RUBUTACCIYA BOOK 2 CHAPTER 7 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

 RUBUTACCIYA BOOK 2  CHAPTER 7 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

                  Www.bankinhausanovels.com.ng 

MUN TSAYA 

Hancinta ya dan ja, ya ce “Wai wa ya koya maki magana ne? Nasan ki magana ma wahala take yi maki.” Juyar da fuskar ta yi tana kallon wani abu can ta ce, “Malamina ne ya koyar da ni tun ina jaririya.”

Hannunsa yasa ya juyo da ita yana
Www.bankinhausanovels.com.ng
murmushi, “Yanzu kin fi malaminki iya komai, kin fi shi iya tsara zance.”

Ta kasa jurewa irin sakon da yake aika mata cikin salonsa na dauke hankalin duk wata mace da ke kusa da shi. Da rabin hakan ya dauke hankalin Zakiyya da take jin za ta iya daukar wuKa domin yaki da ko wace ce a kansa.

A hankali ta yi magana cikin sanyinta, “Idan kana gefena, kana katange

-ni daga dukkan damuwa, damuwa tana samun muhallin zama ne a zuciyata da zarar * kayi min nisa. A lokacin ne nake jin kaina yana KoKarin raba kansa da jikina. Da ace zan 1ya yin ihu inyi shela inkirawo mutane su amsa kirana, da na ambaci mijina a gaban dubban jama’a a matsayin gwarzon da babu irinsa. Da zan sami dama, da na shiga daji, na kirawo za ki da kura, da dukkan wani nau’in ababe masu rayuwa a cikin dokar daji, in tambaye su akwai za ki kamar mijina? In tambaye su da kai da su waye jarumi kuma waye gwarzo?” Sosai ta hada fuskarsu wuri guda, numfashinta yana sauka a bisa hancinsa, “Na tabbata amsar

ZAMU TASHI 

daya za su taru su bani. Babu wani sai mijina. Kai ne na farko a cikin zuciyar Nasreen haka kaine na Karshe. Wannan maganar da nake gaya maka, ba daga bakina suke fitowa ba, a’a daga cikin zuciyar Nasreen din Deedinta suke fita. Don Allah mijina gaya min waye yake da sa’a kamar Nasreen dinka?” Sultan ya shaki Kamshinta mai sake rikirkita shi, ya lumshe idanu ya sake bude su tsaf a cikin nata. Idanun suka lume a cikin na juna suka shiga cikin jijiyo zuwa cikin kwanyar kansu; daga nan suka nausa duniyar jijiyoyin jiki suna bada wani irin ma’anoni da su kansu sanyin jikin su bai iya barin su sun gano wani abu da yake shirin wanzarwa ba. Cikin nuna alamun kalamanta sun dade da tafiya da shi ya ce, “Nasreen ina son idanunki, ina son bakinki, ina son komai naki Nasreen. Na rayu da sonki ne tun kina cikin mahaifiyarki.” Ruwan sama . ya ci gaba da sauka ba tare da iska ko kuma da Karfi ba. Sauka yake yi a hankali yana

Www.bankinhausanovels.com.ng  zuba bisa fuskokin su. A lokacin ne kuma suke amsar sakonnin da_ suke_ baiwa kowannen su. Sun yi nisa, hankalin su ya rabu da jikin su, Nasreen ta ji saukar wani abu mai zafi a cikinta hakan yasa ta saki gigitacciyar Kara. Sultan ya ware idanu a gigice, sai dai kafin ya ankare har Zakiyya da ke rike da wuKa ta fara ja da baya tana . neman hanyar guduwa. Nasreen yake gani cikin jini Zakiyya ta soke ta da wuKa. Bai – san lokacin da ya Karaso gaban Zakiyya da jikinta yake kyarma ba. Wukan ya amshe cikin fita hayyacinsa ya luma mata a ciki ya hankadata ta fadi tana shure-shure.

Wurin Nasreen ya dawo yana jijjigata, ‘“‘Nasreen! Nasreen!! Ki tashi! Na _ yi alKawarin idan na rasa ki sai na Karar da dukkan zuri’ar Zakiyya! Sai ya kasance duk wanda aka ce masa ya san Zakiyya zai ji tsoron danganta kansa da ita.”

Zakiyya da ta gama jin kalaman Sultan tana tsaye akansa ta yi matuKar kaduwa. Ta jijjiga shi ya bude idanunsa

cikin firgici da tsoro. Kansa ya rikKe da Karfi yana jin kan yana sara masa. Har yanzu Mafarkin yana nan manne & kansa, haka kuma ya gaza fassara komai. Zakiyya ta sunkuya a gabansa tana kuka, “Me nayi maka za ka Karar da zuri’a ta?”
Www.bankinhausanovels.com.ng
Haushi da takaici yasa ya ja tsaki ya mike yana dubanta, “Ke kin yarda mafarki gaskiya ce? Idan kika aikata abinda na gani_. a Mafarkin me zai hana ban dauke kanki daga jikinki ba? Kisa kika yi, wanda ya yi – kisa shima a kashe shi.”

Ya shige bandaki ba tare da ya sake waiwayota ba. Gudun kada ta gayawa Umma yasa ya shirya gaba daya ya wuce ‘masallaci, daga can ya yi gaba abinsa zuwa office. Yana kallon kiran Umma tsoro ya hana shi dauka gara dai idan ya dawo ko me za ta yi masa babu laifi tunda yana gabanta ne. Kiran Abbansa da ya gani yasa ya dauka.

Abba ya ce, “Sultan ya maganar neman wanda ya kashe Saudat? Sultan ya

saki ajiyar numfashi ya ce, “Abba ka taya mu da addu’a. Khamis ya je Ashmaan ya yi hira da shi, ya yi bayanin yana da alaKa da ita, kuma ya ci burin sai ya kama duk wanda yake da hannu a kashe ta. To bayan fitar hirar ne, Khamis ya sami kiran waya daga gun wani babban mutum mai suna Alhaji Kabiru, ya yi masa ikirarin idan bai fita a cikin maganar nan ba, zai jawowa kansa ‘ matsala. Haka da lamba iri daya aka‘sake _ kiran Ashmaan shi ma dai ana yi masa gargadi a kan ya kiyayi buga irin wannan abubuwan. Mutanen dai ko su waye suna da wayo haka hatsari ne zaman su a cikin al’ummarmu.

“Mun sa an bibiyi lambar da akayi kiran da ita, babu register a haka aka siya layin. Illolin da masu siyar da sim dauke da register suke yi mana kenan. Haka da muka duba location din ma’ana inda aka tsaya domin amsa kiran, sai muka ga a garin Kaduna ne, a dai-dai bakin ruwa. Da alama wanda zai yi wayar sai da yaje wurin da
Www.bankinhausanovels.com.ng babu gidaje sai ruwan sannan ya tsaya ya yi waya. Haka mun so muje gidan iyayen Saudat din, mun jinkirta faruwar hakanne har sai su Nasreen sun bayyana, ta yadda za su ji dadin ganin jikokin su, tunda angaya mana sun yi kukan rashinta na tabbata za su rungume su a matsayin jikoki, haka gano mahaifinsu zai rage masu radadin da suke ji a game da rashin dangi wanda kullum sai Umma ta yi masu gori. Dazu take ba ni .umarnin insaketa tunda ba asan inda take ba Kila tana can tana iskanci da aurena a kanta.” Abba ya_ girgiza kansa_ yanayin ‘ fuskarsa ta sauya kamar Sultan’ yana ganinsa, “Sultan ku bi case din nan a hankali, bana son ka sa wani abokinka a cikin matsala. Ita kuma mahaifiyarku ba zan daina yi mata addu’ar shiriya ba. Na kawo idanu na zuba mata duniya ce kayi mai kyau “ma ya kaya Kare bare kuma baka yi ba?° Kul! In ji ka yanke igiyar aurenka da matarka, ina yawaita yin Istahara_ ina

ganinta da tarin ‘ya’ya a gabanta, na tabbata wadannan ‘ya’yan naka ne _ Sultan, wadannan ‘ya’yan jikokina ne. Ka kwantar da hankalinka Allah yana tare da kai, kai dai kada ka saki addu’a kamar yadda na saki har mahaifiyarku ta ci galaba akaina. Allah ya yi maka albarka yasa ka gama da duniyar nan lafiya.”

