DR TAHEER CHAPTER 2 BY UMMU ASHRAF

DR TAHEER CHAPTER 2 BY UMMU ASHRAF

               Www.bankinhausanovels.com.ng 

Back to labari…+

Ranan kusan raba dare sukai hira a parlor gaba dayansu har yaran,sai can dare snn kowa ya tafi daki ya kwanta.

Washe garima still hakan ne ya fari,sai bayan sun gama lunch Taheer yacema yaran su shirya zasuje unguwa,hakan kuwa akai duk suka shirya, Al’ameen, Ramadhan da Kuma Layla,sukayima su ummi sallama snn suka tafi.

Gidan Ramla suka fara biyawa wnn karon dai anyi saa Taheer ya shiga ciki Amma basu dadeba yace su tafi,yawo suka shigayi sosae,sunje parks iri iri sunje shopping,su Al’ameen sukace akwai park din da suke son zuwa don haka ya nufi can dasu.

Bayan sun fito a mota ya samu wuri ya zauna su Kuma suka shiga wasanninsu Yana gefe Yana kallonsu,yana Kuma lurada wata yarinya dake gefenshi sai kallonshi takeyi kmr ta samu tv,Yana Shirin barin wurin sai ga Layla ta zauna gefenshi tana mai murmushinta me kyau tace daddy wayana zan dauko cikin mota zamuyi pictures ne”ba tareda yace komai ba ya Mika Mata key din ta tashi ta tafi,tana Shirin bude motan taji sallama a bayanta,ta fasa budewan ta juya tana kallon mai sallaman,budurwa ce kyakyawa tanata

murmushi,itama Layla murmushin tayi Mata snn tace sannu”yawwa”ta amsa Mata kafin taci gaba”don Allah sis taimako nakeso kimin idan ba damuwa”Layla ta gyara tsaiwanta tace umhum inajinki”yarinyan ta juya ta kalli Taheer snn tace don Allah wancan mutumin uncle dinki ne ko brother dinki? Layla ta juya ta kalleshi itama face dinta da murmushi snn tace”daddy na ne”yarinyan ta danyi shiru tana kallonta ta sake juyawa ta kalli Taheer din kmr dai bata yadda da abinda ta fada ba sai ta sake sakin smile tace to don Allah alfarma nake so kimin,tun da kukazo wurin nn nake kallonshi naji ya kwanta min a rai na Kuma kasa tunkaran inda yake,shine nakeso idan ba damuwa dn Allah kiyimin iso wurinshi inason yin mgn dashi,Layla daketa faman doka murmushi kmr an Mata albishir da aljanna tace”u don’t have to beg me plss,idan kika shawo kanshi ni kaina ba karamin farin ciki zanyi ba,so don’t worry bari inyi mgn dashi”tana gama fada ta juya zuwa inda yake zaune dama tun dazu Yana kallonsu Yana Kuma tunanin me suke tattaunawa daya sa Layla farin ciki haka.Ta karaso ta zauna dab dashi snn tasa hanu ta kamo nashi ta wani langabe irin yanda tasan idan tayi mai hakan yana saurin yi mata duk abinda takeso idanunta cikin nashi tace”daddy plss I want a favour from you”ya kauda kanshi gefe ganin yanda har yanayinshi ya fara sauyawa cikeda karfin hali yace”what”ta sake marairaicewa tace daddy waccan matan ne takeson mgn dakai Amma ta kasa zuwa shine tace i should talk to you Dan Allah daddy kar kace aah plsss,at least listen listen to her bakasan me Allah zaiyi ba”ya lumshe ido ya bude Yana sake jin wani baqon al’amari na ziyartanshi,da tasan yanda shagwaban nn nata keda effect a kanshi da bata ringa yimai Shiba,ya daure dai yace alright kice tazo”cikeda murna ta dago hanunshi dake cikin nata ta manna mai peck snn ta mike zuwa inda yarinyan ke tsaye,shiko Taheer mutuwan zaune tayi,gabaki daya ta hargitsa mai lissafi,yai kokarin daidaita kanshi ganin yarinyan ta kusa karasowa inda yake,idanunshi har sun canza launi”Assalamu alaykum”yarinyan ta fada bayan qarasowanta,ya amsa mata ciki ciki snn ya matsa Mata ta zauna,ba tareda ta kalleshi ba tace am sorry idan zuwana ya bata maka rai I just can’t let go of you ne,Amma Dan Allah ko digits dinka ka bani inyaso sai muyi mgn ltr,ya juyo yana kallonta ba yabo ba fallasa yace don’t worry Fadi abinda Zaki fada kawai”ta Dan gyara zama snn tace first inaso in tambayeka yarinyan can tacemin Kai dad dinta ne,da gaske ne?bai san sanda wani murmushi yai escaping lips dinsa ba,Yana kallon cikin idonta yace”ba gaskiya bane,she is my wife”ta zaro ido tace u mean wannan din matarka ce?ya girgiza Kai still smiling yace ya naga kinyi mamaki,baa riga anyi auren ba ai,yarinyan ta Dan kauda Kai snn ta qaqalo murmushi tace shknn Ni zan tafi,am sorry for disturbing u”bata jira cewarshi ba tayi gaba da sauri,shi Kuma ya bita da kallo Yana murmushi ya shafa beared dinshi yace”good girl”Layla na ganin ta tafi ta qaraso inda yake da sauri tana Dan turo baki tace dady me kace mata?ya danyi murmushi snn yace bance Mata komaiba”Amma naga ta tafi ranta a bace nidai am sure ka fada mata wani mgn”ya kamo hannayenta yace of course na fada Mata wani mgn,I have told her ni inada wadda nakeso”ta zaro ido da sauri tace Dan Allah da gske dady,Amma meyasa baka taba fadamin ba,I want to know her plss”murmushi kawai yakeyi Yana shafa gemu yace je kirawo su Al’ameen mu tafi”but dad…bata karasa ba ya katseta”just go and call them baby don’t waste my time”bata sake cewa komai ba ta kirasu,suna zuwa Kuma suka shishiga mota suka tafi.

Saida ya sai musu kayan makwalashe snn suka nufi gida,Layla ce kadai ta shiga ciki su Kuma suka wuce masjid don time din sallah yayi.

Itama Layla bayan tayi sallah bata fito parlor ba Saida tayi isha’i,ba kowa parlon sai nafeesa data fito itama ynxu,ta kalli hibba dake bacci kan kujera tana kokarin daukanta saiga Layla,ta fasa zaukan nata ta zauna tareda daukan remote tace da Layla”dauki hibba ki kaimin ita daki”Layla ta zaro idanu tana kallon nafeesa tace”mami banji me kikace ba”cewa nai ki dauki hibba ki kaita daki,ta sake maimaita Mata,Layla ta Dan marairaice tace”Mami Allah bazan iya daukanta ba”nafeesa ta juyo da mamaki tana kallon Layla tace ban gane bazaki iya daukanta ba,,ta sake langabar da kai tace Allah Mami bazan iyaba kinga tanada nauyi fa Kuma dady yace in dena daukan abu me nauy…bata karasa ba nafeesa ta cillo Mata pillow dake gefenta,tana Mata mugun kallo tace”kin dauketa kin wuce ko sai na gaura maki Mari,sa’arki ce ni da zan saki abu kicemin bazaki iyaba?Layla da har ya fara hawaye ta shiga kokarin daukan hibba dake kan kujera,ta dago hannayenta nafeesa ta daka mata tsawa”karyamin ‘yar zakiyi?Layla bakida hankali koh…daidai nan Taheer suka shigo parlon su Al’ameen na biye dashi,ya kalli Layla dake ta faman share hawaye snn ya kalli nafeesa yace”what’s wrong?yaya wai yarinyan nan ince ta dauki hibba ta kaimin daki take cemin wani wai bazata iyaba…ba tareda yace komaiba ya nufi inda Layla ke tsaye tana sharan hawaye,ya janyota zuwa jikinshi ya shiga share mata hawayen yace”it’s okay stop crying”nafeesa baki da hanci ta bude tana kallon ikon Allah,,ita data kawo mai kara instead of ya mata fada shine yake lallashinta…”yanxu yaya goya mata baya zakayi?kiri kiri nasata abu takiyi Amma har wani lallashinta kake..har ynxu Layla na jikinshi yace”ai ba cewa tayi bazayi ba koh?cewa tai bazata iyaba and mgnr data fada gsky ne bata iya daukan abu mai nauyi infact nine ma na hanata yin hakan,,still nafeesa da mamaki tace yanxu hibba har wani nauyi gareta da zatace bazata iya daukanta ba,..Saida ya zaunar da Layla kan kujera snn yace”wnn katuwar ‘yar taki koni da kyar idan zan iya daukanta”yanzu dai kana nufin bazata dauketa ba,,yace kiyi hakuri gsky ni Bari in dauketa,ya dagata ya kaita har daki snn ya dawo yace to an Kai maki ita sai hankalinki ya kwanta me ‘ya…ta danyi mai hararan gefe tace Kaine dai zaace me ‘ya,,,dariya kawai yayi daidai lokacin su ummi suka shigo parlon,,umma na kallonshi tace akwai fa mgnr da nakeson yi dakai son”ya danyi shiru kmr Yana nazari sai Kuma a hankali yace toh,ta mike zuwa daki ya mara mata baya yayinda ummi Kuma ta zauna nan parlon nafeesa ta shiga bata lbrin yadda sukai da Taheer din,ita kam Layla samu tai ta sulale zuwa dakinta tun kafin ummi ta Ankara da ita.

Suna shiga daki ta zauna gefen gado tareda bubbuga gefenta tace mai “zauna nan”baiyi musu ba ya zauna duk jikinshi a sanyaye,,umma ta fuskanceshi da kyau snn ta fara mgn”tambaya nake son yimaka son and inaso ka fadamin gaskiya abinda na tambayeka”ya jinjina Kai yace InshaAllah…”inaso ka fadamin Taheer kanajin sha’awa ne koko bakaji gaba kwata kwata?ya zaro idonsa da sauri yana kallon umman yace”umma wnn wace irin tambaya ce?ta dakatar dashi amsa nakeson ji ba cewa nai ka tambayeni ba,,,yai shiru na tsawon lokaci kmr dai bazai ce komai ba,har saida ta sake mai mgn snn ciki ciki yace”inaji”then meyasa bazakayi aure ka samu wadda zata dinga kawar ma da sha’awan ka ba,kodai kana neman matane??tambayar ta sake bashi mamaki sai yai shiru kawai ya kasa mgn…Ina maka mgn kayi shiru ko ban isa dakai bane?a hankali yace wallahi ban taba neman mata ba umma,Ni ban taba ma kusantan abunda zai alakantani da zina ba,tace indai abunda ka fada gsky ne meya hanaka aure,sa’o’inka da kannenka gasu nn duk aure garesu da yara Amma Kai ko damuwa ma bakayi,naga alama idan aka xuba maka ido haka zaka kare rayuwarka ba tareda kayi aurenba,to bari kaji in fada maka,wnn shine last worning da zamu baka,kodai ka fito da matar aure ko Kuma mu zaba maka Mata da kanmu,Kuma wlh duk wadda aka zaba sai ka aureta don bazamu zuba maka ido ka lalata rayuwarka ba”umma ta kare mgnr cikin fushi,shiko gaba daya jiyai kmr yai kuka har ya gaji da mgnr auren nn,he wish zai iya fada musu wadda yakeso amma he can’t,haka yanaji yana gani zai auri wadda ba sonta yakeba,ganin yayi shiru umma tace”u know what?bakasan zafin haihuwa ba Taheer don haka bazaka gane me iyaye keji kan duk wani ala’amari daya shafi ‘ya’yansu ba,da kanada ‘da zaka fahimci tsananin qaunar da iyaye kema ‘ya’yayensu snn zaka fahimci me akeji idan mutum yaga wani abu na Shirin faruwa da danshi”a hankali ya dago idanunshi da suka jajir Yana kallon umman yace”umma don’t say this plss,ko ban haihuba inada baby and inayi mata sonda banajin ko ‘ya’yan da na Haifa zan sosu kmr haka,Ina sonta fiyeda yanda nakeson kaina,Ina damuwa da lamuranta fiyeda komai a duniya,umma idan baby na rashin lfy wlh kusan tare muke ciwon,nima kwanciya nakeyi bazan taba samun sukuni ba sai ta warke,idan tana cikin bacin rai ji nake kmr in dauko damuwan in dawo dashi kaina sbd banason ganinta a haka,snn idan tana farin ciki na tabbata nawa farin cikin Yana fin nata kawai sbd farin cikina in ganta cikin farin ciki,inasonta sosae umma and ko a kanta nasan me ‘da yake nufi wurin iyayenshi Kuma nasan yanda sukeji idan abu ya samu dansu Amma umma dn Allah ku bani lokaci,nayi alkawarin zan kawo muku matar da zan aura har gida”shiru umma tayi na tsahon lokaci tana nazarin kalamanshi,,ganin kmr tunani take yasa hanu ya riko nata, ta kalleshi da sauri shi Kuma ya langabe Kai yace kinji umma plss…ta sauke ajiyan zuciya snn tace shknn Allah ya zaba mafi alkhairi ya amsa da ameen,,ya mike ya fita bayan tace zai iya tafiya,ita Kuma ta zauna tana tunano kalamanshi.

Yau Monday tun safe suketa shirye shiryen surprise birthday party da Layla ta shiryama dadyn nata,komai a boye sukeyi don basuso ya sani.Karfe 8:30 ya shigo parlon cikin shirinshi na tafiya aiki ya gaisa da iyayen snn ya wuce dakin Layla daketa faman wrapping gifts din da zata bashi,mamaki sosae ya kamashi dayaji kofan a rufe yasan bata rufe kofa da key,yayi knocking,tace”Al’ameen plss go away idan na gama zan kiraka”mamaki ya sake kamashi jin abinda ta fada to me takeyi?yace baby open up its me”da sauri ta diro daga gado tana zare idanu,ta shiga tattara duk abubuwan data zube kan gadon tana boyewa tana gamawa taje ta bude mai kofan sai kalan murmushi take tace”dady nah”ya bita da kallo yanason gano abinda takeyi yace why did u lock the door?tace dady Al’ameen ne ke takuramin shine na rufe…yai shiru kmr bai yadda da abinda ta fada sai Kuma yace ohk zan wuce clinic toh”tace Allah ya kiyayemin Kai dady ya dawomin dakai lfy,amsa da ameen snn ya juya har ya kusa zuwa parlo tace dady karfe nawa zaka dawo?ya dakatar da tafiyar da yakeyi tareda juyowa yace”what are u up to?ta Dan wara ido tace am no upto anything dady kawai inason jine,kmr bazai fada mataba sai Kuma yace yau inada aiyuka da yawa gsky so zan iya kaiwa 6 ko ma infi haka,tace alright dady saika dawo yace Allah yasa snn ya fita,tana ganin fitanshi ta sauke ajiyan zuciya tana dafe chest tace gsky dady is very smart,har ya fahimci am upto something,well don’t worry daddy na I just wanted to surprise you.Bayan sallahn azahar masu decorations da aka Kira sukazo…without wasting of time suka fara aikinsu a nan compound din gidan…zuwa lokacin kuma mutane na jiki sun fara zuwa….Ramla ma tun around 11 mijinta ya kawota…ummi sai mita takeyi wai don me zata takura kanta zuwa abinda bai zama doleba bayan tana fama da tsohon ciki…haka ma Yusuf da matarshi wurin 3 sukazo yaransu Kuma na islamiyya..sosae gidan ya fara cika da mutane Layla sai hidima akeyi da mutane(Ina ruwan uwar gayya😹)+

5:00pm aka kammala dukkanin shirye shiryen da akeyi,dama tuni akayi delivering manyan cakes din da Layla tai ma dadyn nata order,kowanne da picture dinshi a jiki snn an rubuta Hbd my daddy”sosae wurin yayi kyau, decoration din ba karamin kayata wurin yayi ba,mutane suka zazzauna a plastic chairs din dake jere a wurin,kowane table na dauke da different type of snacks da drinks ga silent music dake tashi a hankali,wurin looks very beautiful hakama mutanen dake wurin…su ummi na zaune gefe table dinsu daya da umma da Ramla da nafeesa sai hibba dake jikin mamanta,umma da ummi suna sanyeda dogon riga na wani brown lace,dinkinsu iri daya and kayan ba karamin kyau suka masu ba,Nafeesa Kuma da Ramla suna sanye cikin Arabian gowns Ash colour sun yafa mayafan a Kai,kallo daya zaka musu jini daya don suna kama sosae little hibba ma baa barta a baya ba,don tayi kyau sosae cikin English gown Wanda ya tsaya Mata iya gwiwanta.

Su Al’ameen Kuma na sanyeda dark blues suit sunyi suma sosae.

Sai Kuma Uwar taro me gayya me aiki hajiya Layla ‘yar gidan daddy…lol😜tana sanye cikin fitted gown black,dinkin nada irin jelan nn kmr na amare da zakaga Yana Jan qasa,rigan ba karamin fito da coke shape dinta yayi don yayi fitting nata sosae,tayi turban style da head dinta golden,Dan kunne da sarqa gold,takalminta gold haka purse dinta ma gold,Ni kaina Dana kalleta Saida nace MashaAllah sbd tsabar kyawaun da naga tayi.

Taheer bai bar clinic ba sai after six,a hankali yake driving cox a gajiye yake sosae,lokacin da ya karaso gida anyi magrib don haka bai shigo gidanba sai ya wuce masjid,Yana idarwa ya taho gida Amma tun daga bakin gate mamaki ya fara kamashi ganin gidan dum kmr ba mutane ba haske to wa kashe bulbs din?shine tambayan dayama kanshi daidai yayi horn mai gadi ya bude mai gate din ya shiga,Sam bai lurada yadda gidan yasha decor ba cox ba haske and hankalinshi bai wurin Sam,bayan ya gama parking ya fito ko briefcase dinshi bai dauka ba ya nufi wurin me gadi da niyyar tambayanshi dalilin kashe kwayayen gidan sai kawai yaga haske ya mamaye wurin,ya tsaya cak da tafiyan da yakeyi ya shiga bin wurin da kallo”happy birthday to you, happy birthday to you”muryoyin occupants din dake wurin ya karade wurin,wani irin mixed feeling ya bayyana a fuskanshi,tsananin farin ciki da Kuma tsantsar mamaki”what a surprise”ya fada yayinda fuskanshi Banda murmushi babu abinda take,a hankali ya karasa inda mutanen suka direct wurin su ummi yaje ya shiga hugging dinsu daya bayan daya yana cewa thank u so very much,bayan duk sunyi wishing dinshi happy birthday yace whose idea is this plss,who organised this party?umma daketa kallonshi da murmushi ta nuna mishi inda Layla ke tsaye tanata kallon yadda abinda tayi yasashi farin ciki and that makes her happy too…wani irin kallo yake binta dashi gabanshi na wani irin faduwa,hakanan yaji he is restless,yes yasan Layla nada kyau Amma be taba ganin tamai kyau irin na yau ba,saida ya dafe saitin heart dinshi da yakeji Yana beating very fast kmr zai fto daga chest dinshi,kmr ana tunkudashi ya nufi wurinda take Yana zuwa yai hugging dinta tightly ya shiga blowing Mata kisses ta ko Ina a fuskanta,,bata hanashi ba sai ma dariya da takeyi sai daya gama ya riko fuskanta da hannayenshi yace thank u so much baby,I love so so very much muuaaaah”ya sake Mata wani kiss din a forehead dinta,ta Dora hannayenta kan nashi still smiling tace it’s my pleasure dady na am happy that you are happy with this and I love u more”gaba daya wurin aka shiga clapping musu,ba Wanda basu birgeba a wurin,ta janye hanunshi a hankali tace you go and freshen up dady Kai muke jira”Saida ya sake Mata wani peck din a hanunta snn ya nufi part dinshi feeling extraordinary happy.

STORY CONTINUES BELOW

Yana shiga a gaggauce ya shiga wanka ya fito yana goge jikinshi da towel wayanshi ya fara ringing,yana yin picking tace dady kayan da zakasa suna kan bed dinka”tana gama fada ta kashe wayan shi Kuma ya juya Yana kallon pure white expensive suit din dake ajiye kan gadon nashi…bai bata lokaci wurin shiryawa ba don yasan shi ake jira,bayan ya gama combing gashin kanshi ya tsaya kawai Yana kallon kanshi ta mirror,shi kanshi baisan he si this handsome ba sai yau,wani irin kyau yaga ya kara na musamman,ya feshe jikinshi da designer perfumes snn ya nufi inda suke.

Bayan ya zauna aka fara gudanar da abubuwan da suka shirya,Layla ce tayi welcoming speech tareda wishing daddyn nata happy birthday snn aka shiga ciye ciye daga nn Kuma akaje sallah bayan an dawo akai cutting cake Layla ce ta fara ajiye gift dinta snn kowa yazo yai wishing dinshi hbd snn ya ajiye birthday present dinshi,haka mutane sukaitayi har suka kare.

Su Layla suka shiga kwasan gifts din daya samu suna shiga dasu ciki bayn kowa ya tafi.

9:00pm dai dai wnn lokacin duk suna zaune parlor suna maida yadda akayi sai dariya suke,Taheer kam Allah Allah yake ya kebe da Layla yanason tambayanta inda ta samu kudinda ta siya mai Rolex wrist watch din da ta bashi as gift dinta,baya tunanin zata samu kudin ta hanya da bai dace ba but he still needs to ask.

Bayan su ummi sun kwanta shima ya mike har fita sai Kuma ya doshi dakinta,fitowanta a wanka knn tana kokarin sa sleeping dress dinta ya shigo dakin… welcome dady…ta fada yayinda ta gama sa kayan ta karasa gefen gadonta da yake zaune ta zauna dab dashi tana cewa”Happy Belated Birthday once again daddy na…Allah ya karo shekaru masu albarka”ya Dan kakalo murmushi snn yace”Ameen”sai Kuma ya tamke fuska yace baby bakijin mgn na koh?…ba na hanaki yin any how dressing kice Zaki shiga cikin mutane dashi ba??…ta wani rausaya Kai tace”ka hanani daddy,Amma gani nai it’s ur birthday so I have to look good”….wato you have to look good…you have to look good for others right?..da sauri tace “not at all dady,why will I dress for someone?..I did it only bcox it’s my daddys birthday shikenan,Amma am sorry”ya firzar da wani iska snn yace”naji amma kar ki sake yin irin haka”…I won’t InshaAllah…yace good girl,,now tell me Ina kika samu kudi  kika siyamin such an expensive wrist watch?…it’s my money daddy,kudin da kake samin account Dina ai ba tabawa nakeba shine naga wani friend dina yayi posting dinsu a Instagram na tanbayeshi yace min na saidawa ne shine na siya maka..don’t you like it dadyy?…ya kamo hanunta yace of course No baby I like it so much infact nafi sonshi ma dake..ta wani turo baki kmr zatayi kuka tace”are serious daddy”yace I was only kidding babyna I love you the most,and am sure babu abinda zanso a duniyan nn fiyeda ke,I love you so very much my little princess muuuaah”ya karasa tareda manna mata peck a forehead dinta ita Kuma sai blushing take daddynta yafi sonta fiyeda kowa…ya mike zai tafi yace oya kwanta Nima zanje in kwanta,ba musu ta kwanta ya rufeta da duvet tareda yi Mata addu’a snn ya Mata off din light ya rufe Mata dakin as always shima ya wuce nashi.

One Week ltr…

Yau Nafeesa suke Shirin komawa sbd hutun yara ya kusa karewa umma kuwa dama yau kwananta biyu da komawa kano..Layla ta shigo daki ta samu nafeesa dake kokarin sama hibba hula akai duk sun gama shiri Taheer kawai suke jira ya kaisu airport,,ta zauna kusada ita idonta har ya kawo kwalla tace”Mami don Allah ko kwana biyu ne ku Kara I don’t want you to go plss”Mami ta janyota jikinta duk sai taji ta bata tausayi ciki lallami tace”hutun su Al’ameen ya kare Layla Ramadan ma har sun koma kinga bazai yiwu mu Kara kwana ba and abbansu shima yau zai dawo daga Singapore kiyi hakuri kinji,kuyi mgn da daddynki idan ya amince sai kizo ki kwana biyu kafin time na post ume dinku yayi”Layla ta daga Mata Kai tace”toh…yawwa babyn daddy kukan ya isa haka kinji,nan ma Kai ta daga Mata tana murmushi ta kama hanun hibba suka fito…su Al’ameen ma duk sun fito kowa rikeda trolley dinshi,ga ummi ma a tsaye jikinta duk yayi sanyi ita kanta bason tafiyan nasu takeba,,Taheer na shigowa suka fara fita da kaya bayan duk sunyi sallama da ummi suka fito,ita kanta nafeesan Saida tayi hawaye hakama ummi.

Taheer na driving yana kallonsu ta mirror duk sunyi wani sanyi ya saki murmushi yana cewa”to kukan ya isa haka madam wa zai rarrashi ‘ya’yan naki..duk kukazo garin nn da kuka kuke rabuwa dagake har ummin kmr wanda bazasu Kara ganin junaba..nidai pls kukan ya isa haka kar ‘yata tayi ciwon Kai”ta galla mai hara tace”ai ba wani yasa ‘yar taka kukan ba”murmushi ya sake saki sai Kuma in a serious note yace to kukan dai ya isa haka for God sake we are all going to miss each other.. beside kwanan nn  zamu sake haduwa fa idan Ramla ta haihu..haka dai yaita consoling dinsu har suka isa airport,suna zuwa ba bata lokaci suka shiga jirgi don time yayi,haka suka tasya har Saida jirgin ya fara tafiya snn suka shiga mota suka tafi..ko a hanya layla sai share hawaye take,jefi jefi Taheer ke kallonta duk ta bashi tausayi,a hankali ya gangara gefen titi yai parking ganin bafa dena kukan zatayi ba..baby..ya Kira sunanta a hankali..Saida ta share hawaye ta snn ta dago ta kalleshi..come here…ya fada tareda bude mata hanunshi aiko kmr jira takeyi ta fada jikin nashi tana ci gaba da kukanta..bai hanata ba don yasan tsakanin ‘da da uwa sai Allah ga Kuma siblings dinta dole zatayi missing dinsu..a hankali yake shafa bayanta har ta dan tsagaita da kukan snn ya dago fuskanta yana kallonta ya manna Mata peck a both cheeks dinta yace”to kukan ya isa haka nan baby kar kanki yayi ciwo plss”..ya gama share Mata hawaye yace ay zakije musu holiday kema tunda time na post ume din baiyi ba so stop crying kinji..Kai ta daga mai snn ta koma ta zauna inda take shi Kuma ya cigaba da driving.Ranan Thursday Layla na zaune sai sharan hawaye take sakamakon kalaban da ummi ke Mata…Sam bata son a taba Mata kai.

Saura befi hudu su gamaba Taheer ya shigo parlon…ya kalli Layla dake ta aikin kuka snn ya kalli ummi data daure fuska tana cigaba da kalaban….yanason yin mgn amma yasan ummi fada zata haushi dashi don haka yayi shiru kawai ya zauna yana kallonsu….kasa hakura yai da ganin yadda Layla ke kukan yace”ummi sannu da aiki…ko Zaki kawo in karasa Mata”…banza tayi dashi batace komai ba….Saida ya sake maimaitawa snn ta dago tana hararanshi tace”in baka ka karasa salon ka kyaleta ta gudu koh…to baka isaba….kullum Kai kake lalata yarinyan nn duk wani abun daya kamata bazaka barta tayi ba….ynxu wnn kan nata kusan watanshi hudu ba kitso sai kace ba mace ba….to na dena Bari wlh… daga yanxu every two two weeks zan dinga tsefe kan da kaina snn inyi Mata wani….idan bata saba da kitson ba haka zaayi Mata aure taje tanayi a gidan miji….to ba zaayi haka daniba…tunda ta fara mgn shiru yayi kawai Yana kallonta….Saida ta gama kalaban tsaf snn ta mike tana karkade jikinta ta wuce daki abinta….da gudu Layla ta fada jikinshi tana cigaba da kukanta tace”daddy don girman Allah ka tsefe min wlh kaina har ya fara ciwo”….ya rungumeta sosae a jikin nashi ya shiga shafa dogon gashin nata yace” shushh ya isa to dena kukan….kinsan ummi bazata Bari a tsefe ba….so kiyi hakuri bazai dade yana miki ciwonba…kafin tayi mgn wayanshi ya fara ringing….”Alhajin Dutse”shine sunan dake kan screen din wayan nashi(N.B Alhajin Dutse shine kakan Layla,shine ya haifi mahaifinta snn Kuma yayan kakanta Wanda ya haifi mamanta)….ya dan janyeta a jikinshi snn yayi picking…”Assalamu alaykum”…aka fada daga daya bangaren… Taheer ya amsa tareda gaisheshi…mutumin yace”Alhamdulillah Taheer ya mahaifiyar taka….tana nn lfy alhaji….”MashaAllah dama wani mgn ne ya taso shine nace let me call you anytime ka samu chance sai kazo muyi mgnr….da sauri Taheer yace alright zanzo gobe InshaAllah…mutumin yace no ba sauri ake ba Taheer….u can take ur time duk ka sama dama sai kazo….da sauri Taheer yace….ba damuwa sir….zan taho gobe in Allah ya kaimu….alhajin yace”shknn Allah ya kaimu goben…ka gaida amaryar tawa…Taheer ya amsa da zataji InshaAllah snn ya ajiye wayan….da sauri layla dake jin me sukace tace “daddy kaje Dani plss….nadade banje Dutse ba daddy don Allah zan bika”….mikewa yai yace”alright idan an samu tickets biyu sai muje…let me talk to ummi first…yana shiga ya fadama ummi yanda sukayi snn ya tafi clinic…ya Kira wani friend dinshi dake airport yace yanason tickets biyu zuwa kano gobe….cikin saa Kuma an samu zasu sauka a kano daga nn sai su karasa Dutse a mota.+

Washegari….

Taheer na zaune parlo shida ummi ya gama shirinshi tsaf…Layla ta fito daga dakinta itama ta gama shiryawa hanunta rikeda Arabian gown dinta da zata Sanya gobe…sai pant da bra dinta data Dora kan rigan…..ta karaso parlon tasa hannu ta dauko Dan jakan da Taheer yasa kayanshi a ciki ta shiga sa natan a ciki itama…ummi daketa kallonta da mamaki taja tsaki tace”kedai zanga ranarda Zaki nutsu kisan kin girma Layla…ynzu breziern ne kika dakkoshi haka gagal gagal ko Dan sakayawa babu??..Layla na cigaba dasa kayanta a jakan tace”to ai naga ba kowa a parlon dagake sai daddy fa….ai ba kunyanku nakeji ba…ummi ta girgiza Kai kawai tace”Allah ya kyauta…Taheer dake nan zaune yana jinsu murmushi kawai yai don baisan me zaice ba….suna gamawa driver yayi dropping nasu a airport suka shiga jirgi zuwa Birnin dabo.

Bayan isansu kano gidan umma suka sauka…saida sukaci abinci suka Dan huta snn driver dinta ya daukesu zuwa jigawa….basu saukaba sai around 4 na yamma….bayan driver yayi parking suka nufi entrance din gidan….wata mai aiki ce ta bude musu kofa bayan Danna door bell da sukayi….tayi musu iso zuwa central parlor snn ta tafi Kira musu matar gidan….bayan mintina kadai sai gata ta sauko daga sama….dattijuwar Mata ta karaso parlon da fara’arta suka gaisa da Taheer….snn ta kalli Layla tace to tsohuwa da fatan dai ba zama kika zoyi gidana ba….Layla na murmushi tace”ay idan baki wasaba har mijin kima sai na kwace kafin na bar gidan….matar ta zaro ido tace”lallai Layla kinyi baki yanxu….ya ummin taki…ummi na nn lfy tace a gaisheki…tace Ina amsawa bari ayi muku mgn da alhajin….ta mike xuwa sashen maigidan nata….bayan minti kaman biyu ta fito tace musu bismillah muje….sukabi bayanta har zuwa part din….yana zaune kan daya daga cikin royal chairs din dake parlon….dattijo ne wanda kallo daya zakamai kagano yanada tarin ilmi….bayan sun zauna Taheer har kasa ya durkusa ya gaidashi hakama Layla da yaketa faman tsokanarta wai bata ajiye komai ba sai tsayi….hajiya ta mike tacema Layla”to tashi muje ‘yar nema ki barsu suyi mgnrsu…ba musu Layla ta mike suka fita tare….alhaji na kallon Taheer yace”yanzu ka fara huta gajiya Taheer….in anjima sai muyi mgn….shidai Taheer ba haka yaso ba….kmr yace baya tareda gajiya Kuma yai shiru….alhaji ya daga waya ya Kira wani….bayan few minutes wani saurayi ya shigo dakin….kyakykyawa dashi ya risina ya gaida Taheer snn alhaji yace”yawwa Usman ka kaishi masaukinshi snn ka tabbatar ka Kai mai duk abinda yake bukata…Usman ya amsa snn ya dauki jakan dake gefen Taheer ya fita….a hankali Taheer ke binshi a baya baisan dalilinda yasa jikinshi yai sanyi hakaba….ya kagu yaji wani mgn ne zasuyi….boys quarter Usman ya kaishi….Saida ya tabbatar ya mai duk wani abu daya kamata snn ya mai sallama ya tafi….Taheer kwanciya kawai yayi yana tunani sai can ya dauko waya ya sanar ma ummi sun sauka snn ya Kira umma itama ya fada Mata ya sake komawa ya kwanta.

