SIRADIN RAYUWA CHAPTER 4 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA

 SIRADIN RAYUWA CHAPTER 4 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA

    Ya jima tsaye gaban mudubi yana qarewa kanshi kallo kai kace wata matashiyar budurwa ce data gama ado tanason tantance meye baiyi ba a jikinta tasauya,saidai shi tsaiwar da yayi sam bata da alaqa da irin wannan,yana tsaye ne yana duban kayan da amminsa ta aiko mishi dasu ayau,wanda yana da tabbacin nuni take masa da cewa ya aje qananun kayansa yakoma irin wannan shigar har zuwa lokacin da zaya koma inda yafito.

     Kayane irin nasu na sarakai,wanda suka ji aiki ko ina dake nuna zallar sarauta,wani irin yadine ruwan bula mai turuwa wanda aka yiwa aiki da goldin din zare,sai wasu lausassan takalma rufaffu masu wata iriyar lanqwasa daga gabansu,hakanan an shirya musu duwatsu masu haske da qyalqyali daga samansu,takalma ne masu matuqar kyau daraja da tsada na zallar fatar damisa da gashin jimina,sai rawani da aka nada mishi wanda yadace da shigar tasa da kuma kalar kayanshi,yasan kuma ta sanya rawanin ne saboda umarnin data bashi nayau ya tabbatar yashiga anyi xaman fada dashi.

     Sosai shigar tasauya kamanninsa,saidai ta qara masa kwarjini dakyau,tasake maidashi wani mai shekaru ta boye quruciyarsa.

      Yana mamakin yadda ammin ke nuna mishi qauna da gata mai yawa amma ta gaza faranta mishi kan abu daya,abu dayan dashi a nashi ganin da kuma wajensa bai daukeshi a wata matsala ba.

     Don kanshi ya gaji da tsaiwar,ya daga kanshi a nutse yaduba agogo,lokacin daya kamata ace yashiga yayi,saboda haka yanufi wayarsa da niyyar sanyata a silent yasakata a aljihunsa.

      Saidai yana tsaka da qoqarin maidatan kira yashigo wayar tashi,kamar kowanne lokaci sunan Safwa yabayyana kan fuskar wayar,saiya tsaya yana duban sunan kamar baqone a wajensa,baisan iya adadin sau nawa tayi kiranshi ba daga dawowarsa zuwa yanzu,saidai kosau daya bai daga ba bare yabi bayan kiran nata bayan ya tarad da miscal,hasalima wasu lokutan shine da kanshi yake rejecting,don sam baiga amfamin ci gaba da tarayyarsu ba,tamkar ciwone,wanda maimakon azuba mishi magani sai ake bashi guba,saboda haka yasanya hannunshi yayi rejecting da kansa kana yaci gaba da abinda yake.

     Kamar hadin baki kiran sufyan yasake shigowa,ya dakata daga qoqarin sakata a aljihu da yakeyi,ya daga kiran yakara akunnenshi

“Mazaaa…..ya mutumina kana gida ne?” Ya fada da alamun nishadi saman fuskarsa,cikin salon maganarshi dake cike da qasaita yace

“Ya akayi?,ina gida….but amma zan shiga wajen maimartaba za’ayi zaman fada dani” wani dan qaramin ihu sufyan yasaki najin dadi

“Kace kawai zaka soma shiga harkoki kaga ya suke?” Qaramin tsaki yaja saboda shi sam a yanzun ba wannan bane babbar damuwar dake neman durqusar da rayuwarsa ba

“Ba wannan ba…..tunda nazo bamu hadu da maimartaba ba yayi tafiya,sai cikin daren jiya yadawo…..”

“Ohkey….anjima zan shigo,ina fata nasamu daddadan labari na amincewar ammi?”

“Aside this matter sufyan,saika shigo kawai” daga haka ya datse kiran yana jefa wayar a aljihu,sannan yasoma ficewa daga dakin.

     Duk inda ya gifta saiya tsaida zirga zirgar duka wani hadimi ko barori dake kaikawo cikin gidan har sai yawuce,kwarjininsa kadai ya isa yacika maka idanu,kowanne sashe yagifta gaisuwa suke miqa mishi,basu damu da yadda yake wucewa ba tare daya damu dako daga musu hannu ba,saboda sun riga sun kwana sun tashi da tsabar miskilanci irin na abdul’azeez din,wannan ba wani sabon lamari bane a wajensu.

     Tun daga nesa ya hangota tana tahowa ita da airah,diyar fulanin masanawa tafarko,wadda duka duka ba zata wuce shekara goma sha biyu ba.

Tunda suka hangoshi kowacce cikinsu tasake shiga nutsuwarta,shikam yi yayi kamar bai gansu ba,saidai yana sane da tahowarsu,saboda komawarshi ta qarshe yaba qwafe da walidan,yasha attempting na koya mata hankali ammi keda dakatar dashi

“Ba abinda bazaka gani ba tattare da yan uwanka…amma abinda bakeso dakai shine,babu ruwanka da ita,kadauke kai da idanu daga dukkan abinda zatayi”.

Saidai wani abu guda,tun yana qanqani mutum ne da baison raini,yadda jinin sarauta ke yawo ajijiyarsa haka kusan dukka halaye da dabi’unsa suke,hakan yasanya lamura da dama babu ruwanshi dasu.

Suna gab da iske juna yayiwa dogarawanshi inkiya,tuni suka bace daga farfajiyar,kowanne yasamu saqo da kunnuwanshi bazasu jiyi tattaunawar abdul’azeez da ‘yan uwan nashi ba yatsaya qyam yana jiran umarni

“Barka da warhaka hamma yarima”airah ta fada cikin girmamawa yayin da walida ke qoqarin wuceshi tamkar ma bata ganshi ba ko bata sanshi ba,duk da yadda zuciyarta ke tsalle saboda tsaro dakuma kwarjinin abdul’azeez daya cika wajen.

Wata gigitacciyar tsawa ya daka mata data sanyata tsaiwa cak,take cikinta yajuya fuskarta tasoma hada gumi,amma sai tayi yunqurin saita kanta sanda kalaman mahaifiyarta yafado mata

“Karki sake karki kuskura kici gaba da bashi wata qofa da xaisa ya rainaki,kin bashi kwanaki kusan dari a duniya kafin isowarshi,karki yadda kwarjininsa ya firgitaki koda kinji razani a ranki…..haka halittarsa take,amma dole mukoyi fada da wannan kwarjinin nasa….wanda nake da yaqinin annamimiyar mahaifiyarsa ce ta nema masa….”.

Taku uku yayi zuwa gabanta yana duban shigarta sama da qasa,shigace da sam bai dace ace tana ratso cikin gidan da ita ba,gidan dake da tarin hadimai maza da mata,ya mata jan kunne kusan kashi uku akan hakan amma bata sauya zani ba,saboda daurin gindi data samu daga wajen mahaifiyarta.

Dauke kai yayi kana ya gotata kadan kamar zai shige,idanunsa kan airah da take cikin yalwatacciyar doguwar riga da wadataccen mayafi,sam mahaifiyarta bata barinta tayi qazamar shiga tun tana qanqanuwarta

“Saunawa naja miki kunne kan dressing dinki cikin gidan nan?” Cikin tsananin jarumta ba tare data iya juyowa ba sun hada idanu tace

“Gaskiya abdul’azeez kafita daga sabgata…..idan ka manta bari na tuna maka,nidin yayarka ce,gaba nake dakai” tana kaiwa tasauke boyayyar ajiyar zuciya,wani qaramin miskilin murmushi yasaki,yamiqa hannu yariqo airah kana yadawo gabanta yatsaya yana duban qwayar idanunta

“Ko kadan baki taba wani abu dazai nuna cewa gaba kike dani ba,beside ma ayanzun koda bakiso nine gaba dake…..shigar qanwarki bata isheki misali ba?” Saiya daga yatsanshi yanunata dashi

“Wannan shine karo na qarshe dazan sake jan kunnenki game da wannan….ki kiyaye” saiya saki hannun airah yasoma tattaki zuwa gaba,kana ya basu alamar ya kammala da abinda yake,cikin sakanni suka bayyana sukaci gaba dayi masa tattaki har zuwa fadar.

ƙawatacciyar fada ce mai girma da yalwa,wadda tana jerin ɗaya daga cikin fadodi na alfarma cikin jerin fadar da sarki mu’az yake da ita,komai na cikin fadar kama daga shimfidu na alfarma zuwa kujerun zama,adon zanen (dagi) dakuma dardumai dake jikin bangon dukka golden ne da ratsin silver gami da maroon wanda kusan yafi yawa.

     Hakimai da yawa sun isa gurin a sannan,harda shi kansa mai martaban,saboda haka yaratsa cikin nutsuwa ya isa gaban mahaifin nashi ya miqa gaisuwa kamar yadda kowa yakeyi sannan ya yiwa kanshi masauki daura da mai martaban.

     Sun shafe a qalla awanni biyu cur ana zaman fada kafin daga bisani mai martaban yasoma sauraron shari’u daga talakawansa,abdul’azeez yana zaune daga gefe yana kallon yadda mahaifinsa kebin komai daki daki cikin hikima,kana yayi hukunci bisa adalci,sosai abun yaburgeshi,saiyaji duk a zaman wannan yafi qayatar dashi,zaman yatashi aka rufeshi da addu’a,maimartaba yawuce zuwa sassansa bayan yasa an shaidawa abdul’azeez umarninsa na cewa yasameshi a sassansa.

    Su biyune rak cikin falon duk girmanshi,sai tarin kayan abinci da kayan marmari da aka ajiye musu

“Matso abdul’azeez” cewar mai martaba yana duban abdul’azeez din cikin tsantsar qauna da kulawa.

      Sau tari abdul’azeez din kanyi mamakin yadda mahaifin nasa ke sakewa dashi sosai,sukanyi hira cikin yanayin da dazaka ganshi kai bakace shine MAIMARTABA SARKIN KAISA BA.

      A bayan fage mu’amala yake musu irin ta uba da ‘ya’yansa,bama iya abdul’azeez din kadai ba,har duka sauran ‘yan uwanshi ma.

     Cikin girmamawa yamatso,yasanya hannu kamar yadda shima maimartaban yasanya nashi hannun,duk da abdul’azeez don ba gwanin cin abinci da hannu bane,amma wannan karon abun saiya qawatar dashi.

      “Yaya makarantar?,da fatan komai yana tafiya yadda yakamata?” Ya jefa masa tambayar sanda suke tsaka dacin abincin,kaiya jinjina yana qoqarin hadiye abincin bakinsa

“Ina fatan babu wata damuwa?,don na qagu lokacin da zaka kammala karatun yayi kadawo cikin ahalinka” kai yakuma gyadawa kamar wani qadangare yana qoqarin boye abubuwan dake yawo saman fuskarshi,don yasani sarai maimartaban ba baya bane wajen iya karantar mutum shima tamkar amminsa

“Ma sha Allah,Allah ya taimaka”

“Amin Allah ya taimakeka” yabashi amsa a ladabce.

     Shuru yasake ratsawa kafin maimartaba yasake magana

“Ga ‘yaruwarka nan….ta dage itama so take tafita koda egypt ne ta hada degree dinta” amamakance abdul’azeez yadaga kai yana duban maimartaba,sai akayi arashi shima shi yake kallo,hakan yasa yadan sauke idanunsa qasa yana ci gaba dakai abinci bakinsa,ko kusa ko alama baya yiwa ‘yan uwanshi mata sha’awar barin qasarsu zuwa wata uwa duniya neman karatu har wata qasar,saboda su kadai sukasan me idanunsu suke ganemusu,yaran musulmi ‘yan arewa hausa amma idan kagansu saika rantse da sarkin daya halicceka basusan wata kalma kota ZO IN KASHEKA da hausa ba,hakanan saika rantse basusan inane alqibla ba bare kayi musu tunanin musulunci,shi a karan kansa yatuna yawan ‘yamnatan dake kara kaina da artabu a kanshi,duk da sautari kwarjininsa na taka musu burki,uwa uba bashi da fuska kamar yadda sauran samari keda ita,sakewa da sakin jiki da fuskawa duk wadda ta doshesu.

     “Abdul’azeez” kiran damai martaba yamasa yadawo dashi daga duniyar tunanin daya tafi,saiya dago yana duban mai martaba,dakatar dacin abincin yayi shima kamar yadda yaga mai martaba ya dakatar

“Ka gayamin meye ra’ayinka kan hakan,don ban sake magana ba kan lamarin ba,ba jirayi dawowarka ne,saboda kaidin watan watarana kaine uba a wajensu,koda kuwa akwai wadanda suka girmeka a cikinsu”.

     Cikin nutsuwa yabude baki yasoma magana

“Inda zai yiwu Allah ya qara maka lafiya….ni a nawa ra’ayin bana sha’awar daya cikinsu tafita wata qasar karatu….koda wacece kuwa a cikinsu…..,zaifi kyau dakuma kwanciyar hankali kowacce tayi karatu a qasarta….koda bazasuyi ba cikin qasar KAISA ba” daga haka yayi shuru yana jiran abinda maimartaba zaice.

     Kai yake jinjinawa,shi kansa wannan hukuncin shine hukunci mafi kwanciya cikin ranshi,sai yaji abdul’azeez din nasake samun wani matsayi na musamman a idanunshi,kamar yadda halayensa da dabi’unsa suka banbanta hakama tunaninsa,duk da qananun shekarunsa da basu haura ashirin da biyar ba

“Wannan tunanin naka yayimin abduk’azeez,Allah ya albarkaci rayuwarka kaida sauran ‘yan uwanka”

“Amin ya Allah Allah ya taimakeka….godiya nake”.

     Daga haka suka shiga tattaunawa kan wasu lamuran daban,wasu sun shafi masarauta ne kai tsaye,wasu kuma sun shafi al’amuran da suka dangancin sarki mu’az a karan kanshi.

      Saida lokacin sallah yayi sannan suka tashi,yafita yabar maimartaba yana shirye shiryen fitowa don halartar sallar azahar cikin jam’i a masallacin dake mallakin masarautar kamar yadda yasaba duk lokacin da yake qasar matuqar ba tafiya yayi ba,wanda hakan yasake tasiri qwarai a zukatan dukka jama’ar gidan dama sauran al’ummar dake wajen masarautar.

     Doka ce cikin gidan naduk wani bawa hadimi ko barori su saki dukkan aikin da suke da zarar lokacin sallah yayi suje suyi,wannan na daya daga cikin sirrika na daukakar masarautar,da samun wani irin kwarjini da haiba na musamman.

     Yana gab da isa masallacin saqo ya riskeshi na nemanshi da amminsa take,hakan yasanya suna kammala sallar yawuce sashen nata,duk da yaso yafita yadansha iska yaga garin sosai,don tunda yazo bai samu ya miqe qafa ba,sai yake jinsa duk a takure,sakamakon sabo da yayi da qasar daya fito,wanda take wadace da guraben hutawa dakuma shan iska.

      A falo na uku yau yayi burki,jakadiya ta isarwa da ammi saqon zuwan nashi,daidai lokacin tana zaune tana waya da babbar aminiyarta qwaya daya a duniya,wadda take iya raba sirrinta da matsalolinta da ita,kamar yadda itama take raba nata matsalolin da ammin,saboda tsabar shaquwa dakuma dadewa da sukayi tare tun zuwan ammi qasar nijeria,saita yanke kiran tana bawa surayya uzurin zata kirata.

     Kamar koda yaushe,cikin shiga ta alfarma dake nuna izza da mulkinta ta tako zuwa falon

“Barka da warhaka ammi” ya furta yana duban yanayin fuskarta,bata amsashi ba har sai data zauna kana ta amsa masa,tare da jefa masa tambaya

“Meya faru tsakaninka da safwa?”

“Takawo qarata kenan as usual?” Ya tambayi kanshi da kansa can qasan zuciyarsa ba tare daya furtawa ammin ba

“Babu komai….takawo qarata ne?” Da idanu ta kafeshi nawasu sakkani sannan ta amsa mishi

“Tabbacin baka da gaskiya kenan,ka gayamin meya faru tsakaninku?…..ta shaidawa jakadiya kadaina daga wayarta tun sanda kadawo,hakan na nufin kasoma daukar mataki na bijiremin?” Kai yakada,sam shibai kawo hakan a matsayin wani abu ba,saidai tuncan mutum ne shi da baison takura ba,bare shidin dabai dauki soyayya abakin komai ba bare tadameshi,hasalima yayiwa kanshi alqawarin bazai taba soyayyar ba,hakan yasanya yabaiwa ammin tashi hadin kai dari bisa dari lokacin data zaba masa safwa a matsayin matar da takeso ya aura aduk sanda lokacin auren yatashi.

    Ya auna safwa kan mizanai saiyaga tacika kaso saba’in cikin dari,hakan yasanya yaga bashi da wata matsala da hakan,zai iya karbarta.

        Safwa diya ce ga wani hamshaqin dan kasuwa ibrahim khalilu attah da yayi suna yayi shuhura hakanan yayi fice a garin kaisa kano jigawa dama sauran garuruwan dake arewa harma da kudancin nigeria,dan kasuwa ne na gasken gaske wanda ya mallaki kadarori masu tarin yawa ciki harda rijiyoyin man fetur,safwa ita daya Allah yabasu,hakan yasanya tasamu gata na gaban misali,hakanan tatashi cikin wadata ba tare da tasan wata kalma da talauci ko babu ba,shagwabbiya ce wajen iyayenta,suna matuqar ji da ita dakuma lelenta,hakanan suna gudun duk abinda zai bata ranta,safwa nada kyau dai dai nata,fara ce qal wanda hakan yasake qarawa halittarta ado,bata dawani kauri ko kadan,don haka bakayi kuskure ba idan ka kirata da siririya.

       Shekararta ashirin da uku,duka duka shekara biyu kacal abdul’azeez yabata,saidai yanayin kwarjini haiba da cikar saiffa yasa zakayi tsammani yabata shekara kusan goma ne.

       Tana masifar son abdul’azeez,don kusanma tafishi farinciki da hadin da akayi musu,duk da cewa tana qoqarin nuna darajarta ta mace,tana danne soyayyar da take masan,abdul’azeez yacika duk wani buri nata kan aure,hakan yasanya tariqeshi da dukkan iyawarta da dabarunta na diya mace.

       Balaifi,tayi tasiri a zuciyar abdul’azeez din,duk da miskilancinsa kan hanashi maida mata martani yadda yakamata,ita kuma hakan yana masifar takurata,soyayya takeso suyi tuquru bawai ta lalacewa ba,aah soyayya irinta turawa wanda ako ina basa iya boye abinda ke zuciyarsu.

       

       Mahaifiyarta na daya daga cikin jerin gwanon qawayen fulani aisha da tasu tazo daya,cikin burikanta na ganin ta gina rayuwar abdul’azeez din da ingantattun dirkoki tako wanne bangare yasa taga babu diyar data dace da abdul’azeez din sai safwa,tana yiwa mahaifiyarta tayi kuwa babu jinkiri ta amince da hakan.

      Akwai banbancin halaye da dabi’u masu yawa tsakaninsa da safwa,saidai dukkaninsu basu daukesu a wani abu can dazai kawowa relationship dinsu cikas ba.

“Abdul’azeez dakai nake fa?” Ammi tasake tambayarsa bayan wasu mintuna dayin shurunsa,dazai iya,dakuma zai yiwu daya gaya mata mawuyacin halin da yake shiga aduk sanda zaiyi doguwar hira da safwa,wanda wannan shine babban dalilinsa na qaurace mata

“Akwai dalili ammi,amma banyi saboda wata manufa data sabawa tsarinki ba….”

“To banaso,ban kuma son naji wani abu mai kama da matsala tsakaninka da ita”

“Ayimin afuwa,in sha Allahu za’a gyara” ajiyar zuciya tasaki,yana daya daga cikin abinda yasa take qaunar abdul’azeez,bai taba tsallakewa umarninta,idan ta nuna tanason abu yakan fita sonshi,baya yarda koya bari wani abu ya bata ranta akanshi

“Allah ya albarkaci rayuwarka,ya baka zuriya ingantacciya wadda zata bika fiye da yadda kake mana”

“Amin ammi,na gode”

     Ganin lokaci yadan ja yasanya ya haqure da fitar,yabarshi idan sufyan ya iso sa fita tare,sai yazarce sassansa don ya kwanta yahuta kafin sufyan din ya iso.

