GANI GA WANE CHAPTER A

 GANI GA WANE CHAPTER A

® *INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION~I.W.A*📚

*{ onward together}*

_*GANI GA WANE…..*_🌷

_*STORY & WRITING ~ BY*_

_*AUFANA*_✍

_Whattpad@Aufana8183_

_*Devoted to -*_ *Maryam Abdallah & Maryam (mamu gee) my granny’s*

✨✨

_*DASUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JINK’AI salati da d’aukaka sukara tabbata ga shugaban farko da karshe fiyayyen halitta annabin muhammad ( S.A.W),, to masoya en uwa dakuma abokanan arziki gani nasake dawowa da sabon littafina mai suna { GANI GA WANE } ina rok’on Allah yanda nafara lafiya yasa nagama lafiya kura kuran dake ciki ya yafeman ameen.*_

+

💫

*GARGADI*

_*Banyardaba kuma ban amintaba wani ko wata suyi amfani da wani sashe ko b’angare na wannan littafe ba, kuma ban amintaba wani ko wata sudauki wannan labarin suyi film dashi idan kuma nakama mutum yamin haka to wallahi ransa zaifi na kuturu b’aci dafatar za’akiyaye*_

_*Jinjina ta bangirma ga zak’ak’uran matasan marubutan matashiyar k’ungiyar nan wato [ INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION ] Allah yak’ara maku basira da hazaka yakuma kareku daga sharrin dik wani abun sharri mutum ne ko aljan ameen yh rabbi*_👏

_*PAGE 1~2*_

_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_

*D’AN TSOKACI*

Garin ZAGA d’aya ne acikin garuruwan dake cikin k’asar KEBBI, kauyene wanda ke kunshe da abubuwan ban al’ajabi acikinsa fulani ne amma bak’ak’en fulani saidai masu kyau ne sosai, garine dakeda rik’on al’ada shekaru masu yawa dasuka shud’e kakanninsu sunada wata mummunar halayya sam basa k’aunar a haifamasu y’ay’a mata saidai maza saboda su aganinsu y’ay’a mata basuda amfani illa aji dad’i dasu kokinaso ko bakyaso namiji dole yaji da’di dake koda kuwa ba mijinki bane, wannan kazamar halayya ta wulak’anta y’ay’a mata su basu daukeshi komaiba wannan dalilin yasa kowa na garin baya k’aunar a haifamasa ‘ya mace wani ma idan anhaifamasa kashewa yake batareda kowa yasaniba,, to a wannan zamaninma har yanzu wasu dagacikin mutanen wannan garin basu bar wannan muguwar halayyarba kubiyoni domin jin cikakken labarin.

***** ***** ***** *****

*GUNDARIN LABARI*

Malam GARSO d’aya ne daga cikin mutanen dake zama a garin ZAGA manomine sosai kuma makiyayi ne, y’ay’ansa biyu mace da namiji macen sunanta NANA ASMA’U sai namijin kuma FARUK wanda wajen haihuwarsa ne mahaifiyarsu tarasa ranta HALIMATU,,,…

Malam Garso mutum ne mai kuzari dikda mutuwar matarsa ta tabasa sosai amma hakan baihanasa ya juri yadinga kula da yaransa saboda yasan komai yai zafi maganinsa Allah. Matar mak’ocinsa Inna tabawa itace ta karb’i faruk tana kula dashi har yakai shekara takwas sannan tamaidashi,,,..

Asma’u nada shekara goma sha takwas mai garin ZAGA yahadata aure da d’ansa ABUBAKAR wanda ake kira da Habu batareda sanin junansuba kuma batareda k’aunar junansu ba, wannan auren kuma yai daidai da zuwan turawa garin ZAGA domin kawomasu ilimin BOKO to ance doka daga gida take farawa hakan yasa mai gari dole badan yasoba yabada yaransa biyu akasaka sunansu acikin waenda zasuyi ilimin BOKO habu da yayansa umaru,, bikinsu da sati biyu suka wuce babban birnin k’asar KEBBI habu kuwa sai murna yake saboda dama garin yaishesa gakuma wannan shegen auren had’in d’akamasa,,,..

Bayan sati hud’u datafiyarsu habu asma’u tafara laulayi gashi kuma itakad’ai ce a cikin gidan gashi kuma tana wahala sosai amai kasala ganda gakuma zazzab’i da ciwon kai wanda kedamunta sosai, abincinta yakare yanayin mace mai laulayi takanyi sha’awa dakuma kwadayin abinci kala kala dakuma kwalama amma itakam tahak’ura ta yafe saboda tasan basamunsu zatayiba,,,..

STORY CONTINUES BELOW

******* *******

Yau kimanin wata biyu kenan datafiyarsu habu amma har yanzu basu ba labarinsu takasa hakura dik en dabarunda takeyi na mata tasamu abinda zata kaiwa bakinta na salati tayi yanzukam tura takai bango,, da dare bayan tagama sallar magrib tayafa mayafinta tawuce gida, bayan taje nantasami mahaifinta tamasa bayanin komai hak’uri yabata tareda yimata nasihohi dakuma tinatardaita ladar dake cikin zaman aure idan mutum yai hak’uri, jikinta yai sanyi sosai nantake ta tashi takama hanya takoma gidan mijinta batafi 15 minute’s dakomawa ba mahaifinta yabama k’anenta Faruk abinci mai yawa da kud’i yace tasamu sana’ar da tai saboda ta rik’e kanta nan takarb’a tareda yin godiya,,,..

Haka kuwa tai dasafe ta’aika faruk kasuwa yayomata siyayya aranar tafara y’an sana’oinmu mata nacikin gida, cikin ikon Allah kuwa tasamu karbuwa dahaka tacigaba tana rufawa kanta asiri batareda wani ko wata sunji sirrinta ba Abba Garso kuwa kusan dik bayan sati d’aya saiyakai mata ziyara domin ganin halinda take ciki kuma yatallafa mata sosai,,,..

Kwanci tashi asarar mai rai yau kimanin wata goma sha d’aya kenan datafiyarsu habu cikin asma’u kuwa nada wata goma amma har yanzu habu baidawoba,, cikinta ya tsufa sosai dikda tsufansa amma baihanata yin sana’arta ba,,,..

Wata ranar jumma’ah ne damisalin karfe 5:00 na maraice asma’u na zaune a gidanta aka aikomata taje gida ana nemanta bata wargantaba kuwa tad’auki mayafinta tawuce,,,..

Daisarta tahango malam tanimu mijin inna tabawa wato makofcinsu a tsaye shi da sauran mutane abokanan Abba garso, k’arasawa tai cikin gidan dasauri taga inna tabawa tazo tarungumeta tana kuka cikin rud’ewa da kid’imewa cike da tashin hankali tafara tambayarsu abunda ke faruwa,, hannunta inna tabawa takama suka fara tafiya gunda su malam tanimu suke a tsaye nan aka bud’e masu hanya suka k’arasa abu tahango lullub’e da farin kyalle alamar gawa cikin kid’imewa tafara tambayarsu “Abba tanimu ina Abba na ina Abba na yake ne…?” dakyar inna tabawa ta tsayarda kwallan dake zuba a idanunta sannan tafara yiwa asma’u magana “asma’u kiyi hak’uri dik abunda yazoma bawa to jarabtace daga ubangiji idan yajure kuma saiyacinye wannan jarabawar” inna kardai kiceman Abba nane kwance anan kardai kiceman Abbana ne yamutu. “asma’u kwantarda hankalinki dan Allah mutuwa ai dolece agun kowanne bawa wajibice abunda akeso kawai ajure ayi hak’uri,, Abban ki yarasu sakamakon hatsarinda sukai ahanyarsu tadawo gida yaje kasar ADAMAWA ne wajen kai d’anuwanki karatun allo bayan yakaisa yajuyo a hanyarsu ta dawowa gida ne sukai hatsari su goma sha shida ne acikin motar goman dik sun rasa rayuwakansu shidan kuma sunsami rauni sosai to mahaifinki yana cikin waenda suka rasa rans….” ai batako k’arasa ba asma’u tafad’i wanwar ak’asa somammiya,, cikin sauri aka d’auketa akashiga d’aki daita ana zuba mata ruwa tajima sosai sannan ta farfad’o tafara kuka mai tsuma zuciyar mai karatu,,,…

Saida akayi sallar isha sannan aka sallaceshi aka kaishi makwancinsa ubangiji yasa mucika da imani ameen,,,..

Aranar dai asma’u taci kuka kamar ranta zai fita yanzu ba uwa ba uba d’anuwanta dazata gani taji sanyi kuma yamata nisa wayyo Allah kaine gatana kashiga lamarina kakuma tausayaman, tafada cikin kuka mai ban tausayi,, tajima anan saida dare yai sannan Abba tanimu yace ta tashi ta tafi gida nan yasaka aka rakata tawuce,,,..

Bayan kwana hud’u angama karb’an gaisuwa asma’u na zaune gidanta daga ita sai wani yaro almajiri maisuna AHMAD wanda suke kira da Amadi d’an malam Malam tanimu ne yabata shi saboda yatayata zama yana d’ebemata kewa kasancewar malam tanimu malami ne mai makaranta harda almajirai lokacinda Abban asma’u yace zaikai d’anuwanta ADAMAWA karatun allo baiji dad’i ba yaso yabarshi agunshi amma yaki ashe wannan k’addara ce kekiransa,,,..

Around 12:00pm suna zaune a k’ark’ashin bishiya kwatsam saiga Habu yashigo hannunsa rik’e da wata jaka, cikin mamaki ta mik’e tsaye domin tarbansa saidai wani abin mamakin datagani ne yaisaurin dakatarda’ita,, wata matace tagani a bayansa gwangwazazza y’ar bariki daka ganta kaga cikakkiyar ‘yar duniya,,,..

Tafiya take cikin wani salo tana yiwa asma’u wani kallon 3 saura kwata hannunta kuma sakad’e dana habu,, dakyar asma’u ta’iya cemasa “barka da zuwa” ko kallonta baiyiba bare ya karb’a mata yawuce d’akinsa tareda wacca suka shigo atare,,,…

Zama asma’u tai ranta namata k’una yayinda zuciyarta kuma ketamata sak’e Sak’e kala kala “to wannan wacece ita kodai wani auren ne yai nikuma yamanta da labarina inkwa hakane wallahi yacuceni” bata ankara ba taji kwallah nabin fuskarta saidai tayiwa kanta alk’awarin idan har bai nemeta ba to bazata tab’a nemanshiba,,,..

Bayan ta sallami Amadi yatafi itakuma tashige d’akinta tai kwanciyarta, tana kwance saigashi yashigo d’akin batareda ya kalleta ba yace “wannan dakika gani matata ce dan haka wallahi karki kuskura kice zakimata rashin mutunci dafatar kinji abunda nace sannan kitashi kimana girki ki doramana ruwan zafi tanaso tayi wanka yanzunnan Inajiranki” yana gama fad’ar haka yajuya Yafita,,,..

Haka ta tashi taje tad’ora girki da ‘yan sauran cefanenta da malam tanimu ya’aiko mata,, murhu biyu tai dole saboda icen basa kamu sosai, bayan tagama girki sannan tadora ruwan zafin,,,..

Bayan tagama yazo yad’auki abincin duka baibarmata komaiba yawuce bayan yakai sannan yadawo yazube ruwan zafin yatafi,, baiwar Allah kuma komai bata cemashi ba har yafita,,..

Alokacinda matar tafito zatashiga ban d’aki mamaki yakama asma’u sosai ganin k’aton cikinta wanda zaikai kimanin wata bakwai zuwa takwas aranta tace “wato ashe batun yanzu ya auretaba tinda harga ciki” afili kuma murmushi kawai tai ta tashi taahiga d’akinta,,,..

Kimanin kwanansu biyar amma ba abunda yake had’a asma’u da habu ko gaidashi tai saiyaga dama yake k’arb’awa wulakanci kuma kowacce rana danata kala abinci idan ta girka wanda yagadama yake ragemata Amadi ne yafahimci haka yaje yafad’awa malam tanimu abunda ake ciki baizoba kuma baice komai ba amma kullum da dare sai d’an malam Amadi yakawomata abinci a b’oye,,,..

Kwanansu bakwai da zuwa habu yashirya yakoma yabar matarsa anan tareda asma’u ammafa yaiwa asma’u kashedi akan karta kuskura tabar matarsa mai suna Maimuna tayi aiki mai wahala wai cikinda take dashi yana wahaldaita,, hmm to itakuma nata kenan ba ciki bane Allah i shiryardamu,,..

Aranarda yatafi da dare nak’uda ta tada asma’u har safe tana abu d’aya maimuna taga har 10:00am bata fitoba amma tak’i zuwa tadubata ko lafiya kuma tasan ba halinta bane dikda cikinda take dashi amma idan tai sallan asuba bata kwanciya bacci fitowa take koda batada aikinyi,, saida aka tada su Amadi daga makaranta yazo yatararda ita acikin wannan mawuyacin halin dasauri yajuya dagudu yaje yafad’awa inna tabawa cikin sauri inna tabawa ta shirya suka fita,,..

Koda sukaje kuwa har yanzu dai haihuwar batazoba sai wahalar kawai, misalin 2:00pm Allah yasauke asma’u lafiya ta haihuwa cikin koshin lafiya tahaifi y’a mace kyakkawa sosai mai kama da mahaifinta, saida inna ta yanke cibi sannan tafito ta d’ora ruwan zafi bayan suntafasa tazube takai band’aki nantake tayiwa asma’u wanka sannan tayiwa jinjirar itama,,,..

Bayan ta tsabtacesu sannan takoma gida, girki tamata mai kyan gaske ferfesun naman zabuwa ne da tuwon garin dawa……

#/Vote

#/Share

#/Comment

”’AUFANA for life”’

*I.W.A*🖊® *INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION~I.W.A*📚

   *( onward together )*

   _*GANI GA WANE….*_🌷

_*STORY & WRITING ~ BY*_

     _*AUFANA*_✍

_Whattpad@Aufana8183_

                      💫

_*Devoted to – Maryam Abdallah and Maryam (mamu gee) my granny’s*_

    _*PAGE 3~4*_

_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_

Bayan ta tsabtacesu sannan takoma gida, girki tamata na musamman mai dad’in gaske, ferfesun naman zabuwa ne da tuwon garin dawa da miyar kub’ewa d’anya, girkin yai da’di sosai,,,..+

Bayan tagama sannan tad’auka takoma takaiwa asma’u nan tasakata agaba saida taci abincin sosai, bayan tagama tafad’awa Amadi yaje yakirawo malam tanimu yanacan daji yafad’a masa asma’u tahaihu Amadi kwa bai tsayaba yaje yafad’amasa atare suka dawo,,,…

Saida yadawo sannan suka d’auki asma’u suka tafi gida da’ita, da misalin k’arfe hud’u na rana malam tanimu yashirya yacewa inna tabawa zaije gidan mai gari yashaidamasu fa asma’u ta haihu inna kwa bata masa musuba tace “Allah yakiyaye hanya”  yace “ameen” sannan yafita,,,..

Bayan ya’isa sannan yai sallama wani yaro yafito malam tanimu yace masa “mai gari na nan kuwa” yaron yace aa bayanan. Shuru malam tanimu yai kamin yace “to dan Allah shiga kafad’awa uwargida kace tazo nine malam tanimu zan barmata sak’one” yaron yace “toh” sannan yatafi,, baifi 15minutes datafiya ba saiga wata mata tafito sanye da mayafi ajikinta tana isowa tai murmushi sannan tace “Ah malam tanimu kaine” eh wallahi tababa nine nazone gun mai gari sai yaro yace wai bayanan. “Eh wallahi yad’anyi tattaki ne yaje garin gwandu ziyara ince dai lafiya koh” murmushi malam tanimu yai “ah wallahi lafiya lau dama nazone nafad’a maku sirikarku asma’u ta haihu tasamu ‘ya mace kyakkawa mai kama da mahaifinta sak” shuru tababa tai sannan tace “to masha Allah ubangiji ya raya mana” yace ameen “insha Allah idan mai gari yadawo zansanardashi” malam tanimu yai murmushi sannan yace mata “toh bakomai ni zanwuce” nan sukai sallama sannan yawuce,,,..

Har kusan kwana hud’u da haihuwa amma bawanda yazo daga gidansu habu a rana ta biyar ne tababa tazo da y’an wasu kaya acikin leda nan tabasu hak’uri sannan tad’auki yarinyar tagani tareda sakamata albarka, cikin nutsuwa tadubi asma’u tace “asma’u komai kika gani agun habu da mahaifiyarsa kiyi hak’uri wallahi dikansu basa k’aunarki barekuma tinda sukaji akace mace kika haifa suka k’ara tsanarki wad’annan kayan ma mai gari yabada yace akawomaki da abinda kika haifa gakuma kud’i naira dubu biyar” tamik’a mata kud’in sannan tacigaba da magana “habu yaji kinhaihu amma yace baruwansa dake kuma bazaizoba danhaka kirik’a yarki karki damu dasu” inna tabawa ce tashigo tana fad’in “hmm aidama tini nazaci haka a raina tinda aka kai yarinyar nan banda wahala ba abunda takeyi tin farko idan yasan bayasanta meyasa bai fad’a ba sai yanzu” hakane amma shi mai gari yasan bayaso wallahi amma yace sai anyi auren, yanzu dai tinda abun yazama haka kuyi hak’uri dan Allah yarinya kuma ubangiji yarayata yasanya mata albarka. Suka amsa da ameeen,,,..

Sake kallon asma’u tai cikin murmushi tace “asma’u wane suna kika sanyawa y’arki ne…?” tafad’a cikin fara’ah “nasanya mata KHADIJATUL KUBRAH amma inaso adinga kiranta da KUBRAH”  masha Allah suna mai dad’i Allah i rayamana KUBRAH. tad’an jima tana k’ara basu hak’uri daga bisani kuma tawuce,,,…

Ranar suna har kusan 8:00am ba ragonda zaayanka bak’in ciki yacika malam tanimu asma’u kuwa kuka take sosai saboda bak’in ciki, inna na zaune malam yashigo yakalleta yace “tabawa wannan takaicin yaisheni haka wannan wulakanci ya’isa yarinya kamar shegiya kawai danka haifi y’a mace saikazama abun wulak’antawa, tabawa na yanke shawara zan d’auki ragona danake kiwo nayankawa yarinyar nan”  shuru inna tabawa tai sannan tace “shikenan malam Allah i biyaka da mafificin alkhairi nima nagoyi bayanka” ameen yace sannan yaje yaciro ragon daga inda aka daureshi sannan yajashi yafita dashi aka yanka,,,..

Bayan anyanka ragon angama gyara naman aka kawo cikin gida wannan naman ne inna tadinga d’iba tanayiwa asma’u ferfesun dashi tanaci malam tanimu kuma kusan dik bayan kwana biyu saiyaje daji yaharbo tsintsaye manya yakawo agyarawa asma’u taci, haka sukacigaba da kula da’ita dakuma ‘yarta KUBRAH yar lelen Amadi dan idan yananan bamai d’aukanta saishi,,,..

Satin asma’u uku da haihuwa sukaji maimuna matar habu tahaihu tahaifi tagwaye maza zallah hmm aranar suna kuwa haka sukai shagali da bidiri kwanan habu hud’u dazuwa amma ko kallon asma’u baiyiba bare yazo yaga abunda tahaifa har suka gama bidirinsu suka koma shi da matarsa da y’ay’ansa,, haka rayuwa tacigaba da tafiyarwa asma’u da ‘yarta KUBRAH yayinda inna da malam tanimu kebasu cikakkiyar kulawa,,,..

     *******  *******

Kwanaki natafiya watanni na shud’ewa yau kwanan KUBRAH arba’in da haihuwa tai dub’ul dub’ul da’ita gwanin birgewa hakama asma’u tai kyau sosai,, saida suka k’ara sati biyu akan kwana arba’in sannan malam tanimu yashiryamasu aka maidasu gidansu,, asma’u nakula da ‘yarta malam tanimu yak’ara mata kud’i yace tacigaba da ‘yar sana’arda takeyi saboda ta rufawa kanta asiri,,,..

Satinta biyu da wowa watarana tashirya taje gidansu habu, two balaifi inna tababa takarbeta ammafa inna hauwa kam ko kallo bata ishetaba barekuma abarda ta haifa haka tawuni acan ganin basarki sai Allah yasa tashirya tadawo gidanta,,,…

     ***** **** *****

Yau kimanin watan KUBRAH takwas da haihuwa ta’iya rarrafe kuma barikallah yarinyar kyakkawa ce sosai tasaba da Amadi sosai idan tana kuka dataganshi zakaga tafara tsalle tanaso yad’auketa idan yaje kasuwa ko yaje bara inzai dawo saiya siyomata alawa,, ranar asabar da safe asma’u taga wasu mutane sunshigo sunfara gyaran d’akin maimuna hakan yatabbatar mata da dawowa zatayi nantake taji gabanta na fad’uwa, to kome ta tina oho,,,..

Anyiwa d’akin fentin angyarasa sosai da daren ranar kuwa maimuna ta dawo saidai wannan karon itakad’ai tazo sai yaranta dasuka girma sukai wayo gogan kuma baizoba,, dasafe bayan asma’u tai sallah taje d’akin maimuna tamata barka da kwana, kamar karta karb’amata saikuma ta karb’a da “lafiya” kawai, murmushi asmau tai sannan tawuce d’akinta,,,…

Haka sukacigaba da zama idan asma’u tayiwa maimuna magana saitagadama take amsawa itakuwa bata damuba kuma bata fasa yimata ba,,,…

Ranar jumma’ah around 12:00pm asma’u nad’akinta KUBRAH kuma nawaje tana wasa maimuna na waje itama ak’ark’ashin bishiya, KUBRAH nacikin wasa saita rarrafa taje kan rijiya maimuna na kallonta amma takyaleta harta cigaba da tafiya akan rijiyar hartakai bakin riniyar tana kallonta batazo ta d’auketaba,, cikin rashin sa’a saka hannu da KUBRAH zatayi kawai saitayi suluu tafad’a cikin rijiyar, maimuna na kallo tana wani murmushin mugunta saida taga tafad’a sannan ta taso tazo dagudu d’akin asma’u tana mayarda numfashi tana fad’amata KUBRAH tafad’a rijiya,,,…

Cikin tsananin kid’imewa asmau tafito d’aki dasauri tana kiran sunan KUBRAH sannan tahau kan rijiyar tana lek’on inda zata ganta,, dikda kid’ime ta daburce hankalinta baya kanta dagudu tafita waje tana neman mutane, ko’ina taje bamutane bata jira komaiba tawuce dagudu izuwa gidan malam tanimu k’afafuwanta bako takalma,,,..

Koda ta’isa kuwa cikin sa’a ta tarardashi yafito zaije masallaci tareda almajiransa, a yanayinda yaganta ya tabbatarda akwai natsala tambayarta yake amma takasa bashi amsa shed’arta nema take ta d’auke da hannunta take nunamasa hanya dakyar ta’iya furta sunan KUBRAH……

#/Vote

#/Share

#/Comment

”’AUFANA for life ”’

    *I.W.A*🖊® *INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION~I.W.A*📚

   *( ơŋщąγɖ ɬơɠɛɬɧɛγ )*

  _*GANI GA WANE….*_🌷

_*STORY & WRITING ~ BY*_

     _*AUFANA*_✍

_Whattpad@Aufana8183_

_*Devoted to – maryam Abdallah and maryam ( mamu gee ) my granny’s*_

   _*PAGE 5~6*_

_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIN*_

Jin sunan KUBRAH data fad’a yak’ara tabbatar masa da akwai matsala, sallayar dake hannunsa yamik’awa d’aya daga cikin almajiransa sannan yakalli Amadi yace “kaje kafadawa tabawa tayi sauri tazo tsameni gidan asma’u yanzi yanzinnan” Amadi yace “toh malam” yatafi shikuma malam tanimu yajuya suka wuce,,,..+

Dasuka isama gidan asma’u kasa magana tai sai kwallah dake fita a idanunta da hannu kawai tadinga masa nuna da rijiyar shed’arta taji ta d’auke kawai tazube k’asa wanwar somammiya, hankalin malam yak’ara tashi cikin sauri yarik’o asma’u saboda kar kanta yabugu da k’asa yakwantar da’ita sannan yatashi domin yad’ibo ruwa yazuba mata hakan yai daidai da shigowar inna tabawa, ganin asma’u a kwance yasa hankalinta ya tashi tak’araso dasauri tana tambayar malam abunda ke faruwa,, nan yaimata bayanin iya abunda yafahimta, maimuna ce tafito daga d’akinta cikin kissa da kisisina irinta mata fuskarta dikta b’aci da hawaye tana sharan kwallah tak’araso gunsu sannan tafara masu bayani “Wallahi muna cikin d’aki bamusaniba KUBRAH ta rarrafo cikin rashin sa’a tafad’a rijiya” Rijiya……!!! Suka fad’a atare cike da tashin hankali, innalillahi wa’inna ilaihi raji’un hazbiyallahu wani’imal wakiil abunda malam da inna suka dinga maimaitawa kenan cike da tsintsar tashin hankali,,,…

Dasauri malam yamik’e tsaye yafita itakuma inna tacigaba da kokarin taimakon asma’u domin numfashinta yadawo,, baifi 15minutes dafitaba yadawo tareda wasu maza guda hud’u cikin sauri suka d’akko wani k’aton ice suka d’ora abakin rijiyar sannan suka daura wata igiya mai tauri sosai akan icen, bayan sun d’aura sannan d’aya daga cikinsu yadaura igiyar a k’ugunsa nan yafara shiga rijiyar ahankali har yakai tsakiyar rijiyar,, wani abun mamaki dayagani ne yabashi tsoro dakuma mamaki KUBRAH ce zaune acikin wani rami dake gefen rijiyar nesa da ruwan cikin rijiyar sai raba idanu take tana kalle kalle kaman habu yashiga gaba tabi bayansa, hhhhh Lol,,,…

Bismillah yai sannan yakai hannayensa yad’aukota yadaureta a k’irjinsa da sauran igiyar sannan yafara tafiya sama ahankali har yafito, yana fitowa yakwanceta dasauri asma’u takarbeta ta rungume tana sharan kwallah inna tabawa ma kuka take hakama Amadi malam ne kawai yadaure shima danyana namiji ne amma abun akwai ban tausayi,,,..

Bayan yaron yamik’amasu KUBRAH ne yake basu labarin inda yaganta acikin rijiyar hamdala sukai tareda godiya ga ubangiji saboda wannan ikonsa ne dayaso saita fad’a acikin ruwan tamutu amma saboda yanuna ikonsa saiyagina rame kuma yasakata aciki kuma tazauna dikda yaro akwaishi da kiriniya amma tazauna batanemi ta fitaba, tabbas ikon Allah dagirma yake,,,…

Bayan angama komai malam yabiya yaran suka wuce sannan yazauna yadinga yiwa asma’u fad’a akan karta sake barin KUBRAH itakad’ai a waje idan zatashiga d’aki to tashiga da’ita amma karta sake barinta itakad’ai, ganin komai yawarware yasa malam yafita yawuce zuwa masallaci tareda Amadi inna kuma tawuce gida, suna fita asma’u tagoya KUBRAH nantake kuwa tai bacci,,,..

Tindaga wannan lokacin asma’u batasake barin KUBRAH itakad’ai a wajeba saidai idan Amadi na nan amma ko sallah zatayi da’ita take tafiya d’aki kuma saita janyo k’ofa tarufe saboda karta rarrafo tafito,, kwana uku dafaruwar haka habu yadawo aranar kuma itace dashi tinda waccan tafiya dayai a d’akin maimuna yakwana amma a maimakwon yazo d’akinta saiyawuce d’akin maimuna hakan kuwa bak’aramin b’ata mata rai yaiba saidai tabama zuciyarta hak’uri tanuna kaman abun baidametaba,, da dare kuwa haka tagaji da jiransa tai bacci can cikin dare tafarka tagansa a gefenta murmushi kawai tai tacigaba da baccinta,,,..

Washe gari tin asiba ta tashi bayan tai sallah tad’ora ruwan zafi tai wanka ta tsabtace jikinta sannan tayiwa KUBRAH, bayan tagama kuma shima tad’ora masa,, hmm dayatashi kuwa ko kallonta baiyiba datamasa barka da safiya ma saida yai nisa da’ita sannan yakarb’a yawuce d’akin maimuna dikda ranta yab’aci dahakan dayamata amma batace dashi k’ala ba tasandai komai yai zafi sauk’i zaizo kusa kuma *BAYAN WUYA* sai dad’i,,,…

Haka asma’u tacigaba da hak’uri da’irin halayyarda habu da matarsa ke nunamata wani lokacin saitai kamar tai magana saikuma ta tina da hud’ubarda mahaifinta yamata saikawai tafasa takyalesu idan kuma abun yamata yawa saitashige d’akinta tai kwanciyarta,tsakanin KUBRAH da mahaifinta habu kuwa ba’acewa komai dan yanda yakeji daya ganta gwanda yaga mutuwarsa kokad’an baya k’aunar ganinta abunka da yaro kuwa dikwanda yakejin sanyi agunsa shi yake mannewa idan ka nuna baka k’aunarsa shima bazaiko kulaka ba haka KUBRAH take batadamu dashiba idan Amadi baya nan tana a bayan asma’u kotana wasa,,,…

Haka rayuwa tacigaba da gudana yauda dad’i gobe ba dad’i, malam tanimu yasaka asma’u taje takoyo sak’a cikin watanni k’alilan kuma ta’iya dayake tanada basira sosai, bayan ta’iya kuma yasiyamata keken sak’ar saboda aganinsa zatafi samun kud’i idan tana sak’ar, cikin wata daya tasak’awa KUBRAH riga da wando da hula tasak’awa Amadi riga abun gwanin birgewa sunyi kyau sosai Amadi kesiyomata kayan sak’ar a kasuwa idan tai kuma shike mata tallah dahaka takesamun ‘yan kud’inta tana rufawa kanta asiri,,,..

     *****  *****  ******  ******

Ahalin yanzu KUBRAH tacika shekara uku da haihuwa asma’u kuma tanad’auke da ciki na tsawon wata bakwai zuwa takwas, maimuna tasake haifar d’a namiji wanda yaci sunan mai gari Ibrahim suna kiransa da Gyalbarki  ‘yan biyu kuma sun girma sosai dan girmansu yafi shekarunsu yawa ammafa rigimammi ne sosai basajin magana kokad’an idan KUBRAH taje wajensu saisu dinga dukanta suna yakutarta wani lokacinma harda cizo, tin ranarda sukamata wani cizo harsaida hannunta yai jini tin lokacin batak’ara zuwa inda sukeba kuma maimuna batace masu komaiba hakama asma’u batace komaiba tadaihanata zuwa gunsu,,,..

Amadi da KUBRAH sunzama aminanjuna sosai data ganshi tazafara murna shikwa dik yafita idan zaidawo saiyayomata tsaraba ko alawa ko taliya ko hanjin ligidi ko d’an tamalele,, haka yake shagwabata sosai idan suntaso makaranta yagama aikinda zaiyiwa asma’u saiya d’auketa sutafi gida acan take wuni sai maraice sannan yadaukota sudawo,, azimi yazo yananin yanda cikin asma’u ke wahalda’ita dakuma yanayin rayuwa yasa take ajiyewa idan tai yau gobe tahuta jibi kuma tad’auka haka tadingayi har aka gama gabad’aya, day’an kudinga take samu tayiwa asma’u dinkin sallah habu ya’aikowa su y’an biyu da kayan sallah amma banda KUBRAH bare kuma asma’u yadai aikomasu da nama shima bamai wani yawaba,, inna tabawa ma tayiwa KUBRAH dinki mai kyau malam tanimu kuma yasiyamata sark’a da awarwaro kuma yasiya asma’u atamfa d’inkakka kuma yasiyomata nama ya’aikamata dan farinciki saida tai kwallah nan taita murna tana sakawa malam albarka dakuma yimasu kyakkawar addu’ah dakuma fatan alkhairi agaresu,,,…

       ******  ******

Cikin asma’u yatsufa yashiga watanni haihuwa akoda yaushe kuma akowanne lokaci suna duban zuwan haihuwa, kwance take a d’aki tana hutawa KUBRAH kuma tana a waje tana wasa Amadi kuma baizoba,, maimuna ce tafito takira KUBRAH wai tazo mak’e kafada tai alamar bazatoba dikda ranta cike yake damugun nufi amma haka tadaure taimata murmushi mai kamada na yak’e tasake matsowa kusa da’ita sannan tabata alawa aikwa tanaganin alawa tafara dariya taje maimuna ta d’auketa tawuce da’ita,,,..

D’akinta tawuce da’ita suna isa tasauketa tashiga uwar d’akin wata kwalba naga ta d’akko maikama da ta tirare wani murmushin mugunta tai sannan tajuyo gefenta tad’akko wani zane mara girma sannan tafito zuwa gun KUBRAH,,,..

Tana fitowa takamata tad’auremata baki sannan tafizge alawarda tabata tasake kama hannayenta tayi baya dasu tad’aure, kwalbar data d’akko tabud’e sannan tabud’e day’an idon KUBRAH tafara fesa matashi a ido k’amshinsa danaji yatabbatarmin da tirare ne,,,..

Jin zafinsa yakai a kwayar idonta yasa tabuga wata iriyar k’ara mai k’arfi amma dayake ta d’auremata baki sai k’arar batafitoba, haka zuciyarta ta toshe tacigaba da zubamata tiraren a idonta idan tazubawa wannan sai tabud’e wannan tazuba masa,,,..

Fizge fizge KUBRAH keyi na neman ceto da d’auki amma ina babu mai ceton sai ubangiji, innalillahi wa’inna ilaihi raji’un duniya ina zaki damu zuciyoyi sun rufe sun k’ek’ashe babu tausayi ba tsoron Allah k’aramar yarinyarda batada laifin kowa batada hak’k’in kowa saina mahaifiyarta itace za’ayiwa wannan cin zalin saboda rashin iimanii ubangiji ka shiryardamu tafarki madaidaici ameen…..

#/Vote

#/Share

#/Comment

”’AUFANA for life ”’

  *I.W.A*🖊® *INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION~I.W.A*📚

   *( ơŋщąγɖ ɬơɠɛɬɧɛγ )*

   _*GANI GA WANE….*_🌷

_*STORY & WRITING ~ BY*_

    _*AUFANA*_✍

_Whattpad@Aufana8183_

_*Devoted to – maryam Abdallah and maryam ( mamu gee ) my granny’s*_

    _*PAGE 7~8*_

_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_

Cigaba da zubamata shi takeyi yayinda itakuma keta fizge fizgen neman taimako saboda azabarda takeji a idanun, saida taga numfashinta na neman d’aukewa sannan tadakata da zubamata, wata iriyar dariyar mugunta da jin da’din abunda ta aikata tai sannan taje tamayarda sauran tiraren tadawo takwance d’aurinda tamata sannan ta toshe mata baki saboda kartai k’ara asirinta ya toni nan tad’auketa tafita,hmm tamanta da ubangiji yana kallonta baya bacci baya gyangyad’i Allah ka shiryardamu ameen,,,..

Ahankali tadinga tafiya tana sand’a har takai k’ofar shiga d’akin asma’u sannan tasauketa a dai dai k’ofar shigar taisauri da gudu takoma d’akinta,, jikin KUBRAH yai laushi batada wani kuzari sosai saboda taci kuka sosai gakuma fizge fizgen dataitayi hakan yasa batada wani k’arfin jiki sosai, dakyar take rarrafe tana kuka muryarta kuma bata fita sosai, kamar daga sama asma’u kejin sautin kukanta kad’an kad’an dasauri kwa ta taso tafito, yanayinda taganta ne yamatuk’ar tayar mata da hankali dasauri taduk’a tad’auketa tana dubanta tareda tambayar abunda ke damunta, bata ankaraba taji KUBRAH tasake gaba d’aya alamar ta suma,,,..

