HAUSA ARAB CHAPTER 7

 HAUSA ARAB CHAPTER 7

Wata zabura Daddy yayi daga zaune kamar zai kifa don tsananin dimuwa da tashin hankali! Mami ma saura kadan glass cup din ta ya subuce daga hannunta, tai maza ta taro shi jikinta na tsuma kamar sabon kamun zazzabi.

Kamar saukar aradu haka maganar Mahmud ta rufto musu a ka babu zato babu tsammani babu tunanin ta yanda zai iya sanin hakan.+

Halin da suka shiga ya sanya Mahmud jin wani irin tausayin kansa da na iyayen na shi. Shi kansa ba’a son ransa zai nuna musu ya san wannan maganar ba. Amma matukar muhimmancinta a wajen sa ya sanya ba zai shiru a tafi a haka ba musamman da yaji cewa Dada ta tayar da balli akan hakan. Wai yau an wayi gari mutumin da yake tunkaho da shi yake jin sanyi da salama da peace of mind idan ya tuna shi a mahaifin shi ya subuce masa ya koma bare gare shi. Yasan Mami bata haife shi ba kuma sanin mahaifiyarsa bai taba bashi sha’awa ba a ganinsa so da kulawa da tsantsar kaunar da Mamin take masa sun ishe shi a rayuwa. Idan da bukatar yasan wadda ta kawo shi duniya watarana zai sani. Tana raye ko bata raye bai sani ba kuma bai damu ya nemi sanin inda take ba tunda bai taba jin ta neme shi ko wani daga cikin danginta sun neme shi ba.

Gaskiya yana bukatar sanin gaskiyar al’amari game da rayuwar shi. Yana so yasan asalin shi da duk wanda ya shafe shi.

Dakyar ya samu sukunin sarrafa busassun lebbansa ya soma magana cikin taushin sauti.

“Daddy kayi hakuri! Ban nemi jin wannan sirrin domin na tada maka hankali ba, ba kuma don sanin asalina yafi ku muhimmanci ba. Daddy saboda halin rayuwa da kalubalen da ke iya fuskanto ni a dalilin haka. Bazan taba iya chanza ku ba Daddy, ku din iyayena ne na hakika wadanda har abada sunanku ba zai chanza ba a zuciyata. Bazan taba jin feeling din da nake ji gare ku ga wasu mutane ba a duniya. Daddy kune gatana, farin cikina, da kwanciyar hankalina.

Nasan za kai mamakin yanda akai naji wannan maganar zaka so sanin wanene ya gaya mun? A lokacin da kake gaban gadona ranar da kazo kuke waya da Mami Allah ya farkar dani daga halin da nake ciki na dawo hayyacina. Sai dai kafin na samu sukunin bude idanuna kunnena yaci karo da munanan kalaman da har abada nasan bazan sake jin kalamai masu muni irin su ba. Wannan ya sakani cikin halin da na fada na tsakanin rayuwa da mutuwa. Babban dalilin da ya sanya ni rufe idanu na tambayeka Daddy saboda naji cewa Dada ta dau maganar da zafi, tana jin bacin ran yanda ta aje ni a matsayin data dade tana bani a matsayina na bare ba jininta ba. Sannan tayi fushi da ku.

Daddy nasan da wahala but i really  have to go through this! Dole mu fuskanci wannan kalubalen mu warware shi mu kuma fahimtar da duk wanda ya cancanci sanin wannan al’amari yanda komai yake kafin ranar da duniya zata fallasa asirin da kanta.

Daddy you can never keep a secret for a lifetime. You can’t! Idan kai ba ka bayyana da kanka ba toh tabbas wataran asirin da kanshi zai tona kansa. Hakan kuma yafi komai tozarshi da tashin hankali! Please Daddy ka nutsu ka kwantar da hankalin ka kayi mun bayanin komai dalla dalla. “

Ajiyar zuciya mai karfi Daddy ya sauke kafin ya soma magana cikin zubar hawaye masu radadi da kunan rai da fallasa asirin halin bakin cikin da zuciyarsa take ciki. MAHMUD shine abinda yafi komai muhimmanci a rayuwar shi domin shine silar mayar da rayuwarshi ingantacciyar da ta zama yanzu. Shine farin cikin da Allah bashi a dunkule, kullum yake warwarewa yana alfanuwa da ni’imar da ke cikin shi. Mahmud is a gift from God!! Allah ne ya bashi ba wani Dan’Adam ba kuma Shi kadai yasan hikimar sa akan hakan.

Mami kam kuka kawai takeyi mai cin rai da tsuma zuciya cikin wani irin tashin hankali da bakin ciki mara misali. Ita kanta ba Daddy ba Mahmud na daya daga cikin rahamomin ubangiji a rayuwarta. Ya shigo rayuwarta tun kafin tasan yanda iyaye suke yi su so Dan da suka haifa, sannan ya hanata maraici da jin zafin matsalar haihuwa ya kuma debe mata kewa. Taci sa’a zamanin akwai tsantsar kara da sanin ya kamata, domin bayan Inna Badi’a babu wanda ya taba furta mata kalmar gori akan Mahmud.

Babu wani bambamcin da take ji tsakanin Zara da Mahmud, kai idan tsantsar shakuwa da soyayya ce ma zata iya bugar kirji tace Mahmud ya doke Zara. Tana watanni bata tuna cewa wai ba ita ta haife shi ba ko tunanin yanda yazo gare ta saboda shagala da tayi cikin kaunarsa.

STORY CONTINUES BELOW

Ga Mahmud kuwa abun yafi komai tsauri. Zuciyarsa yake tambaya shin wacce asara ce ta wuce kubucewar wadannan nagartattun bayin Allah a matsayin iyaye? Me yafi ciwo da radadi fiye da gano cewa Daddy is not his biological father! Yana jin ciwon rashin kasancewar Mami ‘Natural mother’ dinsa. toh amma da yake da Uba ake ado ake tunkaho, sai subucewar Daddyn tafi gigita shi.

Ko da ya gano iyayen da suka haifeshi ya tabbatar da sai dai kaunar su tazo ta bayan su Daddy shima albarkacin haihuwar kadai zai janyo haka.

A matsayinsa na cikakken gynaecolgist yasan muhimmancin uwa da kalubale da wahalhalun da take fuskanta kafin ta kawo ďa duniya. Shiyasa ya ragewa mahaifiyarsa waje a zuciyarsa inda zai sanyata kuma zai yafe Mata duka abinda tayi masa ba tare da wani tunani ba. Amma zancen so da kauna da shakuwa ta amana da gaskiya Mami ta mamaye filin ransa. Uwa daya ce tak! Ta cike wannan gurbin ta dauki wannan ragamar ta rike.

Acikin ýaýan da suke tasowa da uwa da uba da gata da arziki zai iya cewa za’a ajiye casa’in da tara kafin a samu wanda yayi irin sa’ar shi. “They are parent like no other! They are his greatest blessing and biggest weakness”

Basu samu nutsuwa da kwanciyar hankalin yin maganar ba sai da daddare. Babu wanda ya iya yin dinner sai Mahmud da ya kokarta ya shanye kunun da Mami ta hada masa kamar madaci don kawai ya basu kwarin guiwar tunkarar sa.

Cikin karfi  hali Daddy ya soma magana cike da nutsuwa da sanyin jiki.

“Dada ýar asalin garin Yola ce ta jihar Adamawa su biyu kaďai mahaifiyar su ta haifa ta rasu, sai suka taso tsakanin kishiyoyin mahaifiyar su waďanda suka matsanta musu fiye da tunani suka mayar dasu barorin gidan Malam Barkindo wani shahararren masanin addini a garin Yola.

Bayan an aurar da Dada sai kanwarta Zainabu ta shiga ukubar da tafi wadda suke ciki a dalilin babu me kula da ita a gidan, babu daďewa bayan lokacin Allah yayi wa Malam Barkindo rasuwa abinda yayi sanadin dawowar Zainabu hannun Dada da umarnin mijinta Manga. Ýaýa biyu ta haifa a gidan, Badi’a da Sulaiman sai Allah yayi masa rasuwa a hanyar fataucin da yake zuwa.

Babu irin kuncin rayuwar da Dada bata shiga ba a dalilin rasuwar mijinta. Babu sana’ar da bata yi ba wajen ganin ta samu abinda za ta rike kanwarta da ýaýanta ta rufawa kanta asiri.

Dada wata irin mace ce mai kamar maza, jaruma, jajirtacciya, tsayayyiya kuma mai juriya da karfin zuciya. Tana da zafi kamar wuta saboda haka ake shakkarta amma kuma bata taba yin faďa akan rashin gaskiya. Bata yarda ta durkusa ta nema a wajen kowa ba, Zata yi kowacce irin sana’a domin ganin ta kare haqqinta da mutuncin ta da na iyalin ta. Dada tana da ibada da addini da son taimakon wanda ba shi da shi, tana da kyauta da alkhairin da ya janyo mata soyayyar Jama’a don haka tayi suna a cikin unguwar su.

Ana cikin haka Lamiďo ya dawo daga kasar turai karatu, mahaifin Lamiďo dacta Mamman principal ne a makarantar boko, a wannan lokacin da karatun boko bai da wani tasiri da farin jini a zukatan mutane gidan Dacta Mamman sai sunyi karatu sun gyatse. Don haka iyalan gidan suka futa daban a cikin garin, domin al’adar su da ra’ayin su yasha bambam da na kowa.

Cikin haka Lamiďo ya faďa tarkon son Dada a lokacin tana aikatau a gidan su.

Ba sai na ba ka labarin yanda wannan alaka tayi bakin jini a gidansu Lamiďo ba na san kaima zaka yi wannan kiyasin. A dalilin soyayyar da Lamiďo yake yi wa Dada har korar sa mahaifin sa yayi daga gidansa yace ya yafe shi amma sam yaki ji yaki gani duk da cewa ita kanta Dadan ba wai ta damu da shi bane.

Babu ta inda Dada da Lamiďo suka dace da juna a matsayin ta na bazawara mai ýaýa biyu, ýar talakawa mara galihu, shi kuma sankacecen saurayin da ko ýar gwamna yace yana so za’a ba shi da gudu. Ga kyau ga ilmi ga gata ga Kuďi. Amma shi kam bai dubi komai ba sai soyayya.

Mahaifin Dacta kakan Lamiďo shi ne ya kira Mamman yayi masa nasiha mai ratsa jiki ya kuma nuna mi shi girman kaddara da rabo da kuma abinda ja da hukuncin Allah yake haifarwa.

Ba da son ran Dacta mahaifin sa ya wuce gaba aka yi auren Dada da Lamiďo ba kuma ba wai hakura yayi ba.

STORY CONTINUES BELOW

Wannan aure ya sha maganganu da ce-ce-kuce ďin mutane amma da yake Allah ya kaddara haka aka yi, Dacta daman ya rantse ba zai ba shi gida ba, sai Dadan tace ita ma ba zata so futa daga cikin gidanta wanda ya zama gadon ýaýanta ba.

Ko sau ďaya kalma mai kyau bata taba shiga tsakanin Dada da ýan’uwan Lamido da iyayen sa ba balle wata mu’amalar arziki. Ita ma da yake wuta ce bata ďaukar raini sai ta kebance kanta daga shiga cikin su. Iyakacin ta kawai gidan Kakan Lamiďo. Haka suka ci gaba da rayuwa cikin kaunar juna da farantawa juna rai, ya ďauki ýaýanta kamar shi ya haife su yana kula mata da su da duk karfin da.

Shekarar su ta farko da aure ta haifi ďa namiji yaci sunan kakan Lamiďo wato Yakub. Watannin Yakub bakwai Lamiďo ya samu babban aiki a garin Lagos a hukumar fasa kauri. Ba’a son ran Dada ya tafi wannan aikin ba duk da cewa yayi yayi da ita su tafi tare tace babu inda zata je Yola kaďai ta sani ta kuma amincewa zama a ciki.

Shekarun Yakub uku aka haifeni, lokacin an tura mahaifina wani course kasar Portugal daga wajen aikin su, don haka bayan kakan mahaifin mu babu wanda yazo gani na a dangin mu.

Mahaifiyar Dada fulanin tashi ne, hanya ce da rabo ta kawo su Yola, Malam ya ga mahaifiyar su yace yana so mahaifin ta ya bashi aka yi aure ta tare, watannin su uku bayan auren suka tashi daga Yola suka kara gaba, tafiyar da basu sake juyowa ga ďiyar su ba kenan har ta koma ga Allah. Don haka Dada bata da kowa sai mahaifin ta wanda Allah ya karba.

Tunda mahaifin mu ya tafi wannan karatu bai dawo ba sai dai yayi mana aike, tun Dada ba ta damuwa har ta soma damuwa, tun tana lissafin kwanaki har ta soma yin na watanni, sai da ya shafe shekaru uku cur sannan ya dawo. Yana dawowa aka kara masa matsayi a wajen aiki, nan da nan rayuwar mu ta sauya muka koma ýan gata, makaranta mai kyau muke zuwa, kayan sawar mu duk daga Lagos yake kawo mana, muka futa daban a cikin family, wannan ya sake janyo wa Dada tsana a wajen iyayen mahaifin mu domin gani suke yi ya tattare komai a wajen ta da agolan ýaýanta.

Cikin tsananin mamaki Mahmud yace

“Daddy kana nufin ku da su Inna badi’a ba mahaifin ku ďaya ba?”

Murmushi Daddy yayi yace

“Mahaifin su rasuwa yayi kafin Dada ta auri mahaifin mu ta haife mu. Suna amfani da sunan mahaifin mu ne saboda basu da wanda ya fi shi, basu san baban su ba balle kulawar sa ko soyayyar sa, mahaifin mu suka buďe ido suka gani yana ďaukar nauyin su, sun yi shekaru sama da goma kafin su gane cewa ba Baban mu ne ya haife su ba. Da sunan shi suke amfani a makaranta kuma bai taba ware mu a cikin su ba don haka basu yi maraicin uba ko ďaya.

“Baban mu ne ya aurar da Zainab ga wani ma’aikaci a ma’aikatar su mai suna Aliyu ďan jihar katsina. Bayan anyi auren ya ďauke ta zuwa garin Lagos suka zauna. Shekarar ta ta farko ta haifi ýa mace, taci sunan babar Aliyu Hajara suke ce mata Laila. Daga yaye Hajiyar su Aliyu ta kwace ta a hannun su ta koma da ita Kurfi.

Shekarar da ta zagayo ta sake haihuwa, amma wannan karon tazo mishkila ta dinga jijjiga sai tiyata aka yi mata aka ciro yarinyar, Allah da ikon sa bata sake farfaďowa ba.

Mutuwar Zainab ta wujijjiga Dada ta ďaga mata hankali ta susutar da ita fiye da kwatance, sai da addu’a da taimakon Allah dakyar ta samu kanta. Ita ce ta ďauki babyn wadda aka yi wa Zainab takwara wato Maminku. Dada taso shayar da ita babanmu ya hana, shi ya ďauki nauyin madarar gwangwanin da ta dinga sha har ta girma ta isa cin abinci. Shi ya ďauki dukkan wasu nauyi da jariri yake bukata at the same time kuma yana bawa Dada kwarin guiwa don ta samu juriya da karfin zuciyar rainon ýar Zainab.

Mu dukan mu muka taso cikin wata irin kulawa da tarbiyya mai kyau, daga fannin Dada da Baba kowanne yana iyaka bakin kokarin sa a kanmu. Kamar kowanne ďa a family ďin babanmu shima ba shi da burin da ya wuce muyi karatu mai zurfi mu zama wasu abubuwa waďanda al’umma zata amfana da su. Kullum kuma yana jaddada mata cewa ko bayan ran sa ta cika masa wannan burin ta bamu ilmi mai zurfi. Yawan faďin hakan da yake yi ya sanya Dada maida himma wajen ganin muna yin karatu yanda ya kamata, bata taba barin wani dalili ya hana mu zuwa makaranta sai dai ba ciwo don haka muka taso da himma da son karatu.

Dada bata dogara da abinda mijinta yake da shi ba, bata saka idanu akan albashin sa ba, sana’ar ta take yi ka’in da na’in wadda Allah ya sanyawa albarka ta dinga habaka. Ga kiwon shanu da ya karbe ta ta haďa garke guda tana amfana da su. Don haka duk wanda ya kalli Dada sai ya kara saboda hankalin ta a kwance yake, a hankali sai ýan’uwan babanta suka dinga lallabowa suna zuwa wajenta kamar ba su ne suka banzatar da rayuwar ta a lokacin da take bukatar taimako ba.

Da yake tana da halin dattako da son alkhairi bata duba baya ta kore su ba, sai ta rungume su ta dinga taimaka musu suka koma zumunci sosai.

Shekara ta goma cif lokacin da aka sake tura Baba kasar Agentina karo ilmi. Wannan karon Dada ba karamun tashin hankali ta shiga ba, haka kawai taji hankalin ta bai kwanta da wannan tafiya ba, taji ta tsani aikin na shi da ma boko gabaďaya saboda wannan dalili, dakyar ya shawo kanta ta amince ta yarda muka yi sallama da shi ya tafi ashe tafiyar ba ta dawowa bace.

Jirgin da ya ďauke su ko mintina talatin bai yi a sama ba yayi haďari ya faďi.

Mutuwar Baba ta saka mu cikin wani irin mawuyacin halin da bazan iya kwatanta maka ba. Dada kwana tayi tana suma tana farfaďowa kamar ita ma zata bi shi, mu kuwa babu abinda mu ke yi sai koke koke. Har akai kwanaki arba’in Dada bata samu nutsuwa ba sai da wani kanin mahaifinta ya dinga yi mata rubutun dangana da addu’o’i kafin a soma samun kanta.

Tun da Baffa ya mutu babu ďan’uwan shi da ya kalle mu balle yayi mana gaisuwa balle azo kan ďaukar nauyin mu a matsayin su na ýan’uwan shi.

Kakan shi ne kawai yake zuwa wajen Dada ya kawo mata kayan abinci da kuďi, ya dinga yi mata nasiha da nuna mata muhimmancin hakuri kafin shima ya kwanta ya mutu.

Idan na zauna baka labarin wahalar da Dada ta sha akan mu da cikawa mahaifin mu burin shi na tsayawa mana muyi karatu ba zan kare yanzu ba. Amma Dada tayi namijin duniya tayi kokarin da ko yana da rai iyakacin abinda zai yi mana kenan. Ko da wasa Dada bata taba neman taimakon iyayen Baba ba akan dukkan lamuran mu, gadon shi ma da aka raba cewa tayi mun yafe bata so, ta rasa shi ma ta hakura balle abinda ya bari. Sai da kanin mahaifinta ya shiga maganar yace ai hakkin mu ne idan ita ta yafe nata mu dole a karbar mana namu. Sannan ta yarda ta karba ta baiwa baban Zainab ya siya mana hannun jari a banki aka manta da su.

A Rumfa college ta jihar Kano muka yi makarantar gaba da primary da shawarar Uncle Aliyu mahaifin Zainab wanda ya zame mana tamkar kanin mahaifi, duk wani shige da fice akan karatun mu shi yake yi, don haka Dada ta samu saukin wasu abubuwan. Anan kuma Allah ya ya haďa ni da ambasada wanda ya kasance ďan asalin garin Kano ne. Bayan mun kammala karatu ne na samu damar samun scholarship zuwa kasar America inda na soma degree na farko a fannin na’ura mai kwakwalwa, anan muka rabu da amsabasada mahaifin shi ya sama mi shi gurbi a jami’ar ATBU

Shikuma Yakub yana gab da kammala degree ďin sa a jami’ar ABU yana karantar siyasa. Shikuma da burin da ya tashi kenan tun yana karami, ya girma yayi ilmi ya zama gwamna ko shugaban kasa, Dariya ake yi masa ana kallon abun a haukan kuruciya, sai da ya girma yayi hankali burin na shi bai chanja ba sannan aka gane da gasken gaske yake yi. Ita dai Dada da addu’a kawai take bin mu da fatan alkhairi.

Bayan ya kammala ne shima ya samu damar tafiya jami’ar Oxford a dalilin namjin kokarin da yayi ya futo da flying colour daga jami’a sai gwamnati ta ďau nauyin sa don ďora matakin karatu na gaba a zamanin babu abinda ake bukata irin yaran da iyayen su suke amince suyi karatu mai zurfi.

A shekarar da ya tafi Badi’a tayi aure a jihar Kano bayan ta kammala haďa degree ďinta a fannin kimiyya da fasaha. Auren bai wani daďe ba ya mutu a dalilin mugun rashin kunyar ta da neman fitina. Badi’a tun tana karama bata da tsoro bata kunya kuma bata son zaman lafiya, ko baka kula ta ba zata takale ka da rigima balle kuma ka shiga sabgar ta.”

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai!

Dukkan yabo da godiya su tabbata ga ubangiji maďaukakin sarki

Salati da sallama da aminci ga mafi alkhairin duniya da lahira sayyidina Rasulallahi saw.

Assalam alaikum masoyan Hausa Arab!!

Wannan shine farkon cigaban labarin Hausa Arab wato kashi na biyu, ina fatan zaku bani hadin kai kwarin guiwa da goyon baya kamar yanda kuka yi a wancan karon.

Wadanda suka manta na baya ya kamata suje suyi revision saboda kada su zama confused a cigaban labarin, a wannan karon zaku ji ainihin tushen labarin daki daki da kuma cigaban abinda ya faru a kashi na ďaya.

Insha Allah labarin zai kayatar da ku.

Kada ku manta, likes, votes da comments ďin ku shine kwarin guiwata, idan kuka yi shiru bayan kun karanta nima likimo na zanje nayi.

No comments no update shi ne tsarin.

Let’s begin…………

Ma’assalam

Cutyfantasia.”Yaya Sulaiman kuwa rashin kokari ya sanya duk muka zo muka kamo shi a makaranta har ma daga baya muka wuce shi. Rashin jituwar mu ta samo asali ne tun lokacin da muka samu damar futa kasar waje karatu shi bai samu ba, tun anan muka gane cewa Sulaiman mutum ne mai hassada da ratsin son ganin wani yaci gaba. A jami’ar ABU shima tayi nashi karatun amma Allah bai kaddara yana da nasibi ba don sau uku yana maimaita shekara sai da ya gaji ya ajiye wannan course ďin ya koma wanda ya fi shi sauki sannan aka dace ya samu ya kammala.

Tashin hankali na farko da ya bullo a tsakanin mu shi ne lokacin da uncle Aliyu ya tunawa Inna zancen shares ďinmu na banki kowa a bashi nasa tunda duk munyi hankali, Sulaiman da Yakub na shirin yin aure.

Zunzurutun kuďaďen da aka ďanka mana sun tsorata Sulaiman sun kuma tayar masa da hankali ya rasa inda zai tsoma numfashinsa. Duk da cewa mun cire musu 20% shi da Badi’a hakan bai sanyaya ransa ba.

Yarinyar da Yakub ya nema mutuniyar Yobe ce, a ABU suka haďu da shi, amma basu tashi wulakanta shi ba sai da biki ta rage satika sannan suka ce yayi hakuri sunyi bincike daga dangin mahaifin mu sunce su basu da ruwa da tsaki cikin rayuwar mu kuma ba zasu yi mana waliccin aure ba. Wannan abu ya Kona ran Dada. A satin ta wanke kafa ta tafi Kurfi, bata dawo ba sai da shafa fatihar auren Yakub da Zainab, Mamin kammala sakandire ďin ta kenan.

Da yake ýan albarka ne babu wanda yayi wa Dada musu. Kodayake ba mutum irin Dada ake yi wa musu ba, domin wannan faďan da zafin na ta tana girma yana kara ninkuwa ne don haka babu fuskar yin zargi a tare da ita.+

Sulaiman ya samu aikin karantarwa a nan Yola, a gidan ma’aikata kuma suka fara zama da matar sa Zaliha. Shikuma Yakub ya gyara bangare ďaya daga cikin gidanmu suka zauna da Zainab, wani irin zama mai ban sha’awa da jindaďi gasu ga Dada cikin gida ďaya suna faranta ran juna. Badi’a ce kawai matsalar su, domin ta tsani Zainab ta takura mata amma kasancewar Zainab ďin tana da hakuri sam bata kula ta.

Rayuwa taci gaba da tafiya Dada burinta kawai ta ga nayi aure, amma ni  ba wannan ne a gabana ba, wannan jinin na kaunar boko na family ďin Baba yafi tasiri a jikina fiye da kowa a cikin ýaýan da ta haifa da naga zata matsa mun sai na karbi aikin da aka bani a liverpool university anan garin London. Wannan shi ne mafarin kaddarar mu ni da kai Mahmud, daga nan rayuwar mu ta soma.

Esha Salah  abokiyar karatuna ce, African American ne musulmai mazauna garin London. Daga ni har ita bamu san lokacin da soyayya me karfi ta kullu a tsakanin mu ba, daga karatu da neman karin sani a wajen juna muka rikiďe muka koma aminai. Ni kaina idan aka ce ga dalilin da ya sanya nake kaunar Esha bansani ba. Domin ba ta da tarbiyya irin ta addinin musulunci, marabar su da kafiran turawan suna yin sallah da azumi kuma suna rufe gashin kansu amma bayan wannan duk ta’adar yahuwadawa basu ajiye kowacce ba.

Farkon soma kasuwanci na wani zuwa ne da nayi Nigeria, Uncle Aliyu ya tuntube ni akan siyan wani mataccen kamfanin fata a nan jihar Yola. Dada ma ta bada goyon baya akan wannan shawarar, da kuďin gadona na siya wannan kamfani nayi amfani da kuďin asusuna na tayar da shi aka ci gaba da aikin sarrafa fata.

Wannan shine mafarin arzikina, duk da cewa bana kasar Uncle Aliyu ya sa idanu ya tsaya akan komai. Cikin ikon Allah daga ni har Yakub sai muka samu wani irin nasibi mai ban mamaki, a karo na biyu muka sake kulla wata harkar ta kamfanin sarrafa shinkafa ni da shi, suma kafin wani lokaci sun habaka…..

Duk lokacin da nazo Dada zancen ta bai wuce na dawo na samu mata nayi aure ba. Idan ma na ga bazan koma Nigeria ba na ďauki matar mu koma. Tun ina son zuwa ganin gida har na daina.

Shekaruna talatin da biyu a lokacin amma su Dada gani suke yi kamar na shekara hamsin banyi aure ba.

Tun ina boye boyen alakata da Esha har na bayyanawa Yakub halin da nake ciki. Yakub mutum ne mai sanyin hali da hakuri mai tsananin biyayya ga Dada, da farko ya ďau zafi yayi ta mun faďa amma daga baya da ya fahimci cewa soyayya ba da wasa ta kamani ba sai ya koma yi mun nasiha da nuna mun illar abinda tarayyata da Esha zai haifar mun amma da yake nayi nisa kwata kwata ban saurare shi ba.

STORY CONTINUES BELOW

A wata shekara da nazo hutu gida Dada ta sakani a gaba da faďa da kuka akan maganar aure na, sai kawai nayi kundunbala na gaya mata halin da nake ciki. A wannan rana mun ga tashin hankalin faďan Inna irin wanda bamu taba gani ba. Sai da nayi danasanin zuwa Turai karatu tunda da  banje ba kila da ban haďu da wannan masifa ta soyayyar Esha ba.

Wannan ne kuma dalilin da ya sanya Dada tayi tur da boko da ýan boko ta haďa duk mai ra’ayin boko tayi musu kuďin goro ta kuma yi rantsuwa da tana da wasu ýaýan ba zasu yi karatu mai zurfi ba tunda ta gane babu abinda bokon yake koyawa sai bijirewa iyaye da addini. Na dinga baiwa Dada hakuri amma ko gizau, dakyar uncle Aliyu ya shawo mun kanta ta hakura da sharaďin ba zan sake komawa London ba nace naji na yarda don a wannan halin da nake ciki ko wuta Dada tace ma faďa zan faďa.

A tunanina abu ne mai sauki na cire Esha a raina, ashe tunanina bai bani daidai ba domin wani irin tashin hankali na shiga mara misaltuwa, a hankali sai gani rigif a kwance cikin tsananin rashin lafiya.  Sai da nayi watanni biyu ina jinya kafin na soma sabawa da rashin Esha duk da na kasa cire ta a cikin raina.

Bayan na nutsu ne nayi shirin tafiya London domin tattaro komatsaina da ajiyar da nayi a bankuna, Amma Dada bata yarda na tafi ba sai da ta aura mun Intisar, wata kyakykyawar matashiyar da ke taken kyau a Yola, mahaifinta attajirin gaske ne kuma almajirin mahaifin Dada, don haka tana neman haďin auren bai ja ba ya amince cikin farin ciki.

A wannan lokacin bani da zabin da ya wuce na karbi wannan aure domin idan ban karba bani da wadda zan gabatar wa da Dada, rashin yin auren a wannan lokacin kuma na nufin tabbatar bakin Dada a kaina saboda tsananin fusatar da tayi da ni. Wani katon kangon da yake jikin gidanmu na siya na tayar da gini mai kyau, na haďa da gidansu Dada na shafe na gyara sannan aka yi biki amarya ta tare.

Intisar itace kaddarar rayuwa ta ta biyu, domin ban taba ganin abinda ya bani wahala irin ta ba. Wata irin yarinya ce mara ihmani da tausayi da kunya, ashe itama akwai wanda take so tursasa ta babanta yayi ta aure ni, don haka ban taba jin daďin zama da ita ba ko na minti ďaya. A gaban Dada kamar zata yi mun sujjada saboda biyayya amma idan muka koma gidanmu ko kurar da take takawa ta fini daraja a wajenta. Akwai ranar da na hasala na mare ta, ta ďau mayafi da gudu ta tafi wajen Dada yana kuka, a karon farkon da Dada ta shigo gidana tun bayan auren kenan, ta zageni tatas sannan tayi rantsuwa idan na sake ďaga hannuna akan Intisar bata yafe mun ba.

Haka muka ci gaba da zama cikin wata irin rayuwa mara daďi tsayin watanni goma kafin dakyar da jibin goshi ta bar ni na tafi London yin harkokin gabana.

Ranar da na sauka a Liverpool naci karo da tashin hankalin da bazan taba mantawa ba.

Doctor Ilyas makwabcina ne, balaraben kasar Lebanon ne mai kirki da addini da tsananin kamun kai da nagarta. Kyawawan halayen Ilyas da addinin sa suka sanya ni amincewa da abota da shi duk da ya ďan girmemun.

lecturer ne a bangaren medicine a cikin jami’ar liverpool kuma kwararren likitan mata a ciki asibitin makarantar. Idan da akwai wanda yayi supporting ďin soyayyar mu da Esha toh Ilyas ne. Ya bani shawarwari da dama akan yanda zan bullowa al’amuran da suke tsakanin mu da Esha amma Allah ya kaddara ba zamu yi aure ba.

Ko hutawa banyi ba yace nayi masa rakiya zuwa asibiti yana da patient ďin da yayi wa aiki yana so yaje ya ganta

Ba tare da damuwa ba na shirya muka shiga cikin asibiti. Lokacin da ya buďe ďakin da patient ďin take kwance tsayawa nayi still kamar gunki kirjina na wani irin bugun fanfalaki a sakamakon ganin wadda take kwance a kan gadon marasa lafiyar.

Esha ce kwance cikin kayan asibiti rungume da baby a jikinta tana kuka a hankali.

Gabaďaya kaina ya kulle, tunanina ya tsaya cak! Domin hoton da nake gani a gabana maijego ce da ďan labubun jinjirin da ta haifa wanda bai fi awanni biyu ba a duniya. Yaushe Esha tayi aure ta haiwu bansani ba? Waye ta aura? Yaushe ta manta da ni ta amince da soyayyar wani? Sai na mayar da kofar na kulle na koma gida cikin wani irin tashin hankali da ruďani. Duk yanda Ilyas yaso shawo kaina ban yarda nayi magana da shi ba a wannan yammaci.

Washegari shi ya fara buga mun kofa, ina ganin shi na mayar da kofar na rufe na koma gida, duk wata magiya da roko  sai da Ilyas yayi mun amma ban kalle shi ba saboda ji nake yi kamar babu wanda yaci amanata irin sa. Kusan kowanne wata muna musayar sakonni amma bai taba gaya mun Esha tayi aure ba, bai taba gaya mun halin da take ciki ba, ashe shiyasa ya dinga bani hakuri yana yi mun nasiha akan na hakura na bi abinda mahaifiyata ta zaba mun na bar maganar Esha. Toh ko dai shi ya aure ta??

Habawa! Sai naji kamar anyi mun allura na mike da sauri ban nemi ko jacket ba na futa daga gidana na tafi gidan Ilyas……

Ina shirin kwankwasawa na gan shi ya futo a ruďe cikin sauri, cikin wani irin yanayi ma karyewar zuciya da roko yace

“Kayi wa Allah da Annabin rahama ka biyoni kayi magana da Esha watakila yauce ranar ta karshe a duniya. Watakila akwai maganar da take gayamaka wadda ba zata sake samun dama ba idan baka je wajen ba a yau”

Ji nayi hankalina yayi mugun tashi na bi bayan shi babu shiri muka shiga mota muka yi asibiti cikin mu babu me cewa komai da nannuyan numfashin da muke saukarwa na tashin hankali daga ni har shi. Lokacin da muka isa Esha ta galabaita sosai, tana cikin ICU karkashin taimakon na’urorin likitoci.

Idona jajir na dubi Ilyas nace masa

“Ka gaya mun meye yake damun Esha? Me ya faru da ita bayan tafiya ta?”.

Cikin hawaye ya kama hannuna ya zaunar dani sannan ya soma magana a nutse.

“Ahmad da farko ina so ka yarda dani ka amince cewa duk abinda zan gaya maka babu son rai ko karya a ciki. Billahil azeem iyakar gaskiyar abinda ya faru zan gaya maka””Cikin gamsuwa nake jinjina kaina domin a iya zaman da nayi da Ilyas na san cewa ba shi da karya, ba shi da yaudara kuma ba shi da munafunci. Wani irin mutum ne salihi managarci mai dattako irin na kyawawan musulmai.

“Tun bayan tafiyarka Esha ta shiga matsanancin hali, musamman lokacin da ka gaya mata halin da kuke ciki da Mamanka! Ni take samu tayi ta kuka ina kwantar mata da hankali, duk hanyar da zan bi naga auren ku ya kullu da Esha wallahi Ahmad nayi, ni da kaina sai da na nemi brother ďinka Yakub nayi mi shi iya bayanin da zai gamsu, nan yayi mun cikakken bayani akan Dada da kuma halin da ake ciki da yanda ta ďauki zafi a kanka.

Ahmad ni masoyin ka ne na gaskiya, da kwayar zarra bazan so ka bijirewa iyayenka akan mace ba, saboda ko kaci nasara ka aure ta auren na ku bazai yi muku albarka ba. Don haka na ďauki ďamarar kawo masalaha a tsakanin ku, kai na dinga yi maka nasiha ina goya maka bayan yi wa Dada biyayya da hakuri da Esha itama kuma Esha na futo fili nayi mata bayanin komai sannan  dinga nuna mata muhimmancin iyaye da hakkin ďan su a gare su. Jikinta yayi sanyi sosai, kuma ta shiga mugun yanayi, amma ta dangana ta fawwala Allah, a dalilin ka muka yi wata irin shakuwa da Esha ba tare da na sani ba, musamman nake zuwa har gidansu ina ďaukar ta darasin addini da al’qurani domin tun daga lokacin da na bata lokaci nayi mata nasiha akan hakkin iyaye da wajabcin kyautata musu sai taji ilmin addini yana bata sha’awa. Tun daga kan tsarki zuwa alwala sallah muka fara da Esha, ina yi mata gyare gyare ina koya mata abubuwan da bata iya ba, cikin watanni uku Esha ta chanja ta koma kamila nutsatstsiya wadda zaka yi wa kallo ďaya ka fahimci musulma ce ita mai riko da addini. Daga baya saboda rashin lokaci ta shiga online Islamic lesson take kara sanin wasu abubuwan.+

Nine na yanke muku contact ta hanyar baka shawar daina magana da ita saboda ka samu ka manta da ita, ita kuma da kanta ta zabi daina magana da kai saboda ka samu damar yi wa Mamanka biyayya. Ahmad Ehsa tana tsananin sonka fiye da duk yanda zan zauna nayi maka kwatance, soyayya mai tsabta da armashin da ta sadaukar da farin cikin ta saboda ka rabauta kayi wa iyayen ka biyayya.

Watanni shida da komawar ka Nigeria fire accident ya faru a gidansu Esha lokacin tana cikin makaranta dalilin da ya kubutar da ita kenan ta rayu domin dukansu mutanen gidan babu wanda aka samu da rai. Ba sai na gaya maka halin da Esha ta shiga ba, ka kiyasta a ranka. Faruwar wannan abu ya sanya na sadaukar da lokacin hutuna gabaďaya wajen kasancewa da Esha, nayi mata nasiha nayi mata karatun al’qurani na janyo mata ayoyi da hadisan da suke magana akan kaddara da mutuwa da muhimmancin hakuri. Tayi matukar juriya da hakuri kuma ta karbi kaddarar ta. Ana cikin haka Uncle ďin ta Waheed yazo tafiya da ita America inda yake zaune saboda bata da kowa a London, hankalinta yayi masifar tashi domin shi Uncle ďin na ta mugu ne, ba sa shiri da babanta kuma ta tabbatar da akwai manufar da ya sanya yake son tafiya da ita. A wannan lokaci ne ta durkusa har kasa tana kuka tace na taimaka na aure ta, idan yaso bayan wani lokaci sai na sake ta, ita burin ta kawai ta kubuta daga hannun Uncle Waheed. Nayi matukar kokarin nuna mata babu auren manufa a addinin musulunci amma halin da take ciki ya sanya ta kasa fahimta ta.

A wannan lokacin nayi niyyar auren Esha da zuciya ďaya da gaskiya da amana ba don ina son ta ba sai don kawai na ceto rayuwar ta daga halin da take ciki. Wannan shi ne sanadin aurena da Esha kuma shine dalilin kubutar ta daga hannun Uncle Waheed wanda yaso handame dukiyar da iyayenta suka bar mata watakila ita ma ya tura ta inda suka tafi.

Naso Kwarai na tuntubi gida kafin muyi aure da Esha amma taimakon gaggawar da take bukata bai bani dama ba da kuma sanin cewa mahaifa na basu da tsaurin ra’ayi akan ýaýansu. Iyayena sun rasu ina yaro, daga ni sai kanwata muka taso a hannun kakanninmu don haka babu bata lokaci muka yi aure da Esha.

Watanni biyu bayan auren na ďauke ta muka tafi Beiruit, ga mamakina gabaďaya dangina babu wanda ya karbi Esha, babu wanda yayi murna da aurenta, asali ma kora ta kakana yayi yace na koma wajen aikina baya bukatar ganina.

Hankalina da na Esha ba karamun tashi yayi ba, duk yanda nayi kokarin shawo kan su basu amince da ni ba, bacin ran su da nayi aure basu sani ba kuma na bar kabilar mu naje na auri bakar fata. Ban taba tunanin dangina suna da irin wannan nuna bambamcin yare da al’ada sai a wannan lokacin, bazan iya rabuwa da Esha ba saboda ni ne gatan ta nine uwarta ubanta danginta. Na tabbatar idan na sake ta sai hakkin ta ya kamani don haka na ďauko ta muka dawo London da alkawarin a hankali da yardar Allah dangina zasu karbeta watarana.

STORY CONTINUES BELOW

Tunani da damuwa suka haďu suka gayyatowa Esha ciwon zuciya, kodayake suna da gadon shi amma sai wannan lokacin muka sani. Tun lokacin take shan wahala Ahmad, bamu san ma tana da ciki ba sai da ga baya, cikin halin yau lafiya gobe ciwo take har zuwa lokacin da muka yanke za’ayi mata aiki a futo da yaron wanda shima muka gano yana da irin ciwon na ta. At this stage nagano  cewa Esha bani take so ba, ta aure ni ne saboda gujewa Uncle ďin ta amma so ďaya ne tak! Kai take wa shi kuma ba zata daina ba, dalilin da ya sanya condition ďinta yake kara zama worst kenan!

Zuwa wannan lokaci sai dai muyi wa Esha fatan alkhairi saboda tana stage D ne kuma babu wani alamar nasara a yanayin jikinta…..

Lokacin da Daddy yazo nan duk yanda yaso hawayen shi basu riku ba. Tissue ya saka yana gogewa  cikin dabara wasu na kwaranyowa kamar an balle famfo. Mahmud sarkin raunin zuciya kuka yake sosai, saboda yaji a jikin sa shine wannan jaririn da Esha ta haifa, wata irin soyayya da tausayi irin wanda bai taba tunanin zai ji ba akan mahaifiyar shi ya lullube shi.

Mami ma kukan take mara sauti, duk da ba yau ta san wannan labarin ba amma tuna shi kaďai ya kan sanya ta hawaye balle yanzu da ake maimaita shi a gaban Mahmud!

Sun kai mintina goma sha biyar babu abinda yake motsi a falon sai shashshekar kukan su. Dakyar Daddy ya tsayar da kukan shi yayi gyaran murya yaci gaba da labarin…….

“Bamu samu damar sake magana da Esha ba, bamu kuma haďuwa ba Allah ta ďauki abar sa. A wannan lokacin ni ne na daure nake rarrashin Ilyas saboda mutuwar ta dake shi fiye da tsammani duk da cewa ya san karshen ciwon na ta kenan. A karkashin kulawar asibiti aka bar ka Mahmud kafin Ilyas ya samu nutsuwa.

Ranar da na fara ganin ka ranar Allah ya kinkimo wata irin soyayya mai ban mamaki ta saka mun a raina. Kamar ku ďaya da Ilyas, sai ka ďebo duhun fatar Esha, ban taba ganin wata halitta da aka cuďanya jinina da bargo da kashi da jijiya da ita ba irin soyayyar ka Mahmud. Ni Ilyas ya sanya nayi maka huďuba da sunan mahaifin shi sannan ya samo nurse mai kula da kai a cikin gidansa.

Shi sai ya daure ya tafi aiki amma ni bana iya ďarawa daga gefen ka, a kanka na koyi raino, bayar da madara, chanja diaper, wanka da komai na jarirai. Shi kansa Ilyas mamakin irin son da nake yi maka ya dinga yi, amma sai ya danganta hakan da soyayya ta ga mahaifiyarka.

Watanni na uku a London ban waiwayi gida ba, ba don ina da abun yi a London ba sai don kar na tafi na barka. Sai da Dada ta buďe mun wuta sannan na hakura na tafi. Ina komawa gida naci karo da sabbin masifa da bala’in intisar. Amma gabaďaya bana kula ta, bana ďaga ido na kalleta ko da zagina zata yi, mutuwat Esha da tausayin rayuwar da tayi ya buge ni ya tsaya mun a rai. Ga soyayyar jaririn da ta bari wadda ta shafe son da nake mata, ji nake kamar na kwato ka a hannun Ilyas na taho da kai Nigeria.

Haka rayuwata ta koma cikin zarya tsananin London da Nigeria ba tare da an san abinda nake yi a can ba. Tun Dada na mita har ta hakura saboda na koma wani sabon mutum abun tausayi mara karsashi da walwala. Sau goma Dada zata sakani a gaba tana tambaya ta abinda yake damuna sau goma zance babu komai. Tun tana tsangwama ta har na koma bata tausayi, har suka gaji suka hakura da sabon mutumin da na koma.

Shekara ta shuďe daga Zainab har Intisar babu wacce ta haiwu. Abun duniya ya taru yayi wa Dada yawa, ga Badi’a babu aure sai neman magana da take saka ta. Sulaiman matar shi ta juyar masa da hankali ba ya takowa sai tata. Ýaýan sa duk maza ne guda uku amma bata barin su zuwa wajen Dada, tun Dadan tana kulafucin su har ta hakura ta daina. Zaliha ita ta kara hura wa Sulaiman tsanar mu a zuciyar sa, ta dinga ďora shi akan cewa Dada bata kaunar shi mu take so saboda mahaifin mu ya mutu ya bar mata dukiya. Abubuwa suka taru suka yi Dada yawa, babu wanda yake tausar ta sai Zainab da Yakub, sai Uncle Aliyu idan yazo.

Wata ranar larabar da ba zata goge ba a tarihin rayuwata na sauka a garin London da asubahi ana ta ruwan sama.

Duk da haka ban iya wuce wa masaukina ba sai da na fara zuwa gidan ku domin na ganka anan na samu Ilyas cikin tashin hankali an yi mishi sako kakanshi ba shi da lafiya.

Yana son tafiya amma bai san yanda zaiyi da kai ba, ba zai iya tafiya da kai a wannan halin ba saboda bai san me zai ce musu game da kai ba, tunda har wannan lokacin kakannin shi na kan bakan su na cewa kar ya sake zuwa gare su sai ya rabu da wannan matar tashi bakar fata. A karshe sai karya yayi musu yace sun rabu, lokacin Esha na gab da haihuwar ka, ciwon ta yayi tsananin tashi. Toh yaje da kai yace musu me? Babu wani dogon tunani nace masa ya bar mun kai yaje ya dawo.

Cikin farin ciki ya yarda domin ya tabbatar da cewa ko shi ba zai gaya mun kaunar ka ba. Tunda aka haife ka bai siya maka wani abu domin wajabci  ba sai dai don sha’awa. Tun daga kan madarar ka zuwa kayan sawa da kayan amfani, kai har kuďin da ake biyan nurse na rainon ka ni nake biya. Duk abinda nagani na sha’awa na yara sai na siya maka, gabaďaya hankalina a kanka yake, wata irin soyayya nake maka mara misaltuwa wadda shi kan shi Ilyas ďin yake mamaki.

Ni ne na raka shi airport tare da kai, sai da jirgin su ya tashi sannan muka dawo. Da na dawo gida korar nanny ďin ka nayi saboda bata da amfani tunda ni nake yi maka komai, tun daga kan wanka, ba ka abinci, har goya ka nake yi a bayana kayi bacci. A wannan tsukin wata irin muguwar shakuwa ta shiga tsakanin mu, idan ba’a jikina ba ba zaka yi bacci ba, idan bani na baka abinci ba ba zaka ci ba. Kiri kiri kaki mai rainon ka ta taba ka komai sai ni.

A haka muka kwashe gomaki goma sha tara, sannan Ilyas yayi sako yace kakan na shi ya rasu kakar shi na cikin wani hali a dalilin rasuwar mijinta. Yana ganin cewa zaman shi a London ya kare dole ya koma kasar su yaci gaba da kula da kakar shi.”Sai da ya cika kwanaki talatin sannan ya taho a dalilin kirana a waya da Dada ta matsa da yi lallai na dawo gida, saboda ba wata harka nake yi a London ďin ba sannan ita tun a kan Esha ta tsani London gabaďaya ta tsani taji nace zan tafi garin London.

Ranar da Ilyas ya dawo sai da nayi mamakin irin rama da bakin da yayi. Gabaďaya ya fita hayyacin sa, ya koma abun tausayi. Sai bayan ya nutsu sannan ya soma yi mun bayani cikin tsananin damuwa

“Ahmad ina cikin wani hali na tashin hankali da tunani! Kakannina sune komai na a rayuwa, sune duniya ta sune farin cikina, sune gatana. Tunda na rasa iyayena kulawata ta koma hannun su, sune suka tsaya mun har na kai wannan matakin, Ahmad idan akwai abinda nake tsoro bacin ransu ne. Kakana ya rasu, kakata tana cikin wani hali na jimami da damuwa, abinda yasa na yanke komawa kasar mu kenan saboda ta dinga gani na a kusa da ita naci gaba da kula da ita.+

Damuwa ta guda ďaya ce wannan jaririn da bai san komai ba! A tunanin dangina tuni na rabu da Esha naci gaba da rayuwa ta, ďaukar yaro na kai musu a matsayin ďan da muka haifa wani gagarumin tashin hankali ne a gare ni, kakata zata kuma shiga wani halin da bansan abinda zai janyo mun ba. Sannan ko da sun yarda sun karbi Mahmud billahillazi ba zasu taba kaunar shi ba a dalilin mahaifiyar shi. Wannan duhun fatar tashi kaďai zai janyo masa tsangwama da hantara a cikin su. Mahmud marayan Allah ne wanda nake wa fatan ya samu intacciyar rayuwar da ba zai kukan maraici ba, amma bani da wannan damar bani da wannan ikon. Ahmad ya zanyi da Mahmud?”

Sai ya fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya da tada hankali.

Wani irin tausayi da karyewar zuciya ya kamani, mu gidanmu muna can muna neman jaririn ido rufe bamu samu ba, wani ya samu yana kukan yanda zaiyi da shi. A take wani tunani yazo mun, wanda nake jin zan iya fuskantar duk wani kalubale a kan shi.

A sanyaye na durkusa a gaban Ilyas ina hawaye nace

“Ilyas don Allah ka bani Mahmud! Ina son shi ina kaunar shi, so da kaunar da nake jin ko abinda na haifa bazan iya yi wa su ba. Nayi maka alkawarin Mahmud ba zaiyi kukan maraici ko na damuwa ko wahala ba. Wallahi zan rike maka amanar Mahmud har zuwa lokacin da zaka daidaita da dangin ka. Idan kuwa zaka yi mun lamunin bar mun shi har abada, Zan fi kowanne mutum farin ciki a rayuwata.”

Da mamaki ya dinga kallona hawaye na gudu akan fuskar sa.

“Ahmad zaka iya rike mun Mahmud? Zaka iya yi mun wannan alfarmar?”

“Ba alfarma zan maka ba Ilyas! Kaine za kai mun alfarmar bani wannan damar ta kasancewa da abinda nafi so a rayuwa.”

Cikin kuka yace

“Me zaka gaya wa Dada?”

“Kada ka damu da wannan mai sauki ne! Nayi alkawarin fuskantar kowanne irin kalubale akan Mahmud kuma nayi alkawarin rike shi amana har karshen rayuwata”

Sai ya rungume ni muka fashe da kuka gabaďaya har kaima ka taya mu.

Wannan shi ne silar kasancewar ka tare da ni Mahmud, shi ne dalilin samun ka da nayi a rayuwa. Mafi girman alkhairin da na taba cin karo da shi a rayuwata kuma mafi girma.

Washegari ya tattaro dukkan takardun asusun Esha da kadarorin da ta gada a wajen iyayen ta ya danka su a hannuna. Cikin rashin fahimta na kalle shi sannan nace

“Ilyas me zan yi da wannan? Mahmud kawai nake bukata ka bani, wallahi bazan karbi wani abu da ya danganci kuďi a wajen ka ba.”

A nutse ya soma bayani

“Ahmad wannan kuďin haqqin Mahmud ne! Gadon shi ne na mahaifiyar shi kuma babu wanda ya cancanci ya rike su sai kai saboda rayuwar Mahmud ta koma hannun ka, ta koma karkashin ikon ka, kaine za ka kula mi shi da dukiyar shi har lokacin da zai girma yayi hankalin da za ka iya mallaka masa su. Bansan me rayuwa za ta shigo da shi ba, bansan me zai faru ba amma ina ji a jikin bazan yi rayuwa da Mahmud ba………

Ahmad na bar maka Mahmud duniya da lahira, duk ranar da Allah ya bani iko zan zo da kaina Nigeria, Zan neme ka kuma zan ďauke ku kai da Mahmud na sada ku da ahalina. Idan Allah ya bamu aron numfashi.

STORY CONTINUES BELOW

Daga wannan rana sunan ka ya tashi daga Mahmud Ilyas ya koma Mahmud Ahmad Lamido, birth certificate ďin ka ne kawai yake ďauke da sunan mahaifin ka. Wanda shima daga baya nayi maka renewing ďin shi da Sunana.

Daddy yana kawo wa nan ya dubi agogon hannun shi,

“Lokacin sallah Mahmud”

A sanyaye duk suka tashi suka shiga ďakunan su don yi  alwala sannan Daddy yayi musu jam’in sallar magrib.

Duk yanda Mami taso su ci wani abun babu wanda ya iya kallon abincin balle ya kai bakin sa. Gani irin kaguwar da Mahmud yayi ya sanya Daddy komawa wajen zaman sa yaci gaba daga inda ya tsaya.

“A kwanaki bakwai muka kammala duk shirin mu kowanne yayi niyyar tafiya kasar shi ya fuskanci sabuwar rayuwar da take jiran shi. Sai da Ilyas ya ga tashin mu ni da kai a jirgi sannan ya koma gida. Ina cikin jirgi a zaune kana rungume a jikina kana bacci, ban iya saka ko lemo a bakina ba saboda tunanin yanda zamu kwashe da Dada.

Na tabbatar wani gagarumin rikici ne yake jirana sai dai zuciyata tayi wani irin tauri da shirin da babu abinda ba zan iya fuskanta ba a kanka. Nayi ďamarar fuskantar kowanne irin kalubale a kanka, kuma nayi alkawarin babu mahalukin da ya isa ya raba ni da kai in dai ina numfashi.

A cikin wannan halin muka sauka a garin Lagos! Sai da nayi kwanaki biyu da kai a asibiti a sakamakon zazzabin da ya kama ka kafin mu tafi Yola.

Karfe bakwai na daren ranar alhamis ďin watan December muka sauka a Yola a kofar gidanmu.

Yakub da Yaya Sulaiman na fara tozali da su a kofar gida sun dawo daga masallaci kenan! Ganina da yaro ya katse musu hanzari suka zuba mun idanu suka kallo cikin tsananin mamaki. Nikuwa na ďaure fuska tamau kamar bangane me suke nufi ba. Su suka taimaka mun da luggage ďinmu zuwa cikin gida nikuma na tsaya na sallami driver ďin sannan na biyo su.

A falon Dada na same su gabaďaya. Dada, Yaya Sulaiman, Zaliha, Zainab, da Intisar da Badi’a dukansu a gaban Dada. Da sallama na shiga falon, amma tsananin mamaki ya sanya su kasa amsa mun sallamar saboda yanda na kake a rungume a kirjina cikin ďamarar goyo ta bature kaďai ya isa ya tabbatar musu da cewar daga Turai na taho da kai. Balle yala yalan gashin kanka baki siďik da ya rufe maka fuska, sun tabbatar babu me irin shi a Nigeria ko cikin mu fulani.

A sanyaye na ciro ka daga cikin ďamarar ka. Na saba ka a kafaďa sannan na isa gaban Dada na durkusa kaina a sunkuye. Ta kai mintina biyar bata iya magana ba, sannan dakyar da tsoro da fargaba tace

“Ahmad a ina ka samu ďa?”

Bakina ne yayi mun wani irin nauyin da na kasa buďe shi balle na zaro wata kalma daga cikin sa.

“Kar kace mun Ahmad aure kuka yi da wannan baturiyar kuka haiwu? Ahmad kar Kace mun yaron nan ďan ka ne?”

Cewar Yaya Sulaiman cikin karaji.

A take naji wani irin abu ya yanyameni, wani sanyi ya ratsani na sabuwar idea ďin da ta shiga kaina. Ashe ina da wannan damar? Idan haka ne ai ba sai nayi amfani da wata hanyar ba wannan zata fi mun masalaha duk da mugun haďarin da yake cikin ta.

Cikin wani irin matsanancin mamaki da tsoro da ruďani Yakub yace

“Ahmad shirun ka na nufin maganar Sulaiman gaskiya ce? Aure kayi da Esha?”

Ni dai ban ďago kaina ba balle nace wani abu sai wasu irin hawaye da nake zubarwa masu tsananin zafi.

Cikin haka ka farka ka soma kuka a hankali. Na sake rungume ka a jikina ina jin kamar za’a kwace mun kai.

“Toh wallahi kayi kaďan! Kayi tsararo kayi karya ka kawo mana wannan yaron cikin gidanmu cikin ahalin mu! Yanda kazo da shi haka zaka koma da shi kuma ka tsammaci sakamakon abinda ka aikata ga Dada.”

Yaya Sulaiman yayi magana a karo na biyu. Sannan Intisar tayi wani tsalle ta dire cikin tsananin masifa da bala’i.

“Kasan Allah? Wallahi billahillazi kayi kaďan kayi tsararo ka kawo mun ďa na rike maka. Wallahi ba ka isa Ahmad? Ďan shege a gidanmu? Waye zai rike maka shege?”

Sai a lokacin talalar bakina ta kwance na ďago kai cikin wani irin fushin jin sunan da ta kiraka nace

“Kar ki sake ce masa shege! Ďan sunna ne kamar ki”

Cikin wata irin kuwwa tace

“Au dagaske auren ta kayi? Auren baturiyar kaje kayi? Dalilin da yasa kenan idan ka shura kafa ka tafi London baka iya dawowa sai Dada tayi fushi? Ahmad rashin mutuncin da kayi wa Dada kenan? Toh wallahi yau zamu ga wanda zai rike maka wannan yaron a gidan nan zamu ga wajen kwanan shi “

Sai lokacin Yakub yayi magana cikin sanyi da wani irin tone mai nuna irin yanda zuciyar sa ta karairaye da abinda yake faruwa.

“Brother dagaske ka auri Esha? Kuma wannan ďan naka ne?”

Bansan yanda akai na tsinci kaina da girgiza mai kai ba alamar tabbatar wa.

Wani irin salati Badi’a ta rattaba ta soma kuka tana cewa na cuci Dada na

Na cuce su kuma ba zasu taba yafe mun ba. Yaya Sulaiman da Intisar na taya ta da la’antar halina da abinda na aikata.

Cikin wani irin hali Dada ta mike ta shiga ďakin ta kamar za ta kifa, Yakub ya tashi da sauri ya bita yana rike ta. Yaya Sulaiman ya mike yana cewa

“Bari naje na kirawo likita don na tabbatar Dada na dab da shiga wani hali.”  Ya yafuto Badi’a da hannun shi suka futa tare. Intisar kuwa kuka ta saka tana masifa tana tsinuwa da Allah ya isa, Kafin ta ďau mayafin ta tana cewa

“Ni na tafi gidanmu wallahi bazan sake zama da kai ba”

Har lokacin a tsugune nake kana kan cinyata hawaye ya wanke mun fuska, zuciyata na wani irin zafi da zogi da ciwo kamar zata futo. Fargaba da tunanin hukuncin da Dada zata yanke a kaina suka lullubeni. Da wani taushi da laushin sautin da wani mahaluki bai taba yi mun magana da shi ba Zainab ta matso tace

“Yaya Ahmad ni zan rike maka wannan jaririn zan taya ka rainon shi kuma zan yi supporting ďin ka akan shi komai runtsi komai wuya domin ni na yarda da kaddara kuma na tabbatar da cewa rabon wannan yaron ne yayi aiki a kanka ka aikata haka. Ko babu komai ina farin ciki da ya kasance ba ta mummunan hanya ya futo ba aure kuka yi kuka haife shi. Ka bani damar kulawa da shi Yaya Ahmad, ni ďin bani da burin da ya wuce samun jariri a tare dani.”

Waďannan kalamai na Zainab bazan manta da su ba har na mutu domin ban taba samun kalaman da suka sani farin ciki da kwanciyar hankali ba irin su. Wannan dalili ya sanya bazan daina ganin darajar Zainab ba har kasa ta rufe mun idanu. Domin ita ce mutum na farko na ta ba taimako a lokacin da kowa ya juya mun baya.

Ina nan tsugune ta haďa ruwa mai zafi tazo ta karbe ka tayi maka wanka ta shafa maka mai ta suturta ka ina miko mata dukkan abin amfani, sannan ta haďa maka madarar ka ta baka, ga mamakina ba ka yi wa Zainab kuiya ba kamar yanda kake wa dukkan mutumin da yayi kokarin taba ka a jikina. Kana shanyewa ta sanya ka a baya ta goya ka sannan ta ďauki kayan ka tayi ďakin ta da su ta dawo.

“Kaje kayi wanka ka huta! Nayi maka alkawarin sai inda karfina ya kare akan wannan yaro! Kallo na farko nayi masa ya shiga raina, ko ba jikin ka bane zan rike maka shi amana balle ďan da ka haifa a cikin ka. Nayi maka alkawari zamu fuskanci kalubalen tare kuma zamu yi nasara””Da taimakon Zainab nayi wanka nayi sallolina amma ban iya saka komai a bakina ba na futa daga gidan zuwa gidana na zauna ina tunanin abinda zai faru damu ni da kai. Da matakin da Dada zata ďauka a kan mu.

Yanda naga rana haka naga dare duk da gajiyar da take tare da ni, sai gabbanin asuba sannan wani bacci mai nauyi ya ďaukeni bani na farka ba sai karfe takwas. Ina buďe idanu naga Yakub a kaina alamar shi ne yake tashina. Jiki a mace na mike na shiga banďaki nayi alwala na gabatar da sallar asuba da lazimina, domin yana tashin nawa ya juya ya futa.

Banyi gigin shiga gidan mu ba duk da ina bukatar ganin ka, amma bani da kwarin guiwar haďa idanu da Dada. Haka naci gaba da zama a wajen da nayi sallah babu wanka babu abinci babu bacci kamar maraya ina sakawa da kwancewa akayi sallar azahar.

A ďakin nawa dai na kuma yin sallar saboda kafafuna sunyi laushin da ba zasu taku su futa ko kofar gida ba.

In gajarce maka labari dai a wannan halin na wuni tunkur ďigon ruwa bansa a bakina ba. Daga nan wani irin zazzabi ya lullube ni na soma rawar ďari jikina yana wani irin rawa. Kaina kamar zai tsage don ciwo da tunani da tashin hankali, tun ina gane halin da nake ciki har na futa daga hayyacina.

Bayan wani lokaci na buďe idanu na ganni akan doguwar kujerar falona hannuna ďaure da drip. A hankali na ďaga idona domin ganin wanda suke falon. Da kaifafan idon Dada na soma tozali, nayi maza na mayar da kaina kasa cikin wani irin yanayi. Har likitan ya kammala nazarce nazarcen sa a kaina ban sake ďagowa ba sannan naji yana cewa+

“Yunwa ce da damuwa suka yi masa yawa yayi losing control, amma ba wata matsalar. A bashi ko tea ne yasha zanje na siyo magungunan na dawo”

Sai naji muryar Yakub yana yi masa godiya ya futa. Rufe idanu nayi wasu hawayen suka balle mun kamar an kun a famfo. Jikina ya sake ďaukar wani zafin yana rawa kamar mazari. Babu zato babu tsammani naji tattausan hannun da yafi na kowanne mutum saukar da nutsuwa a jikina yana shafa goshina sannan ta soma magana da sautin da bamu taba sanin ta da shi ba, wato mafi taushin sauti ta soma magana

“Kwantar da hankalin ka Ahmad kada wani ciwon ya kama ka! In dai nice na yafe maka duniya da lahira kuma na karbi kaddara. Ita wannan kaddarar rabon yaron ina zan kaita? Idan nayi fushi zan dawo da hannun agogo baya ne na goge abinda ya faru? Allah ya kiyaye na gaba Allah ya sanya iyakar kaddarar kenan.”

Wata irin nannauyar ajiyar zuciya na sauke wadda ta tafi da dukkan ciwukan da nake ji a jikina ta dawo mun da kuzari da nutsuwa da kwanciyar hankali. Bansan lokacin da na tashi na rungume Dada ina sakin wani irin kuka ba. Cikin kuka nake rokon ta gara da yafiya ina cewa bazan sake ketare maganar ta ba.

Sai da muka nutsu sannan Yakub yayi gyaran murya ya soma magana.

“Ahmad abinda ya faru ya riga ya faru amma duk da haka sai nayi maka faďan rashin kyautatawar da kayi. Abinda kayi ya bani mamaki ya bani kunya kuma ban tsammace shi daga wajen ka ba. Ina ilmin ka da tarbiyyar ka da biyayyar ka? Kayi aure ba da izinin magabantan ta ba Ahmad? Me kake tunani? Wanne irin shaiďan ne yayi maka huďuba?”

A sanyaye na kama hannun shi nace

“Yakub ka yarda dani, wannan abun da ya faru wata irin kaddara ce wadda bazan iya kufce mata ba. Wallahi  billahil azeem ina gudun bacin ran Dada da fushin ta fiye da komai a rayuwata…….wallahi banyi niyyar cutar da Dada ta hanyar cusa mata irin wannan bakin cikin ba. Ku yafe mun ku yarda dani”

Da matukar dauriya Dada tace

“Ina take yanzu?”

Kaina a kasa nace

“Ta rasu! Tana haihuwar shi ta mutu”

Wani irin shock da tausayi ne ya bayyana akan fuskokin su, Dada ta soma share hawaye tana cewa

STORY CONTINUES BELOW

“Allah ya raya shi! Allah yasa mai albarka ne!”

Sannan Zainab ta shigo da kai a goye a bayanta. Ta sauko ka ta miko mun kai na karba rungume ina sake fashewa da kuka mai tsanani na farin cikin samun damar rike da nayi.

Wannan shine mafarin shigowar ka cikin rayuwar mu. Sai Allah ya sakawa ahalina kaunar ka.  Dada wata irin azababbiyar soyayya take maka irin wadda zaka yi mamaki, bata rabo da ďaukar ka da yi maka wasa, Zainab kuwa ko kuda bata bari ya taba ka, hakana Yakub yake ji da kai. Sai ya kasance ni kaina dakyar nake samun ďaukar ka, idan na cika zakewa Dada tace na fiya ratsin kunya don haka na kama kaina na hakura da kula ka duk da cewa bani da burin da wuce haka.

Sai da akayi wata uku ana rigima kafin Intisar ta dawo. Naso ace basu dawo da ita ba amma Dada ta matsa da bada hakuri sai da ta dawo.

A cikin gidan nan baka da matsala sai ta Badi’a. Kullum cikin yi maka mugunta take, Kyara da tsangwama kala kala, suyi ta faďa da Zainab tunda a kanka Zainab bata da hakuri bata ďaga kafa. Don haka zaman nasu gabaďaya yaki dadi, ita kuma Badi’a taki aure sai neman magana da tashin hankali.

Bansan ya aka yi ba Dada sukayi magana da Yakub akan mu tafi da shi London na jaddada masa shaidun aurena da Esha da kuma inda muka zauna. A wannan lokacin ne na samu Yakub dole na feďe mi shi komai.

Yana da sanyin hali da saukin fahimta don haka ban sha wahalar shawo kansa ba. Muka tafi London tare da shi a cikin satin.

Tun bayan wannan lokacin ban sake neman Ilyas ba, saboda tsabar gudun kada yace ya daidaita da danginsa a kanka. Na dinga addu’a Allah yasa kada ya waiwayo mu don kar ya chanja shawara ya rabani da kai. Duk da nayi mamakin yanda aka yi na rasa lambar wayar da nake samun sa ta gidan su kuma shi bai nemi ba. Amma ban wani damu ba saboda soyayyar da nake maka.

Haka rayuwa taci gaba kana hannun Zainab kana samun kulawa da tarbiyya mai kyau. Sai bayan shekaru shida Intisar ta haifi Abubakar, Dada tayi matukar murna domin ta fara tunanin ko iya rabon namu kenan, shi ma Yakub da Zainab shiru babu labari don haka ta ďauki soyayyar duniya ďora akan jikokin ta. Bayan shekara biyu Intisar ta sake haihuwar Umar, inda tasha matukar wahalar da sai da aka cire mata mahaifar gabaďaya aka huta.

Haka rayuwa taci gaba cikin aminci da kwanciyar hankali kana samun dukkan kulawa daga wajen Zainab da Yakub kamar su suka haife ka, ganin haka ni kuma sai na danne mugun son da nake yi maka na bar musu ragamar ka a hannun su.

Abu na gaba da ya ďaga mun hankali shi ne halin da Intisar ta shigo da shi na son raba kanku kai da ýan’uwan ka. Ta dinga kokarin cusa musu tsanar ka kai kuma tana kokarin nuna maka na Zainab ce babar ka ba, babar ka baturiya ce ba ma musulma ba. Badi’a ma kamar ta janyo ka ta jefa ka a wuta saboda tsana da tsangwama. Toh Allah dai ya taimaka ta samu miji a garin Kano, Dukanmu ba karamar murna muka yi ba, saboda ko Dada ta gaji da zama da ita. Aka yi biki aka kaita garin Kano hankali ya kwanta, shekara ďaya tak Allah ya sauke ta lafiya ta haifi ýa mace, murna a wajen Dada ba’a magana, aka ďauko ta aka dawo da ita gida wanka. Komai Zainab ce take yi wa babyn nan amma hakan bai janyo mata farin jini a wajen Badi’a ba, ta riga ta sakawa ranta tsanar ta.

Yaye ne yayi sanadiyar dawowar Nuratu hannun Dada, ga tsohon cikin da Badi’an take fama da shi. Sai Dadan ta ďauko ta, daga nan kuma ta rike ta ta karfi da yaji domin Badi’a bata so ba don dai Dadan tafi karfin ta ne.

Matsin lambar da kake fuskanta daga wajen Intisar da tsoron gurbatattun kalaman da take gaya maka kada suyi tasiri a kanka ya sanya kana kammala primary school na ďauke ka zuwa kasar Turkey, a wannan lokacin ina harkar shigo da kayan gida daga kasar Turkey, haka kawai kasar ta kwanta mun, sai nake ganin yanayin ta zai dace da jikin ka, sannan ina yawan zuwa, kusan rayuwata a can ma tafi a Nigeria yawa.

Harkar wannan kayan gida gabaďaya da kuďin ka na shige ta da niyyar na kafa maka kasuwanci da su wanda nake fatan ya habaka kafin lokacin da za ka girma kayi hankalin da zan danka maka komai. Zainab tayi bakin ciki da takaicin raba ka da nayi da gida amma da nayi mata bayanin dalili na sai ta gamsu. Sai dai ita da Yakub basa rabo da zuwa ziyarar ka akai akai.

Kana aji biyar a sakandire Allah ya baiwa Zainab rabon Zahra! Na san ba ka manta irin farin cikin da aka yi ba, lokacin Yakub ya shiga harkokin siyasa tsumdum ana damawa da shi. Duk lokacin da nayi tunanin Ilyas sai hankalina ya tashi, tun bana damuwa har na tabbatar cewa shirun nan ba lafiya bace. Na shiga binciken inda zan samu contact ďin shi amma cikin rashin sa’a babu wanda ya san takamaimai ďin garin su da cikakken adreshi sai dai sunan garin kawai.

Ragon azancin da nayi shi ne rashin karbar cikakken adreshin Ilyas kamar yanda na rubuta masa cikakken namu adreshin da ko daga ina ya taho Nigeria ba zai bata ba.

Abu na biyu da sake ďaga mun hankali shi ne lokacin da Intisar ta dinga yi wa dukiya ta ďauki ďaiďai tana salwantar wa bansani ba. Na karshen shi ne lokacin da muka tafi grad ďin ka Turkey har da Dada, inda ta kwafi sign ďina ta take banki ta cire makuden kuďaďe ta gudu. A zahirin gaskiya tun daga wannan lokacin na samu karayar arziki domin tayi wa dukiya ta illah ba karama ba, amma da yake akwai business ďin da nake yi da kuďin ka ba’a ankara da hakan ba. Ganin haka ya sanya na ďaga ďaya cikin gidajen da Esha ta mallaka guda biyu a garin London na siyar da ďaya, wannan kuma wanda muke ciki shine asalin gidansu Esha inda suka yi rayuwa.

Da kuďin gidan na gina cement factory a Nigeria wanda yayi wata irin karbuwar ban mamaki. Tun daga lokacin kasuwa ta buďe mun, duk abinda na taba sai Allah ya sanya masa albarka kuďin kamar ninka ake yi ba da ciniki ba.

Tun a lokacin nayi kiyasi na kayyade cewa 40% ne kuďina a cikin dukkan harkokin da nake yi 60% naka ne. Nayi rubuta akan komai na ajiye ina tunanin ranar da zan  mallaka maka haqqin ka.  Lokacin Yakub yana kujerar governorship na Yola, ba shi da wani lokaci sosai sa na harkokin siyasa don haka abubuwa suka kara dagule mun.

Na sha niyyar yin kundunbalar sanar wa da Dada gaskiya amma tunanin abinda zai biyo baya sai ya sage mun guiwa ya bani tsoro, ina kuma ganin kamar akwai lokaci a gaba, watakila kuma Ilyas yazo ya neme ni. Sai na kwantar da hankalina naci gaba da addu’a.

Lokacin da Yakub ya zama kakakin majalisa, mun zauna mun shirya magana sosai akan hanyar da zamu bi mu gano inda Ilyas da dangin sa suke saboda tunanin tabbas wataran gaskiya zata yi halin ta kuma a wannan lokacin daga ni har kai zamu bukaci sanin ahalin ka. Har yayi magana da ambasadan kasar Nigeria a Lebanon akan hanyar da za’a bi ayi binciken, Ilyas yace mun family Hassan El-masry fitattu ne a garin su amma kuma sunan shiyyar da suke ne ban sani ba, na dai san cewa a Beuruit suke wato babban birnin kasar Lebanon. Munyi maganar nan da sati biyu Allah yayi wa Yakub rasuwa. Mutuwar da taso tafiya da hankalina da tunanina da nustuwa ta gabaďaya. Ban taba tunanin zan warke daga raďaďin ciwon mutuwar Yakub ba, ban taba tunanin zan dawo dai dai har na koma harkokina ba. Daga wannan lokacin na jingine maganar Ilyas a gefe na maida hankali ga halin da Dada da Zainab suka shiga na mutuwar Yakub, a lokacin da nima na tattaro na dawo Abujan gabaďaya saboda na ga hankalin Dada yafi kwanciya anan tun lokacin da Yakub ya ďauko su gabaďaya sanda zai shiga office.

A haka rayuwa taci gaba da tafiya abubuwa suna juyawa, a hankali na samu nutsuwa hankalina ya dawo jikina naci gaba da gudanar da harkokina cikin karfin hali domin rashin Yakub ya bar mun wani babban gibin da ba zan taba maye gurbin shi ba a rayuwa ta.

Sai kuma wani tashin hankalin ya sake faďo mana a dai dai lokacin da nake kokarin saita al’amuran da suka cuďe mun, wato rasuwar Jawahir, ina dab da cimma burin ganin kayi aure ka ajiye iyali, watakila sai nafi samun hanyar da zan sauke nauyin da yake kaina a saukake.

Tun daga lokacin mutuwar Jawahir na shiga fargaba da ruďanin yanda zanyi da kai, saboda yanda ka nuna kuru kuru baka sha’awar business aiki zaka yi  duk hanyar da zan bi na karkato da ra’ayin ka na bi amma banyi nasara ba. A dole na rabu da kai ka dawo kasar nan saboda abu biyu, na farko kwanciyar hankalin ka da nutsuwar ka a sakamakon halin da mutuwar Jawahir ta jefa ka a ciki. Na biyu, gani nake yi kamar wataran Ilyas zai waiwayi kasar nan, ko ya turo wani na shi, Dalilin da ya sanya na dage ka taho Liverpool university kenan a maimakon university ďin da ka zaba.

Kullum kwanan duniya zullumi na karuwa yake yi game da yanda zan sauke wannan babban nauyi a kaina ba tare da asiri na ya buďu ba. “

Tun ina ganin ina tsammanin Ilyas na gaji na futar da rai da zuwan sa. Na tabbatar akwa dalilin da ya hana shi neman mu amma bansan ko menene ba. Na fara tunanin mutuwa da yanda rayuwa take da rashin tabbas, komai na iya faruwa ba tare da shiri ko tsammani ba. Na tabbatar idan na mutu da wannan nauyin na bar baya da kura kuma ban sauke amanar ka ba don haka na nemi lawyer na muka yi rubutu akan komai na gaya masa duk abubuwan da ya kamata ya sani sannan na saka hannu.
Na daďe ina wasiwasin yanda zan bullowa tunkarar ka da wannan magana na rasa hanya. A dalilin ciwon ka da baya son bacin rai da tashin hankali. Na tabbatar komai zai iya faruwa idan kaji wannan tarihin. Naje saudiyya nayi addu’a yafi a kirga akan wannan lamari, na daina bacci na daina walwala na kasa samun nutsuwa, gani nake kamar zan iya mutuwa ban sauke wannan nauyi ba. A karshe nayi kundun bala na kira ka na baka umarnin saka hannu akan wannan takardun, da niyyar ba zan gaya maka komai ba saboda tsoron ciwon ka, nayi imanin idan kaji wannan magana babu abinda zai hana ya tashi.+
Sannan neman maka auren Amina nayi shi ne saboda na san kana bukatar macen da zata yi supporting ďin ka a gaba, wadda zata tsaya maka a lokacin da ka shiga ruďani da tunanin tarihin ka, mace ba irin Safna mara tarbiyya ba. Wadda za ta tallafa maka ta inganta maka rayuwa ta kuma tarbiyyantar maa da ýaýanka tarbiyya irin ta addinin musulunci. Ko da wasa banyi tunanin za ka amshi tayin auren Safna ba, amma ganin kaji ka gani kana so ya sanya bana son matsanta maka tun da namiji mijin mace huďu ne sai na yanke hukuncin nemar maka wata matar nutsatstsiya irin wadda ta dace da rayuwar ka. Ko da ba lallai ka gane hakan ba sai a gaba. Nayi matukar sa’a kai ďin mai biyayyar da ba ka tambaya ne akan hukuncin da na yanke a kanka balle kayi mun musu.
Sai bayan wannan lokacin ne kuma Barrister ya gayamun cewa ya kamata na yi wa Dada bayanin komai domin gudun tashin hankali da ruďanin da za ta shiga idan taji maganar daga sama ba daga gare ni ba. Nine na san yanda zan bullo mata da bayanin da zanyi mata.
Shi ma na daďe ina sakawa da kwancewa kafin na samu karfin guiwar yi wa Dada bayani. Shi ne tayi ďaukar zafin da na daďe ban gani a tare da ita ba. Tace lallai sai an haďa family meeting nayi bayani a gaban kowa kafin ta san hukuncin da za ta yanke a gare ni da Maminka.
Na taho London domin na same ka nasan ta hanyar da zan bullowa yi maka wannan irin tsatstsauran bayani sai na same ka kwance rai a hannun Allah babu inda kake…….
Mahmud wani irin yanayi yake ji a jikin sa irin wanda ba zai iya fassarawa ba. Ko ba komai ya godewa Allah da ya kasance ya futo ta tsatson musulmai kuma ta hanyar aure musamman da Daddyn ya tabbatar masa da nagartar halayen mahaifin sa da taimakon da yayi wa mahaifiyar sa. Sai yaji wani sanyi da salama, haďe da wata irin kewa da bukatar ganin su a rayuwar shi ko da a hoto ne, wata tsabtatacciyar soyayyar su ta mamaye zuciyar ci kamar ya rufe idanu ya buďe ya gan shi a duniyar su. But Yaya zaiyi? Kaddarar shi kenan! Godewa Allah zai yi da bai faďa mugun hannun ba, bai shiga hannun da zai yi danasani ba. Asali ma wannan silar ce ta samar mi shi irin wannan nagartacciyar ingantacciyar rayuwar mai cike da tarbiyyar addinin Islama. Idan har yayi danasanin kasancewar zama karkashin kulawar iyaye irin Mami da Daddy toh yayi wa Allah butulci yayi wa kansa rashin adalci. Abu guda ďaya ya tsaya akai, dole ya taimakawa Daddy wajen futar da shi daga cikin matsalar da yake ciki. Zai ba shi kwarin guiwa goyon baya wajen tabbatar da yin duk abinda Dada ta bukata daga gare shi. Kwarai babu mutum irin Dada da ba zaiyi fushi da irin wannan babban al’amari ba.
Yayi alkawari sai ya daidaita tsakanin Dada da Daddy, sai ya gyara tsakanin Dada da Mami kuma zai tsaya tsayin daka wajen ganin cewa kan wannan family bai rabu a dalilin shi ba.

Kwarai Mamud ya baiwa Daddy da Mami mamaki! A tunanin su ciwon ss zai koma ýar gidan jiya ko kusa da haka, ko kuma samun wani sauyi na fuska daga gare shi, amma sam babu ko ďaya! A maimakon hakan wata irin nutsuwa ce ta saukar masa da kamewa tare da haba haba da su kamar wani abu bai gifta ba. Duk da bai ce komai ba, a kalla ba su hango tashin hankalin da suka tsammata daga gare shi ba.

STORY CONTINUES BELOW

Washegari karfe takwas na safe Mahmud ya shigo gidan cikin shigar gym domin likitan sa ya futar masa da tsarin motsa jiki wanda zai taimakawa lafiyar shi. A kitchen ya samu Mami tana gasa bread ďin da zasu ci da naman kan ragon da ta bararraka tun shekaranjiya ta saka a fridge suke tsakura suna warming da safe.

“Good morning Mamina!”

Sai da ta sauke ýar ajiyar zuciya sannan ta juyo cikin farin ciki tace

“Morning my son! Ka kwana lafiya? Ya jikin ka?”

Cikin murmushi yace
“I am feeling very good Mami”

Daga nan ya zauna akan kujerar dinning ďin kitchen, suna hira tana aikin ta har ta kammala. Anan suka karya su biyu saboda Daddy ya wuce Oxfordshire tun da asuba.
Washegari bayan sun idar da sallar magrib Mamud yayi gyaran murya yace

“Daddy ina son nayi magana da ku don Allah”
Yana ganin yanda yanayin su sauya, hankalin su ya tashi, ya lura sun koma very sensitive tun shekaranjiya, ko motsi yayi sai su razana, idan zai yi magana sai tsoro ya bayyana karara a fuskokin su.
“They love him too much! They are afraid to lose him! (Suna tsananin kaunar shi! Suna tsoron rasa shi)”

Murmushi yayi sannan ya soma magana cikin soft tone(sauti mai taushi)

“Daddy next week ne follow up ďina daga shi sai bayan sati shida zan koma ganin likita! Ina so idan na kammala mu tafi Nigeria!
Ina so muje gida mu fuskanci wannan matsalar mu warware ta.
Daddy idan har wannan labarin da ka bani shi ne asalina toh ni banga abun kaico a cikin sa wanda zanji kunya idan an bayyana ba. Labarin babu komai a cikin sa sai soyayya da sadaukarwa. Bana danasanin abinda ya faru dani kuma bana jin kunyar fuskantar kowanne mahaluki da wannan sabon sunan nawa kuma bana jin tsoro ko fargabar kowanne irin kallo za’a yi mun.
Weakness ďina guda ďaya ne Daddy!
Fargaba ta da tsorona guda ďaya ne!
Na wayi gari ba kwa tare dani, na wayi gari kun juya mun baya, na wayi gari kun chanja mun matsayi!
Shine kaďai abinda zai gigita ni a duniya. Idan har zaku cigaba da tsayawa a bayana, zaku ci gaba da sona, zaku ci gaba da kallona a wannan babyn da kuka raina da hannun ku, zaku ci gaba da kasancewa tare da ni, ina tabbatar muku da cewa babu abinda zai girgiza ni. I will survive kowanne irin tashin hankali da kalubale komai girman sa.
Daddy zamu je Nigeria da ku, za’a tara family gabaďaya kuma za ka maimaita wannan labarin da ka bani a gaban kowa! Zamu fuskanci hukuncin Dada tare, zamu karbe shi komai tsaurin sa.
Bar maganar mutanen duniya da hayaniyar su, ba zai anfane mu da komai ba Daddy! Ita gaskiya komai ďacin ta tafi karya komai zakin ta.
Do this favour to me Daddy don Allah! Wannan shi ne rokona da bukata ta a gare ka. Don Allah kada kace a’a Daddy!

Sai kuka! Kamar mace, Kamar karamin yaro, Kamar wannan little Hausa Arab ďin da Mami take yi wa laqabi tana wakewa idan yana kuka. Takan ce

“Hausa fulanin ne ko Arab ne?”

Shikuma yayi ta bangala dariya.daga nan sai ta koma kiran shi Hausa Arab, saboda kamannin larabawan da kullum kwanan duniya suke kara bayyana a jikin sa. Idan suka je asibiti likitoci sun dinga tambaya kenan

Wannan dai baban shi ba Hausa bane sai dai Arab? Sai tayi murmushi tace
“Duka biyun! Hausa Arab ne”.

Ita take kiran shi wannan sunan kuma don rigima sai tace kar wanda ya kira shi da hakan, wai bata so sunan shi ya bata. Dada takan yi dariyar wannan drama ta Mami. Tana kuma mamakin irin wannan so da take yi wa Mahmud wanda Zahra bata samu ko quarter daga cikin sa ba duk da shekarun da ta kwashe kafin ta same ta kuma bata sake haihuwar ba bayan ta. Dalilin da ya sanya kenan Dada ta kwace ta a hannun Mamin tun tana shekara ďaya taci gaba da kula da ita.
Sai da suka yi kukan su suka koshi sannan suka goge fuskokin su, bayan sun amince da rokon da Mahmud yayi a gare su. Daga nan sai lamarin ya juya zuwa hirar wancan lokaci da irin abubuwan da suka dinga faruwa.
Mahmud yace
“So Daddy yaushe ka gaya wa Mami? Ko Uncle Yakub ne ya gaya mata?”

Daddy yayi murmushi yace
“Zainab ai aminiyata ce, bana boye mata komai, amma duk da haka bata sani ba sai lokacin da kayi wata rashin lafiya na gagara ba ka jini, abubuwan da ta hango akan fuskata suka sanya ta zargin da sai da na zauna nayi mata cikakken bayani akan ka!.
Kuma ga mafi girman mamakina, kara sonka tayi, kara kyautata maka tayi, kara shakuwar da ke tsakanin ku tayi.”

ABUJA, NIGERIA.
……………………………………………………………….
Wayewar garin alhamis na tashi ina jin wata irin kewar Mamina da tunanin halin da Ya Mahmud yake ciki. Na kai awa ďaya da tashi ban iya motsawa ba saboda tsananin sanyin jikina. Ina cikin wannan tunane tunanen waya ta soma ringing, na mika hannu kan side drawer na ďauko.
“MUBARAK”

sunan da ya futo kenan a kan screen ďin wayar. A hankali nayi sliding wayar na kara a kunnena ba tare da nayi magana ba.

“Hello sweetheart”
A hankali na amsa

“Uhmm! Ya kake?”

Cikin damuwa yace
“What is wrong with you these days(me yake damunki a kwanakin nan) zara?”

Cikin sanyi nace

“Babu komai I’m fine”

“No! Wani abun yana damunki. Ko Surayya bata daina yi miki waya bane?”

Nace

“A’a! Ba maganar Surayya bace. Kawai dai yanayin rayuwa ne, and ina missing Mami da Ya Mahmud!”

“Everything will be fine Zara!(komai zai yi daidai) ki kwantar da hankalin ki kinji? Kuma Mahmud yana samun sauki menene abun damuwa? Kamar yanzu ne zaki ga sun dawo.”

Minti talatin muka ďauka muna hira kafin muyi sallama. Na mike a sanyaye na shiga toilet nayi wanka na futo. Na daďe akan stool a gaban mudubi kafin na samu kuzarin shafa mayukan jikina. Na gyara gashi na sannan na shirya cikin ďaya daga cikin sabbin collection ďin “HUDAYYA”
Riga da skirt masu sulbi da wata blazer mai launin beige. Na nannaďe fuska ta da mayafi kalar kayan sannan na ďauko jaka da takalmi na nufi ďakin Dada wanda yanzu sam bata futowa daga cikin sa. Yini take karatun al’qurani ta kwana nafilfili, kullum bakinta cikin azumi, ranar juma’a kawai take hutawa. Don haka gidan bana jin daďin sa ko kaďan, su ya Sadik da Ya Omar sun ďauke kafa, idan kuma suka zo gaishe da Dada kawai zasu yi su juya su tafi. Everything is soo boring.

A hankali nayi sallama a kofar ďakin Dada, ragowar sallamar ta makale mun a lokacin da naji abinda take faďa
“Ki taho da dukkan yaran ranar litinin za’a yi taron! Ina bukatar kowa a cikin gidan nan.”

Ta ďan saurara sannan tace

“Ranar lahadi da asuba zasu sauka, ai Mahmud ďin yaji sauki za’ayi taron ba shi ne bayan makasudin taruwar akan shi za’a yi ta?”

Ta ďan yi jimm!
“Toh Allah ya kaimu! Ki gaishe mun da Maigidan na ki”.

A sanyaye na shiga ďakin na zauna jikina yana rawa.

Cikin wani irin sanyin jiki murya na rawa nace

“Dada zan tafi gidan Ya Omar”

Sai da ta kare mun kallo tsaf tana nazari na sannan ta ce

“Sai kin dawo”

Na tashi na ďau jakata na futa ba tare da tsayawa breakfast kaman yanda Baba Rabi ta roke ni ba. I am just not in the mood, abinda yake shirin faruwa gare mu ne yake bani tsoro da bakin ciki. Mahmud of all people Dada zata tarawa Family ta tozarta? Wanne irin hali zai shiga? Wacce irin damuwa zai faďa bayan bai ma gama wartsakewa daga ciwon sa ba? Toh so take ya mutu ya huta tunda ba jinin ta bane shi? Shin ita Dada irin ta kenan a duniya?
A sannu a hankali nake tukin har na isa gidan Ya Omar ina sumbatu ni kaďai. Bayan nayi parking sai na kifa kaina jikin steering ina numfarfashi. Mahmud mutum ne cikin family ďin mu wanda bai cancanci ko wacce kalar rashin kyautatawa ba koda kuwa babu alakar jini a tsakanin mu da shi. Shigowar sa cikin mu ta gayyato mana alkhairai mara sa lissafi don haka idan ba’a ce mi shi sam barka ba me yasa za’a aibata shi?
Ina cikin wannan tunanin waya ta ta fara ringing, kamar ba zan ďaga kaina ba na daure na tashi zaune na buďe jakata na ciro ta.+

“Big brother”

Screen din ya bayyana, wato ďan halak yaki ambato. Sai na saisaita kaina da muryata na ďaga wayar cikin kewar shi.

“Ya Mahmud I miss you(nayi kewar ka)”

Shine kalmomin da suka fara sauka a cikin kunnen shi daga kanwar ta shi. Kalmomin sun sanyaya mi shi jiki, Yaya zata ji idan ta gane wanene shi? Ya zasu ci gaba da kallon shi idan suka fahimci matsayin da suke bashi bai cancanshe shi ba? Wanne irin sauyi zai fuskanta daga gare su? Wacce irin alaka zasu musanya da shi a tsakanin su?

“Are you there(kana jina)?”

Yayi firgigit daga tunanin da ya tafi ya soma magana cikin taushi.

“Zara zamu taho Abuja ranar Saturday!”

Jikinta yayi sanyi sosai tausayin shi ya tsirga mata.

“Mami ta gaya mun! Allah ya kawo ku lafiya”

Sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan yace

“Zara akwai al’amura masu yawa tattare da dawowar mu, abinda nake bukata a gare ki Zara alfarma ďaya ce”

Cikin wani irin matsanancin tausayin sa tace

“Ka wuce kowacce irin alfarma a gareni Ya Mahmud ka faďa kawai and consider it done”

Ya sake tausasa harshe yace

“Take care of Mami!(ki kula da Mami)
Ko ina nan ko bana nan ina so ki zame wa Mami ýar da zata yi alfahari kiyi kokarin cika mata burin ta Zara don Allah ka ki yarda ranta ya dinga baci,…….”

A sukwane ta katse shi cikin tashin hankalin tunanin ko dai guduwa yake so yayi yake mata wannan nasihar
“No! Ka tsaya! Ka daina Ya Mahmud! Kaina ba shi da kwarin da zai iya ďaukar irin waďannan maganganun. Kai ne za ka kula da Mami tunda ka fini kusa da ita kuma kai ke tafi so kusa da ita fiye da komai a rayuwa.
Ya Mahmud anything can change in this world, but not the position you occupy in our hearts!( komai zai iya sauyawa a duniyar nan, amma banda matsayin da kake zaune a cikin zuciyar mu) Ina so kasani cewa no matter what, Mami bata da tamkar ka kuma ba zata taba yi ma tamka ba har duniya ta tashi. So zancen bani amanar Mami under any circumstance bai taso ba.”

Shiru yayi kamar ruwa ya cinye shi. Yana son ya sanar da wani wannan maganar ko da mutum ďaya ya gwada jin menene ra’ayin su akan shi kuma wacce irin fassara zasu yi lamarin sa da wanne irin yanayi zasu karbe shi amma yana jin tsoro kada su ragargaza masa kwarin zuciyar da ya samu kafin yazo ya fuskanci Dada. Don haka yayi kokarin ture wannan maganar ya shigo da wata.

STORY CONTINUES BELOW

“Ba abinda nake nufi kenan ba Zara amma tunda kin bar mun Mamin gabaďaya na karba nagode. I wish i deserve it.”

“You deserve all the happiness and love on this planet kaji Hausa Arab ďin Mami?”

Bai san lokacin da yayi dariya ba. Yarinyar ta ga gadon kwanan shi, tafi kowa sanin abinda yake amusing din shi da weakness ďin shi amma duk da haka tafi kowa sanin darajar shi da girmama shi. Kuma yana matukar appreciating wannan karramawa daga gare ta. A maimakon yanda wayar ta fara very emotional, sai ta rikiďe zuwa hirar zumunci zallah mai tattare da fahimtar rayuwar juna. Sai da kuďin wayar sa suka kare kaf sannan yayi mata sallama suka ajiye.

Daga nan ta samu kwarin guiwar shiga gidan Omar ganin twins. Ya Sofi sai murna take yi, mai taya ta raino tazo, don Zaran ta san ta kan yara, idan tazo ta kan samu yin abubuwa masu dama yaran basu neme ta ba don haka take jindaďin ziyarar Zara.

Sai bayan sallar la’asar Zara ta nemi hanyar gida ba’a son ranta ba. Gidansu ya koma mata kamar jeji, very strange and boring, babu komai wani irin shiru mara daďi mai sanyaya guiwar duk wata karazana da kuzarin ďan’adam.
Lokaci kalilan rayuwar su ta juya ta koma wata irin rayuwa mara armashi mara daďi mara farin ciki, lokaci guda amintacciyar alaka da soyayya na niyyar rushewa a bisa wani kuskure kadan wanda idan duk aka sallamawa kaddara lamarin ba abu me zafi ba.

A cikin kwanaki biyu duk wani mai ruwa da tsaki cikin iyalin Dada ya sauka a garin Abuja. Inna Badi’a ce ta fara isowa a yammacin juma’a da iyalanta kaf samari guda takwas, biyu masu aure da iyalansu, shida samari bi da bi. Tuni Dada ta saka an buďe ďaya sasan na gidan mai kamar girman wanda suke ciki da kuma boys quarters an share an gyara tsab an zuba kayan da baki zasu bukata. Kowanne yazo sai a bashi muhallin da zai ishe shi da iyalan sa. Cikin dare jirgin Egypt ya sauke Dr.Mansur da Ya Nuratu da tsohon cikinta da Amal, a airport suka kwana sai da asubahin asabar Ya Sadik yaje ya ďauko su.
Nuratu na ta murnar zuwa Nigeria a tunanin ta zumuncin su Dada take son ďabbaqawa shi yasa ta haďa wannan gagarumin taron family da basu taba yi ba. amma tunda ta kalli fuskar Ya Omar sau ďaya hanyar cikin ta ta murďe, fushi mara lankwasuwa a tare da shi da wata irin kamewar da bata taba ganin ta a tare da shi ba. He is a jovial person, mai tsokana da wasa da dariya. Wannan karon ko Amal bai yi wa wasa ba don haka jikinta yayi sanyi murnarta ta koma ciki.

Sun futa daga airport ďin kenan tayoyin  British airways suka sauka a filin jirgin, Ya Sadik na tsaye yana kallon saukar jigin ransa na kara jagulewa, basu san komai game da abinda yake faruwa ba amma sun san fushin da Dada ta ďauka da Daddy da Mami kuma ta tabbatar akan su zata yi wannan taron. Iyaka kurewa Dada ta kure Sadik da Omar akan abinda tayi wa mahaifin su, domin ba sa tunanin za’a samu mutum mai mukamin Daddy wanda yake kaffa kaffa da tattalin mahaifiyar sa irin shi. Tunda suka taso basu taba ganin ranar da Dada tace eh Daddy yace a’a ba. A hakan kuma bata ďaga ma kafa ta duba matsayin sa, ko ya ya kuskuro zata rufe idanu tayi mi shi tatas kamar bata san daga inda ya futo ba. Toh har yaushe? Mutum ba ya girma da irin wannan tozarcin? Ko su Daddy bai taba yi musu abinda Dada take mi shi ba su da basu kai ko idon sawun sa a biyayya ba.
Don haka suka ďauki mugun zafi wannan lokacin suka kuma kudiri a niyyar ba zasu taba zuba idanu a tozar ta musu mahaifi ba, atleast not in the presence of Kawu Sulaiman da Inna Badi’a, mutanen da suka mayar da Daddy makiyin su, abokin hamayyar su.
A duk lokacin da Mami tayi tafiya ta dawo tana sauka a airport ranta ke sanyi idan ta zuki iska ta fesar  ta tabbatar ta dawo kasar gadonta kuma mahaifarta cikin ahalin ta lafiya. Wannan karon ji tayi kamar ta shaki poison, domin wani tari ne ma ya turnuke ta daga farko sai da Mahmud yayi ta bata ruwan tana kurba a hankali sannan ya lafa. Daddy kansa a wannan hali idan aka auna jinin sa ba za’a same shi dai dai ba, kirjinsa bugu kawai yake cikin sabawa ka’ida hankalin sa na kara tashi. Shi kuwa Mahmud ya koma wata sabuwar halittar da ta sake mayar da shi bako a cikin su. A tantagaryar Hausa Arab ďin shi ya sauka wanda idan kaji kalmar hausa a bakinsa zaka iya faďuwa don mamaki. Ya koma fari tas a maimakon wankan tarwaďa inji hausawa. Gashin sa ya kifo a jere ya zagaye kansa kamar an kifa hula, yayi yala yala iskar asubahi na kaďa shi yana bajewa yana haďewa, ko gashin ka tsaya kallo morewa zaka yi.
Wannan ramar da yayi ta kara mi shi tsayi da bayyanar ainihin nationality ďin sa ba kasar Hausa bace don bahaushe irin wannan tsayin yayi mi shi tsada. Ko farcen Mahmud abun kallo ne balle fuskar shi da haiba da kamala suka lullube, gashi da kwarjini na musamman irin wanda bai bari ka zuba masa idanu kayi ta kallo gabanka bai faďi ba. A gajarce, idan ana neman wani abu da za’a kwatanta kalmar kyau da aji da kwalisa su haďe waje ďaya toh Mahmud abun misali ne cif cif, zai dace da wannan mizanin. Bakin wando ne a jikin sa da sky blue ďin shirt, ya rataya jacket ďin da ba zata saku a irin weather ďin Nigeria ba komai sanyin ta. Yana tafiya mutane na kallon shi, domin ya futa daban daga cikin al’ummar da suke kaiwa da komowa a cikin filin jirgin. Haka yake very attractive don haka yake gujewa shiga cikin mutanen da ba farar fata ba, yanzu sai a mayar da shi talabijin ayi ta kallo.

Da sassarfa Ya Sadik ya isa gare su yana yi musu sannu da sauka, suka amsa fuska kadaran kadahan domin shima damuwar da ke dankare a tare da shi ta kasa boyuwa.
Daddy ya fara saukewa a Transcorp Hilton inda zasu haďu da ambasada sannan ya wuce da Mami da Mahmud gidan Mamin kowannen su yayi shiru yana sake sake a cikin ransa.

Basu ko isa gidan Mami ba A.laila ta sauka ita ma da ýaýanta guda biyu suka wuce gidan Dada kai tsaye.

Da yammacin ranar kuma Kawu Sulaiman da iyalin shi suka sauka, sai wata irin far’a yake yi kamar wanda aka yi wa bushara. Tunda suka samu labarin hatsaniyar da ta faru a tsakanin Dada da ýan gaban goshin nata shi da Badi’atu suke murna suna fatan Allah yasa watan hambarewar gwamnatin Daddy ce tazo. Musamman da suka yi wannan kiran gaggawa daga Dada wanda bata taba irin sa kuma akan Daddy sai murnar su ta kara ninkuwa don sun tabbatar lamarin yayi muni kuma ya baci.
Shima gidan Dadan ya sauka amma bai samu ganin keyar ko ďaya daga cikin ýaýan Daddy ba sai direbobi ne suka dauko su shi da Zaliha da ýaýan shi masu auren guda huďu da sauran kowanne yana tunanin rabon sa da ganin Dadan da garin Abuja ma gabaďaya. Tunda ya koma Lagos ya kawwame kansa saboda ganin hakonsa ba zai taba cimma ruwa ba, Daddy is beyond his imagination kuma ba zai taba kamo shi ba komai saurin sa. Nasibi ce ita rayuwa, shi Allah  baiyi nufin tara mi shi dukiya ba sai dai albarkar ýaýa gasu nan kowanne tabarakallah amma babu wanda za’a ďaga duniya ta aminci sunan sa kamar yanda yake buri. Shi kuwa Daddy ýaýan guda uku ne amma kowanne ka ďaga ba baya bane ba, Ya Omar is an architect, yana aiki da Julius beger a Abuja kuma alfahari suke yi da shi saboda kwarewa da nasibin sa.
Ya Sadik shi ne mataimakin Daddy a dukkan al’amuran kasuwancinsa manager mai nagartar da na kasa da shi suke yabon kirkin sa da hakurin sa. Kullum kara futo da nasibin kamfanunnukan Daddy yake yi. Ga kuma uwa uba can likita bokan turai, Wanda yayi shaharar da wasu asibitin daga wasu kasashen ke zuwa karbar aron sa akan ayyukan da suka sha musu kai. Duk da abubuwan da suka yi tambari kawai suka sani akan Mahmud basu san ainihin wanene shi ba, a  wannan bangaren ko Daddyn bai san wanene shi ba balle wani. Tunda bankaďa halin da yake ciki ba ďabi’ar sa ce. Wannan kenan!Karfe huďu da rabi na yammacin ranar lahadi gabaďaya family ďin Dada suka hallara a cikin babban falon da Daddy yake zama da mutanen sa idan yazo gidan. Kyakykyawar bafulatanar dattijuwar ta kame akan tsakiyar 3 seater cikin shigar shuďiyar super holland ta rufe jikinta da farin wadataccen mayafi, fuskar nan a hade kirtif kamar bata san wata kalma murmushi ba. Wannan ya sanya kowa ya shiga taitayin sa, ya kama kansa ya nutsu iya nutsuwa.

Ina daga gefen kujerar Dadan A takure cikin hijab a dalilin mugun zazzabin da na wayi gari da shi wanda damuwa da tashin hankali suka saukar mun.

Falon yayi shiru tsit ana sauraran isowar waďanda aka shirya taron domin su.

A hankali muka ji nishin motocin su Daddyn, hantar jikina ta juya ta dunkule na runtse idanu cikin tsananin tashin hankali. Da yar karamar sallama Daddy ya soma shigowa falon, cikin wata irin kwalliya mai cike da kwarjini

Daga bayan shi Amsabada ne da Alhaji kurmi mai atamfa mahaifin Amina fiancee ďin Mahmud. Suka shigo suka zube a gaban Dada suka kwashi gaisuwa, ta amsa cikin nutsuwa da sanyin muryar da zaka yi mamakin ta iya.+

Sai da suka nutsu sannan Mami tayi sallama ta shigo, cikin shigar abaya ruwan kasa da mayafin ta, hannun ta cikin na Ya Mahmud, wanda mamakin yanayin da ya koma ya saka ni hangame baki saboda mamaki. Da farko tsananin farin da yayi wadda ya futar da shi daga layin bakar fata mai duhu ko mai haske, na biyu wani irin gyaran gashi da yayi wa gashin na sa, na uku kwalliyar larabawan da yayi ta bakar jallabiyya mai shaking. Balarabe sak babu sirki babu babu tambaya babu jayayya.

A nutse suka isa gaban Dada suka gaishe ta, ta amsa ba tare da ta ďago kanta ba. Jikin mu ya kara yin sanyi. Sai da kowa ya nutsu ya samu wajen zama sannan Dada tayi gyaran murya tace

“Salati goma ga Annabi”

Aka amsa da “salallahu alaihi wa sallama”

Ta ja addu’a gajeriya kafin ta ďora da bayanin ta kamar haka.

“Na san kowa yayi mamakin dalilin da ya sanya na haďa wannan taron domin ban taba yin irin shi ba, musamman kuma da nace taron akan Ahmad zanyi shi.

Wato wani babban al’amari ne ya taso wanda ya ďaga mun hankali ya bani mamaki kuma ya saka ni cikin ruďu da tunani. Ban yi tunanin cewa wani abu makamancin wannan zai gifta a cikin iyalina ba da sani ba ba, rashin sanin nawa shi ne ya ďaga mun hankali ya kuma janyo hankali na da tunani akan cewa idan har irin hakan zai faru a waďancan shekarun na baya, toh fiye da shi zai iya sake faruwa kuma faruwar irin hakan ba karamun hatsari bane ga iyali kowanne iri don haka na tara kowa da kowa baki ďaya saboda na warware wannan matsala na ďauki mataki kuma nayi kashedi mai tsauri akan ku gabaďaya domin gudun samun makamancin wannan al’amarin anan gaba.

Ahmad banyi haka domin na muzanta ka ko na kunyata ka ko na bata maka ba, nayi hakan ne saboda shi ne abinda ya dace nayi kuma shi ne daidai. Zafin da na ďauka da ku gabaďaya nayi shi ne saboda ku fahimci girman laifin da kuka yi mun ba domin Mahmud ba. Don haka ina so Ahmad ka mike tsaye a gaban kowa ka feďe musu biri har wutsiya, ka bada wannan labarin da ka zo gabana kayi mun kowa yaji.”

Falon yayi shiru kamar ruwa ya cinye mu, tsoro, fargaba da tunanin wanne irin al’amari ne wannan ya hana kowa kwakwkwaran motsi balle magana. Cikin wata irin dauriya Daddy ya mike yayi gyaran murya, yayi sallama yayi godiya ga Allah da salati ga Annabin rahama kafin ya soma bayani.

“Kafin nace komai Dada ina rokon afuwar ki da gafarar ki, a bisa wannan kuskure da na aikata, a wancan lokacin soyayya da sadaukarwa da alkawarin da nayi ne suka rufe mun idanun tuna rana irin wannan. Kuma ban taho daga inda na taho da niyyar na rufe miki ba, kalamai ne suka yi wa bakina karanci, na rasa kowanne irin kuzari da kwarin guiwar da zan bayyana miki wannan babban al’amari. Kiyi mun afuwa ki yafe mun don Allah.

Abu na biyu shi ne, ina so na tabbatar wa da dukkan wanda yake wajen nan cewa Mahmud wani bangare ne na jikina kamar ido ko baki ko hanci ko zuciya, wanda ba za’a iya raba jikin ďan’Adam da shi ba a zauna lafiya. Soyayyar Mahmud a cikin jinina Allah ya zuba ta, idan har za’a iya cire ta toh sai dai idan za’a zuke jinin jikina kaf, a sauya mun wani. Mahmud wani halitta ne da farin cikina da kwanciyar hankali suka ta’allaka a ciki. Taba shi kamar taba farin cikina ne, Kamar yanda ba za’a chanja mun suna ba, haka ba zaiyu a chanja matsayin Mahmud a cikin zuciyata ba.

Idan kun gane kun rike wannan ina ganin zan wuce kai tsaye na baku labarin kaddarata da Mahmud”

STORY CONTINUES BELOW

Bayanin Daddy ya sauya mood din da yake kan fuskar kowa zuwa mamaki, ruďani, zargi da ayoyin tambaya mara sa adadi. Zukatan kowa sun zaku su ji menene wannan ya sanya Daddy kuzanta Mahmud da bayyana irin kaunar da yake yi masa a gaban Dada a matsayin shi na babban ďan da ya haifa? Don haka kowa ya buďe kunnuwan shi da hanci da baki da ido domin karbar wannan al’amari mai girma.

Tiryan tiryan Daddy ya ďauko labarin sa, tun daga kan ranar da suka hadu da Esha……..bai boye komai ba sai batun gadon Esha wanda Ilyas ya ba shi amana tare da Mahmud a dalilin rokon da Mahmud ďin yayi mi shi akan ya sakaya wannan bangaren. Kafin ya kai aya shashshekar kuka da ke tashi tayi tsamarin gaske, Mami, Ni, Ya Nuratu, Ya Sadik, Ya Omar, Aunty Laila da ýaýanta dukan mu kuka muke yi mai tsuma zuciya.

Wani irin yanayi nake ji yana lullube ni mai kama da mafarki, almara, tatsuniya. Wani abu bai taba girgiza ni irin wannan ba, wannan labari ya shammaci tunanin mu da hasashen mu da hangen mu.

Ba yau ne ranar da naji cewa Mahmud ba ďan Daddy bane, amma wallahi ban taba zama nayi tunanin wanene ainihin Ya Mahmud ďin ba saboda tashin hankalin da tunanin hakan yake gayyato mun. Ko kusa ban taba kawowa wai irin wannan al’amarin ne mai tsauri ke biye da tarihin Ya Mahmud ba. Wani irin abu wanda ya ninka tausayi ya baibaye duk wata gaba ta jikina ya saukar mun wani irin zafin zazzabi mai daddatsa zuciya da gangar jiki.

Mintina uku da kammala bayanin Daddy Kawu Sulaiman ya mike cikin wani irin fushi ya soma magana

“Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un! Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun!! Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun!!! Amma wallahi Ahmad ka bamu kunya! Ka cutar da mu kuma kaci amanar zumunci da ahalin mu gabaďaya. Ka yi mana bakin Fentin da bai goge a zukatan mu ba.

Ka rasa irin cin amanar da zaka yi wa Dada sai ta ďauko Ďan da bata haďa jini da shi ka sako mata cikin zuri’ar ta? Ka kawo mana ajnabi cikin ahalin mu da zummar namu ne? Wallahi Ahmad ka cuce mu!( sai ya fashe da kukan tsantsar munafunci)

Inna Badi’a ta karba cikin na ta gunjin kukan kamar wadda zata hau iska

“Ahmad ka yi mana illah, wallahi ka cuce mu, ka wulakanta mana zuri’a.

Ka ďauko ďan budurwa ka kawo gida a matsayin danka? Toh waye mahaukaci da zaka zauna ka shiryawa wannan banzan labarin? Wanne mutum ne zai haifi ďan sunna ya bayar da shi ga wani mutum da basu haďa jini ko kabila ko kasa ba? Karya ne wallahi wannan yaron ba shi da nasaba sai dai idan shege ne ba shi da uba domin babu uban da zaiyi kyautar ďan sa ga bakon da zaman gari kawai ya haďa su”

Wani irin abu mai kama da saukar ruwan dalma Mahmud yaji yana ratsa duk lungu da sako na jikinsa yana illatawa. Wannan kalma ta “shege” ta kinkimo wani mugun fushin da bai taba tunanin da akwai irin shi a duniya ba ta zuba a zuciyar shi. Jikin sa ya soma wani irin kaďawa kamar gangi, yayin da idanun sa suka juye kamar wanda ya sha kayan maye, suka kaďa suka yi jazir kamar garwashin wuta. Duk wani annuri da far’a da hasken da suke kan fuskar sa suka ďauke cak wani irin fushi da fusata suka maye gurbin su.

Mami sunkuyar da kanta tayi tana jin dama yau wayar gari tayi a kabari, da wannan tozarcin da bakin cikin da suke fuskanta a wannan lokaci. Mahmud ďin ta aka tarawa wannan taron ake wa wannan cin mutuncin da keta alfarma? Kuma suna kallo babu ikon tare masa? Meye ya kai mata wannan bakin cikin zafi a duniya?.

Fili fa ya koma hannun Kawu Sulaiman da Inna Badi’a, sun buďe wuta suna huce haushi da hassadar da suke dako a cikin ransu shekara da shekaru na Daddy. Kalamai na batanci da muzanci da Allah wadai kawai suke antayowa suna furzarwa ba tare da la’akarin uwar da ta haife shi da ýaýan da ya haifa suna zaune suna kallon su ba.

Kawai dai an ji tsit maganar da Kawu Sulaiman ďin ya ďauko ta tsaya cak a sakamakon wani mugun naushi da Ya Omar ya kaiwa bakin shi, a take hakoran shi guda biyu suka faďo tare da ýar guntuwar tsokar lebensa.

Ýaýan sa suka yi kukan kura zasu yo kan Ya Omar Ya Sadik yayi maza ya ja shi suka futa waje jikin sa na rawa kamar mazari, sai wani irin huci yake futarwa kamar mayunwacin zaki.

Inna Badi’a ta ďau ihu da salati, kukan mu ya kara karfi sosai, yayin da wasu ke mikewa suna barin falon cikin wani irin yanayi ďaya bayan ďaya Dada kanta a duke bata ce uffan ba.

Sai da ya rage babu kowa sai Daddy, ambassador, Alhaji mai atamfa, Mami da Mahmud, sai ni da zazzabi ya gana katabus da Ya Nuratu da cikin ta ya dunkule waje daya ya hana ta mikewa.

Cikin tsananin karfin hali ambasada ya soma magana

“Dada Allah ya huci zuciyar ki! Allah ya huci zuciyar ki Allah ya baki hakuri Allah ya sanyaya miki zuciyar ki!

Allah ya sanya hakan kaffara ne a gare ki! Allah ya baki hakuri Dada! Mun tuba, kiyi hakuri ki yafewa Ahmad Dada!!…….”

Sai dauriyar sa ta kare ya soma kuka kamar yanda Daddy yake yi babu kakkautawa.

Kunsan kuwa yanda kukan jaruman maza irin su Daddy yake saukar da tashin hankali da masifa da bala’i ga zuciyar masu sauraron su? Wanda ya taba gani ko jini kawai zai iya kwatanta mawuyacin halin da zukata suke shiga.

Cikin wata irin kamala da nutsuwa Dada ta soma magana

“Ai nayi fushina na huce! Ni na isa na hana Allah ikon shi? Fushina zai juya bayan agogo a sauya faruwar wannan lamari ko kuwa fushina zai warware waďannan matsalolin? Idan ban hakura ba faďuwa zanyi na mutu ko kama shi zanyi da kokawa na kashe shi? Ka gaya mun idan banyi hakurin ba me zanyi? Ai idan lokacin da ya aikata abun bai yi tunanin komai ba yau gashi nan yana ji yana gani ake mi shi tozarci da cin mutuncin shi ya siya da kuďin sa, yau kuma ya tabbatar da girman laifin da ya aikata ya kuma fahimci dalilin da ya sanya na haďa wannan taron. Kowa ya San abinda yake faruwa kuma kowa ya shiga hankalin sa, Idan da akwai me irin tunanin shi ya sake tunanin ya dawo baya. Kuma ina so kasan cewa ba kanka kaďai ka cuta ba har da wannan marayan da bai san komai ba, kayi mi shi sanadin da raba shi da dangin sa ba tare da tunanin cewa watarana zai bukace su ba. Ahmad baka yi tunani ba kuma bakayi mun adalci ba, baka yi wa kanka adalci ba kamar yanda baka yi wa Mahmud adalci ba.

Ke kuma Zainab kin bani mamaki! Da ke aka boye mun wannan irin al’amari tsayin shekaru talatin da takwas? Idan shi ba shi da hankali zaman turai ya hargitsa masa lissafin kwakwalwar sa ke kuma fa? Idan da kun mutu kafin wannan lokacin wacce irin badakala zaku bari? Waye zai warware wannan lamarin??

Ta inda ta Dada ta shiga ta nan take futa ba, tayi hausar tayi fillancin ta fashe da kuka kamar wadda zata tayar da iska. Daddy da ambasada ba gurfane a gabanta suna bata hakuri cikin hawaye masu zafi da raďaďi. Dakyar da cibin goshi tayi shiru ta hakura sannan ta bukaci kowa yaje yayi sallah kafin a dawo zama na biyu.Da yawa cikin mu bamu san raka’a nawa muka yi sallar wannan magrib ďin ba balle surorin da muka karanta. Har muka je muka kammala abubuwan da zamu yi muka dawo bakinmu bai buďe munyi magana da juna ba. Ashe wani tashin hankalin yafi gaban magana? Ashe wata matsalar tafi gaban tattaunawa? Ashe wani kukan yafi gaban tsayawa? Ban taba sani ba sai a wannan rana.

Karfe bakwai da ashirin da biyu muka sake hallara a wannan falon, Ya Omar ne kawai babu domin haukacewa yayi sai da Ya Sadik ya saka shi a ďaki ya kulle ýaýan Kawu sulaiman suka yi asibiti da babansu. Bakin na shi ya haye yayi sintim gwanin ban dariya sai zare idanu yake yi, amma saboda tsabar hassada da mugun bakin rai bai zauna a ďaki ya huta ba sai da ya dawo ganin hukuncin da Dada zata yanke akan makiyansa.

Cikin nutsuwa Dada tayi gyaran murya ta fara bayani kamar haka.

“Hakika nayi bakin cikin abinda ya faru kuma naji ciwo da bacin ran abinda Ahmad ya aikata sai dai idan aka yi la’akari da cewa ita kaddarar mutum bata kauce masa kuma bata wuce faďawa akan kowa ba sai na hakura na fawwalawa Allah!

Abu na farko da nake son jan hankalin ku gabaďaya akai shi ne, duk abinda za ka aikata ka hango gaba kayi tunanin abinda wannan abun zai iya haifarwa ko zai juye ya koma. Sannan kaji tsoron Allah ka kuma kiyaye amana musamman amanar iyaye da ta ýaýansu. Ina faďakar da ku cewa wannan laifi ba karamun laifi bane me muni, Ahmad ba sai kace mun kai ne ka haifi Mahmud zan bari ka rike shi ba, ni wacece da zan ja da yin Allah? Ba ďauko Mahmud ne laifin ka ba, karyar cewa kaine ka haife shi ita ce laifi domin ko babu komai zaka tara naka ýaýan da dukiya, waye zai warware wannan badakalar idan ka mutu baka sanar da kowa ba? Shi kuma ďan wacce irin cutarwa kake tunanin kayi masa? Kana tunanin wannan sirrin zai ta rufuwa ne har abada? Ba zaiyu ba Ahmad! Komai daren daďewa sai wani sanadi ya tono wannan sirrin ko kana raye ko bayan mutuwar ka. Zaka iya yi wa ďa kowanne irin so da gata da kauna amma ba zaka iya mayar da shi ďanka ba saboda ita wannan alakar Allah ne kaďai yake haďa ta ba mutum mahaluki ba. Ďan ka ba zai taba zama ďan wani ba kamar yanda ďan wani ba zai taba zama naka ba komai soyayyar da take tsakanin ku. Ina fatan wannan al’amari zai zama darasi da izina a gare mu gabaďaya.+

Abu na biyu shi ne ina so na sake jaddada maka cewa Mahmud ba shi da gadon ka, manufar ka ďaukar wani kaso cikin dukiyar ka ka bashi ba laifi bane amma ba kashi 60 a cikin ďari ba. Idan kayi haka, kayi zalunci kuma zaka raba kan ýaýan ka

Abu na uku shi ne idan har kana son futar da Mahmud daga cikin zargin mutane ka samo mi shi daraja da mutunci da kamala toh dole kaje ka nemo ka kawo hujjoji kwarara waďanda suke tabbatar da ďaurin auren Ilyas da mahaifiyar shi, da shaidun ido da na takarda. Idan kuma da hali ka san hanyar da zaka bi ka nemo mi shi dangin mahaifin shi saboda su ďin ne kawai gata da mutuncin shi a idanun duniya.

Abu na uku shi ne daga wannan lokacin ni Faďimatu na haramtawa dukkan zuri’a ta ďaukar wani ďa a matsayin riko ko aro daga kowanne mahaluki kuma na haramta muku bayar da naku ýaýan ga kowanne irin mutum komai kusancin ku da shi. Ban yafe wa duk wanda ya karya mun wannan dokar ba.

Abu na karshe ina so kuyi wa ďan’uwanku uzuri da alfarma ku yafe mi shi ku tattara wannan al’amari ku ďora a mizanin kaddarar Ahmad wadda ba zai iya gocewa ba….”

Ta ďauki lokaci mai tsayi tana yi musu nasiha mai ratsa jiki kafin ta ja doguwar addu’a sannan ta sallami kowa. Mami da Ya Mahmud ne suka fara barin falon kamar yanda shigo tare. Sannan Daddy da aminan sa suka bi bayan su suka shiga motocin su zuwa masaukin su.

Ni dai ina gefen da na takure a zaune idona sunyi wani irin nauyi saboda kukan da na sha wanda rabon da nayi irin shi tun rasuwar Aisha. Kaina sarawa kawai yake yi kamar ana buga mun dutse mai tsananin nauyi. Zazzabi na ratsa dukkan wasu gabobin jikina.

Dakyar na iya maida jikina kan kafet ďin falon na kwanta ina karkarwa wadda ta janyo hankalin Dada.

Cikin tausayi ta dinga yi mun sannu sannan ta saka Ya Nuratu kiran Ya Sadik su kaini asibiti.

STORY CONTINUES BELOW

A ranar dai a karkashin kulawar likitoci na kwana, sai da aka tsira mun alluran bacci masu karfi kafin kwakwalwata ta samu sukunin rintsawa. Ya Nuratu tana gefe na taci kuka ta koshi, Mahmud aminin ta ne wanda take sharing dukkan damuwar ta da shi kamar ýaruwa mace domin sau da yawa ta kan ce “He is the sister she never had)”. Ba zata iyakance taimakon da yayi wa rayuwar auren ta ba, ba zata irga lokutan da yasha tashi daga London zuwa garin Riyad akan ta ba. Hidimar shi a gare ta tafi karfin baki ya lissafa, don haka take ganin girman shi kamar babanta, take son shi kamar ďan’uwan da suka futo ciki ďaya, wannan labarin da aka bayar na shi bai saka ko dai dai da kwayar zarra wani burbushi na girma ko matsayin sa ya ragu a idanun ta ba, sai ma wani tausayi da kauna ta tsakani da Allah da take ji akan shi. Mahmud mutum ne nagari wanda hasken zuciyar sa da halayen sa zasu iya rufe kowanne irin bakin tarihi ne da shi komai duhun sa komai munin sa.

Lokacin da Mami suka futo daga babban falo, sasan Dada tayi da niyyar jiran Dadan ta dawo ta sake jaddada neman afuwar ta su sasanta kafin ta tafi. Amma irin mugayen kalaman da Inna Badi’a ta dinga jifanta da su ya sanya ta kasa hakura ta shiga ďakin Zara ta dinga kuka mai tsuma zuciya sannan ta wanke fuskar ta ta futo don tafiya gidanta tunda har wannan lokacin Dadan bata shigo gida ba a dalilin zazzabin da ya rufe Zara. Ashe kafin Inna Badi’ar ta shigo wajen ta daga wajen Mahmud take.

Yana tsaye a gaban motar Mami ýaýan Kawu Sulaiman suka zo wuce wa suka kalle shi suka kwashe da dariya suna nuna shi kafin su wuce cikin gida. Sunkuyar da kansa kasa yayi yana kiran sunan Allah a hankali domin ya kawo mi shi salama kada ciwon shi ya tashi! Yayi alkawari he will be strong for Daddy and Mami, ba zai bari a ci lagonsu ba.

Yana tsayen dai Inna Badi’a ta taho tare da ýaýan ta suna tattauna abinda ya faru suna jefawa Daddy da Mami duk wata mummunan kalmar da tazo bakin su. Sai kawai suka hangi Mahmud ďin a tsaye!

Cikin kasaita Inna Badi’a ta iso gabansa tana tsaya tana yi mi shi kallon wulkanci

“Sannu sannun ka ďan gwal ďan gatan Alhaji da Hajiya na gaban goshin Dada. Ashe kuma sai reshe ya juye da mujiya? Ai daman duk inda kaga mutum yana ďaga kai yana kasaita yana hura hanci toh a bincika asalin sa, wannan Kaine kyal kyal banzan, a fili kyau kamar kai kayi kanka amma mummunar nasaba ta dagula komai. Sannu fa! Ga ka bature ga ka balarabe ga ka bahaushe idan aka bi ta kalen dangi. Allah dai yayi mana tsari da jinin yahudu da nasaa dom………..”

Jajawur din idanun shi da ya ďago ya zuba mata wanda suka sanya mata jin wani mugun shock ďin da ya haddasa mata wata irin faďuwar gaba. Ashe daman da take yi mi shi ratsin mutunci son ranta ba kallon ta yake ba. Allah yayi mi shi wata baiwa ta kwarjini da kamala irin wadda take ceto shi daga kowanne irin wulakanci da tozarci a wajen kowannen irin mutum. Duk girman ka ko mulkin ka ko isar ka ba zaka iya kallon cikin idanun shi kayi mi shi cin mutunci ba sai dai idan ya sunkuyar da kai.

Toh Irin shi ne yau ma ya kashe masa bakin Inna Badi’a wadda ba don kar ace tayi qarya ba da sai tace har balbalin wuta ta hango a cikin kwayar idanun na shi tana ci bal bal bal. Ai basu kara minti ďaya ba suka bar wajen kamar munafukai.

Shine daga nan ta shiga sasan Dadan ta samu Mami ta ďora daga inda ta tsaya. Dalilin da ya sanya Mami da Ya Mahmud barin gidan kenan ba tare da ganin Dadan ba.

Daddy da aminan sa hotel suka wuce kai tsaye, amsabasada ne ya zauna yana ba shi hakuri yana yi masa nasiha tare da kwantar da masa hankali. Da kuma jaddada masa cewar Yana tare da shi kuma zai ba shi kwarin guiwa, zai taimake shi su fuskanci wannan kalubalen tare.

Anya akwai aminai irin su ambasada? Duk da cewa Daddy bai taba buďe mi shi wannan sirrin ba sai yau ďin nan ya sani amma sam baiyi judging Daddy ba, bai yi criticizing ďin shi ba, sai yayi la’akari da cewa duk abinda ya faru ya riga ya faru ya kuma kalli halin da Daddyn yake ciki ya mayar da hankali wajen taimakon shi ya warware wannan matsalar ya kwantar masa da hankali. A tunanin shi “That’s what true friendship is”

Shikuwa Alhaji Kurmi har lokacin bai buďe baki yace ta tafas sauke ba. He is neutral, ba zaka gane cewa fushi yake da Daddy ko bayan shi yake bi ba.

Ya dai yi shiru yayi zurfi cikin tunani, su ma basu damu da jin ta bakinsa ba.

Washegari suna tashi da safe yace Kano zai wuce ba tare da yace komai ba game da abinda ya faru ba, Daddy yayi mi shi godiya ya saka a kai shi Airport ya tafi cikin matukar mamakin sa domin ba haka yake ba.

A wannan daren Mahmud ba zai iya kwatanta irin kwanan da yayi ba.

Lokacin da Daddy ya ba shi labarin nan a London ya ji babu daďi kuma zuciyar sa ta karye, amma abinda ya faru yau ya ďaga masa hankali fiye da yanda yake tunani! Bai taba jin cewa zai iya jin matsananciyar bukatar iyayen shi ba a duniya sai yau! Bai taba tunanin cewa akwai ranar da Daddy da Mami ba zasu ishe shi madogara ba sai yau.

A wannan rana ba shi da burin da ya wuce ya buďe idanu ya ga iyayen shi a tare da shi ko wanne iri ne su, ko daga ina suke, saboda su ne kaďai zasu rufe masa asirin da ake tone masa, su ne kaďai zasu kankaro mi shi darajar shi a idanun duniya, su ne kaďai zasu ba shi farin cikin da yake bukata a yau.

Wayar shi tayi kara yayi sauri ya duba, amma a maimakon text ďin Amina da yake tsammani sai yaci karo da text ďin MTN, ya zuki iska ya fesar yana tunanin lallai zuwa yanzu ya san Amina ta ji komai, so yake yaji yanda ta ďauki maganar, so yake tayi mi shi magana masu sanyi irin wadda ta saba yi mi shi idan ta gane yana cikin damuwa.

Da farkon lokacin da suka haďu da ita ya san cewa babu soyayyar ta a zuciyar sa. Amma a yanzu zai iya bugun kirji yace ta mamaye fegi mai yawa a cikin rayuwar sa, ya tabbatar yana sonta, so mai tsanani a dalilin kyawawan halayen ta da mu’amalar da tarbiyyar ta. Sau da yawa ta kan tuna mi shi Jawahir, yanayin sanyin halin su da rashin kwaramniya da biyayya kamar uwa ďaya ce ta haife su. Wannan ya kara sakawa Amina ta kwanta ma sa a zuciya, haka nan ya karaci jiran text ko wayar ta har yammacin litinin, idan ya kira wayarta ta kuma a kashe.

Yayi matukar dauriyar danne halin da zuciyar sa take ciki saboda ya baiwa iyayen shi kwarin guiwa da salama a zuciya, amma da za’a tona yanda yake ji, ya tabbatar babu mahalukin da ba zai tausaya mi shi ba. A ranar yini suka yi da Faisal a ďakin shi yana rarrashin shi, idan kuka ga yanda Faisal yayi zuru zuru ya rame sai kuyi tunanin shi ne Mahmud ďin, ji yake yi kamar ya ciro zuciyar Mahmud ya goge ta ya cire duk wani bacin rai da bakin cikin da yake cikin ta. A cikin haka Sadik da Omar suka iso gidan Mami, da farko tausayin shi ne ya hana su zuwa, sai daga baya Sadik yayi tunanin kuma kar Mahmud ďin ya ďauka suna cikin layin waďanda ba sa tare da shi. Ya rarraso Omar daga komawa wajen Kawu Sulaiman don cewa yayi sai yaje yayi mi shi kashedin babu ruwansa da abinda ya shafi rayuwar Daddy da tasu, shi ma yaje yaji da kansa.

Suna zaune kan dinning ďin Mami suna tura abincin da aka jera kamar masu cin maďaci su Ya Omar suka yi sallama suka shigo. A sanyaye Mahmud ya ajiye cokalin abincin sa yana kallon su, kirjina na bugawa cikin tsananin sauri. Babu abinda yake tunani sai irin gori da cin mutuncin da zasu zo suyi masa su ma, tunda duk yanda wani zai ji zafin abinda ya faru ai bai kai su kusanci da Daddy ba.+

Hannu suka fara mika masa kamar yanda suka saba ya mika musu na shi hannun a tsorace suka yi musabaha sannan Sadik yayi mi shi murmushi mai kwantar da hankali yana daga tsaye ya soma koro bayanan da yazo mi shi da su.

“Muna fatan abinda ya faru yau ba zai shafi alakar mu da kai ba Yaya Mahmud!
Muna fatan abinda ya faru ba zai saka ka chanja mana matsayin da muke da shi ba a wajen ka, a wajen mu matsayin ka da girmanka da wannan alakar jini ta ýan’uwan da suka futo daga iyaye ďaya tana nan cikin zuciyar mu kuma babu wani dalili da zai iya chanja ta. Muna rokon alfarmar ka don Allah kaima kada ka chanja mana mazauni a ranka.
Billahil azeem jin labarin ka bai rage darajar da kake da shi a idanun mu ba illah ma karawa da yayi! Kai mutum ne maganarci salihin da babu mahalukin da ba zaiyi farin cikin haďa dangantaka da kai ba, Idan har da akwai abinda zai sanya mu bakin ciki a tsakanin jiya da yau, toh rasaka ne da muka yi a matsayin da muke ďaukar ka iya rayuwar mu. You are an the best brother anyone could ever pray for! Ka saka a ranka cewa muna tare da kai ko da duk duniyar nan zasu juya maka baya, ka amince kaunar da take tsakanin mu babu abinda zai tsinka ta komai karfin shi. Kasa a ranka kai namu ne mu naka ne har abada………”

Bai karasa Mahmud ya mike a faďa jikin sa suka rungume juna tare da sakin wani irin kukan ban tausayi. Sai da ta jikawa Sadik kafaďar rigar shi da ruwan hawaye. Toh daman ya lafiyar kura balle tayi hauka? Abubuwa kanana ke karya zuciyar Mahmud yayi kuka, a yi ta mamaki ashe hakan bai rasa nasabar shi da jinin larabawa ba.
Wani irin union ake a wajen kamar a cikin emotional Indian movies ďin nan, Mami na zaune tana na ta hawayen tana hamdala a cikin zuciyar ta. Daman ta san cewa Allah ba zai tozar ta su ba, ta san cewa Mahmud ba zai rasa masoya ba kuma ba zai rasa masu share masa hawaye ba.

Ya Nuratu da ta rasa hanyar da zata haďu da Mahmud saboda tausayin shi da take ji ba zai bari ko waya ta kira shi taji muryar shi ba, a maimakon haka, sai ta ďauki wayarta ta dinga rubutu sai da ta yi paragraphs guda goma sau shida sannan ta tura masa. Lokacin ya zo kwanciya bacci kenan ya tsinkayi sakon a email din shi, sai ya zauna ya fara karantawa, tun yana hawaye, har ta koma murmushi a karshe sai da ta saka shi dariya. Ya mayar da laptop ďin ta rufe yana jin wani irin girma na wannan family a cikin zuciyar sa. Ya laluba wayar sa ya kira Daddy, ringing biyu ya ďauka cikin ďari ďari da abinda zai futo daga wajen Mahmud ďin.

“Daddy are you ok? Don Allah kada kayi stressing kanka da damuwa? Ka dinga cin abinci kana hutawa! Do this favour for me Daddy!”

Nannauyar ajiyar zuciya Daddy ya sauke yana jin wata soyayyar Mahmud ďin sabuwa fil tana sauka cikin jikinsa. Yayi imanin babu wani abu da zai so kwatankwacin Mahmud a rayuwar sa kuma ya tabbatar cewa farin cikin sa a rataye yake a jikin na Mahmud. A duk lokacin da Mahmud yake walwala Daddy ya fi shi farin ciki, a duk lokacin da ya shiga damuwa Daddy ya fi shi bakin ciki. wannan soyayyar daga rabbul izzati ce ba haďawar mutum ba.

STORY CONTINUES BELOW

Daddyn da ke nannaďe cikin duvet yana malelekuwar tunani sai ganin shi kawai ambasada yayi yana bin kwanukan abincin da aka kawo yana zubawa suna hira da Mahmud da yaren Turkiya suna annashuwa. Bai yi aune ba Daddyn ya tashi da malmalar pounded yam guda biyu ya kora da lemon five alive. Kabbara kawai ambasada ya dinga yi a ransa yana tsarkake ubangijin da yake halittar zukata ya kulla soyayya tsakanin su. Toh tunda wanda yake jiyya ya wartsake shi ma me yake jira?
Sai ya taso ya saka na shi abincin shi ma yaci ya koshi yana sakawa Mahmud albarkar ladan cikin dattijan da ya samu.

Wanne tudu wanne gangare safiyar talata sai wayar gari aka yi da hotunan Daddy da na Mahmud cikin jaridu da mujallu da manyan shafukan yanar gizo gizo an buga take labarin da manyan baki
“The truth has been revealed! Mahmud is not the biological son of the famous business tycoon Alhaji Ahmad Lamiďo”

Daga nan sai su rattabo Labarin dalla dalla har da karin maggi da gishiri irin na ýan jarida. A wannan rana Daddy, Mahmud da Mami sai kashe wayoyin su suka yi saboda kiraye kirayen ýan’uwa da abokan arziki da duk wanda yake da alaka da su domin jin menene gaskiyar lamari. A gidan Dada kuwa sai ranar su Inna Badi’a suka yi shirin komawa gida, a wannan karon duk dauriyar da Nuratu take tayi wa Inna biyayya sai da ta gaza, tunda suka dawo daga asibiti da Zara basu sake futowa daga ďakin ba sai da suka tabbatar duk bakin gidan sun tafi.

Zara da Nuratu na matukar matukar so su je wajen Mami da Ya Mahmud amma gudun zuciyar Dada ya hana su nuna hakan akan fuskokin su. Sai dai kowannen su kalla za ka gane ďumbin damuwa da sanyin jikin da suke ciki.
Gidan yayi shiru babu armashi ko kaďan, ko ýar Amal ďin da za ta dame su da surutu babanta ya tafi da ita Kano gidan iyayen sa. Sai Baba Rabi da ke shige da fuce tsakanin kitchen da falukan gidan, yanda kuma take abincin haka take dawowa ta kwashe kayanta babu wanda yake tabawa.
Ita ma abun duniya sun taru sun cuďe mata, Mahmud na wajen ta ne, koda yake shi mutumin kowa ne saboda kyautatawar sa da sakin fuska ga na kasa da shi musamman waďanda suka girme masa. Suna zama da Baba Rabi sosai suyi hira suyi wasa da dariya kamar ďan ta, a cikin hirarrakin na su ba’a fi watanni huďu ba suke hirar London yake bata labarin sanyin da ake yi, duk sha’awa ta kama ta saboda ita mutum ce mai son yanayin sanyi, ai kuwa ya buďe wayar shi ya soma nuna hotunan snow, lokutan tsakiyar January ďin nan da idan sanyin yayi dusar kankara take zubowa, idan mutum ya buďe zai yi magana hayaki ya turnuke. Wannan abu ya baiwa Baba Rabi sha’awa har Dada tana yi mata dariya. Wai ashe Mahmud bai bar maganar iya nan ba, a cikin satin ya sanya Omar ya kaita gidan passport bayan ya futo ya saka aka shigar mata da visar London. Ko da a haka suka tsaya kawai ba ta kai ga zuwa London ďin ba Mahmud ya gama da zuciyar ta.
Yanzu ga passport ďin ga visar amma rashin kwanciyar hankali ta saka an mata da ita, a ranta ta kance
“Watakila iya rabona kenan! Fasfo da bisar. Amma tunda naje na sauke farali na kewaya ďakin Allah na ziyarci Manzon sa ai na gama yawon duniya”
……………………………………………………………….

Washegari Alhaji Aliyu Kurfi(mahaifin Mami) ya iso Abuja tare da A.laila wadda ta tafi Kurfi bayan an kammala meeting ďin Dada tayi masa bayani a tsanake saboda ya fahimci Mami.
Uncle Aliyu yayi aure har sau uku bayan mutuwar Zainab mahafiyar Mami amma Allah bai sake ba shi haihuwa ba.
Da farko ya ďauki mugun zafi amma yanayin da ya samu Dada da bayanin da ta tayi mi shi sai Allah ya taimaka ya sauka daga dokin fushin. Yayi ta ba ta hakura har sai da ta nuna bacin ran ta kafin daga bisani suka tafi gidan Mamin shi da A.laila.

Lokacin da Mami ta ganshi hankalinta ya tashi domin shi mutum ne mara wasa, kuma rashin zama tare da shi ya sanya basu shaku ba kwata kwata tana bala’in tsoron shi. Sai dai a maimakon yayi mata faďa, sai ya haďu su gabaďaya ya dinga yi musu nasiha mai ratsa jiki wadda ta sanya su nutsuwa da kwanciyar hankali. Babu yanda bata yi da shi ya kwana a gidan ba yaki, yace ai tuni Daddy ya saka an mi shi booking cikin hotel ďin da suke shi da ambasada domin sai bayan sati ďaya zasu tafi. Dakyar yayi kwanaki biyu yace zai juya, anan kam rufe idanuna nayi na daure naje na roko Dada cewa zan bi shi Katsina zamu dawo da A.laila.
Ba tare da musu ba ta amince, duk da cewa zuwa na Kurfi sau biyu ne tak, kuma ba wani daďin garin naji ba a wannan lokacin gani nake yi shi ne wajen da zai fi ko’ina yi mun daďi a wannan yanayin da zuciyata take ciki.
Ita kanta Dadan na fuskanci ta fahimci dalilin son tafiya ta shiyasa ta barni.
Haka na haďa kayana a trolley na bi su ba’a son ran ya Nuratu ba kuma ba tare da na ga Mamina da Mahmud ba don yanda naso hakan.

Da yammaci muka sauka a garin katsina ta jirgi, personal driver ďin Baban Mami yazo ya ďauke mu zuwa gidan shi.
Har wannan lokacin ba’a shawo kan Baban Mami ya futo daga cikin kauyen Kurfi zuwa cikin gari ba. Sai dai gidan da yake ciki a garin idan ka shiga ba zaka so futowa ba.

Wani shuďin gini aka yi mi shi hawa biyu tantagaryar ginin gargajiya mai tsari da ban sha’awa. Ga wani kayataccen lambu da yake zama yayi karance karancen shi wanda yafi mun ko’ina daďi a gidan. Matar Baba Asma’u mai kirki ce kuma mai son Jama’a, cikin awanni kaďan muka saba sosai ta cika gaban mu da kayan motsa baki da Lallausan tuwon masara da miyar ďanyar kubewa taji kaji zuku zuku.
Duk damuwar da nake ciki sai da na zauna na cika cikina taf da wannan kayan arziki sannan na koma ďakin da ke kusa da na Inna Asma’u na shiga toilet nayi wanka saboda tsananin zafin da ake yi, duk da cewa an ware Ac an kunna generator ko’ina ya ďau sanyi. Ina futowa nayi shafa nayi sallar magrib ban tashi daga wajen ba sai na ďora sallar Isha’I sannan na shirya cikin kayan bacci na na kwanta idona har yaji yake yi, da niyyar idan na farka zuwa karfe tara zan kira Dada da su Mami. Ai ban tashi buďe idona ba sai karfe huďun asuba.
Mamaki ya kamani, koda yake naci bashin baccin ne ba ďan kaďan ba, sai naji kaina ya rage nauyi sosai jikina kuma ya warware.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page