SIRADIN RAYUWA CHAPTER 17 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA

 SIRADIN RAYUWA CHAPTER 17

 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA

K’arar sakin data yiwa tray din hannunta ne ya janyo hankalinsa ya kuma ankarar dashi

“Subhanallah” ya fada yana sauke su amatullah daga jikinsa wadanda yaketa musu tambayoyi iri daban daban ta yadda zasu sake jiki sosai dashi.

     Taga tahowarshin amma saita kasa daga qafarta,saboda tana tsammanin ba’a zahiri bane,har ya iso inda take tsayen ya durqusa ya tattare dukkan abinda ta zubar din ya dora saman farantin,saiya miqe yana dubanta.

     Sunyi mugun dab da juna,wanda da zai qara taku guda tak zai iya yin masauki a jikinta

“Ki dinga bi a hankali,kada ki jima kanki ciwo kija mana asara maman twince” ya furta cikin wani irin salo da sautin murya,hucin bakinsa da numfashinsa duka na dukan wuyanta,wanda ya sabbabawa tsigar jikinta zubawa,ya kuma qara gudun zuciyarta

“Muga hannun,Allah yasa bakiji dai ciwo ba” taji yana fada,bata ankara ba har ya kama hannun nata ya sanya nashi tafin hannun cikin nata,ya soma murxawa a hankali

“Alhmdlh,babu abinda yayi” kamar wadda ta farka daga wani mafarki ta fusge hannunta da mugun sauri,ta juya da niyyar barin falon,amma ina ya fita zafin nama,caraf ya kamo faffadan qugunta daya qawata da mazaunai,wadanda suka bayyana sakamakon yadda rigar tabi jikinta.

   

     Taku ya qara tana sake rage tazarar dake tsakaninsu,kamar mai rada yace

“Na gode da halaccin da kikamin,na gode da kikabar yarana suka rayu a mahaifarki sa’annan kika haifesu,kika shayar dasu kika tarbiyyansu duk da abinda suka faru,na gode na gode…..” Iya qarfinta ta saka ta hankadashi,sa’annan cikin gudu kamar wata qaramar yarinya ta cilla zuwa dakin anty zuhriyya qirjinta na mugun bugu.

       Da kallo yabi bayanta har ta bace masa sannan ya lumshe idanunsa lokaci guda kuma ya budesu

“Oh my god,ya rabbi” ya furta can qasa,ta yadda idan ba bakinsa ka kalla da kyau ba bazaka fahimta abinda yace ba,murmushi ya qwace masa saman fuskarshi.

      Sam ya manta da yaran saida yaji muryar amatu na cewa

“Uncle….” Ya bude idanunsa a kansu,ashefa duk suna tsaye suna kallonsu,saiya sake musu murmushi suma,ya duqa gabansu yana kama kumatun amatun

“Not uncle,its daddy right?” Saita daga kanta tana murmushi.

      Kusan morewarsa yayi shida yaransa cikin falon,don babu wanda ya sake fitowa,shi da kansa yake mamakin yadda yaran suka saki jiki haka dashi,kamar dama can sun sanshi,sai kuma ya tuna cewa jini fa ba wasa bane,daga qarshe ya jasu qofar gidan cikin motarsa,ya dinga musu hotuna kamar dama ya siya wayar ne kawai saboda su.

      Bilkisu kuwa a razane ta shiga dakin anty zuhriyya wadda ke tsaye tana linke hijabin jikinta,saita saki hijabin tana kallon bilkisun

“Kin gani ko anty,wallahi ya shigo yana falon,yana tare dasu amatu anty ya akayi ya shigo,kada ya debemin yara na” kafadarta ta kama

“Babu inda zashi dasu,ki kwantar da hankalinki” baki kawai antyn ta saka ta zubawa bilkisun idanu ganin yadda ta gaza nutsuwa,tana mamakin yadda take razana fiye da kima a duk sanda zata ganshi kamar haka,tabbas akwai dalili bayaga tsoron tafiya da yaran da take.

       Sai daga baya ta fuskanci antyn ta zuba mata idone kawai tana kallonta,hakan yasa dole ta arowa kanta nutsuwa ta kuma zauna tana maida numfashi,ganin haka yasa ta juya taci gaba da ninkinta ba tare data ce da ita komai ba,ta barta tana qoqarin daidaita nutsuwarta.

      Shikam daga can saiya kwashesu kawai zuwa shago mafi kusa dasu,ya dinga sanyasu suna zabar duk abinda sukeso,duk da basu rasa komai ba,haka ya dunga lodar musu siyayya harda ta banza da wofi,ya kashe musu kudi masu nauyi ba tare da yaji ko darr ba,saida suka cika motarshi da siyayya sai wajen zamansu kawai ya rage.

      So yake yayi wani abu da zai iya zama madadi koya cike gibin da ya afku a rayuwarsu shekaru bakwai baya,yanajinsa wani babban mai zunubi kuma mai sabo idan ya tuna an raini cikinsu ba’a gabanshi ba,an haifesu ba’a gabanshi ba,an ciyar dasu abincij wani gidan ba nashi ba,basu taba sanya suttura tashi ba ko amfanuwa da wanu abu na mahaifinsu ba,duk tarin dukiyar da Allah yayi masa,yanajin ciwo da quncin hakan sosai cikin ranshi,amma yana fata nan da lokaci qanqani komai zai zama tarihi.

      Sanda su ateeq suka gama shigo da siyayyar mamaki ya kama anty zuhriyya,tayi tsaye kawai riqe da baki da hannunta,sam yaran ma su basusan me ake ba,sai nunawa su ateeq kayan suke daya bayan daya,kowa na daukar nashi yana fadin wanda zai baiwa.

  

      Bilkisu dake daki batasan me akeyi ba,sai data fito duka a sintirinta na ganin yaran sun dawo sannan tazo ta tadda kayan.

      Sosai ranta ya baci,taji kamar ta tattara kayan ta cinna musu wuta,musamman data lura anty zuhriyya kamar bata nuna damuwa ba,kuma me yasa ma ta bari aka shigo da kayan cikin gidan

“Kun sanshi ne da kuka bishi kuka karbo kaya?,roqo kuka soma abdul?” Cikin tsoro suke kada kai,saboda basu taba ganin bacin ran mahaifiyar tasu irin haka ba,fada ta kama sosai duk idanunta sun rufe,har sai da anty zuhriyya tayi kiran sunanta kana ta tsagaita

“Ku tattara kayan kukai dakinku,najwa ki jera musu cikin kayansu,wanda zai lalace kuma ki sakasu cikin fridge”

“Amma ummi….”bilkisu tayi hanzarin fada

“Ya isa” ta dakatar da ita,ba wanda ya sake cewa komai cikinsu har sai da duka yaran suka bar falon.

      “Zauna” antyn ta bata umarni cikin nutsuwa,ba musu tabi abunda tace ta zauna,antyn tayi shuru tana dubanta na wani lokaci kafin tace

“Lokacin da suka kore cikin jikinki,saninki ne cewa bashi ubansu bane da kanshi ya aikata hakan,mahaifiyarsa ce tayi gaban kanta ta aikata hakan,bilkisu,duk duniya bayan ke kanki babu wanda ya kaini jin zafin abinda ya faru dake,hakanan har yanzu inajin zafin hakan cikin raina…amma kinsan wani abu?,akwai wasu abubuwa da nayi nazarinsu cikin taqaitaccen lokaci,abu na farko…” Ta fada tana daga yatsanta

“Daga ni ke da duk wani mai qaunarki babu wanda zaiso ace yaran nan sun tashi ba tare da sunsan waye mahaifinsu ba,ba tare da sunsan asalinsu kuma tushensu ba,idan wasu sun musu kallon ‘ya’yan halali saboda sunsan sanda aka daura aurenki,da yawa zasu musu kallon shegu ne,kalmar da sai ta kusa tarwatsa zuciyarki fiye da yadda zuciyar taki taso tarwatsewa a baya,duk yadda zanso daukan fansa nuna fushi ko jin zafi kan lamarin bilkisu,bazanso su abdul su rayu ba tare da sanin waye ubansu ba” shuru tayi tana kallon bilkisun kafin ta dora

“Abu na biyu kuma…dukka hasashena da abinda ya bayyana garemu….mahaifiyar yarima ita keda alhakin komai,ta shirya komai kuma ta tsara faruwarsa yadda taso saboda tana jin cewa qarfin izzarta isa iko da kuma mulkinta sun isa susa komai dai daita,ban sani ba koda goyon bayansa,ban sani ba ko babu,hakanan ban san ko tare suka shirya ba,amma abinda nafi gasgatawa shine ita ta shirya,zan iya cewa a yanzun kamar dama kika samu,dama kika samu da zaki nuna mata kurenta,dama kika samu da tana kallo zaki kasance da yaronta ba tare data tsara faruwar hakan ba” kamar wadda aka mintsina sai bilkisun ta miqe tana kada kai.

         Murmushi anty zuhriyya ta saki tana nuna mata kujera da hannu

“Kwantar da hankalinki ki zauna,hasashena ne,kina iya yin dukka yadda kikaso a yanzun damarki ce” saita koma ta zauna din,anty zuhriyya ta dora

“Abu guda nakeso ki fahimta kuma ki gane,wannan dalilan nason yaran susan ainihin tsatso da mahaifinsu yasa na bashi damar shigowa gidan da kuma ganinsu bawai wani abu ba daban,abu daya kuma zuwa biyu nakeso na fahimtar dake,ki daina zafafa qiyayyar mahaifinsu gaban idanunsu,saboda shaquwa da qauna mai qarfi na iya shiga tsakaninsu,ta tadda zasu fara iya gano aibun abinda kikeyin,zasu kuma iya bin bayanshi nan gaba,sannan duk koma meye ya farun ba hurumin su sani bane,don haka ki dinga qoqarin dannewa,amma baya ga haka,babu abinda ya sauya game dasu a zuciyata,hakanan ba wani sassauci ko sauran dama a kanki,sai abinda kedin kika zaba”……

      *_ABDUL_AZEEZ_*

       Ranar yau din jinsa yake daban,jinsa yake kamar an sauyashi,wani irin farinciki ke ratsashi wanda ga duk wanda yasan shi,yasan ainihin zahirin fuskarshi zaiyi mamaki qwarai idan yaga wannan yanayin saman fuskar tashi.

     Cikin nutsuwa da kuzari yake tuqin nasa,cikin zuciyarsa kuma yana wassafawa gami da ayyana yadda zai shawo kanta,yana ganin matuqar yaran suka shaqu dashi,shaquwar tasu zata taimaka qwarai wajen janyo nata hankalin.

        Sassanyan murmushi ya subuce masa sanda ya gama hasaso kansa tare da bilkisun cikin wata duniya ta musamman wadda dagashi sai ita.

      Komai ya katse masa sanda wayarsa ta soma ringing,yaja qaramin tsaki yana jin haushin yadda kiran ya katse masa daddadan tunaninsa,yanajin me yasa ma bai kashe wayar ba.

       Dai dai lokacin da fulani kenan ke tsaye tsakiyar falonnata cikin tashin hankali,tana kuma sauraron mama sodangi dake mata kiran yariman.

       Ganin ya kusa isa gida ya sanya baibi takan wayar ba,har sai daya isa wajen parking,yana tsaidata idanunsa yakai ga wayar wani kiran na shigowa,sunan mama sodangi daya gani ya sanyashi kashe motar kawai yayi,ya daga kiran ba tare daya fita a motar ba.

       Ga mamakinsa muryar ammi ce ta soma shiga kunnensa a maimakon mama sodangi

“Barka da war…..” Ya soma yunqurin gaidata

“Dakata yarima!” Ta dakatar dashi a matuqar tsawace,tsawar data ratsa kunnuwansa da kwanyarsa dakyau

“A yau na yarda da cewa nidin ba koman komai bace a wajenka,ni ba wata tsiya bace….sanna yaudarar daka jima kana min tsaho shekaru game da bilkisu a yau Allah ya bayyana min komai,na gani da idona,gani kuma na zahiri,saidai abinda nakeso ka sani,ka tafka kuskuren da zai jawo rushewar komai,qimarka da tawa,darajata da taka,martabarmu gaba daya,hotunanku ya fara yawo cikin masarauta kai da yarinyar cikin yanayi na abun tur da Allah wadai da bai kamata aga dan qwarai a haka ba…..bana so ka wuce satin sama ba tare da kazo ka sameni cikin kaisa ba,sa’anan daga yau a yanzun nan nake cewa…..idan ka sake rabar yarinyar ban yafe maka…”

“Ammiiiii” ya kira sunan nata cikin wani irin sauti na gigicewa da razana

“Kada kiyi haka,kada kuma kice haka,ina buqatar yin magana dake,akwai abubuwa da yawa da baki sani ba wanda ya kamata ace kin sani”

“Abdul’azeez!,ba kana magana bane da sa’arka ba,mahaifiyarka ce idan ka manta na gaya maka,bana buqatar sani ko jin komai,ruwanka kabi umarnina koka saba,furucina zai bika” daga haka ta katse kiran ta baiwa mama sodangi wayar,cikin tashin hankali da bacin rai ta soma magana

“Inason cikin barorina a zabo min amintattu mutun talatin da zasu shiga kowanne lungu da saqo na masarautar nan,su kuma zaqulo gami da fiddo hotunan a duk inda suke,hakanan suyi aiki ba dare ba rana,subi dare subi rana su tsince hotunan a duk inda sukaga an yar a qonasu,ba shakka wannan wani shirine da aka jima anayi ana bibiyar sawunmu don a tarwatsa mu,saidai kamar kowanne lokaci, a wannan lokacinma ina da babban zaton shirinsu ba zaiyi tasiri ba,amma fa…..sai munyi babban aiki,ta yadda hotunan ba zasu shiga hannun maqiyana abokan zamana ba,bare kuma…..” Sai tayi jim tana tuna girman lamarin

“Mai gaba daya mai girma mai martaba,ayi gagggawar aiwatar da abinda nace cikin sirri,kada a samu kuskure”

“An gama” umma luba ta fada suka miqe tare da mama sodangi suka fice,yayin da mama sodangi tayi nisa cikin tunani gami da nazarin al’amarin,yadda zata kaya,da yadda zata kasance,meye qarshen abun?.

_kuyi manage,banson yin muku fashin posting,babu yawa,da babu gwara babu dadi ko?inji hausawa_😁

      Da qyar ya samu ya iya kai kanshi falonshi ya zube yana jin wani jiri jiri,astagfirullah kawai yake ambata a fili da boye,don wannan karon bayajin zai iya bin umarnin fulani kwata kwata,zaije ya tunkareta kamar yadda takeso,amma kuma bada lamarin da takeso din ba,a yanzun yana jin a shirye yake ya bayyanawa duniya bilkisu matarsa ce,a bayyane yake ya amshi matarsa da dukka yaransa,a yanzu ya sake shiryawa tunkarar duk wani qalubale daka iya fuskantoshi.

      Yanaji wayar tana sake ringing,daya duba sai yaga safwa ce,baida kuzari ko sha’awar yin magana da kowa,a yanzun kadaici yake buqata fiye da kullum don ya shiryawa tunkarar abinda zai dososhi,don haka ya maida wayar silent gaba daya,harta qaraci burari da kiranta ta gaji ta ajjiye.

 ¶¶¶¶¶¶¶¶    ¶¶¶¶¶   ¶¶¶¶¶¶

         Idan tace tayi kyakkyawan bacci ko taci abinci ya tsirga mata kota zauna ta samu hutu da nutsuwa ba tare da fargaba ko tashin hankali baa kwanakin ta yiwa kanta qarya,koda yaushe cikin zulumi da aikin tsinto hotunan suke,abun yana neman ya gagari kundila saboda yadda kullum wayewar gari ake tsinto mata hotunan rututu,magana harta so ta zagaye kusan rabin masarautar,ya soma zama wani topic mai zaman kanshi da duk inda kaga mutane sama da biyu zaune suna hira kusan zancam da sukeyi kenan,don ma alkhairinsu cikin masarautar ya taimaka qwarai wajen rage yawan zargi da cecekuce.

       Saidai kuma akace dan adam baka iya masa ba,dan halak shike rama halacci,wani duk yadda kakai ga kyautata masa akwai lokacin da zai rufe idanu ya shiga sahun masu cutarka ayi dashi,koda ka shekara dari kana masa alkhairi ne kuwa,shi yasa hausawa sukace dan halak shike rama halacci,to kusan hakanne,da yawa daga cikinsu da basu duba kyautayi kyauta gamida halaccin fulanin ba,sun gauraya da ‘yan kora masu aiki qarqashin fulani adama suna sake hura wutar zancan lungu da saqo,wannan yakai har kunnan fulani yadda maganar ke yawo.

         Tashi hankali sosai ta shiga,tana duba girman abinda ka iya zuwa ya dawo matuqar maganar taci gaba da wanzuwa har zuwa lokacin da baqi zasuci gaba da sauka masarautar domin halattar wannan gagarumin hawan daya tara al’umma da yawa,daren data masa barci,ta jima tana ta zirya gami da tunani da son hasaso wanda ya qulla dukkan wanna tuggun,duk da zarginta yafi ga mutum biyu,adama ko saratu,a binciken data saka aka mata kusan mutanen fulani adama su fi yawa cinin masu tofa albarkacin bakinsu game da lamarin,don haka zarginta yafi karkata a kanta.

        Ta fannin fulani adama kuwa labarin dukkan yadda lamuran ke tafiya yadda takeso na zuwa mata kunnunta,abun ya mata dadi qwarai da gaske,tayi shewa tayi dara tana kuna jira da dakon ranar da zata isa gaban mai martaba fa miqa hotunan,ranar da zata samu dimbin shaidun al’umma na suma sunga hotunan na yawo a masarautar,ranar da zata tarwatsa farincikin fulani aishanta cusa mata kadan daga cikin baqincikin data jima itama tana cusa musu

“Allah ya baki yawan rai,ta qara yawan ma’aikatanta masu kwashe hitunan a duk inda muka sakesu”

“Ina umartarku daku qara yawan hotunan ninkin baninkin abinda aka saba bugawa da zubdawa,ku qara yawan sasannin da kuke ajjiyesu,so nake ya zamana hatta da maqasqanci mafi qarancun matsayin bawa a masarautar kaisa,babba da yaro ya tsinci hoton bawai labari kawai ba,ta yadda qimar abdul’azeez da mahaifiyarsa zata tafi daga masarautar nan,tafiya ta har abada” wannan shine umarnin da fulani adaman ta bayar.

        Sannu sannu saiga hoton har a hannun fulani saratu,ta jima tana qarewa hotunan kallo cike da mamaki da jinjina lamarin,tana kuma sauraren bayanin da daa daga cikin bayinta keyi.

        Murmushi ta saka daga qarshe tana ajjiye hoton a gefanta,ta zauna cikin nutsuwa tana fadin

“An hana yaranmu fita zuwa wata qasar karatu da zummar kada su lalace,lallai ya kamata nayi tattaki har zuwa sassan fulani na soma miqa jajena a qareta,tare da jiran ranar da labari da idanuwan mai.martaba zaikai kai wannan danyan aiki da yarima kaisa keyi a qasashen turawa” tana fadin maganar tana jin zuciyarta wasai,yanzun lokaci yayi da ko qaqa zata samu ta rama wani yanki daga haushi da takaicin aishan gami da kishi dake cin ranta.

   ¶¶¶¶¶    ¶¶¶¶¶    ¶¶¶¶¶

     Kamar kowanne lokaci yauma tana zaune cikin daya daga cikin falukanta da ayau ta zabi ta zauna,duk da zamane kusan na alhini da fargabar abinda kowannw second na awannin ranar zai iya haifarwa,zamane kamar na makoki take,zaman tattara dukkan wasu hotuna da aka zubar a ranar,wanda kafin ta koma ciki sukan tara hotuna masu yawa,wadanda a yanzu haka hotunan har sun ninka nada,hakan ke sake tabbatar mata lallai lallai akwai zagon qasa da kuma saran boye cikin lamarin.

        Sanda aka nemi izi inta kan shigowar fulani saratu tayi mamaki qwarai,taso ta hana,sai kuma tayi tunanin idan har ta hanata din kamar tana basu isharar cewa tasan meke gudana,ko kuma haka abun yake,don haka tasa aka kwashe hotunan da ake tarawar zuwa inda kullum suke qonawa,kana ta bada umarnin ta shigo.

      Cikin wani irin taku da take jin ranta fes ta shigi zuwa falon,ta daga kanta a fakaice tana kallon yadda aka narkawa falon dukiya da tsari gamida zubi irin na masarautar mali,falo ne da aka shirya nata shi takanas daga can masarautar iyayenta,kama daga ma’aikatan da sukayi aikin zuwa dukka kayan da aka zuba din,tana kishi sosai na yadda kullum gado na sarauta ke bayyana daga wajen aishan,tanajin da tana da iko ko qwanjin qwacewa da tuni ta qwace wannan nasabar.

     Fulanin a yau tana lura da yadda take qarewa falon kallon,sabida kanta tsaye a yau takeyin hakan

“Bismillah mana” fulanin ta fada cikin qoqarinta dakiya gamida jarumta.

        Sauke ganinta fulani saratu tayi saman fuskar fulani aisha sannan ta saki wani irin murmushi wanda ya haddasawa gaban fulani aishan faduwar gaban da tunda take bata taba jinta ba akan kishiya,sai saratun ta bude baki a nutse tace

“Haifaffiyar diya ga masarautar mali,mata ga sarkin yau,uwa ga sarkin gobe ko?” Ta qarashe maganar ta sigar tambaya,bata tabajin ta kasa magana ba tsahon rayuwarta don sun yada mata magana ba sai a yau,ta hadiye wani abu mai tauri idanunta tsakiyar na saratun kamar yadda itama take kallonta,tana kuma jin dadin sauyin tanayinta

“Shi jaje ai ba lallai sai a zaune akeyinsa ba,basai na zauna ba,don a duk yadda ta kama yinsa ake,fata dai a taya wanda akewa jajen alhini” saita soma takawa tana nufar qofa,sai kuma ta tsaya

“To uwar yarima….au a yanzun fa bai kamata ke daya a rinqa kiranki da wannan sunan ba,muma ya kamata mu shiga ciki,don da alamu damar zama hakan ta zama ta mutane da yawa,duk da bamu da cikin haifar diya maza,sai ya huwacewa yaran namu mata,kinga ko cikin jikoki a laluba,wala’alla a dace da kinin abdul’azeez,kinga shikenan…..baki alaikum” ta qarasa tana sake sakin murmushi

“Kinga dai na manta zan fita ban miqa saqon jajena ba,ina miki fatan nasarar tsallake wannan guguwar data kunno muku,duk da bawai har can qasan zucia ba,na tabbatar kina sane da dukka dokokin masarautar kaisa ko?,to Allah ya sanya iya kanta kawai yariman namu ya tsaya,kada aje allura ta tono garma kuma…..na barki lafiya” daga haka ta saka kanta ta fice tana jin wani nishadi da farinciki yana yawo da ita,don tunda take bata taba ganin damuwa firgici saman fuskar aisha ba sai yau,abinda suka jima suna son gani amma basu gani din ba sai yanzu,ba shakka ita duk wanda ya aiwatar da wannan shirin ya mata dai dai,tana kuma fatan abun ya tsawaita,ta yadda zaiyi wancakali da dukkan dama da dajarta harda martabar aishan da iyalanta..

       Fulani saratun na fita itama ta miqe tana jin kamar saman allura take,jikinta ko ina zufa yake fitarwa,ba shakka maimartaba na gab da sanin wannan lamarin tunda har takai ga kunnuwan abokan zamanta,wani tsanar bilkisu ta darsu a ranta,yarinyar tana son zame mata tauraruwa mai wutsiya,anya kuwa ba komayya tayi suka hada hannu da abokan gabanta aka shirya dukkan wadan nan abubuwan ba sabida a rusata?,tunda yarinyar ta shiga cikin rayuwarsu komai yake tafiyar mata a hagunce,amma babu babban mai laifi irin azeez,lallai wannan karon zata ture dukkan wata soyayya ta hukuntashi yadda zaisha mamaki shi karan kansa.

      Zaune yake saman daya daga cikin kujerun falon yana kurbar coffe mai zafin gaske kamar zai qona harshe,dagashi sai boxer wanda hakan yayi silar tonuwar asirin qaqqarfan jikinsa dake a murde,da kuma lallausar gargasar data yiwa jikin mashi qawanya,kama daga qirjinsa singalalin qafafunsa zuwa na hannayensa.

       Fuskarsa a yamutse take qwarai,kamar yadda zuciyarsa take a yamutse,tun jiya yake lissafin yadda zai tafi nigeria ba ya barsu a brasil,ji yake kaman zaiyi wani nisa dasu mai yawa wanda kamar ba zasu sake haduwa ba kenan,kaman zasu bace masa bat.

      Wayarsa dake gefe ta dauki ringing,saiya shareta kawai,tayita kida tana katsewa har sai daya gaji ya duba mai kiran nashi.

      Daya daga cikin informers nashi ne daya dauka haya,tunda yaga sunan yasan cewa akwai labari,don haka babu jinkiri ya daga wayar ya kara a kunnensa

“Nigeria?….ok thanks” ta fada yana katse kiran.

      Cilla wayar yayi saman kujera yana fidda nannauyan numfashi daga bakinsa tare da hancinsa,tabbas ta sauqaqe masa kewarsu da yakeji,tafiyar tata kuma zuwa nigeria tayi masa dai dai,hakan shi zai bashi cikakkiyar damar da zai daidaita dukkan al’amuran,yanajin zuwa yanzun shima babu wani abu daya rage masa ko ya masa saura a brasil,don haka ya aje cup din kai tsaye ya nufi daki bayan ya dauki wayarsa,ya kuma yi booking flight,wanda ya kama zai isa nigeria ne ranar da ake gabatar da hawan daba din.

  *_ABUN BOYE…….._*

    Rana ce ta musamman ga dukkan jama’ar qasar kaisa bama masarautar kadai ba,saboda rana ce da akanyi hawa na musamman,sarkin kaisa yakan kewaya jama’arsa waje waje,sukan tattaru su miqa masa gaisuwa ga wanda baida zarafin ganinshi cikin fada,wanda kume keda zarafin ganin nasa kan riskeshi acan ya miqa tashi gaisuwar,yakan zauna har zuwa lokacin sallar la’asar,wanda daga sallar la’asar dinne kuma zai wuce cikin gida ya gana da ‘ya’yansa gamida jikoki da kuma ‘yan uwa da suka samu halartar bikin.

       Kowanne sashe na gidan kan zamana cikin baqi,hakanan kowa kan kasance cikin ado kamar bikin sallah,yaudinma haka ta kasance,saidai ga fulani aisha,sam bata taba ganin birkitaccen bikin hawan daba da yazo mata a hagunce,a kuma yanayi mara dadi ba irin wannan,don gaba daya bata nutsuwa ko kwanciyar hankali,ta sake baza da linka masu duba mata hotunan fiye dana baya,wanda akaci gaba da tsintosun kuwa kamar ana ruwansu.

       Abinda ya sake tada mata hankali kenan,duk da tarin kwalliya da adon daga caba da sutturu masu azabar tsada da daukar idanu,duk wani abu data saba yiwa mai martaba a irin wannan rana batayishi ba,donko zuwa da suke masa rakiya sanda xai hau doki bata samu zuwa ba,wannan ya faranta ran adama da saratu,musamman adama da tuni ta gama shiryar tashin bomb a yau wanda zai qarasa gille sauran dukkan wata nutsuwa data yiwa aishan saura.

        Tsaye take a daya daga cikin bedroom dinta,tana duban tulin hotunan dake cikin wata babbar leda,yayin da guda daya ke riqe ahannunta ta tsura masa idanu,saika rantse da Allah kallonsu take,saidai tayi nisa ne a duniyar tunani da kuma neman mafita.

       A nutse afnan data yi ado sosai cikin suttura ta alfarma wadda ke alamta inda ta fito,ta turo qofar dakin mahaifiyar tata gami dayin sallama,adan firgice fulanin ta dago tana amsawa gamida qoqarin kifa hotunan saman madubi.

       Tuni afnan ta riga data fuskanci me take boyewar,wanda tuni ita ta ganshi tama mallaki wasu daga ciki,kamar yadda wasu daga cikin jama’ar masarautar suka mallaka.

       Idanunta akan mahaifiyar tata ta qaraso dakin

“Lafiya afnan?….ya akayi?”

“Su yaaya sumaira ne ke jiran fitowarki tun daxun shuru” tayi maganar tana miqa mata hotunan data shigo da su.

      Batabi takan maganar jiranta da yaran nata keyi ba,illa miqa hannu da tayi da hanzari tana karbar abinda afnan din ke miqo mata,cikin zuciyarta tana fatan Allah ya sanya ba wani mummunan saqon bane.

     Hotunan nan ne dai da kullum idaniyarta ke kwana su wuni suna kalla,ta kuma kwanta ta tashi tana mafarkinsu,hotunan dake barazana da kwanciyar hankalinta nutsuwarta darajarta da martabarta,saidai abun yakai har afnan ta samu itama?,lallai nan da wanu dan lokaci zasu isa hannun mai martaba.

      Muryar afnan itace ta katse mata dukkan tunanin da takeyi

“Ya azeez….da tsohuwar matarsa,qawata bilkisu bilyamin….yarinyar da aka tsigeta daga karatunta,aka rabata dashi,sannan akayi mata auren dole ba tare data shirya ba,aka katse duk wani buri da mafarkinta saboda laifin da bata aikata ba,saboda biyan buqatar wasu,yarinyar da nake kwana na tashi kullum.ina tunanin ko tana ina?,ko a wanne hali take yanzu?,ashe da zuriata kuma jinina wajen cutatar da rayuwarta” takai qarshen maganar da alamun abun yana mata daci a rai,hakanan idanunta nakan fulani,wadda itama ra kafeta da idanu tanason karanta da kuma fahimtar me afnan din ke cewa.

       Tsaf qwaqwalwarta ta soma shirya mata kalaman,saita hade rai sosai tana duban afnan

“Ke….banason sakarci,ki barmu da yarfe da bata sunan da akeson mana,shine ke kuma zaki shigomin da wasu kalaman banza” murmushi ta saki

“Kimin afuwa,ki kuma yafemin,ba yarfe ko bata suna bane ya kamata ace ya dameki ba ammi,saboda dama duk nisan jifa qasa zai fado,hakanan komai daren dadewa dole wannan sirrin ya fito….abinda yafi dacewa ki damu dashi shine,yadda kika sarrafa rayuwar baiwar Allah ta hanyar da kikaso,sannan kuma yaya rayuwar tata ta kasance bayan nan?,naga bakya qauna ko kusa atuna miki ta taba zama surukarki ko ammi?….to yanzu dai hanyoyi guda biyu suka rage mu daga ragowar martaba da qimarmu…na farko….inma ki fita ki shaidawa duniya cewa wannan din tsohuwar matarsa ce da suka taba aure,an dauki hoton sanda suke a matsayin ma’aurata duk da nasan ba haka bane,to amma ta yaya zaki musu bayanin yadda auren ya gudana?,shin zasu gamsu?,tunda basu da masaniyar sanda aka qullashi?,…..wa imma kuma ki bar mutane kowa yaci gaba da tofin alatsine garesu gami da aibatasu,ana mata kallon karuwa da kwartonta,wanda aikata hakan kamar qarin wani zunubinne akan wani,kuma shizai qarasa rugurguza martaba da qimar da kiketa mana tattalinta…..” Tsawa tayi saurin dakawa afanan,tanajin kanta ya soma yamutsewa,dukkan idea na kubuce mata daya bayan daya,saita nuna mata qofa da yatsa

“Fita ki bani waje tun bsn bata miki ba” murmushi afnan ta saki ta soma takawa zata fita din kamar yadda ta buqata

“Ke mahaifiyata ce da bani da kamarki,hakanan bazanso naga kin shiga kowanne irin hali ko yanayi mara kyau ba shi yasa na tunkareki da wadan nan maganganun,kiyi haquri ki dubasu dakyau tun lokaci bai qure mana ba” daga haka ta fita din kamar yadda ta buqaceta.

       “Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un” ta soma ambata a fili,kana ta zame ta zauna gefan gadonta tana zame dankwalin kanta da takejin ya mata nauyi,yaya akayi tayi sake haka lamura suka kwabe mata ne?,wannan itace babbar tambayar da take jifan kanta da ita.

      Kusan cikin dakin ta wuni,har sanda akayi sallar la’asar,ta soma jiyo muryar mai martaba cikin masallacin dake cikin gidan,yana daura auren wasu daga cikin barorin gidan maza da mata da suka samu mazajen aure,wanda yake kamar aikinsa ne,ya dorwa kansa alhakin aiwatar da haka duk shekara indai aka samu masoyan da suka daidaita kansu,yakan sanya a hada bikin daba din da bikin auren nasu,hakanan shike musu komai na aure,yakan ce Allah ya sanyasu ne qarqashinsu domin muma muyi musu hidima,ya sanya wasu daga cikinsu sun zama bayi a garemu,bayan ga mahaliccinsu kawai wannan bauta take,kyautatawarmu a garesu shike nuna zallar godiyarmu ga mahaliccinmu kan ni’imomi da baiwa daya mana masu tarin yawa.

       Kusan duk abinda zaiwa barori matan da shawara da kuma sanya hannun fulani aisha yake aiwatarwa,wanda kusan ita ta qarfafi wannan shawarar tashi tun shekarun baya,takan kuma sanya itama nata kason a cikin hidimar masu kayan aure,badon mainartaba ya gaza ba,a’ah,tana yine da sunan sadaka da kuma neman lada,saidai a wannan shekarar kusan komai saidai taji labari,don bata da wannan nutsuwar,illa kudin dai data saba bayarwa bata fasa ba.

       Sai da aka gama daura auren kaf a kunnunta sannan ta miqe da qyar ta shiga bandakinta dake cikin dakin ta daura alwala ta tada salla,koda ta idar tana saman abun sallar tana tunane tunane,ta duba lokaci,taga akwai sauran kusan awa guda daga sanda zasu isa wajen maimartaba,don haka taci gaba da xama saman abun sallar tata.

       Saidai me?,bata jima ba saqo ya risketa ta hanzarta zuwa sassan mai martaba da gaggawa yana da buqatar ganinta,ta zuba jakadiyar idanu gabanta na wani matsanancin faduwa,yanayin yadda aka kawo mata saqon yana nuna kamar ba lafiya ba.

       Alkyabbarta kawai ta zura wadda ke aje tun daxun a gefe,sabanin daa da saita tsaya ta sake wanka,ta kuma fesa ado na qasaita,irin adon da tasan mai martaba na mutuwar so,irin adon da tasan zai tafi da hankalinsa,saidai a yanxun duka bata jin wannan nutsuwar.

       Tun a hanya ta lura da yadda masu satar kallonta suka yawaita,tun a nan dukka wani karsashi da qwarin gwiwa da take baiwa kanta ya soma bajewa yanayin nasa guri,tana tattaroshi amma yana sake sulalewa,da haka ta isa ga sassan mai martaba,kana ta qarasa kai tsaye ga turakarsa.

        “Wannan babban abun tashin hankali ne a garemu baki daya…..abun kunya tur da ala wadaine,tun sanda nasamu saqon na kasa samun nutsuwa bare barci,abdul’azeez fa Allah ya taimakeka?” Abinda ta soma tsinta kenan daga muryar adama,wadda ke zaune gaban mai martaba tana sharce qwalla.

        “Ya Allahu,ya naseru”ta furta cikin ranta,tana neman daukin ubangiji sanda suke hada idanu da maimartaba,wanda bisa alamu shigowarsa sasaan nasa kenan,ya soma rage kayan jikinsa adaman ta cimmasa,don bai gama fidda kayan da yayi hawan gaba daya ba.

     Karon farko a rayuwarta dataji ya mata wani mugun kwarjini,irin kwarjinin da takanji jama’ar da yake mulka wadanda suke qarqashinsu suna labari lokaci zuwa lokaci,gwiwa a matuqar sanyaye ta dauke kanta daga adama daketa hada hawaye bilhaqqi,ta isa gabanshi ta zube cikin sanyin jiki qwarai da sanyin murya tace

“Barka da warhaka”

“Barka kadai aishatu” ya amsa mata cikin kulawa yana jin tausayinta a ranshi,saboda ya lura da yadda jikinta yayi sanyi qila itama ta samu labarin komai katsam kamar yadda ya samu,yake raya haka a ranshi,saidai kuma,akwai alamun bacin rai a muryarshi da yake dannewa sanda yayi maganar.

       Kai tsaye ya miqa mata hotunan data tabbatar cewa sune,ta kuma soma gajiya da kallonsu,don ba azeez da yake danta ba,hatta da bilkisun ta haddace dukkan surori da kuma kamanninta tsabar kallon hutunan.

        Kamar ba zata karba ba,sai kuma ta tuna aikata hakan kamar bada wata qofa ko dama ce ga adama dake zaune a gefanta ta zuba mata idanu kamar tsohuwar mayya,wanda ta tabbatar tanason ganin reaction dinta ne kawai,don haka tasa hannu biyu a hankali ta karbi hotunan,ta dawo dasu gaban idanunta,tayi kamar ta kalla kana ta kifasu saman cinyarta tana fadin

“La haula wala quwwata illa billah” tana rufe idanunta saboda yadda taji zuciyarta na wani irin bugawa

     

       “Hmmm…ana zaton wuta a maqera,sai haquri,yaran yanzune ka haifesu amma baka haifa halinsu ba” adama ta soma zuba,mai martaba ne ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu yana kallon aisha

“Kina da masaniya kan wani abu daya danganci hoton?” Ta yaya zata amsa masa gaban wannan makira kuma azzalumar matar,wanda daga shigowarta zuwa yanzu ta fahimci ita ta shirya komai,sannan tayi tattaki ta kawo masa hotunan har dakinsa,don haka kawai saita girgixa kai alamun a’ah.

      Dauke dubansa yayi daga gareta,kana kai tsaye ya janyo wayarsa ya soma laluben lambar abdul’azeez kai tsaye.

       Daidai lokacin da yake xaune falonshi,kace kace tsakiyar takardu laptop da wayoyinsa,bayan ya gama tsara da jiran awannin tafiyarsa su cika.

      Wayoyi yake amsawa tare da kira,yana kuma tsarawa kansa hutu da na tsahon wata guda daga dukkan kamfanoninsa da harkokin kasuwancinsa,yana tura takardun inda sukka dace su sani,yana kuma nada wakilansa,sabida a hasashensa yana saka ran zuwa wata guda mai zuwa ya gama settling komai,yana fatan hankalinsa ya soma dawowa jikinsa.

     Da sauri sauri yake komai,saboda yana riqe da awannin da suka rage masa na tafiya airphort don sauka a qasarsa nigeria.

       Wayar dake hannunsa ce ta dauki ringing,ganin sunan mai martaba ya sanyashi sake nutsuwa,ya ajjiye biron dake hannunsa ya kwantar da bayansa a makarin kujerar sannan ya daga wayar cikin girmamawa da nutsuwa.

       Baice masa komai ba har suka kammala gaisawa,kana yace

“Inason a yau ka nemi jirgi duk inda yake,ka tabbatar ka kwana a masarautar kaisa” umarnin daya soma bashi kenan,duk da yayi mamakin hakan amma saiya danne yace

“In sha Allahu nan da awa hudu zan iso qasata”

“Allah ya nuna mana” ya fada yana katse wayar,idanunsa kan adama,tariyar maganganun da abubuwan data gaya masa masu yawa ke masa kai komo kan yaron nasa,bayason yace komai bisa zargi,bayason ya yanke komai bisa labari kawai,hakanan bayason wai wai da ance ance,amma magangun data gaya masa kan yariman ba qananu bane,duk da haka shidin babba ne mai hankali,kuma jagora shugaba,yana da buqatar nutsuwa da kwantar da hankali kan duk wani hukunci da xai yanke

“Dukkanku kuje,zan sake nemanku” ya sallamesu gaba dayansu,don yana buqatar yin nazari sosai.

       Wayar azeez yabi da kallo bayan maimartaba ya katse,saiya saki ajiyar zuciya yana sake kwanciya sosai,gefe guda kuma yaji ya sake qaguwa daya isa nigeria,tuni ya gano inda bilkisu ta yada zango,yanajin kuma shine abu na biyu da xai gabatar bayan ya saurari mai martaba,sabida yana da yaqinin akwai dalilin da yasa ya kirashin ya kuma nemi tahowarsa again bayan wanda mahaifiyarsa ta buqata.

     ¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶

    Ba abinda take sai kaiwa da kawowa tsakanin falukan nata ta dangane da daki cikin tsantsar tashin hankali,tashin hankalin da bata taba shiga makamancinsa kamar yau,ji take inama ace zata iya tsaida komai cak ta kuma sauyashi zuwa dai dai,zuwan abdul’azeez ba qaramar barazana bace a wajenta,gashi mai martaba bai gaya masa dalilin kiran nashi ba bare ya dauki haske,ko kuma tun acan ya gama tsara abinda zaya gaya mishi idan ya iso,uwa uba tanata kiran wayoyinsa gaba daya sunqi shiga,alamu ne dake tabbatar da cewar yana hanya kenan,koya gama shirinsa na baro qasar daga yanzu zuwa kowanne lokaci,idan da so samune zataso ace ita ta soma tozali da azeez din,don suyi magana,su kuma san ya zasu bullowa lamarin,ta yadda komai bazai kwabe ba.

      A wannan yanayin taci gaba da kasancewa,har zuwa lokacin da akayi sallar magariba,sam yaranta sun kasa gane kanta,don basusan meke faruwa ba,bayaga afnan ita kadai,wanda itama babu wanda ta shaidawa banda mama sodangi.

       K’arfe uku na dare agogon brasil,takwas na dare agogon nigeria ya taso zuwa nigerian,sam sai yakega kamar jirgin baya sauri,tafiyar awanni taran ya dinga jinta kamar tafiyar shekaru tara,duk bayan wani daqiqa yana jin kamar ana sake kusantashi da bilkisune da ahalinsa,yana ji a jikinsa wannan tafiyar kamar wani mabudi ne da warwara na dukka matsalolinsa.

       Ga fulani kuwa kusan kwanan zaune tayi,dukkan wani tunani da idea nata sun watse,abu na qarshe data zabawa kanta yi shine,ta kira daya daga cikin malaman da suke mata sauka,ta shaida masa tana da damuwa ayi mata sauka daga nan zuwa safiya a yi sadaka,ta aika mishi da kudin saukar kamar yadda ta saba lokaci bayan lokaci.

       ¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶

     Ana kiraye kiraye na sallar asubahin nigeria cikin masarautar kaisa motarsa ta soma shigowa babban ginin masarautar,wanda ke nuna zallar sarauta da alfarma gamida qarfin mulki da gidan sarautar keda shi tun tale tale,hakanan har yanzu yana nan bai gushe ba.

      Kai tsaye sassansa ya nufa kamar yadda ya yankema ranshi,yana ganin yanzu yayi safiya da yawa ya nemi ganin wani cikin mahaifansa ko makusantansa,wanda yana da tabbacin zaije ya samu komai a sassan yadda ya kamata,duk da cewa safwa ta shaida masa ta koma tun shekaran jiya,amma akwai wadatar ma’aikata,barori da bayi.

      Kamar kuwa yadda ya zata din,komai na killace cike da tsafta da tsari,sai ka zaci akwai dan adam a sassan,yayi masauki a katafaren dakin gadonshi wanda yake dai dai da aljannar duniya.

      Abu na farko daya fara hada ruwan wanka mai dumi sosai wanda zai dace da yanayin da yakeso,yayi wanka sosai,yanayi yana duba lokaci,duk da yasan da wuya ya samu jam’in sallar asubar,don yaji sanda suka tayar.

      Jallabiyya kawai ya sanya ya tada tashi sallar,bayan ya idar baiyi gaggawar tashi ba kamar yadda ya saba,saidai yau zaman nashi ya banbanta dana kullum,hakanan yaji ya dade saman abun sallar yana addu’o’i,qari akan wadanda ya saba,baibar saman abun sallar ba,sai daya duba lokaci,yaga yayi dai dai da lokacin da maimartaba kan zauna da duka ahalin nasa a irin wannan safiyar ta washegarin hawan daba,duk da baccin da yakejin yana fusgarsa sama sama amma haka ya yakiceshi,yahau shiryawa sosai cikin shigar dake bayyana gadon sarauta gaba da baya,jinin mulki da qasaita,shigar data qara masa kyau qima da kuma kwarjini qwarai da gaske.

      Duk wannan abun dake faruwa tun daga shigowarsa masarautar har isarsa sassansa fulani adama nada labari daga mutanenta data baza,saboda ta tabbatar yariman zaya iso kamar yadda yace,daga sanda maimartaban yayi kiransa zuwa kowanne lokaci za’a iya ganinsa.

      Murmushin jin dadi ta saki lokacin da ake shaida mata ya riga daya iso din,a hankali ta furta

“YAU ZATA FASHE!” Abun yana mata dadi sosai cikin rai,tana hango tozartar aisha ayau din,don haka ta janyo wayarta ta shaidawa haj fauziyya dake nata sassan wanda takan sauka duk sanda tazo,daga can ita kuma ta kira kamal,suka gama dukka tsare tsarensu ta hanyar wayar.

     Cikin dauriya da dakiya,da kuma rashin son baiwa abokan gaba qofa da zasu fahimci galaba akan dukkan tsarinsu a safiyar fulani aisha ta shirya,cikin shigarta dai tayau da kullum ta qasaita dake tsone idanun abokan xamanta,saidai a yau din maimakon alkyabba,tsadajjen mayafi na musamman ta nade jikinta da lallausar atamfar da tayi adonta,ta kuma iso katafaren dakin cin abincin da aka tanada saboda ranaku ire iren wadan nan cikin yaranta da ‘yan jikokin da aka haifa mata.

      Kusan kowa cikin walwala yake a wajen idan ka debe ita,duk da tayi qoqarin qaryata hakan akan fuskarta,da kuma qoqarin da tayi ta aro walwala ta saka fuskar tata,saidai kallo daya mai martaba yayi mata ya fahimci ainihin halin da take ciki,saiya alaqanta hakan da abinda ya faru jiya,wanda koshi din zuciyarsa ta cika da damuwa,damuwar kada ace gudan jininsa da yake saka ran xai gajeshi,gudan jininsa da duniya duka take kallo take kuma sake tambara sunanshi da matsayinsa ya jawo musu wani abun fada da zai rusa darajarsu da martabarsu,hakan har a ransa yaji tausayin aishan,saboda yasani cewa tana da tsaiwa kan ‘ya’yanta,don haka saiya yawaita sakota a hirar tasu.

     Duk da wajen akwai surutai na tashi,kowa na hirarsa da wanda tasu tafi zuwa daya,amma saratu da adama na ankare,kowacce kuma abinda take saqawa cikin zuciyarta daban.

      Sallamarsa cikin dakin yasa surutan suka dauke cak kamar anyi ruwa an dauke,hakanan numfashin fulani aisha yaso daukewa cak itama,cak ta tsaya tana addu’o’i cikin ranta,addu’o’in Allah ya sanya bashi bane,Allah yasa kunnuwanta ke mata gizo,duk wannan addu’ar da take ta kasa waiwaya ta tabbatarwa idanunta abinda kunnuwanta suke ji din.

      Daidaiku ne suka amsa sallamar tashi,ciki harda me martaba daya zuba mishi idanu cikin zuciyarsa shima yana addu’ar Allah ya sanya abinda ya gani din ya zama ba gaske bane,jikinsa yaji yayi sanyi sanda suka hada idanu da me martaba,kusan yana daha cikin mutanen da suka san halayyarsa tsaf,suke iya gane magana daga idanunsa kafin ya fadeta.

       Kamal shike zaune kan kujerar da a qa’ida nan ne wajen zaman azeez din a duk lokaci irin wannan,yauma bai fasa nufarta,idanunsa cikin na kamal din,kamar yadda kamal din shima ke kallonsa.

       Mai guri yazo dole me tabarma ya nade,hakanan yanaji yana gani ya miqe ya bashi wajen,ya koma kujerar dake kusa da ita,yana qwafa cikin ransa gamida fadin yau dai za’a yita ta qare ko?.

       Cikin girmamawa ya gaida dukkan wanda ya girmeshi a wajen,saura dake qasansa kuma suka gaidashi harda yayyensa mata da tazarar dake tsakaninsu bata da yawa,duk da ransu baison hakan amma dole suka gaidashin,musamman walida da takejin kamar ta ciji harshenta,batasan me yasa suke raina kwanaki arba’in da wani abu data bashi ba,duk tsiya aidai ta girmeshi.

     Baima san me suke ba,don cikin kulawa ya maida hankalinsa ga iyayensa yana tambayarsu lafiyarsu,hakanan kowanne ya danne abinda ke ranshi ya amsa mishi,daga haka cin abincin yaci gaba da gudana,amma saidai hirarrakin dake tashi dazun sun ragu qwarai,hakanan shima dai yana zaune ne kawai ba tare daya dauki komai yaci ba,don dama haka al’adarsa take,ya riga daya saba,hakan zauna din,amma bai fiya cin komai ba har a tashi.

       Dan gyaran murya kamal yayi kamar wanda ya qware bayan sun hada idanu da fulani adama,yasa tissue yadan goge gefan bakinsa badon ya baci ba sannan yace

“Ko yaushe sake zama manyan qasa kuke,sati biyu daya wuce na ganku a dubai a hotel kai da wasu baqi mata,hala abokan kasuwancinka ne kazo kama musu masauki?” Dago kanshi yayi daga amminsa da yake ta nazari tun daxun,ya lura akwai raguwa kuzari da walwala tattare da ita,yana fatan hotunan datace masa ta gani ba daukakar lamarin tayi ta sakashi haka cikin ranta ba,yana addu’ar wannan karon lamarin yazo da sauqi,ta tsaya ta fuskanceshi,komai yazo qarshe.

     Idanunsa masu cike da kwarjini ya xubawa kamal din yana mamakin meya kawo wannan zancan a irin wannan wajen,gaban qannenshi da yayyensa da yaransu,sannan uwa uba gaban mahaifi da mahaifiyarsa,baya ga haka baima fuskanci wadanne mata ya gansu tare ba,hasalima shi ba kasafai ya fiya qulla harkar cinikayya da mace ba komai kudinta ko qasaitarta,saidai ko ta hadashi da ɗa miji ko ɗan uwanta,don shi yace sam bazai iya jure musu ba,baya tolerating nonsenses.

      “Kamal….kaima da tone tone kake,banda abinda mutum kamarshi,da dukiyarsa irin haka kyau da asali ka rabu da ganinsa da wasu…..”

“Gaskiya fa….to ai wayewar kenan,zamanin ne yazo mana da haka” adama ta fada tana tsiyaya kunun acca a cup,tana bada amsa kamar wadda ke magana bilhaqqi.

     Gyaran murya mai martaba yayi,wanda hakan yasa kowa ya shiga taitayinsa,kana ya shigo da wani xancan da kusan ya shafi kowa dake zaune a wajen.

      Tsahon awa guda da rabi sannan ya sallami duk wani wanda yake qasan yariman ne,ma’ana azeez din ya girme mishi,sai sa’anni da wadanda suke shekaru guda ne kadai sukayi saura,kana ya buqaci kowa ya fito zuwa babban falon hutawar dake maqale da dakin cin abincin. A sanyaye fulani ke takawa,daqyar kuma ta samawa kanta mazauni waje daya tana qoqarin sake daidaita kanta da numfashinta.

       Doguwar addu’a mai martaba ya fara jaa,sannan kowa dake wajen ya bashi hankalinsa bayan an shafa,da wanda yasan meya zaunar dasu a wajen,dama wanda bai sani ba,gyaran murya yayi,idanunsa kan azeez sannan ya fara magana.

     Wanda fulani ta dinga jin kamar yana fita da numfashinta ne

“Abdul’azeez….iyakar abinda na sani kuma Allah shine shaida,munyi dukkan wani qoqari daya kamata ace munyi wajen baka tarbiyya,mun baka kulawa da tarbiyyar data dace dakai,mun sadaukar da komai namu saboda rayuwarka ta inganta,na tsaya tsayin daka na nuns maka me kyau da mara kyau,na nuna maka halas da haram,duk da nauyin dimbin al’ummata dake kaina hakan baisa na sarayar da haqqin tarbiyyarku daga wayuna ba,daga kai har ‘yan uwanka…..amma abun mamaki….abun takaici abdul’azeez,sai gashi komai yana shirin tashi a banza…..giyar kudi ta soma dibanka,kanason watsa mana qasa a idanu,abdul’azeez me kakeson zama ko kuma meka zama?” Ya qarashe maganar cikin nuna takaicinsa qarara

“Allah ya baka yawan rai….akwai wasu abubuwan da kana gani ana aikata ba dai dai ba amma kake yin shuru,kusan wannan ba shine farau ba,banson yin magana ne kawai saboda kada ayi maka fassara ta daban…..amma kamal gashinan….tare suka zauna ai a gida daya a mexico,babu abinda bai gaya min ba kan irin lamuran da yaga yana gudana,nace babu ruwanshi ya cire idanunsa yayi tasa sabgar saboda gudun fassarar mutane” hannu sarki abdallah ya daga mata ba tare daya dubu sashen da yake ba,bayason ta qara masa wani ciwon kan wanda ke damunsa,kota dora zuciyarsa bisa bigire na zargi ko zato,sai ya saka hannunsa gefan tuntun daya dora hannun nasa akai,ya ciro hotunan da adaman ta bashi tun ranar ya miqa masa

“Wacece wannan abdul’azeez?”

“Saidai kace tun yaushe suke tare ai” adama wadda tunda aka fara batayi magana ba sai a sannan,saboda sam ba haka taso ba,babban tonon silili taso gaban su waziri da sauran ‘ya’yan fada masu tarin yawa,amma ko a yanzunma indai ya ɓaci idanun mai martabar ai kwalliya ta biya kudin sabulu

“Saboda lamarin ya girgixani sosai….ina ganin hoton saiga kamal ya shigo,shiya shaida min sun jima tare,tun a mexico” ta fada tana sake kaurara maganar donta samu mazauni me kyau a zuciyar maimartaban.

      “Bilkisu ce,kuma matata ce” abdul’azeez ya fada karon farko tunda aka fara maganar,cikin wata kakkurar murya dake cike da dakiya da kuma jarumta,idanunsa da suka juye suka sauya launi saman fuskar adama,wadda bai taba jin ya tsaneta ba irin yau,saboda muraran ya hango zallar qiyayyarsu cikin idanunta,qiyayyar daya jima yana jin amminsa tana fadin ita adaman tana musu.

      Kusan dukkansu babu wanda wuta bata daukewa ba,saboda kalaman da suka fita a bakinsa babu wanda ya tsammaci jinsu,ta sashen abokan hamayya basu so samun amsa irin wannan da wurwuri daga bakinsa ba,inda unda sukaso a fara dashi,daga bisani a zarce da maganar DADIRONSA CE,duk da a yanzun ma basu yarda da kalmar mata daya fada ba,sunfi zaton ya fada ne kawai don ya kare kansa,ya rage girman laifinsa idanun sarki abdallah,shuru ya ratsa falon na wasu sakanni,kafin sautin salatin hajiya fauziyya wanda ya taho da kukan munafurci ya gauraye falon

“La’ilaha illallahu….muhammadurrasulullahi,sallallahu alaihi wa sallam……ke kuwa aisha kina me har dan cikinki xai wannan aika aikar baki sani ba?” Ta fada tana kama haba tana duban fulani aisha,wanda ba komai take fuskanta ba a wajen

“Tabdi,lallai inda ranka kasha kallo…abun har yakai ga auren dadi……”.

      Da sauri maimartaba ya daga mata hannu

“Ya isa!” Ya fada da kaushin murya,wanda ya sanyasu shiga taitayinsu,sai mai martaban ya dubi sauran wadanda ke gurin dukkansu ya basu umarnin tashi su fita,ha rage daga matan nashi sai haj fauziyya.

      A hankali ya kuma sauke idanunsa da suka sauya kala kan azeez

“Kasan abinda bakinka yake fada azeez?” Cikin wata dakiyar ya gyada kanshi yana sadda kan nashi qasa,karon farko da wani irin kunya da nauyin mahaifinsa ya kamashi

“Afuwa nake nema,amma na sani,matatace,kuma har yanzu matatace” kalmarshi ta qarshe ita ta farfado da fulani ta daga nata idanun ta sauke akanshi.

      Wani nannauyan numfashi mai martaba yake saukewa,kana ya maida dubanshi kansu su da sukayi saura

“Ku tashi ku bani waje,abdul’azeez kawai nake da buqatar gani a nan” dukkaninsu ba haka rayukansu suka soba,kada ma hajja fauxiyya da adama suji labari,amma babu wadda keda ikon musa masa,dole suka miqe suna kakkabe jikinsu,wanda fulani saratu ita tayi saura a qarshe,domin dukkan abinnan dake faruwa ganinshi take kamar a majigi,ita kadai tasan iya adadin kudaden data kashe akan azeez din,an riga da an mata albishir din cewa….tabbas babu makawa mace daya azeez din zai aura har qarshen rayuwarsa,macen kuma zata haifa masa diya mace qwaya daya itama,zai rayu bashi da baya,bashi da wani magaji,hakanan rayuwarshi ba zata yauqaqa ba bare tayi tsaho,sai gashi a yanxun ana maganar yana da wata matar daban wadda dukkaninsu basu san da zamanta ba,tabdijan,turqashi!,qaqa qara qaqa,Allah ne kadai yasan yawan kudin data sadaukar ta kuma sarayar,haka ta dinga takawa qafafunta kamar ba zasu iya daukarta ba.

       Fulani aisha ce kawai tayi saura a wajen,saiya dubeta

“Har ke,kema ki bamu waje” kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki ta miqe itama,amma saita kasa tafiya bayan ta fita,ta zauna a falo na farko kafin wannan falon,ita kadai shuru,tana jin kamar ana yamutsa duniyarta,ta riga data sani a yau kam babu wani sauran rufa rufa ko boye boye,lallai yau komai zai bayyana,kamar yadda Allah ya yiwa azeez din kwarjini to ya gada ne daga mahaifinsa,ta tabbatar tunda ya sallamesu yana son jin gaskiyar komai ne daga bakinsa,wanda ta riga ta sani da wahala ya maka irin wannan titsiyen ka iya boye masa gaskiya,saidai ta wani sashen tana ji a zuciyarta tamkar gata ya mata,kamar wani rufin asirine ya mata daya sallamesu gaba daya,wannan tonuwar qatoton asirin ba’a yishi ba gaban adama da saratu.

      “Koda baka tambayeni ba,koda komai bai bayyana gareka ba ayau nayi niyyar shaida maka komai,amma ina mai neman afuwa daga gareka nida ammi akan dukkan abinda zakaji”

“Sanar dani komai,ban buqatar ka boyemin komai” ya fada kansa taaye,cikin ranshi cike da addu’ar Allah ya sanya ba babbar kwaba da zata rusa lahirarsu gaba dayanta suka aikata ba.

      Babu abinda abdul’azeez din ya boye masa,ya bayyana masa dukkan wani abu daya faru a can baya din

“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un,lahula wala quwwata illa billah” shine abinda kawai mai martaba yake iya furtawa,kansa da idanunsa na kallon qasa,shuru ya ratsa falon,kowa da abinda ke kai kawo a ransa.

       Sosai abdul’azeez yakejin wani abu mai nauyi yana ratsashi,kunya da nauyin mahaifin nasa na sake dabaibayeshi,amma wani sashe na zuciyarsa yana jinsa sakayau,wani nauyi da zuciyarsa ta dade tanaji a yau din sai yakejinta fayau,sai yakejinta empty kamar babu wani sauran nauyi daya rage a cikinta,amma kuma wani sashe na zuciyar tashi cike yake da fargaba tashin hankali gami da taraddadin irin hukuncin da zai yanke masa.

       Yasan halinsa sarai,bashi da sauqi ko kadan,hakanan baya qyalewa idan har ka aikata wani abu na ba dai dai ba,komai kuwa kusancin da yake tsakaninka dashi.

       A qalla sun kusa kwashe mintuna a shirin a zaune a haka ba tare da wani canjin yanayi ba,daga bisani ya tsinci muryar mai martaba yana cewa

“Tashi kaje abdul’azeez,tashi ka bani waje” bashi da wani zabi daya wuce ya tashin,don idan ya zauna ma bashi da sauran wani abu da zai fada,ko kuma wani abunda zai iya kare kansa ko ya kawo masa sassauci daga wajwn mai martaba,haka ya miqe yana takawa gami da laluben hanya da idanunsa da sukayi jajur,adam’s apple dinsa ba abinda yake sai motsawa sama da qasa,alamun akwai wani abu daya taba zuciyarsa shima.

      Tana zaune ya giftata amma saita kasa ce masa komai harya wuce,da alamu ma bai lura da zamanta a wajen ba,sai daya bacewa ganinta sannan ta miqe cikin wata iriyar tafiya tana harhada hanya ta koma ciki.

      Tun kafin ta qarasa sallamarta ya daga mata hannu gami da yi mata nuni kan ta fice,bata musa ba ta juya wani abu yana tokare mata wuya.

*_tofa!_*

           *_Bilkeesu_*

       Kai tsaye garinsu abbaa kawai suka wuce a mota bayan jirgi ya saukesu a filin sauka da tashin jiragen sama na malam aminu kano don su fara duba jikin mama.

       Kusan wannan ne zuwansu amatu na farko tun bayan da sukayi wayo,hakan ya sanya sukaita baza ido suna kalle kalle tun a hanya har bacci ya daukesu.

        Babban gidane gidansu abbaa,gidane na masu sukuni wanda ya qunshi mahaifi da mahaifiyarsa,sai kakanninsa wadanda suka haifi babansa,saidai tuni Allah ya yiwa kakanshin rasuwa,sai matarsa da har yanzun take raye suna kuma zaune tare da it,hajiya fatsima,tsohuwa mai ran qarfe,macace mai son jama’a da dattako,hakanan tasu tayi mugun zuwa daya da bilkisu tun ma tana qaramarta,da Allah ya sake hadasun yanzun kuma sai sabon nasu ya dora,don lokaci zuwa lokaci takan kira ta ko sanda tana brasil.

      .

      Sanda suka isa sashen maman abbaa din suka sauka gaba dayansu,macace itama mai kirki faran faran da son jama’a,alamu sun nuna cewa taji jiki sosai,amma ba laifi sauqi yana samuwa.

      A yunwace suka qaraso,hakan ya sanya babu dadewa ma’aikatan gidan suka gabatar musu da abincin,saida sukaci suka qoshi sannan bilkisu ta wauce sashen hajiya fatsima da suke kira da hajiya.

      Da murnarta ta tarbeta tana tsokanarta tamkar dai yadda ta sabawa jikokinta,bilkisun na maida mata cikin dariya ta zauna suka gaisa,sun sha fira sosai kafin ta sanya mai aikinta ta gyara mata daki daya cikin dakunan dake sassanta,wanda su biyune kadai a sassan daga ita sai wata jikarta data dauko take tayata zama.

       Sanda ta miqe ta miqe da niyyar isa dakin hajiya ta fadi maganar data tsaidata

“Har yanzu dai ‘yata babu maganar wani?,ina nan inata kasa kunne naji kin kawomin ango,ko yanzun ma dana ganku,na zaci abunne ya taso” murmushi kawai ta yiwa hajiyan,saboda ko wancan watan abbaa da kanshi ya soma tada maganar,ita kuma a yanzun babu abinda ke daga mata hankali irin zancan aure,da wanne fuska zata kalli dukkan wanda ta aura ta gamsar dashi irin auren da tayi a baya

“A tayamu dai da addu’a” ta bata amsar data fi yawan bayarwa,don ita kanta tasan babu yadda za’ayi dama su zuba mata idanu ko tace zata dawwama a haka,amma kuma yaya tafiyar zata kasance?,me goben zata haifar mata?,wadan nan sune tarin tambayoyin da batasan amsarsu ba.

      Da zancan a ranta ta shiga dakin,wanka ta soma yi saboda huce gajiya,ta aika sassan mama akira su amatu suyi wanka aka shaida mata tuni sunyi,don haka saita qyalesu,ta bayar aka siyo mata sabon layi,don nata tsohon na ainihi yana gidan anty zuhriyya na nan,saisun isa kaisa sannan zata daukoshi ta dora,yanzun kuwa tanason yin waya ne.

      Hannatu ta fara kira ta shaida mata sun iso,nan da kwanaki kadan zasu qaraso kaisa,murna kamar tayi me

“Yanzu kuwa zanje na gayawa baba,nasan zaiyi murna” murmushi kawai bilkisu tayi,tana mamakin sauyawar mahaifin nata haka,abun kamar a mafarki,bata zata zai canza ba sai gashi lokaci guda ya canza din.

      Bayan ta gama da ita saita kira farida qawarta,ta shaida mata itama sun iso lafiya,suka sha hira sanna sukai sallama,tana niyyar ajewa saita tuna da assadiq,tasan yana nan yana tsimayen samun numberta tanan,ta jima bataga mutun mai haqurinshi ba,koda dr adam bai kama qafar assadiq wajen haquri ba,don haka ta laluba ma’ajiyar number dinta tayi kiranshi.

      Sosai yaji dadin kiran nata,har ya kasa jurewa sai daya fadi

“Harna cire tsammani,ashe jan ajinne har haka,nidai a tausayamin don Allah,a jani a hankali” dariya ma ya bata,saita sake sosai ta bashi lakacinta suka sha hira,inda daga bisani ya barta ta huta.

      Kwanansu biyu a ringim qanwar abbaa ta haihu,washegari anty zuhriyya tasa suka shirya gaba daya tace zasu rakata barka.

      Acan suka kusan wuni saboda an dade ba’a hadu ba,yammaci lis suka taho,kan hanyarsu sunata hira yaran na hayaniyarsu,basuyi nisa sosai ba gungun shanun dake tsallake titi suka sanyasu tsaiwa dole,haka suka dinga wucewa kamar ba zasu qare ba

“Kai bafulatin mutum.baidai wayo ba,yanzu wadan nan shanun idan kinji biliyoyin kudinsu zaki mamaki,amma ya gwammace yayita bautata musu ya qare rayuwarshi a jeje,guda bazai iya yankawa yaci ba,ke idan yaga ma tana ciwon ajali zama yake yayita mata kuka harta mace don bazai iya yankata ba” dariya sosai anty zuhriyya ta bawa bilkisu,saidai batayi mamaki ba,don tasan wasu daga halayyarsu na qaunar dukiyarsu,sai kuma dariyar tata ta soma raguwa,saboda tuna hauwa’unta da tayi.

       Duk tsayin shekarun nan yarinyar na maqale a ranta,da burin samota take kwana take kuma tashi,ya zuwa yanzun ta tabbatar ta sake girma ta zama budurwa,fatanta kullum Allah ya hada fuskokinsu da alkhairi,saita buda murfin motar tana cewa

“Na dade bansha madarar shanu ba irin tamu anty,don Allah minti biyar naje naji ko zasu tatsar min,wlh sha’awarta nake”

“Saikin dawo,saiki tfi da kudi,don kinsansu dason kwabo da sisi,bare suga daga mota kika fita yanzu zasu tsawwala miki kudi,Allah yasa su saida miki ma” ni huguma nace lol,fillo bayinmu,badai son kudi ba😝😜😜,murmushi bilkisu tayi tana ficewa daga motar tana tsokanar antyn

“Anya anty ba kishiya fillo xa’a miki ba kuwa?”

“Haba shi yama fara” ta amsa mata tana gyara zaman qaramin yaronta dake saman cinyarta.

      A hankali take dan bin bayan shanun da suka rage,ba jimawa ta soma hango wata ‘yar qaramar rugga,da alamu anan suka yada zango,daga nesa tana hango yadda suke hada hada da shanun ana daure na daurewa,’ya’yan kuma da ba’a dauresu kowa yana daura da uwarshi.

         Daga nesa ta hango budurwar bafulatanar tsaye riqe da qugunta,duk da ta juya mata baya bata iya hango fuskarta amma shanun take kallo da alama,saita qarasa bayanta a hankali ta tsaya sannan tayi sallama.

      Waiwayowa tayi tana amsa sallamar da harshenta daya karye da fulatanci,bilkisu ta sakar mata murmushi tana ganin kamar ta taba ganin fuskar a wani wajen

“Sannu”

“Yauwa sannu” ta amsa mata da alamun kallo rashin sani

“Madara nakeso don Allah ko zan samu?,muna hanya ne zamu wuce” kanta tadan sosa kadan sannan tace

“Kash,gashi kuwa yanzu muka dawo daga kiwo….ba lallai a samu ta arziqi jikinsu,saidai akwai wadda adda ta tatsa dazu,idan kinaso saina kawo miki,ita ta sake tatsar wata”

“Eh inaso hakan”

“Shikenan….zo muje” ta fada tana nufar wata bukka bilkisu ta bita a baya.

       Daga bakin bukkar bilkisu ta tsaya jiranta ita kuma ta dan yaye labulen zanin ta shiga,saidai daga inda bilkisun ke tsahe tana jiyo banbamin fada daga cikin bukkar,wani da fulatanci,fiye da rabinsa kuma da hausa,data saurara saita fahimci ana maganar yin aure ne da wata bataso.

      Muryar da taji ta soma magana cikin kuka kuka hakanan taja hankalinta,ba al’adarta bace,amma saita matsa gaba kadan ko zata iya hango cikin bukkar saboda labulen daya dage ya maqale a jikin karan da aka gina bukkar dashi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page