya shiga tafiya Sadaf Sadaf har ya zagawa inda Laylan ke kwance..yasa hanu ya yaye duvet din data rufe har fuskanta dashi…sai ya saki murmushi ganin idonta nata motsi yasan ba bacci takeyi ba..ya sunkuyo saitin kunnenta murya can kasa yace”saura Kuma kimin ihu”…itadai Layla batace komai ba sai gabanta dake dukan tara tara…a hankali Taheer ya sunkuyo tareda daukanta cak ya rungume a jikinshi…snn ya fara tafiya a hankali har ya fita daga dakin Kai tsaye ya isa dakin Laylan ya bude kofar ya shiga ciki..ya ajiyeta gefen gado snn ya koma yai locking kofar hadda sa Mata key.

Me mutumin nn ke Shirin aikatawa ne🤔

Masoyan doctor yace yana gaisuwa..yana godia da supporting dinshi da kukeyi kan baby🤪

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page