NAMIJIN KISHI CHAPTER A BY JANNAH JAY

 NAMIJIN KISHI CHAPTER A BY Firdausi S Ahmad JannahJay                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

*NAMIJIN KISHI*

By *JANNAH JAY* (Firdausi S Ahmad)

Wattpad  *@jannahjay8*

© 2019

بسم الله الرحمن الرحيم

*Asssalamu alaikum, wannan littafi mai suna asama k’agaggen labarine wanda ya k’unshi illar zazzafan kishi dayakan jefa wasu ga zargin abokan zamansu wanda ak’arshe baya haifar da komi sai rashin zaman lafiya da nadama.Duk da kasancewar manzon (S. A. W) yace”duk wanda baya kishin iyalinsa bazai ji k’amshin aljannaba” Hakan bai bamu damar mudinga zafafa al’amuraba, wannan abun yazama ruwan dare awannan zamani daga bangaren kowane jinsi ma’ana maza da mata, ina fatan da d’an karamin fad’akarwar da zanyi wasu su amfana.Don Allah wanda yaga kuskure ko shawara k’ofa abud’e take asanarmin, pls adinga comment. Nagode*😘

01

*KHAIR* ce tsaye suna magana itada *Ibrahim* wanda ya kasance immediate elder brother na friend d’inta *khadija mu’az* suna tsaka da magana basu san hawa ba basu san saukaba kawai *Ibrahim* yaji an rufeshi da naushi, sai da aka kaimasa naushi karo na uku gaba d’aya suka ji muryar *YA ADAM* yana jefa mata tambaya lokaci d’aya yana k’ara kaimasa duka yace ” uban waye wannan? ” Tuni hantar cikin *KHAIR* ta kad’a bata iya bashi amsaba sai hawaye daya fara zubowa a idonta, tana d’an karkarwa take bashi hak’uri akan yasaki wuyar rigar *Ibrahim* don tuni ya cakumeshi har idonsa yayi ja duk da ta alak’anta hakan ne da b’acin rai

Yanzu ya sakeshi sai dai bai daina jifansu da wani irin kalloba, take *Ibrahim* ya wuce batare da ya tankawa *Adam* ba wanda darajartane ya hanashi amma batun bacin rai ba’a magana don yaji ba dad’i

Ganin haka yasa *Khair* binshi tana “don Allah *ya Ib* kayi hak’uri, nasan..  ” gani tayi ya k’ara hanzari tada motarshi

Hak’urin da *Khair* ta bawa *Ibrahim* shiya k’ara tunzura *Adam* take ya fizgota ya d’ora mata mari, dafe kuncinta tayi ta fashe da kuka kuma adaidai lokacinne *Hajiya Hassu* ta fito daga gida zata je unguwa, akan idonta akayi marin watsamasa kallo tayi na warning

Take jikin *Adam* yayi sanyi don yasan tsaf zata sab’a masa, nuni tayi masu da su biyota cikin gida, basuyi k’asa agwuiwaba suka bi bayanta, itakam *Khair* har lokacin tana hawaye suna zubowa tana sharesu da yatsunta

   Tsugunne suke gaba d’ayansu kowa ransa ab’ace, baya ita *Khair* da bama marinne ya dametaba illa cin mutumcin *Ibrahim* da yayi, anasa bangaren kuwa kishi ke nuk’urk’usarshi ya za’ayi ta tsaya tana b’arewa wani baki suna hira har tana dariya. Cikin dakakkiyar murya *Hajiya Hassu* ta fara magana ” *Adam* wannan shirmen naka ya fara  yawa koda baku fad’amin meya faruba nasan bai wuce kaganta da wani ba, ba damar kaganta na uzuri da wasu sai ka tsiri tada mata hankali, gaskiya yakamata ayiwa tufkar nan hanci gara azo ayi auren nan kowa ya huta, ke kanki kya sarara *Khairi*, idan yaga yasameki kinzama tasa ai ya san ba’a auran maza biyu daga ranar sai ka kwantar da hankalinka, kasan cewa takace kai kad’ai” jin k’iran sallar da tayine yasa tace “tashi kaje masallaci kuma kadinga yiwa kanka Addu’ar sauk’i” mik’ewa yayi koda yazo fita sai da yaso ya had’a ido da *Khair* ita kuwa tuni ta d’auke kanta don yau kam *Ya Adam* bak’aramin b’atamata rai yayiba, ji take inama *Ya Habib* ta zab’a da tuni ta huta da masifar *KISHINSA*

Bayan fitarshi *Hajiya Hassu* ta umarceta da tayi sallah, ta tashi ta shiga toilet dan d’aura alwala,  ita kuma *Hajiya Hassu* (Mama) ta kira *Safiyya* ta kawowa *Khair* abinci

Bayan *Safiyya* ta kawo mata Abinci, kasa ci tayi don har lokacin bak’aramin damuwa ta shigaba, sau tari takan shiga tunani akan yanayin rayuwar da zatayi da *Ya Adam* bai iya controlling *Kishinsa* ko kad’an, sauk’i d’aya da takeji shine mutane dayawa sukance mata da zarar yaga tazama mallakinsa zai daina damun kansa.Ganin *Khair* tana ta juya spoon batare da tana cin abincin ba yasa *Safiyya* ta sauko daga kan couch d’in da take ta koma kusa da *Khair* ta dafa kafad’arta tace “Sis har yanzu damuwa kike akan abunda *Ya Adam* yayi? Hmnn baikamata ace kin ajiyeshi arankiba har yakai da ya hanaki sukuni, karki manta bayau ya faraba idan da sabo yaci ace yanzu kin saba” tabbas *Khair* tasan da hakan inda sabo yaci ace tayi amman dizgin yayi yawa, tamkar an zugo hawayen da suke idontane su zubo, bata damu da ta shareba ta kalli *Safiyya* tace “Bazaki gane yanda abun nan ya bani haushiba ace wai d’an uwan *Khadija* akayiwa haka, inaga yaci ace *Ya Adam* yadaina irin haka har marina yayi fa” lallashinta *Safiyya* tacigaba dayi, itakam *Khair* ji tayi batason cigaba da maida zancen, jin shigowarshi cikin gidan yasa ta mik’e ta ce “Bari na k’arasa gida inason k’arasa wani Assignment” kallonta tayi ta jijjiga kai tace ” kedai kawai kice kinji ya dawo bari ki tafi saboda baki huceba” basarwa *Khair* tayi tace “Nidai in Mama tafito kice mata sai da safe na tafi” daidai lokacin *Adam* ya bud’e curtain d’in d’akin zai shigo kuma tsaf yaji sallamar da take akunnanshi, hakan ya tabbatar masa bata huce ba, bata damu ba da ganin sa atsaye yana kallonta saima sunkuyar da kanta da tayi don bata son kallon fuskarshi sosai idonsa zai mata illa wajan tursasata ga hucewa, cikin hanzari ta nufi k’ofar ta takura jikinta dan ta wuceshi, shikuma yana sane yak’i matsawa daga wajan, tagane nufinsa amman saita d’aure fuskarta tana fita daga d’akin yace “Hmm dagaske fushin kike da har yakai ki fara gaba dani” cikin hanzari ta wuce don karma tak’ara jin wani furuci daga gareshi, bin bayanta yayi da kallo tare da sakin ajiyar zuciya.

*khair* na shiga gida ta hangi mahaifiyarta na aiki a kitchen, batason tasan me yafaru tayi sauri ta shiga cikin falo da sand’a ta shige d’akinta ta shiga wanka. Ita kuwa *Hajiya Aisha* tasan daga inda *Khair* ta dawo shiyasa bata damu da taganta ba, sai dai taga tana sand’a tanason sanin dalilin hakan

  ……. *Khair* na fitowa daga wanka tasa kayan baccinta red gowan ne har k’asa cotton ta shafa perfumes tare da zira hula net fara k’al, ta janyo wayarta domin kiran *Ibrahim* saida tayi mashi 2 miss calls sannan ta ajiye wayar tare da rafka tagumi tashiga uku yau *Ya Adam* yanaso ya b’ata masu zumuncinsu da su *Khadija*  tajima tana tunane tunane tunowa tayi da randa ya Adam yaje har islamiyyar da take alokacin ya tsinkawa malaminsu mari akanta, da aka tambayeshi sai cewa yayi ai yaga kullum sai ya biyo bayanta idan aka tashi daga makaranta k’arshe saida aka cireta daga islamiyyar, yasa aka dinga gulmarta amakarantar kuma daga ranar ko gaida malamin tayi sai ya d’auke kansa, sai daga  baya ya huce dayaji labarin halin *Adam* donshi da ya d’auka sharrin mata tayi mashi tasa akayi masa hakan

Sai da akayi isha’i  sannan *Adam*  ya dinga kiran *Khair*   ita kuma tak’i dauka, duk da yunwar dayake ji yakasa cin abinci sai jan tsaki yake *Khair* matsala gareta bata ganin son dayake matane yasa yake irin haka, dafe kansa yayi yaja tsuka mata matsala garesu wallahi ya furta afili

  *Khair* kam sai 9 tafito tasan lokacin Ummi tana part d’in mahaifinta, zuwa tayi kitchen ta duba taga akwai ragowar fura ta d’auko ta nufi d’akinta taci sa’a bakowa ayaran gidansu balle sujata da magana. Tana shiga d’akin taga miss calls daga *Ya Ib* bayan na mutumin nata ajiyar zuciya tayi don taji dad’in haka don haka batayi k’asa agwuiwaba tayi call back,  bayan yad’auka ta bashi hak’uri yace karta damu ko k’iran da tamishi bai kusane yasa bai d’aukaba bawai don fushiba ai ya dad’e da sanin *KISHIN* *Adam*

   Bangaren *Adam* baiyi zuciyaba ya cigaba da k’iranta sai yaji busy lokacin tana waya da *Ibrahim* sai yaji wani irin k’unci ya kamashi yaji kamar ya tashi yayi hauka… Kwana yayi yana juye juye sai b’arawon baccine ya d’aukeshi

BY JANNAH JAY

*NAMIJIN KISHI*🙆🏼

By *JANNAH JAY*  (Firdausi S Ahmad)

Wattpad  @ *jannahjay8*

© 2019

02

  “Wannan shirin hakafa naga har wani sauri kake fa Dr” bai juyoba yacigaba da taje sumarshi agaban mirror, bata damuba ta k’ara maimaita maganar, sai daya tabbatar da yagama gyara sumarshi yanda yakeso sannan ya juya ya fuskanceta yace ” madam meye laifi idan nayi sauri karki manta na fad’a maki akwai test da zanyiwa dalibai,  kinga kuwa baikamata na b’ata lokaciba” turb’une fuska tayi tare da magana asigar k’unk’uni tace ” kai dai ka fad’a ko akwai wadda kake son gani” sarai yajita amma ya basar yasan za’ayi hakan domin yagane take-takenta tabbas *Jamila* bazata canza halintaba, tsaki yaja tare da d’aukar wayarshi dake kan gado ya nufi hanyar fita daga d’akin

   ….. Yana shirin bud’e k’ofar motarshi k’irar *Accord* ta k’araso tare da dan washe fuskarta tace ” Adawo lafiya mijina kuma ka kularmin da amanata” shima binta yayi da yak’en yace ” Amin, karki damu wifey don Allah karki manta da zan aiko akarb’amin breakfast d’ina” asanyaye tace “to” ya lura da yanayinta sai dai idan da sabo ya saba, cikin hanzari ya k’arasa makarantar dayake aiki *F. U. D (FEDERAL UNIVERSITY DUTSE) * dake birnin *Dutse Jigawa*  Shi lecturer ne a biology department yanzu haka shine examinar awajan+

  Daga zuwanshi bai kai ga k’arasawa ba ciki ya hangi da Dr Umar daga nesa kuwa *Umar* ya k’ira sunanshi yace ” *Dr Jahun* dama kai nake nema” yana maganar yana k’ara kusantowa inda yake, shikuma sai ya tsaya domin yaji meke tafe dashi

Abangaren *Jamila* jan tsaki tayi tace ” Idan harkar abincine bawanda yakaishi son wahalar da mace, amman ya iya kule-kulen mata.. Mtss” takoma cikin gida tare da shiga kitchen don k’arasa girkin da yanzu ta d’ora, sam bata damu da yin girki kafin mijinta ya fitaba daidai da arzik’in ruwan lipton baya samu daga gareta,tun yana  d’iba ruwan a dispenser har ya koyi had’awa atukunya ya dafa batare da yadamu da nemanta ba, abunda yasani game da ita shine *Jamila* tana *Kishinsa* ba kad’an ba, don bata k’aunar taga mace ta rab’eshi gashi aikinsa na jama’a ne tunda yana fama da Students gashi mata sunfi yawa

  

Bayan gama had’a breakfast d’inta bata jira zuwan mai karb’ar abincin ba, zuciyarta tad’inga mata sak’ar kawai taje dakanta idanma munafurta zaiyi ai zata gani, tuni turnkuk’in kishinta ya sata gasgata zargin cewa wata yakeson gani, d’aci tafara ji yana bin bakinta, tuni ta tuno dawata k’awarta da ta bata labarin yanda *Dr Ahmad Jahun* mjjinta kenan yayi suna a *F. U. D* tab take taji zata iya fito na fito da kowacce shegiyar student da takeson mijinta, bata damu sa yin kwalliyaba ta zari mayafi black ta d’ora kan kayan jikinta ta d’au basket d’an madaidaici ta saka cikin k’aramar honda civic d’inta sai *F.U.D*

  

.. Ya rubuta topic akan whiteboard na hall d’in ya juya ya jefa tambaya ga students d’in sai wata ta bada amsar daya masifar bawa kowa dariya, duk da *Dr Ahmad* ya kasance mai d’aurewa sai da ya dara still  yarinyar tana tsaye bata zaunaba komai akan idon *Jamila* batayo wata wataba ta dire basket d’in akan barandar ta karasa cikin hall d’in kamar kububuwa ta tsinkawa yarinyar mari, kowa hankalinsa yayi kansu take yarinyar ta d’aga hannu zata rama, domin kuwa ita batasan wace hakanba kuma ma bata taba ganintaba akan me zata kyaleta, tsintar tsawarshi sukayo yana cewa ” meye haka *Jamila* wanne irin sakarcine wannan, kizo har makaranta ki mari yariinyar mutane ” jin hakan yasa *Salima* gane matar malamin ce ta zauna akan sit d’in, ita kuwa *Jamila* juyowa tayi don tak’arasa tijararta sai dai bai bata damaba ya fuzgota yayi waje da ita bai saniba yayi fatali da basket d’in sai ga indomie da tagama dafewa fara k’al ba kala ta zubo, sukuwa students sun mik’e suna hango komi ta window kuma suna jiyo maganar *Jamila* tana ” wallahi sai ka k’yaleni naci abu takazar uban wancan shegiyar, shegu masu son mazan mutane” sai kuma tasa kuka tana cewa ” Dama cin amanata kake yiko” har tasa wasy daga wani hall din suna lek’ensu bai mata maganaba sai ma nuni daya mata da ta tafi, yanda taga b’acin ransa dole ta kunna motar tana hawaye bakuma ta damu da ta shareba, wato ita za’a rainawa hankali yazo yana washewa wata banza baki, dama ai angayata sonshi yan mata dayawa suke aschool d’in, tana tafe tana tunane-tunane

…… *Ahmad* shikam ji yayi k’arahen kunyata yayita, ace kamarshi respective Lecturer kuma Dr ace matarshi ta kunyatashi cikin school gaban dalibansa, dafe kansa yayi ya d’an daidaita nutsuwarshi ya koma class d’in, sunyi tsit bamai tari ce masu yayi ya d’aga test d’in sai gobe

STORY CONTINUES BELOW

Yana fita kuwa tuni  students suka shiga gulmar abun, ita kuwa *Salima* ta kifa kanta tana sharar hawaye, takaici ga kunya,  gaskiya ansha da ita mari! Hmmn ta ajiye ajiyar zuciya wallahi ji take inama k’asa ta tsage ta shige, duk maganar da na gefenta ke mata donjin ta bakinta tayi biris yau tasha dizgi agaban mates d’inta duk ajinta da ake gani, anan wasu suka d’inga zagin *Jamila* wasu har cewa suke da sune sai sun rama marin,wasu kuma nacewa daman dole tayi *Kishinsa* ai don ya had’u uwa uba ga ilmi da farin jini, wasu suce bata da hankali, sukuwa mazan ajin sai suka maida abun iskanci suna Allah ya rabasu da mata masu irin halinta sukace daga gani juyashi take agida, ranar dai shiyazama topic of discussion a *F. U. D* wanda basanan ma sai da sukaji zancen agroup

******                  ************

 

Washegari *Adam* tun kafin ya tafi office ya shiga gidansu *Khair* don yasan zai sameta tana taya *Ummi* had’a breakfast, yana shiga falon gidan yasami Ummi ta d’auko teaflask zata wajan Abba ya tsugunna har k’asa ya gaidata, ta amsa tare da tambayarshi lafiyar mutanen gidansu, suna cikn gaisawa *Khair* ta fito da bowl ahannunta d’auke kanta tayi shikuma ya bita da kallo har taje ta ajiye kan dinning, wucewa Ummi tayi don tasan shigowar ta Khairintane, tana b’acewa ganinsa ya matso dinnin arean yace * Baby love ba magana ne? Kinsan bakyau kwana da mutum fa, amman naga har yau baki huce abunda ya faru jiyaba” k’in bashi amsa tayi sai tagaidashi kawai batare da ta d’ora kallonta akanshiba, shikuma yasan halinta indai tayi fushi dama ita bata hayaniya ko fad’in maganganu kawai zata d’auke wutane, sannan bazata kalli fuskarshiba, hak’uri ya sake bata tare da cewa “kinsan sonkine yake kawomin matsanancin kishin wallahi *Khair* ganii nake wani zai k’wacemin ke ki duba baiwar da Allah ya miki” sunkuyar dakanta tayi tariga ta yafe mashi sai tace ” Ya Adam yakamata ka gane cewa da sonka na tashi kuma dashi nagairma, baka buk’atar bayani amma kasani *Khair* takace” yaji nutsuwa amma saida ya tambayeta waye donshi ko fuskarshi bai kulaba sosai tace mashi d’an uwan khadijane Ya Ib, sai yaji kunya don yasan khadija k’warai awajanta har magana suke shida ita ta waya, kallon wristwatch yayi yace bari ya wuce kar ya makara tamashi adawo lafiya, kallonta yayi yace ” ba rakiya kuma? ” tace ” la rufamin asiri kai Ummi ta dawo taga nabar mata girki kan wuta, kuma kaga ai da kunya taga natafi raka ka” murmushi yayi yace ” Allah yakaimu lokacin da za’a ajiye kunyar nan” koda yazo fita sai da yayi kiss ahannunshi ya huro mata, itakuma cike da kunya ta rufe fuskarta

K’arfe goma Mama tashiga gidansu *Khair* ta sami Ummi tana zaune tana yanke farcenta,bayan sun gaisa sai Mama ta bijiro da maganar Auran Adam da Khairi,gaba d’aya ta maida mata wasu cases na kishi da ita kanta Ummi bata san dasuba da, jinjina kai tayi tace “Gaskiya Mama kim yanke shawarar mai kyau tunda dama bai wuci 6 weeks ba tak’are karatun nata inaga gara asaka date na bikin” murmushin jin dad’i Mama tayi tace ” Gaskiya naji dad’in hakan, yanzh kawai Abbannasu zakiyiwa magana sai muji yaushene, ni wannan hayaniya tashi ds takura shiyake bani takaici wallahi” Ummi ta gyad’a kai tace ” Nikuwa gani nake zai daina hakan, da zarar tazama tashi kinsan kowa da kalar kishinsa itama kuma tafita taurin kai, inkasan halin mutum sai kake kiyaye abu ai” sun dad’e suna maida zance akan yaran nasu

*Khadija* bataji abunda *Adam* yayiwa yayantaba domin bai gaya mataba, don haka koda suka had’u aschool da *Khair* bata ga alamar komiba, sai ita ke d’an jin nauyinta anata tunanin taji har saida suka shiga masallacine ta k’ara sakankancewa bata saniba, ana hira ta b’alle masu akan samarinsu Khadija tace “Ya Amin ya kawo kud’ifa” cikin jin dad’i  Khair tace ” kice kema kina hanya, amma gaskiya naji maki dad’i don yakai mijin nunawa sa’a” yamutsa fuska Khadija tayi tace ” Ni yanzu bawani murna nakeba, sai naga kamar baya Sona sosai” jikin mamaki Khair tace ” ke kuwa wacce alama ce tasa kikace haka, baya sonki ya kawo kud’i” kama hannunta Khadija tayi tace ” kwata kwata baya kishina wallahi, kuma kishi alamar sone kiduba kigani ko dawa zai ganni bazai tab’a nuna damuwaba ko wani tashin hankali, rannan fa gani na yayi da A.k amman kawai mik’a mashi hannu yayi suka gaisa ya shiga cikin gida, nasan da *Ya adam* ne da sai ya d’aga hankalinsa, amman shi ko ajikin safa kamar irin baya tsoron wani ya k’wace mashi nine” tsabar yanda maganar tabawa *Khair* mamaki kama baki tayi takewa *Khadija* kallon baki da wayo, sai daga baya taja ajiyar zuciya tace ” Ni dayake haukan kaina cemiki nayi inajin dad’i? Bakison takurane in yagi yawaba, barin in fad’a maki wallahi kishi idan yayi yawa mutum zargi yake komawa yi sannan kuma ke kanki sai kiga idan mutum ya birkice ya koma mami kamar mara hankali, wallhi duk class da wayewar *Ya Adam* yana fara fad’a nake ganin ya birkice, karki so yakasance mai tsananin kishi don wallahi sai kinzo kina dana sani, nifa yanzu indai kinji nayi fad’a dashi to akan kishine rannan ma marina yayi, darajar iyayene yasa ban ajiye sonshiba dakuma k’arfin soyayyar mu” sam *Khadija* tak’i yarda da hakan saboda haka har suka rufe wannan hirar bata yarda da hakan ba

  Dr Ahmad daga cikin school kawai wucewa yayi gidansu sai dai bai shiga cikin gidaba, sai ya tsaya ad’akin k’aninsa Bilal, ya kwanta sai da yad’au lokaci yana tunani sannan baci ya saceshi, yana cikin baccin nan *Jamila* ta k’irashi hakan yasa ya tashi ad’an firgice saboda vibration d’in wayar, kanshi sai da ya sara bai d’agaba sai yayi rejecting k’iran, sannan ya mik’e don tafiya gidan nasa.

….  “Kuttt ni zaiyiwa rejecting waya? Lallai ma wato yana can yana rarrashin wannan yarinyar, wallahi sai na k’untata maka Ahmad” tafad’a tare da fashewa da kuka, ko yunwa bataji duk da cewar kuwa batayi breakfast ba. Yana shiga falon da sallama ta taho da ido jage-jage da hawaye takalleshi tace ” wannan ne kalar tanadin da kwad’aitamin agidan naka? Ashe amanar da su Daddy suka baka haka zakayi wasarere da ita” kallonta ya tsaya yakeyi batare da yayi niyyar bata amsaba, sai kawai ta rushe da kuka mai murya, baya son kukan don haka yayi hanzarin shigewa bedroom d’insa ya shiga toilet.. Ita kuma sai ta bishi da kallo tace ” wato ni bankai matsayin rarrashiba kawai ta d’oru akansa, tana shiga taga ya shige toilet sai ta kwanta akan gado ta d’ora da hawaye

JANNAH JAY…..

*NAMIJIN KISHI*

By *JANNAH JAY* (Firdausi S Ahmad)

Wattpad @ *jannahjay8*

HIKIMAH WRITERS ASSO

© 2019

03

Yad’au kimanin minti 15 acikin toilet din bai fitoba, amma har yafito Jamila na kwance na sharar hawaye kuma tana tanadar kalolin wulak’ancin da zata zuba agidan matukar bai sauko yamata gamsashen lallashiba, yana fitowa d’aure da towel ya bude idonshi alamar mamaki naganin still tana zubarda hawayene a idonta, tunawa yayi da rikici irin na madam d’in tashi sai ya saki fara’a wadda ta k’ara fitowa da asalin kyau da kamala irin tashi ya k’araso kan gadon ya sunkuyo daidai fuskarta yasa hannunshi dake da laima na ruwan wankan ya shafe hawayenda alokaci ya fito daga idonta, batayi k’asa agwuiwaba ta ture hannunshi, bai damuba ya k’ara kaiwa yana shafa fuskarta yace “Sweety da zaki gane zafin da zuciyata take aduk sanda hawayennan ke zuba da kin adanasu, bazan jure ganin wannan kyawawan idonki masu sanyayamin rai suna zubar da hawayeba” harara ta watsa mashi duk da acikin ranta taji dad’i don Jamila aduniya tanason taji ana yaba kyau wani abu nata, yace “Duk hukuncin da zakimin zan iya d’auka amma banda ganinki cikin yanayin damuwa” tad’an fara saukowa tace “bakaine ka tsaya kana mata fara’a ba, kuma kasan bana k’aunar naga kana doguwar mu’amala da kowacce mace aduniya domin kaid’in nawane nikad’ai”sai da gabansa ya fad’i da tafad’i hakan duk da bayaune karo nafarko da take ik’irarin natane d’inba, kamo ta yayi ya had’a da jikinshi yana shashafata in romantic way yana magana yace “Kin dad’e da sanin koni waye amatsayina na lecturer dolene kinga nake dan sakin fuska ga d’alibaina wani lokacin amma badon sun isaba, kinsan ko ak’uruciyata ban yi zarar ‘yan mataba balle yanzu da nakejin nafara iyali… Yak’ara sauke muryarshi cikin salon soyayya yazo daidai saitin kunnanta ya rad’a mata “Ahmad na Jamilane nobody could separate us” ya masifar kashe mata jiki saboda yanda hucin muryarshi ke shiga ta kunnanta tabi duk wani sassa na jijiyoyinta kawai sai ta k’ara k’amk’ameshi, dama Jamila ba wuya jikinta ya saki afagen soyayya duk taurin kanta salo kad’an yake mata ta bada kai, sai da yayi kissing dinta na tsawon minti 3 wanda yayine da salo nadaban da gaba daya takejin kaman bata duniya sannan ya saketa, tayi lak’was akan gadon sai lokacin cikinta yayi k’ugin yunwa, murmushi yayi yace “Sweety kardai zama kikai da yunwa? Tashi ki shirya mufita muci abinci” dad’i kaman ya kasheta cikin nata salon kisisina tace “tsabar rud’ewane naganin kana wa wata fara’a kasan yanda sonka yake acikin zuciyata” kamo hannunta yayi yace “Nadad’e da sanin haka amma tashi ki shirya first qurratu ainiy”yayiwa hannunta peck+

KANO

Iyayensu maza sun zauna sun yanke shawara akan bayan gama exams d’inta da wata d’aya sai ayi bikin, wannan abu ya k’ara saka shauki da soyayyar Khairi azuciyar Adam jiyake kaman tazama tasa, itama anata bangaren hankali kwance take karatunta, tun abunda yafaru da Ya IB wani tashin hankalin bai k’ara faruwaba sai ma zuba soyayyarsu da suke

Tana zaune gaban lecture hall d’insu da handout ahannunta Khadija da Safiyya suka k’araso inda take d’auke da leda ahannunsu, saboda yanda hankalinta ya tattara ga karatun har suka zauna kusa da ita bata saniba sai da Safiyya ta kwace handout d’in sannan ta dago kanta ad’an tsorace, dariya sukayi gaba dayansu sannan Safiyya tace “Gaskiya kidinga rage wannan karatun ko kwakwalwarki zata huta” murmushi tayi tace “Bazaki ganeba yanda nake jin karatun kowanne course ba saboda kinga irin karatun danakesone, so nake jarabawata tayi kyau nasamu entry to university asauki don nazama BMLS (bachelor of medical laboratry science) ” Khadija da take shan coke ta ajiye bottle din tace “Allah ya taimaka amma duk da haka kidinga hutawa, kina da kokarinkifa no need kidinga takurawa brain dinki atleast take a break ko karatun zai fi zama” ajiye handout din tayi cikin handbag dinta tana fito da hannunta wayarta ta fara ringing sunan da tagani kan phone din ne yasa ta saki fara’a, ganin haka suma sukayi murmushi suka shiga hirar wani novel da suka karanta don sunsan Ya Adam ne dole adau lokaci ana magana dashi

Khair kam sai da ta shafe 10 minutes suna magana kafin yace bari ya kyaleta tayi break, bud’e ledan tayi ta dauko coke tafara sha, sunyi mamaki da har suka gama waya Safiyya tace “Yau kuma har angama kenan” murmushi Khair tayi tace “Kyaji dashi sa ido ko” sun jima suna tad’i kafin su koma cikin lecture hall inda ita Safiyya tayi nasu hall d’in ba course d’aya sukeba

F. U. D HOSTEL

Juyi tak’arayi akaro na biyu akan gadonta tare da jan tsaki, budurwar dake kusa da ita tace ” Leemah ashe dama ba bacci kike ba? Ina fata dai ba matar nan ke damunkiba” k’ara jan tsaki tayi tace “bari kawai Nucy Wallahi nakasa daina tunanine yanzu kowa nunani ake ana cewa itace aka mara wai har cewa suke eh wai ai tagane take takena kanshine yasa na mari, tsabar k’arya wasu cewa suke wai ina kiranshine taganeni shiyasa tazo marina kinsan gulmar hostel dai” itama kanta Nucy taji awani room ana hirar kuma dama haka abu yakan kasance ahostel ga yanda yake amma in kaje wani wajan kaji ana maida zancan sai kaji compelete an canzashi, tasowa tayi daga kan gadonta tazo kusada Leemah tace “Koma mene yariga ya faru bakya bukatar damun kanki, kinsan wasu don suna jin haushinkine yasa suke kara zuzuta labarin kasancewar ajinki da yanayin kinfisu komi shiyasa” tashi tayi ta zauna tace ” Nasan da hakan amma wallahi bazan kyaletaba sai tasan wa ta tab’o shegiya ballagaza, wannan in niyar k’wace mijinta akai ai yafi kwatan lolipop ahannun yaro sauk’i dubeta fa ba aji ba tsafta ji wani kazamin indomie da tayi wai ta taho all d way from home takawo mishi” dariya Nucy tayi da ta tuno shigar da Jamila tazo da ita da farar indomie da suka gani tace ” Gaskiyarki amma dai kiyi ahankali karki rura wuta agidan ma’auratan bayan ma haka nanda 3 days zakiji an rufe chapter d’in” minti uku tad’auka tana wani nazari sannan tasaki murmushi tacewa Nucy “Akwai sauran macaronin nan ko?’ gyada mata kai tayi tare da cewa “Sai yanzu da kika huce kenan zakici abinci’ tayi dariya Salima irin matannan ne masu zuciya da daru na shagwaba kasancewarta diya mace kwal da mahaifinta ya haifa yayyenta maza biyu gashi yanada dukiya k’warai, gata ta ko’ina kana ganinta kasan ba’abunda tarasa shiyasa wasu ke kyashinta ahostel ga gayu da kyau

Tana gama cin abincin tayi brush takwanta lokacin k’arfe goma da rabi koda saurayinta ya k’irata saka wayar silent tayi saboda ta k’udurtawa ranta early in the morning zata fita neman details kan Jamila

KANO

Tana kwance cikin shigar kayan bacci riga da wando tana waya da Ya Adam inda yake tambayarta yanayin fenti da takeson yayi mata inda ta bashi zabi kowanne irine, shikuma yayi insisting kan sai yaji zabinta tak’i, shine yace mata to zai nemi k’awarta ta fad’a mashi favorite colour d’inta, bayan sun rufe chapter na gida suka shiga hirar duniya anan ne ya cigaba da fad’a mata yanda yake sonta da matsayinta azuciyarshi da yakejin bazai iya jure rashintaba arayuwarsa, sai da bacci ya fara d’aukarta sukayi sallama

F. U D…

Da safe bayan Salima tayi wanka ta shirya cikin Abaya bak’a sai shek’i take alamar mai tsadace tayi rolling mayafinta, bak’aramin kyau tayiba ta d’au handbag d’inta tare da black shade na Dior ta manna a idonta ta d’auko takalminta coverd amma mai tudu tasa, fuskarta bakomi ta fita,juyi cikin bacci Nucy tayi taganta tana fesa Perfumes tacewa Nucy “Ni nafita amma bazan dad’eba zan dawo’ ta fice Sai Pol science department.. Zama tayi kan gossip chair saboda taga wanda tazo nema bayanan Tun 8 tafito amma taga almost 10 baizoba tafara sarewa, cikin yanga ta taka cikin lecture hall ta tambayi wani tace “Mal Ayuba kuwa zai shigo yau? ‘ Yace mata “Gaskiya yayi tafiya zuwa Cotonou zai kai wajan 3 weeks bai dawo ba’ tamashi godiya ta wuce cafeteria ta sayo chips don batajin girki yai saboda haushin rashin ganin Mal Ayuba. Daf da zata shiga Hostel ta hangi motar Dr Ahmad yana parking shima ya hangeta suka kalli juna sannan at the same time kowa ya d’auke idonshi da sauri ta wuce cikin hostel… Tana tsaki tana cire Abayar jikinta ta kwanta rub da ciki lokacin Nucy ta shigo d’akin itama ta shirya cikin gown na atampa tace “kin dawo kenan ga tea na dafa dama ina tunanin me zamuci” takarasa fad’a tare da janyo ledan takeaway d’in……..

JANNAHJAY….

*NAMIJIN KISHI*

By *JANNAH JAY* (Firdausi S Ahmad)

Wattpad @ *jannahjay8*

HIKIMA  WRITERS ASSO

© 2019

04

Tun bayan abunda yafaru ranar da Salima tasha mari wani tashin hankalj bai k’ara gittawa ba tsakanin Ahmad da Jamila,  yau kimanin kwana goma kenan da wucewar abun, kamar kowanne bayan sati biyu na kowane wata Ahmad yakanje School of healthtechnology dake garin Jahun yimusu lecture, ya shirya cikin shigar suit sai dai ya cire jacket din yabar shirt d’in, bak’aramin kyau yayi ba ya fito daga d’akinshi ya wuce dinning table domin yin breakfast har yazauna akan kujera bata kawo break d’inba duk da cewar goma da rabi tayi,  tasan usually 11 yake barin garin Dutse inda kafin 12 yake isa Jahun amman hakan baisa ta tanadar mashi komiba, sai da yayi minti biyar da fitowa sannan ta fito d’auke da uban tray ahannu sai ka rantse abincin dayawa tayi, bai sha haushiba saida yaga zallar bread ne da tasaka cikin k’wai ta soya, tunowa yayi da uban muryarta da tadinga ce mashi bank’arsaba sai kace wani abinci kala daban daban take, bai nuna mata fushinsa afuskaba sai ma cewa yayi da ” Sannu da aiki sweety’ washe baki tayi tare da gyara zamanta kan d’aya daga kujerun dinning d’in tace “Yawwa My One’ shi ya had’a tea d’inshi yasha tare da d’aukar slice na bread guda d’aya sam baiji dad’iba, shi mutum ne mai girmama breakfast d’inshi saboda sau biyu yake cin abinci arana, hakan yasa zakaga gidanshi baya rasa danginsu irish, plantain, yam da buhun flour saboda adunga sarrafa mashi yanda yakeso….+

Mik’ewa yayi bayan yagama da slice din daya d’auka ya nufi cikjn palourn ya d’auki jakar system d’inshi mai d’auke da 1set nashi da jallabiya da wasu abu da zai iya bukata irisnu brush da perfumes, dake yakan kwana wani lokacin,har tabarshi zai fita da ita sai taji kunya kuma tace “Kawo na tayaka d’auka mana ko yau ba’ason rakiyata? ‘ ta karasa da yanga d’an yak’e yayi yace “Haba wane ni na hana sarauniyar mata rakani koba komai nayi bye bye da wad’annan fararen idon naki’ Aikuwa tuni tayi masa far dasu ita an yabeta, tsabar shirme bataji aranta duk yawan abincin yaci kwaya bataji zata tambayeshi dalilaba bayan tasan yama cikinshi kad’an. Sallama sukayi bayan yamata kalamanda suka sanyaya mata zuciya ya shiga motar sannan takoma cikin gida. Tana komawa ta d’auki wayarta tayi dialling number k’awarta Samira    tana d’agawa ko gaisawa bata tsaya sunyiba tace “Yaushe zaki shigone mu cafcafke yariga yatafi don Allah karkice sai bayan Azahar don zai iya shigowar Yamma fa” daga can bangaren Samira ta amsa tace “Ai nariga nafito nanda minti goma zaki iya ganina cikin gidanki inaso naji labarin ai’ dariya sukai gaba d’aya sannan takoma dinning taciga da yin break d’inta

Ko minti goman bata cikaba sai taji sallamarta cikin  fara’a ta amsa inda ita Samiran tayi cilli da handbag d’inta da veil kan Sofa ta zauna tace “Zokiban nasha Uwargida kuma amarya agidan Dr Ahmad Jahun’ kai wannan maganar da Samira ta fad’a tayi mata zak’i k’warai cikin yauk’i ta taso ta taho cikin parlourn dake dinning d’in na daga dan tudu da zai sadaka da kitchen  tace “Ai dole abaki labari kinga wutar da na bud’e mashi cikin school har marin wata yarinya nayi nasan hakan da nayi dole ya tsorata wasu su kyalemin miji, gara da Allah yasa kika fad’amin da wuri ai akan sonshi da ake, tunda nayi hakan bakiga lallab’a dayakemin ba’ tafawa sukayi Samira tace “Kai k’awata kin bada wuta kin bada show wallahi, gaskiya kin burge to amma mai kika tanadawa yaran healthtech Jahun? Kodan tunda kika gama da gogaggun yan Jami’ar kinsha round k’awata’ nan suka cigaba da hira wanda rabi alwashine kan bazasu bar mazansu su k’ara aureba ko ta halin k’ak’a. Suna tsakiyar hirane Farida childhood friend d’in Jamila tazo, bayan gaisawa suka cigaba da hira tare, kalar kalamansu ne ya bata mamaki  inda tadinga basu shawara akan sassautawa kansu k’arshe sai taga zai iya zama masu rikici tayi masu sallama, dama biyowa tayi don su gaisa dake ta shiga Quaters d’in su Jamilane wajan yayarta… Sun dad’e suna hirar  har 5 na yamma suna tare

Ahmad dayaga yagama komi akan lokaci shiga yayi gidan yayar mahaifinshi ya karbo nono da fura sai kwan zabi dake ba laifi Jahun suna dashi, yama Jamila text akan zai dawo gida wurin magriba Insha Allah,   duk da kuwa har lokacin bata kirashiba balle taji ko ya sauka lafiya. Tana tsakiyar yin sallama da Samira taji text d’in taja tsaki  tace ” Nabani yanzu sai nayi girki? Ohh kash’ dake ita da Samira  kayan k’walama suka ci da rana sai awara da suka sayo mak’ot, don Jamila malalaciyace bawai iyawane batayiba tsabar k’iwane da son hira yahanata yi, gyara zaman mayafinta Samira tayi tace ” Aikuwa ya kamata kiyi masa koda simple spaghettine da stew, karki manta da d’inkinmu pls “ta amsa mata kan zata fita jibi ta amso masu zata shigo Estate d’innasu takawo mata

KANO

Bangaren iyaye kam sai shirin lefe suke inda Ahamd ya k’ara kasawa ya tsare akan Khairi gani yake tazama tasa, dama can da dokoki kanta dayasa yanzu sai ya k’arasu, itakuma gudun fitina da hak’uri irin nata yasa take kiyayewa. Kamar yanda yakan kasance duk week end ita da Safiyya sukanje wani islamiyya da tayi fice akan karatun Fiqhu da Hadith wanda mafi Aksarin matan ciki masu Aurene, sun je Islamiyyar sun tashi ahanyarsu na dawowa gida suna tafe da manyan hijabansu har k’asa sukazo wucewa ta wajan majalisar samarin da ke kan corner na shiga layinsu, wani saurayi da bai dad’e da dawowa unguwar ba ya hangi Khairi inda take yaji bazai iya shiruba duba da baiwar diri da Allah  ya mata, suna d’an wucewa daga inda samarin suke ya tab’o na kusa dashi yace “Baba kaga wata Haja anan la’ilaha illallhau Allah yayi halitta anan, bala’i!!!! ‘ ya fad’a tare da murza hannunsa bai lura da shirun da nagefen nasa yayiba ya cigaba da zuba ” Kaiiii wallahi wannan za’a huta da ita kaga yanda Ukwunta ya cika fammmm!!!…  Kafin ya k’arasa yaji sauk’ar naushi abakinsa sauran samarin suka tashi agigice duka yakeji tako’ina gashi bamai niyyar k’watarsa, tsabar zafin nama irin na Adam ko damar kare fuska Saurayin bai samu damar yiba, kan kace kwabo yayi jina jina dashi, sai ga saurayin ya zub’e ak’asa yana don Allah kayi hak’uri ya juya ya kalli abokin dayake bawa labarin yana “Batozi don Allah kubashi hak’uri wallahi bansan k’anwarsa bace’ Adam kuwa saboda tsananin k’ulewar da yayine yasa ko magana yakasayi, yanzu jikinsa har karkarwa yake saboda b’acin rai, khairin tasa ce ake irgawa diri har ana cewa cika fam wai harda cewa za’a huta da ita, wani abune yazo ya soki zuciyarsa  da sai da ya duk’a k’asa, hakanne yabawa su Batozi damar k’watar gwaska ahannun Adam, sai Batozi  yace ” Kaima aboki baikamata kake maganganun kan siffar mace ba bakyau, irin haka ai sai ayi zaton kai din mabiyin matane, idan yimaka tayi ai gara ka bita ka nemi soyayyar ta’ Adam dayaji k’arshen statement na Batozi sai abun yabashi haushi ya cakumo Batozi yace ” kai dak’ik’in ina ne da zaka bashi shawara akan ya nemi matar wani, ko so kake ka nunamin duk zaman ka a unguwar nan bakasan Khairi ce zan auraba’ cikin yanayin tsoro Batozi yace “Wallahi mu duka anan muna kallon ai dake ku ‘yan uwane k’anwarkace kurum amma kayi hak’uri yallab’ai’ sakinshi yayi yace bari nakira commisioner of police azo anan koya muku hankali don inaga nan gaba zaku fara bin matane kuna lalatawa, ai tuni wani asauran samarin wajan yayi hanyar guduwa Adam ya buga masa tsawa yace “tsaya anan wallahi nagane ka ko tafiya kayi sai an kamoka agidanku’ rok’onshi sukai tayi sannan ya k’yalesu, daman suna shayinsa kasancewar shan kamshi da kama girma irin na Adam banda gaisuwa ba abunda ke hadashi dasu, yanzuma wani yazo nema wanda gidansu jikin inda ake kafa majalisarne yasa yaji komi…. Adam yana tafiya sauran samarin sukayi kan gwaska da masifa yajamasu bala’i dole yadaina zama awajan, shidai Batozi k’ok’ari yayi ya kaishi chemist aka gyara masa ciwukan da Adam yaji masa….

Adam duk da bala’in da yayi baisa ya dawo normal ba, koda ya koma gida kwantawa yayi yana ta tunanin yanda zai kawo k’arshen wani yake tanka Khairinsa, tabbas ba yau aka faraba domin duk wanda ya kalleta yasan tanada jiki maikyau duk da afanni kyau Safiyya tafita, ammafa in dirine zaka  jera mata dayawa bakaga mai irin nataba, baiwar da Allah yamata kenan, tunowa yayi da furucin gwaska na za’a huta da ita, dafe zuciyarsa yayi kai gaskiya gayen nan yacuceni Allah ya isa, ya muskuta ya d’au wayarsa dole na kira Khairi…

Khairi da suka jima da shiga gida tana zaune tana cin sakwara cikin  farin ciki don tanasonta sosai taga wayarshi, bayan ta d’auka tace “Salamu Alaikum’ dakyar ya amsa yace ” Babyluv wato fad’an da namiki kan canza tafiyarki bakiyiba  ko, gashinan kinsa wani yana neman ya kasheni, wallahi bana iya jure jin wani yana yabonki koda kuwa halinkine balle halittarki’  shiru tayi ita batasan mai ya faruba kuma dayake maganar tafiya ya zatayi da nature d’inta, cikin sanyinta tace ” Yaya meye ya faru kuma? Wazai kashemin kai?’ sai da ya had’iyi miyau me d’aci yace “Dazu kun dawo daga Islamiyya wani d’an iska yana ta zuzuta jikinki, wallahi banda sun bani baki da sai an daureshi na shekara da horo mai tsanani, shiyasa nace ki canza tafiyarki, za’a canzo miki hijaban Islamiyyar’ shiru tayi aranta tana jinjina abun kai itakam Ya Adam har tsoro yake bata wannan wane irin abune, haba dole yayi hak’uri duk munin mace sai an tankata balle amajalisa, kuma ma ai ba ita kad’aice mace Aduniyaba, amma don takwantar masa da hankali tace “To kayi hakan kuma zaiyi k’ok’ari na gyara, amma don Allah kacire damuwar nan bakaji yanda muryarka tayiba, banason jinka adamuwa pls, nasan k’ila bakaci abinci ba i cant forgive myself’ kwarai bayajin yunwa amma yanzu da ta marairaice mishi akan yaci yaji wasai donshi yanason shagwaba, yace “Shikenan zanci yanzu’ tace “promise? ‘Yace “Yeah, promise babyluv d’ina nikad’ai’ sai da ta danne dariyarta tace “Bye’…

JANNAH JAY… 

*NAMIJIN KISHI*

By *JANNAH JAY* (Firdausi S Ahmad )

Wattpad @ *jannahjay8*

HIKIMA WRITERS ASSO

© 2019

05

Cikin hukuncin Allah komi yana tafiya daidai sai d’an Abubuwa da baza’a rasaba, abangaren mu’amala Khairi tana tsananin kiyayewa ganin komi bai wakana tsakaninta da Ya Adam ba, hakan ya k’ara bawa iyayensu farin ciki da damar warewa naganin an tsara kayan lefe da sauran kayan Al’ada da akeyi, basuyi la’akari da kusancinsu ba. An kai kefe Akwati na goma 2 set, kuma ansaka kaya masu kyau daidai gwargwado, hakan ba abun mamaki bane in akayi la’akari da Adam shine d’a nafari kuma mahaifinsa yana da kud’i ba laifi.

DUTSE….

Hall d’in cike yake taf da d’alibai abun saida ya bawa Dr Ahmad dariya, don zai iya rantsewa tunda semester yakama basu taba kaiwa kaman hakan ba, bakomine ya jawo cikarsu ba illa test da yace zaimasu wanda yayi ik’irarin shine C. A mafi tsokar maki, cikin nutsuwa yake zagaya raws na hall d’in tare da taimakon malamai guda uku saboda baison satar amsa ko kad’an, ko’ina in ka waiga zakaga kowa ya nutsu yana rubuta abunda yasani, yana cikin  tafiya yazo daidai inda Salima take ya kalleta ya basar amma yayi recalling fuskarta saboda marin da tasha, ya wuce tare da tsayawa can kusa da board, yana tsaye wayarshi tayi k’ara Jamila ce fita yayi varendar bayan yad’aga take sanar mashi zata gida dubu gidan Samira yace mata shikenan amma kar ta dad’e,  saboda yana azumi ya fad’a mata kalan abincin dayakeso tamashi.+

KANO

Adam yana zaune tare da abokansa AK da Sabeer suna hirar duniya suna tsaka da hirar wayar AK tayi k’ara fad’ad’a fara’arshi yayi yace “To guys ina ga nizan wuce wifey na jirana’ hararar wasa Adam yamashi yace “Ok gorin Aure akeso ayimanako, to muma munkusa hawa network d’in ‘ cikin zolaya yace ” Eh sai ku bari idan kunzo wajan sai mud’ora amma yanzu dai bazaku ganeba, bari nayi sauri nak’arasa’ Dariya  Sabeer yayi yace “Adam shareshi kawai yaushene wai yabar gwaurancinne, musai kagama d’okinka zamu shigo namu lokacin zakaga namu salon’ Dariya yayi mai sauto yace “Kunga bari na kyaleku karku janyo wifey tagaji da jirana, bari na ratsa tacan wajan.. ‘Sai suka tafa da Adam yace “Kana burgeni ‘ Bayan tafiyar AK tafiya sukayi zuwa gidansu Adam,  dake da suna gidan da Adam yagina ne sunje ganin yan gyare gyare da ake, don ya dad’e dayinshi wearing da chandeliers da sauran kyale kyalene baiyiba sai yanzu da aka tsaida rana

DUTSE

Jamila tunda tasa k’afa ta tafi gidan Samira bata dawoba sai wurin k’arfe shida, kasancewar lokacin ba Azumi bane baifi saura minti 38 asha ruwaba, shiyasa takarbo jallop na macaroni awajan Samira da niyyar in tazo kawai tea zata dafa mashi tayi frying egg kawai, tana shiga saboda sauri ta manta bata canza macaronin daga flask d’in samiraba tayi sauri ta shiga kitchen ta d’ora tea d’in, tare da fasa k’wai, murnarta d’aya bataga motarshi  ba tasan bai dawoba k’ila yana gidansu…. Bayan sallar magriba  taga anyi parking motarshi amma bashine ya fito ba Abokinshi ne Dr Umar yana parking motar taga Ahmad ya shigo da jallabiya ajikinshi alamun daga masallaci yake, ya karbi key shi Umar ya fita…

Yana zaune kan carpet dake cikin parlourn yana cin dabino tazo tace “My one anan zakaci ko zaka hau table’ kallonta yayk na seconds sannan yace “kawoshi nan nagajine sosai’ bayan ta ajiyesu ta zuba mashi komi cikin plate bai ce mata cikankiba sai dai daga tea din da kwan bai taba macaronin ba, kallonshi tayi tace “My One mai yafaru naga kak’i cin Abincin?’ sai da yayi kaman bazaiyi maganaba, hakan yasa tafara shan jinin jikinta tak’ara kallon fuskarshi taga b’acin rai ya bayyana kuma ya d’aureta tamau, sai ta sunkuyar dakanta yace “Jamila dame narageki agidannan? Wane hakkine naki bana saukewa? Wane irin d’abi’u ne nakeyi da bakiso? ‘Bata da bakin magana don tasan yau babinta ya bud’e yacigaba da magana ” Amma ni ban isa na umarci abu kiyiba, duk irin kauda kai da nake kan laifukan da kikemin, kina sane da cewa atsawon shekara uku da mukayi a aure watan farko za’a d’auke da kika kiyayi cikina amma sauran duk ashiririce kike komi, bayan haka tun shigowarki yau naga komi wannan abincin bake kika dafaba, har takai ki tafi yawan nuna tsiya gidan kawarki salon ace bana ajiye abinci komi? Nayi azumi don kawai kiyi frying yam and sauce kiki haba, to indai laifi nake maki ki fad’amin zan kiyaye nima don ki fara kyautatamin’ Ranshi yakai k’ololuwar b’aci akan macaronjn nan, ganin in yacigaba da zama zai iya furucin da bai daceba ya tashi tsam ya shige bedroom d’inshi.. Takasa motsi yau ya amayar mata fa don bai fiya nuna yaji haushin abu ba,tashi tayi ta kama zarya afalkn kafin ta shige kitchen tayi abunda ya umarta, yanajin motsinta kitchen sanda zai fita zuwa  sallar Isha’ee.. Bayan ya dawo ya shige d’aki ta biyoshi da abinci, yi yayo kaman bai gantaba, tadinga bashi hak’uri tace ai batajin dadine yasa bata dawoba, duk da bai gamsuba haka ya kyaleta… Wannan kenan

Khairi sun fara final exams karatu basauk’i. Abangaren Adam kuwa iyakar k’okari yanayi naganin tayi karatu don ta cimma burinta, ko wani littafi yagani daya danganci lab sai ya kawo mata, dama haka Adam yake indai ta fannin bajintane da bautawa masoyi to tabbas za’a yaba mashi, kuma saboda haka ya rage yawan time nasu na wayar dare, hakan yana k’ara mashi k’ima a idonta da na mahaifanta don suna ganin lallaai d’iyarsu tayi miji nagari.

Yana tafe ahanyarshi na dawo daga office yayi deciding bari ya shiga super market ya saya mata chocolates saboda takejin dadin karatu, wasu psychologist sun yi suggesting yin hakan gamai karatu saboda sharrin bacci, tsayawa yayi yayi parking motarshi ya shiga, ya had’ota mata su tare a different biscuits da wafers dadai sauransu, har yagama d’iba ya tuno wani lokacin idan yasayowa Khair Abu Safiyya kan zolayeshi da mata tafi k’anwa, murmushi yayi tare da k’aro quantity na kayan, yabiya ya nufi gida, tun amota ya rabasu, sai da shiga gida yayi parking sannan ya fito ya nufi gidansu Khairi dake lokacin past 4 ne, yak’irata awaya yaji she’s available sannan yashiga, kaishi d’akin Ya Muhsin tayi takai mashi kunun aya favorite d’inshi da dambun nama da cake da bata d’ade dagama yiwa Abbanta ba, cikin murmushi yake tsokanan ta kan duk ta rame saboda karatu, tace  “Ashe kaima kabi sahun su Khadija sunce nafiya nacin karatu dama medicine nake zaifi’ kallonta yayi cike da k’auna yace “Yanada kyau kike bawa brain d’inki hutu’ sun d’an jima suna hira sannan dayaga six tayi ya ajiye mata ledar ya mata sallama, tamashi godiya sosai har saida yace bande ina nesa dake da kinsha rank’washi.

Yau yakama saturday tana zaune acikin  d’akinta ita kad’ai tana karatu,  Khalid k’aninta yashigo yace “Ana sallama da ita awaje yanzu malam ilya yashigo ya fad’a’ cikjn mamaki tace “Sallama kuma? To amma waye wannan?  Hmnn to ko network ne babu yasa aka kasa samuna, k’ila class rep ne zai bani book d’in nan’ Duk aranta take zancen tashi tayi ta zira hijab akan gown dake jikinta… Tana fitowa k’ofar gida taga Malam yahuza, mamaki kasa b’oyuwa yayi afuskarta ta gaidashi tace “Malam bismillah mushiga daga ciki’ yace ” A’a fa nanma Alhamdulillah,dama bawani jimawa zanyiba, wani babban Al’amarine yake tafe dani Ummulkhairi wato nadad’e ina k’aunarki da Aure sai dai ina ta tunanin kallon da zakiyiwa abun, k’ila kice namaki tsufa ganin kunkusa gama exams  naga yakamata nasanar miki’Wani abune yazo ya tsayawa Khairi azuciya wannan wane irin zubarda kaine hakan, gyara muryarshi yayi yace “Bakice komiba’ buga get sukaji anyi suka dago arazane Adam ne yace “Me kake tunanin matar aure zatace maka, munafiki irinkune masu lalata yara ajami’a ko, lallai yakamata Ministry of Education susan da irin abunnan, ko kunya bakajiba yarinyar da ka haifa kake fad’awa kalamai’ Malam Yahuza shiru yayi Adam yacigaba “Fad’amin yataba bijiro miki da maganar banza?’ Shiru Khairi tayi ganin inta kyale Adam zai iya jaza mata masifa aschool yasa tace “Baida mugun halifa kawai cewa yayi yanasona yanzu kuma tunda yaji Aure zanyi ai shikenan’Ta juya ga Malam dayayi shiru yakasa magana tace “Malam kayi hak’uri yanzu haka bai wuci sati biyarba za’ayi bikina wannan shine wanda zan aura’ murmushi yak’e yayi ya bawa Adam hak’uri yana jijjiga kai.. Cikin huci Adam ya tareshi dazai wuce yace “Ina Baba ai ba yanzune lokacin da zaka tafi ba sai ka fad’i k’udurinka kan yarinyarnan wallahi in ba haka ba wannan maganar sai anje har makaranta ko Ministry nayi reporting adau mataki kanka, in ta kama amaidakai makarantar maza’ hakuri Khairi tafawa bawa Ya Adam inda ya daka mata tsawa yace ta shige gida Malam Yahuza ya silale ya gudu… Cikin Kuka Khair tashiga gida tana cewa tashiga uku kar Ya Adam yajazamata matsala aresult dinta don Malam yahuza sune manya ….

JANNAH JAY

*NAMIJIN KISHI*

By *JANNAH JAY*

Wattpad @ *jannahjay8*

HIKIMA WRITERS ASSO

© 2019

06

Kuka sosai Khairi take sanda tashiga gida, bayan gama fad’an ya biyo bayanta cikin gida, kafin nan mahaifiyarta ta tasata da tambayoyi amma tsabar kuka takasa maida mata yanda abun ya faru, sai gashi ya shigo main parlour na gidan, cikin kallon tuhuma Ummi ta kalleshi tace “Adam ko da kai wani abu ya had’aku?’ Sai da ya saita nutsuwarshi yace “Kwarai kuwa amma ni nakasa gane mene yasata kuka, saboda solution nasama mata, ta taba baki labarin wani malaminsu dake  bibiyarta?’ Dan zaro ido Ummi ido tayi bayan fad’uwar gaba da ta ziyarceta tace “Bibiya kaman yaya? Ni bamu taba maganar wani da itaba, amma  yimin bayani yanda zan gane’ Kallonsu gaba d’aya take da ido kawai, shikuma  sai da ya kalleta yace “Ummi yanzu naganshi wallahi tsohone yayi Abba (mahaifin Khairi ) ahaife amma yazauna yana tsara mata wasu zantuka, wannan kad’ai ya isa asan ba Allah ranshi waya sani ko irin munafikan lecturer d’in nan ne masu son lalata yara’ Take hankalin Ummi ya tashi tace “Ke  khairi kinyiwa mutane shiru kimana bayani’ sai da taja zuciya tace “Nifa bawani maganar banza daya tab’amin kar ad’au alhakinsa, bai taba mun doguwar maganaba in aka wuce cikin class ayi tambaya kawai, amma Ya Adam baka fuskanci maganar nan daidai ba, gashinan yanzu kamashi wulak’anci zaka jami, kamanta result dina zai iya samin matsala kuma.. .. Kawai sai tak’ara saka kuka, shiru Ummi tayi shikuma Adam ya fad’awa Ummi exactly abunda yaji, anan Ummi takwantarwa da duka su biyun hankali, inda ta nunawa Adam zai iya yiwuwa bai zo da niyyar cutarwaba amma tunda yariga yace mashi Aure zatayi tana tunanin maganar ta wuce, ita kuma Ummi tace mata karta damu indai dagaske sonta yake bazai d’au abunda Adam yayiba against her result, alokacin ta nuna komi ya wuce mata amma aranta ba haka bane, don sosai tasaka abun aranta tana jin tsoro….+

Malam Yahuza bak’aramin jin kunya yayiba kuma baiga laifin Adam ba, kowaye zai iya kawo negetive thoughts idan akayi la’akari da ansaba samun issues a Universities, amma bakomai sai dai zuciyarshi taji ba d’adi mummunan zaton da akayi masa, shi mutum mai k’imane kuma yanada kamun kai ajiyar zuciya ya aje tare da furta “Bazan k’ara son kowacce yarinya ba gara na nemi bazawara zai fi’.

DUTSE..

Dr Ahmad ya bawa Class Rep papers yayi sharing ma students, sai dai kowa da yayi yasamu banda Salima,  hankalinta in yayi dubu ya tashi, wane irin masifa ne wannan kenan zata goya carryover tashiga level 4,ina bazata zaunaba, tunkarar Rep tayi da maganar yace zai wa Dr Ahmad magana zuwa gobe, duk da tasa hope sai da ta share k’walla…

Jamila cikin shigar da skirt na atampa da suka amshi jikinta ke kai kawo tana ajiyewa Ahmad abinci a dinning, sai murmushi yake kwana biyu suna d’asawa shida ita komi zam zam, tun ranar daya bud’e mata ido yayi mata fad’a ta saitu, fatansa d’aya ta d’ore serving d’inshi tayi tare da komawa gefe ta zauna,yanda ya saba yi haka yayi mata godiya, sannan yafara cin abinci… Yana tsaka da cin abincin wayarshi tad’au k’ara Jamila ta tashi ta d’auko masa yace “waye ke k’ira? ‘ tace “Rep 3’ yace bani wayar ta mik’a masa, bayan sun gaisa sai Rep yamashi akan wata tayi test bata samu paper d’inta ba ko zai duba record na scores , yace bamatsala zai duba amma yamashi text na admission no da sunanta.

Yana zaune kan kujera ita kuma ta d’ora kanta kan cinyarshi tana game awayarta suna d’an hira jefi jefi abun sha’awa, irin wannan rayuwar yake so agidansa gashi ya fara samu, murmushi yayi tare da shafa fuskarta itama tamaida masa martani, sallama mai gadi yayi yace ana nemansa ak’ofar gida ya fita. Yana dawowa ya tuna da maganar paper nan ya shiga d’akinsa ya duba yaga still ba sunan abun yabashi mamaki, amma ko meye zai ga fuskar yagani ko tayi sai yasan yanda zaiyi da ita…

KANO

Kwana Khairi tayi tana juye juye dama matsalar ta kenan ga tsoro ga saka abu arai, da safe suna fita driver na jansu ita da Safiyya ta labarta mata abunda ya faru amarairaice tace “Don Allah meye shawara wallahi tsoro  nake ji kinga sune manyan dake kula da exams na department d’inmu’ kama hannunta tayi tace “Ina ganin kawai Addu’a zakiyi sannan muje mu bashi hak’uri har Office, amma ki kwantar da hankalinki, wallahi kina k’ok’ari da Ya Adam’ Dan yak’e tayi tace “Shikenan sai mun shiga dai tukun, anya zai barni na dora karatuna kuwa naga abun nashi ya fara yawa’ da hirar dai suka shiga school d’in, dake sai 11 zasuyi Exams sai suka samu wuri suke kara karatu, suna wajan Khadija ta kira Khairi taji inda suke, bayan tazo ta samesune Safiyya ta tafi wajan course mates dinta  suyi discussion

Tagama mata labarin abunda yafaru khadija tace “Gaskiyane shawarar Safiyya tayi yanzu yau yakamata muje musameshi mubashi hak’uri, amma kidaina ganin laifinshi don Allah yazaiyine kinsan Allah ya haliccemu mabanbanta maybe nashi yanada zafi komi zai wuce indai kunyi Aure Insha Allah’ Ajiyar zuciya Khairi tayi tace “In anyi aure kikace anya kuwa nifa wallahi banda karna maida hannun agogo baya da anfasa bikinmu an bari saina gama Degree d’ina, ina ganin kaman zai hanani’ jijjiga kai Khadija  tayi tace “Gaskiya karma kisake wannan tunanin shifa aure lokacine tunda naki yazo bai kamata kike wannan tunaninba’  Khadijace taita kwantar mata da hankali sannan ta samu relief, shikuwa oga kwata kwata Adam sai da ya tsara message mai kyau ya tura mata kafin tashiga exam tare da wishes, bazatace bataji  dadiba sai dai ta mashi fatan Allah yasa yarage hali da tayi masa..

Suna gama paper suka nufi office d’in Malam Yahuza tin daga yanayin tarb’ar daya musu suka fara samun nutsuwa suka bashi hak’uri anan yanuna musu bakomi kuma yana musu fatan Alkhairi ita da Adam sannan kuma abashi hak’uri, sosai sukaji dad’i cikin walwala suka koma gidajensu..

F. U. D

Yana zaune a office d’insa tare da Rep akan maganar papern Salima, cewa yayi ya nemo mashi d’alibar yaga face d’inta ko zai ganeta indai tabbas tayi zai sake mata wata, tunda baiga paper dinba kila ahad’awa aka yada mata nata,ya fita yaje ya kirata, cikin nutsuwa ta shiga office din tana sanye da laffaya da ta nade jikinta, sai da ya d’aure fuskarshi sannan yace “ke tsakaninki da Allah kinyi test d’innan?’ yanayinta na shagwaba yasa bawuya tafara hawaye rau rau tayi da idonta tace “Tsakanina da Allah nayi koda za’a tambayi wasu cikin class din’ Yasan yaganta ranar kawai baiso ya nuna mata yasan da zamanta class dinne don dama haka yake akan kowacce mace cikin school d’in, yace”Shikenan ya wuce then since you wrote my last paper u must be ready to answer any questions” ana cikin office d’in yabata paper yace taja gefe tayi yamata wasu questions nadaban, yabata lokaci..

Suna tafe cikin mota itada Samira zasu Fatara estate sai Samira tace “Kinga na tuno ma k’awata danake fad’a maki mai saida tsumi yar Sokoto tabawa kanwarta sako dake nan cikin F. U. D hostel ko zamu shiga mu karba, shikenan ma mun huta’ Sun gama yanke shawara suka nufi cikin F. U. D. Bayan sun shiga sai Jamila taga fitowar Dr daga office sai dai shi baigantaba dake ya juya  bayanshine,tacewa Samira “Ajiyeni nan naje nayi magana dashi kafin nan kingama’

Yakoma cikin office d’in kenan ya d’an sunkuya yana had’a wasu papers kawai yaga tashigo ba sallama wanda tana sane tak’iyi, saboda tayi bazata ko zata kamashi da wata Cak ya tsaya tare da k’ura mata ido cike da mamaki inda ita kuma ta cigaba da wulga idanuwanta ta ko’ina acikin office d’in tanayi tana k’ara takowa cikin office d’in.. ….

Firdausi S Ahmad..

*NAMIJIN KISHI*

By *JANNAH JAY*

Wattpad @ *jannahjay8*

HIKIMA WRITERS ASSO

© 2019

07

Ajiyar zuciya tayi da taga bakowa ta k’irkiro murmushi tace “Nayi suprising d’in ka ko? Hmnn munzo amsar sak’one yasa nazo naga ko an tarawa My one aiki banso awahalar min dakai kasan’ murmushi shima yayi duk da aransa tabashi mamaki yasan harda zargi yasa tashigo, yace “As you can see bawani aiki sosai yau, kungama da F. E ne ko sai yanzu zaku tafi?’ zama tayi tace “A’a yanzu zamu’ wayarta tayo k’ara tana daukar wayar taga Samirace tace mashi “Bari na wuce My One sai mundawo’ yace “okk ki kulamin da kanki’

Tana fita ya jijjiga kai yace “Jamila kenan Allah ya taimakeni dataga ana test da ya zanyi? duka yaushe yarinyar nan tafita a office lallai Allah ya ceceni da mitar ta. ‘ Yayi dariya..  Daya tashi daga Aiki gidansu ya wuce..

Ana ta preparation agidansu Khairi na saye sayen bikinta don yau mahaifiyarta suna cikin kasuwa sayan kayan kitchen tunda biki sai k’ara matsowa yake,  saura wata daya da kwana biyu dan jibi zasu gama exam d’insu, Khairi na zaune suna hira ita da Safiyya agidansu suna cin wainar fulawa da yaji Ya Adam yayi sallama inda take Khairi ta ware veil da ta d’aura zuwa yafe suka amsa gaba d’ayansu, ya shigo ya zauna suka cigaba da hira tare, duk sabonda sukayi amma saboda soyayya ta shiga yasa Khairi taji ta takura, ta d’auke hannunta,  Safiyya ce ta sako Adam cikin hirar tasu tace “Ya Adam wane events kake ganin za’a fara ne tsakanin cocktail da dinner?’ Wata harara ya watsa mata yace “Dinner dai irin wadda mukai abikin A. K? Hmnnn wakike tunanin zan bari tasaka irin wannan gown dake fidda jiki agaban uban maza da mutane? Karma kusa aranku za’ayi irin wannan don bazan daukaba’ Sakin baki tayi kafin tace “Haba Ya Adam kenan salam zamuyi bikin namu, kana nufin banda kamu da iyaye ba abunda zamuyi’ yace “Fadar waye hakan, ke ni kamun ma don ba yanda zanyine fa, amma baki ganin yanayin kayan da ake sawa adinner duk afidda jiki ga maza tako’ina anan wani zaizo dole yayi pics da amarya duk ya damuk’ar maka mata’ Tace “Haba agabanka za’ayi kuma kasan muma bazamuyishi ba tunaniba shiga na mutumci za’a mata, ai sai ka bari za’a je kusa da itama ayi pics kamanta tare zaku zauna kan stage’ Duk yanda Safiyya taso ya fuskanta yak’i shidaga kamu babu wani, duk events mai maza baiso amma idan iya matane shidakanshi zai  biya kud’i suyi, ita kuwa Khairi ko tak batace ba dama tasan za’ayi hakan.. Adam kenan+

Sungama exams d’insu cikin nasara yanzu kuma sun maida akalarsu ga shirin biki, yau suna can gidan kakannin su Adam, zasuyi kwana biyu, sun jima basu zauna da cousins dinsu ba, yanzu suna zaune cikin makeken falon Hajiya Inna wato mahaifiyar Baban Adam tare dasu Kabir da Abbaty suna hira da su Jidda duka rabin hirar ta ta’allak’ane ga shirin bikin nasu, kowa yana da buri akan hakan domin Khairi mutumce mai warewa da kowa sosaitaimakeni dataga ana test da ya zanyi? duka yaushe yarinyar nan tafita a office lallai Allah ya ceceni da mitar ta’ Yana tashi wucewa gidansu yayi

Sungama exams d’insu cikin nasara yanzu kuma sun maida akalarsu ga shirin biki, yau suna can gidan kakannin su Adam, zasuyi kwana biyu, sun jima basu zauna da cousins dinsu ba, yanzu suna zaune cikin makeken falon Hajiya Inna wato mahaifiyar Baban Adam tarr dasu Kabir da Abbaty suna hira da su Jidda duka rabin hirar ta ta’allak’ane ga shirin bikin nasu, kowa yana da buri akan hakan domin Khairi mutumce mai warewa da kowa sosai Sannan hardly kaji anyi fad’a da ita saboda sanyinta, wayaryace tayi k’ara ta d’auka kakartace tawajan mahaifiya bayan sun gaisane Baaba take cemata “Yaushe zakizo Jahun kimana kwana biyu, yakamata kizo ai kafin aurenki in ba so kike ‘yan uwa sumiki goriba ranar bikinki’ Dariya Khairi tayi tace “Baaba kedai kawai kice kinaso ki ganni ba sai kin fake da hakan ba, dama inason zuwa wani satin kinsan banjima da gama jarrabawa bane shiyasa’ sun jima suna hira kafin ta yanke wayar inda taji su jidda suna cewa za’a fita gaba d’ayansu aje yawo, abun yamata dad’i sosai…

  Salima da ta k’allafa rai  kan samun details kan Jamila shiru har yanzu malam Ayuba bau dawoba daga sati uku yanzu har an shiga na biyar, gashi batasan wajan wa zata sami number  dayake amfani da ita yanzun ba hakan yasa ta watsar da maganar, gashi ta baya Ya Fahad labari yayi mata ansiha akan ta k’aleta karta had’a husuma, yanzu tana jiran taji score d’intane amma tana tsoron tambaya don Dr ba wasa, suna zaune suna  karatu itada Nucy dake exams sun fara kusantowa malamai dayawa suna masu test ne, taga shigowarsa school kaman taje kamar kartaje haka dai ta hak’ura don batason dizgi….

Jamila da ta faro abun kirki batayi cikakkun sati uku ba ta fara watsarwa, yana lura da ita amma sai yayi shiru kaman baigani, shikuma bai fasa komi na faranta mataba, yanzu haka ya kawota Sahad suna sayayya zasuje gaida iyayenta dake Asokoro(commisioners quaters) , itama kuma tad’auki kayan shafe shafe, sungama sayayyar yace ma Jamila ta shiga motar shikuma ya d’ebo kayan adaidai lokacinne wata yarinya da tasha gayu tazo zata shiga cikin Store d’in wani irin takaicine ya tasowa Jamila kawai tai butt ta fito daga cikin motar da sauri tace “My One dan Allah kayi sauri’ dak’arfi wanda tayi hakanne don yarinyar tajifa da wata yazo don taga kaman tanawa mijinta karairayane, tuni Ahmad yagano Logon Nata kawai yayi murmushi yace “Hali zanen dutse’…

Duk wasu abu daya dace nagida angama tanadarwa Khairi, kuma akwai wata mata dake bayan layinsu itake zuwa gida tana mata gyaran jiki, sukuma su Khadija da Safiyya sune akan dinkinta don bata fita yawo, tun bayan dawowarta

daga zaga dangi ana saura sati biyu biki, yakama yanzu saura kwana biyar ad’aura Aure.

Hajiya Hassu itace tayiwa Khairi kayan kamshi kasancewarta Kanuri tamata komi kaman yanda zatayiwa Safiya,  harda su tsumi take aikowa wani lokacinma Safiyya tasa ta take agaba in taki sha tace zata fad’awa Maman, aikuwa dole takeshansa, bak’aramin kyau jikinta yayiba banda k’amshi daya zauna jikinta saboda na turare da ake mata, hatta gashin kanta da kalar turarenda ake samishi shiyasa ta kowane sak’o najikinta silent scent ke fita

An d’aura Aurensu inda dubban mutane suka shaida, mutane bakadan ne suka zoba musamman tabangaren babansu Adam kasancewarshi dan siyasa, hatta mutanen Jahun sunzo dana Kura, sunyi kwana biyu sun halarci kamu da walima da akayi, donkuwa dinner sam Adam yahana ta sudai ajunansu mata sun had’a bridal shower sunyi da yanmatan danginsu atsari, bak’aramin kyau kuwa sukayiba, ancu ansha sannan kamunsu yayi tsari sun raba komi awadace don mutane sai yaba tsarin da akayi suke.

Akayi rakiyar amarya aka kaita gidanta daya tsaru don Adam amatsayinsa na Architecture shiya zana gidanshi, duk da bak’atone canba amma fa ya tsaru, suma kuma iyayenta sunyi kokarin saka kaya na zamani, 2 bedrooms ne nata shi yana da daya sannan dawani kusa da kitchen na baki daga waje kuma yayi guestroom (saboda bak’inshi maza)  wajan parking, sannan yasaka flowers sosai shiyasa gida akwai iska, komi atsare…

Kuka take sosai inda su Safiyya suka dinga tsokanar suna kara tunzurata da zarar ta shanye kukan sai su saki maganar da zai ballo mata ruwan hawaye, ahaka dai angwaye suka shigo sannan ne suka kyaleta….

Firdausi S Ahmad

*NAMIJIN KISHI*

By *JANNAH JAY*

Wattpad @ *jannahjay8*

© 2019

08

Gidan  yayi tsit daga ita saishi,  kaman yanda kowacce budurwa akan sameta da fargabar irin wannan daren to haka yakasance ga Khairi,  shikuwa Adam da za’a bud’e zuciyarsa da tabbas za’a tabbatar bai taba tsintar farinciki ba irin na wannan lokaci, yau Khairi tazama tasa, kaman yanda Addini ya tanadar mana haka sukayi sallah sannan ya dafa kanta ya nema musu albarka Aure da neman tsari na sharri, lokacinne kuma idon Khairi ya k’ara tsuru-tsuru, shikuwa yagano har wani ‘yar karkarwa take sai danne dariya yake, cikin salon son sata ta ware yace mata “kalleni Babyluv ko nacansa kamane na koma zombie? Na lura dake duka yau bakyason kallon fuskata’ uhunm kawai ta iya cewa amma ba baki, dama already tayi wanka tasa kayan bacci manya duk anata salon zata rufe masa k’ofa kuma gashi ya rutsata, shiyasa yanzun take ganin bata da wata madafa sai dai ta mik’a wuya, fita yayi zuwa waje mintina kad’an ya dawo da containers da leda ahannunshi, dak’yar ta iya cin naman wanda har kwalla sai da ta share kan ya tilas ta mata, yanayi yana sako wasa amagana don ta ware, fita yayi zuwa dakinshi yayi brush sai da yadau lokaci yadawo wanda yana sane da hakan, kaman yanda ya zata hakanne tafaru, takwanta ta rufa da bargo taji shigowar shi sai tayi kaman tayi nisa abacci, daukarta yayi gaba d’aya ya nufi bedroom d’insa da ita, har yanajin bugun zuciyarta saboda tsoron da taji, zuwa dakinsa dayayi da ita shiya koya mata darasin da ba’a ganewa har sai anshiga ajin, sai da yafara tura yan aike kaman yanda manzo ya koyar (romancing/wasanni) aranar yayi nasarar fara karbar budurcinta cikin hanya maisauk’i da salo, bai gwada mata k’arfiba, duk da haka kuka tayi bana wasa ba shikuwa dayasan shiya kar zomon dole yayi ta lallashi da saka mata albarka, wani matsayi da so da kishintane ya darsu aransa.+

Washegari da tsananin kunyarsa Khairi ta tashi, ita tun cire mata kaya dayayi tafada tunanin yanzu Ya Adam da tasanine ke lalubarta jiki, takasa koda kallon kafarshine balle asa rai da fuska, ga canjin jiki da takeji jitake ko’ina namata ciwo, hatta idonta ya canza dama ga saurin kuka balle kuma an tab’ata,tana zaune gaban mirror tayi kwalliya da wani rantsattsen voil maroon da milk flowers and black bak’aramin kyau tayiba, sai dan sauran kumburin  idon takasa fita palour sai takai bakin kofa sai ta dawo ga yunwa na dibanta. Shiru-shiru baiji fitowarta ba ya nufi d’akin tana jin shigowarsa tayi sauri ta juya bayanta, yar dariya yayi mai sauti kafin ya rungumeta ta baya yana shakar kamshin jikinta, cak tayi inda gaba d’aya wani kuzari nata ya tsaya, ganin taki juyowa yasa ya fara sinsinar wuyarta tare da bata kananun pecks masu fita da iska iska da sigar kashe jiki, aikuwa yayi nasarar hakan dan tuni taji tsaiwa na gagararta, ganin ta gama sukurkucewa ne yasashi fashewa da dariya, yace “Babyluv duk kunyane yahanaki fitowa kikeson wahalarmin da cikinki da yunwa”ya k’arasa fadar maganar tare da shafo cikinta ta cikin riga, kaman k’asa ta tsage ta shige haka takeji, dakyar ta iya cewa “Yanzu nagama shiryawa’ juyo da ita yayi sukai facing juna yace “Ok, to mutafi don tun d’azu aka kawomana breakfast’ cikin sarkewar fuska tace “To kayi gaba gani nan zan zo’ Yace “Nope gaskiya tare zamu tafi’ ita kuwa Khairi duk nauyi takeji karyaga yanda skirt din yamata don bakaramin fitarda shape nata yayiba, ganin zata cigaba da jayayya dashine yasa ya sungumeta tana mutsu mutsu yayi dinning da ita, ranar dai dak’yar idan taci abincin kirki saboda kunya…

F. U. D

“Umar inaga dai zaifi kyau yarinyar takawo details d’inta, saboda nakasa ganin gyaranta na level 3 d’in, kace tazo tasameni a office d’ina gobe’ daga can bangaren Umar ya amsa da “Ok to Shikenan zansa ayi hakan, don damuwata shine wallahi so muke tasamu ashiga da ita camp batch A d’innan, da sunfito za’ayi Auranta’ Yace “Tazo da exam card nata, kodan ta taho da komi nata it would be okay Insha Allah, ku kwantar da hankalinku’ Bayan yagama wayar yacigaba da tsara questions da yakeyi a system, cikinshi yaji na k’ugin yunwa, cikin takaici yaja tsaki yanaga gara ya nemo wani student d’in amashi takeaway acafeteria, cikin satinnan kullum da yunwa yake fita, yasan gulmar dalibai kar su shaida fuskarshi ahakan suke cewa yanada aurenshi yana yawo cin abincin titi, fitowa yayi daga office d’insa ya nufi na Dr Umar yana shiga yaga Dr ya tak’arkare yana zuba loman chips dayaji sauce acikin katon flask da maza hudu sa iyaci harda wani bread agefe da kayi toasting dawani abu, k’amshinsane yasa yaji kwadayin ci, k’arasowa yayi yace “kai kuma ina kasamu wannan, sai had’a zufa kake nasan kuma madam batanan’ murmushi yayi yace kaima kazo kayi joining kafin kaji wa yayi, ganin dayawa yasa Dr Ahamd gyara hannun riga suka d’ora, harda teaflask da 2 cups cikin basket agefe da plates, tsaban yunwane yahana Dr Umar  rufe flask din amma aplate yakeci, sunyi nisa aci Dr Ahmad ya tashi ya had’a tea tare da daukan break din ashe wani hadine ciki na kwai da baked beans akayi toasting, sai da yayi nak sannan sukai parking kayan gefe, gaskiya abincin yayi dad’i don shikansa chips d’in saida aka  mashi hadi na kechup da carbagge aka hadesu jikinshi chips din. Kallon Umar yayi yace “Wane restaurant kasayo wannan?’ murmushi yayi yace “Daga hostel ya fito wannan da kake gani, ina wata yarinya danace maka d’iyar cousin dinace itace ta hadomin saboda tasan Sadiya batanan’ yamutsa fuska Ahmad yayi yace “Student ce ta hado wannan kayan uhunmm har naji kunya, inajin kana fad’ar ta har yau bantaba ganintaba’ yace “Eh tana nan kasan inada relatives dayawa anan maybe kataba ganina da ita amma bakasan ita bace’ sosai suka yabawa niece d’in tashi, koda Ahmad yakoma gida bai damu da yasamu abinciba alokacin snacks daya saya su yaci da lemo.

Cikin lumshe ido da murya da tayi k’asa k’asa cikin yanayin jin bacci tace “Yawwa nan haka baka tab’a wurin’ ta nuna gefen hagu na kanta, shikuma yace ” Ok nan baisan anayiba kenan’ yana yar dariya yana sosa mata gashinta gaba d’aya wani bacci bacci takeji, tana k’ara bararrajewa kan cinyartashi, bacci ya fara d’ibanta sai jitayi da salon tafiyar tsutsa yana wucewa zuwa k’irjinta, tana dan murmushi take tare wa da hannuta tana sakin sound “u’unmm plssss, karka fara’ sunkuyo da kanshi yayi zuwa kunnanta yace ” saboda me babyluv’ cikin rad’a da wani salo kafin ya dawo saitin bakinta ya dora da kissing dinta…

Zaman lapiya ake gidansu Khairi bak’aramin kulawa da soyayya take samu daga wajan Adam ba, gaba d’ayansu sun samu nutsuwa, hakan yasa ta tabbatar bak’aramin so yake mata shiyasa kishinsa yake dayawa kanta, abokansa sunzo inda tamusu abinci mai rai da lafiya haka yasata ta zumbulo k’aton hijab suka gaggaisa.

Safiyya na tayata girki suna hira dake yau tazo mata yini don tuni Adam yakoma bakin aiki, cikin jin dad’i safiyya ke fad’awa Khairi yanda alak’arsu ke tafiya da Ya Muhsin, inkaga yanda Khairi ke fara’a kaman an mata bushara tace “Gaskiya naji dad’i zanso ace nanda wasu months ayi aurenku wallahi, kinga shikenan still jikokin su Abba zasu tashi kai ahad’e’ itama Safiyya cikin nuna gamsuwa tace “Kwarai kuwa kinga  da ace mazan sun dauko wasu matan daban suzo su raba mana kan zuri’a’

Sun gama shirya komi “Sopie shiga wanka mana, nima bari nashiga na can d’akin’ Safiyya kuwa d’aukar veil d’inta tayi tace “Ina ai yanzu zan kama hanya natafi banison mijinki yazo yasameni ku kafurtamin ido da fitsara, don ban manta last zuwa da nayi yanda yake ta janki jikinshi agabana ku a nema kumanta ina nan’ kama baki Khairi tayi tace “Au shedar da kika mana kenan? Zakiyi auranne muga ke yazakiyi k’ila sai kin hana zuwa gidanki saboda cakumar miji’ dak’yar tasamu tasata tayi wanka ta shirya, kafinnan tasaka abinci da snacks wasu cikin warmer akai gidansu danasu Adam d’in, suna cikin hira sukaji k’arar motarshi, yana shigowa ta tafi ta tarb’eshi ya rik’ota ta gefenshi d’aya tare da kama bakinshi, da hanzari ta gudu d’aki sai lokacin yasan ba ita kad’ai bace, ya kalleta bayan ta bashi ruwa yasha yace “wace ta gudu d’aki? ‘Tace “sophie ce’ yar dariya yayi yace “maganin masu zuwa tsurku gidan amare sukai yamma’ naushin wasa ta mashi a kwanji tace ” Haba nice na rik’eta fa kaga sai ka mayarta anjima kad’an’ d’an matsa lips dinta yayi yace “Tunda kin sayamin rigima shikenan naji zan maidata, banda kece kikace da sai dai takoma dakanta meya kaita kaiwa irin time d’innan magriba fa kawai don ahana mutane sakewa ko’ yak’arasa fad’a tare da shafar lips d’inta…

Yana kwance bayajin dad’in jikinsa duk da ya lura da yamakara amma yakasa tashi, wayarsace tayi k’ara kafin ya sauko daga gafo Jamila tashigo ta d’auka mistakenly ta tab’a screen ta daga taji muryar mace “salamu alaikum, ina kwana? ‘ saka wayar tayi handsfree ta mik’a masa wayar tare da kafeshi da ido

Firdausi S Ahmad

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                         
loadιng………..✍🏻

*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*

© 2019

09

Cikin sanyin murya aka gaidashi yake amsawa still idon Jamila nakanshi jira take kawai taji me yarinyar zatace “Malam dama nice niece d’in Dr Umar nashigo school baka nan inaso naji sanda zaka shigone’ dafa fuskarshi yayi shaf yamance da case d’inta yace “Ok nanda 1 hour Insha Allah zan shigo school d’in saboda haka karkiyi nisa, ok’ tace “To nagode’ yana gama wayar ya nufi toilet don shirin wanka cikin rashin kunya da zafin kishi tace ” Wallahi baza’a rainamun wayoba, wace wannan d’in da har take da damar kiranka haka har kana cewa wai kartayi nisa bud’emin meke tsakaninku’ k’ura mata ido yayi na wasu seconds kafin ya k’ara mika hannunsa ga handle na toilet tace “kajini ka shareni sai afake da students ana cin amanata ko? To wallahi bazan d’auka ba, ina iyakar alakarka dasu can cikin makaranta amma har suna iya samunka ta waya’ cikin rashin son fitina yace “Look banason fitina don Allah ki rike hayaniyarki i dont get your time haba kullum ke cikin  zargin mutum, kodan ba mamaki duk matan da basu fiya kare hakkin auransuba dama sun fi kishi saboda basu yarda dakansu ba, ke kinsan da nayi ra’ayin mace biyu wallahi da tuni nayi kodan hakkin cikina and mark my word in kika fiya jingina ni da mata zaki zana kaddararki wallahi’ kawai sai ta rushe da kuka “Eh kana da damar fadin hakan mana tunda bana haihuwa’ ta tsugunna awurin tadinga kuka shikuwa yashige wankansa, gaba daya yaji gidan ya isheshi….+
Cikin farin ciki take amsa wayar “Don Allah dagaske khady result ya fito? Kai amma bakiji yanda gabana ya fad’iba amma dai kinji labarin anci sosai?’ adaya bangaren Khadijan tace “Eh kwarai ance anyi kokari sosai nima gobe zan shiga school muji ya ake ciki’ sun jima suna hira kafin ta kashe ta shiga kitchen tak’arasa girkinta, tana gamawa ta fad’a wanka yau tashirya saka kayan shan iska da bata tab’a sawa ba atsawan auransu, shortgown ne da saman k’irjin akayi zargiya da igiya igiya kalarta black sai ta gyara gashinta tasa chinese pin ta sokeshi instead of ribborn, tasaka golden hooks /barima. Adam da ya biya ta Grandsquare yamasu sayan kayan mak’ulashe ya nufi gidansa cikin farin ciki as expected gida yad’au kamshi sannan rabbatul bait d’inma ta fito kai ba’abunda zaiyi face godewa Allah daya mallaka masa ita, salon da ta tareshi dashi bak’aramin  burgeshi tayiba, bai tab’a ganinta a irin shigarba, lallai ya yarda darasinsa nashiga don gashi ta fara ajiye kunyarshi, koda ya rungumeta hannunshi gaba d’aya yakasa daidaituwa daga buttokchicks dinsa zuwa hips dinta, kai tabbas Allah yayi diri awajan….
Yana zaune suna cin abinci atare sai binta yake da kallo, anan take bashi labarin result d’in  su ya fito yace “Insha Allah gobe zan shiga school d’in muji  yaushe zasu fara badawa ko? ‘ tace “Yawwa nagode’ daga mata gira yayi “yiwa kaine ai’ ya fad’a tare da kissing hannunta da ta mik’a mashi loman a spoon, har so yake ayi Isha’i ya dawo gida don gaba d’aya Babyluv ta rud’ashi, koda yazo fita saida yace pls karki cire rigarnan har saina dawo…
Alhaji Aliyu mahifin Khairi ke zaune da abokinsa tun na secondary wanda yanzu yake kan matakin commisioner of health, suna cikin hirane suka sako kan iyalai inda yace da zarar result nasu Khair yafito amishi magana Insha Allah zai sa abata aiki kafin ta d’ora da degree d’in, sosai abun yamashi dad’i, aikuwa zai sanarwa Baban Adam tunda har Safiyya za’a samawa
F. U. D

Da b’acin ran Jamila yafito ko ruwan tea baisamu shaba, yana zaune a Office Bahijja tasameshi da takardunta, yana zaune yana ta bincike don asamo mata score na wani jarrabawarta ta level three, gashi tagama school anzo karbar result akaga da matsala, sosai kanshi yad’au caji, yafita ya dawo shine can shine can duk yagalabaita ga yanayindama baijin dadi akwai ga bacin rai ga yunwa, wayarshice take tak’ara in bai mantaba wannan ne karo na 10 , jan tsaki yayi ya d’auko batare da ya duba sunan mai k’iranba cikin daga murya tafara “Wallahi Ahmad nafi k’arfin ka wulak’antani akan mace da har ka tsallake gida kabarni cikin wasi wasi amma ka tafi gareta, wato gara ni raina ya b’aci da nata.. kashe wayar yayi wannan wace irin masiface ne, cigaba yayi da aikin tabbas Jamila tana nema tak’ureshi he’s tired, sai wajan k’arfe biyar yagama shan matsalar don yasamo wasu records d’in…
Yana tashi daga wurin aiki yashiga gidan nasa ya tarar batanan cikin ransa yake sak’e sak’e “Kodai yaji  tayi? Tab amma kuwa da tagama raina mishi hankali abunda  ya tsana yaji ance mace tayi, amma zai nuna mata iyakarta’ fad’awa toilet yayi yayi wanka yana fitowa ya had’a tea sannan yasha panadol ya kwanta…
KANO

An karb’o result kuma yayi kyau sosai, wannan abu yawa Khairi dad’i bakad’anba gab’a d’aya farin ciki ya cikata, gashi yaune rana na farko da tafita daga gidanta ta zagaya danginta har dare tana gida cikin ‘yan uwanta har k’anwarta Humaira tadawo daga boarding gidansu complete suna nan sai 10:00 nadare suka koma, suna shiga kowa d’akinsa ya shiga sukayi wanka, wani white lacey  night gown tasa wanda ta sauka har k’asa saidai ta kasance shara shara ta kwanta tare da rage speed na A. C, bata jimaba bacci ya fara fizgarta, cikin bacci taji ana zame rigarta, ture hannunshi tayi tace “U’unmn hearty’ cikin murya k’asa kasa yace mata ” I just want feel your warmbody i know you are tired, huhh’ ya ajiyemata huci akunnanta kad’an tare da yimata wasu kissess awuyanta, cire mata rigar yayi tare rungumeta tare da lullubesu jikinta mai dumi shiya k’ara sakashi kasala, itakuwa bacci yaci k’arfinta, ya k’amk’ameta.. Sha kuruminka Adam bamai k’wace maka  ita
Cikin bacci yayi mummunan mafarki wani ya auri Khairi da salati ya farka saboda razanar da yayi baisan sanda ya cakumeta da k’arfiba, yana salati yana had’a zufa duk da A. C dake aiki ad’akin, farkawa tayi tajita cakume ak’irjinshi gashi tana jin bugun zuciyarsa cikin  kid’ima ta shafa fuskarshi tace “Hearty meya faru? Pls kafad’amin meke damunka?’ Bayaso tasan yana wani yanayi yace “Bakomai i just had a nightmare, Khairi zaki iya zama dani  akowanne irin yanayi? Zaki iya hak’uri  da juriga akan duk wani tsanani don ki kasance dani? Don Allah ki amsamin karki bari wani ya shiga rayuwarki’ k’amk’ameshi tayi tace “Wane irin tunanin kake hakan? Ba’a auran maza biyufa kuma insha Allah auranmu mutu karabane’ ka kwantar da hankakinka sai da sukayi mintina 5 kafin ya had’a nutsuwarshi ya mayarda mata rigarta tare da mik’ar da ita tsaye suka shiga toilet sukayi alwala suka yi nafila tare

Jamila dai sai da takwana agida tamusu k’aryar tafiya yayi don iyayenta dattawane bazasu bari takwana ba matukar sun san yaji tayi, bawanda yadamu da mata magana sai da takwana biyu kafin k’anwarta ta tona tace tajita da dare tana kuka kuma tana fadawa kawarta sun samu matsala da Ahmad, kan haka babanta yamata fad’a bana wasaba yasa antyn ta ta maidota gida, amma kuma sunyi mamaki narashin zuwansa, shikuwa Ahmad  ciwone yaci karfinsa shiyasa kuma shi baiga laifin dayayiba balle yakira gidansu yasa wani uncle nashi yabi sahunta,  yana zaune  afalo sanye da jallabiya Aunty Sa’a tashigo da ita awaje kuma yayan Jamilane, cikin girmamawa yagaidata ya fita ya shigo dashi suka zauna afalo, don ta tsara komi ta fadi karya da gaskiya da ido yake binta kawai, ya masu bayani kan bahijja tare da cewa dama takan zargeshi da abubuwa, anan akamata fada dama sun san Jamila da jarabar kishi, shiru tayi badon fad’an yashiga kunnantaba, ta tashi ta fita rakasu, bayan sun fita waje Aunty  Sa’a ta jata gefe ta mata fad’a anan take cemata “Sau tari wasu mazan hankalinsu bai kaiwa ga matan anma idan kafiya zargi da magana akan mata tamkar kana masu isharane zuwa garesu, yawan yin hakan da kike zaisa tun baya tunanin k’ara auren yayi kinga kuma ke kika jawa kanki, idan kina ganin kaman  masifarkine zaisa yak’i wallahi Allah zai sa yayi yaga idan ko abunda  kikene zai hanashi, ki kama kanki wannan tsinannan k’iwar da kike ki ajiyeta gefe’.. … Zamu gani ko zata canza
Firdausi S Ahmad
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                         
loadιng………..✍🏻

*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*

© 2019
10
KANO
Amakare suka tashi amma hakan tayi gaggawar tashi tayi musu breakfast tareda shiryawa cikin  riga da skirt na holland da akama zanin wraffer skirt sai kaga yanda yayi daidai da jikita, baida kuzari sosai ahaka ta tayashi shiryawa tare da tsareshi yaci abinci yafita, kwanciya tayi bayan fitashi take chat da Khadija tace mata Insha Allah yau zatazo ziyara, abun yayiwa Khair dad’i don zaman kad’aici bai da dadi ko kad’an, sanin tanada snacks da dai abun saukar baki yasa bata tashiba suka cigaba da hira  da ‘yan uwa…+
DUTSE
Tabbas Jamila tayiwa Ahmad laifi don bak’aramin b’acin rai yajiba da yajin da tayi amma sai ya cije yabata hak’uri inda ita kuma adaran ranar tayi ta cunkushe cunkushe tana cika tana batsewa anata tunanin  zai nemeta, don tasan bai juran rashinta na fiye da kwana biyu koyayane sai ya rage zafi, amma ga mamakinta sai taga ya kwanta ya juya mata baya batare da ko neman romancing ba, takaicine ya taso mata k’arshe ita tunane tunane da b’acin rai ya dama.
Da safe da ta tashi tayi k’ok’arin shirya komi tayi kwalliya tare da komawa normal, bayan yagama cin abinci har bakin motarshi ta rakashi tare da mashi adawo lafiya yaji dad’in hakan tare da fatan d’orewarshi.
BAYAN WATA BIYU

Abubuwa da dama sun faru masu dad’i da marasa dad’i, abangaren zaman Auren Adam da Khair zamu iya cewa suna zaman lafiya, kuma kowa yaje gidan zaifita da fad’in sun bashi sha’awa don kowannensu yana kokarin farantawa d’an uwansa, kuma ansaka ranar bikin  Khadija Saura wata d’aya ayi. Itakuwa Jamila zamu iya cewa hak’uri da kawaicine yasa atsawon lokacin ba’a samu b’araka ba tsakaninta da Ahmad don akwai ranar da k’anwarshi Naja’atu tazo gidan tasami tana mishi halin jarabar ta kwashe komi tafad’awa Ummu (mahaifiyarsa) wanda dama sunajin red’ed’in jarabarta da sakacinta kanshi, hakan yabawa ‘yan uwansa haushi bakad’anba kuma sunce duk randa sukaji abu agabansu zata taka masa burki zatayi masu fad’a

Suna zaune gaban iyayensu acikin babban falon mahaifin Adam,gabad’aya zuriyar Alhaji Aliyu kura (mahaifin Khairi)  dana Alhaji Abdullahi A K’waru (mahaifin Adam) ana hira cikin  jin dad’, anan ne aka gabatarwa dasu Khairi appointment letter d’insu inda ita Khair zatake zuwa asibitin nasarawa bangaren Lab, itakuma Safiyya ba yanzuba  zata fara zuwaba sai bayan bikinta da Muhsin, bayanin su su Abban shine saboda idan tafara zuwa take zuwa matsayin matar Aure, bak’aramin nauyi k’irjin Adam yayiba wanda kawai don iyayensune sukazo da abin da ba abunda zai hana fasashi, daurewa yayi yayi godiya…
Da dare bayan sun dawo gida Allah Allah yake tagama shiryawa suyi magana, ta shigo d’akin sanye da silk nightwears da hula mai net ta zauna a otherside nagadon, cikin kulawa tace “Na lura tun muna hanyar dawowa gida mood d’inka ya canza meke damunka?’ kallonta yayi yana nazarin wasu abu akan fuskarta “Ko bakajin dad’ine?’ ta matso kusadashi tare da d’ora hannunta kan cinyarshi “Khair ke kikace anema maki aiki ko?’ yamutsa fuska tayi tace “Banganeba? Kaman ya ni? Kasan dai ni ara’ayina ma nafiso sai nayi degree sannan zanyi aiki so that i can play agood role in lab’ kallon bakinta yake yana k’issima hanyar da zaifi yagoge mata ra’ayin aiki yace “Kenan su Abba sukayi decidin, anyway Wallahi banason kiyi, i can afford everything you want’ k’ura mishi ido tayi k’irjjnta na dukan uku uku yatashi zaune ya janyota jikinsa tare da matse hannunta yace “Babyluv you know i freaking love  you, kuma kinsan ina kishinki, i want know kin nemi abu kinrasane agidannan? Ko kuwa kina ganin nan gaba buk’atunki zasufi k’arfin samuna? Tell me truth pls’ Kana  ganin yanayinsa kasan  har cikin  ransa bayason abun don ga damuwa kan fuskarshi ko yaro k’arami zai fuskanci hakan idonshi yayi ja, jijjiga kanta tayi ta sauk’e muryarta tace “Ko kusa ni ban kawo neman abun duniyaba asali kaman yanda kasani inada ra’ayi kan Lab sannan kuma kasan wannan karatun normally ana aiki  dashi is not like other causes da zanje ace bussiness or something else, taya zan mori karatun ba tare da asibitiba pls karkayi ruining dreams d’ina pls, wallahi zan kiyaye hakkin aurena kasan kalar tarbiyyar damuka samu daga iyayenmu, pls kadaina damun kanka’ dukansu  da alama kowa bazai iya sakarwa dan uwansa uzurinshiba, takwanta jikinshi kowa yana sauraran bugun zuciyar d’an uwansa

STORY CONTINUES BELOW
“Yanzu kaman ni duk kishina matata take wanka tana fita ta yini tare da wasu mazan matsayin abokan aikinta, suyi ta kallonta ta saba dasu susan part of her life infact hours da take dasu yafi nawa, oh no kilama zatayi ta daukar jinin different maza, ta tab’a jikinsu’ bai san sanda ya runtse idonsa ba duk da azuciyarshi ya hasaso wad’annan abubuwan, kiran sunanta yayi yace “Inaga kicewa su Abba bakison aikin yanzu sai kingama degree d’inki’ kallon idonsa tayi tana zargin wayo zai mata daga haka tayi loosing fa kenan aikin da ido rufe ake nemanshi tace “Ai dama an tsara bazan jima inayiba zan tafi k’aro karatu kaga shikenan no need ace baza’a karbi  aikinba’ Ranshi  ya k’ara b’aci kenan dabararshi batayi aikiba, cikin zafin rai yace “Kai gaskiya ni bazan d’auki hakan ba ya za’ayi for godsake duka auranmu bai dad’eba kifara raba lokacinki da wasu’ yadinga fad’a ita kuma bazata iya maida masa martani ba,  hawayene yafara zubowa daga idonta tana sharewa ta tashi ta koma gefe tacigaba da dauke hawayen dake zuba a idonta…
F. U. D

Examinor kai yad’au zafi kasancewar an fara exams a F. U. D yakan dad’e bai dawo gida ba, hakan fa yana damun Jamila sau uku tana shanyewa batayi masifa ba, sai dai zaiga anata cika ana fushi dashi yabata hakuri.
Kwance take tana jiran dawowarshi daga Jahun yakwana canne saboda yayiwa ‘yan healthtech test, doguwar rigace bak’a ajikinta sai tsaki take “Ko me yatsaya yi shida yace by 9 yazo amma har 12 yak’i yazo, bari nakirashi naji’  Ta d’au wayarta tare da k’iranshi, yace mata tak’a hak’uri wani abu yataso ya tsaidashi amma insha Allah nanda 30 minutes zata ganshi jan tsaki tayi bayan takashe wayarta, ta tashi ta kunna tv

“Salamu Alaikum’ sai da tayi kallon yanayin harara sannan ta amsa murmushi yayi tunda yasan shi yayi laifi yace “Ayi hak’uri nad’au lokaci ban dawoba Asibiti nakai Yakumbo batajin dadi (k’anwar mahaifinsa)’ bata damu taji ya yakasanceba itadai tasan ammata laifi, yanda tajima tana jiranshi har da kiransa sau uku kafin zuwanshi zaka rantse wata gwaninta ta tanadar masa,  sanda ya bude flask na abinci macroni yagani sai stew ad’ayan, tadad’e da sanin cewa Ahmad pasta yana d’aukansu kaman abincin dare ne barikeshi suke da ranaba, haka yadaure yaci rabin plate tare da kora ruwan hollandia daya shigo dasu, ita kuwa mutuniyar sai d’aci take da kumbura anmata laifi

Da dare yana kwance yana jiranta tashigo d’akin don sosai yake da buk’atarta, kwana wajan shida ko kiss bai had’ata dashiba, shigowarta ce tadawo dashi daga dogon tunanin daya shiga kallonta yake da mamaki wata rigar material ce ajikinta dinkin umbrella,ita kuwa ta basar ta kwanta  duk da tagano yana mamakin abunda tayi, ta bashi baya tare da kashe bedside lamp taja comforter takwanta, sai da tayi minti 5 da kwanciya yayi gyaran murya yace “An ma dai kinsan ke nake jira ko?’ cikin k’unk’uni tace “Kake jirana kaman ya? To in ma jiranne bagashi nashigo ba’ jije leb’ensa yayi yace “Ko hakkin nawama fara wasa zakiyi dashi? Haba wai mene ne hakanne in laifi namaki pls kigayamin basai kin hukuntani tanan wajanba’ Tace  “Ni bance kamin komiba ai kuma ban hanakaba’ kwantawa yayi tare da nemawa kansa mafita yajima yana binta da salo tun tana buzgewa har tabada kai da zafi zafi yadinga sarrafa harshensa cikin  bakinta cike da  bukatuwa yanayi yana kaiwa jikinta shafa, to itama Jamilar ankwana biyu dole ta ware suka raya wannan daren, sai da yace don Allah tadaina saka irin kayan nan in zasuyi bacci dake tana mayen lovemake ne har da bashi hak’uri…
KANO

Cikin dare yakasa bacci don gabad’aya yinin ranar Khair bata da walwala tun rikicin da sukayi jiya, karo nafarko dayin auransu daya kasance basu kwana cikin jikin junaba sai yau gashi za’a maimaita, takwanta tuni tabashi baya yatabbatar ba bacci takeba kuma koda tafara yasan baiyi nisaba, kwanciyar magirbi tayi hakan yasa yaje ta bayanta ya zauna tare da mike kafarshi ya shafo fuskata yace “Babyluv yanzu akan aiki kikeso ki tarwatsa mana farincikinmu? Kiyi hak’uri da masifar da namiki jiya  wallahi bazaki gane yanda zuciyata ke radadiba idan natuna wasu zasu ke kallemin ke’ Ajiyar zuciya ta ajiye tace “Nasan dama bakowanne namijine yake jurar matarsa tayi aikiba amma kaga yanayin karatuna meye amfaninsa in banyiba, kuma kaga shawarar iyayenmune ni banida tacewa’ ganin yafara samun daman abunda  yakeso tayi yasa ya janyota kan cinyarshi ya zamanto tana kaman rigingine suna kallon juna yace “Inaso kicewa su Abba bakison aiki sai zuwa nan gaba, inaga kaman za’a iya ajiyewa matsayin kin tafi karatu kafin nan kinga kin kara zama full matar aure’ shiru tayi tana nazarin maganar “Gaskiya bazan iya tunkarar su nace baniso ba, sai dai ko kai kamusu magana tunda sun san kana da right kan matarka’ ashe yarinyar nan tana da wayo yake fad’a aransa “Shikenan zan gwada amma dai duka ko amarci bamu gama shaba fa’ yak’arasa fad’a tare da shafar saman kirjinta, take ta lumshe idonta tare da shiga wani tunani, kwata kwata batasan  damuwa amma ta lura kan aiki suna iya kai ruwa rana itadashi, tsakanin jiya zuwa yau har d’an fad’awa idonta yayi dama gata gwanar saka abu arai, har yanzu hannunshi  bai tsaya wuri d’ayaba ajikinta yace “Ya naji kinyi shiru tunanin me kike? Pls ki ajiye komi insha Allah zansan yanda za’ayi’ ya kamo fuskarta tare da hadeta da tashi lokaci d’aya suka saki ajiyer zuciya, hannunshi yakai bayanta tundaga mafarin spinal code nata yake shafawa ahankali har zuwa buttockchicks d’inta, taja sheshska sai tin kunnensa, sai da ya lumshe idonsa,  itama hannunta takai zuwa cikin sumarshi da tafara cika zuwa k’eyarsa cikin salo sun jima suna romancing junansu, daga jiya zuwa yau kad’ai bakaramin missing junansu sukayi ba saboda they are  addicted to eachother,  sannan sukayi Addu’ar bacci suka kwanta

Cike da kulawa take kallonshi tace “Nak’ara maka abincin? Naga bakaci dayawa ba’ murmushi yayi yace “Sweety kenan bakiga kin cika plate dinba yanzu jinake cikina  kaman zai fashe fa, ko so kike nayi katon tumbi’ da murmushi take bashi amsa “Nikuwa ya za’ayi naso kayi tumbi kafi k’arfina’ takarasa tare da kanne masa ido d’aya, da hirar soyayya tarakashi har bakin mota, farin ciki  bai boyuba afuskar Ahmad don sosai yaji dadin jiya da yau inama zata d’ore ya furta afili lokacin yana tsaka da duba  wasu takardu kafin yatashi sau biyu tana kiranshi, sai yake jinsa wani nadaban
Firdausi S Ahmad

lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                         
loadιng………..✍🏻

*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*

© 2019

11
Kasancewar week end ne yau Adam yana gida bai fita ko’ina ba, kwance yake akan couch yana karanta jaridar Daily Trust inda ita kuma Khair tseke hada hadar had’a abinci, tayi waya da ‘yan uwa na k’ofar k’waru zasuzo su Jidda kenan, wayarshi tayi k’ara yad’auka “Ok Sabeer yanzu kenan zan iya fitowa? Kaban 30 minutes insha Allah zaku ganni’  komawa yayi d’akinsa ya canza shigarsa daga jallabiya zuwa  dakakkiyar shadda skyblue tare da fesa turaruka yad’auko rafar yan 500 yasaka a aljihunsa ya nufi kitchen, yana zuwa ya tarar ta juyawa k’ofa baya tana wanke lettuce a sink rungumeta yayi tare da ajema wuyanta kiss yace “Kinji tafiyar nan an dawo da ita yau yanzu Sabeer yak’irani sai na dawo’ Juyowa tayi “Shikenan nida naketa murna zaka wuni gida ashe yau ne’ takara fad’a tare da cuno bakinta yar dariya yayi yace “Babyluv da kilibibi tun dazun fa na lura sai rawar k’afa  kike  zakiyi bak’i dama dana zauna agidan d’an kallo zan zama’ dariya sukai gaba d’aya tare da yin kiss alips “Basai kin rakaniba cigaba da aikinki, take care’ yasaketa ya fita+

Sai wurin 12 sukazo  aikuwa gida yacika da hira, su biyarne  banda yara guda biyu, duka cousins ne gasu Adam, jidda, Abdul, salma, khalifa, nana sai su khalil yarane, sallah ke fitar da mazan

Sun dawo daga sallar la’asar suka zuba abinci matan a tray d’aya mazan ma haka, dake falon nata nada girma kawai eating mat suka dora, sunaci ana tab’a hira, cikin hirar tasune asako zancen aure inda su Khair suke zolayar Abdul yak’i ya fito da mata daman ya fiya yaudara in baiyi wasaba sai ya auri mummuna, suka kyalkyale da dariya daidai lokacinne Abdul yace “Haba Khairi har dake amun wannan fatan ko, ni da nakeso kisamo min mace irinki… Salamu Alaikum gaba d’ayansu suka had’a baki wajan amsa mashi, ranshi ya masifar b’aci banda su Abdul basu da hankali baligai manya dasu sun bararraje agaban matarshi, wata harara ya kwad’awa Khairi alokacin suna  mishi sannu da zuwa ya wuce d’akinsa, tashi tayi ta biyoshi sukuma suka dasa hira, su Abdul kuwa dake mazane sun d’an gano sauyi daga gareshi

Kallonta yake fuska ba  annuri yace “Khairi gaban su Abdul kike zaune ba hijab? Haba har kina wani wage baki sakaka kina hira dasu, kinmanta ke matar aurece yanzu’ Tunowa tayi ana fad’in  maza ko dan uwankane suka  ganka dashi sai sunji kishi don nasu daban yake, koda kuwa namijin bai kai Adam kishiba to haka suke tace “Kayi hak’uri ai naga ba su kad’ai sukazo ba dasu Jidda shiyasa, kuma dama yanzu suna gama cin abinci zasu tafi’ naushi dayan  hannunsa yayi yace “To dan basu kad’ai bane sai me? Shiyasa kika tsaya suke kalleki ko, to barin in gaya maki banason haka gaisawa da dan hira sama sama ban hanaba amma ace tun wurin azahar kuna tare dont repeat this again’ shiru tayi to wai ya zatayine zatace karsu zo mata gidane ko ya? Ai ko ba Adam ta auraba dole suzo gidanta “Kayi hak’uri’ ta fada tare da fita ta shiryo masa abinci ta kawo masa

Bayan takoma har sungama su Jidda sun gyara falon, sukuma su Abdul sun koma kan kujera suna sipping mango juice da tayi, kallonta yayi yaga kaman tad’an canza yacewa su Jidda “Bari muba amare waje, kuma kunsan zamu dubiya gidan Baban Yola ko?’ Sukace hakane  cewa tayi su shiga dakinta su gyara fuskarsu sai su wuce, takoma tace mashi zasu tafi 10k ga bata ta basu ita kuma tashiga dakinta ta basu cosmetics. Ahanyar su nakomawa Abdul yake cewa Khalifa “kasan halinmu na maza bakaga Ya Adam yak’i  warewa muyi hiraba’ kyalkyalewa sukayi da dariya suka tafa sukace “muma dai munkusa mushiga netwk dinnan’ Su Abdul sune mabiyan Adam ne ahaihuwa shekara biyu yabasu da ‘yan watanni

Ya fito daga wanka ta mik’a mashi mai cikin son zolayarta yace “Yau bazaki shafa minba’ dan yak’e tayi don wallahi taji haushin abunda yayi d’azu, shikuma yanzu ya huce yace “Shikenan bari na shafa dakaina yau ba’a ji dani’ karb’a tayi ta shafa masa jefi- jefi yana jan ta da hira tun tana amsawa dakyar har dai ta ware

STORY CONTINUES BELOW
DUTSE

fara’a take tayi da alama wayar da takeyi mai dad’ice can tace “Don Allah kizo mana mundad’e ba’a zanta ba, ki taho min da wannan curry d’in nagaya maki basu kawo wa nan’ amsa mata akai daga can sannan  tace “Yawwa ko kefa ai yakamata mu yini maje sunan Farida ma’  Fitowa yai cikin shigar manyan kaya yace “Kin shirya mu wuce?’ Tace “Eh bari nad’auko mayafina da jaka’ yafita  zuwa parking lot itakuma taje ta dauko su, sai da suka tsaya jikin wani shop nasaida beverages yayiwa gidan nasu sayayya sannan suka nufi Commisioners quaters, cikin girmamawa Ahmad suka gaisa da iyayen nashi sannan ya nufi part na Alhajinsu bayan Jamila tagaisa dashi ta dawo cikin gida, shikuma ya zauna acan kwana biyu bai samu zama da  mahifin nasa ba
Acikin gida kuwa kwanciya Jamila tayi ta cigaba da chat awaya agroup dinsu na MATAN K’ASAITA,  rabi hirar da ake akan kishiyane aikuwa ganin ansako abunda ta tsana yasa ta tsaya aka cigaba da hirar da ita, inda tabi bayan masu kushe kishiya, anan wasu subada shawara mai kyau wasu su bada tabanza, wadda duk wadda tafi ta’allak’a ga k’in kishiya  ita Jamila ke nad’ewa akanta

MONDAY

Tagama shirin komi hatta breakfast tagama duba agogon hannunta tayi taga 7:10 ta nufi d’akin Adam, yana tsaye kusada closet ya saka wani men material takarasa tare da tayashi saka links na hannunshi, ta juya ga dressing mirror ta d’auko Perfumes ta saka mashi, brushing lips dinsa yayi kan idonta tare da mata peck kan lips dinta dayasha lipstick plum colour yace “Thanks Babyluv, bakiga kyaun da kikayiba yau’ murmushi tayi tare da kallon kanta, sanye take da Gown na Drylace milk colour da akayi manyan flowers da plum colour jiki da dan mix na pitch kad’an, tadaura agogo tare da manyan fashion ear rings akunnenta, tana fitarda  k’amshi mai sanyi, tace mashi “Thanks Hearty muje breakfast is ready’ suka sarkalo hannunsu tare suka nufi dinning, anutse suka gama breakfast d’insu kafin 8,  tashiga d’aki ta dauko folder na credential dinta don yau zata fara zuwa asibiti, shikuma already tafito masa da briefcase d’insa, afili kana iya cewa kaman bakomi aran Adam, sai dai cikin zuciyarsa da zaka bud’eta bakin ciki ke cinsa yau Khairinsa ta fita da kwalliya  zata yini different maza su kalleta bama mutum d’aya ba, har sun shiga mita tace “La namanta Lab coat d’ina’ bata jira amsarshiba tadanyi sauri ta nufi cikin  gidan, jan tsaki yayi afili yace yanzufa dole take yawo da wannan abar da mini hijab cab lallai za’ayi rikici dani….
Yana office yana cike- cike atakaddu  ya ajiye biron hannunshi ya shiga tunani “Bari natashi naje Asibitin  naga abunda ke wakana, kodan kuma fa yau tafara zuwa k’ila bazatayi aiki sosai ba za’a nuna mata yanda abubuwa ke tafiyane kawai’ Tallafar goshinsa yayi da duka hannayensa ya  furta “Ya salam wallahi banda su Abba sun isa dani da dole  tabar aikin nan’

Khair kuwa cikin mutum tawa tagaisa da college d’in nata, inda H. O. D Lab department yasa aka nuna mata komi, cikin  farin ciki tazauna awajan, gabanta mata masu zuwa gwajin ciki sukai ta zuwa wajan tana k’ara lak’antar yanda abokan aikinnata keyi, k’arfe uku  ta fito daga Asibitin dake ba nisa zuwa gidanta ta tari adaidaita sahu ta nufi gida, ajiye jakarta kawai tayi ta nufi kitchen  ta d’ora white rice tare da wanke kayan miyarta dama tana da tafashen nama ta soyashi sama-sama, shaf shaf tayi stew ta yanka su cabbage ta hada mashi macaroni salad, tana gama azkar din bayan kowacce sallar farilla ta tashi ta had’a masa pine Apple juice, ta koma d’aki tayi wanka tasa three quater skirt tareda crop longsleeve top, kwantawa tayi tare da canza channel zuwa zee world, tunowa tayi sunada water melon saura zai iya lalacewa kusa ta d’auko tare da dicing cikin white bowl tasa whitefoil ta rufeshi, ta shiryasu kan dinning

Kan hanya tunani yake k’ila bata dad’e da dawowaba, shikenan yanzu zaike d’iban yunwa agidanshi don dole sai anyi delay nayin abinci, jan tsaki yayi mutanen ‘da’ sunji dad’i da matansu basa dogon karatu balle suyi tunanin aiki. Tana kwance cikin falo bacci yad’an fara fuzgarta saboda haka bataji shigowarsa ba, k’ura mata ido yayi yana kallon bayanta da shape d’insa yafita askirt d’in ya ajiye ajiyar zuciya “Yaufa wasu yini sukai suna kalle k’ugunta’ ya runtse idonsa ya tako har jikin kujerar da take kwance tad’an dukunkune shiyasa komi  nata yafito sosai shafa flat cikinta yayi sannan ne ta bud’e idonta ahankali “Hearty kadawo ashe banjiba’ tana fad’a tana kokarin tashi zaune, bai amsaba sai kawai ya jijjiga kai ya nufi d’akinsa, biyo bayansa tayi tuni ya shige toilet don ahankali tayi tafiyar kasancewar baccin da tafara ya saukar mata kasala, fito masa da k’ananun kaya tayi ta ajiye kan gadon, bayan tasaka wanda ya cire a inda ya dace, yafito yana goge jikinshi ta k’arasa inda yake tare da fara shafa masa mai abayansa, cikin  sanyinta tace “Ya naga kayi sanyi dayawa wani abu ya faru a office?’ jijjiga mata kai yayi tare da rike hannunta da take kokarin shafa masa mai ga wuyanshi yace “Kawai hankalina ne ya tafi ga yanda ta kasance maki a hospital,yakamata naji naso kirankima wani abu yashamin kai’ murmushi tayi tace “Komi ya tafi daidai na lura suna da kirki yan wajan especially H. O. D’ k’ura mata ido yayi yace “Kuma sun san matar  aure ce ke?’ ya saki hannunta yanzu hakan yasa takarasa shafa masa awuyan nasa ta shafawa fuskarshi tare da pecking forehead  dinsa tace “Ai tuni ma suka sani kamanta nataba shiga kwanaki’ uhunmm yace tace ” Tashi muje kaci abinci nasan kana jin yunwa’
Zuwan Samira dama baya kasancewa Alkhairi awajan Ahmad, domin yau sai da aka kwatanta masa hali, daya dawo gidan ba abinci sai indomie ta masa, ta dinga yan kame- kame, baiyi fad’aba sai Addu’ar shiriya daya mata, shi abu d’aya ke bashi haushi da ita shine matukar ta maka laifi zaka ga kuma tana cika tana batsewa wai don karka ga fuskar yimata fad’a…
Cikin dare yana zaune yana shigar da wasu abubuwa cikin  system d’insa tazo ta zauna agefensa “Myone jiya aka fitar da Ankon gidan Kawu Mustapha’  bai kalleta ba yace “Nawane kud’in?’ cikin  jin dad’i tace “Dubu 25 kudinsu banda na accesories da na dinki’ yace kimin total harna gudummawar da zaki basu ” inaga 50k zai min’ yace “Ok nanda yaushene zai kama? Don bazan iya baki kudinba yanzu sai ko zuwa nextweek’  Turb’une fuska tayi “Eh to zai kai 2weeks amma kasan saboda d’inki zanso nasaya da wuri ko? Kasan tailors basu da alk’awari’ kallonta yayi bayaune karo nafarko da take mashi hakaba,saboda Jamila irin mutanen nan ne masu wutar ciki ba sauk’i in suka nemi abu dole amasu shi sanda suke so, zumbure zumburen baki takamayi tana k’unk’uni, kallonta ya tsaya yake ” shi sau nawa take take masa b’uk’atunsa yana sharewa amma ita yanzu dake ita keso har tana ganin he must do it instantly’ yi yayi kaman baiji mai takeba yacigaba da danne dannensa, har ta tashi zata bar d’akin taji wayarshi nak’ara kallon wall watch tayi taga past 10′ To waye yake kiransa yanzu? Aikuwa sai naji waye’ takoma tazauna lokacin tuni ya d’aga wayar “Eh shine yake magana, haba dai yaushe hakan tafaru? To.. To ina zuwa kaban d’an time kasan da yar tafiya’  Tashi yayi ya mik’e ya zura doguwar jallabiya tare da saka p-cap, ya zari key d’in mota ya saka kudi a aljihunsa, ita kuwa sai binsa take da ido, kallonta yayi yace “Wani abu ya tashi zan shiga school yanzu zan rufe gida in nadawo zan bude ta waje, karki damu.. Yakamo fuskarta yace ok? Take care’ da ta daskare awajan daga baya kawai ta d’oro abayansa tana kiransa dake da sauri yake tafiya sai da yazo parking lot ya bud’e mota sannan ne ta isa gareshi da dan gudunta, zai rufe k’ofar motar ta rik’e “Wallahi baka isa ba ina zaka atsakiyar darennan kuma ma wai school, bafa zakake rainamin wayo ba da hankalina gun wace shegiyar zaka?’ Daidai lokacin aka k’ara kiransa “Ganin nan na taho ku kara hakuri’ kallonta yayi bayan ya had’e ransa “Don Allah sakarmin kofa natafi, i dnt hv enough time’ kama kugunta tayi tace “Kaga wallahi bazan saki kofar nan ba’ Kawai sai tayi wuf ta shige daya side din ta baya, kallonta  yayi yace “Jamila kaman ya zaki shiga kibini da shigar kayan bacci ajikinki’ kawai sai tafara kuka “Wallahi sai na bika’ ganin zata bata masa lokaci yace shiga cijj kidauko hijab dinki amma ki hanzarta, wuff ta zare key na motar ta fita zuwa cikin gida…
Hello fans zakujini shiru na wasu kwanaki

You can drop your comment or corrections at jannahjay8@gmail.com

lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                         
loadιng………..✍🏻

*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*

© 2019

12

Da sauri yake tuk’in motar don haka abun ke k’ara bata haushi, suka isa Hostel aka fito da wata budurwa da bata ko motsi sukayi  Asibitin Shekoni. Bayan sunjene aka yi inda ya dace da ita sannan ne Jamila tad’anji relief duk da ita gani take pretending ne irin na ‘yan makaranta tsabar idonta ya rufe, yana zaune kan kujera tare da Habibu daya kirashi wanda yakasance chief security na school d’in, agefe kuma wata budurwa ce da tasha kuka har idonta yayi ja bakad’an ba, da alama yar uwa ko k’awace ga mara lafiyar, in kaga yanda Jamila ke wurgawa yarinya harara zakayi mamaki, sai da sukaga tadawo tana numfashi,  Ahmad ya tambayi bills yagama settling komi sannan ya juya ya tafi akan sai zuwa gobe za’a sallameta, yacewa d’aya student d’in ta biyoshi su d’auko metron na hostel, haka kuwa akayi ya d’auko metron d’in sannan ne suka koma gidansu lokacin Jamila bak’aramar k’osawa tayiba, amma kuma gefe d’aya ta jinjinawa kanta k’ok’orin da tayo naganin ta bishi anyi komi agabanta….+
KANO

An samu kimanin sati biyu da fara fitar Khairi zuwa Asibiti, alokacin har ta fara sabawa dasu inda anan shima H. O. D nasu yagane kwazonta da kyaun hali irin nata, zaune take tana karbar container da mata suke fitsari su basu, tanayi tana ticking awata takadda, sallama wata sister tayi tare da cemata taje H.O.D na nemanta, wata tayi replacing ta fit.
Bin bayanta yayi da kallo “Ina kuma zata? Naga kaman office d’in wani ne? Bari naga iya gudun ruwanta’ An d’au yan mintuna yana nan dai  inda yayi parking motarshi yaga sun  fito dashi tana d’an murmushi shikuma yana d’an kallonta yana bayani da hannunshi, idan har ba idonsa yamasa gizoba  kallon ne mai manufa daga idon mutumin, wani irin abune ya taso masa ya danne masa k’irji, meye hakan? Yana cikin wannan tunanin har tabar wajan bai gantaba, cikin rashin sanin makama ya tashi ya nufi office d’in daya ganta jiki daf da zai shiga yaga wani cleaner yatambayeshi sai ya nuna masa inda ake d’iban jini yace nan tayi, sai da yaje inda mutane ke zaune sukuma staff na ciki kuma ba’aso mutane su shiga, yana ganota ta cikin window tare dai still da mutumin suna magana, wani irin zafi yakeji kaman zaiyi hauka, har ya zauna kuma yaji bari ya tafi amma fa dole yad’au mataki, shid’in wannan d’in meye dalilin sa nabinta da irin wannan kallon… *kuskuren da wasu mazan keyi kenan, zuwa wurin aikin matansu,  ba abunda yake jawowa face dasa zargi ko kawo rikici, domin shaid’an yana iya rura wani abun da baikai yakawoba a idonka k’arshe aje ayi b’aceceniya*

Adam bai iya komawa office d’insu ba gidanshi kawai ya wuce ya kwanta, saboda tsananin kishi dake nuk’urk’usar sa sai juye-juye yake, gaskiya an shammaceshi saboda bai tab’a tsara arayuwarsa matarshi tayi aikiba, shi ji yake duk duniya bawanda yakaishi kishi wani irin mashi ke cakar zuciyarshi matukar yaga wani namiji yabi Khairi da kallo balle har su tsaya tana masa murmushi shikuma yana kafeta da ido, bari tazo sai ta fada mashi mene yake gaya mata da har take blushing, aiki ba haukabane don tana abokiyar  aikinsa bai bashi right da zai ke abu son ranshiba.
Sai da tagama da wad’anda tayi ma test kan H.I.V, mata biyune da maza biyu suna shirin aure, har gynoetype aka masu, sannan bayan tafito daga ciki main Lab d’in  ta nufi office d’insu da sukan kula da mata masu zuwa kan ciki, anan taga miss calls daga Khadija kiranta tayi tana magana da ita tana had’a kan kayanta don tafiya gida don lokacin tashi yayi.
DUTSE
Kallonshi tak’arayi akaro na uku, ta yatsina fuska tace “Wannan saurin da kake nacin abinci ai sai ka k’ware, kuma duka yanzu 8 batayiba ai’ yasan neman hanyar k’orafi take yace “Amma kinsan munada patient a asibiti,  anyi rashin sa’a ne mai kula da wannan affairs din bai nan shiyasa kikaga an nemeni’ kallonshi tayi cike da jin haushi tace ” Hakane kuma sai yakasance kai kad’aine zai iya daukar hakan ko?’ bai tankamata ba sai ya kafa kanshi kan cup ya shanye sauran tea daya rage ya mik’e ya d’au briefcase d’insa yayi waje, batayi k’asa agwuiwaba ta biyoshi, yasan mezatace bai cemata k’alaba. Sun daidaita kan titi sannan taware veil data d’aura yasauka kan gown sake jikinta.
Yarinyar taji sauk’i sosai dama sickler ke gareta, tana zaune k’awarta ta tana had’a mata tea, sai da suka gaidashi tare da Jamila wadda dakyar ta amsa hakannan taji yaran ke bata haushi, ga kishi daga haka sai kaji so yashiga fa ta raya aranta,    tambayarsu yayi me Dr yace sukace yace nanda evening za’a sallameta, yace basu buk’atar komi sukace eh sannan ne yafita tare da yiwa metron Alkhairi, yana tuk’i ya kalleta yace to “Ke ya zanyi dake dan kinsan school zan wuce kuma gaskiya bazan koma gidaba’ tsuke fuskarta tayi tace “Kawai kace zaka ajiyeni zaifi kyau, kodan ajiyeni gidan Samira’ yace “Amma dai nasanar maki zamuyi bak’i daga Jahun kinga yakamata ki koma gida kiyi abinci da wuri ko?’ Turo bakin ta tayi tace “Ai har nakoma tunda kace sai wajan 2 zasu shigo kafin 12 zan bar gidan nata nima bajimawa zanyiba, yarinyarta ce bata da lafiya’ yace “To Allah yabata lafiya ga 2k ki saya mata sweet’
Tana shiga taga Samira na kurban wani tsumi ajarka “Kai k’awata bakya sanya ina kika samo wannan?’ sai da ta had’iya na bakinta tace “Wannan yar sokoto d’innan man kinsan na yarda da ingancin kayanta, gashi sauran ki shanye duk da na lura ke  baki fiya damuwa dasu ba’ batayi k’asa agwuiwaba ta d’auka ta shanye  tace “Kai kinji wannan baya wannan dandanon marasa dadi, kinsan ni haka ke hadani da wasu magungunan’ daga nan suka d’ora da hirarsu “Kai namanta inata so natambayeki mai ya fito dake haka yau da wuri 9 fa’ anan ta bata labarin abunda ya faru da dare zuwa yau kama baki Samira tayi tace ” Kai kinji matsalar lecturer d’in ko? Hmnn nifa banison kilibibin matan Jami’ar nan haba, yaushe haka mijinka za’ake sa tsakiyar dare yana fita yaje yana gwamuza da yan mata tashin zamani, amma fa kin burgeni da anan zasuyi masa karairaya in gaya maki’ anan tayi ta tura Jamila kan tayi aiki daidai tacigaba da hakan

*****                         *********
Tana shiga taga motarshi amma da tashiga parlour ba motsinshi sai ta kawo yadanje wani wajan kusa dasu, ganin akwai sauran time kafin atada sallah sai tayi alwala tafad’a kitchen ta d’ora ruwan zafi, ta koma kan kayan miya kafin ya tafasa, yana tafasa tasa shinkafar tuwo, sannan ta shiga d’akinta don yin sallar la’asar. Koda Ahmad ya fito baiyi tunanin ta dawoba ya nufi masallaci yana jan tsaki aransa

Tana had’a egusi soup  bayan tagama da tuwon,ta bud’e deep frizer nata taga tana da sauran dafaffen zob’o ta fito dashi ta had’a takai dinning, bataji motsin shigowar mutum ba don haka kai tsaye ta shige toilet tayi wanka tasa armless gown cotton da turban cap ta fito parlourn, yana zaune yanzu kan couch fuskar nan tasa ba annuri, cikin murmushi ta nufi inda yake tace ” Sannu da zuwa Hearty ka shigo ina toilet’ kallonta yayi shaid’an yana rura masa wutar haushinta yace ” Ai na dad’e da dawowa, amma ke yaushe kika shigo?’ ta ga kaman da haushinta cikin ransa amma sai ta kanne tace “Kafin la’asar na shigo nayi tunanin ka fitane, muje kaci abinci’ kallonta yayi nawasu seconds, takasa gane meye hakan kamar dakyar yake mata magana ma, koda sukaje ba wani salo ko armashi acin abincin nasu, sai muzurai yake shikad’ai…
“Ikon Allah sai yanzu zaki dora abincin gaskiya baki kyautaba’ shiru tayi yace “Shikenan ki d’ora iyamu don sun fasa shigowa yau wani abu ya tashi’ ajiyer zuciya ta ajiye don wallahi dama ita yin abinci yafi komi bata mata rai, ganin babusu yasa kawai ta rage ruwan ta zuba cous cous, takoma gefe ta yanka alayyahu ta hada miyarshi kawai saci dashi yafi mata.
Bayan yadawo daga masallaci d’aukar key d’insa yayai yace mata “Zanje asibiti nadauko yaran nan nagama ladana kuma, don inaga cikin week d’innan  shima zai dawo’ kallonshi tayi ta d’auko mayafinta dake kan kujera “Ok mutafi’ ta fad’a tare da d’aukan phone d’inta, murmushi ne ya kwace masa shi har tadaina bashi haushi
Sun fito baranda zasu fito waje don tarar adaidai sahu don su koma hostel, lokacinne kuma tak’araso inda suke tace “Ina  zaku kuma ko har an sallameku?’ kallonta Furaira tayi (patient) tace “Eh wallahi Salima nasamu sauk’i sosai’ lokacinne Ahmad da Jamila suka k’araso inda suke, kallon Salima Jamila tayi ta kuma kalli Ahmad, itama Salima d’aure fuskarta tayi, wani tukukine ya tasowa Jamila bayama da taga uban gayun da Saliman tasha cikin  masifa Jamila ta nufi Salima take k’are mata kallo tabbas itace  yarinyar dana mara kwanaki, hmm ko meye na zuwa bansa azarbabi, kila saboda tasan shine kan abun yasa tazo zuciyarta ke kitsa mata hakan, aikuwa batayi k’asa agwuiwaba tak’arasa inda take ta saka hannunta  ta d’an bugi kafad’arta tace ” Ke wace irin jarababbiyace wai duk inda mijina yake kina nan? Wallahi ki fita hanyarshi ina gargad’inki….

2
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                         
loadιng………..✍🏻

*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*

© 2019

13

Wata uwar tsawa ya daka dasu kansu saida suka tsorata ” Yace wanne irin abune hakan, wai meyasa idonki ke rufewane, bakya tunanin ko friends dinta ne su’ zata sake magana yace “Wallahi kika sake kikayi magana ranki sai yayi masifar baci ki wuce mota kuma’ tuni itakuma Salima tafara hawaye ta juya tabar wajan, d’an waigawa tayi taga Jamila ma ta nufi parking space d’in,  aikuwa tace bari kiga dai yau na rama bak’ar magana koda d’ayace ta juya zuwa inda taga Jamilan tayi inda motarsu take,  tana zuwa ta saki murmushi ta kalleta sama da k’asa sai ta kwashe da dariya kuma tace “Hmnn gaskiya ‘yar uwa action d’inki yana burgeni saboda kin cancanci kike hargagin kishi akan mijinki idan akayi la’akari da zubinki da tarin nak’asu da kike dashi daga halitta har zuwa wayewa, gaskiya ki dage don nakyasa mijinki kuma tunda yamin zan bi duk hanyar daya dace don nasameshi kodan ma wazaiga galleliyar budurwa kamata yakasa amsa tayin soyayyar ta’ cikin  bacin rai ta zaburo daga zaman da tayi cikin motar da niyyar cakumar Salima don yanda ranta ya taso jitake zata iya shak’eta har lahira, ja da baya Salima tayi alokacinne BG friend d’inta daya kawota amota ya hangota ya taho da sauri yazo “Subhanallah  meya faru kuma?’ cikin masifa Jamila tace “Malam ka matsa naci kan uban yarinyar nan wallahi yau sai naga wanda ya isa agarinnan yahanani koya mata hankali’ hak’uri ya fara bata tana kokarin sai ta cafko Salima, suna haka su Ahmad suka k’araso wurin ranshi bak’aramin b’aci yayiba, kuka kawai Salima tasaka tana buga k’afa cikin  muryar shagwaba da b’aci tace “BG ka k’yaleni wallahi matarnan ta dad’e tana cimin fuska wallahi darajarshi take ci’ ganinshine yasa ta juya BG ya na bata baki suka nufi mota, bayan ya gaida Ahmad shima student ne, da kumfar  baki suka bar wajan wanda tsabar b’acin rai da Ahmad yashiga kasa magana yayi sai tunane tunane yake kan matakin dazai d’auka kanta , da alama ta rainashi tunda bai isa ya mata magana tabar abu ba.+
Suna shiga ya nufi d’akinsa ya kwanta cikin kuka ta shigo d’akin “Wallahi bazan yardaba har yarinyar can ta isa ta wulak’antani kaji maganganun da tagayamin? Kodan kai kajamin tunda ka nuna takai kuyi soyayya tare’ tashe yayi  da niyyar wanka mata mari amma sai ya rarumi wayarshi ya cillata jikin bango ta bada wata k’ara tare da fashewa, ya nunata da yatsa idonsa tuni sunyi ja yace “Wallahi kishiga hankalinki Jamila’ jikinsa yana rawa jijiyar kanshi kuwa duk sun fito, bata tab’a ganinsa a irin wannan yanayin ba hakan yasa taja k’afarta ta tafi gabanta har dukan uku uku yake, amma wallahi zata saka k’afar wando daya da wannan yarinyar

KANO

Tun bayan cin abinci da sukayi ya fita sallar Magriba bai dawoba, sai da yayi Isha’i ya dawo, lokacin tana zaune tana kallon wani Indian series, bai damu da ya amsa mata sannu da zuwan da ta mishi ba ya wuce d’aki,sai da taga yayi  kaman 3 minutes da shiga d’akin sannan ta shiga, yana  kwance arigingine yayi nisa atunani ta k’arasa  inda yake tare da zama daga inda kanshi yake tace ” Hearty meyake damunkane duk naga kayi wani iri? Ko wani  ne ya tab’amin kai’ kallonta  yayi wanda yafi kala da harara yace “Pls ki fita kibani wuri  banason kalen yaudara’ gabantane ya buga tace  “Yaudara kuma kaman ya?’ sai  da yaja tsaki yace “Inaso kisan darajar aure, don aure bawasa bane kuma wallahi wallahi karkiga nabarki yin aiki kidauka zakije kiyita warewa kowanne kato bakinki, kiji tsoron Allah!! kiji tsoron Allah Khairi!!’ yak’arasa fad’a yana ishara da yatsansa wani irin takeji  ak’irjinta, meya kawo wannan maganar ne? Dole akwai dalili kallonshi tayi tace “Insha Allah zan kare hakkin Aure, sai dai yanda kake maganganun nan meya faru ne?’ Da yayi niyyar fad’a mata sai kuma yayi wani tunani na daban yace “Kawai dai na jadda damikine saboda inada labarai kala kala kan masu  aiki a asibiti, at times sukan yi cheating abokan  zamansu’ bataji dad’in furucinnasa ba amma sai ta kanne tace “Hmnn lallai basawa kansu adalci ina tarbiyyar da aka bas? Kadaina kawo wannan tunanin akaina kasan yanda nake jinka araina kuwa, inaganin tamkar ba wani namiji kamarka balle asamu wanda zai d’au hankalina’ yadanji dad’i sai dai da yaso ya tambayeta meye hadinta da wancan, sai ya d’an saki murmushi ta sunkuyo kan fuskarshi tare da rage muryarta kad’an tace “Wad’annan labaran ne suka birkitamin kai kenan?’ ta fad’a tare da murmushi yace “Uhmmn kinsan bani da sauki kishi akanki’  dariya ta saki mai dan sauti da salo na jan hankali shikuma ya janyota sosai kan jikinshi yace ” Yau bakimin welcome  kisses ba fa’ D’an ware idonta tayi tare da had’e bakinsu tare, bayan wasu minutes tace ” Me zan dafa makane something light’ yace “A’a karki damu bari nafita asayo suya koya kikace’ murmushi tayi tace “Duk yanda kace Hearty’ Tashi yayi zaune tare da daukar jallabiyarshi da ya cire ya d’ora kan short najikinshi yafita, har yaje waje tace ” Hearty da yoghurt na Habib ko Rufaida’ cikin son zolaya yace ” Wannan bakin naki da son kwadayiko?
Yana tafe yana tunanin abunda yagani “A’uzubillahi minash-shaid’aninrrajim’ yayi ta maimaitawa don sai shaid’an ya maida masa da abinda ya faru don ya tunzurashi, da k’arfin Addu’a ya dawo normal har ya dawo gida suka ci tare sannan sukayi shirin kwanciya.
Bacci ya fara d’aukarta taji yana mata tafiyar tsutsa ak’afarta, tun tana daurewa har tafara gantsarewa tana dariya “Don Allah Hearty bacci fa’ tafad’a da shagwaba “Aikin lada yafi wannan baccin ai, karki damu 20 minutes kawai zaki aramin’ yafad’a yana lalubar bakinta

********          *******       ***
K’arfe biyu da rabi na dare yana kwance sai juye -juye yake yakasa runtsawa, tabbas yafara gajiya da halayen Jamila, shi bazaice ta k’ware afanni kula dashiba hakanan kuma ga taurin kai da rashin jin maganarsa, gefe d’aya ga zuba d’anyen aiki da zubar mutumci, yana takaicin abunda tayi masa a asibiti yanda yayi popular agarin dutse hardly wani abu ya k’etara awajan al’umma ace wani wanda yasanshi bai ganshiba, gashinan mutum sunfi uku suka kirashi kan abunda tayi, yanzu har maganar taje kunnan mahaifinsa, yakirashi ya tamabayeshi sai wata k’arya da yayi masa sannan ya kaucewa abun, ita kuwa mahaifiyar sa tana jiransa gobe yaje don bata yarda da k’anzon kuregen da yayi ba,  tashi yayi ya tallafi fuskarsa sannan ya maida kallonsa gefen gado, bata nan yasan kuma dama za’ayi hakan kalar hargagin da ya mata yasan dole ne taji tsoron zama ad’akin nasa. Yana shiga d’akinta yasameta tayi bacci akan chinese carfet dake bedroom d’in nata ko kayan jikinta bata cireba, yanayin fuskarta zai tabbatar maka tasha kuka bakad’anba,kallonta yayi fitinarta tayi yawa duk da yasan sone yasa kishin amma nata ya kauce hanya, saka mata hular bacci yayi sannan dazai fito ya kashe bulb da ta bari.
Nafila yazo yayi tayi har zuwa k’arfe uku da rabi sannan yad’an kishingida kafin lokacin Asuba.
F. U. D

“Kinga yanda idonki suka kumbura kuwa? Tab kalli mirror d’innan kigani’ tafad’a tare da kwashewa da dariya, jan tsaki Furaira tayi tace “Nucy sai tunzurata kike kinsan dai wallahi abun da ciwo, ga duka ga tsinka jaka. ‘ Share kwallar da ta fito a idonta tayi tace “Kedai bari wallahi bawanda yake cimin kashi duniyar nan kamar matar can, ni bani da alak’a da mijinta amma ta takuramin thank god cikin week d’innan zamu gama exam nabar garin nan, darajarshi take ci da tuni na biya ‘yan  iska sun gigitamin shegiya’ Mik’a mata cup tayi da tea tace “Hakane ki rabu da ita saura nawa ma mubar garin, amma kidaina kukannan tun jiya  abun nan yafaru k’ila ita tana can hankalinta kwance’ da hirar case d’in suka yini sunayi, su Furaira mak’otan su Salima ne ahostel dakinsu jere yake, suna mutumci sosai… Wannan kenan

Tana ji yana k’wankwasa mata k’ofa takasa motsi kanta ya mata nauyi bakad’an ba, sai 6 ta iya mik’ewa tayi sallar Asuba,  adaddafe tagama ta kwanta tana azkhar daga kwance, shima Ahmad yana dawo daga masallaci bai iya yin karatun dayake yiba ya kwanta da tunanin yanda zasu k’are da mahaifiyarsa, ahakan bacci ya saceshi asannan yasamu nutsatsen bacci…

lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                         
loadιng………..✍🏻

*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*

© 2019

14

Anutse take shafa mai ajikinta yanda take shafawa zakai tunanin tausayin fatarta take, yana lura da ita ya kanne, da alama bacci bai ishetaba koma dai meye ai ita tad’orawa kanta fita aiki da tuni in yafita tana da damar komawa baccinta, ya fad’a aransa yanacigaba da shiryawa, yana gamawa ya fita zuwa parking lot ya kai wasu kaya cikin boot d’insa ya dawo, kafinnan ta saka kaya riga da skirt na atamfa da yazauna jikinta  d’as abun sha’awa, tana k’arasa ajiye food warmers kan table d’in, bin bayanta yayi da kallo lokacin da takoma kitchen dan d’auko wani abu, wani irin abune ya taso ak’irjinsa gaskiya bazai bari tafita da kayan nan najikinta ba, suna gama cin abincin ya kalleta yace “Babyluv je ki cire kayannan kisa gown’ kallon kanta tayi batare da takawo komi arantaba tace ” Kayan basumin kyauba ko? Ko kuma atamfar bai makaba?’ dake sabon d’inkine bata tab’a sawa yaganiba, jijjiga kai yayi “kedai kije ki cire zan fad’amiki meyasa nace hakan, sannan meye nacewa basumiki kyauba daman dole in zaka fita sai  kayi kyaune amatsayinki na mace?’  Bata tsaya jan maganaba ta tashi ta canza da wata Gown d’in ta dawo,yace “Ko kefa ace wai sabon kaya bakisa nafara ganiba zaki fita dashi wasu suk’are maki kallo dashi’ tace “Kayi hak’uri namanta bansaka maka shiba ne’ Kallonta yayi bai ce komiba ya fita tuni ya murtuke fuska. Bayan ya ajiyeta ya nufi nashi office d’in yana tafe yana mitar abun wai batayi kyau bane? Kenan har so take tayi kyau alhalin zata fita, kai shifa aikin nan wallahi kwata kwata baso yakeba yaja tsaki.+
DUTSE
Sanye yake da white singlet yana tsaye jikin cabinet na kitchen yana jiran ruwan dayasaka ya tafasa yasamu yasha tea kafin ya tafi gidansu, yaji k’arar bud’e k’ofa amman bai damu da ya juyo ba, cikin dasashen murya ta gaidashi ya amsa mata dak’yar sannan tace “Bari na dafa mana indomie kaina ke ciwo shiyasa ban tashi da wuriba’ ko cikanki bai ce mata ya juyo ruwan acup bayan yasa lipton da sugar ya fice ya bar mata kitchen d’in, kaman yanda  tace hakan tayi ta d’ora indomie shaf-shaf, yana gama shan tea dinsa ya shiga wanka bai wani  b’ata lokaciba ya fito ya shirya anutse, yana shirin fita daga falon ta kalleshi tace ” Ga indomie nagama’ kallonta yayi kaman ya kyaleta sai kuma ta bashi tausayi yace ” Aa aci lafiya sauri nake namakara’ Tasan girman laifintane yahanashi tsayawa ci don in baiyi fushi dayawaba baya k’in cin abinci agida, ruwane yafara taruwa a idonta tashiga uku ya zatayine da Ahmad, dakyar ta cuccusa indomie don tabbas tana jin yunwa, tunda jiya  tun abincin da sukaci kafin zuwa asibitine acikinsu

Tunda ya shiga Umma take zabga masa harara sai sunkuyar dakansa yake, ahaka ta amsa gaisuwarsa ta kalleshi ” Kasan ni bazan yadda da wani labari can da ka tsarawa mahaifinkaba, wai ai kunga suna fad’ane Jamila zata musu sulhu shine mutane suka d’auka da ita ake ko ba haka kace ba?’ yayi shiru dama yasan za’ayi haka tacigaba ” To wannan iskancin da take sun  isheni, itace hayaniya acan itace anan don naji abunda tayi aschool naji wanda tayi aquaters kan wata yarinya alayinku, ina hankalinka ya tafi kabar mace sai  hauka take ka kasa d’aukar mataki, sai zubar mana da mutumci take da tayi abu zakaji ana surukar Chief of Justice ce, to ku fita a idona nafad’a maka’ Sai da tamasa tas- tas yadinga bata hak’uri sannan Yaya kishiyarta ta bata baki, yana zaune nan yana jiran babansa ya shigo su gaisa sai Yaya tace “Bari akawo maka breakfast, akwai su chips da kuma d’umamen tuwon  alkama nasan ka da tuwo wanne kakeso?’ yace “Yawwa tuwon zaifi da kunun gyada’ tuni umma tafara fad’a “Bazaici mana tuwoba yana mai aure kice zaki bashi, kinkuwa san Faisal zai ci, yanada mata ya fito baiyi break ba kodan naji fa gwanar bakaunar girki takeba sai aukin hayaniya tunda ya daure mata gindi’ shidai ya shiga uku da mita sai da Yaya ta tare mashi sannan yaci abincin don Tabbas da yunwa atare dashi…
Bak’aramin haushi tajiba da ya sace mata gwuiwa duk da dai tasan ita keda laifi, ya zatayine gashi yau sukayi dashi zai bata 50k na bikin nan, dole nasan yanda za’ayi mushirya nasanshi da saurin saukowa..
KANO

Ta d’auko syringe ta zuk’i jinin sa, yau tunda ta shigo asibitin aikin da take tayi kenan yanzu ak’alla tayiwa mutum na goma kenan, hakan bai rasa nasaba da yanda sai an kai medical report an sakawa afiles na sabbin d’alibai a university ba, wasu sunzo karatu basuyiba shine sukazo amasu anan, daga nesa ya hango ta takai hannunta ga jikin wani gabjejen namiji wani irin haushi ya taso masa ak’irji wane irin abu Khairi take yine ya tambayi kansa, cikin sauri ya k’arasa wurin inda kafin yaje har ta k’ara maida kai ga d’aukar jinin wani, da wani irin sauri ya k’arasa ya tunkud’e hannunta take  saurayin yayi d’an k’ara cikin jin zafi abun tsautsayi allurar bak’aramin shiga jikinsa tayiba, arazane take kallonsa take kuma kallon hannun saurayin jini tuni ya balle ahannunsa cikin salati sauran abokansa suka maida kallonsu ga Adam “Malam wane irin abu kayi haka dubi yanda kazo zaka jamasa lalura’ d’aya acikin samarin yafad’a, wani acikin staff din Lab din ne yayi  sauri ya saka cotton ya danne wurin tare da jan yaron zuwa emergency, don kan jijiyar hannunsa  allurar ta shiga, ita kuwa Khairi ta daskarene takasa motsi sai hawayen dake zubowa daga idonta, bai damu da yabawa saurayin amsa ba sai fuzgarta da yayi ya janyota zuwa parking lot, bata da k’warin kwace hannunta “Wane irin sakarcine wannan? Eye kizo kina cakud’i cikin wad’annan k’attin? Har kina kama hannunsa’ dan zaro idonta tayi cikin mamaki kama hannu kuma? Lalle idonsa ya rufe ko fatarsa bata gogaba ta tabbata, don cak ya tsaya bayan ya tallafi hannun da zata ja jinin nasa da d’ayan hannunsa,bayan hakama da handgloves ai, kuka mai sauti ta rushe dashi  ganin yanda wasu sukaga abun da ya faru har zuwa janyotan da yayi, tanada k’ima da daraja a idon ma’aikatan wajan, cikin d’an k’ank’anin lokaci suka saba har zuwa cleaners da masu gadi, tasan yau sai zancen ya yad’u, bai damuba yadinga zazzaga mata fad’a wallahi banda yaga allurar tayi haka da sai ya kwadawa yaron nan maruka, kokarin jan motar yake tanason tadauko jakarta tana gudun kar collegues dinta suga tana kuka, aikuwa suna tsaye sai ga Maryam Tafida takawo mata kayanta, batace komiba ta juya ta tafi tuni labari yaje office

Allah yaso abun baiyi tsananiba sai dai yaron ya hasala matuk’a, ana gama gyara mashi wurin suka koma Lab d’in, sun jima suna surutu akan abun yayinda shikuma victim d’in ya k’ira Daddynsa cikin shagwaba yafad’a masa, sai wani staff dinne ya canji Khairi
Cikin gudu bana wasaba yake tuk’i har suka shiga gida, sai mita yake ita kuwa ko magana d’aya bata yiba saboda kuka dama ita bata iya kace-nace dashi sai dai da yafara hayagagarshi ta ke hawaye, lokacin biyu saura ganin batayi sallah ba yasa ta nufi toilet ta d’auro alwala, shima anasa bangaren hakanne takasance, ta idar ta dora kanta gefen gado tana jan ajiyar zuciya, shigowa yayi dakin “Har yanzu baki bani amsar tambayar da namikiba, dama haka kika saba damuk’ar hannun wasu ko yau kika fara? Kuma inaso kigayamin gaskiya’ Cikin raunanniyar murya tace “Kasan dai haka yanyin aikin yake bayau  bane sai dai…’ Wani irin nishi ya ajiye yanda yaji wani abu ya karci zuciyarshi bayau bane yafada muryarshi na rawa kaman mai shirin kuka ya cakumota da k’arfi har saida taji zafi yace “Kikace bayau bane kawai, Khairi ina saninki yake? Ina darajar aurannawa dake kanki har kina iya saka wannan hannun naki ki kama wani d’a namiji bani ba, na shiga uku’ ya saketa ya zauna dirshan  ak’asa ya tallafi goshinsa gumine  kawai yake yankowa aduka sassan jikinsa, wani sabon kukanne ya kwace mata gaba d’aya tayi jage-jage kana ganinta kasan hankalinta atashe yake, wani irin murd’awa cikinta yayi take taji wani masifaffen amai ya taso mata da gudu tafad’a toilet tadinga kwarashi kaman hanjinta zai fito, yanajin yanda aman ke fita har cikin jikinsa yake jin tausayinta amma kishinta da haushi yasa yakasa mik’ewa ya riketa, tana gamawa ta fito adaidai k’ofar jiri ya d’ebeta anan ne bazai iya jurewa ba ya tallofota zuwa jikinsa idonta sai juyewa yake tana fad’in washh ahankali dan banda tana jikinsa ba abunda zaisa yaji, sannu ya fara yimata ita kuma tana furta ” Don Allah kayi hak’uri, kayi hak’uri don Allah’ daukota yayi ya nufi gado har yanzu  bakinta yana furta hakan amma idonta arufe “Shishh is okay kinga zazzabi har ya rufeki, ko dama  bakida lafiya?’ Jijjiga  masa  kai tayi alamar a’a, jan bargo yayi ya lullubeta sannan yaje yad’auko mata maganin zazzabi ya kawo mata tasha sannan ya rungumeta ajikinsa sai rawar sanyi take takai 30 minutes ahaka sannan bacci mai k’arfi yayi awun gaba da ita, shikuwa Adam tuni yayi nisa atunani baisan ya za’ayi yake controlling kansaba gashi sai yayi ta hurting babyluv din tasa duk kuwa da tarin kawaici da hak’uri irin nata

Jamila kuwa abinci mai kyau ta daure tayi, tare da yin wanka da kwalliyar da rabonta da ita tun tana amarya, ta k’ame afalo tana jiran dawowar Ahmad don su shirya….

lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_

   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                         
loadιng………..✍🏻

*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*

© 2019

15

Da sallama ya shiga falon lokacin k’arfe shida saura, cikin  yauki ta k’araso gareshi tare da mashi sannu da zuwa ta karbi ledar hannunshi, amsawa yayi yana binta da kallo,ta nufi kitchen ta kawo masa ruwa da lemo ta ajiye kan centre table, yana cikin shan ruwan tace masa “Wanka zaka fara ko kuwa abinci’ Bai daure fuskaba hakanan kuma ba fara’a yake ba yace “Sai na dawo daga sallar magriba sannan zan zauna cin abincin’ Gani yayi ta shiga dakinsa  da alama yau ya samu arzikin had’a ruwan wanka, dan murmushi yayi ya furta ahankali  Hajiya Jamila ta Ahmad, shima ya d’oru abayanta zuwa d’akin, koda ya fito daga wanka ta fito masa da moroccon jallabiya ta jiye masa duk abunda yake buk’ata….. Ashe dai Jamila ana sane ake watsar da miji.+
Ta tashi yanzu ba zazzabi ajikinta sai kanta dayake dan ciwo kad’an, kuma jikinta ba k’arfi baya nan ga fita masallaci, a daddafe ta isa toilet tayi alwala sannan ta dawo ta tada sallah, sanin ya barota batajin dad’ine yasa ya wuce wani eatry ya masu order farfesun kayan ciki da friedspaghetti sannan ya sayo fruits da yoghurt, yana shigowa yaga bata d’aki nufar kitchen yayi yaga ta d’ora tukunya kan wuta, da sauri ya k’arasa kusada ita ya rik’e hannunta “Me zakiyi ke da baki da lafiya? Ko wani abu kikeson ci?’ Jijjiga kanta tayi tace “A’a abinci da zan dafa mana nasan kana jin yunwa’ wani tausayintane ya kamashi ya rike chicks dinta yace “A’a basai kin wahalar min dakankiba, na sayo mana abinci please karki sake wani abun, ok?’ ya daukota ya dawo da ita falo ya ajiyeta kan L   shape couch dake falon yasa k’aton pillow ya dan kishingida ta, ya koma kitchen ya yanko fruits d’in sanin k’aunarta ga banna and pineapple sai yasakosu da yawa da folk, ya zauna yake bata tana ci ahankali, sai da yaga tasha daya sannan ya dauko abinci tace sai anjima zataci, bai tursasa mata ba yasan zatacin, ya shanye sauran fruit na bowl d’in kana ya fita zuwa sallar Isha’i…
Mamakin Jamila Ahmad kawai yake sai nan nan take dashi, shikuwa ya kyaleta yaga gudun ruwanta yana dawowa daga sallar Isha’i ya tarar harta kwanta ad’akinsa cikin night wears na riga da wando 3-qtr,  kwanciya yayi ya na d’an danne danne awayarsa, kawai sai jin mutum yayi abayansa an zira hannu ta cikinsa ta rungumeshi dake kwanciyar gefe d’aya yayi, cikin sanyin murya tafara bashi hak’uri da alk’awarin ta daina sharrin zuciyane, bai juyoba yace mata shikenan ya hak’ura, bata dai sakeshiba tadinga  jansa da hira tun baya warewa har yadan sake mata kad’an, ganin haka  yasa  tayi ta seducing d’inshi har saida ya fara romancing d’inta suka nufi wata hanya  tadaban..
Tun d’azu yake lallashinta akan tayarda taci abincin tak’i, k’ara yamutsa fuskarta tayi tace ” Wallahi banjin cin komine ko sphagettin balle wancan ta nunashi farfesun da yatsa, kawai ka k’ara bani banana shi zan kuma ci’ shafa fuskarta yayi na wasu seconds sannan yace “A’a yakamata kici wani abun kuma, kinga kar yunwa ta lahantaki fa’ saboda  yadage yasa ta bud’e bakinta yadinga bata farfesun kan dole lomanta na biyar ta tureshi ta nufi toilet tun akofarshi aman ya k’wace mata ta dingayinshi ba sauk’i, yana rik’e da ita ta baya,  sai da tagama yajata zuwa ciki ya wanke mata bakinta da fuskarta, yana ta jera mata sannu, tundaga wannan kaman an bud’e wa amaine kafin safiya sau uku tana k’ara yin aman gashi bawani abun kirki acikinta, gaba d’aya ta galabaita. Da safe ya nufi da ita asibiti aka buk’aci yimata test, sai sannu yake  mata wasu sun san ta tunda staff din asibitinne, ba b’ata lokaci aka fara musu komi amutumce

Sakamakon daya gani ne yasa ya k’ura mata ido sai dai bai mata maganaba sai smiling yake, kafin nan suka nufi mota sai da ya bud’e mata  k’ofa yasan ta shiga sannan ya rufe tare da cemata zai dawo tabashi 5 minutes, yakoma gun likita aka bashi shawarwari daya danganci masu ciki, sannan ya dawo yana driving d’ayan hannunshi ya rike nata, fuskarsa kaman gonar audiga, duk ya cikata  da mamaki ita bai fad’a mata komiba, da suka je gida hanata taka k’afarta yayi ya kaita d’aki, sai da suka gama nutsuwa sannan ya fad’a mata, wani irin abu takeji na shiga ranta sai hawayen farin ciki tanayi tana hawaye tare da k’amkame hannunsa…
BAYAN KWANA UKU

Kwance yake yana d’an danne danne awayarshi gefe kuma Jamila ke tsintar wake aplate,  yau ogan yace shinkafa da wake yakeson ci jefi-jefi suna hira, gyara muryarta tayi tace “Myone ya maganar kud’in bikin nan kuwa kaga abun sai k’ara kusontowa yake’ tashi yayi yazauna yace “Eh ina sane dashi anjima umar zai kawomin kud’in dake ya shiga bank yau’ cikin jin dad’i tace ” Allah yasaka’ yace “Ameen’
Aikuwa da yamma saiga kud’i an kawo masa ya d’auki 60k ya bata, ran Jamila k’al tunda harda k’ari yamata mai neman 50 yasamu 60,tasan zata samu damar yin bikinta cikin fantamawa, cikin kwanakin yasamu nutsuwa agidan nasa har ya fara d’an murmurewa.
Bak’aramar kulawa Khairi take samuba daga bangaren Adam harma da familynsu, adalilin haka har gida iyayen sai da sukazo wanda shine karo na farko bayan kawota da sukazo, ranar bak’aramin farin ciki tayiba, dake sun taho da kanwarta Humaira nazaman placement zatake tayata aiki agidan, kuma tasamu sauki sai abunda baza’a rasaba irin na ciki, don haka takoma aikinta, shikuma oga Adam yana danne zuciyarsa naganin bai daga mata hankaliba, don yaji cewar damuwa na iya zubar dashi  musamman yanzu dayake k’arami.
Tana zaune kan mirror stool tana shafa powder afuskarta,  ya shigo d’akin ta mudubi ta k’are mishi kallo sai ta tub’ure fuska kaman zatayi kuka, sanin dalilin dayasa tayi hakan yasa ya saki dariya mai sauti yace ” Sai hak’uri naje wajan an rufe nikuma sanin nawajan kikeso shiyasa ban sayo makiba’ mik’ewa tsaye tayi tana gyara zaman towel din jikin nata daya fara mata kad’an saboda fara cikar da ciki yasata ta fara buga kafarta ahankali da sigar shawagwaba tace “Kana shigowa naga ba leda nasan baka sayomin ba, kuma yau bamai bacci agidan Allah’ tare da kirkirar kukan shagwaba ganin yazauna yana mata dariyane yasa ta cillamashi tube d’in lipgloss da tashafa, ya cafeshi da hannunsa kara daukar wani tube tayi ta cilla mashi sannan yace ” Yi hak’uri Babyluv nasayo nasakashi a fridge ne ganin kina wanka saboda kar ya fara narkewa okhh?’ ya k’arasa tare da jan hancinta da d’an k’arfi sai da tayi kara ta biyoshi shikuma ya gudu ya nufi falo, dole ta koma don saka kayanta…
Gidan bikin cike yake da mutane kasancewar gidan mai girmane, daga cikin karamin falo kana iya hango yan mata sunfi yawa ciki saboda amaryar ma naciki sai hira ake jefi-jefi, wayartace tayi k’ara ganin sunan angone yayi appearing kan screen dinta ta mike tare da fita don tasamu daman dagawa, yan matane su biyar suke hira akan maza lumsy ta kalli faty tace “Wallahi  in kinsan yanda malam Ahmad ke burgeni har jinake inama yazamo mijina’ wani irin zafine ya taso azuciyar Jamila amma sai ta kanne tanaso taji waye wanda ake maganarsa, itama Fatyn sai ta kalleta tace ” Ai bake kad’ai ba mata dayawa acikin department suna sonsa, gashi ance matarsa gwanar kishine kodan banga laifintaba in akayi la’akari da had’uwar mijin nata’ Tagefensu ce ta cafe tace “Wallahi da Dr Ahamd Jahun zai mikomin tayin soyayyarsa da gudu zan amsa ba ruwana da wani kishi irin na matarsa’ wani irin zafi take ji zuciyarta nayi ta ture hannun samira dake cinyarta suna hira ta fara takowa zuwa kan kujerar da yan matan ke zaune tana zaro ido ga gumi yana yankowa daga fuskarta….

lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                         
loadιng………..✍🏻

*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*

© 2019

16

K’arar mari kawai sukaji yarinyar ta mik’e tace ” Kan ubancan wallahi sai na rama” masu hirar suma mikewa sukai cikin mamaki sukace “Baiwar Allah lafiyarki kuwa?” don sai tunanin su ya tafi ko irin aljanu gareta tace “ku rufewa mutane baki banzaye snachers wallahi kudai uwarku tayi asarar haihuwarku”  Yarinyar  da aka mara kuwa banda Faty ta riketa da tuni ta rama amman duk da haka mutsu-mutsu take ana nata baki akan sai ta rama, sai hayaniya suke zagi tako’ina suke zubawa junansu ana haka amarya ta shigo, ta dafe kirji na ” Na shiga uku wai meyake faruwane? Ya Jamila meye aka miki ne?” Lumsy ce ta fara fad’a mata kama baki amarya tayi tace “Sai dai kiyi hak’uri da marin da aka miki don wannan d’in itace matarsa kinga kuwa dole taji kishi kuna son mijinta, laifinta daya da ta mareki tunda kan rashin sanine” Nan aka dinga basu baki gaba d’ayansu yarinyar da aka mara (tsumagiya)  bata sake magana ba sai jijjiga kai da takeyi, suma sauran matan auren dake tare da Jamila gani suke tayi good shiyasa basuyi maganaba, takoma ta zauna kusa dasu suka cigaba da zugata, ita kuwa tsumagiya ta tashi tad’au handbag d’inta tace “Amarya sai mun had’u a dinner” Tana murmushi ta fice, amarya tabita rakiya tana bata baki ta kalleta “Bakomai kawa na fuskanta kishi ke damunta Nagode”+

KANO

Cikin sauri take had’a jakarta tunda H.O.D yace mata daga inda zasuyi aikin zata wuce gida, sallama Dr Kibiya yayi yace mata taje su wuce sallama tayiwa sauran collegues d’inta ta nufi k’ofa, suka shiga mota suka nufi emir palace.
Yau takanas ya nemi excuse kan zai tafi gida da wuri saboda yanayinta, har ya nufi unguwarsu yayi u turn zai je k’ofar k’waru ya duba kakansa sharp sharp sai ya wuce gida

Daga nesa yake hango su wani irin bugawa zuciyarsa tayi idan ba idonsa ke masa gizo ba kamar Khair yake gani da wannan mutumin na rannan kuma harda wani dake cikin suit da farin glass, binsu yayi har suka isa yaga ta fito shikuma wannan mutumin yana rike da wani box da bazai iya tantance yanda takeba, sun fito dukansu fuskarsu da yanayin murmushi harma Khair tayi wani murmushi da yafiso afuskarta, yanayinshi tanayine tana d’an rufe fuskarta irin sigar kunyarnan, yana kan nazari yaga sun b’ace masa , wani mahaukacin bugu zuciyarsa keyi har ji yake kaman ba oxygen a inda yake sai hura hancinsa yake don yaji iska ta shiga jikinsa, dama ba’a maganar hular dake kansa ya fada kujerar baya, sunfi awa d’aya basu fito ba abun yana bashi mamaki “Ko uban me sukeyi achiki could that be… No no this should not happen ni ba mabiyin mata bane hakan bazai faru daniba” Sai da aka share wajan awa d’aya da minti 46 yaga sun fit, wannan karon wani dattijone ya rakosu jikin motarsu tare dashi da wani saurayi kana ganinsu kaga kalar hutu da kudi da sarauta, sai dariya suke gaba d’ayansu sai yaga mutumin ya nawa Khair magana ita kad’ai ta sunkuyar da kanta tana d’an murmushi tana dan bashi amsa jefi-jefi nan ma dai sun d’au lokacin da yakusa 20.

Sanin in ya dad’e yana  kallonsu zai iya misbehaving gashi gurun is full of security yasa ya juya akalar motarsa zuwa gida, bak’aramin gudu yake ba kan kace me ya isa gidan nasu, da kayansa ya shiga toilet ya tsaya ruwa yana zuba kansa ko zaiji cunkushewar brain dinsa ta ragu, yana yanayin ne yaji k’ira ya shigo wayarsa dake cikin pocket d’insa har ta fara jik’ewa bai d’agaba sai yayi cilli da ita zuwa cikin bedroom d’insa saboda bai rufe k’ofar toilet d’inba, lucky enough  wayar ta fad’a kan dreesing mirror ta watsar da wasu abun sukayi k’asa, ya dad’e ahakan kafin ya fito ya zauna dirshan akasan floor

Cikin farin ciki ta shiga gidan ta ajiye handbag d’inta aparlour ta nufi kitchen, yau tana shirin tayi masu snacks da zata ajiye for a week tunda tasamu yau ta dawo da wuri tana da kusan 2 hours kafin ayi sallar la’asar, tana daga tsaye ta windown kitchen ta hango motarshi tayi mamaki “Yanzu ya shigo? Ko kuwa tun d’azu ne da zan shigone ban kulaba?” tana d’ora ruwan zata per boiling rice d’inta “Kodan bari naje na duba d’akinsa ko yana ciki” ta ajiye tukunyar

STORY CONTINUES BELOW
Asanyaye tak’arasa d’akin saboda yanayin da taganshi gabanta yana dukan uku-uku, zuwa tayi zata tsugunna akusa dashi ya buga mata wata mahaukaciyar tsawa “Karki fara nace maki karki fara, karki fara tunanin sakamin hannunki ajikina don ni bankasance mai k’azantaba, wallahi kin ban mamaki me kike nema aduniya? Meye kud’in zai miki?” Kanta ya kulle wai meyake nufi ne, wanne irin bala’ine wannan, ta rabu dashi lafiya da safe amma yanzu yana wasu maganganu she’s tired matsalar Adam is too much duk akan career d’inta haba, amma sai ta dake since ita keso don tana jin dad’in aikin bazata iya barinsaba ta k’ara matsowa zata rik’eshi tana kama hannun rigarsa yayi wani irin motsi dayayi sanadin wullata gefe can ta fad’i ta cikinta ta kwalla wani irin k’ara, sai alokacin yaga katobarar dayayi ta fad’a can falo ne wanda bedroom dinsu na d’an tudune sai kayi step d’aya ka hau inda suke, atake yayi saurin zuwa inda take “Khair Khairi?!!” kiran sunanta yake yana jijjigata idonta kuwa dakyar take bud’esu sai kuma yaga sunkoma sun rufe, agigice ya kinkimeta yayi asibiti da ita…
****                              **********
Yayi tagumi yarasa ya zaiyi kiran AK yayi ya gaya masa inda shikuma yace gasunan zasu  taho da matarsa, komi ya kwancewa Adam ga takaicin abinda yagani gashi yana ganin yanda jini ya dinga fita ta k’asanta kafin zuwansu asibiti, yarasa ta ina zai fara fad’awa gida don laifi nasane, ganin Dr yayi ya fito cikin  azama ya nufi inda yake “Dr don Allah meyake faruwa? Meya sami mata ta?” sai da yaja numfashi sannan yace “Gaskiya matarka ta bugu dayawa kuma kaga yanayin cikin k’aramine, amma zamuyi iyakar k’ok’arin mu muga yanda abun zai kasance” Take wata ajiyar zuciya ta kwace masa don da yayi tunanin Dr zaice ya zubene, gefe ya koma ya zauna ya dasa tagumi yana jinjina hauka da rashin control irin nasa, ahaka Ak yasameshi sukai musabaha yagaida matarshi, jansa gefe yayi yace wai ya abun yakasance tsaf yakaranta masa nan Ak ya bashi laifi bakad’an ba yace ” Ai saika bari kaji meye ya fitar da ita, karka bari kishi ya fara saka kake zargin matarka, kamanta tarbiyyar tane awajema fa ba samari ta tsaya tayiba duk da farin jinin da tayi, kuma ba ita kad’ai ka gani ba kasani ko wani babba aka nemi suje suyi wa aiki, haba Adam kasan girman zargi kuwa kasam girman zina? To ko da a hotel kaganta sai ka bari kafara bincike kafin ka zartar da hukunci” Yayi shiru yana nazari gaba d’aya sai yake jin kunyar kansama tun kan ya tabbatar, sun dad’e suna tattauna abubuwa dayawa shida AK….
F. U. D

Tunda tadawo take faman cin d’aci (fushi) kasancewarta mace mai zolayar mutane da yawa kuma faran faram, sai abun yabawa mutane mamaki sam tak’i walwala har wajan k’arfe shida na yamma, k’awar iya shegenta ce tazo tadinga janta da tsokana amma bata responding sai ma tsaki da takeyi akai akai ganin hakan yasa zinariya tace “K’awata waye ya tabamin ke ne, mu fasa taro mu bashi ciwon kai” Dafa kanta tayi tace “Yau an tab’oni ne wallahi wai wata banzar mace ne zata fidda hannu ta mareni? Akan ance ana son mijinta daga hira tsabar ita kucakace an gaya mata zamanin wannan haukar bai wuceba” Dafe k’irji Zinariya tayi tace “Mari? Lallai ta tab’owa kanta dama mun dade  bamu d’au maganaba agarinnan inaga so take mu sosa jikinmu da ita” Wani murmushi Tsumagiya tayi tace “Wannan ba irin wadda zamuyi dakanmu bace saboda tsaro don mijin nata nada kirki sawa zamuyi amana maganinta da ko had’uwa tayi taganni kwance kan cinyarshi sai dai tayi mana sannu” kawo hannu Zinariya tayi tace “Kodai wushishi za’a mata ko kuma ai mata kaduna to Abuja” Dariyar k’eta suka fasa Tsumagiya tace ” Ko kuma muyi mata Mbc Action ba” su duka sun san kalar yaren nasu, don baji suke ba sai dai su basa shiga huruminka in ka shiga nasune to ba sauk’i  suna abune at times kaman ‘yan daba, dakansu suka bawa kansu sunayen, asalin sunan Tsumagiya (Tayyiba wasu suce D’ayyiba)  ita kuma Zinariya (Zulaiha) saboda bikinne yasa ma suka tsaya don sungama nasu Exams d’in, suna cikin zancen ne Furaira tazo taji ta fashe da dariya tabasu labarin abunda matar tayi ta yiwa Salima, hakan yasa sukace aikuwa bazasuyi k’asa agwuiwaba sai sun koya mata darasi

Bayan sallar magriba Khairi tafarka daga baccin da aka mata allura, gaba d’aya sukaje gareta suna mata sannu shikuwa Adam kunyarta ta rufeshi, ko daya bata nuna  fushintaba amma dai asanyaye take komi, kuma tayi hakanne saboda kar afuskanci komi, Ak kuwa sai yaja matarsa suka fita don yabasu wuri, dake private hospital yakaita na kusa dasu bakowa adakin sai su, zai fara mata wata magana takwanta ta juya masa baya yayi shiru ita kuwa sai hawayene ke sauka a idonta tana nazarin rayuwarta, wani irin wahalallen ciwon cikine ya taso mata tafara murkususu da sauri ya fita kiran Dr

Dinner…
Gurin d’inke yake da mutane wanda mafi yawansu matasane Jamila da Ahmad yabarta akan zai zo d’aukarta karfe 10 shima don yasan na familyne, sai fara’a take don bikin yana mata sai busawa take ita lallai isashiya suna tsaka da hira da Samira da Mum Albany sai kira yashigo wayarta ganin uban gayyarne yasa tak’i d’agawa,  daga baya daya sake kira ana biyu sai ta d’aga “Kinsan munyi dake k’arfe goma zanzo ko? Ina fatan kingama  shiri kar nazo  kimin nauyinku na mata” sai da takirkiri dariya ta kisisina tace ” La basai ka wahalar da kanka bama zamu taho da Mum Albany,itama lokacin zata fita,  nasan ka gaji ka huta MyOne” sukayi sallama tace ” Aikuwa sai sanda aka ganni suka d’ora daga inda aka tsaya

….. Kallonta yake da sigar tausayi ya rasa yanda za’ai yagaya mata cewa cikin dake jikinta ya zube sakamakon abunda ya mata, hawayene ya sauko a idonsa ya d’auke, ta tashi kuma cikinta kad’an kad’an yake mata ciwo amma hankalinta yakasa kwanciya saboda tana jinta somehow, an basu sallama suka nufi gida, har lokacin wata sahihiyar magana bata shiga tsakani su ba, bata jima ba da zuwa gida takwanta ta fad’a tunanin rayuwarta.
Tunda suka fito daga wurin itada Mum Albany lokacin 12 saura, yanayin garin yayi shiru suna cikin tafiya suka hango mutane sunyi layi agabansu kad’an, cikin tsoro Mum Albany take k’okarin juyar da motar sai dai kash takasa saboda ita d’in learner ce bata dade da fara tuk’inba, dole suka nufi wurin tsabar tsoro dakyar ta tsaida motar daidai inda suke, wata irin dariya suke  irin ta tatattun ‘yan iska babban su yace ” Kai ku tsaya ke fito kizo nan” Ya nuna Jamila take cikinta ya bada k’ululu ta dafe kirjinta “Don Allah kuyi hak’uri” daka mata tsawa yayi yana daga kaftareren Adda suma sauran suka daga nasu  su bakwai har babban kenan, cikin hayaniya yace ” Ko ki futo ko mu cinnawa motar wuta ku mutu gaba d’ayanku” cikin  tsoro Mum Albany tace ” Ki tausaya mana ki fita k’ila kud’i zasu nema” Dakyar ta tako ta fito lokacin ne suka kara tahowa  zuwa bakin motar da wata irin karkarwa take k’ok’arin bud’e motar don  takoma….
Ko me zasuyi mata?
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_

   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                         
loadιng………..✍🏻

*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*

© 2019

17

Cikin dakakkiyar murya ta dabanci yace  “Karki sake kiyi tunannin komawa don wallahi zakiyi dana sanin rayuwarki” tsayawa tayi k’em tana karkarwa,yazo har inda take ya nuna wani da yafi kowa k’ank’anta acikinsu yace “B’ank’aremin ita nayi mata abunda tasabayi” Aikuwa tuni yaron yazo ya fincikota ya murd’e mata hannaye,daya zabga mata mari d’aya sai da hancinta ya fara fidda jini ya kara zabga mata ad’aya kumatunta,ta k’walla ihu sai da yamata kyawawa guda biyar kankace me hanci baki duka suna fitarda jini, shikansa kumatun ya suntume yayi taruwar jini,har ihunta baya fita ya nuna wani again ” Kai kawomin k’ulk’in nan na kwantar mata da k’aikayin dake tasowa jikinta” Cikin magana dakyar take cewa “Don Allah kayi hakuri wallahi bawani kaikayi ajikina” sai ya bushe da dariya yace “Hajiya dama ke bazaki ganiba mune muke gani kibari muyi miki magani don in kika bar nan bamai iya baki maganin nan” Gaba d’ayansu suka bushe da dariya sai da ya jibgi bayanta san ransa suka yarda ita awajen, in baka kuramata idoba bazaka gane tana numfashiba,ga fuska ta haye tayi sintim,Ita kuwa ta mota sai ruwan hawaye ke zubowa a idonta, atsorace tafito  tazo tana tab’ata sai ga ‘yan mata guda biyu sun fito ta hanyar da kattin suka koma, Tsumagiya da Zinariya kenan taya Mum Albany sukayi suka sakata amota sai asannan Tsumagiya ta sunkuya daidai idon Jamila tace “K’awa haska mata fuskata tagani dakyau” takarashe da dariyar izgilanci takalli Jamila tace “Kad’an kenan don hakama naraga miki saboda mijinki, inaso daga yau haukar da kike ma student kan mijinki kidaina idan bahaka ba wallahi sai na maidashi dadirona, nahanashi mu’amala dake namaisheshi sex machine d’ina muga ta tsiyar” ta juya ta kalli zinariya “Koba hakaba kawata, sai muhanata jin dandanonsa muga ta tsiya,kinsan ke ba komai bace me kika ajiye amatsayinki na mace banda gayyar shirme da hayagaga mutum kullum nacin abinci a cafeteria” duk da azabar ciwon da takeji bai hana maganganun Tsumagiya tunzurata ba wai mijinta za’ayi tasting, nan suka karaci mata maganganu na fitsara da iskanci,itakuma Mum Albany tsabar tsoro takasa cewa komi don is clear sune suka turo kenan don haka taja bakinta tayi shiru+

Tafiya take da gudu don ta isa G9 Quarters inda suke kenan don bazata iya kaita hospital ba. Ahmad da ransa yagama b’aci jira yake kawai yaga ta inda Jamila zatazo don ya zuba mata miss calls batai picking ba, sallamar Mum Albany yaji ya tashi tare da zubawa kofa ido cikin hawaye take cemasa Jamila ba lafiya,tuni ya nufi waje don yaga ya take aikuwa yasha mamaki shiga yayi motar Mum albany suka nufi Shekoni specialist kafin nan Jamila ta some takai sau uku

KANO

Tunda suka dawo ya nemi mata magana ta nuna bata bukata yaja bakinsa yayi shiru,shi kansa bai san ta ina zai faraba,duk da nisan da dare yayi ba ko digon alamar bacci atare da ita, tunane tunane kawai takeyi akan alak’arta da Adam da yanayin kusanci na iyayensu, yanzu tak’ara tabbatarwa da abunda wasu ke fada kan auran zumunci, bataso ko digo iyayenta susan abunda yafaru don bataso alakar da aka k’ulla tun kafin haifarta ta lalace, wasu hawayene masu d’umi suka zubo mata bata damu da ta sharesuba, tabbas Abba mutum ne ko yazaiji ranar da auranmu ya lalace? Don Alamu sun nuna rikici yana gaba har yau ban cika shekara d’ayaba da aure ba ace yamin sanadin miscarriage, tabbas issues na aure kan iya raba zumunci, tunowa tayi da yanda iyayensu suke

*ASALINSU*

Ummulkhiri (Khair) d’iya ta hud’u awajan mahaifanta Alhaji Aliyu Kura haifaffen garin Kura mazaunin Kano,da Hajiya Aisha Jahun Jigawa state kusan zamu iya cewa aurene ya zaunarta kano kuma ta hadu da shine tun kawoshi aiki da akayi garin jahun zamanin Jigawa na hade da Kano, sunada yara guda shida daya ta rasu yanzu biyar ne Ya Abubakar(Muhsin) yana aiki  sai Ya Sayyid yana Ghana karatu sai Khair da Humaira da auta Isma’il, yanzu Alhaji Aliyu  Permanent secretaryne a ministry of Education ta kano, sun taso cikin tarbiyya da kulawa, Khair macece mai madaidaicin kyau,amma Zubi Allah yamata da ko yar uwarta mace sai dai hassada yahanata fada bata jiki can sai albarkatu hakan yasa adam yakeji kaman idon kowanne namiji na kanta, tana da hakuri da kawar dakai sai dai takan ajiye abubuwa aranta suyi ta cinta,takanso zuwa wajan yan uwanta na Jahun ahutu sosai kodan taga kakarta gashi kowa na faman ji da ita, tana da warewa cikin mutane duk da kuwa surutunta baiyi yawa can ba, duk wanda yazauna da ita zai yabeta da hakuri sannan zakasan tanada burin aiki a asibiti, jamb ce tahanata shiga unversity shiyasa tayi karatunta a Hygien Lab Technician, wannan shine burinta
Adam Abdullahi k’waru mahaifinsa asalinsu yan kofar kwarune, mahaifiyarsa Hajiya hassu barebarin yobe ne iyayenta amma sun tashine a Kano,tanada yara guda Uku Adam sai Hafiz yana tare da Muhsin a Ughanda daga shi sai Safiyya,Hajiya Hassu nasan Yara mata shiyasa take son Khair tun tana k’arama fikonsu kadanne da Safiyya ahaife.

Haduwar jininsu ya samo asaline saboda makokantaka da ta hadasu akofar k’waru gashi ma’aikata daya suke aiki,haka Abban Adam yakesawa ake bawa Aliyun abinci saboda baida iyali,kafin Abban su khair yayi aure lokacin shikuma an haifi Adam, sosai Aliyu yake jan adam ajikinsa komi yakan sayomasa ahaka har suka d’inke sosai yazama kamar dan gidansu,kasancewar ba nisa daga gidan iyayensu abdullahi yasa suma sukasan aliyu kuma yana girmamasu sosai, ahaka har iyayesu suka saba suka zama tamkar yan uwa,ayanzu idan kaga khair gidansu kakanni Adam zaka rantse gidan kakanninta na jini ne,haka suma sukan dunguma suje Kura kafin rasuwar iyayen Aliyun, kaf duniya daga alhaji abdullahi har alhaji aliyu yanda suka dau junansu ko dan uwansu na jini albarka,kuma sai Allah ya kara karfafa abun tunda matansu sun hade kansu basa rikici, shiyasa da zasu sake gini suka sai fili a unguwa daya suka gina duk da ba ajere bane amma suna kusa sosai,yaransu ma sun had’e kansu don haka da adam ya bijuro da maganar Khair tamusu dadi, bakadan ba hatta cousins na adam sukanzo gidansu khair kaman yanda zusuje gidan uncles dinsu najini.

Adam namijine mai kyau a ilmi yana da tsayi daidai gwagwado don jikinshi zakace kaman ya taba gym ne, yana aiki yanzu a ministry of commerce sannan yanada shop na soft drinks da shopping, yana da kirki da aji amma babbar matsalarsa rashin iya danne bacin rai especially akan kishi sam idonsa rufewa yake,yana da fad’a in aka taboshi gason girma, aduniya bai taba jin son mace kaman Khair ba tun tana karama yafifita kan Safiyya dake Hajiya Hassu kan karbota raino ta hada, dake tanada son yara balle mata gashi bata haihu dayawaba, saboda son da yake wa Khair yasa batayi samari dayawaba kowaye ya biyota matukar Adam yaji labari sai ya watsa abun kuma ya mata hayaniya dolenta tadaina sauraran kowa, sannan kuma tana sonsa itama,

Akan iya dadewa bakaji tarihin abokantaka irin na iyayensuba domin shi alhaji Abdullahi sai daya kai permanent secretary yayi retire ya fad’a siyasa yayi dan majalisa sannan yayi senator, amma duk da haka bai yada amintakarsuba, sosai yakeson Aliyi duk da ya girmeshi shine amini kuma abokin shawararsa,kuma sabin abokan siyasa da yayi sunsha nuna hada yaransu amma shidai yafiso Adam din ya auri khairi

Rayuwa suke ba kyashi dan wane yafi nawa ko wani abun, lokuta da Alhaji Abdullahi yake jinya haka alhaji aliyu kan bashi jininsa sannan duk wata matsala tasa yakan karbeta ya magance shima hakan yakeyi, lokuta da dama sai kaga sunyi ankon kaya kusan komi tare sukewa iyalansu,kowa yana daukar d’an dan uwansa amatsayin nashi…Wannan kenan

Ajiyar zuciya ta ajiye abubuwa da dama sunsha faruwa tsakanin iyayensu da zasusa bazakaso zumuncinsu ya watseba, gani tayi ya shigo dakin ta  tuni tayi sauri ta juya bayanta don ayanzu fuskarsa kan kaita wani mataki na bacin rai, d’an tarin gyaran murya yayi, yanaso ne yau yasa ta huce so yake ya bata hak’uri don haka bai damu da juya bayanta da tayi ba ya karaso jikin gadon nata….

lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                         
loadιng………..✍🏻

*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*

© 2019

18

Duk da tabashi baya yasan tana jinsa sai dai tak’i magana “Khairi nasan ni mai laifine agareki, bani da bakin neman yafiyarki amma don Allah karkice zaki saka kanki damuwa ki rik’e abun nan aranki, inaso ko hukuncine ko wani mataki da kike ganin zaisa ranki ya huce kidauka akaina wallahi zan jure, matuk’ar bazaki bar damuwar nan arankiba, kisani lokuta da dama kishi kansa namiki hayani na b’ata miki rai, amma nakasa controlling zuciyatane ki tayani da Addua don Wannan bak’aramar masifa bace tunda gashi tana nema take tarwatsa mana farin cikinmu” Ko tari batayiba duk da kuwa kalamansa sun shigeta ba kad’an ba, gabansa sai dukan uku uku yake baisan me zatayiba, sai da yadau minti uku yaga bata da niyyar magana sannan yacigaba ” Don Allah Khairi karki bari wani agida yasan nine silar zubewar cikin nan, kinsan hankalinsu zai tashi ki taimaka karki fad’a musu kodan zumuncin iyayenmu” Yana zuwa kan maganar cikin nan kuka mai sauti ya k’wace mata tuni ta tafi tunanin irin azabar da ta nad’a akan b’arin nan duk kuwa da soyayyar da takewa d’an cikin nata, jikinsa yayi sanyi bak’aramar nadama yake jiba don ko ita da take jin cikin ajikinta bata kaishi sonshiba “Kiyi hak’uri Khairi kaddarace ta afka akan cikin nan kinsan babu yanda za’ayi naso rasa gudan jinina kuma..  Tashi tayi ta bar gadon zata shiga toilet tana matsanancin kuka  da hanzarin sa ya nufeta yace “Zan fita basai kin cutar dakanki ba kidawo ki kwanta kuma don Allah kidaina kukan nan har cikin raina nake jinsa” Jin furucinsa na karshe ne yasa ta watsa masa wata harara sai dayaji faduwar gaba don Khair bata fiya kallon idonsaba balle harara ta had’asu, yasan bata d’au abun da sauk’i ba, haka ya d’auki kafarsa ya koma falo ya shiga tunani…+
DUTSE

Babu yanda Ahmad baiyi da Mum Albany akan takoma gidanta ta kwanaba tak’i, acewarta tsoro takeji kar ko sun biyosu tun farko suzo itama sumata dukan kawo wuka kamar Jamila, haka suka sab’e daren gaba d’ayansu a asibitin, sai bayan sallar Asuba ne ya kawota gida sannan ne yafara tunanin shin ya fad’awa mutanen gidansu ko kuwa yayi shiru, kanshi bak’aramin kullewa yayiba, bai fad’awa kowaba ya shiga kitchen ya dafa tea ya soya kwaai sannnan ya taho ahanya ya sayo bread…
Tana kishingide akan gado yana mata sannu dakyar take iya bud’e bakin ta don ya kumbura suntum lebunanta sun yi kauri sosai, sai ambaliyar hawaye take ya mata tambaya yafi sau biyar akan suwaye suka mata haka ta kasa cewa komi, duk tausayinta ya lullub’eshi yasaka hannun sa zai rik’e nata ta kwalla k’ara don hannunma ciwo yake taji bank’arewa, ba’a magana sauran jiki don sunji dukan sanda, tallafar fuskarshi yayi yana kallonta ransa na suya don gaskiya an zalunci Jamila, shidai yasan baida abokin fad’a balle yace to koma waye haushinta ne yasa yamata haka saboda haka yakeso yaji, ko kuma yan fashine suka bukaci kud’i wurinta bata basu ba suka daketa, to amma meyasa basuyiwa Mum Albany ba? Kodan Mum Albany tace ita suka kira suka daka to amma batasan meye alak’arta dasuba gashi bakinta yak’i magana, fita yayi ya je motarshi ya sake dawowa tare da paper da biro yace “Kidaure ki rubutamin main event d’in da suwaye” Dakyar ta iya d’auka ta rubuta masa k’arshe ta rubuta “Don Allah karka ce zaka d’au mataki akansu nice na mareta gashi takamai mai bansan sunayensu ba” Abun yabashi mamaki kuma yaso yabashi dariya munin halin da take ciki ne yasashi bai kwashe da dariya ba, amma sai ya kanne ya dinga fad’a yana wallahi da yasan suwaye sai yasa an koresu amakarantar, sai ya kalleta yace “Dole amarya tasan su tunda sunzone don ita, kodan nasan plan da zanyi nagano suwaye, yanzu bari naje gun Dr naji halin da ake ciki” kafin ya fita sai da ya had’a mata tea sannan….
STORY CONTINUES BELOW
Simple gown ce ajikinta na material tana soya doya da kwai, abun ya bashi mamaki ya karasa cikin kitchen din kaman zai dau wani abu yace “Babyluv ina kwana? ” ta amsa masa batare da ta juyoba ta cigaba da kwashe doyar, ganin fuskarta ba annuri yasa ya koma parlour don yaga iya gudun ruwanta, tsaf ta jera breakfast dinta kan dinning ba tare da ta kalleshiba tace ga break nan ta nufi dakinta da mug ahannunta, bin bayanta da kallo yayi yace “Kome take nufi da hakan?” Biyo ta yayi ya murd’a kofar yaji arufe ta waje yake cemata “To ke bazakiyi bane? ” ko tari batayiba duk kuwa da taji, haka yajima atsaye sannan ya wuce ya tsakuri abincin kadan don sam ranshi ba dad’i, yasan fushinta badaina komi zatayiba amma baruwanta da harkarshi. Kasancewar Ranar ta kama asabar sai bata sanarwa da kowa ba monday takeson fara shiga asibitin don ta ragewa kanta radadin tayi hira cikin mutane, gashi jikin nata da sauki sosai, bata fasaba da rana ma sai da tayi abincinta ta fada masa tayi shigewarta dakinta anan dai sai ya tareta kafin ta shige d’akin nata yace “Khairi ya kike tunanin matsayin matar da take gaba da mijinta” shiru tamasa shikuma ya kafe ta da ido inda ita kuma ta sunkuyar da kanta, ganin ba maganar zatayi ba yasa ya matsa ta shige d’akin…
Jamila likita ya sallameta tare da jibgin magani, suna shiga gida ya taimaka ya had’a mata ruwan d’umi don tagasa jikinta,  aikuwa tana fitowa da tasamu tasaka short gown tayi ruf da ciki sai baccin wahala, sai da ya tabbatar tayi bacci sannan ya fita ya nufi gidan Kawun Jamila

Bayan gaishe gaishe dakomi  yace yanason magana da Amarya gashi dama lokacin ake shirin kaita gidanta, har suna cewa ya  basu ga Jamilan bane tazo, ita da tace da wuri zatazo, sai yace musu ai ta tashi da dan ciwon cikine shiyasa, nan suka ce aduba ta. Bayan Amarya ta fitone yace mata tabashi labarin abunda  ya faru rannan ta gaya mishi komi amma tace bazai san yaranba saboda ba ‘yan biology bane, amma yayi hak’uri kar yasa amusu komi “Karki damu bazan saka akoresuba inaso na tsorata sune saboda nan gaba karsu sake yiwa wani, don inda abun yazo da tsautsayi da sai mutum ya mutu kinga abu yazama babba, amma karki bari kowa yaji maganar  nan abakinki” da haka yayi sallama dasu ya fito kan hanyar dawowa ya musu takeaway, koda yake mutuniyar tsamin jiki ya isheta sai ambaliyar hawaye take tana wash wash sai zama yayi yacigaba da jinyar matarsa, in ajima ta fasa kara wayyo kuguna ko kaji wayyo kafad’ata,  da tausayi amma yanda kunburi ya maida muryar Jamila abun sai da yasa Ahamad kaikaice fuska yana dariya.
Washegari

Duk da d’aurewar da take masa daurewa take don tuni ta jima da yafe masa kawai tanaso nan gaba idan fushinsa ya tashi yadaina kokarin tureta don wata ran in abun yayi gaba zai iya dukanta, shiyasa  take so taiwa tufkar hanci, ciwon rai ke taso mata tunda bawanda tabari yasani shiyasa abun ke cin ranta, ita kad’ai take zaune a dakinta tayi nisa acikin kogin tunani kawai sai tafara magana afili “Meyasa kayimin haka, meyasa kakeso ka tarwatsa farin cikinmu, yanzu gashina ka biyewa zuciyarka kamana sanadin rashin cikin dake cikina, wai ni kake gudun hada jikinka dani har ka hankadeni kamar kaga kazanta kasa na d’andani azaba tare da bak’in cikin rashin d’a, tabbas zuciyarka tafi k’arfinka” kawai ta rushe da kuka maganganun tadingayi anata tunanin tana fada duk da bakowa hakan zaisa taji relief, tana jin hakan kaman tafad’awa wani ne kamar yanda wasu sukai believing fadar matsala kaman kayi solving rabin tane, sunyi cirko-cirko abakin k’ofar d’akin nata Safiyya da Humaira, sun jima suna rafka sallama ak’ofar parlourn nata batajiba shine suna shigowa sukaji tashin maganganu da alamar kuka yasa sukayi sak sukazo jikin wurin,gaba d’ayansu jikinsu yayi sanyi komawa sukayi kan seats na parlourn sannan Safiyya tace  “Humaira inaga zaifi kyau mu nuna mata bamuji maganar nan ba, sai munga reaction dinta kan case d’in in ta fad’a mana shikenan in bata fad’aba k’ila sun rufe maganar ne tsakaninsu, kuma kinga bai dace ba mu watsa al’amarin kodan farin cikin iyayenmu” ta gamsu da shawarar Safiyya saboda haka sai suka zauna aparlourn kowanne acikinsu da kalar sak’e-sak’en da yake, baya Safiyya bakaramin tausayin tane ke damunta ba,  sai ta danna number Khair, tana dauka tafada mata sunzo ta kashe

Sai da ta share hawayenta sannan ta d’auko powder ta goga tare da shafa gloss abakinta ta k’irkiro murmushi ta fito, ganinsu bak’aramin dad’i tajiba sukuwa sai nazarin yanayinta suke, haka suka deb’e mata kewa har dawowar Adam da zasu tafi sai yace su tsaya zai saukesu, alama yamata da ido akan ta biyoshi ganin da ido kansu yasa ta bishi bedroom d’insa koda taje tsayawa tayi agefe tare da sunkuyar da kanta yace “Zan kaisu gida don na sanar masu cewa kinyi miscarriege inaso idan an kiraki karki nuna da wani dalili” yanda yake maganar adaurene don baiso taji zata b’ata masa budget yaga  bata nuna saukowaba balle yaji ko zata boye sirrin nasu, sai da yaso bata dariya don  a ganinta borin kunyane ko kuwa nade tabarmar kunya da hauka, sai taki magana kawai ta juya tabarshi atsaye, dafe kansa yayi “matsalar mutane masu sanyi kenan in suka dau abu sai sun k’ona mutum” Ya fad’a aransa tare da fita..
Sai da yayiwa duka iyayen nasu sayayar Drinks Catorns sannan yaje ya gaidasu, anan ya sanar da Hajiya Hassu bakaramin damuwa ce ta bayyana afuskartaba tace ” Yanzu abun ba yau akayishiba kaki fadamana, bayan kai da ita bakusan kan komi ba ai tana bukatar kulawa da kuma shawarwari ko” sai ya marairaice irin damuwar nan ta isheshi balle kwana biyu yad’an fad’a saboda case din tace ” Amma abun da nakeso dakai kayi hak’uri Allah daya baku shi zai kara baku, zamuzo har gida mu mata jaje, amma yakamata ta huta koda na satine” An soso masa inda yake mar k’aik’ayi dama bayaso ta k’ara fita sai sun shirya, da yasanarwa iyayentama suma jajenne da ban hakuri, zuciyarsa fes ya baro gidan iyayen abu d’aya yarage shine yaga zuwansu batare da ta fada masu asalin abunda ya faruba.
Kwance take da singlet ajikinta sai wani Three Q wando, tana danne danne awayarta ya shigo d’akin take ta juya bayanta bayan ta amsa sallamar…

lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                         
loadιng………..✍🏻

*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*

© 2019

19

Har ya k’araso jikin gado ta side da fuskarta ke bata nuna tasan da inuwarshiba balle zahirinsa, hakan ya kanne ya ce ” Khairi sak’one daga gida” jin ya fad’i hakan ta sauke wayarta da tadaga ta kalli gefen fuskarshi tace ” Inaji” sai kuma yayi shiru ganin baida niyyar magana kawai tamaida kanta ga wayar “Ga wata leda nan Mama tace akawo maki sannan tace kike shiga ruwan zafi” kaman mai ciwon baki tace ” Nagode tunda ka hutar dani daga k’irkira wani abu na daban” yasan magana take son caka masa sai  ya cije lip d’inshi nak’asa yace “Khairi yanada kyau ace kin ajiye komi mun fuskanci gaba don Wannan abun k’addara ne, kuma komeye dalili ai ba iya nike da laifi ganinki da wasu mazan awani guri daban ne yasa hankalina ya tashi, har yau abun kan kai kawo a zuciyata” Sak tayi yayin da zuciyarta ta fara bugawa da k’arfi wani irin faduwar gaba hade da bacin rai suka mamaye zuciyarta har d’aci take ji abakinta, tashi tayi ta zauna daidai akan gadon tace “Gara da kafad’i maganar nan yau nasan matsayina awajenka, kawai ka fito fili kace zargi na kake, ko kuma bakai trusting d’ina ba, kasan illar Aure dake da zargi kuwa?” shiru yayi tabbas zargi ba inda yake kai aure, yanzu hawaye ke ambaliya afuskarta ta nufi jikin closet d’inta ta zaro babban hijab tare da juyawa ga bangaren bag hang nata ta janyo guda d’aya still jikinta na rawa kuma hawaye basu daina saukowa afuskartaba, atsorace ya nufeta ” Khairi me kike shirin yi ne? Gida zaki tafi awannan lokacin? ” tsabar yanda take jin jikinta takasa kwatar kanta maganarta ma sun koma kamar haki -haki, da wannan damar yasamu yamata runguma bata wasaba tun rana kwacewa har tadaina nan ne ta k’wace da kuka mai sauti bana wasaba, tanayi tana maganganun da zuciya ta hana su fita yanda zai gane, ba abinda ya iya sai “Sheeesh is okay don Allah kiyi hak’uri ki sassautawa zuciyoyinmu tabbas nayi kuskure da nakasa bincike da kuma zuciyata take ingizani ga mummunan zato, Babyluv wallahi na yarda dake kinsan da haka  kawai sharrin shaid’anne” dak’yar ya shawo kanta sai da tayi kuka to her satisfaction yanda taji dutsen daya tare mata wuya ya wuce, sannan ta d’inga ajiyar zuciya still bai daina bata baki da nuna mata darajarta da tsananin regretting da yayi ba, wani irin baccine ya kwasheta to dama tunda  abun ya faru bata samun isasshen bacci, don haka har yakaita gado ya rungumeta batasan me akeba, shikuwa zubawa fuskarta ido yayi yana yiwa kanshi fatan Alkhairi, d’an rikicin nan da tayi masa bak’aramin tsoratashi yayiba, fatan sa d’aya in ta tashi taji bazata koma gidanba kuma su dawo normal…+
DUTSE

Aranar Dr Ahmad yayi contacting abokinshi dake Sociology Dep don yanasan details akan su Tsumagiya, yana zaune gefen Jamila da bai dad’e da sayo mata balangu ba tagama ci, ya ce mata zai had’a mata ruwa tayi wanka, ta kalleshi anarke tace ” An ya zan iya kuwa banison koda tashi bakaji yanda nake jin baya na bane” cikin sigar lallashi yace mata “Ki daure dai kawai abunda nakeso kawai ki amsa don ni dakaina zan maki, na lura bakison gasa jikin naki yau zakiji  in namiki zakiji daban” zaro ido tayi tace ” Kace mene? Haba kamin wanka kuma haba MyOne sai agirma kuma aci k’asa, kawai dai zaka taimakamin na mik’e” Murmushi yayi yasan za’ayi hakan, don tun bayan incident d’in yake cewa hakan take k’i , hakan yayi kuwa ya taimaka mata sannan ne ta yarda tayi, sai da ya tabbatar ta shirya sannan ya fita zuwa sallar Isha’i…
Har ya dawo daga sayo mata kayan tand’e tand’en yaga bata tashiba, da alama baccin ya mata dad’i amma ganin time yana k’urewa yasa ya tada ta akan ta tashi taci abinci sai ta koma, saboda yanayin baccin da take ji ga kuka da tayi dak’yar take magana, wanda muryarta ba k’aramin fuzgarshi tayi ba, ba yabo ba fallasa tunda ya nuna mata kayan da yashigo dasu tamashi godiya kawai, haka taje ta wanko bakinta, anan ya fad’a  mata Mama tace yakamata ta huta in ta yarda gobe zai fad’a a office d’insu, da ‘to’ ta amsa mishi sai da yayi gathering courage d’insa sannan ya sake mata tambaya kan wad’anda yaganta dasu don gaskiya he wont have peace of mind until he know abunda yakaita Wancan  wurin, kamar yanda AK yace masa kuwa hakane wannan  mutumin daya gani sarauta gareshi a sokoto wazirine  kuma ana fakon rayuwarshi da  na yaronsa, shiyasa ma da rashin lafiya yasame yaron basuje can ba shiyasa suka nemi da atura masu  as a guest na kano government suka nemi aturo masu DR sai aka tura Dr Umar Kibiya don kwararene kowa yasanshi infact yana zuwa manyan hospitals per time, saboda ana bukatar wani abu da ya shafi LAB shine H. O. D yace atafi da ita, yafi yarda da ita sannan yasan zatayi abu anutse kuma komi zata gani bazata tankaba bata da gulma ko zarmewa..  wannan kenan.  K’ura mata ido yayi sai kuma ya janyota daga yanda take azaunen ya rungumeta yana d’an buga bayanta yacigaba da bata hak’uri asanyaye in a romantic way, sunyi missing dumin juna har ita kanta daga haka sai da suka rage zafi don da ya rike bakinta sai da yasa tadaina jin taste na ice cream da tasha alokacin , dayaga hakan bazata kaishi ba cire singlet din yayi na jikinta sukayi wasanni, yanda take jinta itama tayi missing dinsa basu taba tsintar kansu a yanayi na nesa da junaba for this long time, sai bata hanashiba duk da bata wani responding sosai,sai da ya dan samu nutsuwa sannan ne suka shirya bacci…..

  Su Tsumagiya ganin buk’tarsu ta biya tun washegarin ranar suka ware garinsu, yanzu duka anyi hutu ba wani students amakaranta, saboda haka Ahmad ya bar komi sai zuwa bayan hutu. Salima kam da taje gida sai da tabawa ‘yan uwanta labarin Jamila, dariya suka dinga mata baya immediate d’inta sai da tasa kukan shagwaba sannan nefa ta sami lafiya.
*Bayan wasu kwanaki*

Tun bayan abunda ya faru lahadi tsakaninsu sai ta dan sauko duk da basu koma normal ba, amma takan biye wa hirarshi sannan in ya bukaci wasanni da ita bata hanawa, amma shi afanninsa sai ya dage da cusa kansa awajanta, takanas ya tafi kasuwaya sayo mata  wani lace daya ji tana hira da Khadija aweek din da tazo mata jaje,  yaji tana fadin gaskiya tanaso ta sayeshi, tana fita rakiyar Khadijan ya shiga wayarta yaga pic dinshi,  ranar taji dadi sosai still washegari yaje ya sayo masa komi, kama da veil jeweleries da shoe and bag da zasu shiga da lace d’in yakashe kud’i sosai, itakam sai da ta nuna mashi karfa ya takura kanshi ai bai zama lalalle ta dinkashi kusa ba, yace mata bawani takura he can do morethan that ai yanada damar yine shiyasa, kuma karta manta ba ita ta nemi yamata ba, ya bata 10k na tailor, sai ma ya fake da ai yaga zai mata kyaune, ita kuwa ganin har colourn da tace shiya sayamata tasan tabbbas hirarsu yaji, duk hanyar da yasan zata had’asu ta mishi yar doguwar magana sai yayita, hakanan idan yanason abu agidan ko kitchen koda yaganshi sai ya fake da bai ganiba don kawai su had’u wuri d’aya, haka zatazo ta d’auko masa, tun bata ganeba har ta gano yana sani yake hakan, there was a time daya runtse idonsa akan lallai yaji ya shiga sai da ta hure mashi idon ta lura ma ashe bread yake ci da jam so ba wani  abu daya danganci yaji, ranar da yasa dariya ta k’wace mata kuwa sai da yazo zai fita yana sani yakurbi tea ba daidaiba ya b’ata mashi gefen bakinshi sanin sanda suna normal life zata goge mashi ne da kanta har yakan kamo hannunta in ta goge mashi ya mata peck jiki ko light kiss, amma ranar da yayi hakan sai da ta bari ya bude kofan ya fita daga nesa tace mashi ya duba bakinshi ta mirror na mota in ya fita, bai so hakan ba don b’aro-b’aro tagano a idonshi… Wannan kenan

Collegues dinta  Mata sunzo mata jaje a sakon su H. O. D kuma an bata two weeks ne,  nan ne ma Maryam Tafida ta bata wasu yan abubuwa da zatayi using saboda b’arin na gyara haka amma ba tarkaceba. Iyayen su sunzo inda suka mata jaje da shawarwari ranar har hawaye sai da tayj da zasu tafi anan Ya muhsin yace mata duk da tayi aure bata daina tab’araba meye na kukan, oga Adam ko cike yake da fargaba karta fasa kwai hankalinshi bai kwantaba sai dayaga tafiyarsu tsaf batare da ta cemusu komiba, don yana sane ya makale yaki fita daga gidan gudun kar taga baya nan tafadawa Ummi ko Mama. Suna tafiya ya dawo ya dinga shi mata Albarka ta cece shi kawai murmushi tayi batace  komiba.
Tana kwance yazo bayanta ya kwanta tare da ziro hannunsa ta kugunta yana shafa cikinta, bata yi motsiba duk da sakon nakai mata kai ganin bata motsawa ahankali yake kai hannunsa zuwa kirjinta, tagane kwana biyu  jaraba yakeji, sai dai tayi dariya ya manta tana jinin biki duk da ba haihuwa bane, kan dole ta biye mishi don ranar yana sani ta dinga tudashi da salon diffrent kisses style tana masa kuan shagawaba badaban, ogan kuwa tuni yakara gigicewa anyi kusa sati biyu ba mace ahaka har ya samu nutsuwa batare da kauce hanyaba

Jamila jiki ya ware inda Samira tazo sukai ta cika baki agidan,dake ranar Ahmad yana nan tazo dayaji suna kurin zasu yi wani abun kawai dariya ya dingayi daga dakinsa don yaji labarin ba abunds ta iya banda tsoro, daga baya ma sai ya musu sallama ya tafo Jahun….

lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                         
loadιng………..✍🏻

*NAMIJIN KISHI*
By  *JANNAH JAY*
Wattpad *@jannahjay8*

© 2019

20

Adam a tsakanin kwanakin 2 weeks da aka bata sai da yasan yanda akai yasa ta huce suka koma normal life d’insu, abu d’aya yake jira kawai jini ya d’auke mata, yasan kuwa soon don yaji ana fad’an in b’arine wasu baya jimawa kaman na haihuwa, da an mata wankin cikima da bai kai wannan lokacin ba k’ila. Yau  dukansu suna gidansu saboda bikin su Safiyya da za’a fara next week,  dukannin anko da komi an tanadar mata, sai dare suka baro gidan nasu gobe zata koma kan aikinta hakan yasa suna dawowa ba b’ata time tayi wanka tagama shirin baccinta ta kwanta, aranta tanaso su zauna for the first time ta karanta masa yanayin aikinta ko zasu samu wasu matsalolinsu su gyaru, bangaren Adam daya gama shirin baccinsa ya zauna jiranta don yasan yanzu tana zuwa d’akin nasa, bai fi minti 5 da zama ba ta shigo da sallama tana sanye da k’aton hijab sai da ta kwanata bayan ta kashe bulb na d’akin sannan ta cire hijab d’in nata ta ninke tare da sakashi cikin bedside na gefenta, shikuma ya kwanta sai ta zauna ta jingina jikin gadon tace masa tana buk’atar magana dashi yace “Okay ina jinki” ya zauna ta fara anutse “Dafarko inaso nabaka hak’uri akan saka damuwa da nake, saboda na zauna nayi tunani k’ila baka gama lak’antar yanda aikinmu yake kamawaba, ana iya d’aukarmu zuwa wani guri karka manta muna under government sannan ana iya canza min wuri at any time  zaka iya zuwa inda kake gani na kullum kaga na koma office na H. O. D ya danganta da abunda ya taso, kuma duk da ana kokarin ganin mace tayi taking issues na mata wataran tana iya kamawa ba wani kiyiwa wani namijin sani abun,hakan kuma yasa zakaga banda kaidar aiki nasa handgloves kodan darajar aiki zakaga at times inasa white handsocks saboda irin wannan tsarin, don Allah inaso ka dinga daurewa zuciyarka zargi ko wani abu,  kasani ba wani namiji awaje dana bata time dina dashi balle yanzu da na shiga matakin aure sannan ko zakaje cikin asibiti zakaga bana cikin ma’aikatan da kan saba da wani collegue kodai wani ma’aikavi da za’ace yazama friend dina ko kowa yasan ai mutimina ne babu wannan a tsarina, kasani most of time har mamaki kake yanda nake dawowa da wuri saboda da an tashi nake fitowa mata ma ban waremasu ba balle maza please kadaina saka damuwa aranka kabarmu muyi rayuwar farin ciki acikin gidan nan” Shiru yayi don baisan me zaice ba amma shifa kwata kwata bayason aikine  tagane, bazai iya jurar wasu mazan da itaba awajw d’aya, haka ya daure ya dinga bata hak’uri kan baya itama tana k’ara wayar masa dakai akan aikinsu… Wannan kenan+

DUTSE
Tun zuwan da Samira tayi ta tuna mata rashin haihuwarta, yanzune tagano sakankancewa da tayi don duk yak’in hana kishiya da take akan haihuwa ana iya saka Ahmad ya sake Aure, kwana biyu gaba d’aya ta tattara tunanin ta kan abun, tana zaune kan stool d’in mudubi tana gyara fuskarta ya shigo tare da bata wraffer kud’in don tace mashi zasuje gidan wani mai maganin gargajiya ita da Yayarta, bai hanata ba don ko shi yanason haihuwa auransu yana dad’a turawa amma sai da yayi calming d’inta akan komi lokaci ne, bai tab’a ji aransa wata damuwace da zai ga laifinta ko yaji rashin haihuwar zaisa yaji zai k’ara aureba, kuma an gwadasu duka a asibiti bamai matsala acikinsu kawai lokaci zasu jira, yanzu haka tana shiryawane zai ajiyeta gidansu sai su tafi, ta mishi godiya sannan ya fita..
*******                         ********
Khairi takoma kan aikinta  komi yana tafiya mata yanda yakamata, yau yakama friday normally akan tashi da wuri daga wurin aiki don haka da takoma tayi girkinta mai rai da lafiya, sannan ta fesa wankanta gashi tun alhamis da safe tayi wankan tsarki oganne bai d’ago ta fara sallah ba, tana zaune akan kujera tana kallon wani american film ya shigo tare da sallama, saboda yanayin yanda gaba d’aya hankalinta ya tafi ga TV bataji shigowarsa ba,  sad’af sad’af yake takunsa sai ji tayi an rufe mata fuskarta, tasan bamai mata hakan sai shi amma saboda tak’arawa abun armashi sai ta fara kukan shagwaba kaman irin ta tsoratane dariya yake  mata, kafinnan ya b’ude mata fuskar sannan ne taganshi ta tashi tare da zagayowa inda yake, kafeta da ido yayi cikin riga da skirt na wani voil lace da yamata cif cif figuren ta ya fita, bayama boobs d’inta da suka yi sama kana ganinsu sosai ta saman rigarta nan fa ya shiga starring tare da zuzuta kyaun da tayi har sai da taji nauyinshi…
Ba’abunda yakai rayuwar aure mai cike da farin ciki dadi aduniya, abunda Adam yake ayyanawa aransa kenan daya tuno abunda ya kwana da suka ci abinci d’azu, bak’aramin nutsuwa da faraga yagani afuskarta b, saboda haka yasan yau zaiyi enjoying night d’insa duk da yasan tana kan jininta, yana cikin tunanin ne ta shigo da hijab d’inta irin na jiya, sai da yaji fad’uwar gaba kardai yau baida daman jin d’umin jikinta, ta lura da sanyi da jikinsa yayi saboda haka sai ta kyalkyale da wata shu’umar dariya ta jan hankali ta zare hijab d’in ahankali, sanye take cikin wata fitinannen night gown ja mai shaking da kad’an tazo tsakiyar cinyarta, ba abunda ta boye na jikinta ga wani nutsetsen k’amshi dake fita ajikinta,  kamota yayi in romantic style ya lakuce hancinta yace “Babyluv harda zolayata ko? Bakisan yanda najiba i thought still baki yafe min ba” sai ta kalleshi da wani salo bai jira komiba yafara romancing  d’inta tana tayashi da duk wani sigar wasa da yazo mata dashi, hannunshi ya fara kaiwa k’asanta yaji ba alaman pad cikin kunnenta yace “Wow you have done with that thing amma kika k’i fad’amin ko?” ajjiye masa numfashi kawai tayi “uhmnn’ tuni suka cigaba da rud’a junansu da wasanni sannan ya karanto Addu’ar iyali da fatan Allah yasa ya zira kwallo cikin raga, ranar sai da Adam yayi aries don anfi sati uku bak’aramin daurewa yayiba, ita ma kanta Khairi bak’aramin missing mijinta tayiba, daren kam sai da ya shiga sahun manyan ranaku na rayuwar Auransu.

Bangaren Jamila kuwa maganin kwana biyu aka bata akan kar suyi wani sex da mijinta harna kwanakin, sai ana ukun hakan yasa yau ta tashi da shiri na daban shima kansa maigidan dake yasan da maganar yana yin Isha’i yadawo, aikuwa ya ga tarb’a ta musamman dan har dariya yayi, wato ita Jamila in kaga ana kula dakai har sai yakama tana  da bukata awajan mutum, tun daga kan night wears ta kunnashi kafin yakai hannjnsa gareta takai zai iya rantsewa a shekarun auransu wannan shine karo na uku da tabashi had’in kai bana wasa ba, don takanas ta tsaya ta karanta wani post namatan aure da usually in tagani ignoring d’insu take, amma ranar saboda target na d’a takaranto kala kala, shiyasa salon nadabanne agadon shi dakansa duk da cikin yanayin da suke sai da ya tamabayeta “Dama kin iya irin wannan kika barmu da boring life” bata iya bashi amsaba saboda yau ta saka duk mighty d’inta naganin sun cimma wata manufa, dake an bata shawarar style ma da yafi saka sperm namiji ya shiga can jikin  mace yasa tayi yanda akace suyishi, shikuwa Ahmad saboda enjoying ya bata komi na akalarsa, yasamu  abu ab’agas don da a normal days ne bazata yarda suyi sau uku arana ba amma ranar, sai da yagama first round yana maida numfashi badon ya gamsuba sai dai gudun halinta amma ga mamakinsa sai kawai ta k’ara b’ullo wani salo da ya kunnashi ta k’ank’ame masa jiki tana nishin kissa da yakan kunna wasu mazan, bata taba yimasaba sai ranar tuni ya birkitoto, ranar Ahmad yasan yana sahun isassun maza…. Jamila and her target

Asubar fari bayan ya dawo daga masallaci yaga Jamila tayi wata shu’umar kwanciya, baisan sanda ya kwashe da dariya ba lallai hud’ubar haihuwa takawo sauyi arayuwar Jamila, ganin yau saturday yasa yabi yarima asha kid’a ranar duk inda ya tab’a jikinta ba korafi, shiyasa duk wasu guntayen maita sai da ya kautar akwanakin da mai maganin ya tsara mata. Suma su Adam sabbin amare  suka koma wani tattali nadaban suke bawa junansu, dama su ba wani tauyewa kowanne acikinsu burinsa d’ayane yabi duk hanyar da zai farantawa d’an uwansa matuk’ar bai sab’a k’a’ida ba.
Su Khairi bikinsu suke anutse duk inda take bini- bini zaka ji kira daga Adam, har zolayarta yan uwa suke suna cewa ku duk da auranku ya tafi shekara baku daina ba, alokacin wasu suce suna burgesu, komi itace kan gaba da Khadija, hatta ‘yan uwansu Khairi na kura sunzo dana Jahun, shi dake Muhsin ba ruwansa har dinner akayi aikuwa ranar ko taku biyu bayaso tayi daga inda yake don baiso akalle masa mata, gashi ranakun tayi tas abinta, don ba yanda zaiyi da Mama ne da sai ya hanata zuwa, haka suka gama bikinsu amarya ta tare agidanta.
Suna cikin LAB wasu sukazo suka zo wajanta kan Dr Umar yace tayi masu test tace “To cewa yayi kuzo Lab ko kuma kuzo wajena?” murmushi matar tayi tace “Yace muzo kiyi mana test d’in ne don yace in bakinan mujira kidawo” Murmushi na kusa da Khairi yayi yace ” shidai Dr komi yafiso kiyi daya dangance shi hmnn had’uwar jini kenan” sai da gabata ya fad’i amma sai ta nufi aikin matar tanayi tana cewa dole ta takama collegue d’inta burki akan kar yake fad’in haduwar jinin nan, batason matsala sam arayuwarta…

lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_

   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                         
loadιng………..✍🏻

*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*

© 2019

   Wannan shafin complete na masu voting da comment ne.. Im appreciated

21

Sati Biyu Jamila tayi bata k’orafi akan duk wasu al’amura da Ahmad zaiyi da jikinta, in ka k’are masa kallo har d’an kumatu ya k’ara, shikuwa ya dage da shigo da fruits da su zuma abunda yasan kan k’arawa mace ni’imah through cima, itadai burinta d’aya wata ya cika da karb’o magani taje amata test taga ko akwai, don an fad’a mata gaskiya malamin yawanci in ya bada magani akan dace 99 percent, yana zaune kan carfet ya mik’e k’afafuwansa ya baza takaddu yana aikin result saura kwana tara students su dawo zasu kafe masu result before dawowarsu, ita kuma Jamila tana kitchen tana had’a banana shake aka doka sallama falon, ya gane muryar wace k’anwarsa ce Naja’atu cikin sakin fuska ya amsa mata ta shigo cikin d’auke da bucket k’arami da had’in gyada nayin kunu, sai da tafara gaidashi sannan ne yace “Wannan sak’ona ne ko kuwa na wani gidan” Dariya tayi tace ” Anya kuwa nakane, ni banji sanda ka nema ba, gidansu Yaya zan kai” yace ” Shikenan tunda sai an rok’a akeyi da mutum idan na shiga gidan gobe sai na ce nima ahad’amin” daidai lokacin Jamila ta shigo falon fuskarta ba yabo ba fallasa suka gaisa har tana tambayar Naja’atu Jahun, dake satin da ya wuce taje musu kwana biyu, tashi tayi tace “Bari na wuce saboda kaiwa sak’on, sannan Umma tace tanason ganinka cikin satin nan” yace “To shikenan ba matsala ki gaidasu” ya zaro 2k yace gashi tasa kati ta amsa tamishi godiya, ita kuwa Jamila tunda taji ance Umma keson ganinshi gabanta ya yanke ya fad’i tsoronta d’aya kar ace maganar Haihuwa za’a mishi, kamar yanda Samira ta nuna mata kan dangin mijinta zasu iya kawo mata cikas su saka ai mata kishiya, idonta tuni ya kawo ruwa, yafi minti biyu yana rubutu ya d’ago  idonsa yaganta cikin wani yanayi cikin  nuna kulwa yace ” Ya yadai wani abu ya farune?” Jijjiga mishi kai tayi yace “Gashi yanayinki ya canza da alama kuka kike sonyi, tunanin me kike?” yanzu ya mik’e ya nufi kan kujerar da take ya zauna akan hannun  kujerar ya janyo fuskarta  zuwa facing d’inshi yace ” C’mon indai akan haihuwane yakamata ki kwantar da hankalinki, Allah bai manta damuba matuk’ar kinga bai bamu yanzuba lokacin mune bai zoba” Sai hawaye shar shar ya rungema kanta ak’irjinshi yana mata maganganun lallashi ita kuwa kaman ansaka ambaliyar ruwa a idonta, hangowa take kawai anmata kishiya ya zatayi? ….+
KANO
Tun bayan bikin Safiyya sai yau ta shirya dake yakama Saturday Adam zai kaita yini, sanye take cikin lafaya da ta mata kyau sosai, tun ahanya yake nanata mata ba ita ba fitowa tunda dai tasamu ya barta ta nad’a lafayar, itadai sai binshi take da “to’ don bak’aramin dad’i take jiba, zasu had’e da k’awayenta sunyi da Khadija ma zata zo gidan amaryar next month kenan, yana parking cikin d’oki tayi cikin gida da d’an gudunta ” Aahh wane irin abu kike kika sani ko maigidan yana nan” burki tayiwa k’afafunta sannan ta saita kafafunta suka shiga tare, sai da sukayi sallama sau uku sannan amaryar ta fito cikin kwalliya mai kyau ta nufi Khairi ta rungumeta sai ga Ya muhsin shima ya fito, da alama fita zaiyi  tunda yaji jiya tana Khairi zata zo yace bazai zauna ba yasan zasu cika gidan da hayaniya ne, sai da ya zauna suka d’an tab’a hira da Adam sannan suka fita gab’a d’ayansu suka bar matan agidan, kamar jira suke suka b’alle bakin hira anan ne Safiyya take cewa Khairi “Dama haka auran yake? Gaskiya Aure wata makaranta ce ta daban da baka isa kagane taba sai ka tsinci kanka aciki” Murmushi Khairi tayi tace “Kwarai kuwa ko ya wani zai zauna ya baka labari bazaka ganeshi kai tsayeba, Ina  fata dai komi lafiya” suna cikin maganar sai ga Khadija ta shigo nan dai gida ya d’au hira, rabin hirarsu ya ta’allak’ane ga shawarwari da kuma abunda ya  danganci kitchen, sannan ne suka fad’a kan hirar bikin Khadija da za’ayi…
STORY CONTINUES BELOW
**********                     *********
Zaune take ta k’ura mata ido tana jiran taji me zatace, cikin tausasa murya tace mata “Jamila lafiyarki k’alau kuma bakya d’auke da komi” d’ora hannunta tayi akanta tace “Nashiga uku na lalace” lokaci d’aya hawaye ya fara sintiri akan fuskarta, kwantar mata da hankali Farida take tace “Ai kigodewa Allah tunda kince likitan daya dubaki kwanaki yace lafiyarki k’alau kinga kenan at any moment kina iya tsintar ciki ajikinki, kawai lokacin kine bai zoba k’ila Allah ya miki wani tanadine, kika sani  ko aries zakiyi ki haifo triplet lokaci guda” itadai sam nutsuwarta bata nan sati biyar kenan tana dagewa agado da bin k’aidar komi ace babu, yanzu ya zatayi ne wai, ahaka tana cike da tunani ta k’ira wayar Ahmad ganin bai d’aga ba kawai ta yankewa kanta shawarar tafiya gidansu taje tasha kukanta ta more, don ta lura shi bai damuba tunda zai iya kawo wata ta haifa masa, ita ke cikin matsala, daga nan asibitin ta samu adaidaita tayi gidansu, tana shiga ta fad’a kan kujera ” Hajiya na shiga uku” cikin fargaba mahaifiyarta  tace ” Kin shiga uku yan nan meya sameki? Ko Ahmad ne ba lafiya?” sai da tad’au mintina tana kuka sannan tace mata an duba magani baiyi aikiba, sai asannan uwar ta saki ajiyar zuciya tace ” Haba Jamila daga farawa da iyawa karki manta duka auranku baiyi shekara biyar bafa, kuma ma meye Allah baya b’oyewa, ki kwantar da hankalinki zamuje  gun wani Dr sai asake gwada wata sa’ar agani” dakyar suka samu suka lallasheta, shikuwa Ahmad daya biya ta asibitin yaga bata nan sai ya kirata, lokacin bata wayar take ba sai k’anwartace ta d’aga  tace masa gata agida, sannan ne ya nufi gidan nasu, yana zuwa yaga mutuniyar tasa idonta yayi ja har d’an fad’awa tayi, mahaifiyarta ta musu nasiha da kwantar da hankali tace nan da laraba tanaso yabasu dama akaita, ko kuma ta had’asu da Dr da zai iya duba Jamilan suje tare..
Tun ahanya yake aikin lallashinta inda zuciyarta kawai take bata raina mata hankali zaiyi shi bai damu ba saboda yasan in yakara aure ai adad’in sane, in bata mantaba saura baifi sati biyuba su cika shekara hud’u da Aure, wadanda akai auransu a month d’aya wasu yaransu biyu wasu kuma suna jiran na biyun, masu kwanika kam sunyi uku, har suka isa gida hankalinta ba kwance yake ba, ranar shiya gama komi don da tayi wanka lafkewa tayi agado ta shiga tsananin tunani,, still bai fasa lallashintaba. Yanzu suna kwance don shi har bacci ya fara d’ibarshi ita kuwa baccin yak’i zuwa , zuwa tayi ta rungumeshi ta baya, cikin bacci sama – sama yaji ruwan hawaye na shiga singlet dake jikinsa ya juyo ya rungumeta yace mata ” Sweety har yanzu baki hak’ura bane? Sau nawa zan gaya miki rashin haihuwar nan ko daya bazai rage duk wani abu dakike dashi a wajena ba, ni nasan Allah  yana sane damu” sai da taja sheshekar kuka tace ” Kamin Alk’awari bazaka k’ara Aureba” Ras!!! Gabansa ya fad’i  shi bai isa yace  bazai karaba, duk da kuwa ayanzu baiga wata yarinya da ta kwanta masaba, yace mata “Dama nayi mamaki yanda lokaci d’aya kika birkicewa haihuwa, bayan da baki taba nuna damuwarkiba sai yanzu, kina tunanin kan Haihuwa zan k’ara aure? Wayasan tsakanin nidake waye bai da haihuwar ta iya yiwuwa nine silar hakan, don haka karki damu kanki kinji” cikin damuwarta kaso arba’in ta tafi amma sai ta ce masa ” Kana ganin daga gidanku baza’aso ka k’ara Aureba, karka manta kaine namiji na farko agidanku, tsoro nakeji” ta k’ara k’ank’ameshi tana nishin kuka ” tsoro nakeji kar wata ta shigo rayuwarka, wallahi bazan iya jurewa ba ina ganin zuciyata zata iya bindiga idan har na tabbatar wata na dauke da igiyar auranka” ta k’arasa da kuka sai aikin lallashinta yake daga nan lallashi yakoma zazzafar soyayya… Hajiya Jamila ta Ahmad
KANO

Sun shiga hidimar bikin Khadija gadan-gadan amma kwana biyu tana fama da lalaci, sam jikinta sai take jinshi very weak, hatta collegues d’inta sunga ta rage zafin nama a aiki, suna zaune ita da Maryam Tafida bayan sun idar da sallar Azahar Khairi ta nemo mai sai da awara, har yarinyar tagama zuba masu yaji zata tafi Khairi tace “K’anwata d’an k’aramana yajin mana, ko shima sai an kara kud’i” tafad’a da sigar zolaya yarinyar tayi murmushi ta k’ara mata, sai da yarinyar ta tafi Maryam tace “K’awa anya baki harbu ba kuwa, yanzu meye laifin wancan yajin? Ni da har ina ganin kaman ta samana dayawa” Sai da ta dangwali yajin takai awarar bakinta tare da lumshe ido tace ” Bana jin hakane amma dai kwana biyun nan wani d’an karan kwadayi nakeji, baya yaji don jiya da nayi wata jallof nikad’ai na iyaci” Dariya Maryam d’in tayi tace ” Aikuwa ki duba kanki don b’arinki ya tafi wata biyu da yi mai yiwuwane kiga cikin” Lumshe idonta tayi tace “To Allah ya tabbatar” sukayi dariya gaba d’aya. Kamar koyaushe tana zuwa shirin girkinta tafara ta d’ora tafashen nama akan wuta tasa kayan k’amshinta komi su thyme da garlic da albasa, ta d’ora ruwan da zata dafa macaroni don yanzu ita take muradin ci, bayan ta fere irish guda hudu manya tasakasu cikin ruwan, tayi alwala ta shiga d’aki yin sallah, bata gama azkar ba ta fito tanayi abakinta ta nufi kitchen,  kamshin tafashen nama nan yana dukan hancinta taji wani irin juwa da amai ya taso mata, da gudu tayi toilet d’in cikin falon ta d’inga kwara amai, tana wanke bakinta ta dawo falon amma ina wani sabon aman ne ya taso mata kwata kwata kamshin nama bazai iya barinta ta zaunaba, lokacin ne Adam ya shigo da saurinsa yaganta kwance ak’asa tana maida numfashi, da hannu take masa alama ya je kitchen tace “yakashe wuta” haka yaje gaba d’aya ya kashe harna ruwan kafinnan ta k’ara wani aman, sai daya taimaka mata ya wanke mata baki ya kaita d’akinta, tunowa yayi wancan cikinma haka tafara tuni wani murmushi ya k’wace masa yace “Allah ka tabbatar” Ya shiga d’aki tana kwance ta lumshe idonta bakknta ba abunda yake buk’ata illa taji abu mai yaji, sannu yake jera mata bayan ya zauna agefenta cikin  sanyin murya tace “wani abu nakeson cifa, don Allah kayi min sauce kawai iya attaruhu da albasa, ruwannan kuma macroni nakeson dafawa” Kama bakinsa  yayi yace “Babhluv wace miyace zallan attaruhu kuma ai sai k’irjin mutum yayi ciwo” aikuwa tuni ta kwararrabe zatayi kuka tace ” Nidai shi nakeso bazan iyacin komiba, in bazaka iyaba ni zan iya” ta fara mutsu- mutsun tashi yace “Kiyi hak’uri zan yi browsing naga yanda ake ko Safiyya ta fad’amin” fita yayi yana d’an ciza yatsa shi bai iya dafa komiba in ka d’auke ruwan shayi da farar taliya, k’iran Safiyya yayi ya fad’a mata sai ta kyalkyale da dariya yace ” Ke wallahi karkiga kinyi aure zanyi maganinki, ki turomin method yanzu kuma karki sauka online don idan inayi zanke haska miki in tayi kice tayi” haka ta danne dariyar ta tace ” La yaya tankwa take nufi wanda normally yan boarding ke tafiya dashi baya lalacewa da wuri, amma in da d’an yawa zakai zaka iya saka  tumatir d’aya ko biyu ko uku,kasa attaruhu da albasa enough da mai sai maggi, haka ake soyashi” yafara grating attaruhu dayazo kan albasa yaji yaji ya shige masa ido haka  yad’inga micin cina ido yanayi, daya fara soyawa sai ya kirata ta vedio call ya haska mata tace yak’ara barinta, ahaka dai ya had’awa khairi miyar nan, dama already ya zuba macaroni yana dubata, ya zuba aplate yakaimata, ta tashi yanda kasan   mai tsananin jin yunwa haka tadinga ci tana lumshe idonta, daukar  spoon d’in yai yakai loma d’aya,  da sauri ya furzar ya kai hannunshi side daya dicing mata irish d’in yadinga ci, sam baiji normal ba sai da yaje kichen ya hambud’i madara abakinshi ya dawo yace “Babyluv yanzu wannan abun kike iyaci? har yanzu bakina fa bai daina yajiba” kyalkyalewa tayi da dariya tace ” Haba dai kar ka bada maza mana” agabanshi yaga tana shan miya da spoon kawai tsayawa yayi yana kallonta full of suprise gefe d’aya kuma murnar cikin yake… To sai dai muce Khairi Allah ya inganta
   Kwana biyu comment yayi shiru fa

lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                         
loadιng………..✍🏻

*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*+

© 2019

  Wannan shafin na masoya Namijin kishine dake Watsapp ako’ina suke… 😍

22

Kusan zamu iya  cewa Adam yafi farin ciki da wannan cikin akan na farko, har Addu’a yake Allah kar yasa yayi wani abu da zai kawo musu cikas akan wannan cikin, yana k’okarin danne abubuwa dayawa  koda zai ga Khairi da wasu Cousin dinshi ko nata yana d’an dannewa, don tabbas haushine baya fasa ji koya yaga tana fara’a da wani namiji. D’aura d’ankwalinta take akan dogwar rigar cotton material dake jikinta sannan ta d’auko veil d’inta ta d’ora akai, ta juya ta kalleshi tace “Nashirya” inda idonsa k’yam akan kugunta daya k’ara fad’i yayi shiru kaman baiji me tace ba, sai da tak’ara nanatawa ya kalleta yace ” Gaskiya inaga yau bazaki aikin nan ba” cike da mamaki  tace ” hahh amma dai wasa kake yi ko?” don ita takawo irin  zolayar nan ne na mata da miji, d’aure fuskarsa yayi yace “Yace ko kusa da gaske nake,  wallahi banso naga k’afarki ta taka k’ofar gidan nan” ya tashi tsaye ya juya zai bar d’akin, take taji ranta ya b’aci har hawaye ya fara suntiri afuskarta ” Don Allah karka min haka mana, kaga last month fa nayi fashi akan bikin Khadija, yanzu kuma wane excuse zan bayar, kadad’e da sanin inason kiyaye halak d’ina” a zafafe ya juyo yace ” Nidai nace yau bazaki fita ba matuk’ar nine mijinki kuma na isa dake” yanzu  kam ta tabbatar da gaske yake ba da wasa ba don haka ta zauna akan gado, ranta na suya ita takan rasa gane kan Adam lafiya lou zaka ganshi yanzu amma in ya birkice sai ka rantse abu aka mashi.
Tafiya yake yana sak’e- sak’e aransa ” Dama ni sam aikin nan baya gabana, bazata gane bane tunda dana yarda bawai ina nufin zan kyale bane, dolene naita hanata har takai ai mata query, hmm dani  suke zancen” sosai yake  jin d’adi yau tunda yasan ya  hanata fita, don haka ana tashi daga office gidan Sabeer ya fara zuwa suka d’an taba hirar sannan ya nufi nasa gidan, koda yaje an fara  kiran sallah don haka ya fara shiga masallaci sannan ya dawo, yayi tunanin zaiga tana fushi amma sai ta tarbeshi as in komai normal, ta gabatar mishi da abinci yana ci yana bin ta da kallo cikin bumpshort da armless top, ta jima bata tsuke mishi kamar hakaba don haka ya gigice sai da yayi romancing d’inta kafin Isha’i..
DUTSE

A lalace wajan masu magani uku su Jamila sukaje kowanne da nasa salon tsarin amma shiru kake ji, kwana biyu saboda  tasaka  damuwar aranta har rama tayi, yanzu haka tana zaune akan kujera suna maida zance da Samira tana k’ara nuna mata dole ta bazama neman haihuwa koda sanin Ahmad ko babu, don shi baida matsala dole taga yana calming d’inta da sunan k’addara, ta rafka tagumi tana tunani daga baya tace “Samira bari na tashi naje naga magriba na neman yi, sai kinji ni awaya zamuje,  kacako jibi k’ila asake wani” sukayi sallama sannan ta nufi gida, bata fi minti uku da shiga gida ba ya shigo cike da gajiya da tsananin yunwa, baiyi mamakin ganin dining wayan ba abinciba, don tun lastweek ta fara dawo da d’abi’arta dama ance mai hali baya  fasawa, haka kurum yaji ransa ya b’aci don yunwar bak’aramin kamu ta  masaba, tunda ya amsa sannu da zuwan da tamashi taga ba annuri fuskarshi kallonta yayi ad’aure yace “Kafin na dawo daga masallaci ki samamin abinda zanci” bin k’eyarshi tayi da harara tare da jan siririn tsaki, ta nufi kitchen ta d’ora ruwa sharp sharp ta dafa indomie wanda sai da takusa gamawa ta zuba 2 spoons na miya aciki, sannan taje ta d’auko juice afridge da cup ta ajiye masa, ita already taci abincinta gidan Samira sai k’ila dare  ta samu wani abun taci before ta kwanta. Koda yadawo ya tarar da indomie baiyi mamaki ba, loma biyu yayi ya ajiyeta, ya d’au key din motarsa  ya fita zuwa bakin titi ya sayo nama da gurasa ya dawo gidan, sai da yayi nak sannan ya shiga d’akinsa a inda ya zauna taga wani ledan daban da bai tab’a ba, tasan nata ne ko kunya bata jiba ta d’auka ta adana shi akitchen sai 9 zata nemeshi.
STORY CONTINUES BELOW
Yau dake ya makara sai 8:30 ya tashi yaga tulin miss calls, sai da yayi wanka yasa kayanshi sannan ya bi, daga can b’angaren ake sanar mishi tulin masu k’orafi dake jiranshi abakin office d’insa, jan tsaki yayi haka zaita fama da masu  complain an sa musu absent ko wani baiga score d’inshiba, cikin sauri ya fito ya tarar ta ajiye bread da ruwan zafi, ta d’ade da sanin bayason tea haka yafiso ahad’a masa shi adafa, ya lura tsiyar ta takeso ta dawo da ita, zai ga k’arshen rashin kunyarta  kuwa yanzu da wani maganin ance ayi wasu intercouse da kaga tarairaya saboda  k’in kishiya, amma zaiyi maganin ta soon, ya lura tana sane take komi bawai iya kula da mijin ne bata  iyaba tsananin k’iwa da son jikine, don haka bar mata table d’in yayi ya fita.
Suna tsaye dayawa abakin office d’in daga mata har maza kallo d’aya  ya musu ya d’auke kai, sun san baida magana amma yau rashin annurinsa ya fita daban, daga nesa Sumayya take zungurar k’awarta tace ” Billy kinga fuskarshi kuwa? Anya yau da nasara? Gaskiya kizo mutafi don ni banason wulak’anci” jan tsaki billy tayi tace ” Matsala ta dake saurin karaya, wai ya zamu yarda adinga mana walle-walle aresult haba absent fa where as munyo komi ai irin haka sai agida ace muna dodging class ne” shiru tayi ta sunkuyar da kanta, haka aka d’inga shiga masu complain har akazo kansu Sumayya lucky enough komi ya tafi daidai sai sujira gyaran, haka zaita fama da d’alibai baya mata wasu da niyya zasuje suyi ta masa  karairaya, inda in ya kalli yarinya cikin ido sau d’aya sai ta nutsu.
Sai 1:46 ya nufi masallaci yayi sallah anan suka had’e da Dr Umar cikin fara’a suka tab’a hira, yamutsa fuska Ahmad  yayi yace ” Bari naje cafeteria naci abinci yunwa nake ji” dariya Umar yayi yace ” Kazo muci nida nake da k’annai da diya a skl dinnan, an kawo min abinci” harararshi yayi yace ” Kai dai  baka jin kunya wallahi sai kasamu abincin yara kaita zurawa cikinka, yakamata ka fara masu cefane wallahi, ko kuma kahana madam zuwa Yola kowa ya huta, ni har kasa naji kunya” Dariya yayi yace ” Kaga kar kayi fulako kazo muje, ka tuna wani chips da mukaci kwanaki to yarinyarce yanzu nan wani cefane na musu shekaranjiya, shine yau tace don Allah zata kawo man abinci, suna nan cikin basket” haka dai yai insisting sai ya bishi, inda k’arshe tare sukayi office d’inshi dake chemistry department, pan cake ne tayi sai doya da ta soyashi white tare da liver sauce,sai pepper fish kad’an da ta mashi had’in da attaruhu da albasa suka lik’e jikinshi da yankakken cucumber agefenshi, daga gani zaiyi d’an yaji, gefe d’aya an dafa tea sannan ta had’a masu oat, sai da Ahmad ya kalli oat d’in yace ” Wallahi na dad’e rabon da nasha abun nan” kallonshi yayi yace “Haba dai laifinkane amma, baka sayanshi ne ai da zata had’a maka abun shaf shaf ne fa” shiru yayi suna nan dan gongoni yakai biyar, kawai Jamila bata da lokacin had’a mashi ne, sai da suka gama taf suke jin su ya kalli Umar ” Kai gaskiya yarinyar nan mijinta ya more arayuwarsa, amma shekararta nawa?” d’age gira Umar yayi a sigar zolaya yace ” Ma guy kodai kana ciki ne” Dariya yayi ya mik’e tsaye yace “Kaga tafiyata in na biyeka sai na jima anan, bayan ga aiki can na jirana” intai wari maji cewar Dr Umar

BAYAN KWANA BIYU
 
Tana shiri tana Addu’a aranta akan Allah yasa yau ya barta ta fita, sai da tagama komi ta dawo d’akinshi don tace mashi ga breakfast, taganshi kwance baisa kayan da ta d’auko mashi ba, asalima ya kwantane yana latse-latse awayarsa tace ” Ya naga bakasa kayan kaba, kaga takwas takusa kazo  kaci abinci” sai kuma ya tashi “ahh namantane kinga yau ban fad’a maki na tashi da sha’awar d’an wake” kebe fuska tayi ta kalli agogon hannunta 7:41, amma gudun kar taja dalilin da zai hanata sai tace “shikenan’ ta nufi kitchen tana d’ora ruwan ta koma dinning ta zuba dayan break din alunch box, tasan time da zata gama mashi d’an wake bazai yiwu ta zauna ciba, dawowa falo yayi ya tasa TV yana kallo, haka tagama ta ajiye mishi ta d’auko su tomato ta fara yanka mishi, tsabar sauri wuk’a ya shiga hannunta kadan, haka tacigaba, shikuwa  yana lura da ita sai da tagama had’a mashi vegetables d’in tasa mashi, sai ya kalleta yace ” Kinga gumin da kike had’awa kuwa tsabar sauri, ni inaga tunda kin makara why not kibari sai gobe, gashi naga kaman hannunki ya yanke” yanzu tagano neman dalili yake tunda gashi ta yanke da bai nuna yasaniba sai yanzu, just small cut ne zai hanata zuwa office kaman ba mace ba, ta kalleshi na tsawon lokaci cike da b’acin rai, ta juya ta koma d’akinta, hakanan yaji ba dad’i aransa din yaga bacin rai akwayar idonta sai yabi bayanta ” Babyluv ya akai muna magana kuma kika dawo ciki ke baza kiyi break d’in bane?” maganarshi ce ta mak’ale abakinsa ganinta yayi ta zauna ak’asa ta d’ora kanta akan k’arshen gado, kobai duba fuskarta ba yasan hawaye take “Nifa matsalata dake kenan in mace na da ciki  sai saurin hasala, ni fa wasa nake miki muje yanzu kici abinci zanyi dropping d’inki, nadawo in antashi ma ni zan d’auko ki, yau bani zuwa office” sai da ta share hawayenta tace “A’a kabarshi basai naje ba, tunda kaji aranka bakaso kawai abarshi” tsura mata ido yayi na wasu seconds yace ” Sai dai in zuciya kikai” girgiza kanta tayi ta k’irkiro dariyar k’arfin hali ta nufi falon, yabi bayanta kawai don gudun damuwarta da cikine yasa shi barinta bawai don yanaso ba, dakansa yakaita office  har collegues d’inta na zolayarshi, daidai zai fita ya hangi wani classmate nashi  awajan office na Dr Kibiya saboda haka ya nufeshi sukai musabaha, alokacinne  wani ma’aikaci Lab ya shiga office jim kad’an sai gashi ya fito da Dr yana ce masa ” Wallahi kuwa gatanan yanzu mijinta ya kawota, inaga zaka iya mata maganar yau” su sam basu kula da Adam dake adjacent d’insu ba, zuru yayi ya bi bayan  Dr Kibiya da kallo alokacin ji yake kaman ya je ya d’inga dukansa har sai ya daina motsi, haka dai ya danne zuciyarsa ya  nufi gida, daya tuna wai wata magana sai shaidan ya tafi gaya masa hauka da hankali, har ji yake kaman ana baking azuciyarsa..
****            ******
Tunda suka je kacako take ta fara’a don an zuzuta mata aikin mai maganin, don haka da ta dawo ta sami nononta kindirmo ta dama maganin tasha, tasan nanda bayan isha’i ya cika lokacin da zai fara aiki ajikinta, dogowar rigace ajikinta tawani rubber yard ta manne mata ajiki,ta kwanta kan kujera tare ta  lumshe idonta tana tunanin gata nan ta haihu sai ta saki murmushi “Jamila!!” firgigit ta tashi tace ” La sannu da zuwa banji shigowarka bane” yace “Kwarai kuwa tunanin ne har yanzu? Nayi sallama yakai sau biyar baki amsaba” ta karbi jakarshi ta nufi bedroom d’insa shikuma yabi bayanta yana tambayarta “Ya gajiyar hanya? Ina fata kun samu ganawa dashi?” cikin farin ciki take bashi amsa, har tana cewa zai ci abinci kafin sallane ko sai ya dawo, yace karta damu bari ya dawo tukun, sosai take binshi asannu har zuwa dare, inda ta samu wata silk night gown d’inta ta kama ajikinta, yagano take takenta ayau yayi niyyar nuna mata yana sane da baida amfani wajanta sai tana da wata buk’at, don haka tunda suka kwanta yaji tana ta binshi  da salo yake kannewa, ta shafa mashi kirji asigar tafiyar tsutsa yayi banza da ita, sai tayi dif da aka jima ta koma ta bayanshi tana goga masa boobs d’inta, yi yayi kaman bacci ya saceshi, ganin wannan baiyi aikiba sai ta koma zira mashi harshe ta cikin  kunnensa tana wasu yan nishe nishe, bai isa yace bai ji zumm ajikinsaba amma yakamata ta gane banbancin ‘da’ da yanzu, still yaki responding dawowa tayi ta facing d’inshi taga ya rufe idonsa wanda ta tabbatar ba bacci yake ba, kawai ta mik’a hannunta zuwa wandonsa caraf ya rik’e hannunta tare da kunna side lamp da dayan hannunsa yace ” Jamila raping d’ina zakiyi kuma?” kawai sai ta fashe masa da kuka mai sauti “Don Allah meye haka ne, kasan dai na karb’o magani karkamin bak’in ciki mana” sai da dariga taso kwace masa ga bata fuska ya kalleta kuka take tana rokonsa….
  To zamu ji ko Ahmad zai yarda ko kuwa dahaske bak’in cikin yake mata

3
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                         
loadιng………..✍🏻

*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*

© 2019

  This page is dedicated to wattpadians… 😍

23

Rok’onshi take amma yak’i nuna zai bada had’in kai, daga bayama sai ya tashi ya sauka daga kan gadon ya zauna akan bedside drawer ya kalleta yace “To ma meye na damuwane, kin manta minti 10 cikakke bakya jura zakice nafiya naci ko kiyi ta mita bayan angama, ni yanzu ai kin riga kinsa na sakankance har mantawa nake da sex arayuwata, yaushe rabon da na ji dumin jikinki? ” kallonshi tayi tace ” To meye na tone-tone? Ai shiyasa yanzu zan baka akalar rayuwata kome zakayi kana iya yi, idan ba so kake ka tabbatar min  cewa don zaka iya haihuwa da wata shiyasa baka damuba, burinka kawai agaji agidanku ko kai kagaji da rashin haihuwata ka k’aro aure ko?” ta k’arasa fad’a hawaye na zubowa a idonta, shikuma ya d’auke kansa don tausayinta ke neman nuk’urk’usar sa, ya juyo yace ” Abu nawane bakyamin agidan nan, kinason ki cusamin ra’ayin son mata, ba abinci isasshe ba tarairaya haba? Ina zansa kaina ina ji nane kaman gwauro fa, gaskiya dole na k’ara aure matuk’ar bazaki kiyaye wad’ancan abubuwan ba ehe” tuni tafara rantse-rantse ” Wallahi tallahi Ahmad zan kiyaye haba meye wata macen zatayi ni bazan iyaba, ka zuba ido kagani ganzu dai kabani dama don Allah” sai ya koma kan gadon yace ” and lastly banison mita kome akayi, karkizo kina ai nagaji jiya baka kyaleniba anything concerning nagging about sex banso you hear” yafad’a tare da jan kunneshi tace “Naji zan kiyaye” wani murmushi ya saki tare da fatan Allah yasa abun ya d’ore, tuni ya shiga binta da zafafan wasanni koda ga yanayin wasannin dayake da booobs d’inta tasan yau za’ai aries ne, sai daya d’au lokaci yana mata wasanni yanda takai mak’ura sannan yayi Addu’ar raya sunnar ma’aiki (S. A. W)+
KANO
Cikin nutsuwa take duba takaddun dake gabanta, yayinda shikuma yake driving, ganin sunzo kusa da asibitin ne ya kalleta yace “Yau ina sha’awar dambun shinkafane da kunun Aya” murmushi tayi tace “Yau kuma anyway insha Allah zaka zo ka sameshi” tayi mashi peck akumatu ta sauka.
  Har ta had’a jakarta Maryam Tafida ta sanar mata ana nemanta acikin main Lab, haka ta ajiye jakar tare da jan tsaki tace  “Oh yau ni k’addarar ta fad’awa kenan, quater to four fa” ta nufi can Lab d’in haka suka shiga aiki ba ita ta baro asibiti  ba sai k’arfe shida saura, tana shiga baifi da 2 minutes ba sai gashi ya shigo, fuskarshi kadaran kadahan, don yaga sanda napep d’insu ya wuce yasan bata dawo kan lokaci ba,  bayan ta mishi sannu da zuwa ta bashi drink ya d’an kishingida akan sofa, da sauri da sauri take tankad’e shinkafar dama tana da ajiyayyen nik’akke, tana shirin had’awa sai gashi ya shigo ” Kin fara ganin halin aikin ko? Ya za’ai mace ta had’a aiki  da aikin gidanta, look at you ko hutawa bakiyiba kin fara tunanin girki, gashi yanzu za’ai magriba ga yunwar da nakeji you already new that im not use to eat outside” bata damuba kawai cewa tayi “Kayi hak’uri’ jan siririn tsaki yai yafita, haka ta dinga sauri ana kiran magriba taje tayi ta dawo kitchen din, ta d’auko kayan had’in coleslow ta fara yankawa

Yana falo sai kumbura yake sosai yake jin yunwa, bakalar zugar da shaid’an bai masaba, yamanta cewa duk sauran days da take ajiyewa kafin yazo, bai isa ya zageta kan abinciba don bata masa wasa dashi, sai wurarane 8 ta kammala had’a masa kan dinning, lokacin in yazauna ci zai rasa jam’i haka ya hak’ura sai bayan Isha’i yazo, har kunin Ayar ta had’a mashi, tazo tayi serving, ta zauna shiru tana juya nata da tad’iba a mini bowl da baifi ake fasa 3 eggs cikiba, ya d’ora da kushe aiki dambu sarkin shak’e mutum balle ana ci ana magana, tuni ya k’ware ya fara tari sannu ta d’inga mashi  bayan ta mik’a mashi  kunun Aya a glass cup, ya kurba tana mashi sannu, k’ura mata ido yayi yace ” Kin barni ina ta magana ni kad’ai” sai da  takoma ta zauna kan kujerar ta sannan tace ” Ai laifi namaka shiyasa bani da  tacewa, amma kaga kaman rashin saurin da ka tayani da ko dicing vegetables d’inne kaga da anfi gamawa da wuri” yasan gaskiya ta fad’a amma dake akan aikine sai yace ” Ai a irin wannan time d’in kinsan ban fiya tayaki aiki bako? Ok kodan nagane awajen aikinne ake zugaki kan sai na tayaki ko? To ai ni nasauke nawa hakkin” yai ta bambamin fad’ansa tana ji, sai da ya gaji sannan ta k’ara ce amsa ” Allah ya baka hak’uri Insha Allah zan kiyaye nan gaba” ta mik’e tabarshi a dinning d’in

STORY CONTINUES BELOW
Tagama shirinta na bacci tana chat dasu Khadija ya shigo d’akin, alokacin k’arfe tara ta gota kirkirar  murmushi tayi tace “Kana buk’atar lipton tea ne ko green tea?” ya sosa k’eya yace ” Kowanne ma, ki kaimin d’akina” tace “Shikenan’ ta ajiye wayar ta nufi kitchen
Tunda ta ajiye tea d’in yake kara nazarin fuskarta ko zaiga fushi amma sam yaga babu, kuma yasan ga d’abi’a irin tata bata saba da fad’aba yanzunnan zata fara ruwan hawaye, amma yau baiga tayiba,umartarta yayi da ta zuba shayin don ya lura bata wani ci abincin ba, haka tasha ta wanke bakinta atoilet d’insa ta dawo ta kwanta, koda ya nemi jikinta bata nuna komiba ta bashi had’in kai kaman normal days.
Har Jamila ta k’are shan maganinta  bata yarda ta sab’awa Ahmad ba, kuma ko minti nawa  zai d’auka yana abu d’aya da ita bata nuna damuwa ko mita, sai ya fitane zatake yan k’unk’uninta ita kad’ai, yanzu tana jiran nanda k’arshen watane tani changes na ciki ko taje ayi test, zaune take tana yanka orange kan plate suna tad’i da kawarta Farida, anan take nuna mata tsananin k’aguwar da tayi taji ance tana da ciki batasan kalar farin cikin  da zatayiba, ita kuma Farida tana nuna mata komi yana da lokaci, inta kwantar da hankalinta tana zaune zataji lokacin da bata tab’a tunaniba, haka hirar tasu ta kasance har tazo tafiya sun fito farfajiyar gidan ne sai ga motar Ahmad ta shigo gefenshi Umar ne abokinsa, nan Farida tace ” Ga oganan ya shigo sai munyi waya” da tazo wucewa suka gaisa da su ta wuce, cikin murmushi ta tare su tare suka shiga ciki, sanin yanzu Jamila nakan neman abu wajansa  yasa ya d’ebo Umar cin abinci,  da dane bazai faraba don yasan kunya zai sha, bayan sun gaisa da Umar ne ta nufi kitchen inda ta had’o musu Abinci da drinks, suna ci suna tab’a hira har yana zolayarta, bayan nan ta basu wuri takoma d’akinta ta shiga waya da ‘yan gidansu

F. U. D

Su Tsumagiya sai da suka maidawa su Salima duk abunda  sukai, ranar bak’aramin jin dad’i Salima tayiba taso ace har ita akaje wallahi, amma ko ba komai  yanzun ma tasan Jamila zata kiyayi Students. Abangaren Ahmad ganin anfi wata da dawo wa yasa aka binciko masa su Tsumagiya, don yasan zuwa yanzu yakai kowaya dawo school, basuyi mamakin kiranba tunda sun san sanda suka jewa Jamila basu b’oye kansuba, suka gurfana gabansa yace “Inason kowacce acikin ku tafad’amin gaskiyar Al’amari idan ba hakaba kuka min k’arya wallahi sai an koreku amakarantar nan, don zan daga case dinku har senate” ba wani tsoro suka fayyace masa komi sannan suka d’ora da ai dama sunji labarin tasha yiwa wata Student, shiyasa suka ga yakamata su taka birki so that su samawa mates d’insu lafiya, kawai tsayawa yayi yana kallonsu, ganin haka suka bashi hak’uri sosai sannan ne yamusu nasiha, yakuma gargad’esu karsu k’ara don kawai saboda jyayensu ne bazaisa akore suba, kuma su sani ba namijin da zai bari ataka mashi mata ya k’alesu su kiyayi gaba, suka tashi suna thank you sir, bayan fitarsu ya dad’e yana al’ajabin rashin tsoronsu k’arshe cewa yayi “Allah ya shirya’

   Tana zaune ta rafka tagumi sam cikin sati biyunnan bata jin dad’i, don aiki yana yawan ritsata a asibiti bata dawoba tasha sababin Adam, dake dama jira yake kwata -kwata ya birkice mata, in dai abu ya danganto da silar aiki ranar sai ranta ya b’aci, yanzu haka jiya sunje barkar haihuwa matar H. O. D d’insu, duk da tagaya mashi daga aiki zasu wuce amma da ta dawo yaga lokaci ya k’ure haka ya runtse ido ya mata masifa, har yana  cewa zai kaita k’ara gaba, ko kuma ya hana aikin, share kwallar da ta zubo mata tayi a ido, bai dad’e da fita daga gidanba kan yaga suna maida magana da mai adaidaita akan canji bai sam farkon zancenba ya datsa, da ta shigo yadinga sababi wai ta tsaya tana marairaicewa mai Adaidaita sahu murya, duk kuwa da cewa ba halinta bane neman ragi, matsalar Adam rashin tsayawa yaji  kanun zance matuk’ar ya shafi namiji he just jump up in to conclusion ya b’ata mata rai, shafa cikin  jikinta tayi tace ” Allah ka inganta min wannan, nikad’ai nasan azabar da nasha ab’arin kwanaki” tana kan share hawayenta ya shigo bayanshi Ya Muhsin ne da Safiyya, waras ta mik’e ta ruk’unk’umota tana “Amarya ashe kin fara fitowa” yak’e Safiyya tayi saboda takaranci damuwa awajan Khairin, shikuwa Muhsin samun wuri yayi ya zauna yace ” Bi min mata ahankali kar kiji mata  ciwo mana” suka k’yalk’yale da dariya  gaba d’ayansu, sannan suka shiga gaisawa, sosai ta sake inda  Adam duk inda tayi yana binta da ido yaga motsinta kar sugano wani abun..
Shafa fuskarta yake zuwa bayan gashinta, d’if tayi kaman tana bacci, bai damuba don ba’abunda zai hanashi aiwatar da abunda yake so yau, ya zauna daidai  tare da zare mata riga, tana jin haka gabanta ya buga don wallahi tafara gajiya da Ahmad abjne baka saba ba, tunda aka fafa harkar maganin nan baya d’aga mata k’afa its kuma bata saba ba, murza nipples d’inta da taji yana yi da zafi- zafi yasata bud’e idonta, ta marairaice masa ” Don girman Allah kayi hakuri MyOne tun da yamma nake fama da ciwon kai, ko d’azu don kar kace na foya rakine yasa na biyeka” k’ura mata ido yayi yace ” Shikenan naji, kwanta kiyi baccin ki” ya fara k’ok’arin maida mata rigarta, tsorone ya shigeta karfa zuciya yayi naje nan gaba ya b’atamin shirina, sai kuma ta rik’e hannunsa lokacin yana k’okarin maida mata maballin jikin rigat tace ” Shikenan na yarda kayi, bawai mita na bane kawai da gaske kaina ke ciwo” Baiyi magana ba ya k’ura mata ido yana karantar idonta, tuni Jamila ta gigice ta shiga masa magiya….