Arikice tafara bubbugata tana jijjigata wai ta tashi ina KUBRAH ba rai, d’aki tashiga tad’akko mayafinta tafito tawuce dasauri tana rungume da’ita maimuna nakallonta hartafita,, tafiya take sam bata ganin gabanta saboda yanayinda take ciki Amadi ne yahad’u da’ita ganinta daukeda aminiyarsa kuma da’alamu kamar batada lafiya ne yasa yabi bayanta shima yana tambayarta abunda yasami KUBRAH,, bata’iya cemasa komaiba hakan yasa shima yabi bayanta harsuka iso gida,,,…

Koda suka iso kuwa inna na a zaune tana d’umame malam kuma yana a zaune yana karatu, ganin yanda tashigo a rikice Amadi kuma yana bayanta yasa sukai saurin tasowa nan tamik’awa malam KUBRAH tana kuka mai cike da tshin hankali tambayarta sukashigayi amma takasa basu amsa danhaka suka juyo suka tambayi Amadi shikam yace baisaniba shima a hanya yahad’u da’ita ganin yanayinda take ciki ne yasa yabiyota,, janyota inna tai tazaunar tabata ruwa mai sanyi tasha sannan tashiga tambayarta dakyar tamasu bayanin iya abunda tasani, ruwa masu d’an sanyi inna tad’ibo ta tub’e KUBRAH tasakata aciki cikin ikon Allah kuwa numfashinta yadawo, wata k’ara tayi mai cike da tsananin firgici nan malam yadinga mata addu’oi yana tofamata dakyar tadaina fizge fizgen datakeyi saidai bata daina kukan ba kuma har yanzu tak’i bud’e idanunta, malam yakula dahakan kuma yaga sun kukkumbura sosai jijiyoyin idanunta diksun firfito a waje gakuna k’amshin tirare datakeyi sosai kallon inna yai yace “tabawa akwai matsala inaganin yarinyar tak’i tabud’e idanunta sannan ki kula idanun sun kumbura sosai kuma k’amshin tirare take” eh wallahi nima malam nalura dahakan amma mud’auketa mukaita gun malam  ballo komenene shi idan yaduba zai gayamana. “to shikenan muje can kawai” nan suka tashi suka shirya inna tagoya KUBRAH malam yashiga gaba tabi bayansa suka fita akabar asma’u da Amadi gida,,,..

Dazuwansu kuwa malamin yatabbatar musu da tabbas tirarene akazubamata a idanu kuma zai iya haifar mata dakowacce matsala shikansa bashida tabbacin zata cigaba da gani saboda tiraren anzubamata shi sosai,, ran inna dama na malam yayi mummunar b’aci ba kadanba to wanene yai wannan mugun zalincin ga k’aramar yarinya kamar KUBRAH metamasa wane laifi tamasa, dakyar malamin yabud’e idanun yawankesu da ruwan zam-zam saboda masifaffen zafi takeji shiyasa tak’i bari harsaida malam da inna suka dafeta sosai inna kuwa kuka take tana tausayawa rayuwar KUBRAH dama ta mahaifiyarta,,,..

STORY CONTINUES BELOW

Saida yawankesu tass sannan yazubamata magani kuma yabada wasu wad’anda za’acigaba da sakamata kullum idan anwanke idanun yakuma bata wad’anda za’adinga bata tanasha insha Allah zatasamu sauk’i, haka malam yabiyasa inna tagoyota suka dawo gida jiki ba kwari,,,..

Wunin ranar haka sukayisa ba da’di kowa jikinsa yai sanyi Amadi kuwa har yanzu kuka yake yana tsinuwa gadik wanda ya’aikatawa aminiyarsa wannan mugunta hakama inna wuni tai tana Allah tsine gadik wanda yayiwa y’ar jikallenta wannan muguntar asma’u dai tazama shuru shuru ko magana ma wuya take mata, sai dare sannan takoma gida KUBRAH kuma malam yace bazata komaba harsaita warke,,,..

     *****  *****  ***** ***** 

Kimanin sati biyu da faruwar wannan abun Alhmdllh kuma KUBRAH tasami sauk’i sosai idanun sun washe dik wannan jinin daya kwanta yacire kuma jijiyoyin dik sun koma idanun sunyi fari tass saidai fa bata ganin komai sai duhu amma idan mutum yazo kusa da’ita tozataji alamunsa kuma tasan muryar kowa,, dikda KUBRAH yarinya ce amma tasan bak’in cikin rashin gani musamman ita dayake daga baya abun yasameta wani lokacin haka kawai sai agatana kuka idankuma aka tambayeta meya faru saitai shuru takasa bada amsa amma inna tasan komai saboda ita ba yarinya bace kamar asma’u da Amadi,,,..

Har KUBRAH tai wata d’aya amma malam yace bazata komaba haka sukacigaba da bata kulawa sosai tsintsar k’auna suke nunamata bama kamar Amadi dayakejin kamar yamaidata ciki saboda k’auna sam baya gajiya da kula da’ita wani lokacin haka kawai zaigoyata yaje yawo da’ita yasiyamata abubuwa kala kala masu dad’i kuma wa’danda takeso,, wata rana yafita da’ita yasiyomata abun busa kullum idan basuda makaranta yakan zauna yaita busa mata tana dariya tanajin da’di,,,..

Haka rayuwa tacigaba da tafiya, aranar da KUBRAH tacika shekara hud’u da haihuwa ranar ne asma’u tasake haifar ‘ya mace kyakkawa sosai itama dai kamarsu d’aya da mahaifinta habu,, tinda mahaifiyar habu taji asma’u tahaihu kuma y’a mace tahaifa tasako mayafinta tazo gidan cike da masifa nanfa taita balbalawa asma’u masifa “wato kedai dana daga ganinki ba irin arziki bace to barikiji nagayamaki wallahi wannan rashin arzikin naki da wannan k’ashin naki na tsiya bazaki goga mana shiba bazan d’auka ba sam wallahi tin yanzu kinfara haifamasa mata biyu bare kuna nangaba watakil ma goma zaki haifamasa to wallahi sam bazan d’aukaba dole kisan inda dare yamaki tinkan nayi tamaulan yara dake sha sha mara arziki irin tsiya wato kinga d’an gaye d’an arziki shine zaki mannemasa kiyita zubamasa d’iya mata kina kasheshi tin lokacin mutuwarsa baiyiba to sam banlamuntaba kuma bazan d’aukaba” haka taita yiwa asma’u cin mutunci da rashin arziki, har tagama abunda take k’ala asma’u bata’iya cemata ba kanta a duke tana kwallah,,,..

Saida tamata iya san ranta sannan takama hanya tawuce, tin ranarda asma’u ta haihu tasanyawa y’arta suna HALIMATU SADIYYA wato sunan mahaifiyarta data rasu saidai kash kwana hud’u kad’ai yarinyar tai itama takarb’a kiran ubangiji takoma ga mahaliccinta,, asma’u tai kuka sosai saboda tamafi saka yarinyar a rai fiyeda KUBRAH saboda sunanda tasanya mata amma yazatayi dole tai hak’uri,,,..

Kwana biyar da haihuwa habu yadawo, gidansu yafara sauka aikwa nan mahaifiyarsa taita zigashi tana balbala masa masifa danme zaibar asma’u gidansa taita haifamasa y’ay’a mata tana janyomasa fatara da talauci nan tashiga tafita taita balbala masa masifa dakuma k’ara zigashi nantake yaji tsanar asma’u da KUBRAH tak’aru acikin zuciyarsa,, daya dawo gida ma hakane itama maimuna zigashi d’in tashigayi,, asma’u na a kwance d’akinta taji shigowarsa yabugo k’ofar dak’arfi kaman zai b’allata mik’ewarda zatai domin ganin mai shigowa bata ankaraba taji saukan duka da bulalar delbejiya abayanta, a rikice tai saurin mik’ewa tsaye saitaga ashe habu ne,,,..

Wani mugun kallo yakemata mai cike tsintsar tsana yana zazzaro idanu kaman mahaukaci sabon kamu, a yanayinda tagansa ne yabata tsoro taisaurin kama hanyar fita domin ta tserewa sharrinsa saidai ina k’arfi ba d’aya ba, dasauri yakai hannunsa yajanyota saita fad’i a k’asa nan yacigaba da dukanta iya k’arfinshi itakuma tacigaba da kokarin neman hanyar fita, dakyar tasamu takufucemasa tafita bai kyaleta yabi bayanta yanadukanta harsuka kai tsakiyar gari,,,..

