RUBUTACCIYA BOOK 1 CHAPTER 5 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

 RUBUTACCIYA BOOK 1 CHAPTER 5 BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO

Www.bankinhausanovels.com.ng 

A JIYA MUN TSAYA 

Ruwanku ne Hafsat da Haidar subi bayanta, sai dai ku sani irin naku rashin hankalin yafi kama da na uwar da ta haifeku, don haka binta zai fi burgeni fiye da zamanku a nan.” Ya sa kai ya fice a fusace. Nasreen tasa kuka, wanda ya jawo hankalin Alhaji Mu’azzam kansu. Wani irin faduwar gaba ya tsinci kansa da shi wanda bai taba jin irinsa ba. Bai taba ganin yaran ba, saboda irin tsanar da ya yi masu, sai yau da ya hada idanu da su. Bakinsa ya mutu murus, dole ya nemi wuri ya zauna, yana kallon yadda Hajiya Salma take kuka, Duk wanda ya san meke faruwa zai gane kukan korarta da Alhaji ya yi take yi. “Salma ki yi haKuri ki share hawayenki, ki zauna da ‘ya’yanki, Kada ki yarda akan ‘yar Karamar matsala ki baro dakin mijinki. Ni zan san matakin dauka haka zan lalubo inji wacce yarinya ce ya aura ma danki, Ki kwanter da hankalinki.” 

ZAMU TASHI 

Daman ko bai ce ba, Hajiya Salma ba za ta iya tafiya ko nan da can ba. Don haka suka yi Sallama ya fice. Nasreen ta sa sandarta a Kasa tana KoKarin ficewa tun kafin fushinta ya sauka akansu. Nawfal ya rike mata sandar suka fice. Yau Sultan ya dawo garin, yana shaKar iskar garin Kaduna ya ji wata natsuwa tana shigarsa. Yana farin ciki yau zai ga twins dinsa. Mota tana yin parking a lokacin mahaifinsa ya fito zai fice. Farin ciki ya kama mahaifinsa, duk da sai da gabansa ya fadi. Rungume juna suka yi cike da farin ciki, haka yana nan a tsaye yana amsa gaisuwar ma’aikatan gidan. Daga nesa ya hangota fuskar nan dauke da farin ciki, tana rike da

sandarta tana laluben hanya. Nawfal ya Karaso wurinta ya rike mata sandar yana cewa, “Idan na gadama insakar maki sandar inrigaki zuwa inyi masa oyoyo. Nasreen ta yi dariya, ta ce, “Ai nasan ba za ka yi min haka ba.” Sultan yana magana da mahaifinsa ya kasa Karasa abinda yake fada ya kafeta da ido babu ko kiftawa. Ya rasa wannan wani irin wasan kwaikwayo ne haka? Abbansa yabi inda yake kallo.da kallo, ba tare da ya furta komai ba. Www.bankinhausanovels.com.ng Nasreen tana Karasowa ta saki sandar ta ce, “Didina ka kama hannuna intabbatar da kai ne.” Sultan ya kasa yin motsi sai kallonta kawai yake yi. A zatonsa wasa take yi, amma yanzu ya tabbatar da babu wasa a lamarin nan. Nawfal ya kama hannun Sultan yana cewa, “Didi sannu da zuwa. Na riga wata yarinya rike hannun Didi.” ‘ Nasreen ta saki dariya ta ce, “Babu damuwa zan rama watarana.” A lokacin ta sami daman rike hannunsa kawai ta rungume shi. Hawaye suna sauka daga idanunta zuwa bayansa. Yana jin digar hawayen hakan yasa ya dan rintse idanu ya ware su da Karfin gaske. A lokacin ne Hafsat da Haidar suka fito. “Sannu da zuwa Yaya.” Su kansu bai amsa masu “ba, hakan yasa suka tsaya suna duban yadda ya yi kamar wanda ya mutu a tsaye. Da gaske ya rasa me zai ce, wacce tambaya ya kamata ya fara yi, kuma idan zai yi din