RUBUTACCIYA BOOK 3 CHAPTER 8 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

RUBUTACCIYA BOOK 3  CHAPTER 8 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO 

                  Www.bankinhausanovels.com.ng 

MUN TSAYA 

Nasreen ba ta san lokacin da ta saki murmushi ba. Ya sunkuya dai-dai fuskanta yana gaya mata kalamai a hankali kuma ya dinga hura mata iska a fuska, tana jin kasala tana shigarta, hade da barci wanda ba ta san lokacin da barcin ya yi awon gaba da ita ba. A fili yace, “Allah ya baki lafiya Wife.” Ya sumbaci goshinta ya fice. A falo ya sami Umma da hafsat fuskar nan tata ta kumbura gwanin ban tausayi. Www.bankinhausanovels.com.ng

Har zai wuce Umma ta ce, “Zo nan ina son magana da kai.” Babu musu ya dawo ya zauna yana duban Umman, sannan ta fara magana, “Ka ji tsoron Allah Sultan ka gaya min me Hafsat ta yi maka haka da zafi da har kayi mata irin wannan dukan? Gaya min me ta yi maka? Idan babu laifin da ta yi tsabar mugunta ce kawai, ka gaya min sai in dauki mataki.”

Sultan bai ji dadinl da Umma za ta yi masa magana irin hakan a gaban su Hafsat ba, wannan kamar ta ce gobe su sake aikata irin laifin ne. A natse yake magana kamar babu abinda ke damunsa, “Umma ina daki yarinyar nan ta fado min babu Sallama, ta yaya za ayi da girmanta ta dinga shigo wa mutane babu Sallama? Ashe karatun addininta, da yadda kika ba mu tarbiyya

ZAMU TASHI 

akan ko falo ne bamu isa mu shigo maki babu Sallama ba, baiyi mata amfani ba. Shiyasa na koya mata darasi ta hanyar nan.’’ Umma ta zaro idanu, “Shi ne dalilin irin wannan duka? Ai ni ina zaton sata ta yi maka, ka kama ta da duka irin na barayi. Sultan fito ka gaya min kawai kafi son Nasreen akan Hafsat. Ko kuma ka gaya min baka da gaskiya shiyasa kake tsoron a shigo maka daki babu Sallama.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Sultan dai ya yi shiru ba tare da ya sake furta komai ba. Kafe Kanwarsa da idanu ya yi yana jin tausayinta yana ratsa shi. Bai kula da irin barnar da ya yi mata ba, sai yanzu. Ta tsorata sosai da shi, domin ko a yanzu din ta kasa sakin jikinta, a falon haka ta Ki yarda su hada idanu. Ita kanta Madam rawar kai Zakiyya ta shiga hankalinta. A hankali ya kirawo sunanta, wannan shi ne karo na farko da kallon Rahama ya hada ta da Yayanta. A hankali ta dago hawaye suna sake bin idanunta. Da kai ya

kirata, ta matso jikinta yana rawa. Hannunta ya duba zuwa fuskarta. Jikinsa ya sake yin sanyi ya ce, “Hafsat kin gani ko? Kullum ina kiyaye taba lafiyar jikinki amma kin kasa fahimta, har sai da kika Kure ni. Tashi mu je in kai ki asibiti.” Muryarta na rawa ta ce, “Don Allah Yaya kayi hakuri.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Girgiza kansa ya yi cikin rauni da soyayya irin ta jini ya ce, “Ya wuce Hafsat, bana son kukan.” Ta shiga goge hawayenta. Umma kuwa jikinta ne ya yi sanyi a karo na farko, duk a tunaninta Sultan ya tsani Kannansa ne, amma yanzu ta ga asalin Kauna a Kwayar idanunsa. Haka ta sauko sosai daga irin fushin da ta yi da shi. Idanunsa ya mayar kan Umma yana dubanta, “Umma ki yi hakuri ki yafe min bata maki da nake yawan yi. Na fi buKatar addu’arki fiye da irin wannan fushin. Fushin ki masifa ce a gareni.”
Umma ta girgiza kai, “Na yafe maka Sultan, Allah ya yi maku albarka, ya Kara hada min kawunan ku.”
Gabadaya suka amsa da Ameen, sannan Hafsat ta fito suka shirya zuwa asibiti.
A can Garin Kaduna, Mairo ce tsaf da ita ta Kara kyau da haske. Dama rashin gyara ne duk ya canza ta. A yanzu kuwa ta zama ‘yar gayu da ita sai Kamshi ko ta ina a cikin gidan. Shi kansa Abban ya sami natsuwa sosai. Yau Hajiya Ladidi ta biyo ta Unguwar, don haka zuciyarta take gaya mata tunda babu Hajiya Salma za ta iya zuwa da sunan duba Alhaji Lukman. Sai da ta sake gyarawa tsaf sannan ta doshi hanyar gidan. Naufal baya nan yana Makaranta, gidan babu kowa daga ita sai Abba. Don haka tayi ta kwada Sallama. Abba ya dubi Mairo dake matsa masa Kafafu yace, “Maryama kamar buga Kofar nan ake yi, maza je ki ki ga waye.” Mairo ta mike ta nufi Kofar, Abba ya bi ta da kallo, tana matuKar _ KoKari wajen kyautata masa, sai dai soyayyar Salmarsa halitacciya ce a zuciyarsa. Yana yi wa Salma soyayyar da ita kanta bata san da ita ba. Sai dai zuciya tana son mai kyautata mata, rashin kyautatawar Salma shi ya rage kashi daya daga cikin manyan kason da ke ransa. Mairo tana bude Kofa aka hau kallon kallo. Hajiya Ladidi ta yi bala’in rudewa sai kallon Mairo take yi cike da mamaki da tsoro. Mairon da ta sani da, a yanzu ba ita ba ce ta sauya fiye da tunanin mutum. Baki sake Hajiya Ladidi take dubanta. Duk da ta gaisheta da girmamawa, amma kuma ba kamar yadda take yi mata a baya ba, ta saba sai ta durkusa har Kasa take gaida ta, ba kamar yanzu ba, da ta dan rankwafa. Hajiya Ladidi bata amsa ba, ta sa kai ta shiga tana sake dubanta. Abba yana ganin Hajiya Ladidi ya ji gabansa ya fadi, domin har yanzu tunani yake yi duk ranar da Salma ta san wannan lamarin, bai san ta WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG yadda za a kwashe ba. Mairo kuwa shige wa ciki ta yi gabanta yana fadiwa da Karfi. Hajiya Ladidi ta sake bin hanyar da Mairo ta bi da kallo tana jinjina kai, dole da akwai wani abun da ke faruwa wanda ake boye wa. Sama-sama suka gaisa ta dube shi tace, “Amma na ga Maro ta sauya sosai ko ta daina aiki a nan ne?” Abba ya sha mur sosai yace, “Da ta daina aiki a nan me za ki ganta tana yi kuma?”  Hajiya Ladidi ta saki yaKe ta ce, “Haka ne kuma. Dama na zo ne in gaya maka abinda ya’dade a cikin zuciyata. Tunda Hajiya Salma ba dawowar yanzu bace ba, shi ne na ce me zai hana mu yi aure sai zumuncin mu ya Karu?” Abba ya dube ta kawai yana girgiza kai, mata kenan su babu ruwan su da abinda zai je ya dawo. Babu ruwansu da matsalar ‘yar uwarsu idan har su din za su sami abinda suke so, basu damu da matsalar wata ba. Kullum cewa ake ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ce, wannan ba haka yake ba, zai fi amincewa da ace ciwon ‘ya mace na da namiji ne, domin da namiji a yanzu shi ne mace za ta gaya masa matsalarta ya nemo mata mafita ba tare da ya bari wani yaji ba, sabanin ‘ya mace da kana gama gaya mata matsalarka za ta nuna a gabanka ta tausaya, idan aka sami makira har ta fara kuka, kuna rabuwa za ta yi dariya, ta sanya katin dubu ta fara kira tana gayawa duniya dukkan abubuwan da ke faruwa. Zai fi kyau mace ta kama Allah ta rabu da duk wata Kawa, idan ma za ta yi Kawar ta yi wacce za a hadu a gaisa ayi dariya a rabu, haka ta boye mata matsalarta ta bayyana mata samunta. Dubanta ya yi sosai ya gyara zama ya ce, “Amma Hajiya Ladidi kin bani mamaki sosai, ban yi tunanin duk irin amintarku a ce za ki iya zagayowa ki ce za ki auri mijin aminiyarki ba. Kada ki manta akan farin cikin ‘yarki ta bar gidana taje ta Kwato mata ‘yancin da take tunanin Sultan zai tauye mata. Abin mamaki sai ga shi kin zaga yo ke baki da burin da ya wuce ki aure mata Www.bankinhausanovels.com.ng miji, ki Kuntata mata.” Hajiya Ladidi ta dubi Abba cikin kissa irin nasu na ‘yan duniya ta ce, “Alhaji ba haka bane, naga tuni Hajiya Salma ta fita batunka, tunda tana samun maza masu debe mata kewa, tana
harkokinta, gidan malamai ma da ita muka je ta ce a mallake mata,kai. Abubuwanta sun Kazanta. Bari ka ga gaskiyata.Ta bude wayarta ta bude masa sakonnin message din da tabbas da lambar Hajiya Salma ce, wanda babu komai sai maganganun da suke . nuna cewar tana alaKa da wasu mazan. Sai dai kuma ba lallai abinda take nufi kenan ba, idan aka yi la’akari da mutum yana iya yin wata magana a sauya masa, haka kuma ko hoton Hajiya Salma aka kawo masa tana tsirara tare da wani, ba zai taba yarda ba, zai fi amincewa kansa kwamfuta ce ta hada wannan sharrin ba dai Salmarsa ba. Salma ta tsani mazinaci, fiye da irin tsanar da za lta yi wa wanda ta ga ya kashe rai, me zai sa a lokaci guda a dangantata da zina? Murmushi ya yi sannan ya ce, “Na gode da wannan sheda da kika bani akan Salma, na kuma ji dadi sosai.” Yana duban yadda Hajiya Salma take aikin murmushi da alama murna take yi ta ci galaba za ta tsinka igiyoyin aure, farin ciki take yi za a girgiza al’arshin Allah, farin ciki take yi za a aiwatar da abinda shaidan yake murna a kai, Allah yake fushi akan aikata shi. Yace, “Hajiya Ladidi shaidun da kika kawo min sun yi min kadan akan Hajiya Salma, zai fi kyau ki bari sai idan tana cikin hotel sai ki kirawo ni inganta da idanuna, kai Wallahi a cikin hotel din ma, sai Salma ta rike ni ta ce min Lukman ni ce Salma matarka, uwar Sultan da Haidar da Hafsat. Kila idan na ga hakan in amince cewa Salma fasiKa ce. Ki fadi wani abu akanta ba zina ba, ina cikin daya daga cikin mazajen nan masu dogon tunani da nazari kafin daukar mataki, ina daya daga cikin mazajen da suka amincewa iyalansu. Idan har Salma za ta iya aikata fasiKanci babu shakka nima zan kasance daga cikin su, ban kasance fasiki bana
Kasance mai kyakkyawar zuciya, bana zaton zan zauna zaman aure da fasiKa. Ki bar ganin dana Sultan ya kasance da ‘yarki, ki yi tunanin halayyar dana iri daya ne da halayyar “yarki. Ko daya babu ta inda Sultan ya zama mai irin wannan halayyar. Allah ya Kadarta auren su ne, saboda ya nuna wa Salma ishara, domin ta tsani masu aikata munanan laifika a maimakon jawo su jiki da nuna masu abubuwan da suke aikatawa Allah ya haramta hakan. Ke kanki kin sani, a gabanki Salma tana nuna Kyama da irin wani

