RUBUTACCIYA BOOK 2 CHAPTER 4 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

 RUBUTACCIYA BOOK 2  CHAPTER 4 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

Www.bankinhausanovels.com.ng 

MUN TSAYA 

Sultan ya gyada kai yana dubanta, “Za mu mayar da ku gidanku, zamu sa ‘yan sanda su kula da shige da ficenku. Ina buKatar sanin inda zan je inga Sani a kwana biyu kacal. Kada’ki wuce hakan. Maganar miliyan dayanku da muka yi maku alkawan ‘yan sandanmu za su tafi maku da kudin sai kuyi amfani da su. Ya zama dole mu gano

wanene azzalumin da ya aikatawa Saudat fyade ya kuma aika aka kasheta.” Sai da aka fice da su kafin suka zubawa juna ido da alama sun rasa mafita.

Ashmaan ya fara magana yana duban su, “Zan watsa hotunan Saudat a duniya, zan rubuta muna neman wanda ya kasheta, akwai kyauta mai tsoka. Bayan nan da wasu kwanaki zan watsa hotunan Nasreen da Nawfal in kuma ambatar babban kyauta ga duk wanda Allah yasa ya gansu.”

Mahbub ya dube shi a tsanake, “Mene ne fa’idar yin hakan?”

Aslaf ya zare glas din idanunsa yana sake duban Ashmaan, “Idan kayi hakan

ZAMU TASHI 

Ashmaan za a sami matsala. Wanda muke nema zai gane magana bata mutu ba, daga nan zamu fara wasan buya.”

Al-ameen ya girgiza kai ya ce, “Tabbas zai iya ankarewa da muna nemansa, ko ya gudu, ko kuma ya sanya mu fara farautar juna.”

Haisam ya ce, “Zai fi kyau mu fara gano wanene Sani? A ina za mu gan shi?” Barrister Tajuddeeen idanunsa yana kan Laptop da alama shi ba zai yi Korafin ba. Sultan ya zare glas ya ce, “Abinda Ashmaan yake fada akwai alamun hakan za a yi. Yanzu lalube muke yi a duhu, a yanzu ne za a fara wasan. Kawai ya gudu a cikin daji mu kuma muyi farautarsa. Idan muna binsa a boye zamu ci gaba da samun matsaloli, gara yasan muna nemansa, ta hanyar guduwarsa ne za mu iya gane shi.”

Ashmaan ya ce, “Very good mutumina. Hasashena kenan. Idan muka sa hoton Saudat zamu yi amfani da kalamai wajen jawo hankulan jama’a akan abinda ke
Www.bankinhausanovels.com.ng faruwa, daga nan hankalinsa zai tashi, zai fara farautar Anti Nora. Ita ce macen da yake da tabbacin inhar hukuma ta gana da ita, kashinsa ya bushe. A lokacin da za a kaiwa Nora farmaki, mu kuma mun dauke su daga wannan wurin, haka yaranmu za su yi ta kula da motsin kowa. Tarko zamu kafa masa insha Allahu zamu kamo shi. Amma idan aka ce a nemo inda Sani yake, amsar ita ce babu wanda yasan a wacce duniyar  Sanin yake ciki a yanzu. Kun ga ashe wahala za mu ci gaba da sha, har mu ji mun

gundura da abin. Ku bar min wannan aikin @ hannuna ni na san yadda zan yi. Sai mu dage da addu’a domin ba a fara ba, yanzu dai za a fara wasan.”

Wannan bayanai na Ashmaan da Sultan ya gamsar da kowa haka kowa a wurin ya jinjina wa kaifin tunanin su. Haka suka tashi taron kowa ya kama gabansa.

Dukkan abubuwan da Ashmaan ya tsara, ya tsara su ne tare da taimakon Sultan, cikin ikon Allah aka_buga bayani akan

Www.bankinhausanovels.com.ng mutuwar Saudat, yadda aka kasheta, da kuma yadda ake neman Nora, da kuma wanda ya yi kisan, ganin Nora kadai ne zai Sa a gano waye ya yi kisan nan. Hankula sun tashi, yanayi ya sauya, wurare sun canza Haka sun dauke Nora da mijinta, Abin mamaki da al’ajabi sai gashi anshiga an sace Nora da mijinta, a lokacinne ‘yan sanda suka ci nasarar kamo wanda yaje da ninyar yin kisan. Sai dai yin hakan ya Kara tada hankalin wanda ya aikata wannan . mummunar aikin. Haka Karin jin dadinsa bai bari wadanda ya tura sun san fuskarsa * ba, bare har a ambaci sunansa a Police Station. Wahalar duniyar nan sun sha a – wurin Sultan amma babu takamaiman bayani. Wannan abu ya Kara jefa Sultan a cikin dogon tunani. A kwanaki biyun nan  babu ranar da ba zai yi mafarkin Nasreen ‘. dinsa a cikin wahala da masifa ba. A cikin garin na Kaduna Sultan ne tsaye yana , Karewa gidan su kallo da har sun mance da ‘ wata Nasreen da ta yi rayuwa a cikin su.
Www.bankinhausanovels.com.ng Yana shiga ya sami babu kowa, don haka ya kwanta, wani irin barci na babu gaira babu dalili ya kwashe shi.

A Katon falon da shigowarsa kenan ya samu. Ya sami Abban zaune a falo ya Kurawa tv idanu, ita kawa Umma sai aikin masifa take yi, tana yi tana Karawa.

Cike da mamaki ya shigo falon, sai ya dubi Umma sai kuma ya dubi Hafsat da take kuka kamar ranta zai fita. “Yauwa gara da Allah ya kawo min kai, ba zan iya ganin wannanr tashin hankalin ba.”

