NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 5 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 3 CHAPTER 5 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

MUN TSAYA  

Murmushi kawai Adamu yayi yana satar kallon Salmanu wanda ke ta shan tsallen

murnarsa a zuci, amma fuskarsa ta Ki nuna duk wata alama da zata bayyana abinda ke ransa. Sai Adamu ya shiga tararradin ko kudi ne Salmanu baya son ba shi, Www.bankinhausanovels.com.ng

“Na ga kamar ba ka yi murna ba, alhalin da kana nuna min ka fi ni son na auri Husna”.

“Ba na son na yi murnar ne kuma na dawo na yi kuka, gara na bari idan na ga tabbatar abin sai na yi da hujja’. . In ji Salmanu. . . Adamu ya masa da alamun karsashi, “In sha Allah wannan karon zan dage na ga cikar burinmu”,

, “Zan tayaka”. Shi ma Salmanu ya amsa tun daga Kasan ~ zuciyarsa. Sannan yayi fuska ya ce, – “Yau ba mu da wasu muhimman baki me zai hana ka tafi yanzu?”

Adamu ya dan yi shiru alamun akwai wani abu a Kasa, ;

Cikin zaKuwar jin ba’asi kawai Salmanu ke kallonsa, har Adamun yayi ta maza ya ce,

“Zuwa yanzu kudin da muka tara zasu ishe Www.bankinhausanovels.com.ng

– ni aure?”. . Tanimu da Salmanun suka fashe da dariya

‘don yanzu suka gane inda Adamu ya dosa, Salmanu ya janyo hannunsa yana cewa, – “Kana da shakku a kaina Adamu? Ban — cancanci haka ba wallahi”. Dariya kawai Adamu yayi ya tashi ya fice.

**********

Hajiya nata ina ka saka ina ka aje da Adamunta duk duk da ya zo mata da fuskar shanu sai faman cin magani yake yana hura ~ hanci, amma dai ta’ yi farin cikin ganinsa musamman ganin yadda yayi Kiba yayi haske tamkar ba Adamunta mai busasshen lebe kullum ba. Kodayake canjin nasa ba Karamin kada ta yake ba, tun tuni dama take son ganinsa don dama tana cike da labarin cewa Adamu fa na bacewa kamar walkiya ba a sanin inda yake zuwa, sannan shagon da aka tude masa domin ya rike shi ba ya zama a cikinsa, kai bai ma damu da sha’anin shagon ba iyakacinsa ya bidi kudin cefane ya bawa Salma, hasalima an.ce bai taba shiga lamarin shagon ba kusan komai a hannun Salman yake. a Ina Adamunta yake zuwa kuma wacce wainar yake toyawa? Wannan ya dami Hajiya

ZAMU TASHI 

kwarai, har ta fara danasanin auren da aka yi wa Adamu, don tana da yakinin in a kusa da ita yake dole zata matsa ta bincike shi halin da yake ciki, kuma ta san halin kayanta sarai, ba zata bata wani lokaci ba zata gane halin da yake ciki domin shi Karya ba ta karbe shi ba, in dai zai dade yana jan ta sai ya fallasa kansa. Ta sha nemansa a waya ba ta samunsa, in — ma ta same shi sai ya gaishe ta a gurguje ya kashe wayar da zummar zai kira ta daga baya, ba zata sake jin duriyarsa ba.  To yau ga dama har gida ta samu, don haka ta dinga marabtar abinta duk da yana ta faman sha mata Kamshi tamkar ya ga ‘yar adawarsa. Hakan ne kuma ya bata shaidar da bukata yazo, don haka cikin nutsuwa ta fara bugun cikin _ abinta. . *Adamu komai naka na nuna lafiya kake, Www.bankinhausanovels.com.ng 
Salma ma duk lokacin da ta zo gidan nan in na  bincike ta sai naji lafiya kuke zaune, amma yanayin ka gaskiya kamar yana nuna min babu lafiyar…”.


Ai Salma muguwa ce, dole ta. dinga wakilta ta mana tana ce miki lafiya nake…”. Da Hajiya ta tsammaci wannan amsar ai da babu abinda-zai sanya ta yi masa wannan- – tambayar. Hankalinta a dan tashe ta tsura masa ido kawai tana kallonsa, ta lashi labbanta da suka bushe sannan ta kawar da kai. Shi kuma ya cigaba da numfarfashin da ba sa nuna komai sai zafin kai kamar ashana. “Allah ya kyauta”. Hajiya ta fada da ta lalubi abin fada ta rasa. . — Cikin ci da zuci Adamu yace,” “Amin”. – Sannan don kar a bar maganar ta yi sanyi ya sake dorawa da cewa, “Kin fi kowa sanin ba zan yi lafiya ba.tun ~ * da ba na tare da abinda nake so, ita ma Salman ai _ ta san ba zan yi lafiyar ba tun da matsa min aka * yi na aure ta. A dan tsorace Hajiya ta tare shi. _ – “Adamu! Na -zaci wannan maganar ta wuce…”. — Ya tare ta a raunane kamar zai fashe da _kuka don ya san babu abinda zai yi ya sake raunana Hajiyar tasa sai kukan, a —“Ya wuce ya je ina? Ashe kin sha mafarkin -a canja miki ni Hajiya don kawai kin fifita =~ zumuntar Www.bankinhausanovels.com.ng Salma a kan‘tawa?”. Kawai sai Hajrya ta shiga tafa hannu tana sallallami, ta ma rasa abinda zata cewa Adamu. Adamu ya tamke fuska iyakar tamkewa duk dan hajiya ta san cewa ba da wasa ya zo’ba,  “In dai ba ku na tunanin Salma kawai aka halitta don ta ji,dadin rayuwarta ba, kun aura mata abinda take so to nima a aura min yarinyar  da nake so, a gidan su an ba ni nan da kwana ‘ ‘biyar na fito…” Hajiya ta tsurawa Adamu ido da kyau don ta gane cewa ciki -hayyacinsa yake ko kuma ‘ ganye ya banko ya fado mata gida? Tun tuni . dama ta fara fitar.da ran cewa idan Salmanu bai ~ . janye mata da ya lalataba. . Adamu bai saurara ba ya cigaba da sakin ° maganganu cikin wauta da tabara har ya gajiyar_ da Hajiyar ta tanka,“Mu Kaddara kana da Karfin hali da na – aljihun riKe mata biyu Adamu, wanene zai yi maka jagorar auren, abin nufi wanene zai dauki nauyin hidimar aurenka Adamu? Na san in na rantse ba zan yi kaffara ba Adamu, Yayanka ba zai goyi bayan wannan danyen aikin naka ba…”. . Adamu ya tare ta a Kuntace, – . . “Ni dama ban sa rai da samun wani abu a wajensa ba, abinda na sa rai tuni na riga na samu, wato ya Kuntata rayuwata ya aura min abinda ba – na so, yaje kawai Allah ya biya shi wannan aikin da yayi’’. . Hajiya ta sake dafe kai kawai dakin na juyawa da ita, ba ta shakkar idan wani abu bai taba mata kwanyar auta ba, ta san adamu tun tuni . . da salon rashin kirki da wauta, amma ba ta taba _ganin sun kai irin wannan girman shafar kowa ba tare da manta alkhairan baya. .. . ’ Tagumin da Hajiya take da neman fashewa da kukan da take tamkar tunzura Adamu ta yi, ya — sake gyara zama ya ce mata, “Idan ya zo gobe ki shawarce shi, babu abinda nake nema daga gareshi sai hadin kansa, . tun ranar da na fara ganin Husna na san:cewa an halicce ta ne don na yi nema na same ta ni kadai, – darajarta ta wuce in kwanta a daki wani ya nemo -min kudin da zan aure ta ko in ciyar da ita”. . An zo gabar da Hajiya take so don haka ta karbi maganar bakinta na karkarwa, “Dama ina nemanka Adamu, ina son sanin sana’ar da kake ko wajen da kake zuwa, ina da . labarin komai ba ka zama a gida ba ka zama a ‘ shagon naka…”
Kai tsaye ya amsa, —_ “Amma dai tun kafin na fara
na sanar miki zan fara aikin gini ko Hajiya?”.Aikin gini ne zai yi maka aure da gaggawa Adamu?”. Ya sake janyo rigimar Karfi da yaji, “Na san zaki fadi haka Hajiya, don ba wani – mai gaskiya a wajenku sai Salma, ta sanar ‘miki bana zama a gida kin yarda, amma ni na fadi . abinda na sani kina neman Karyatawa, don Allah ku fada mini abinda salma ke muku-na gata da har tafi ni irin wannan Kyallin goshin da harshen gaskiyar…”. . : ‘ Www.bankinhausanovels.com.ng Yanzu Hajiya ta fara. sallamawa, jikinta a sanyaye ta tare shi, “Idan ka cigaba da irin wannan Kalubale, — to babu shakka zargin rashin adalci ne zai sanya Yayanka ya hana ka wannan auren, tun da ka zo kake fadin kana son Husna, amma ko sau daya Salma bata ci albarkacin kyan halinta ka ji kunyar cin fuskarta ba…”. . . Adamu zai yi magana ta tare shi, “Ni wannan-tada hakarkarin ya ishe ni, ka je gobe ka dawo ka ji yadda muka yi da yayanka”. . Sannan Adamu ya kishingida. sosai a hankali ya fara sakin ,fuska yana jan Hajiya da hira.  Hajiya amsa masa kawai take, amma gabadayan hankalinta ba ya tare da shi, ba Karamin rudu ta shiga ba da wannan tashin tashinar ta adamu, ita dai ta san ba zata taba mutuwa ba in dai ba samun abinda yake so yayi. ba, don ba yau take da shi ba, tana da yakinin yarinya Husna da yake magana tana daga cikin – abubbuwan da idan ya fara so ba ya bari, don haka ta fara tunanin yadda zata shawo kan Yayansa ya yarda da lamarin a kashe bos din kowama yahuta Ranar bai bar gidan ba sai Karfe tara da rabi na dare.

*************

Cikin tsananin kadaici Husna ta iso gidan Boka Salmanu,ba ta so zuwa ita kadai ba, amma cikin Jamila da Amina ta rasa mai rako ta, gashi kuma babu damar ta daga zuwan tunda Bokanta ya ce mata in dai Adamu ya zo washegari ta Zo ta sanar da shi. Kodayake ita a dokance take tazo ,

ta sanarwa bokan cewa, Adamun ya zo yayi alKawarin turo magabatansa nan da sati,

Salmanu na tabbatar da cewa Husna ce zata – shigo, yayi dabarar korar Tanimu sallar la’asar da bai ba, ya kuma san halin Tanimu sarai in dai ya je sallar sai ya kishingida, don haka ba shi da tararradin cewa Tanimu zai kwanta a matsayin Aljani har ya jiyo abinda zai wakana tsakaninsa da: Husna wanda zai iya sanyawa ya shanshano wacece Husna kuma waye saurayin da ta kawo.  Wannan karon cikin nutsuwa Husna ta sanar’ da boka yadda aka yi, sai dai kanta na sunkuye alamun kunyarta na nan tare da ita. . Abinda kuma ya birge Salmanu kenan ya Kara tabbatarwa dole son Adamu yayi mata ya sanya ta abinda sam bai karbe taba. Www.bankinhausanovels.com.ng 

Tana jiran ta ji wata sabuwar cewar daga Salmanu akan bayanin da ta yi masa, amma sam shi bai kamo wannan ba, cikin muryar shan Kamshi ya mika mata wata takarda dauke da lambarsa yana cewa, :

“Ga lambata nan, duk lokacin da zaki zo ki dinga kira ni da safe kina sanar da ni, rannan bayan kin tafi Alajani Sharwaziyo yazo da
wani batu, akwai wata mahaukaciya da ke zuwa shan magani gidan nan, jininku bai hadu ba, in tayi arba da ke labari zai iya shan bamban”. Wata irin razana ta tasowa Husna tun daga _kwanya, hannunta na karkarwa ta mika ta karbi takardar, wannan wanne irin bala’! ne? ta sami wajen share hawaye kuma wata Katuwar mahaukaciya zata hana ta zuwa? Haka dai ta hadiye tsoronta ta cewa Salmanu, “Na gode Allaha Kara arziki”.“Amin’. Salmanu ya masa sannan bai jira cewarta _ «ba ya cigaba da cewa, “Yaya kika ga yanayin Adamun, kin gamsu da yadda yake ko kina da wani shakku?”. Husna tsakaninta da Allah ta amsa, “Kulawa kadai ta ishe ni daga Adamu, tsakani da Allah nake sonsa ba na buKatar ko ~° _ kadan ya cutu… haka ma yayi mun, in dai ba zai bar ni ba wannan ya ishe ni…”. Salmanu yayi murmushin da ba ya shakka tun daga zuciyarsa ya taso. Ya kada kai ya ce, “Wacce rana kike son ya kawo kudin? Za mu sanya shi ya kawo a ranar’. Cikin doki Husna ta ce,  “Kwana uku nan gaba yayi Malam?”, : Salmanu ya kada kafada, “Babu laifi yayi”. ; _ Cikin fara’a Husna ta shiga godiya. Salmanu ya katse ta da tambayar, “Kamar nawa kike son ya kawo?”, . Da sauri Husna ta girgiza kai a raunanc tace, – “Ba ni da zabi Malam, yadda dai ba zai -takura ba”. , ‘Salmanu ya sake murmushin jin dadi,-ya_—_, dauko Kullin lalle ya jefa mata. Ga shi nan ki tafi da shi ki cigaba da ado _ da shi a yatsun hannunki, kin kama Adamu kin gama, har abada ba zai fasa sonki ba”. ~ . . Husna ta cafe cikin barin jiki tana cigaba da godiya, sannan tace,* ‘‘Nawa zan bayar Malam?”. Kai tsaye ya amsa,“A’a ki je kawai, zai aiko da manyansa nan da kwana uku ko hudu kamar yadda kika zaba”’. , Sai Husna ta rasa da bakin da zata gode masa, jikinta a sanyaye ta yi masa sallama ta fice  ta bar Salmanun da fargabar ta inda zai yaki Adamu ya kai kudin aurenta nan da kwana uku, Www.bankinhausanovels.com.ng 
shi da kansa ya fara jin lallai ya kinkimo da kauri wannan lokacin. . Washe garin ranar suna tare da Adamu da: sanyin safiya lokacin babu Tanimu,. Adamu ya“,. sami kira daga yayansa cewa lallai yazo yanzun nan. Cikin dakewa Adamu ya dubi Salmanu yace,  “Salmanu da gaske mun tara kudin da zasu ishe ni aure? Wancan mutumin: ya kira-ni na.kuma san kurari zai yi min na in na‘ tarko aure’ na aura da kudina”.Cikin kwanciyar hankali Salmanu ya dafa kafadar Adamu,“Mun tara, kar ka damu Adamu, in ruwan bikin ma ya ce sai mun siya zamuiya” Nan da nan Adamu ya Kara fara’a, . ‘ “Ina alfahari da kai Salmanu”. Salmanu na dariya ya amsa, ~ “Dole ka yi alfahari da ni, domin ba ni da kowa sai kai’. an ‘ Suka kyalkyale da dariya sannan suka tafa. Salmanu na rike da hannunsa ya ce, ” “In ka je ka ce jibi kake son a kai maka  Adamu ya tare shi, . . “Idan ya matsa min ma zan tura masa haushi da cewa a kai min yau ko gobe, ina sane nake birkicewa na yi ta tura musu haushi”’. Salmanu ya sake bashi hannu suka tafa suna cigaba da dariya.

*******

Kamar yadda suka shiraya kuwa, da fuskar shanu Adamu ya shigarwa Alhaji, har ma Sa’adatun da ta dinga hidimar shige da ficen . kawo masa abin karin kumallo duk da hantsi ne, amma dai tunda ta laKanci kamar mutane ba a Zuwa gidanta ta bar mutum baki bude. Ko kallon abincin Adamu bai yi ba ya cigaba da zaunewa gaban Alhaji yana ta faman latsa waya. –

Tun daga wannan kumburin nasa Alhaji ya san ba zasu kwashe ta dadi ba, don haka shi ma ya kinkimo gizago ya makawa girar idonsa. Yaiyalin?”. .

Alhaji yayi fuska ya fara da wannan.Ba tare da Adamu ya daga kai ya dube shi ba ya daga hannu ya ce,  “Suna can gida”’. Alhaji ya hadiye haushin amsar ya ce, “To madalla”, Www.bankinhausanovels.com.ng 

Yayi shiru Adamun kuma bai yi alamar . tankawa ba, dole sai shi Alhajin ne ya gyara zama ya debo abinda yatarasu, “Jiya ka tashi hankalinmu gaskiya, . musamman mahaifiyarka da ka hana runtsawa”.
Cikin daurarriyar fuska Adamu ya daga kai ya dube shi, amma bai ce komai ba. Alhaji yacigaba dacewa, “Cikin dare wallahi kasa bacci ta yi dole ta kira ni a waya ta ce na zo na ji danyen hukuncin dakazodashi’, .. Kawai sai Adamu ya daure gira ya sake yin Kasa da kai. oy . -Cikin fishi Alhaji yace,
Anya Adamu ba-zaka bar rayukanmu ni. da mahaifiyarka ya zauna lafiya ba, kullum mu kenan cikin saKa da warwarar yadda zamu ga ka , zama mutumin kirki kai kuma kana baudewa?___ Wai me ke damun hankalinka ne?”Adamu ya sake bata rai, murya a cunkushe,  yace,” “Ni wallahi ban san abinda yanzu nayi,,,,, Alhaji ya tare shi da sauri,

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page