NA SHIGA ALJANNAH BOOK 1 CHAPTER 6 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

 NA SHIGA ALJANNAH BOOK 1 CHAPTER 6 BY MAIMUNA IDRIS SANI BELI

Www.bankinhausanovels.com.ng 

A JIYA MUN TSAYA 

Ungo wannan ka rike a hannunka ko zata buKaci kudin dinki, ka ga ba sai ka bada maza ba” : Ya sa hannu ya karbe kudin ya kalmashe a aljihu yana tura wa Salma ashar cikin Zuciyarsa, ya rasa da abinda wannan tulun yariyar ta rudi su Hajiya har suke ganin bata da abokin rayuwa sai zukeKen saurayi irinsa. Ya sake jaddada wa Hajiya godiya sannan ya sa kai ya fice da kaya a hannu zuciyarsa wadda ya dinga rantsewa ko tayi kwalliya ba kyau take ba, lallai mijinta zai sha barnar kudi 

ZAMU TASHI 

kuma babu biyan buKata, don ko Zinarin duniyar nan zata sanya ba zai mata kyau ba. 

************

Husna kyakkyawar doguwar yarinyar da ta taso cikin maraici ‘ sakamokon _rashin ‘mahaifiyarta Zainab sanadiyar . haihuwarta kuma haihuwar fari, ta sha hannun raino iri-iri tun daga kan hanun Kakarta Innaa mahaifiyar Zainab dinwadda ta dauke ta taci gaba da rainonta  taré da dan da take goyo Yunusa. Ita ma Allah ya karbi ranta Husna na shekaru hudu, sai riKonta ya koma gurin ‘yar — mahaifiyarta mai suna Rakiya wadda shekaru biyu kacal tayi Allah ya raba zaman dalilin. mutuwar auren Rakiyar kuma bata da Karfin cigaba da riKonta, wannan yasa ta danKka amanar Husna ga autarsu Jamila, amma ba’a yi sa’a ba halin Jamila tamkar ba ciki daya suka fito da ‘yan uwanta ba, sai ta dinga gasa Husna_ tamkar ba jininta ba, yadda take matufar gallaza mata yun daga unguwa har kafatin dangi babu wanda bai san irin mawuyacin halin da Husna ke ciki ba. . Mahaifin HUsna Malam magini mutum ne mai tsananin kawaici, shi ne dalilin da yasa ma ya dauke hankalinsa daga kan Husna duk da kasancewarta ‘yar fari kuma ‘ya

daya tilo daya . .Mallaka a duniyarsa. Gashi kuma dangin Zainab sun baibaye shi da karamci, kana sun baibaye shi.da lissafin hakKin riKon Husna ‘ahannunsu yake.. ~~ ~ _ Bayan rasuwar mahaifiyarta yayi aure har sau biyu, farko Suwaiba wadda da alama bata da rabon haihuwa, suka shekara biyar tare _ son ‘ya’ya ta kaishi auren Jummai, amma muguwar fitinarta ta sanya yayi mata saki uku da tsohon ciki ta koma gidansu ta haifo ‘yan biyunta. ‘Ya’yansa uku kenan a dangin matannsa matatciya da rayayyiya. Www.bankinhausanovels.com.ng  Da aka sake diban shekara daya da rabuwarsa da Jummai sai ya sake auro Hajara, wadda tana zuwa ita ma ta ci karo da nata rabon, a auren Hajarar ne kuma ya fahimci ashe akuyar Jummai ce tayi kuka kawai, bambancin ya saba da rike mace da ne Www.bankinhausanovels.com.ng Zainab sannan Suwaiba, lallai rashin kyawun halin mace yafi bayyana idan tana da kishiya, wato dai ya yiwa jummai bahaguwar fahimta ita kanta Suwaiba baa rasa nata laifin. Wannan  dalilin ya sanya ya riKe su da halinsu ya kuma cigaba da hakuri haka. – A shekarar da Hajara ta haifi ‘yarta Khadija hakurinsa da kawaicinsa akan rikon da Jamila take way yarsa ya gaza, ya shafe wa idonsa tokay a karri ‘yarsa, babu wani jan ido Jamila ta bashi abarsa, .dama ba Kaunar rikon., take ba kasancewarta mai muguwar karaya da Kyashi. Da babu. gara babu dadi, amma. Husna ta baro wata wuyar ne ta fado wata, duk da akwai dan sassauci kasancewar a.tsakanin kishiyoyin da keda mugun kishi také, wadanda kulawarsu gareta bata motsawa sai idan zasu cutar da_juna, inba haka ba bata da sauran wani gata ko’ amfani a wajensu, sannan’ko da sun cutar da ita idan idon mahaifinta ya kai kan cutar ya kan tsawatar daidai gwargwado. : Sai dai wannan halin ko in kular da tare da Kalubalen da rayuwarta ta taso a ciki ya koyar’. da ita dabi’a gwagwarmaya  tare da koyar Www.bankinhausanovels.com.ng  tsayuwa da Kafafu., ta taso mace mai jarabar neman kudi kamar tayi sata, it ace wannan ” sana’ar gobe waccan, karshe dai ta tsayar da guda wadda ta fi Kwarewa a kai kuma wadda tafi ko wacce kawo mata kudi wato dinkunan mata, kai har na mazan ma tabawa take idan ta sami rarar lokaci tun da dinkin matan yafi sauri tare da kawo kudi masu kauri. Wannan-jarabar neman kudin nata ne ma ya ‘ sanya dakatar da karatu daga kammala babbar sakandare kawai, a cewarta ai karatun book _dan sana’a kawai ake-saboda haka ai ita ta samu sana’a Sai dai nakasun da za’a duba a rayuwarta da gwagwarmayarta it ace, shegen sabo da kasha kudi, tana da kirki sosai amma yawancin alfarmarta ta kudi ce da KoKarin kere sa’a. gata ‘yar kyakkyawa mai kyan diri don haka ta -_ budi ido da farin jinin samari fiye da Kima, ita. kuma tayi amfani da wannan dammar ta dinga yashe duk saurayin da tsautsayi ya kawo shi shirgin ta saboda tana da dankaren wayo da iya tsara kalami bugu da kari gata mace mai Sanyin murya Www.bankinhausanovels.com.ng Wannan dabi’ar tata ta dami mahaifinta Kwarai, kullum cikin fada da nasiha gareta yake tare da fatan ganin ta tsayar da miji ya © aurar da ita amma ita sam hankalinta.baya kan auren, ta ci alwashin sai tayi wanki zata yi aure © kuma ma dai har zuwa yanzu bata ga saurayin – daya kwanta mata a rai ko kuma ya cika sharudan zamowarsa miji gareta ba.Amma wani hukuncin Ubangiji wanda ya sanya ta sakankancewa tabbas rayuwa ba abinda ka tsara tun fari zuciyarka ke dorewa a kanta ba kuma ko ana yiwa komai tsari to tabbas So ba a yi masa tsari. kuma ba zaba masa muhalli ake ba, kawai shi yake canka ya zuba sheKa, Tun ranar da ta hadu da Adamu a shagon kayan .dinki sai ya bi zuciyarta ya timmike, ya zamana dukkan mafarkinta a mijin aure kan Adamu yake fadawa da kudi ko babu, in ta wassafa shi a mai kudi sai ta hango musu wata aljannar duniya mai cike da kyawawan ‘ya’ya da rayuwat jin dadi, in ta -wassafo shi a talaka kuma sai ta hango © rayuwarsu mai mutumci da karrama juna tare da son ‘juna tsakani da Allah. A wannan gabar Www.bankinhausanovels.com.ng har hango kanta take yi tana daukar nauyin gida a sana’ar da take shi kuma Adamu na ta Kara sonta yana shi mata albarka tare da cin alwashin daga ita babu Kari, kuma duk lokacin da Allah ya yassare masa sai ya jiyar da ita dadin da babu wanda ya taba jiyar da matarsa ko masoyiyarsa irinsa. _. Wannan jumurdar da ta sami kanta ciki ta rage mata kuzari ainun, so take ta fasa wannan son da zuciyarta ta kinkimo mata amma duk yadda ta kwaso fasawar sai ta ji ta kasa, sai fasawar ta rikede dubunnan soyayyar Adamun su hadu da fatan samunsa su yi ta faman wahalar da ita. Musamman idan taji faduwar gaban yadda za’ayi ta samu din tunda ba ta. ~ cikin duniyar da ake mutunta matar da ta ga namiji tace masa tana son sa. | Cikin kwana biyun nan haka ta dinga tsirar zuwa shagon kayan dinki musamman dan ta ‘ganshi, ko akan allura ne bazata aiko yaro ba sai dai ta wanko Kafa ta taho amma bata taba katarin sake sanya shi a ido ba, kuma duk yadda sonsa yake gasa mata gujjiya a hannu ta kasa samo dabarar da zata i wa mai shagon Www.bankinhausanovels.com.ng dinki ta nemi Adamun ko kuma ko da sunan Adamun ya tuna mata wanda ya kwanta mata a rai kafin zuciyarta ta zabe shi » gwarzonta na har abada. : 

*******

. A gurguje kafin karasowar Salmanu Adamu ya fada wanka sai dai bai yi katari ba ya fito ya tarar da Salmanun har ya Karaso yana kwance kan kujera yana jiransa tare da rera wakarsa ta Dauri kasancewarsa mai son wakokin mutanen Da. | “Haba ashe ba banza ba Allah yayi maka ajiyar son wakokin su Dan anaci da su. Duna, ashe Boka mai gani har hanji zaka zama” Da shegantakar da Adamu ya tare shi – kenan. _ Suka tuntsire da dariya suka tafa. Salmanu ya ce, “Malam dafa kai na yi niyyar ka zama Bokan” Adamu ya kai masa duka a fusace, Www.bankinhausanovels.com.ng “Ba na son rainin hankali, saboda ni na – kawo shawarar kuma na san yadda ake yi?” | “Saboda kai baki ne ni Kuma fari, ka san ba a saba ganin bokaye farare ba.. | Adamu ya sake kai masa – duka cikin _ dariya, “Shege! Ni ne bakin? Al nima ba baki ba ne malam’. . Suna kacamewa da’ dariyarsu Salmanu yace, “Amma ai baki za.a kira ka a kaina” , “An ji, kuma nine mai masoyiyar ‘da babu irinta ko, Husna mai sunan larabawa” — Adamu ya fada cikin raha. Salmanu ma ya zolaye shi bayan ya kawar | da kai yana Kunshe baki, “Allahu Akbar! Na rantse da Allah na zaci . Salma zaka ce, ita ke sonka, waccan ba ta san bikin da kake ba Kila ma matar aure ce ma “anayi mata miji’”. . | Fuskar Adamu ta nuna damuwa amma sai ya girgaza kai ya jefar da comb ya yi gaba ya dauko man shafawa ya nemi gurin zama, sai da ya fara shafa man ya amsa wa Salmanu – Www.bankinhausanovels.com.ng 