STORY CONTINUES BELOW

Layla kuwa tana can sashen kakarta sai labarai take bata ita Kuma tanata faman dariya….mahaifinta ya Kira a wayar kakar bayan sun gama gaisawa dasu Al’ameen tace mai ga Layla ma sunzo dazu itada uban nata….Layla ta wani turo baki tace ni ki dena cewa ubana….babana zakice ko daddyna….in kikace ubana kmr zagi nefa….hajiya ta Mika Mata wayar tace ungo ni uwar kinibibi….bazaace daddyn naki ba….Awwal dake jinsu ta waya murmushi kawai yake…Layla ta amsa wayan da fara’arta tace Abba Ina yini….yace”ba wani Ina yini keda ko nemana bakyayi…ta zaro ido tace”Allah Ina nemanka Abba…idan tafiyane bana samunka a waya shiyasa…yace shknn ai Ina daddynki….tace”daddy Yana nn lfy abba tare mukazo nan dashi….yace iyye yar gidan daddy wato ko Ina sai anje dake koh…tana dariya tace eh mana….daddyna yanaji Dani sosae…haka sukaita hira da mahaifinta daga baya su Al’ameen suka amsa nanma suka cigaba da hirarrakinsu sai da akai magrib snn sukai sallama.

Bangaren Taheer ma bayan ya dawo daga sallahn magrib kwanciya ya sakeyi…bai San meyasa har ynxu yakejinshi very week ba…bai dade da kwanciya ba aka kawo mai abinci da drinks kala kala amma babu abinda ya taba…ana Kiran isha’i ya sake mikewa zuwa masjid dake nn kofar gidan.

Bayan sun idar tare suka dawo da alhaji da kuma Usman…shi usman ya shiga part din hajiya yayinda Taheer Kuma yabi alhaji zuwa nashi part din…bayan sun zauna alhaji na fuskantar Taheer yace”dama wata mgn ce muhimmiya nake muyi dakai Taheer…da kaina naso zuwa Abuja in sameka sai wani al’amari ya bullo Wanda shi hanani zuwa…Taheer da ya matsu su fara mgnr yace”ba komai alhaji…ai nine ya kamata inzo dama tunda nine karami…Kuma kmr mahaifina na daukeka…. don haka duk lokacin da kakeson gani na just give me a call ni Kuma zanzo InshaAllah…Alh ya jinjina kai cikeda gamsuwa yace hakane Taheer….na Kuma gode Allah ya saka ma da alkhairi…Saida ya danyi shiru ya fara mgn kmr haka”dama mgn ce akan ‘yar wajen taka…wnn yaro Usman shine yazomin da batun yanasonta da aure….da farko ban bawa mgnr tashi muhimmanci ba Amma da naga yanda ya damu Kuma yakemin magiya naga ya kamata in duba…wani irin faduwar gaba ya riski Taheer a lokacin…ya sunkyar da kanshi qasa yana mai karanto sunayen Allah a ranshi…alhaji ya gyara zama snn yaci gaba”Taheer kar kace zaka duba alakar dake tsakanina da yarinyar nan…aah ka daukeni a matsayin wanda yake nemawa dansa auren ‘yarka….kaga yaron nan maraya ne…nina haifi mahaifinsa snn tun rasuwar mahaifin nashi ni na rikeshi snn namai tarbiyya…don haka bashi da Wanda zai shigemai gaba kan mgnr nn sai ni….amma hakan ba yana nufin ayima yarinya doleba Sam ba haka bane….kafin ma mgn yaje kunnen yarinya inaso Kai ka fara dubawa ka gani…a matsayinka na uba Kuma waliyyi a gareta…kayi bincike kmr yanda addinin musulunchi yace ayi…idan har Usman bayada qualities din da zaka dauki yarka ka bashi…to kar kaji komai ka sanar dani kuma nayima alkawarin cewa bazan taba ganin laifinka ba…sbd nasan irin sonda kakema yarinyar nn…. Kuma bazaka taba zaba Mata abinda zai cutar da itaba…sbd haka kar kaji komai…ni matsayin dana na daukeka…don haka na baka lokaci kaje kayi tunani…snn nafiso itama yarinyar ta farajin mgnr a bakinka tunda tafi sabawa da Kai…Kuma idan har bata aminceba to bazaa taba yi Mata dole ba…nasan kuma bai zama lallai kanada burin yi Mata aure nan kusaba….don haka koda an daidaita…to bazaayi aureba har sai zuwa lokacinda kaji zaka iya aurar da ita sai ayi sbd bana son a shiga hakkinku…Allah ubangiji ya zaba mana mafi alkhairi….Taheer tunda ya sunkuyar da kai bai sake dagowaba…zuciyarshi yaji ta tattare waje daya kmr ta dena aiki….jin alhaji yayi shiru ya samu ya tattaro ragowar nutsuwarshi yana murmushin yake yace”na gode sosae da wnn karramawar taku a gareni…Allah ya saka da alkhairi…Kuma InshaAllah zanyi tunani kmr yanda kace snn in har baby ta amince nima na amince ubangiji Allah ya tabbatar da alkhairi…na gode kwarai…ya karashe mgnr cikin sanyi…nan alhaji shima yai masa godiya snn ya mike yace zaije ya kwanta…sukayi sallama da alhaji snn ya fita…har zai nufi masaukinshi ya tuna ummi tace ya hadata da Layla suyi mgn….sai kawai ya nufi part din…yana shiga parlor abinda idanunshi suka gani yaji kafafunshi sun kasa daukanshi…yai saurin zama kan kujera dake kusa dashi yana kokarin saita kanshi..

Layla ce zaune a parlon kanta ba dankwali itada Usman din da yasan yana sonta…da sauri Layla tazo inda yake tace daddy baka da lfy ne??kasa cewa komai yayi kawai ya mike yana takawa a hankali ya fita a parlon…yana isa masaukinshi ya fada kan gado tareda lumshe ido…wasu hawaye masu dumi suka shiga bin kuncinshi…a hankali yakai hannu fuskanshi ya taba yaji fa tabbas hawayene yakeyi…hawayen tausayin kanshi…ya tabbata yanason abinda bazai taba samuba…idan ya tuno maganganun da alhaji ya fada sai yaji zuciyarshi ta sake tsinkewa…irin kara da mutanen nn sukamai ai komai sonda yake ma Layla basu cancanci ya musu butulci ba..sbd sun fishi iko da Layla amma basu yanke hukunci Kai tsayeba sai da aka kirashi snn Kuma akace shi zaiyi deciding idan zai bada aurenta idan ma bazai bayarba….ya sani Yana son Layla Amma baya ganin sonda yake Mata zai kaishi ga aikata tsantsar butulci irin haka…yes zai bashi ita kmr yanda suka bukata amma Kuma yasan tamkar tashi rayuwar zai dauka ya bayar…ya sake lumshe ido har yanxu bai Dena hawayeba daya tuno a yanayin da ya samesu zaune a parlor sai yaji kmr ya cire zuciyarshi ajiyeta gefe…yanxu tana can tana hira dashi…ya gama ganin gashinta maybe har rike mata hannu yayi…”innalillahi wainna ilaihi rajiuunnn”ya fada da karfi yayinda yake buga kanshi da jikin gado…sam bayason zuciyarshi ta dinga ayyana mai abubuwa irin haka don a yanda yakeji din nn zai iya hadiyan zuciya ya mutu.Itama Layla ganin a yanayinda daddyn nata ya fita ta Mike da sauri zuwa masaukin nashi ta shiga knocking jin kofar a rufe take…”daddy plss open the door bakada lfy ne?..ta fada daga nn inda take tsaye…tayi kusan minti goma tana bugu Amma no response Usman ne yace Mata maybe baya ciki haka nn ta hakura suka koma ba don ta yadda ba…sai tunani take to meyake damunshi??+

Taheer kam kafin dare yayi nisa zazzabi me zafin gaske ya rufeshi…yana kudundune cikin blanket sai rawan sanyi yake…yanata kokarin ya dena tunanin komai Amma his heart is not helping matters at all…ya kasa dena tuna maganganun da sukai da alhaji da yai tunanin Layla zata auri wani kuwa ji yake tamkar zuciyarshi zata dena aiki..gaba daya ya susuce sai surutai yakeyi shi kadai”ya rabbi why me?rabbi ka taimakeni ka ciremin son yarinyar nn daga zuciyata…Allah ka yayemin wnn soyayya ko zan samu sassaucin abinda nakeji”haka yaita surutai har garin Allah ya waye bai samu bacci ba sai da yai sallahn asuba bacci barawo yayi gaba dashi.