A nutse take karantar hauwa’u yadda tazauna tana dinke rigar dataketa saurin tasaka da zare da allura don kada ta makara makarantar Allo yaaya maigado tayi mata fada.
      Karo na wajen hudu dinkin yaqi yiwuwa tasaki rigar kamar zata sanya kuka,tausayin yarinyar yakamata,kusan dukka suturunsu akode suke hakanan a dangale suke ma’ana sun musu kadan,hatta da ita bata tsira ba,saidai dama dama itan,saboda tana da dabarar tattala kayan dakuma ware na fita dana zama a gida,bugu da qari kuma kayanta masu tsada ne wanda su take sawa a zamanin da anty zuhriyya na rayuwa kusa da ita,hakan shiya sauqaqa musu tasu kodewar.
      Sai a sannan ta tuna da kayan da umma luba tabata,koda bata sonsu dole tabasu su suyi amfani dasu tunda suna da buqatar hakan,kuma babu wata hanya data wuce tabasun,saboda haka ta sauke ajiyar zuciya,ta laluba inda tasakaya qullin wanda ba wanda ya taba taba kayan cikin yaran bare ya tambayeta meye a ciki,haka suke da wannan ladabin
“Kinga hauwa kulun majadan,ajjiye wannan kayan naduba miki wasu ki saka” ta qarashw maganar tana ware qullin,cikin zumudi hauwa ta aje kayan ta isa gaban qullin tana ware idanu akan kayan cikin murna
,bakin yarinyar ya kasa rufuwa,saidai batace komai ba tana dai kallon kayan har bilkisu tagama duba mata wadanda zasuyi mata dai dai tamiqa mata
“Saka mu gani” dasauri ta amsa tamiqe tasoma zurawa bilkisu na kallonta harta gama
“Ba shakka sutura itace mutum” bilkisu tafurta a zuciyarta,kayan sai suka haska yarinyar tasake wani kyau,ita kanta yarinyar kallon kanta da kanta take farinciki fal ranta,sai juyawa take tana dudduba jikinta
“Yaaya….gaskiya kayan nan sunyi kyau,kinga yaaaya sunmin kyau ko?”
“Sosai kuwa hauwata” sai kuma ta dakata da murnar da take ta dubi bilkisu
“Yaaya,dama ajjiyewa mukayi saida sallah ko?” Tausayinta yasake kama yarinyar,kusan su biyune ita da ita basu samun damar sanya sabbin suttura da salla,saboda daga ita har ita sun rasa dangin mahaifiya da zasu nuna musu kulawa,har gwara sauran akan kawomusu daga dangin mahaifansu koda ‘yar leda ce,aqalla kala daya ko biyu,ga zatonsu qarine kawai,mahaifinsu na musu,abinda basu saniba shine,ya manta rabon daya siya fallen atamfa wa yaransa,amma yakan iya hadawa bazawara lefe akai yabiya sadaki ya aurota yakawota gidansa.
      Saita soma daure kayan tana bata amsa
“Saka abinki,kita addu’a da salla nayi miki ko guda daya ne kinji?” Fuskar yarinyar ta washe ta nuna zallar farincikinta
“Aikuwa kullum ina miki yaaya,amma zan sake dagewa”
“Yauwa kuluta” cikin farinciki da walwala tatafi makarantar allon tana cewa yau duk makarantar babu mai irin kayanta.
       Sai data gama duk abinda zatayi sannan tazauna,umma luba bata nan,ta gaya mata zatayi kwana biyu a gidan aikinta,asabar da lahadi,to itadinma yau yazama ranar hutu a wajenta,babu makarantar boko babu zuwa wajen aiki,saboda haka tayi kwanciyarta cikin daki tadauko litattafanta na makarantar dare tasoma bibiya.
       Bata fita ba saida fitsari ya matsota sannan ta aje littafin tamiqe tazura hijabinta kafin tafitasaboda tasan koda yaushe ba’a rasa mutane cikin gidan nasu.
      Tana fita hasken fentin da ake shafawa ginin da aka kammala daga gefe guda na tsakar gidan nasu ya haske tsakar gidan tarwai,baka ganin komai sai qyallinsa da qamshinsa,idan aka dauka maka hoto na sashensu da sashen da ginin yake saika rantse da ubangijinka cewa gida biyu ne bawai dukka ginin suna qarqashin gida guda bane.
      Duk yadda taso dauke kai kamar yadda tasaba amma sai data maida idanunta ga mahaifinta daketa faman fara’a yana hira da masu fentin,tunda aka soma aikin ginin ya sallamawa fita ya tare gindin ginin,ya zazzage duka kudadenshi da yake boyo da mammaqo akan ginin,ya saba wannan ba farau bane kanshi,kusan duk sanda zaiyo sabon aure hakance take kasancewa,saidai wannan karon kamar abun na daban ne,da alama ita wannan din tafi duka sauran nabaya da aka auro wayewa.
      Saita tuna awa guda baya data wuce yadda akayita tababa dashi kan yabada kudin sukari azuba akunu yara susha,har yake kumfar bakin bashi dako asi,yana ganinma yayi qoqari da ayau xai ciyar dasu abincin safe rana harma dana dare
“Nifa matsalata dake kenan katti,baki da godiyar Allah ko kadan,duk fadi tashin da mutum yake akanku da zarar yace zai raya sunnar ma’aiki saiki tattaro dukka bala’in duniya da tsangwama ki aza masa,ina laifina ma da aka samu qwayar hatsin da za’aci din?” Hannu ta tafa baqinciki na ciciyar ranta,ta rasa me yasa wannan karon auren nashi yafi ci mata rai fiye dako yaushe,kodon yadda yaketa rawar qafa ne oho
“Tsakanin ni dakai ai za’a gane wanda bashi da godiyar Allah,kai har kana da bakin magana ma?,ai wallahi idan dakunya a idanunka malam baka data cewa” saiya miqe yana karkade rigarsa yana cewa
“Saikiyitayi ai,idan kunso karkusha kunun ku zubar” yasanya kai yafice abinsa,bayan tana ganin sanda ya aika umaima tasiyo masa nashi sukarin na talatin yajuye dukka cikin kunun yashanye abinsa.
      A sanyaye taci gaba da takawa zuwa rubabben bandakin nasu dayake matuqar buqatar gyara amma yakasa sanya masa koda kwano daya na sumunti ayi masa kwaskwarina,gashi yayi gini sukutum da guda,a maimakon ayi musu kara ahada da bandakin a gyara amma sam su basu da wannan darajar,umma katti kuma tun kafin sannan ta rantse ta maya silai biyar ba zata sanya ta gyara bandakin ba,qatti suda ubansu suzo su dinga tsugunawa,kowa ya karba a haka.
      Koda tafito dakin nasu tasake komawa ta kwanta,tajawo littafin da niyyar ci gaba da karatu saidai wannan karon karatun ya gagara,tilas ta ture littafin gefe,ta gyara kwanciyarta sosai,saita fada cikin duniyar tunani,wanda duka tana tunanin makomar rayuwarsu ne ita da sauran ‘yan uwanta.
     Hakanan taci gaba da kwanciya har suka dawo sukaci abincin rana suka wuce islamiyya,wanda wani malamine cikin layin nasu yadaukesu kyauta fisabilillahi,gidan yau tamkar sallah yake a wajensu,saboda yadda akaci aka qoshi abinda suka jima basu samu ba.
     Bayan sallar la’asar yaro yayi sallama 
“Wai ana sallama da bilkisu” kalmar tashiga kunnenta,duk da tana kwance sai data miqe tazauna sosai tana kasa kunnenta dakyau waiko bataji dadi dai bane
“Kai….kace tana zuwa” caraf mahaifinta ya bada amsa ba tare daya damu da tambaya ko bin diddigin wanda yake sallamar da ita ba.
      Ba’a rufe cikakken minti daya ba ta tsinci muryarshi yana qwala mata kira
“Me gado!,ke me gado!!” Ba shiri ta yayibi hijabinta dake aje gefanta ta yafa tafito.
      Saman jarka tasameshi zaune riqe da kwandon wanka,da alamu ma wankan yake da shirin shiga amma yafasa
“Maza jeki waje ana sallama dake….kya sama mana ma abun cefanen gobe,don gaskiya aljihuna ya gaza,mawuyacine asamun na tuwon gobe,gashi tattali nake kafin zuwan amarya,kada tazo ya zamana babu komai a hannuna” kamar an dasata a wajen haka tayi shuru tana juya maganarsa,shi abinda ma yadameshi kenan?,ba damuwarsu bace tashi damuwar,abinda yadameshi daban,nashi tunanin daban?,bata taba tunanin ya taba kwana da matsalarsu da har zai tashi da ita ya sanyata cikin jeri da lissafin matsalolinsa
“Tashi mana ki wuce kije a’ah,kijimin yarinya anata maganar kamar kurma” maganarshi ta dawo da ita daga duniyar tunanin data tafi,kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki haka takoma bakin qofar dakin nasu tadauki takalmanta tadurfafi qofar gidan tana tunanin waye wannan haka?.
     Tunda ya hangi tahowarta ya zuba mata idanu yana dubanta,saiya tuna ranar farko da yaji matasan layin nasu suna wassafa halittarta da tsarinta,tashin farko yaji wani susa cikin ranshi,yayi hanzarin dauke idanu lokacin da take gab da isowa inda yake.
      Idanunsa yalumshe lokacin da tayi masa sallama,ba shakka muryar ta dace da mamallakiyarta yafurta a zuciyarsa kana ya amsa mata yana daidaita nutsuwarta,kallo daya tayi masa ta sadda kanta qasa bayan ta furta masa kalmar
“Ina yini” saboda yadda taga kamalarsa ta banbanta data sauran wadanda take gani,hakanan bata sanshi ba,bata taba ganinsa ba,bata kuma san me yake nema a wajenta ba,da fari ta tsammaci hamxa ne yadawo daga tafiyar da ya aiko mata da saqon zaiyi,amma ga mamakinta sai taga sabanin hakan.
       “Malama bilkisu,ina fatan ban miki dirar mikiya ba….,ina neman afuwar zuwana ta wannan siga,duk daba haka naso ba,naso na fara neman izini daga wajen baba kafin nakai zuwa gareki,sai zuciyata ta kasa haqurin hakan,karna cikaki da surutu da yawa,da farko dai ni sunana abubakar saddiq,haifaffen garin nan mazaunin unguwar daaba,wani uzurine yakawoni nan unguwar taku cikin layinku naganki,kuma lokaci daya naji kinyimin…dalili kenan dayasa na kasa nutsuwa harsai danasan wacece ke” kalmarshi ta qarshe ya sanyata daga fararen idanunta takalleshi dasu,bata fahinta ba,don kawai yana sonta saiya samu lasisin bin diddigin rayuwarta?,akanme?,bayan ita batasan da wanzuwarshi doron qasa ba?,ita batasan meke birgesu dangane da ita ba,bataga abu ko guda daya ba,amma su sun damu cukurkudaddiyar rayuwarta,amaimakon sun qyaleta da aikin warware rayuwartata tamiqe kamar takowanne mutum,saisu sake aza mata wani nauyi na daban da take kallonshi a amtsayin abinda xai sake tauyeta.
     Saman fuskarta ya karanci kaman ta amshi xancan nashi abaibai,saboda haka yasake mata qarin bayani
“Sai dana binciko gidanku dakuma lokuttan dazan sameki,ina fata zaki karbeni hannu bibbiyu kamar yadda zuciyata tashin farko ta amsheki” nannuyar ajiyar zuciya tasauke kai kace tseren gudu tagama,ita duka bata fahimci ma me yake nema ba,amma a iya qaramar fahimtarta kamar yanason yace mata soyayyarta yake nema?.
       Yakamata zuwa yanzu bakinta yasoma buduwa,tadinga bude baki tana bayani wa duk wanda yazo da quduri makamancin wannan a kanta,cikin lallausan muryarta da tayi kama da wanda yajima shuru ba tare da yayi magana ba tace
“Ni bana soyayya,kayi haquri don Allah” ga mamakinta murmushi saki lokacin da take yunqurin komawa cikin gida
“Dan tsaya mana malama bilkisu” saita tsaya cak ba tare data waiwayo ba,yasake dawowa bangaren da zata iya ganin fuskarsa sosai yace
“Ni ba sauri nake ba,kuma ba gaggawa nake ba,inason ki bani dama mu fahimci juna na wani lokaci tukunna kafin ki yanke hukunci,zuwa lokaci na yadda dukka hukuncin da zaki yanke din daga zuciyarki yafito,ba kamar wanda kika yanke yanzun  ba” tana qoqarin sake wuceshi yafidda kudi daga aljihunsa yamiqa mata
“Ga wannan ki karba don Allah” duban kudin tayi sannan ta dubeshi,duk wanda zai mata kyautar kudi a yanzu gani take kamar ya raina inda tafito ne,abinda yaduba kenan yadauki kudi yabata,saboda haka kamar yadda tasaba saita girgiza kai tayi shigewarta cikin gidan da hanzarinta.
*_wannan littafin na kudine,kuma amana ce a hannun duk wanda yasiya,idan kina da buqatar siya kema,ki tuntubi wadan nan lambobin donki siya ki karanta cikin aminci_*
0903 234 5899
Ko
09033181070
      “Kai amma bansan kana haifar yaro dan baqincikinka ba sai yau,yanzu ke don tsohuwarki ina da buqatar kudin nan yaron nan yabaki kudi kiwuceshi kamar yabaki kashi?,to tun ranki bai baci ba ki koma ki karbo kafin yayi zuciya yawuce da abinsa” muryar mahaifinta kenan data mata dirar mikiya lokacin data fado tsakar gidansu,mamaki yasata tsaiwa kamar an dasata,kenan yana labe yana kallo da sauraren dukka abinda ke faruwa?
“Ba zaki koma ba!” Yafada cikin kurari da hargagi kamar mai shirin bugunta,hakan ya bata tsoro daya sanya ta juya a sukwane tana tsara yadda zata kubcewa qudirinsa,sai sukayi karo da yaro hannunshi riqe da kudin
“Wai gashi a baiwa bilkisu inji saddiq,wai yatafi” kafin yaron yadire sauran kalaman bakinsa tuni malam bilya yayi caraf da kudin cikin hannunsa yana cewa
“Yaro jeka,kaima Allah yayima albarka,da ina da naira biyar dana baka” yayi maganar yana irga kudin,sum sum ta gotashi tawuce daki,bata iya tsaiwa baqinciki da takaici fal ranta,tana baqinciki da takaicin halayen mahaifinta,yana girmama kudi fiye da komai,shin yaya rayuwar qannenta zata tashi nan gaba?,wannan dalili yasa ta maida hankali qwarai wajen cusa musu kyakkyawar tarbiyyar da take da yaqinin zata kama gangar jiki da ruhinsu matuqa.
       “Kai kai,kan uban nan,kyautar naira dubu biyar cas lokaci guda?,ah….lallai mai gado hasashena na cewa zaki zama mabudin arziqina yazama gaskiya,ina kika samo wannan yaron?” Ita baki daya kunya yake bata baya ga mamaki,saita gaza amsa masa sanda yaje matsowa bakin qofar dakin yana jiran amsarta,wanda muryar umma katti data fito daga daki dauke da kwanuka ta gasa masa harara takuma ce
“Andaiji butur wallahi,anan kafi kauri,ka gama daijin kunya” kusan tunda sabon ginin dake cikin gidan ya kammalu duk wani kuzari nata da karsashinta ya ragu,bacin ranta yadadu
“Ke wa yake ta tataki,aike yanzu allurar kishi ce take damunki,kuma haka zata gama motsa mikin ki kuma haqura” saiya bar wajen ya dauki botikinsa daya cika da ruwan wanka yanufi bandaki yana sake bude sabon babin mita da manufa biyu,yasan taji nawa yasamu,kada tasamu fuskar tambayarshi wani abun
“Ruwan wanka ma a matsayinka na miji an mance rabon da akai maka bare na alwala,Allah dai ya sawwaqa,wannan ba dole ka nemo mai maka ba” maganar data tunzura zuciyar umma kattin kenan tahau sababin bala’i itama,itadai bilkisun tana jinsu,tun maganar tata bata cika mata kunne ba harta dameta,saboda haka tamiqe tahau rakito ayyukan da ada babu su cikin dakin,sam sai taji ashe fitar da take aiki ko makaranta rahama ne,da batasan yaya zaman gidan xai kaya mata ba.
      Sai yamma lis su hannatu suka dawo daga islamiyya,tana zaune suka shigo,saita lura fuskar hannatun ita da hauwa’u fal take da bacin rai,da kallo tabisu kana daga bisani tace
“Lafiya?,hauwa’u me yafaru?” Cikin fushi hannatun tamiqawa bilkisu wata ‘yar guntuwar takarda,saida bilkisun ta karba ta duba,sai taga sunan wani littafi ne na koyon larabci ajiki
“Meya faru?” Muryarta na nuna zallar bacin ranta tace
“Tun rannan malamin ajinmu yake mana bulala saboda bamu dashi,bamu nuna miki ba saboda baki da kudi yaaya,sai yau muka nunawa baaba koxai siya mana,waisai yace mutafi mubashi waje bashi dakudi,ko mukai miki ke zaki siya mana,wai baaba komai mukace yasiya mana sai yace bashi da kudi yaaya?” Kafin takai ga saisaita tambayar yarinyar akanta hauwa’u ta jeho mata wadda tafita nauyi
“Wai baaba bashine ya haifemu ba?” Sai tambayar hauwa’un tafi jan hankalinta akan ta hannatu,duk da qarancin shekarunsu hakan yana nuna halin ko inkula dayin biris dasu da yakeyi yana ci musu rai kenan?,kuma suna sane da komai,bata fuska bilkisun tayi tana duban hauwa’u,alamun maganar bata mata dadi ba,tuni yarinyar ta karance ta,don haka tadora
“Kiyi haquri yaaya,baaba baya mana irin abinda abbansu nawal da abbansu amira yake musu,su komai sukace sunaso abbansu yanayi musu amma banda mu”.
     Ajiyar zuciya tasauke tadubi hannatu dake tsaye
“Zauna” tace mata,saita zauna din,yanayin fuskarta yasanya yaran duka suka nutsu,tasoma magana cikin sigar lallami da kwantar da murya
“Baaba yana sonku kuma shiya haifemu gaba daya,abinda yasa kukaga baya mana komai saboda bashi dashi ne,kafin ahaifeku baba yana mana komai,yanzune bashi da kudi,kunga kuma dole muji tausayinsa ko?,duk sanda kukayi sallah kudinga masa addu’a,Allah yabashi kudi,Allah yasa yadinga muku abinda kukeso,amma daga yau banason in sake jin hira mai kama da wannan,idan nasamu kudi nan da kwana goma zan siya muku littafin,kuyi haquri kunji?” Duk suka gyada kansu,saidai da alama bayanin data musun bai gama ratsa su ba,don haka ta bagarar da zancan ta hanyar cewa
“Kowa yaje yayi alwalar sallah magariba,yau muna gama cin abincin dare zan muku tarihin sahabbai” sai kuma duka suka warware cikin murna da farinciki,don suna son tarihi sosai,tasaki murmushi sanda suke fita,saita sauke idanunta kan kwanon abincinsu da yake tazarce wanda duka umma katti ta gwamutsasu ta hado musu na dare da rana,ba tare da la’akari da zai ishesu ba ko kuwa a’ah.
Rashin samun damar malamin na halartar darasin sa a ranar yasanya daidai period din ajin yazama dandalin hira ga daliban,duk da cewa yawanci koda malami bazaizo ba to akwai wanda zai riqe mishi hissarsa ta ranar,to amma yau hakan bata samu ba,kasancewar yau da gobe sai Allah,hakanan tafi gaban wasa.
        Rukuni rukuni ne na dalibai kowa ya kama dabarshi,wasu na saman wajen rubutu wasu na kan kujerunsu na zama,kusan group din afnan Abdallah mu’az yafi kowanne cika da yawa,saidai kana dubansu kasan kowacce tana jine da kanta,duk da hira suke haiqan amma babu wata hargowa a ciki,duk wannan abun da ake bilkisu na saman nata kujerar karatun,ta dora kanta saman wajen rubutu takwantar tamkar mai bacci,saidai ba bacci take ba,littafi ne a hannunta tana nazarin c.a da za’ayi musu a gobe.
      Duk yadda ta maida hankalinta ga karatun hakan bai hanata jiyo hirarrakin group din afnan ba,kusan kowacce tana bada labarin yayyenta maza ne na gida da sauran abubuwan daya shafesu,afnan din tana tsakiya batace komai ba sai binsu da kallo da take tana kuma saurarensu,yayin da wani tsagi na hankalinta kuma jifa jifa yake kan bilkisu,haushinta na kamata,itakam tana mamakin yadda mutum yake iya rayuwa baya magana,yadda mutum yake iya rayuwa shi kadai,babu ‘yan uwa ba abokai bare qawaye,ta tabe bakinta lokacin da hanan tace
“Princess baki bamu labarin naki yayun ba,nasan it will be sweeter than ours” wani murmushi tasaki tana tuna miskilin yayan nata,ya azeez mai aljanun miskilanci,miskili kafi mahaukaci ban haushi,sa baka dariya sai hamma tatuna wasu daga cikin kirarin da ammi kan masa musamman idan yabata haushi
“Yayana guda daya ne,prince abdul’azeez” ta qarasa maganar cikin nuna alfahari,sautin muryarta na cike da nuna qauna da kulawa ga dan uwanta,da kuma wasu alamu dake nuna tana matuqar ji dashi,sai dukka suka sake bata kunnuwansu,don dama bata taba musu wata magana makamanciyar wannan ba,kowa ya zaqu yaji me zatace
“Uhmmm….tell us about him” hanan da kusan tafi kowa zaquwa tafada tana murmushi.
“Komai zance akan yaa prince na dabanne kamar yadda yake na daban,i have never ever seen mutum kamarshi,shi na musamman ne koda cikin gidanmu ma,tun daga yanayin halittarshi zuwa attitude nashi,kyakkyawa ne yayana,har wataran nakanyi buri dama nice nake da kyanshi” zaro idanu hanan tayi tana cewa
“Wow!,duk yadda kike din nan afnan?” Kaita gyada tana dubanta
“Yes,kyansa ba irin nawa bane,ya hade da kwarjini,kinga banson miskilancinsa,i hate miskilanci”sai kuma tayi shuru tana duban bilkisu a sace,wanda ta tabbatar bilkisu taji abinda tace
“Yana iya wuni shi daya,koda yana cikin mutane kina iya irga maganan da yayi qwara nawa ce,mma duk sanda naso inyi masa mita ko qorafi….u know what?” Duka sai girgixa kai
“Daya kalleni saina kasa cewa komai,there is something special in his eyes,kwarjini….yayana badai kwarjini ba”
“Wow…wow” hanan tasoma fada tana tafa hannayenta kana tasake matsowa gaban afnan sosai
“Pls friend….ki bani yayan nan naki mana,wallahi har naji nakamu” ihu duka wanda yake team din yasaki wanda yashiga har tsakiyar kan bilkisu,ta runtse idanunta don sam batasan hayaniya,saita kifa littafinta saman kan nata,amma duk da haka bata tsira daga jiyo cecekucensu ba,kowacce tana fadin saidai ita.
     “Wait…..relax ‘yammata” afnan tafada tana duban kowaccensu
“He already taken out” duka sai sukayi shuru suka zuba mata idanu,yayin da itakuma take murmushi
“By who?”
“Miss Safwa ibrahim khalilu attah”
“The attah’s daughter?” Humaina daya daga cikinsu tambaya tana zare idanu,waiwaya afnan tayi ta dubeta sannan ta kada kai
“Qwarai” saita sauke ajiyar zuciya tamaida jikinta ga kujerarta tana cewa
“ƙarshen magana?”
“Kaman yaya?” Hanan ta tambaya da alama maganar batayi mata dadi ba
“Zan gwada sa’ata indai zaki hadamu” tasake cewa da afnan,dubanta tayi kana tace
“Da zan baki shawara dasai nace its better ki haqura,nasan ya azeez farin sani,daya daga cikinmu ina da yaqinin ba zata taba burgeshi ba,nasan halayenshi da tsarinsa,even safwa ammi ce ta hadasu…,bayaga haka ma….ya azeez hanan am sorry to say yana da tsada mai yawa,tun a yanzunma da yake da shekara 25 ya kike tunanin gaba,he’s belong to mata masu aji da tsada,ina da tabbacin zai rainaki ne saboda yana da kamar safwa….duk fadin makarantar nan wa kike tunanin tafi kowa kyau?” Dukkaninsu kuma lokaci daya idanunsu yakai kan bilkisu,hakanan cikin jikinta taji idanuwa barkatai a kanta,hakan yasa lokaci daya taji wata irin tsarguwa da takura.
        Dariya afnan tasaki saboda ta karanci inda suka maida hankulansu
“Koda za’a maidata cikin sahun wasu a duniya,banajin zatayi attaracting dinshi…he’s diffrent kamar yadda na gaya muku a baya”.
       Tsam bilkisu tamiqe bayan ta aje littafinta tasoma ficewa daga ajin,don gaba daya hirar tasu tasoma gundurarta duk da bada ita akeyi ba,amma ta fuskanci wasu al’amuran an soma jefata a ciki wanda ba huruminta bane.
       Bata dawo ajin ba har sai data tabbatar malami yashiga sa’an nan takoma,ta tattara hankalinta dukka kan karatun,saidai wata sabuwa kuma,yunwar dake sakadar cikinta ta hanata fuskantar wasu abubuwan,saboda jiya abincinta su hauwa’u ta barwa,don a jiyan baban nasu baiyi cefane ba,da safe ma bata samu abinda zataci ba,amma yau tana saka rai,saboda umma luba tadawo zata leqa gidanta aiki,a haka taci gaba da daurewa har lokacin tashi yayi.
      A gajiye tulus ta isa unguwar tasu,kamar ko yaushe ta karya layinsu cike da fargabar yau kuma wanne sabon abu zata tarar a gidan nasu.
      Karaf kuwa sai idanunta suka sauka kan ‘yar qurqurar anata sauke kaya da sukafi kama dana jere ana shiga dasu cikin gidan nasu,hakanan gabanta ya yanke yafadi,baban nasu bazaidai haqura ba kenan,tunda yadaura niyya sai yayi kamar yadda yasha maimaitawa kullum kwanan duniya?.
      Jiki a salube ta isa qofar gidan sanda masu qurqurar suka tasheta da niyyar qarawa gaba,tafidda wani dunqulallen farin hayaqi daya wuce kai tsaye zuwa hancin bilkisu,ta shaqeshi har huhunta,wanda a take yasake murda mata ciki yakuma tashi yunwar dake sakadarta.
       Tana shirin shiga gidan saiga umaima da bushira dauke da babban faranti,samansa kwanuka ne jere reras a kai,idanu tazuba musu tana dubansu har suka qaraso,take ta fahimci daga ina suke,ranta yabaci qwarai,ta tsuke fuska tana dubansu sannan ta jeho musu tambayar 
“Daga ina kuke?”
“Umma kattice tace mudaukar mata abinci mu zaga mata dashi yau bazata siyar a gida ba” cikin bacin rai ta daka musu tsawa tana dubansu
“Talla?,tallah umaima?,mena gaya muku game da talla?,” shuru sukayi dukkaninsu,jikinsu yayi sanyi sosai,a rayuwarta babu abinda ta tsana irin tallar diya mace,ta yarda suyi dukkan wani aikin wahala a biyasu amma banda talla,tallan ma yara qanana kamar umaima da bashira da basu gaza shekara takwas goma ba?,kawai saita isa gabansu ta debe kwanukan daga kansu tamiqa musu jakar makarantarta tanufi cikin gidan suka rufa mata ba.
     Bayaga sallama bata qara kan komai ba,saboda ranta dake bace hatta masu jeran amaryar baban nasu ma bata duba ba,wanda bakajin komai cikin gidan sai karadinsu,ga kular abinci da lemon roba baja baja da alama sunci sun hantse,sai data isa qofar dakin umma kattin sannan ta aje kwanukan gabanta,suka dakata daga hirar da suke ita da baquwarta da alama tana labarta mata abinda ke faruwa ne
“Ina kudina?” Abinda tasoma tambaya kenan tana miqawa bilkisu hannunta,saita waiwaya kawai ta miqawa itama su umaiman hannu,sunsan mai take nufi,don haka suka miqa mata kudin tamiqawa umma kattin taja hannunsu,bata tsaya jin mitar da take ba nasun dawo mata da saura,hala ma hamshaqiyar yayar tasu ce ta hanasu.
       Duban umma kattin baquwar tayi
“Wai wannan ma diyarsa ce?” Tabe baki umma katti tayi cikin takaici
“Hmmm,aiba lallai harki tafi ki gama shaida yaransa ba,don wasu ma basa garin sun bazama neman kudi”
“Amma kuwa tubarkalla ma sha Allah da ita,ashe yana da zankadediyar yarinya har haka?,wannan wallahi dazai bada ita akai aikatau ba qaramin kudi zaku samu ba” baki umma kattin tariqe
“Rufani ki sayani,wannan da kike gani da qanwar uwarta na kusa ma ba lalle kiganta a gidan nan ba,donma uban ya kafe kai da fata aida tuni bata a nan” nan tadan labartawa baquwar tata wani abu game da bilkisun.
       A daki kuwa dukkaninsu sunyi shuru suna kallonta saboda ba kasafai suka fiya ganin fadanta ko bacin ranta ba,saiduk kowa jikinsa yayi laushi,don bacin rai bata bi takan danqararriyar dafa dukan da aka aje mata ba ta daura zani da hijabi tashiga wanka,sai data fito tasanya wata doguwar rigar atamfarta da itama tasoma nuna gajiyawarta sannan taja abincin ta tsakura
“Ku tashi ku shirya mu futa gaba daya” ta basu umarni sanda tature kwanon tanajin taste din bakinta babu dadi.
     Daga shigowarta zuwa yanzu cikin gidan anyi guda anyi habaici har batasan sau nawa ba,sai taga haqurin umma katti yau daya da bata tanka musu ba duk da rashin haqurinta,kuma wala’alla baquwartace ta hanata.
     Bata bar gidan ba duka sai data kada kansu takaisu har qofar islamiyya suka shiga sannan tawuce gidan umma luba.
******   ******
“Yar halak,yanzu nake zancanki balaraba kinganta ta iso” cewar umma luba dake zaune qasan rumfar dake qofar dakinta tamiqe qafafunta,gefanta wata matace wadda a qalla zasuyi shekaru guda itada umma luban,murmushi bilkisun tayi ta qaraso gefan shimfidar ta zauna tana cewa
“Ina hanya ai,makaranta,yau banyi sauri a hanya ba”
“Aiko tunda nadawo na kasa kauda koda tsinke ina zaman jiranki” murmushi kawai tayi wannan karon,ta gaida umma luban kana ta waiwaya da niyyar gaida baquwar tata,sai suka hada idanu,tun dazun da alama bilkisun take kallo,tadan kauda kanta itama bilkisun haka,ta gaidata ta amsa cikin sakin fuska,daga haka bilkisun tamiqe tasoma aikinta.
Duk giftawar da zatayi idanun matar yana kanta.
      “Nikam lubabatu ina kika samo wannan yarinyar haka?” Baquwar ta tambayi umma luba
“Wai bilkisu?,can qasanmu take wallahi”
“Amma kinyi sa’ar yarinya ta iya aiki,saidai nayi mamakin yadda take dakyau haka luba amma aiki take”
“Wallahi balaraba,halin rayuwa,amma banda haka bikisu ai tafi kyau da babban gida,nikaina wani lokaci nakan kalleta na qara,a haka ma wai don bata kwalliya,kullum haka dai zaki ganta cikin tsummokaran kayanta”
“Ma sha Allah,gaskiya Allah yayi mata baiwa,wannan kyanta tasamu wani babban gidan ko wani babban mutumin yayi wuf da ita” dariya umma luba tasaka
“Tunanina da naki ya zama daya,yanzun duk wannan kyan idan ba’ayi wasa ba saiya tafi a banza,saikiga wani qaramin yaron daga can cikin loko ya kwashi garabasa,bayan matar manya ce” qarasowar bilkisu wajen yakawo qarshen maganar tasu.
       Batafi awa biyu ba baquwar tayi musu sallama tatafi,saiya zamana daga bilkisun sai umma luba,bakin umma luban baya shuru,bata taba iya zama haka,haka tadinga jan bilkisun da hira kamar yadda tasaba,yau kusan duka hirar tata kan yariman kaisa ne,maganganun afnan na daxu zuka dinga dawo mata,kusan maganganun saunyi daidai da nata,sam hirar bata wani bata sha’awa ba,ita da zatayi shuru da bakinta tabarta ma tayi tunanin yanayin da gidansu da rayuwarsu zasuci gaba da kasancewa da yafiye mata wannan hirar.
       Gab da magariba tagama komai da komai,saita sanya hijabinta tana yiwa umma luban sallama
“A’ah,bazaki tsaya kici abincin ba?” Murmushi kawai tayi,umman tasanta da alkunya,wala’alla tanaso amma bazata iya tsaiwa ci ba,saboda haka tace mata
“Dauki kwano ki diba kyaci a gida”.
☀️☀️☀️☀️☀️☀️☀️☀️☀️☀️
      Sanye yake cikin wata jibgegiyar rigar sanyi baqa wadda taqara mishi qiba sosai,saidai ta masa kyau ainun,an nata wani irin adon zane da jan zare wanda yasake qara mata qawa,abun mamakin duk sanyin daje busawa a wajen yasaki hular rigar baya,bayan kanshi babu komai sai gyararriyar sumarshi daketa qyalli.
       Wandon jikinsa sosai yadace da rigar jikinsa,sai rufaffen takalmi hightop wanda yasake qawata adon nashi.
         Shi dayane zaune saman table din,gabanshi kwalabe ne na lemuka guda uku da kofuna guda biyu,duk da cewa darene amma wajen tarwai yake da haske kamar kayar da allura kuma kasunkuya ka dauki abarka.
        Kallo daya zakayi mishi kasam cewa ranshi a bace yake,yazuba lemon yasha shi kansa baisan adadin kofi nawa bane.
        Kusan dukkan yarinyar dake wajen babu wadda bai dauki hankalinta ba,matane kala kala a wajen birjik nau’in yare daban daban,kama daga turawa larabawa ‘yan africa da ‘yan asia,saidai akwai wani babban abu dake hanasu qarasowa inda yake,kwarjini!,kwarjininsa yacika wajen gaba daya,hakanan ya dusasar da kyau da qasaitar duk wani namiji dake wajen.
        Ajiyar zuciya tasauke mai nauyi tana duban wayenta guda biyu
“Friends….gaskiya banjin zan iya haqura dashi a yau,nayifa qoqari,watanni nawa ina faman boye mishi kaina,haqurina ya qare,ya kamata na bayyana mishi kaina,sonshi yayimin yawa a raina,kullum cikin mafarkinsa nake,ya kamata koyaya nashiga jikinsa” cewar wata farar budurwa ma’abociyar tsayi,saidai matuqar kana wajen zakayi mamakin jin yaren hausa na fita daga bakinta,saboda kallon farko idan akace ka yanke mata addini ko qabila ba zaka taba dangantata da qabila ko yaren hausa fulani ba,caraf takusa da ita ta riqe mata hannu
“Minal….kibi a hankali,bakisan waye prince ba shi yasa kike tunanin tunkararsa kanki tsaye” zame hannun nata tayi tana miqewa 
“Na sani,nasan ba ordinary bane kamar sauran samari da muka sani,anyway zanje na tareshi yau komai ta fanjama fanjan,tunda shima mutum ne ai kamar kowa ko?” Tafada taba dage musu gira,sun fahimci me take nufi saboda haka suka sheqe da dariya gaba dayansu itama tana tayasu,kana tasoma takawa tana nufar inda yake zaune cikin wani salo da sauya tsarin tafiyarta.
      Abun haushin shine harta isa baimaga tahowar tata ba,wannan karon harya miqe tsaye yana duban agogonshi bisa dukkan alamu tafiya zaiyi
“Hey!” Ta fada a hankali lokacin da take tsaye dab da bayanshi,a nutse yawaiwayo sai suka hada idanu,take murtikewar fuskarshi ta ninka yadda take ada
“Ina fatan ban matsawa prince ba ko?” Tafada tana jifanshi da wani shu’umin murmushi gamida dan kada jikinta cikin dabara,har yanzu dai dubanta yake ba tare daya amsa mata ba,hakan kuma ita yayi mata,saboda haka still tana murmushi tamiqa masa hannunta
“Am minal abdulhamid” hannun nata yabi da kallo wanda sukaci fixing na faratan ‘yan kanti zaqo zaqo dasu,sa’an nan aka bisu da jan farce aka lullubesu dasu,sai qyalli suke zubawa.
      Dauke idanunshi yayi yamaida cikin nata,wani kallo daya sanyata faduwar gaba,da kanta tasauke hannun nata ganin yana niyyar qagewa ba tare daya maida mata martanin gaisuwarta ba
“Kaman baka da interest da gaisawa da mata b…..”
“Hey!” Yafada cikin kaushin murya
“Getout of my sight” yafada calmly kamar bamai bacin rai ba,murmushi tasaki itama kamar maganar tashi bata dameta ba
“Calm down yarima…..niba fada nazo muyi ba,nazo ne…..”
Wani mugun tsaki yaja wanda har sai daya janyo hankalin mutanen dasuke daura dasu,dukka suka waiwayo suna dubansu,hannunshi yasanya yadauki wayarshi yasoma takawa don barin wajen.
       Gaba daya sai taji ta muzanta yadda aka zuba mata idanu,har kamar ma sauti sautin dariya take jiyowa daga wani sashe na wajen,ranta taji ya sosu,cikin kunya da sagewar gwiwa tasoma tattaki don barin wajen itama,saboda yariga daya gama kunyatata har a gaban wadanda take daga musu kai,bataga sauran abun zama tayi ba kuma
“Batasan waye prince bane” sanda tazo gifta wasu ‘yammata fararen fata taji sun furta cikin harshen turanci,batako waiwaya ta dubesu ba saboda idanunta da suka cika da qwalla taci gaba da fita daga wajen.
       Tana isa farfajiyar wajen abdul’azeez na ficewa da motarsa daga wajen da gudu,sai tabi motar da kallo tana jin ciwon ran abinda yayi mata,tunda take ba’a taba yarfata irin haka ba,amma taci alwashin saiya kawo kanta gareshi sai yadda ta juyashi.
        Tsararriyar unguwa ce mai kyau da tsari kamar yadda mukasan yanayin unguwannin qasashen qetare suke,gaban wani qayataccen dan madaidaicin gida yayi parking motar tasa cikin sauri yakasheta,bai damu yada kulleta ba yashige cikin gidan.
      Spare key din dake hannunshi yasanya yabude qofar yatura yashiga kamar wanda wani abu ya biyoshi.
       Matsakaicin falone wanda bai cika girma ba can,saidai kuma ya qawatu da kayan alatu iri iri cikin tsari da burgewa,saman daya daga cikin kujerun wani kyakkyawan matashine,saman cinyarsa wata matashiyar budurwa cikin qazamtacciyar shiga suna sumbatar junansu,da alama sun soma nisa a duniyar da suka lula,amma qarar bude qofar da abdul’azeez yayi yadawo dasu hayyacinsu.
      Cak ya tsaya yana watsa musu wani irin kallo daya sanya yarinyar cikin rawar jiki sauka daga kan cinyar saurayin,sannan cikin rawar jiki tasoma tattare ya nata ya nata tun baice komai ba ta lalubi qofa ta fece,yayin dashi kuma idanun abdul din suka masa nauyi,amma saiya waske kawai yahau yarfar da hannu kana tamiqe yana maida botiran rigarsa,yabude baki zaiyi magana abdul’azeez ya rigashi cikin bacin rai da kaushin kurya
“Kamal….sau nawa zan gaya maka?,sau nawa zan gaya maka kamal?” Cikin dan daure fuska wanda ake kira da kamal din yayi taku biyu yasake matsowa gaban abdul 
“C,mon haba prince,waime yasa kake babu kamar ba wayayye ba,kana da matsala wallahi ka cika kwafsawa mutane….” Kanshi yanuna da muqullin motar dake hannunshi
“Nine ma nake kwabsawar?” Saidai kafin kamal ya bada amsa an turo qofar falon an sake shigowa da sallama,duk cikinsu babu wanda ya iya amsa sallamar sai carko carko da sukayi,abdul’azeez naci gaba da fidda hucin bacin rai.
       Matashine shima wanda a qalla zaiyi shekarunsu ya qaraso yana dubansu
“Weting d hapin guys?,kuka tsaya kamar zakaru?”maimakon amsa sai abdul’azeez din ya maida idanunshi kan kamal
“Na baka awa daya,ka tattara komai naka kaficemin daga gidana…”
“Ah….kamar yaya?,meya farune?,azeez!….tsaya mana” matashin daya shigo yanzu yasoma yunqurin tsaida abdul’azeez wanda tuni yayi hanyar corridor din da anan dakin gadonshi yake,ko waiwayowa baiyi ba don haka yamaida hankalinsa ga kamal
“Kamal,kasake maimaitawa ko?” Yajefa masa tambayar,kafadunsa duka ya daga 
“Eh sai meye?,taqamarshi yace nabar mishi gida,to hell shida gidan nashi,saime don na tafin?ko yaushe shi sai zafin rai da yiwa mutane fada,waye ya girma ne a cikinmu” Kaiya soma girgizawa yana matsawa gabanshi
“A’ah kamal,kada kace haka,azeez yafika gaskiya,kai kanka kasan abinda kuke aikatawa din ba dai dai bane,tunda koda wasa ba zaku taba bari yaje kunne ko idanun iyayenku ba,kuma kafi kowa sanin ba abinda ya kawoku qasar nan kenan ba,bugu da qari kasan situation na abdul’azeez,yana da duk wata dama da zaiyi yadda yakeso ya gusarwa da kansa wannan damuwar,amma koda yaushe qoqarin kaucewa da takatsantsan yake saboda bin umarnin Allah,donme shi yana kiyayewa amma ku kuna qoqarin jefashi a matsala kunayin abubuwa irin wannan a gaban idanunshi yana kallo,bayan kusan raunin dake cikin zuciyarsa?”
“Kaga….kaga malam mustapha dakata da Allah,sauraramin,dama mun dade da sanin kaine munafukinsa dan shishshigi kuma,daa kafin zuwanka aiba haka muke zaune ba,duk da yana magana amma ba kamar haka ba,kasan dai wata kusan tafi wata ko?” Murmushi mustapha yasaki,ya gane kamal nason mishi gori ne,saboda shi din d’ane ga qanwar maimartaba,shi kuwa mustapha haduwar jini ce kawai da Allah yasanya tsakaninsa da abdul’azeez din
“Na sani,amma duk inda gaskiya take dole a gaya maka ita kamal koda bazakaji dadi ba” wani mugun tsaki yaja sa’annan yajuya yashige dakin da yake nashine shida abokin kwanansa yasoma tattare komai nashi,sam hakan baiwa mustapha dadi ba,yasani dole ne suga kamar shi yashiga tsakaninsu,saboda haka ya juya yanufi dakin abdul’azeez kai tsaye.
Da sallama mustapha yashiga dakin,saidai abdul’azeez din bai samu amsawa ba,yana zaune gaban gadonshi gefan drower ya zazzage magunguna daga kwalayensu yana balla daya bayan daya.
      Idanun mustapha a kanshi harya qarasa gaban gadon yatsaya akanshi hannayenshi harde a qirji yana duban abdul’azeez din harya jefa magungunan yakora da ruwa,duk da yaga tsaiwar mustapha amma baice mishi komai ba,saiya soma ma qoqarin rage jibgegiyar rigar sanyin dake jikinsa saboda gumin dake yanko mishi,yazareta ya wurgar gefe,ya fidda takalmin qafarsa saura safa kana yakoma saman gadon yamiqe sosai rigingine.
       Sai a sannan mustapha ya magantu
“Azeez….sai naga kamar baka kyauta ba da korar kamal da kayi daga gidan nan,ko bsbu komai jininka ne fa” idanu abdul’azeez kawai ya zubawa mustapha tsayin wani lokaci yana dubanshi,kamar bazaice komai ba kana ya motsa bakinsa
“Shine hukuncin da yafi dacewa dashi,bazan zauna a banza ina yaqi da kaina da qoqarin kare mutuncina ba suna son maida min hannun agogo ba” ya qarashe maganar yana maida numfashi,shi daya yasan me yake ji cikin gangar jikinsa,maganinma sam kamar baya mishi aiki zuwa yanzu haka yakeji
“Gaskiya ka fada,amma haka zakayi haquri tunda kai kanka kasani mai martaba ne da kansa yahadaku zama tare….”
“Koshi da zaiji meke faruwa sai ran kowa yabaci ciki harda ni danaqi qaya masa”
“Duk da haka,tafiyarsa fa kaman yasake samun dama ne tayin duka yadda yaso babu mai cewa bari…..”
“We will talk later pls musty” ya fada yana tashi da hanzari,yajawo locker dake kusa dashi din dai again yaciro ruwan allura da syring,daidai lokacin da mustapha ke duba kwalayen magungunan daya gama sha yanzu bai samu maidawa ba.
       Da wani irin zafin nama ya warce syring din daya cika da ruwan allurar da nufin yiwa kansa cikin hargagi yana fadin
“Baka da hankali ne azeez?,ka haukace?!” Kai yake girgizawa mustapha
“Kar kace zaka hanani pls”baibi takanshi ba ya tsiyaye ruwan alluran saman carfet din dake gaban gadon cikin bacin rai,kana yakoma kusa dashi yazauna yana tattare magungunan waje daya
“Azeez,kanason ka nakasta kanka ka yiwa kanka illa haka kawai?,kasan illar wadanda tablet din da injection din daka soma yiwa kanka?,hakan fa na nufin tablet din sun daina aiki a jikinka sabida yawan yadda kakesha saidai allura?,kanason ka wayi gari duk sanda kayi aure yazamana baka da wani desire irin ta da namiji saboda already ka kashe taka da qwayoyin kasheta?” Da idanunsa da suka sauya launi yake duban mustapha
“Bani da wani zabi daya wuce wannan….indai ba halaka kukeso na fada ba” daga haka yasauka daga saman gadon cikin rashin qarfin jiki yawuce toilet.
      Ko kayan jikinsa bai cire ba ya sakarwa kansa shower,sanyin ruwan yadinga ratsashi tun daga tsakar kanshi har tafin qafarsa,tun shekarun baya da suka shude tun baisan meye ba lamarin yake damunsa,ya rasa wacce irin halitta gareshi,yana da yaqinin aure shine kadai hanya daya ta maganin matsalarsa,saidai ya rasa dukkan wannan damar saboda ammi taqi fahimtarsa,azumin litinin da alhamis baya wuceshi amma wani lokaci kamar ma bayayi,rashin mafita ya sanyashi tilas rungumar magungunan kashe sha’awa badon yana so ba saidon babu yadda zaiyi,ko sau daya istimna’i ko romance da mace ko duk wasu hanyoyi da wasu matasa ke amfani dasu don ragewa kai zafi basu tab burgeshi ba,bare uwa uba zina,abar da yafi qyamata kaf rayuwarshi ita da shaye shaye.
     Yajima kafin yayi wanka gaba daya duk da sanyin da ake a qasar kana yafito,sanda yadawo dakin mustapha ya riga daya fita,saidai ya tattare dukka magungunan yafice dasu harda na locker dinsa,sai yasa qafarsa yatura locker takoma ciki,ya isa ka makunni yakunna room heater yaqure zafinta donta dumama mishi dakin dakyau,ya qarasa bakin qofa ya murza ke yarufe dakin kana yadawo yashurya cikin wasu kaya masu laushi da kauri.
      Rub da ciki yadawo yayi saman gadon nashi yana lumshe ido yanajin yadda dumi ke ratsashi,duka ranshi a jagule yake har yanzu babu dadi,takaicin zuwanshi club din da jamil yajashi hakanab ba gaira ba dalili har yanzu yaqi barin zuciyarshi,kawai yana wasafa rashin mutuncin da zaiwa jamil dinne shima.
             *NIGERIA*
       Daidai lokacin da safwa ibrahim attah ke zaune cikin dakin hutawarta ita da qawarta islam,zaune take saman wata qawatacciyar kujera doguwa mai azabar taushi,irinta qwaya daya tak duk cikin dakin,sanye take da dogon wando silk ruwan qwaiduwar qwai,sai wata riga sakakkiya wadda bata kamata ba sam,sphaghetti hand ce mai wani madauri daga gabanta peach colour,kanta dake da santsi da tsaho na fake tsakiyar kanta,tamiqe dukka qafafunta saman kujerar daga gefanta dan madaidaicin table ne dake dauke da lemo mai sanyi da wasu qananun kofuna na alfarma,sai dan qaramin plate da aka dora gasashshiyar kaza mai romo ‘yar kadan,da alama ta kwadayi ce kawai.
        Islam na gefanta saman wani kafet mai azabar laushi,tayi rub da ciki da system a gabanta tana kallon wani series na koria.
       Tsadajjiyar wayarta ce a hannunta tana laluban number yarima abdul’azeez,tana zuwan kan sunan data sanya masa wato Sweetberry ta lumshe idanunta tana fatan yau taci sa’ar samunsa,tabude idanun nata sannan ta dannan kiran.
       Islam din na ankare da ita tun dazun data fuskanci shurunta yayi yawa,bata tanka ba sai yanzu
“Addu’ar neman nasarar daga wayar prince din ake?” Hannu ta dora mata saman lebanta alamun tayi shuru,batace komai ba tamaida kanta ga kallonta tana sauraren jiran jin abinda zai biyo baya.
       Idanunshi da suka soma nauyi yabude jin qarar wayarshi,banda yana tunanin kada ammi ce takirashi da babu abinda zai sashi kula wayar,a kasalance yajanyo wayar yana duba me kiran
“Sweetsafwa” sunanta ya bayyana saman wayarshi,sunan data sauya mishi da kanta bayan ta gama mita ranar dayaje gidansu ana ya gobe zai dawo bisa umarnin ammi.
      Maida wayar yayi wajenta bayan ya sanyata a silent don sam bazai iya dagawa ba,yasan tabbas idan yadaga zata karya duk wani budget nashine,abu na farko da zata soma masa wannan shagwabar tata da ba kasafai yake iya jureta ba.
     Baisan sau nawa takira ba,baisan me yaci gaba da faruwa ba sakamakon bacci da yayi awon gaba dashi.
       Kyaɓe fuska tayi sosai wanda hakan ke nuna koda yaushe kuka zai iya suɓuce mata.
      “Please sweetberry,please ka daga mana” ta qarashe fada kuka na kubce mata,ganin harta masa irin kiran da baiso wato sama da sau biyu amma bai daga ba,sai islam kawai tasaki baki sororo tana kallon ikon Allah
“Safwa….ke kikema namiji kuka?” Ta tambayeta cike da mamaki,saboda itadin shaida ce kan irin dimbin mazan dakeson safwa din,banza safwan tayi mata sai data gana qwallarta sannan tamiqe tashige dan bandakin da aka tanada cikin dakin saboda buqatar gaggawa,fuskarta ta wanke sannan tafito tagogeta da qaramin towel,ta wurgar dashi kana tazauna kan wata kujerar daban sabanin wadda tatashi akai
“Kina mamaki islam?” Pause tasanyawa film din da take kalla kana tamiqe daga rub da cikin da tayi tazauna sosai ta gyada kai tana duban safwa din
“Karki mamaki,ana magana ne akan abdul’azeez abdallah mu’az,yariman garin kaisa,d’a daya tilo namiji ga mahaifinsa,ke kanki kin sani koda ban fada ba prince azeez ya cancanci kowacce irin soyayya tako ina hakanan takowanne fuska,inason azeez irin son da bansan iyakarsa ba,kuma shima yana sona,amma kullum yana sanyani inajin kamar alfarma yayiwa rayuwata yasoni,miskilancin azeez shine abu nafarko da yake hadani dashi,na rasa ta yadda zan canzashi” hannayen islam cikin najuna tana dubanta,hakanan tana fahimtar abinda take fada,tasani safwa tayi nisa a soyayyar yariman kome kuma zaka gaya mata babu lallai ita taga hakan kamar yadda kai kake gani a idanunka,duk abinda tafada kan abdul’azeez haka yake,amma bata da abinda zatace mata,don haka saita dage kafadunta tadan taɓe baki
“Hakanan zakici gaba da tolerating miskilancinsa tunda kina sonshi harki saba,mai yiwuwa nan gaba ya rage koya daina idan kuka zama mallakin junanku” kalmarta ta qarshe ta faranta ran safwa sosai,harta saki murmushi data kasa riqeshi
“Allah yasa qawata,harkin faranta min” murmushi itama islam din tayi tana komawa kwanciyarta,saita sake daukar wayarta ta tura mishi gajeran saqon kar takwana sannan ta lalubi number daya daga cikin cook na gidan donta kawo musu abincin rana ta kwashe na gabansu.
        ☀️☀️☀️☀️☀️☀️☀️☀️☀️☀️
      Tun daga nesa ta hangeshi tasoma neman wajen buya,saidai ina tuni ta makara don kuwa ya hangota.
      Hamza ne fuskarsa fadade da fara’a,sabanin fuskar bilkisu da take a dinke kamar koda yaushe,wanda idan ba farin sani kayi mata ba da wuya kasan murmushinta.
      Duk yadda taso tawuce amma dole hakanan ta tsaya,don batason yabita har cikin layinsu bare yakai qofar gidansu
“Ranki ya dade,tun dazu kina raina,ashe kina kusa dani” tanajin nauyin mutumin daya girmeta ta tsallakewa gaidashi,don haka cikin sanyin muryarta tace
“Ina wuni”
“Lafiya qalau gimbiyata…da alama kamar bakiyi kewata ba ko?” Ya jefa mata tambayar,saita dan motsa kadan
“Sauri nake inason nawuce gida” sanya hannunshi yayi cikin aljihunsa yana cewa
“Babu damuwa,yaushe zan shigo mu gaisa,dazu nadawo daga tafiya,koma ki tambayeni?”
“Sannu ya hanya” tafada cike da nuna qaguwa,don dukka hankalinta ya karkata ga gida
“Alhmdlh” yafada yana miqa mata wani dan qaramin kwali dake cikin leda
“Ga tsarabarki,ki qarasa gida da ita,kina iya hadawa ki kunna kafin na shigo din” sai data dubi abinda yake miqo matan sannan ta girgixa kai
“Ka barshi,na gode” cikin hanzari tayi baya kadan sannan tawuceshi,saiya bita kawai da kallo,yana mamakin halayya da dabi’un bilkisun,komai nata daban yake,shi kansa sautari cikin jikinsa da zuciyarsa saiya dinga jin anya zaya samu bilkisu?,anya bilkisu tayi dai dai da tsararshi?,yakanyi saurin qaryata zuciyarsa da kwabar kanshi,yana ganin kamar maganganun wasu daga cikin abokansa dake maza hasashen yiwuwar rashin samun bilkisu suke son tasiri a ransa.
      Baibar wajen ba har sai daya daina hangota,saiya saki ajiyar zuciya yana juyawa don barin layin da niyyar randa zaije zai tafar mata da ita,don a ganinsa ya kamata zuwa yanzu ace tana riqe waya a hannunta,kodon yasamu damar jin muryarta koda baya nan.
      Saura kadan yaci karo da abokinsa dake tsaye bayanshi yana kallonshi,suna hada idanu yasaki murmushi mai kama da dariya
“Irin wannan kallo haka?,ko daukota kawai zakayi ku wuce?” Dariya hamza yayi yana dan dukan kafadar mudassir
“Mtsweew,bari kawai abokina,yarinyar tashigemin rai da yawa,fatana kawai shine nagama samun kanta,tana da dan wuyar sha’ani da rashin saurin sabo,har yanzu ta kasa sakin jikinta dani bare na fahimta komai” yana maganar ne lokacin da suka fara tattakawa tare shida mudassir
“Top class mace kenan,haka akeso ai,bawai kawai tashin farko ta sallama komai da komai ba,kamar wata haaja a kasuwa” hannu yabawa mudassir suka tafa
“Allah mutumina?”
“Allah kuwa,kaidai kaci gaba da jumuri” sake tafawa sukayi cikin dariya kana sukaci gaba da takawa tare suna ci gaba da tattaunawa kan bilkisun da irin halayenta daya fuskanta.
       Bayan sallama datayi a tsakar gidan nasu sai kuma tasoma binsa da kallon mamaki,kullum abun mamaki bai qarewa cikin gidan nasu,baqine dangin abbanta daga nijer,qannenshi biyu sai yayarsa da kuma qanwar mahaifiyarsa wadda take tamkar a maxaunin mahaifiyarsa tunda tajima da rasuwa.
      Ba zata iya tuna lokaci na qarshe da suka zo gidan dan uwan nasu ba da sunan ganin iyalinshi ba,koda yaushe idan ka gansu to baban nata ya tashi qara aure ne,abun yana daure mata kai,tamkar basu damuwa da rayuwarshi,kamar bashi da mafadi?,kamar basu bibiyar al’amuransa,haka siddan duk lokacin daya tashi qara aurenshi zai gayyatosu ne,su kuwa tinqis tinqis haka zasu taso su taho biki,batajin akwai wadda ta taba tuhumarshi ko tambayarsa labarin matarsa da sukazo biki wancan karon meye rabashi da ita?,amma abinda ta fuskanta shine,kamar yana riqa maqudan kudade ne yaje yamusu yayyafinsu.
        Jiki a mace ta jingina da bangon da yasha fentin farar qasa albarkacin zuwan amarya,wanda iya tsakar gidan akwai yayiwa,dakunansu kuwa ko oho,tazame tanemi gefan tabarmar da suke kai tazauna.
       Cikin nuna girmamawa tayi musu sannu da zuwa,saidai sam babu wani sabo ko sakin jiki a tsakaninsu,don hatta yaran sun sansu dai a idanu amma basu wani saba ba,don ba ganinsu din suke ba bare ace wani shaquwa ta shiga tsakaninsu,don haka itama tana gama gaidasun tamiqe,tana jin yadda suke yaba girmanta da kyanta,saita jefesu kawai da murmushin yaqe,harta shiga dakinsu bataji motsi ko taga gittawar umma katti ba,batasan cewa tana qule a daki ba,baqinciki da bacin rai kawai ke sakadarta,shi yasa tunda tabasu tabarma suka shimfida nan tsakar gidan bata sake bi ta kansu ba.
      Abun mamaki da daddare saiga kular abinci lafiyayya ana shela kowa yafito ya karba,tana zaune inda take bata ko motsa ba amma ta tura yaran su su karbo suzo suci su kwanta,har suka gama ci suka gama santinsu tana kallonsu bata motsa ba,sai data tsinto muryar mahaifinta yana qwala mata kira kana tamiqe a sanyaye tafita da faranti a hannunta.
      “Yarinyar nan bilya babu inda tabaro maimunatu,ai bilya kayi asarar mace,har yau baka maida kamar maimunatu ba”
“Hmmm,bari kawai binto,ai maimunatu diyar albarka ce,bansan dame zan saka mata ba,maiminatu ‘yar aljanna ce na shaida hakan tun kafin ta rasu”itadai tana tsugunne mariya qanwarshi na zuba mata abincin batace komai ba har aka zuba matan tamiqe zuwa daki.
      A gaba tasaka kwanon abincin,tunanin mahaifiyartata ya bijiro mata,kewarta ta bijiro mata,zataso sake rabarta,zataso tasake jin duminta,ta jingina a jikinta ta gaya mata damuwarta,saidai tasan ina,mai rabawar ya riga daya raba,babu wani sauran abinda yarage sai haquri dangana da kuma binta da addu’a.
*****   ******    *****
      A nutse yake fitowa daga dakin nashi sanye da farar riga mai dogon hannu da rufaffen wuya,farace tas ta kama jikinsa duk da cewa tana da dan kauri,sai wandon jikinsa shima farine kamar rigar daya zarta gwiwa duk da cewa sanyi akeyi,fuskarsa tayi fresh babu wannan fushin ko digo daya shigo dashi dazun,saidai wannan daurewar da miskilancin na tattare dashi.
     Zuciyarsa ta rage nauyin datayi,saboda yasamu cikin baccinsa yayi mafarki wanda hakan ya qara mishi relief,kai tsaye falon yanufo hannunshi riqe da wayarshi yana neman layin safwa,don yasan halinta sarai,yanzu haka qilan tana nan a dame.
      Mutum biyune zaune a falon jabir da mustapha suna kallo,hada idanu sukayi da jabir saiya dauke idanunshi gamida mazewa,yayin da azeez ya jefeshi da wani kallo wansa shi jabir din yasan ma’anarsa sarai,kuma yasan laifinsa,dauke kansa azeez din yayi yanufi kitchen,a can yasamu abinci a cooler,yasan aikin mustapha ne,don kaf gidan shi kadai yake da juriyar dafa musu abinci suci,saidai yau an samu akasi sam baya sha’awar abinci kowanne iri ne,don haka ya hada coffe mai zafi yajuye a wani qawataccen qaramin flask wanda yafi kama da butar shayi,yadauki cups dinsa guda biyu bayan yazuba dambun nama daya taho dashi tun daga gida nijeria a wani dan qaramin plate sannan yafito zuwa falon.
      Yana shirin zama mustapha yace
“Kafito kenan” kaiya gyada mishi daidai lokacin da safwa tadaga wayar tashi,kamar kuwa yadda yazata hakance ta kasance,kukan shagwaba ta sake masa,shuru yayi idanunsa a lumshe yana saurarenta kana yana neman daukin Allah,sai daya barta ta rage qorafinta sannan yadakatar da ita cikin sanyin muryarsa fiye da yadda take ada saboda yanayin jikinsa da babu qwari kamar yadda yasaba jinsa,ko mustapha dake gefansa baijin me suke fada
“Don’t stress your self sweetberry….duk tyn din da kiks kira kikaji banyi picking ba to ina da uzurine zan duba kiran kuma zan biyo ,i made it clear?”ya qarashe maganar da sigar tambaya,daga haka suka dan taba hira duk da batayi tsaho sosai ba,yace mata baijin dadine yau sosai,amma idan yasakeyin bacci yatashi zaiji fresh then zai kirata,yasauke wayar daga kunnensa yajawo kofin shayinsa yasoma shan a hankalin yana hadawa da dambun.
       Akaran kanshi shurun azeez din yasa yasake tsarguwa,cikin sigar jan hankali yakirashi
“Prince” shuru yamasa kamar baiji ba,bayan wasu mintuna yasake maimaita kira,sai azeez din ya aje kofin hannunsa ba tare daya dubi sashen da jabeer din yake ba yace
“Wannan shine lokaci na qarshe jabir,karka kuma maimaita abinda kayimin yau”
“What?….daga yin abu don na taimakeka?” Sai a sannan yadubeshi ya watsa mishi wani kallo kana yace
“To hell with your taimako,banaso kuma kar ka sakemin irin wannan” yasan qwarai ya fusata,yana qoqarin danne dariyarshi ya hada hannyenshi biyu waje daya yace
“Is ok,ba za’a qara ba,am so sorry” saiya janye idanunsa daga kanshi,kana yamiqe a nutse yasoma takawa ya isa gaban socket din kayan kallo zai cire charger din system dinshi,yanaso yayi amfani da ita cikin daki
“Amma yarima…..kamal fa,kayi haquri yadawo” sake waiwayowa yayi yadubeshi fuska a dinke
“Abokin cin mushe?” Kai ya girgixa dariyar nasake cinsa
“Nooo….tunda kamasa haka surely zai sauya”
“Ba yanzu ba” ya bashi amsa yana takawa zuwa dakinsa abinsa ba tare daya waiwayo ya dubeshi ba.
      “Prince taurin kai,prince kafiya,kai wannan mutum….” Jabeer yafada yana tsalle gamida tsallakowa zuwa inda azeez yatashi yaja cup din tea din yasoma surbewa yana hadawa da sauran dambun,kafada mustapha ya daga
“Yadai fiki gsky magana ta haqiqa,kawai kuyi qoqari kuma ku sauya a karan kanku kodon mutuncin addininku”
“Zamu sauya amma ba yanxu ba,don banga dalili ba hakanan da quruciyata,da dukiyata da kyauna nazauna ban mori rayuwata ba,shima yanaso,tsabar iya takura kaine” dubanshi kawai mustapha yayi,da alama shima yafara sallama lamarinsu,dukkan alamu sun bayyana wanda yayi nisa bayajin kira saidai gyaran Allah kawai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page