KASHE FITILA COMPLETE BY BATUUL MAMMAN

KASHE FITILA CHAPTER 4 BY BATUUL MAMMAN

 KASHE FITILA CHAPTER 4 BY BATUUL MAMMAN

                Www.bankinhausanovels.com.ng 

Laminde ta sake cewa “ruwan asiri”

Gimbi ji tayi kamar an sauke guduma a cikinta ganin Laminde zata tona mata asiri.

A daidai lokacin Mama ta shigo kuma ta ji abin da Laminde ta fada. Kawu ne ya kara matsawa bakin gadon zaiyi mata tambaya sai daya daga cikin ‘yan sandan ya dakatar dashi.+

Da sauri Gimbi ta kirkiro kuka harda hawaye. Ita kanta mamakin saurin zubar hawayen nata tayi. Kan Laminde ta fada tana rusa kuka

“Abban Haris kaji wata masifa, Laminde ba dai tabin hankali kika samu ba”

Nafi’u ya matso da sauri yana tambayarta ko ta gane shi. Gimbi ta samu yana tayata kukan duk ta cika dakin da karaji.

“Yallabai ku nemo mutumin nan da ya kadeta. Wallahi bazamu yarda ba idan ta haukace”

Tsawa Awaisu ya daka mata ganin itama ta zama kamar mahaukaciyar

“Meye yake damunki ne, dubi tana son yin magana kin hanata”

Ko motsi batayi ba domin tasan muddin Laminde ta fadi abin da ta gani kowa yarda zaiyi. Musamman Awaisu da ta kula yanzu kamar ma ya tsaneta da Mama da take saka mata ido.

‘Yan sandan suka ce kowa ya fita zasuyi mata tambayoyi. Gimbi ta wani kankame Laminde

“Babu inda zani sai na tabbatar da lafiyarta. Laminde amana ce garemu. Ni satar da na kamata zatayi min na yafe. Ki yafe min, duk laifina ne da na kasa hakuri ban saurari dalilin da yasa kika shigarwa Abban Haris daki ba”

Maganar ta doki kunnen Laminde cikin kaduwa, _sata!_. Yanzu sharrin sata Gimbi ta kala mata. Hawaye ta soma yi tana kallon danta wanda aka zubar mata da mutumci a gabansa.

Sake bude baki tayi zata fadi gaskiyar abin da ta gani Gimbi kawai ta mike tsaye tana dafe kai

“Wayyo kaina, washhhh”

Sai gata ta fadi a kasa gaban Kawu. Duk abin Awaisu da gudu ya fita neman likita. Mama wadda tun shigowarta bata ce komai ba sai lokacin tayi wani murmushi mai ciwo. Iyakar abin da Gimbi tayi a gabanta yanzu ya tabbatar mata da gaskiyar Laminde. Fita tayi jiki a sanyaye tana bakincikin wannan al’amari. Tana shiga mota ta sanar da dreban inda zai kaita.

*****

Da gaske Gimbi taki farfadowa har kusan rabin awa. Likitan ya rasa gane mene ne yake damunta. Da ya auna jininta ya ga ya hau. Awaisu yayi wa bayanin cewa a kula da ita domin ciwon Laminde ya tsaya mata sosai. ‘Yan sanda suka gama bincikensu suka tafi. Iya abin da Laminde ta fada bai wuce cewa ba sata tayi ba kuma bata shiga dakin maigidan ba.

Bayan fitarsu Kawu ya tilasta mata ta fada masa gaskiyar me ya faru. Tana fada tana kuka tace dole zata sanarwa Mama.

“Laminde mutanen nan ba sa’aninmu bane. Wannan matar idan har gaskiya kike fada tafi karfinmu ta ko ina saboda haka ki bar maganar nan”

Kokarin zama tayi Nafi’u ya tayar da ita sosai “iyalin mutumin nan musamman mahaifiyarsa suna cikin hatsari. Da ace kana ganin irin yadda uwar mijin take rayuwa a gidan bazaka ce nayi shiru ba. Ba sharrin sata ba ko me zata yi min sai na fadawa ‘yan sandan nan gaskiya”

Kafin Kawu ya bata amsa yace Nafi’u ya basu wuri. Ya kama kofar zai fita Gimbi ta shigo fuska cike da hawaye.

“Laminde ki rufa min asiri. Abubuwan da kika gani sharrin shaidan ne. Kada ki tona min asiri ki raba sunnar Annabi SAW. ”

“Kinga Hajiya daga nan garinmu zamu wuce da ita. Ina rokonki da kiyi hakuri ki janye satar da kika dora mata. Daga yau kin dena ganinta ma”

Farinciki ne ya bayyana a fuskar Gimbi har ta kasa boyewa Kawu. Kudi ta debo a jakarta ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu.

