Hausa Novels

BABBAN GORO BOOK 3 CHAPTER 7 by sumayyah Abdulkadir

BABBAN GORO BOOK 3 CHAPTER 7 by sumayyah Abdulkadir

                     Www.bankinhausanovels.com.ng 

‘yan’ uwantaka suke? 

Tun iyayensu na raye take rike da Shatu, ita ta yi mata aure ta yi mata gadon daki. Lokacin da Baban Danejo ya rasu, ita ta ci gaba da rikonsu ita da ‘yarta, ta aurawa Lamido. 

In kana son ganin bacin ran Hajiya Nadeeya, ko kai wane to ka yi batanci ga Danejo ko ka fadi laifin ta. 

Lamido bai isa ya ce Danejo ta yi mishi laifi ba, yanzun nan za ta gwale shi, ta zage shi ta uwa ta uba. Wai duk duniya bayan iyayensa ba mai kaunar shi kamar Danejo, don tun ba shi da ko sisi take tare da shi. Yanzu da ya samu shine zai nemi ya tozarta ta. 

Lokacin da Lamido ya fara yin kwari, ya so ya kaita ta sauke farali amma ta ce sai Shatu da Danejo sun fara zuwa. 

An ba shi auren ‘ya’yan manya har ba adadi, ta hana shi karba saboda Danejo. Dubi tijarar da ta rika yiwa Malam a kan auren Lamido da Safah. Ba don Malam din namiji bane, da ba a yi auren nan ba. Tsakaninta da Shatu da Danejo sai Allah Ya yi musu hisabi. Wata shari’ar……SAI A LAHIRA! 

An cafke Danejo da yara biyu a Airport din kasar Neitherland. Shari’ar da aka yi ba doguwa ba ce, domin shaidu sun bayyana, yaran kuma sun tabbatar ita ce ta sasu, komai a rubuce yake da kwanan wata da sa hannunta. 

Taso ta yi gardama Shatu ta kwada mata mari ta 

ce, “Ke kika sa su, haka kawai da tsufana kinsa an daura min ankwa saboda mugun kishinki mara amfani, kin rabani da ‘yar’ uwata daya da ta saura mini a duniya”’. 

Sai tasa kuka. Danejo ta ce, “Idan ni na sasu ba ke kika gaya min yadda za a yi ba? Na taba cewa zan ci gadon Lamido ba ke kika ce mu ci ba? Kwadayinki ya ja miki amma ni son Lamido nake saboda Allah ba don abin da ya mallaka ba…..ko na kashe Lamido, wallahi a kan ina son shi ne, nima a kashe ni don ban ga amfanin sauran rayuwata ba tare da Lamido ba……” Tasa kuka. Haka Alkali ya gama rubuce-rubucensa, ya yanke hukuncin da shari’a ta bayar. Danejo da Shatu daurin rai da rai wato (life inprisonment). Sauran yaran kowa ya karbi hukuncin da shari’a ta ba shi. 

Wannan bai wanke zuciyar Abdulkarim da Nadeeya ba, karfin imani kadai ke rike dasu. Jigon gida ya tafi, babban bango ya fadi. Zuciyoyi sunyi duhu, idanuwa sun kode don kuka, kuzari Ya tafi, walwala ta dushe, baki yayi gummm! Sai zuciya ke azabta. 

In ka ga wannan family sai ka zub da musu hawaye, don kowannensu babu karsashi, farin cikinsu daya likitoci sun ce akwai yaron ciki a jikin Safah. 

Malam da Deputy sun hada dukiyar Lamido waje guda, kyautar da ya yiwa Malam da Safah malamai sun ce bata halatta ba, domin ya yi ta ne ba 

1 2 3 4 5 6 7Next page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Related Articles

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE