RAUDHA CHAPTER 7

 RAUDHA CHAPTER 7

Idanuwan ta ne suka lumshe sabida jinin ta dake faman kwaranya a ƙasa, ta faɗi babu alamun numfashi a tare da ita..

+

Sosai hankalin Suhaib yayi ƙololuwan tashi da jin kausasan kalaman ƙanwar sa, kiran sunan ta ya soma yi but babu amsar ta, da sauri ya katse kiran.

       Kamar mintuna biyar sai ga Rayyan ya shigo ɗakin sabida kiran da Suhaib yayi masa, ba don tashin hankalin da abokin sa yake ciki ba babu yanda za’a yi ya zo duba ta

Ganin ta a yashe cikin jini hankalin sa ya tashi matuƙa, domin be taɓa tunanin zata iya yin ma kanta illa ba, dasauri ya ƙarisa gaban ta yana kiran sunan ta, sai dai ganin ba ta numfashi sai yayi saurin ɗaukan ta ya aza ta kan gado, rasa inda zai samo abinda zai ɗaure mata hannayen yayi, da sauri ya cire t.Shirt ɗin jikin sa ya yaga tare da kamo hannun ta ya soma ɗaure wa, shi kansa tamkar yayi kuka sabida tsaban tausayin ta da ya shige sa, domin ba ƙaramin illa tayi wa hannayen ta ba, gaba ɗaya ta yayyanka sai zallan nama ake gani, “Anya yarinyan nan tana da hankali kuwa? Wanene zai yi wa kansa wannan mummunan hukuncin?”

Numfashi kawai yake sauke wa har ya gama ɗaɗɗaure mata hannayen, wayan shi dake ƙara ya ɗauka ya kara a kunne ganin Suhaib ne

Tambayan da Suhaib ɗin kawai ya jefo masa ya kiɗima sa, but sai yayi jarumta wajen tattaro nutsuwar sa tare da dai-dai ta muryan sa yace, “Dude ka kwantar da hankalin ka babu abinda ya same ta, ka ganta nan a gaba na wayan ta ta rotsa a ƙasa, kuma na ba ta nawa tayi magana da kai taƙi, kasan ƙanwar ta ka akwai taurin kai”.

Shiru yayi yana sauraron Suhaib ɗin

Murmushi ya saki yace, “baka fi Ni son ta ba Dude, ƙanwar ka ƙanwata ce, bazan ɗau matakin da zai mata illa ba, da yardan Allah zan yi iya ƙoƙarina wajen nuna wa RAUDHA hanyar Gaskiya, zan kula da ita sosai”.

Numfashi yaja idanun sa a kan kyakykyawar fuskar RAUDHA, sai da suka yi kamar two minutes suna wayan kafin ya tsinke, Numban wani abokin sa ya lalubo ya kira, bayan ya ɗauka sun gaisa ya buƙaci ya samo masa doctor, daga nan katse kiran yayi ya saka wayan a aljihun wandon sa, gefen gadon ya zauna yana tsira mata idanu tamkar zai cinye ta, tunani ne kawai fal a ransa duk zuciyar sa ta cinkushe, fesar da numfashi daga bakin sa kawai yake faman yi, har sanda abokin sa ya kira sa ya sanar masa ya kawo doctor ɗin, tashi yayi ya fita haraban gidan, acan suka haɗu suka gaisa sannan suka shigo da doctor ɗin, shi kuma abokin ya tafi don a tunanin sa Ray ɗin ne babu lafiya duk da kuwa ya faɗa masa ba shi bane, amma kuma sai yaƙi yarda sai da yazo ya gani da idanun sa.

     Da suka shiga ɗakin likitan ya soma duba ta

Shi kuma Ray zama yayi kan stool ɗin dressing mirror bayan da ya ɗauko wayan ta dake yashe a ƙasa, danne-danne ya soma yi aciki na ɗan wani lokaci kafin ya ajiye, ya mayar da hankalin sa kan aikin likita

Time ɗin ma likitan har ya gama yana naɗe mata hannayen da bandage, bayan ya gama ya juyo ya fuskanci Ray yana masa bayani ta yanda za’a kula da hannun, sallama suka yi sannan ya fice

Rayyan tashi yayi ya iso bakin gadon ya tsaya yana kallon ta, ya daɗe ahaka yana faman tunani idanun sa akanta kafin yaja dogon numfashi ya juya ya fice, ɗakin sa ya koma ya kwanta yaci gaba da tunanin sa, sai da aka kira sallan magriba kafin ya tashi ya ɗauro alwala ya fice.

      Sai wajen ƙarfe 08:30pm kafin RAUDHA ta farka, yanda taji hannun ta na mata zugi babu shiri ta runtse idanuwan ta tana hawaye, abubuwan da suka faru daga jiya zuwa yau suke ta kai kawo cikin zuciyarta, nan da nan hawayen fuskarta suka ci gaba da ɓulɓulowa tamkar an kunna famfo, buɗe idon tayi ta ɗago hannayen ta tana kallo tana tsiyayar hawaye, ta jima ahaka kafin ta tashi zaune, ahankali ta sauko tayi cikin Toilet daƙyar, so take yi tayi fitsari but hannun ta gaba ɗaya ciwo ne, daƙyar take iya ma sarrafa hannun ta, haka dai da dabara tayi fitsarin tana kuka sannan ta fito, yunwan dake cin ta yasa ta nufi hanyan fita.

      Parlour’n babu kowa sai hasken lantarki, kan dainning ta nufa ta zauna tana tsira wa coololin wajen kumburarrun idanunta, sai kawai ta fashe da kuka tana kifa kanta saman table ɗin ta soma rerawa.

      Rayyan da tun jiyo motsin ƙofan ta yafito yabi bayan ta, sai dai daga ƙarshen benen ya tsaya yana bin ta da ido, sosai ta ba shi tausayi don ya san babu yanda za’a yi ta iya cin abinci, ahankali ya soma takawa yanufi wajen dainning ɗin, har ya ja kujera nesa da ita ya zauna bata sani ba, sai da ya soma buɗe coolarn ya ɗauki Plate kafin tajiyo motsi ta ɗago tana kallon sa

Idanun ta kawai ta saka masa tana sake jin tsanar sa na ƙara kumbura a zuciyarta, bata motsa ba har sanda ya nuna mata abincin da ya zuba “wai taci”.

Ƙanƙance idanuwan ta tayi cikin baƙin ciki da tsananin fushi tace, “I hate youuuuuuuu so much”.

Tamiƙe da gudu tayi hanyan Steps ta wuce ɗakin ta

     Da kallo ya bi ta, kafin ya taɓe baki yajuya kai ya soma cin abincin, a ransa yana tunanin wace iriyan yarinya ce wannan? Ba ya tunanin ma ƙwaƙwalwan ta ƙalau ne.

      Tana shiga ɗaki tayi kan gadon ta tazauna gefen gadon ta soma rusa kuka, tana yi tana saka damtsen hannun ta tana share hawayen ta, sabida ko ganin ɗakin ba ta yi yanda hawayen ta ke kwaranya, ta jima tana zaune tana kukan kafin tayi shiru tana sauke ajiyan zuciya, tsaban kuka har datse harshe take yi sabida sauke ajiyan zuciya da take yi akai-akai

Miƙewa tayi ta isa bakin Fridge, ahankali ta saka hannu ta buɗe taciro Robbern coke guda biyu ta ajiye a ƙasa, rufewa tayi takoma wajen kayan zaƙin ta, anan ta samo cake da ya rage guda ɗaya ta dawo gaban Fridge ɗin ta zauna, haka ta dinga kora lemun tana haɗawa da cake ɗin daƙyar, har ta cinye

Sai da ta samu ruwa cikin Fridge ɗin ta kuskure bakin ta ta zubar a wajen kafin ta tashi ta haye gado, nan wani sabbin hawayen suka soma sintiri a face ɗin ta, sosai take jin azaban hannun ta, ga kuma jikin ta dake faman mata ciwo saboda haukan da tayi jiya, tana buƙatar wanka amma babu hali, ƙiri-ƙiri ta kasa yin barci a wannan daren, kuka kawai ta dinga yi sai da kanta ya ɗau zuuu yana mata ciwo sosai kafin ta shafa wa kanta lafiya, tuni zazzaɓi ya rufe ta, har ta miƙe da ninyan kwaso kayan mayen ta ta afa ko zata samu salama, sai ta tuna babu ko ɗaya, haka ta koma takwanta tana sake jin tsanar Ray na sake shigan ta, tasan babu wanda ya isa ya kwashe mata sai shi.

      Idanunta da suke a kumbure suka ƙanƙance ta aza a kan wayan ta dake faman ƙarar shigowan message a inda Ray ya ajiye, lumshe idanun tayi tana jin zafin zazzaɓin har cikin idanun ta, bata sake motsa wa ba har barci ya ɗauke ta daƙyar.

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐

        Washe gari ƙarfe 08:30am. Ray ya fito cikin shirin sa na sojoji, ɗakin RAUDHA yabi da kallo kamar ya shiga sai kuma ya sauka abun sa, acan Parlour ya haɗu da Ester tana gyara, ya kira ta ya bata Numban sa ya umarce ta “ta kula da RAUDHA, idan akwai matsala sai ta kira sa”.

Cikin girmamawa ta amsa masa

Sannan ya taka ya wuce.

