RUBUTACCIYA BOOK 2 CHAPTER 2 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

 RUBUTACCIYA BOOK 2  CHAPTER 2 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

Www.bankinhausanovels.com.ng 

A JIYA MUN TSAYA 

Ranar Lahadi Www.bankinhausanovels.com.ng insha Allahu za ku nemo min ma’aikata masu aikin abinci za su kawo mana lunch, ina da baki.”
Da girmamawa suka amsa masa.

. Sultan ya Kurawa gefen titi idanu, har yanzu yana nan da halayyarsa na son kallon gefen titi. Haka abubuwan da suka faru shekarun baya suna nan manne a ransa sun Ki gogewa. Yana jin yanzu ne zai dauki fansa akan koma waye ya ingiza rayuwar Saudata ° cikin Kunci.

Nasreen tana zaune a gaban Mansur ° ya ajiye mata nama zuciyarsa cike da farin cikin yadda Nasreen ta kwantar da hankalinta. Doguwar riga ya kawo mata ya ce ta sauya wanda za ta yi zaman takaba da ita. Yana fita ta rungume doguwar rigar ta shaki kukanta yadda ranta ke so. Sannan ta sauya kayan kamar yadda ya buKata. Bata san ya shigo ba, sai muryarsa ta ji, “Kin yi kyau sosai. Bari ki gama takabanki za ki ga yadda zan mayar da ke Nasreen. Idan har za ki dinga bani hadin kai ni kuma zan mayar

ZAMU TASHI 

da kea bin alfahari a idon duniya. Ki kwantar da hankalinki zan nuna maki ba Sultan ne kadai mai Kaunarki ba.”

Kuka ya taho mata da gudun gaske ta shanye kukanta tana sakin ajiyar zuciya. Tana jin dadi ne idan ta tuna bata da idanun da za ta dube shi bare har bakin cikinsa ya kasheta. Shi dai Nawfal yana nan daga waje, yaki amincewa ya yi nisa da inda suke, gani yake yi kamar Mansur zai iya cutar da ita.

Mansur ya fahimci abinda Nawfal yake nufi don haka ya yi masa wani inn kallo kafin ya bushe da dariya ya Kara da cewa, “Ji dan tatsitsin yaron nan! Wanda baka wuce in fyato ka daga hancina ba, wato ka tsaya kai a dole ga mai gadin ‘yar uwarsa. Idan wani abun zan yi mata tuni zan sa a banKare min kai a wancan bishiyar.” Ya nuna wata bishiya dake tsakar gidan. Nawfal ya dube shi ido cikin tdo babu wata alama ta tsoro, ““Ni ma ban ce maka www.bankinhausanovels.com.ng ina gadinta ba. Haka baka isa ka yi mata abinda Allah bai tsara zai faru da ita ba.”
Mansur ya sake bushewa da dariya, hakan yasa Nawfal wuce shi ya afka dakin da Nasreen take. Ya rada mata a kunne ta yi wata magana da za ta nuna alamun tana son Mansur. Nasreen ta cije lebbanta tana jin daci a wuyanta sannan ta daure ta fara magana muryarta tana rawa, “Nawfal me ya sa za ka gayawa Mansur magana? Ka mance shi yake shirin taimakona ya aure ni duk da bana gani? Ka mance shi ya rabo mu da zaman KasKancin da muke yi a Kankia ya kawo mu nan? Ba mu da matsalar abinci, haka shi yake bamu dukkan abinda muka buKata. Ka daina gaya masa magana ka ji Nawfal?”

: Mansur da ya labe yana sauraransu farin ciki ya kasa barinsa har sai da ya bayyana a gabansu. “Nasreen za ki ji dadina fiye da tunaninki. Zan mayar da ke tauraruwa a cikin gidan nan. Kai kuma kayi min biyayya.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Nawfal ya hade rai yana dubansa, “Babu biyayyar da zan yi domin ban gama yarda da kai akan ‘yar’uwata ba. Idan da gaske kana son ta me zai sa ni ma ka dinga takura min kana hanani yin abinda nake so? Idan ita mace ce ai ni namiji ne, a bar ni infita in nemo gumina saboda ban saba da zama ba.” Mansur ya dan yi shiru, “Za ka iya sana’ar fashi da makami?” , Nawfal ya zaro idanu, “Allah shi kyauta ya tsareni. Ce maka na yi zan je in nemi halalina ba hakkin wasu ba.” Mansur ya yi murmushi ya fice yana jinjina Karfin taurin kai irin na Nawfal.