Abba ya dube ta cike da _ takaici, wanda hakan ke nuni da idan ma asirin ake banka masa, to Allah ya kubutar da shi, “Kada ki kuskura ki sa min da a cikin shirmanki da ‘ya’yanki. Ba su ba ne ‘ya’yan so? Alhamdulillahi. Tun yaran nan suna Kanana nake gargadinki da ki daina zagin ~ ‘ya’yan wasu, amma kika sawa kunnenki auduga kika toshe. Ke baki son mazinaci ko? Kin tsani zina ko? ‘Ya’yan zina ba su isa su zauna a cikin gidanki ba, har sai da

Www.bankinhausanovels.com.ng kika kora su suka bi duniya. Yau ga ‘yarki da dan zina a cikinta, kuma Wallahi! Babu mai zubar da cikin nan sai an haife shi. Haka babu matakin da zan dauka ‘yarki ce ki yi duk yadda kika gadama da ita. Daman ‘ya’yan so ai Karshen su kenan.”

Sultan da yaji wani irin jiri mai Karfi ya shige shi, ya fada cikin kujera cikin wani irin jiri wanda bai san lokacin da ya zauna din ba. Yana ta kallon Hafsat na kallon tsoro da firgici. Hafsat ta Bata wayonta, amma bai ga laifin kowa ba, sai laifin mahaifiyarsa. Mace ce mai tsananin son kanta, sai Allah ya nuna mata ishara tun a gidan duniya.

Yana son ya yi magana Abban ya daga masa hannu. “Babu ruwanka ban kuma yarda kayi magana ba, ka zuba masu idanu su Karata can. Ai kaf zuri’arsu babu mazinaci, don haka babu wani yaro da ya isa ya aikata zina a gidan Hajiya Salma.”

Sultan ya mike ya dinga kifa mata mari yana Kwallo da ita, domin ji yake gara ya kashe ta da ya ga irin wannan abin

Www.bankinhausanovels.com.ng kunyar. Firgigit ya farka daga irin barcin da yake yi, jikinsa duk ya jike da gumi. Idanunsa ya watsa a kan Hafsat wacce ita ta zo tashinsa.

A dimauce ya ce “Ke zo nan. Uban me kike jira baki fitar da mijin aure ba? So kike sai kin gama zama Mama a gida kafin ki yi aure?” Hafsat ta turo baki tana mamakin nawa take da har za ta yi aure yanzu?

Shi dai Sultan ya kasa dawowa hayyacinsa da irin mummunar mafarkin da ya yi akan Hafsat. Haka sai kallon cikinta yake yi kamar mai son dole sai ya tantance cikin gareta ko kuwa sharrin mafarki ne? Tirkashi! Duk ranar da Hafsat ta yi cikin shege babu ko tantama kashe ta Umma za ta yi ta huta. Ya fi kowa sanin yadda Ummansa ta tsani zina, ko da yake tsanar Zina a jinin zuri’ar Umma yake, kaf dinsu ba su Kaunar mazinaci ya matso inda suke, shi ya sa kullum a cikin tsaftace kansu suke. Www.bankinhausanovels.com.ng

Nasreenn ta farka cikin dare tana ja da baya, haka hawaye masu yawan gaske suke zuba daga idanunta. Tabbas ta ji hannayen wani a jikinta, amma kuma ba ta san ko wane ne ba, sannan tana da tabbacin Mansur baya gidan, hasalima yayi mata sallama da zai yi tafiya. Idan wani ne ya shigo ina masu tsaronta? Lalubawa ta yi tana neman Nawfal bata ji shi ba, ga hucin mutum a dakin,

Cikin kuka ta fara kwala kira, “Nawfall” Ji ta yi an toshe mata baki, ta yadda baza ta iya Kwacewa ba. Tashin hankali ya sake bayyana a bisa dakalin fuskarta. Da Karfi ta daddage ta ingice shi ta yi hanyar waje da gudu, sai dai bata sani ba, ta doshi bango ta buga kanta da karti. Tsananin azabar da ta tsirga mata yasa ta ja da baya, duk da haka bata daina Kofarin ficewar ba.

Hannunsa yasa ya dawo da ita baya, yana Kokann banKadeta, Tana son yin ihu babu dama haka kuma karfinta ya soma

Www.bankinhausanovels.com.ng Karewa. Mutumin da ke kwance akanta yaji anbuga masa wata sanda, mai girma da kauri. Da Karfi ya rike kansa sannan ya dago yana mazurai.

Nawfal ya zaro dukkan idanunsa, “Mansur! Kai ne? Kai da ka yi tafiya yaushe ka dawo har kake KoKarin kashe Nasreen? Innalillahi wa inna ilaihirraji un. Nasreen Mansur ne yazo yake son nakasa maki rayuwa. Ai na gaya maki mutumin nan baya sonki amma kika nuna min Karya nake yi. Ga shi ai shi yake baki wahalar nan.”

Nasreen ta shafi goshinta da yake mata radadi, “Nawfal ai Mansur baya garin nan ya akayi ya dawo? Mansur baka sona ka fitar da ni daga wannan gidan Wallahi na gaji.”

Mansur ya dan shafi kansa. “Kin gane ko? Kawai ina can ne aka yi min waya wai kuna son ku gudu ku bar gidan nan, ni kuma ” da na ankare sai na shammaci kowa na dawo. Abin mamaki sai na sami kuna nan, Shaidan ne ya rinjayeni a kan ki Nasreen ke

Hmmm ASHA RUWA A KOMA AIKI LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page