DR TAHEER CHAPTER 4 BY UMMU ASHRAF

DR TAHEER CHAPTER 4 BY UMMU ASHRAF

            Www.bankinhausanovels.com.ng 

Washegari umma ta tura Layla dakin Taheer..ganin har wajen 11 bai fito ba..tace aje a gano ko lfy..Layla na shiga Kai tsaye dama bedroom dinshi ta nufa…yana kwance kan bed…ya kudundune cikin bargo..sai rawan sanyi yake…da gudu Layla ta haura kan gadon ta yaye bargon tana kallonshi tace”innalillahi wainna ilaihi rajiun..daddy meke damunka”…a hankali Taheer ya shiga kokarin mikewa zaune amma ya kasa…sai kawai ya koma tareda sake kwanciya…Layla ta fashe da wani matsanancin kuka tace”na shiga uku…daddy wai meke damunka haka”sai Kuma ta shiga kokarin sauka daga kan gadon tace”Bari inje in Kira umma”…tun kafin ta sauka Taheer yai karfin halin mikewa ya dawo da ita kusa dashi…ya rike hanunta gam cikin nashi…yanason yin mgn Amma ya kasa…a hankali ya maida idonshi ya lumshe kawai sai ya fara hawaye…baison yin kuka gaban

Layla..amma he couldn’t stop himself…hawaye yakeyi sosae kmr karamin yaro…Layla ba karamin tashin hankali ta shiga ba..ganin yanda yake hawaye…ta dora duka hannayenta a Kai ta sake rushewa da uban kuka tace”na shiga uku na lalace…kuka fa kakeyi daddy..don girman Allah ka fadamin mene matsalanka…meke damunka haka da har zai saka kuka daddy.. pls tell me”…a hankali Taheer ya bude idanunshi yana kallonta..kuka takeyi da gasken gaske…hakan Kuma ba karamin hurting dinshi keyi ba…ya gwammace yaita zama cikin yanayin da yake ciki yanxu..da dai tayita kuka haka…da kyar ya tattaro sauran energy dinshi ya janyota jikinshi..ta rungumeshi tsam tana ci gaba da kukanta…a hankali yasa hannayenshi ya rungumeta shima…sun dauki kusan 3 mins a haka kafin ta dago..idanunta a kanshi still bata dena hawayeba..kafin tayi mgn Taheer yai cupping fuskanta da hannunshi yace”banason kukan nn baby…I’ve told you babu abinda ke damuna…but definitely idan zaki cigaba da wnn kukan komai ma na iya faruwa Dani..you have no idea yanda zuciyata keyi idan kina kukan nan..sai ya saki face dinta ya kama hannayenta gam yace”ki taimaka min ki dena  domin Allah baby…bazan iya daukaba wlh…abubuwan zasumin yawa plss”…da sauri Layla ta shiga goge tears dinta tana girgiza Kai tace”na dena kukan daddy…bazan karaba InshaAllah…but daddy don Allah mene ke damunka…ko ince umma ta kira doctor ya dubaka…or better still in Kira maka dr.salees yazo ya dubaka…inada number dinshi ay”…lokaci daya Taheer ya hade rai jin abinda tace…ya kalleta a kausashe yace”wane dr.salees?…Layla tadan buda ido snn tace”dr.salees na clinic dinka mana daddy… friend Dina ne a…bata karasaba yasa hannu ya buge Mata bakin…yana Mata mugun kallo yace”don’t you dare..kar ki kuskura ki sake cemin wani namiji is your friend…Layla na shafa bakin daya buga da hanunta kmr zatayi kuka tace”to kayi hakuri daddy”…Saida ya koma ya sake kwanciya snn Mata”you can leave”…ta kamo hanunshi tace”daddy nace kayi hakuri fa”…idonshi a kulle yace”naji…ki tashi ki tafi baby I want to sleep”…ganin yanda yai mgnr rai a bace ta sauka a gadon zata fita..ta sake juyowa tana kallonshi kafin tayi mgn yace”baby leave..don’t let me repeat my tself”…bata sake yunkurin mgn ba ta fice daga dakin… yanajin ta fita ya mike da kyar ya sama kofan key snn ya koma ya sake kwanciya…yasan for sure zata fada a halinda taganshi and ko ummi batazoba yasan umma sai tazo…shi Kuma bai shirya amsa tambayoyin da zasu fito a bakin umma ba so it’s better ya rufe kofanshi kawai…he needs to be alone and think of a way out of this mess.+

Har yamma Taheer bai fito ba…duk anje part dinshi Kuma yaki bude kofa…both umma da ummi are very worried…Layla kuwa dama baa mgn..don tun dazu take musu kuka wai a Kira doctor yazo gida ya dubashi…Saida umma ta kusan maketa snn tayi shiru…but har zuwa yanxu bata bar hawaye ba…she is so worried about halinda taga daddy a ciki..she can’t stand seeing him like that…she can’t.

Suna nan zaune jigum sai gashi ya shigo bayan isha’i…yanata kokarin boye damuwan dake fuskarshi ya shiga binsu da kallo…kawai sai ya fashe da dariya ganin yanda suke zaune kmr gidan mutuwa…a fusace ummi tace”bakada kirki wlh Taheer…ya zaka sanyamu a damuwa snn kazo kana mana dariya sai kace abokan wasanka…Taheer ya Dan tsgaita da dariyan…ya samu wuri ya zauna snn yace”well am sorry ummi…kune kuka bani dariya Naga kunyi jigum kmr gidan makoki…tsaki ummi taja snn ta mike zuwa dakinta…cikin ranta kuwa tasan duk dariyan nn da yakeyi…yake ne…zuwa yanxu ba karamin tausayi yake bata ba…she prays maganin da aka bashi yayi aiki…tasan InshaAllah zai Dena duk damuwan da yakeyi..don ita har ga Allah tunaninta baida lfy ne…shiyasa baya sha’awan yin aure.

STORY CONTINUES BELOW

Bayan ummi ta tafi ya koma kusada umma ya zauna tareda kamo hanunta yace”ba komai fa umma..bacci ne kawai ya daukeni”…dukda umma bata yadda da abinda yace ba…bata nuna mai ba…sai ta shafa kanshi tace”shknn…but don’t try anything like this again Taheer…you scare the hell out of us”…Taheer na murmushi yace”bazan Kara ba umma”…bata sake mgn ba ta mike itama zuwa daki… Layla ta taso a hankali ta dawo kusa dashi tace”daddy are you sure ba abinda ke damunka Kuma”..Saida yai pecking dinta snn yace”am pretty sure baby..so ki dena damuwa okay?…tana murmushi ta daga mai Kai itama snn ta fada jikinshi tace”I love u daddy”

One week ltr…

Bikin Taheer da Sameera saura sati 3 ciff…both bangarori nata shirye shiryen biki amma Banda Taheer…Saida ummi tayi da gske snn aka samu yaje ya ba Sameera duk abunda take bukata na biki…ya kuma tabbatar Mata da ko event daya bazaiyi attending ba…ita kuwa ummi cewa tayi a Dena bi takanshi…shirye shiryensu sukeyi hankali kwance itada umma.

Akwai events da suke arranging…ranan Thursday zasuyi mother’s Eve… Friday bayan daurin aure zaayi dinner da dare…bayan an kawo amarya staurday Kuma zaayi traditional day snn ayi welcoming amarya into their family.

Daidai da kayan da Taheer din zaiyi amfani dasu a bikin duk ummi ta tanada…don yadda taga yake iskancin nn tsaf zata iya tara mutane shi Kuma yazo ya bata kunya…Sam bazata yadda ya kunyatata gaban mutane ba.

Ana kawo invitation cards dama Yusuf ta Kira ta damkasu a hanunshi…tace lallai lallai ya rabama friends dinsu snn har clinics din da Taheer din ke aiki duk yaje ya Kai musu…harkan gabanta kawai takeyi batabi ta kanshi don bata son bacin rai…she have made up her mind Taheer indai ba mutuwa yayi ba…to bazaa fasa wnn auren ba(wlh kiyita shirinki ummi..muma duk kika gayyacemu biki zamuzo miki😌)…bazai yiwu suyita zuba mai ido yana zaune ba auren ba…shekara arba’in ai ba nan kusa bane..so yake sai ya tsofe Mata a gida..inaa Sam bazai yiwu ba.

Yau Taheer na zaune parlonshi bayan tafiyan Yusuf abokinshi…yazo kan arrangements din biki da zaayi amma Sam Taheer yace ba abunda zaiyi…Yusuf sai hakura yai kawai ya tafi…ya Kira ummi a waya ya sanar da ita yanda sukai da Taheer din…tace ya rabu dashi kawai…duk abunda ake ciki zata nemeshi.

Layla ta shigo dakin da tab dinta a hanu ta zauna kusa dashi tana nuna mai tab din tace”daddy tayani zaban gown din nn plss…inaso inyi order ne…next week kayan zasuzo”…ya amsa tab din ya shiga duba gowns din da take nuna mai…maimakon ya zabar Mata din saiya tabe baki yace”me zakiyi da wnn kayan baby?…ta Dan wara ido tace”na biki ne mana daddy…as your daughter ya kamata da bikinka ace nafi kowa yin kyau…nasan idan nasa kayan nn duk Wanda ya kalleni sai ya sake kallona sbd ba karamin kyau zasumin ba”…Taheer ya daure fuska tamau tareda kashe tab din ya ajiye a gefe yace”wato duk Wanda ya kalleki ya sake kallo abi?to bazaa sai kayanba”ta marairaice tace”daddy karka hanani plss…ba abinda nake nufi knn ba…Ina nufin ya kamata inyi kyau ranar bikinka”…ya sake girgiza Kai yace”na fada maki bazaki sa kayan nn ba…zan kaiki ki sai duk abinda kikeso kikai a dinka maki…amma bazan Bari ki sai wnn gown din kisa in public ba”…da sauri tace”daddy ummi fa duk ta siyamin irin wadan nn…shi wnn daban ne daddy…don Allah kar ka hanani…ya sake girgiza Kai yace”na fada maki bazaki sa wnn gown din ki shiga cikin mutane dashi ba baby…so kima dena pleading don ba canxa mind dina zanyi ba…nace bazaki sa ba and that’s final”…shiru kawai Layla tayi tana kallonshi kafin tace”toh”…da ganin yanda tai mgnr ba yanda zatayi ne…Taheer ya mike tareda daukan car key dinshi yace”tashi muje in kaiki ki siyo yanxu”…ba musu ta mike..Saida ta Sanya hijab dinta katoto snn sukama su ummi sallama suka fita…sai turo baki take ita a dole ya bata Mata plan…bata San me zata siyaba bayan uban kayan da ummi ta siya Mata Kuma…tasan ko zata shekara cemai tanada su ba yadda zaiyi ba so gara ma ta bishi ta zabo wasun kmr yanda yace don ko zata shekara mai bayani ba hakura zaiyi ba.

Gidan su Sameera suka fara zuwa…basu wani dadeba suka tafi don dama sako yaje Kai Mata…ran Sameera ba karamin baci yai ba…wai shi duk inda zaije dole sai ya tafi da wnn yarinyar me kamada aljanu ne??..dole ma tayi mgnin yarinyar nn wlh…

Kai tsaye inda suka saba siyayya suka nufa…Saida ta zabi duk abinda takeso ya biya kudin snn suka tafi.

