ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 7 by Sumayyah Abdul-kadir
ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 7 by Sumayyah Abdul-kadir
Www.bankinhausanovels.com.ng
kin gane?”
Ummi ta tafa hannu tayi dan fitoo, ta ce.
“Yeho! Yarinya wallahi kinci a baki kyautar amsarki. Indai wannan shi ne hauka, don Allah a nada min sarautar mahaukatan duniya akan umarnin iyayena nake ba kuma zan taba ganin ba dai-dai ba, tunda na bisu, su nakewa biyayya.
Ke kuma mai hankalin da yafi na kowa da kika tasarma kisan kai fa? Waima tukunna ina hankali ga matar da ta titsiye mijinta da duka da zagi ya saketa? Matar da ta dauki kwalba ta rotsawa mijinta ai ta tabbata tsinanniya”.
(Baki kasan me zaka fada baka san me za’a mayar maka ba-TAKORI).
Zaneerah ma aka cire mayafi aka jefo min. Eh naji kamshin (212) din yaya Aliyu kam babu shakka amma itama ta cancanci a tanka ta duk dai da ban san ita din dame zata mayar min ba.
“An dai ji kunya wallahi, tsofai-tsofai ga goyo ga tirtsetsen ciki amma ba’‘a fasa jaraba ba, shima Yaya Aliyun…”.
Daga labulen dakin yayi yana fadin.
“Zaneerah ina wayata da na baki ki sa min caji?” Dif! Kake ji na dauke wuta, kamar ba ni ce mai magana ba. Ya dube mu suna ta sheka dariya kamar sun samu motsatstsiya ya ce.
“Me take cewa ne?”
Na mike gaba-gadi na dauki dankwalina na daura na bar musu dakin. Ina jinta tana cewa dashi. “Zaginmu take yi”.