Tana cikin tafiya tai karo dawani dutse yakadata tafad’i k’asa nan yasamu yanda yakeso yacigaba da zabgamata bulalarnan kankace me wajen yacika da mutane suna kallonsa yana dukanta tana kuka tanasaka hannayenta tana karewa, Amadi ne hanya tabidashi KUBRAH na’abayansa yahango taron mutane danhaka shima yace bara yaje yaga komenene, da’isarsa yahango habu ne ke dukan asma’u aikwa dasauri yajuya dagudu yawuce gida,,,…

Koda ya’isa inna na diban ruwa a rijiya malam kuma isowarsa kenan daga daji, cikin shesheka yafad’a masu habu nacan na dukan asma’u a tsakiyan hanya aikwa ba shiri inna ko mayafi babu suka wuce, koda suka isa suka tararda wasu abokanan malam garso mahaifin asma’u a tsaye suna rik’e da’ita shikuma yana tsaye yana furzarda numfashi, ganin irin d’anbanzan dukanda yamata harda jini yasa inna tafashe da kuka hakama malam kwallah ke fita daga idanunsa,, cikin tsananin b’acin rai malam yace “amma dai Allah wadarai da halinka Allah wadaran mummunar halayya irin taka Allah wadaran mummunar ak’ida irin taka wallahi Abubakar saikayi nadamar abunda ka aikatawa asma’u saikayi nadamar halinda ka sanyata ita da ‘yarda ta haifamaka har kake wulakantata akanta saikayi nadama alokacinda batada amfani agareka kuma wallahi saika nemi abunda asma’u tahaifa dakanka,, nayi nadamar amincewarda mahaifin asma’u yai akahadaku aur…” baiko k’arasa ba habu yakatsesa dafad’in “kai malam dakata indai akan wannan bala’in da masifar ce kake man wad’annan kalaman to kaje gatanan nasakeki saki uku kuma nakara fad’a nasakeki saki uku zan k’ara maimatawa saboda wanda baijiba yaji asma’u y’ar gidan muhammadu garso ni Abubakar d’an gidan mai gari ibirahimu nasakeki saki uku” yana gama fad’a ya kyalkyale dawata dariyar mugunta sannan yacigaba “malam tanimu mai almajirai nasaki asma’u gatanan kaika aura saitacigaba da haifamaka y’ay’a mata idankuma fatara da talauci sukamaka sallama karka kuskura ka tinkaro gidan mahaifina dan wallahi kwayar gero d’aya bazan aminta abaka ba, ‘yace kuma banaso nabaka kadauka danni gidana gidan y’ay’a maza ne kawai bawajen zamanta aciki” yana magana yana tafiya harya wuce,,,..

Inna tabawa ce tarik’a hanun asma’u suka wuce sannan kowa ya watse, suna isa gida malam yace asma’u tasaka mayafinta nantasaka suka fita, kai tsaye gidansu habu suka wuce gun mai gari koda suka isa baya fada danhaka suka zauna sannan malam yasaka wani yaro yakirasa,, suna zaune yashigo nan malam tanimu yabashi hanu sukayi musabaha suka gaisa sannan mai gari yazauna,,,..

Bayan yazauna ne malam tanimu yafara masa bayanin abunda yakawosu nanyafetse masa biri har witsiya ba abunda yabari dik abunda yasani saida yafad’a masa,,  mik’ewa tsaye mai gari yai ransa cikeda tsananin b’acin rai kasa cewa komai yai kawai yawuce cikin gida,, baifi 5minutes dafitaba yadawo tareda matansa biyu mahaifiyar habu dakuma abokiyar zamanta, cikeda b’acin rai yadubesu sannan yace “adik k’arshen wata inabada hatsi da abinci akaiwa yarinyar asma’u ina kuke kaishi” sukai shuru akarasa mai magana acikinsu sai faman kame kame suke, juyowa yai gun malam yacigaba da magana “asma’u dan Allah kiyafeni wallahi ina iya kokarina wajen kula dake mugwayen mata Allah yabani shiyasa adik karshen wata sainabada abinci akaimaki ashe basa kaimaki” yanacikin magana saiga habu yashigo mai gari naganinsa yatamke fuska tamkar baitab’a sanin me akekira da dariya ba ganin yanayin fuskar mahaifinsa yasakashi yarazana dakyar yak’araso a gabansa yadurk’usa,, wasu kyawawan maruka yasauke masa har biyu masu zafin gaske sannan yafara magana cikin izza da d’agawar sauti “wallahi Abubakar kabani mamaki kuma kabani kunya amanardana baka ashe bakarik’eman itaba ka kunyatani to kasani wallahi bazantaba yafemaka ba kuma daga yanzu har izuwa karshen rayuwa inacikin fushi dakai” juyowa yai yakalli asma’u yace “‘yata dan Allah kiyafeni kinji ki gafarceni danasan hakace zata faru datin farko ban yarda nahad’aki da wannan azzaliminba” yasake juyowa ga malam tanimu yace “malam tanimu kuje gida zankiraku daga baya” nan malam tanimu yace “toh” sannan yatashi suka wuce, suna fita mai gari shima yafita ransa a b’ace yabarsu habu anan yana,,,..

Adaren ranar habu bai kwana garin ZAGA ba yatattara nasa i nasa da matarsa maimuna da yaransa uku yabar garin mahaifiyarsa kuwa sai tsinuwa take ga asma’u wai dik itace silar faruwar hakan dabatashigo rayuwarsu ba dadik hakan bata faruba,,,..

A b’angaren asma’u kuwa kwana biyu ta murmure tawartsake tai k’iba  kyanta yafito sosai bayan tagama jego tagama iddah nan tacigaba da kasuwancinta na sak’ar datakeyi takanyi dayawa saitabama masu saye su siyar, haka tacigaba da rayuwarta tana kula da y’arta adik lokacinda suka zauna saitaita bama KUBRAH labarin d’anuwanta faruk kuma saita dinga fad’amata kamanninsa “farine tass mai d’an tsayi adaidai sumarsa akwai tsaguwa wacca yasamu watarana alokacinda yana yaro yafadi saiya bugu da dutse shine bayan ya warke sai tsaguwar tafito, hak’oransa a harhad’e suke wani kan wani” hakadai zatadinga lissafamata kamanninsa dayake KUBRAH akwai wayo ga basira saikwa dik tahaddace kamannin nasa saboda KUBRAH akwai wayo wayonta yafi shekarunta yawa,,,..

       Hakadai rayuwa tacigaba da tafiya cikin rufin asiri da wadatar zuci…….

#/Vote

#/Share

#/Comment

”’AUFANA for life ”’

   *I.W.A*🖊_PAGE 9~10_

Haka rayuwa tacigaba da tafiya cikin rufin asiri da wadatar zucii,,,

Kwance take akan tabarma tana lazimi KUBRAH kuma nawasa saiga Amadi yashigo, tana ganinsa tai murmushi yak’araso yagaida asma’u sannan yazo yadauketa suka fita, alawa yasiyomata sannan yadawo yasauketa yad’auki tsintsiya yafara shara bayan yagama sannan yaci abinci,, yana cikin ci asma’u tace mashi “Amadi idan kagama ga kayanan nagama sak’awa kad’auka ka kaiwa sale mai kanti kuma kacemasa yabaka tsohon kud’i ka kawoman” saida ya had’iye lomarda yasaka abakinsa sannan yace “toh, yau baza a kaiwa rabi dillaliya ba” kai nagaji da shegen bashinnan nata sai d’auka take batareda tabiya tsohon kud’i ba. Cigaba yai dacin abincinsa,,,Bayan  yagama sannan ya wanke hannunsa yasha ruwa sannan yad’auki kayan yafita, harya fita kuma yadawo yakalli KUBRAH yai murmushi sannan yace “KUBRAH na bazaki rakani ba” itama murmushin tai sannan tace cikin tsamin bakinta “zaka siyaman d’an malele da hanjin ligidi” har zaiyi magana sai asma’u tai sauri tace “haba kekam kullum bakida aiki sai kashe kud’i kinacin kwalam da mak’u lashe wallahi kiyi hattara dani dan banasan shirmen baza”  b’ata fuska tai ta turo baki agaba, shikuwa dariya yai sannan yaja hanunta suka wuce,,,,.+

Yau takasance laraba kuma yaune kasuwarsu keci dan haka tinda wuri malam yashirya yafita Amadi ma bayan yagama aikinsa shima fita yau yawuce kasuwar,, saikusan 5:30pm sannan suka dawo wasu kyawawan awarwaro Amadi yasiyowa KUBRAH aikwa nantaita tsalle tana murna day’an dauke yake da sunan KHADIJA d’ayan kuma AHMAD rubutun anyisane da ajami ( ARABIC) kuma yai kyau sosai a hannu biyu yasaka mata yacemata na kawance ne karta cireshi cikin zumudi da jindad’i tace toh, itadai inna kallonsu take kawai,,,

sanyin la’asar yasakko yanayin gari yai dad’i Amadi mutum ne maisan zuwa daji kasancewar dajin garin ZAGA bashida nisa da cikin gari hakan yasa kusan kullum idan bashida aikinyi acan yake tafiyansa shi da abokanansa sai dare sannan sudawo gari to yauma kamar kullum, ranar yau antashi yanayin garin gwanin birgewa yanayin akwai dad’i sosai haryakama hanya saikuma yadawo yad’auki KUBRAH sukatafi a tare,,,

bayan sun isa yagoyata a bayansa yahau wani k’aramin ice da’ita saida yazaunar da’ita sannan shima yazauna ‘yar abar busar nan mai kama da sarewa yaciro ahankali yafara busata woww sautinta kuwa daddad’a ne sosai nan KUBRAH tai shuu tana sauraren sautin sarewar gashi Amadi ya’iya busata sosai harda wani gwaninta yake saboda yaga KUBRAH tanaso kuma tanuna taji dad’insa,, haka yacigaba da busamata itakuma tana rera masa wak’a irin wacca yaran kauye keyi idan sunje dan dali wasa,sunjima a can sosai daga bisani yarik’o hannunta suka dawo gida,,, haka shak’uwa tacigaba da shiga tsakanin KUBRAH da Amadi ahankali ahankali yakoyamata busa sarewar har ta’iya,,,

Wata rana kwatsam mahaifin amadi yazo yad’aukesa yatafi dashi garinsu saboda yanaso yaje yatayashi aikin gona saboda lokaci yayi aikwa ranarda zai tafi shi kuka KUBRAH kuka dakyar aka bamb’areta daga jikinsa sannan suka wuce, tafiyar amadi tazamewa KUBRAH tamkar rasa mahaifinta habu hhhh Lol, tadawo shuru shuru so silent tafiyarsa ce tasa tai k’awa mai suna Hindu y’ar mak’ociyarsu rabi dillaliya wacca take karatu anan makarantar malam tanimu,, Hindu kyakkawace sosai kamar KUBRAH kuma kusan sa’ar KUBRAH ce d’an haske da manyan idanuwa kawai KUBRAH tafita,, kullum Hindu saita biyowa KUBRAH idan anshiryamata saisu tafi makaranta atare hakama idan zataje yawo saitazo ta tafi da KUBRAH ko aikenta akayi saitazo KUBRAH tarakata,,,

Sannu ahankali kawancen KUBRAH da hindu yacigaba da wanzuwa sun shaku sunzama aminan juna sosai dik inda kaga hindu saikaga KUBRAH, wani bawan Allah yabama KUBRAH sanda mai kyau kyauta wacca take dogarawa idan tanaso tai wani abu babu mutane kusa da’ita, ahankali kyanta sai bayyyana yake dara daran idanuwanta sai kara fiffitowa suke idan kaganta zaka rantse da Allah ba makauniya bace tana gani saboda girman idanuwanta gasu farare tass tamkar auduga,,,

Watan Amadi uku a gida sannan yadawo koda yadawo ya tararda KUBRAH tai k’awa yaji da’din hakan sosai koba komai zatashiga cikin y’an uwanta mata kamar kowa kuma zatayi k’awaye kamar yanda kowacce mai gani keyi,, haka rayuwarta tacigaba da tafiya cikin jindad’i dakuma taimakon mutane,,,

”’After 5 year’s ”’

Ahalin yanzu girma yafara kama KUBRAH shekarunta 9 da haihuwa Alhmdllh kuma komai natafiyarmata dai dai tana rayuwarta kamar yanda kowanne mai gani keyi domin itama tana gani da zuciya wani abun ban mamaki yanzu har ajinta na musamman malam tanimu yabata wanda take koyarda yara hadda saboda itama da haddan tai karatu shekaranta 6 tasauke Qur’an da haddah yanzu haka hizifi sittin ne akanta kuma Alhmdllh tasan fannin fik’ihu sosai abunda yake b’ata alwala dakuma wanda yake b’ata sallah hukunce hukuncen jinin haidha dana nifasi wankan tsarki damakamantansu,, dai dai gwargwado malam yabata ilimi sosai wanda mutane da dama kemamakinsa ganin yanda take makauniya mara gani amma tasamu tarin iliminda komai gani iya abunda zaisamu kenan.

#/Vote

#/Share

#/Comment

”’AUFANA for life ”’

  *I.W.A*🖊

_Page 11~12_

Zaune take akan tabarma hindu kuma na a gefenta tilawa take hindu naduba mata amadi kuma na’agefenta yana yiwa yara rubutu a allunansu, inna ce tashigo tamik’o masu d’umamensu sannan tabama Amadi nasa,,,+
Ahalin yanzu zan iya cewa Amadi yakai shekara 20 dahaihuwa saboda yanayin girmansa ma yafi shekarunsa,, bayan sungama tilawan ne sukaci abincin sannan suka tashi sukawuce gidansu hindu, acan ma sunjima sosai sannan hindu tamayarda KUBRAH  gida kasancewar yauba makaranta alhamis ne,,, zaune take itakad’ai asma’u na a gefenta tana sakarta saitajuyo kamar tana ganinta tace “mami inaso naje kasuwa wannan satin dan Allah kibarni naje tareda hindu innarta zataje cin kasuwa” KUBRAH mamai take kiran asma’u yanda taji Amadi nakiranta. Kallonta tai cikin murmushi sannan tace “gaskiya KUBRAH banason kina yawan yawo nesa amma bakomai tinda tareda hindu da dillaliya zakije na’amince Allah yakaiku lafiya yadawo daku lafiya” cike da jindad’in zancen mahaifiyarta takai hannunta fuskarta tace “nagode mami na nagode sosai”  karki damu farincikinki shine nawa.
A ranar laraba kuwa ko makarantar safe batashigaba saboda zumud’i haka tadami inna saida ta shiryamata tamata kwalliya tasaka mata tirare,, bayan tashirya mata sannan tad’auki sandarta tadogara tafita saboda yanzu ko’ina KUBRAH nazuwa indai acikin unguwarsu ne bare kuma layinsu ko’ina tasani, koda taje gidansu hindu kuwa haryanzu basu shiryaba aikwa hindu taita mata dariya wai tana zumud’i zataje kasuwa, bayan sun shirya sannan suka fita hannun hindu hard’e dana KUBRAH rabi dillaliya kuma nagabansu sannan suka wuce,,,
Wannan fitarda KUBRAH tai sam Amadi baisaniba koda yadawo akafada masa fad’a yadingayi meyasa zaabarta taje har kasuwa gashi akwai nisa sosai kasuwa dikda nisanta baihanasa tafiya ba saboda yadawo da’ita,,, saikusan 11:00am sannan suka isa kasuwa sashen masu kayan make up suka fara shiga dikda batagani amma yanda takejin hayaniyar mutane yasakata farinciki sosai da nishad’i, bayan sunsiyi abunda zasu siya sannan suka wuce hindu hannun KUBRAH taja suka bar mahaifiyarta anan, sunsha yawo sosai acikin kasuwar sungaji danhaka hindu taja KUBRAH sukawuce masallacin dake cikin kasuwa saboda su huta,,,

Basufi 30minutes da zama ba KUBRAH tace hindu tarakata tai fitsari kallonta tai sannan tace “KUBRAH aini bansan inda ake fitsariba anan kasuwar amma mufita mugani bazamu rasa inda zakiyi fitsarinba” toh. Tace sannan suka tashi suka fita,,, a can bayan kasuwa sukaje kusa da babban titindake shigowa garin ZAGA  acan wani gefe takaita sannan itakuma tafito tace “kitsaya anan kiyi zanje gun umma na nadawo karkine ko’ina kinji yanzu zan dawo” toh. KUBRAH tace sannan hindu tawuce, bayan tawuce KUBRAH tai abunda zatayi tagama tai tsarki sannan tadinga amfani da ganen zuci tana ayyanawa aranta gainda suka biyo dazasu zo gakuma inda suka biyo ahaka harta fito sannan tai tsaye anan tanajiran dawowar hindu,,,
Harkusan 15minutes amma hindu bata dawoba tagaji da tsayi sosai hakan yasa tafara tafiya ahankali batareda tasan inda takebiba saboda hanyar yanzu tarikicemata,, tafiya kawai take amma sam batasan inda takebiba batasaniba ashe hartakai kan babban titin bata ankaraba kawai tafarajin sautin kukan motoci daban daban sunamata hon, arikice kuma a kid’ime dikta rikice sai kukan hon d’in motoci takeji cikin rashin sa’a bata ankaraba wata mota tai sama da’ita tabama k’asa kanta yafara kai k’asa saida yabugi motar sannan yadawo k’asa nantake jini yafara zuba daga cikin kanta,,, mamallakin motarne yafito saboda kaddararda ta afka masa, cikin kid’imewa yafito hankalinsa a tashe yafito yafara janye mutanenda suka rufeta ya’isa gunta.rikicewa yai yarasa me zaiyi wani dake gefensa ne yaji yace “wallahi dole kadauketa ku masu kudinnan kunriga dakun raina wayon mutane yanda kukaga dama haka tuki kowa zaku kashe kukashe baruwanku tinda kunada kud’i” kallonsa yai cikeda mamaki amma tashin hankalinda yake ciki yasa baima damu da abunda yafad’a ba,,,
Cikin sauri akidime yakai hannayensa yad’auketa cakk yawuce sannan yabud’e murfin mota nabaya yasaka sannan yashiga yatada motar yawuce,,,

Tada motarsa yai daidai dazuwan Amadi yana nemanta, ya’iso kenan saiga hindu ta’iso

#/Vote
#/Share
#/Comment

”’AUFANA for life ”’
    *I.W.A*🖊

® *INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION~I.W.A*📚
*( ơŋщąγɖ ɬơɠɛɬɧɛγ )*

