KASHE FITILA CHAPTER 5 BY BATUUL MAMMAN

KASHE FITILA CHAPTER 5 BY BATUUL MAMMAN

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

Jin karar rufe gate din yasa hantar cikin Shuhada kadawa. Ba karamin tsorata tayi da ganin Anti Bebi ba har Awaisu ya gane. Ita kanta Anti Bebin taji tsoro kada Shuhada ta bata mata shiri. Karasawa tayi gabansu tana murmushi+

“Awaisu? Shuhada?? Me kuke yi a nan???”

Sunkuyar da kai Shuhada tayi tana fargabar kada ta gane me tayi niyar yi

“Anti ina tambayarsa mai jiki ne”

Kawar da kai yayi gefe yana tunanin akwai abin  da suke boye masa “ni zan shiga ciki, ku gaida gida”

“To sai gobe na sake turo ta sai tayi muku girki ko don yara tunda akwai makaranta” da jin muryarta ba haka taso ba. Niyarta suyi hira kamar yadda Wangesi yace idan Awaisu ya fara son Shuhada like mata zai rinka yi ko kaska albarka.

Ciki suka shiga tare suka yiwa Maamu sallama. Tana hada ido da Anti Bebi taji irin yadda taji dazu. Gani take ko me zata saka ta ko ta nema a wurinta da gudu zata yi domin faranta mata. A duniya bata ga ko ji wani da take son farantawa rai kamar Anti Bebi ba.

A asibiti kuwa Gimbi kwana tayi cikin kunci da bacin rai. Ace tun safe tana asibiti ko abinci ba a kawo ba balle wani ya kwana da ita. Ta tabbatar idan bata koma gidanta ba komai yana iya lalacewa reshe yazo ya juye da mujiya. Saukinta ma daya tasan Anti Bebi ba daga nan ba wurin mayar da mutane tamkar rakuma da akala idan taso juya su.

******

Asubar fari Shuhada ta tashi bayan tayi sallah tayi wanka ta shirya cikin wata shadda mara nauyi dinkin doguwar riga. Ta kwashi kusan minti shabiyar tana kwalliya. Da ta gama falo taje ta zauna tana danna waya. Wurin karfe takwas Alh Maitama ya fito tare da Anti Bebi tana ta kwarkwasa. Shuhada ta danne bacin ranta ta gaishesu.

Mamakin ganinta a haka da sassafe yasa Daddy tambayarta ina zata je. Murmushi tayi tana wasa da wayar hannunta taki bashi amsa. Ya sake maimaita tambayar ta saci kallon Anti Bebi sannan tayi magana can ciki muryarta bata fita sosai.

“Ka tambayi Anti”

Anti Bebi bata san lokacin da ta kwashe da dariyar murna ba ta rungume Shuhada

“Shege Wangesi na kan tudu. Kaddai jirana kike yi muje gidan Awaisu?”

Kai ta gyada a hankali tana murmushi.

Har wani rawar jiki Anti Bebi take yi ta kama hannunta ta rike

“Alhajina ‘yata tayi miji, kasan bazan taba zuba ido namiji ya wulakanta ta ba. Ba dai Tajuddeen ya sakota ba, yana ji yana gani haka zan aurar da ita ga wanda yasan darajarta. Bari naje nayi wanka kinji.”

Ko sallama bata karasa yiwa maigidan nata ba ta koma sama da sassarfa. Murna kuwa bata misaltuwa. Shi dai Alh Maitama maganganun sun kara daure masa kai amma kamar kullum yau ma bakinsa a kulle yake bai iya tsawaita tambaya ba yaji gidan ya gundure shi dole yayi gaba.

Sai da ya fita Shuhada ta sauke ajiyar zuciya. Yau Allah Ya bata ikon jin sunan bokan Anti Bebi. Idan da rabo a hankali zata gano komai na sihirin da sukeyi ita da Gimbi.

Tana wannan tunanin Anti Bebi ta sauko kamar ta cinyeta don farinciki suka tafi gidan Awaisu. Yau ma maganin jiya ta rike hannun Maamu duk ta shafe mata shi. Shuhada ta shige kitchen kamar gidanta ta dora girki yadda Anti Bebin ta umarceta. Lokacin da suka je dama yaran duka sun tafi makaranta.

Awaisu ya fito a makare yana daura agogo zai shiga dakin Maamu yaji motsi da sautin ruwa a kitchen din. Komawa yayi da sauri ya leka.

A tsaye Shuhada take gaban sink tana wanke nama ga wani kamshi da bai san ko na menene ba yana tasowa daga tukunyar da take kan gas cooker. Shagalta yayi da kallonta na dan lokaci kafin kuma ya dawo hayyacinsa ya daka mata tsawa.

STORY CONTINUES BELOW

“Me kike yi a nan? Yaushe kika shigo?”

Duk da ta jima da jikinta ya bata ana kallonta amma tsawar ta bata tsoro.

“Dama…uhmmm….uhm..da”

“Kinga bana son zancen banza kizo ki fitar min daga gida. Haka kawai don samun wuri ki shigo har kitchen kina girki a gidan mutane kamar wata matar gida”

“Awaisu me ya sameka kake yiwa bakuwata tsawa?”

Juyawa yayi yaga Maamu ta hade rai ga Anti Bebi a bayanta. Kafin ya bata amsa ta cigaba da magana.

“Tunda nazo gidanka Awaisu ranakun jindadina kadan ne kuma kaima ka sani. Mutanen nan gasu ‘yan uwan matarka amma halinsu daban yake. Tun da suka shigo yarinyar nan take kitchen ta dora ta sauke duk don ta faranta min “

Gudun bata mata rai yace  “to an gode mata Maamu amma ai ba a haka. Me zaisa ta shigo har kitchen batare da izini na ba?”

Maamu ta hade rai “to nuna min gidanka ne”

Anti Bebi ta shige ta kamo hannun Shuhada “bashi hakuri mu tafi gida. Da nasan taimakon zai zama haka da bamu zo ba. Awaisu banyi niyar hadaka da mahaifiyarka ba. Kuyi hakuri”

Maamu ta sha gabanta “kuna fita nima zan bi bayanku. Awaisu idan har ni na haifeka to na umarceka da auren yarinyar nan” ta nuna Shuhada.

Tsabar jin zancen kamar saukar guduma kasa magana yayi. Anti Bebi ta nuna tsantsar mamaki tamkar ba ita ta fadawa Maamu ta fadi hakan ba saboda Wangesi yace dole ayi biki kasa da wata guda idan ba haka ba aiki ya lalace.  Ita kuma Maamu asiri ya ci jikinta ta bi umarninta.

Tsoron Anti Bebi da Shuhada ne ya kamashi a take. Yanzu da ya fara farfadowa yasan akwai wata a kasa indai Maamu daga haduwa jiya zata ce ya auri Shuhada. Ficewa yayi batare da ya bada amsa ba. Sai ga Maamu tana bawa Anti Bebi hakuri tare da alkawarin aure tsakanin Shuhada da Awaisu babu fashi.

*****

Da fitarsa asibiti ya wuce. Gimbi ya tarar a bakin kofa ta matsa lallai a sallameta. Da ganin Awaisu ta rungume shi tana kuka tana rokonsa ya yafe mata duk laifin da tayi masa. Da kyar ya iya rabata da jikinsa ya koma gefe.

“Abban Haris ko aiki nake a gidanka ban cancanci wulakanci ba. Kazo ka ajiyeni babu kai bare wani yazo ya dubani”

“Kina da bakin magana dama Gimbi? Ki fadawa Maamu maganganu son ranki kina min kallon wani shashasha ban san darajar uwata ba”

Gabanta ne yayi mugun faduwa ta kara tabbatarwa asirinta ya karye Awaisu zai iya sakinta.  Kwantar da kai tayi tana ta rokonsa ya dai sakata a mota zasu wuce gida wayarsa ta hau kara.

Muryar Harisu yaji da ya daga suka gaisa. Harisu ya sanar dashi zai zo daukar Maamu da Rumana su tafi hutu Fika karshen sati. Awaisu hakan yayi masa daidai domin yana ganin kamar haukata shi za ayi a gidan nan. Ga Gimbi ga Maamu da Anti Bebi ke juyawa sannan ga wata sabuwa wai ita Shuhada.

*****

Kafin su isa gidan Anti Bebi ta tafi bayan ta nanatawa Shuhada ta dage wurin kyautatawa Maamu sai bayan magariba zata dawo daukarta.

Fitarta dama wurin Gimbi tayi niyar zuwa ta tunzurata. Tana isa asibitin aka tabbatar mata an sallami Gimbi. Gidan Alh Mudi ta wuce ta sanar da Mama cewa Gimbi babu lafiya. A nan ta tarar da kannen Gimbin duk sun zo gidan. A gabansu ta soma kukan gulma ganin ko kadan zancen bai dami Mama ba.

“Yaya Amina kinyi min muguwar fahimta game da Gimbi. Indai saboda tana mu’amala dani ne kika gujeta to daga yau babu ni babu Gimbi.”

Mama ta tabe baki rai a bace  “Bebi ko zakiyi kisisina yakamata ki san cewa ni bazatayi tasiri a kaina ba. Halinki sai dai na bayar da labari ga wasu. Ke da shaidan kun fitsare kan Gimbi sai yadda kika ce takeyi a gidan miji, to gaki ga ta. dubiya dai zamuje don neman lada amma matsawar bazata dawo daga rakiyar halayen da kika koya mata ba to taje duni… “

STORY CONTINUES BELOW

“Mama don Allah kada kiyi mata baki”cewar Umar autansu  Gimbi.

Shiru tayi bata karasa magana ba sai suya da ranta yake yi. Bakincikinta daya yadda ta tsani halayyar kanwarta ace yau ‘yar cikinta ke kwatanta hakan. Wasu lokutan har tuhumar kanta take yi ko akwai inda ta kuskure a tarbiyar yaranta.

Anti Bebi kuwa ficewa tayi sumsum ita a dole mutuniyar kirki. Wangesi ta kira suka gama wasu kulle-kullen sannan ta koma gidan Awaisu.

*****

“Ke kuma daga ina?”

Shuhada tayi turus ta wurin ta kasa karasa kwashe sharar da take yi a falo.

Yadda Gimbi tayi maganar zai nuna razana da tsoron da ya mamaye zuciyarta. Kwana biyu kawai a asibiti har Awaisu ya sami damar kawo mace cikin gidansa.

Tsoratar da ya ga tayi yayi masa dadi kuma yaji baya son yi mata wani bayani da zai kawar mata da zarginta. Yadda yasan Gimbi dra kishin masifa ko da wanan ne sai ya bata mata yadda ta batawa Maamu.

Shuhada na ganin yayi shiru tace

“Anti Gimbiya ina kwana, yaya jiki?”

Idanu a rufe rai a bace ta kalli Awaisu tana nuna shi da yatsa a gaban Maamu da hayaniya ta fito da ita.

“Kayi kadan kayi min irin wannan cin kashin.” Ba don ciwon kafa ba karshenta sai ta kaiwa Shuhada duka.

Duk wannan hargagin a idon Anti Bebi akayi. Hakan yayi mata dadi Gimbi tana kara bata rawarta da tsalle. Tana ji ta cigaba da masifa Awaisu idanunsa suka rine suka yi ja don bacin rai. Maamu kuwa ta kara tsanarta da halayenta. Sai da ta bari ta soma zagi sannan ta shigo da sauri ta tafi gabanta ta tsaya.

“Gimbi meyasa baki da lissafi ne? Shuhada ce fa na taho da ita tayi girki saboda su Amir”

‘Yar nutsuwa ce ta saukar mata ta sake kallon kyakkyawar budurwar don bata yi kama da bazawara ba. Babu kunya ta danyi murmushi jin cewa saboda yaranta tazo. Kuma ta san cewa Anti Bebi bazata cuceta ba.

“Idona ne ya rufe Anti”

“Shine kuma zaki rinka yiwa mijinki fada kamar sa’anki?”

Da farko ko a jikinta sai da Anti Bebi ta kifta mata ido sannan ta dan russuna ta bashi hakuri. Sake zungurinta tayi ta juya a dakile ta gaishe  Maamu. Itama a dakilen ta amsa fuskarta na nuni da rashin jindadin dawowarta gidan.

Hannunta Anti Bebi ta kama ta rakata daki. Bayan ta rufe kofa take yi mata fadan ba’a saurin sauke makaman yaki idan babu tabbacin asiri yana ci. Ma’ana banda asiri dole ta hada da kissa da kisisina idan tana son yin galaba. Sannan tace zata bar Shuhada a gidan ta rinka sakata aiki kafin ta sami lafiya.

“Mace kamar wannan zaki bar min a gida, gaskiya tafi da abarki nagode”

Harararta Anti Bebi tayi “banza, ana ga yaki kina ga kura. Yanzu banda na gama da ita nasan dole tayi yadda kike so me zaisa na kawota? Sauki nake nema miki kada waccan tsohuwar ta sami faraga ta fara miki iko da gidan miji. Ko kinsan jiya da  na zo har girki Rumana tayi”

“Yarinyar nan zata ci ubanta. Ita fa ta janyo min kwanciyar nan” Gimbi ta fada tana hura hanci.

Zuga sosai Anti Bebi tayi mata sannan ta tafi ta bar Shuhada sai dare.

Awaisu dakin Maamu yaje yake sanar da ita tahowar Harisu a karshen sati. Tsabar murnar zata je Fika harda hawayenta. Shima kawar da kai yayi gefe baya so ta ga kwallarsa. Zuciyarsa duk ta karye da ganin yadda take murna. Wato ba karamin tauye mata hakki akeyi a gidansa ba.

“Maamu ki yafe min don Allah. Kuma idan akwai abin da kike bukata daga gareni umarni kawai zaki bani na cika miki. Ki yawaita yi min addua. Wasu abubuwan sai naga kamar cikin bacci nake aikatawa”

Murmushi tayi masa “yarinyar nan kawai nake so ka aura ka faranta min”

Shiru yayi na dan lokaci sai dai kafin yayi magana ya jiyo muryar Rumana tana ihu ga muryar Shuhada tana bada hakuri. Duka su biyun tare suka fita da sauri.

STORY CONTINUES BELOW

Gimbi suka tarar ta daga daya daga cikin sandunan da aka bata a asibiti na tafiya ta zata sake kwadawa Rumana a karo na biyu yayi saurin karba ai kuwa ta fadi wanwar saboda yadda ya turata.

Daga shi har Maamun babu wanda ta saurarawa saboda tuni tayi turaren Wangesi a cikin gidan tana zaton komai ya koma kamar da. Sai dai tuni Wangesi ya karya duk wani asiri da ya bata.

“Awaisu ka janye mahaifiyarka ku bar wurin nan kafin na dawo kanku. A wane dalili wannan matsiyaciyar zata shigar min kitchen?”

Wasu kyawawan mari taji sun saukar mata har biyu a kumatun hagu masu zafi. Kafin ta gane a ina take ya sake kara mata wani. Shuhada wadda aka fara komai a gabanta ta tsorata sosai. Allah Yasa dreban baije dauko su Haris da wuri ba itama Rumana takowa tayi da a gabansu za ayi komai.

Da kyar Maamu ta samu ya bar dukan Gimbi bayan ya dankara mata saki daya da umarnin ta fice masa daga gida..

Mamaki karara a fuskarta yadda ya sami dama da bakin yi mata haka. Ko dai asirin ya dena masa aiki ne? Wani zafi taji ya mamaye jikinta ta kasa cewa komai don kidima. Da kyar ta iya cewa Shuhada ta kira mata Anti Bebi.

*****

Rabin awa a tsakani sai gata. Ta nuna damuwa sosai akan wannan abu sannan ta umarci Gimbi ta tashi su tafi. Ita kuwa da har yanzu ta kasa gaskata faruwar lamarin tace babu inda zata je. Awaisu kuma yayi rantsuwa bazata kara kwana a gidansa ba. Kan kace meye wannan rikici ya kaure tsakaninsu har sai da Anti Bebi ta kirawo Mama. Haka ta taho gidan rai a bace suka dauke Gimbi tana karamin hauka. Ranar gidan gabadaya ya juye. Harisu Maamu ta nema ta sanar dashi komai yace yana tafe washegari.

*****

Kafin uku na rana ya iso haka akayi ta maida zance. Abin mamaki Anti Bebi tayi kane kane cikinsu tana bada hakuri an rasa mai korarta.

Alh Mudi Maibuta shima yasha takaicin halin ‘yarsa. Yayi ta bawa su Maamu hakuri tace babu komai. Ranar Jumaa ana yin hutun makaranta suka dunguma har yaran Awaisu sai Fika. Shi kadai ya rage saboda aiki. Da suka isa Maamu na shiga dakinta ta rinka shafa bangon tana hawaye. Kowa yayi zaton kewa ce banda Rumana. Su Baaba Hure duk sun dauka rashin kunya kawai Gimbi take yiwa Awaisu da Maamu ya janyo mata saki.

A gidansu kuwa babu mai shiga sabgarta tsakanin Mama da Alhaji. Ko kuka ta kasa saboda bata taba tsammanin haka daga Awaisu ba. Yadda tayi imani da Wangesi bata kawo daidai da rana daya ba aikin zai lalace. Zuciyarta ta kara bushewa tana tunanin ba don kafa ba da tuni ta koma wurinsa an sake sabo.

A bangaren Anti Bebi kuwa duniya tayi dadi. Haka kullum take kiran Maamu tana fakewa da gaisuwa tana kara hura mata wuta akan auren Shuhada da Awaisu. Lokaci kankani duk walwalarta ta kau ta matsawa Baaba Hure lallai a tilasta Awaisu aurenta. Abin ya basu mamaki ko sati uku baayi ba da sakin Gimbi. Abu yazo yayi tsananin da Maamu har kuka tayi akan anki fara maganar aure.

Da Awaisu yazo yaji labari ya dage sam bazai aureta ba. Gidansu Gimbi yaje bayan ya koma ya ce ta fadawa Anti Bebi idan ta sake kiran Maamu a waya sai yayi kararta. Kuma maganar aurensa da take son hadawa da Shuhada ta sani ko mata sun kare ya gama auren danginsu.

Tun da Awaisu ya saketa sai yau tayi kuka. Dama kafarta na warkewa ta fara yawon wurin Wangesi yana ta tatseta kamar mai amma babu biyan bukata. Ita ta sawa ranta komawa gidab mijinta kamar tayi ta gama ne. Wasu lokutan ma da Anti Bebin suke zuwa. Wani mugun murmushi ta saki ga hawaye ya jika mata fuska

“Lallai Anti Bebi kin taro match din da bazaki kai labari ba”

Numbar wata mai wanke bandakin bankinsu ta kira tace tana son ganinta. Ba dadewa da kwatance Gimbi taje gidan da take. Apartment ne yaji komai kamar gidan amarya. Kuma a haka daga shara sai wankin toilet take yi.

“Ovi taimakona zakiyi ko nawa ne zan baki. Nasan kina da bokan da yake miki aiki domin naji kuna magana da kunnena. Ko wannan gidan ya isa ya sanar dani cewa akwai wanda ya tsaya miki”

Ovi kamar yadda aka kiran matar tayi dariya kawai. Bokanta babu abinda zata bukata ya kasa bata. Har gidansa ta raka Gimbi da ta fuskanci ‘yar hannu ce.

*****

Kwanaki biyu da zuwan Gimbi wurin bokan Ovi Anti Bebi tana dawowa daga wurin masu kujeru da take son saya na bikin Shuhada taji wani sanyi yana ratsata gashi ita take tuki.

A hankali ta fara jin kamar wani ke zaune a seat din motar ita kuma akan cinyarsa. Tsoro ya fara shigarta sai ji tayi kamar ana yi mata numfashi a wuya. Nan da nan tsigar jikinta ta tashi tayi saurin taka burki da karfi a gefen titi.

Kamar daga sama ta bangaren kunnenta na dama taji an danyi kara “washhhh kin take min kofato”

Wani fitsari ne mai dumi ya silalo daga mararta ta dan duka kadan a wayance tana kallo kasan motar inda kafarta ta taka burkin. Cikinta ne taji ya kulle ganin ‘yar jar kafa kamar ta akuya sanye da cover shoe baki shima mai shape din kofato.

