HAUSA ARAB CHAPTER 6

 HAUSA ARAB CHAPTER 6

Halin da su Mami suka samu Mahmud a ciki ya daga hankalin su matuka. Domin idan ka ganshi ba zaka taba tunanin zaka futa ka dawo yana numfashi ba. Su kansu likitocin sai da suka tambayi wani irin mummunan labari aka sanar masa? Wanne irin bacin rai ya shiga Wanda ya girgiza shi haka? Rashin sanin amsar ya sake firgita su Daddy musamman idan suka tuna mummunan labarin da yake jiran sa idan ya farfado wanda babu tantama zai iya kashe shi ko ya mayar da shi irin halin da yake ciki a yanzu.

Har wannan lokacin Dada bata daukar wayar Daddy don haka komai ya sake jagule masa. Komai nashi ya tsaya cak! Don a yanzu duka farin cikinsa da walwalarsa da nutsuwarsa sun ta’allaka ne ga samun lafiyar Mahmud da warware matsalar da suke ciki. Bai ki ya rasa duk abinda ya mallaka akan samun lafiyar Mahmud ba. Wani irin so yake wa Mahmud irin wanda baya yiwa Sadik da Omar, wani irin so me tsanani da karfin da ba zai iya kwatantuwa ba. A tsakiyar ransa duk abinda ya shafi Mahmud yake,duk motsin sa yana nan cikin ransa kamar Wanda aka dasa don haka shi bai ga wani abu a duniya da zai raba shi da Mahmud ba komai girmansa. Bai ga mahalukin da zai iya shiga tsakaninsu ba don haka ne ya daura damarar fuskantar kowanne irin kalubale daga Dada da ma duk wanda zai shigo cikin wannan magana a shirye yake da shi.+

Ta bangaren Mami babu abinda take yi sai addu’a da karatun al’kurani tun zuwansu. Tayi saranda ta tattara duka lamuranta ta mikawa ubangijin sammai da kassai! Kuma tayi imani da cewa Yana sane da su da halin da suke ciki sannan ta shirya karbar kowacce irin kaddara ce zata sake kutsowa cikin rayuwarta. Domin ita kam ta sare da yanayin da Mahmud yake ciki, tasan wani mawuyacin abu ne ya tashi domin tunda ciwon ya kama shi bai taba tsamari irin haka ba. Idan kuma wata zuciyar tace mata zaiji sauki hankalinta ya dan kwanta sai ta tuna bakin labarin da yake jiransa wanda ta tabbatar ba jinsa zai sake hargitsa lissafin zuciyarsa koma ya tashe ta daga aiki gabadaya. Wannan tunani ba karamun raunana ranta yake yi ba, tayi ta zubar da hawaye cikin sujjada tana neman alfarma wajen Allah tare da tawassali da Annabin sa akan ya bar mata Mahmud kada ya dau ransa a wannnan halin da rayuwarsa tafi komai muhimmanci a gare su.

Kwanaki uku muka dauka cikin wani irin hali na tashin hankali da fargaba. Tun su Mami na daukar waya ta har suka gaji suka daina saboda basu da abin cewa. Babu wani cigaba a jikin Ya Mahmud, likitocin sun tabbatar musu da cewa zuciyarsa tayi matukar weak. Matsalar da yake fuskanta a yanzu itace cardiogenic pulmonary edema, wanda matsalar ciwon zuciya ta haifar masa. Dalilin da ya sanya shi tari mai tsanani da jini kenan da kuma saurin daukewar numfashi. Gazawar jijiyoyin da suke kai jini zuwa zuciya yake sanyawa jinin ya dinga komawa cikin hunhun Dan Adam.

A yanzu dai abubuwan da ake so su kammala sune blood tests, echocadiogram, electrocardiogram da cardiac catheterization. Idan duk wadannan sun kammala ne za’a Dora shi kan cikakken medication din da yake bukata.

Prognosis din lalurar da take damun Mahmud ba mai dadi bane, domin cuta ce da take mugun kisa, duk da tsamarin ta bai kai yanda za’a futar da rai da samunsa ba amma likitan Mahmud ya yi wa Daddy cikakken bayani akan cutar da abinda yake haifar da ita, da kuma hanyar da za’abi a kubuta. Ya kuma yi masa alkawarin sai yanda karfin sa ya kare akan Mahmud. Gudunmawa daya suke bukata daga Daddy shine, su nisantar da zuciyar Mahmud daga damuwa da bacin rai, su hana shi lokacin tunani da lissafi mai yawa sannan a inganta abincin cinsa zuwa wanda lalurar sa take bukata. Ya rage stress din da yake dorawa kansa. Da wannan Insha Allahu za’a samu gagarumar nasarar cin galaba akan ciwon sa.

Daddy ji yake bai ki ya dau Mahmud su koma wata nahiyar daban suyi zamansu su biyu cikin kwanciyar hankali da farin ciki ba.

Duk wani babban Shehin malami da waliyyi da ya sani ya buga waya ya nemi alfarmar addu’a a wajen sa. Sannan a kwanaki ukun nan mutum Goma sha biyu mabukatan zuwa kasa mai tsarki wanda basu da halin zuwa ya diba ya biyawa Umra musamman suyi wa Mahmud addu’a. Addu’a daya ya gaza samu daga bakin da yafi kowanne tasiri a rayuwar shi wato bakin Dada. Hakan yake sanyaya jikinsa yake ganin kamar ba za’ai nasara ba domin shi bai ga wani abu a rayuwa wanda ya taba fuskanta bai same shi ta hanyar sa albarka da addu’ar Dada ba komai girmansa. Duk abinda ya zama a rayuwa albarka da jumurin addu’o’inta ne sanadi. Bai taba tunanin akwai wata rana da zata zo wadda zai bata ranta har ta daina magana da shi ba. Duka yan’uwan sa guda biyun Sulaiman da Badi’a zazzafan kishinsa ne a zukatan su da wata tsangwama ta babu gaira babu dalili, mahaifin Zara ne kadai babban amininsa kuma masoyinsa na haika balle yace zai kama kafa dasu a wajen Dada ta sakko daga fushinta.

STORY CONTINUES BELOW

…..NIGERIA………..

……………………………………………………………….

Gabadaya duniyar tayi mun zafi a dalilin rashin kwanciyar hankalin da family na ke ciki. Jikin Ya Mahmud yafi komai daga hankali da raunana zuciya domin tunanin zamu iya rasa shi kadai idan nayi nake jin zazzabi ya rufe ni kirjina ya dinga bugu kamar zai balle. Hakika Ya Mahmud wani mutum ne mai matukar amfani da daraja da girma a cikin rayuwarmu. Nayi tunanin hanyar da zanbi na tafi London na rasa, bansan wanne kalamai zanyi amfani da su wajen tambayar Dada izinin zuwa ba balle kuma wanda zamu tafi tare da shi. Ya Omar tuni yabi jirgi ya tafi, koda yake na fuskanci shima fushin ya dauka da Dada mai tsanani domin tun randa ya debo mu daga airport ya sauke mu a gida bai sake waiwayowa ba. Bayan kullum ta duniya suke zuwa gaida Dada watarana ma sau biyu idan bukatar hakan ta kama. Ta fannin Dada kuwa daga dakin nan nata bata futowa, tana kan sallaya tana karatun al’kurani ko Jan jarbi. Nakan rasa wanne abu ne wannan ta sanya a gabanta mai tsauri haka? Gajiya nayi da zaman tunani na shiga toilet na wata ruwa tare da dauro alawalar la’asar. Bayan na shafa mai na shirya cikin fitted gown din swiss lace charcoal colour mai raisin lilac da pink. Na yafa gyalen da ya dace da flat din takalmi. Sannan na fashe jikina da daya daga cikin turarukan Swiss Arabian. Na dau mukullin mota na futo ina tunanin abinda zan gayawa Dada.

Da sallama na tura kofar dakin tare da tsayawa na samu izinin shiga. Sai da tayi gyaran murya sannan na bude kofar sosai na shiga na zauna gabanta cikin ladabi. “Barka da yamma Dada” daga mun kai kawai tayi, wannan ya sanya na sake nutsuwa. Cikin sanyin murya nace “Dada zanje gidan Ya Sadik” a hankali ta dago ta kalleni kallon tsaf mai cike da ma’anoni da dama sannan ta sunkuyar da kanta ga takardar addu’ar da take karantawa. Sai da ta kammala karatun tsab tayi dogowar addu’a bayan ta shafa kuma ta tafi sujjadar da ta dau mintina goma a cikinta kafin ta dago. Ni dai nayi tsuru-tsuru gabana na luguden daka.

A nutse ta soma magana cikin sautin nan nata mai kwarjini da dukan zuciya. Ta mako mun tambaya.

“Menene cikin abubuwan biki Wanda suka rage miki ba’a siya ba?”

Mamaki ne ya kamani, acikin halin da muke ciki me ya kawo zancen biki da hidimomun shi? Duk da bikin saura watanni biyu amma ai lalura ta danne komai. A bari mana aga farfadowar shi kafin a cigaba da koma menene. Kodayake ciwon nashi ba damuwarta bane yanzu tunda ya futa daga sahun wadanda ta damu da su.

Ganin yanayin da na shiga ya sanya ta sake mun magana cikin karkashi. “Ina sauraren ki” a sanyaye nace “Dada wallahi bansani ba duka list din yana wajen Mami.” Cewa tayi “ba kayan daki nake nufi ba, ke abubuwan da kike bukata na futar biki kamar kayan sawa da takalma da sauransu”. Nayi ajiyar zuciya nace “kayan kadai aka siya amma kusa gama dinkawa. Bayan su ba’a siya komai ba.” Shiru tayi sannan tace “Zara’u ko dai zaki yanki ticket kibi mahaifiyarki ne? Naga yanayin ki gabadaya ya koma tsantsar damuwa da bakin ciki, idan kinason binsu ki shirya ki karbi kudi ki tafi ko gobe ne.

‘Danka ma yace baya yi da kai ka hakura balle jika? Ai ba daku nazo duniyar ba anan na same ku kuma anan zan barku, babu amfanin da yawanku zai mun a lahira don haka duk mai son dauke hanya daga layina na bashi dama. Ni dinnan na isa kaina komai kuma Wanda na Dogara da Shi ya isar mun. Bana bukatar lallai sai kun bini akan dukkan ra’ayina kowa yana damar yin irin rayuwar da ya zabawa kansa. Idan cutar da ku nake yi akwai sakayya a wajen Allah! Idan don nafi karfin ku nake muzguna muku nikuma Allah yafi karfina kuma shi zai saka muku zalincina”

Idona cike da hawaye taf na dago na kalli Dada! Yanayin da nagani akan fuskarta ya sanyani mayar da idon nawa kasa da sauri hawayen na zirarowa kuncina da mugun speed. Ba wannan jarumar Dadan me fada da taurin rai nagani ba. Wannan wata mace ce wadda take cikin damuwa da dimuwa da fargabar rasa wani abu Wanda tafi so fiye da komai a rayuwarta. Wata tsaftatacciyar soyayyar wannan baiwar Allah ta mamaye kirjina. Tunda na taso a hannunta na tashi, domin shekarata daya kacal ta karbeni daga wajen iyayena ta yayeni a dalilin tafiyar su Mami aikin Hajji. Da suka dawo kuma bata sake mayar musu dani ba. Wani irin gata na samu da kulawa da tarbiyya a wajen Dada irin wanda ko a hannun iyayena na tashi ba lallai na samu hakan ba. Ta nunamun gata da soyayya ba irin na sangarta da lalacewa ba. Cikin tarbiyya da ladabi da biyayya da wata irin nutsuwa tayi rainona, na dade ban gano cewa Mami ce mahaifiyata ba sai da nayi wayo sosai.

Babu wani abu wanda na taba nema na rasa a wajen Dada komai girmansa. Fada da zafi halintane wanda wanda ba ba za’a sauya mutum ba. Amma bayan tsatsauran halinta da zafin ta ni banga wani mutum mai kyautatawa iyali irinta ba. Toh kuwa idan har wani abu ya shigo na zabi Mami na barta ai na tafka babban butulci da rashin adalci. Musamman kuma da ita din ba bare ce wajen Mamin ba, yayar mahaifiyar Mami ce wadda Mamin ta taso a hannunta, ta bata tarbiyyarta da kulawarta a karshe ta aura mata danta. Ko anan aka tsaya Dada ta cancanci kowanne irin girmamawa da biyayya da sadaukarwa a wajena don haka na tausasa murya na soma jero kalamaina cikin gwaninta da nutsuwa

“Dada babu wani abu a duniya da zai raba ni da ke, kuma babu wani hali da zaki shiga na guje ki komai muninsa. Babu wani hukunci da zaki yanke a kaina na bijire sannan babu mahalukin da zan iya zaba akanki. Ba tafiyar Mami ke sanyani damuwa ba Dada. Jikin Ya Mahmud ne yake bani tsoro da sage mun guiwa. Kowa ya fidda rai da samun sa, tun suna daga waya cikin kwarin guiwa har dauriyarsu ta kare. Dada bana so Ya Mahmud ya mutu……..”

Na karashe maganar cikin fashewa da matsanancin kukan da na dade ina rikewa sai yanzu ya samu damar kwatar kansa daga can karkashin zuciyata. Dagaske nake jin babu wata matsala a rayuwa da kai mun nauyin ta rashin lafiyar ya Mahmud. Bansan ina mishi irin wannan tsaftatacciyar soyayyar ta jini ba sai wannan karon. Allah yana kallo bazan iya jure rashin Ya Mahmud ba.

A hankali Dada ke buga bayana cikin sigar lallashi da tausayawa kafin ta soma magana cikin dauriya da jarumta.

“Zara’u nagode sosai da irin wannan matsayin da na samu daga gare ki wanda banjin zan iya samunsa wajen wani duk cikin jikokina kuma hakan ya kara miki girma da matsayi da daraja a idona irin wanda bakya zato. Ki kwantar da hankalinki Zahra’u! Mahmud zaiji sauki kuma zai taka da kafafunsa. Zai dawo gare mu da yardar Allah…..” a hankali taci gaba da yi mun wasu maganganu wadanda suka mayar da kukana murmushi har ma bansan lokacin da nayi dariya ba.

This is the side of Dada I have never known! Cikin farin ciki nai mata sallama na futo daga dakin na saka takalmana na futo.

Futowata tayi dai-dai da shigowar wata dalleliyar mota baka wuluk kirar BMW.

Sai na dan saurara naga waye zai futo daga cikin motar. Sai da aka bata wajen mintina biyu kafin a bude motar a hankali. Daga bisani mai motar ya futo cikin wata irin tsararriyar kwalliyar bakar shedda wadda ta haske farar fatarshi. Bakina ne yayi forming O shape cikin tsananin mamaki na tsaya still kamar an dasa ni a wajen.

A hankali yake takowa yana tahowa cikin nutsuwa! Kowanne taku daya na karamun mamakinsa da tambayoyi iri iri a kaina…………….

Eid Mubarak to you and your Family!

May we live to witness more of it’s kind.

So waye yazo wajen Zahra? Guess!

Me Dada ta gayawa Zara?

Did I ever mentioned Mami as niece din Dada? We don’t know alot about this family……….muje zuwa.Cikin matsanancin mamaki lebbana suka motsa a hankali.

“IMAMU”

Yaushe ya koma hayyacinsa da kuzarinsa da gayunsa da nutsuwarsa bayan haukacewar da yayi akan warwarewar maganar auren mu. Ni tunda nayi blocking shi na kuma daina daga bakuwar number sai na samu nutsuwa. A hankali ya dauke kafa daga zuwa kofar gidanmu da bibiyar al’amurana har ma na manta gabadaya da labarinsa sai da mikin da ya barmun  wanda ba ba zai gogu lokaci daya ba.

Toh duk ma ba wannan ba! Me ya kawo shi gidanmu? Da wacce yazo? Me zan masa?

Cikin sauri na daure fuskata tamau kamar bansan garin da ake dariya ba. Na sake gyara tsayuwata cikin jarumta da rashin barin ko ta kwana.

A hankali ya karaso dai dai inda nake tsaye sannan yace “Good day beautiful!”

Na dago na kalle shi a banzace. Ya rame sosai amma ya kara fari sannan babu wannan mayaudarin murmushin akan fuskarsa. Hakan ya sanya masa wani kwarjini na musamman!

Cikin muguwar daurewar fuska nace “Me ya kawo ka gidanmu?”

Guntun murmushi yayi yace “hmmm Zara wannan ne sannu da zuwan da zaki mun?” Wata muguwar harara na zuba masa sannan nace “kai kana mafarkin zaka samu sannu daga wajena a cikin wannan duniyar? Wanda ake maraba da shi ake wa sannu da zuwa ba wanda ba’a bukatar gani ba! Bana son dogon zance don haka ka fadi abinda ya kawo ka ka juya ka futa don babu wani abu a gidan nan da yake maraba da kai balle ya karbi bakuncinka “

Sosai ranshi ya baci matuka da kalamaina har sai da launin idanunsa suka sauya. Ya koma wani serious babban mutum. Tabe baki nayi na juya masa keya ina sauraren abinda zai fada.

Cikin karyewar sauti da tsananin sanyin jiki ya soma magana.

“Zara ba anan naso muyi wannan maganar ba saboda muhimmancin ta but I have no option tunda kin daina yi mun kallon mutum na koma miki kamar wani dabba abun kyama.

Zara nasan bani da hali kuma bani da dabi’a bani da kirki kuma na aikata manya manyan laifuka da kura-kurai masu yawa a rayuwata. Na zalunci mata dayawa ba yaudare su, na bata musu suna, nayi abinda nake so a rayuwa ba tare da tunanin cewa dama Allah ya ara mun ba, ba tare da tunanin akwai makomar abubuwan da nake aikatawa ba. Ni kaina idan ina tuna wasu abubuwan nakan kwana ban runtsa ba saboda tsananin tashin hankali da tunanin illar da abubuwan da nayi zasu haifar mun a gaba. But trust me Zara! Billahil azeem daga lokacin da kika shigo rayuwata nagane so na hakika na bambamce son gaskiya da na yaudara. A lokacin na soma tunanin nima zanyi aure nayi building rayuwata na aje rayuwar da nake yi duk da nasan ba abu ne mai sauki ba.

Zara Allah ya jarabce ni da sonki jarabta mafi azabtuwa da radadi. Ban taba sanin menene tashin hankali ko bakin ciki ba a rayuwa sai ranar da aka janye maganar aurena da ke. Daga lokacin na tabbatar hakkin mutanen da na zalinta ne zai tambayeni domin na san cewa rashinki a rayuwata wata muguwar masifa ce da zata tarwatsa ni da duk abinda na gina a rayuwata. Daga ranar na koma ga Allah, na tuba, nayi nadama mai tsananin gaske tare da daukar aniyar cewa akan ki sai inda karfina ya kare. Sai dai hakan bai samu ba, domin laifuka na gare ki masu tsananin girma ne wadanda ba kowanne mahaluki za’aiwa ya yafe ba. Ganin ba zan taba samunki ba ya sanya na saduda na koma ga Allah na tafi Saudiyya tsayin watanni biyu ina bautar Allah tare da jinyar zuciyata har Allah ya bani hakuri da dangana da nutsuwa. Sau biyu ina haduwa dake a Haram a wannan zuwan da kuka yi amma bani da kwarin guiwar da zan iya fuskantar ki a wannan waje ko dan gudun kar na tuna miki abinda nayi miki ki kai kara ta a wannan wuri mai tsarki da daraja kila ma addu’ar da nazo yi a dawo mun da ita.”+

Dakatawa yayi da maganar yana lashe lebbansa da suka bushe tare da gyara tsayuwa. Nikam jikina ne ya soma sanyi duk yanda na dau zafin ganinshi da haushin sa da nake ji sai da naji nayi rauni. A hankali yaci gaba da cewa “a yau Zara nazo wajen ki ne ba don na dame ki ba, ko na bata miki rai akan neman alfarmar soyayyarki! Nazo ne nayi miki godiya Zara godiyar da babu mahalukin da ya cancanci irinta bayan ke a rayuwata.”

Cikin mamaki na juyo gabadaya ina kallon shi. Kallon rashin fahimta da tuhuma. Hade hannuwanshi yayi waje guda yace  “yes Zara! I want to thank you! Saboda Kece silar shiriyata! You have changed my life! Kin sauyani daga batacce zuwa mutum nagari. Kin ceto ni daga halaka kafin lokaci ya kure mun kuma kin dawo dani hayyacina kin koyar dani darasi kafin duniya ta koya min. Gayamun ta ya zan iya gode wannan alkhairin naki a gareni? Wallahi ko da ban aure ki ba shigowar ki rayuwata shine alkhairi mafi girma da na ci karo da shi. Don haka nazo wajenki domin na tabbatar miki da cewa a duk lokacin da kike tunanin aikin da kikai na lada a duniya, abinda zaki fara lissafawa shine kin samu nasarar shiryar da babban lalatacce irina zuwa hanya mai kyau. Na tabbatar Allah will reward you for this. Ba zan iya nemar alfarmar yafiyarki a yanzu ba, sai dai kiyi mun lamuni ki yafe mun kafin Allah ya dau numfashina. Don ina tsoron Allah ya kamani da hakkin ki Zara.

STORY CONTINUES BELOW

Duk cikin matan da na yaudara ke kadai ce kintsatstsiya nutsatstsiya mai tarbiyya. Sauran duka irin halina gare su sannan akwai abubuwa da yawa da na kulla wadanda nake jin kunyar dosar ki da su akan aminiyarki Aisha! Zara na tsoratar da ita, nayi mata barazana kala kala kuma  nq azabtar da ita sosai ta hanyar amfani da soyayyar da nagano tana yi mun! Zara naji mutuwar Aisha fiye da tunanin ki, kuma bakina bai taba wuni ya wayi gari bai mata addu’a ba. Musamman da na fahimce meye so da martabar shi ga Wanda yake cikin shi. Wallahi tunanin abinda nayi wa Aisha kadai na hanawa idona runtsawa…..”

Ga tsananin mamakina sai gani nayi Imamu yana hawaye! Irin hawayen nan masu tahowa daga karkashin zuciya. Hawaye masu gangarowa da gudun da yake tabbatar da nadamar da ke cikin zuciyar mai fidda su. Tuni tausayin shi ya soma kamani ba tare da na shirya ba, domin na tabbatar da cewa wannan Imamun ba Imamun da na sani bane, wannan wani sabon mutum ne wanda ya ke cikin halin nadama da Dana sani da dimuwa da kuma fatan shimfida kyakykyawar rayuwa a gaba.

Ban aune ba nagan shi ya durkusa guiwoyinshi biyu a kasa! Cikin shaking voice ya ci gaba da cewa

“Zara don girman Allah don son da kike wa Manzon Allah saw! Ki taimakeni ki rage mun nauyin da yake kaina ki karbi tubana ko na samu sukunin fuskantar ubangijina wajen sallah! I am truly sorry Zara! wallahi tallahi babu digon karya ko yaudara akan abinda nazo miki da shi….”

Ji nayi idona na cika da ruwa alamar kuka na son kwacemun a kowanne lokaci daga yanzu. Cikin sanyin jiki nace “ba sai ka durkusa mun ba! Na yafe maka! Allah ya yafe mana baki daya”

A hankali ya tashi tsaye yana murmushi da hawaye lokaci daya bai damu da kade kasar da ya kwaso a guiwarsa wajen durkuson da yayi ba yace “Nagode Zara! Nagode! I’m very grateful! I can’t thank you enough for you kindness! You are sure one in a million a cikin matan wannan zamani! na tabbatar da wata ce……”

Karar bude gate ce ta hanani jin karshen maganarsa hankalina kacokan ya koma bakin gate inda sabuwar Mecedes Benz fara sol ke turo hancinta cikin gidan. Tsananin duhun gilasan motar ya sanya ban tantance waye a cikin motar ba. Da dai Ya Omar yana nan ne sai nace shine yazo yayi mun mun bazata don babu abinda rayuwarsa ke so irin mota. Sai dai me? Futowar me motar ya sanyani kusan sakin fitsari a tsaye.

Yanda motar take fara sol haka voile din jikin shi yake fari kal na birkidediyar babbar Rigar da aka cika ta da aikin zare mai tsari. ya karya kwanar hular ‘zanna bukar’ akan askakkiyar sumar shi. Looking too matured to be my fiance.

Yana futowa daga motar yayi arba dani da Imamu a tsaye muna mishi kallon kurilla. Take ya dauke wuta yayi kicin kicin kamar zai hadiye mu daga wajen da yake! Ji nayi cikina ya bada wani sauti “kuluuiiiuullu” har sai da Imamu ya juyo ya kalleni. Shima din tashi fuskar a daure take tamau, kukan da yayi ya sake mayar da fuskar jajawur abunka da jar fata. Nikam Allah ne kadai yasan yanda zanyi da wadannan samudawan.

Cikin muguwar dauriya na dan ja baya na gyara tsayuwata da zaman gyalena a kafadata kirjina naci gaba da dukan tara tara. Sai da yazo dab damu yaja burki ya tsaya. Kaina ya wani Sara, kamshin Tomford na Imamu ya hade da 212 din Mubarak ya bada wani kamshi mai hada husuma don kowanne ji yake da kanshi.

Cikin isa da kasaita da bacin rai yake kallona ya zura dukkan hannayensa a aljihu kamar wani kanin Ubana. Bayan igiyar aure muke shirin kullawa. Ai shi ya kamata yayi biyayya duk girmansa tunda shi ya gani yace yana so ba talla akai masa ba balle yazo yana mun muzurai. Kawai sai naji wata dakiya tazo mun balle da na tuna iskancin da matar shi ta dinga shukamun a waya. Ya kamata yasan cewa bai kai matsayin da yake baiwa kanshi a zuciyata ba.

Murmushin karfin hali nayi nace “Laa zuwa babu notice! Sannu da hanya” a kufule ya amsa da “yauwa” inaga rashin nuna tsoro ko fargabar ganina da yayi tare da wani ne ya sake bata mishi rai.

Wani murmushin na sake kakalowa ina kallon Imamu nace “Imamu meet my fiance Mubarak!” Sannan na dubi Mubarak nace “Mubarak ga Imamu” wata irin dauke wuta ya sake yi kamar zai hadiyeni don takaici. Imamu bawan Allah abun tausayi ya ciro hannunsa ya mika masa suyi musabiha amma Mubarak yayi funfurus ya sake nutsar da hannayenshi cikin aljihun shi.

Ganin haka Imamu ya kalleni a sanyaye yace “Zara I think I need to go! Sai wani lokacin!” Ya kare maganar yana soma takawa baya. Don na kara hadawa Mubarak zafi sai na bi bayansa ina cewa “ok Nagode Imamu! Ka gaida su Mummy! Sai munyi waya” a hankali ya juyo yana kallona da mamakin jin abinda nace. Sai kuma yayi shiru ya mayar da kansa yaci gaba da tafiya baice kala ba. Sai da na raka shi har gaban mota sannan nayi masa sallama na juyo. Ina tafiya ina juyawa har ya bar farfajiyar gate din.

Lokacin da na dawo wajen Mubarak na dauka zai rufeni da duka ne. Wani irin naushi yayi wa bangon da ke gefena Wanda ya sanyani matsawa baya da sauri. Cikin mamaki nace “dukana zakayi?” Kawai huci yake yi kamar zai fashe daman shi gashi kato abun tsoro.

Babu shiri  na lallaba bakina da rashin kunyata na mayar da su gefe. A nutse na wuce hanyar Guest room din da muke zama na bude. Na zata ba zai taho ba sai kuma naga ya biyoni.

Sai da muka zauna sannan na gaida shi ga mamakina sai ya amsa da dan sakin fuska. Harda tambayan mutanen gida nace masa kowa lafiya. Mikewa nayi da nufin naje na kawo masa abun motsa baki, sai ya dakatar dani ta hanyar daga hannu sannan yace “No! Bana bukatar komai yi zamanki ba dadewa zanyi ba” duk da banji dadin maganarsa ba ban nuna hakan ya dame ni ba. Sai na koma na zauna ina kallon yatsuna, dagaske mutumin nan babba ne, don ba yanda ma za’ai kace bai girmi Ya Mahmud ba. Ko ya akai ma na amince zan aure shi ni bansani ba, idan yasha kunu sai kace ya kai shekarun Daddy.  Shi ya katse mun tunani ta hanyar cewa

“Nazo ne naji abubuwan da kike bukata na hidimar biki da events din da zaki shirya. Ta fannina colleagues dina sun shirya dinner a Lagos bayan an gama biki. Sai Mother’s eve da budan kai a gidanmu. Me kike son yi kuma nawa kike bukata?”

Rasa me zance nayi don ban kammala wannan lissafin ba muka tafi Saudi rashin lafiyar Ya Mahmud kuma ta shigo. A nutse nace “Ban samu damar wani shiri akan events din ba saboda rashin lafiyar Ya Mahmud. Kuma idan ma akwai abinda zanyi bai wuce bridal shower ba sauran su Mami ne zasu yi deciding komai.”

Cikin gamsuwa ya girgiza kai sannan yace “ok Allah ya bashi lafiya! Nima ina jin a cikin satin nan zamu tafi da Surayya hado lefe London din, zanje na duba shi”

wani mugun kallo na watsa mishi na rashin fahimta ba tare da na sani ba nace “lefen wa?” A kasaitance yace “naki da nata”

Wani shock ya sake ziyartar kirjina da wani bakin ciki. Cewa nayi “daman kishiya ce take hada lefe? Ba a gidanku za’a hada ba?” Wani Smirk yayi na yarda da kai sannan yace “idan kinga anyi haka sai idan uwargida fitininniya ce. Amma mace irin Surayya ai har wedding planning din na hannunta.”

Cikin mugun fushi nace “Ai ni a sanina irin su ba’ai musu kari! Ba’a kai kusu kishiya saboda cancantar su”

Dariya yayi sosai sannan yace “No wannan kuma layin shi daban! Wa ya gaya miki sai Uwargida na da aibi ake karo wata? Karin aure ai sunna ne da kuma ra’ayi”

Tuni idona ya soma kawo ruwa. Na gyara zama nace

“Aww ashe kai ka bata lasisin da take daukar wayarka ta kirani taci mun mutunci?”

Ya sake murmusawa sannan yace “wannan kuma halin kishin ku ne na Mata idan ya motsa. Lallabata zakiyi a matsayin ta na babba kece karama ku zauna lafiya. Kinsan ita za’ai wa laifi sai da lallami…….”

Ban jira ya karasa ba na tashi na bar masa falon da sassarfa kamar zan fadi zuciyata na wani irin zogi. Inajin kiran da yake kwallamun amma Sam ban juyo ba na zura takalmana na bar falon. A maimakon na koma cikin gida sai na shiga mota ta na tayar na soma kokarin futa daga gidan, dai dai lokacin ya futo shima yana kirana. Ganina cikin mota ya sanya shi saurin daga mun hannu yana cewa “wait tsaya kiji Zara” ko kallonsa ma nayi. Da gudu na figi motar na futa daga gidan ba barshi yana kokarin shiga tashi motar.

Assalamu Alaikum!

It’s coming late again! I am sorry!Wani irin tuki nake yi bana ganin gabana don tsabar takaicin da Mubarak ya hada mun. Cikin ikon Allah na isa gidan Ihsan, ko amsa gaisuwar mai gadi ban tsaya yi ba na figi motar a guje zuwa cikin gidan. A tsakiyar harabar filin nayi parking na balle murfin motar na futo. Sai dai ban ma kai ga shiga gidan ba na ga maigadin ya sake wangale gate din, motar Mubarak ta danno kai wanda ban San lokacin da ya biyo ni ba.

Tsaki nayi na fasa shiga ta ainihin fuskar gidan don kar na tsaya danna bell yazo ya taddani na zagaya na bi ta kitchen na shiga ainihin babban falon Ihsan. Ina shiga suna saukowa daga bene ita da Faisal yana dauke da Amani a hannunsa. Ganin halin da nake ciki ya sanya su karasa saukowa da sauri Ihsan ta nufo ni tana cewa “Zara! Lafiyarki kuwa? Me ya faru?” Kawai rungumeta nayi na sa kukan da ya sake basu tsoro! Faisal ne yace “kinga ku zauna! Calm down Zara! Ki nutsu dan Allah ki gaya mun me yake faruwa?” Dakyar Ihsan ta kaini kan kujerar da ke gefena muka zauna shikuma Faisal ya dora mata Amani akan cinyarta sannan ya zauna akan kujerar dake saitin mu yana kallona cikin damuwa. Ban samu sukunin yi musu magana ba mai rainon Amani tayo sallama ta shigo, sannan ta durkusa tace “Alhaji kana da bako a waje” cewa yayi yana zuwa ya mike ya futa cikin sauri.

Ihsan ta sake matsowa kusa dani ta dafa kafadata tace “Zahra don Allah kiyi shiru ki gaya mun abinda yake faruwa kin daga mun hankali wallahi! Ko jikin Ya Mahmud ne?” Girgiza kai nayi a hankali ta sake cewa “toh menene?” Cikin sanyin murya nace “Ihsan gaskiya na hakura da auren Mubarak! Idan na aure shi ciwon zuciya zai saka mun” na sake fashewa da wani kukan, takaicin abinda yayi mun yana dawowa kaina daya bayan daya.+

Shiru tayi na wasu dakiku tana kallona kafin ta mike ta nufi hanyar kitchen. Mintuna biyar ta dawo dauke da madaidaicin tray a hannunta tazo ta aje a table din da ke gefen kujerar da nake zaune sannan ta dauki kwalin fresh milk ta girgiza ta cika mun karamun glass cup ta miko mun.

Babu musu na karba na kafa kaina na soma kwankwadar madarar sanyin ta yana ratsa zuciyata da jikina yana saukar mun da salama. Ban tsaya numfashi ba sai da na shanye tass na aje kofin.

Zanyi magana kenan Faisal ya shigo, daga kofa ya tsaya yace wa Ihsan “saka gyalenki Mubarak zai shigo” kallona tayi ta saki murmushi sannan ta mike taje ta dauko gyale ta dawo ta zauna tana kallona cike da tsokana. Ni kuwa na daure fuska tamau kamar ban taba dariya ba. Faisal ne ya sake turo kofar ya shigo Mubarak na biye da shi yana wani munafikin murmushi. Sai da ya soma daukar Amani da ke kwance akan kujera sannan ya dawo ya zauna a gefen Faisal yana cewa da Ihsan “Madam Sannu da kokari ban samu zuwa ganin baby ba sai yau”

Cikin tsokana Faisal yace “ah toh gashi nan ai biko ya kawo mana kai” sukai dariya gabadaya sannan suka soma gaisawa da Ihsan sai wani sunkuyar da kai take yi kamar wani surikinta. Nidai ko kallon inda yake banyi ba.

Sai da yayi gyaran murya sannan yace wa Faisal “toh tunda ga Magistrate sai a karanto mun laifina na kare kaina kafin a yanke mun hukuncin da ya dace” Dariya sukai gabadaya, Faisal yace “wai Ihsan ce Magistrate din?” Cewa yayi “ah! itace mana tunda kaga an dauko mota an taho gidanta a fusace ai matsayin da take da shi kenan!” Ihsan tayi murmushi tace “to ai ni har yau banji komai ba zaman rarrashi da ban baki nake yi tukunna! Taki gaya mun abinda ya faru”

Mubarak ne ya gyara zama yace “watakila tasan bata da gaskiya ne shiyasa! Ihsan kiyi alkalanci na tsoron Allah da gaskiya! Tun daga Lagos na bar ayyukana na taho kawo mata surprise visit amma kawai sai zuwa nayi na ganta da wani kodadden mutum kamar albino sun tsurawa juna ido kamar masu acting movien soyayya. Da yake shakiyancin shi ya kai ya kawo wai har miko mun hannu yayi muyi musabiha, sa’ar sa daya gidan surukai muke tsaye da sai na zubar masa da hakora. Bai isheta ba wai yace zai tafi zungui zungui ta kama hanya ta raka shi ga Gaula a tsaye wanda zuwan shi ya kawo cikas….

Amma ita duk wadannan bata karanta su a laifi sai kawai don nace mata zamu je hado lefenta da Surayya ta birkice ta soma masifa kamar idonta da bakinta zasu fado har da cewa wai a ina na taba ganin kishiya ta hado lefe…..”

Gabadaya falon dariya suka kwashe da ita wadda ta kular dani na mike tsam zan bar musu wajen Ihsan tai maza ta fuzgo hannuna na dawo na zauna. Wata muguwar harara na watsa mata nace “tunda na zama mahaukacciya meye ruwanku da zamana anan?”

Faisal ne yace “haba Amarsu ai ba’a haka! Hakuri zaki yi a yankewa mai laifi hukuncin sa don gaskiya bai kyauta ba! Ihsan kinji fa ruwan da ya ballo kuma yake zaune hankalinsa kwance” zama ta gyara tace “toh gaskiya wannan laifi ya kai makura wajen girma saboda haka Ango sai ya bada hakuri”

STORY CONTINUES BELOW

Faisal ne ya mike yana cewa “ai ina ganin ita da kanta ya kamata ta yi wannan hukuncin ko Ihsan? Mu dai munyi nan” ya karasa maganar yana tafiya….Ihsan ta mike tana dariya ta bi bayan shi. Na sake daure fuskata ina muzurai.

“Toh wai ke daman baki san wasa ba Zahra? Wasa nake miki kawai don kiji irin abinda naji akan wannan maulallaen mutumin da tarar da ku tare. bansan hankalin ki zai tashi ba! Gashi ko bari baki yi na gaisa da Dada ba kin dauko mu kin kawo mu nan”

Banza nayi mishi yayi ta babatun shi da ban hakuri ban tanka ba har da cewa ya ja wa Surayya kunne sosai akan kirana a waya musamman da wayarsa  kuma idan ta sake kirana na gaya masa akwai matakin da zai dauka. Sai da ya shiga maganar jikin Ya Mahmud sannan na sauko muka ci gaba da tattaunawa. Ya sake cewa

“Lefe an dade da hadawa jikin Mahmud ne kawai ya sanya aka dakata saboda su Daddy basa cikin nutsuwa kuma babu hannun Surayya a ciki, duka shawarata da Ihsan Faisal ya hadani muka yi ta gaya mun taste din ki, da brand din da kike amfani da su da sizes din kayanki,ke da da duk wani information da ake bukata. Duk abinda kika ga bai miki ba a cikin kayan laifin Ihsan ne”

Kunya naji ta kamani da mamakin Ihsan da iskancinta. Ko wanne wulakancin ne ya hana ta gayamun oho! Koda yake tasan cewa zanyi kar ta gaya masa, Wato har sun saba kenan da shi. Duk da yake abokin Faisal ne amma ai bata san shi ba sai yanzu da maganar aure ta hada mu da shi.

Bamu muka bar gidan Ihsan ba sai wajen 8. Ina gaba yana bina a baya har ya rakani gida sannan ya wuce da alkawarin gobe zai dawo su gaisa da Dada jibi zai wuce Lagos.

                TWO WEEKS LATER

Cikin matsananciyar nasara wadda karfi da tasirin addu’a ya haifar Ya Mahmud ya farfado daga mummunan halin da yake ciki. Numfashinsa ya daidaita yana iyawa da kansa ba tare da taimakon oxygen ba. Yana gane mutane har yana magana mara tsayi.

Murna wajen Daddy da Mami ba zata misaltu ba. Muma da muke Nigeria ba karamun farin ciki muke ciki ba. An samu nutsuwa da kwanciyar hankali da kuma sa rai akan rayuwar Ya Mahmud. Take shirin biki ya kankama domin Daddy yace ba za’a daga ba suna fatan kafin lokacin bikin Ya Mahmud ya kara samun karfin jikinsa kuma tunda a London zasu zauna yana kusa da likitocinsa ba za’a samu matsala ba.

Bayan Sati biyu aka sallame shi daga asibiti suka tattara suka koma cikin garin London tare da Mami wadda ta dauki duka dawainiyar shi ta dora a kanta ba tare da gajiyawa ba!

Daddy dakyar ya yarda ya koma bakin harkokinshi don cewa yayi sai yaga fadawar komai. Sai da Mami tayi tayi masa magiya likitocin kuma suka tabbatar masa da komai zai tafi dai dai sannan ya hakura.

Yammacin talatar da ta rage sati shida bikina da na Ya Mahmud Mami ce a cikin kitchen tana hadawa Ya Mahmud lunch, domin tunda suka futo daga asibiti ita take sarrafa masa abinda zai ci musamman suka zauna da likita yayi mata bayanin duka abubuwan da ake bukatar patient din zuciya suci da wadanda ya kamata su nisanta. Sannan bata yarda yasha wani ruwa da ya wuce zam-zam. Wani lokacin ta zauna ta tofa masa addu’o’i a ciki yasha ya shafe jikinsa. Hakan kuwa ba karamun tasiri yake wajen raguwar ciwon na shi ba.

Tana cikin aikin aka danna kararrawa ta tsame hannunta ta gyara gyalen jikinta taje ta bude kofar. Daddy ne a tsaye tare da mahaifin Safna. Cikin mamaki take kallonsu domin tunda Mahmud ya kwanta a asibiti ko da wasa Safna da iyayenta basu je duba shi ba har ya gama jinya ya futo daga nan suka dawo London inda suke makotakar juna amma shiru. Suna yawan maganar da Daddy akan wannan al’amari mai daure kai, ga Amina da suke Nigeria zuwanta biyu da mahaifinta suna duba Mahmud amma wadda take kusa bata je ba. Sun yanke maganar dai akan watakila maganar auren Mahmud da Amina ne ya janyo haka.

Sai da Daddy yayi gyaran murya sannan ta dawo daga tunaninta ta basu hanya tana yi musu sannu da zuwa. Suka wuce parlour ita kuma ta hada kayan motsa baki akan tray ta shiga musu da shi. Sannan suka gaisa don shi kansa Daddyn saukar sa kenan daga America.

Bayan sun gaisa Daddy yace “ina Mahmud yake?” Cikin sanyi tace “yana dakinsa yana bacci bari na duba naga ni”

Daga nan ta mike ta shiga ciki inda dakunan suke jere ta kwankwasa kofar dakin Mahmud! Sai da ya bata izini sannan ta murda handle din ta shiga. Yana tsaye a gaban mudubi da alama daga wanka ya futo cikin shigar Gucci jean da farar chiffon top din Louis Vuitton. Yana combing himilin kwandon gashin shi da Mami tasha artabu da shi akan yaje barber’s saloon a rage masa tsayinsa a gyara masa shi amma fafur yaki yarda domin idan akwai abinda yafi baiwa muhimmanci a jikinsa toh bai wuce wannan gashi ba. Bai yarda kowa ya taba masa shi ba shi yake gyaran abunsa da kansa idan kuma bai samu sararin yin hakan ya gwammace ya barshi a kanannaden sa hankali kwance.

Gabadaya ya chanja sosai, yayi mugun fari sannan ya rame, tarin gashin da yayi masa yawa ya sake sauya nationality dinsa zuwa cikakken baralabe usul da za kai mamakin jin kalmar hausa a bakin sa.

Ganin yanda take kallonshi yayi murmushi yace “Mamina na sauya miki ne? ” murmushi tayi tace “ta karfi da yaji dai ka koma HAUSA ARAB din ka, wannan gashin don Allah baya yi maka nauyi?” Dariya yayi yace “Kai Mami wanne irin nauyi kuma? Ki shigo Mami kin tsaya zaki gaji” cewa tayi “ba zama zanyi ba ka futo Daddy ne yazo tare da baban Safna”

Wata juyawa yayi a sukwane yana kallonta fuskarsa ta sauya cikin second daya kamar ba shi yake dariya yanzu ba. Ba tare da yace komai ba ya aje comb din ya futa daga dakin cikin sanyin jiki.A nutse yake shigowa cikin falon kai tsaye ya wuce kujerar da Daddy yake zaune ya rungume shi suka gaisa tare da yi masa ya jiki  sannan ya juya ga Eng. Garba Galadanci ya gaishe shi fuska a daure. Daga nan ya nemi kujera ya kame yana muzurai wanda zai sa kayi shakkar kawo masa wargi. Gane hakan da Daddy yayi ya sanya ya murmusa sannan yayi gyaran murya yace “Ahm wato Mahmud Baban Safna ne yazo da wata magana wadda ni bansan yanda aka yi hakan ya faru ba don ba kai mun wata magana da ta dangance ta ba.” A kasaitance Mahmud yace “wacce magana kenan?” Yana kallon Engineer.

Sai da gaban Eng ya fadi saboda ganin yanda Mahmud ke cika yana batsewa. Cikin sanyi ya soma magana

“Mahmud sati hudu da suka wuce zuwa biyar mukai magana da kai a waya kake tambayata Safna nace maka tana Scotland wajen kawarta. Ka tambayeni me taje yi na gaya maka sannan ka kashe wayar. Sati daya dai dai bayan wannan lokacin Safna ta shigo da yamma cikin wani irin yanayi tana ta kuka kamar ranta zai futa, duk iya tambayar da zamu yi mata munyi taki bamu amsar dalilin da ya sanya ta kuka. Kwanaki uku tana cikin wannan halin kafin tace wai Mahmud ne yace babu shi babu ita. Maganar ta daure mun kai matuka, na tambaye ta mai tayi maka? Tace wai kawai saboda taje gidan kawarta. A lokacin ne nayi ta neman wayarka ban same ka ba, na kira Alaji yace mun baka da lafiya ne shiyasa amma idan ya nutsu zamu yi magana.

Tunda Safna taji ance baka da lafiya ta sake daga mana hankali… na rasa yanda zanyi da ita. Cikin haka tafiya ta taso mun zuwa Florida sai muka tafi gabadaya domin dai ta samu ta warware ta samu nutsuwa. Daga nan muka wuce Nigeria sai  Last week muka dawo, amma tace kullum sai ta kira wayarka baka dauka, nima bana samun layin Alaji idan na kira shi sai dakyar shekaranjiya na same shi na yi masa bayanin abinda yake faruwa yace idan yazo zamu yi magana.”+

Zama Mahmud ya gyara tare da bada hankali ga Eng da Daddy. Sannan ya soma magana a nutse yana kallon Eng.

“Tun farkon haduwar mu ba Safna ce ta hada mu ba don haka ba zata zamo dalilin rabuwarmu ba. Kai da kanka ka gayyaceni dinner gidanka a matsayin likitan da yayi nasara akan matsalar yarka. Ban cika amsa irin wadannan gayyatar ba saboda gudun mutane amma karamcin ka da girmanka ya sanya na kasa yin haka. A wannan zuwan da nayi ka bijiro mun da maganar da ta hargitsa mun lissafi da kwakwalwa. Wato maganar yarka Safna, bayan ka labarta mun rayuwar ta da maraicin da ta taso a ciki wanda yayi matukar girgiza ni. Ba soyayya bace ta kulla mu’amala tsakanina da Safna, tausayi ne da ganin kima da darajar ka.

A hankali muka saba muka yi wata irin shakuwa da Safna, sannan ne kuma nagano abubuwa da yawa a game da ita wadanda banyi hasashe ba.

Na farko dai I am sorry to say

Safna bata da tarbiyya, idan nace tarbiyya ina nufin rashin kamun kai da sanin addininta da yanda zata tafiyar da rayuwarta a matsayinta na musulma.

Na biyu Safna sangartacciyar yarinya ce da bata san menene rayuwa ba. Ta taso ne akan duk abinda take so dole zata same shi ta kowanne hali, bata san ta nemi abu ta rasa ta hakura ba.

Na uku duka mutane da kawayen da Safna take mu’amala dasu shaidanun turawa ne wadanda ko cikin turawan basu da kirki.

Wadannan abubuwan guda uku kowanne zai iya zama dalilin da zan raba da hanya da Safna amman banyi ba. Saboda na dauki damarar gyara Safna na shiryar da ita da yardar Allah na kuma daidaita mata rayuwar ta iya bakin iyawa ta. Nasan hakan ba zai mun wahala ba saboda soyayyar da take mun na tabbatar babu irin biyayyar da ba zata tayi mun ba.

A hankali na soma rabata da rayuwar club, da kawayen banza da kuma banzar shigar da take yi kullum. Daya daga cikin abinda ya bani wahala akan Safna Joyful ce, wannan kawarta ta da ke Scotland. Joyful shaidaniyar gaske ce irin wadda ko turawa tsoron sharrin ta da kaidin ta suke yi. Gashi sun matukar shakuwa da juna amma haka na dinga bin dabaru kala kala har na samu nayi musu iyaka da ita. Ban taba tunanin yaudarar Safna ba, duk da ba wai son ta nake ba amma akwai shakuwa da fahimta mai karfi tsakanina da ita wadda nake ganin zan iya zaman aure da ita.

Watanni hudu haka da suka gabata na fara ganin sauye sauye a wajen Safna. Ta rage yi mun waya, ta rage daukar tawa wayar sannan duk sanda na kira ta her voice is weak kamar mai bacci ko tunani ko mara lafiya. Nayi matukar kokarin naga ta gaya mun menene matsalarta amma sai kullum sai tace babu komai.

Kullum abu karuwa yake yi a dalilin zamana Nigeria bana tare da ita balle na gano abinda yake faruwa. Ranar da na kira ka abinda naso yi maka bayani kenan domin ka tambaye ta menene matsalarta, sai ka tabbatar mun da cewa tana tare da Joyful a Scotland babu wani kwakwkwaran dalili. Shiyasa ban ma tsaya cigaba da jin me zaka ce mun ba na kashe wayar.

STORY CONTINUES BELOW

Cikin tashin hankali na bar komai na taho garin nan domin sanin ainihin abinda yake faruwa. Idan akwai wadda na tsana tare da Safna a duniya babu kamar Joyful. Da nazo ko hutawa banyi ba na nemi addreshin gidan Joyful na dauki kafa na tafi Scotland domin ganin komai da idona. Gidan da aka tabbatar mun suna ciki sai da nayi kwanaki ina zirga zirga kafin na samu ganin su.

Halin da naga Safna a ciki ya tsorata ni kuma ya bani mamaki, sai lokacin kuma na gano cewa Safna ta wuce sanina da tunanina. Mahaukaci ta mayar dani kawai amma babu wata alaka da ta yanke tsakaninta da Joyful. Ranar da na shiga cikin gidan na samu Safna a halin da nake zargin ta jefa kanta. Wato shaye-shaye!!

Da karfi Daddy ya zaro idanu yana karanto “innalillahi wa Inna ilaihi raji’un” shikuwa Eng kawai sunkuyar da kansa yayi ya kasa cewa komai.

Mahmud yaci gaba da cewa “tana zaune akan gado tayi bajakolin syrup kala kala da kwalaben barasa gabadaya ta futa hayyacinta. Rasa me zanyi mata nayi, rasa matakin da zan dauka nayi a lokacin ba tare da nayi barna ba. Sai kawai na zabi wanda yafi kowanne sauki nace mata babu ni babu ita har abada. Bazan iya cigaba da rayuwa da ita ba, ko da kuwa bayan auren mu nagano haka balle yanzu. Dalilin da ya tayar mun da ciwona kenan, da ajali yayi kira ma sai dai ayi mun lissafin kwanaki yanzu.

Ko da baka zo ba nayi nufin samun Daddy na warware shi komai don kar ku sha wahalar cigaba da shirin biki tunda nasan ba lallai ta gaya muku ba. watakila kuma idan ta gaya mukun kuyi tunanin sasantawa. Toh abinda zan gaya maka shine ba zan auri Safna ba. Na fasa kuma duk duniya babu wanda zai tirsasani akan haka bayan iyayena, su kuwa ba zasu yi fatan na auri mace irinta ba. Nayi iya kokarina akan ta, kuma Allah yaga niyyata ta alkhairi kuma zai bani lada amma batun aure wallahi na fasa. Duka abinda nayi mata bana bukatar ku dawo mun da komai saboda Allah nayi. Allah ya shirya ta idan da rabon zata shiryu.

Yana kaiwa aya ya mike tsaye, cikin sauri Eng ya durkusa zai soma rokon shi Daddy yayi maza ya maida shi da hannunsa yana cewa “no! Don Allah kada kayi haka”  wannan ya baiwa Mahmud damar fucewa daga falon zuwa dakinsa.

A nutse Daddy ya dubi Eng yace “kasan cewa Mahmud mara lafiya ne kuma babu abinda lalurar sa bata so irin bacin rai ko damuwa ko? Shi yaga Safna yace yaji ya gani zai aure ta mu kuma saboda farin cikinsa muka yarda da ita domin mu bamu san makasudin abinda ya hada su bama banda yanzu da yake fada da bakinsa. Don haka gaskiya Enigneer hakuri za’ayi! Ba zan tursasa shi ba ko da kuwa bashi da hujja akan janye auren balle kuma wannan hujja ce mai karfi da zata iya rushe maganar aure. Shaye shaye a wajen ‘ya mace? Me ya kai wannan masifa? Yaya akai Eng kayi sake haka ta faru? Meyasa baka sa ido akan rayuwar Yarinyan ka ba har abun ya kai ga haka?”

Wasu hawaye masu zafi ne suka dinga biyo kumatun Engineer kafin cikin sanyin murya ya soma bashi tarihin rayuwarsa da alakarsa da mahaifiyar Safna da rasuwarta har zuwa lokacin da ta ga Mahmud ta tubure babu wanda take so sai shi. Sannan ya dora da cewa

“Duk abinda Safna take so idan banyi mata shi ba gani nake kamar naci amanar marigayiyia ne. Duk abinda tayi haka nake hakura na barta na kyaleta don gudun zubar hawayenta. Alkawari nayi wa kaina cewa in dai ina raye Safna ba zata yi kukan wani abu a rayuwa ba. Ashe hakan da nayi ba shine so ba, ba shine gata ba, ba shine kuma zai futar dani wajen mutane da ita kanta Safnar ba. Don a yanzu haka dangi sun sakani a gaba da zagi da bakaken maganganu cewa ina sane na lalata rayuwar Safna na inganta na yarana. Na basu tarbiyya kuma na sama musu mazajen aure ita na barta tana gantali a kasar turai.

Farfadowar kimata da daraja ta shine auren ta da Mahmud yazo nema. Basu taba zaton zata samu miji musulmi mai addini dan babban gida irin Mahmud ba don haka kowa bakinsa ya rufu aka dinga sa albarka. Toh yanzu aji cewa Mahmud ya fasa auren Safna kuma ga dalilin da ya saka shi fasawar ina zan sa kaina? Ita kanta Safnar ba karamun tashin hankali zan fuskanta daga gare ta ba, don tun yanzu ta soma cewa wai ni ne na cuceta ban tsaya a kanta ta zama mace tagari ba irin su Farida.

Alaji ina cikin tsaka mai wuya! Ina cikin tashin hankali don Allah kai kun rai ka taimakeni.”

Daddy hawaye ne kawai baiyi wa Eng ba don tsananin tausayin sa da yaji. Da dai wata alfarma ce ba wannan ba, da ya yi masa. Dama ace alfarmar ta kudi ce ko kuma akan wani daga cikin yayansa ne ba Mahmud ba, da ya tursasa su sun auri Safna sun rufawa Eng asiri. Amma magana ake akan Mahmud! Wanda idan yana da iko ko kuda ba zai bari ya gifta ta gefen zuciyar sa ba balle bacin rai ko damuwa. Ya godewa Allah da ya riga ya nemarwa Mahmud auren Amina ba za’a fasa auren gabadaya ba.

Ajiyar zuciya ya sauke yace

“Eng. Naji matukar tausayin ka, na kuma yi maka jaje da faruwar wannan al’amari. Kuma tabbas ba don lalurar da take damun Mahmud ba da wallahi sai na tursashi na ya aure ta. Sai dai hakan ba zaiyu ba, saboda bama fatan wani abu wanda zai tashi hankalinsa ko ya sanya shi damuwa. Auren Safna kuwa abinda yake nufi kenan.

Kayi kuskure Eng tunda farko, soyayyar gaskiya da gata shine baiwa yaro cikakkiyar tarbiyya da wadataccen ilmi da koyar da shi yanda yanayin zamantakewar rayuwa rayuwa take. Toshe kunne ake ga duk wasu maganganu na mutane da yan’uwa. Ranar da  yaron ya zama wani abu, ranar da ya zama abun alfahari a cikin al’umma sai kaga ana ta yaba maka.”

Cikin jinjina kai Eng yace “hakane Alaji! Hakane wallahi! Nayi kuskuren da ba zai gyaru ba, nayi kuskure.”

Dakyar Daddy ya rarrashi Eng ya lallabashi ya tafi gidanshi cikin nadama da dana sani mara amfani.

Karfe takwas na dare Mami ta kammala musu dinner ta shirya komai akan katuwar daddumar tsakiyar falon bayan ta shimfida ledar cin abinci domin Daddy bai cika son cin abinci a table ba. Tuwon laushi ta mulluka musu tare da kunun shinkafa shikuma Mahmud ta yanka masa kayan marmari irin wadanda yake bukata domin bai dade sosai da cin abinci ba.

Suna ci suna mayar da magana akan Safna, Daddy na basu labarin halin da Eng ya shiga na ban tausayi. Mami kam murna ce ta ishe ta domin daman bata kaunar Mahmud da Safna don dai babu yanda zata yi ne tana son yayi auren shiyasa ta hakura. Amma sai ta kame bata nuna hakan akan fuskarta ba.

Bayan sun kammala ne Mahmud yayi gyaran murya ya sadda kansa kasa yace “Daddy akwai maganar da nake so muyi amma bansan ta inda zan fara ba, bansan kuma yanda zaka dauki maganar ba, sai dai ina fatan zaka bani amsar duk abubuwan da suka shige mun duhu Daddy ba tare da wani tunani ba kuma zaka yi  mun kyakykyawar  fahimta. “

Jikin Daddy ne yayi sanyi gabansa ya soma faduwa don yana tsoron kada Mahmud yace itama Aminar baya so ko kuma a daga bikin zuwa wani lokaci. Daurewa yayi ya hadiye fargabar sa yace

“Mahmud  ka gaya mun ko menene kai tsaye ba tare da kuskunda ba. Ni me fahimtar kane lokacin da kowa ya jahilceka, sannan kasa a ranka ba zan taba juya maka baya ba.”

Murmushi yayi mai kama da yake sannan ya sake saukar da kansa kasa ya tausasa murya cikin rauni yace

“DADDY MENENE TARIHINA? WANENE MAHAIFINA? WACECE MAHAIFIYATA? A INA KUKA DAUKONI? WANENE NI DON ALLAH? DADDY KAYI WA GIRMAN ALLAH DA MANZON ALLAH SAW KA WARWARE MUN WANNAN AL’AMARI MAI DAURE KAI”

TIKISA!!!

Toh fa masu karatu anzo wajen!

Did you smell this coming up?

A ina Mahmud ya jiyo wannan magana?

Wanene Mahmud?

Ina tunanin wannan shine gundarin labarin Hausa Arab! Ya kamata musan wanene HAUSA ARAB din shi kansa? Su wanene iyalan Dada?1

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page