MY BESTIE’S HUSBAND CHAPTER 5 BY REAL FAUZAH TASIU

 MY BESTIE’S HUSBAND CHAPTER 5 BY REAL FAUZAH TASIU

               Www.bankinhausanovels.com.ng 

Miqewa tayi ta gyara gurin ta shiga daki tayi wanka ta shirya cikin kayan baccinta ta sanya hijjab ta dauki hisnul muslum tana dubawa tana daukan addu’o’i ta Jima zaune sannan tayi addu’a ta kwanta, Shiru goma sha daya har daya bataji Motsin Ja’afar ba wayarta ta dauka ta danna numbersa ta kirasa har tayi ring Bai dagaba sake Kira tayi.

Taji an daga taja ajiyar zuciya tace “Allah yasa dai lfy kake najika Shiru….” Jitayi anyi murmushi sannan akace “dake zama kikayi kina jiran dawowar abinda aka baki aronsa to ai dama kwanciya kikayi kikayi bacci  zaifi Miki sauqi Ja’afar kam yayi nisa saidai Kuma gobe idan naga dama na baki aronsa, sorry fah babie”

Qit aka kashe wayar taja numfashi tare da tashi tsaye cike da al’ajabi a ranta take tambayar kanta to dama ana haka kenan? Batada me Bata amsa hakan yasata ta koma ta sake kwanciya kishi na azalzalar zuciyarta hawaye nabin idonta tana karanto addu’ar annabi Yunus “ La’ilaha illah anta subhanaka inni kuntu minazzalumin” dahakadai daqyar bacci ya saceta itakam tana ganin rayuwa to me tayiwa Ja’afar haka ne daya fara juya Mata baya yana kantafi da mutuncinta.

+

Washegari har hudu bai shigo gidan ba batayi zuciya ba ta Kira wayarsa akayi rejected takaici ya kamata Amma saita dake saboda kullum Amminta tana fada Mata ibada batada sauqi aljanna ce me sauqi idan ka iya sarrafa zuciyarka tare da naiman daukin Ubangiji a duk lkcn da wani Abu ya kulleka.

Text ta rubuta Masa da zafafan kalamai da tasan zasuja hankalinsa Amma har dare babu reply hakan yasa ita da kanta ta fara zargin ko wani laifi tayi masa ta sake rubuta Masa saqon ban haquri ta tura Masa bai biyota ba har wayewar gari idan barawo ya rintsa itama ta rintsa.

Da sassafe saiga Hajiya Kaltume suka gaisa tace “ina me gidan ko ba anan yake bane?” Qaqaro murmushi tayi tace “Eh ba anan ya kwana ba” murmushi tayi tace “nikam Rafi’ah Anya bazan baki shawara ba a zaman da nayi dake na fahimci kinada tsayawa akan addini sosai alhmdllh Zaki dace a rayuwa Amma fah sai kin tashi tsaye, in baki wani lbr Mana surkarki da tatafi Damagaran bafa kowa take dashi ba neman asiri ta tafi na mallakarwa kishiyarki mijinku ta yanda da quruciyarki da komai zaki zama bora bance kiyi shirka ba Amma ki dan tashi tsaye ki tallafawa kanki rayuwarnan ta yanzu baa zama wlh duk wanda kikaga yana fantamawa to ya miqe”

Kallonta takeyi da rashin fahimta tace “ban gane ba Hajiya” miqewa tayi ta rufe qofa ta dawo ta zauna tace “saboda munafukai masu fakar ido am Rafi’ah da Hausa nayi Miki bayani ki miqe ki dage ki zama tauraruwa a gurin mijinki ta hanyar yan shige² nifa bance ki fita ba aa ki barmin komai zanyi Miki nidai hadin kanki nakeso”

Saurin girgiza kai tayi tace “astagfirullah Hajiya aa bazan iyaba nikam babu wanda nake dashi daya wucce Allah shine zai iyamin” Shiru Hajiya Kaltume tayi tana nazarin mgnrta kafin tace “Eh hakane kam kin Kama dahir Allah yasa mu dace” miqewa tayi tace “zan wucce kidai duba maganganuna akwai gyara a rayuwarki idan ba hakaba kinaji kina gani Zaki zama yar kallo” sallama sukayi ta tafi Rafi’ah ta tabe baki tace “dama Hajiya Innah ta fadamin ba Allah ne take kawoki ba kaji mace yar kalan masifa zata liqamin tsiya ta jamin raba tsaba da mahalicci na” shigewa tayi daki tayi duk abinda zatayi dare yayi tayi addu’o’inta kamar yanda ta saba ta kwanta tanajin cikinta yanata motsi tasan harma da yunwa kasancewar damuwar rashin mijin nata ta hanata cin abinci.

Ita burinta bai wucce ko a waya taji lfyrsa ba inda ya kasance duk Kira ana rejected haka ta wanzu idan taga dare yaqi tafiya takan tashi tayi alwala ta nufi mahaliccinta da, da yamma ta gama duk wani shirinta na karbar miji har dare tana tsara girkinta ta kashe lkcnta wajen shirya masa abinci tagama ta dauki wanka ta harde tana duba agogo takwai Tara goma sha daya Shiru.

Cikin tsananin mutuwar jiki ta dauki wayarta ta katsa numbersa gabanta na faduwa ta Kira cikin saa ya daga batare da yace komai ba taja fasali tace “barka da yini” qaramin tsaki yayi yace “inajinki” a sanyaye tace “lfyrka nakeson ji kwana uku bamu gaisa ba” wata qaramar dariya yayi yace “idan banida lfy nan nake jinya saboda haka indai Ina wajen gdannan kikajini Shiru to qalau nake” Shiru tayi maganganun nata suna hautsina nutsuwarta ta hadiye wani Abu me ciwo tace “ba nufina kenan ba gani nayi baka nemana idan na kiraka ma sai kayi rejected don Allah ka yafemin Best wlh nakasa tuna kuskurena gareka iyakar sanina dakai cikin watannin da mukayi baka iya barin Abu a ranka wannan ba dabi’arka bace tawace nima Kuma kullum Ina addu’ar Allah ya sassautamin nauyin baki saboda gudun kamuwa da wani ciwon akan matsalar da zan iya maganinta da harshena”

Maimakon yaji kalamanta sunyi tasiri a zuciyarsa saima tafasa da yaji zuciyar tasa tanayi yace “saime idan kin kamu da ciwon bake kika dorawa kanki ba kwanane yau ban shirya yinsa anan ba ni bama na Bauchi Ina Abuja Kira Kuma banaso ki daina idan kinqi kuwa ranki ne zai baci a banza sakarya kawai….”

Ajiye wayar tayi da sauri saboda a duniyarta takan hadiye kowacce irin damuwa Amma banda cin mutuncin iyaye shikuma ta lura hakan yafi Masa komai sauqi, zuciyarta suya takeyi sosai nadamar Kiran nasa takeyi da tasan abinda zai fada Mata kenan, kuka kam har saida taji jijiyar kanta na daurewa ta hqr tasha magungunanta ta kwanta zuciyarta nayi Mata wani irin zafi.

Abu kamar wasa tafiya sai qara miqawa takeyi daga sati antafi wata babushi babu alamarsa waya kam tun ranar da ta kirashi yaci mutuncinta take tsoron kiransa Amma ta wajabtawa kanta kullum saita tura masa saqon barka da safiya dana Saida safe shi kansa abin na damunsa sosai yarasa ya zaiyi ne wani sharadine Ni’imah ta gindaya masa wai idan ya kuskura taji lbrn yaje inda Rafi’an take sai tasa ya saketa shikuma tsoro ya shigeshi wani mugun tsoronta yakeji saiya daga waya zai kirata sai ya tuna cewa idan tasan ya kira Rafi’ah cin mutuncinsa zatayi hakan duk zafin kansa zai hqr ya share, wasa wasa har gashi da wata biyu a Abuja.

Yau tun safe ya tashi dajin wani qwarin gwiwa nason ganin Rafi’ah yana qissima watannin cikinta fitowa yayi daga daki ya tarar da hakimar tasa a zaune tanata fama da tuffa ya dubeta yayi mata murmushi yace “gimbiya yau watanmu nawa rabonmu da Bauchi ne?”