“Salmanu, addu’ar da nake wa yarinyar nan ina tsayuwar dare akanta, idan ka ga ban aureta ba ko kuma Allah bai jefa mata sona cikin zuciyarta ba, to ka tabbatar Allah ya ajiye min wadda ta fita wadda kuma Zan sO fiye da ita din ne” . Salmanu ya saki wani ihu sannan ya dora da cewa, | _“Ka san abinda yafi birge ni da kai?” Adamu ya girgiza kai. Salmanu yace,“Yarda da kanka wallahi” ‘.. Adamu ya sake kada kai, . Ai ba yarda da kai ba ne, — yarda da wanda ya ce idan an kira shi zai.amsa ne, idan kuma aka tsaya a Kofarsa ya ishe mu to shin na kai wa kuka na kuma ina da yakinin ba zai tankwabar ba. Irin wannan addu’ar na yi a -karatun bokon da aka yi niyyar mayar min addni, ka ga cikin sauki Allah ya raba mu” Jikin Salmanu a sanyaye ya amsa masa, .  “Ai game da karatun nan gata ne yayi maka yawa Adamu, in ni na sami wannan: gatan Www.bankinhausanovels.com.ng wallahi ba zaka ganni a wannan kwararon ko wannan sana’ar ba”Sai jikin Adamun shi ma yayi sanyi, ya basar lokacin da Husna ta mamayo zuciyarsa, wadda ya hakikance in dai akwai karatu nan a gabansa tabbas sai aurenta ya tsere masa. -Zai yi Magana kenan ya jiyo motsi kamar daga cikin gida, zargin ko Hajiya ce zata leKo ya sanya ya. mike da sauri ya Zo wajen Salmanu ya hau yi masa radar yadda suka yi da  ita akan sabuwar sana’ar da suke son farawa. Cikin sakanni_kadan Salmanu yayi hadda kuma akazo aka wuce.suka ‘gane cewa yara masu siyen Goro ne. Salmanu ya mike,  “Bari na je na gaishe ta kafin ka shirya. ya shirya har Salmanu ya fito. Salmanu ya nemi guri ya zauna ya fito da _kudin ‘aljihunsa ya hau Kinga, kana ya daga kai ya dubi Adamu, “Ni an sami dubu goma ba dari daya a jikina, kai  nawa za,a samu a jikinka?” Www.bankinhausanovels.com.ng Maimakon Adamu ya amsa kai tsaye saiya fara Kalubalantarsa.. _ “Dari dayan ma nasan fasa dubun kayika sha sigari. : Salmanu yayi dari“Kamar ka sani?” _ “Yo kama ce ma? Ai sani nayi kawai” An ji, kar kuma ka ja mana zance mu yi – abinda ya kawoni lokaci na Kurewa”  _ Adamu ya kawar da kai, Haka ne, to ni ban tara komai ba” Salmanu yayi masa wani_ ‘kallon banza, amma ganin bai san yana yi ba sai a hasale ya ce, “Ba ka tara komai ba. fa ka ce?” Adamu ya juyo ya kalle shi, | “Eh, naje ba sa,a na matsa layar zanar na _ : kasa Bata” Salmanu ya shanye haushinsa ya dan yi murmushi, kamar zai basar amma sai ya yi dabarar tashi ya shammaci Adamu ya dakumi aljihunsa ya zaro naira dubu biyun da Hayiya ta ba shi kudin dinkin Salma, a“Makaryaci wannan fa?”Www.bankinhausanovels.com.ng  “Tsakaninku kallo” Adamu ya kawar da kai ya fada.: – : “Wallahi baka isa ba, sai ka bayar dasu sun shiga cikin ‘yan uwansu, na karba a haka aida ~ hanau gara mannau” Ya hada su da dubu goman wajensa ya — mikKawa Adamu, Ungo ajiye mana ka zauna ka mmji bayani”’ Ba musu Adamu ya karba ‘ya cusa aljihu . -sannan ya gyara zama yana duban Salmanu. Salmanu ma ya zauna zaman nutsuwa ya fara koro jawabi. “Abu na farko da zamu tanada shi ne, Guri, wato muhalli da ‘ya dace da malamai ko bokaye,; dan guri kebabbe nesa da mutane, ko kuma cikin mutane inda baasanmuba’. . Adamu ya ci gaba da kallon Salmanu saroro * da alamun rashin fahimta, kuma cikin alamun . son nuna juriyara ya fahimtar. _ “Wannan bos din na gama kashé shi tun – daren jiya, ina gidan gonar Ogana da nake kular masa da shi  na nan Zawaciki kusa da mu?” Www.bankinhausanovels.com.ng Da Kyar Adamu ya daure ya kada kai Saboda tsabar rudewa. Salmanu bai damu da rikitar Adamu ba ya cigaba da ba shi lissafi, “To dama tuni Alh. ya daina zuba Kaji a nan, sai kawai ya ce na sawa gidan ido na dinga kula da shi, ai mun taba zuwa ka ga girman gidan ko?” Nan ma Adamu ya kada kai, | “To daya bangaren za mu iya mayar da shi fadar tsubbunmu ba tare da.wata mishkila ba,. gashi Alh. yana shirin zaune wa a Japan ‘har na tsawon shekara hudu, abin Allah jiya aka min -wannan albishir din” Ikon Allah” =. Adamu ya daure ya tanka. Salmanu ya janyo jug ya tsiyayi ruwa ya sha, sannan ya dubi Adamu da kyau, “Wadannan kudin ko basu hada dukkan kayayyakin ba na san zasu kusa, zamu sai kayan saki irin na ‘yan bori, har da su tabarmi, kore, shantu da kaskwayen wuta, kai har da su .tsintsiya da faifai duk masu fenti irin na masu — shirka….” : : Www.bankinhausanovels.com.ng “Har girkar zamu dinga yi kenan? Adamu ya fada cikin tsura wa Salmanu ido ‘ yana hadiyar yawun fargabar yadda Salmanu ke son aikensu zunguro sama da kara. Salmanu ya tuntsire a dariya ya amsa, “Haba wa zai aike mu wannan danyen . hukuncin? Mu fa Jabun ne, masu girkar asalin ne Orijinal, hanyarsu daban tamu daban kawai _ dai sunan sana’a kusan daya mu ke” “Shikenan, ina jin ka” Adamu ya fada cikin sallamawar da bata kai . zuci ba. Kana ji ko?” ) | In ji Salmanu. Bai jira cewar Adamu ba ya cigaba.| “Wadancan kayan ‘yan ‘borin ba su ne kayan sana’ar ba, su ne dacoration din wajen  yadda zai dace da sana’ar, amma dai zamu dan yi hake-haKe a wajen yadda zamu jona butotanmu….”. “Meye wani butotai?” Adamu ya fada kamar a Kule. Har ga Allah – maganar ba Karamin gundurarsa da bata masa rai take ba.’ Www.bankinhausanovels.com.ng  Salmanu ya buge shi a kafada._. | “Kai dallah malam: ka ware, duk ka bi_ka wani cukwikuye” : | “Ai kai ka cukwikuye ni, malam in zaka yi _sauri ka ware ni, ka yi wallahi ka fara sa min © ciwon kai” , : Salmanu ya di inga tuntsira masa dariya har sai da Adamu ya dinga barazanar bar masa dakin sannan Salmanu ya riko bannunsa cikin tsananta dariya, —, | “Kaga in ma’anar Butotai ne zo,in fada | maka mu kashe wannan bos din mutumina” Yana cigaba da dariyarsa | bai jira cewar -_ Adamun ba yacigaba,. . SO – “Tiyo nake nufi da butotai, ko baka san an ace masa bututu ba? In kaje makaranta ai kasan za’a iya kiran jam’insa da butotai. To ba. wai amfaninsa kawai tarar ruwa daga famfo zuwa tanki ba, a’a, a tamu.sana’ar da shi ake ~ ‘maganar aljanu duk zaka ‘gani idan munje wajen “To” | . _ Adamu ya fada domin ya hutar da zuciyarsa Www.bankinhausanovels.com.ng  da-zuyata na jiran fahimtar Salmanu tare da Kokarin cirewa ransa damuwar da ta addabi ransa. Amma sai ya dage ya mayar da hankalinsa ga Salmanu wanda ya zage yana yi masa bayanin yadda ake wannan sabuwar ‘ sana’a ta wankin ido ba tare da an je wajen wani malami neman sa’a ko siddabarunsa ba. Hankali kwance kuma a wanke bayin Allah. Adamu ya kwashi gayar mamaki da yadda salmanu ya kwatanta masa yadda ake binne hankali da azancin masu yawon neman asiri, yadda ko shi aka yi wa wannan siddabarun sai – ya yi muguwar bayar da gaskiya. Kai tsaye Adamu ya gane wannan sana’ar sunanta damfara haKKun, amma tunda da tsoka kuma Salmanu ya baibaye shi da hujjar dama duk wanda zasu cuta ko su damfara Allah ya bari ya kama gaibu, ba laifi in an nuna masa yadda ya kama Kafar wala. Wata hujjar da Salmanu ya gabatar masa itace, sana’ar na kawo Kazaman kudi, a sauKaKe zasu kawo masa  kudin da zai auro masa Husna cikin wata daya kacal! 

HMM KIYA ZATA KAYA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU DOMIN JIN YADDAH ZATACI GABA DA KAYAWA WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page