RUBUTACCIYA BOOK 2 CHAPTER 10 KARSHE BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO KARSHE THEND

RUBUTACCIYA BOOK 2  CHAPTER 10  BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO KARSHE THEND

                  Www.bankinhausanovels.com.ng 

MUN TSAYA 

ciki, su kuma suka zauna suna ci gaba da tattauna hanyar da ya kamata su bi wajen ganin komai ya zo masu a cikin sauki ba tare da wata matsala ba, musamman wajen yin takatsantsar da su Nasreen, domin suna son su buga cewa ‘ya’yan da Saudat ta Haifa suna nan da rai, kuma sun girma a yanzu. Www.bankinhausanovels.com.ng

Haka suka zauna su Kullawa wannan su kwance wancan, har aka kira Sallah suka mike suka nufi Masallaci. Da Karfe goman dare yana nan zaune a falonsa Zakiyya tana latsa remot, ita a dole fushi take yi da shi, kasancewar kwana biyun nan duk ya sauya mata, haka yaki tsayawa ma ya ji matsalarta bare har ya bata hadin kai akan rayuwarsu ta aure. Lokaci zuwa lokaci tana satan kallonsa amma shi ko waiwaye. Shi ji yake kamar bai da lafiya a jikinsa, musamman ta bangaren kiyaye hakkin aure. Ji yake idan har wannan abin shi ne auren, to baya daya daga cikin irin mazan da suke da lafiyar aikata hakan. Haka zamansu da Zakiyya zai yi wahala, domin ita bata san komai a aure ba, sai

ZAMU TASHI 

wannan abin, ko gyara gado bata sani ba, yadda ya fita ya bar gadonsa a haka zai dawo ya same shi, yadda ya fita ya bar kitchen haka zai dawo ya same shi, wataran ma shi da kansa yake zaKewa ya gyara abubuwan, musamman idan yaga ya yi datti. Zanen gado kuwa tunda aka kawo ta cikin gidan nan bata taba sauya zanen gado ba, har ya fara canza kamanni. Gara ma na dakinsa idan ya gaji da ganin kala daya yana sauyawa da kansa. _ Komai a gidan kaca-kaca kamar ba Sultan _ din da ba. Www.bankinhausanovels.com.ng 

Da ta gaji ta tabbatar ba zai kawo kansa ba, ta mike ta shiga ciki ta manna wannan turaren. Tana fitowa ya riga ya kintsa yana sauri Zai je ya duba Nasreen. A lokacin kuma ya sami nasarar shakar Kamshin, amma saboda yana sauri ya kasa tsayawa yana tafiya tana binsa, “Ka tsaya mana don Allah. 

Bai tsayan ba, ya ce, “Kada ki damu yanzu zan dawo.” 

Yana jin wani abu yana fizgarsa amma baya jin da akwai dalilin da zai tsaida shi daga zuwa duba Nasreen. A wahalar ce ya iso

Www.bankinhausanovels.com.ng 

gidan bai ga Nawfal ba, bai kuma duba shi kamar yadda ya saba ba, kawai ya zura kansa falon tare da Sallama. Babu kowa a falon ya kwantar da kansa yana lullumshe idanunsa kamar wanda yake jin barci. Nasreen kuwa tunda aka ce ga Sultan take jin wani irin sany1 yana ratsata. Fitowa ta yi cikin shigarta ta atamfa ta yi mata kyau. Ta riga ta saba da inda yake zama. Ya so Kwarai da yana da 

” karfi a jikinsa, da ya fara tarota kafin . 

, isowarta. Yana nan zaune yana kallon yadda take tafiya, rashin idanun nan suna damunsa_. sosai. Tana zama yasa hannu ya jawota gaba daya jikinsa tare da sauke ajiyar zuciya, wanda ke nuni da alamun yana cikin wani hali. Shinshinar Kamshinta yake yi, cike da gamsuwa da irin kulawan Yumnah haka tana shan albarka a cikin zuciyarsa. Yana son ya — yi mata magana amma kuma a irin halin da yake ciki yasa ya kasa magana, jikinsa babu inda baya rawa. Tun Nasreen tana daukar Www.bankinhausanovels.com.ng 

– wasa yake yi har abin ya fara zarce tunaninta. Ta gigice da yawa, don haka ta fara kuka, 

“Deedi menene wannan? Dee kayi hakuri ba zan iya ba, ina jin wani iri.” 

Ba ya jinta baya fahimtarta, Zakiyya ta manna masa jaraba ta barshi da abin kunya a cikin gidan jama’a. Nasreen ta samu ta fizge kanta ta ruga cikin gida, tana tafe tana hadewa da garu. Yana kallonta bai yi yunKurin hanata guduwar ba, shima zai so hakan gudun kada ya yi abinda bai kamata ba a cikin gidan jama’a. Rufe idanunsa. gyam! Ya yi yana da buKatar komawa gida ya sami Zakiyya. Idan ba haka ba, a yadda yake ji , komai zai iya faruwa da shi. Ita kuwa Nasrecn dakinta ta shige jikinta yana kyarma. 

A haka Yumnah ta shigo ta same ta kasancewar tana kitchen ta hango shigowarta a gigice. Dafa ta ta yi hakan yasa ta sake razana, “Don Allah ka yi haKuri ka bar ni.” 

Saboda gigicewa ta kasa bambance hannun Yumnah da na mijinta. “Ki natsu Nasreen menene haka? Me ya faru?” Nasreen ta riga ta dauki Yumnah a matsayin ‘yar uwarta ta jini don haka ta fara magana, “Wai Dee ne… Wai…” Sai kuma ta yi shiru. 

Yumna ta ce, “Ki yi magana mana wai mene?” Www.bankinhausanovels.com.ng 

Sai da ta shaki iska ta saki ajiyar zuciya mai Karfi, “Yana min wasu abubuwa kamar_ . ya fita hayyacinsa.” Murmushi Yumnah ta yi ta ce, “Amma dai Nasreen na raina wayonki. Menene ba mijinki bane? Ashe duk irin son da Yaya Sultan yake gwada wa akanki a wurinki ba haka ba ne? Na tabbata idan da ke ce kike cikin mawuyacin hali irin wannan da babu abinda zai hana shi ya taimaka maki ko da kuwa a tsakiyar kasuwa ce. Baki kyauta ba, da baki tarerayi mijinki a lokacin da yake da buqatar hakan ba. Yanzu idan ya tafi titi ya nema fa? Me za ki cewa Allah? Maza tashi kije ki taimaka masa, na tabbata duk irin fita hayyacinsa da ya yi ba zai ce zai dauke budurcinki a lokaci irin wannan ba, zai so ya sami wuri mai cike da natsuwa domin ya kafa tarihi mai wahalar gogewa. Maza ki je ki sami mijinki.Nasreen da natsuwa ya shige ta ta girgiza kai, “Ina son Dee, amma ina tsoro ba zan iya ba.” Da Kyar Yumnah ta samu ta lallabata har ta sake fitowa, sai dai tana ta 

lalube tana cewa, “Dee kayi hakuri ba zan sake gudunka ba.” Shiru hakan yasa ta yi , waje tana lalube. 

Nawfal ya hangota ya Karaso da sauri, ganin za ta ci Karo da tukunyar filawa yasa ya riKeta, “Menene kuma? Ina za ki je?” 

Idanunta cike da hawaye ta ce, “Dee nake nema. Nawfal Dee ya tafi ko?” Dariya ma abin ya bashi cikin dariya ya ce, “Tun 

_ yaushe? Ai bai ma jima ba ya tafi, kuma ko? gaisawa bamu yi ba, ina sauri inKaraso har ya shige mota abinsa. Fuskarsa kamar dauke * take da damuwa me kika yi masa? Kai nasan ba ke bace domin ko giyar wake kika sha ba za ki taba iya bata masa rai ba.” 

Hankalin Nasreen ya Kara tashi ta dinga girgiza kanta. Ganin tana hawaye yasa Nawfal ya zare idanu, “Mene ne haka Nasreen? Me kuma ya faru?” Www.bankinhausanovels.com.ng 

Juyawa ta yi ba tare da ta iya cewa komai ba, ganin tana cikin wani yanayi yasa ya yi mata jagora. Abinda bata sani ba, Sultan yana nan zaune yana kallonta haka shi ya 

Kyaftawa Nawfal idanu har ya fahimci abinda yake nufi. 