Kwakwalwarta taji ta zama fayau babu sauran tunani sai na neman hanyar tsira. Muryar ta sake ji ta koma matsowa jikin kunnenta kamar ana yi mata rada da yar dariya

“Bebi kin jikani da fitsari fa ko zaki bani aron naki zanin na daura”

Mutuwar zaune tayi na ‘yan mintuna kafin daga baya dabara ta fado mata.

“Hmmm ashe fa yau ban zubawa motar nan ruwa ba. ” ta fada da dan murmushi ita a dole bata ji komai ba “Shiyasa take zafi. Bari na fita n kirawo mai pure water ya kawo na zuba……Kai mai ruwa zo nan” ta fada da karfi

Kama kofar motar tayi zata bude taji an damki hannunta ko motsi ta kasa yi.

Wani irin numfashi Anti Bebi ta rinka saukarwa mai kama da gurnani. Bata san tsahon lokacin da dauka a haka ba sai ji tayi ana kwankwasa glass din motar ta saitin inda take. A firgice ta bude ido ta saukesu kan wasu jajayen idanu manya. Tafiya tayi luuuu zata sake suma taji ance

“baiwar Allah lafiya kike?”+

Mace ta gani a kusa da mai jajayen idanun taji hankalinta ya kwanta. Da sauri ta bude ta fito. Sai a lokacin ta kula mutane sun kai biyar da suka zagaye motar ana tunanin ko wani abu ne ya sameta. Karyar ciwo tayi musu ta kulle motar ta nemi tasi ta shiga. A cikin motar ma duk da shata tayi ta zauna a baya amma haka taji duk an matseta. A takure ta isa gida babu damar magana don shi kanshi dreban motar tsoronsa take yi.

******

Da shigar Anti Bebi gida ta soma kiran Wangesi baya dauka. A yadda take jin jikinta kamar ana daureta dole ta tafi wurinsa neman taimako. Drebanta ta kira bata la’akari da yamma ta kawo kai tace su tafi kan tudu wurin Wangesi.

Sun isa farko-farkon magriba. Jikinta duk ciwo yake mata saboda wata irin matsuwa da tayi a bayan motar. Gashi dai ita kadaice amma kamar su biyar ko shida take jin sun zauna a takure. Tsabar sauri kafarta daya babu takalmi haka ta fada cikin gidan Wangesi. Dakin da yake ganin bakinsa irinta ta shiga ko iso bata tsaya yaransa da suke masa aiki sunyi mata ba.

Mata uku ta samu a wurin suna gabatar masa da matsalolinsu. Yana ganin Anti Bebi kamar an jehota daga sama ya mike tsaye

“Hajiya Bebi lafiya?”

Haki take yi tana maida numfashi da kyar murya a sarke tace “ina fa lafiya Wangesi yau nayi gamo”

Matan da suke dakin suka fara kallon-kallo. Wangesi ya samu ta dan nutsu ta labarta masa abubuwan da suka faru da ita tun daga farko.

Wani tsalle ta ga ya daka ya daga hannuwa sama

“Ehooooooo, Ehooo. Waye yace dani bani ba? Sai ni nan uban kan tudu mai aiki da hatsabiban aljanu”

Juyi yake yi yana furzar da yawu ransa yayi matukar baci. Can ya fita ya dawo da wata tukunyar kasa sai wari take yi.

“Bebi tun farkon zuwanki wurina sama da shekara goma me  na fada miki?”

A daburce ta tambayeshi “meye hadin farkon zuwana da wannan masifar da na tashi da ita?”

“Bari na tuna miki idan kin manta. Aljanin da yake miki aiki baya son kishiya kuma na sanar dake duk ranar da kika je wurin wani bokan yace a bata duk wani sihiri da aka taba yi miki. Sannan ki jira abin da zai biyo baya. Na tabbata wurin wani kika je shiyasa haka ta faru”

Idanu ta zaro kamar su zube a kasa “ni kuwa me zai kaini wurin wani ina da kai….na rantse maka da…..”

Tusssss taji kafin ta gama rantsuwar ya saki tukunyar da take kunshe da dukkan wani asiri da ya taba yi mata.

“Aljanin bashi da hakuri ko kadan Bebi. Ki fita daga gidan nan kafin yazo mu duka mu fuskanci bacin ransa.”

Matan nan uku na jin haka suka runtuma a guje. Anti Bebi kuwa a gaban tukunyar ta durkusa tana wanj gunjin kuka

“Wangesi ka tona min asiri. Cikin kasa da awa biyar duniya tayi min juyi irin wannan? Na shiga uku….”

Kara murtuke fuska yayi “ke kika janyowa kanki ko ma menene. Ki fice min daga gida kafin ya iso gareki”

Jikinta sam babu kwari ta mike tsaye da kyar. Zuciyarta ke fada mata ko dai mafarki take yi duk wannan bala’in ba gaske bane. Da jan kafa ta fita waje. Tana sa kafa a wajen taji an rungumeta tsam ana yi mata magana a kunne har tsigar jikinta na tashi

“Oyoyo Bebi, kika barni ina ta jiranki a nan. Zo mu tafi na fara jin yunwa”

Drebanta yana cikin mota ya hangota ta fadi a sume ya fito a guje ya fara neman yadda zai sakata a mota.

*****

Maamu ta gama cin tuwo kenan Baabu Hure ta shigo dakin suka fara hira. Cikin hirar Baaba ta sako zancen auren Awaisu da yake ta matsowa

STORY CONTINUES BELOW

“Yanzu Maamu kina ganin babu matsala wannan auren na yaron nan? Kin dage sai anyi auren nan ba kya tunanin kada matsala ta taso ganin akwai alaka tsakaninta da Gimbiya”

Hannun Baaba ta kama ta rike tana magana a hankali “Baaba Hure ina ganin a bar maganar auren nan kawai. Ni bansan me ya kaini tunanin hadasu ba “

Baki Baaba ta saki tsabar mamaki ya cikata. Maamu da har kusan kuka take yi akan anki gaggauta auren shine zata ce ta fasa. Anya mutanen nan haka suka barta kuwa?

Katse mata tunani tayi da muemushin da yafi kuka ciwo

“yarinyar nan Gimbi nake so ayi masa bikonta. Ita kuma waccan sai a basu hakuri. Ba kiji yadda raina ke suya ba idan na tuna uwardakinta Bebi dinnan. Matar tsoro take bani.”

Baaba kasa magana tayi don abin yafi karfin mamaki. Maamu sai magana take yi mara kan gado. Karshe ta kwanta ta juyawa Baaba baya. Tashi Baaban tayi zata fita taji sheshshkar kukan Maamu. Fita tayi tana share kwalla. Ta rasa mene ne yake damun Maamu da har take kuka amma ta kasa fadawa kowa damuwarta.

*****

Daren ranar Anti Bebi tamkar tayu hauka. Dadinta ma Alh Maitama yayi tafiya. Shuhada kuma ganin yadda ta shigo musu a birkice ko ta kanta bata bi ba.

A bangaren Gimbi tun da ta koma gida ta kasa nutsuwa. Zuwa yanzu yaci ace aikin bokan Ovi ya fara kamawa. Idan taji shiru har safiya tasan akwai matsala dole ta canja salo. Wurin shadayan dare wayarta tayi kara alamun text ya shigo. Tayi zaton kamfanin layin wayarta ne ta share. Sai dayan dare ta dauki wayar zata duba lokaci ta ga sakonni sumfi hamsin daga Awaisu wanda  mugun son Gimbi yayi masa kawanya a zuciya.

Murmushi tayi ta duba na farkon

(Na mayar dake Gimbiyata ki dawo gareni

Na biyun kuma

(Ki bani izinin kiranki a waya)

Haka tayi ta bin sakonnin tana karantawa a tsaye don zama ya gagareta. Murna take yi mara misaltuwa. A daren ta hada kayayakinta ko runtsawa ta kasa yi. Kafin takwas na safe ta turo akwatunanta falo tana kiran maigadi yazo ya kai mata mota.

Hayaniyarta ce tasa Mama fitowa ta ganta a shirye zata fita.

“Ina zuwa da sanyin safiyar nan?”

Fuskarta na nuni da tsananin farinciki ko gaishe da Maman bata yi ba ta mika mata wayarta

“Gida zan tafi Abban Haris ya mayar dani”

Marinta Mama tayi niyar yi sai ta fasa ta samu wuri ta zauna a sanyaye

“Gimbi a tunaninki abubuwan nan da kike yi kin dauko hanya mai billewa kenan? Da ban fito ba sai dai mu nemeki mu rasa kenan ko. Hmm bazanyi miki baki ba amma ina mai baki shawara ki kiyayi duniya. Komai nisan jifa kasa zai fado, komai nisan dare gari zai waye…karshe kuma ki sani abin da ka shuka shi zaka girbe.”

Kallon Mama tayi na dan lokaci sai kuma ta figi karamin akwatinta tayi gaba tana cewa ta gaishe da Babanta idan ya tashi. Tana fita Mama ta fashe da kuka tana yiwa Anti Bebi Allah Ya isa.

******

Cikin bacci yake ta buge buge batare da ya sani ba. Kana ganinsa kasan duk yadda akayi mugun mafarki yake yi. Mutanen kusa dashi suka fara juyowa ana kallonsa. Hakan yasa abokinsa da suke tare Kamilu ya soma girgiza shi.

“Kai T a train muke fa. Meye haka?”

Tajuddeen ya bude idanunsa da suka masa nauyi a hankali. Hannun Kamilu ya damko tamkar wanda zai gudu ya barshi.

“Kamilu meyasa na saki S?”

Harara Kamilu ya jefa masa sannan ya fizge hannunsa

“Dalla malam cikani”

Tajuddeen ya sake rike masa hannu

“wallahi Kamilu da gaske nake. Haka kawai fa ranar na shiga gida na hauta da fada mara dalili sannan na saketa”

STORY CONTINUES BELOW

Kamilu sake hararsa yayi sai ya kula hawaye Tajuddeen yake yi. Zuciyarsa ce ta dan karye ya dafa kafadarsa.