Dagowa tayi ta dubeshi a banzace tace  “wata biyu da sati biyu mana wani abune?” Gabansa ne ya fadi yace “aa kawai dai na tambaya ne” yatsina fuska tayi tace “ok na dauka tunanin waccan yar iskar yarinyar kakeyi” dagowa yayi da sauri sosai kalamin ya tabashi Amma suna hada ido sai yayi qasa dakai yace “ah haba dai kawai dai tunanin cikin jikinta nakeyi”

Wani banzan kallo tayi masa tace “to ko zakaje ne” qasa yayi da kansa yana wasa da yatsunsa kamar wani qaramim yaron da yaje jiran umarni ta daka masa tsawa tace “tambayarka nakeyi ko zakajene?” Saurin girgiza Kai yayi tare da dagowa kawai sai idonsa ya ciko da qwallah ya miqe da sauri ya haye sama ta sheqe da dariya tace “sakaran banza da kace bakaji saura shegiyar baqar kadarar can labarinta ma saiya shafe a duniyar mutane daga ita har cikin jikin nata muga ta tsiya

Tunda ya shiga dakin ya hade Kai da gwiwa kuka yakeyi sosai kamar yaron goye zuciyarsa na azalzalar sa ya tafi Azare ya gano lfyr matarsa da cikin jikinsa Amma babu dama tsoro yakeji kada Ni’imah ta fahimci inda ya dosa ji yake kamar idan ya bata Mata rai qonashi Ubangiji zaiyi dabara ce ta fado masa ya miqe da sauri ya rufe qofar ya shige bandaki da waya a Hannunsa ya fara duba number Rafi’ah Amma Babu a wayarsa tsoro ya qara cikashi gami da mamaki duk inda zai duba baigani bs hakan yasashi kiran Hajiya Innah ta  jima tana ring sannan ta daga daga yanayin muryarta yasan akwai damuwa.
A gaggauce yace “Am Innah Ina Rafi’ah?” Numfashi taja cikin tausayawa halin da dan nata yake ciki tace “anya magaji kana addu’a kuwa” katseta yayi da cewa “inayi Inna please kibani Rafi’ah magans nakeson yi da ita” murmushin qarfin hali tayi duk jikinta yayi sanyi tabbas akwai alamun nasara wata biyu an tafi uku ita kanta baya kiranta tunda ta kirashi tayi masa nasiha tare da fada masa halin da matarsa take ciki na yawan damuwa da kuka ga ciwon Kai daya sata a gaba ko abinci tasa a gaba saita kasa ci idan ta tambayeta sai tace  ita ba damuwarta yazo gareta ba damuwarta ya daga wayarta taji lfyrsa Amma yayi block contact nata kota Kira baya shiga.
Sake katse Mata tunani yayi da cewa “don Allah Inna kibani ita wlh inajin idan banjita ba komai zai iya faruwa Inna ko wani abu ya farune?” Numfashi ta sauke tace “akwai damuwa me tsanani a tattare da Rafi’ah yanzu dai ma kar naja maka zance bata gidannan tana babban asibitin Bauchi suna treatment nata sakamakon jininta da ya hau yaqi sauka yau kwana uku batasan waye akanta ba Amma sunankia take ambata dazu ma da mai martaba yazo sunce indai jininta bai sauka zuwa wayewar gari ba to zasuyi Mata Cx su cire cikin jikinta me watanni bakwai saboda idan aka basshi zaa iyayin biyu Babu ba itan babu shi….”
Katseta yayi da cewa “Wht Innah Amma shine baku fadamin ba” murmushinsu tayi na manya tace “ai Wai da mukaga ba sune a gabanka ba Ja’afar duk da nasan wani abun bayin kanka bane Amma yana ishe hali nidai banga abinda yarinyar nan zatayi maka ba ka dauki wannan matakin akanta kafi kowa sanin yanda akayi auren nan bataso iyayenta basaso rabone kawai me gaggawa ya baka saar mallakarta Amma tazama abar wulaqantawarka kada ka sake kakai hqrn mutum me haquri da zurfin ciki qarshe idan ya kwance maka rawani duk duniya babu Wanda ya Isa ya daura maka so ka kiyaye”
Kashe wayar tayi ta shiga dakin da Rafi’ah take kasancewar itace a gurinta taqi bari a fadawa iyayenta abinda yake faruwa koda sukazo asibitin kafin jikin ys rikice tace kada a fadawa Abbanta idan yaji akwai matsala, hakan tasa sukayi Shiru Mai martaba da Hajiya Innah da Karimah sune suketa jele sai Badi’ah yar Hajiya Kaltume ce Amma itama zakkace batayo halin uwa ba  zuba Mata ido tayi cike da tausayi duk ta kumbura ta dashe kamar bayan hawan jinin ma akwai wani abin dayake damunta daidai lkcn ta wani zabura alamun allurar ta saketa idonta a rufe Amma sai bige bige takeyi ta qarasa da gudu ta riqeta abinda ya janyo hankalin Karimah ta shigo da sauri ganin yanda matar yayan nata ta datse harshenta tana make make jikinta yana jijjiga yasata fita a sukwane ta Kira likita ya biyota da sauri suka shigo daqyar ya samu yayi Mata allurar kashe jiki sannan ya Kira sauran ma’aikatan ya dubesu yace.
“Wannan bazatakai gobeba a yau ayi Mata aiki arabata da cikin nan idan ta qara awa daya zata farka alamominta sun nuna zata iya kamuwa da ciwon jijjiga Wanda zai iya haifar Mata da depression domin kuwa akai damuwa danqare a zuciyarta” Babu bata lkc suka sanya Mata kayan theater suka turata suka shiga da ita dakin theater  sai a lkcn ne Hajiya Innah ta Kira Mai martaba ya daga take fada masa halin da ake ciki tare da cewa “Ranka ya dade fah abinnan yafi qarfin Shiru a fadawa iyayen yarinyar nan likitoci sun shiga da ita dakin aiki Amma sunce sai wani shaqiqinta ko mijinta ko mahaifinta yasa hannu sannan zasu tabata” miqewa yayi daga kishingidar yace “to bari yanzu zan fito” dakansa ya tuqa mota hankalinsa a tashe sai office din Abba ya rakitosa suka tafi asibitin Abba baisan meye yake faruwa ba Saida sukaje likitan yayi masu bayani ya shiga rudu da tashin hankali ya dago yace “ina mijin nata to ranka ya dade ai huruminsa ne wannan” qasa Abba yayi da kansa yace “bayanan yana Abuja baimasan abinda yake faruwa ba Amma zamu sanar dashi yanzu dai kasa hannu a ceto rayuwarta yafi komai muhimmanci.
STORY CONTINUES BELOW
Cikin sanyi jiki da mamaki ya sanya hannu jikin takardar daidai lkcn da taxi ta tsaya Ja’afar ya fito suka zubansa ido yana sallamar me motar ya nufosu Mai martaba gabansa ya fadi ganin irin muguwar ramar da dannasa yayi ga wani baqi da yayi qarasowa yayi ya russuna cike da ladabi ya gaida mahaifin nasa da surikinsa suka amsa tare da tambayarshi hanya yace “alhmdllh” Shiru ce ta dan ratsa kansa na qasa kunyar Abba yakeji tunaninsa ko yasan meye yake faruwa tsakaninsa da Rafi’ah ganin babu wanda yabi takansa yasashi miqewa ya matsa kusa da Innah ya zauna ya rafsa uban tagumi.
Lkc yaja sosai sannan wata likita mace ta fito dauke da jaririn a towel me kauri tana zuwa ta tsaya tace “Waye Ja’afar M Wakil?” Miqewa yayi da sauri yace “Gag…gani” gabansa na faduwa ya nufi nurse din tayi ajiyar zuciya tace “petiant dinka ta farka tun dazun saidai bata cikin hayyaci sai yanzu muka samu ta dan samu so Kuma tunda ta farka take sharar hawaye munyi munyi ta fadi me take buqata bakinta baya fita sosai Amma na iya fahimtar tana cewa Ja’afar M Wakil meyesa kayimin haka me nayi maka alqawarin farin cikin da kayimin kenan irin tukuicin da na cancanta gareka kenan?
Wadannan kalaman tuhumar su taketa maimatawa shiyasa naga ya kamata idan kana gurin kaje kaji meye take buqata”
Numfashi ya sauke me qarfi tare da miqa hannu ya karbi bebien dake nade cikin towel ya bude fuskarsa yaja wata qaqqarfar ajiyar zuciya yace “barakallahu ahsanal khaliqin” kyakkyawan yaron me muguwar Kama da ubanshi saidai qanqanta kamar an fyatoshi a hanci.
Juyawa yayi ya nufi dakin da yaga nurse din ta fito rungume da dannasu dan qarami kamar yar tsana, tana kwance saman gadon ya tsaya a kanta yanajin bugawar zuciyarsa da numfashinsa suna neman daukewa Koda bata cikin yanayin lfy da Kuma walwala ya sani Kuma ya shaida shidin rahama ce garesa a duk lkcn daya rabeta sai yaji nutsuwa tana wanzuwa a cikin ruhinsa.
Idanunsa ya sauke saman nata da suke lumshe ruwan hawaye na kwarara, tausayinta ysna ratsa gabbansa ya rasa meye yasa ya qaurace Mata har tsayin lkc haka Kuma ya yanke duk wata hanya da zata sanya ta samu sauqi yanada tabbacin duk wannan halin da ta kasance a ciki shine sanadi domin da ace bashidin bane bazai kasance Abu na farko da zata bude baki dashi a wannan yanayin me hatsari ba tabbas aikine ja a gabansa ya dawo Mata da farin cikinta fiye da baya.
Miqawa nurse din babien yayi yace “Asashi a Inquivertor” ficewa tayi shikuma ya tsugunna a gaban gadon ya riqo hannun Rafi’ah da yake daure da callular ya hada tafin hannunta da nashi ya matsa a hankali ya dora harshensa saman kuncinta yana lasar hawayen da yake zuba a idonta taja ajiyar zuciya tare da daga hannunta dayan ta dora a kansa sai ta fashe da kuka ta qanqamesa shima hawaye ne suka zubo masa ya janye da sauri yana qoqarin rarrashinta yace “kinga Rafi’ah ki bari kukannan Kinga aiki akayi miki baa buqatar yawan numfashi ma me qarfi balle kuka”
Ajiyar zuciya tayi ta bude idonta akansa shima itan yake kallo cike da tausayi da kunya yace “please kada ki tuhumeni wlh bansan ya akayi hakan ta faru ba ki tayani da addu’a kawai” lumshe idonta tayi kawai kamar mai bacci Amma idonta biyu tabbas tuhumarsa takeson yi saidai ya riga ya katse Mata hanzari a hankali tace “ina fatan kana lfy ba wani abune yasa hakan faruwa daya shafi lfyrka ba” a hankali take mgnr wanda sai mutum yasa nutsuwa sosai zai fahimci me take fada tausayinta ya qara cika zuciyarsa yace “lfy Lau ki huta idan kinji sauqi zamuyi mgn na gde da kyautar dan da kikayimin mai kama dani” bata Kuma ce Masa komai ba suka zauna na kusan 15 minutes a haka kafin ya fita Innah ta shigo ita da su Mai martaba da Abba bude idonta tayi ta saukeshi akan mahaifinta shima Saida gabansa ya fadi ganin irin muguwar ramar da tayi, matsawa yayi ya riqota qoqarin hadiye damuwarta takeyi yace “anya babu wani abu a qasan zuciyarki uwar manya nasanki da baqin zurfin ciki menene waye?”
Yana mgnr ne a rikice idanunta ta sauke akan Ja’afar da yake shigowa da kaya a hannunsa yaji tambayar da Abba yakeyi Mata hakan yasast saurin kadanta Kai ko bai haneta ba bazata iya fada ba a ganinta wannan sirrin gidanta ne tsakaninta da mijinta, ganin bazata fadaba yasa Abba furzar da iska yace “shikenan uwata banayi Miki dole Allah ya kawo Miki mafita” sakin hannunta yayi ya fice tabisa da kallo gabanta yana faduwa tasan bai gamsu da shirunta ba to Amma ya zatayi sirrin ciki sai hanji tasan babu abinda yàke tabbata a rayuwa dadi ko wuya komai me wuccewa ne zata hqr ta jurewa komai akan mijinta musamman da yake uban danta qaddara ta ko Ina ta hadasu batada yanda zatayi dashi bashida yanda zaiyi da ita dole su rufe sirrin juna,
Kwananta uku a asibitin ta samu qwarin jikinta kullum suna tare a asibitin duk da ta lura har yanzun ba daidai yake ba Basu cika magana ba saidai kallo da ido amma yana kula da ita matuqa ya daukewa likitocin duk wani Abu daya shafeta su kansu suna jinjinawa qwarewarsa tare da mamakin yanda akayi hakan ta faru yana matsayin consultant doctor matarsa ta hadu da irin wannan matsalar me wuyar sha’ani wadda ko mutum ya warke idan ya shiga damuwa take taba tunaninsa.
Ba huruminsu bane shiyasa basu zurfafa ba a fakaice dai suke bashi shawara suka sallamesu kwanaki biyar lkcn yaron yayi qwari sosai abu na masu abu kamar Wanda aka hurawa iska ya wani cika abinsa jajir dashi qirar ubansa duk Wanda yaganshi sai yace “masha Allah kamar ba bakwaini ba” daganan gdan sarautar akaso wuccewa ya tubure akan cewa shifa bazaa mayar da matarsa gidannan ba tunda dai ta haihu idanma can dinne baaso ya Gina Mata wani gdan akaita can zai zuba masu kula da ita Hajiya Innah ce ta dage itama akan cewa wlh bazaa kaita gidansa ba a dakinta zata zauna har sai tayi arba’in ita ba lfy ba shima Kuma ba lfyr ya cika ba kansa na cikin kwartanniya yace akaita can waye zai kula da ita da jaririn”
Daurin gindi ta samu gurin Mai martaba dole ya hqr badon yaso ba suka wucce da ita fada ananma yaso hana kaita part din Hajiya Innah Amma Babu fuska yanaji yana gani aka wucce da ita bangaren Hajiya Innah daki guda ta ware Mata da parlour aka gyaranta aka zubawa jariri kayan buqatarsa shima wannan da yana ganin gata a gurin wannan family inda yake fuskantar adawar qarqashin qasa ta mafi yawan bangarori,
Sunada wata Al’ada a gidan idan aka haifi jikin farko na da namiji qanne mahaifinsa ne zasu siyansa gadon bacci da kayan fitar suna harda bargon dauka a yanda tsarin yake idan baayi yaro hakan ba to qasqancine anayin wannan ne tun kwana biyu da haihuwa ko uku Amma shi gashi har kwana biyar duk Wanda ya kamata yayi Hajiya Fatsum da Hajiya Kaltume sun hanasu wannan Abu ya damu zuciyar Hajiya Innah da Ja’afar gashi ya siyo gadon anqi kwantar da yaron akai wai banasa akeso ba itakam rafi’ah bata wani damu ba saboda batasan zafin al’adar ba sai daren rana ta shidda da Ja’afar ya shigo dakin tana kwance tana feeding din yaronta ya zauna ya zuba musu ido duk ya susuce yace “ina cikin damuwa fah Rafi’ah meye yasa hakan take faruwa dana ya kasa samun gata a dangina idan har akayi suna baa kawo gadonnan ba shikenan bazai gaji sarautar gidannan ba meyesa komai daya shafeki yake zuwarmin a baibai Meye karfa Rafi’ah dazu Hajiya Kaltume take cemin wai duk matar data haifi Lil Prince aka kasa samun gadon  baccinsa daga dangin ubansa to karface Kuma  asalinta jinin bayice harma tana cemin indai akayi suna baa samu ba to wajibine a cireki daga cikin zuri’a domin zaki bata iri meye kalmar karfa take nufi ne…..”
Duka na sosai kalamansa sukayi Mata Wanda suka sanya zuciyarta lugude itakam wannan abu na wannan fam yana bata ciwon kai ta rasa meye laifinta meye ta tsare musu, shirun da yaji tayine yasashi cigaba da cewa “Al’amura sai lalacewa sukeyi gashi wadda zatayimin wannan alfarmar daga Badi’ah sai Karimah to Badi’ah mahaifiyarta ta hanata dazun take fadamin ta siyi gadon Amma Hajiya Kaltume tace idan ta bada Allah ya daidaitata ita Kuma Karimah babu ita a jadawali saboda kasancewarta qarama a gidannan na rasa ta Ina zan bullowa lamarin nan  Allah kibani mafita”
Numfashi taja tare da yunqurawa ya taimaka Mata ta tashi zaune ta dubeshi tace “in advise ka cire jinin bayi Kuma karfa daga sashinka hakan zaisa ka rinqa samun matifa cikin rayuwarka Ja’afar don Allah kayimin wannan alfarmar inaji ajikina idan naci gaba da zama matsayin mata a gareka zamu wanzu cikin rayuwar qunci Koda kasancewar nasan duk wani Abu daya fado rayuwata to yardar sarkin sarkice Wanda baa masa dole,
+
Ja’afar bandamu da nakasance cikin farin ciki ba indai farin cikina zai tafa darajar wani shiyasa a rayuwata bancika damuwa da dole saina rabi wani ba tabbas abinda Hajiya Kaltume ta fada maka gsky ne Koda akasin hakan ne Toni na gasqata maka Ni yar bayice Amma ba qasqantattun bayi ba bayin Allah wadanda suke yarda da duk wani hukunci nasa a ban qasa Ina jiran ka yanke duk hukuncin da zaka yanke Allah na roqeka kada bakawa kowa ikon kawo gadon daraja idan hakan ta kasance ku koremu daga garin azare….”
Saurin rufe Mata baki yayi yana girgiza Mata Kai ta zabura ta miqe cikin bala’in da baitaba tunanin ta iyaba ta nunashi da yatsa tace masa “saime Ja’afar shine me danka kirani baiwa kuka ka kirani karfa Ina taka baiwar daka halitta sannan Ina taka karfar to duk abinda zakace ko a fada  maka ka fadamin na shirya karbarsa Allah ya tsinewa Wanda ya fas….” Dauketa yayi da Marin daya sanyata kifewa a gadon daidai lkcn da Hajiya Innah ta shigo ta rafsa salati tace “meye hakan magaji bakada hankali zaka Kai hannunka jikinta yarinyar da ba lfy ta isheta ba meye ma ya farune”
Huci yakeyi kamar Wanda ya hadiyi maciji ya sake nunata da yatsa kawai sai ya juya ya fice a fusace Hajiya Innah ta matsa da sauri ta riqo Rafi’ah tace “meye ya farune kun ninkeni baibai fah” cikin kuka ta rinqa zayyanewa Hajiya Innah abinda ya faru taja fasali tace “to shine zaki tada hankalinki har kina daga muryarki sama da tasa bayan kinsan halin mijinki ko qalau yake ba hqr ya cikaba balle yanzu da kansa yake dawa Rafi’ah dole ke hqr ya Kama domin ke aka cuta”
Sosai ta rinqa kwantar Mata da hankali harda tayi shiru ta dauki jaririn ta fice dashi tunanin duniya ya damu Rafi’ah gabadaya komai ya daukar Mata zafi tanason ta samu wanda zatayi Hira dashi taji dadi babu Hajiya Innah ta saka Mata ido ko yan’uwanta ne sukazo bata barin dakin saboda kada ta fadi wata mgn da zata fallasa sirrin gidan sarautar tayi kuka kamar ranta zai fita ita daya kamata a rarrasa ita akewa tsawa harda mari saboda gskyrta wannan dare dukka bangarorin babu Wanda ya rintsa Ja’afar tunanin maganganun da Rafi’ah ta fada masa ne da Kuma mafitarsa da dansa ya hana idonsa rintsawa ita Kuma alhinin wannan jarabar rayuwa ta zaman qasqanci da boranci tun zamanin quruciya sune suka hanata rintsawa Hajiya Innah kuwa tunanin ta inda zasu bullowa wannan al’amari da yanda zaayi su samu gadon daraja ne ya hanata bacci inda Hajiya Fatsum Kuma bokanta yace daga ita har Ni’imah su tube tsirara kowacce a bangarenta su tsaya a tsaye su kwana a haka kada suyi gyangyadi domin sunayin bacci asirin da suka qullo na haukata Rafi’ah kansu zai koma itakuwa Hajiya Kaltume neman ta inda zata fara bullowa Ja’afar da iyalinsa ya hanata rintsawa Abu na farko daya kamata tayi shine tasan yanda zatayi ta qara shiga tsakaninsa da Rafi’ah sannan ta sace wannan jariri kafin wayewar gari.
Kiran sallar asubar farko Rafi’ah ta tashi da wani matsanancin ciwon Kai ta riqe kan da sauri tare da fara karanta izaja’a ta dan samu relief daidai lkcn da taji an bude qofar an shigo kasancewar da duhu bataga me shigowar ba ana gama shigowa Kuma sai aka haskenta ido da wata fitila me masifar haske ta yunqura zata miqe abinka da mara cikkakiyar lfy sai tashin ya gagara ta rintse idonta daidai lkcn da taji an watsa Mata wani ruwa anyi baya da sauri.
Aikuwa saita wani yi tsalle ta miqe ta qwallah qara tare da damqar jaririn ta qanqame Hajiya Innah da Ja’afar har gware sukeyi wajen shigowa, Hajiya Innah ta kunna glub ta rintse idonta da sauri saboda tashin hankalin data gani inda Ja’afar ya nufeta a guje yana fadin “ Innanillahi wa innah ilaihirraji’un Rafi’ah meye hakan lfyrki kuwa tsirara fa kikayi….” Daukeshi tayi da wani mahaukacin mari tana qara matse danta a qirjinta tana wata dariya me hade da kuka tana cewa “ina ruwanku munafukai azzalumai algungumai dukkanku saina kasheku duk Wanda yazo gurina saina harbeshi danane ni na haifi abuna babu me rabani dashi daga yau nasa masa suna mai martaba Muhammadu Mahir eh sunansa kenan sunansa kenan Allah sunansa kenan dana sunansa kenan Ja’afar ya mutu Mahir maraya ne hhhhhhh Ja’afaru ka mutu ka huta nima na mutu na huta kowa ya mutu ya huta…”
Wani baqin tashin hankali da dimuwa Ja’afar ya shiga ya matsa gurinta saikuwa ta rarumi kaskon wuta ta jefosa dashi tana qyalqyala dariya tana cewa “bazan baka danaba nawane ni kadai kufice ku fice nace ku fice ko na yankaku na shanye jininku hhhhhhh suwaye nan kowa bayasona Ni inason kowa kowa bayaqina ni inaqin kowa..…..”
Tashin hankali yasa Ja’afar yin kanta a guje aikuwa suka Kama kokawa daqyar yayi nasarar karbar yaron ya miqawa Hajiya Innah da taketa sallallami da kuka ya dauki doguwar riga yasa Mata ta hankadeshi ta miqe ta nufi qofa a guje shima ya bita yasawa qofar key ya daka mata tsawa itama kuwa saita daka masa tsawa tare da fuzge ribbon din data kame gashinta dashi ta kurma ihu tana wani dukan iska tana cewa “ni kubani dana Babu inda zaa kaimin dana abani abuna ….” Hadata yayi da jikinsa ya rungumeta sosai a jikinsa kawai saiya fashe da kuka ya bude baki yace “wai… Waime kikeyi ne haka Rafi’ah meye yake damunki ne bakiga bakida lfy bane….” Hannunta ta dora a bakinta tace “shitttttt ni qalau nake nafika nafi babanka nafi babarka lfy ba sunana Rafi’ah ba sunana Deluwa yehhhhh Deluwa takan bola Deluwa takan titi Deluwa ta kowac….”
Hade bakinsa yayi da nata ta kuwa gasa masa cizo ya janye da sauri harshensa har saida ya tsage ya koma gefe yana kallonta Hajiya Innah daketa salati ta Kiran sunayen Allah tsarkaka tace “sai hqr Ja’afar sun haukata maka Mata innanillahi wa innah ilaihirraji’un…..” Dagowa yayi da sauri yace “wht hauka Kuma Innah wanne irin hauka” sake kwashewa Rafi’ah tayi da dariya tace “eh da gaske ni mahaukaciya ce daga yau sunana Deluwa mahaukaciya yar macukule………..
Zubewa yayi rijib a qasa sumamme tsabar tashin hankali Hajiya Inna tayi wajen gdan a guje tana ihu tana Kiran a kawo Mata dauki nan hadimai sukayo ciki a guje daidai lkcn da Jamal ya shigo gdan shima isowarsa kenan daga Rasha ya tawo ganin dansa dan yayansa da matar yayansa da baitaba gani ba ya siyo gadon da aketa badaqala akan samuwarsa sannan ya hadowa matar yayansa kayan fitar suna akwatu guda.
Tun daga bakin qofa yasan gidan babu lfy yana shigowa yaga wata mace ta fice qunshe da Abu a hijjabinta da mugun gudu ganin yanda gidan yake a hargitse ga Kuma gajiya yasa baibi takanta ba ya nufi cikin gidan inda ya hangi mutane dodo guda a qofar bangaren Hajiya Innah haka ya rinqa kukkutsawa har ya Isa cikin part din wata muguwar faduwar gaba yaji lkcn daya riski yayan nasa warwas a qasa kamar matacce aikuwa wata alkafura yayi ya dira kansa ya fara danna Masa qirjinsa tare da neman ruwa ya fara quga Masa tsayin lkc sannan ya fara sauke ajiyar zuciya ya bude bakinsa da sunan matarsa.
Sai lkcn aka ankara da bata cikin dakin aikuwa nan aka bazama nemanta lungu da saqo Amma Babu ita babu lbrnta Jamal ne yace lkcn da Yana shigowa yayi karo da wata mace ta fice daga gdan a guje Amma baibi takanta ba ya zaci mahaukaciya indo ce, salati Innah da Mai martaba dama sauran mutanen dake gurin suka dauka Ja’afar kam hade Kai yayi da gwiwa duk wani tunani ya qwace masa baimasan meye zai tuna ba a hankali yace “suwaye suka haukatata me tayi musu suka azabtar da ita da ciwo me cin zuciya da lalata ruhi Ina zata Ina take me suke nema me tayi musu sun illatata…….”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page