abun da kike aikatawa, ita haka take bata iya boye tsanar da ta yi wa abu Kin yi matuKar KoKari wajen zuwa gaban miji, uban ‘ya’yanta ki aibatata da munanan kalamai. Bana jin zan taba mance ki. Kina iya tafiya.” Jikin Hajiya Ladidi ya yi matukar sanyi, bata ji dadin irin wannan gwasalewar ba, ita kanta ta sani Hajiya Salma mace ce mai tsananin gudun zina, haka ta tsani mai aikata shi, amma kuma duk wanda ya ganta tana Kawance da Hajiya Ladidi dole ya kawo wani abu a cikin ransa. Ta saki ajiyar numfashi ta sake dubansa, “Ban san wacce yarda ce take a tsakaninka da matar da ta gujeka, ko wayarka bata daga wa, saboda yadda ta riga ta cireka a cikin tsarin mazajen da take so ba ada can baya. Kuma ni iya gaskiyata nake gaya maka matarka dai tana mu’amala da wasu mazan.” Ransa ya soma Baci da irin Batancin da Hajiya Ladidi take yi wa Salma, don haka ya gyada kansa cike da bacin rai, ““Na ji na gode. Ina sonta a hakan, idan ita ce magajiyar karuwai, ni a wurina mai tsafta ce, bana daya daga cikin sakarkarun mazan da kike tunani. Don Allah tashi ki bar min gidana. Kuma da kike maganar ta mallakeni, idan da abinda yafi mallaka, ina son tamin ta cancanci mallakeni din tun tuni Hajiya Ladidi ta mike tana yamutsa fuska, Sai da ta tabbatar da ta yi nesa da gidan, Kafin ta zari wayarta ta kira Hajiya Salma. Bata iya jin gaisuwar da Hajiya Salma take yi mata ba, tace, “Ni tsaya min. Yanzu na dawo gidanki, nazo wucewa nace bari in leKa mu gaisa. Abin mamaki sai na kama mijinki da mai aikin Ki a filin falo, suna aikata abinda ba zan iya furtawa ba,, Yanzu haka na tafi na barshi da Kunya da kame-kame, Duk, da Hajlya, Salma, tayi WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG matuKar,razana da gigicewa, har bata san lokacin  data furta, “Kan uba! ,Wacce Mairon?’ Wai da wa Kika kama ta? Mijina Alhaj_Lukman din?* Daga baya kuma taja bakinfa ta tsuke kamar Wacce aka yiwa, ishara data rufe bakinta, ta _kuma dawo cikin hayyacinta. hakan yasa a lokaci guda ta tattaro dukkan ‘yar sauran natsuwar da ta rage mata, ta hada su wuri guda, sannan ta saki ajiyar zuciya, har ta koma tana jin ‘haushin kanta. “Amma dai Hajiya Ladidi yadda kika ci nasarar jefa shaidan a zyciyata, Allah ya rama min. Me kike fada ne? Abban Sultan’ Har abada ‘babu wanda zai danganta Abban Sultan da abinda kike fada in gasgata shi koda Kuwa Wacce ta tsuguna ta haife nine ta kirawoni tana gaya ‘min mdganar nan bazan amince ba  Bare Kuma ké da kika Kware wurin‘makirci. Ta yaya ma zuciyata zata  Aminta dake? ‘Yaushe’ ya fara aikata masha’a bayan Shekarun da yayi a turai, inda ya hadu da mata masu jida kansu ya kaucewa sharriin su Saida ya dawo kasata’ Najeriya, da girmansa, zai aikata hakan? Kuma agun mai aikina? ‘Ki dai tuna ‘abinda’Kika gan shi ‘yana aikatawa ba” abinda Zuciyarki ta Sanar dake ba” Hajiya Ladidi -tayi ‘rantsuw tana -yi_ tanta sakewa, *don haka ‘Hajiya Salma ta fara’ jin zuciyarta’ tana ‘rawa yar yardar data bashi ta nemi fizge abinta da Karfin tsiya jin tayi shiru yasa Hajiya Ladidi ci-gaba da’yi mata famfo,-har sai da jikinta ‘ya kama rawa‘ta datse waydr tana ‘jin ’wani irin’ Kunci a ranta’ ji take! har abada ba *zata iya zama da miazinaci ba haka ko  ranta za,a ‘zare ba za ta iya rabuwa da“ soyayyar’ Alhaji Lukman’ba’ da tayi mata rassa! Ta hade da jinin jikinta.“Ta -‘rasa me take ji a ranta ‘a tsakanin tsanarsa’ da“ tausayinsa’ da “Kuma: kishinsa da ‘ sonsa?  Ta tafi ta bar shi ne saboda tana tsoron Nasreen ta ci galaba akan danta, haka kuma tana da tabbacin Sultan ba zai iya kwatanta adalci a tsakanin Zakiyya da Nasreen ba. Kankat! Ta zo nan ne domin ta sake raba Nasreen da zuri’arta. Can daki ta shige yadda babu mai iya jinta, sannan ta kira Alhaji Lukman a waya. A lokacin yana zaune tare da Mairo fuskarsa da alamun damuwa, Mairo ta yi magana cikin sanyi, “Abba me yasa za ka damu da maganar Hajiya Ladidi? Kafi kowa sanin duk a cikin zancenta babu gaskiya. Na zauna da Umma nasan halinta, nasan abinda za ta iya aikatawa nasan wanda ba za ta iya ba. Maganar mallaka kuma da take yi Karya take, ita ce ta WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG yaudari Hajiya ta ce, akwai wani malami a cikin Alqur’ani yake ciro addu’a ya yi idan ya yi addu’ar sai ta sha mamakin irin yadda za ka koma tamkar yaron Umma. A kunnena na ji Umma tana cewa ita idan har ta tabbatar da babu kaucewa za ta iya yi, saboda kana yawan yi mata gardama akan kome ta gaya maka. Ka ji ta inda ta yi wa Umma dabara kenan, kasancewar ta san Umma ta tsani shirka. Haka maganar bin maza duk Karya ce, ina ji wasu lokutan Umman ke yi mata fada akan rayuwarta, har ma tana nuna Kyama ga Hajiya Ladidi. Don haka ka daina damuwa.” Abba ya saki ajiyar zuciya, “Lallai sun yi hakan kuma sun sami nasara akaina, ba wai don bana ibada ba, sai don Allah ya aiko min da jarabawa kuma na karbeta. Maryama ba maganar Hajiya Ladidi ya sanya ni damuwa ba, don bana jin akwai abinda za ta fada akan Salma har ya dameni, nasan wacece matata tun Kuruciya, na santa da zafafa kiyayyarta akan abinda ta furta ta ce ta tsana bata so. Kawai-ina jin damuwar yadda Salma ta yi zamanta a gidan danta ta nuna bata damu da ni ba, duk irin son da take gwada min.” Ya Karashe cikin damuwa, sai -kuma ga kiran wayarta, don haka jikinsa na rawa ya dauka, domin ji yake kamar ana Kara masa sonta. Yana yin Sallama ta kasa jurewa, sakamakon wani kishi da ya tokareta, ta fasa kuka. Iya gigicewa Alhaji Lukman ya gigice, tambayarta kawai yake waye ya mutu? Cikin kuka take cewa, “Abban Sultan yau ni za ka yi wa haka? Duk yadda na baka kulawa na hana kaina kwanciyar hankali don in kyautata maka, yau kuma dan bana nan shi ne za ka kasa jure wa har sai ka aikata Barna?

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page