Tana shigowa falon taja ta tsaya. “Mu je mana in raka ki.” 

Girgiza kai take yi, “Nawfal Dee yana cikin dakin nan yana nan a dakin nan bai yi nisa da ni ba. Don Allah Dee idan kana nan ka yi min afuwa ka yi magana, rashin aikata 

, hakan zai iya sawa in kwana cikin bakin ciki da dogon tunani.” 

: Da hannu ya yi wa Nawfal alamun ya fita kawai. Nawfal ya fice yana dariya. Jin falon shiru ya sa ta ce, “Nawfal! Ina kuma ka. shiga ne? Allah sarki don kun ga bani da idanu sai ku dinga yi min abinda kuka gadama. Babu damuwa na gode.” 

Ta juya za ta tafi, har ta kai bakin Kofa tana son ta ji ko daya daga cikin su zai yi magana amma shiru. Hakan yasa ta sauya hanya da gangar ta nufi bango gadan-gadon. Sultan ya rintse idanunsa ya ce, “Nasreen tsaya!” 

Babu musu ta ja ta tsaya fuskarta cike da farin ciki. Ba ya son sake tunkarota, domin 

zai iya nanata abinda ya aikata da farko. A nutse ya Karaso yana duban labbanta. “Ki je ki huta zuwa anjima zan dawo muyi magana.” 

Gyada kanta ta yi ba tare data kawo komai a cikin ranta ba. Ya manna mata sumba a goshi ya dawo bisa labbanta. Murmushi ta yi bayan ta lashe dukkan tausasan labbanta, haka ta kasa ci gaba da__, tafiya. Komai na Sultan daban yake da sauran maza. Bai cika yin abu cikin garaje ba, shi ya sa komai nasa yake cikin tsari. Yana nan tsaye har ta shige sannan ya saki ajiyar zuciya ya fice abinsa. , Www.bankinhausanovels.com.ng 

Yana isowa gida bai yi wata-wata ba ya biyewa Zakiyya har ya faranta mata fiye da tunaninta, kasancewar da Nasreen ya dawo a zuciyarsa, don haka ya shigo mata da tarkacen Nasreen. Farin ciki kamar ya kashe ta, bayan ya kintsa ne yana zaune a falo ya kirawo Zakiyya ta zo ta zauna ya dube ta sosai ya ce, “Zakiyya kina son zaman mu ya dore?” 

Ta gyada kanta, “To don Aliah ki dinga 

tsafta. Hatta jikinki yadda kike tsafta ce shi bai yi ba. Banga dalilin da za ki yi wanka amma kuma sai ki fito kina wari ba, dole akwai dalilin faruwar hakan. Haka ba zai yuwu gidana ya zama Kazantacciyar gida ba. Saboda kina ciki ne shi ya sa na sallami mai aikina, ankawo maki mai aiki amina banga amfanin da take yi ba. Ke kallo ita barci. To na kai Karshe idan kina son mu shirya gara tun wuri ki gyara halayyarki. Bana son Kazanta, babu zama da Kazami a cikin tsarina”” 

Zakiyya da ta gama muzanta ta yi yake, “Zan gyara insha Allahu.” 

Zakiyya ta koma daki tana shinshinar kanta amma bata ji warin ba, tana mamakin ta yadda babu kawaici kawai za ace mata tana wari, kai tsaye ba tare da tunanin abinda za ta _ ji a cikin ranta ba. Wannan kalma ta Kona Mata rai, domin tasan tana wanka tana iya bakin KokKarinta wajen bulbula turare. Ya zama dole ta ci gaba da sanya turaruka masu Karfi, domin ta burge shi. Abinda Zakiyya ta 