wa zai wa? “Abba Nasreen ta daina gani ne?” Wannan ‘tambayar ce ta Kwace masa da karfin gaske ta : fizzo kanta ta samu ta fito. Abba ya girgiza kai, “Nasreen bata ganin komai. Kaddara ce ta Ssameta, muna fatan mu samu mu cinye. Ku zo Www.bankinhausanovels.com.ng  mu shiga ciki.” Hannunsa daya yasa ya dan shafi bayanta kafin ya dagota daga kwancen da take, yasa hannu ya dauke mata hawayen idanunta, sannan ya riKe hannunta suka shiga ciki Har yanzu jikinsa a sanyaye yake haka ya kasa gazgata abinda ya gani. Dakinsa ya shiga ya kintsa sannan ya fito falon ya iso har gaban mahaifiyarsa ya duka ya gaidata. Ita kanta Hajiya Salma ta sani, kaf cikin ‘ya’yanta babu mai biyayyar Sultan, sai dai wani ra’ayi nata da yasa take jin haushin abinda yake aikatawa. A hargitse ya yi maganar da yasa kowa yake kallonsa, “Abba ashe ba zan iya barin amana a rike min ba? Waye zai aikatawa Nasreen irin wannan mugun abun? Nasreen ta makance amma ba a taba gaya min ba? Ko waye ya aikata mata wannan abun ba zan taba daga masa Kafafu ba.” Ya ajiye maganar ba yadda ya kamata ba. Nasreen ta Karaso tana lalube har ta iso gabansa, “Dee, wanda ya aikata min hakan ya fi kowa sanin dalilin da yasa ya yi min. Kuma ni na yafe ma wanda ya yi hakan, Kada bakin ciki yasa ka furta wasu kalaman da suka cika yin nauyi. Kayi haKuri kamar yadda Abba ya ce min  inkarbi Kaddarata haka kaima ya kamata kayi. Ni bana jin damuwa, ina gode wa Allah a yadda ya ‘ bar ni. Idan kuma kace za ka dauki mataki bansan wurin wa za ka je daukar matakin ba, domin nima bansan wanda ya aikata min hakan ba.” Sultan ya dubeta yana jin zuciyarsa tana yi masa wani zafi. Yana kallon manyan idanun nan masu tsari yau sunée a rufe bata gani da su. “Nasreen zan yi bincike zan kuma dauki mataki kamar yadda na fada. Bincike biyu ke gabana kuma Insha Allahu duk sai na aikata su. Duk wanda ya aikata maki hakan babu ko shakka zai iya yin kisan kai.” Hajiya Salma ta yi maza ta tari numfashinta, domin Sultan gaf yake da zageta, “A’a ya isheni haka. Idan ka tashi yin binciken sai ka hado da ubanka domin shima a gidan ya kwana, ko kuma duk ka kama mu ka rufe har sai ka gama binciken. Idan za ka wuce kaje ka ci abincinka ka wuce, idan kuma tsayawa za ka yi ka samu a gaba kana yi mana tambayoyin rainin hankali Bismillah.” Sultan ya duKar da kansa-ba tare da ya iya furta komai ba. Abbansa ya dafa shi, “Sultan, ka yi haKuri, kullum da Nasreen Www.bankinhausanovels.com.ng  nake kwana da ita nake tashi a zuciyata. Na rasa gano wanda ya yi wannan aikin. Ka je kayi bincikenka, nima idan na kama wanda ya aikata min wannan aikin insha Allahu zan tsaya sai naga anhukunta shi, ko wanene kuwa. Haka kaima ka dauki mataki, tunda a lokacin da za ka fara aiki, sai da kayi alkawarin tsayawa akan gaskiyarka, ko da kuwa ni mahaifinka ni ka kama da irin wannan laifin, don Allah ka dauki mataki kada ka ragawa mutum. Idan kayi hakan zan san dana ya tabbata a cikin dan sandan mai amana da gaskiya. Allah ya yi maka albarka. Zan – bayyana maka matarka da zarar ta kammala Makarantarta, wanda bana jin za ta dauki lokaci, domin tana shekararta ta Karshe ne. Tashi kaje ka ci abincin.” Sultan ya dan sami natsuwa da kalaman mahaifinsa, kafin ya tashi Nasreen ta fara tashi, tana lalube saura Kiris ta fadi ya Kwala mata kira, “Nasreen! Tsaya.”’ Babu musu ta tsaya ya Karaso ya kama mata sandar suka fice. Hankalin Hajiya Salma idan ya yi dubu to ya tashi, Sai taga kamar da Nasreen ta makancen sai abin yafi sake yin muni, Hankalinta ya Kara tashi ne da Hajiya Ladidi ta tabbatar mata, tunda Www.bankinhausanovels.com.ng anyiwa danta aure, to Alhajin ne da kansa zai auri Nasreen din, domin kuwa shi namiji bashi da kunya. Zai reni abu ya kuma aureta. Hauka ne kawai Hajiya Salma ba ta yi ba, domin ita ta kasance mace mai zafin kishi, akan Alhaji Lukman za. ta iya kashe rai. Sultan ya tashi hankalinta Kwarai akan maganar binciken da ya ce, zai yi domin kuwa kallonsa take yi a matsayin mayen ‘yan sanda. A _ dalilin Kwarewarsa yasa ake ta Kara masa girma. Dole ta yi yunkurin daukar mataki akan abubuwan nan tun kafin tana ji tana gani danta ya garkameta a Police Station ‘yan jaridu su sami daman watsata a duniya. Haidar ta aika ya kirawo mata Sultan yana shigowa ta dube shi sosai. “Kana jina? Idan na sake jin ka sami ‘yan aiki kana yi masu bincike ko Kannanka ban yafe maka ba. Nasreen wani Kato ya shigo ya rufe mata baki ba mu ji ba, ya yi mata wannan abin. Kai baka yarda da Kaddara ne? Kai ka sani ko mugayen da suka kashe mahaifiyarta ne suka gane akwai yaran a gidan nan? Ni shi ya sa tun farko ban so rikon su ya zamana a nan ba. Bana Www.bankinhausanovels.com.ng  son kaje garin tone-tonenka ka jawo mana masifa har cikin gida.” Sultan ya zubawa mahaifiyarsa idanu kamar mai son gano wani abu. Hankalinta ya Kara tashi ta ce, “Laaahh! Ni kake kallo haka kamar ka sami barauniya? To tashi ka wuce na gama magana. Bai ce komai ba, bai kuma tashin ba. Can ya nisa ya ce, “Umma wai har cikin dakinta aka shiga aka aikata hakan duk baku sani ba? A lokacin kina…” A zafafe ta ce, “Ina dakin ubanka ne a lokacin. Ingama ce maka ka bar maganar nan amma kuma saboda tsaurin idanu za ka koma yi min tambayoyi? Sultan wai yaushe ka sauya ne? . Zuwan yaran nan rayuwarka sun sauya mun dana. Yauwa Sultan wai wacece matarka? Na yi bincike sosai antabbatar min ba ‘yar gidan Alhaji Mamman ba ce. Anya ya kamata ka amshi auren nan kuwa? Bana son yazo baka yi sa’ar mata ba, dan nuna min ita ko a hoto ne.” A lokaci guda bayan ta gama masifar ta yi Kasa da muryarta kamar mai rada. Sultan da ya gaji da tsugunnon da yake, ya jawo wata ‘yar kujera ya zauna yana Www.bankinhausanovels.com.ng  fuskantar mahaifiyarsa, bayan ya dauki dabino | daya ya Sa a bakinsa. “Umma ban santa ba, ban taba ganinta ba, ban san sunanta ba, haka ban san ko ‘yar gidan waye ba. Kasan da ta tafi karatun ma ban san shi ba. Kawai abinda nake buKata addu’a Umma. Idan kika yi min hakan kin gama yi min komai. Kuma insha Ailehu zanyi maku biyayya wajen karbar zabinku.” Umma ta Harare shi, “Wajen karbar zabin mahaifinka ko kuma zabina? Ni zabin da na ‘baka ka karba ne? Ina son ka bude kunnunwanka da kyau ka ji ni. Ka je ka sami mahaifinka kace sai ya hadaka da matarka ko gaisawa ce ku dinga _ yi. Ya zama dole musan wacece da me za ta shigo gidan. Idan ba ta yi ba, sai ka botsare masa ka saketa kawai ta kama gabanta.” Muryar Abba suka ji yana magana, “Allah kadai zai iya shiryaki Salma. A duk ranar da shawararki ta yi tasiri a zuciyar danki ina tabbatar maki sai kin yi mugun danasani. Ba zan bayar da hoton ba, bazan kuma hada su ba, har sai lokacin da na gadamar yin hakan. Kai Sultan zo ka wuce.” Babu musu ya mike ya fice abinsa yana al’ajabin mahaifiyarsa. Ita kuwa hajiya Www.bankinhausanovels.com.ng Salma dubansa ta yi ta ce, “Ka dai san babu kyau labe ko? Babu daman inzanta da dana sai ka hau masifa?” Dubanta ya yi ya ce, “Labe? Waye dan naki? Yaron da kika ware shi a_cikin ‘yan’uwansa kika jawo masu rashin shaKuwa da juna? Ai da wannan kadai idan na bar ki Salma sai Allah ya hukuntaki.” Bai tsaya saurarenta ba ya sa kai ya fice abinsa. Sultan yana nan ‘tsaye, bayan ya tabbatarwa mai tsaronsa ya wuce kawai ga shi nan zuwa. Yana nan a tsaye yana kallon tsakar gidan. Hafsat ta fito da wani dutse ta ajiye a hanya ta koma ciki. Ba ta kula da shi ba, haka shima bai kula da abinda hakan ke nufi ba, domin kuwa tunaninsa ya yi nisa. Nasreen ta fito tana lalube sai kawai ta ci tuntube da Katon dutsen nan ta fadi a wurin.Sultan ya zaro idanu a lokaci guda kuma Hafsat ta fito daga maboyarta tana kwasar dariya. Zata wuce kenan ta ji anfinciko ta. A razane ta dago tana hada idanu da yayanta ta tsure, “Yaya me nayi?” Dau! Ya dauke ta da mari, daman kuma hannunsa babu kyau, a take fuskar ta kumbure ~ ta yi jazir, abinka da farar mace. Ya sake daga hannu ya yi ta kwada mata. Sannan ya watsar da ita. A gujen gaske ta yi cikin gida, domin wannan shi ne karo na biyu da ya taba dukanta a duniya, kuma duk akan mutum daya. Karasowa ya yi inda Nasreen din ke zaune ta yi shiru kawal. Yasa hannu ya kamota suka koma inuwa suka zauna. Yana jin dadin Kare mata kallo, baya gajiya da hakan. Ciwon da ta dan ji yake dubawa, bayan ya kama hannunta. A hankah yake shafar ciwon wanda yake sanya mata wata kasala, tana sake lullumshe idanunta, labbanta kamar za ta yi © magana, amman hakan ya gagara. Yanayin da ta shiga yasa mamaki ya kama shi, tambayar kansa yake ko dai ba Nasreen ba ce? Irin yanayin nan masoya kadai ke iya kasancewa a cikinta. Dayan hannunta tasa ta rike hannunsa tana girgiza kai, “Dee.. Na daina jin zafin yanzu.” Murmushi kawai yaji, kafin kuma muryar Umma ta wargaza masu yanayin da suke ciki. Www.bankinhausanovels.com.ng “Sultan! Yanzu akan yarinyar nan za ka yi wa Hafsat irin dukan nan? Ba ka da hankali ne ko mene ne haka?” Sultan ya yi magana kamar baya son yl, “Umma idan kannena suka yi laifi babu daman in hukunta su kenan?. Haba Umma meyasa zaki wareni daban a cikin ‘yan uwana? Laifi ta yi na hukuntata. ”  Ta yi Kwafa kamar za ta kai masa duka, “Ita ta kusa da kai ba ta laifi ne ko me? Kada ka sake dukar min yara na gaya maka.” Bai bata amsa ba haka bata daina masifar ba, har sai da ta gaji ta juya abinta. Shi kuma ya kamo hannun Nasreen suka shiga mota. Wani wuri ya kaita © mai dauke da sanyi irin na korama. Tana zama ta shaki irin Kamshin da wurin yake yi, ta ce, “Deedina ina jin wani irin yanayi mai dadi a jikina. Dee da ba ka nan na yi ta kewar ka, amma kuma ina yi maka addu’a.” Sai da ya zauna bayan ya gama kallonta sannan ya ce, “Nima nayi kewarku ke da Nawfal kamar insa a kawo min ku, sai nayi tunanin karatun ku. Nasreen zaki iya tuna wanda ya watsa maki abu a idanu?” Www.bankinhausanovels.com.ng Hawaye suka gangaro fuskarta kamar daman tana jira ne, “Deena bansan waye ba. Ka bar maganar nan abinda Allah ya aiko kenan.” Jawota ya yi ta kwantar luf a Kirjinsa tana sakin Wani irin ajiyar zuciya. Hakan ya haifar da abubuwa masu girma da wahalar fassarawa a tsakanin su. Sultan kenan! Kowa kallonsa yake miskili mara son hayaniya, haka alamu sun nuna idan ya kama mai laifi baya sarara masu. Idan ka ganshi tare da Nasreen za ka iya rantsuwa ba Sultan dan sanda bane. A kunnenta yayi magana, “Kada ki damu, akwai zaman da zamu yi da abokaina akan wata matsala, don haka zanyiwa Dr. Aslaf magana, akan idanunki zai bamu shawarar Kasar da ya kamata mu tafi da ke sai a duba idanunki. Idan ba haka ba, waye zai aurar min Nasreen dina a haka?” Wani irin tafiya ta yi mai kama da tafiyar barci. Ga iska yana Kara kada su. Tana murmushi tana magana kamar wacce ta sha wani abin maye, “Deena, zan zauna tare da kai ba zan auri kowa ba.” Dagata ya yi saboda da gaske ya gane tana cikin wani yanayi. “Tashi muje Office dina.” Www.bankinhausanovels.com.ng Girgiza kai ta yi, “Ina son indauwama a nan wurin. Kamshin filawowin suna sanya min nishadi da sanyi a zuciyata, wanda rabon da in ji – hakan na jima. Dee wani abu ke tsaya min a Kirji yana min zafi sosai, ko nasha ruwa baya wuce wa.” Wannan Karon tausayinta ya kama shi, Nasreen ta yi Karama da yawa da shiga irin wannan yanayin, “Ki dinga addu’a Nasreen kin ji? Mu je Office dina akwai abinda zan dauka.” Da isar su Office din, “yan sanda suka taso ° suna sara masa, shi dai yana rike da hannun Nasreen. Gaba daya mutane idanunsu akan Nasreen yake, wani ma cewa ya yi koda take makauniya zai iya aurenta inhar Oga zai ba su ita. A kujera ya ajiyeta, a lokacin ne kuma aka gaya masa wani case ya ce, a shigo da matar a gurguje. . “ Tana shigowa tana bayani bai dago daga abinda yake yi ba bare ya dubeta, “Yallabai mijina ne ya zaneni,” Yana rubutunsa ya ce, “Me kika yi masa har ya duke ki?” Ta share hawayenta ta ci-gaba da magana, “Ya musuluntar da ni ne, ya raba ni da kowa, ya Www.bankinhausanovels.com.ng ce min addinin musulunci shi ne addinin gaskiya, nasha wahala da iyayena har na rabu da su, na zabe shi da addininsa. Amma tunda na aure shi kullum sai ya yi min gori akan addininsa, kullum idan na yi kuskure sai ya ce min matsalar tubabbe kenan. Yallabai ina son a raba aurena da shi, zan koma addinina, ko