“Wannan ba magana bace ta nan T. Ka bari mu karasa gida sai muyi a nutse. Kaga sai kallonmu ake yi”

Ba don yaso ba ya hakura amma da shigarsu gidan Kamilu ko zama basu yi ba Tajuddeen ya sake tado maganar.

“Wai T kayi gamo ne a train dazu? Dama wani shure shure naga kanayi cikin bacci har kasa ana kallonmu. Anyways me kake son ji game da rashin mutumcin da ka aikata”

Sunkuyar da kai yayi yana tuna ranar da ya saki Shuhada da irin wulakancin da yayi mata.

“Bani da wani dalili na abin da na aikata Kamilu. Haka kawai kamar wanda akayiwa asiri. Saki har uku” ya karashe hawaye na bin kuncinsa.

Duk irin haushinsa da Kamilu yake ji dole ya tausaya masa.

“Al’amarin nan naku da daure kai. Kasan da ka dena kiran mutanen gida akan fadan da suke maka na sakin da kayi Umma ni take nema. Kuma abin mamaki ana nake jin ashe itama Mummynsu Shuhada itama nata auren ya mutu”

Tajuddeen ya dan kada kai “kasan labari mara dadi babu amfanin bayar dashi. Shiyasa ban taba fada maka ba. Baffanmu ya bani labari ba karamar soyayya bace tsakanin iyayen S. Kasan duk garinsu daya. Shiyasa muka yi mamaki sosai da yayi sakin. Tunda ya auro wata mata Bebi shikenan gidan ya rikice.”

“Bebi fa kace” Kamilu ya maimaita da sauri.

Kai Tajuddeen ya gyada masa kawai.

“Bebi dai wata doguwa siririya ko, idan tana tafiya duk jikinta sai ya motsa”

Murmushin dole T yayi saboda yadda Kamilu yake kwatanta Anti Bebi

“Ita ce, ka santa ne?”

“Allah Masani amma ina kyautata zaton ita ce sanadiyar wannan sakin naka da na baban Shuhada. Ta taba auren wan mamanmu, cikin wata biyu sai da ya saki matansa uku da suke gidan. Dama cikon ta hudun ya saka ya aurota. A shekara dayan da sukayi tare sai da ya zare hannunsa kan duka yaransa daga shi sai Bebi poison yadda yaran suke kiranta”

Lallai biri yayi kama da mutum. Dama irin labaranta da yaji daga wurin S da kuma wanda ido ya gane masa yasan zata aikata.  Muguwar tsanarta ce ta kara shigarsa ya fara tunanin irin hukuncin da zaiyi mata.

Kafadarsa yaji an dafa ya kalli abokinsa Kamilu

“Wallahi bata ci bulus ba. Gida zan koma a cikin watan nan. Kafin nan za ka rakani wurin Suhail a makaranta”

*****

Awaisu tun jiya ya kasa zaune ya kasa tsaye saboda tunanin Gimbi. Kafin gari ya waye sau uku yana kukan da ya rasa dalilinsa. Shi dai a iya saninsa da kansa ya saketa saboda baya son halayenta. Yanzu kuma ya rasa wace jarabarce tasa duk da baya son halayen nata yake jin idan bai dawo da ita ba komai zai iya faruwa dashi. Haka nan a daddafe ya jira gari ya waye ko wanka baiyi ba ya fita zuwa gidan Alh Mudi bikon matarsa.

Mama da Alhajin ya tarar suka gaisa a mutumce sannan suka sanar dashi ta tafi gida. Ko sallamar kirki bai iya yi musu ba ya fice.

“Amina kada fa Allah Ya kamamu da hakkin Awaisu. Kinga babban mutum ya zama wani lusari akan mace.”

“Alhaji na fika damuwa domin ta bangarena Gimbi ta samo wannan mugun halin. Na rasa yadda zanyi da ita” kuka ne ya kwace mata na takaicin halin ‘yarta Alhaji yayi ta rarrashi da bata baki akan su dage da addua.

Gida Awaisu ya wuce ya fara karo da wani mugun hayaki da Gimbi ta soma yiwa gidan. Suna hada ido ta fito rike da kasko a hannunta yaji jikinsa ya mace bashi da wani kuzari. Da fara’a ta tarbe shi suka shige daki yana binta kamar rakumi da akala.

Ko awa biyu batayi da dawowa ba tace ya tura dreba a dawo mata da yaranta. Haka kuwa akayi babu musu ya tura dreban yace a dauko harda Maamu da Rumana da sassafe washegari su taho.

Rumana tayu kuka har hawaye suka nemi kafe mata saboda bakincikin komawa Abuja. Maamu kuwa bata iya cewa komai ba. Haka suka shirya da safe Harisu yana ta mita suka tafi. Bayan fitarsu ya kira Awaisu ya nuna rashin jindadinsa game da hakan amma yayi masa uzuri tunda babu mata a gidan. Awaisu bai nuna masa Gimbi ta dawo ba sai da yace zasu taho biko sannan ya fada masa. Har ya ajiye wayar yana ta mamakin sauyi irin wannan daga kaninsa.

*****

Anti Bebi na kwance a daki tayi zuru zuru saboda yadda aljanu suke wasan ‘yartsana da ita a daki. Tana zaune zata ji ana fadan waye zaiyi mata wanka da mai taje mata kai. Gashi Alhaji ranar zai dawo. Shuhada ta leka dakin sau biyu tana ganinta a zaune ko gaban mudubi ko a kan gado shiyasa bata kawo komai a ranta.

Kofa taji ana tabawa ta zabura ta tashi tana jan bargo zata rufe kanta. Alh Maitama ne ya shigo a fusace Shuhada tana biye dashi tana tambayar me ya same shi. Wurgi yayi da jakarsa da babbar riga da ya dawo dasu a hannu ya haye gadon ya finciko Anti Bebi.

“Munafuka algunguma zo ki fita daga gidan nan”

Tunda Wangesi ya juya mata baya dama tasan tata ta kare sai dai batayi tunanin abin zai kai haka ba. Tattaro dan karfin hali tayi harare shi

“Alhaji ni kake yiwa tsawa haka”

Mari ya rinka zabga mata Shuhada da take gefe ta tsorata sosai. Tana kallo babanta yayiwa Anti Bebi duka kamar bazai barta da rai ba sai da ya gama ya koma wurin ‘yarsa ya rungumeta yana kuka

“Shuhada kuyi hakuri na dauko muku jaraba ta wargaza mana gida. Ni yanzu Kaduna zani wurin Mummynku.”

Kukan farinciki take itama tace zata bishi. Cewa yayi ta shirya tana fita ya rufe kofar dakin da mukulli

“Hajiya Bebi so nake duk inda takardun kadarorina suke ki dauko ki bani tun muna shaida juna. Na rantse miki ko tsinkina bazaki tsira dashi ba.”

Dan abin da take sa ran tsira dashi taga Alhaji zai shiga tsakani ta fara tsiwa baki bai mutu ba. Ai kuwa ta jawowa kanta sabon duka. Sai da taji kamar bazatayi rai ba ta tashi da kyar ta dauko masa wasu da suke dakin. Sauran kuwa a wani store taje ta dauko. Security yasa suka tafi da ita police station yace zaiyi waya da komishina. Burinsa a tsareta har ya dawo daga wurin uwar ‘ya’yansa.

Sai bayan sati uku aka maida auren iyayen Shuhada. A lokacin Anti Bebi duka accounts dinta Alh Maitama yasa an rufe ya bita da saki uku kwarara.

A bangaren su Gimbi wannan dawowar su Maamu suna gasuwa sosai. Kanwar Ovi mai suna Rita ta dauko matsayin mai’aiki. Itace kuma yar aike zuwa gurin boka. A haka ne wahala tayi wahala Rumana tayi suman karya ta samu ta koma Fika gaban iyayenta.

*Wasa farin girki*

Maman Rumana ta daga labule ta shigo daki da sallama ta tarar da Rumana tana zazzaga madarar cowbell a hannunta tana lasa. Har wani lumshe ido take yi tana kada kai duniya ta samu. Ran Mama ya baci ta kai mata duka a gadon baya.+

“Tun dazu nake kiranki kunnenki kamar an toshe da auduga kin kasa ji bare ki amsa”

Watsi tayi da madarar ta hau sosa wurin da hannuwanta duka biyu ta soma bata hakuri. Mama ta cigaba da mita

“Tun da kika dawo gidannan sai cin tsiya da kwadayi kamar ‘yar yaye. Da girmanki kike wani lasar madara”

Rumana ta dan murmusa “wallahi Mama protein ne yayi karanci a jikina.”

“Ke kika sanshi ni ban sanshi ba”

“Mama wai baza’a dauko Maamu bane? Ta fini shan wahala sosai” sai kuma ga hawaye ta fara kukan rayuwar da ta baro Maamu a ciki. Sau biyu tana mafarkinta kwana biyun nan duk ta damu. Jin Maman bata ce komai ba ta dan matsa kusa da ita.

“Mama don Allah ki yiwa Baba magana kada ta mutu da yunwa..”

“Kada na sake jin wannan maganar a bakinki. Yanzu haka babanku zaiyi bincike kuma wallahi idan karya kika shara mana don kawai ki dawo nan kema kinsan bazata kare miki da kyau ba. Kuma zamu tattaraki ne a mayar”

Zumbur ta tashi tsaye jin hakan “Mama ni da gidan Uncle Awaisu fa har abada. Kai ni ko Abuja bana fatan Allah Ya sake kaini. Mama! Mama!! idan kuka mayar dani Abuja wallahi guduwa zanyi na shiga duniy… “

Bakin nata Mama tayi saurin dokewa kafin ta kai karshe. “Bana son sakarci kinji ko, wace irin magana ce wannan fita ki bani wuri”

Rumana ta juya  ta fita baki na radadi suka hada ido da Baaba Hure wadda ta gama jin hirarta da mahaifiyarta. A guje ta bar wurin tana tsoron ko kakarta taji abubuwan da ta fada.

Sai dare Harisu ya dawo Baaba Hure ta zaunar dashi ta fada masa abin da Rumana ta gayawa Mamanta.

“Tun da Rumana ta iya bushe ido da zuciyarta ina kara tabbatar maka da cewa da wuya idan karya take yi musu. Kafin abubuwa su kara lalacewa gara ka shirya kaje Abujan kamar yadda ka fadawa Maamun a waya kuyi magana da ita. Idan akwai cutarwa ta dawo nan muyi zamanmu. Ana uwar miji na gasa suruka ita kuma matar dan ce mara kirki “

Harisu da baya son rigima yace “haba Baaba ai baki tabbatar ba. Ba don al’amura sun taso min ba ai da tun shekaranjiya zan tafi Abujan ma”

Haka suka yi ta shawarar yadda tafiyarsa zata kasance jibi sannan ya tashi ya tafi nasa dakin. Rumana duk abin duniya ya isheta saboda kewar Maamu da halin da ta barota.

*****

Kwance Gimbi take tana karkada kafa daya tana tunanin yadda take cin karenta babu babbaka. Yanzu jin kanta take yi daidai da kowa. Miji yana da kudi kuma yana tafin hannunta.

“Uwarsa kuma ta zama hoto abin kallo.” ta fada a fili tana murmushi. Kafin ta hanata zaman gidan mijinta ita tayi saurin maganin abin. Anti Bebi ce ta fado mata ta kwashe da dariya har da kyakyatawa. Ko ina take yanzu oho. Cikin dan lokacin da bai wuce wata guda ba ta gina fadarta yadda take so. Agogon wayarta ta kalla biyar da rabi ta dan wuce ta fito zuwa dakin Maamu.

Tana zaune akan abin sallah ta kara ramewa duk ta dashe ta jingina bayanta da bango tana kallon fanka tana tunani. Jin muryar Gimbi a kanta ba karamin tsoro ya bata ba ta dawo da kallonta gareta.

Sai da ta zauna a kusa da Maamu sannan ta kwalawa Rita kira akan ta kawo abincinta na rana. Ragowar dankalin hausa ne da aka soya musu da yara da Awaisu suka ci da farfaesu da safe tasa aka kawowa Maamun. Sai dai ita nata banda bushewar da ya fara babu farfesun sai yaji aka dan barbada a gefe. Idanunta da basa rabuwa da hawaye taji sun soma cikowa ta sunkuyar da kanta.

STORY CONTINUES BELOW

Gimbi tayi murmushin keta ta janyo mata plate din tare da daukar daya ta dangwalo yajin.

“Bude na baki a baki kinji Maamuna. Ai cewa Rita nayi yau kada a baki shinkafar rana saboda kada dankanoma ko basir su kamaki”

Da yake hausar tayi mata tsauri da yawa bata fahimta ba ta bude bakin a dole saboda yadda take tsoron Gimbi. Dandanon yajin mai azababben fada ne ya fara sauka a harshenta kafin taji an tura mata dankalin dukkansa.

Kwarewa tayi ta soma tari sai ga Awaisu ya taho amma daga bakin kofa ya tsaya yana tsoron kada ya karaso Gimbi tayi fada. Zuciyarsa babu dadi don yasan ba’a kyautawa Maamu amma cikin lokaci kankani sai yaji ya manta ko abin ya dena damunsa a rai. Kasa jurewa yayi yadda Maamu take cin dankalin tana kwarewa ko ruwa babu a kusa. Juyawa yayi zai tafi Gimbi ta kira shi tana wani shu’umin murmushi

“Abban Haris yau ka ganmu a baki nake bawa Maamu abinci ko. Kasan nice ‘yar gatanta kai ka nemi wata”

Maamu ya kalla ya ga ta tsira masa idanu tana yi masa kallon ka ceceni. Ji yayi kafafunsa har rawa suna yi ya fice batare da ya tankawa Gimbi ba.

Yana tafiya Maamu tasa kuka Gimbi tayi ta rarrashinta wai me take so. Da ta gaji ta fito falo suka kebe da Rita.

“Madam wai yaushe zaki mayar da matar nan garinsu tunda aiki yayi kyau ita da Oga duka a hannunki suke”

Dariya tayi “na fasa mayar da ita saboda wadannan munafukan dangin nasu masu sa ido. Gara mu zauna a nan tare irin haka bata isa tasa ko ta hana ba bare tayi min iko da gidan miji.”

Rita ta gyada kai “haka ne kuma”

Bayan Gimbi ta shige wurin mijinta Rita ta tafi kitchen ta dauko robar ruwa ta kaiwa Maamu a daki. Tsayawa tayi a kanta tace ta sha ta bata robar kada Gimbi ta gani. Maamu sai da tasha rabin robar ta mika mata. Rita ta dan share kwalla. Daga ita har Ovi ba mutumci garesu ba amma ta fuskanci Gimbi lamba daya ce a rashin imani. Sosai take jin tausayin Maamu yana shigarta albarkacin yawan adduar  da Maamu take yi na neman sauki.

*****

Washegari da wuri Harisu ya sanar da Awaisu zai taho da safe ya nuna masa farincikinsa sosai kuwa. Wurin azahar sai ga waya daga Katsina garinsu Baaba Hure yayanta da take bi ya rasu. Cikin gaggawa suka shirya kusan rabin gidan suka kama hanyar Katsinan. A hanya Harisu ya sake kiran Awaisu yana fada masa. Yaji mutuwar domin yasan  mutumin dattijon kirki ne.

“In sha Allah ranar uku zai kama asabar zan taho Katsinan. Ka yiwa Baaba gaisuwa kafin na kira”

Yana ajiye wayar Gimbi dake zaune a cikin office dinsa ta hade rai “ina zaka je?” Ta tambaya a gadarance.

“Yayan Baaba ne ya rasu zanje Katsina”

Ta kyabe fuska zata yi masa kuka “kai da ayyuka suka yi maka yawa nake so weekend dinnan ka samu hutu shine zaka tsiri tafiya. Haba Abban Haris ka tayani kula da mijina mana. Kana bukatar hutu. Next weekend sai muje Katsinan tare”

“To” yace yana kallonta tana wani kwarkwasa kamar a gidanta. Ganin yana samun kudi sosai ga kasuwancinsa ko shi kadai suke dashi zasu wataya son ransu yasa ta ajiye aikinta. Amma kullum sai taje office din Awaisu kai masa abincin rana. Har an ganeta ana tsokanarsu da cewa soyayyarsu tana burge mutane. Ita kuwa mata ne bata so yayi mu’amala dasu don yadda ya kara kyau da haske saboda zaman naira kishinsa a ranta ya karu.

Su Harisu sun isa Katsina nan suka zauna har akayi sadakar uku babu Awaisu babu wayarsa. Idan ya kira shi ma baya dauka sai can dare yayi masa text wai aiki yayi yawa. Jikin Harisu yayi sanyi so yake kawai ya ganshi a Abuja. Abokansa har na Fika sun zo gaisuwa ga Alh Saminu na Kano dashi suke komai sai kaninsa ne zaice aiki yayi masa yawa. Duk hakuri irin nasa baiji dadi ba ko kadan.

Sun koma Fika da iyalansa ya bar Baaba cikin ‘yan uwa tace sai tayi wata guda zata koma. Kwanansa biyu da komawa tunanin canjin da yake gani daga wurin Awaisu ya dame shi. Hada kayansa yayi ya kira babba cikin yaransa maza mai sunan babansu suna kiran shi Abba yayi masa rakiya zuwa Abuja.

Suna isa kamar ya kira Awaisu ya fada masa sun shigo sai kawai ya fasa suka wuce gidan. Maigadi ya gane shi babu shamaki ya barshi ya shiga.

Gimbi ta tafi park shakatawa da yaranta sai Rita a falo tana kallo. Sallama Abba yayi ta fito kofar wajen da dan skirt wanda da kyar ya rufe rabin cinyarta. Harisu ya sunkuyar da kai Abba yasa kai zai shiga ta hana wai bata sansu ba.

Harisu yace mata shi yayan maigidan ne daga garinsu. Sai ta danyi murmushi

“Kaine baban Rumana ko, duka sun fita mutan gidan amma Maamu tana ciki muje na kaiku dakin”

Abba na gaba Harisu na bayansa suna bin Rita har kofar dakin Maamu. Dakin duk yayi kura saboda shigowar sanyi  da gani ba’a sharewa. Wani sauti mai kama da kuka Abba ya saki wanda ya kai hankalin Harisu kan Maamu da Abban yake kallo tana tsaye a bakin gado.

Wata tsohuwa ya gani tukuf don har tafi Baaba Hure nuna tsufa mai kama da Maamu. Sanye take da riga da zani amma saboda rama hannu daya ya sabule har kusan kirjinta. Fuskar nan ta koma tamkar kashi lullube da fata. Gabadaya ta rame sosai sai idanu sun firfito ga kasusuwan wuya. Zani ne a hannunta take kokarin daurawa yana ta sabulewa saboda rashin isasshen wurin da zai zauna. Kuka Harisu yasa tamkar karamin yaro yaje ya rike hannuwanta duka biyun ya durkusa yana bata hakuri.

“Maamu bansan zantukan Rumana gaskiya bane…., har raina naso ace karya take yi dan uwana bazai wulakanta aljannarsa ba. Ki yafe mana Maamu, ki yafe mana “

Kuka Maamu ta fashe dashi irin mai ratsa zuciyar nan. Duk wani bakinciki da bacin rai da take dannewa a lokacin ya bayyana. Kukan nata ya sake tayarwa da Harisu hankali. Abba yana tsaye daga gefe idanunsa shima sun kada sunyi jawur. Tsanar Kawun nasa Awaisu ce ta dirar masa a zuciya yana mai kara tabbatar da labaran da Rumana ta basu da ta koma.+

Bayan tayi shiru Harisu ya soma kokarin taimaka mata ta zauna a bakin gado fafur taki.

“Maamu ki zauna muyi magana don Allah” ya fada muryarsa tana rawa. Yau da wani ya bashi labarin an ganta a wannan yanayin bazai taba yarda ba. Rama ce tayi tamkar ta shekara a kwance. Cikin muryar da ta dashe da kuka ta dafa kafadarsa

“Harisu ka mayar dani cikin ‘yan uwana kafin ku fitar da gawata”

Agogon hannunsa ya kalla ya ga biyar ta kusa. Ya dan tausasa murya

“In sha Allah gobe war haka kina dakinki a Fika.”

Hannu ya ga ta daga masa “Wallahi Harisu bazan kara kwana a gidan nan. Indai ina da sauran gata a duniya ko yaya ne kuma ina da kima a naka idon kayi min wannan alfarmar don Allah”

Ji yayi ta kara karyar masa da zuciya ya kira Abba da ke tsaye kamar dogari yace ya bude drawer ya hada mata kaya.

Kai ta girgiza ta dauko hijab dinta akan abin sallah.

“Ni da nake jiran lokacina yayi me zanyi da kaya Harisu?”

Maganar ta tsaya masa a rai sosai ta kara masa tausayinta. Wannan duniya ina zaki damu yake ta fada a ransa. Shi dai Abba ya rarumo duk kayan da hannunsa ya kai garesu. Haka suka fito suka nufi indai ya ajiye motarsa da ya tuko su. Itama Awaisu ne ya cika masa ya saya.  Duk da cewa yayi matukar gajiya saboda baya dogon tuki haka ya sake shiga mazaunin dreba zai tuka su. Abba ne ya shiga rokonsa akan ya bari ya tuka yayi masa alkawarin bazaiyi gudu ba. Da kyar ya shawo kansa ya bashi mukullin bayan dogon gargadi. Da shigarsu gidan da sake kama hanyar Fika ko cikakkiyar awa daya ba’a samu ba.

Rita tana ganin sun fita daga gidan ta sauke ajiyar zuciya. Burinta su fita kafin uwar gayya Gimbiya ta dawo. Wannan tsohuwa ba karamar wahala take sha a gidan ba.

*****1

Hayaniyar su Mu’allim ce ta sanar da Rita dawowarsu ta fito daga dakinta sanye da wani gajeren wando da riga damammiya mai karamin hannu. Gimbi ta saki baki tana kallonta kafin ta hau ta da fada

“Wani sabon iskanci ne zaki fito min a haka lokacin da mijina ya kusa dawowa? Common go and change.”

Rita da bi jikinta da kallo sannan ta kalli Gimbi a yatsine sannan ta koma daki. Ita fa ba don Ovi ta nace tazo gidan ba babu abin da zaisa ta zauna ana mata cin kashi. Amma bari dai hakarsu ta cimma ruwa.

A falon suka bararraje ana ta ciye ciyen kayan kwalama da Gimbi ta saya musu. Binsu take yi da kallo dadi na ratsa zuciyarta saboda yadda take son yaranta. Daula wadda ta tafi fitsari tun shigowarsu ta kwala mata kira daga ciki. Yanayin kiran yasa ta tashi da sauri ta nufi dakin da take. A korido suka hadu Daula tana nuna dakin Maamu

“Mummy Maamu bata nan”

Tsaki ta ja da karfi tana hararar yarinyar “saboda haka kike yi min wannan mugun kiran? Daga zuwa fitsari me ya kaiki dakinta”

Daula ta sunkuyar da kai. Gimbi tayi gaba zuwa dakin Maamu tana ta surutai. Rashin ganinta a dakin bai dameta ba tayi tunanin bandaki ta shiga. Sai ta kula babu haske. Kamar ta fita sai ta koma ta buga kofar da karfi

“Maamu” ta kwala mata kira kamar sa’arta. Shiru taji ranta kuwa ya baci.  Jiya ta sake zuba mata wani maganin kwantar da zuciya wanda zata mallaketa kamar yadda ta mallake danta. Shine kuma taki amsa kiranta? Lallai da sake. Tura kofar tayi inda taji tsamin abinci ya bugi hancinta. Da sauri  ta kunna fitila sai ga kwandon shara ya soma cika da abinci ya lalace.

STORY CONTINUES BELOW

Baki Gimbi ta rike tana gyada kai “wato kwana ukun nan matar nan asara tasa na dafka. Kaddai ace bata cin abincin tun na ranar da na soma saka maganin”

“Mummy me kika ce?” Daula ta kura mata idanu.

“Babu komai kirawo min Rita”

Bata jima ba suka dawo tare harda su Haris ta tsegumta musu Maamu bata nan.

“Kinga fitar Maamu ne?”

Murmushi da soma yi domin duk yadda Gimbi taso boyewa kana kallonta kasan hankalinta a tashe yake. Boka yace kada ta bari Maamu ta fita daga gidan. A haka ne zata fi iya juya Awaisu hankali kwance.

“Anzo an tafi da ita”

“Me?”

“Waye yazo?”

“Ina aka kaita?”

A gigice take maganar Haris da yafi sauran wayo shima hankalinsa ya tashi. Amir kuwa kuka ya saka

“Mummy ko saceta akayi? Sai da nace miki mu tafi da ita Park  din kika ki”

“Rufe min baki” ta daka masa tsawa sannan ta koma ga Rita ta sake tambayarta waye ya dauki Maamu.

“Baban Rumana ne fa.”

“Harisu yazo gidan nan? Yaushe?”

Yau ko dan jarida ya shafawa Gimbi lafiya a tambayoyi. Rita ta fada mata cewa sun zo babu kowa suka fito da ita suka tafi.

“Haba Rita bayan kinsan komai yaya zaki bari su tafi.”

Wayarta ta dauka ta tafi daki harda rufe kofa. Awaisu ta kira tana kuka ta fada nasa Harisu yazo ya dauki Maamu batare da saninsu ba.

Yana cikin office har lokacin ya nuna mata babu matsala zai kira shi dama sunyi magana.

A harzuke tace “da saninka dama yazo. Shine zai tafi da ita don a nuna ni ban iya kula da ita ko me?”

Jin ta fara fada ya soma bata hakuri. Haka nan ya hada kayansa ya tafi gida batare da yasan me zuciyarsa take ji game da tafiyar Maamu ba.

*****

Duka ‘yan uwan Harisu mata ya kira a waya yace komai dare idan mazansu sun amince yana bukatar su zo gidansa. Kowacce hankali a tashe ta nemi izini ta tafi. Sannan ya kira wani cikin yaran kawunsa da ya rasu yace a bawa Baaba Hure waya. Bayani yake son yi mata sai kuka ya kwace masa. Me zai fada to. Ya ga Maamu a yanayin da zaka rantse  ta fito daga kasashen da yunwa tayiwa kamun kazar kuku ne. Rama ce irin wadda ake nuna mutanen a TV ace a taimaka musu rashin kwanciyar hankali a kasarsu ya hade da yunwa.

Baaba ta razana sosai da jin kukansa. Mutum babba kamarsa yana kuka tasan babu lafiya.

“Harisu kaine kake kuka kamar ba namiji ba? Me ya faru?”

“Maamu ce”

Zumbur ta tashi daga zaune ta tsaya baki na karkarwa  “wani abun ne ya faru?”

“Na daukota Baaba. Don Allah ki taho gobe”

Baaba duk ta tsorata ko rasuwa tayi ya boye mata ta soma kuka itama. Maamun ya kalla tana kwance a bayan mota inda yayi mata pillow da babbar rigarsa. Idanun nan duk sun.shige loko sai jirwayen hawayenta yake gani yana jika rigar tasa. Wayar ya dan kara mata a kunne tayiwa Baaba Hure sallama.

Ajiyar zuciya Baaban tayi tace mata gobe da asuba zata taso.

Matarsa ta uku wadda dama yau girkinta ne ya kira ya sanar da ita suna hanya ta fadawa kowa. Sannan ya umarceta tayi abinci mai rai da lafiya yana tare da Maamu. Jin sunan Maamu ta fita da sauri ta sanar da abokan zamanta. Rumana na jin haka tace a bata mukulli zata gyara mata daki.

Su Anti Baraka kusan tare suka shigo gidan da kannenta suna mamakin wannan kira na Harisu. kamar hadin baki ma da niyar kwana duka su ukun suka taho don sun san babu lafiya.

Shadayan dare ta wuce suka iso kusan duka gidan aka fito tarbarsu. Motar yarabsuka kusan rufewa suna ihun Maamu tazo. Sai dai me. A bayan mota take kwance kai kace karamar yarinya ce saboda yadda ta kankance. Anti Ummukulsum ce tace kowa ya matsa ta mika hannu ta riko Maamu. Ai tana fitowa da ta kare mata kallo bata san lokacin da kuka mai sauti ya kwace mata ba.  Nan fa sauran suka matso kowa ya ganta sai kuka. Maamu sai murmushin yake take yi

“Ban mutu ba Kaltume, meye na kukan”

Rumana kusan bangaje iyayenta tayi tazo ta rungume Maamu. Sai a lokacin Maamun ta soma nata sabon kukan. Harisu kasa hanasu yayi shima zuciyarsa tayi rauni. Da taimakon Rumana Maamu ta soma tafiya zasu shiga cikin gida sai ga zaninta yana neman faduwa saboda yayi mata yawa da nauyi ta kasa daurawa. Duk wanda ya kula da hakan sai da kukansa ya karu don tausayi.

Suna shiga ciki dakinta aka kaita sannan aka kori yaran don sun cika dakin. Cewa tayi duk su dawo babu mai fita yau Allah Ya yaye mata kadaici.

Abinci aka jere mata tuwon semovita ya tuku da kyau an kulla a leda da miyar kuka wadda taji daddawa da wake da naman kazar da tsabar dahuwa yasa ya soma fashewa. A wani flask ga kunu mai zafi sannan ga kayan tea da ruwan zafi da bread.

“Idan akwai abin da kike so Maamu ki fada na dafa miki” cewar Anti wadda tayi girkin.

Godiya tayi mata tace wannan ma ya isa. Wai ita ce da wannan kwanuka a gabanta duk nata ne taci iya cinta. Lallai ashe da ranka da lafiya da kuma matsayi da mukami lomar abinci ma sai Allah Ya yarda zaka samu. Ita da arzikin danta ya isa ace tana daukar dawainiyar wani ma ta fanin ciyarwa ita ce ta koma haka saboda yunwa. Rumana ce ta zuba mata abincin har lokacin tana zubar da hawaye da takaicin me yasa ta gudu ta bar Maamu. Dama sun dade da ramewa su biyun tun kafin ta taho amma abin yayi muni yanzu da ta ga Maamu.

Abinci Maamu taci sosai ta kora da kunu sannan ta bukaci ruwan wanka don ko sallar magariba basuyi ba bare isha. Cikin ‘yan matan kannen Rumana wata ta kai mata ruwa ta sirka mata. Mama ta kaita bandaki ta dawo suka hau maganar wannan abin al’ajabi. Harisu yana jinsu yace suyi shiru sai Baaba ta dawo gobe zaa san me ya kamata ayi amma tabbas zaman Maamu ya kare a Abuja. Suna wannan tattaunawar ne Rumana ta shigo a guje. Dama a kofar bandakin ta tsaya tana jiranta.

“Baba ga Maamu can tana ta amai”

A gurguje suka fito dukkansu suka nufi bandakin inda suka sameta a bakin kofar tana durkushe tana amai ta baki ta hanci. Cikin kankanin lokaci ta galabaita sosai tana neman fita daga hayyacinta. Abinka da mata sunfi yawa a ciki sai koke-koke da salati suke yi.

Harisu ya kinkimeta Abba ya fito da mota ya sakata a ciki suka fice sai asibiti.

*****

“So nakeyi ka kira Harisu kace ya dawo min da Maamu yadda yazo ya dauketa”

Gimbi ke wannan furuci tana karkada kafa daga zaune a gaban Awaisu. A ladabce ya ke bata amsa

“Kiyi hakuri nasan zai dawo da ita”

“”Wai kai baka ji haushi bane yazo har gidanka don gadara ya dauke maka uwa. To meye nufinsa?”

“Naji haushi mana, tunda ranki ya baci nima naji haushi amma nasan baiyi da wata manufa ba. Don ma ina ta kiransa ne bata shiga da tun dazu na ce gobe ya dawo da ita”

Tsaki ta buga masa ta tashi. Gashi dai ta mallake shi amma ita bata jindadin yadda ya zama baya iya wani tunanin kirki akan komai sai tayi magana. Maimakon yaji haushi sai wani shirme yake yi mata.

Wani asibiti suka nufa nan cikin garin Fika. Suna zuwa Harisu ya dauko Maamu ya shiga da ita. Likita aka kira yana ganin yadda take ya fara bawa nurses umarni. Haka suka rinka guje-guje a dauko wannan a dauko wancan. Ba su suka samu ta dan daidaita ba sai gabanin asuba don sumanta biyar. Likitan kansa ya jigata. Harisu ya nema yace lallai su kaita babban asibiti a cikin Damaturu don gaskiya tana cikin mawuyacin hali. A ambulance aka sakata suka bi bayansu shi da Abba da Anti Baraka.+

A hanya suka kira gida wanda suma duka sukayi kwanan tashin hankali suka fada musu an canza asibiti. Dama ana kokarin hada musu abin karin kumallo ne.

Suna isa gado aka turo domin daukarta ganin a ambulance aka kawo mara lafiyar sun san abin babba ne. Wata likita ce akan Maamu tana ta gwaje gwaje. Jininta ma da kyar aka samu don an bulata yafi sau shida basa samun jinin yadda suke bukata. Maamu ta galabaita iyaka don ko magana ta kasa yi sai hawaye akai akai da yake zirarowa ta gefen idanunta. Kusan awa biyu sannan likitan ta fito ta tafi office dinta tana yarfe gumi. Tun kafin ta fita iyalin Harisu suka iso suna ta koke-koke don kallo daya zaka yiwa Maamu kayi tunanin kafin ka matsa ta cika. Cikin yaran ma mutum uku aka taho dasu harda Rumana wadda tafi kowa kuka. Idanunta sun kumbura sosai ga ciwon kai matsananci.

Wani mutum wanda da alama masinja ne yazo ya kira Harisu zuwa ofishin likitar. Yana shiga godiya ya fara yi mata amma bata ko amsa ba ta jefo masa tambaya.

“Mene ne tsakaninka da mara lafiyar nan?”

Dan gyara zama yayi yana tsoro me zata ce ya sami Maamu “Babata ce”

“Babarka? Babarka?? Amma shine….” Ta soma magana murya na rawa sai ga hawaye shar. Hannuwanta biyu da ta dora akan tebur din gabanta tasa ta rufe fuskarta.

Harisu yayi mamaki sosai don sai da ta kwashi kusan minti uku kafin ta ita daidaita kanta ta dago jajayen idanu tana masa wani irin kallo cikin bacin rai

“Lokuta da dama sai ace likitoci suna kashe marasa lafiya bayan kune ba kwa tashi kawo su asibiti sai lalura ta cinyesu”

Harisu ya dubeta “hakane likita amma kowa kika gani baya rasa dalilin faruwar hakan”

Dr. Yana bata san lokacin da ta daga murya ba don ba karamin haushin ‘yan uwan Maamu taji ba a irin yanayin da ta ganta.

“Malam babarka tana cikin mawuyacin hali zaka ce kana da dalili? Wannan ciwon fa ba na lokaci daya bane”

hannu tasa ta fara masa lissafi da yatsunta

“Kaga da farko jininta yayi mugun hawa ina tsoron Allah Yasa kada ta sami matsala a zuciya, na biyu ulcer tayi mata mugun kamu har kirjinta ta taba, na uku malaria ta jima da shigarta baa dauki mataki ba. Na karshe shine malnutrition. Wallahi kun zalinci matar nan ba kadan ba”

Duk da fada take yi wani hawayen ne ya taso mata. A awa biyun da ta tsaya kan Maamu tasan ba karamin jin jiki take yi ba. Matar da ko tari ta kasa yi saboda kirji ya rike.

Dr. Yana mace ce mai matukar tausayi da jinkai. Asibitin suna ji da ita. Duk tausayinta kuma a tsaye take bata bata sake da aikinta. Idan kaji ana Dr. Barrister to da ita ake don idan taga mara lafiya kamar akwai cutarwa cikin lamarinsa to fa ta tsaya masa kenan ayi ta dauki ba dadi da ita. Zuwanta kotu yafi a kirga bada shaida idan aka cuci mara lafiya.

Shi dai Harisu tunda ta hau lissafi yake salati. Karamin tsaki ta ja don a ganinta aikin banza ne. Da can baa kula da ita ba sai yanzu da ciwo ya gama cin karfinta.

Mikewa tayi tsaye tana masa nuni da kofa “muje  ka sallami masu kukan nan domin damunta kawai zasuyi. Sannan akwai irin abincin da nake so a rinka bata musamman madara saboda ulcer din.”

STORY CONTINUES BELOW

Kai ya gyada ya bi bayanta. Haushin Awaisu yake ji ta yadda da zai ganshi a lokacin baiga wanda ya isa ya hanashi kai masa duka ba. Anya yana ma cikin hankalinsa kuwa. Maamu ce fa mahaifiyarsa. Matar da aljannarsa take tattare da farincikinta.

Da suka karasa kofar dakin sanar dasu yayi su tafi dama shima kukan nasu ya ishe shi. Nan suka fara shawarar masu zama tunda akwai tafiya. Suwaiba autarsu Harisu da uwargidansa aka bari. Yaso zama suka dage akan lallai ya tafi gida ko wanka yayi saboda tafiyarsu ta jiya. Rabonsu da abinci shi da Abba tun jiyan kafin su kama hanyar Abuja. Sai da sukayi musu siyayyar kayan bukata musamman na Maamu suka dau hanya da alkawarin dawowa da sassafe.

*****

Tsaki Gimbi tayi don ganin Awaisu har yanzu yana kwance tun bayan sallar asuba akan abin sallah. Tsaya masa tayi a kansa ta soma mita

“Hala dai yau baka da niyar zuwa aiki?”

Kansa ya rike duk da a kwance yake “Gimbi I feel sick. Jikina duka babu kwari ga fargaba da take damuna na rasa dalili”

Jin ya dauko zancen da take so yasa ta zauna a gefensa ido ya ciko da kwalla zata yi masa kuka “Nasan rashin Maamu a kusa da kai ne yake damunka. Ni kaina abin ya dameni. Kuma ko ka yarda ko kaki yarda dan uwanka bai kyauta ba. Maamunmu ko shine ta haifa tunda a gidan nan take bai kamata ya dauketa bamu sani ba.”

Shiru Awaisu yayi yana nazarin maganarta. Ta kuma rissina kai ganin zancen ya soma shigarsa.

“Ni yanzu ta yaya gidan nan zaiyi min dadi babu Maamu? Na riga na saba da ita kamar mahaifiyata. Tana bani shawarwari wanda naga amfaninsu sosai. Ko ba don kanka ba ka dawo min da Maamu zanfi samun kwanciyar hankali “

Kukan munafurci ta rinka yi hawaye kamar famfo. Hankalin Awaisu ya tashi yayi ta bata hakuri da alqawarin zai dawo mata da ita. A gabanta ya rinka kiran Harisu yaji shiru ba amsa. Yace tayi hakuri zai kara nemansa zuwa anjima. Murmushi tayi masa ta fita daga dakin. Zuciyarsa ya ji ta sake shiga kunci sai dai ya rasa meyasa tafiyar Maamu tayi masa dadi maimakon yaji bacin rai. Har kasan zuciyarsa yana jin zamanta wurin Harisu ya fiye masa kwanciyar hankali.

*****

Bayan kwana biyar Rita tana goge falo taji sallama. Bata ankara ba Haris ya taho a guje har yana bangajeta saboda muryar da ya gane. Wadda ya gani ya nufa da gudu sai kuma ya tsaya turus alamun kunya an fara zama samari ya kasa karasawa. Murmushi ta sakar masa kafin tayi magana su Daula taji suna kokarin kayar da ita. Rungumesu tayi don tayi kewarsu duk irin tsiyar gidan.

Ihun yaran ya fito da Gimbi daga daki da waya a kunne suna magana da wata kawa da tayi a gidan Bokan Ovi. Sakin wayar tayi ba shiri tare da wangale baki a dan tsorace

“Laminde”

Laminde ta dan murmusa fuskarta babu yabo babu fallasa. Jikin Gimbi yayi sanyi ta daure tace yaran su saketa haka ta wuce ciki su gaisa sosai.