manta ko ince bata sani ba, wannan wankan tsarkin da ba ta yi shi yake kawo mata dukkan matsalolin nan, tana da Karancin ilimin addini sosai. Ko da yake dama ita bata taba yin wata Islamiyya ba, Kyale ta dai da boko. Ita dai tasan ana cewa mutum yaje ya yi wanka, kuma tabbas tana yin wankan, ko da kuwa ta jinkirta hakan. Haka wani abinda ya sake jawo mata babbar matsala a farjinta idan ta gama iskancinta sai ta shirya ta fice ba” tare da ta wanke lungu da saKo ba, hakan ya jawo danKarewar datti, wanda yake haifar ~° mata da mugun’ warin gaba. Ita kanta tana jin warin bare kuma Sultan. Kullum burinsa ya daure kada ya gaya mata har ankai matsayin da dole ya fito yagaya mata domin a zatonsa za ta iya gyarawa ne. Sultan ya kasa samun natsuwa dukkan motsin da ya yi sai ya tsargu sai ya dinga jin warin jikinta a jikinsa. Ya yi wanka a Kalla sau hudu, amma bai daina ji ba. Ya rasa wani irin shirme ke jawo shi Zuwa gareta. Www.bankinhausanovels.com.ng 

Wasa-wasa sai da Sultan ya yi kwana uku bai je ya duba su Nasreeen ba, aiki yayi

masa yawa, duk da yana da daman ya Zo ya dubata din ya yi hakanne saboda yana son ya nesanceta kada ya aikata abinda zai bata mata. Ita kuma a can ta dami  da kuka, akan Sultan ya yi fushi da _ ita ne.Yumnah ta yi masa kiran duniya amma yaki daukar waya, da yake sun san halinsa, mutum ne mai wahalar daukar waya. Hatta iyayensa kuka suke da shi, wanda tuni ya riga ya zama jinin jikinsa, duk yadda yaso ya ga ya gyara wannan hali abin ya _ faskara. (Hallayarsa sak! Halayyar Yaya Adamu.) Aslaf yana zaune a falonsa yana karanta jarida Yumnah ta Karaso, “Doktona ka kira Yaya Sultan ‘yan biyun gidan nan sun daina yiwa kowa walwala saboda rashinsa. Na kira shi ka dai san halinsa ya Ki daga wayar.” Aslaf ya janye jaridar daga idanunsa ya dubeta sosai, “Kin yi kyau likitan zuciyata.” Murmushi ta yi tana jin dadin yabawan mijinta akan komai nata. Ya zaro wayarsa ya kira wani dan sanda da ya tabbatar ko wani irin lokaci suna tare. “Kai baiwa Sultan wayar.” . ; 

A take ya Karasa kusa da Sultan ya sara masa kafin ya miko masa wayar. Bai karba ba ya dube shi, “Waye ke kirana?” 

“Yalla6ai Doctor ne sir!” 

Sultan ya gane waye, don haka ya ci gaba da danna Laptop dinsa sai da ya gama : komai tsaf sannan ya waiwayo ya karba, Baka da layina ne za ka kira layin yarona?” 

“Eh ba ni da layinka. Idan mainadaita , bata da rijista don haka babu amfanin kiran layin wanda marabarsa da layin da aka binne__a Kasa, shigowar kira. Malam ba abinda ya kawo ni kenan ba, na kiraka ne ingaya maka, ka zo ka kwashe ‘ya’yanka domin idan suka mutu bana jin kai ka isa ka tambayeni dalilin mutuwarsu.” 

Sultan ya shaki iska ya waiwaya hakan ya sa kowa ya fice ya bashi wuri, “Aslaf ba za ka gane bane. Aiki ne ya yi min yawa, amma su zama cikin shiri zan zo inkwashe su a wannan hutun Karshen makon zan kai su gun Abba. Sai ka shirya ka raka ni idan ba ka wani abu.” 

Aslaf da ya ji damuwa, domin har ya saba da nawfal sosai, haka yaransa ma sun saba da ‘yan biyun bare Yumnah da take jin kamar a bar mata Nasrcen ta zama Kawarta. 

Aslaf ya girgiza kai, “A’a Sultan kamar ya yi wuri ka dauke su, ka dai dinga basu lokacinka idan ka yi hakan zai rage mesu kewarka. Kuma idan ka kai su wajen Abba acan za ka bar su?” 

Gabansa ya fadi da Karfi da ya tuna da wacece Umma. Shafar kansa ya yi yana jin 

tarin damuwa a zuciyarsa. “Aslaf akwai matsala sosai. Idan naje zamu yi kwana biyu, sannan indawo da su. A take zan raba masu girki ita da Zakiyya, kowacce _ inbata bangarenta, shi kuma Nawfal Makaranta zan tura shi, shi dai dan sanda zai yi, daga nan sai muyi zaman meetin yadda za a yi a sami Doctor din da zai yi aikin idanun sai ya bamu Date. [dan idanun Nasreen sun gyaru, ka gaa lokacin sai mu shiga aiki sosai da sosai, dama rashin yaran yasa muka dakatar da komai. Don haka zan zo kamar yadda na gaya maka zan tafi da su. Na gode Aslaf Allah ya Kara Www.bankinhausanovels.com.ng 

mana zumunci.” Aslaf ya katse shi da cewa, “A’a menene kuma na godiya? Mun riga mun zama daya, zai fi kyau ka ajiye godiyarka. Ka rike wayar zan aika wa Nasreen Kila mu sami dariyarta yau.” 

Girgiza kansa ya yi kamar yana ganinsa, “A’a ka cewa Yumnah ta rike wayarta zan kira sai ta ba ta.” 

Aslaf ‘ya dubi Yumna ya ce, “Fushi take yi da kai, ta kiraka har ta ji babu dadi, amma  baka daga ba.” 

Murmushi ya subuce masa, “Ka ce mata ta yi hakuri da ni. Kuma babu kyau Kanwa tana fushi da yayanta.” Haka suka kashe suna raha, ya kira mai wayar ya bashi, sannan ya ci gaba da abinda yake yi. Da yamma likis ya dawo gida kawai ya shige dakinsa ya rage kayan jikinsa sannan ya shiga wanka. Sai da ya gama natsawa tsaf! Sannan ya haye gadonsa shi kadai yasan abinda ke cikin zuciyarsa. Tunanin Nasreen yana neman ya illata shi. Daga wayarsa ya yi ya kira Yumnah bata daga ba, ya sake kira a karo na biyu, har ta kusa tsinkewa sannan ya 

ji alamun anraba Karar bugun da wayar, wannan ke nuna masa ana kan layi. “assalamu alaikum.” 

Ya ji sassanyar muryarta ta wuce ta kunnensa ta isa har makogoronsa. Sake lumewa ya yi cikin gadonsa, yana jin sanyi yana tsirga masa. Www.bankinhausanovels.com.ng 

“*Yar babyna, mai kuka don ba ta ga Deedinta ba. Oya yi min kukan yanzu in ji ko 

“kin iya ko inzane dan bakin nan da bulala na . mai zafi.” 

Fara’a ce kwance a fuskarta hakan yasa Yummnah ta fice tana girgiza kai. “Deedina ina yini? Ya su Anti Zakiyya?” Kiran sunan Zakiyya da ta yi ne ya sa ya ankare da yana da wata matar. 

– Murmushi ya yi ya ce, “Lafiya lau. Zakiyya tana fushi da ke, tunda ba ki kula mata da mijinta.” 

Rau-rau ta yi da idanunta sannan ta ce, “Dee fushi kake yi da ni ko? Kayi hakuri ba zan sake ba. Dee bana son fushinka yana hanani barci.” 

Bangon dakinsa ya kafe da ido kamar mai karanta wani sako mai mahimmanci, sannan ya bata amsa, “Kin taba ganin inda Yaya yake fushi da Kanwarsa? Ba na fushi da ke aiki ne ya sha kaina. Nasreen duk yadda naso ki dinga jin yadda bugun zuciyata ke sauyawa a duk lokacin da muke tare bakya ji. Na tabbata da kina ji, da ba za ki dinga kallo na a matsayi wanda zai cutar da ke ba.” Www.bankinhausanovels.com.ng 

“Wayyo Dee ban taba kallonka a * hakan ba. Nima ina sonka haka Deee. Shi ya sa kayi mana yaji ko? Ko bana ganinka idan * kazo ai zuciyata tana ganinka kuma tana sauraren ka. Nawfal ba ya dariya da kowa saboda rashin jinka da ganinka.” 