Sultan ya nemi damuwarsa da ciwon kan da yake fama da ita tun mafarkin da ya yl ya rasa. Jinsa yake kamar babu wata sauran damuwar da ke cikin Kwakwalwarsa. “Na gode mahaifina.”

Suka yi sallama cikin so da Kaunar juna. Yana son mahaifinsa, kuma ya tabbata babu mutumin da yake sonsa sama da mahaifinsa. Lumshe idanunsa ya yi, ga dai yunwa yana ji, amma tarin damuwa sun hana shi neman abincin da zai ci. Yau bai jima a Office din ba, ya dawo gida, kada damuwa ta kashe shi, gara ya zo ya zauna da mahaifiyarsa zai fi samun _natsuwa.

Haka ya kwashe dukkan tarikitan shi ya fice da su.

Gudu suke shararawa a bisa kwaltan ba tare da sun ja burki a ko ina ba, sai cikin katafaren gidan da suke ajiye dukkan – mutanen da suka sato. Nasreen ta laluba ta rike Nawfal bakinta dauke da addu’a. “Nawfal ina ne nan kuma? Yau mun shiga uku. Haka zamu yi ta gararamba har lokacin mutuwarmu tayi?” .

Wani takurarren tsoho ya dube ta sosai, ya tabbatar makauniya ce, ya ce, “Yarinya kwantar da hankalinki ai lokacin mutuwar taki tayi. Ke dai kawai ki yi fatan cikawa da imani. Tsawon shekaru ashirin ana tsafi a nan gidan kin ga kuwa zuwanki ba zai sa a fasa ba.” Nawfal ya dubi takurarran tsohon nan da bai wuce a hure shi ya fadi Kasa matacce ba, ya sake waiwayawa, yara ne sun fi ashirin a Katon dakin.

Www.bankinhausanovels.com.ng    Nasreen ta furta cikin sanyi da karaya, “Hasbunallahu wani imal wakil! Allah mun

shaida babu abin bautawa da gaskiya sai kai Allah. Allah kai kake aiko mana da_  jarabawa, Allah ka bamu ikon cinye dukkan jarabawar da ta tunkaro mu. Bamu da dabara, bamu da wayo haka ba mu isa mu tambaye ka dalili ba. Ya Allah ka .hada ni da Deedina ko sau daya ne kafin ka dauki raina. Allahumma ajimi fi m sibati wa akhlifni min khaira minha. Allahumma…” Wata Kara suka ji mai Karfi da ya hargitsa su, haka ya kusa kaseewa Nasreen dodon kunne, wanda yasa ta yi saurin tura dukkan hannayenta a kunne ta. Da kuma ta tuna da Nawfal, tuni ta saki kunnen ta rarumo shi gam!
Bata yada ko kashe su za a yi, a fara kashe mata Nawfal ba, ta fison – ya fara ganin gawarta zai fita dauriya akan ita ta daina jin motsinsa. A hankali Karan ya sauka sai kuma wata mata da ta bayyana tana magana cikin wata murya wanda tunda Nasreen take bata taba jin labarin irin muryar nan ba, “Idan kika sake yi mana addu’a a nan babu shakka za ki bakunci lahira tun lokacin tafiyarki ba ta yi ba. Za
mu toshe maki maKogoro, kin ga baki gani kuma ba ki ji bare ki mayar. Mun fi buKatarki a kan kowa da ke dakin nan. Kinsan iya lokacin da muka kai muna binki? Tun ranar da aka dauki cikin ki. Sai dai ranar da muka zo mu dauke ki, a ranar wani yaro yasa aka daukeki suka ci gaba da baki kariya da Addu’a. Idan mun zo cikin . dare za mu dauke ki sai mu sami mayen yaron nan yana kanku yana yi maku addu’a. Akan rashin kawo ki nan yasa har yanzu ba a bani kambuna na sarautar Sarauniya ba. Yanzu ina murna burina ya cika shi ne za ki fara yi mana addu’a?l Ki kiyayi kanki!” Bat! Suka nemeta sama ko Kasa suka rasa. Nasreen ta sake fasa kuka, tana jin labarai masu kama da almara a cikin dan takurarren rayuwarta. Ko ina nemanta ake yi kamar wacce ta yi masu sata. Wani irin Kaunar Sultan ya sake mamaye zuciyarta, tabbas Sultan namiji ne, ya taimakawa rayuwarsu. Mahaifiyarsu haihuwarsu kawai

