DR HISHAAM CHAPTER A

 DR HISHAAM CHAPTER A

Bismillahirrahmani-rrahim

Chapter 1

HANAAN

A zaune take a babban falonta kayatacce da duk wanda ya gani zai zaci dakin matashiyar macece radio ta kunna take sauraro cikin nutsuwa akalla zata kai kimanin shekaru sittin da wani abu har zuwa saba’in ma garamm taji an buga kofar shigowa falon a firgice ta juya tare da kashe radion tata tana shigowa tayi cilli da jakar tare da sakin kuka cikin nuna kulawa ta matsa kusa da ita tare da dafata tace Hanaan me kuma ya faru cikin sheshshekar kuka ta fara magana ayya+

tace na’am yar ayya ina jinki waya tabaki ne ayya anya kuwa Baffa dankine kece kika haifeshi duka ta kai mata tace yarwofi kece kika haifeshi to ayya naga babu abinda ya hada halinki da nashi ke gaki da jajircewa ga son gaskiya ga kyautata wa amman shi wlh badan ke ba da bazan taba adarda komai ba ki duba kiga tun ina jaririya mahaifiyata ta rasu cikin matan sa aka rasa wadda zata rikeni bayan harda me shayarwa a cikinsu abarni ma a cikin gidan azaba ta hanani rayuwa kina gani sai dakyar kika karboni shima sai a boy’s quarter muka samu muka natsa kuma har yanzu masifar yau daban ta gobe daban to yanzun me ya kawo wannan maganar?

Cikin kuka tace wai daga na tsaya kwafar note shine suka sa ado ya gudu ya daukosu suka barni a makaranta kuma kinaga fa kullum inna shiga cikin gida saina jirasu kuma sainaje kowane part na gaida kowacce bayan bakaken maganganu da nake sha ga habaici da tsan iri iri karshe kullum sai na rasa period din farko to ba saiki godewa Allah ba tunda naga makarantar kudi ai ba’a dukan makara to ayya indai ka rasa karatu ai ka rasa kawai to naga Amal ita tana shiryawa da wuri ko?

ai daman anisa ce me matsala kuma kinga umma goyon bayanta take sai ta gama duk iya rashin mutuncin da zatayi sannan za’a kaimu to yanzun ya akai kika dawo gida?daman da ragowar kudin da kika bani to goge hawayenki daga yau insha Allah kin daina binsu ai daman saboda ku kara zumunci nake turaki can din yanzu ko tunda abin ba arziki kin daina zuwa bara buhari yazo daga yau ya dinga kaiki yana daukoki a adaidaita sahu na meye amfanin sa share hawayenki maza ki tashi kiyi mana girki nan da nan Hanaan ta hada rai ta turo baki haba ayya wai duk inda naje na dawo sai nayi girki ke baza kiyiba yar kundu so kike inyi miki aure baki iya komai ba irin yanuwanki daman gashi suna ce dake goyon kaka to ayya ba goyon kakar bace ni?

Eh amma ai kinfi wanda ba goyon kakar bako? to ayy…..kinga malama ina cikin girkina a rasho dina kikasa ubanki ya siyo min wannan abar gas din ko kusa da ita ban san zuwa tayaya kike saka ran inyi girki da ita ai daman kanki kika hada da wahala kawai.

Hanaan ta tashi ta cire uniform dinta ta shiga kitchen bayan ta dora girki ta fito ta fara yi musu wanki a injin wanki komai nasu tsaf tsaf tana jin zafin yadd mahaifinta yake ko inkula da ita amma tana jin dadin yadda yakejin maganar ayyanta saboda duk abinda suke so yana siyo musu musamman ma in ayya ta fada masa da kanta.

HISHAAM

Bismillah ta fada tareda zama akan daya daga cikin kujerun falon na alfarma jaridar daily trust take karantawa lemon dake gefenta ta kurba kadan da sauri kamar ta tuna wani abu ta kirata da karfi ni’ima na’am ta amsa can kasa baza kizo bane?

mom ina zuwa cikin shagwaba ta fito mom gani me nace kiyi?iye me nace kiyi ba dakin Hishaam na turaki leken asiriba ko saiyi dawo ya gane me za’ayi tukunna wallahi mom ke kike daurewa yaya gindi gaskiyar Abba haba ke baza ki iya yi masa fadaba saidai ni kullum a leken asiri saikace munafuka zakije koko a’a?

Tafiya tayi tana zumbura baki can cikin abinda befi minti goma ba ta dawo da kwalin taba a hannun ta cikin washe baki hajiya Luba take fadin shi kadai kika samo?ba syrup kenan ya daina komai sai taba ko?au mom ita tabar abar kirki ce yimin shiru salon sai ubanki ya dawo yaji me ake ciki ko…..me ake boyemin kamar daga sama sukaji shigowar sa ba komai inji haj. Luba inda ni’ima tayi saurin boye kwalin abayanta cikin hanzari ya mika mata hannu ba musu ta miko tana Sosa keya inda mom ke galla mata harara.

STORY CONTINUES BELOW

Cikin tsananin bacin rai yace yanzu shekaru ashirin da takwas ta yiwa mutum kadan yayi hankali wallahi duk kece kika bata yaronnan kinfini zama dashi asati sau uku kike fita amma kin kasa sakashi a hanya to zangaya masa koya bari ko kuma zanyi reporting dinsa don bazai ringa wasa da rayuwar mutane ba

Amatsayinsa na likita in yaso in suka kwace license din saiya dawo gida ku zauna ki sake masa sabon so haba alh Dan……babu abinda zakice shi kuma zai dawo ya sameni fuu ya haye sama ya barsu anan.

Tunda ya shigo falon ya gane akwai abinda ya faru hi mom kawai yace ko kallon ni’ima baiyiba ya wuce dakin sa ya gaji sosai kasancewar yau sun sami emergencies da yawa wanka kawai yayi ni’ima ta sanar dashi Abba na kira ko ba’a fadaba yasan be wuce fadaba tunda kullum tsakaninsu kenan fada cikin hanzari ya gama ya wuce sashen abban a zaune yake yana jiransa kamar yadda yayi tsammani fadane hakan kuwa akai bayan ya gama masa fadan tas ya dubeshi cikin takaicin ko kare kansa ya kasa yace me kuma kake jira

yadan muskuta Abba dama game da sakon dana bawa mom ne ta fada maka, eh ta fadamin amman sai nayi shawara amma Abba…

kaga ya katseshi ta hanyar daga masa hannu kaje kawai sai nayi shawara nace cikin yanayin damuwa yace na barka lafiya ya fice da sauri

A zaune yake a office kira ya shigo wayarsa cikin hanzari ya daga tareda sallama bayan sun gaisa yace inba damuwa inason ganinka yanzun to ba matsala zan jiraka sai ka zo. Cikin abinda baifi minti goma ba sai gashi bayan sun gaisa cikin shakuwa da girmamawa da kowa kewa dan uwansa

alh Umar ya fara magana wato alh na rasa yadda zan bullowa al’amuran yaronnan Hishaam idan an hanashi sata saiya koma sane kaga da syrup yakesha duk irin kwakwalwar da Allah ya bashi sai ya fara samun matsala daga baya dana dage Allah ya shiryeshi to har yanzu yaki rabuwa da taba gashi yanzun kullum sai ya Aiko min mahaifayar sa akan yanaso ya koma gidansa da zama saboda ya gaji da zama damu nikuma ina tsoron karya bar gabana kuma ya hada harda neman mata

alh ridhwan yayi shiru nadan lokaci can ya nisa yace to alh mezai hana kayi masa aure nan da nan fara’a ta bayyana a fuskar alh Umar yace kaga kumafa hakane in yaso sai matarsa ta sa masa ido ta kula dashi amma wannan shawarar tayi to in hakane mezai hana a hadashi da yar’uwarsa Hanaan alh ridhwan yayi shiru cikin nazari can ya nisa yace alh ban tari hanzarinka ba amma yarinyar nan sai wasu watanni gaba zatayi shekaru sha shida akwai tarin wauta a tare da ita kuma bugu da kari gata miskila kamar shi Hishaam din kaga a aure kuwa anaso a saba halaye

kuma gashi ayya bazata amince ta aurar da ita yanzu ba kuma duk ba anan takeba abinda zaifi shine ka tambayi shi Hishaam din idan babu wadda yakeso inyaso ai Maryam ta gama karatunta sai a hadasu ko kuwa alh Umar ya nisa yace to tunda ka kawo wannan hanzarin za’a gwada insha Allah akan haka sukayi sallama Abba yana ta juya zancen cikin ransa.

Wato alh Umar shi kadai ne da gurin iyayensa sai bayan sun manyanta Allah ya basu y”a mace asalin fararen kasar niger ne masu asalin kyau da kwarjini musamman ma kanwarsa Hindu bayan mahaifinsu ya rasu wani attajirin dan Nigeria cikin Abuja ya aureta inda ta taho dasu baki daya anan Hindu ta gama kara tunta tareda amina babbar yar yayanta alh Umar kasancewar akwai rata me yawa a tsakaninsu taso zama gidan yayanta amma rashin jituwa tsakaninta da haj Luba ya hana bayan rasuwar mahaifayar su a dole ta koma gidan yayanta suna rayuwar su da amina da karamin yaronsu alokacin Hishaam.

Ba dadewa samari suka sakosu agaba musamman ma ita Hindu da zaka zata balarabiya ce ko India daga karshe aminin sa mai kamar dan uwansa alh ridhwan ya nuna ya dade yana dakon sonta bayan ta amince alh Umar ya turza saboda yasan rigimar matansa haj Bilki da Aisha musamman ma Aisha datake kan rigimar ta ganin itace karama daga baya dai dakyar ya amince

da alkawarin kar yaji kar ya gani lokaci daya aka aurar dasu ita da amina kuma kusan lokaci daya suka haifi yayan su duk yanmata ta amina aka saka mata zainab ta Hindu kuwa Hanaan ba dadewa ta fara rashin lafiya inda saboda tsananin tsangwama aka rasa me jinya sai dai shi alh ridhwan dayasan muhimmancinta saboda a aurensa da Hindu ne ya gane yayi aure sai da abin yaki ne mahaifayar sa ta dawo gari da zama take kula da ita da jaririyar har Allah yayi mata rasuwa lokacin haj Luba ta haifi ni’ima ba dadewa inda Aisha itama ta haifi twins amma aka rasa me shayar da Hanaan

STORY CONTINUES BELOW

Abba ne ya hana haj Luba ta shayar da Hanaan saboda yana sa ran hada zuria da ita daman haj Luba bataso tunda daman can kishi take da Hindu saboda son da danuwnta yake mata bayan alh ridhwan ya aureta kuma sai suka hade mata kai da su haj Bilki tunda daman kawayenta ne.

Ayya taso komawa inda take saboda gudun rigingimun gidan dannata amma ganin irin halin da Hanaan zata iya shiga yasa ta fasa inda aka gyara mata boys quarter ta tare acan da yar jikarta alh Umar yayi naci abashi Hanaan har ya gaji ayya ta hana saboda sanin halin matarsa inda shikuma hakan be hanashi sai mata komai da yake saiwa ni’ima ba inda ni’ima ta taso tana kishi da Hanaan din itama kaf a dangi anti Amina da yarta zainab su kadai Hanaan ke jin dadinsu suma sai in sun hadu a taro danba inda suke zuwa bafffansu yasa an koya musu mota amma yayan gidan ne kadai ke fita da motocin gidan.

Haj Bilki yayanta hudu duk mata ne sunyi aure ya hadiza itace babba sai ya naja sai ya furera me sunan ayya sai karamarsu ya fiddausi bazaka taba cewa haj babbace ta haifesu ba saboda irin halin baffa ne dasu in banda ya hadiza ita kuma bakin halinta har yafi na mahaifayar ta.

Haj Aisha yayanta hudu itama ya ma’aruf shine babba sai ya maryam sai anisa da Amal twin sisters dina haj Aisha taso ta bata ya ma’aruf amma sam Allah baiyiba sai abin ya kare akan ya maryam da anisa.

Hishaam

Azaune yake yana busa tabarsa cikin jin dadin abinda yakeyi aminin sa Idris yana gefe yana karkada kafa yace Kai mutumina kana likita amma kana shan taba abin yana ban mamaki it’s injurious to your health fa, Hishaam ya kalleshi ta gefen ido yace to yanzun da shan taba da neman mata wanne yafi Idris yayi dariya da gefen bakinsa yace ba gwara… karya kake Hishaam ya katseshi ai kai kawai sai addu’a taba cutarda kaine zina kuma cutar da al’ummah ne gabadaya kuma sab’awa Allah ne yanzun tundazu nake kallon ka kayi nisa a tunani kuma nasan bazai wuce tunanin mace kake ba.” kai wallahi ina mamakin yanda ka gama sanina Hishaam kamar kasan tunanin wata yarinya nake jiya sanda ka kirani nace umma ta aikeni ai aikena tayi in dauko hauwa a makaranta ina zuwa na tarar suna ta cacar baki da wata yarinya sam bangane me sukeba saboda hankalina ya tafi akan bala’in kyaun yarinyar nan kasan bansan na kama mata hannu ba sai marin data shararamin ne ya dawo dani hankalina”

Kai amma dai ka bada maza babu wani mutunci a bariki gara ka daina yanzu gashi yarinya karama sa’ar qaramar qanwarka ta mareka a banza, “ai bakama san sharrin ba wallahi gashi fuskata ta mara amma straight marin cikin zuciyata ya shige saboda har yanzu ita kawai nake gani gashi danayiwa hauwa maganar ta tace wai duk mazan makarantar kowa ita yake hari amma bata kula kowa” Hishaam yayi murmushi wato dai abokina if am not mistaken taci bulus kenan ko?

To ya zanyi sanda zan rama bana hayyacina da wallahi ko dan in kara tab’ata sai na rama. Wato Idris kana ban mamaki kana darajta  kyau ni kuma nafi darajta hali. “Eh babu mamaki saboda ai kai kana dashi mufa?”Sam ba haka bane kawai ni nafison kamilar mace kamar shukra dariya Idris ya barke da ita Hishaam ya dan hada rai sai kuma yace sorry na shukra Hishaam ya mike tareda aje kan tabarsa akan ash tray yana fadin inada round up sai mun hadu anjima har yakai bakin kofa Idris yace” kasan kuna kama mutumina”  dawa Kenan?da ita wannan yarinyar me kyau mahaukaci kace kwakwalwar ka ta mara kafin zucitarka ya fice yana mamakin irin halin Idris din.

Chapter 2

Hishaam

A gajiye ya dawo gida ko parking ma direban mom ya bawa key din yayi ciki hanzari yake tafiya ya kagu yadan watsa ruwa sama ya haye ya doshi dakinnasa tilo dayake jin haushi cikin rashin sa’a daidai lokacin Abba ya turo kofar falonsa Hishaam ya kira na’am Abba inason ganinka yanzun to yace jakar sa kawai yakai daki da Labcoat dinsa ya fito yana shiga ya taradda Abban azaune fuskar nan ba yabo ba fallasa cikin dari-dari ya zauna nesa kadan yace gani.

Cikin kasaita ya fara magana mamanka ta sanar dani bukatarka ta son tashi daga gidannan to iname farin cikin sanar dakai cewa na amince da bukatarka washe baki yayi hade da shafa kwantacciyar sumarsa da tagaji da gyara da cin kudi yace Abba godiya nake…. a’a ai ba’a zo nan ba tukun domin inada sharadi dum gabansa ya fadi Abba me..ye..sharadin? sharadi na kuwa shine sai kayi aure sai ka tashi ai daman shekarun ka sunkai kuma ina son ka nemi daya daga cikin yayan baffa ridhwan ka aura yawun bakinsa ne ya kafe a lokaci guda tare da mummunan sarawar Kai nan da nan yafara jin amai dawata irin tsana tana taso masa abban ne ya katse masa tunani banji kace komaiba.

STORY CONTINUES BELOW

Abba i hate to say this but Abba please banason ko d’aya “ko zan iya sanin dalilin ka?”  Abba kasanfa yaransa gaba dayansu basuda tarbiyya ko ka’dan ko yayan haj babba kafin suyi aure har club suke zuwa saboda gidansa yafi karfinsa Abba ridhwan kuma har gwara nada akan na yanzun, tsawa ya daka masa dakata da Allah karka gayan maganar banza mara tushe da makoma kaid’in tarbiyya kafisu kuma ma yaushe kake zuwa gidan ballantana kasan abinda suke ciki ko babu komai su an isa dasu tunda suna zuwa su gaishemu kaifa?ko da wasa ban yarda ka k’ara aibata yay’an d’an’uwana ba Abba ban fada don inbata rankaba amma……amma me?amma abba wallahi babu wadda zan iya aura acikin su.

Akwai watane daban? zuciyarsa yaji ta fara dena yajin da takeyi masa muskutawa yayi ganin anzo bangaren dayake so yace eh Abba akwaita to waccece kuma y’argidan waye da har ta fimaka yanuwanka Abba sunanta shukra yar gidan alh babayo tsohon kwamishinan kudi tare muka fara aiki da ita kuma har yanzun tare muke aiki babu abinda ban saniba na daga kyawawan dabi’unta ya isa haka kana nufin wata yarinya da nake ganinka tare da ita anan asibitin kenan ko?

Abba…… dakata me kake kokwanto bari in warware maka ai anfadamin ka fara yawo da mata don haka kullum sai na je gurin aikinka  duk abinda kuke ciki na sani wannan yarinyar batada kunya kuma sannan tayi sa’arka ina zaka kaita ni danake son ka auri matar da zata sa maka idanu ta kula da gidanka banga wadannan qualities din agurin wannan yarinyar ba. Wallahi Abba tana da kunya ga da’a tafi duk wad’anda kakeson hadani dasu okay to yanzun nagane me kake nufi Hishaam tunda anyi haka zanyi bincike akanta idan na sami akasin abinda ka gayamin akanta alkawari ya warware ka amince?eh Abba kuma idan alkawari ya warware dole abi zabina ka yarda eh Abba na amince ya fada da sauri tareda dan sosa gefen wuyansa to tashi kaje kabani sati biyu to Abba nagode.

Bayan ya koma daki ya dauko wayarsa inda ya tarar da missed calls dinta nan ya shiga danna kira tare da gaya mata labari me dadi na nema masa auranta dafatan dai babu wata matsala ko?babu wata matsala inji shukra sanin kanka ne Hishaam banida waninka a zuciyata nan suka cigaba da hirar su me cike da shauki da soyayya me yawa saika zata sunyi shekara basu haduba musamman ma shi yanda yake ganin dagakan shukra mata nagari sun kare.

Yau alh Umar dakansa ya tafi gidan alh ridhwan saboda a matse yake da ganinsa bangaren ayya ya fara tsayawa ya gaidata kamar kullum inda Hanaan ta gaidashi cikin da’a da ladabi shikam yana tsananin son yar yar’uwarsa ga yarinyar me hankali gashi ta fita daban da sauran yaran gidan

amma be saniba kodan son dayake matane da mahaifayar ta oho? ayya ce ta katse masa tunani da cewa jiya amina tazo da zainab da sauran yaran ai ita akwai zumunci ba irin Hishaam ba d’an kundu na manta rabon da in sashi a idonnan nawa oh insha Allah zan turoshi ya gaidake yauma kamar kullum yayi musu sayyaya fal ya ajiye musu yace to ayya zan shiga cikin gidan to a fito lafiya.

Bayan sungama cin abincin dare a falonsa alh Umar ya fara magana da cewa to danuwana kaji yadda mukai da danka Hishaam

to a gaskiya yarinyar nan nayi bincike akanta bangano wani mugun abuba illa dai ance tanada samari da yawa wannan kuma ina ganin awajen mace ba wata matsala bace mai wuyar sha’ani illa dai wallahi bazan boye maka ba yarinyar bata kwanta minba to yanzu babu abinda yafi sai muyi addu’a Allah yasa hakan yafi alkhairi to amin dan’uwa yanzu zan sanar dashi abinda na yanke in yaso saiku sa ranar da zakuje maganar auren ko? to abu yayi kyau alh Allah ya sa a dace Amin.

Chapter 3

Hishaam

Gaba daya rayuwa ta canja komai cikin nishadi da annushuwa yakeyin sa saboda tabbacin soyayyar su da shukra gamida yaqinin babu matsalar da zata faru.

Yau weekend ne kowa yana gida a dakinsa yake sam baya cikin nutsuwa saboda rabon sa da shukra tun alhamis ga wayarta a kashe ya kira har ya gaji inda ya yanke shawarar ya tafi gidansu kawai key ya zara ya mike cikin hanzari tun kafin ya sauko ya fara jin bambamin fad’an Abba gabansa ne ya fara faduwa ahankali yake saukowa kamar me sand’a here he is inji Abba.

STORY CONTINUES BELOW

Hishaam na’am Abba “nine na haifeka ko Kuma kana da wani uban bayanni? a’a Abba kaine….,to indai nine na haifeka babu kai babu zuri’ar gidan alh babayo dummm! naji kaina yayi nan da nan naji zuciyata tana zafi har zuwa yaushe?harzuwa yaushe zankai anamin katsalandan acikin harkokin rayuwa ta…? Abba yacigaba banda wulakanci sai bayan ya shanya mutane kusan one hour sannan yazo ya karewa zuri’ar mu cin mutnci kamar ni Umar ake tuhumar irin tarbiyyar dana baka, ai ga irin tanan ka gama cewa yanuwanka basuda tarbiyya kaima yau kasami wanda ya raina taka tarbiyyar ya kiraka da Playboy to indai na isa dakai kuma nine ubanka babu kai babu ita kuma ina fatan kana sane da alkawarin da mukayi?

Abba wane alkawari kuma? zancen auren ka da daya daga cikin yanuwanka mana Abba please…… shut up aure babu fashi “to Abba na fasa auren gaba daya abb…..” fuu ya wuce ya basu guri haj Luba da tunda ya fara bambamin tayi quri sai a lokacin ta dubi Hishaam cikin tsananin tausayinsa ta matso ta dafashi cikin rarrashi ta fara bashi baki Hishaam kayi hakuri kaj……, “haba mom for how long? for how long akeson in rayu a haka,?iye laifinane? eye nace laifinane saboda kina tsananin sona kamar yadda yake fada meye laifina aciki da Abba zai dauramin zani da tsanani haka me nakeyi a gidannan nayi karatu for him mom ina aiki for him na dogara da kaina for him mom just….. for him then what do you people want from me? huh… “Hishaam calm down please son”  no mom not anymore a gaskiya ki sami mijinki kiyi masa bayani bazan iya yadda yake soba this time around so ya janye maganar nan.

Yaya kayi hakuri mana jiba yadda jijiyoyin kanka ke tashi ni’ima keson kwantar masa da hankali da hanzari ya wucesu zuwa dakinsa saboda ji yake inya cigaba da tsaiwa anan zai iya zubewa.

Adakinsa ya wuni sur abinci yadda aka hau haka ake saukowa dashi inda hakurin mom ya kare kofar dakinsa taje ta tsaya buga kofar take amma kamar babu kowa a dakin spare key ni’ima ta kawo koda ta shiga yana bakin gado yasha taba ya koshi ta dubi ash tray din daya tara ragowar tabar tace Hishaam kasan maganar nan babu wanda ya isa ya canza ta meye na bacin ran haka akan abinda bakada mafita saidai addua kawai.

Jajayen idanuwansa ya dago ya dubeta dasu yace mom kina sona kamar yadda ake fada? Har saika tambaya? to inhar kinasona ya kamata ki tserar dani daga shiga wuta dan wallahi in nayi aurennan saina shiga wuta dan bazan taba zama da abinda banaso ba. To naji ka kwantar da hankalinka zan jarraba haka taita rarrashin dan lelen nata har zuwa wani lokaci.

Hanaan

Yau da wuri aka tasomu daga makaranta kasancewar mun fara CA test har na dora girki na haye kan sink kamar yadda nake wasu lokutan ludayi ne a hannu na nayi nisa duniyar tunanin irin tarin maqiyana ko sai yaushe zan sami masoyi oho? ayya ce ta katsemin tunani yar ayya me kike tunani haka ko tunanin aure kike? har kunnena saida yayi ja sabida kunyar datasa naji “haba ayya haka kawai zaki wani tsiro da zancen aure?” eh mana, yanzu gayamin irin mijin da kike son ki aura .

Nidai irinki nakeso ba sawa ba fitarwa ba kyara ba tsangwama sai tsabar so da kauna yar kare kice da namijice ni sai kawai ayi ko? ta dungureni tana dariya nikuwa Hanaan kinsan irin mijin dana keso ki aura nace a’a cikin sonjin me zatace tace wanda zaice a wankeki tas akaimasa yayimiki komai nan da nan fara’a ta ta dauke nace yanda innayi masa laifi zaice fita a yadda kikazo ko?duka ta kawomin na kauce gashin kaina taja nadanyi kara tace yar kundu daga fara zancen aure ta fara zancen saki ayya ai gaskiya ne to Allah ya kyauta komai saina kaiki dashi kinji y”a dirowa nayi na rungumeta muna dariya tace yarjakar uba.

Yau da safe ina gab da tafiya makaranta baffa ya shigo na gaisheshi yace anfito nace eh yace to Allah bada sa’a sam babu wata kwakwkwarar shakuwa tsakanina dashi inya dade a guri sai inrasa me zance masa ina fitowa na tarar buhari na jirana harda Amal a gurguje ta shiga ta gaida ayya muka wuce makaranta.

A kwance nake da ear phones a kunne na ayya ta cire tace shiyasa sai aita magana bakyaji kin toshe kunnen da wannan abin banzar, menene Kuma ayya? zancen auren yar’uwarki ne ya taso Maryam da danuwanki wane d’an uwannawa? Hishaam mana to Allah Sanya alheri amin abinda baffanki yazo ya fadamin kenan dazun da kuka tafi makaranta jibima zasuzo ya qara ganinta. Da wuri akeson yin abin, to Allah sa dai dan Allah za’ai ayya tace jibin anason ku had’u acikin gidan baki daya nace su had’u dai ni mezai kaini?.

Zancen wofi kenan ai inkinga baki jeba to jibi batayiba kawai na zumb’ura baki na juya na cigaba da sabgata ayya tace eh ko bakinki zai fad’o saikinje ehen.

Hishaam

Sam wata aba walwala ya daina yinta musamman ma daya tabbatar da abinda ya faru daga bakin shukra dad’i d’aya yaji daya fahimci ta fishi damuwa sosai don yanzun duk lokacin da suka hadu sai tayi kuka gashi amincin su da hadiza yana neman ya samu matsala don tana ganin harda hadizan aka hada kai akeson abawa Hishaam d’in qanwarta Maryam ya aura. Hishaam d’in ke kwantar mata da hankali da alqawarin komai jimawa zasuyi aurensu donshi ita kadai ce mace a idonsa shukra tana jin dad’in yadda Hishaam ke nuna mata k’auna ta zahiri musamman ma yanzu abin kamar gaba yakeyi.

Kamar kullum yauma yana zaune yana tunanin yadda akayi baban shukra ya tsaneshi haka Idris ne ya katse masa tunani da cewa wai mutumina zancen auren nakanedai har yanzu?, dan iska to yaushe ma aka fara ballantana a gama? Idris yace ai da nine da tuni an wuce gurin “da gaske? Idris yace kwarai kuwa to dayaya?

Idris ya matso da kujerar sa yace kai bakada dabara ba’a ja da iyaye musamman ma irin mahaifinka in ya saki hannun ka bakada wani gata a garinnan sanin kanka ne wannan aikinnaka babu abinda kake samu dashi in kayi la’akari da dukiya irin ta mahaifinka, me kake son kace?

Yawwa badai sunan auren akeson ajiba ace maka me aure to shikenan kayi auren sanin kanka ne wannan auren shine mabud’in duk wani y’anci a rayuwarka don haka kadena gaba dashi. Da zarar ka aureta sai tagane baka sonta amma kafin nan ina da tambaya wane irin aure zakayi miji da daddare makiyi da safe? ko

Kuma……

mtsss Allah ya kiyaye ai kai kasan ba irin halinmu d’aya dakaiba in inayi to inayi amma idan banayi to akai kasuwa sam babu ruwana da ita kuma kasan yadda tsarin rayuwata yake babu mata biyu acikinta da mace d’aya tak zanzauna arayuwata kuma ba wata bace illa shukra.

Yauwa to yanzun aikinka zaiyi kyau idan akayi auren ita da kanta zata cewa iyayenka ka saketa, to amma in tafad’i abinda nake mata fa?ya za’ai ta fa’da? ai tun farko zurmata zakayi kace duk abinda takeso shi zatayi kada aurenka ya hanata yin komai

in tazo kuma ayi wata harka kace kaifa daman ba lafiyayye bane ai wallahi a matan yanzu wata shidama ya mata yawa. Shawara ta karshe karka sake nuna qin aurennan saboda gaba duk abinda tace ka mata abban da kansa zaice aikuwa wane be nuna qin aurennan sosai ba kuma abinda mutane dayawa basa ganewa shine idanfa kayi musu biyayya akan abinda suke so wallahi koda niyyarka ba me kyau bace wlh sai Allah yasa alheri mai girma a rayuwarka kuma kogaba saika godemin akan shawarar nan dana baka Hishaam ya miko masa hannu yace shegge saikace mutumin kirki suka tafa yace dukme shawara aikinsa baya baci Hishaam yace eh amma kuma ai asirinsa baya rufuwa ko?

A lokacin dana koma gida dare yayi sai kawai na gama abinda zanyi na kwanta inajiran safiya tayi.

Sassafe naji ni’ima tana bugamin kofa yaya yaya yay….. alarm clock din gafen gadon na wurgo ya daki kofar inajin ajiyar zuciyarta nace grow up har yanzun bakisan yanda ake tashin mutane ba ko? Mom ce zata fita takeson ganin ka kice ina zuwa yaya fa….. Get lost.

Sai bayan nayi wanka na shirya tsaf  na dauko kayana da lab coat dina na fito a dining na tarar dasu amma mom harta fita anan na sanar dashi amincewa ta yayi farincikin dana manta rabon da naga yayi irin sa bansan yadda akayiba sai naji hakan yamin dadi harzan fita ya sanar dani cewar komai shizeyi banida bukatar yin komai tun kafin na fita naji yana waya da mom yana bata labari bayan naje wajen aiki mom ta kira tanata wani lallabani

uwa Kenan tafasan banaso amma saboda Abba…. kanajina ta katsemin tunani eh nace da kinamin rabin son dakikewa mijinki da na sami rangwame a abubuwa da dama to Allah yayi maka albarka Amin nace.Chapter 4

Hanaan

Yaune ranar da’aka shiya za’a zo ganin ya Maryam sam na manta saboda banason saka kaina a abinda zai dameni daman kuma asabar ce muna dawowa daga islamiyya nida Amal daman mu kadai ke zuwa sai ya ma’aruf Amal tace yaunefa

Me kenan? Na tambaya sa ranar ya maryam mana to Allah Sanya alheri na fada tareda d’an tabe baki meye kuma na tab’e baki haka Hanaan?

To ai abinda babu ruwanka dad’in jine dashi ya zakice babu ruwanki? to inbanda ke waye yasan da existence dina a gidannan? saiko ya ma’aruf shima sairanda ya tuna. muna gabda rabuwa nace kyamusu Allah Sanya alheri don gaskiya ba lallai ne inshigo ba+

Ba matsala bayan munyi sallama na shigo yau ankawowa ayya tarin snacks da wasu abubuwan da dama bayan na idar da sallar azahar bansamu ma naci komi ba bacci yayi awon gaba dani kiran sallar la’asar ne yasa na farka kamar daga sama naji sallamar ya hadiza gabana ya yanke ya fad’i har ga Allah jinina behadu dana ya hadiza ba saboda ina iya ganin tsanata qarara a idanunta

Bayan ta gaida ayya ta dubeni a wulaqance na gaidata ta amsa dakyar ta juya gurin ayya tace wannan kalaluwai-kasoqai din bazata cikin gidan bane?ayya tace zata mana saisunzo tukun, sai sunzo ko saisun tafi? ai har Hishaam din duk sun hallara ayya ta dubeni tace maza tashi ki shirya kije.

Wanka nayi kayan da Abba Umar ya kawomin daga wata tafiya dayayi su na dauko nasa riga da skirt ne farare masu jajayen duwatsu da wata irin jar kwalliya ajikinsu

Jan mayafi siriri na yane gashin kaina dashi banda sajen daya kwanta agaban da bazaka ce akwai wani gashi ba lip balm nad’an saka sai kwalli a dara daran idanuwana dan siririn agogo na manna a farar fatata cikin nutsuwa na fito ayya ta kalleni tace ahaka zaki tafi babu yarhoda kai ayya na turo baki tace koma ki sa kinji’yarkirki kadan nadan shafa don banson hayaniya da yawa a fuskata

Turaren romancia me sanyin kanshi na fesa a hankali nake tafiyar gakuma faduwar gaba saboda bansanme zan tarar ba tun a harabar gidan na fara jin hayaniya da alamun gidan a cike yake a hankali na shiga

Kafatace ta fara rawa saboda kallo da yayi yawa dana tuna abinda suke so kenan kawai saina wawwaro idona nima ina kallon kowa ‘dai’dai

Hajiya babba na fara gaisarwa ba yabo ba fallasa ta amsa sai umman su Amal dakyar ta amsa daman ita dani take kishi tunda ba mahaifiyata anisa ce ta kalleni a banzace tace sai yanzun?ana abu agida dondai komai sai an nuna hali

Eh ai ba invitation aka baniba bare ace na sab’a lokaci Amal dake gefe tace kinyi kyau my sister nad’an rungumeta harga Allah inason Amal saboda yadda take tsananin kaunata babu ruwanta da ‘yanubanci Sam

Mayafina akaja ta baya na saketa na juya da sauri surprise! zee yaushe kikazo?ina ya aminan?

tananan tare muka zo tund’azu rungumeni tayi nima na rungumeta saboda ita da Amal shiyasa qawaye basu dameni ba.

Mun gaggaisa da mutane da dama dukdadai yawancin gaisuwar bata kai zuciba saidai dangin uba kawai

Can na hangi ya Maryam Tasha ado kamar amarya gabanane ya yanke ya fadi karon farko da muka ha’da ido dashi nadan dauke kaina daga gurinsu amma abin mamaki har yanzun ni yake kallo haka kawai naji inason qara kallonsa ya canza yayi wani bala’in kyau

Sam a maza irinsu basuda yawa kyansa ya dire habarsa ta loba ka’dan irin tawa tabbas muna kama kamar yadda ake fad’a ammafa yaso yafini kyau sai wani had’arai yake nima saina had’e raina kallon ya Maryam nayi sam bata dace dashiba sabida tana sahun farko na munanan gidanmu gata fara amma batada kyau intai dariya saita kara muni har gara ma tayi kuka gashi yau ta dage sai faman fara’a take

Shadda ce tsadaddiyar gaske a jikinsa riga da wando da hula kana iya ganin mur’dadden jikinsa acikin kayansa gashinnan ya gaji da kyau da gyara sai kyalli yake ga wata kwantacciyar ‘kasumba data dace da farar fuskarsa fatarsa har kyalli take kamar baya komai a rayuwarsa ya Maryam na kalla na sake kallon sa nace a raina gaskiya wannan had’in wai Tom and Jerry kawai sai naji dariya ta kamani

Ina d’aga kai muka sake ha’da ido dashi murmushin shakiyanci nayi na juya zan fita kenan….. ke

Naji ya Maryam tace kamar banjita ba nawuce ke Hanaan bakiji ina kiranki bane? juyawa nayi ahankali na nufi inda suke ina zuwa na had’e raina saboda nasan halin wulakancin ta saita dizgaka agaban koma waye na had’e hannayena guri daya

Bakiji ina kiranki bane? naji, kawai dai ban zaci dani kike ba saboda naji kince ke amma koda kika kira sunana aikinga nazo na karasa maganar da sauri “kece bazaki zo ki gaisheshiba?”  ina wuni a kyankyame ya amsa lafiya raina naji yana wani masifar d’aci nace araina gidan kazo tace baki sanshiba ko? “ba BOY bane?” da sauri ya d’ago kai muka ha’da idanu na kafeshi da idanuwana

Ke ba haka sunan sa yakeba sunansa Hishaam. Eh nasani amma ai anacemasa boy, wai haka? kamar bazai bata amsaba yace eh amma ya akai a shekarun ta tasan wannan sunan? Maryam tace ya akayi kika san wannan sunan? nace kinsan blood is thicker than water murmushi naga yanayi alamun maganar ta masa da’di amman bayaso agani nace Allah sanya alkhairi zanje inyi karatu.

Na dade da lura da wani a kusa dashi tundana shigo na lura wani yana masa rad’a

Sam na manta kamar ance juyo sai karaf muka ha’da ido dashi mutumin danafi tsana da kowa a rayuwata namiji na farko dana sake ya ta’ba fatar jikina ba muharramina ba nan da nan naji na fara jin zafi sabida takaici kowa na gurin saidaya gane

Yanamin magana me yake cewa oho.

A hasale na fita nabar gurin ina shiga ayya ta biyoni da sauri ya akayine Hanaan ayya wan hauwa nagani anan wanda ya rikemin hannu rannan bari inje yasha kulki dan ubansa ubanme yazoyi nan gidan ayya abokin ya Hishaam ne fa anya kuwa Hishaam dinnan mutumin arzikine?duka ta d’a kamin a cinya nayi tsalle nace kai ayya eh nadakeki ‘yar’kundu da ubansa da uwarki cikinsu daya to ayya ko uwarmu daya ubanmu daya in halinsa mara kyaune ya za’ai?

Halinsa me kyaune yana karami bansan yadda akayiba ya zama wani iri ato nidai nasan ba yadda zaai mutumin kirki yay abota da mutumin banza

Ya ganeki Hishaam din? wlh bansan masaba nidai na ganeshi ba shikenan ba shi idrisun me ya hadaki dashi? kanwarsace bata note nabata aron note dina ta b’atarmin ina cikin mata magana ta nemi ta zageni nikuma na caba mata magana nima shikuma yazo d’aukanta ni wallahi data kirashi jinake hakuri zai bani kawai naji ya faramin masifa shima kuma kin hanani yiwa babba rashin kunya sai kawai na juya zan bashi guri kenan kawai sai jinayi ya rikemin hannu bansnma na maresaba saidaga baya.

Ai kinmin daidai wallahi da baki maresaba da dakaina zanje har gidansu in casashi kallon ta nayi tanata faman fada na kyalkyale da dariya nace wai harnaga ayya taje neman fada kamar iyawa zatayi

Nace ai ayya mutanen yanzu basu dauki rike hannu amatsayin wani haramba ko wani abu to kedai na gayamiki duk ranarda wani ya rikeki da yardarki to mutuwa zakiyi bansan sanda dariya ta kufcemin ba nace c’mon ayya wannan zamaninfa ya wuce tunyaushe aka dena yayin wannan kisamo wani mana ta cigaba da zancenta muna ta shan dariya

Hishaam

Dakyar mom tasa muka fito daga gida karfe biyu da rabi wai karmu makara a gidan baffa ridhwan karfe uku tayi mana aka shiga abinda ya kawomu an saka rana wata biyu yan gidan sukazo aka kafa dandalin hira nikuwa bana saka musu baki donni natsani raini arayuwata

Idris ne ya tabani da sauri amma kodana kalleshi hankalinsa baya jikinsa inda yake kallo nima na kalla wata yarinya yake kallo shekarunta basu wuce na ni’ima ba kamar nasan fuskar……kai anti Hindu….. Ha….n..aan eh hakane Hanan itace ta girma haka? ta shigo da wani dan mayafi sai kallon banza takewa mutane araina nace kyan d’an maciji kenan

Dan iska ina cewa kuna kama kana rainani ashema kanwarkace

Eh saime kuma ah saikaimin hanya abani ita kawai dan wannan ta aurece wlh wanke hannu ka ta’ba dan kuwa kasan neman kai ake dasuba amman ita wannan kakar bazata bakaba saikasa baki wlh ko hanci zansk….kafin ayi haka ya buya

Waikai meye matslarka wlh Hishaam bazaka ganebane kaga tana kallon ka to saime? yarinyar da batada kunya bakaga irin kallon datakewa mutane bane?

SHUKRA

Babu abinda ya canza tsakanina da Hishaam saima tashen sona dayake karawa mun gama break kenan na koma bakin aikina ina shiga office na tarar tana jirana a’a saukar yaushe tace’yar iska ai na lura yanzu shareni kike shiyasa nazo ayita yau ta ‘kare

To ba dole inshare kiba kun matsa sai’kanwarku ta auremin masoyi kuma kunsan ni yakeso sarai ai wallahi babu adalci a harkannan. Kinga shukra laififa daga gurin Abban ki yake

Na sani amman ko yanzu zan iya shawo kan matsalar”to ai ba anan takeba in an fasama wata za’a zaba masa Abban sa yace bashi bake be gayamiki bane” dam nayi sam be gayamin ba. Amma wata shawara zan iya canza aurennan yadda baze zama matsala ba

Kamar ya? Na tambaya cikin za’kuwa dason jin amsar ta gyara zama tayi ta fara magana
Yanzun kinga nice babba agidanmu yarannan dukkansu agabana aka haifesu kinga Maryam wallahi ta auri Hishaam kedashi saidai kallo bangane ba? “yawwa yanzun zan ganar dake Maryam tanason mutum me tsananin kyau kamar Hishaam daya ha’da komai akwai yaron dayake sonta yake mata’barin ku’di amman ta yarda zata auri Hishaam saboda ta yadda shi’din na nunawa ‘kawayene kuma inkika bari ta aureshi wlh da kissa da kisisina da asiri da taimakon uwarta saita hanashi koda kallon kine yayi+

Amman kinga da kamar yadda aka tsara da farko ya auri Hanaan da kwa’barmu bazatai ruwaba”.

Meyasa kikace haka? Yawwa saboda Hanaan batada wayau kuma batada kunya Hishaam kuma ga son girma ita kuma bazata duba girmanka ba muddin kayimata saita rama tun daga nan zasu fara samun matsala kuma ga karancin communication saboda itama miskilace kamarshi kuma ai muma bama barsu hakaba muna gefe muna qarawa wutar  petrol koya kikace kawata? mika mata hannu nayi muka tafa inajin wani da’di yana ratsa dukkan ilahirin jikina

Nace Dr.hadiza daman k’aunar nan tana nan?”to ina zataje kinga daganan da kansu wa’danda suka ha’da abin zasu raba musammam yadda abban sa yake matu’kar son yarinyar ke kuma kawai saimu kaiki”

Nace anya babu wata matsala kaf danginku fa ance babu me kyawunta “ke dalla karkicimana fuska mana”uwa uba ga kuruciya “rabuda namiji idan bayason abu wlh duk bazega wadannan abubuwan da kika ganiba.

To yanzun ya za’ayi”kibar komi ahannuna yanzu daga nan gida nayi dana gama komai zakiji amman koda wasa karki bari yasani” bakida matsala da hakan hannu na mi’ka mata muka sake tafawa ahaka muka rabu ina jiran sakamako.

Ya hadiza tana zuwa gida ko part dinsu batajeba part dinsu Maryam ta wuce tayi sa’a Maryam din suna zaune da maman su tace yawwa daman gurinku nazo haj Aisha tace meya faru don naga arikice kike tun shigowar ki ya hadiza tace duk yadda za’ayi a fasa aurenki da Hishaam saboda sungama lalacewarsu da wata abokiyar aikinmu badan nake tsoron bata masa sunaba da har video saina muku saboda ku samu hujja to dan haka karki sake ki bata rayuwar ki akansa ai daman abinda yasa baffa ya nace sai shi kenan sabida uban yarinyar dayake so yace bazai bashi auren’yarsaba shine ke aka jona miki babu abinda baffa be saniba akan lalacewarsu da ita ke kuma naga ko kura ta mutu tafi karfin acemata Allah sarki ko kuwa?

Haj Aisha tayi jim tace tab’dijan da ni za’ayi wa wannan cin mutuncin ke Maryam ina yaronnan da kike so tace Sagir haj Aisha tace eh shi kimasa magana yadda inma ubanki neman kai yake dake kinada masoyi ni kibarni zanyi komai aure da Hishaam kuma akai kasuwa. Murna hadiza tafara ganin tayi nasara nan take

Bayan taje part dinsu takira shukra tace to na gama ha’da komai saura kijira sakamako suka cigaba da hirarsu ta aminai.

A ‘dakinsa suka sameshi tana gaba maryam na baya yana ganinsu yasan akwai matsala cikin rashin sanin meye yace Aisha meke tafe daku?kuka ta saka yanzun alh lalacewar Maryam takai kayi kyauta da ita ga yaron dakasan ya gama lalata da wata awaje? kuma magana harta fita harma an ta’ba hanashi aure akan haka?.

STORY CONTINUES BELOW

Ga yaron dake sonta haryaje zaifa’da rijiya saboda ita subhanallahi ya fa’da haj Aisha tacigaba to wallahi indai nice uwar Maryam baza’a min hakaba
To yanzun Aisha me kike son na fa’da masa kace kawai daman da masoyinta kuma yanzun tace saishi “saboda dai komai sai annuna ban isa da gidanaba? Baffa ba haka bane kaida kanka ai bazaka so ace ya ma’aruf yanson wata anyi masa hakaba..,.ke rufamin baki dalla, tunda kinada wanda kikeso uwarki ta rakoki harnan kin gayamin to naji yafito nanda lokacin da akasa ranar aurenki da Hishaam zan bashi aurenki da ubanwa yasaki amsa ai koda farko bance doleba, shikuma Hishaam zanyi magana da ayya za’a ha’dashi da’yar’uwarsa ta jini hanan ku tashi kuje.
Sum sum suka fice ya bisu da kallon takaici da rashin sanin abinda zai gayawa mahaifayar sa akan Hanaan.
HANAAN
Ina kwance na gama duk ayyukan danakewa ayya sai naji sallamar baffa gabana ne ya fara faduwa saboda baffa baya shigowa tsakar rana haka saidai da safe ko da daddare tashi nayi na tsuguna na gaisheshi yanayin kallon dayake min ne yasa naji wani iri na sunkuyar da kaina ‘kasa ana haka saiga ayya tashi nayi tsam na basu guri na tafi ina gwada wani girki dana gani a tv da daddare.
******************
Tunjiya na fuskanci yanayin ayya ya canza tun ina daurewa har na kasa hakuri nace wai ni waye ya ta’bamin kakata ne hannuwana ta kamo tace zauna nan ba musu na zauna ta fara magana a hankali Hanaan na’am nace tace nasan kinajin haushin rilwanu amma inason kisan yana matukar sonki kamar yadda kowane uba keson’yarsa
Kuma karki ta’ba sab’a masa kinjiko? na gya’da kaina a hankali alamun to tace kuma duk abinda kikaji nan gaba ki karb’i qaddarar Allah ki d’auka shine mafificin alkhairi atare dake ku ringa yiwa Allah kyakykyawan zato sai kuga komi na rayuwar ku ya zama me kyau kinji?
Ayya wani abin baffa yace “eh wasu abubuwan alkhairi yakeso dake amman sai yayi magana da amininsa tukunna Hanaan zanyi farinciki in wannan abin ya tabbata dake saboda tun kina k’arama nake tunanin hakan “ko? Tace kwarai kuwa nace to Allah ya tabbatar da abinda yafi alkhairi amin tace. Jikina duk a sanyaye nake komai ba tare da nasan manyan al’amuran dasuke shirin samuna ba.
Yau na lura tunda mukai zancen nan da ayya take cikin farinciki har satar kallon ta nake, can ta gane tace ko inmatso kifijin dad’in kallon nawa ne? Ayya kodai aurennawa ne yazo? cikin mamaki ayya take kallo na tace waya gayamiki?
Nace to inba aurenane yazoba kince ranar aurena saikinfi ko yaushe farinciki tund’azu na lura da irin murnar dakike abin yafi na kullum shirin kwanciya ta gama tace gobe da labari insha Allah nace to Allah ya kaimu lafiya Amin tace muka kwanta
Aqa’idata ina na saita alarm amma kullum ayya ke tashi ta tasheni yauma kamar kullum tayimin magana hartayi alwala na wuceta ta tada raka’atanul-fajr nayo alwala na tarar da ita tana sujjada na tada sallah na idar bata dagoba to nasan tana’dan da’dewa a sujjadar qarshe karatun Qur’an na fara har gari ya fara haske sai alokacin na lura bata d’ago daga sujjadar ba
Dasss naji gabana ya yanke ya fadi ayya nakirata ayya babu ko gyaran murya ayya na kira da karfi cikin firgici kusa da ita na matsa ka’dan na ta’bata ganinta nayi ta fa’do kan cinyata ina zaune alokacin bansan yanayina ba bansan mutuwaba banida kowane irin wayau lokacin da mahaifiyata ta rasu amma nasan’dacinta ban ta’ba ganin gawaba ban kawo mata mutuwaba babu abinda ya sameta babu wata alama…..
Ahankali nake jijjigata ko wasa take amma ina harna fara kuka hannuna na kara dai dai hancinta naji iska bata fita da gudun da bansan na iyashiba na fita ina kuwwa ina salati su baffa basu dade da dawowa daga masallaci ba da sauri suka fito shida ya ma’aruf baba megadi ma ya taso baffa ne yake tambaya ta menene? Ke menene ayya…..baffa ka taimakeni…. ayya….. baffa… Agurin na zube na fara shidewa da gudu baffa yayi sashen ayya daga nan ban sake sanin komiba sai farfadowa nayi naga taron jama’a ko ina anan na tabbatar da abinda nake zargi innalillahi wa inna ilaihirraji’un ita nake ta maimaita wa babu adadi kenan ayya ta rasu?
STORY CONTINUES BELOW

Banga zahiriba saida aka’dauko ayya za’a kaita makwancinta rasa inda zansa kaina nayi damanfa ita ka’dai gareni yanzu na zama babu kowa kenan bin mutane kawai nake da ido sai hawaye da kuka mara sauti sai Amal da zee ko yaushe suna kusa dani har akai bakwai kowa ya watse babu kowa a sashen sai dai ni kadai duk inda na kalla sai in tuna da ita itace komaina na rayuwa babu abinda ke min da’di yanzu samada kuka gashi bani da appetite balle inci abinci ga rama sai dare yayi in kudundune in kwana cikin tsoro da kuka da kewar ayya.

Yau sati biyu kenan da rasuwar na dawo daga makaranta na tarar kofata a bude a hankali cikeda tsoro na shiga ina sallama baffa na gani a zaune a falo alamun ni yake jira sauke ajiyar zuciya nayi ganin shine ruwa na kawo masa kamar yanda ayya keyi na koma gefe na rakube ganin bashida niyyar magana na fara magana

Baffa ya dago ya dubeni nace dan Allah baffa kakaini boarding da sauri ya kalleni ban kalleshi ba na cigaba da magana ina hawaye meyasa Hanaan? Baffa hakika idanna cigaba da zama a gidannan mutuwa zanyi dan Allah ka kaini inda zan sami wasu yanuwan

Na lura jikin sa yayi matu’kar sanyi da zancena yace Hanaan akwai shwarar da na yanke akanki bansan yadda abin zaizo mikiba ga kwanciya r hankalina da naki baki daya idan kin amince zan aurar dake inda za’a kulada ke fiye da yadda kowa zai kula dake musamman yanzu da kike bukatar kulawa

A iya sanina kinfi yaran gidannan masoya amma babu wanda kike kulawa sabida irin tarbiyyar ki bazan miki doleba saikin amince amma ina tabbatar miki shine zaifi agareki “baffa ayya ta sani? kwarai kuwa kuma tayi farinciki da hakan fiye da komai. Na amince kawai nace ba wani tunani dana tuna irin farincikin datake kafin ta rasu na tabbatar akan zancenne

Daman can dake abbansa yaso a ha’da sai naji tsoron rashin amincewar ayya a wannan lokacin daga baya kuma abin mamaki ta amince tareda sanar dani ta dade tana sha’awar hakan kasancewar sa ‘dan uwanki……… baffa wa kenan? Shi HISHAAM din……baffa dan Allah dan Allah dan Allah bandashi”meyasa bandashi?” Saida ya maryam tace bataso sannan kuma baffa ai ba cewa yayi yana sona ba

Hanaan har kullum iyaye suna zaba wa ‘ya’yansu abu mafi kyau hakika na tauyeki a abubuwa da dama na rayuwa dan haka yanzu nake burin kiyi rayuwa mai kyau da tsari

Kukane ya subucemin nace yanzu baffa kowa a gidannan yasan don ya maryam tace bataso ne to ke zakiqi dan’uwanki ne?kai kawai na iya girgiza masa wato na fuskanci a duniya tabbas gatana ya kare kenan baffa yasan mom din ya Hishaam bata Sona kuma yasan bama shiri da ni’ima sam amma dukda haka kuma Hishaam kyamar yangidanmu yake ga mugun hali ga shaye shaye yanzun ance harda neman mata……amma shine ze kaini can abu daya yake sanyaya min jiki idan na tuna irin yadda Ayya keson in auri Hishaam zancen daya sakata farinciki lokaci guda

Kaina na saka tsakanin kafafuna inata garzar kukana baffa ya gama nasiharsa yace zan baki kwana uku kiyi nazari zan dawo donjin amsarki band’ago kainaba kai kawai nad’aga masa alamun to.

Babu abinda ban saqa na warware ba qarshe na dukufa da addua na barwa Allah komai amma na kasa kwanciyar hankali koda ka’dan duk nabina rame ga kadaici
Wace rayuwa ce me kyau da tsari baffa yake fada ai ko rantsuwa zanyi akan ya Hishaam baya sona nasan bazanyi kaffara ba ni kuwa yadda naga zan iya haka zan rayu innaji bazan iya zama dasuba to zanshiga uwa duniya kawai matsaya ta kenan.

Abu daya ne yasa nakeson aurennan inna tuna farincikin da ayya take lokacin da zancen auren yazo sai indanji nutsuwa kuma inna tuna zanbar ba’kin gidanmu donnasan ko yayane zan sami haske ka’dan.

Hishaam

Koda Abba ya sanar dani canjin baikon da’akayi banji komai ba kawai dai gabana yana yawan faduwa idanna tuna abin na rasa dalilin hakan mom tanata k’ok’arin taga ina farinciki amman harkokin aikinama sun isheni

Sam mantawa nake da zancen yarinyar danma shukra tana yawan damuna da maganar inda nake tabbatar mata dacewa ita ka’dai zan iya so arayuwata.

Babu abinda nayi ko nasiya komai sai Abba ya gama ake nunamin sai ince yayi kawai abinda yafimin da’di gidajen da Abba yakaini in zaba na zabi wani mai part uku’katon gidane sosai babu wanda zaisan da zaman wani Abba ya dade yana kallona inda na basar kamar ban san yana kallona ba, unguwar babba ce sosai cike da manyan gidaje Kuma GRA.ce babu ruwan wani da wani daman haka nakeso

STORY CONTINUES BELOW

Bantab’a attempting’din inje gidansu ba saboda haushi sam banso aka sakata a plan dina ba saboda mamanta tana da kirki bana manta irin son datakemin

Sam yanzu nadena zaman gida saboda banason ayita maimaita abu da’ya kullum muna tare da shukra. Idannace banajin haushin mahaifinta nayi karya amma ganin bata loosing hope akaina shiyasa nima bana nuna gazawata.

Hanaan
Babu irin tunanin da banyiba qarshe na yanke shawarar auren kawai koda baffa ya tambayeni kai tsaye na nuna amincewa ta amma nikadai nasan irin fargabar danake ciki soyayyar Abbansu dakemin ita na dogara da ita

Abu har yayi nisa amfara shiye-shiryen biki Maryam ma haka habaici kuwa har gurina ake shigowa musammam ayishi tun rasuwar ayya daya shigo gaisuwa ban kara ganinsa ba yanzu Hanaan wannan shine abokin rayuwar ki besaniba kinmutu kina raye oho zuciyata ke saqa da warwara ita ka’dai ido kuwa sai abinda ya saba wato kuka

Yau saran sati uku auren kamar yadda aka saka ina kwance abakin gado na rungume teddy ta can qasan maqoshi naji sallama da sauri na na’de kaina da mayafi doguwa rigace mai adon duwatsu ajikina falo naji an shigo
Na fito ahankali kamar me san’da yana tsaye mamakin zuwansa nayi pitch shirt ce ajikinsa me gajeren hannu adon duwatsu ne ajikin rigar an rubuta handsome ajiki cream colour wando ne ajikin sa sai farin glasses ya kwntar da sumar sa baya tari yadanyi sai na dawo cikin hankalina kunya naji ganin ya gane ina kallon sa
Girarsa ya daga duk biyun yace ko in turo miki hotona ne? Dakyar na hadiye yawu ko banfa’daba nasan har kunnena yayi ja sabida kunyar danasha

Basarwa nayi na wuce kitchen na ha’da masa drinks masu sanyi kadan na fito kaina a sunkuye na kasa gane irin kallon da yakemin kamar yanson gane wani abu, abu da’ya nasani shine bayajin kunyar kallon mutane ko ka’dan can gefe naje na rakube nace barka da rana be kalli inda nakeba yace barka kadai dakin yayi shiru ya zuba lemon tamarind ya kurba ka’dan ya daga kai ya dubeni kamar bazaiyi maganaba yace Abba yace in tambayeki meye ra’ayinki gameda aurena?

Rasa me zance nayi maganar tayimin bazata”ko kinada matsala da hakan? Feel free kifadamin inma bakya so kifadamin kinada kowacce irin dama kifin nabar gidannan inma ni’din banyimiki ba zan iya sanar da hakan karkiji wani abu ko kuma kinada wanda kikeso bakida matsala”lemon sa yasake kurba da alamun yana masa da’di

Zuciyata tamin nauyi ganin badon kansa yazoba Abba ne yasakashi kuma be damu da aurenba sam kamar yadda na zata tun farko kaina na ‘daga na dubeshi ya kalleni shima sam na kasa karantar yanayinsa na wannan lokacin nace kai meye ra’ayinka game da wannan auren? murmushi yayi har kyawawan haqoransa dogaye farare suka bayyana
Ya muskuta ka’dan yace ni banida matsala ko ka’dan da wannan auren dukma abinda be yiwu yanzu ba zaiyiwu nan gaba kadan kuma kema bana tunanin zaki sami kowace matsala da wannan auren insha Allah

Abba yace ki bada account number dinki da phone number dinki damnayi sabida nasan abban yanada phone number ta murmushi nayi ka’dan ganin bazaice yanason phone number naba ina gama fa’da mai ya mike sai amjima yafada tareda ficewa gabadaya

Naso qwarai hirarmu dashi tayi tsayi saboda na fahimci wasu abubuwan amma hakan bai samuba bana k’in ya Hishaam saboda yana yawan burgeni musamman Rashin maganar sa gayunsa qamshinsa da wadansu ‘dai’daikun abubuwan amma ina tsananin jin haushin kyamar dayake nuna mana da wulakancin sa inya raina mutum abinda na’dau alwashin bazan taba juraba.

Kaya na fitar hankali aka kawo gidanmu inda a take ya Maryam tayi nadamar qin aurennan koda bata fadaba akwatuna goma sha biyar harda qaramin akwatu na gold kaya babu irin wanda babu kamar kowace mace nakanyi burin wasu abubuwan amman banta’ba tunanin zan sami hakanba

Kankace kwabo labari ya baza ko ina babu wanda a gidanmu yasan arzikin Abba Umar ya shahara haka saita dalilina nan fa qiyayya taci uban tada duk taqama ta qarewa su ya maryam nikuwa sai alokacin na kara son auren ma

STORY CONTINUES BELOW

Yau saura kwana biyu afara bikin amman haryau babu shi babu wayarsa ga faduwar gaba da naketa famanyi saboda masu son haka
Da’di d’aya naji dangin ammina wato dangin Abba umar dasuka tashi wannan karon agurina suka sauka inda baffa yasa aka shigar mana da kayanmu cikin gida yace anan za’ayi bikin gabadaya.

Ina kuka nayi sallama da sashen mu nida ayya ta danake kewarta fiyeda komai muka koma cikin gida gyaran jiki da komai da nasu suka taho daga niger kayan mata da kunshi duka gashi komai sukeso Abba umar kawai aikowa ya ke saiya zama bikina ne ke daga na ya maryam

Acikin kwanakin al’adata nake na wanke kunshina kenan uddu ta kalleni tace Hanaan sallah fa nace sai ankwana biyu na sunkuyar dakaina suka kece da dariyar dana rasa dalilin ta abokiyar wasan su kakarmu ce tace to Allah yaba mijinki dangana suka sake kwashewa da dariya fitsari na faraji sabida tsoro namanta da nan bangaren shaf

Daman ga bala’in ciwon mara wataran har sai an dawo dani gida ‘dan maganin da ayya ke sawa akawomin bansan inda ake samoshiba gashi yanzun batanan
Na rasa me yakemin da’di agida akayi kamu akayi walima
Washe gari daurin aure da dinner washegari fargabata ta ninku musamman dana tabbatar an’dauramin aure ni Hanaan atake zazzab’i me zafi yakama ni ga ciwon mara nafara kwara amai daki na tafi na kwanta daga nan bansake sanin me akeba

A hankali na bude idona saboda hasken dakemin zafi a cikinsu akansa idanuwana suka sauka kallon gurinnayi tsaf naga agidane d’akin cike da mutane shikuma yasha manyan kaya ga wata mace a gefensa da mask a fuskarta kallona kawai take hannuna dayasha kunshi na kalla a b’ule ansaka min kanula

Haushi ya kamani wato shi baka ganinsa sai irin haka ta faru cikin hanzari ya kawo hannun sa dai dai girjina nayi saurin doke hannun da bayan hannuna cikin fargaba.  Abin jin bugun zuciya yasa a qirjina ya kama tsintsayar hannuna yana duba agogon hannun sa daya gaji da kyau ya dace da farar fatarsa me qyalli na ture hannun uddu tace kuzo mu fita Anisa dabansan munafincin daya kawotaba taja tsaki mtsss tace donfa ta ganmune ku wuce muje dariya ya farayi yana kallon matar dake kusa dashi dagani itama dariyar take amman ita bana iya ganin bakinta sabida idontane kawai ake gani qwalla ce ta ciko a idona sabida tsabar takaici

Na yunqura zan tashi ya komar dani ya kwantar na dubeshi cikin takaicin abinda yayi nace nifa maza basa dubani dan tsaki yayi yace kamar gaske hakan yasa qwallar danake matsewa ta zubo nace eh koba gaske bane banason wani ya dubani sai mace kuma canake kai likitan qwaqwalwa ne ai nan ba field dinka bane ido ya zazzaromin nima na zazzaro masa nawa

Bude idonki sosai yace nayi masa banza fitoda harshen ki najuyar da kaina saboda hawayen da yaqi tsayawa “kamar haka” yana gwadamin na rabudashi kayan aikin ya miqa mata ya fice nabi bayansa da harara

Bayan ta gama dubani tace “ina muku fatan kowa aniyarsa ta bishi” na yunqura na zauna nace wannan addua kenan? tace eh nace Amin. Ciremin wannan abar bana buqata ta dubi hannun nawa tace aiba ninasaba nace eh amma ai kin iya cirewa ko? A kyankyame cikin mugunta ta ciremin.

Ko awajen dinner yayita wulakanci iri iri ko a jikina ya amina itace kangaba a komai zee da Amal sunyimin qoqari sosai don sune jigon rayuwata a yanzun ina mamakin farincikin ayya akan aurena da mutumin nan ina fatan Allah ya nunamin alherin datagani a tareda hakan

Yaune za’a kaimu ya Maryam aka fara kaiwa sai ankaita gidan surukanta sannan zasu wuce nima sai amkaini gidan Abba umar sannan zamu wuce gurin baffa aka kaini yamin fa’da sosai akan biyayya da haquri da tsafta ya qara da cewa yayan mahaifayar ki wato uban mijinki ya nemi kar akaiki da komai inda kaitsaye na sanar dashi cewar ayya bata yadda da hakanba duk abinda uba yakeyi nayi miki ina alfahari da hakan dukda nasan danuwanki bazai ta’ba miki goriba Allah ya miki albarka yabaki kyakykyawan rayuwa amin nace ina kukan dabansan dalilin yinsaba.

Har gara akai mana kowacce mota guda da kaya gidan Abba umar aka kaini bantab’a ganin farincikin saba kamar yau lallashina yake tayi da yabon ayya da irin kokarinta akaina kukana ya qara tsananta jin an ambaci ayya ranar danafi buqatar ta

Mom dinsa kuwa cikin qunci takemagana abinda zai amfani’danta kawai tayimin fada akai nace araina nima da ubana ya isa da gidansa yadda mijinki ya isa da nasa gidan wlh daban auri d’ankiba. Ya amina cike da farinciki da’doki tace munyi karambani mun canza miki makaranta ganin can duk labarin auren ya cika ta kuma Abba yafison me tsada sosai sabida ki samu sauqin karatu sosai zee ce tayi tsalle a gefe tace yanzun makarantar mu’daya ya amina tace harma da Amal naji wani dad’i sosai.

Sadakina Abba damqamin yace baffanki ya wakiltani ya amina ta amsarmin ya sake miqo mukullin mota yace ga wannan motace na baki gudunmuwar aurenki amatsayina na uba agareki Allah ya jikan mahaifayar ki amin akace gabadaya.

Gidan da’aka kaini banta’ba mafarkin irinsa da sunan gidanaba fuskata arufe take amma nayi matukar mamakin tsaruwar gidan nace dole yadinga walaqanci tunda babanshi nada ku’di b’angaren damane nawa sama da qasane ko’ina da baranda sama da qasa harabar gidan qatuwar gaskece tasha shukoki iri iri da fitilu masu kyawun gaske da wasu fararen liluna masu abin sha’awar gaske da wani garden daidai wajen shiga sashena kowa cewa yake Masha Allah

Murna ta isheni ganin kowa sashensa daban harda wani extra abinka da quruciya ban kawo komiba

Gidan ya tsaru iya tsaruwa dakina aka kaini king-size bed ne adakin komai na kayan dakin farine tas akwai sofa guda biyu daya a gaban gadon daya kuma adaidai tagar dakin akwai corridor kana fita corridor din kuma sai brandar sama na lura akwai qofa acikin dakin da zata sadaka da wani guri dabansan inabane

Tsofaffi suna tamin wasa ko burgeni bayayi saboda ni kaina nasan nayi qanqanta da aure sai yanzu na shiga s.s.two ban shirya komi ananba shi kansa saina gane inda ya dosa tukunna sallama mukai da dangin mahaifiyata don su kadai ne suka rakoni a’yan gidanmu kuwa sai Amal ka’dai saikuma qawata yaruwata zee sai qawayenmu na school bayan suntafi ina lullube aka rako ango da abokansa sukayi siyan baki abokansa suka dinga zuba kud’i anata raha wani abokinsa dr.sadiq me nutsuwa yamin nasiha inda mutumin danafi tsana wato idirisu inji ayya ya fara zancen shakiyanci wasu suna dariya wasu suna kwabarsa

Bayan angama komai suka kwashi su Amal ya tafi rakasu na tashi da sauri na rufe qofata gam na dawo nayi nafiloli nakaiwa Allah kukana nayimana addu’a hardashi da auren bakidaya da sabuwar rayuwata.  Da kayan jikina na kwanta na qudundune ina tasbihi ga Allah da neman’dauki dakyar nayi bacci har asubha banji motsin komai ba saboda ina bacci ina farkawa sabida tsoro da rashin sabo. Koda safe banga kowaba ga gidan qato amma na fuskanci babu me aiki ko daya ko awaje sai masu aiki maza ko’ina don rashin kishin kai tsuru nayi agidan daga baya na yanke shawarar yin komai da kaina inbarwa Allah ikonsa.

Sama na hau’dayan dakin inda anan kayana suke oh…my….God .. shine abinda na fada a fili irin walk-in closet dinnan ce aciki ga full-length mirrors a gefe kayana na canza nasa masu sauki na sauka don in qarasa abinda yayi saura ina gaf da shiga kitchen naji wani irin qamshi da sauri na leqa ta daya daga cikin tagogin shine ya fito harda Labcoat dinsa a hannu kenan aiki zashi yau? Na tambayi kaina to inbeje aikiba me zai miki mutuminda baisan yadda kika kwana ba sabuwar motarsa kirar Audi danake zaton Abba ne shima ya bashi ita ya hau yayi horn megadi ya bude masa ya fita aguje ko kallon sashen danake beyiba

Harkan gwiwoyina na tsuguna ina neman mafita hade da sirrin kuka na.  saiyaushe zanji da’di arayuwata? wace irin rayuwa na bari? wacce nazo na tarar? ranar babu abinda nayi haka na wuni ina fatan ko da daddare zai shigo yace inyi hakuri emergency ne ya kama su misalin karfe takwas na dare naji mota ta tsaya na leka ta bolcony na na sama shine ya dawo da brief case a hannun sa ko kallon sashena baiyiba ya wuce yaron gidan ya bishi da kayan da ya shigo dasu.HISHAAM

Sam haushin yarinyar nakeji tunfarko ganin na bata satar amsa amma takasa tace bata son auren abuna biyu sam yarinyar batada kunya shekaruna sun kusa ninka nata amma agaban shukra take wani dokemin hannu bayan ragowar tabawar wasu ce na tabbata.

Tunda kuwa ta sake ta shigo da kanta rayuwata toyarage nata yau lahadi kwananta bakwai kenan tun ranar datamin wulakancin nan bata kara ganin ido naba koya take oho.

Banida wani aiki sosai danhaka sai ten natashi a bacci zuwa shadaya da rabi na shirya sam na gaji dacin abincin gurare gashi banson zuwa gida inci magana taje gurin Abba gashi bazan taba cin jagwalgwalon wannan yarinyar ba shawara na yanke gidan ya amina zanje inci acan zuwa shabiyu na kwashi mukullaina na fice+

Ina zuwa nace akwai abinci tace bari a dafa maka bayan mungaisa zainab tace ina aunty Hanaan nace tananan ya amina tace kamarya tananan tana lafiya?na’dan tab’e bakina oho nace rantane ya b’aci tacewa yaranta suje d’aki bayan sun tafi ta balbaleni da fad’a “Hishaam ban gane abinda kake nufida oho ba kanason ka shiga wutane?” To bahaka kukesoba ku kinsan ban iya k’aryaba gaskiya rabona da ita tunranda aka kaita gidannan kuma daga haka babu abinda zan iya qarawa

Shiru tayi nad’an lokaci kafin ta nisa tace to wallahi ka gyara ko kuma inhad’ka da Abba ko akuya aka d’aure da sunanka ai yakamata kasan halin datake ciki meye amfanin aurenka datayi?to me kikeso inyi? Wlh kashiga hankalinka na zata kanada hankali shiyasa na qyaleku amma yanzu tunda haka kake to zansaka maka sharadi kullum kaje ka dubata sau biyu safe da dare

Zandunga yi mata waya duk ranar daka sab’a hakan zaka amsa kiran Abba watoma kasan abinda kake ba daidai bane amma babu ruwanka ko? to yanzu inma mutuwa tayi bakasaniba kenan” gabana ne ya fara faduwa tacigaba kuma daga yau ka gamacin abinci a gidannan kaje kacina matarka” Allah ya kiyaye inci jagwalgwalon wannan yarinyar kuma ka tashi ka tafi yanzun…karar wayarta ne ya katse zancen ta daga da sallama

Abba ina wuni gabana ya fadi jin Abba ne kullum sai ya min waya akan wannan yarinyar maganar ya amina ce ta katsemin tunani da cewa au gidan Hishaam zaka? yanzun?to

Abba kayimasa wayane? mukullaina na d’iba na daga mata hannu na fice sai gida

A bakin kofarta na tsaya cikin rashin sanin abinyi, ahankali na tura kofar wani sassanyan qamshine ya daki hancina da daddare na shiga gurin sam banlura da yadda aka qawata shiba saiyau sai sanyin aircon dayake tashi gabadaya yanayin qamshin part d’in nata kamar aci

Kamar me sand’a nake tafiya babu koda motsi a wajen mummunan faduwar gaba naji nace kardai wani abune ya sami yarinyar nan na fara tafiya da sauri daidai qafar benanta naji motsin ta a kitchen

Kujerar dake saitin kitchen d’in naje na zauna tana tsaye a kitchen d’in da mopp a hannun ta tanata gugar kitchen sai a lokacin na tuna ba helper agidan gashi abba yanzu zaizo tundaga kanta na fara kallon ta har qafar ta nayi saurin dauke idona nace shameless girl batasan wanda zaizoba amma jibeta bum short ne ajikinta sai blouse ta daure gefen rigar koyaya ta motsa ana ganin cikinta a fili kanta da wata hula iyaka tsakiyar kan kawai ta rufe wayarta tana aljihun rigar ta saka earphones a kunne gashinta wasu yan jeloli sun fito ta gaba

Sam batasan da mutum a falon ba bansan yadda akayiba na sami kaina da qare mata kallo ban taba ganin mace a yanayi irin wannan ba nace a raina da badan rashin tarbiyya ba ai da anyi mace anan koda yake shedan ma zai iya qawataki don ance mace tana tahowa ne da siffar shedan kuma tana bada baya da siffar shedan shetan kuma na tambaya ba shedan sai dai mala’iku su qawatata ka manta matarkace haushin tunanin danake ne kawai ya kamani kamar ance juyo karaf muka ha’da ido da ita kafeni tayi da idanuwanta masu cike da tambayoyi she have a sexy eyes qwalla ce tafara cika a idonta nace araina ai daman alokacin kukanki kike yarinya ni kuwa ba raino nazoba balle inyi lallashi

STORY CONTINUES BELOW

Kanta ta sunkuyar a qasa remote na dauka na kunna TV bayan qofa ta koma ta boye sam daina kallon gurin nayi nace araina yau sai surukinki ya ganki ahaka zanga qarshen zama ba kaya sai misalin biyu sannan Abba ya qaraso inajin motarsa na fita da sauri abin mamaki kafin mu shigo da Abba harta saka abaya ta nad’e kanta tsaf ita kanta saidata gane kallon mamakin danake mata

Kayan hannun Abba na hana yaran gidan su karb’a na karb’a da kaina bayan mun shigo ya zauna sai gata da sauri ta durqusa ta gaisheshi ina mamakin irin sonda Abba yake mata aqasa ta zauna bayan sun gaisa ta tashi ta nufi kitchen na bita don kartayi kwab’a ruwa da lemo ta hado a tray ta d’auko ta wuceni ta fito na biyo bayanta na karb’a na ajiye na zuba masa bayan ya natsa yace inbata kayannan ya fara mata bayani fa cewar”Hanaan ga uniform dinki nan da duk abinda zaki buqata na makaranta

Gobe zaki fara zuwa nasan kinada tarbiyya da kamewa amman inason kiqara saboda yanzu ke matar wanice ba’a zuwa da mota ba’a zuwa da waya makarantar duk abinda kikeso ayi miki ki tambayi mijinki gashinnan ko babu aure’dan’uwanki ne akwai ni’ima da Amal da zainab naji anmaida Anisa ma kinga akwai tarin yanuwanki acan kiyi karatu sosai kinjiko? ta gya’da kai

Abba be gusheba saida yayi mana nasiha ya sanar damu haqqin mace akan mijinta ya sanar damu haqqin miji akan matarsa lallai Kam abin babbane yayita sa mana albarka inata amshewa cikin jin da’di ina sosa kai ita kuwa na lura abin ya shigeta sosai

Hargurin motarsa muka rakashi ta juya da sauri zata wuce nace inason magana dake Bismillah tace ta wuce gaba ina bayanta muna shiga falon banjira tayi wani abuba na fara magana.

Kinji abinda Abba yace? shiru tayi tana kallona da alama ma haushina takeji inda hakan ya bani qwarin gwiwa nacigaba idan kinji to yatsaya iyaka fatar kunnuwanki karki sake ya shiga cikin kanki idan kuma bakijiba to haka nakeso dan banason gaba kice nabaki false hope

Shiru ne ya ratsa dakin kodana fuskanci babu abinda zatace juyawa nayi zanfice”meyasa ka amince da aurennan?”abinda tace kenan naji dad’in tambayar datayi dominni mutumne dabayason b’oye b’oye murmushi na saki nace is the same thing da abinda yasa kika amince wato aurennan shine freedom d’ina kamar yadda yake naki kema shikenan dalilin ka na aurena?  eh shikenan donhaka banason ki kira aurennan da sunan aure ki d’auka nan gidan hayane da muka ha’da kudi muka kama ni da ke babu mai tashin wani kuma babu mai iko da wani karki ta’ba zaton wai saikin tambayeni akan duk abinda zuciyarki ta raya miki kiyi. zaki iyayin duk abinda kikeso bazai dameni ba hawaye naga tanayi banason kuka shiyasa na sake juyawa zanfice tace to in aurene meyasa saini

Na juyo da sauri na d’aga kafadata nace wannan ne kuma nima bansaniba tunda ni bance ahadani dake ba ko da wata asalima da yarinyar danakeso kuma banjin zan iya son wata mace bayan ita

To donme yasa baka gayaminba?cikin kuka take maganar nace ai nabaki duk satar amsa akan kice bakyason aurennan kikaqi ni kuma daga bangarena ban’isa ince banasoba danhaka kada kiga laifina.

Meyasa baka auretaba ka batamin tsarin rayuwata akan wani plan d’inka na daban mara amfani wannan ki tambayi b’angarenki kuma karki sakarai zanzama direban ki ko in zama me raino dinke baki wuce rainoba agurina

HANAAN

Tabbas haushin sa nakeji kuma shi koyaushe saidai katsam kaganshi ina tsaka da gugar kitchen na ganshi yana kallona daman shi baya kunyar kallon mutane kamar be ganniba nikuwa nace gidan ka tarar mamaki nake meya kawoshi out of nowhere da besan da mutum a gidan ba saiyau jinai ina neman kuka b’oyewa nayi abayan’kofa saboda bana buqatar yaganni ahaka

Qarar mota naji daman bana saukowa ahaka abayata na zura na yane gashina da mayafinta Abba ne a fili mamakin sa ya fito ganin jikina a rufe cikin qanqanin lokaci harda wani biyoni kitchen sai a lokacin na gane abinda ya kawoshi sashena sabida Abba zaizo ne bayan Abba ya tafi banyi niyyar kulashiba sam saiyace yanada magana maganar datafi wuta zafi ataredani

STORY CONTINUES BELOW

Tun lokacin da muka gama maganar nan na shiga tunanin irin rayuwar dazan tsarawa kaina don gudun wulaqanci haka na kwana ina saqa da warwara da addu’ar mafita mekyau daga ubangiji. Tun asubha danayi sallah na zauna na fara rera karatun Qur’an nina bayan gari yayi haske na shiga kitchen na ha’da breakfast nad’an ci ka’dan uniform d’in farar t-shirt ce me dogon hannu da collar a wuyan sai falmarant d’inta ash skirt d’in ma ash a bude yake gabadaya sai farar socks da farin hijab talha iyakarsa wuya sai baqin cover shoe na dade ina kallon kaina a madubi nace lallai Kam banwuce raino ba.

Harabar gidan na fito tun bakwai da ashirin ina zaune har takwas ina kan lilo nayi nisada tunani na rungume jakata kamar ance kalli sai gashi ya fito yasha ado cikin qananan kaya yayi wani masifar kyau tsanarsa ce takamani dana tuna yanada wadda yakeso baniba a hankali nataka zuwa inda yake tunda na taho yake kallona ni kuwa yanzun in yana kallona bana damun kaina daf dashi na tsaya nad’an rusuna barka da asubha hannu kawai ya dagamin hade da cewa lafiya

Na cije labena na qasa saboda haushin rashin darajata agurin wanda na zaci shiyayi ra’ayin aurena da kanshi kodana d’aga kaina sainaga yana murmushi har ana ganin hakoransa”how childish”nan da nan nafara tafasa da irin rainin hankali dayakemin. Nace ba zuwa nayi kayimin dariya ba lift nake da buqata saboda banwaye da gurin dazani ba kuma naga yanzun kake fita”kash yau ba yanzu zanfita ba yafada tareda dafe kai kamar yana magana da yar shekara uku bantsaya wata-wata ba na juya na koma kan lilon cikin garden ina kuka can natuno da buhari ciki na koma da sauri na dauki waya na kirashi ko minti goma ba’a yiba sai gashi na kulle ko’ina ina qoqarin fita yazo fyuu ya wuceni da mota bansan ina kukaba saida naji hawaye masu dumi sunabin kumatuna buhari ne ya miko min tissue na shige muna tambaya atake aka kwatanta mana dayake sananniyace banda agurin kifin rijiya irina.

Yau tayi da’di abinda na fuskanta daya da makarantar shine babu tarbiyya kamar tsohuwar makarantar mu ga anisa kuma harda ni’ima Allah yaso ba ajinmu daya da anisaba amma ni’ima ajinmu daya kowa abinda yaga dama yake kamar makarantun danake gani a turai mazan sai cakumar matan suke nikuma daman can natsani irin wannan harkar.

Muna karatunmu successfully makaranta ka’dai ke deben kewa shikuwa sai inyi sati banganshiba kullum dai yanzun yana zuwa in yaji motsina koda be ganniba saiya wuce nakan leqo inga kwalliyarsa kafin ya fita. Yau asabar ina gida farar shirt ce qal ajikina da bakaken stones an rubuta lucky me da duwatsun wuyanta qatone sai bakin wando jeans iyakarshi gwiwata banason gashina yayi qura saboda ba kullum nake jiqashiba hulace baqa a tsakiyar kaina kawai take nasa pin na maqaleta

Ice cream na dauko a fridge na fito falo da zummar zama kawai sai ganin su nayi ko ba’a fadaba nasan itace yarinyar dayake so saboda yanayin kallon dayake mata. Kamar ana cakamin mashi aqahon zuciyata haka nakeji kallon banza takemin yana gani saina tuna cewa ni’din fa ba kowa bace sai kawai na hade raina na d’aga kafadata da girata alamun tambaya cikin dariyar raini yace bakuwa na kawo miki ku gaisa daman kinsan da labarinta.

Zuciyata naji tanamin yaji sai na saki murmushi nace oh you are welcome zasu shigo nace wait suka tsaya suna kallona takalmin d’aki na d’auko musu suka canza ba musu. Bayan sun canza suka shigo atare kitchen nashige ina sauke numfashin dayake barazanar barin jikina kuka kawai nakeson nayi amma nayi alqawarin bazai tab’a ganiba waishi meyasa duk lokacin dana dade banganshiba ganina dashi baya zama alkhairi Allah ka tainakamin, lemuka na kawomusu ashe ya iya hira ban saniba sai yau arziqin wata.

Banzuba musuba shiya zuba musu saboda ban iya kinibibi ba suna sha suna hira na lura zamana bashida amfani agurin na tashi nace to baquwa afwan akwai ayyukan dazan qarasa yanzu kigaida gida na juya da sauri yace itama tafiya zatayi kamar ba haka tasoba amma sai tayi murmushi tace na tafi nace mungode da ziyara sai wani lokacin na rakasu harya bita nace Dr yajuyo da sauri cikin mamaki nace minti daya ba musu yace inazuwa yana shigowa na dubeshi nace meye alaqata dakai dazaka kawomin baquwarka? azaman haya there are some rules so karka qetara don’t cross the limit  after all kanada part dinka why don’t you just take her there?

Me kike nufi? kina nufin inkaita dakina? me yayi saura tunda ka kawota dakin matarka karki qara kiran kanki da matata kuma karki qaramin rashin kunya.

Yamm naji kaina yanayi nace waito meye matsayina agurinka shiru yadanyi kafin yace you are  part of my property, tunda nake banta’ba jin rashin mutunci irin na yauba kuka ne ya subucemin na kalleshi mury na rawa nace did you just call me your property? Am not… anyone’s… property kuma nagane abinda yasa kakemin wannan abubuwan harda kawomin mace gida so kake kayimin kora da hali so for your kind information ban ta’ba sonkaba Kuma bazan tab’a sonkaba sabida baka layin irin mutanen daya kamata asoka ko baka kyautatamin dan komai ba zaka kyautata min saboda qaunar datake tsakaninka da mahaifiyata amma tunda ka manta daga yau na manta alaqar datake tsakanina da kai kuma bazaka ta’ba samun abinda kakeso ba domin bazan tab’a rabuwa dakaiba yanda ka batamin budget kaima saina tarwatsa duk burinka i dare you kafadawa Abba duk lokacin daka gaji da zama dani.

Koba’a fad’aba maganganu na sunshigeshi cikin b’acinrai ya kamo dantsen hannuna duk biyun ya matso dani dafda fuskarshi yace me kika d’aukeni? zakice inkai mace d’akina cikin tsiwa nakalleshi nace yadda kad’aukeni cikin mamaki yake kallona na fizge jikina na wuce na barshi atsaye cikin mamaki.

Tun wannan lokacin na daina yin duk inda zamu hadu dashi.

HISHAAM

Hishaam yarinyar nan zarginkafa take am sorry to say zama fa zargi haramun ne kuma kafi kowa sanin haka nifa ina bala’in jin tsoron yarinyar nan Hishaam karta qwacemin kai shukra ke wadannan maganganun a gefe ina tuqi zan kaita gida harga Allah banso shiga gonar yarinyar nan ba dondai shukra ta matsane kuma banason b’acinrai tun ranar banqara ganintaba wani abin mamaki bantab’a ganin tana magana da daya daga ma’aikatan gidannan ba bakuma ta fita ko’ina sannan kullum da asubha karatun Qur’an nintane ke tashina abarci saboda bedroom dina da nata qofa kawai ta rabasu.

Yau a gida naci abinci mom ce ta shigo tana tsaki nace mom meya faru tace a abinhaya na dawo wai direban bashida lafiya. Yawwa boy dan Allah jeka d’aukomin ni’ima a makaranta mana ba musu dukda dai banson shiga cikin yara a motata na tafi harqofar ajinsu na tsaya ita ta fara fitowa tsayawa tayi tsaf tana kallona cike da mamakin ganina wani dan ajinsune ya fito bazaifi sa’antaba yace uncle wannanfa batason kallo kagane ni’ima ce tafara masifa bakasan yayana bane haushine ya kamani na dubi ni’ima nace mom tace inzo in d’aukeki kuma banason bata lokaci

Zee ce taje tace anti Hanaan mubi uncle Hishaam mu tafi baza’a zo d’aukarmuba yau tace “kibishi nizan tafi kawai” da sauri ta fara tafiya ta barmu a tsaye ina kallon su zainab tabi bayanta wasu y’an ajinsu suka bisu abaya suna cewa yau gorgeous ranta ya b’aci muje mu rakata daya ya karb’i jakar ta d’ayan kuma sai zuba zance yake na rasa meyasa sainaji raina yayi mumminan b’aci

Da gangan na bada musu qura na wuce ni’ima ta leqa tanamusu dariya raina ya qara b’aci na take burki da qarfi tayi gaba ta buga kai jikin dashboard cikin haushi nace why don’t you grow up you are so annoying “sorry Yaya”  tace ina kaita gida bantsaya shiga gidaba gidana na wuce zan shirya inkoma aiki. D’akina na wuce nayi wanka na fito ina goge jikina sheshshekar kuka nakeji can qasa qofar d’akina na matsa dake cikin dakinta inajin sheshshekar ta ahankali

Jikina ne yayi sanyi wani lokacin inason yimata wasu abubuwan amma sai inrasa amfanin hakan kasa fita nayi dr Sadiq nayiwa magana yayi covering d’ina kwanciya nayi inajin motsinta cankuma sai shiru

Jinayi inason ganinta yarinyar ce hartama fini jidakanta tsaki nayi na miqe ahankali nake tafiya qofar falonta na farko na tura sainaji a kulle nace au fita tayi kenan mukullin qofar na d’auko na bude na shiga ahankali abin mamaki tana zaune a carpet tayi tagumi gashinta ya rufe fuskata da kafadunta gaba daya Masha Allah nace bansanma nafada ba gyran murya nayi ta juyo a tsorace ido ta tsareni dashi ciki mamaki da tsana gashinta ta nad’e ta dauki mayafi ta rufe ta dubeni cikeda tsiwa tace tsarin naka hayar kenan?

Narasa ma meya kawoni can idea tazomin nace ina kallon ki kina yawo da wasu yara harkuna hada kafada ko? Meye matsalar ka da hakan?babu nace tace to don Allah karka qara zuwa nan wlh nagaji da ganinka arayuwata kuma duk sanda naganka hakan baya haifar da alkhairi. Maganar ta daki zuciyata nace eh amma ai kinason ganin wasu qarti ko?eh tafada da qarfi

Saboda qartin su suka damu dani kuma duk matsayinsu dai bankaisu gidan waniba ko ba kamar waniba daya dauko wata ya kaita gidansa. Iyakacin quluwa na gama quluwa nace idan kika cigaba dayimin rashin kunya wataran zan cire bakinnan ta murguda bakin tace wannan bakin wanke hannu ka ta’ba ne nace kokuma ka ta’ba ka wanke hannunkaba tace koma dai meye yafina budurwarka na kasa bata amsa ta wuce ta bani guri.

Sam kwanan nan ya kasa gane kansa tana yawan yi masa rashin kunya amma saiyaji cewar ita ka’dai ta iya hakan kuma abin ya fara daina bashi haushi wani lokacin ma saiyaji ya bashi dariya sam yanzun bayason zama inda Idris yake saboda yana yawan magana akanta shikuma yanzu haushin abin yakeji sam Idris bashida hankali.

A bangaren shukra kuwa ta sanar dashi babanta ya amince ko yanzu yakeson aurenta abin mamaki maimakon yayi murna saiya cika da mamaki hardai shukra ta kula da hakan tace love ko baka farinciki ne?

Ko ka’dan kawai dai ina matuqar mamakin yadda kikayi convincing dinsa ya haqurane yanzu kibani lokaci saina shiryawa Abba na tukunna.