dan inhuta da gorinsa da na ‘yan uwansa.” Tun bayan da ta ambaci ta koma addininta ya ajiye rubutun yana dubanta. Damuwa ce shimfide a fuskarsa. Har yaushe musulman mu za suyi hankali? A hakan wasu suke son jawo wadanda basa addininsu su dawo addinin su? Bai yi magana ba, har sai da ya gama nazari sannan ya ce ta fada inda za a ga miinta. Ta kwatanta ‘ya bada umamnin a je a kawo masa shi yanzu. Ya dubi matar ya ce, “Amma kafin in ce komai,  daina daukar musulunci haka yake. Musulunci abu ne mai sauki da kuma dadi. Idan kina cikin musulunci zaki sami hanyoyin warwarewar matsalarki, wanda ina ganin baki bi hanyar bane shi ya sa kike dan samun matsala. Haka kuma mu a cikin addininmu akwai jarabawa, da Allah yake yiwa bayinsa. A Karkashin jarabawar nan Www.bankinhausanovels.com.ng  zaki sami hanyar shiga Aljannah. Misali a cikin Alqur’ani akwai waraka a ciki. Ko malamin da ya musuluntar da ke bai gaya maki hakan ba?” Sunkuyar da kanta Kasa ta yi ta ce, ‘“Malamin ya yi min bayani. Amma bai gaya min musulmi zai lya yiwa wanda ya aro addininsa gori ba, haka bai gaya min akwai duka a cikin sharuddan aurenku ba. Ina zuwa Islamiyya har yau ban ji inda malaman ta ce ana gorin addini ba.” Sultan ya rintse ido yana kallon rubutun suna komawa kamar yashi. Saudat! Ita ta fado masa arai. Mahaifiyar Nasreen da Nawfal. Tasha gori akan addininmu amma kuma tana rike da mu. Hatta mahaifiyarsa har yau tana yi wa su Nasreen gori akan addinin da Saudat ta aro. Sultan ya girgiza kansa, “Hakane, haramun ne ma musulmi ya ci zarafin dan uwansa musulmi. A cikin addininku akwai na banza akwai na kirki, haka muma a cikin addinin mu, akwai irin hakan, Amma mu ba mu gorin addini, haka kuma ke kin fi shi rashin zunubi, saboda kin tuba kin musulunta. Addinin musulunci akwai dadi idan kika natsu a cikinsa. Dokokin mu basu da Www.bankinhausanovels.com.ng  tsauri. Haka a KarKashin wannan auren da kike son a raba zaki shiga Aljannah. Haka ina son ki zuba ido ki gani, tun aduniya Allah zai saka maki, akan mijinki idan har da gaske yana zaluntarki. Shi Allah baya barin azzalumi. Kada zuciyarki ta yi rauni kawai dan namiji yana cuzguna maki, ki dauka irin taki jarabawar kenan. Idan Allah ya dubi zuciyarki ya tabbatar a wadace take da imani, da son addininsa, sai shi kuma ya saka maki. Kada ki ce wai sai kin ji dadi sannan zaki yabawa addinin musulunci.” A lokacin kuma aka shigo da Bala mijin Karima. A Kasa yasa ya zauna yana aika masa da mugun kallo mai cike da tsana. “Ka san wannan ko?” Ya nuna masa Karima da hannu. “Yallabai na santa matata ce, shekarun mu uku da aure da ita.” Sultan ya dinga jinjina yayi wuri ta fara fuskantar matsala, “Ta ce tana son a raba aurenku, saboda kana dukanta, don haka zan tura ku kotu, daga nan zaka amshi irin naka hukuncin.” 

HMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KO SULTAN ZAI GANO WANDA YA WATSAMA NASREEN ABU A IDO KU DAI KUCI GABA DA KASANCE DAMU DOMIN JIN YADDAH ZATACI GABA DA KAYAWA WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page