Yana fita ya dubi Nasreen ya ce, “Kin gani ko? Sai kin dinga daurewa idan kina son mu fita daga gidan nan lafiya lau. Bana son koke-koken nan da kike yawan yi bana jin dadi. Ki daurewa zuciyarki za ki iya Nasreen.” Gyada kanta kawai take yi, amma ita kadai tasan menene a can Kasan zuciyarta. Www.bankinhausanovels.com.ng

Ashmaaan ne zaune a cikin mota a unguwar Magajiya da ke Kaduna. Idan bai yi Karya ba nan ne gidan su Kawar Saudat da aka nuna masa, wanda aka tabbatar masa a nan gidan take aure da ‘ya’yanta. Ya rasa ta yadda zai yi ya sami shiga cikin gidan ba tare da wata matsala ba, kasancewarsa musulmi. Dole ya aika yaro a yi masa kiran mai gidan. Aka tabbatar masa da baya nan .. yaje gona, sai dai matarsa. Idan lissafinsa ya yi dai-dai zuwansa na shida kenan yana . neman gidan bai taba cin sa’a ba, sai yau da aka tabbatar masa da nan ne gidan Nora. Haka hoton Saudat da ya nuna angane ta har aka furta sunanta da Justina. Yana nan zaune har Allah ya fito masa da matar da yana ganinta ya gane ta, ita ce ta cikin hoton nan. Fitowa ya yi daga motarsa ya Karaso kusa da ita, “Sannu madam.” Ta dube shi da tsoro a idanunta ta ce, “Yauwa sannu.”

Bakinsa ya rufe ne sakamakon yadda take tafiya tana waiwayarsa, alamun ba za ta www.bankinhausanovels.com.ng tsaya ba. Da sauri ya taka ya biyo a, “Madam ina neman gidansu Justina ne.” Ya fada hakan ne domin ya sa mata razana a jikinta, kuma ya ci sa’a domin kuwa jikinta yana kyarma ta dawo da baya, tana dubansa. “Ka ce kana neman waye? Justina?” Ashmaan ya daga mata kai alamun haka ne.

Matsowa ta yi daf da Ashmaan sannan ta ce, “Justina ta dade da mutuwa, ba mu ga

; gawanta ba, ba mu san inda take ba. Amma ta mutu. Ni ban santa sosai ba, a unguwa kawai mun tashi.”

Ashmaan ya zaro idanu, “Ta mutu? Ina neman ta ne in bata kudadenta miliyan biyu da ta taba ba Babana aro, shi ne ya ba ni hotonta ya kwatanta min unguwar nan ya ce duk ranar da na dawo Kasar nan in neme ta in ba ta saboda ta taimake shi.” Nora ta zaro idanu kasancewarta mayyar abin duniya, “Miliyan biyu? Waye ne zai ba Justina miliyan biyu? Ina ganin Alhajin nan ne zai bata, ita kuma saboda
Www.bankinhausanovels.com.ng tsoro za ta bada aro. Ka yi haKuri mu koma inuwa, nice babbar Kawarta bata da Kawa kamana a nan unguwar.”

Ashmaan ya saki ajiyar zuciya ganin abinda yake nema zai same shi ba tare da yasha wahalar da yake tunani ba. “Tunda ke babbar Kawarta ce na san kin san family dinta sosai, zan iya ba ki kyautar dubu dari biyar ki hada ni da iyayenta domin in ba su _ – kadarorinta.” Nora ta rufe ido ta sake budewa. – Tunda take bata taba ganin ko da dubu hamsin ba, amma yau gashi ance za a bata dubu dari biyar domin kawai ta fada inda gidan su Justina yake. Tuni ta sauke daron da -ke kanta tana dubansa, “Babu komai Alhaji.” ; Ashmaan ya dan saita abin daukar maganarsa, ya ce, “Amma me ya kashe ta ne?”
A nan kuma sai Nora ta yi sit! Domin ba ta mance irin gargadin da aka biyo ta har gida aka yi mata ba,
Www.bankinhausanovels.com.ng kasancewarta wacce tasan komai akan rayuwar Justina. Girgiza kai ta yi, “Ban sani ba woo.. Ka ba ni kudin in kai ka gidan da kake so ka sani, ba mu da nisa.” Ashmaan ya rikKe kansa, ya san zai sha wahala a gun Nora matuKkKa. “An ce an kashe ta ne?” Nora ta yi wani irin zabura, sannan ta dauki daronta ta aza a kai ta yi gaba abinta, tana tafe tana sake waiwayo Ashmaan, sai kuma ta yi kamar za ta dawo idan ta tuna makKudan kudaden sai kuma ta tuna da rayuwarta tana gaba da komai, don haka ta hakKura ta ci gaba da tafiyarta. Mutuwar Justina ta dawo mata sabuwa, tana son Justina fiye da tunanin mai tunani.

Ashmaan ya rikKe kansa, dole ya tattara ya koma Hotel din da yake ya kwanta shiru. Kewar Ibtihal dinsa yana sake damunsa, dole ya jawo waya ya kirata. Sai dai ‘yan tagwayensa ne suka dauki wayar, hakan ma ya yi masa dadi, domin sun taimaka masa wajen rage masa dukkkan damuwar sa yake
Www.bankinhausanovels.com.ng dauke da ita. Sai wajen yamma, a lokacin wurin ya yi sanyi, don haka ya fito cikin shigar Kananan kaya. Abin mamaki Sultan ya gani, shima cikin shigar kayan gida, yana daga zaune yana latsa waya. Har zai yi masa magana, ya Kyafta masa idanu, don haka ya basar kawai. Wannan karon mai gidan ne ya fito da kansa, Sultan ya ba shi hannu suka gaisa. “Ba ka gane ni ba ko? Ni abokin Samuel ne. Ina neman gona ne shi ne ya ce min in zo wurinka za ka taimaka min.”

Daniel ya cika da farin ciki, ya san zai dan sami wani abu, don haka ya washe bakinsa suka sake gaisawa. Ashmaan yana daga nesa yana mamakin irin salon Sultan.

Zama suka yi yana bashi labarin yadda wuraren suke da kuma irin amfanin da zai samu. Sultan ya aikawa Ashmaan text a kan ya zo ya aiwatar da aikinsa,. Ashmaan ya Karaso ya ba su hannu duk suka gaisa. Sultan yana yi masa wani irin kallo kamar bai taba ganinsa ba. Www.bankinhausanovels.com.ng

Nora ce ta fito da nufin zubar da shara, tana ganin Ashmaan ta zaro ido tana nunawa Danicl ta ce, “Daniel ga mutumin nan shi ne.”

Daniel ya ce, “Sannu. Ka yi haKuri ba mu San mene ne ya samu Justina ba.”

Sultan ya dube su ya ce, “Wace ce kuma Justina? Ko matar nan da ta mutu shekaru kusan ashirin baya?”
Gabadaya suka kafe Sultan da ido. Ashmaan ya dubi Sultan, ya riKe shi, “Don Allah kana da labarinta ne?”

Sultan ya fizge kansa, “Sake ni mana malam. Na sani lokacin ina yaro Karami.” Ya fada tare da kawar da kansa. Ashmaan ya ce, “Zan ba ka miliyan daya idan har za ka gaya min labarinta. Kawai abinda nake son naji kenan, sannan ka dauke ni ka kai ni gidan iyayenta.”* Jin miliyan daya ya sake kidima Nora da mijinta. Sultan ya ware idanunsa ya ce, “Miliyan daya? TirKashi! Ni yanzu ma sai in gaya maka. Justina an kashe ta ne, saboda www.bankinhausanovels.com.ng tana da cutar Kanjamau, shi ne wasu suka sassare ta suka kashe ta. A kan idona abin ya faru. Da farko ma ana tunanin tana da ciki ne, ashe duk sharrin mutane ne, bata dauke da komai. Nora da Daniel suka zaro idanu jin Sultan yana ta sakin Karya kuma hankalinsa a kwance. Yana gamawa ya ce, “Sai muje innuna maka gidansu ka bani kudina.” Ashmaan ya ce, “Amma na gode abokina. Nayi maka alKawarin inhar _ maganganun da ka gaya min gaskiya ce, zan daukeka har Kasar nan ka bari. Kai musulmi ne?” Sultan ya kalle shi ya ce, “A’a ni _ inyamuri ne.” Ashmaan ya yi murmushi, “Kayi haKuri ba fada bane.” Daniel ya ce, “Wannan labari akan Justina ba gaskiya bane. Mune munsan gaskiya.” Nora ta ware – idanunta ta ce, “Daniel! Ka zo mu yi shawara ya dawo gobe.”

Sultan ya ware idanu, “Au labarin da zaku bayar ne sai kun yi shawara? Ga kudi har miliyan daya? Wanda za ku iya yin shekaru goma kafin ku same su. Ni babu
Www.bankinhausanovels.com.ng ruwana ka Kyale su kawai ka zo mu je ingaya maka komai.”

Daniel da ya kidime ya ce, “Pls ka dawo gobe zamu san abin yi, har ka ji yadda akayi Justina ta mutu.” Ashmaan ya yi masu sallama ya wuce.

Yana tafiya Nora ta dubi Daniel gaba daya ta mance Sultan yana wurin, kuma ko ta tuna ba za ta kawo komai a ranta ba, kasancewar tare da mijinta ta gan _ shi. “Daniel kasan mutumin nan a lokacin irin wahalar da ya dinga bamu saboda kawai yana tunanin zamu je mu tona masa asiri? Ni ina jin tsoro kada ya kashe mu.” Daniel ya girgiza kai, “Yanzu mutumin ya mance — da mu, yasan kowa ya manta da maganar mutuwar Justina, don haka babu idon kowa akanmu ki yarda da ni.” Sultan ya rufe idanunsa ya nausa duniyar tunani, “Waye wannan mutumin? Me yasa yake bin duk wanda yasan yana da alaKa da _ sanin mutuwar Justina? Insha Allahu komai ya kusan zuwa Karshe.” Nora ta koma ciki  Daniel kuma ya dubi Sultan yana harararsa, “Kai ina tunanin wani Alhaji ne mai kudi,  da kazo maganar gona, sai gashi kana jin ance miliyan dayaka gigice. To noman nawa za ka yi?” Sultan ya dube shi yana sake nazarinsa, “Dubu hamsin gareni na kawo a bani gona muyi noma.” Daniel ya zaro ido, “Duk a dubu hamsin din?” Sultan ya ware idanunsa yana gyada kansa domin kan yana matuKar sara masa, ji yake kamar ya shake su. Daniel su gaya masa komai._ Daniel yaja dogon tsaki, “Ka tafi kawai. Ban san inda za ka sami wadannan – – abubuwan ba.” Sultan ya wuce abinsa yana taka Kasa kamar mai tausaya mata. Kansa a Kasa yake tafiya tunani ne kala-kala a cikin kwanyar kansa. “Sai ka zo mu tafi.” Muryar Ashmaan ya ji, don haka ya waiwaya, ya Karasa tare da bude motar ya shiga. Duk kwanar da suka zo sai Sultan ya ce su dakata, abin mamaki duk inda suka tsaya ‘yan sandansa ne cikin shigar fararen kaya. Ashmaan duk yadda yake tunanin www.bankinhausanovels.com.ng lamarin Sultan ya wuce hakan. Sun nausa titi babu wanda ya iya cewa_ uffan! Ashmaan ya yi magana ba tare da ya dube shi ba, “Zamu wuce wurin da aka kashe Saudat!” Sultan idanunsa suna kafe a bisa titin kamar mai son sanin yawan motocin da ke wuce wa. “’ Yan sandana suna wurin. Na sa daya aikin faci a wurin, na kai daya koyon kanikanci na babbar mota, daya _ _kuma yana can ya zama mahaukaci bashi da wurin zama da ya wuce wurin da akayl kisan nan. Suna nan dai sun mamaye wurin.” Ashmaan ya gyada kai, “Da haushi kake bani da nake zaton baka dauki abin da mahimmanci ba, amma yanzu na gama ganewa kalar naka daban ne. Ya akayi ka gano su Nora? Bayan komai yana hannun mu?” Sultan ya dan waiwayo ya dube shi, ‘Na gano ta ne, a dalilin C.1.D na, su suka yi min wannan KoKarin.” , Babu wanda ya sake cewa uffan, har suka iso Hotel din da Ashmaan ya kama Hotel. Ashmaan ya zauna a falo yana www.bankinhausanovels.com.ng mayar da ajiyar zuciya, Sultan kuma ya wuce ciki ya watsa ruwa. Abincin da aka jere masu babu wanda ya dubi abincin. Sultan ya mike ya dauki Power Horse ya kai bakinsa, yana jin yadda sanyin ruwan ke sauka a cikin maKoshinsa. Yana nan tsaye a _ windo yana duban waje, sannan ya saki labulan ya dawo yana magana, “Ashmaan matar nan tana da shegen kafiya, da wahala ko goben ka koma ta saki jiki ta bamu_ .abinda muke so. Ya zama dole mu nemo mafita, domin ita ce take dauke da dukkan .bayanan da muke nema. Ina son sanin waye mahaifin Nasreen! Ko ma waye mahaifin Nasreen akwai wani boyayyen lamari a tsakani mai girman gaske. Ashmaan ko ban sake ganin Nasreen ba, zan_ sauke alKawarina da na dauka! Ni zan zama gatan Anti Saudat, ko da kuwa yin hakan zai iya sawa inrasa aikina, inrasa iyalaina, inrasa mutuncina, in rasa dukiyoyina. Zan aikata hakan da Karfin guiwana. Ashmaan mu www.bankinhausanovels.com.ng nemo abin yi tun kafin wannan damar ta kubuce mana.”

Sultan ya yi nisa, sannan ya ce, “Zan tura ma’aikata su kwaso min ita da mijinta, ba tare da sanin kowa ba. Yin hakan zai taimaka mana wajen sanin abinda ya kamata mu sani. Lokaci baya jiranmu, yau idan mutumin da ya aikata wannan laifin ya mutu ba tare da ya san da akwai Kwansa a duniyar nan ba, ba zan yafe wa kaina ba, zan kalli kaina a matsayin mutum mai sakaci da rashin mayar da hankali a kan abu mai mahimmanci.”

Ashmaan ya gyada kansa, “Hakan zai iya yuwuwa. Amma Sultan baka ganin idan aka kama su ta Karfi za su iya botsare mana su hana mu jin abinda muke son ji? Kasan ita Nora tana da kafiya, duk baKar talaucin da suke ciki hakan bai sa ta saki jiki da mu ba.” Sultan ya sake kai Power Horse bakinsa ya zukKa, sannan ya dawo da dubansa ga Ashmaan, “Dan sanda yana sa Shugaban ‘yan daba ya yi bayanin da kudi www.bankinhausanovels.com.ng basu isa su sa shi ba. Muna da abin da za mu jona masu suyi bayani ko basu yi ninya ba.” Ashmaan ya yi murmushi, “Kada ka wahalar da su, na tabbata za su yi bayanin.” Zakuda kafadunsa ya yi, “Kada ma su yi. Idan miliyan daya bata sanya su bayani ba, ina tabbatar maka batir da wayan wuta za su kawo bayanai dalla-dalla.”

Sultan yana nan zaune, yana jin yadda Ashmaan yake soyyaya da matarsa kamar yau aka daura masa auren. Sai da ya sauke wayar Sultan ya dan dube shi ya ce, “Kasan wani abu ne? Wallahi ina mancewa ina tare ~ da wata mata a cikin gidana. Abinda ke daga min hankali yarinyar nan duk abinda muka yi sai ta gayawa mahaifiyarta? Kai ranar da naji da kunnena ban iya barci ba.”

Ashmaan ya shafi kansa ya ce, “Mahaifiyarta fa ka ce? Wannan kam yafi Karfina. Wayewar ta yi yawa.” Sultan ya ce, “Yauwa kasan Allah? Idan ka sake ce min ni musulmi ne sai nasa anboye min kai, inga yadda Ibtihal za ta yi . Baka san dazu

HMMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GANA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page