Yau juma’a da wuri suka tashi a makaranta gidan ya amina zee tajata suka tafi suna shiga suka nannade hannun riga ya amina ta sasu kwab’in d’anwake

Hanaan na kitchen taji ya amina tana masa waya ashe mayen d’anwake ne ko minti sha biyar baiyiba sai gashi+

Suna kitchen ita da zee ya amina tace akawowa baqona d’anwake asa mai dayawa da quli-quli yaji kuma ka’dan don bayason yaji dayawa zee ce takawo

Tunda ya faraci yake santi can yace kai sister baku taba d’anwake me dad’in wannan ba
Hanaan tana kitchen tana murmushi for the very first time yau yaci abincin data dafa tanata mamakin yadda yake wasa dasu yake sonsu bata ta’ba ganin wannan side dinnashiba shiyasa take kishi da ni’ima ganin irin sonda yakemata

Ya amina tace toyaya?yace everything normal saidai ba ruwa muna kitchen tace a kawowa baqona ruwa na had’a a tray nacewa zee kai masa tace tab keda mijinki nida bashi ruwa ta qara qwallowa ko babu hali? zee ce ta turoni har bakin qofa kamar zan kifo nayi burki karaf muka ha’da ido ya kafeni da manyan oily eyes dinsa na qaraso a hankali na aje ruwan ya amina tace to ke mijinki yace kinfimu iya girki saboda haka daga yau kidinga bashi abinci inna qara ganin qafarsa zan koro mikishi tari Hishaam ya fara

Ruwana miqa masa ya karb’a yace amma ai nace kanwa yayi yawa qaramin yaronta Abdul yace kai uncle banji kace kanwa yayi yawa bafa

Suka dinga tsokanarshi ana mishi dariya

Bayan mun gama muna gyara gurin zee ta dubeni tace anti Hanaan rayuwarki tana burgeni wlh babu wanda ke takura miki kije inda kikeso a sanda kike so kiyi duk abinda kikaga dama

Na nisa nace zainab rayuwata ta daina burgeki ki nemi alkhairi wato akwai tsananin takaici arayuwar daba Wanda ya damu dakai kuma hakan bashi yake nuni da kayi abinda kaga dama bane

Wato zakiyi mamaki matanda basu kaini komiba a kaisu store suyi shopping a d’ebar musu yaran su abiya masu kudi akaimusu kayansu mota ana rungume dasu nikuwa sai yaran shago

Kuma duk abinda nake bashida labari akaina kinga badan inada ilimin addini ba sai inyi abinda naga dama komai ki roqi alkhairi

Ya amina ce tashigo tace Hanaan mijinki zai tafi gida kije ku tafi baki na turo nace nifa ba yanzun zan tafiba tace to yau na koreki hannuna ta kamo zee ta d’auko min jakata daman tsaf nake abakin qofa na zura takalmana yana harabar gidan yana waya dayan hannunsa a aljihun wandonsa na dade ban qare masa kallo ba sai yau

Dauke kaina nayi saboda banason yaga ina kallon sa na juya masa baya ji nayi ya gama wayar na juyo da sauri kallona yake wucewa nayi zanshiga baya don banta’ba shiga mota dashiba ke! yace na kalleshi cike da tsiwa nace Hanaan!Hanaan sunana

Okay catch ban yi auneba ashe mukullin mota ya cillo min yayi sa’a ya fa’do a hannuna yace get in and drive whaaaat…? Yace yes am not your driver.so am i? Whatever nafada tare da zagayawa bangaren driver na tada mota tundana fara tuqi ban kalleshi ba amma inaji ajikina ni yake kallo.

A junction danja ta tsaidasu kanta ta juyar bangaren sa hadeda kare fuskarta hannun rigarta ta sauke Hishaam ya qura mata Ido anan ya gano wanine ya mayancewa kallon ta haushine ya kamashi da mamakin yanayin data shiga lokaci d’aya

STORY CONTINUES BELOW

Danja na bada hannu ta matse shi ajikin gini ta tsorata shi ta wuce abin yayi matuqar burge Hishaam yakama dariya ta dubeshi ta gefen ido bata ta’ba ganin dariyar sa hakaba sai dai murmushi. Batasan yadda akai ba saita sami kanta dayin murmushin itama saidai batason yagani

Me gadi don gulma har leqe yake yagansu tare sai kirari yake musu Hanaan tabashi ku’di Hishaam ya dubeta yace donme zaki bashi kudi oooh sbd ya miki kirari ta tab’e baki tace aiba maroqi bane ma’aikatan kane

Kyautatawa ce ooooh kinason impressing d’ina ko? murmushi tayi tace tab’dijan saikace banida aiki duk abinda zanyi bazaga hakan ba to why zanyi Westing time aena kaje wanda kakeso tayi impressing dinka but not me saita lura kamar beji dad’in maganar ba

A daidai nan tayi parking ya fita da alama sauri yake ya wuce part dinsa. Wucewa tayi itama zuwa bangaren ta safar ta cire da takalmin ta daga rigar gabadaya zata cire tari ya qwacewa Hishaam yana tsaye abayanta da sauri ta juyo tana sauke rigar cikin kunya da tsoro ya lura ta kasa kallon sa wannan kunyar kuwa ta gaskece? ko shukra batajin kunyarsa hakan bayansa  ya juya da sauri

Cikin haushi tace sallama fa? knocking fa? for God sake….woaa easy girl ya daga hannuwansa i didn’t see anything ya fara matsowa tace mekake buqata yace “where’s my key”?
Oh tace ta d’auko tace catch ta jefeshi da qarfi amma kafin ya sameshi ya cafe bataso hakanba yace oops you missed

Matsowa yaqarayi yace kidinga qulle qofa kafin ki canza kaya kuma ga gurin canza kaya can ya nuna da hannun sa gya’da kai kawai take ta matsu yabar gurin

Harya juya ya juyo hannun sa ya miqo ya shafa cikinta yace “what’s this”? Yayi winking idonshi ɗaya yana smirking, cikin tsoro ta kalleshi dariya yayi  sai a lokaci tasan duk abinnan dasuke cikinta a buda yake ta rintse idonta da qarfi tace noughty yafita yana dariya harda wani rufo mata qofa

Fita taji ya qarayi tace yanzun hakama gurinta ya tafi kanta ta kalla a mirror ta rufe fuskarta tana murmushi. Tanason qamshinsa da murmushin sa shiyasa wani lokacin bata jin haushin budurwarsa sosai sbd shi’din abin aso shine kowace mace zata iya fadawa tarkonsa

Badan miskilanci bama aida yanzun yanadasu dayawa. Ranar cikin farinciki take komai har dare suna fara waya da Amal ta bugo jirginta

Da daddare ya dawo ya gaji sosai ya gama duk abinda zaiyi yunwa ta sakoshi gaba bayason fita donhaka yafara neman abinda zaici amma be samu komiba kwanciya yayi yace bazanci jagwalgwalon wannan yarinyar ba

Danwaken nan ya tuno da sauri ya tashi ta dakin baccinta yaso ya shiga yayi tunanin karya bata tsoro

Zagayawa yayi ta babban falonta ya shigo cikin san’da Hanaan ta gama cin abinci kenan tana kitchen tana wanke kwanuka taji motsi abayanta kasa juyawa tayi sbd tsoro
Cikin sa’a frying pan ne dama a hannunta yana zuwa dab da ita ta juyo cikin zafinnama ta daga da qarfi zata sauke masa ya riqe cikin zafinnama

Yace waike are you a fighter or what? babu abinda kika iya sai dukan mutane? idanunta data rintse ta bude ahankali sannan ta fara ajiyar zuciya ido ya kafeta dashi tayi saurin jan’yar b’ingilar rigarta

Da sauri ta wuceshi ta zura doguwar riga ta rufe kanta tana fitowa ta taddashi atsaye a inda ta barshi

Nesa dashi ta tsaya tace agidan hayafa ba’a sneaking haka musamman ma da daddare fitilar kitchen din ya kunna ya bude fridge yana dube dube

Yace za’a sami danwake dariyar qeta Hanaan tayi tace a’a zadai ka’dan sami abinda zaka samu darajar maqwaftaka

Angaya miki komai nakeci inbakacin abinda ka samu saika haqura ai tahowa yayi har inda take yace waike bakisan yanda ake lallabani ba tab’e baki tayi tace ai wanda yake lallabaka shima lallabashi kake ai nifa?
Ko a gianmu lallabani ake cikin tsokanarshi tace Mama’s boy tsuke fuska yayi danya lura yarinyar nason rainashi dayawa daf da ita ya matso harta d’an tsorata yace meyasa kikeda tsiwa ne?banason tsiwa ta kautadda kanta gefe tace wannan maganar zaka iya fa’dar ta ko daga nesane murmushi yayi ganin yadda zuciyarta ke bugawa yana iya gani yace sbd me?tsaiwata akusada ke tanasaki jin wani abune game dani?nan da nan tafara blushing fuskarnan ta koma kamar package d’in marshmallow daman abinka da fara da gangan ya qara matsarta yanason gano hakan ya canka kenan hannuwanta tasa da qarfinta ta turesa ta wuce tana daidaita numfashin ta sbd karya gane a microwave ta dauko abincin ta sa masa a dining

Harta gotashi zata wuce yace haka zakibar qofarki abude tace to meye amfanin rufewa tunda gaka ka shigo uninvited guest to inna daukar miki wani abinfa tace feel free ta wuce

Akwance take amma ta kasa komi jitake kamar ta koma wajensa amma tana tsoron wulaqanci tanajiyoshi sama sama yana rufe mata qofa bayan ya kwanta a dakinsa tajisa yace thanks for the food dad’i ne y isheta nata gama murna ba tajishi yana but the food is too spicy

Shiru tayi masa kamar tayi bacci.

Sam yanzun bayajin dadin zuwa wajen aiki saboda idris na matsa masa da zancen ta besan meyasa ba bayason hakan dan haka ya dena keb’ewa dashi saidai su zauna da team dinsu gabadaya

Yana mamakin yawan tunanin ta dake damunsa kome yakeyi yanzun sai kawai ya fa’da tunanin ta hakan yana damunsa babban abin mamakinma shine yanzu ko shukra intana hirarta sai yaji hakan yana masa dad’i inkuma kishiyar maidad’i take fa’da sai yaji bayaso

Yauma kamar kullum sunfito ya tafi zekai shukra gida motar shiru saboda ya fuskanci akwai abinda ke damunta kwana biyu. Can tace ka fa’da mata? Ya dubeta cikin rashin fahimta yace pardon? Tace eh ina nufin ka fa’da mata kana sonta?

Wai me kike nufi? ni da wannan yarinyar? Allah ya kikyaye shekaruna sun kusa ninka natafa oh come on shukra. Kana nufin bakasan kana sontaba? sam bazan iya sontaba kunyar hakan nakeji zata rainani kuma kinsan how much na tsani raini

Ko shiyasa naga ta qaro rashin kunyar ta….. Daman ku mata irin idea dinku daya for God’s sake yaza’ayi…… amma kuma….no shukra it’s just your suggestion
Cikin farinciki shukra tacigaba da hira dashi shikuma sam saiya rasa me yasa kamar something is missing but he don’t know what was that thing

Haushin yarinyar yakeji ganin wai kamar shi ana zargin wai sonta yake sam ya daina yadda su hadu ko zaije bangarenta saiya tabbatar ya shammaceta ko ya saci kallon ta daga nesa.

********************************
Kwanci tashi asarar me rai har mun shiga s.s.three mun kusa cinye second term babu abinda ya canza arayuwata banda abinda ya qaru musamman da ya maryam ta haihu

Saikace wata kishiyata ya Hishaam harna fara murna yadda alaqata dashi ta fara tafiya amma daga baya sai gabadaya ma nadaina ganinsa ko a gidansu da muka ha’du rannan dayake babu idon Abba be kulaniba

Ni kuwa dukda zuciyata tana azalzalata akanshi banta’ba yadda ya ganiba harna saba da rayuwata a haka.

Illar hira da budurwa akan mata qalubale gareku maza

Babu abinda shukra bata saniba na tsakanin Hishaam da Hanaan shiyasa bata wasa da damarta ko ka’dan wajen burmashi akanta

Abangaren idris kuwa aikin na shukra yana masa kyau donshi jira yake tsautsayi yasa Hishaam sakinta ta yadda ya aureta inyaso ko uwar watsece ayi.Kamar kullum yauma bayan sallar asubha karatun Qur’an nina nake rerawa kuka ne ya qwacemin mai sauti ganin rayuwata mecike da rashin ma’ana da amfani agurin na kwanta hargari yayi haske

Qofar dakinsa dake cikin d’aki na na bacci na d’auko mukullin ta na bude ganina kawai yayi adakin a kwance yake ko riga babu ajikinsa cikin magagi ya fara murza ido yana kallona cikin rashin sanin me nake sonyi

Koda ya wartsake ya fara qaremin kallo ban damuba saboda daman sana’arsa ce kallo na tashi zaune yayi mur’dadden jikinsa ya qara bayyana+

Da wasu layika a shafaffen cikinsa da sauri na kautadda idona d’aga kansa ya sakeyi yayi ajiyar zuciya yace where are your manners?

Haushi ya kamani nafara magana. Nasan banida muhimmanci agidannan amma inada muhimmanci agurin wanda ya kawoni cikin rayuwar gidannan

Azatona hakan shizai zaunar dani agidannan amma ina, na gaza da muzantacciyar rayuwar nan na sauka daga kan alqawarina na bazan rabu dakaiba.

Kukane ya fara qwace min, na matuqar gajiya so ina ganin abinda yafi zan bar gidannan kafinnan ka sakeni dukda ba’a matsayin mata nake agurin kaba niba jahila bace nasan da auren ka akaina donhaka ka sakeni nagaji da igiyoyin aurenka da ka daureni dasu

Kaje kayiwa budurwarka albishir da nabar rayuwarka har abada

Da sauri ya d’aga kansa ya dubeni nace eh bazan qara zama dakaiba dantsen hannuna ya damqa duka biyun ya fizgoni har jikinsa

Yace tunda kika shigo rayuwata sanda kikaso to sai sanda naga dama sannan zaki tafi ai nagaya miki.

Nima kuma na gaya maka ni ba property d’inka bace banbancina da property kenan bakada iko dani, kuma bakada iko da jikina cikani………matsewa yaqarayi na rintse ido don azaba yace kinason ha’da ni da mahaifinane?

Eh a shirye nake da in ha’da ka da kowa don in rabu dakai hannuwana nakeson qwacewa amma ina. Na dubeshi nace you are hurting me hannuwansa ya d’aga duka biyun kamar me surrender yace okay na yarda zaki rabu dani nima zan rabu dake amma ban shiryaba kibani lokaci

Hanaan ta dubeshi cikeda takaici tace wata goma sha uku be ishekaba ko saboda kana zuwa gurin wata to ni babu wanda nake zuwa gurin sa…..

Yamutsa fuska yayi ya dubeta da fad’in ke ……..me kike nufi? ko ke da kike mallakina bana sakaki a lissafina ballantana wata haramun karki kara zargina domin bakida hurumin yin hakan

Ficewa nayi ban manta da buga masa qofa da qarfi ba

Tun ina shiryawa buhari yacemin yazo amma kodana fito harabar gidan atsaye naganshi ta gabansa nazo zan gifta qofar motarsa ce ta tokareni

“get in”  yace nace “no thanks”  na wuce gabana yasha yace “don’t test my patience”  nace “but you can’t force me to get into your car”

“of  course I can”

“you  can’t”

“i  can”

“You  can’t”

kuma idan natafi bazan dawoba be saurareni ba waje yaje bansan me yacewa buhari ba kodana fito ya tafi motarsa ya tsayar daidai inda nake ya budo qofar na zumbura baki na shiga ina qunquni

Har cikin makaranta ya kaini saidaya dangane da qofar ajinmu ihu yan ajin suka farayi anacewa saurayina ya kawoni kai kundace yasmin tace amma naga kuna kama nan da nan idea tafado min nace yaya nane tace dan Allah ina sonshi shades dinsa ya saka yaja motarsa batare da ya kula kowaba narasa dalilin dayasa ya kawoni yau sam basu barni nayi karatu ba majalisa akayi qawayena kowa abinda yake fa’da daban kai dama akwai wanda ya dace da most beautiful girl d’in makarantar mu

STORY CONTINUES BELOW

Inda Yasmin tayi shiru can tace Hanaan ya kuke dashi kince wanki ne Hanaan ta fara inda inda tace he is my cousin yasmin tace yess saida tasa kowa ya juyo saboda ihunta

Tace amma fa irin kallon dayake miki Hanaan kodai sonki yake? tsaki Hanaan tayi tace to yana da budurwa yasmin tace ai indai bake bace ba matsala

Saboda me? saboda inkece zan iya barmiki shi amma inba keba babu wadda zan iya barwa shi aiko kyasha wulaqanci donko ya iya wulaqanci bani numbarsa zee ce qiri qiri ta hanani bada numbarsa amma saidata bani wasiqa da alqawarin zan kaimasa

Ina dawowa daman lokacin dawowarsa beyiba kan gadonsa naje na dora masa na gudo

Har nasaka kayan bacci saijin mutum nayi adakina da sauri nayi crossing hannayena a qirjina sbd tsaro dariya ya fara harda rufe baki da bayan hannunsa yamin kyau sosai amma saina haɗa rai

Haushine ya kamani nace what are you laughing at? cigaba yayi nace “what’s so funny” ? yace “chill there’s nothing to see” tareda nunani gabadaya na niyya nayi infita inbar masa dakin caraf ya riqeni ya jawoni har saida jikina ya ha’du da nasa cikin hanzari na matsa baya wasiqar yasmin ya manna min ajikina yace meye wannan?

Murmushi nayi nace“wasiƙa ce qarin masoyiya ka samu” a hasale yace kece me kawowa mijinki wasiqar wata? qarfina na ha’da na tureshi nace“miji kuma? Kuma budurwa ai saidai kayi qari amma daman ai kanada ita “ke bakida kishine”?

Lebena na ciza na qasa harnaji zafi nace kishifa kace uh? Katab’a kishina? To why did I have to waste my precious time on someone like you? Dunguri na yayi da yatsansa yace “What do you mean by someone like me?”

Kibud’e kunnuwanki da kyau ki saurareni by the time kika qara karbo wani saqo kika kawomin sai na gayawa kowa a makarantar alaqata dake….kinjini ko and you know i can do it right? “go-ahead…… am fine with that as long as zaka iya cewa ni property n kace”

Zangaya musu ke matanace. mamaki abin ya bani kafin nayi magana ya bar dakin au daman yasan ni matar sace?

Yanzun bana bari mu ha’du balle yace zekaini makaranta

Yau yayansu yasmin ne yakawomu gida sauri nake sbd ina zargin lokacin period dina yayi da sauri na shige gida daqyar nayi bacci sabida marata yanzun abin qaruwa yakeyi

Yana zaune a office yau sbd yayi aiki ya gaji gashi har lokacin yana tsaye zamansa kenan wayarsa ta dauki qara da hanzari ya daga ganin mekirannasa

Bayan ya gaisheshi ya sanar dashi ya koma gidansa yanzu za’a kawo Hanaan gida sbd batada lafiya Abban sane

Besan meyasa ba maganar ta dakeshi sosai cikin hanzari yake tuqin yana zuwa motar makarantar tana tafiya da sauri ya shiga aqofar bedroom dinta yayi karo da takalmanta da d’anhijabinta a rigingine ta kwanta kanta yana lilo inda gashinta ya zubo har qasa

Da sauri ya qarasa inda take a gefen kanta ya zauna ya fara dubata yace “meke damunki? ido kawai ta bishi dashi duvet din ya janye da qarfi fararen cinyoyinta suka bayyana a fili yayi saurin rufe idonsa sbd yanayin dayaso shiga lokaci guda

Ahankali ya bude idon cikin son ya sake gani amma kash taja duvet ta rufe kafar kallon ta yake ta lumshe dara daran idanunta red lips d’inta yake kallo how he wish to kiss….em

Babu zato yaji tace “Stop…. stop staring”, shaquwa yafarayi “fucckk” ya fa’da a hankali ganin ta kamashi

Inane ke miki ciwon? Ba ko’ina qara yaye rufar yayi da sauri ya miqe ganin yadda tasa mayafinta ta tamke cikinta kwancewa yayi da sauri yace zaki cutar da kankifa da qarfi yayi maganar sbd ya tsorata da abinda tayi

Kina ciwon marane? fuskarta ta rufe sannan ta d’aga kanta kallon ta yake cikin mamakin abinda take yi “daman yana miki hakane? kai kawai ta sake d’aga masa yace “you are so childish”

STORY CONTINUES BELOW

Dagata yayi cak ya zaunar da ita ya bata magani tasha ba’a jimaba tafara kwarara amai duk yabi ya rikice kamata yayi ya kaita toilet yana qoqarin taimaka mata

Amma Sam taqi ta rufo qofar tunda ta fito da rigar wanka yake qare mata kallo ganin yadda fatarta take qyalli ga gashinta ya manne a wuyanta da fuskarta

Gyara gurin yayi yace yakamata a samo helper tace no thanks indan yau ka kwashe amai ne tunda ayya ta rasu nake kula da kaina ni dazaka rage mazan daka cika gidannan da suma da yafi sauqi

Kaya tayi niyyar sawa amma yaqi tafiya kwanciya tayi ta rufa sbd ta farajin yanayin zazzab’i sosai

Tunani ya wuni yanayi abinda yafi damunsa yanzu duk wata haka takeshan wannan wuyar amma ko labari bashida shi ga yarinyar da dauriya abinda be iyaba bayajin zai iya barinta ita ka’dai donkomai zai iya faruwa

Kuka take sbd azaba ga kewar ayya ko tashi ta kasayi ballantana ta taimaki kanta sai marar kawai take dafewa qofar dakin ya bude ya shigo kinyi bacci?

Shiru tayi masa kamar tayi bacci kusa da ita ya zauna hucin jikinta yaji yayi saurin yaye rufar dagata zaune yayi ya jinginata da jikinsa yabata magani tasha

Zamewa ta ƙara yi ta kwanta tareda kamo hannunsa ta ɗora saman marar ta ta danna da ƙarfi tace “danna min Please banida ƙarfin dazanyi da kaina” saurin janye hannunsa yayi yace “this is not the right thing to do”

Ruwan ɗumi ya samo ya ɗauko clean towel a wash room ya tsoma a ciki ya matse kaɗan ya kwance rigar tata ganin pant ɗinta da ƙasan ƙirjinta na neman fitowa yasa shi kawar da kansa gefe.

Inda ya laluba ya fara danna mata ruwan ɗumin sannu kan hankali daɗin hakan na ratsata inda da ta fuskanci ya matse saita kamo hannunsa ta dannan a gurin har bacci ya fara ɗaukanta sbd ta galabaita

Gashinta daya mammanne mata yake gyara mata yana kallon ɗan ƙaramin bakinta data turo gyara kwanciyar ta tayi sai kawai yaji cikinta yana ƙugi da alama yunwa ce.

Kitchen yaje cikin sa’a ya sami ragowar soup ya dumama ya kawo mata daqyar ya tashe ta tasha ta kwanta daya gefen ya zagaya zai kwanta ashe batayi bacci ba ta juya cikeda rashin kuzari murya qasa-qasa tace “Mr Hishaam what are you trying to do”? “Can’t you see I’m just trying to have some sleep”.

Whaaaat? Cikin rashin kuzari ta yunqura ta zauna tace gaskiya bazan iya kwana dakaiba murmushi mesauti yayi yace baki yadda da kanki bane tace na yadda da kaina kainedai ban yadda dakaiba

Nan d’akina ne nikuma nan gidanane marairaicewa tayi please banida qarfin fa’da dakai ahaka nake rayuwata agidanka. Ahaka kuma kikeson kicigaba da rayuwarki? juyawa tayi ta kwanta tana qunquni i don’t want anybody’s sympathy tace

Rawa jikinta yake cikin dare ayya ta fara kira a hankali tausayinta ne ya kamashi ya matsa ahankali ya jawota jikinsa bacci take besami matsala da hakan ba zafin jikinta ke shigarsa da wani sabon yanayi rikicewa ya nemi yayi be ta’ba kusanci da wataba kamar yadda yake ayanzun qoqarin tashi take hakan yasa ya rufe idanunsa

Ahankali ta fara bude idanunta jin mutum kusa da ita akansa idanuwanta suka sauka dim light din dakin ta bata daman qare masa kallo dama dae Ace wannan ba tausayi bane so ne, da nafi kowacce irin mace sa’a a duniya abinda take saƙawa kenan

Gashin idonsa dake matuqar burgeta ta shafa ahankali ta sauko kan hancinsa tana shafawa ahankali ta sauko ta shafa bakinsa ahankali ta bude idonta dayake qoqarin rufewa da kansa ta kafawa lebensa idanu ko ba’a fadaba tasan takamu da sonsa tuni amma bata tsammanin wani abin kirki daga gareshi koda yasan hakan bata tsaya tunani na biyu ba ta matsa ta ha’da hancinta da nasa tana shaqar qamshinsa datake masifar so

Kamar numfashinsa zai dauke yarinya qarama tana neman jamasa aiki alokacin da hancinsu ya ha’du numfashinsa ya nemi ya sarqe bakinta yaji akan nasa hakan yasashi bude oily eyes dinsa agajiye kallonsa take idonta a nasa cikin nutsuwa take kissing dinsa kamar soko kallo kawai yake binta dashi tayi tsammanin hakan daga gareshi daman kamar sweet haka take jin lips ɗinsa ahankali take sucking har saida taji zazzaɓin na neman dawowa janyewa tayi daga jikinsa ahankali tayi murmushi ganin irin shock ɗin data sashi a ciki ta juya bayanta

STORY CONTINUES BELOW

Ya dade yana kallon bayanta he needs more abinda zuciyarsa ke fa’da kenan amma sai ya gimtse ya shafa kansa miqewa yayi zaifita tace

“thanks”

yace “night”

tace “good night doc”

Gabantane yacigaba da faduwa ta dafe tana fadin mena aikata haka daman yana ganin banida kunya shikenan rintse idanunta tayi harta samu bacci yayi awon gaba da ita

Kwana yayi yana mamakin yarinyar kar ko….ahaba dai kodayaje dubata da safe abinya bashi mamaki har break fast ta ha’da komai kallon sa take ya matuqar yimata kyau green shirt ce ajikinsa da black wando jeans da black jacket sai wani green shawl

Are you done checking me….. out….?

Fuskewa tayi tace ina kwana mamaki ya bayyana a fuskar sa yace daman kin iya gaida mutane? tace bismillah ga abinci kamar yaqici ya tuna kullum saiyaje gida yau idanyaci anan ya huta

Komai yayi dadi chips din ya soyu yadda yakeso saidai soup en yayi yaji ruwa kawai yake kwankwad’a dariya takesonyi masa yace what’s so funny? tace saikace yaro jiba yanda yaji ka’dan yasaka gigita inda babu shiri dariyar ta subuce gaba daya

Ya miqe yana fadin kisha magani akan kari zan neman miki appointment gurin dr hadiza tunda field enta ne saiki ganta____kuma in kika ƙara bani anything too spicy a bakin nan naki zan goge shi tass ya shafa leɓanta da yatsansa kafin tayi magana ya fice

Yau koda yaje gida beci abinci ba ni’ima ya kalla yace bazakice ya jikin qawarkiba? gabadayansu ita da mom suka juya suna kallonsa kafadarsa ya d’aga alamun tambaya irin me ya faru kuke kallona dinnan

Ni’ima tace lallai yaya kanajida Hanaan kodan yau tabaka abinci? eh din marakunya au dagaske kaci abincin ta lallai Kam yau anci jagwalgwalo kece zakice mata jagwalgwalo to wlh ta iya girki yadda bazaki ta’ba iya kamotaba garama kisan me kike ciki mom kallon sabon yanayinsa kawai take haushi kamarya kashe ni’ima saboda ta fuskanci yaya ya fara tarewa matarsa tace to wlh samarine da ita a ajinmu da sauri ya galla mata harara ta gimtse abinda ta fara fa’da inda babu zato hakan ya faɗar masa da gaba

Awajen aiki office din shukra yaje yanason suyi magana kasancewar tanada ragowar patient yasashi jira bayan suntafi ya fara mata magana shukra ina ganin abar maganar aurennan for now…. sabida me?

Saboda bazan iya adalci atsakanin mata biyuba tunda nakasa yiwa dayama

Kiduba kiga yarinyar nan batada lafiya amma ko sani banyiba shukra ina tsoron karya dokokin ubangijina

Daman kuma yaudarar ta nayi na aureta ranar dana bata labarinki saidatayi nadamar aurena a take, banason incigaba da aikata sabo dagangan

Ka yarda ka kamuda sonta yanzun? bansaniba ko inasonta abinda nasani shine akwai wani abu tsakanina da ita dabazance gashiba kuka shukra ta fara

Shukra ki d’auka qaddararmu Kenan don yanzu innace zan rabu da ita zaizama kamar rashin adalci kuma hakan bayana nufin mun daina zumunci ba kenan.,… Hishaam kabar zancennan kawai kabarni nikadai for now please ba musu ya fita yaja mata qofar

Dariyar idris ce takatse Mata kukan daga bayan labulenta ya fito yana tafa hannu yana dariya yace me nagaya miki? kika karyatani shukra ta goge hawayenta tace aidaman nasan halinsa indai akwai wani abu saiya fa’da donshi besan wani abu b’oye b’oyeba

Amma kaicon Hishaam sam banso shigarda boka cikin al’amuranaba saidai kashh yayi gaggawar sanar dani nasa tsarin nikuma yanzu kobayaso saiya aureni

Dariya Idris ya qarayi yace gaskiya babu adalci ki nace kice kamammen mutum kamar Hishaam saiya auri ragowa irinki ahasale shukra tace kai shashasha yamuke dakai dakake harin qaramar yarinya bayan kasan halinda rayuwarka keciki Idris yace garani aure tayi ta rabuda mijin zan aura kekuwa ragowace ba auren kikayiba amma gara bazawara dake

STORY CONTINUES BELOW

To yanzu aganinka zai saketa bayan munyi sakaci dagani harkai to dukwaye yajawo?nice amma yanzu zangyara komai inmun gama komai da hadiza zakaji zancen.

Ciwon marar ne ya dawo ruwan dumi tasha ka’dan ta kwanta tana jira kozai shigo.

Bayan yasa kayan baccinsa masu taushin gaske farare tas ahankali ya tura qofar dakin irin kwanciyar jiya tayi amma yau ta d’aure gashinta kusada kanta yaje ya zauna ahankali ya lura ta rame ka’dan yace kinji sauqi? ta girgiza kai murmushi yayi yace ke wace irice?

Qarya kakeson inyi? Amma at least saikice alhamdulillah to alhamdulillah. Yawwa kokefa matswa tayi kan pillow ta kwanta tace asubha ta gari kusada ita ya matsa ta zazzaro masa ido yace wazaki gayawa ido shima yafara zazzaro mata nasa dariyace takamata

Matsawa ta sakeyi amma yana sake matsowa hartakai qarshen gadon hannunta ta miqe ta tokare qirjinsa tace ya isa hakanan yace hey if you don’t mind i can help you

Cikin sonjin wane taimako zaimata tace inaso mezakabani? gyran murya yayi yace if you want we can have… a…. s-word cikin rashin fahimta tace what does this s-word means?

Dariya yayi sosai harda dafe ciki saidaya gama yace how old are you? seventeen tace da confidence enta wata dariyar yafara yanason rufe bakinshi haushi ya kama Hanaan tace bansan kanada yawan dariyaba saiyanzun

Yace seriously… shekarunki sha bakwai tace yep! yace shiyasa bazaki ganeba kunnen ta yamatso yarad’a mata s-word means sex we can have a sex

Tureshi tayi tace Allah ya kiyaye tareda rufe fuskarta da duka hannayenta. mamakinta yake sosai ganin yadda taji kunya da tsoro akan d’an abinda ya fada beqarasa tunanin saba tace amman yau a dakinka zaka kwanako? Sabodame?

Saboda i need some privacy uhm privacy manya yafada yana kwaikwayanta haushi abinya bata tashi tayi ta dauki pillow zata koma kan kujera ta kwanta

Yace easy girl kikoma gadon zan kwanta anan ba musu taja bed sheet din data nannade jikinta dashi ta koma yana hardeta kallon ta yake

Gabad’aya abinda yake zargi akan tarbiyyar ta ba haka bane irin kallon dayake mata sam ba hakatakeba kenan abbansa yasan hakan sam bata qoqarin yimasa shishshigi a al’amuran sa daman ya tsani hakan shiyasa bayayin yanmata sam sbd mace tana kulashi to yasakata a sashen marasa aji

Ya fuskanci tayi bacci lallabawa yayi kangadon ya kwanta yana kallon fuskarta mecike dakyau da kwarjini yana tunanin daren jiya tsigar jikinsa ce ta fara tashi yace “damn my hormones” juyawa yayi amma ya kasa bacci saida kyar bayan ya rungume ta ta baya.

Ba sallah zatayi ba shiyasa bata tashiba hargari ya fara haske ka’dan huci takeji kusada ita muskutawa takesonyi amma kamar an daureta daqyar ta bude idonta mamakine ya cikata ganin yadda suke kwance qafarsa ta hagun akan qafafunta kansa akan kafadarta ita kuma tana kan hannunsa na dama na hagun kuma shit..yanakan cikinta kokuma fatar cikinta qugi cikinta ya farayi

Taqura masa ido batako qyaftawa motsi yafara tayi qoqarin ta matsa amma ina ko motsin kirki ta kasayi ahankali yake bude idonsa rufe nata idon tayi kamar me bacci quramata ido yayi yana kallon tsabar kyawunta gabansa na faɗuwa sosai, tabbas tafi dayawan matan daya sani komai halayen dayake kwadayi yake zargin batadasu suma ahankali yafara samunsu

Yanayin su ya kalla sai yayi murmushi tunawa da batasan ya kwanta a jikinta ba, hannun sa ya kalla a cikin rigarta a hankali ya sake shafa cikin ta tsigar jikinsa na tashi.

Runtse idanunta tayi sbd yadda yanayin ya shige ta hancinsa ya goga a wuyan ta yanajin daɗin ƙamshinta na wani abu da take amfani dashi me strawberry kamar aci ya ɗaga kansa yana kallon lips ɗinta ya haɗiye yawu daƙyar.

Kamar ya tashi amma ya kasa matsawa ya ƙarayi ya manna mata Kiss, a goshinta murmushi tayi ta gyara kwanciyar ta da alama tanajin daɗin baccin ta. Inji shi fa 😜

Kyau tayi masa ya ƙara matsawa yana ƙare mata kallo yanajin zuciyarsa na wani irin bugu inda itama Hanan kejin hakan, kamar wanda magnet ke ja ya ƙara matsawa har saida leɓensu ya haɗu guri guda.

Atake tsigar jikin sa ta mimmiƙe ya kasa janyewa ya kuma kasa komai yana kallon ta jikinsa yayi wani irin sanyi gaba ɗaya.

Kasa komi Hanan tayi itama zuciyar ta na azalzalar ta tanajin kamar ta janyoshi jikinta sosai karya fasa abinda yayi niyya koba komai zata rage jin kunyar Kiss ɗin data masa itama.

Abinda yake mata shi ya katse mata tunani tareda kasa daurewa ta buɗe idanunta instantly, leɓenta na ƙasa yake tsotsa a hankali cikin nutsuwa tareda matse ta gam a jikinsa kamar yana tsoron kar a ƙwace masa ita.

Idonta ta waro hakan yasa ta ɗan buɗe bakin ta kaɗan cikin ɗumbin mamaki hakan  yabashi damar shigar da bakinsa gaba ɗaya cikin nata yana smooching lips ɗinta ƙasa da sama tareda zura harshensa cikin bakinta yana yi yana shafa cikinta da hannun sa dake cikin rigarta har yanzu , inda tayi saurin runtse idanunta tareda damƙe rigarsa data kama sbd wani irin yanayi da take ji .

Tsoro ne ya dira a ranta lokaci guda musamman ma data tuna ita ɗin ba kowa bace a gurinsa bata wuce abar wasan sa ba.

Da kansa yaga abinda yake yi ya fara wuce ƙaida yayi saurin matsawa yana kallon ta numfashinsa na fita da sauri da sauri, saurin tashi yana janye hannunsa ahankali tareda kallon idanunta data runtse su taƙi buɗewa yana shafa sumar kansa gami da lashe lips ɗinsa da yake jin test ɗin nata akansu .

Tunda ya fita yake mamakin abinda yayi, ji yake kamar ba shi bane yau banda tunanin ta kuma babu aikin da yake faman yi har abin ya fara bashi haushi “she’s just seventeen fa what’s wrong with me”?

Nothing yabawa kansa amsa, koda yake ai laifin ta ne ba nawa ba sbd ita ta fara hakan ni kawai ramawa nayi. Murmushi tunanin ya bashi yana tuƙi yana murmushi har ya isa

Koda yaje asibiti wajen hadiza ya wuce ya farayi mata bayani. “Hishaam kasani basai namaka bayaniba kuma aurennan fa ya dade ai ya kamata ace kayi wani abu kodon lalurar nan ga Maryam har yarinyar ta tafara wayau”

You know at this stage she can easily get pregnant and she’s too young for that. Amma it’s better ai zatafi samun sauqi fiyeda yanzu

Amma idan babu damuwa zanbaka maganin hausa kakai mata, nifa kinsan bana shiri da abinda bayada k’a’ida eh amma ai ita tanada tunda ayya ke karba mata inkayi mata bayani tasan maganin ai datayi wanka zata fara sha

Kawai dondai kince tasanshine amma da gaskiya bazankai ba Hishaam ga shayi yace aa yaukuma harda shayi inada aiki badan hakaba da nasha to katafida flask en mana saika aiko dashi nasanka akwai son shayi ba musu ya d’auka tareda yimata godiya yafice

Da sauri shukra ta fito daga inda ta buya suka rungume juna tana fad’in munjefi tsuntsu biyu da dutse daya to sauran aikin idris kuma.Lokacin daya dawo gida goman dare zatayi bayan yayi parking daya daga cikin yaran gadan ne yazoda gudu yace ranka yadade ga mukullanka yallabai Idris ne yakawo yace mantasu kayi shiru  yayi kafin daga baya yace tun yaushe ya kawo yace tun rana

Lokacin dayazo matar gidan tananan? a’a yau taje makaranta besameta ba harya fito daga wanka mamakin yadda akayi ya manta mukullansa yake bayan kullum yana tare dasu

Yau azaune ya ganta tana game awayanta miqa mata yayi ta karba tana kallon sa yace ya hadizace ta karbo miki tace ayya tana karbo miki lebenta ta ciza da qarfi Hishaam ya dubeta yace” hey don’t do that”

Harara ta watsa masa tace meyasa ka gayamata? to qarewa ba ita zata dubakiba kuma naga yayarkice eh dukda haka juyawa yayi zaifita tace yau kaine kashigo dakinnan dabana nan daidai kunnenta yace aljanina ne ta juyo da sauri hular kanta ya cire yayi gaba da ita yana baki iya godiyaba sai fa’da ko?+

Nagode, haryayi nisa ya jefo mata hular akan fuskarta ta fa’do ta janye ta juya amma harya fice zuwa d’akinsa

Na dade ina tunanin yadda rayuwata take canzawa kamar baniba wannan yarinyar akwai tarin baiwa atare da ita….wayata ce ta dauki qara shukra ce da sallama tafara maganar ta cewar tanason ganina

Kasancewar yau bata dadewa a aiki nayanke cewar muhadu agidansu

Video take nunamin awayarta nayi saurin miqamata nace sanin kankine bana son kallon irin wadannan abubuwan nafi girmama mutunci akan rashinsa

Maganar bataimata dadiba amma hakan bai dameniba murmushi tayi tace ba abin mamaki bane kaima gobe aga naka kaida matarka haka

Kamarya kenan? na tambaya tace wannan badalar daka gani qawar matarkace tayi ta tura musu haka sukeyi da qawayenta to naji ance layi yazo kanka shiyasa nayi maka rugakafiSam bazatayi hakaba, to kayi bincike

Da sauri na koma gida nayi sa’a batanan dakinta nafara dubawa abin mamaki anboye camera gurare daban daban sanyi naji qafafuna sunyi

Ko a film banta’ba ganin rashin mutunci irin wannan ba wato nafara sakarmata fuska, wato ita ba zuciya daya take zaune daniba kenan yanzu harzata iya nuna sunna ta da ita ashe abinda nake zargi akanta yama wuce hakan

Har rawa jikinsa keyi sbd tsananin bacin rai ya kai qololuwar quluwa sam jiyake ya tsaneta gaba daya yayi nadamar fara bata dama yayi nadamar saurin rabuwa da natsatsiyar budurwarsa ta shekara da shekaru

Yayi alqawarin tsayawa da ganin iya gudun ruwanta

Yau jinin ya dauke mata tayi wanka bayan ta dawo daga makaranta agidan ya amina suka wuni sai gabda maghrib da dawo gidan zuwa dare har tayi shirin bacci taji baidawoba hankalinta ne yakasa kwanciya

Wayarta ta jawo cikeda fargaba sbd bata saba kiransa ba ta danna lambarsa ringing daya ya d’auka

Assalamualaikum ya amsa aciki shiru tayi yace babu abinda zakice kika kirani maganar batayimata dadiba amma tace lafiya naga baka dawoba….daman kina gadinane?

Maganar mace taji akusadashi tace kana ina? Ina tareda shukra meye? Qit takashe wayar zuciyarta ta dafe sbd yajin datake mata

Wato ni abar wasansa ya d’aukeni kenan to yaje ya qarata da ita maganinta ta d’auko cikin rashin sanin ta kurba ta sake kurba ta mayar fridge ta aje

Da’di ne ya ishi shukra jin abinda Hishaam ya fadawa Hanaan tace aranta inkikasha maganin nan yau in Allah ya yarda saiya kamaki da megadi inyaso inga qarshen soyayya

Zafi ta faraji kamar da wasa har saida ta fara cire kayan jikinta wasa farin girki toilet ta shiga ta sakarwa kanta ruwan sanyi har saida jikinta ya mutu murus ta fito mai ta d’auko zata shafa wata irin sha’awa ta taso mata abin harya fara wuce hankali sbd yadda takeji.

STORY CONTINUES BELOW

Tunaninsa ne yafara fa’do mata da yanayinsa da qamshinsa da yadda takeji aduk sanda ya tab’ata da rayuwarsu tad’an kwanakin nan kamar zautacciya da rarrafe cikin sauri ta d’auko wayarta babu tunani na biyu ta qara dialling numbarsa be dagaba sai akaro na biyu ya amsa dakyar yace ya akai? muryarsa ta shiga jikinta tayi ajiyar zuciya tace kadawo yanzun please

Lafiya? a’a… meyafaru?bansan me yafaruba “bakida lafiya ne?” eh banida lafiya kuka tafara yace shshh ya isa am on my way insha Allah

Cikin hanzari ya miqe yacewa shukra zanje gida tace au zaka shiga cikin plan d’inta kenan? yace ko ka’dan batada lafiyane nikuma likitane in kuma lafiyarta qalau fa? wannan ya rage nawa juyawa yayi ya bata guri ya tada motarsa sai gida

Zagaye take adakin tana tunanin sabon yanayin dake tattare da ita abin bata mata rai yake nawa take qarar tsaiwar motarsace ta katse mata tunani kamar ta fita amma ta tsaya cikin hanzari ya bude qofar ganinta a tsaye yasashi yin turus abakin qofar dagudu tazo ta rungume shi yanayin yadda ta rungumeshi da qarfi yasa har saida bayansa ya jingina da qofar d’akin

Yayi qoqarin cireta amman besamu hakanba sbd ba qaramin riqo yashaba har a hannunsa yakejin bugun zuciyarta ahankali ya banbareta daga jikinsa cikin idonsa take kallo atsorace yake kallonta sbd gabadaya yanayinta ya canza

Meyake damunk..,.. bakinta yaji akan nasa tana kissing dinshi cikin nutsuwa rintse idonsa yayi abinya shigeshi sosai maganar shukra tayi amsa kuwwa a kunnuwansa yayi sarin janyewa ya rabata ya wuce tareda tamke fuska musamman ma daya lura haryanzu cameras dinnan sunanan

Tabaya ta rungumeshi tabbas yana daf dafadawa komarta hannunta ya zame ahankali ya juyo ya fuskanceta d’anyatsansa yasa ya d’aga habarta yace meke damunki? kai kawaita girgiza masa ya daga girarsa duk biyun cikin alamun tambaya bakida lafiya ne? taqara girgiza masa kai “ko kina buqatar wani abune? jajayen idanuwanta ta kalleshi dasu shima ita yake kallo cike da sonjin me zata fa’da

Cikin rawar murya tace I…. i… need….i…..a…. s-word sosai ya daga girarsa har goshinsa yadan tattare yace whaaaat?

Kuka tafara tana magana bansan meke damunaba kawaidai……..kinga dantsen hannunta ya kama ya kaita bakin gado ya zaunar da ita yace kinga shi wannan abin dakike buqata yanzun it’s not possible da sauri ta kalleshi cikin karaya tace why?

Yace akwai dalilai da dama wanda inkinji bazakiji da’di ba so ki haqura da safe zamuyi magana go to sleep now tashi yayi ta kamo hannunsa da sauri tace i insist ha’da ransa yayi ya dawo yace

Kinga da farko wannan abinda kikeso yana buqatar haduwar zuciya bata jikiba kawai kina sona? bansaniba ko inasonka amma dae am damn sure that banta’ba tsanarkaba kuma koba komai ai akwai aure tsakanina dakai ai

To ni inada matsala da hakan cikin rashin fahimta take kallon sa miqewa tayi tareda fuskantarsa tace mene matsalar?

Dafarko dae kinga am not ready to be your puppet me kakeson cewa?kinfi kowa sanin abinda nake nufi. Batajin zata iya doguwar hira yanzu sbd abinda takeji qaruwa kawai yake matsawa tayi ta riqo hannunsa tace please

Yace kinga inma nace zanyi wani abu dake to agaskiya babu abinda zanji saboda me? Niba mace bace? Ke macece amma bakida abubuwan danakeso ajikin mace lebenta ta ciza na qasa”may be she knows that she have that affect on me”

Basarwa yayi yacigaba da magana kuma gashi kinyi qanqanta kinsan banason raini shiyasa tunda aka kawoki gidannan bana kallonki amatsayin mace sbd banason irin haka ta faru hawayene ke zubo mata hawayen ya ta’ba yaga na gaskene mamaki yake yadda dukta rikice lokaci guda kamar gaske hakan qara jin haushinta yake sakashi yarfe hawayen yayi yace good night

Da sauri ta qara riqeshi tafara kissing dinshi ahankali batare da zaton zai maida martaniba matsar da ita yayi ta sunkuyar dakanta qasa dukda yadda takeji da ragowar kunya atareda ita

STORY CONTINUES BELOW

Tace meyasa bakajin wani abu game dani kamar yadda nakeji gamedakai? to na yarda ka d’auka masoyiyarka ce da sauri ya kalleta yace babu kyau ai kema kinsani hannun sa ta d’auko tafara shafa jiknta dashi tundaga goshinta ta fara zuwa kan dogon hancinta zuwa pink lips d’inta zuwa wuyanta zuwa qirjint…… stop shine kawai abinda ya iya fitowa daga bakinsa sbd bazai iya jurar hakanba. Are you not confident?ko kadan

Hannuwansa tasa akumatunta ta ha’da goshinta da nasa tace yanzufa ya girgiza kai murmushi tayi tafara kissing lips dinsa hartafara jansa batare da ya saniba inda hakan ya tunzurashi ya tureta da qarfi yace kozakiyi tsirara agabana bazaki ta’ba samun komai daga gareniba towel din jikinta ta damqa zata warware cikin hanzari ya riqe hannunta yace are you that desperate?

Hawayene kawai ke fita a idonta tace meyesa kakeyin haka yace banason kiyi abinda zaki dinga jinkunyana nan gaba

Amma ai kasan this is not haramun”kibari bayauba today am not interested and am not in the mood

Ficewa yayi yabarta anan qara ta kwalla da qarfi had’eda sakin wani gigitaccen kuka tashi tayi zata fita ta tafi koma wajen waye musamman yadda mazake kallon ta koda yaushe ashe hakan nada manufa. Can cikin ranta abubuwan da ayya ke fa’da mata ke dawo mata sabr sabr sabr

Allahumma la sahla ta farayi ta durqusa tareda hade qafafunta guri guda tana rabzar kuka toilet ta shiga tareda sakarwa kanta ruwa zama tayi dirshan qarqashin shower abin yadan fara raguwa ka’dan ta fito ta fara salloli nafiloli da addu’o’i

Yanajin kukanta daya fita yace yarinya kekikayi disgracing kanki abanza amma yakasa gane wannan al’amarin me kamada gaskiya. Sam yakasa bacci harwajen uku ahankali ya leqa dakin cikin san’da yatarar tayi bacci fuskannan tayi jajir sabida kuka.

Kodata tashi tunanin abinda ya farune ya dawo mata kuka ta sake garza sosai hadida nadamar da bazatai amfaniba niyya tayi taqi zuwa makaranta amma tanason ganawa ta musamman da yan’uwanta a sanyaye take shiryawa harta gama horn taji yanayi ta leqa ta barandar ta tasama yana tsaye cikin qananan kaya yayi matuqar kyau simple shirt yasaka fara tas da black pants hannun sa yaqara zurawa ya danna horn

Kamar ance ya d’aga kansa sai a idanunta kallon kunya baqinciki tsana Hanaan ke aika masa dashi kallon ta yake yana karantar halin datake ciki horn din yasake dannawa jakarta ta ajiye ta koma ciki tareda jan labulen da qarfi ta rufe abutaji ya fa’do mata aka tayi saurin dubawa camera ce qarama tana blinking red light

Hannun ta narawa ta d’auka tana dubawa kamar mahaukaciya tafara dudduba ko’ina acikin dakin kowacce corner saidata sami camera guda d’aya kuka tafashe dashi me sauti cikin hanzari ta tashi ta fita barandar amma ya tafi qafa ta buga ta dawo ta zauna ta rasa meke mata dad’i

Kenan sbd ya nunani gurin budurwarsa shiyasa ya wulaqantani to ya akai yasan hakan zata faru…………kardai…… innalillahi

Amma anya Hishaam zai cutardani kuwa zuciyarta ke saqa hakan idankuma yayine donki fa’da halaka ya sami hujjar rabuwa dakefa? Kuka tasaka me cinrai da d’aga hankalin dukme sauraronsa

Anan ta wuni har bayan azahar sallamar Zee ce ta farfado da qamewar datayi cikin dumbin tunani

Dagudu tazo ta rungume Zee tana wani irin kuka ta dad’e tanayi kafin Zee tacirata akaraye tace anti Hanaan meyasameki kinga yadda kika gigice kuwa yau kawai

Kukantake har lokacin, zaunar da ita tayi ta bata ruwan sanyi tad’an sha ka’dan tace anti Hanaan menene? babu abinda ta b’oye mata daman daga ita sai Amal su kad’ai ne sirrin ta aduniya

Kamata tayi sukahau sama ta d’auko mata maganin Zee tace cewa yayi a inda ayya ke karbowa Hanaan ta d’aga kanta Zee tace to zankai gurin me maganin mamanmu yarsokoto abinda tafada shizai tabbatar da gaskiya ko rashin gaskiya acikin wannan al’amarin

Ko wanka yau banyiba sbd banida sukunin hakan faten dankali nadanyi da daddare nasha sama na hau acikin d’akina naganshi baqinciki da tsanarsane suka tasomin

Juyawa nayi zanfice daga dakin yace meyasa yau bakije makaranta ba? sbd me kake tambaya na? Sbd ina biyan kudina kinga there’s no way indau asara banza naba ajiyarsa nayi ficewata harnazo steps din bene ya damqoni da qarfi

Daman ni’ima tafadamin samari kikeyi a school yau naje d’aukanki nagani da idona

Inyi samari ko kar inyi wannan zabina ne bakada kaico dahakan na ta’ba tambayarka wakake kulawa inka fita ko nataba tambayarka labarin karuwark……..huci naji dab da kumatuna sauran qiris ya saukesu akai nayi sauri matsawa nace wlh duk ranar dakayi gangancin tabani duk abubuwan danafi shekara ina biyesu saisun bayyana

Kuma ni ina tsoron Allah ba irinkabace matuqar da aure akaina bazanyi shashanciba, ka kwana adakin tunda kanasonsa rab’ashi nayi nayi wucewata.

Yau tunkafin ya shirya ta gudu makaranta taje ba da’dewa Zee taje basu sami lokacin zantawa ba anata karatu sbd sunkusa gamawa. Koda aka tashi gidanta suka wuce

Zee tace aunty Hanaan inamejin kunyar gayamiki cewa abinda kike zargi akan uncle yazama gaskiya . Rawa jikin Hanaan yafarayi tana zargin hakan amma tana addu’ar Allah yasa ba hakan bane me kikeson kice zainab? yarsokoto ta fadamin wannan maganin yanada hatsari yawanci tsofaffi ke amfani dashi ko wa’danda basa sha’awa kwata-kwata

Durqusawa tayi tana kuka tace Zee menayiwa mutanen duniya gabadaya kowa ya tsaneni haka?wane mugun hali gareni? Zee kifadamin tsakaninki da Allah Zee babu yadda za’ayi ace kowa bayasonka ace bakada mugun hali rungumeta Zee tayi tana cewa jarrabawa ce kawai.

Zee betashi wulaqantani ba saida nafara sonshi Zee tunda kike aduniya kintabajin namijin dakeson matarsa ta aikata zina sbd ya kafa hujja da hakan ya rabu da ita

Zee ina yawan yafewa mutanen dake cutata shiyasa suke ganin gazawata wallahi wannan karon saina rama abinda yayimin. A’a Hanaan kodai kimasa magana kuji matsalar a inda take

Matsala agurinsa take duba kiga wannan camera na tsinta adakin baccina wake shigowa nan inbashiba ya bani magani ya saka camera ya wulaqantani sbd yanason ya nunawa budurwarsa toni bazan nunawa duniya shiba amma wlh saiyayi nadamar abinda yayi.

Mezakiyi? Musulunci yayarda da ramuwa matuqar zaka rama dai dai da abinda akayi maka saiyasha wannan tonic en kuma bazai ta’ba samun abinda yafi buqataba a wannan lokacin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page