Suna tafe a hanya ya kalleta yace”can I ask you something?..ta juyo tana fuskantarshi tace”of course daddy”…Saida ya maida kallonshi kan titi yace”will u miss me idan nayi aure?…lokaci daya mood dinta ya canxa…idonta har ya kawo ruwa…ita kadai inta zauna tana wnn tunanin har hawaye takeyi…bata taba nuna mai bane sbd tasan zai fita damuwa…tace”sai nafi kowa missing dinka daddy…am going to miss you like crazy…shknn idan kayi aure daddy ba Wanda zaina kaini skul…ba Wanda zaina zuwa dakina duk dare yamin addu’a snn ya kashe min haske…ba Wanda zai na petting dina idan nayi fushi…snn ba Wanda zaina kula Dani idan bani da lfy…duk kafi kowa iya kula dani in bani da lfy daddy…ummi tai tamin fada tana cewa na fiya raki da shagwab…sai ta kasa karasawa ta rushe da kuka…da sauri Taheer ya gangara gefen titi yayi parking…yasa hannu ya janyota jikinshi…shima kmr zaiyi kuka yace”no baby stop crying plss…I promise I won’t let you miss me even for once…I will come every night in saki bacci snn in maki addu’a in maki duk abinda na saba…first thing in the morning Kuma zanzo in kaiki skul…idan bakida lfy ma I will always be there for you…duk kike bukatan wani abu just let me know…zanyi maki without wasting of time…I will never let you miss me okay?so stop crying plss…I will talk to ummi ta bani ke kawai mu tafi tare…da sauri Layla ta girgiza Kai tace”ummi bazata yadda ba daddy and nima I don’t want to leave her all alone…she will be lonely without the two of us…so I prefer to stay with her”…Taheer na goge Mata tears yace”then stop this crying baby kinsan banaso… InshaAllah you won’t miss me okay?..ta daga mai Kai tana murmushi…shi Kuma yaja kumatunta yace”my cry cry baby…kuka baya maki wahala”…tai murmushi kawai snn ta koma seat dinta…shima ya gyara zama snn ya kunna motan suka cigaba da tafiya…deep down he’s thinking ita missing dinshi kawai zatayi…amma shi loosing dinta zaiyi for good.

Yau Friday…ya kama saura sati biyu daurin auren Taheer…Layla ta samu ummi ta sanar da ita Usman ya kirata…ya ce Mata akwai wani aiki daya kawoshi Abuja…so yanaso yazo ya ganta…ba bata lokaci ummi ta aika a gyara bq inda zaa saukeshi…ita Kuma Layla ta tafi daki ta shirya.

4 pm daidai Usman ya karaso gidan…Layla ta shigo dashi ciki…in no time aka cika mai gaba da kayan ciye ciye.

5 Taheer ya dawo gida…bayan ya gama duk abinda ya saba ya nufi part dinsu…ummi…umma duk suna zaune parlor…ya karasa shima ya zauna duk ya gaishesu…umma tace”ga abinci can a dinning”…ya wani langabe Kai yace”umma feed me plss…idan da kaina zanci bazan iyaci da yawa ba…ba musu umma ta mike tana murmushi tace”to muje dinning din in baka”..shima ya mike suka nufi dinning din…ummi na binsu da kallo tace”yo ba dole ma Layla tayi iskanc da ta6ara ba a gidan nn…kalli fa uban ma da kanshi abinda yakeyi don Allah…katoton namji kaman kai ka wanice bazaka iya cin abinci da kanka ba sai an baka…Allah ya kyauta”su dai basu ce Mata qala ba…umma ta shiga bashi abincin a baki har yace ya koshi…suna dawowa parlor Layla ta shigo ciki…Kai tsaye inda yake ta nufa…ta zauna kusa dashi tace”daddy Ya Usman ne yazo…he said I should ask you..wai yanaso ya kaini shopping”ta karasa mgnr kanta a kasa…shiru Taheer yai na ‘yan mintina yana binta da kallo…sai Kuma a hankali ya janye idonshi a kanta snn ya daga Mata Kai alaman she can go…da fara’a Layla ta mike tayi pecking left cheek dinshi snn tace”thanks my daddy”…snn ta juya da sauri ta fita…ummi ta kama haba tace”lallai yarinyar nn batada kirki…dubi yanda tayi kmr bata ganmu a wurin nn ba Aisha…tayi mgn da uban kawai tasa kanta ta wuce sai kace shi kadai ne keda iko a kanta…to zata dawo gidan nn ta sameni”…umma murmushi kawai tayi batace komai ba…shiko Taheer abun duniya duk ya isheshi…wani wai zai kaita shopping tsabar rainin hankali…sai kace an fada mai tana bukatan wani abun…zaman parlon ma yaji duk ya gundureshi…sai ya mike kawai ya fice zuwa part dinshi.

Layla bata dawoba sai after magrib…sukayi sallama da Usman ya koma…ba yanda basuyi dashi ya kwana ba amma Sam yaki yadda…ya fada musu akwai hotel da sukai lodging…so a can zasu kwana tareda colleagues dinshi…

Layla ta shigo gida da Kaya Niki Niki a hanunta…ta nuna ma su ummi snn ta wuce zuwa dakinta.

Washegari Nafeesa da iyalanta suka iso…wnn karon hadda maigidanta…zaibi flight din 6 zuwa Dutse.

6 din kuwa daidai Taheer ya kaishi airport ya wuce.

Gida ya fara cika…ko da yaushe cikin hidima suke…an gama hada lefe tun last week amma Taheer yace a Bari sai an shiga satin biki sai a Kai…ba don ummi taso ba haka ta hakura sbd magiyan da umma ke Mata

Bayan kwana biyu suna zaune gaba dayansu a parlor…Ramadhan ya shigo parlon hanunshi rikeda waya…ya mikama mamanshi yace”Mami gashi Abba na Kira”…da sauri Nafeesa ta amsa wayan tayi picking tareda sallama…tayi shiru tana sauraron abinda yake fada a daya bangaren…sai Kuma ta mike tsaye da sauri tace”Subhanalillahi”…duk suka dawo da hankalinsu gareta…ta sake yin shiru tanajin me yake fada kawai sai ta fashe da kuka tana”innalillahi wainna ilaihi rajiun”…gaba daya sukayo kanta kowa na tambayan abinda ya faru…ita Kam kuka kawai take tana salati…Saida tayi kusan 3 mins snn cikin sheshsheka tace”Umma Usman ne”…Duum Layla taji gabanta ya Fadi jin an ambaci Usman…da sauri ta karaso inda suke itama tana zare ido…a kidime ummi tace”Nafisa kiyi mgn mana…meya faruda Usman din?…”He is no more…yayi accident a kan hanyarshi na komawa gida”…Nafisa ta fada da kyar…gaba dayansu salati suka saki…ummi tace”ban gane yayi accident ba Nafisa…baa jirgi suka tafi ba dama?…Saida nafisa ta share hawaye snn tace”jirgi sukabi amma a kano suka sauka…a hanyanshi na komawa Dutse sukayi accident din”…lokaci daya duk suka gigice…Layla kuwa dama tunda taji ance he is no more…ta toshe bakinta da hannu tareda rugawa zuwa dakinta…ta fada kan gado ta shiga rusa kuka kmr ranta zai fita(am also crying baby😰)…kuka take tana tuna every single moment da sukayi spending tare…she remember irin yanda yake sonta…yanda yake riritata yana fada mata mata how much she means to him…”innalillahi wainna ilaihi rajiun…taketa maimaitawa tana jujjuya Kanta from one side to another.

A can parlor kuwa…Taheer da shigowanshi knn suka sanar dashi rasuwan…shi kanshi ji yai kaman kafafunshi bazasu iya daukanshi ba…yanxu Usman din ne ya rasu… innalillahi shima ya shiga fada har karshe sai Kuma ya mike zumbur yana kalle kalle….”Ina baby”ya fada yana binsu da kallo…nan da nan Kuma hankalin kowa ya dawo jkinshi…Sam ba Wanda ya lurada bata parlon…da sauri Taheer ya nufi dakinta…tana nan inda take Kuma har yanxu bata bar fadin innalillahi tana kuka ba…da hanzari ya isa kan gadon ya zauna tareda sa hannu ya janyota jikinshi…kmr abinda take jira knn ta rungumeshi gam tana Kara karfin kukan da take…su ummi duk suka biyoshi dakin suna kallon yanda take kuka…ba Wanda bata bama tausayi ba a cikinsu…Taheer daya rasa ta inda zai fara lallashinta kawai shima sai ya fara hawayen…Allah kadai yasan yanda yakeji sbd kukan nan da takeyi…abubuwa biyune suka taru suka tsaya mai…na farko kukan nata dako a mafarki bai son jinshi…sai Kuma kishin wanda takeyin kukan dominshi…dukda Usman din is gone amma ya kasa hana zuciyarshi jin kishin kukan nata…umma ce ta karaso inda suke tace”ya zaka sata a gaba kaima ka fara kuka Taheer…Kai daya kamata ka lallasheta Kuma sai ka biye Mata kuyita kuka sai kace ba namiji ba”…a hankali yasa hanu ya goge hawayenshi…itama ya dago fuskanta ya shiga share Mata nata…ta rike hannayen nashi a nata tace”daddy don Allah da gaske ya Usman ya mutu…da gaske ya tafi bazan kara ganinshi ba daddy?…still Yana share Mata hawaye ya daga mata Kai alaman yes…sai ta sake fashewa da wani kukan tace”Dan Allah daddy kace ba gaskiya bane…ummi Dan Allah kuce mafarki nakeyi ba gaskiya bane… yacemin zaizo daurin auren daddy…Dan Allah kuce masa kar ya tafi ya barni…he means a lot to me don Allah kar ya tafi ya barni”a hankali Taheer ya janyeta daga jikinshi tareda mikewa tsam ya fice daga dakin…bazai iya jin abubuwan da take fada ba sam…da sauri Nafisa itama ta fita daga dakin tana fashewa da kuka …she really feels for her daughter…wani tausayinta taji ya kamata… ummi ce tayi karfin halin karasawa inda suke ta kamo Layla ta rike da kyau tace”Dan Allah ki dena kukan nn Layla…so kike ki jama kanki wani ciwon…kiyi hakuri kiyi mai addu’a kinji”…kawai ta fada jikin ummi tana fashewa da wani kukan.(me neman kuka ne dama aka jefeshi da kashin awaki😹)

Taheer tunda ya shiga daki ya kwanta sai ya rasa inda zaisa kanshi yaji dadi…Allah ya sani baiji dadin mutuwar Usman ba amma bai San dalilinda yasa yakejin kishin kukan da Layla takeyi sbd shi ba…wnn ya nuna Layla na son Usman knn…wani abu yaji ya tokare mai a makoshi…gaba daya ji yake inama baije inda takeba.

STORY CONTINUES BELOW

Da dare Taheer ya shigo dakin Layla da har yanxu ummi da umma ke ciki…ya kalli Layla da dakyar aka samu tayi bacci bayan maganinda aka bata Wanda shine ya sata baccin…ya samu wuri ya zauna gabanshi na faduwan abinda zai fada yace”Ummi dama inaso ne ki Kira uncle ki fada mishi anyi mutuwa snn don Allah ummi kice mai inaso a dan daga bikin nn ko sati biyu ne a Kara kinga bazai yiwu ayi biki ana cikin alhinin mutuwa ba”…yana gama mgn yayi kasa da kanshi praying Allah yasa ummi ta yadda…umma na girgiza Kai tace”aah bai kamata a daga biki ba Taheer…Wanda ya mutu ya riga ya mutu addu’a kawai yake bukata”…a hankali ummi tace”aah Aisha bai kamata ayi biki a wnn halin ba…yaron nn fa shine yake neman auren Layla…ko don wnn bai kamata ayi bikin ba…zan Kira uncle din naka ko sati biyun sai a Kara”…wani dadi Taheer yaji da ya dade baiji irinshi ba…bai taba tunanin ummi zata yadda cikin sauri haka ba”

Washegari karfe 8 suka dauki hanya…wnn karon a mota suka tafi…ko a hanya ba Wanda ke cewa wani abu a cikinsu…Taheer na driving yana duban Layla data kudundune kanta wuri daya…har yanxu bata bar hawaye ba…”so she loves him this much”…ya fada a zuciyarshi…a wani bangaren Kuma yanajin dadin daga biki da ummi tace zaayi.

Sai yamma suka isa Dutse…zuwa lokacin an rigada ankai Usman gidanshi na gaskiya (Allah ka kyautata mana makwancinmu na gsky🙏🏻)

Mutane nata zuwa gaisuwa…yayinda duk Wanda yaga Layla sai ta bashi tausayi sbd yanda ta koma…kallo daya zaka Mata kasan mutuwar ba karamin girgizata yai ba.

Kmr yanda ummi ta fada…sunyi mgn da uncle din Taheer ta Kuma sanar dashi tanaso a Dan daga biki…da farko bai amince ba…sai daya baya yace shknn zaiyi mgn da magabatan Sameera ko one week sai a Kara.

Ranan da akai sadakan uku suka koma kano…gidan umma suka sauka…Saida suka koma Dutse ranan bakwai snn suka koma Abuja.

Zuwa yanxu Layla ta Dan fara warewa amma har yanxu walwalarta bata dawo daidai ba kmr nada.

A bangaren Taheer kuwa ga koshi ga kwanan yunwa…ga dai Usman din dayake gani kmr shi zai rabashi da Layla ya rasu…ga kuma shi bazai iya bude baki ya furta Yana sonta ba…gaba daya he’s confused…ga aurenshi dake Kara matsowa…har yanxu Kuma baiji yanason Sameeran ba.

Yau Tuesday Taheer tunda yazo office bai aikata komai ba…kmr yanda biki ke Kara matsowa haka matsalolinshi ke karuwa…shi kadai yasan yanda yake jin jikinshi these days…kullum da fever yake kwana ga ciwon Kai mai zafi ko baccin kirki rabon da yayi har ya manta…ya tabbata yanzu idan aka gwada BPnshi zai iya haura 200…damuwa har yawa suke mai ya rasa da wanne ma ya kamata yaji…yana kwance bedroom din dake office dinshi yaji ana knocking ta waje…ya danja tsaki snn ya mike ya fito…ya riga ya sanar da nurses kan bazai iya duba kowa ba yau and Dr.Eze is around…so baisan wayake mai knocking ba kuma yanxu…yana bude kofan ya juya ya koma ciki ba tareda ya tsaya ya ga wanda yai knocking din ba…a hankali Layla ta karaso ciki tareda ajiye basket din dake hanunta…tai shiru kawai tana kallonshi…duk ya rame…haka nan takejin tausayinshi…”Daddy”..ta fada a hankali…da sauri ya bude idanunshi dake lumshe ya azasu a kanta…sai Kuma ya sake maida idon ya rufe ba tareda yace kala ba…Layla tayi dan yi murmushi snn ta karasa zuwa inda yake…kan table din gabanshi ta hau ta zauna tana facing dinshi tace”daddy”…shiru ya sakeyi ba amsa…ta kwabe fuska kmr zatasa kuka tace”daddy plss…talk to me mana”…har yanxu idon nashi a rufe yace”who are you?…ta dan wara ido sai Kuma ta saki murmushi tace”it’s me…your baby”…ya dan tabe baki snn ya shiga girgiza Kai yace”No you are not…babyna dana sani ba haka take ba…my baby used to be happy and always smiling…so stop saying you are my baby cox you are not”…a hankali ta kamo hannayenshi ta rike snn tace”daddy mana…I’ve told you nice…ka bude idonka ka ganni”…ba musu ya bude idanun nashi ya dora a kanta.. yai cupping fuskanta yace”you’ve changed alot Layla…you are a Muslim so ya kamata kiyi accepting faith and move on… addu’anki kadai Usman ke bukata yanxu…not those tears”..ya karasa tareda pointing idanunta da har sun fara kwalla…ta dora hannayenta kan nashi tace”daddy kaima you’ve changed…Dan Allah daddy ka fadamin abunda ke damunka…nasan for sure akwai abunda kake boyewa”… murmushin takaici ya saki snn yace”somethings are better left unsaid baby…ba komai ya kamata ake fada ba”…shiru tai tana kallonshi sai Kuma ta fara hawaye tace”nidai dn Allah daddy ka fadamin…I promise bazan fadama kowaba…I don’t want to be seeing you like this plss”…ta sauri ya fara girgiza kai yace”baby kuka Kuma…stop crying plss…tashi muje ki zubamin abincin”ya fada don ta Dena kukan…Saida ta gama don kanta ta share hawayenta snn ta sauka ta karasa inda ta ajiye abincin…ta zuba a plate tareda Dora mai kan table…duk yana kallon yanda take turo baki yace”fushin na meye Kuma baby”…murguda baki tayi snn tace”nidai daddy kar ka sake cemin Layla plss…ko dadima baiyi ba”…ya Dan wara ido yana fara cin abincin yace”Laylan ne ba dadi Kuma”..da sauri tace”No a bakinka ba dadi…just call me baby kmr yanda kake fada…duk kace Maryam ko Layla Allah bana jin dadi”…dariya sosae Taheer ya saki kawai yana kallonta…wai ba dadi…Saida ya gama dariyan yace”to naji ban sake fada tunda bakiso kinji…now taso muci abincin”…ba musu ta mike zuwa inda yake suka shiga cin abincin tare…wani irin farin ciki Taheer ya samu kanshi ciki…ga dai damuwan nashi na nan cikin ranshi but he feel relieved just by talking to her…inama zasu cigaba da kasancewa a haka har abada amma inaa…

Basu suka bar clinic din ba sai after five…basu dade da komawa gidaba akai magrib…ya shigo da sallam parlon waya kare a kunnenshi…umma ce kadai zaune a parlon tana kallonshi…Saida ya gama wayan snn ya gaisa da umma…tana kallonshi da kyau tace”yau ka iya cin abincin knn”…ba tareda ya kawo komai a ranshi ba yace”yeah ai tareda baby mukaci”…umma tai shiru tana kallonshi…shi Kuma hankalinshi na kan wayanshi…Layla ta shigo parlon ta zauna kusa dashi tana nuna mai hanunta tace”daddy kaga  wnn zoben daya Usman ya fara bani…ban San Ina son ring dinba sai yanxu da Ya Usman ya mutu… at least zan ringa tunawa dashi snn inyi mai addu’a…Allah ya Kai haske kabarinshi…duk wani walwala dayai saura a fuskan Taheer nan take ya 6ace 6att…bai San time din da ya daure fuska tamau kmr bai San me ake nufi da dariya ba…ya kama hanun nata ya rike…har ya kai hanu zai cire ring din sai Kuma ya tsaya cakk…kmr Wanda ya tuna da wani abun…a hankali ya kewayo da idonshi kan umma yaga idanunta kyam a kansu…da sauri ya saki hanun nata ya shiga ‘yan kame kame…umma kallonshi kawai take batace komai ba…daya ga kmr kallon tuhuma take mai sai ya mike da sauri ya fita daga dakin har Yana yin tuntube😹

Part dinshi ya nufa Kai tsaye ya shiga tareda murzama kofan key ta ciki…nan bakin kofan ya durkushe yana salati… zuciyarshi sai bugawa take fat fat fat…yasa hannayenshi ya dafe Kai dasu…Allah dai yasa umma bata gano asirin zuciyarshi ba…bai San meya kaishi ga aikata hakan ba…bai San wane irin kishi yake dashi a kan yarinyar nn ba…”Allah ka rufamin asiri…Allah kar ka bari ta gane abinda na dade Ina boyewa…rabbi ka taimakamin plsss”…ya karasa mgnr hawaye na sauka kan kyakyawar fuskarshi…bai San lokacinda ya zama mai saurin kuka haka ba…da ba haka yake ba…it’s very hardly kaga hawayenshi amma yanxu a kan Layla abu karami sai yaji hawaye nabin fuskanshi…

Ita kuwa umma binshi tayi da kallo har ya fice snn ta mike a hankali zuwa dakinta…Layla na kokarin mikewa Nafisa ta shigo parlon tana dubanta tace”Ina daddyn naki ya tafi kuma”.. tace”yanxun nn ya fita Mami…Bari inje in kiras…bata karasa ba Nafisa tace”ba saikinje ba Bari in kirashi a waya”…Tai dialing number tasa a kunne…har ta gama ringing bai daukaba sai ta sake Kira…wayan na aljihunshi…da kyar ya zarota yana kallon me kiran…kmr bazai dauka ba sai Kuma yai picking tareda daidaita muryarshi yace”hello”…a daya bangaren Nafisa tace”bro kayi nisa ne?…yace”No Ina gida…what’s wrong”…tace”don Allah so nake if you are less busy ka kaimu shopping in anjima…akwai abubuwan da nace zan siya idan munzo nan Kuma ban samu na siyaba sbd rasuwar nn…gashi time ya fara kurewa…tun dazu naso fita ummi tace I should wait for you”…Taheer da ko kadan baiso hakan ba yace”ba damuwa…ana idar da sallah sai mu tafi”…”to shknn thank u so much bro…bari mu fara shiryawa”yace alright snn ya ajiye wayan.

Nafisa na gama wayan ta koma ciki ta sanar dasu ummi zasu fita yanzu…suma yaran duk tace su shirya snn ta tafi don shirywan itama.

Daga masallaci ko part dinshi bai koma ya nufi cikin gidan…duk sun shirya shi kadai suke jira…Nafisa ta dubi Al’ameen tace”kaje ka Kira Layla idan Kuma bazataje bane muyi tafiyarmu…yarinya sai shegen nawa”…Dan hararanta Taheer yayi yace”sai in fasa kaikun ma wlh…ai tasan ni zan kaiku so dolene ku jirata”…dariya nafisan tayi tace”Allah ta cika nauyi da yawa ko yaushe sai an jirata”…ya bude baki zaiyi mgn Layla ta shigo parlon Al’ameen na bayanta…kaff yaji yawun bakinshi ya kafe karkaff…mgnr da yakeson fada ya makale a bakin…wani irin kyau yaga tayi tamkar Wanda zataje gasan kyau…Arabian gown ce a jikinta a black…tana da adon manyan flowers yellow masu stones a jikinta…tayi veiling da mayafin abayar… fuskanta ko powder babu sai kwalli da tasa a idonta…takalmin kafarta vine slippers ne shima yellow…sai wayanta dake rike a hanunta…umma da fitowanta knn itama…tai tsaye tana kallon yanda yake binta da ido tamkar bai taba ganinta ba…suna hada ido da ita ya sunkuyar da kanshi da sauri tareda juyawa ya fice daga parlon.Yana zaune cikin mota suka fito…Layla ce karshen fitowa tana rikeda hanun hibba…ya sake kafeta da ido yana jin ciwon fitan da zatayi a haka…ba don umma da yaga namai kallon tuhuma ba…da bata isa ta fita da wnn kayan ba wlh…duk ranshi ya kara baci…tana isowa ta bude front seat ta shiga tareda  dora hibba a kan laps dinta…Taheer yai ma motan key suka fita daga gidan…Saida suka hau kan titi snn ya kalli Nafisa ta mirror yace”ranki ya dade ina Muka nufa?..dariya tayi tace”ko inama bro ai Kaine Dan gari…duk inda kasan zamu samu kaya masu kyau”…bai sake mgn ba ya dauki hanyar store din da suke siyayya…tafiyan 15 mins ne ya kaisu wurin…bayan yayi parking duk suka bude motan suka fita…Layla ta Dan saci kallonshi…ganin fuskar nn a tamke ta fita daga motan da sauri…duk ya hade fuskan nn wlh tsoro yake bata…Taheer na ciki yana binsu da kallo har suka shiga ciki…ya kifa kanshi da starring motar Yana sauke numfashi…bai san wane irin kishi yake dashi a kan yarinyar nn ba.