Laminde ta bi bayansu suka shiga ciki. Ajiyar zuciya tayi da ta tuna yininta na karshe a gidan da yadda al’amura suka kasance. Rabonta da Abuja tun da aka sallamota daga asibiti gashi har an bawa shekara baya. Da ta koma gida ne Allah Ya kawo mata miji tayi aure. Karamin ma’aikaci ne a wani kamfani amma an basu gidaje a Quarters din kamfanin kanana saboda nisa. Shine tazo ganin su Maamu.

A kan kafet ta zauna Gimbi tana ta tsaneta da idanu har sai da tayi danasanin zuwa. Har ga Allah lamarin Maamu ya tsaya mata a rai kuma shine musabbabin zuwanta ta duba baiwar Allah.

Gimbi ta hakimce akan kujera sannan ta sa yaranta suka bar falon suna ta kunkuni. Bayan sun fita ta kalli Laminde

“Ince ko dai lafiya kika zo. Idan aiki kika dawo ni na dade da daukar wata”

Laminde ta kalli Rita. Mace har mace tasa kananun kaya irin wannan tana yawo a cikin gida wai ‘yar aiki a zamanin nan da kafin shaidan yazo zukata sun riga sun gama rauni da sabon Allah.

STORY CONTINUES BELOW

“Na shigo garin ne na leko mu gaisa” tana magana tana dan waige waige ko zata ga giftawar Rumana ta tambayeta Maamu.

Tabe baki Gimbi tayi “basa gidan wadanda kika zo ganin. Sai ince a gaida gida ko tunda ba wurinmu akazo ba”

Laminde ta fahimci korarta akeyi ta soma haramar tafiya. Wani dan saurayi taga Rita ta shigo dashi yana ta dariya suka gaisa da Gimbi da gani sun saba wasa da dariya. Tape ya dauko dama da bironsa a saman kunne yace “Hajiya Gimbi sauri nakeyi fa kizo na gwadaki na bar mutum yana jirana a waje”

Sam ta ma manta da Laminde bata fita ba tace “Kezy ka rainani fa. Ni zan karaso nan ko kai zaka zo”

Da murmushinsa ya karasa gabanta ta mike tsaye. Karamin mayafin da yake kanta ta daure a saman kan dama bai kare komai ba. Nan tela ya hau gwajin dinki fa. Haka ta rinka daga hannuwa yana zagayeta tana cewa so take rigar tayi mata das a jiki saboda dinkin kece raini za’ayi. Laminde ji tayi wani abu ya tsaya mata a wuya. A cikin ranta ta zabgawa Anti Bebi tsinuwa. Tabbas ko da can Gimbi ba wani kirki gareta ba amma ko kadan halayyarta bata yi kama da ta Gimbin yanzu ba.

Sa kai tayi zata fita ta kusa karo da mutum. Da sauri ta kauce Awaisu ya shigo baya ko ganin gabansa da kyau don ko bi ta kanta baiyi ba bare yaji gaisuwar da take yi masa. Gimbi ya kalla da Tela ana nan ana ta gwaji amma ko a jikinsa bare ya hana. Laminde da tayi zaton za’ayi tashin hankali akan wannan gwajin wulakancin sai taji yace

“Inata kiran wayarki baki amsa ba”

Ta dan bata rai “tana daki bana son damu ne”

“Ai gara ki rinka hutawa. Dama takarda aka kawo office dinmu zan cike sunayen masu zuwa workshop Lagos jibi. Shine nayi ta kira in tambayeki nasa sunana ko kuwa”

Kezy Tela ya kwalo idanu yana jin ikon Allah. Duk tsagerancinsa abin ya daure masa kai. Gimbi ta kula dashi da Laminde mai tafa hannuwa daga kofar shigowa falon sai ta fakaice da cewa “amma dai abban Haris ka iya rigima. Wato don kada nace ka tafi ka barni ko. To na yarda kasa sunan amma idan kaje babu ruwanka da yan mata”

Kai ya dan rissina yana mata godiya ya kuma fice. Laminde tabi bayansa ta tsaya suka gaisa da maigadi. Nan yake fada mata ko sati Maamu batayi da tafiya ba. Duk tausayin Maamu ya kamata tace ko akwai number da zata iya samunsu yace bashi da ita. Daga nan tayi masa sallama ta tafi.

*****

Dr. Yana ce ta kalli su Baaba Hure tana ta bata rai “wai don Girman Allah waye wannan Awaisun ne? Haba baiwar Allah tun da ta farfado kullum sai ta kira shi kunki ku kawo mata shi. Mara lafiya na bukatar kulawa bare ma ita da abu yake neman kaiwa zuciya. Indai ba mutuwa yayi ba ku kira mata shi don Allah”

Maamu tana daga kan gadon sai kalmar mutuwa taji ai kuwa ta soma kuka tana cewa shikenan ta kashe shi. Anti Ummukulsum ta gallawa Dr. Yana harara.

“Wai ke wace irin likita ce kullum sai anyi fada dake a dakin nan. Dame kike so taji ne. Ciwon ko irin wannan maganganun naki”

Nurses biyu da suke tare da ita suka soma dariya. Indai da sabo su kam sun saba da jajibo rigima irin na Dr. Barrister. Kanta tsaye take gabatar da komai nata shiyasa wasu basa fahimtar ta. Ga yan uwanta kuwa cewa akeyi gaboncin ‘ya’yan fari ke damunta.

Tsuke baki tayi ta maida hankalinta ga Baaba Hure.

“Iya don Allah idan da hali ku kira mata wannan Awaisun ku huta itama hankalinta ya kwanta mu samu ta warke da wuri. Kwanaki haka aka kwantar da wata a dakin nan kuma kan gadon nan ma itama tayi ta kiran mijinta iyayenta suka ki sanar dashi wai saboda ya sakota. Ranar nazo dubata tace in fada masa ya yafe mata amma sharri kishiyar ta kulla mata. In gaya miki washegari ta cika. Iyayenta suna ta kuka da mijin yazo yana son neman gafararta ya gano gaskiya suna cewa da ma sun sani sun hadasu sunyi maganar karshe gashi ta tafi ba’a cika mata burinta ba”

Harisu yana bakin kofa zai shigo yaji tana wannan labarin ya rike baki. Kullum burinta ta tsorata su ne, me zai sa ta rinka dauko zantuka irin haka. Shi kam dole ya nemi babba a asibitin a canja musu likita. Baaba Hure tana hada ido dashi ta taso

“Harisu don Allah ka sanar da Awaisu halin da Maamu take ciki kada ta cika bai nemi gafararta ba”

Dr. Barrister ta murmusa daga gefe. Ko da bata jin yaren taji an ambaci Awaisu ga kuma alamun tsoro a idanun Baaba Hure. Ba don Maamu na jin jiki ba so take ta tambayeta labarinta taji kwaf don a yanzu duka bata yarda dasu ba. A ranta tace kowa cikinsu mulmul dashi sai ita kadai a wannan mawuyacin yanayin.

Bayan ta fita ne Harisu ya zauna a gefen gadon Maamu yana kare mata kallo. Tun zuwansu jininta yaki sauka shi kuma yayi rantsuwa bazai kira Awaisu ba kamar yadda ko waya idan yayi masa baya dauka. Duka ‘yan uwansa ya umarcesu kada su kuskura su sake daukar wayarsa. Idan ya damu da ita ya biyo bayanta. Baaba Hure tace ita dai idan har ta isa dashi to a yau take so ya kira Awaisu ya fada masa. Zuwansa ko rashin zuwan ya rage nasa. ‘Yan uwan Maamu suma Harisu yace da farko kada a fada musu sai ta dan murmure don a haka bai san inda magana zata tsaya ba. To a yadda Dr. Barrister ta tsorata Baaba suma sai tace a fada musu. Tunda yanzu idan ta rasu basu da madogara zaace ya daukota babu wanda ya sani.

Dan kallonta yayi sannan yayi murmushi tare da kwafa  “waccan shu’umar likitar duk ta birkita miki lissafi. Zanyi yadda kika ce Baaba in sha Allah”

Sauran ‘yan uwansa dake dakin da iyali suka goyi bayan a sanar din shi yafi ko don gudun zargi nan gaba.

Duk abin da akeyi Rumana tana gefe don kullum sai tazo saboda shakuwarsu da Maamu. Shima Harisun baiyi tunanin hanata ba. Tausayin Maamu take ji sosai a ranta ta fita daga dakin ta bar iyayenta suna magana. Wani dakali ta zauna tana ta tunanin irin ukubar da suka sha a Abuja.

Dr. Yana ta dawo daga wurin Director na asibitin yayi mata kashedi sosai akan yiwa marasa lafiya katsalandan ta fito rai a bace tana kumburi. Rumana ta hango kuma ta gane yarinyar mai shegen kukan nan ce a dakin da ta baro dazu. Wani birki taja tare da komawa ta dafa kafadar Rumana.

A dan firgice ta dago sai ta maida kai da ta gane wace. Dr. Yana ta zauna a gefenta ta fara mata nasiha akan cuta ba mutuwa bace da sauransu. Sai da ta gama ta hau bugun cikin Rumana akan alakarsu da Maamu. Rumana an sosa mata wurin da yake mata kaikayi nan fa ta hau bayani tana kuka ta zayyanewa Dr. Barrister alakarsu da zaman birnin tarayya da suka yi.

“Jakar uba….amma kuna da hakuri wallahi. Har naji babanki yayi daraja a idona “

Saurin dagowa Rumana tayi wanda yasa Dr. Barrister ta dan wayance “kara daraja yayi nake son cewa. Dama da darajarsa na ganshi”

Tashi tayi ta koma office dinta tana ta tunani. Gaskiya taimakon irin wadannan jihadi ne fa wanda bata so a barta a baya. Kai dole ma ta shiga a dama da ita saboda wannan dattijuwa mai siffar salihan mata bata cancanci cin kashi daga wurin surika ba.

“Yadda kika kashe fitilar zuciyarta ina mai tabbatar miki da taimakona kece zaki zauna a cikin duhun ba ita ba” ta fada a fili tana kallon ceiling din office dinta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page