        Sai da ta gama gyaran kafin ta wuce ɗakin RAUDHA, time ɗin tuni ta tashi daga barcin, duk da kuwa jikin ta babu wani zazzaɓi yanzu, but zafin jikin ya ƙi sauka, sai kuma kanta da har yanzu yake mata ciwo, tana kwance har a lokacin

Zuwan Ester sai taji daɗin ganin ta, nan ta nuna mata inda zata ɗauko mata magani tasha

Daƙyar ma Ester ɗin ta iya jin abinda ta faɗa mata, domin ko kaɗan muryan ta ba ya fita, gaba ɗaya ya disashe sai kaɗan

Ester fita tayi ta haɗo mata tea me kauri kamar yanda ta buƙata, sannan ta kawo mata, ta koma tasoma gyaran ɗakin da yayi kaca-kaca, a ranta tana mamakin abinda ya faru ɗakin ya hargitse haka, gashi can ma Parlour ta ga an tarwatsa Centre table, sai dai babu halin tambayar tunda bata ga fuska wajen wanda zata yi mata tambayan ba, aikin ta taci gaba da yi, sai da ta kwashe Glassess ɗin ta fitar dashi sannan ta soma share wa.

        Koda RAUDHA ta gama shan tea ɗin sai ta kora da magani, ta miƙe ahankali tanufi Toilet, wanke bakin ta tayi sannan tayi buƙatar ta; ta fito tanufi kan sofa ta zauna, don alokacin Ester na gyaran gadon ne

Wayan ta tasaka Ester ta miƙo mata, ta’amsa ta riƙe da yatsun ta, don su ne kaɗai zata iya sarrafa wa, ta soma latsawa tana neman Numban yayan ta, duk da ta ga messages but bata duba ba, sai dai numban nasa ba ya shiga saboda network, sai ta mayar da akalan kiran ga Rash, ringing biyu ta ɗauka, magana RAUDHAN ta soma yi sai dai Rash ba ta jin ta, dole ta katse tashiga message inbox tasoma yin mata typing:

         ”'”Rash Ina buƙatar ki zo gidan mu yanzu ina neman ki, ki taho da mota please”.”’

Babu jimawa itama ta dawo mata da reply ɗin ta:

_”Ok! Me ya faru ne wai Babe? Mun kira wayan ki duk bamu samu ba, mun biyo sawu kuma gidan a rufe, wanene mutumin nan da ya ɗauke ki a Club? Gaba ɗaya mun shiga tashin hankali wallahi, kuma sai ga shi baki zo school ba”._

Nan RAUDHA ta soma faɗa mata abinda ke faruwa, sun jima suna chart ɗin, suna ƙulla yanda zasu zo su ɗauki RAUDHA tabar gidan gaba ɗaya, daga nan ta koma can da zama.

        Har zata fita daga text message ɗin kuma; sai ta tsaya duba message ɗin da takula an yi mata har sau biyu, da baƙon number ne, koda ta buɗe na farkon an rubuta:

     _”Aslm alaikum ya ke wannan kyakykyawa, Barka da arziƙin kasancewar ki cikin ƙoshin lafiya da kuma samun asalin nasarar cafke zuciyar da bata san komi ba face soyayyar ki ya ke me cikon burina, ɗumbin gaisuwa me cike da fatan alheri a gare ki, tabbas na daɗe ina kallon taurarin samaniya yayinda naga wacce tafi ko wacce haske, sai na ga ba kowa bace nake gani sai ke, sannan na daɗe ina neman wata kalma wadda babu wanda ya santa, sai gashi a lokacin da na same ki sai na samu wannan kalman, RAUDHA ke ta daban ce, kuma ke kyakkyawa ce, kin zarce sauran mata. Haƙiƙa so gamon jini ne, kuma ya kama Ni, don a yanzu ina faɗa miki yarigada ya zama jinin jikina, ƙaunar ki RAUDHA ta rigada tayi min dabaibayin da ba na tunanin zan iya kufce wa face na mallake ki ba, ina son ki RAUDHA, Ina matuƙar ƙaunar ki, na zaɓi wannan hanyan ne don sanar dake abinda ke cikin zuciyata, domin shi ne kaɗai hanya me sauƙi da zan iya fahimtar dake abinda ke raina. Ki kasance cikin farin ciki har abada pretty”._

      Ɗayan ta sake buɗe wa ta soma karanta wa

_”Ba zan iya rayuwa idan ba tare da ke ba, a mafarki da kuma a cikin soyayya babu abinda ba zai iya faruwa ba. Ina son ki sosai hakan ya sa nake ji tamkar ba zan iya rayuwa idan ba tare da ke ba. Ba na fatan rasa ki a rayuwa ta, domin kuwa a duk kan lokacin da na rasa ki, na tabbatar da rayuwata zata shiga garari, ina son ki kuma ba zan taɓa sanja wa ahakan ba, ke ce murmushi na, domin da akwai miliyoyin furanni a cikin lambun masoya a wannan duniya. Da ace zan tsunko ko wanne fure na baki shi a hannun ki, hakan bai isa ya bayyanar da adadin yanda nake son ki ba, pretty ke ce murmushi na! kuma ke ce farin cikina! ina matuƙar ƙaunar ki da dukan zuciyata! ki bani dama don Allah, dama ɗaya tak”._

     Shiru RAUDHA tayi tana tunanin wanda ya aiko mata da wannan text ɗin, sai kuma taja tsaki tana jin ranta na mugun ɓaci, domin a rayuwa babu abinda ta tsana sama da soyayya, ko kaɗan kalaman nan basu burge ta ba, sai ma ɓacin rai da jin haushin wanda ya turo ya saka ta

Ajiye wayan tayi ta kwanta tana me lumshe idanuwan ta.

Bata fi mintuna biyu da ajiye wayan ba, kiran Suhaib ya shigo, tashi zaune tayi tana peacking ta kara a kunne, sai dai taƙi yin magana sai ta fashe mishi da kuka+

Suhaib ya rikice don ya ɗauka wani abun ne, ya soma rarrashin ta cike da sanyin murya, don a yanzu sosai ya shiga damuwa da yanayin da ƙanwar ta sa take ciki tun tahowar su, ko yaushe kuka

“Baby menene? ki faɗa min abinda ke damun ki kar ki saka zuciyata ta buga, kullum a cikin damuwa nake saboda halin da kike ciki”.

Cikin kukan tace, “Yaya ni bazan zauna da mutumin nan ba, don Allah ka dawo ka tafi dani, ba na ƙaunar sa, na matuƙar tsanar sa fiye da mutuwa, wlh yaya sai na kashe sa duk sanda na zama soja, da bindiga na zan harbe sa”.

“Baby soja kuma? Taya zaki zama soja? Please baby ki dena kiyi haƙuri bazai sake miki wani abu ba, baki fahimci halin Abokina bane, amma shi ba mugu bane..”

Kuka ta saka mishi, dole yayi shiru ya hau rarrashin ta kamar zai yi mata kuka, sosai yake jin kukan nata har cikin ransa, ya rasa ya zai yi, don duk yanda ya so ya rarrashi RAUDHA ta ƙi, daga ƙarshe ma kashe wayan ta tayi, koda ya sake kira sai taƙi ɗauka, haka yayi ta kira but taƙi peacking, dole ya hakura ba don ya so ba

Ita kuma kukan ta kawai taci gaba da yi ko kallon wayan bata sake yi ba, sai can daga baya ta sake jin wani kiran, har zata share sai kuma ta tuna ko Rash ne, ilai kuwa ita ɗin ce, tayi saurin ɗaukan wayan tana kara wa a kunne bayan tayi peacking

“Hello kin zo ne?”

Daga can Rash tace, “wlh Baby babu yanda za’a yi mu shiga gidan, domin sojoji ne kewaye a gidan, kuma sun hana Ni shigowa duk da nayi musu bayanin wajen ki muka zo, sun ce ogan su yace, “kar su bar kowa idan wajen ki zai zo…”

Ba ta ma tsaya jin ƙarisan bayanin ba tayi jifa da wayan ta hau rusa kuka, azuciye ta miƙe tayi hanyan ƙofa ta fice, Parlour ta nufa sai dai babu kowa, sai ta koma saman ta nufi ɗakin Ray, tura ƙofan tayi da karfi, sai dai babu shi sai sassanyan ƙamshin sa da ya shige mata hanci, wurwurga idanu ta soma yi cikin ɗakin kafin ta ƙarisa ciki tana jan majina, tsayawa tayi tsakiyar ɗakin, har ta juya zata fice sai kuma ta dawo ta soma bincike ta inda zata gano kayan mayen ta da ya kwashe, but bata samu ba, har Fridge ta duba babu a ciki, sai da tayi masa baja-baja da kaya sannan ta fice, ko bi takan gyarawa bata yi ba, ɗakin ta ta koma ta faɗa kan gado tana lumshe idanun ta, tunanin kawai abinda ya kamata tayi take yi, zuciyarta sosai take ta tafarfasa tamkar zata fito, idanuwan ta gaba ɗaya sun juje sun yi jazur kamar garwashin wuta, sai kawai ta soma wani irin kuka kamar na kenwa, ta silalo ƙasa tana fizge-fizge tana tafiyan maciji kamar zata shige ƙasan kujera.

     A wannan time ɗin Rayyan ya shigo gidan, sanda ya iso saman yaji kamar ana dariya da koke-koken jarirai cikin ɗakin ta, sai ya tsaya yana kasa kunne, abun sai ƙara ƙaruwa yake yi hakan yasa ya taka zuwa bakin ƙofan ya buɗe ya shiga.

      Ɗakin dunɗum babu haske duk da kuwa ba dare bane, domin time ɗin ƙarfe 02:50pm ne, but abun mamaki duhu sosai, duk da kuwa ga windows har biyu haske na shigowa, saurin saka hannu yayi ya kunna fitilan ɗakin tunda akwai wuta, nan ɗakin ya gauraye da haske, ɗakin kuma ya koma yanda yake da hasken shi tarwai

Idanun sa ne suka sauka kan RAUDHA dake yashe a ƙasa ta dunƙule waje ɗaya, gashin ta duk ya barbaje ya rufe mata fuska, tsayawa yayi kawai yana kallon ta da tsantsan mamakin ganin ta a haka, sai da ya jima yana tunani a ransa kafin kuma ya taka zuwa wajen ta yana kiran sunan ta

Sai dai ko motsi bata yi ba

Ahankali ya duƙa gaban ta ya saka hannu ya yaye gashin da ya rufe mata fuska, idanuwan ta a rufe suke, sai numfashi da take sauke wa ahankali alamun barci take yi, kawai tsayawa yayi yana kallon kyakykyawar fuskar ta, zuciyar sa cike da tunanin “anya yarinyan nan ba ta da aljanu? Ko kuma shaye-shayen da take yi ya taɓa mata ƙwaƙwalwa”.

Sai a lokacin idanun sa suka sauka kan hannayen ta da duk bandage ɗin ya cire na wani wajen, duk da ciwon be wani warke ba amma yayi sauƙi kasancewar ya rigada ya bushe sabida maganin da aka saka mata

Shiru yayi na wani lokaci; kafin ya tashi ya ɗauke ta zuwa kan gadon, shimfiɗe ta yayi ya juya ya fice ya shiga ɗakin sa, wanka ya soma yi sannan ya fita zuwa ƙasa ya zauna cin abinci, har ya gama ya dawo ɗakin RAUDHA tana nan a yanda ya aijiye ta, ko juyawa ba ta yi, ba don numfashin da take fitarwa ba ba ya tsammanin tana da rai, zama kawai yayi a ɗakin ya tasa ta gaba yana ta kallo, zuciyar sa cike tab da wani irin nishaɗi, sosai ya shagaltu da kallon halittar da duk duniya babu abinda yafi masa a cikin ransa, tabbas tun a kallon farko da ya fara haɗuwa da ita, zuciyar sa ta hautsine da ƙaunar ta, sai dai kuma be taɓa tunanin zai sake ganin ta ba a rayuwan sa, a ranan da ya haɗu da ita anan gidan, ya kuma tabbatar da ƙanwar Suhaib ne, tabbas ranan ya kasa barci, sabida tsantsan farin ciki da ya cika sa, abun mamaki sai gashi ita ɗin ba yanda ya ɗauke ta ba, domin a tunanin sa ba ma ƙabilan su ɗaya ba, duk da rashin tarbiyyar ta be sa ya ji soyayyar ta ya fita a ransa ba, sai ma ƙara ƙaruwa da yake yi, be taɓa soyyayya ba sai akanta, tunda ya ɗaura idon sa a kanta be sake samun sukunin zuciya ba, be san kuma ya zai yi ya bayyana mata ƙaunar sa a gare ta ba.

Ajiyan zuciya ya sauke jin ana kiran sallah, ya miƙe ya fice.

      Rayyan be dawo gidan ba sai bayan isha’i, amma koda ya sake shigowa ɗakin RAUDHA, abun mamaki tana nan dai a yanda take ɗin sai barcin ta take yi, yanzu kuma sosai ya tsorata da wannan barcin na ta, zuwa yayi gaban gadon ya soma tashin ta, but ko motsi bata yi ba, duk yanda ya so ya tashe ta amma taƙi motsa wa, dole ya fita a ɗakin zuciyar sa na ayyana masa tabbas babu lafiya.

      Be daɗe ba suka dawo da doctor, shi ya tabbatar masa da lafiyan ta ƙalau, barci ne kawai take yi, sannan ya sake wanke mata ciwon ya saka mata magani ya rufe, sallama yayi masa ya tafi, sai shima ya fice ya koma ɗakin sa, a taƙaice dai haka Rayyan ya kwana da tunanin RAUDHA a ransa, ko kaɗan zuciyar sa ta kasa ba shi damar da zai sukuni, daƙyar ya iya samun barci gab da asuba, wanda sai da ya makara sallah ma, ƙarfe 07:30am ya tashi yayi sallan ya sake komawa barci, zuwa ƙarfe 09:00am. Ya gama shiryawa ya fito, be samu damar shiga ɗakin ta ba yabar gidan.

          🌐🌐🌐

       Zuwa biyu ta farka daga barcin ta, ta daɗe kafin ta tashi daga kan gadon, sai faman juya kai take yi tana faman yamutsa fuska, sakamakon ciwo da kan nata ke yi, hannayen ta tabi da kallo fuska babu fara’a, sai kuma ta tashi ta shiga Toilet, haka nan ta lallaɓa yau tayi wanka tafito ta sauya kaya, riga da wando ƙanana ta saka ta ɗau wayan ta ta haye kan gado, duba wa ta soma yi, nan ta ga kiran yayan ta har ten missed calls, sannan na Ramcy, sai Zen da Rash, sai kuma texs message guda biyu na baƙuwar Numban jiya, duk ka babu wanda tabi kiran, haka ma text ɗin babu wanda ta duba ta ajiye wayan, rufe idanunta tayi; tayi shiru abun ta

      Koda Ester ta shigo ta gaishe ta, bata amsa mata ba, ko motsa wa ma bata yi ba, haka Ester tayi aikin ta tafice

A ranan haka RAUDHA ta wuni a saman gadon nan ko sauka ba ta yi, sai idan tana buƙatar zuwa Toilet, shima Kuku har ɗakin ya rinƙa biyo ta da abincin ta, yanda ya ajiye haka yake zuwa ya ɗauka, sai na dare ne ma da ya kawo yaga ta taɓa kaɗan.

     Da Rayyan ya dawo, ɗakin ta ya soma wuce wa don duba lafiyan ta, koda ya shiga da sallama

Tana kan gadon ta kwance, kallo ɗaya tayi masa ta maida idanun ta ta rufe, batare da ta amsa sallaman nasa ba, tunda bata saba yin hakan ba

Iso wa yayi gaban gadon ya tsaya, be yi magana ba illa kallon ta da yake yi, tsawon mintuna biyar kafin ya juya ya fice zuwa ɗakin sa.

       Yana fita ta buɗe idanun ta tana mayar dasu ta lumshe, zuciyarta na sake cinkushe wa sabida ƙamshin turaren sa dake shiga hancin ta, tamkar ta mutu haka take jin ta sabida tsantsan tsanar da take masa, ko kaɗan ba ta ƙaunar sake tozali dashi a rayuwan ta.

     Rayyan da ya shiga ɗakin sa, wanka ya soma yi ya saka riga da wando na shan iska, sannan ya zauna a gefen gadon sa yana tunani a ransa, ya jima ahaka kafin ya ɗauki wayan sa dake gefen sa ya soma typing akan Numban RAUDHA da yayi mata serving da PRETTY:

        *”DA AKWAI WASU LOKUTA DA NAKE ZUBAR DA HAWAYE SABODA KE, NA SAN ZAKI CE SABODA ME? DA AKWAI WANI LOKACI DA YAKE ZUWA NA JI TAMKAR NAYI FIKA-FIKAI NA TASHI SAMA, KIN KUWA SAN DUK SABIDA MENE NE? SABIDA MOTSAWAR SON KI A CIKIN ZUCIYA TA! DA TSINTAR KAINA A CIKIN MATSANANCIN SHAUƘI A DUK KAN LOKACIN DA NAJI MURYAN KI KO NA TUNA DAKE, KAMAR YANDA KO WACCE BISHIYA KANYI RASSA A SAMA, KUMA TAYI SAIWA A ƘASA, HAKA SON KI YA MAMAYE DUK KAN JIKI NA, IDAN NA KALLE KI SAI NAYI FARIN CIKI, IDAN NAJI TATTAUSAN MURYAN KI, SAI NISHAƊI DA WALWALA TARE DA ANNASHUWA GAMI DA FARIN CIKI SU MAMAYE ZUCIYA TA. I love U so much pretty”.*

     Sending yayi, sannan ya koma ya kwanta saman gadon.

            🌐🌐🌐

     Shigowar message daga wayan ta ne ya sa tasake buɗe lumsassun idanuwan ta da suka soma sauya wa zuwa ja, hannu ta saka ta ɗauki wayan tana kallo, tamkar bata taɓa ganin wayan ba; ko tana neman wani abun aciki haka ta koma, sai kuma daga baya ta buɗe ta soma karanta text ɗin, sai da ta gama sannan ta buɗe sauran biyun da aka yi mata tun jiya, ɗaya na ƙunshe da:

_”Sama cike take da taurari masu hasken da ke haske duniya a cikin ko wanne dare, amma haske mafi haskaka fuska da yaye duhun zuciya, na ganshi ne a cikin idanuwan ki. Ki kula min da kanki. Ina son ki Pretty”._

   Ɗayan kuma na ƙunshe da saƙon:

_”SO gamon jini ne, haƙiƙa son ki ya zamo jinin jiki na! Domin na kan raba dare ina mai roƙon Allah don neman biyan Buƙata, ko kin san ke ce Abu na farko da nake roƙon na samu?”_

Ajiye wayan tayi kawai batare da tayi wani tunani ba, har ta ɗaura hannun ta saman goshin ta ta mayar da idanun ta ta rufe su, sai ta sake jiyo wani saƙon ya shigo, kamar ta share sai kuma taji tana sha’awar gani, ta yiwu me turo mata waɗannan kalaman ne da ba gane su take yi ba

Hannu ta saka ta ɗauki wayan ta buɗe ta soma karanta wa:

”'”Soyayya abar girmamawa da tarairaya ce, ko kusa kada kiyi tunanin cewa soyayya ƙarya ce, sam ba ƙarya bace, domin tana da asali da tushe ko nasaba mai girma daga mahaliccin kowa da komi. Kiyi tunani Pretty”.”’

     Ta maimaita wannan ɗin a ƙalla sau uku, so kawai take yi tayi tunani irin na masu hankali but ta gaza, sai ta ajiye wayan ta sake gyara kwanciyar ta, sai dai wannan karon bata rufe idanun ba, ta tsira wa jikin bango idanu tana me afka wa tunani akan sanin “wai shin menene so? Sannan wanene wanda yake turo mata saƙon nan? Sannan me yake nufi dasu ne?” But ko kaɗan zuciyar ta bata taɓa mata tunanin ta kira Numban ba, ko kuma taji wanene, domin bata buƙatar hakan.

      Ahaka har barci ya ɗauke ta bata sani ba.

 Yanzu RAUDHA gaba ɗaya ta dena fitowa ko ƙofar ɗakin ta ne, kullum tana ɗaki komi na ta a ɗaki take yin sa, kuma tayi hakan ne duk sabida nesan ta kanta daga haɗuwa da Rayyan, duk da some time yana shigowa har ɗakin ta ya duba ta, amma ko kallo be ishe ta ba, duk maganar da zai yi baza ta kula sa ba har ya fice, sosai ta tsane sa fiye da komi da kowa dake duniya, musamman yanda Rash ta kira ta; ta sanar mata sun soma Exams, tayi yunƙurin sake fita but bata samu dama ba, wannan dalilin ne yasa ta sake tsanar sa a ranta, duk son ta da karatu gashi tana ji tana gani wani banza ya hana ta fita, a ranan kwana tayi kuka, kuma ta rufe ƙofar ta har tsawon kwanaki taƙi ta buɗe, duk bugun da Rayyan zai zo yayi ma ƙofan tana ji, amma ba ta buɗe wa kuma ba ta kula sa, haka zai gaji yabar wajen, kuma be daina tura mata saƙo ba na kalaman soyayya, tun tana ɓata time ɗin ta tana karanta wa har ta dena+

Yanzu ta kai ko sallah ma da take yi ta dena da daɗe wa, tuni ma ta manta cewa ana sallah, idan tana jin ƙunci sai ta kunna music a ɗakin ta ƙure ƙara, hakan ke saka take samun nishaɗi a zuciyarta, sabida yanzu ko yayan ta ta dena ɗaukar wayan sa har yanzu fushi take yi dashi.

     Ahaka rayuwan taci gaba, har yanzu wajen sati biyu kenan da tafiyan su Suhaib, an samu an yi wa Haneep aiki a ciwon dake cikin sa, tun sanda suka isa can da kwana biyu, yanzu haka zuwa nan da Three weeks ake son sallaman su, kuma alhmadulillah ciwon da yake fama dashi shima ana neman magani, kuma suna ganin sauƙi ba kamar da ba.

      Sanda suka cika kwanakin dawowar su, ana gobe ya kira Rayyan ya sanar masa, sai dai a time ɗin ma Rayyan kwana biyu kenan ba ya nan, a ranan shima zai dawo.

      Lokacin da ya dawo wajen ƙarfe 10:00pm. Ne na dare, ya so ya shiga yayi wa RAUDHA albishir ɗin dawowar Yayan ta, sai kuma yaga hakan be dace ba tunda dare yayi, sai ya bari sai gobe.

      Ɗakin sa ya wuce, wanka ya soma yi da ya shiga, ya saka jallabiya fara ya hau gabatar da sallan isha’i da be yi ba.

          🌐🌐🌐

      RAUDHA a time ɗin tana tsaka da barci, sai ta hau mafarkin da ta saba yi a kwanakin baya, ga ta a ƙaton baƙin jeji da manya-manyan halittu masu ban tsoro, wannan dai macijin da ya saba bin ta yau ma shi yabi yo ta, su kuma sauran halittun suna sakin wani irin gurnani da dariya me tsananin sautin da ya mamaye ilahirin jejin..

A dai-dai nan ta farka tana kurma ihu, gaba ɗaya komi dake faruwa a mafarkin sai da ya dawo mata ƙwaƙwalwa, hakan ya haddasa mata mugun tsoro har take ganin tamkar ga macijin ya biyo ta a gaske, dama ga ɗakin yayi duhu tana jin ihu, ai aguje ta dira daga kan gadon tayi hanyan waje cikin firgice wa.

         A haukace ta burma ɗakin Rayyan, sai ganin ta kawai yayi ta faɗo kansa tana wani irin kuka, hankalin ta ba ya jikin ta, kawai faɗi take yi, “ya tamaike ta za su cinye ta, ga sunan sun biyo ta”.

Nan hankalin Rayyan yayi mugun tashi, ya riƙo ta da take ƙoƙarin shigewa jikin sa, magana ya so ma mata yana faɗin, “tayi shiru babu abinda ya biyo ta”. Amma ina ko jin sa ba ta yi, duk ta gama rikicewa jikin ta sai faman rawa yake yi

Hakan da ya gani sai ya saka ta a jikin sa ya rungume ta, ya soma tofa mata addu’a, don tunanin sa ya bashi mafarki tayi ta tsorata ainun

Ya daɗe yana mata addu’a bata dena kuka da iface-ifacen ba, daƙyar ya samu nutsuwar ta ta soma dawowa jikin ta

Duk da ta gane a inda take yanzu, but ta gaza motsawa bare ta fito daga jikin sa, illa sake shige masa da take yi tana ma tsar hawaye, har yanzu tsoron be bar ta ba

Numfashi Rayyan yaja kafin ya soma ƙoƙarin raba ta da jikin sa yana faɗin, “RAUDHA tashi ki je ɗaki kinji? Babu abinda zai same ki mafarki kika yi”.

Memakon haka sai ma fashe masa da kuka da tayi, tana sake shigewa jikin sa akan baza ta je ba

Shiru kawai yayi yana tunanin wannan sangarta irin na yarinyan nan, ga dai ta da shekaru, amma kuma babu hankali, har yanzu jin ta take yi tamkar yarinya, yaran ma sun fi ta sanin abinda ya kamata, shi fa gaskiya bazai iya barin ta ajikin sa ba, haka kawai taja masa matsala

Hannu ya saka ya finciko ta ajikin sa yana miƙe wa tsaye

Ai itama zumbur ta miƙe ta nufe sa tana sakin kuka me ban tausayi, don sosai ta tsora ta da abinda tagani a mafarki yau, gani take yi duk idan ta jirga zata sake ganin mugayen halittun nan ne, ji take yi tamkar macijin nan na biye da ita, idan ta motsa zai cinye ta

Ganin zata sake tabaibaye sa, sai yayi saurin matsawa yana cewa, “RAUDHA ki nutsu mana, ba kya ganin Ni ba muharramin ki bane? Yayan ki kaɗai kike da damar mishi haka amma ban da Ni”.

Kuka ta sake fashe mishi dashi tana sake bin shi, ta shige jikin sa, don ko kaɗan bata ma fahimci me yake nufi ba

Guntun tsaki ya ja yana bin ta da kallo, duk da yana tsananin jin tausayin ta amma ba zai yarda da wannan naniƙen ba, iska ya fesar daga bakin sa kafin ya kalle ta yace, “mu je na raka ki ɗakin ki to”.

Maƙe kafaɗa tayi ita baza ta je ba

“To yanzu ya kike so in Yi dake? Kin san dai bazan zauna ki naniƙe Ni ba ko?”

Idanu ta zuba mishi, sai shima ya tsaya yana kallon ta, sosai ya shagaltu da kallon ta, yayinda itama ta kasa ɗauke idanun ta a kansa

Tsawon mintuna kafin ita ta lumshe idanuwan ta, tana sake ƙanƙame sa a jikin sa

Ɓoyayyen numfashi ya sauke kafin yace, “to je ki kwanta a nawa gadon ko?”

Buɗe idanu tayi ta sake ɗaura su a kansa, sai kuma ta maƙe kafaɗa

“To ya kike so in Yi dake, ahaka kike so mu kwana?”

Shiru tayi masa tana sake gyara ƙafafuwan ta sabida gajiyan tsayuwa

Tafiya ya soma yi zuwa bakin gadon, ya janye ta daga jikin sa ya zaunar da ita, sannan ya juya da zummar rufe ƙofa da tabar sa a hangame, sai jin ta yayi ta sake ƙanƙame sa ta baya ta fasa mishi kuka, jikin ta na matuƙar rawa

“Wayyo Allana! na shiga uku”. Ya faɗa a ransa yana runtse idanu

Ko motsi ya gaza yi illa sauraron kukan ta da yake yi, daƙyar ya iya jarumtar jan ƙafafuwan sa zuwa bakin ƙofan ya rufe suka sake dawowa, kan gadon ya nufa ya sake janye ta ya zaunar da ita sannan shima ya zauna, ganin zata sake shige masa jiki yace, “kee kina da hankali kuwa? Ko kina son in cutar dake ne? Kin ishe Ni fa”.

Hakan be sa RAUDHA ta dakata daga abinda tayi ninya ba

Sai yayi zumbur ya tashi yana daka mata tsawa

“Keee! Ki koma ki kwanta ko ki bar min ɗaki na”.

Sosai RAUDHA ta tsora ta da ganin yanda ya kirne fuska, gashi tsawan da yayi mata har tsakar kanta sai da ya amsa, nan ta sake rikice wa ta hau fasa masa kuka, sai dai ta kasa motsawa daga inda take, cikin rawan baki tace, “tso..roo nake ji..” tayi maganar numfashin ta na sama tamkar zai ɗauke

Sai ta bashi tausayi matuƙa, shima ba wai yana hakan sabida ba ya so ta raɓe sa bane, gudun kar wani abu ya faru ne, ya zo ya aikata dana sani, abinda ba ya fatar kasancewar shi

Komawa yayi ya zauna, cikin lallami ya soma rarrashin ta, daƙyar ya samu ta kwanta a bakin gadon, shima sai da ta riƙe masa riga gagam kafin ta rufe idanun ta, kuma ba ta yin mintuna biyu take sake buɗe idanun don ta tabbatar yana wajen, duk da kuwa tana riƙe da rigan sa

Shi dai Rayyan tagumi ya zuba kawai yana kallon ta, ji kawai yake yi da ma matar sa ce? Har ya ga abinda zai biyo baya

Numfashi kawai yake sauke wa tsawon wasu awanni, sai da ya tabbatar da ta daɗe da koma wa barci kafin ya janye rigan sa ahankali, tashi yayi ya shiga Toilet yayi uzurin sa, sannan ya dawo ya ɗauki pilow ya koma kan sofa ya kwanta, sai dai ya kasa barci, tsananin tunanin RAUDHA ya hana sa sukuni, sai juye-juye yake yi, daga ƙarshe gyara kwanciyar sa yayi; yayi Facing ɗin ta yana kallon ta, ahaka be san sanda barci ya ɗauke sa ba.

      Da asuba da ya tashi ya ɗauro alwala, sai ya nufi inda take ya hau tashin ta, but ko motsi taƙi yi, juyin duniya yayi ya tashe ta but taƙi, aransa tunani yake “ta cika mugun barci, sai ka ce wata gawa” ganin zai yi latti sai ya fice abun sa.

      Koda ya dawo ma, ya gwada tashin ta, nan ma be yi nasara ba, tsayawa yayi kawai yana kallon ta

“Anya ma yarinyan nan tana sallah?” Yafaɗa a ransa

Sai kuma ya saka hannu ya birkito ta yana faɗin, “ke RAUDHA tashi mana, ki tashi kiyi sallah”.

Shanyayyun idanuwan ta tabuɗe akan sa, tana yi tana rufe wa

“Tashi ko”. Ya sake faɗa yana ɗan bugun kumatun ta

Sake langaɓe wa tayi tana son koma wa ta kwanta

“Keee tashi mana, wannan wani irin barci ne haka, tashi na ce ko in ɗibo ruwa in zuba miki”.

Tarwai ta buɗe ido akansa, kallon sa kawai take yi tana son tunano abunda ke faruwa har tagan shi kusa da ita, jujjuya kanta ta soma yi tana kallon ɗakin

Shi kuma sai yaja ƙafafuwan sa ya nufi kan sofa ya zauna, sannan ya mayar da idanun sa kan ta ya ce, “ki tashi kiyi sallah lokaci na tafiya”.

Bata motsa ba illa lumshe idanu da tayi tana matse gashin kanta da hannu ɗaya, sai a time ɗin komi ya dawo mata ƙwaƙwalwa, sake ware idanuwan ta tayi tana kallon sa

Shima dai ita yake kallo, sai ya ɗauke kai abinsa, be sake bi ta kanta ba illa wayan sa da ya ɗauka ya soma latsawa

Ita kuma taƙi ta tashi, sabida baza ta iya barin ɗakin ba, gani take yi idan ta koma can ɗakin zata ga waɗannan halittun da ta gani a mafarkin ta, shiru tayi ta faɗa tunani, sai yanzu take jin kewar yayan ta, ta tabbata da akwai shi, da a yanzu tana nan maƙale dashi, kuma baza ta ji tsoro haka ba.

         Ray ganin taƙi tashi ta fitan masa a ɗaki, sai ya miƙe ya nufi Toilet ya shige, wanka yayi sabida ganin gari ya soma haske, sai ya fito ɗaure da towel yana tsane jikin sa, ko a jikin sa be damu don akwai ta a cikin ɗakin ba, ta yiwu ma tabar masa ɗakin idan taga yana shirya wa

    Amma be san cewa RAUDHA ko a jikin ta ba; wai don ta gansa a haka, tunda ta kalle shi sau ɗaya ta ɗauke kai ta yunƙura ta tashi zaune tana faman matsa cinyoyin ta.

    A sace yake kallon ta, ganin taƙi tashi sai kawai ya taɓe baki, aransa yana faɗin, “dama ya za’a yi ki ji tsoron gani na ahaka tunda kin saba ganin gardawan banza”.

Sai maganar ya ƙular dashi, sabida tsananin kishi da yaji ya turniƙe shi, tamkar wani ne yayi maganar ba shi ba, kallon ta yayi suka haɗa ido, ya ɗaure fuska tamau ganin yanda take bin sa da kallo

“Ke tashi ki fitar min a ɗaki zan shirya, tunda ke baki da kunya Ni ina dashi”.

Tamkar sokuwa haka take bin shi da kallo, sai dai maganar na sa sun yi mata tsauri, don ta kasa fassara su

“Baza ki tashi bane ina miki magana kina kallo na? Fitar min a ɗaki na ce zan shirya, tunda ba a gaban ki zan shirya ba”.

Sai anan RAUDHA ta fahimci inda ya dosa, sai ta taɓe baki cike da tsantsan tsanar sa ta ce, “menene a jikin naka da zan kalla? kai baka isa ka kai namijin da zai tsole wa RAUDHA ido ba, nafi ƙarfin ka har ABADA”. Ta ƙare maganar tana zaro masa ido

Ran sa yayi mugun ɓaci, be yi wata-wata ba ya nufo ta, ya saka hannu zai…

Marin ta ya so yi, sai kuma ya dunƙule hannun nasa ya duki iska

Ko kaɗan shi ba mutum bane me son dukan mata, bare kuma ita tana da babban matsayi a zuciyar sa, shiyasa da zaran ya so ɗaukan mummunan mataki akanta yake kasa wa, amma ba don haka ba; wlh da tuni ya nuna mata kuskuren ta a rayuwa, domin baza ta taɓa manta shi ba, shi mutum ne da ba ya ɗaukan raini.+

     Hannun sa ya saka ya finciko ta daga kan gadon

Ƙwalla ƙara tayi sabida a zaban da ya ziyarce ta, sakamako jan mata hannu da yayi har sai da yayi ƙara tamkar ya karye, kuma be barta haka ba sai da ya matse hannun ta yanda zata ji zafi sosai

Waje yayi ya jefar da ita a bakin ƙofan, sannan ya mayar da ƙofan ya rufe garam

Kuka ta fashe dashi, ta taso da gudu tana dukan ƙofan, kuka sosai take yi tana kiran sa ya buɗe mata ƙofan

But Ray na jinta yayi biris da ita, a ganin sa in ba iskanci ba taya zata maƙale masa a ɗaki; daga taimako?. Ran sa duk a ɓace yake haka ya gama shirin sa cikin uniform ɗin aikin sa, kayan sun bala’in yi masa kyau sun sake fito da zallan yarintan sa da hasken skin ɗin sa, gaban mirror yaje ya gyara suman kansa tare da siririn sajen sa, sannan ya feshe jikin sa da parfomer’s masu shegen ƙamshi, sake gyara zaman wandon sa yayi sannan ya nufi bakin gadon ya ɗauki wayan sa tare da nufo wa bakin ƙofan

Yana buɗe ƙofan ta faɗo kansa, da sauri ya sake riƙe ta yana kallon fuskarta da yayi caɓe-caɓe da hawaye, lumshe ido kawai yayi yana jin saukar ajiyar zuciyar ta a ƙirjin sa, ko kaɗan ya kasa janye ta a jikin sa sabida wani irin kasala da ya ziyarce sa

Ita kuma RAUDHA tunda taji ta a jikin sa ta kasa motsi, illa lumshe ido da tayi tana shaƙar daddaɗan ƙamshin turaren sa, sai sake lafe masa take yi

Numfashi yaja yana buɗe idanun sa da suka soma sauya kala ya aza a kanta, ahankali ya saka hannu ya janye ta a jikin sa

Firgigit tayi tamkar wacce aka tasa daga barci

Hakan sai ya bashi matuƙar mamaki, yabi ta da ido cike da zallan soyayyar ta, duk idan ya kalle ta sai yaji komi na sa yana kwance wa, tamkar dai ana sauya masa komi da komi dake duniyar, yana jin kamar su kaɗai ne a cikin ta, sannan yana jin wani irin farin ciki da annashuwa na mamaye sa, duk wani ƙunci da ɓacin rai da yake ji akanta, ko kuma fushin da yake so ya ɗauka akanta sai ya ji ya nema ya rasa, sai tarin ƙaunar ta a zuciyar sa.

       Idanun ta ƙyarr a kansa tana hawaye tace, “Please ka tafi dani ina jin tsoro, zasu dawo su cinye Ni ne”.

Waro ido yayi cike da mamakin ta, sai kuma ya ɗaure fuska yace, “in tafi dake wajen aikin nawa kike nufi?”

Ta gyaɗa masa kai still tana hawaye

“Babu inda zan je dake, waɗanda zasu cinye ki ɗin su zo su cinye ki, Ni ba maƙale mata mammanne mata sunana ba, idan yayan naki ya dawo sai kiyi masa wannan sakaracin, amma ban dani, zuwa anjima yace min zai dawo”.

Daga haka ya juya yayi gaba abun sa

Sai ta biyo bayan sa tana hawaye, a waje a bakin ƙofa ta tsaya tana kallon sa har ya isa wajen motan sa, ya shiga yaja yanufi bakin Gate

Ta cikin Glasses ɗin motan yake kallon ta, sosai ta ba shi tausayi ganin yanda take ta hawaye, tabbas ba ƙaramin abu ne ya tsorata ta ba, tunda har ta kasa zama a gidan tana son bin sa, ji yake yi tamkar ya koma ya ɗauko ta su fita tare, but ba shi da inda zai ajiye ta; tunda shi dai ba babban Aljihu ne dashi ba, ahaka yana ji yana gani ya bar gidan.

RAUDHA dai bata tashi a wajen ba, sai kuka take yi, daɗin ta ɗaya tana hangen sojojin dake bakin Gate ɗin, sai ta saka hannu tana share hawayen ta tana tuno maganganun sa da yace mata Yayan ta zai dawo yau, sosai taji daɗi a ranta, ko ba komi zata samu salama.

     Tana nan tsaye Ester ta zo gidan, wannan dalilin ne ya saka ta samu ta koma ciki, amma sai dai ta hana Ester yin aikin ta, a dole Ester CE zata raka ta tayi wanka, har Toilet suka nufa tare da ita, Ester ta tsaya a bakin ƙofa har tayi wankan ta gama, tafito ta shirya cikin wando Three qwater baƙi, da jan riga me layi-layin baƙi, suka fito Parlour

A taƙaice dai duk inda Ester ta saka ƙafa, RAUDHA na biye da ita tamkar jela, har ta gama aikin ta suna tare, sai dai ta zauna kusa da ita tana kallon ta ba ta cewa uffan.

Ƙiri-ƙiri RAUDHA ta hana Ester tafiya koda ta gama aikin na ta, dole ta zauna suka koma Parlour suna kallo.

🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐

     Wajen ƙarfe 04:30pm. Drever ya tafi ɗauko su Suhaib a airport, kasancewar kafin Rayyan ya fita ya sanar masa zuwa ɗauko su; tunda shi bazai dawo ba sai dare.

     Koda drever’n ya isa har jirgin su yayi landing, shi ya taimaka musu wajen saka kayan su cikin Boot bayan da suka gama gaisawa, sannan yaja motan suka taho gida.

      Sanda aka buɗe Gate ɗin gidan, RAUDHA dake kwance saman dogon kujera tana jin ƙaran buɗe wa, but bata yi motsi ba don a tunanin ta Rayyan ne ya dawo

Ester itama tana zaune tana kallo.

    A time ɗin ne suka shigo parlour’n da sallama

Jin muryan yayan ta a cikin kunnen ta, ai babu shiri ta wuntsilo daga saman kujeran ta ƙwalla ƙara, tatashi ta nufe sa a guje ta ɗare jikin sa

Bakin Suhaib gaba ɗaya yaƙi rufuwa sabida ganin gudan jinin sa, sai shilla ta yake yi yana juyata a cikin parlour’n, ita RAUDHA tsaban murna har da kukan ta, dole ya koma rarrashin ta yana tambayan ta abinda ke damun ta, dama haka take so sai ta fara masa shagwaɓa

Farida tuni ta nufi cikin parlour’n, ta zauna kan kujera suna gaisawa da Ester

A lokacin ne Suhaib suka ƙariso su ma cikin parlour’n, yana maƙale da RAUDHA suka zauna

Sannan ne Ester ta gaishe da Suhaib, ya’amsa mata cike da fara’a, sallama tayi musu ta fice abun ta

Farida tace, “Ƙanwata babu gaisuwa? Tunda kin samu Yayan ki ko missing ɗina ma ba kya yi”.

Kallon ta RAUDHA tayi tana murmushi, sai kuma ta tashi daga jikin Suhaib, ta koma kusa da Faridan, ta ɗaura kan ta a kafaɗan ta tana faɗin, “a’a Aunty nayi missing ɗin ki sosai da sosai”.

Gaba ɗaya murmushi suka yi me haɗe da farin ciki, don sosai suka ga sauyi a tattare da RAUDHA, tabbas kallo ɗaya kayi mata zaka san tayi sanyi sosai

RAUDHA dai bata sake bi ta kansu ba, sai ta koma yi wa Haneep dake cinyan Farida wasa, tana jan kumatun sa tana tale masa wai sunan wasa, shi kuma ya zuba mata fararen idanuwan sa yana mata dariya yawu na zuba

Ɗaga kai tayi ta kalli Suhaib ta ce, “Yaya har yanzu be dena zubar da silver ɗin ba, be samu sauƙi bane?”

“Ya samu mana Baby, baki ga ciwon cikin sa ya warke ba, shima a hankali halittar sa zai koma normal idan muka ci gaba da nema masa magani, tunda an samu sauƙi yanzu”.

Gyaɗa kai kawai tayi alamun ta fahimta

Tashi Farida tayi ta miƙa wa Suhaib yaron, sannan ta wuce ɗaki ta bar su nan, RAUDHA tuni ta koma kusa da Yayan ta tana ci gaba da jan kumatun Haneep tana sauraron hiran Suhaib ɗin, wanda shi kaɗai yake maganar sa, sai dai ta kaɗa masa kai, ko ta amsa masa da “Umm..” ko “a’a”.

   Kafin dare sosai suka sake ganin sauyi a tare da RAUDHA, gaba ɗaya ta maƙalƙale su, duk inda suka saka ƙafa tsakanin Farida da Suhaib, to, nan itama zata saka nata, tana manne dasu a ko ina, duk a tunanin su tayi missing ɗin su ne sosai, har Suhaib yana tsokanar ta, don shi mamaki abun ya ba shi, tunda wajen kwanaki bata yin masa magana tana fushi dashi, be yi zaton idan ya dawo zata kula sa haka ba, sai hakan ya ƙara saka sa farin ciki, musamman da yaga tayi sanyi matuƙa tana ladab tamkar ba ita ba, sai duk tunanin sa Rayyan ne ya sauya ta, tunda dama ya ba shi amanar ta ne don su samu sauyi, ya san halin abokin sa ba ya ɗaukar raini, bazai yarda da duk wani banzan halin ta da zata iya nuna masa ba, shiyasa yayi tunanin ko a sanadiyar sa zata shiryu, ya sauya mata hali tunda shi bazai iya ba. Kuma abinda ya ƙara basa mamaki ko kaɗan bata yi maganar Rayyan ba, bare kuma ta kawo ƙarar sa akan abinda yayi mata.

     Wajen sha ɗayan dare Rayyan ya dawo a ranan, time ɗin ma RAUDHA tuni tayi barci a ɗakin Farida

Sosai abokan suka yi murna da ganin juna, nan suka yi ta hira suka raba dare.

       🌐🌐🌐

     Tun daga ranan koda yaushe RAUDHA a ɗakin Farida take kwana, har a time ɗin tsoron kwana ita kaɗai take yi, duk da bata sake yin mafarkin ba amma tsoron yaƙi barin ta. Yanzu ko bi ta kan Rayyan ba ta yi, ko kallo ma be ishe ta ba, dayake shima ba zama yake yi sosai agidan ba a kwanakin, don haka ba sa wani haɗuwa, idan kuwa yazo ya tarar dasu suna zaune a Parlour gaba ɗayan su, to ɗayan biyu ne, ko ta tashi ta bar wajen; ta koma ɗaki. Ko kuma dama tasan ba zama zai yi ba zai fita ne

Shi dai Rayyan mamakin hakan yake yi, abinda ke ɓata masa rai kuma, ko kaɗan ba ta kallon sa, idan har zai dawwama idanun sa akan ta ne, to har yabar wajen bazai ga ta kalli inda yake ba, shi kuma hakan na ƙona masa rai, yana so ma ko ɗan faɗan nan ne ma ya taƙale ta don ta kula sa, amma ba ta zama inda yake, Kuma a kwanakin sosai yake tura mata text message love, koda sau ɗaya ne bata taɓa dawo masa da reply ba, har kiran ta ya gwada yi amma taƙi ɗauka, ya kan rasa wacce iriyan yarinya ce wannan, shin ko dai ba ta soyyayya ne?

Abinda be sani ba ita gaba ɗaya, ta dena karanta message ɗin na sa, duk da ba ta goge wa but taƙi ta buɗe ta karanta.

    Haka kwanaki suka fara shuɗe wa, time ɗin RAUDHA ta dawo normal ta dena jin tsoron da take ji, yanzu a ɗakin ta take kwana, ta so koma wa school but Rash ta sanar mata sun tafi hutu, don haka a ranan ta soma shirin fita yawo, tsawon watanni biyu kenan ko ƙofar Gate bata sake fita ba

Koda ta gama shiryawa ta sauko daga sama, Farida kaɗai ta tarar a parlour’n, tunda a time ɗin Suhaib yana wajen aiki, shima haka Rayyan, shi two days ma ba ya kwana agidan sabida aiki

Sallama tayi wa Farida kaɗai tafice abin ta

Itama Faridan bata tambaye ta inda zata je ba tunda ba yau ta saba fita bata sanar mata ba.

       Direct RAUDHA gidan su Rash ta wuce

Rash tayi murnan ganin ta ba kaɗan ba, haka ta rungume ta suna murna, kafin suka zube akan kujera

Rash tace, “Babe wlh kinyi mugun sauyawa, Ni da zan ganki kin rame kin yi baƙi sabida azaban wannan sojan, amma kuma sai naga kin sake haske kinyi ƙiba abun ki, tamkar baki da wani damuwa”.

Hararan ta RAUDHA tayi, sai kuma ta taɓe baki tace, “ina su Maan?”.

“Maan ya tafi garin su, acan yake hutun sa, d same shima Zen ya tafi hutu can asalin garin su, yace “bazai zauna ba tunda babu ke, shiyasa garin ba ya masa daɗi ya zaɓi yin hutun sa acan”.

RAUDHA bata sake magana ba dai, illa sauraren Rash dake ta faman zuba mata surutu take yi, labarin duk abinda ya faru da ba ta nan take ba ta, sannan ta sanar mata akwai casun da zasu haɗa sati me zuwa, birthday ɗin Maan za’a yi, kuma agidan nan zasu yi ba sai sun je club ba.

   Haka dai sukai ta hiran su, daga ƙarshe suka fita yawo. sai dare suka dawo, sai da RAUDHA ta sauke Rash a gida sannan itama ta wuce, tana yin peacking ta ɗauki jakan ta ta fito daga motan ta rufe, koda ta shiga parlour’n babu kowa, ɗakin ta tawuce ta zube akan gado tana riƙe kanta, lumshe idanu tayi tsawon mintuna goma kafin ta tashi zaune ta hau ciro ƙwayoyin da suka siyo, buɗe wa tayi ta ciri tables guda uku ta afa a baki, sannan ta ɗauki sauran ta adana a cikin drower ta saka keey, sannan ta zare ta ɓoye, tashi tayi ta shiga wanka, bata jima ba ta fito ta shirya cikin kayan barcin ta ta haye gado, a time ɗin daƙyar take iya ma sarrafa kanta, burin ta kawai taji ta a gado; shiyasa bata damu ta haɗu da kowa ba, ko kuma taci abinci; tunda sun yi ciye-ciyen su a wajen yawon su, babu jimawa barci ya ɗauke ta me tsananin daɗin da ta daɗe bata yi irin sa ba, domin ƙwayoyin sosai suka taimaka mata wajen yin barci me nutsuwa sosai.

_______📖 A ranan da su Maan suka shirya gagarumin birthday ɗin shi, ƙarfe 05:00pm. RAUDHA ta shirya ta wuce, kasancewar dama da yamma za’a soma har zuwa dare.+

    Sosai partyn ya haɗa manya-manyan guys masu ji da kansu, gashi ba ƙarya an kashe kuɗi sosai a wajen, wines ɗin ma da akayi ordaring ɗin su masu tsananin tsada ne

Haka suka wuni suna cashewa, ita kanta RAUDHA sosai ta saki jikin ta, ta shige cikin su Zen ana ta raha. sosai a ranan ta bugu, don ƙwayoyin da tasha ma sun fi ƙarfin ta, sai dai Rash ne ta dawo da ita gida, a time ɗin ƙarfe 08:pm. Ne na dare, lokacin Suhaib na masallaci sai Farida dake zaune a Parlour ita kaɗai, tunda Rayyan ba ya nan

Hankalin Farida ya tashi sosai sanda Rash ta shigo da RAUDHA tana surutai tamkar mara kai, sai dariya take yi tana maganganu, amsar ta tayi tana kallon Rash tace, “ke wai me tasha haka take wannan abun?”

Rash na sosa Kai tace, “kiyi haƙuri aunty, wlh party muka yi..” Sai tayi shiru ta kasa ƙarisawa

Tsaki Farida taja tana hararan ta tace, “dalla wuce ki bar mana gida, wlh idan baku ji tsoron Allah ba, watarana zaku yi nadama”.

Ita dai Rash bata ce komi ba, tayi gaba abunta.

    Har ɗaki Farida ta shigar da ita, a time ɗin RAUDHA tayi ta kwarara amai kamar zata amayar da hanjin cikin ta, babu yanda ta iya dole ta wanke mata, sannan ta sauya mata kaya. har a time ɗin bata bar surutun da take yi ba tana ɓaɓɓaka dariya, kwantar da iya tayi ta fice a ɗakin

A Parlour ta tarar da Suhaib, nan ta faɗa masa duk abinda ke faruwa, ai babu ɓata lokaci yayi ɗakin RAUDHA, a kwance ya ganta idanun ta a rufe fuskarta ɗauke da murmushi

Ƙarisawa yayi kusa da ita ya zauna a gefen gadon yana kiran sunan ta

Buɗe idanun ta tayi ta aza a kansa, sai ta ƙyalƙyale da dariya ta hau yin masa maganganu, har da su zagi, ko kaɗan babu kan gado

Ajiyan zuciya ya sauke, ya ɗaura hannu a kanta ya soma tofa mata addu’a cike da damuwa a cikin ransa, ya daɗe yana mata addu’a, har sanda barci ya ɗauke ta sannan ne ya tashi yabar ɗakin.

      A taƙaice dai kwana biyu cur RAUDHA tana cikin wannan halin, taƙi komawa normal, dole Suhaib ya ɗauke ta zuwa asibiti. Sai dai bayanin da likita yayi masa, ya ɗaga masa hankali matuƙa

Ƙwayoyin da tasha sun taɓa mata ƙwaƙwalwa, that’s why take irin Wannan abun

Har kuka sai da Suhaib yayi, ya rasa yanda zai yi, nan ya kira Rayyan ya sanar masa halin da ake ciki, shima hankalin sa yayi matuƙar tashi, nan ya taho asibitin akai ta zirga-zirga dashi, sannan aka ɗaura RAUDHA akan magani

Bayan kwana biyu ta ɗan samu sauƙi aka sallame ta, a ranan ne ta sake mugun mafarkin da ya ɗaga mata hankali, take ta farka tana kwatsa ihun da ya karaɗe ilahirin gidan

Lokacin da su Suhaib suka taho ɗakin ta hankalin su a tashe, time ɗin ta rigada ta sume, sun zuba mata ruwa amma bata farka ba, dole suka wuce da ita asibiti, tare da Rayyan suka tafi, sai aka bar Farida a gida.

     Duk iya gwanintan likitoci akan su samu ta farfaɗo amma abin ya gagara, sun yi iya yin su sun kasa, dole suka barta suka ci gaba da bata taimakon iya abinda suka gani, ahaka har kwanaki uku suka yi amma RAUDHA bata farfaɗo ba, su Suhaib sun rasa yanda zasu yi, ana cuku-cukun fitar da ita ƙasan waje ne, sannan ne ta farka, sai dai ko kaɗan taƙi yin magana, sai dai tayi ta ɓaɓɓaka dariya

Likitoci sun gano cewa ƙwaƙwalwan ta tarigada ta taɓu, sai dai a ɗaura ta akan magani ko Allah zai sa adace, kafin ciwon ya kai ga nisa

Kuka me sunan kuka, shi Suhaib ya dinga yi, kamar ransa zai fita, ko kaɗan be kalli girman sa ba, haka zai zauna yayi ta kuka, Rayyan shine me rarrashin sa, gashi shima ba ya zama sabida aiyuka sun yi masa yawa, yau suna nan; gobe suna can, ga tarin damuwa shima da ya riske sa, ya kasa samun nutsuwar zuciya.

     Ita kanta Farida ta kasa samun sukuni, ga rainon Haneep mara lafiya, ga halin da mijin ta yake ciki, ga kuma tashin hankalin da suke ciki akan ciwon RAUDHA, bata da maraba dai da mahaukaciya, bige-bige ne kaɗai ba ta yi, amma gaba ɗaya ba ta gane wanda ke kanta, tamkar ƙaramar yarinya haka ta koma, wani time ɗin kuma sai su ga ta koma normal kamar ba ita ba, sai dai ta dinga kuka kenan tana taɓara karasa ma me take so.

     Dole Suhaib yaci gaba da cuku-cukun fitar da ita ƙasar India a duba ta.

    Sai dai a time ɗin ne wani cuta me suna *Corona Virus (Covid 19)* ya shigo duniya, hakan yasa be samu damar fita da ita ba, don an ce ko wani ƙasa su rufe ƙasar su. babu me shiga bare fita, daga ciki kuwa har da ƙasan Nigeria, duk da a time ɗin jita-jita ake ji a Nigerian.

     Allah da ikon sa kuma, acan ƙasan Chaina cutan tayi yawa matuƙa, dole shugaban ƙasar ya ba da umarnin duk wanda ba ɗan ƙasan bane, ayi gaggawar mayar dashi ƙasar su, sannan a rufe musu ƙasa babu me shiga bare fita, a time ɗin har an soma mutuwa, domin acikin ɗan ƙanƙanin lokaci an rasa mutane kusan dubu da ɗorawa. Dole aka saki su Daddy aka mayar dasu ƙasar su

Farin ciki wajen Daddy ba ya misaltuwa, domin a wajen sa ma zan iya cewa yaji daɗin shigowar cutan, tunda gashi a sanadiyar sa an sake su, memakon su yi shekara ɗaya, sun yi FOUR months.

    Koda jirgi ya sauke su, sai ya kira Numban Suhaib.

      Lokacin Suhaib na cikin asibiti, ya tasa RAUDHA dake barci agaba yana ta faman tunani, ringing wayan sa take yi, but tsaban tunani ya kasa ji

Sai da Nurse ɗin dake gyara wa RAUDHA ruwan da aka saka mata, yayi masa magana sannan ne ya dawo hayyacin sa

Fito da wayan cikin aljihun sa yayi, ganin sunan Daddy ya fito raɗo-raɗo da numban Nigeria, ai zumbur ya miƙe tsaye hannayen sa suna rawa tamkar zai yar da wayan

“Daddy”. Yafaɗa yana bin wayan da kallo batare da yayi yinƙurin ɗauka ba

Sai da ta katse aka sake kira, sannan ne ya ɗauka ya kara a kunne

Anan Daddy yake sanar dashi yana airport na Abuja, ya zo ya ɗauke sa

Ai babu ɓata lokaci ya fice, tsabar murna ma ya manta da cewa ya bar RAUDHA babu kowa a wajen ta, tunda dama Farida tana gida, sai idan zata kawo abinci take zuwa, shi kuma Rayyan aikin sa ba ya barin sa, sai idan ya sami time ne yake leƙowa.

     Sai da Suhaib ya kusa isa airport ɗin ne, ya tuna da halin da ƙanwar sa take ciki, sai yanzu ma tunanin sa ya kai ga cewa Daddy fa zai ɗauko, shin ta ya ma zai tunkare sa da maganar ciwon RAUDHA?

“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un”. Abinda ya ke ta maimaita wa kenan

Gaba ɗaya idanuwan sa sun yi ja, sai tarin damuwa dake cikin ransa. Ahaka yayi ƙarfin halin ƙarisawa airport ɗin, duk jikin sa a sanyaye, gaba ɗaya ya rasa nutsuwar sa sai tarin damuwa da fargaba dake tare dashi, abu biyu ne suka haɗe masa a yau ɗin, ga farin cikin dawowar Daddyn sa, ga kuma baƙin cikin halin da ƙanwar sa take ciki, memakon yayi farin ciki sai baƙin ciki da damuwa su suka cika masa ilahirin zuciyar sa.

     Yana shiga airport ɗin ya hangi Daddy, fitowa yayi a motan ya nufe sa da sauri

Shima Daddy tun kafin ya ƙariso ya hange sa, nan da nan ya nufo sa fuskar sa cike da fara’a, sai dai yayi mamakin ganin Suhaib shi kaɗai ban da RAUDHA, amma kuma sai ya kau da zancen daga zuriyar sa ya rungume ɗan nasa da ya iso gare sa

Suhaib tsaban murna har da ƙwallan sa, sai faɗi yake yi, “I miss You Daddy! I miss you”.

Ban da buga bayan sa babu abinda Daddy ke yi, murmushi kwance a kyakkyawar fuskar sa.

     Sun ɗau kusan mintuna biyu ahaka kafin Suhaib ya janye jikin sa daga runguman da Daddy yayi masa, kallon mahaifin nasa kawai yake yi cike da so da ƙauna, gami da tarin tausayin sa a ransa. Tabbas idan ka kalle sa zaka ga tsantsan raman dake fuskar sa, ga kuma baƙi da yayi duk ya tara ƙasumba, har wani tsufan dole ya ƙara

Daddy dake tsaye riƙe da hannun Suhaib ɗin, murmushi kawai yake zuba wa yana kallon sa, ganin ya ƙure sa da idanu, sai da yaga be da alamun magana sannan ne yace, “My dear Son halan na sauya maka ne?”

Sai a time ɗin Suhaib ya dawo dogon tunanin da ya lula, ya kalli Daddyn yana ƙirƙirar murmushi yace, “Daddy ka matuƙar sauya wa sosai, idan ba don Ni ɗanka bane babu ta yanda za’a yi na gane ka”.

Sai Daddy ya saki dariya yana dukan kafaɗan Suhaib ɗin yace, “ka ganka ko?” .

Shima dariyan yayi yace, “Allah kuwa Daddy, don baka ganka bane, Allah dai ya saka mana duk wanda yake da hannu wajen saka wa a kama ka”.

Murmushi Daddy yayi yace, “Amin, amma ban ga Baby ba, ko bata san na dawo bane?”

Take zuciyar Suhaib ta buga da ƙarfi sabida fargaban da ta shige sa, sai dai ya daure ya ƙi nuna wani alama, illa murmushi da yayi yace, “ban sanar mata bane, sai mun koma ta ganka, nasan hakan zai fi saka ta farin ciki”.

Daddy ya murmusa yace, “ok Mu je to, but mu wuce gidana ne don bazan zauna a na ku ba, inyaso sai ka ɗauko ta ita da matar taka gaba ɗayan su”.

Gyaɗa masa kai Suhaib yayi, batare da ya sake furta komi ba, suka yi gaba suka shiga motan.

    Direct gidan Daddy suka wuce, shima babban gida ne da babu kowa sai ma’aikata, su ma jefi-jefi suke zuwa gyara gidan tunda ana biyan su duk wata, Daddy ba ya zama a gidan sai idan zai zo Abuja yin wani kasuwanci, ko kuma time ɗin da yake ganiyan siyasa, idan zasu yi meeting anan yake sauka, har da abokan sa.

     Suna shiga Suhaib yayi parcking suka fito, anan ma”aikatan suka taho suna ta kawo musu gaisuwa, Daddy na amsa wa cikin fara’a yana tambayan su iyalai da mutanen gidan, Allah ya ɗaura wa Daddy tausayi shiyasa yake matuƙar girmama duk wani talaka, ko kuma wanda yake aiki a ƙarƙashin sa, be yarda ya wulaƙanta su ba a matsayin sa na me kuɗi, yana ɗaukan su ne duk ɗaya suke, shiyasa su ma suke jin daɗin aiki a ƙarƙashin sa, sam-sam ba shi da wulaƙanci irin na masu kuɗi, gashi da zaran wata yayi zai biya su kuɗaɗen su, duk da kuwa cewa ba zaman gidan yake yi ba, su kuma ba aikin sosai suke yi ba, amma suna samun albashi sosai.

     Shi Suhaib tuni ya shige cikin gidan tunda suka gaisa, ya bar Daddy Nan yana ta tambayan su matsalolin su, tare da musu alƙawura idan ya nitsa duk zai sallame su. Bayan ya gama sallaman su sai ya shigo gidan, first abinda ya fara yi wanka, sai da yayi wanka ya sauya kaya sannan ya ci abinci, atare suka ci da Suhaib duk da tsakura kawai yake yi, sosai Daddy ya kula da shi tun a airport be da walwala, ƙarfin hali ne kawai irin na sa, sai be tambaye sa ba shima, a zumman idan suka koma gida zai tasa shi gaba ya sanar masa.

Bayan sun gama cin abincin sun dawo Parlour, ya kalle sa cike da kula wa yace, “Son wai me ke damun ka? Na kula gaba ɗaya nutsuwar ka ba ya tattare da kai? Me ke faruwa faɗa min inji kaji my son?”

Kamar jira yake yi ya tambaye sa, sai ga ruwan hawaye sun soma zuba a saman kyakkyawar fuskar sa

Sosai hankalin Daddy yayi matuƙar tashi, nan ya soma salati yana tambayan Suhaib ɗin me yake faruwa? Hankalin sa duk a matuƙar tashe, rabon da ya ga kukan Suhaib tun yana ƙarami, amma yau gashi har da iyali yana kuka

Suhaib be iya sanar masa da komi ba, illa kukan sa da yaci gaba da yi.

       Ana haka sai ga Rayyan ya shigo gidan, domin tunda suka dawo Suhaib ya kira sa ya sanar masa da dawowar Daddy, Shine ya ce masa ga shinan zuwa yanzu, amma kuma zuwan na sa sai ya tarar da Suhaib na kuka, ga Daddy na faman rarrashin sa yana tambayan sa abinda ke faruwa hankalin sa a tashe

Duk da Daddy yayi farin cikin ganin Ɗan Abokin nasa, amma kuma halin da Suhaib yake ciki be sa sun gaisa sosai ba, sama-sama suka gaisa inda Rayyan ya faɗa masa komi na halin da ake ciki

“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un”. Shi kawai Daddy yake faɗa jikin sa na wani irin mazari tamkar an jona sa a shocking.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page