tayi, amma Sultan shi ne uwa shi ne uba. Ya yi masu abinda ko iyayensu suna raye iya abinda za su yi kenan. Farin cikin jin Sultan baya barci saboda su yasa ta lumshe matattun idanunta, hawaye suna ci gaba da sauka. Za ta yi magana Nawfal yasa mata hannu a baki ya rufe bakin, “Ke kada ki sake magana. Jirani ina zuwa.” Nasreen ta ‘ Kankame shi, “Wallahi ba za ka tafi ko ina ka barni ba.” Dole ya koma ya zauna kanta ” _-yana bisa kafadarsa.

Nawfal ya kafe yaran da idanu dukkansu suna takure kuma da kayan Makaranta a jikinsu, hakan ke nuni da daga Makaranta aka kwaso su domin cika burikan duniya kacal! Nasreen ta fara magana cikin hawaye, “Idan sun kashe ni, duk yadda za ka yi ka yi domin ganin ka sada gawata ga Deedina. Idan ka yi min wannan ka gama min komai dan uwa.”

Girgiza kai ya yi yana jin Kwarin guiwa ba tare da ya sare ba, “Ba su isa suyi maki komai ba.” Tsohon nan ya sake kallon

Nawfal da alama a Kufule yake da shi, “In ji uban wa ya ce maka ba za a yi mata komai ba? A matsayinta na wace? Iyye! Na ce a matsayinta na wace?”

Www.bankinhausanovels.com.ng   Nawfal ya zabga masa harara ya ce, “A matsayinta na RUBUTACCIYA! Kuma baiwar Allah. Ki kwantar da hankalinki -Nasreen, tunda makircin masu yinta basu kashe mu tun muna ‘yan jinjiraye ba, bana jin Karamin tsafi irin wannan zai iya taba lafiyarmu. Babu wanda ya isa ya sauya abinda Allah ya rubuta. Ina da tabbacin ko zamu mutu Allah ba zai bari mu mutu ta hanyar tsafi ba.” Tsohon ya dube shi ya tabe baki. Kawai sai ya shiga habaici, “I war haka gobe ai har mun manta ansha jinin – wasu, anyi farfesun kayan cikin su.”

Babu wanda ya tanka masa ita dai Nasreen duk addu’ar da ta zo bakin ta yi take yi. Haka shi ma Nawfal idan ya yi addu’ar sai ya tofa mata. Cikin rada ta ce, “‘Nawfal bamu yi sallah ba.”

Girgiza kansa ya yi, “Ba za su barmu muyi Sallah a nan ba. Mu yi addu’a kawai Allah ya kubutar da mu.”

Shiru dakin ya yi sai kukan yara da ke tashi lokaci zuwa lokaci. Cikin dare kowa ya yi barci amma banda Nasreen da dan uwanta. Dukkansu saKe-saKe suke yi kowa da irin abinda yake ayyanawa. Ce mata ya yi zai je bandaki sannan ya samu ta sake shi. Yana fita ya dinga kallon hanyar yana mamakin irin girman gidan. Kai tsaye dakin tsafin ya leKa, a lokacin ne kuma kunnuwansa suka ji yo masa maganganun matsafan, haka kuma ya zura_ idanunsa, idanuwansa suka gane masa abinda ya gigita shi.

Wata ce a shimfide kamar gawa. Shugaban tasu tana zaune a kan kujerarta, wata kuma wacce babu ko tantama ita ce, ta bayyana dazu ta yi wa Nasreen gargadi. Shugaban ta fara magana, “Muna taya ki murnar zama_ sarauniya gobe. Tsawon shekaru ashirin kin kasa karban kambun nan