“Ki ba shi hakuri zan zo mu _ wuce Kaduna wajen Abba, nasan yanzu kun murmure ko?” Bata bashi amsar ba, sai murna da take yi za ta je ta ga Abbanta. “Deee.. wai da gaske an daura mana aure?” Wannan tambayar kullum sai Nasreen ta maimaita ta, haka tana kwana cikin tambayar kanta da gaske ne wai ita matar aure ce? 

Murmushi ya yi ya ce, “Irin tunanin da kike kwana kina yi, irinta nima nake kwana ina yl. Zan gazgata ke matata ce kadai idan har na kaiwa Abba ke ya bani izinin intaho da ke Abuja, inmallaka maki dakinki a matsayin dakin matata. Ki shiga turakana da sunan kin zo wajen mijinki. Idan hakan ya faru a wannan ranar zan kwana ina godewa Allah.” 

Juyi ta yi bisa gadonta ta lalubo filo ta manna a Kirjinta, “Ni kuma a lokacin ina can 

_’ duniyar wahala, na yi alKawarin zan yi azumi uku idan har Deedina yana raye. Ka ga har nayi azumina na kammala. A ranar da za ka kwana kana Sallah, tare zamu kwana Dee, nima bana gajiya da godewa Allah, saboda shi ma baya gajiya da biya mana dukkan bukatun mu.” 

 Sultan ya sake jifan bangon dakinsa da murmushi, ba tare da ya lalubo abinda zai gaya mata ba. Tsintar muryarta ya yi tana cewa, “Na so in riga Nawfal fara ganin fuskarka, naso inga irin kyan da na ji ana kururutawa ka Kara, sai dai hakan bai yuwu ba sakamakon makanta da ta toshe min 

idanun yin hakan. Sai dai kafin Allah ya karbi idanun da ya bani aro, ni shaida ce Dee mai kyau ne, Dee yana da kwarjini a idanun kowa.” 

Kalaman yarinyar suna yi masa kama da mai son cusa masa rauni a Zuciya. ““Nasreen kada ki damu za ki gan ni da zarar muka ci karo da Dokto din da zai yi maki aiki.” Www.bankinhausanovels.com.ng 

Cikin rauni ta ce, “Don Allah zan roKe ka wani abu. Amma sai a ranar da Za a yi min aikin.” 

“Allah ya kaimu ranar.” Ya mayar mata 

da amsa yana jin barci yana son kwasarsa. 

Zakiyya ta shigo dakin tana Kare masa kallo, “Da waye kake waya?” 

Firgigit ya bude idanunsa, “Kin ajiye ni ne kike min tambaya irin wannan? Ban sani ba.” 

Zakiyya ta shaKa iya shaKa ta fara antayo masa maganar da duk tazo bakinta, 

“Wallahi na dade ina zargin ka koma bin matan banza, ga ni a gida sai ka je waje kana 

neman na wasu, saboda haram tana da dadin aikatawa,” 

Sosai ya ware idanunsa, “Ashe kina iya bambance Haram da halas? Idan kika sake danganta ni da aikata zina sai kin yi danasani. Idan na fita waje na nema ina ruwanki? Ki gyara kanki mana ki ga yadda namiji ke zama a like da matarsa. A Kazantar naki ne zan zauna da ke? Ke fice min a daki tun kafin fushina ya sauka a kanki.” 

Zakiyya ta fasa kuka ta fice. 

Nasreen kuma tana gama saurara ta sauke wayar jikinta a sanyaye. Ta fara hango tarin Kalubale a cikin zamanta da Zakiyya. Kalmar warin da Sultan ya yi amfani da ita, ta tsaya mata a rai. Wannan ke yi mata nuni sai ta sake tashi tsaye wajen ganin ta zage dantse domin Kwato mijinta, don ganin ta faranta masa. Www.bankinhausanovels.com.ng 

Mu hadu a littafi na 3 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page