Ganin sun dauki kusan 40 mins basu fitoba…sai ya bude motan ya fita…Kai tsaye ya shiga ciki…Nafisa ya fara cin karoda ta dau duk abinda takeso Al’ameen na tura kayan a trolley…gaban counter suka karasa…shima Taheer din ya karasa snn ya bada atm dinshi don a cire kudin a ciki…ya kalli Ramadhan dake tahowa hanunshi rikeda wasu kayan…yace”Mami ga wani mutum can ya tare Yaya ya hanata tahowa…wai Yana son mgn da ita”…tun kafin tayi mgn Taheer ya dubeshi da sauri yace”where is she?…da hannu Ramadhan ya nuna mai wurin da take…bai sake cewa komai ba ya nufi wurin da sassarfa…ranshi in yayi dubu to a bace yake…Nafisa ta bishi da kallo kawai snn ta maida hankali kan fito da kayan data siya din.

Taheer na Shan corner ya hangota tsaye da wani namiji…bai iya ganin face dinta cox ta juya baya amma he can clearly see yanda guy din ke Mata murmushi…ya karasa wurin da sauri…ba tareda yace komai ba kawai yasa hannu ya shiga janta daga wurin…guy din ya sha gabansu yana kallon Taheer din yace”don Allah please…mgn kawai zanyi da ita ba jimawa zatayi ba”…yana gama fadan haka yasa hannu ya kama dayan hanun Layla dake rikeda wayarta Yana kokarin ya jata kawai yaji saukan Mari a kuncinshi…ya saki hanun nata da sauri tareda dafe inda aka mareshin…Layla batasan lokacin da ta saki wayan nata a kasa ba…tareda sa duka hannayen nata ta toshe bakinta dasu…hawaye ya shiga bin kuncinta wani kan wani…Taheer na kallon guy din dake dafe da cheeks dinshi har yanxu…cikin muryar gargadi yace”don’t you ever…kar ka kuskura ka sake ganinta kayi tunanin yi Mata mgn talkless of dora filthy hands dinka a jikinta”…Yana gama fadan haka ya kama hanun Layla ya shiga janta da mugun sauri…sai da ya bude mota ya turata ciki snn ya zagaya shima ya shiga…dama already su Nafisa na ciki…yaja motan da wani irin gudu suka fita daga wurin…Nafisa na tambaya meya faru…da kyar Layla na kuka ta fada Mata abunda ya faru…ta karasa da fadin”wlh ba laifina bane Mami…ki tambayi Ramadhan Ina cikin tsaiwa na yazo ya faramin mgn”…Nafisa da mamaki ya isheta tace”sai ki dinga kula daga yanxu…ba kowanne namiji ne zaka tsaya kana mgn dashi a wani wurin ba”…shidai Taheer yana jinsu…amma bazai iya bude baki ma yayi mgn ba…don haka yayi musu shiru…yanajin Nafisa nata Mata fada har suka karasa gida…bayan duk sun fito…Nafisa ta zagaya side din da yake…ta Mika mai atm dinshi tana murmushi tace”godia muke bro…Allah ya saka da alkhairi”…sai da yadan kakalo murmushi snn yace”bake nayiwa ba ai…’ya’yana nayiwa”..still dai tana dariyan tace”to ‘ya’yan naka ma sun gode..Bari mu karasa ciki”…Kai kawai ya iya daga mata…ita Kuma ta juya ta nufi cikin gidan… Al’ameen da Ramadhan suka dauki kayan suka bi bayanta dashi.

A hankali Layla ta kalleshi tace”daddy don girman Allah kayi hakuri…wlh it’s not my fault”…Saida ya watsa Mata wani kallo snn yace”ai it’s my fault tunda ni nace kisaka wnn kayan ki fita”…Yana gama fadan haka ya bude motan ya fita…batada zabin daya wuce ta fitan itama…don haka ta bude motan ta nufi gidan tana rusa kuka.

A parlor ta taradda su Nafisa…sun baje kayan da suka siyo su ummi na kalla…umma ce ta fara lurada ita tace”ke meye haka…Zaki shigoma mutane kina kuka?…Layla batace komai ba kawai ta wuce dakinta…Nafisa ta basu labarin abinda ya faru…ummi tace”don kyautawa bata kyauta ba…amma meye zai ringa hanata kula samari ko ance mashi bazatayi aure bane…Nafisa na kallon ummin tace”ummi ai ba cewa akai bazata kula samari ba…amma at least a fara neman izini tukun…ba mutunchi bane ta tsaya kula saurayi a waje”…a fusace ummi tace”to idan bata kulasu a wajeba…taya zaayi har su samu number dinta ko Kuma su San gidansu…idan bata kula samari ba sanyata a gaba zamuyi muyita kalla ko kuwa shi Wanda yake hanata kulasun zai aureta ne”…Nafisa dai shiru tayi donta fuskanci ummi bazata fahimcesu ba…umma kuwa dama shiru tayi tana sake sake cikin ranta.

STORY CONTINUES BELOW

Taheer tunda ya shiga daki bai sake fitowa ba sai asubah…Yana dawowa daga masallaci yai wanka ya shirya…ko cikin gidan bai shigaba ya tafi clinic abinshi…bai son ganin kowa a halinda yake ciki…don ya fuskanci zuciyarshi na gab da tona mai asiri.

Umma tun tana sa ran shigowan Taheer din har ta fitar da rai…har part dinshi taje taga a kulle…ta Kira wayanshi Kuma yaki yin picking…to me yake damun yaron nn ne?

8pm daidai umma tayi sallama parlon Taheer…jin shiru baa amsa ba sai kawai ta tura kofar bedroom dinshi ta shiga…Yana kwance rigingine a kan gado…yayi pillow da hannayenshi…idanunshi na kallon sama…da gani ba karamin zurfi yayi cikin tunani ba…Saida umma ta zauna gefenshi snn tasa hanu ta dan bugeshi…firgigit ya mike tareda zare ido yana kallon umman da baisan lokacin da ta shigo ba…haka nan yaji gabanshi ya Fadi ganin kallon da umman ke mai…ya Dan kakalo murmushi cikin in Ina yace”umma ai…ba…banji shigowanki…ba”…still umma na kallonshi tace”dama yaushe zakaji shigowana bayan kayi nisa cikin tunani”…bai sake cewa komai ba yai kasa da kanshi…saida umma ta daure fuska snn tace”dago idanunka ka kalleni mgn zamuyi”…ba musu ya dago idanun nashi ya kalleta…gabanshi ya sake faduwa ganin fuskarta a daure…wnn alama ne na mgnr da zasuyi mai muhimmanci ce…Saida umma ta dauke Kai snn tace”so nake ka fadamin tsakaninka da Allah Taheer me kake boyewa a cikin zuciyarka…ya dago da sauri zaiyi mgn ta daga mai hannu”kar kacemin ba komai don nasan karya kakeyi…yau bazan bar dakin nan ba sai naji damuwarka Taheer…sai naji abinda kaketa boyewa a ranka that’s weighing you down haka…kar kacemin mgnr biki ne don nasan it’s not…idan Kuma bazaka iya fadaba there are two things involved…ko ka sanar Dani abinda ke damunka…ko Kuma in fita harkanka for good…kar ka sake considering Dina as mahaifiyarka don daka daukeni uwa…bazaka boyemin abunda ke damunka ba…ko a hanya ka ganni kar ka nuna ka sanni Taheer don bazan taba kulaka ba…matukar baka sanar dani abinda nake sonji ba…to ka manta kana da wata kanwar uwa mai suna Aisha…ka manta akwai wani relation a tsakanina da Kai don zan yankeshi for good”…a gigice Taheer ya kamo hanunta Yana hawaye…ya shiga girgiza Kai yace”umma kar kiyimin haka plss…wlh bazan iya fadan abunda ke damuna ba…ko na fada umma ba amfani zaiyi ba..so it’s better kar in fada din…don Allah kiyi hakuri umma kar kice zakiyi breaking ties dani wlh mutuwa zanyi”…a hankali umma ta zame hanunta daya rike gam…tace”it’s ok tunda bazaka iya fada ba…but i want you to put this at the back of your mind…daga yau…bani ba Kai Taheer…ko a hanya ka ganni kamin mgn bazan kulaka ba”…tana gama fadan haka ta mike zata fita daga dakin…da sauri Taheer ya mike ya sake riko hanunta yace”umma na shiga uku…idan kikace haka umma wlh zan iya mutuwa…bazan iya fadan abunda ke damuna ba umma…zuciyata ta cuceni…kunya nakeji umma idan na fada zaku tsaneni”…ganin yanda yake kuka wiwi…umma ta kamashi suka zauna bakin gado…tayi cupping fuskarshi idonta har ya kawo kwalla sbd tausayinshi tace”look at me Taheer ba Wanda zai tsaneka…ba Wanda zaiga laifinka Taheer..don Allah say it…zakaji sauki a cikin ranka…the burden is too much for you…tell me son…I promise bazan ga laifinka ba and zanyi supporting dinka”…ya Dora hanunshi kan nata still yana hawaye yace”umma zuciyata batamin adalci ba…umma I…I…kmr zai fada sai kuma ya shiga girgiza Kai yace”umma am shy plss…bazan iya fada ba”…a hankali ta sauke hannayenta a fuskanshi tana kokarin mikewa ya rikota da sauri Yana cewa”am sorry zan fada umma…just don’t leave me plss”…umma na kallonshi tace”umhum Ina sauraronka”…a hankali yai kasa da kanshi yanajin yanda bugun zuciyarshi ke tsananta gudu kmr zata fito…ya dago ya kalli umma…ganin kallonshi itama take sai ya dauke Kai tareda goge hawayen da suka ki tsayawa a idonshi…cikin raunanniyar murya yace”umma I..I..i love…am in love….with…b..a..b..y”…ya fada words din a rarrabe…a hankali ya juyo da fuskarshi gareta…yanaso yaga reaction dinta…but sai yaga fuskanta normal…ko alamun mamaki ma babu…hannu umma tasa ta rungumeshi tace”why will you punish your self son…why did it take you so long to say”… Taheer wani dadi yaji ya lullubeshi…a hankali ya sauke ajiyar zuciya…at least umma bataga laifinshi ba…”am talking to you son…meyasa kaketa boyewa all this while baka fada ba”…ummi ta fada tana hawaye itama… seriously Taheer ya bata tausayi…ta tabbata Kuma ba karamin so yakema Layla ba…shima Yana hawayen yace”umma tsoro nakeji…ban taba tunanin zan samu support din kowa ba…snn inajin kunya umma yarinyar nn fa uba ta daukeni…she calls me daddy…ban San lokacinda son da nake Mata ya koma hakaba umma…zuciyata batamin adalci ba”…da sauri umma ta Dora hanunta Kan bakinshi tace”stop saying that…Allah ne ya Dora maka…and na tabbata duk duniya babu Wanda zaizo Layla fiyeda yanda kake sonta…so I will support you son…zan sanar da duk Wanda ya kamata ya sani…after all ba muharramarka bace so akwai aure a tsakninku”…wani irin sanyi Taheer yaji Yana sake shiga zuciyarshi…ya dade baiji heart dinshi very okay kmr yanzu ba…wato gaskyn umma ne da tace the burden is too much for him…umma ta riko hanunshi tana kallonshi tace”I want you to come back to your old self Taheer…ka ragema kanka wnn damuwan snn ka ringa cin abinci…I promise zanyi iya bakin kokarina kan mgnr amma sai naga ka dena damuwa..bikinka yau saura 10 days so ya kamata ka nustu ka maida jikinka snn ka dauki hutu wurin aiki cox you are going to be ango soon”…umma ta karasa mgnr da murmushi…lokaci daya Taheer yaji ranshi ya dan baci jin an ambaci bikinshi…ya rausayar da kai tareda kamo hanun umman yace”naji zan dena duk abinda bakiso umma…but plss ki fara tsaida mgnr auren nn tukun”…umma ta Dan wara ido tace”hope bada gaske kake ba koh”…Yana turo baki yace”da gske nake Mana umma…bana son auren nn wlh”…umma ta shiga girgiza Kai tace”kaima kasan wnn Kuma ba mai yiwuwa bane…tunda nace zan taimaka maka…ka hakura ayi bikin…nayi maka alkawarin InshaAllah Layla batada miji sai Kai”…wani irin dadi yaji ya sakeji a cikin zuciyarshi…””InshaAllah Layla batada miji sai Kai””wnn word yafi komai yi mai dadin ji…umma na kallon yanda yake blushing tace”bari in kawo maka abinci yanxu kaci…anjima sai mu karasa mgn…tun bata rufe baki ba yace”no mu karasa yanzu plss umma…ya gyara zama snn ya cigaba”umma kina ganin ummi zata amince kuwa…’yan uwan mahaifin baby suma kinaga bazaa samu matsala ta wurin su ba?…am scared umma nasan bai zama lallai su yadda ba”…idon umma na kanshi tace”why kake ganin bazasu yadda ba?…yace”umma sbd nayi mata girma…mum dinta mafa na girmeta umma nasan bazasu bani itaba”…ya kamo hanun umman ya rike yace”wlh umma idan ban auri baby ba mutuwa zanyi…duk ranar da akace an daura Mata aure da wani umma mutuwa zanyi na sani”…umma na girgiza mai Kai tace”ka Dena wnn tunanin and be positive…Ni nasan ba Wanda bazai yadda ba… Taheer you are a good man…ba Wanda bazaiso hada zuri’a dakai ba…ballantana Layla da kakeda iko a kanta…ko wani ka kawo kace kanaso ya auri Layla nasan duk Wanda kake tunanin bazasuki yadda ba..bare Kai da kowa ya shaida irin kaunar da kake Mata…Kai dai ka kwantar da hankalinka kawai ni nasan me zanyi”…cikeda farin ciki Taheer ya rungumeta yace”thank you so much ummata…Allah ya Kara lfy da nisan kwana…Allah ya saka maki da gidan aljannah”…da murmushi itama umma ta amsa da ameen snn ta mike tace”Bari in kawo maka abinci”baice komai ba har ta fita Yana binta da kallo kawai Yana washe fuska kmr gonar auduga😹he can’t believe yau shine ya fadama umma wnn mgnr…

