NA SHIGA ALJANNAH BOOK 1 CHAPTER 7 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

NA SHIGA ALJANNAH BOOK 1 CHAPTER 7 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

Www.bankinhausanovels.com.ng 

MUN TSAYA 

maganar aljanu duk zaka ‘gani idan munje wajen “To” | . _ Adamu ya fada domin ya hutar da zuciyarsa Www.bankinhausanovels.com.ng  da-zuyata na jiran fahimtar Salmanu tare da Kokarin cirewa ransa damuwar da ta addabi ransa. Amma sai ya dage ya mayar da hankalinsa ga Salmanu wanda ya zage yana yi masa bayanin yadda ake wannan sabuwar ‘ sana’a ta wankin ido ba tare da an je wajen wani malami neman sa’a ko siddabarunsa ba. Hankali kwance kuma a wanke bayin Allah. Adamu ya kwashi gayar mamaki da yadda salmanu ya kwatanta masa yadda ake binne hankali da azancin masu yawon neman asiri, yadda ko shi aka yi wa wannan siddabarun sai – ya yi muguwar bayar da gaskiya. Kai tsaye Adamu ya gane wannan sana’ar sunanta damfara haKKun, amma tunda da tsoka kuma Salmanu ya baibaye shi da hujjar dama duk wanda zasu cuta ko su damfara Allah ya bari ya kama gaibu, ba laifi in an nuna masa yadda ya kama Kafar wala. Wata hujjar da Salmanu ya gabatar masa itace, sana’ar na kawo Kazaman kudi, a sauKaKe zasu kawo masa  kudin da zai auro masa Husna cikin wata daya kacal! 

ZAMU TASHI 

Ko an juyawa dukkan hujjojin baya wannan kadai ta ishi Adamu, domin yana jin HUsna da darajar da ko ta wane hali ne ma ya kamata ya sami aurenta, kuma in ya samu shi ne abinda ya dace da shi duniya da lahira. “Amma idan Goranmu ya kamo Katon kifi, akwai wata hanyar mai bullewa, ita ce ta tsakurar wani kaso daga abinda muka caji kostoma mu nemi Bokan gaske mu bashi aikin ya gabatar, maimakon namu da yake iska, ka gane?” , Salmanu ya karkare dogon jawabinsa da wannan Karin hasken. ~-:. Cikin karsashi Adamu ya kada kai, zuciyarsa na Kara karfin bugu tana hango masa samuwarsa Husna a duniyarsa.  Basu bata lokaci ba suka mike don fara daura damba, daidai lokacin kuma Salma ta kira Adamu a waya, kafin ya daga ya antayo mata ashar ta kai goma, sannan ya daga murya acushe yace mata. Malama lafiya?” | Ta hadiye jin

haushin tambayar tasa ta amsa masa cikin tambaya Www.bankinhausanovels.com.ng “Lafiya da aka yi me? A Kufule ya amsa, Da kika ishe ni da kira kamar ke kika sai min wayar™ Ta yi dariya, Ai ban san a saukar da Ka’idar sai an sai waya ake kiran mai ita ba, in haka ne ni da nake da burika kan kiranka ai yakamata na sai maka waya.. , Yayi tsaki cikin gundura, “Sai ki hada har ni ki siya, don in kin sai wayar ai kamar kin yi baki yi ba” Zata yi Magana ya tare ta,Malama don Allah kar ki cika ni da hayagaga, me nene dalilin kiran?” — Kai tsaye ta amsa, “Ankon nan, sati na sama ne bikin… Kafin ta dire ya tare ta,  “ki aiko a karbar miki zan fita” Ta dan yi ihun murna, Da gaske, kudin ko kayan?” “Oho!” Ya amsa mata. Ba ta damu ba ta sauke ajiyar zuciya Www.bankinhausanovels.com.ng Wallahi ga gidan babu kowa Yaya Adamu, ai na’ san hanya ne, me zai hana ka daure ka biyo min da shi?…” “Ashe ba zaki sanya ba kenan” | “To in fito kenan yanzu na karba? Gaskiya ina son karba yau na miKa wajen dinki”Adamu yayi jim, ya tsani zuwa gidansu, haka kawai shi ko son ganinta ba ya yi bare ace wai takanas wajensa ta zo, saboda haka nan da nan ya tare ta a cunkushe,  “Uwar gantali kenan, zan biyo miki dashi, mu kar ki wani kwaso Kafa ki zo mana gida” – Cike da murna Salma ta shiga gyada kai tamkar yana ganinta, .“Haba dan albarka ko kai fa” Bata jira cewarsa ba ta sauke wayar. Shi ma ya ajiye cikin bata fuska yana sauke idonsa kan Salman wanda ya ishe shi da fuskar tambaya, ya hau bashi labarin abinda ke akwai game da Salma da ankonta. Suna ta hirarsu suka fito dan fara shirye shiryen sana’arsu Adamu dauke da ledar kayan .Salma. Www.bankinhausanovels.com.ng Zancen Husna ne a bakinsa yana jaddada irin Kaunar da yake mata. . Salmanu ya fahimci lallai da gaske Adamu yake sai ya shiga Karfafa masa gwiwa cikin karsashi. Ka kwantar da hankalinka, mace fa ba _wani wahalar farauta ne da ita ba, ko baka da . ranyo in kana da tsari ka gama da ita” Cikin nuna karaya Adamu ya ce, Ayya! Don kana da kyau ne ba sa yi maka. wahalar shiga tarko Salmanu, amma ni ai Sai aikin sa’a kawai.. Ya katse raganarsa zuciyarsa na bugawa — fat-fat har Salmanu na lura da dagawarta, ya daga kai da sauri yana kallon saitin da Adamu ya shanya ido da baki yana kallo, sai ya ga wata kyakkyawar doguwar halitta tana ratsowa,  shi kansa Salmanu sai da tasa zuciyar ta buga ko da kuwa ma’anar bugun tasa da ta Adamu akwai bambanci. Bakinsa na rawa ya ji yana tambayar – Adamu, : “Ba dai wannan ce Husna ba?” | . “Ita ce Www.bankinhausanovels.com.ng Adamu ya amsa a hanzarce kuma cikin nasa . karkarwar harshen zuciya cike da debe Kauna da fata, saboda yadda ya ga Husna rai a bace kuma sun hada ido ta kawar da kai, kawai sai: ya Kaddara fishinsa ne, ya shiga uku! Ta fara Kin sa tun kafin ma ya furta yana sonta. Ya sami bakin Magana gareta karo na farko a matsayin yada manufarsa tun da sonta ya  tsira a zuciyarsa, Ranki ya dade” Ya ambata mata lokacin da ta-zo giftawa, a idonsa tana ta faman shan kamshi kamar jira take a kula ta, ta zabga mari. . – Ga mamakinsa da raguwar fargabarsa sai ta — dan dakata ta juyo kuma tana masa duban ina na san ka? Kwakwalwarsa ta yi shawagi kafin ta cafko makama, “Ko ba Telar nan ba ce?” -Ta kada kai cikin saurin da ba dan Adamu ma a rude yake ba zai gane fuskarta daban, Zuciyarta daban. Salmanu dai na kallonsu da nazari su dukan Www.bankinhausanovels.com.ng Ai na jima ina nemanki Hajiyata – Inji Adamu, yana Magana cikin wasa da zolaya. Husna ta yamutsa fuska da nufin dan rage damarar da ta yi wa fuskarta, ta yi murmushi sannan ta rausaya kai ba ta ce komiai ba. “Halan baki gane ni ba” Ya fada da alamu karayarsa na nema ta bayyana. Wannan karon kai ‘tsaye ta amsa kuma a yangace, “Na gane ka mana, ba Malam mai maballi ba ne wanda muka hadu a kantin kayan dinki” Ya tari numfashinta da karsashi“Yauwa kin tuno ni da kyau, to ya yau?” Ta dubi tsawon hanya da fuska mai nuna Kosawa, “Alhamdulillah. Neman me aka min?” “Dinki ne da ni’. Kai tsaye ya amsa. Ta ji Kirjinta ya amsa, don ba ta so neman nasa gareta ya tsaya a dinki kadai ba, sai dai ta yi saurin jin cewar in dinkin yayi sanadi ma Kila wancan yazo da sauKki. Www.bankinhausanovels.com.ng Ta murmusa ta dube shi ta ce, ~ “Na fada maka ba na dinkin maza” Ai na mata ne, kin gan su ma” Ya amsa kuma ya mika mata kayan Salma da zai kai mata. Salman yayi ta zarya cikin wata irin _-muguwar dariya, sai da Adamu ya yi masa alama sannan ya kama kansa cikin tu’ajibi ya cigaba da kallon wannan dirama. Husna ta karbi kayan ta buda cikin mugun~ sanyin jiki, tamkar ta bace a wajen take ji – gsaboda tsabar fargaba da jin an cita da yaKi. Ta sake daga kai ta dube shi ranta’a dan bace. Wa za’a dinkawa, ko kuma in ce ina measurement?” . : Adam ya dan yi turus Sannnan ya waske ta hanyar Kare mata kallo sama da Kasa, __ Kiyi kamar na jikinki komai da komai”  Ta kasa daurewa sai da ta bi ba’asi cikin tsuke gira, Kamar ni take kenan?”  “Wace ce?” Www.bankinhausanovels.com.ng Inji Salmanu da yaji ya kasa hadiye dariya ko saka baki Adamu ya saci idon Husna ya watsa masa harara, sannnan cikin tsabar yin fuska ya gyada wa Husna kai alamar amsarta Eh kenan. “A matukar gajiye da ciwon zuciya da takaici Husna ta sake: bude ledar kayan ta gani, sai sannan ne ma ta lura ashe ankon bikin aminiyarta Amina ne, wani mugun takaici yayi masifar turnuke ta, ba dan ba ta sai ankon ba, a’a wajen samari hudu ta karbi kudin ankon a wajensu amma a ganinta babu na birgewar da ya kai na Adamu wanda dinki ma sai ya kai wa budurwarsa don tsabar gatantawa. Kodayake ita kanta ta san a baibai ko a tarkon So. take yanke wannan hukuncin, inkai dinki gata ne, fiye da shi ma tana samu a wajen masu sonta, amma dai ta ji yaji da bata sami ko Kasa da haka a wajen wanda ita take so ba.. Ai ankon aminiyata ne ma” Ta hakura da kallon kayan ta mayar da ganinta gareshi tana hadiye hawayen da ke son . kunno mata. Www.bankinhausanovels.com.ng Cikin zumudi Adamu ya ce, “Allah ko? kawai kice an sara akan gaba?” Ta koma duban hanya cikin cin magani. A zatonta duk wannan fara’ar tasa ta zai bayar da. dinki masoyiyarsa ne. Ta nisa ta ce, “To ni zan wuce yaushe ake son dinki?” “Kin fi ni sani tunda kin san ranar bikin” “Haka ne, to yanzu yaya za’a yi? Baka san gidanmu ba bare ka zo karba, kai ko tsoron in gudu maka da kaya baka ji ba?” Ta daure ta Karasa maganarta da dariyar zolaya. Kai tsaye kuma fuskarsa na nuna yakini ya amsa mata, “Haba dai, wallahi kin fi karfin wannan. Ke dai kawai ki je da kaya kiyi min dinki mai dankaren kyau daidai jikinki, yadda za’ay in a karba na san Allah zai kawo” Ta yi saroro tana kallonsa. Abinda ya sanya numfashin Salmanu . bugawa. Sai ga Adamu ya kutsa hannu a aljihu ya dumbuzo kudin da ya bashi riKo ko Kirgawa – .. ba yi ba ya mika mata. “Ga kudin dinki? Www.bankinhausanovels.com.ng Ta dan rusuna kadan ta karba fuskarta babu walwala ta yi musu sallama ta wuce. Adamu ya bita da kallo cikin. shanya baki – Salmanu ya danki hannunsa wanda ya mayar  aljihu suna taba ragowar kudin da ya bari. Cikin fishi ya ce; “Ina fatan wannan matsiyaciyar dubun naka ka bata?” | Adamu bai bashi muhimmmanci ba sai daya tabbatar Husna ta gama bacewa idonsa sannan ya juyo ya dube shi, » “Me ka ce?” . : “Nawa ka bata?” Salmana ya tambaya cikin fishi. ~~ Tun daga zuciya Adamu ya ‘fara shiryawa rikicin Salmanu, cikin dakewa yace, “Sai dai mu koma ciki a Kirga” Bai ma jira cewar Salmanun ba ya wuce ya koma cikin soro ya hau bude dakinsa. | Salmanu ya biyo shi yana maimaita tambayarsa cikin fishi. Bayan sun shiga ma Adamu na neman guri  MUsamman ya: zauna sannan ya fito da kudin_ don a san ba Karamin aikin Salmanu bane Www.bankinhausanovels.com.ng  barnar da yayi wa kudin ba ta yi masa dadi ba yayi masa mahangurba yanzu. . Kai kuwa, hana shi zama Salmanu yayi sai ture shi yake yana hayaniya. Haka dai ya daure ya fito da ragowar kudin, sai ga shi dubu uku, wato ya ba Husna dubu ‘ takwas. Salmanu ya kasa Magana don haushi, Sal kawai Adamu ya basar ya ce, “Mu cancana wannan mu yi da su, na san -albarkacin sadaukarwar da na yi wa soyayya zaka ga Allah ya buda mana.. . Bai kai ga rufe baki ba Salmanu ya gakar masa wani wawan naushi a ciki, wanda ya sanya shi zubewa kasa wanwar a sume, jini na fitar masa ta hanci. Ko kadan Salmanu baiyi nadama ba, domin neman guri yayl ya zauna yana ta kunno ashar, “Dan iska, wannan dukan ma _ “ka _sadaukarwa soyayyar’”’ } : 

********************

Www.bankinhausanovels.com.ng Baason ran Salma ta bi Anti Sa’a unguwar da ta gayyace ta ba saboda saka ran Adamu – yana dab da iso mata da ankon da ya sai mata, kamar yadda ya sanar da ita. Ta yi gardamar. ‘zuwa unguwar, ita ma Anti Sa’a ta yi lallashin _ har sai data. kai ga zagi sannan Salma ta hakura ta shirya suka tafi. – Anti Sa’a na ta faman mita, “Banza ce ke wallahi, na rantse miki da Allah idan muka je-muka dawo, zai yi wahala Adamu ya kwanta bacci ba tare da ya dawo ya nemi inda kike ba”Wasi-wasi da mamakin duniya ya ishi Salma, bayan wani tsantseni da bai taka kara ya karya ba wanda yake kawo wa zuciyarta shawagi. Antinta ta wayar mata da kan inda zasu kai Adamu, gidan wani boka ne mai aiki Kamar yankan wuKa. A duniyar soyayyar Salma Kauna bata ce haka ba ko da kuwa haramci ya kau, to amma dai tunda mutuwar yawa kaka ce Sai ta bi ayari, a yadda Antin tace mata duk ‘matar da bata kai mijnta ko saurayinta gidan Www.bankinhausanovels.com.ng  – boka a wannan marrar ba to tabbas ita take zaman hakuri da shi. Da alama kalaman karfin gwiwa ne Antin ke mata, amma tsofonta ya ci dubu sai ceto, don ta shafa karfi gwiwar ta rasa. Kuma mutane ba zasu ga bekena ba idan aka gan ni budurwa wai na kai saurayi gurin boka dan ya so ni?” Ta furta cikin rawar murya , bayan ita da zuciyarta sun gama sakankancewa sun shiga Anti Sa’a ta tuntsire da dariya tana yi mata kallon mamaki, ta ce,. “Lallai Salma kanki a tukunya yake har yanzu. Shin baki san yanzu ‘yammata ma sun fi matan aure gane aikin boka ba? Zura ido ki Kirga min matan aure da ‘yammata in mun je” _ Da haka Salma ta saduda ta bayar da gari, – yayin da bangaren shirya-mafarki a zuciyarta ya lula ‘shirya mata auren Adamu da kama mata shi a hannu yadda zai amince su shirya iyali masu kyau da soyayya. A can cikin kauyen Bunkure suka iske gidan Bokan. Kamar yadda Anti ta labarta Www.bankinhausanovels.com.ng  Mata yammata sun fi matan aure yawa a wadanda suka tarar a alayi, sai ko dima-diman motocin da suka cika farfajiyar unguwar – bokan. Da Salma ta tambayi Anti Sa’a game da manyan motocin sai ta amsa mata da cewa, ai motocin ‘yan siyasa da ‘yan kasuwa ne, don ko _ ‘yan siyasa sun fi mata.laKantar zuwa gurin boka da matsafa, ta Kare da cewa; “Mata na hada kafada da “yan kasuwa da kuma ‘yan sane” Sai Salma taji zuciyarta tayi wani irin rauni, kamar hawaye ya zubo mata jin cewa har da ‘yan sane tana hada kafada ba ma ‘yan kasuwar ba, kai! Maza ba su yi ba aradu tunda ba sa abinda ake so sai an shaKo su ko an biyo musu ta bayan gida. Ta bar damuwarta a zuci da fuska kadai, ba _tare da gangar jikinta ta kasa aikin bin Anti Sa’a ciki suka hau layi a bencinan dake jere a soro cike da mata. Akwai kuma wani Katon soron wanda maza zalla ke bin nasu layin. Salma na ta rarraba ido tana shan kallon Kosassun matan da idan ta gansu a gari sai taci layar duk inda matsala take ba su san taba bare suje gurin boka neman warakarta, Www.bankinhausanovels.com.ng a ganin Salma ga su da kyau, ga kudi, to me suke nema? Kamar Anti Sa’a ta san abinda Salma take rayawa a ranta sai ta hau Kara mata bayani duk dai dan ta Karfafa mata gwiwa. ‘ _ “Wasu matan ba wai matsalolin miji kadai _ kan kawo su nan ba, zaki sami ma’aikata da masu matsala da dangin miji ko kuma son mayar da kishiya bora, kai wata ma bata dakishiyar sai ‘ya’yan miji, sabda haka su ne kishiyoyinta kuma in ba shan kansu tayi ba to ba zasu taba barinta shakar numfashi a gidan aurenta ba…. Kin ga, dubi waccan!” ta katse bayanin da take mata tana nuna mata wata zankadediyar farar budurwa cikin rage murya. “Kin gane ta?” Cike da mamaki da shakku Salma ta kada kai, “Na gane ta, shahararriyar “yar fim din nan – ce, amma na yi mamaki.. kodayake Kila ta kusa aure”’ : : Anti Sa’a ta tuntsire da dariya tana cewa, “Ana baki kina Kin karba, maganar me. . nake miki dazu? Ba batun da ke sa mutane Www.bankinhausanovels.com.ng  – bin malamai muke ba? Kuma nace miki. ba wai sai matsalar miji ko ta saurayi kawai ke kawo mutane ba, na saba ganin ‘yan film maza da mata a wajen nan suna neman daukaka da _ farin jinni, ke fa nake gaya miki wallahi wata ma mijin makociyarta zakiga ta kawo. Rayuwar ta yanzu gaba daya ta neman dafa’i ce, in kuma ka matse hannun nema to kuwa sai dai-ka zauna a. rayuwar kana ji da gani ka zama mara sa’a, talaka mai bakin ‘jini da mummunar fuska” Sai da Salma ta daga kai ta dubi Anti Sa’a bayan ta diga wa zancenta aya, ta dubi fuskarta da kyau sai ta tabbatar da gaske take a maganar ’ da ta karkare batunta da ita, Salma ta ji hanjin cikinta na wani mugun kadawa da dalilai biyu, na farko in bata nemi wannan dafa’in na zuwa irin wannan Kazamin gurin ba zata zama talaka mai mummunar fuska da baKin jini kuma mara _ sa’a a rayuwa, na biyu idan ta nemi dafa’in _ tabbas tana shirin canjawa ne daga _asalin Salma da ta dade da sanin kanta zuwa wata daban da ba ta gama amanna da irin rayuwar 

HMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page