Itama Layla bata tashi da wuri ba…tayi wanka ta shirya ta dora dogon hijab kan dan towel din dake jikinta ta nufi boys quaters don amso kayanda zatasa a wurinshi…tana isa ta fara knocking daidai fitowanshi daga wanka yazo ya bude Mata…ta shigo cikin dakin idonta a kanshi tace daddy what happened to your eyes?ba tareda ya kalleta ba ya isa gaban mirror ya fara shafa mai a takaice yace daita”nothing” gaban mirror din ta karaso ta riko hanunshi tana kallonshi idonta har ya kawo ruwa tace”I don’t believe you daddy…don Allah ka fadamin daddy bakada lfy ne…ta karasa mgnr hawaye na sauka kan fuskanta…ya jata gefen gado suka zauna ya shiga share Mata hawayen yace”mene abin kuka kuma..lfyna qlou na fada maki…kaina ne kawai kemin ciwo…”to daddy kaje ayi maka allura mana…dukda bacin randa yake ciki Saida ya Dan saki murmushi snn yace”don’t worry idan munje gida zansha magani so stop crying kinji…a hankali ta rungumeshi gam tana share hawayen tace I love you so much Daddy..Ni banaso ina ganinka a haka…nafiso kullum in dinga ganinka kmr yanda kake…wani tsalle zuciyarshi tayi jin yanda ta rungumeshi..a hankali yai hugging nata back shima yanajin kalmar I love you din nn har cikin kwakwalwarshi..kawai sai zuciyarshi ta raya mai wata rana haka zata fadama Usman tana sonshi maybe ma har hugging nashi zatayi..da sauri ya saketa tareda mikewa ya koma gaban mirror zuciyarshi sai kaiwa da kawowa take..kawai the thought of her telling someone she loves him yasa yaji tamkar ya kashe kanshi ya huta..ta sake dawowa gabanshi tace”daddy kayana zan dauka…ba tareda ya kalleta ba yace” gasu can”..ba musu taje ta dauka tana dab da fita taji yace”kiyi sauri ki shirya da wuri zamu tafi…tace toh snn ta fita duk jikinta a sanyaye.

10 daidai sun gama sallama da mutanen gidan sun fito…driver zai saukesu a kano daga nn su karasa Abuja a jirgi…Usman ya zagyo saitin inda Layla take Yana Mata mgn kasa kasa…da sauri Taheer ya dauke kanshi Yana kallon gefe…gabanshi na tsananta faduwa…ganin lokaci na kurewa yacema driver”let’s start going banaso muyi missing flight…nan driver ya tada mota usman ya matsa baya yanata dagama Layla hannu har suka fita a gidan…Layla ta Kai dubanta ga Taheer da har ynxu kanshi na window ta matso kusa dashi a hankali ta rungumo hanunshi a kirjinta ta kwantar da kanta a shoulder dinshi snn ta lumshe ido kmr me bacci…a hankali ya juyo da fuskarshi yana kallon yanda ta makale mai..wasu hawaye suka taho mai yai kokarin maidasu tareda sa hanu ya janyo daya hanun nata ya shiga murxawa a hankali..shi kadai yasan abinda yakeji duk sa’adda ta rabeshi musamman ynxu da yake ganin ya kusa rabuwa da ita rabuwa Kuma na har abada..a haka bacci yai awon gaba dasu basu tashi farkawa ba Saida suka shigo kano driver na tambayan Ina zai kaisu…da sauri yace mai ya kaisu airport kawai…da yayi niyyan su biya gidan umma Amma he can’t..yasan idan yaje a haka zataita tambayanshi meke damunshi and he can’t tell the truth..driver na ajiyesu ya tafi..su kuma suka zauna jira har time na tashinsu yayi suka tafi.

STORY CONTINUES BELOW

Bayan sun sauka drop na taxi ya daukan musu har gida..suna shiga yacema Layla ta shiga ciki shima zaije part dinshi ya Dan watsa sai ya shigo…hakan ta wuce ta sanar da ummi abinda yace snn itama ta shiga dakinta.

Ganin shiru shiru be shigoba har dare yasa ummi tunanin ko bayajin dadine…da kanta ta hada mai abinci kan tray ta bama Layla tace ta kaimai part dinshi.

Lokacinda ta shigo shiru part din nashi kmr ba mutane a ciki..ta ajiye tray din hanunta nan parlor snn ta shiga bedroom dinshi…yana kwance rigingine a kan gado…idanuwanshi lumshe kmr me bacci..ta karaso a hankali ta zauna dab dashi tasa hanu ta riko nashi hanun dake kan cikinshi..ya bude idonshi da sauri…ganin itace ya mike zaune yana kokarin daidaita kanshi kafin yayi mgn ta rigashi”daddy pls what is happening to you?ya Dan qaqalo murmushi yace I have told u baby ba abinda ke damuna it’s just headache…ta shiga girgiza Kai tace ni dai ban yadda ba daddy,,dole akwai abinda ke damunka…yai shiru Yana kallon yanda take girgiza Kai idonta har ya ciko da hawaye…yasa hanu ta riko fuskanta Yana kallon idonta yace mene abin kuka Kuma baby…tace”then tell me abinda ke damunka plss..ya lumshe ido ya bude yanajin yanda zuciyarshi keta kokarin bayyana abinda ke cikinta snn a hankali yace”just keep praying for me baby…kitamin addu’a Allah ya yayemin abinda ke damuna and Allah ya min zabi mafi alkhaiy”…ya share Mata hawayen Yana kokarin murmushi yace u know I hate to see u crying..ki dena banaso”..ta karasa share tears din nata tace ummi”tace in kawo maka abinci..Yana parlor”..yace “alright tashi muje ki zubamin..ba musu ta mike a hankali ta fita a dakin…ya sauke ajiyan zuciya tareda dafe saitin heart dinshi yace”oh Allah am doing better than I expected…Rabbi pls let it continue like this…ka bani ikon danne abinda ke zuciyana kar ya kaini ga aikata butulci ya rabb”yana gamawa yamike zuwa parlon.

tana zaune ta gama serving dinshi abincin..ya karasa ya zauna Yana tunanin yanda zai iya cinye uban abincin nn data zuba mai…har yafara ci sai Kuma ya dago ya kalleta”zo muci”..ta makale kafada tace mai am full..bai sake cewa komai ba ya shiga cin abincin bawai dan yanajin dadinsa ba sai Dan yanaso tabar tunanin wani abu na damunshi..da kyar yaci kusan rabi yasha ruwa snn yace mata na koshi baby..thank u so much”tai murmushi snn ta kwashi abubuwan zata fita dazu..shidai binta kawai yakeyi da kallo..har takai bakin kofa snn ta juyo tace”am coming back right away”murmushi shima ya mayar Mata tareda daga Mata Kai snn tasa Kai ta fita…Yana nn zaune sai gata ta dawo..ta zauna kusa dashi tace I want to talk to you daddy..Ina sauraronki baby what is it?..tace”daddy ai kasan ya Usman na Dutse koh..da sauri ya juyo yana fuskantarta lokaci daya gabanshi yayi wani irin faduwa..yai kokarin saita kanshi snn yace yes na sanshi…ta bude hanunta dake dunkule saiga wani box mai kyau..Mika mai box din tayi tana cewa”shi ya bani wnn ring nace bazan amsa ka hanani..shine hajiya tace i should accept wai idan kace baka yadda ba sai maida mishi..nayi trying musu bayani amma sun kasa fahimta na..wai he is gonna miss me nima i shoud give him something in return”ya bude ido sasai Yana kallonta yace what did u gave him?..ta Dan tabe baki snn tace”I gave him nothing..nace ni banada abunda zan bashi wnn Kuma..ta nuna diamond ring dake Dan yatsanta snn tace”it’s from you so bazan iya rabuwa dashi ba..ta karashe mgnr tana murmushinta mai kyau…shiko Taheer kallonta kawai yakeyi with adoration..komai nata is perfect kmr ita tayi kanta and komai nata yanaso komai nata yana burgeshi amma he has no choice..haka nan yanaji yana gani zai daurama wani aurenta da kanshi..kawai sai yaji hawaye na nemon zubowa a idonshi yai saurin kawar da kai yadan sharesu yanda bazata ganiba snn ya dawo kanshi ya kalleta still murmushi take mai snn ya kalli box din dake hanunta ya karba ya bude wani diamond ring ya bayyana Dan karami me kyau sosae..shiru kawai yai ya kurama zoben ido tamkar shine Usman din…ganin yanda ya kurama zoben ido tasa hanu ta amsa tana cewa”zan bada a mayar mai da kayanshi dady..dama ni bemin kyau ba”..baice komai ba yasa hanu ya amsa box shima ya bude snn ya ciro ring din ya kama dan yatsanta yasa mata snn yakai hanun nata yai kissing yana kallon yanda ring din ya Mata kyau can kasan makoshi yace”ya miki kyau”ta sake wara ido tana kallonshi mamaki sosae ya cikata tace”ban gane me kake nufiba daddy”…Ina nufin you should accept it.. Usman is your brother so bazan hanaki amsan abu a hanunshi ba okay??tasa hanu ta cire zoben tana Dan turo baki tace ni bemin kyau ba daddy..bakin data turo yadan ja da hanunshi yace ya kamata ya miki kyau mana baby..now muje in kaiki ki kwanta Nima bacci zanyi…ta sake turo bakin ta rungume hanunta a kirji snn tace ni yau anan zan kwana..ya wara ido yace hope bada gaske kikeba?..ta juyo tana kallonshi still bakinta a tunzure tace am damn serious daddy..yau a kusa dakai zan kwana..ta karashe mgnr tareda murguda Dan bakinta.. murmushin gefen baki ya saki tareda dauke kanshi gefe..yanda take murguda mai bakin nn kawai se yaji he wants to kiss her..da sauri yai erasing thought din daga mind dinshi kmr Wanda yayi sabo sai Kuma ya mike ya kama hanunta yace muje in rakaki idan kikayi bacci sai in dawo..ta janye hanunta idonta har ya kawo kwalla tace Allah nidai daddy yau a kusa dakai zan kwana..yace”but baby how..taya zakice zaki kwana kusa dani bayan ga dakinki can…ta zame hanunta a nashi tana kokarin rugawa bedroom dinshi ya dagata cak ya nufi part dinsu da ita..har bedroom dinta ya kaita tanata kuka Amma bai saurareta ba ya Mata addu’a ya rufa Mata duvet snn ya mike ya kashe Mata wuta ya fita zuwa part dinshi..haka kawai ta kwana a part dinshi salon tajanyo ya aikata abun kunya..don a yanda yakeji din nn matukar ta kwanta kusa dashi to babu abunda bazai iya faruwa ba..”God forbid”ya fada tareda sauke ajiyan heart.Washegari Monday da wuri yai Shirin office as usual ya shiga part din ummi ba kowa parlor don haka ya wuce bedroom din ummi…tana  zaune kan dadduma tana lazimi Layla Kuma na kudundune cikin blanket a kan gado…ya karaso cikin dakin ya zauna yana mamakin ganin Layla….a nan kenan ta kwana baa dakin nata ba…Ummi ta shafa adduanta snn ta juyo tana kallonshi”ummi Ina kwana”ya fada yana Mata murmushi…ta amsa da”lfy Lou Taheer ya jikinka..jiya Layla tacemin wai kanka ke ciwo..ya Dan shafa Kai yace”naji sauki ummi…sai ya kalli Layla dake kan gadon yace ummi a nan ta kwana ne?..ummi ta ninke daddumarta snn tadanja siririn tsaki tace”ai Layla dai Allah ya nunamin ranar nutsuwarta..kawai sai farkawa nai naji mace a bayana ta wani makaleni kmr zata koma ciki..Taheer ya danyi murmushi ganin yanda unmin ke mgn snn yace “ummi to mene a ciki donta makaleki ummi… dadi ma ya kamata kiji baby ta kwanta a jikinki…tun bai rufe baki ba ummi tace”Allah ya sawake..mudai Layla Kuma ai sedai Allah ya fiddamu kunya a gurin mijinda zata aura…yarinya sai son jiki kmr kyanwa..ta wani makaleni ta hanani bacci kmr jaririya…haka zaayi Mata aure taje tana makale miji ta hanashi bacci knn…dukda yanda mgnr ummin ta sokeshi jin ta ambaci mijin Layla saidaya danyi murmushi jin abinda ta fada din..yasa hanu ya yaye bargon data lulluba dashi don yasan tana jinsu Sarai ba bacci takeba…ta juya baya da sauri tana turo baki…yai murmushi yace”yau ni din ake juyama baya baby…batace komai ba sai kawai ji tayi ya janyota zuwa jikinshi…cikeda takaici ummi tace kaidai Allah ya shiryeka wlh..ya yarinya zata aikata laifi ina fada maka maimakon ka mata fada sai ka wani janyota zuwa jikinka…Kai har yanxu kallon jaririya kakema Layla koh…bazaka dinga tsawatar Mata akan laifi ba saidai ka ringa sangarta ta koh…yai murmushi yasa hanu ya manne Layla daketa mustu mustsu a jikinshi gam snn ya kalli ummin yace”laifi nayi mata fa shine zan bata hakuri…ummi ta saki salati tace”to kuwa abun naku ya zama innalillahi wainna ilaihi rajiun…. wlh tun wuri ma kayi ka fito da matarka…kayi aurenka ka tafi can ka barni inyiwa yarinyar nn tarbiyyan daya Dace…don wnn halin da kake koya Mata Sam ba halin zaman gidan miji bane…tana karasa fada ta fice daga dakin tanata bambami.

Bayan fitanta ya Kai dubanshi ga Layla da tayi luff a jikinshi kmr ba ita ce ke kokawa dashi ba dazu…yasa hanu ya janyeta yanajin yanda abubuwa da dama ke Kai kawo a cikin jini da tsokarshi game da ita…Sam baima ji abinda ummi ke fada da kyau ba cox his heart has gone so far da babu abinda yake tunawa sai ita sai Kuma muradin kasancewar tareda ita har mutuwa…ganin zata fara mai kuka ya girgiza Kai tareda janyota jikinshi yace”baby mana…don’t cry plss…am sorry for sending you away last night hakan bazai sake faruwaba kinji”…ta dago tana kallonshi snn ta jijjiga mai Kai…yai murmushi yace kin hakura?nanma Kai ta sake dagawa…ya manna Mata kiss a forehead dinta snn ya mike yace “alright ki koma baccinki baby na tafi aiki…tace sai ka dawo snn ta koma ta kwanta shi kuma ya fice a dakin…ya samu ummi da Mama hawwa a kitchen yai musu sallama ya tafi ummi nata fadan don me bazai tsaya yayi breakfast ba.+

Koda yaje clinic ayyuka sunmai yawa sosae amma duk da haka batun auren Layla na nan makale a zuciyarshi he wish zuciyanshi na iya mantawa da batun son Layla ya cigaba da rayuwarshi kmr yanda yakeso Amma inaa…ya kasa gane wane irin abune wnn…wane irin jarabawane wnn…why Allah zai jarabceshi da son Layla bayan bazai sameta ba…yai saurin istigfari jin zai fara kauce hanya ya cigaba da aikinshi.

Around 5 sai ga Yusuf yazo…bayan sun gaisa Yusuf ke tambayanshi abunda ke damunshi…yai shiru kmr bazai fada ba sai Kuma daga karshe yaima Yusuf bayanin komai…ya Dora mai da fadin shawaran daya yanke na zai amince da auren matukar Layla ta amince…shawarwari sosae Yusuf ya bashi tareda bashi kwarin guiwa kan abinda yake Shirin yi…snn ya bashi shawaran ya samu ya fidda mata shima yayi aurenshi if possible kafin ayi na Layla don hakan zai taimaka wajen mancewa da son Layla snn zai faranta ran umminshi… Taheer yayi naam da wnn shawara ya Kuma tabbatarwa Yusuf hakan zaayi Amma zai fara mgn da ummi…sai da sukai sallar magrib snn Yusuf ya tafi gida shima Taheer din ya nufi gida feeling exhausted.

STORY CONTINUES BELOW

Saida ya fara shiga part dinshi yai wanka yai changing zuwa kananan kaya snn ya nufi part din ummi…tana zaune parlor tana kallon news..ya zauna kusada ita suna kallon tare Saida aka gama ummi tace”ga abincinka can a dining”…yace “I want to talk to you first”ummi ta gyara zama snn tace umhum Ina jinka…yai shiru na ‘yan seconds snn yace”ummi na fitar da matar da zan aura”…zaro ido ummi tayi cikeda tsantsar farin ciki sai Kuma ta mike ta fara sujada Saida ta gama ta koma mazauninta still tana murmushi tace”Allah alhamdulillah..Allah na gode maka daka amsa addu’ata”..Taheer shiru kawai yai yana kallon yanda mgnr daya fada ta Sanya mahaifiyarshi farin ciki haka..sai ya sake samun kwarin guiwan abinda zaiyi indai zai faranta ran ummi haka to he is ready yai aure ko baya son matar sbd farin cikin ummi…”kasan wlh duk a dame nake kan mgnr aurenka Taheer… tunanina ko bakada lfy shi yasa baka shaawar auren Amma yanxu alhamdulillah Allah ya maka albarka ya tabbatar da alkhairi…ya amsa da ameen cikin ranshi ko mamaki yake wai shi suke tunanin baida lfy…yai murmushi kawai don yasan da lafiya yanama mutum yawa to da shi zaice yamai yawa indai lafiyan abinda suke tunani ne…ummi ta sake mai tunani da fadin”to wacece ita snn a Ina take?..ya Dan sosa Kai yace”sunanta Sameera ummi..a nan Abuja take ai zan kawo miki ita kafin manya sunyi mgn…ummi ta sake murmusawa tace “to Allah ya nuna mana Taheer Allah ya tabbatar da alkhairi…ya sakeyin shiru na ‘yan seconds snn yace ummi baki tambayeni mgnr da mukai da alhajin Dutse ba…ummi daketa murmushi har yanxu tace ai nasan idan mgnr daya kamata in sanine zaka fadamin so I don’t have to ask…shima yai Dan murmushin snn a hankali ya fada Mata duk yanda sukai da alhajin snn da shawaran daya yanke..shiru yai yana ganin ynd farin ciki ya sake mamaye zuciyar ummi.. Saida ta furta Alhamdulillah sau uku snn tace”Amma naji dadin wnn mgn Taheer.. Allah ya tabbatar da alkhairi…kmr sun San ko kullum zullumina bai wuce tunanin mijinda Layla  zata auraba..kasan maza yanzu ba cika gane halinsu akeyi a wajeba…musamman Layla da takeda kyau kana ganin tun yanzu yanda maza ke rububinta Ina ga Kuma nn gaba in ta sake zama yammata…idan kuwa aka tsyar Mata da miji shknn duk Wanda yazo sai ace anyi mata miji…snn kaga har yanxu hankali ba wani isanta yayi ba kullum adduana Allah ya bata mijinda zai dauki childishness din nn nata sai gashi Allah ya kawo…ai Usman baida matsala Allah ubangiji ya muku albarka gaba daya…a hankali Taheer ya amsa da ameen can cikin ranshi ko ji yake inama zai iya fitowa fili ya bayyana irin qaunar da yake Mata tunda su sun kasa ganewa…wai ace har yanxu duk cikinsu ba Wanda ya iya gano tsantsar qaunar da yake Mata…su kullum dauka sukeyi shi babanta ne and bai da right din da zaice he loves her…ya mike kawai batareda yacema ummi komai ba ya nufi dakin Layla…bude kofanshi yayi daidai da lokacinda towel dinta ya subuce daga jikinta yai kasa…ta zaro ido da sauri ta dauko towel din ta sake daureshi a jikinta tana rarraba idanu…ya dauke kanshi a hankali daga kallonta lokaci daya wani irin kasala ya diran masa…ya isa bakin gadonta ya zauna yama rasa da wanne zaiji…Layla ta dafe kirji tareda sakin ajiyan zuciya Allah ya taimaketa daddy ne and akwai pant da bra a jikinta…gefen gadon ta karsa itama ta zauna snn tace”daddy sannu da dawowa…maimakon ya bata amsa sai cewa yai”baby bakida hankali koh..wato a gaban kowama haka kike kunce towel kowa ya kalleki ba kaya abi?..ta marairaice tace”Allah daddy ba haka nakeyi ba yau ne kawai..gaba daya towels din nawane basada girma shiyasa amma kayi hakuri”…a hankali yaketa sauke ajiyar zuciya snn yace”idan kin gama shiryawa ki sameni part dina zamuyi mgn dake”..a hankali tace toh..shi Kuma ya mike ya fita a dakin gaba daya da kyar ma yake iya tafiya duk abubuwa sun taru sun cikamai brain bai ma San da wanne zaiji ba…baibi takan abincinshi dake dinning ba ya wuce abinshi don ummi dama ta koma dakinta.

Yana shiga ya fada kan gado Yana tunanin…yanxu shknn zai hakura da Layla shknn yanxu yanaji yana gani zata auri wani bashi ba.. innalillahiwainnailaihirajiun…duk sa’adda yai tunani makamancin haka ji yake inama Allah zai dauki ranshi ya huta…a yadda yake kishin Layla gani yake bazai iya jure ganin tana tarayya da wani namiji har suyi aure snn har su hada shimfida…innalillahi ya sake maimaitawa sau uku yana me jin kmr ya cire zuciyarshi ya cillar ko zai samu sukuni…shknn shi yanxu bai da guts din da zaice yana sonta sbd kowa kallon babanta yake mai…ita kanta Laylan kallonda takemai knn…”this whole thing is killing me”…ya fada a hankali yayinda hawaye suka shiga sintiri kan kaykawan fuskanshi..bai hanasu zuba ba don yasan shine kadai samun saukinshi…jin an bude kofar parlor yasashi saurin mikewa ya shige bathroom don yasan itace and bayaso tazo ta sameshi a halinda yake ciki…Layla ta ajiye abincin dake hanunta a parlo snn ta shigo dakin nashi ganin bai nn yasa tai tunanin kilan yana toilet…ta zauna kan gado tareda daukan wayanshi dake gefe ta shiga yin game dashi…tana nn zaune ya fito Yana sanyeda bathrobe…ya karasa gaban mirror ya fesa perfumes kadai snn ya nufi closet dinshi ya zira milk jallabiya ya maida bathrobe din toilet snn ya dawo ya zauna kusa da ita…a hankali ya karbe wayanshi dake hanunta yace”mgn fa zamuyi”batace komai ba ta juyo tana fuskantarshi..sai kawai yaji ya kasayin mgn..so yake ko kalma daya ta fito daga bakinshi Amma inaa…banda kallon lips dinta da suke nan ja babu abinda yake…haka nan yaji gabanshi ya shiga faduwa…heart dinshi ya fara beating at a faster rate…kmr ana janshi haka ya cikata gab din dake tsakaninsu…ya tallabo fuskanta da duk hannayenshi…kallon ido cikin ido sukema juna yayinda ita bada wani manufa take kallon nashi ba…shi kuwa ji yake yau  idan baiyi kissing bakin baby ba zai iya mutuwa…ya dade yana controlling desire dinshi a kanta amma na yau is beyond him…baijin zai iya hakura this time around…a hankali ya shiga circling lips din nata da finger dinshi yanajin yanda feelings keta rushing into him(abunku da tuzuru😹)..a hankali ya lumshe ido har ya sunkuyo Yana gab da hada bakinshi da nata sai Kuma ya saketa yai saurin janye jikinshi a nata Yana salati…ya mike da kyar yana hada hanya ya koma toilet din ya rufe don bazai iya hada ido da itaba…yanxu wane irin kallo zata mai…”what am i doing..what has came over me..oh Gosh why can’t i control my feelings…ya rabbi kana gani…rabbi don’t let me suffer plss…not again…Allah ka bani juriya Allah kar kasa na aikata abinda daga baya zanzo Ina Dana sani plsss…ya ya karasa mgnr tareda durkushewa nn toilet yana hawaye wani kan wani.

Ita kuwa Layla har ga Allah bata kawo wai wani abu zaiyi Mata mara kyau ba…kawai dai tayi tunanin peck zaiyi mata kmr yanda ya saba sai Kuma taga ya fasa snn ya koma toilet yana tafiya kmr dan maye…”what is wrong with my dady plss…what’s happening”..ita kadai take maganganun nn sai a hankali ta mike ta fita a ranta tace kilan yau daddy is emotional shiyasa yake acting weird..but she prays Allah yasa ba wani abu ke damunshi ba…zata cigaba da mai addu’a kmr yanda ya bukata.

TAHEER…

Saida ya tabbatar ta fita snn ya fito daga toilet din yaje yayi locking kofar snn ya dawo ya sake kwanciya akan gadon…har yanxu bai bar tunanin meya hau kanshi da har ya kusa sashi aikata abin kunya har haka ba…me yasa yau ya kasa controlling abinda ya dade yana controlling tun tuni…ya sani ba tun yau ba yakeda sha’awan lips dinta…amma ai bai taba attempting kissing dinta ba sai yau…ya sauke ajiyar zuciya wato kmr yanda sonta ke growing very rapid a zuciyarshi hakama desire dinta knn…”well I must definitely put a full stop to this…if not watarana zanyi abin kunya”..Allah ka bani juriya da ikon danne abinda nakeji plss.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page