Kitchen umma ta nufa direct…ta gama hada mai abinci a tray zata fita daga kitchen din sai ga Layla tazo daukan ruwa…umma na kallonta idanunta har sun kumbura sbd kuka…ta Mika Mata tray din hanunta tace”karbi ki kaima Taheer wnn…daga nan ma sai ki bashi hakuri”…ba musu Layla ta amsa tray din snn ta juya ta fita…gabanta har faduwa yake tasan sai ya Mata fada yanzu.

Yana nan zaune inda umma ta barshi…idanunta a kasa ta shigo dakin…shi Kuma Yana ganinta ya mike da sauri ya amsa tray din hanunta ya ajiye nan kasa snn ya kama hanunta ya zaunar kusa dashi…da mamaki sosae Layla ke kallonshi…itada take tunanin zai koreta yace ta bar mai daki sai taga akasin haka…what’s wrong with him?…a hankali ta dago ta kalleshi taga shima kallon nata yakeyi yana smiling… murmushi ta saki itama tace”daddy kayi hakuri plss…I promise bazan Kara ba”…still Yana kallonta yace”na hakura baby…yanxu zuba Mana abincin muci nasan kema bakici abincin ba”…ba musu ta durkusa ta shiga zuba musu abincin…tna gamawa ta janyo stool ta Dora abincin a Kai snn tace”na gama”…baiyi mgn ba ya dauki spoon ya Debi abincin ya nufi bakinta dashi…ba musu ta bude bakin ya zuba Mata abincin…haka yaita bata har Saida tace ta koshi…ya dauki drink ya bata shima Tasha snn ya rufe abincin…tana kallonshi da fara’a tace”daddy you are in a good mood today…what’s the good news?…wani murmushi ya saki Yana cewa”you guess right baby..am in a good mood..but bazan fada maki ba…it’s a surprise”…Layla ta turo baki tace”why daddy plss… remember am your baby fa… your friend…so bai kamata muna keeping secrets ma junanmu ba”…wani murmushin ya sake saki Yana shafa gemu yace”yes you are my baby…my friend…yai kasa da murya yanda bazata jiba snn yace”and you are my wife”…sake turo bakin tayi tace”then tell me daddy”…bakin data turo ya kama da hanunshi snn yace”I promise I will tell you amma ba yanxu ba”…tana kallon cikin idonshi tace”are you sure”…ya dauke idonshi da sauri snn ya daga Mata Kai…wasu electric abubuwa yaji suna transfer daga idonta zuwa nashi…ya sake juyowa ya dan kalleta sai kawai yaji ta sakala hannayenta a kafadanshi tace”am also happy daddy…tinda naga you are happy”… murmushi kawai ya saki snn ya mike yace mata”Bari inyi wanka”…tace”daddy bakaci abincin bafa”…ba tareda ya juyo ba yace Mata”Wanda kikaci ya ishemu..am not hungry”…Yana gama fadan haka ya fada bathroom…ita Kuma ta mike tareda tattara kayan ta fita dasu.

A bangaren hajiya umma kuwa..tun dazu tana daki tana tunanin Wanda ya kamata ta fara tunkara da wnn mgnr…ta dai San ko giyar wake tasha bazata fara tunkaran ummi ba don tasan rikici ne zaayi shi da ita…tafiso ma ummin ta zama itace ta karshe da zaa fadama mgnr.

Bayan ta gama tunane tunanenta…daga karshe dai tayi deciding ta fara sanar da Nafisa…inyaso ita Kuma ta sanar da mijinta.

Washegari…

Ganin ummi bata tashi da wuri ba…umma ta kira Nafisa dakinta tace”mgn nakeso muyi Nafee”…Nafisa na kallon umman tace”inajinki umma”…a nutse umma ta shiga Mata bayani…tun daga lokacinda ta fara zargin Taheer din son Layla yake.. har zuwa yanda sukayi dashi jiya…shiru Nafisa tayi tana jinjina al’amarin…ko kusa bata taba kawo wai soyayyan da Taheer kema Layla sone irin na aure ba…yanxu dama duk sbd Layla yayita zama yaki fidda mace yai aure…umma ta katse Mata tunani da fadin “kinyi shiru Nafee…ko bakiji dadin al’amarin bane?…da sauri Nafisa ta shiga girgiza Kai tace”ko kusa ba haka bane umma…kawai dai Ina mamaki ne da mutum kmr Taheer zaice Yana son Layla…na tabbata son da yake Mata ba kadan bane…na kuma san da kyar idan Layla zata samu Wanda zai sota kmrshi…nidai indai ta bangerena ne umma bani da matsala wlh…na amince 💯 Allah ya tabbatar da alkhairi…cikeda gamsuwa umma tace”yawwa Allah miki albarka…yanxu ki dauki waya ki Kira Awwal ki sanar dashi”…Nafisa na girgiza Kai tace”idan ke kika kirashi sai yafi daukan abun serious…umma ta danyi shiru tana tunani sai Kuma yace”to mikomin wayata gata nan a bayanki”…Nafisa tasa hannu ta dauki wayan a bayanta snn ta mikama umma…nan da nan umma ta lalabo number Awwal ta shiga dialing dinta…cikin ranta tana addu’a Allah sa bazaa samu matsala a bangarensu ba… ringing biyu yai picking da sallama yace”umma barka da safiya”…umma ta amsa da”barka dai Awwal ya Karin hakuri Kuma??yace”Alhamdulillah umma ya shirye shirye”…itama tace”Alhamdulillah Awwal dama inaso muyi wata mgn ne”…yace”to Ina sauraronki umma”…a hankali umma ta shiga mai bayani shima…tun daga farko har karshe…yai shiruu a daya bangaren Yana sauraren abinda take cewa…Saida umma ta gama snnn tace”naji kayi shiru bakace komai ba”

Tofa anzo wurin🤔Jin yayi shiru umma ta sake cewa”Hello”…da sauri yace”eh Ina jinki umma…wnn ai abin farin cikine umma baima kamata a tambayeni ba…kunada iko da Layla tamkar yanda nakeda iko da ita…zanyi mgn da Alhaji duk yanda mukai dashi I will let you know…nasan InshaAllah ma bazai ki amincewa ba…Allah ya tabbatar da alkhairi…cikeda farin ciki umma tace”shknn na gode sosae son Allah yayi Albarka…ya amsa da Ameen Ameen Umma..duk yadda mukai da Alhaji zan kiraki”…umma tace to Ina sauraronka..Allah ya jishemu alkhairi…tana ajiye wayan ta dubi Nafisa da tsantsar farin ciki tace”yace duk yadda sukayi da mahifinshi zai kirani”…Nafisa tace”nasan ma bazai ki amincewa ba”…umma tace Allah yasa”…Nafisa ta danyi shiru for some secs snn tace”amma umma wa zai fadama ummi”…umma tace”so nake naji yanda sukai da mahaifin nashi…idan sun amince zan kira Uncle din Taheer in sanar dashi…shi Kuma sai ya kirata ya fada Mata…nasan dai da kyar idan baayi rigima da itaba amma komai mai wucewa ne..

A bangaren Taheer kuwa…he’s eager yaji amsan da umma zata bashi…tace she’ll talk to duk Wanda ya kamata…and hakan yana nufin har ummi knn…Saida gabanshi ya fadi daya tuna ummi fa bai zama lallai ta aminceba…Karan shigowan text a wayshi ya dauki hankalinshi…ya dauko wayan ya duba tareda sakin murmushi yace”Alhamdulillah”..snn ya mike zuwa part din ummi…Nafisa ce zaune kadai a parlon sai hibba dake jikinta…wata irin kunya da bai san yanada itaba..yaji ta kamashi…zuwa yanxu yasan dole taji mgnr…duk sai ya daburce kmr ya fita daga dakin haka yakeji…Nafisa na kallonshi ta lura kmr kunyarta yakeji…sai tayi murmushi tana cewa”hope dai ba kunyana kakeji ba bro”…Taheer yayi diff…kmr ruwa ya cinyeshi…wai yau shine kejin kunyar Nafisa..his younger sister…ko da yake ai dole ma yaji kunya…shi kanshi duk ya tuna cewa Laylan da yake mutuwar so fa diyar qanwarshi ce sai yaji kunyar kanshi…kwamacala knn😹yana in Ina yace daita”what kind of kunya Kuma?…you know ba haka bane.. it’s just that ban kula dake a wurin ba”Yana gama fadan haka bai jira jin me zatace ba yasa Kai ya fice…Layla ta fito daga dakinta da sauri…tana kallon Nafisan tace”Mami kmr naji muryan daddy yanxu a parlon nn…I want to talk to him”…Nafisa da har yanxu bata bar murmushi tana mamakin sudden change din Taheer din ba tace”yanxun nn ya fita”…Layla bata sake cewa komai ba ta bi bayanshi da sauri…Yana dab da shiga part dinshi ta sameshi…bata mai mgn ba Saida ya bude parlor ya shiga snn ta shiga itama…ya zauna Yana kallonta yace”so kina bayana knn”…tace”yes daddy I want to talk to you”…”alright am all ears”…ya fada yana gyara zamanshi…Layla tace”daddy naji kmr ance post ume result dinmu is out fa”…yasa hanu yai cupping fuskanta…Saida ya manna mata peck a goshi that last for 2-3 mins snn ya daga idonshi a kanta yace”da gaske ne ya fito baby..and you’ve made it…I mean kinyi passing”…Layla ta zaro ido tanajin good news…kawai tai hugging dinshi tight tana fadin”am so happy daddy”…Yana shafa bayanta shima yace”am happy for you too baby…now tashi muje in sayo maki gift”…ta dago tana kallonshi excitedly tace”da gaske daddy?..yace”yes tashi”…ba musu ta mike…ya kama hanunta suka fita daga parlon…tace”daddy zan dakko hijab Dina”…yace”no get into the car…zamu siya a can”bata sake mgn ba ta bude mota ta shiga tana mamakin wai yau daddy ne yace ta shiga mota bako hijab..what has came over him?…shima shiga motan yayi…harga Allah yasan inta koma ciki zatace fita zaiyi da ita…shi Kuma yanxu kunya yakeji…bai taba sanin yanada kunya ba sai yanxu…so it’s better su fita a haka tunda she’s decent and motan nada tint…

Saida ya fara tsayawa ya sai mata very long hijab ready made daya Kai Mata har kasa…snn ya koma cikin motar ya bata…tasa..snn yaima motan key…suka tafi.