Ahhh Jamila karfa ki b’ata rawarki da tsalle?
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                         
loadιng………..✍🏻


*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*

© 2019

24

Sai da tagama surutan rok’onta sannan yace mata “A’a ba nayi fushi bane kawai ki kwanta Allah ya sawak’e” saida taga yana murmushi sannan hankalinta ya kwanta

Cikin rashin kuzari take had’a breakfast d’in, duk wanda yasanta ya kalleta zaisan tana cikin damuwa, rashin zaman lafiyarsu da Adam baya mata dad’i ga yanayin laulayi. Yana zaune yana cin abinci sai sak’e-sak’e yake aransa, shifa tunda yaji hankalinsa bai kwanta da mutane biyunnan ba baya k’aunar yaga taje asibitin nan,  dan baya son iyayensa suji maganar da tuni yasa ta ajiye aikin, jan tsaki yayi ta d’ago ta kalleshi ko tantama batayi tsakin yana da nasaba da ita, haka kurum taji abu yazo ya tsaya mata arai sai hawaye ya b’alle mata kamar wasa sai gashi ta kasa shanyesu sai sheshheka take, a tsanake yake k’are mata kallo tabbas ta fad’a ta rame “Babyluv meye yake damunki kike kuka kuma?” cije lip d’inta tayi ta jijjiga kanta alaman bakomai “Ya zakice haka? Babu komai kawai zakike kuka kinga ki fad’amin ko wani abu ke damunki” bazata iya cewa komiba sai k’ok’arin share hawayenta da takeyi, bata tab’a manta nasihun da iyayenta suka mata akan dannewa da rik’e sirrin aure, kuma gashi tanayi domin har yau bawanda yasan tana samun sab’ani dashi, shiyasa abun ke cinta arai bata tab’a fada, kuma iya bin diddigi da sa’idonka bazaka gane ga yanayin da take cikiba, lallashinta yazo yakeyi yana cewa “Tayi hak’uri haka ciki yagada amma ta samu ta kwanta ta huta, in yaso anjima zai kaita gida” taji haushin maganar da yayi, ya za’ai yace wani ciki ai yasan kalar matsalar da suke ciki, amma bakomai taji dad’i dayace zasu gida ko bakomai zata wataya acan, dama kwana biyu basu jeba…+
   Matane ak’alla zasu kai shida acikin k’aramin tsakar gidan, kowacce da yaranta inka d’auke Jamila da shafa’atu, kasancewar week-end ne sunzo kitso wasu kuma sun kawo yaransu amusu, hira suke kaman yanda  gidan kitso ya gada, d’aya acikin matan ta dubi fatsima mai kitso tace “kinji labarin abunda ya samu shafa’atu ai ko” tallafar kumatu tagefensu tayi itace shafan, kallon ta Fatsima tace ” Kwarai kuwa Barira nasani wai tsabar wulak’anci Nasiru kishiya zai mata akan haihuwa, maza sai abarsu” K’ululu cikin Jamila ya kada ta bi Shafa’atun da kallon tausayi, ita wallahi idan taji za’ayiwa wata kishiya har cikin  ranta takejin abun Barira ta kalli Shafa’atu tace ” Wallahi yar uwa ina ganin k’ok’arinki,  da kika zuba masa ido yake yanda yakeso” Cikin mamaki Shafa’atu tace ” To ya kike so nayi, ai tunda addini ya bashi dama dole ne na hak’ura don namiji yayi niyyar k’ara aure haukan mace baya hanashi saima ki cikawa kwabarki ruwa karshe ya baki Visa” heyy matan gefensu suka saka shewa nan fa kowacce ta shiga cika baki akan abunda  zataiwa mijinta in yace zai k’ara aure, hauka kadai itama Jamila duk da bata fiya surutu a gidan kitsoba sannan bata saba dasu Shafa ba tace ” Tab amma yar uwa gaskiya na jinjinawa k’okarinki, wallahi kishiya ko wani za’ayiwa haushi nakeji balleni, amma dubeki kalau kaman abun bai dameki ba” murmushi yak’e Shafa tayi tace ” To ya na iya da kaddarata sai dai fatan kawai ta zamo tagari” nan Barira ta karbe zancen tace ” A kishiya ina ake tagari, matar da zata shiga da niyyar rabaki da farin cikin ki, kinga ko wannan ‘yar fata na nake mata Allah kar ya nuna mata kishiya arayuwarta” ta kama diyarta wadda bata k’arasa shekara hud’u ba, matan wajan suka saka dariya suna lallai Maman Huda ashirye kike,  ta kalli Huda ta shafa gashinta tace” Ko kina son kishiya?” Yarinya kuwa da batasan kan komiba ta kwantar da kanta jikin uwar tace ” A’a banacon ta Mama” nan suka fasa shewa yiii yarinya ‘yar gari, dole Jamila ta dara ita da Fatsima don abun yabasu dariya, rabin hirar akan kishiyane da irin juyawa mata baya da wasu mazan kan yi in sunyi amarya, da irin reasons da kansa maza k’ara Aure bayama rashin haihuwa, daga masu cewa uwar miji kan zuga ayi ko abokai, iyakar tashin hankali Jamila ta shiga, ana gama mata kitso kuwa da tashiga gida fad’awa tayi kan kujera ta  rushe da ihu ” Allah mai nai maka ka hana ni haihuwa? Ya Allah kaji k’aina kabani haihuwar nan” haka tagama sumbatun haihuwarta kafin ta mik’e ta d’ora girki, taso ta makara Allah yasota Ahmad yaje Gumel d’aurin Aure1

STORY CONTINUES BELOW
  Tunda suka shiga gida idan Hajiya Hassu nakan Khairi taga yanda ta fad’a, sai da takasa daurewa ta tambayeta tace ko laulayin ne yazo mata da wahala tace mata A’a, idan Adam kuwa kyam akanta kafin ta bada amsar, haka suka gama yininsu gidan kowa na nan nan da ita duka iyayen nasu, sai  bayan Isha suka dawo gida, tana kwance tana nazari akan matakin daya kamata ta d’auka, tunda  aikin yafi bada matsala  why not ta koma karatunta, amma kuma bazai yiwu ba abarta ta tafi don yanzune take kan shekara d’aya da fara aikin ya yi wuri ta tafi k’aro karatu, amma zata yi k’ok’arin tuntub’ar su H. O. D taji ko abun is possible

Har bacci ya fara shamayarta taji alamun mutum yana shafa cikinta, tayi kaman bata jiba, kwana biyu dama ya tattarata abunda ke had’asu bai wuce peck da take masa ba idan zai tafi office, ganin tak’i motsawa yasa ya sunkuya daidai kunnenta ya fara kiranta da sigar rad’a “Babyluv.. Babyluv bacci kike ji ne?” bashi amsa tayi ciki- ciki irin na muryar bacci, hmm ya ajiyar zuciya yace ” Tashi kiyi aikin lada in dai baccin baifi k’arfin kiba” Kaman karta tashi don tana jin haushin shariyar da yake mata akwanakin, bai daina wasa da hannun shi ajikinta ba haka ta hak’ura ta bashi had’in kai…
    Sosai yake jan tsaki akai-akai tunda ya taho daga HT Jahun ranshi ke suya akan haukar dayaga yaran sun rubuta a test da ya musu, koda ya shigo gida ya tarar Jamila cikin  shigar hausawa full tayi kyau abinta, k’ura mata ido yayi bayan ta kawo mishi ruwa mai sanyi, ya kora tare da dafa goshinsa yace ” Bansan me yake damun yaran yanzu ba sam basu son karatu sai Jarabar soyayya” kallonshi
tayi gabanta na dukan uku-uku ” soyayya kace fa? Wata student d’in ce  tace tana son ka kokuwa me?” takasan ido ya kalleta yace ” Ni nace miki haka kuma? Kinga bansan jan fitina nace ne basu son karatu sai kula samari” ya tashi ya shigewarshi d’ak, binshi da ido tayi tace “Daga magana kuma sai ya hau sababi taja tsaki mtsss kaji dashi” ta cigaba da kallonta can kuma taji ya k’wala mata kira ta shiga d’akin, yana kwance ya cire kayan jikinshi sai white singlet da blue short ajikinshi yace “Don Allah yankomin fruits d’innan inaso nasha” amsa mashi tayi ta fita, bayan wasu minutes ta kawo mashi ta koma falo, dama tana yin girkine da takoma taga komi ya kammala sai ta kashe ta kai komi dinning, bata jima da gama had’awa ba ta zauna taji ya k’ara kiranta, tana k’unk’uni ta shiga d’akin da alama yad’an jima da kammalawa yana kwance idonshi alumshe, koda ta shiga tace “Gani” yace ” Ok hawo kan gadon mana” cakewa tayi daga gefe inda akwai abun da ta tsana bai wuci rana ko yamma yace zai nemetaba, sam bataso haka don dolenta ta hau gadon ta kwanta, dama d’akinshi koda rana bai fiya haskeba saboda yanayin curtains d’inshi, bai ce mata k’ala ba ya rage mata kayan jikinta ya mannata da jikinsa  yace ” Bakomi dai akan wuta ko?” gyada mashi kai tayi yace ” Fine’ sai da yab’ata lokaci yana kissing dinta sannan ya shiga jagwalgwalata sannan yayi bacci, sai da ajiyar zuciya ta k’wace mata  tace “Allah ya soni bai wuce gona da iri ba” kallon fuskar shi tayi tana jinjina kalar son da take mishi, da kishinsa da take, shafa sajenshi tayi tare da komawa ta kwanta, ta shiga tunani ta k’agu taji ance tana da ciki atleast tasamu abunda zai sa take jin Ahmad bazai k’ara aureba, shikuwa Ahmad baccinsa yake sadidan don yasamu haushin yabar zuciyarsa… Dadin kana da mace kenan.
    Dubawa takaddar gaban ta take tana shigar da wani aiki da sukayi asatin, ganin aikin zai b’ata mata lokaci ta rok’i Maryam Tafida  ta tayata, itam Maryam d’in dake ta lura kwana biyu k’awarta ta ba anutse take ba bata tsaya bata time ba ta karba, dama ita Maryam mijinta a ABUJA  yake aiki, ba mazauni bane shiyasa hardly su sami matsala akan komawarta gida, anutse take tafiya ta isa bakin titi don neman Adaidai Sahu, sam hankalinta ya d’auke so take taje gida da wuri batasan fitina,  bata kulaba tazo tsallakawa dayan hannun da zata samu na hanyar layinsu wani mai mota yataho da gudu duk da k’ok’arin kar ya sameta sai da yad’an bugeta ta fad’a gefen titi ta bugu da pillar na wani shago, da hanzari ya fito ya nufeta yana tambayarta bata ji ciwoba ko, ita kuma ta gaza mik’e wa dole yasa hannunsa ya d’ago ta burinsa kawai yaga bai ji mata ciwoba, sai da ta mik’e taga hannunta rik’e cikin nasa ta wufce hannun nata da  sauri, ta juya tayi gaba binta ya farayi ” Baiwar Allah don Allah kiyi hakuri, tsautsayine kizo muje chemist adubaki kar aje da wani abun” kad’an ta juyo tace ” Aa kabarshi na yafe, ni bana jin ciwon komi” tana ganin wani adaidai ta ta fad’a tace muje, haka ya hak’ura ya koma cikin motarshi

  Sai da yayi parking ya daidaita nutsuwarsa sabida azabar azalzalar da ransa keyi, wani shegen ke rik’e da hannun matarsa? Tabd’ijan yaso ya samesu gaba d’aya awurin da ba abunda zai hana ya lakad’a masa duka, bari yaje gidan yaji abunda yakaita ga  hakan…

Sai da taganta agida sannan hankalinta ya dawo mata jiki, ciwo hannunta yake mata don yafi ko’ina buguwa ajikinta, haka tayi gaggawar wanka da ruwan d’umi,ta fito shikuma yana cikin d’aki sai kumbura yake kamar zai fashe, haka ta ce mashi sannu da zuwa sannan ta isa ga mirror d”inta, ta d’auki Anaconda ta shafe ajikinta, tana zira riga ajikinta ya fincikota ta fad’i k’asa ta saki k’ara dama ga ciwon jikin wancan, jikinsa har rawa yake “Khairi wana d’an iskan nagani yana rik’e miki hannu, karki nemi musamun kuma don daga nesa ina hangoki kaman wannan jakin Dr ko?” Tashi tayi adaddafe tana rik’e cikinta Allah yasota duk wannan abun da ake bai bugu ba, ta k’arasa zira rigar bata ce masa  komiba sai hawaye da take, wannan wace irin masiface haka, yagama k’ulewa da rashin tankashi da tayi yace “Magana ake miki kin min shiru tsabar kin maidani banza ko?” cikin kuka take magana ” Haba wannan wane irin abune, dame zanji an bugeni abakin titi na cinye duk don na iso gida akan lokaci na kiyaye bacin ranka, amma yanzu kazo bajin ba’asi kahau tureni kashemin yaron cikina zakai ko me?” yaso maganar ta shigeshi amma me shaidan da kishin ganin hannun wani akan nata sai tunzurashi suke “Malama karki nemi rainawa kanki hankali mana, ki gayamin gaskiya wannan dan iskan Dr ne ko? Ya rakoki titi matsiyacin harda rik’e hannunki ko?” kuka take yi kawai takasa magana, in banda son ganin laifi ta tabbata sanda ya hangota yaga mutame sun dan kewaye wurin ai yakamata ya sha jinin jikinsa, banda shi in abu ya shafi kishi sam hankalinsa baya kaiwa ko’ina ” Wai don Allah ya kake so nayine, ka duba ka gani duk iskancin da zamuyi har ma iya kawo kanmu idon Al’umma bakin titi muyi haka? Think about it idan bad’ala nake da Umar sai na fito titi na nuna ko kuwa umar baida motar da zai d’aukoni” wani irin cije lips yayi tare da zaunawa kan gado, sai yanzu ya tuno ma da cikin irin fincikotan da yayi in tsautsayi ya fad’a fa, kawai tashi yayi ya bar d’akin da sauri ya fizgi motarshi ya bar gidan

Kuka tayi har hawaye yadaina fita yanzu k’arfe goma sha d’aya da rabi na dare, sam ba alamar dawowar Adam gidan, wannan rayuwar ta isheta, sai ta tuno  irin rayuwar da sukai abaya tana jinjina rikici irin nasa, baruwansa da bincike sai yagama maka hayaniya daga baya yazo yana bada hak’uri, tashi tayi ta kwanta akan gado don tuni wani irin zazzabi yashiga jikinta ga tsananin ciwon kai, sai wajan k’arfe d’aya da mintina taji shigowar motarsa, alokacin ko iya d’aga yatsarta bazata iya yiba, shigowa har d’akin ta yayi idonsa ya kad’a tayi ja  bakad’anba don bata kashe bulb d’in dakinba, ya tsaya akanta ” Khairi meye bani dashi da wani namiji zai ja hankalinki? Kin yimin adalci kenan kije ki raba jikinki dawani, sanyin halinkine yasa kika bari suka samu damar tabaki, ko kuwa tsabar nid’in ne bakiso?” yanzu hawaye ke sauka a idonsa, don yarasa ta ina zai daina jin b’acin ran abu kamarshi Adam A k’waru wani banzan ya kama hannun  matarsa, bazai yiwuba, ita kuma bak’in cikin kalaman dayake jifanta shi ne yake da d’a haura b’acin ranta, har ji take numfashinta na neman kwace mata kirjinta ciwo yake, ba damar hawaye don baida damar sauko wa daga idonta, sai tasbihi take acikin zuciyarta, haka gaba d’ayansu suka raba dare da b’acin rai shi ak’asa bacci ya d’ebeshi, ana raka’ar k’arshe ya tashi ya nufi toilet yin alwala, lokacinne itama ta iya  bud’e idonta dakyar saboda kumburar da yayi…

2
lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻

🌐 _*🇭ιĸιмaн 🇼rιтer’ѕ 🇦ѕѕocιaтιon*_
   🌐( _*Kυngιya Daya Taмĸar Dυвυ*_)
Hikmahwritersassociation2019@gmail.com

                         
loadιng………..✍🏻

*NAMIJIN KISHI*
By *JANNAH JAY*
Wattpad @ *jannahjay8*

© 2019

25

Ta mik’e ta shiga toilet ya gagareta har ya dawo daga sallah, saboda wani irin zafi da hannun nata keyi tana ji k’ila tayi targad’e ga azababben jiri dake d’ibarta, don ciwon kan kamar jira yake ta tashi ya  dawo, shikuwa daya dawo daga sallah kunna hasken d’akin yayi yaganta idonta lumshe sai hawaye dake d’iga,  tuni zuciyarsa tafara k’una ” To me aka mata zatake wa mutane kuka, sai tayi laifi an mata fad’a ta tsiri ruwan hawaye” cikin d’aga murya yace ” Khairi wai bakijin anyi sallah ne ko kuwa salon wani shagwabar ne” idonta ta bud’e da suka shige ciki take kallonsa can kuma ta daure tace  “Don Allah ka taimaka min na mik’e tsaye nakasa” kaman bazai yi motsiba tuna da ciki jikinta yasa ya isa gareta tsautsayi ya kama hannun ciwon aikuwa tuni ta fasa k’ara mai k’arfi da kowaye yaji yasan bata raki bace balle yace tanason shiri ne ta b’ullo da hakan, sannu ya fara mata yana cewa ” Kodai kin kwanta kan hannun ne yayi tsami?” bata tankaba  sai kama sunayen Allah take abakinta still tana feeling pain awajan, haka ta shiga tayi alwala adaddafe tazo ta fara sallah, dakyar ta iya kawosu saboda yanzu banda ciwon kan zazzab’i ya k’ara rufeta, tana idarwa bata iya azkar ba ta mik’e awurin takwanta tana karkarwa, sai alokacin ne ya lura da ba lafiya ce da itaba, amma saboda zafinta dayake ji yak’i tsaywa yabata proper care sai dai tayata da yayi ta kwanta kan gado, yakoma gefe yana cin alwashi akan abunda zaiyiwa Dr Kibiya don bazai kama hannun matarshi  abanza ba… Adai bincika Adam+

DUTSE

   Tayi zuru ta shiga dogon tunani yanzu kam an nufi sati na shida da gwada last maganin ta, so yakamata ta je asibiti agwada tunda bataji wasu changes ba ajikinta, yana zaune yana shigar da wasu details cikin system d’insa, cikin nuna kulawa ya kalleta yace “madam yana ga kinyi shiru ko akwai wani labarin ne ak’asa” kallonshi tayi da wata harara-harara tace ” Yanzu kana  nufin hankalinka baya  kan result na maganin dana gwada kwanaki” ajiye takardar yayi yace “Ina sane da hakan kawai dai ni bana zafafa tunanina, saboda nasan zafin nema baya kawo samu” tab’e bakin ta tayi tace “kwarai dama yaza’ai ka zafafa nema, tunda kasan zaka kawo wata cikin gidan nan in yaso sai amaidani koma baya nazama yar kallo, ko kuma ma asakeni nabar gidan tunda.. Jan tsaki yayi ya katse ta yace “Haba Jamila wacce irin magana ce hakan, pls karki kawo  mana b’acin rai mana, wai ke badamar mu zauna lapiya gidannan sai kin tado mana b’acin rai, meyesa zakiyi tunanin saki tsakani na dake” dama tun tana fadin ko asake ta ta fara hawaye gani take yana nuna i dont care kan issues d’in neman haihuwarsu, tashi yayi  ya k’araso kusa da ita ya d’ora kanta kan kafadarsa yana lallashinta, zamu iya cewa ta samu d’an relief bawai abun ya goge aranta bane, ganin ta daina hawayen yace “Nima inason mu haihu dake Sweety na kuma kinga nifa har yanzu banga wata mace da ta dace daniba, saboda haka karki sawa kanki damuwa, jibi sai muje ganin Dr adubaki bayan nan inaso adaina damuwa da magan ganun maganin nan kar aje kisamu wani ciwon, kinsan lafiyarki tafi komi awajena” gyada kanta tayi ta k’irkiri dariya tace ” Toh MyOne” yace “Ko kefa, yanzu ma kizo mu fita mu sha Ice cream” cikin jin dad’i ta nufi d’akinta don shirya, sai da ya koma kan kujera ya fara kokarin hada takaddun dan ya ajiye yana murmushi “Jamila bata girma da rikici”

  Sai da takwas ta gota ya tashi daga baccin daya kwasheshi afalo, wayan yaga dinning sannan kuma gidan yana nan yanda yake, sai alokacin ya koma d’akin nata abun is worst don numfashinta kaman zai kwace mata, agigice ya d’ebeta ya nufi parking lot da ita lokacin ne Sabir ya shigo gidan ” Yawwa  don Allah tayani da driving mukaita asibiti” hakan akayi kuwa Sabir ne yake tuk’i shikuma yana rik’e da ita abaya,ita kuwa Khairi kusan hankalinta yakusa fita akanta, ba abunda ke amsa kuwwa akunnenta irin maganganun da Adam yake jingina mata na iskanci, cikin dasashiyar murya take cewa “Wallahi ni ba mazinaciya bace bana bin maza” gaba d’aya ya rasa me yake masa dad’i, tun yanajin numfashinta na fita dak’arfi har yadaina lokacin ya cewa Sabir ya k’ara gudu, bak’aramin tashin hankali yake jiba kar cikin jikinta ya zube don bazai iya d’aukaba…
STORY CONTINUES BELOW
Cikin kulawa aka karbeta hannu  biyu, shida Sabir suna tsaye awaje idon Adam ya kad’a yayi ja, d’aukar waya Sabir yayi ya kira Hidaya ya sanar mata yana Asibiti, sai da aka d’au kimanin awa d’aya da rabi tadawo nutsuwarta anan ne take fad’awa Dr daje dubata hannunta, suka duba bak’aramin bugu tayiba amma luckly ba karaya bane, su Sabir sun mata sannu inda shi ya nufi office yabar Hidaya da ta kawo musu abinci, tunda ya shigo yake mata sannu ya rik’e hannunta dayake ba ciwo, fuskarsa kadaran kadahan amma gefe d’aya fargabarshi d’aya kar gida suji jininta ya hau,    bawani magana suke ba don tunda ta tashi ido take binshi  dashi, don ita yanzu kaman wani tsoro yake bata zata iya cewa ya he turn to something else kaman ba soyyayya da tausayi tsakaninsu, ya gaji da shirun da tayi yace “Khairi me kika sawa kanki har jininki yahau amatsayin ki na yarinya infact kinsan ba’ason irin haka gamai ciki ko? Ko so kike na rasa abunda ke cikin ki duk saboda wannan aikin naki” hawaye ya sauko a idonta sai da ta d’au seconds tace “Meyasa bazan saka damuwa arainaba? Ka juye gaba d’aya kamar ka gaji dani duk abunda  kasan zai b’ata raina shi kake, ka duba abunda ya faru baka tsaya kajiba ka hau kana kirana da mazinaciy… Kawai ta rushe da kuka, yanzu yana feeling guilty amma dai fa ba’a kyauta masa ba da aka kama hannunta, shi bai yarda da su Kibiya da H. O. D ba, yace ” Ok kiyi hak’uri na jingina maki magana amma kinsan me wallahi ni banson alak’arki dasu, kuma ma da idona naganki ya  rik’e hannunki” cikin  daga murya tace ” Sau nawa zan gaya maka ba shi bane, wani ne yakama hannu na fa ba Kibiya bane ko zaka taba asibiti ranar yana ciki bai fitoba, kamanta ba time daya muke tashi dasu ba,  beside shi ba kullum yake shiga hospital ba, sai afi 2 weeks bamu had’uba, shi meye had’insa da Lab” gyara rik’on hannun da ya mata yayi yace ” Look do you mean wani ne daban ba Kibiya ne ya rik’e hannunki ba” kai ta furta  ta d’ora hannunta kan goshinta “Ohhh” tagaji da nanacin maganar nan da alama bazai d’aukaba tace, kanta zai fara d’aukar zafi, zuwa Dr tayi tace “Please ka bata koda ruwan zafine da abinci ok” sannan ya fita ya kawo mata dakyar take hadiyar tea d’in, wayarshi ce ta d’au k’ara Safiyya ce ga miss calls na Hajiya Hassu da Ak, bayaso asan wannan maganar kar suzo suji ana jininta ya hau, wayar Safiyya ya bi ” Yaya nazo gidan naganshi abud’e kuma bakowa gashi naje asibitine ance bata shigo ba, meya farune? ” Daure fuska yayi yace “Yawwa shiga ki d’auko mata wayarta ki duba d’akinta zakiga padlock kiyi locking falon ki zo ki sameni a asibiti” tana kan cin wainar kwai ta ke binshi da kallo, sai kuma yace ” Yanzu dai in banda shirmen samarin yanzu awannan titin ya bugeki harda rik’e miki hannu, mtsss Allah ya kyauta, amma dai kisani Dr kibiya yadaina haike maki ehenmm” shiru tayi bata da time d’insa

Safiyya tunda ta shigo take bin  Adam da kallon tuhuma, shikuma sai cin magani yake, tunda taji magana akan cikinsu na baya yasa  yanzu sam tana kallon yayan nata da wane irin  yanayi, maida idonta tayi kan Khairi idonta ya taru da k’walla ta k’araso kusa da ita ta kama hannunta ” Sis sannu Allah ya baki lafiya, kinga yanda kika rame kuwa sai kace bamai cikiba” hararar Safiyya yayi k’asa k’asa ita kuwa bata damuba, don tasawa kanta bai da  gaskiya ita yanzu sam ya sure mata ne tace ” Yaya mai ya sameta ne? ” cikin d’an in ina yace jiya wani ya bugeta abakin titi shine take zazzabi da ciwon kai, kama habarta tayi da sigar mamaki tace ” Bugewar karayane ko kuwa me? Lokaci daya kuma ta zabge ta koma hakan?” b’ata rai yayi yace ” Ah to gata nan tambayeta, ke meye ikon Allah baya sawa, an daiyi sa’a bataji internal injury bama” so take ta kureshi da ido amma ina da girma a idonta, ya fice yace bari yaje gun Dr yana fita ta karaso inda take tace “Sis dagaske ne hakane ko kuwa wani abun yamiki?” murmushi tayi tace “Meyasa zakiyi kokonto hakanne, kuma kinga  ba’a raba mai ciki da ciwon shiyasa gashi na tsorata” hmmnn ta ajiye ajiyar zuciya, tana kara intimidating idonta ” Ke kiji fitsara kin tsareni da ido, nifa yayarkice” inji Khairi jikinta na bata bata yarda da itaba, dariya kawai tayi ta d’au waya ta kira Muhsin ” HoneyB na sameta ashe bata jin dad’ine, yanzu zan zauna awajanta” dariya tayi ta kisisina tace “kaganka ba damuwa we would be fine, basai ka kawomin da kanka ba akwai bakin asibiti zan saya, no need ka taho” duk da batasan me yake cemata ba amma ta lura komeye mai dad’ine, can tace ” Shikenan i love you too” ta ajiye phone d’inta tace ” Kai Ya muhsin sanda muna gida bazakice ya iya kula da mace har hakaba,  wai don ina cin d’ata ne yace zai  kawo min anjima saboda kar naji sha’awarshi babu” itama sofi akwai ciki,  murmushi Khairi tayi tace ” Gaskiya dai kam bazakace zaiyi hakanba, kasancewar ya fiya kalan shiru-shiru kice yanzu ya wuce tunanin ki” wani lallausan murmushi ta saki tace ” Wallahi bazan yi k’aryaba iyayenmu sai  dai mukara masu addua, sau tari nakan yiwa Abba addu’a (mahaifi su khairi)  idan Ya muhsin yana ban kulawa hmn bazaki ganeba” tabbas Khairi na fuskantar hakan  saboda  tanajin labarin kalar karin girmamawa da kulawa da Safiyya kan yiwa iyayen nata, duk da tun da suna daukarsu dayane amma yanzu is quite different, haka suka cigaba da hirarrakinsu, kafin nan ta sanar a asibiti bazata samu zuwa ba itakam Safiyya dama ranar basu da aiki office, muhsin saida ya kawo duk da tahanashi, sai kaffa-kaffa yake da ita,sai Yamma aka sallamesu da sharadin kula da lafiyarta da kiyayar damuwarta, ya ce kar ma Sofi ta fadawa gida maganar.
    Tun zuwansu Jahun take jin jikinta wani iri sai ta d’au hakan as tafiyane ta kawo hakan, sun dawo lokacin k’arfe shida na yamma, dake yini sukayi acan, suna zuwa ta kai nono cikin fridge ta adana shirgin tsarabar da aka masu su manshanu, don yan Jahun badaga nan ba wajan karrama bak’o, adaddafe ta shiga toilet shikuma ya nufi masallaci, da tafito daga wanka gown ta samu ta zira jikinta  tayi sallah awajan ta kwanta , sam jikinta ba d’ad’i jin jiri take da ciwon kai, bayan ya dawo daga sallah bai ganta afaloba ya wuce d’akinsa, shima ya zuba wankan yasa jallabiyarsa ya kira Umar suna gama wayar, ya tuna da nononshi ya fita bakin titi sayan kwakwa da fruits don ahada masa su bayan isha by then nonon tayi sanyi, Jamila kam jinta take somehow kaman bazata iya mik’ewa ba, batason hakan gobene fa zasu je ganin Dr na gwajin cikinta, har ya dawo daga sayosu bai gantaba, sai ya barshi as gajiya ce tasa bata fitoba, zama yayi ya kunna Tv duk da bai fiya kalloba, ya kwanta a L shape couch dake falon yana jiran sallar Isha’i, yana dawo wa daga Isha ya lek’a d’akinta yaganta kan sallayar adan jingine da closet nata, sai ya d’auka yanzun ne ta idar da sallar isha’i, yace ta fito ta had’a masu fura,  saboda ganin likitanta ta dake ta mik’e duk da d’imbin jirin da ke dawainiya da ita, tana fitowa daga falon jirin ya d’ebeta gani yayi tayo k’asa cikin wani irin hanzari ya rik’ota “Subhanallah meke damunki ko gajiya ce?” ina idonta dakyar take budeshi sai ambaliyar hawaye, don Jamila ba juriyar ciwo balle wannan strange abu takeji, bazata iya cewa game ke damuntaba dakyar take iya cewa ” Kaina hhh bansan meke min ciwoba kaman zan mutu” ina agigice ya kwantar ta ya shiga dakin ya dauka car key

   Tuni tazama batasan wake kantaba kafin su isa Hospital, an samata drip yanzu tana bacci, ya k’ura mata ido sai yanzu yaga tad’an d’ashe (haske), an bashi result nata, wani irin murmushi ne ke fulfula afuskarshi, so yake yaga ta bud’e idonta taji bushara her dream comes true, sai wajan  past 9 ta bud’e idonta, bata jin ciwon komi sai rashin k’arfin jiki, yana gefenta yana tapping phone d’inshi, jin juyinta ya maida hankalinshi gareta, ganin idonta bud’e ya sakar mata murmushi yayi ya kama hannunta yana mata sannu, ya tambayeta tace batajin komi sai rashin k’arfin jiki, k’amk’ame hannunsa tayi tace ” Me suka ce yana damuna? na tsorata na dauka mutuwa zanyi, ace lokaci  daya ina kasa komi” Murmushi yayi yace “Sweety kice Alhamdulillah” ta zaro ido tace “Saboda me?” peck ya mata agoshi yace ” Saboda Allah ya cikashe mana baiwar da kowanne dan adam yake so” kama bedsheet tayi tare da runtse idonta tana fad’in “Ya Allah mafarki nake ko kuwa zolayata kake” hawaye yana amabaliya akan fuskarta ” Yace ba mafarki jina dauke da ciki na sati biyar” kawai ta cukuikuye masa riga tasa kanta akan kirjinshi ta fashe da kuka murmushi yake ” Is okay mugodewa Allah sannan ki daina kuka, karkisa muhaifi yaro mara jarumta fa” ya na fada hannunshi na isa ga mararta, yasan babynshi na ciki, itakam tears of joy sunki  daina fita sai ajiyar zuciya take…
   To jama’a abun nema ya samufa Jamila an dace kishiya babu… Su jiddaB😝

lιĸe
coммenт
ѕнare
🌐ѕannυ ѕannυ вaтa нana zυwa ѕaι daι adad’e вa’aje вa.✍🏻

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page