sai gobe za ki karba? Ni nafi ganin rashin Kwazonki ne ya jawo maki wannan abun. Idan ba haka ba, na shiga gidan malamai ma, na dauko yarinya na kuma sha jininta, bare gidan masu alaka da marasa addini? Gobe da kanki za ki ba dodo jininta, mu kuma za mu sha kayan cikinta, za mu fasa kanta mu shanye Kwakwalwarta, idan muka yi hakan za mu sami Karin lafiya.” , Gabadaya suka maimaita yi wa Sarauniyar gobe murnar samun wannan_ kambu. Ta ci gaba da magana kamar ba za ta yi ba, “Kai kuma sai yanzu ka kawo mana wannan yarinyar? To ba zan ce baka yi KoKari ba, ka yi namijin Kokari. Kun burge Kungiya a lokaci guda kun kawowa dodo kawunan da ba zai taba manta ku ba, haka zaku yi ta samun daukaka a duniya. Sai kuma ke Sarsarina, kina da taurin kai, mun baki nan zuwa gobe ki kawo mana mahaifiyarki da ranta, kuma ta budi idanu ta ganki a matsayin wacce ta kawo ta wajen tsafi, ki amshi tsinuwa daga gareta, sannan

Www.bankinhausanovels.com.ng    mu aikata lahira. Kuna gani nan, ban sami daukaka ba, sai da na kawo mahaifina da mahaifiyata da suka dauki son duniya suka dora min, haka nima bani da wadanda nake so kamar su. Amma na rufe idanuna na dauke su na kawo su gaban dodo, suka dube ni cikin dimuwa suka tsine min, suka yi min fatan tsiya, suka ce ba zan gama da duniya

. lafiya ba. Kun ji mutanen da suke Karyar suna sona, amma sun kasa sadaukar min da

– Kaunar da suke yi min ta hanyar bani rayuwar su.”

Gabadaya dakin aka fashe da dariya. Abin mamaki labarin da ya kamata ayi ta mata kuka, wai dariya suke yi mata har da kifawa suna tashi. Sai da ta daga wata sanda sannan duk suka yi shiru.

Www.bankinhausanovels.com.ng  Ita dai wacce aka kira da Sarsarina babu fara’a a fuskarta. “Ya shugabata, ban taba yi maki musu ba, anbuKaci mahaifina na dauke shi na bayar da shi, anbuKaci mijina duk na bada su. Mahaifiyata ta sha wahala akaina, bana _ fatan inzama

sanadiyyar barinta duniya. Ya shugaba a bar ni da wannan daukakar ta isheni, bana son Kungiya ta sake bani wata daukaka ko matsayi.”

Nan da nan annurin fuskar wacce aka kira da shugaba ya bace bat! “Ke! Kada ki kawo mana zancen banza kin ji? Ya zama dole ki kawo mahaifiyarki da kanki ba sako zan ba wani ya kawo min ita ba, albarkar da ) na samu agun iyayena kafin su bar duniya, sai kowannenku ya sami wannan albarkar. Za ki kawo ta ko kuma sai na dauki mataki akanki? Zan iya daureki shekaru dari ina gana maki azaba, bayan kuma na daukota da Karfin tsiya.”

Sake KasKantar da kanta tayi, “Ina neman tuba ya shugabata. Na amince zan kawo mahaifiyata da ranta. Farin cikinki a kullum shi ne nawa.”

A nan suka yi wasu maganganu wanda su kadai suka san abinda suke cewa. Sannan aka ba wani wuka ya karba yana mai sake rusunawa alamun girmamawa.

Wannan yarinyar da ke kwance kawai ya caka mata wukan, wanda yasa Nawfal gigicewa ya ture wani abunda bai san ko mene ne ba, jikinsa babu inda baya rawa.

A gigice suka walwayo basu ga kowa ba, a take aka tura wasu guda biyu su je su bincika waye yake yi masu leken asiri? Jikin Nawfal yana rawa, yana KoKarin komawa dakin da aka kai su sai dai ko sama

Www.bankinhausanovels.com.ng  ko Kasa ya rasa gane wani dakin ne? Hakan yasa ya sami wuri ya labe jikinsa yana kyarma. Ita kuma Nasreen da ta ji shiru, sai kawai ta fito tana lalube tana neman Nawfal. Duk a tunaninta sun tafi da Nawfal dinne shi ya sa ta gigice, tana tafe tana cin karo da abubuwa. Don haka mutanen nan suna fitowa suka yi arba da ita tana lalube. Cak! Suka dauketa suka kai dakin tsafin. Nawfal yana jin shiru ya koma yana duba dakin, da Kyar ya gano dakin yana shiga babu Nasreen babu dalilinta. Ya duba ko ina bai ganta ba, hankalinsa ya sake tashi, ya fito yana dube-dube. Kai tsaye dakin tsafin

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page