Layla nata baza ido taga yayi parking a wani babban shop na electronics haka…ya bude mota ya fita itama ta fito suka shiga ciki…inda wayoyi suke ya kaita yace”choose anyone you like tunda kin fasa wancan”…Layla daketa faman doka murmushi ta zaba wayan ta nuna mai…yana kallonta yace”tayi maki”…ta daga Kai da sauri tace”yes daddy…thank you”… murmushi kawai yai mata suka karasa inda zai biya kudin ya biya snn akai musu packaging suja tafi abunsu.

STORY CONTINUES BELOW

A hanya yana driving yana satan kallonta…he’s just imagining gashi ga Layla as hubby and wifey..yanata murmushi shi kadai…har suka isa gida bai bar tunanin nn ba…yana gama parking yace Mata”ki shiga ciki baby..zanje clinic in dawo”…ba musu ta bude motar ta fita tana daga mai hannu har ya fice daga gidan snn itama ta shiga ciki…su Al’ameen kadai ne a parlor don haka ta wuce bedroom din ummi direct…suna zaune suna wawware wasu Kaya…Layla ta karasa da fara’arta ta shiga nuna musu wayan…ummi ce tadan tabe baki tace”to ba dolema ya sai maki wataba…tunda shi ya fasa maki wancan”…Layla ta kalli ummin tace”ummi bafa shi ya fasamin ba…Ni na yar dashi a kasa da kaina…wnn Kuma ya siyamun ne sbd nayi passing post ume”…ta karashe mgnr da murmushi a fuskarta…ummi taci gaba da abinda takeyi tana cewa”sai kiyi Kuma ai ‘yar nan…ke har abada bazaki taba ganin laifin Taheer ba”…Layla mikewa tai ta fice daga dakin…su kuwa umma da Nafisa ba Wanda yace kala..don har yanxu ummi batasan mgnr nn ba.

Sai yamma snn Awwal ya samu Kiran umma bayan sunyi mgn da mahifinshi…ya sanar da ita shima Alh ya amince…ya kumayi farin ciki dajin wnn mgn…umma rasa inda zatasa kanta tayi sbd farin ciki…she never thought abin zaizo da sauki haka…yanxu fargabanta daya..shine ummi…ba bata lokaci ta Kira uncle din Taheer tayi mai bayani kmr yanda tayima sauran…shima daiki ba…a ganinshi ai hakan ma karfafa zumunchi zaiyi…sedai yace umma ta bari a gama wnn bikin in yaso daga baya sai ayi wnn din…umma taji dadi sosae ta Kuma rokeshi daya Kira ummi ya sanar da ita…yace zai Kira zuwa Safiya tunda yanxu dare yayi.

Cikin Daren umma kasa hakura tayi…tanata zuba idon ganin Taheer tamai wnn kyakyawan albishir din amma bata ganshi ba…mikewa tai kawai ganin har after 9 bai shigoba…ta nufi part dinshi…yana zaune gefen gado…waya kare a kunnenshi…fuskar nn a tamke yake mgn…few minutes back yanajin he’s the happiest man on Earth amma yanxu Sameera duk tayi spoiling mood din…umma na shigowa kmr jira yake yace”my mum is here…I will get back to you”…bai jira cewarta ba yayi hanging tareda ajiye wayan a gefenshi…yana kallon umma da murmushi kan fuskarshi yace”sannu da zuwa umma”…umma ta zauna tana kallonshi tace”tun dazu nake jiranka baka shigoba Taheer”…yace”wlh umma naje clinic ne…I was on call so ban mayi niyyar zuwaba aka kirani wai there’s emergency shine na tafi…yanxun nn na dawo”…umma na girgiza Kai tace”ya kamata dai ka dauki hutu gsky…ta danyi shiru snn ta kamo hanunshi tace”Albishirinka”…ya sake damke hanun nata a nashi yace”goro fari qal ummata”…umma batai wasting time ba tayi masa bayanin yadda sukayi da duk wadanda ta Kira kan mgnrshi da Layla…wani irin farin cikine ya lullube Taheer…ya rasa inda zaisa kanshi don murna sai kawai hai hugging umma tight yace”I love you umma…umma you are the best…umma am lucky to have you…Allah saka maki da gidan aljannah umma…I love you so much”…. murmushi kawai umma keyi tanajin yadda yaketa sambatu…tasan da kyar idan yasan me yake fada…Saida ya gama suburbudo addu’o’in snn ya dago yana kallonta yace”umma am super excited da wnn albishir din naki…you owe me a gift…so tell me duk abunda kikeso I’ll get it”…still umma na murmushi taja cheeks dinshi da hanunta snn tace”babu abinda nake bukata son…wnn excitement dana gani kan fuskan ka kadai is enough to make me happy…Taheer ya sake hugging dinta kafin yace”you are the best ummata…yanxu kina nufin har ummi ma tasan da mgnr nn?…a hankali umma na girgiza Kai tace”gsky bata saniba har yanxu…kasan halin Yaya Taheer Ni ban San ma taya zanyi Mata bayani ba…amma uncle dinka yace zai kirata da safe ya sanar Mata…Saida ta dafa kafadarshi snn tace”ka kwantar da hankalinka don Allah… InshaAllah ma zata amince”…Taheer da lokaci daya farin cikin daya shiga yaji ya fara fading don yasan rigima ne zaa Shashi da ummi…umma ta mike zata tafi tace”a kawo maka abinci?..ya girgiza Kai da sauri yace”am not hungry umma..beside ko inajin yunwa ma wnn good news da kika bani is enough to make me satisfied”… murmushi kawai umma tayi snn tace”to shknn Saida safe…kaima ka samu ka kwanta”…ya biyota da sauri yace”let me escort you umma”…umma batace komai ba suka shiga tafiya tare.

Saida ya rakata har dakinta snn ya fito…har zai fita sai kuma yaji he wants to see her…ya waiwaiga to make sure ba Wanda ke kallonshi…snn ya nufi dakin Layla…a hankali ya bude kofa ya shiga….tana kwance tayi rub da ciki a kan gado tana kallo a system dinta…tana sanye cikin sleeping wears dinta very cotton…wando iya guiwa sai rigan ya Dan sauka kadan…kanta babu dankwali…Saida ya kwashi kusan 5 mins Yana kallonta ba tareda ta saniba snn a hankali ya karasa gefen gadon ya zauna…wani irin kasala yaji ya diran mai at once…hannu kawai yasa ya dauke system din tareda dorawa kan laps dinshi ya shiga kallon abinda take kalla a ciki…ta mike zaune tana mai murmushi tace”yaushe ka shigo daddy”…bai bata amsaba sai cewa yai”mene wnn kike kalla baby”…ta Dana wara ido snn tace”Indian film ne daddy…sunanshi KumKum Bagya….Taheer ya dan tabe daki tareda kashe system din ya ajiyeshi gefe…yana kallonta yace”yau bazakiyi bacci ba knn”…ta Dan daga kafadanta tace”dama am waiting for you to come”… murmushi kawai Taheer yai kafin yace”then ki kwanta yanzu…ai gani nazo…bata sake mgn ba ta kwanta…Taheer kawai tsayawa yai Yana kallonta”tana turo baki tace”daddy cover me pls”…Saida yai murmushi snn yaja duvet dake gefe ya lullubeta dashi…ya risina yayi Mata addu’a ya shafa Mata…snn ya dan ja hancinta murya can kasa yace”sweet dreams”…idanunta a lumshe tana murmushi tace”gud nyt daddy”…mikewa kawai yayi ya kashe Mata hasken dakin tareda rufe Mata kofan snn ya wuce…he’s thinking nan da wani dan lokaci..maimakon ya tafi bayan yayi Mata addu’a sai dai ya kwanta gefenta…this thought kawai yasa yaji mood dinshi is changing😹

Washegari…

Tun safe ya tashi amma ya kasa shiga part din ummi…yana tsoron abinda ummin zata iyayi…yasan zuwa yanxu da kyar idan uncle dinshi bai kirata ya sanar da ita abinda ke faruwa ba…gaba daya tsoron haduwa da itama yake…wayanshi ne ya fara ringing…ya duba ganin umma ce yai picking da sauri yana gaisheta…ko amsa gaisuwan nashi umma batayi ba tace”kazo kayi breakfast..and don’t waste my time”bata jira me zaice ba ta kashe wayar…Taheer ya jingina kanshi da gado yana tunanin yanda zasu kwashe da ummi…ba yanda ya iya haka ya mike tareda daukan wayan nashi ya fita da part din..

Ya kusa minti 15 a bakin kofa amma ya kasa shiga ciki…ganin umma na sake Kira yasa yai gathering courage snn ya shiga ciki…

Ummi na zaune tana ma Layla kalaba…ita Kuma sai matsar kwalla take…umma ma na zaune gefe sai Nafisa dake kusada ummi…kanshi a kasa ya karaso parlon ya zauna snn ya gaishesu…cikeda tsokana Nafisa tace”barka da safiya doctor”…wani irin kunya yaji ya lullubeshi…ya dan kalleta ta gefen ido kafin yace”morning…Ina su Hibba”… still tana murmushi tace”hibba na daki tana bacci…su Al’ameen ko bansan meya hanasu fitowa ba”…Taheer ya jijjiga Kai kawai…umma na kallonshi cikeda kulawa tace”ga breakfast dinka can a dinning”…a hankali yace to umma”…yana kokarin mikewa wayan umma ya fara ringing…Saida gabanshi ya Fadi don yasan da kyar idan ba uncle dinshi bane…ummi mikewa tayi bayan picking call din tacema Layla”Ina zuwa”snn ta shiga dakinta…da sauri Taheer ya mike zuwa dinning…don so yake yayi ya gama kafin umman ta fito daga daki…Layla dake zaune nan kasa ta mike itama tabi bayanshi dinning din…Yana zama taja kujeran kusa dashi itama ta zauna…a shagwabe tace”daddy dn Allah inka gama zaka tsefemin??wlh kiston ummi zafi be dashi”…Taheer yadan saci kallon kitson nata snn ya fara cin abincin gabanshi yai kasa da murya yanda su umma dake parlor bazasuji ba yace”zan tsefe miki amma ba yanxu ba…kiyi hakuri ki dena wnn kukan”…a hankali tace”tohm”snn ta matso da kujeranda take kusa da nashi ta shiga cin abincin dake gabanshi itama…Taheer bai wani ci da yawaba ya mike yana goge bakinshi da tissue yace”baby ina zuwa”…bai jira cewarta ba ya wuce…umma na dubanshi tace”Kai badai har ka koshi ba”…yana tafiya yace”na koshi umma…ana jirana ne”…umma bata sake cewa komai ba sai binshi da tai da kallo…ko saurin me yakeyi oho?…abun kmr hadin baki yana fita kuwa ummi ta fito daga dakinta da sauri… fuskanta kadai zaka kalla kasan ta samu lbrin danyen aikinda Taheer din ke kokarinyi…Saida ta fara duba dinning taga Layla ce kadai zaune tanacin abinci…snn ta dawo da kallonta ga umma a kausashe tace”Ina Taheer”…Saida gaban umma ya Fadi ganin yanda yayar tata tayi kicin kicin da fuska…tace”yanxun nn ya fita Yaya…yace wai ana jiranshi ne”….ummi bata sake mgn ba samu wuri ta zauna…ta dubi Layla dake cin abincinta hankali kwance tace”dauki abincin nn kije daki ki karasa ci”…ba musu Layla ta dauki plate din dake gabanta ta wuce dakinta tana fadin”zancen na manyane knn”..(yes na manyane qawata😆)

Ummi na ganin Layla ta shiga daki ta shiga bin umma da Nafisa da mugun kallo…cikeda bacin rai tace”yanxu Aisha abinda kikayi kin kyauta knn…kin kyauta da kika goyi bayan Taheer akan wnn ta’asar da yake Shirin aikatawa…kinyimin adalci knn Aisha”…a hankali umma ta taso daga inda take ta zauna kusada ummi…a tausashe tace”don Allah kuyi hakuri Yaya…nasan idan na fara fada maki bai zama lallai ki amince bane…amma Yaya Taheer Yana son yarinyar nn…Yana sonta fiyeda yanda zakiyi tsammani Yaya…Yana ta azabtar da kanshi kan abinda ba Haram bane aikatashi…yanata boyewa ne Yaya sbd yasan bai zama lallai ya samu support dinmu ba…don Allah yaa kiyi tunani a kan wnn al’amarin…kiyi tunani da kyau Yaya…nidai banga aibu a yin auren nn ba…Saida umma tayi shiru snn ummi tana dubanta tace”kin gama”…a sanyaye umma ta daga Mata Kai alaman eh…ummi taci gaba”to wlh duk abunda akuyi bazan Bari ayi wnn ta’asar Dani ba Aisha…ta maida kallonta ga Nafisa tace”kema sbd bakida hankali baki San inda ke maki ciwo ba…shine kika goya musu bayan a dauki Layla ‘yar mitsitsiya a bama wnn zabgegen mutumin…mutuminda da yayi auren wuri zai haifi kmrta…salon yaje ya kasheta koh?…to Baku isaba wlh…duk kunyi kadan…ai nike gaba daku gaba dayanku…shima Taheer din ai bazai dawwama a wajeba…zai dawo gidan nn ya sameni sai naci nutuncinshi wlh”..ummi ta karasa mgnr tana hucii…daga umma har Nafisa dai ba Wanda yace takk…sun San hakan zata faru dama.

Taheer ko Yana fita Kai tsaye ya wuce office din Yusuf..cikin ranshi yanata addu’a Allah yasa ummi bazata ki amincewa ba…idan ummi tace bata yadda ba yasan for sure zai iya mutuwa…yanda yake son Layla gani yake wlh indai bai aureta ba…to duk ranan da akace ta auri wani mutuwa zaiyi for sure…he can’t stand seeing her with another…he just can’t…yana kishinta fiyeda tunani…yana Kuma yi mata sonda har ya koma ga Allah baya tunanin akwai halittar da zaiso a doron kasa bayan ta.Yana isa office din Yusuf yayi parking nan waje..snn ya shiga ciki…Yusuf dake cike wasu files ya dago yana dubanshi snn yace”maza yau Kaine a office dina Kuma”…Taheer ya nemi wuri ya zauna snn yace”is that how to welcome a guest”…Yusuf yai dariya tareda ajiye pen dake hanunshi yace”ko ba guest ba…to Kai ba guest bane a nan”… murmushi kawai Taheer yayi snn ya gyara zama yace”guy you know what?…da sauri Yusuf ya girgiza kanshi yace”bani insha my friend…angon Sameera”…Taheer yadan yatsine fuska jin ya ambaci Sameera snn yace”mafarki na ya kusa zama gsky…am soon going to get married to the love of my life”…ya karasa mgn da murmushi…Yusuf ya danja tsaki yace”na sani Mana guy…yau saura kwana nawa ma?…wani harara Taheer ya maka mai kafin yace”meyasa baka ganewa ne wai…cewa fa nayi..am going to get married to the love of my life ba Sameera kaji nace ba”…Yusuf ya Dan bude idanu snn yace”maza ka sake batar Dani fa…just go straight to the point”…tsaki Taheer yaja snn yace”to kwanan nn zakaji na auri baby”…Yusuf ya wani zare ido kmr Wanda yaga abun tsoro snn yace”guy are you for real…I mean anya kuwa bakaci Kai ba?…Taheer ya saki dariya snn yace”kafa naci ba kai ba…kana nan zaune zan kawo maka ita har gidanka bayan munyi aure”… Yusuf da mamaki ya kasa barinshi ya mike daga inda yake ya dawo kujeran dake kusada Taheer ya zauna snn yace”maza fada min yanda akai pls..how comes…ya akai kayi convincing ummi and everyone”…ba bata lokaci Taheer yamai bayanin duk yanda sukayi da umma…wani irin ihu Yusuf ya saki yana cewa”mutumina baka da dama wlh…yanxu ba kunya saika auri ‘yarka kace zakayi rayuwar aure da ita koh”…Taheer yace”mind you..ba ‘yata bace…Mata tace”… Yusuf ya sake sakin wani dariyan yace”ai dole kace ba ‘yarka bace yanxu…tunda kana sa ran aurenta…Shege Kanata yaudaran mutane da wani baby..baby..nan ko baa san kaunar aure kake Mata ba”…tsaki Taheer yaja snn yace”pls be serious Mana Yusuf…ban son irin wnn wasan”… Yusuf ya tsaida dariyan da yake snn yace”ok ok am sorry friend…yanxu ka fasa auren Sameera knn?…Saida Taheer ya Dan tabe baki snn yace”sunce tunda an riga anyi mgn wai dole sai na aureta”… Yusuf na gyada kai yace”so yanxu ka yadda da Sameeran knn?…Taheer yace”idan ma ban yadda da ita ba Yusuf ya zanyi…sunce saina aureta snn zaa bani baby ba yadda na iya ai…dole zan aureta ko banaso”…Yusuf yace”idan na fahimceka knn kana nufin…ka auri Sameera yanxu..bayan wasu shekaru Kuma sai ka sake auren Layla abi”…Taheer ya girgiza Kai da sauri yace”wani irin bayan wasu shekaru…tabbb..ai bana tunanin ma zan Kai shekara daya nan gaba ban aureta ba…kana nufin in barta knn tayita zuwa school salon wani ya ganta ya makale Mata koh”… Yusuf na zare ido yace”kaifa kace bazaka yi Mata aureba sai ta kusa gama sch…shine yanxu zakace bazaka Kai shekara daya ba”…a dan fusace Taheer yace”that doesn’t matter… everything has changed now”… Yusuf yai Dan dariya snn yace”dole kace it doesn’t matter mana tunda Kai zaka aureta…ni mamaki kake bani wlh”…Taheer ya saki murmushi yace”bazaka gane bane Yusuf…I love her…da kasan yanda nakeji akanta da duk bazakayi wnn mgnr ba wlh…ko shekaran ma I don’t think zaa Kai ban aureta ba coz am eager you know…I can’t wait”…Yusuf ya shiga girgiza Kai Yana dariya yace”mugu…ka gama gane musu yarinya snn kazo ka aureta…duk ba abinda baka saniba a jikinta”…tsaki Taheer yaja tareda daukan car key dinshi ya mike tsaye…Yana kallon Yusuf Rai a Dan bace yace”matsalana dakai knn wlh…Dan iska ne Kai…ya zaayi ka wani ce nasan komai a jikinta sai kace wanka nake sata a gaba ina mata”… Yusuf bai Dena dariya ba yace”yo na nawa Kuma…ai saidai kar a kuma”…Taheer bai sake cewa komai ba kawai ya fice daga office din…baiga amfanin mgn da wnn Dan iskan ba…da sauri yusuf yabi bayanshi yace”sorry doctor…wasa nakeyi wlh…pls come back akwai mgnr da nakesonyi da Kai…Taheer yai mai banza yaci gaba da tafiyarshi…sai da kyar Yusuf ya lallabashi suka koma ciki.+

A can gida kuwa ran ummi idan yakai dubu to ya baci…tun dazu take Kiran wayarshi switch off…wato ma Yana sane ya kashe Mata waya…to ya gama duk guje gujen nashi zai dawo gida ya sameta.

STORY CONTINUES BELOW

Taheer bai dawo gidaba Saida ya tabbatar duk sunyi bacci…Kai tsaye ya wuce part dinshi shima ya kwanta.

Da asuba dama kafin ya fita masallachi Saida yai wanka ya shirya…ana idar da sallah bai koma gidan ba ya wuce clinic..shi kanshi yasan wnn gudun da yake kara tunzura ummi zaiyi but he have no choice…gaba daya tsoronta ma yakeji.

4:30 pm akayi knocking office dinshi..ya bude idanunshi da suke lumshe..a hankali yace”come in”…umma ta bude kofa ta shiga ciki…da mamaki yake kallonta kafin yace”umma kece”…ta karasa ciki ta zauna snn tace”nice mana”…Taheer ya shiga Sosa Kai yana cewa”I never expect you umma…daga gida kike?..ta girgiza Kai tace”daga gidansu matarka muke…munje munkai lefe nace suyi dropping dina a nan…wato bazaka dauki hutun ba dai koh”…yace”zan dauka umma sai gobe”…umma ta tabe baki tace”yanxu Taheer kana ganin wnn guje gujen da kakeyi shine zai sa Yaya ta amince da mgnr nn…baka ganin wnn abun Kara bata ranta ma zaiyi koh”…a hankali Taheer yace”na sani wlh umma…but I have no choice…tsoron haduwa da ummi nakeji wlh…Ina tsoron jin abinda zai fito daga bakinta”…umma na girgiza Kai tace”duk da haka wnn ba solution bane..yanxu inaso ka biyoni muje gida..Kuma duk abinda Yaya zata ce karka sashi a rai ya dameka…nasan yanda zanyi InshaAllah…indan Kuma kanaso in zare hanuna a lamarinka sai kaita zama kar kazo muje gidan”…Taheer ya mike da sauri yace”kiyi hakuri umma…let’s go”…itama batayi mgn ba ta wuce suka tafi.

Saida suka hau kan titi yace”umma amma dai baby bata San da mgnr bako”… murmushi umma ta saki tana kallonshi tace”hope dai ba tsoron ‘yar taka kakeji ba Kuma”…da sauri yace”I must be scared umma.. infact kunyarta ma nakeji wlh…ban San ya zata dauki wnn mgnr ba…umma do you think zata amince Dani despite ta daukeni a matsayin uba?…still umma na murmushi tace”InshaAllah bazataki amincewa ba son..ai she loves you”…Taheer na girgiza kai yace”ba irin wnn son take yimin ba umma…idont think she will accept me as hubby…I know she won’t”…ya karasa mgnr Yana hargitsa gashin kanshi…umma dake mai murmushi har yanxu tace”Taheer you are very funny wlh…yanxu babyn kakejin tsoro Kuma…well stop being afraid and think positive okay?…na fada maka I’ll always support you so worry not…ya juyo yana kallonta da murmushi shima yace”InshaAllah na dena ummata…I love you”…Saida ta kama free hand dinshi tayi pecking snn tace”I love you more my Son…angon baby”…wani murmushi ya subuce mai jin sunan da ta kirashi…ya sake kallonta yace”I love you”…ita kuma ta daga masa Kai tana murmushi.

Suna isa gida Taheer yaji zuciyarshi na wani tsalle kmr zata faso kirjinshi ta fito…a hankali ya bude motan ya fita bayan yayi parking…umma na lura da yanda yayi wani tsuru tsuru…ta kamo hanunshi ta rike cikin nata..har suka shiga bedroom din ummi…idanun Taheer a kasa a nemi wuri ya zauna nn kasa…ita Kuma umma ta zaune gefen gado…tunda suka shigo dama ummi ke binshi da wani matsiyacin kallo…ji take kmr ta kwada mai Mari don takaici…murya can kasa yace”umma barka da…..tun bai karasa ba ta daga mai hannu tace”rike gaisuwarka malam…bana bukata”…Taheer yai shiru kmr ruwa ya cinyeshi…cikin daga murya ummi ta fara mgn”ashe dama baka da mutunchi ban saniba…ashe mugu ne Kai Taheer baka da kirki ban saniba…yanxu ba kunya ba tsoron Allah Taheer…duk matan dake duniyar nn ka rasa wadda  zakace kanaso sai Layla…Layla Taheer… yarinyar daka haifeta ka girmi uwarta Taheer… yarinyar dake maka kallon mahaifinta tana kiranka daddy…Taheer duk duniya ka rasa wa zakace kanaso sai ita sbd rashin Imani…ita Kuma uwarka ta goya maka baya sbd tsabar son kai…to wlh Bari kaji in fada maka…tun wuri ma idan zaka cire wnn tunanin daga ranka ka cire don muddin Ina raye bazan bari a cuci rayuwar yarinyar nn a aura mata tuzuru kmr ka ba…bazan taba bari a aura mata tsoho ba haka kawai kaje ka kashe mana ita…ashe dama duk soyayya da kulawar da kake bata ba don Allah kakeyi ba koh..kanayi ne sbd kanada mugun nufinka a zuci kana ganin zaka yaudaremu da wnn koh…to ko ka yaudari kowa Taheer Ni baka isa ka yaudareni ba…kuma muddin Ina raye wnn auren ba mai yiwuwa bane…Taheer da tunda ummin ta fara mgn yake hawaye..duk abinda ummin ta fada yasani gsky ne…gsky ne yayi ma Layla tsufa amma baisan ya zaiyi da soyayyar da yake Mata ba…a hankali  yace”ummi kar kimin haka don Allah…wlh nima bansan ya akai sonda nake mata ya koma son aureba…amma wlh ummi duk abinda nayi mata banyi da wata manufa ba…ki taimakeni ummi wlh idan ban auri baby ba mutuwa zanyi”…ummi ta shiga salati tana tafa hannaye tace”Kai dai bakada kunya wlh Taheer…yanxu Laylan kake cewa idan baka aure taba mutuwa zakayi…ko kunyar mgnr nn bakaji ba dn Allah…to wlh ko kukan jini zakayi kayi ni bazai dameni ba…shiyasa knn kaketa min zaune a gida kaki maida hankali Kai auren..Ashe Kai kanada mugun nufi cikin ranka…to ta Allah ba taku ba…Kuma aurenka da Sameera ba fashi”…Taheer zai sake yin mgn cikin tsawa ummi ta katseshi da fadin”karka cemin komai malan..ka tashi ka bani wuri”…bai sake yunkurin mgn ba ya mike da kyar…yana hada hanya ya fice daga dakin…umma dake gefe tana kallonsu tun dazu…a hankali itama ta mike tabi bayan Taheer…ta karasa da sauri inda yake ta rikoshi da kyau…ganin yanda yake tafiya kmr Dan maye…a hankali ta shiga janshi har zuwa dakinta…ta zaunar dashi bakin gado itama ta zauna…tayi cupping fuskarshi da hannayenta..with so much concern tace”Taheer calm down plss..ka dena wnn kukan..duk maganganun da yaya ta fada ranta ne a 6ace..na tabbata ba har cikin zuciyarta ta fada ba..kayi hakuri yanxu ka dena wnn kukan… InshaAllah sai inda karfi na ya kare kan wnn mgnr…I won’t let you suffer son..so ka dena damun kanka don Allah”…a hankali Taheer ya shiga girgiza kai yace”ummah…zuciyata umma…umma ki taimakamin don Allah…kiyima ummi bayani..indai ban auri baby ba wlh mutuwa zanyi…ki taimakamin plss”…wnn karon saida umma tayi hawaye sbd tausayinshi…wane irin so ne Taheer kema Layla haka…tasa hannu ta janyoshi jikinta…ta shiga patting bayanshi a hankali tace”I promise sai inda karfi na ya kare Taheer..don Allah ka sassautama kanka wnn damuwan..kar wani ciwon ya kamaka”…Taheer dake rungume jikinta bai iya cewa komai ba…wani irin zafi yakeji cikin zuciyarshi…ya tabbata duk dauriyar shi wnn karon indai ummi ta dage kan mgnr nn zai iya kwanciya asibiti…all this while yana daurewa ne baison kwanciya amma a yanda yakeji yanxu…if care is not taken zai iya loosing rayuwarshi gaba daya…da sauri ya mike daga jikin umma…yana kokarin tashi tsaye umma ta rikoshi”Ina Kuma zakaje”…ta tambayeshi with concern…cikeda karfin hali Taheer yace”magani zanje in dauko umma.. I want to sleep..banason zuciyata tana tunanin nn..indai ba maganin nasha ba bazan iya bacci ba na sani..and I want to stop thinking of all that has happened umma…I want to get rid of my worries plss”…Saida umma ta goge hawayen da suka zubo mata..snn a hankali tace”you should relax..Bari inje in dauko maka”…yace”umma I don’t want to sleep here plss..nasan kona fara baccin baby na shigowa zan tashi and I don’t want that”…hannu umma tasa ta kwantar dashi kan gadon..ta mike tsaye snn tace”I can’t leave you all alone Taheer..kayi baccinka a nan..I promise bazan Bari Layla ta shigo ba..so tell me inda maganin yake in dauko maka”…idanunshi a lumshe yace”cikin first aid box”…umma najin haka ta dauka key din part din nashi..snn ta fita…da saurinta ta shiga ciki…ta rarumo gaba daya first aid box din ta taho dashi…don batasan takamaiman maganinda yake so ba…tana zuwa ta bashi..ya mike zaune da kyar ya dauko drug din ya balla…umma ta Mika mai ruwa..yasha snn ya sake komawa ya kwanta..ita Kuma tai zaune kawai tana kallonshi…Saida ya jima snn baccin da yake bukata yayi gaba dashi.

A Daren ranar…ummi ta shigo dakin Layla tana dubanta tace”yanxu Zaki Kwanta ne”…Layla tace”eh ummi..daddy kawai nake jira yazo yamin addu’a sai in kwanta”…ummi da daure fuska snn tace”to dauki abinda zaki bukata ki wuce muje dakina”…ba tareda Layla ta kawo komai a ranta ba..ta shiga gaba ummi na binta a baya suka fita..don ba abinda zata dauka a dakin…suna shiga dakin ummi..ummin tace”to hau gado ki kwanta..Allah ya bamu alkhairi”…da mamaki Layla ta dan dubeta snn tace”anan zan kwana ne ummi”…ummi tace”eh”…da sauri Layla tace”ummi to Bari in dauko wayana in Kira daddy ince mai zan kwana a dakinki…kar yazo yimin addu’a bana nn”…a fusace ummi tace”kina fita daga dakin nn sai na gaura maki Mari wlh…kanin ubanki ne Taheer din da sai kin wani cemai Zaki kwana a nn dakin”…a hankali Layla tace”ummi addu’a fa zaiyimin”…ummi tace”idan kika sakemin mgn saina cicci miki wlh..addu’an ne baki iyaba da sai wani yazo yayi miki snn zakiyi bacci”…mamaki sosae ya kama Layla jin abubuwanda ummi ke fada”..tadan turo baki snn tace”ummi daddy na fa nake nufi ba wani ba”…wnn karon ummi Saida ta jefo Mata carbin dake hanunta tace”bakazi shiga taitayinki daniba ko Layla..na sakeji kin ce daddynki sai na babbalaki a gidan nn”…Layla tayi shiru tana ganin latest attitude din ummi…to meya faru…kodai daddy yayi Mata laifi ne…why take cewa kar ta sake kiranshi daddy…da sauri ta hau gado ta kwanta tareda kudundune kanta cikin bargo ganin ummi tayo kanta gadan gadan…still tana turo baki ta shiga kunkuni..”naga dai babana ne..to meye idan nacemai a dakinki zan kwana”…iyaka tunanin Layla ta kasa gane dalilinda yasa ummi ke behaving haka…har bacci ya dauketa tana addu’an Allah yasa idan daddy yaje dakinta bai ganta a can..yazo dakin ummi..ta riga ta saba duk dare sai ya Mata addu’an nn takejin dadi.

Bayan kwana biyu…

Ummi ta fita harkan Taheer for good…ko gaisheta yayi da kyar take amsawa…abubuwa sun taru sun cika mai Kai..yama rasa da wanne ya kamata yaji…on the other hand Kuma..rabonshi da ganin Layla har ya manta…duk wata hanya da ummi tasan zai hadu da ita…ta toshe…kullum a dakin ummin take kwana…shi Kuma ba zaman gidan yakeyi sosae ba…haka ummi zata hanata fitowa har sai ya fita..tanajin dirin motarshi Kuma zata turata daki…wnn Abu ba karamin daga mai hankali yakeyi ba…lokaci daya ya zabge yayi wani irin haske…kana ganinshi zaka San bashida lfy…kullum sai ya sha magani yake samun yin bacci..har ya fara tsoron kar fa ya zama addicted to Shan maganin bacci.

Bangaren Layla ma ba karamin damuwa take ciki ba…ta kasa gane kan ummi kwata kwata..ta Kuma kasa gane dalilinda yasa take kokarin nisantata da Taheer yanxu..Wanda da ba haka takeyi ba…kullum da kyar takeyin bacci..don ba karamin missing dinshi tayi ba…wataran takance idan ita ummi ta hanata ganinshi why shi bazai nemeta ya ganta ba…ko dai daddyn ne yace tayi masa wani abun…ita ta kasa gane kan al’amarin nn gaba daya kanta ya kulle…ta tambayi umma…ta tambayi Mami Amma ba Wanda ya bata gamsashen amsa…har ta hakura tama dena tambayar.

Umma na dakinta kan darduma..tunda ta idar da sallahn azahar take Kai tanata addu’o’inta…jin wayarta na ringing ta shafa addu’an tareda dauko wayan tayi picking da sallama…a daya bangaren Alh Adam yace”Aisha kin ganni nazo Dutse gaisuwar yaron nn Usman..to ban mayi niyyar yin mgnr Taheer da Layla ba sbd naga suna cikin jimami.. kawai sai kakan nata kemin mgnr da kansa…shine ma ya bukaceni da in Kira a tambayi yarinyar idan ta amince da Taheer din sai a tsaida mgn yanxu tunda gamu mun hadu”…umma da tayi shiru tana sauraron shi tace”to Alh gashi Kuma Laylan bata nn wlh…sunje gidan Ramla itada Nafisa da sauran yaran…Amma Bari in Kira Nafisa in sanar Mata…inyaso ko ta wayarta sai ku Kira kuji..alh Adam yace”to shknn ba matsala”…umma na kashe wayar ta shiga dialing number din Nafisa..Yana shiga Nafisa tayi picking…da sauri umma tace”kina jina Nafee..yanxu Alh Adam zai kiraki wai suna so suji ta bakin Layla ne..Dan Allah Nafisa kiyi iya bakin kokarinki kiyima yarinyar nn bayani yanda zata fahimta..kar ki bari tace bata amince ba don wlh Taheer ban San halinda zai shigaba”…cikeda gamsuwa Nafisa tace”InshaAllah zanyi iya bakin kokari na umma..in Allah ya yadda komai zaizo da sauki”…umma tace”to shknn..yanxu kije kiyi mgn da ita don yanxu zasu kiraki”…Nafisa ta amsa da toh snn ta kashe wayan…umma ta sauke ajiyar zuciya..ita Sam batayi tunanin tambyar Laylan ba.. ubangiji Allah kasa zata amince..ina tausawa yaron nn wlh…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page