STORY CONTINUES BELOW

“Bama neman komai daga gareki. Kina iya tafiya amma kada ki taba mantawa rana dubu ta barawo….”

Dan dakatawa tayi tana auna maganarsa sai kuma tayi saurin  fita saboda Awaisu yana wurin likita ta fito daga dakin da aka bata. Laminde ta kalli Kawu zata yi magana yace ta bar komai a hannunsa. Irinsu Gimbi baka musu fito na fito lokaci guda, musamman idan baka da shaida. Zaiyi iya kokarinsa wurin taya Awaisu da mahaifiyarsa da addu’ar neman tsari.

*****

Naman kaza take ci tana kurbar juice a kofin glass taji an banko kofar dakinta. Duk gidan hatta Shuhada da take iya yi mata rashin kunya wasu lokutan bata isa tayi mata haka ba. Shiyasa tana jin karar kofar ta zabura ta tashi. Kusan karo suka yi da Mama kafin taji saukar mari zazzafa a kuncinta.

“Bebi sai Allah Yayi mana shari’a ni da ke. Me nayi miki haka kika lalata rayuwar ‘yata”

Duk da radadin da kumatunta yake yi bai hanata dariyar keta ba.

“Su Aminatu salihan bayi. To ai kinsan ba’a daya a dangi. Wannan Gimbiyar taki kina ganinta haka ba karamar fitinanniya bace.”

Mama ta kara harzuka “kada kiyi tunanin zan bar maganar nan haka. Naji komai daga wurin Laminde. Nasan kece kika kaita wurin shaidanun bokayenki.”

“Kin kuskuro ‘yar uwa. Wannan karon Gimbiya gaban kanta tayi. Shawara ta daya gareki shine ki nemi Awaisu ya mayarda uwarsa garinsu. Idan ta cigaba da zama to ina mai tabbatar miki yanzu ta fara kwanciya a asibiti. Gimbi ba karamin tsana tayiwa wannan matar ba”

Kallonta Mama tayi sosai. Anti Bebi ko kadan zuciyarta bata rissina ga abin da tayi niyya. Idan aka cigaba da haka watarana ba  auren Gimbi ne kadai zai mutu ba. Su ma iyayenta mutumcinsu sai ya zube a idanun al’umma.

“Bebi ki dubi Allah ki kyale Gimbi tayi rayuwarta. Idan tazo gidanki kici mutumcinta ki koreta. Ke kin sani bin boka da malaman tsibbu haramun ne amma kike takewa. To akan mene ne sai kin hada da ‘yata?”

“Masu ‘ya manya, abin da nake so ki sani shine yaran yanzu idanunsu a bude suke. Kowa ya waye da sanin rayuwa. Idan baki nemi taimako ba kina kallo bakincikin da namiji zai kasheki a banza. Ko zaki ce kin manta irin bacin ran da Innarmu tasha wurin Baba? Tun lokacin nasan cewa namiji zuma ne sai da wuta. Ban ga wani shegen da zan ragawa ba yazo yana cin zarafina”

Mama ta saki baki tana sauraron kanwarta da tayiwa duniya gurguwar fahimta.

“Ba duka aka zama daya ba Bebi. Yanzu kina jindadin zama da mijinki ya zama kamar hoto sai yadda kika juya shi?”

“Wannan ne mulkin, ko da wasa bai isa ya takani ba. Gimbiya kuma ki dena ganin laifina ita ta kawo kanta. Mata da dama a zamanin nan sai da haka suke samun damar cimma burinsu a wurin mazajensu. Me za’ayi da uwarmiji banda takura da sanya idanu”

Anti Bebi tayi nisa. Mama gani tayi cigaba da yi mata magana bacin lokaci ne sai kawai ta juya ta fita daga gidan. Ba abin ta fadawa Innarsu ba tasan babu wani mataki da zata dauka. Komai Anti Bebi tayi daidai ne. Tana zuwa gida ta kira Alh Mudi a waya ta fada masa. Ya rinka fada kuwa kamar ya ari baki. Allah Yasa yana gari yace ta kira masa Gimbi kafin ya karaso gidan.

*****

Sai yamma Gimbi ta sami damar amsa kiran Alh Mudi. Lokacin ta tabbatar Laminde da ‘yan uwanta bazasu cigaba da zama barazana a gareta ba. Shi kuma Awaisu ya wuce kasuwa.

A tsorace ta shiga gidan domin tun fitar Mama daga dakin asibitin jikin Gimbi ya bata akwai matsala. Sama ta hau dakin Alhajin ta samesu duka su biyun babu wanda yayi mata kallon arziki. Haka ta sami wuri ta zauna can gefe. Alh Mudi ne ya fara magana

“Gimbi ki fada min tsakaninki da Allah mijinki yana tauye miki hakki ne?”

1 2 3 4 5 6 7Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE