RUBUTACCIYA BOOK 3 CHAPTER 3 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

RUBUTACCIYA BOOK 3  CHAPTER 3 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO 

                     Www.bankinhausanovels.com.ng 

MUN TSAYA 

Jiki a sanyaye ta mike har ta kai bakin ‘kofa ya ji a zuciyarsa bai kyauta ba, da ya yi mata hakan, ya tabbata da Nasreen ce ta shigo cikin bargo zai maidata. Ya zama dole ya jinga Kokari wajen ganin ya bi shawarar nahaifinsa.

“Zakiyya.” Ya kira sunanta cikin sanyi.

Ta waiwayo cike da mamaki. Har hawaye sun sami daman zubowa.

Gabansa ya fadi, domin ya san kai tsaye gun Umma za ta wuce. Hannu ya mika mata, hakan ya sa ta dawo da sauri ta kama hannunsa ya zagayo da ita kusa da shi. Hijabin da tasa ya yaye sannan ya hadata da jikinsa. Warin attachment din kanta da Karni suka dake shi, ya dan kawar da hancinsa sannan ya fara magana cikin lallabawa, “Zakiyya ba na son ina bata maki rai amma ke kike sawa. Ki yi hakuri kin ji? Ba na son a yi maki kallon mara kunya ce, ki koma cikin jama’a.”Www.bankinhausanovels.com.ng 

Zuciyar Zakiyya fari sol! Ji take yi kamar duk duniya babu ‘ya macen da ta yi dacen da ta yi. Yana kallon ta ta fice tana ‘yar dariyarta. Ajiyar zuciya ya Kwace masa, yana son ganin Nasreen yana son ya yi barci wuri guda da ita, ta haka ne zai iya samun natsuwar da yake da buKata. Sai dai maganar mahaifinsa ita ke danne shi, dole ya mayar da kansa kawai ya kwanta.

*********

A daddafe suka kai kwanaki biyu, yau ne kuma suke sa ran tafiya. Shiru-shiru Sultan yana jiran mahaifinsa ya hada su amma bai yi hakan ba, don haka ya ci gaba da zuba idanu. Yana daki yana shiri aka aiko Nawfal wai ya zo. Babu bata lokaci ya iso falon, abin mamaki dukkan halittun dake cikin gidan suna nan zaune a falon nan. Nasreen tana zaune kusa da Abba kanta a Kasa. Umma kuwa ta cika ta yi fam! Sai girgiza Kafafu take yi.

ZAMU TASHI 

Abba ya _dubi Nasreen’ ya _ ce, “Althamdulillahi, dukkan godiya ta tabbata ga Allah da ya sake ba mu aron wannan ranar. Nasreen na sanki mace ce mai hakuri da rashin son hayaniya, tun a lokacin da naga shakuwarki da Sultan na tabbatar da babu namijin da zai riKe ki irin rikon wanda ya san darajar kansa ya san abinda yake yi sai Sultan. Ya fi kowa sanin darajarku ke da dan uwanki, yana sonku fiye da ~ tunanin mutum, saboda shi ya reneku tun kuna cikin tsumma. A yau zan damKa masa ke a matsayin matarsa ta har abada. Sai ki yi hakurin ; zaman aure, ki kwantar da hankalinki, ki yi wa mijinki biyayya. Allah ya yi maki albarka, Allah ya ba ki sa’an yi wa aure bauta.”’

Nasreen da ta ji wani abu ya tsirga mata, a yau dai ta tabbatar da da gaske ne ita matar aure ce, auren ma na Sultan dinta. Kuka take yi sosai tana jin ko iyayenta ne iya abinda za su yi mata kenan, tausayin kanta ya kamata, tsoron wani irin zama za ta yi da kishiyarta suka sake wanzuwa a zuciyarta. Bata fatan ta baiwa Abba kunya a cikin rayuwar aurenta.

Abba ya dan goge Kwallar da suke _ Kokarin zubo masa ya dubi Sultan, “Allah ya yi Www.bankinhausanovels.com.ng

maka albarka Sultan, tabbas da ba dan kai ba, da ban samu tarin ladan nan ba. Ga matanka nan Zakiyya da Nasreen, ka riKe su amana, ka zama adalin namiji, kada ka yarda gidanka ya lalace ta hanyar baiwa wata Karfin da za ta mulki gidanka. Ka zama jarumi a cikin matanka. Daga Nasreen har Zakiyyar dukka naka ne, sai ka dinga kallon su a matsayin jininka.” Ya dawo da dubansa ga Zakiyya ya ce, “Zakiyya ga Nasreen nan ‘yar uwarki ce ba kishiyarki ba, kada zuciyarki ta sa maki da kishiya kike zaune a’a da ‘yar uwarki ce ta jini. Ga amanarta nan na baki. Kin girme ta nasan za ki fita hankali da sanin abinda ya . kamata. Ku hada kawunanku kuyi ta zane Sultan a cikin gidan.”

. Zakiyya ta yi murmushin da ba ta yi ninya ba. Haka Abba ya ja masu kunne cikin sigar lallashi. Ya dubi Umma ko za ta yi magana, sai ta kauda kanta ta ce, “Wacce  magana kuwa zan yi? Allah ya tsare sai na zo.”

Babu wanda ya gane abinda take nufi. Nawfal a nan gidan zai zauna tukuna kafin ya wuce Makaranta. Nasreen ta sa kuka ba za ta tafi ta bar Nawfal ba. Haka ta KanKame Nawfal tana kuka mai tsuma zuciya.

Jikin Sultan ya yi sanyi ya dubi Abba ya ce, “Abba a bar mana Nawfa! don Allah.” Www.bankinhausanovels.com.ng

Abba ya girgiza kai, “Idan Nasreen tana kuka saboda babu Nawfal ranar da ya tafi Makaranta kuma fa? Kai ka san irin kukan da za ta yi ? Ku tafi kawai.”

Nasreen ta sake sa kuka, Nawfal ya yi mata magana Kasa-Kasa, “Ki daina kuka  Nasreeen zan zo insha Allahu. Ba rabuwa muka yi ba.”

Shi ma hawayen ke zuba sosai a idanunsa, . domin yau ce rana ta farko da za su rabu. Tausayin ‘yan biyun ya kama Abba.

Nasreen ta laluba ta kama Kafar Abba kawai tana kuka, gaba daya ta kasa magana.

Abba ya shafi kanta, “Allah ya_ tsare hanya. Allah ya yi maki albarka.” Abba ya dagata ya kai ta har cikin mota. Kuka take yi tana kiran Nawfal, amma ina babu Nawfal sai

” dai Sultan. Kukan da take yi yana daga masa hankali, ga shi Zakiyya ta kafe ta tsare bare ya bata kulawa.

Duk da hakan sai da ya zaKala hannunsa cikin gyalenta ya ce, “Kiyi haKuri ki daina kuka kinji? Gobe insha Allahu Nawfal zai iso. Shiru

kawai ta yi tana ajiyar zuciya ba don ta yarda

‘ da abinda yake fadi ba. Zakiyya tana kula da

» Nasreen yadda take kwance a kafadar Sultan, hakan ya sa ita ma ta kwanta tana gyangyadin Karya. Duk yana kula da ita bai ce komai ba.

Suna isowa cikin gidan su gaba daya gidan ya sauya komiai sabo. Ita dai Nasreen bata san komai ba, domin ba idanu gareta ba, sai lalube take yi. Sultan ya kamo ta suka shiga ciki. A nan falon dukkansu suka zauna. Duk da gidan ya burge Zakiyya, amma sam ba ta yi farin ciki da wannan gyara ba, domin lokacin da za a kawota babu wani gyaran da akayi, a take kishin babu gaira babu dalili ya kamata, haka ta kasa tashi ta basu wuri. Gani take da zarar ta je ko nan da kitchen ne za a yi wani abun. Shi kuwa idanunsa Kyar a kan tv, wanda a zahiri ba tvn yake kallo ba, Nasreen yake kallo ba tare da Zakiyya ta ankare ba. Ya dube ta cike da Kosawa ya ce, “Tashi ki je ki hada min ruwan wanka.” Zakiyya ta dube shi sosai, ta fahimci yana

son raina mata hankali ne, domin bai taba sanyata tara masa ruwan wanka ba. Zamanta ta gyara tana hamma, “To zan tara maka zuwa anjima yanzu na gaji da yawa ne.” Www.bankinhausanovels.com.ng

Nasreen ta mike, “Deedi ina ne hanyar dakina?” Shima ya mike yace “Zakiyya, dama kin san sashenki. Ita kuma bari in kaita nata falon da kuma dakinta, wannan babban zai zama nan ne mahadinmu tunda falona ne.”

Zakiyya ta saki baki tana kallonsa. Kafin ya kama Nasreen har Zakiyya ta kamo ta tana fadin, “Mu je sashen naki daga nan in gani.”

Babu musu ta bi bayanta Sultan ya yi shiru yana nazarin matakin da ya kamata ya dauka don ba zai yarda da wannan iskancin ba. Haka ya taka Kafafunsa bai bi su ba ya shige bandaki ya watsa ruwa. Ya fito yana tsane jikinsa, Zakiyya ta shigo tana dubansa. “Na kai ta dakinta bangarenta gaskiya ya fi yi min kyau sosai.”

Ko dubanta bai yi ba ya ce, “Bayan mun je wurin Abba da ya ganta ya tambaye ni kayan dakinta na ce masa na siya maku iri daya ya ce ai alhakin siya mata kaya yana wuyansa ne, shi ya bada izinin aka kwashe irin nakin na zuba su a dakin baki, shi kuma ya sa aka shimfida mata wanda ya bada kudi aka siyo. Don haka idan basu yi maki ba, sai ki gayawa Hajiyarki ta siya maki wasu.”
Www.bankinhausanovels.com.ng
Baki a sake take kallonsa, yadda ya soka mata magana ya kuma daure fuska. “Kana nufin gori kake yi min kenan? Na gode Allah ina da uba, kowa yasan ubana ba haihuwar titi ba ce.” Sultan ya juyo cikin tashin hankali, ya daga hannu ya wanke fuskarta da mari, yana dubanta, “Na san za ki iya yin karambanin nan, amma ba zan dauka ba. Wallahi duk ranar da kika kuskure kika yiwa Nasreen irin wannan gorin har ta ji, sai kin sha mamakin irin matakin da zan dauka a kanki. Ban auro Nasreen domin inkawota ki ce za ki taka ta, da haukan da ke kanki ba. Ubana shi ne uban Nasreen, zan bugi Kirji infadawa duniya hakan. Babu wanda zai sheganta min ~ mata in zuba idanu ina kallonsa, babu. Yadda kike taKamar namiji ya yi cikinki aka kawo ki gidan duniya, haka Nasreen ma za ta bugi Kirji ta ce namiji ne sanadiyyar kawo ta duniya ba mace ita kadai ba. Fice min a daki.”

Jikinta na kyarma, hannunta a fuskarta ta fice. Tsoro da firgici suka shige ta, ba ta taba ganinsa a cikin bacin rai irin na yau ba. Ta fahimci yana iya yin Kasa-Kasa da ita. Tana shiga daki ta rufe Kofa ta shaki kukanta. Can ta wanke

fuska ta fito domin tana tunanin Kila yana can wurin Nasreen.

A falonsa ta same shi, bai je gun Nasreen din ba, sakamakon Kuncin da kalaman Zakiyya suka sanya shi. Yana nan kwance ya ji Sallama

_ don haka ya daga kai ya ga ko waye. Mamaki shimfide a fuskarsa yake duban mahaifiyarsa. “Umma? Me ya faru kuma? Lafiya? Ina Abba?”

Gaba daya ya rude yana tunanin ko wata matsalar ce ta sami Abbansa shi ne har ta taso ta ZO.

Umman ta harare shi sannan ta shigo tana ~ bayar da umarnin inda za a ajiye mata Katon akwatinta. “Lafiyar ta kawo haka. Zuwa na yi ni ma in huta in yi kwana biyu, mahaifinka ya karbe office dinsa, don haka zan zauna a nan in sami hutu sosai. Hafsat ta dan durKusa tana gaida Sultan Www.bankinhausanovels.com.ng

Shi kuwa mamaki da bakin ciki sun taru sun hana shi sakat. Duban Hafsat ya yi ya ce, “Yanzu fa muka taho muka bar ku a Kaduna. Ke Hafsat makarantar kuma fa?” Hafsat ta ce, “Ai sun yi hutu.”

Kan Sultan ya sake daurewa bai fahimci dalilin da zai sa mahaifiyarsa ta yi wannan abin

ba, bayan ta san mahaifinsa bai da wata mata idan ba ita ba. “Amma Umma shi Abban da wa kuka bar shi a gidan?”

Umma ta ja tsaki ta nemi wuri ta zauna tana fadin, “Wash!” Tta gaji.

Sultan ya sake maimaita mata tambayar ransa a bace. Umma ta zazzaro idanu, “To zo ka dake ni ubana! Ko kuma kawai ka ce min in bar gidanka sai in san na haifi dan da ya gagare ni. Kana kallon yadda kake yi min magana kamar ubana? Ban sani ba! Ka je ka gaya masa ya Kara aure mana tunda na ga kaine ubanmu daga ni har shi! Ban bar shi da kowa ba, sai ka nemo masa mace ka sa masa a cikin gidan. Shashashan yaro kawai mara kishin kansa. Ke dauki kayan nan ki kai min dakin Nasreen a nan zan sauka.”

Zakiyya da farin ciki ya gama kashce ta, ta kwashi kayan ita da Hafsat suka nufi dakin Nasreen. Tana zaune bisa dadduma tana lazimi, sai kawai ta ji shigowar mutane babu sallama, mamaki yasa take tambayar ko su waye.

Zakiyya da Hafsat ba su yi magana ba har sai da suka dire kayan sannan suka dawo gabanta, “‘Umma ce da Hafsat suka zo, za su yi

kwana biyu, shi ne muka ajiye kayan a dakinki don a nan za su sauka.”

Nasreen ta Kara cika da mamaki, don haka tace ‘“Wacce Umma kuma? Haba ba dai Umma ba, yaushe muka tafi muka barta a gida? Ko ba Umman Kaduna kike nufi ba?” Zakiyya da Hafsat suka yi ta mata dakuwa da hannu suna yi mata gwalo, sannan ta bata amsa, “Mence ne na yi min irin wannan tambayar? Ko dai in koma in ce mata kin ce a kwashe kayanta ne? In ba haka kike nufi ba meye na dogon magana?”’ Www.bankinhausanovels.com.ng

Nasreen ta yi murmushi ta ce, “Babu wanda ya isa ya hana Umma zama a duk inda ta gadama. Kuma ni farin ciki nayi da har ta – tsallake dakin kowa ta zabi dakina. Ina yi mata barka da zuwa. Ga ni nan fitowa.” Duk suka bita da kallo, sannan suka fito suna cewa Umma Nasrcen sai tambayoyi take yi masu.

Ran Umma ya sake baci ta zabura za ta shiga dakin Sultan ya mike ya sha gabanta. “Don girman Allah Umma kiyi hakuri.”

Umma ta dawo ta zauna tana dubansa duba na takaici. Sultan ya mike ransa a Bace ya fice ya kira mahaifinsa, “Abba meke faruwa ne na ga Umma? Ko wani abu ya hada ku ne?”

Abba da yake zaune a tsakar gida ya yi tagumi, idanunsa jazir saboda bacin rai, ya ce *Wallahi ban sani ba. Bayan kun tafi kawai naga tana shiri ban ce mata komai ba, har sai da suka gama kintsa kayansu sannan ta gaya min wai gidanka za taje Duk yadda nayi domin ta ajiye tafiyar amma taki. Na_ gaji da lamarin mahaifiyarka sakinta zanyi.” Sultan ya ji babu dadi, haka ya ji tausayin mahaifinsa, amma fadin sakin nan yasa gaba daya Karfin guiwarsa ya suki. Baya Kaunar dalilin da za ace mahaifiyarsa bata tare da auren mahaifinsa. Don haka ya ce, “A’a Abba ka yi hakuri kada ka yi min haka. Abba mu ‘ya’yanka ba za mu taba son a ce wai babu mahaifiyarmu a gidan mahaifinmu_ ba. Shawara daya zan ba ka Abba, ka duba a cikin mata masu hankali da natsuwa ka aura.”

Abba ya dan yi shiru cikin dogon tunani. Daga bisani ya ce, “Sultan ni wa na sani da zan aura? Ka barni kawai inzauna ni dayan babu komai watarana sai labari.”

Girgiza kai Sultan ya yi cike da tausayin mahaifinsa, “Abba ka auri Mairo mai aikinmu, naga tana da hankali da natsuwa. Yin hakan Kila

ya sanya Umma ta dawo hayyacinta.

A zuciyar Abba ba ya son wata “ya mace . da ta wuce matarsa, Haka ba shi da ra’ayin Kara aure, amma halin masifa irin na Salma ya saya amince da abinda yaron ya gaya masa, don haka suka sa ranar da Sultan zaije a yi magana. Yana datse Wayar ya rintse idanu yana jin tausayin mahaifinsa da gaske.

Nasreen da ta jima tsaye tayi magana cikin muryar kuka, “Deedi da bakinka kake cewa ayi wa Umma kishiya? Me yasa ba za a lallaba ta ta koma ba? Ina jin tsoron abinda zai je ya dawo.”

Sultan ya mayar da idanunsa kan. makauniyarsa ya ce, “Nasreen na gaji da halin Umma. Idan aka yi mata kishiyar Kila za ta _ sauya. Amma kishiya kam dole sai Abba ya yi mata.

Nusreen taci gaba da cewa, “Kishiya ba ita bace mafita kayi tunani da kyau.” Www.bankinhausanovels.com.ng

Sultan ya karaso gabanta yana_ son Nasreen fiye da tunanin mutum, “Nasreen ki bar wannan maganar na rufe ta. Ya aka yi kika zo nan?”

Ajiyar zuciya ya Kwace masa.  Mai aiki ta saita ni har inda kaKake. Su Umma suna

ciki suna cin abincin da dan sanda ya kawo. Yanzu kana ganin haka zamu zauna ana siya mana abinci? Ni ba idanu gareni ba bare in shiga kitchen.”

Sultan ya ce, “Wallahi ni kaina abinda ke damuna kenan. Yanzu ya zaa yi?”

_ Sai da ta jingina da bango kafin ta ce, “Ina ganin a shawara, ka sanya a nemo mana mai aiki wacce ta Kwarai a iya ayyukan abinci sai mu mayar da ita mai girkinmu. Amma ya ka gani?” Www.bankinhausanovels.com.ng

Sai da ya lakaci hancinta sannan ya ce, *‘Abinda kika ce shi za a yi. Wannan ma shawara  ce mai kyau. Yanzu kin gane dalilin da yasa Umma ta sauka a dakinki?” Girgiza kai ta yi cike da rashin fahimta, : “Wallahi ban gane komai ba.” : Nan da nan fuskarsa ta nuna bacin rai, “Umma ta zo garin nan ne saboda ba ta son mu _ kadaice ni da ke. Na rasa irin wannan abinda Umma take yi.” Nasreen ta yi murmushi, “In dai haka ne ai ni ta taimaka. Allah ya Karawa Umma lafiya.” Mamaki yasa ya murde hannunta ya ce, “Maimaita abinda kika ce. Ni kuma tunda kika

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page