_*GANI GA WANE….*_🌷

_*STORY & WRITING ~ BY*_
_*AUFANA*_✍
_Whattpad@Aufana8183_

_*Devoted to – Maryam Abdallah and maryam ( mamu gee ) my granny’s*_

_*PAGE 13~14*_

_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_

Tada motarsa yai wanda kuma yai dai dai dazuwan Amadi yana nemanta, ya’iso kenan saiga hindu ta’iso saboda tad’auketa suwuce,,,+

Amadi naganin hindu cinkin b’acin rai yace “ke ina KUBRAH meyasa zaki dakkota kutaho har kasuwa bayan kuma kinsan lalurarda take d’auke da’ita” itama cikin rashin sanin me zatacemasa dakyar tasamu kalamanda tahad’a tace mace “wallahi anan nabarta zatai fitsari nikuma naje gun ummana nakarbo mana abinci shine yanzu nadawo banganta” zaro idanu Amadi yai cikin rashin fahimta yace “mekike nufi dahakan” ganin tsintsar gaskiya afuskarta yasa ya’aminta da abunda tace kawai yajuya,,,..
Ganin yajuya yasa itama tabibayansa, fara dube dube sukai suna zuba idanu tareda kiran sunan KUBRAH ganin bako alamunta yasa suka fara tambayar mutane, wani mutum ne suka samu a gefen titin yana juya kai fuskarsa cike da tausayi Amadi yamasa sallama dakyar mutumin yakarb’a sannan Amadi yace “malam dan Allah wata yarinya muke nema fara ‘yar kimanin shekara tara zuwa goma makauniya ce dan Allah kokaganta” wani kallon tausayi mutumin yamasa sannan yajuya fuska cike da tausayi yamasa nuni da hanu sannan yafara magana “bawan Allah wallahi yanzinnan kuwa wani mutum mai kud’i yabigeta akan titinnan acan wajen yanuna masa da yatsa, kuma wallahi tayi muguwar rauni dan sam bamumasaka ran zata rayuwaba saboda koda yad’auketa ma bata rai” zaro idanu Amadi yai cike da tsananin tashin hankali hakama Hindu itama kuka tafashe dashi dakyar Amadi ya daidaita nutsuwarsa sannan yace cikin watairiyar murya “dan Allah toh wanene wanda yabigeta din kuma ina yaje da’ita” toh wallahi muma bamusansa ba kuma da’alamu ma bak’one badan nan kauyen bane” juyawa kawai Amadi yai batareda yasake tsayijin wasu zancenba hakama hindu bin bayansa tai,,,..
Cikin sauri Amadi yakoma gida yasanarda Su asma’u da malam tanimu abunda ke faruwa hankalin kowa dake cikin gidan yatashi musamman asma’u dik wani kauye dake kewayen garin ZAGA dakuma wad’anda ke makwabtaka dagarin tosu malam tanimu sunje neman KUBRAH amma babu labarin komai ganin abun bawani cigaba yasa Amadi yashirya zuwa babban birnin k’asar KEBBI nan yafad’awa malam tanimu shima kuma yabashi had’in kai dan haka yashirya yawuce saboda yaje manyan asibitocin dake cikinta ko Allah zaisa yaga wanda yabigeta,,,..
***** ***** ***** ******

Yana tada motar direct wata katafariyar hospital yawuce da’ita mai suna FEDERAL MEDICAL CENTRE Birnin kebbi, da’isarsa kuwa akaisaurin karb’anta domin bata taimakon gaggawa,, d’akin I.C.U aka wuce da’ita kankace me tini asibitin tagauraye da zancen KUBRAH wai ankawo wata yarinya wacca tai accident b’atacce, likitoci hud’u suka taru a kan KUBRAH ciki kuwa harda likitocin kwakwalwa guda biyu,,,..
Kusan 2hours suka b’ata akan KUBRAH amma har yanzu basu samu yanda suke so ba ta farfad’o tana numfashi amma saidai haryanzu ko motsin kirki batayi bare kuma tagane wanda kekanta,,,..
Zaune yake akan kujerar dake kallon d’akinda take kansa a duke da’alamu yanacikin damuwa sosai, sallam d’ayan likitocinda suka duba KUBRAH yaimasa ahankali yad’ago cikin sanyin jiki sannan yakarb’a sallamar cikin muryarsa mai rauni,, masha Allah kyakkawane sosai ba fari bane shi chocolate colour ne fuskarsa mai d’an tsayi ce wacca ke mallakar dara daran idanuwa farare masu d’auke da eye Lash’s bak’ak’e wulik hancinsa mai tsayi har yakusa tab’o lips d’inshi na sama saboda tsayi kuma har yad’an lankwasa bakinsa dai dai shi bashida girma kuma ba karami bane kaman na mata,, bashida tsayi sosai kuma shiba gajere bane k’irjinsa faffad’a ne kai atakaice dai kyakkawa ne sahun farko,,,..
Ahankali yataso tsaye yakalli Doctor cikeda zumudin sanin halinda take ciki, kallonsa doctor yai sannan yace “malam kai d’an uwantane ko yayanta” rasa sanin me zaice yai kawai yatsinci kansa da fad’in “ni yayanta ne dan Allah doctor kafad’a man wane hali take ciki” come down my bro kwantarda hankalinka muje office namaka bayani.,,,
Nan suka wuce office d’in suka zauna yajuya yanakallon doctor, cikin hikima da sanin aikinsa doctor yakallesa sannan yafara masa bayani “azahirin gaskiya bazan boyemaka komaiba saboda idan nai haka nacuceka kuma ban kyautawa kaina ba amatsayina na likita, d’an uwa k’anwarka tanacikin wani stage wanda take buk’atar cikakkiyar kulawar manyan likitoci bazancemaka tai loosing memory nata ba saboda zai iya yiwuwa idan kukaje daita out side suyi nasarar shawo kan matsalar ammafa saikunyi sauri saboda a yanzu haka ma munkasa cin nasarar kwaso sauran jininda yashiga tacikin kunnayenta wuce a kwakwalwarta sakamakon rashin kayan aiki isassu amma kaga k’asashen waje su sunada isassu kayan aiki sosai kuma sunfimu kwararrun doctor’s, saboda haka inabaka shawara amatsayina na likita kawai kawuce da’ita waje domin nemamata lafiya indai har kanada zarafin yin hakan kuma kanada k’arfin yin hakan” gabad’aya dik jikinsa yai sanyi sosai cikin murya mai rauni yace “yanzu doctor kana ganin wannan hanyarce kawai mafita” insha Allah.yafad‘a atakaice hmm…!!! yanisa sannan yamik’amasa hannu tareda mik’ewa tsaye “thank doctor zanje nabiya komai insha Allah gobe zanwuce da’ita out side saboda nemamata lafiya” Ok good Allah yasa adace. Yace “ameen” sannan yafita,,,..
Yana fita yaje yai dik abinda ake yabiya kud’in komai sannan yai wasu cike ciken file’s yatsaya yanajiran abashi umarnin d’aukanta,,,..
****** ******

Amadi ya’iso BIRNIN KEBBI daisowarsa kuwa bai zaunaba yafara bincike, damisalin 4:00pm ko sallah yakasa samun nutsuwa bare yaje masallaci yayi, kusan kowacce hospital yaje amma banda federal medical centre,, wani mutum yasamu akusada masallaci yai masa sallama sannan yatambayeshi dikkanin asibitocin dake wannan garin nan yafara lissafo masa sunayensu anan ne yaju sunan Federal medical centre hospital, cikin sauri yamasa godiya sannan yajuya yawuce, adaidaita sahu ya tsayar sannan yafad’a masa inda zaikaishi,,,..
Isowarsa hospital d’in yai dai dai da and’akko KUBRAH akan gado anasakata acikin motar asibiti, ta bayansa akawuce da’ita rufe kaman gawa shikuma yawuce cikin hospital d’in,, bayan ansakata sannan akatada motar yashiga a gaba sannan motar ta hospital tabi bayansa,,,…
Bayan Amadi ya’isa cikin hospital d’in ne yashiga tambayar mutane wata yarinya wacca wani mutum mai kud’i yakawo tasamu accident ne kuma ita makauniya ce, jin bayaninda yai yasa nantake akafahimci wacca yake nufi dikda yawan asibitin amma haka suka ganeta saboda yau itakad’aice aka kawo wacca kecikin irin wannan mawuyacin halin,, nantake suka masa bayani yanzu yanzinnan aka wuce da’ita zuwa wata babbar asibiti saboda matsalarta babbace nan basuda isassun kayan aiki, idan ran Amadi yayi dubu to yab’aci cikin b’acin rai yabaro hospital yai shirin komawa gida ZAGA,,,…
***** ***** ***** *****

Hanyar k’asar yola ADAMAWA naga sun hau hakan yatabbatarmin da can suka dosa….

#/Vote
#/Share
#/Comment
”’AUFANA for life ”’
*I.W.A*🖊® *INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION~I.W.A*📚

     *( ơŋщąγɖ ɬơɠɛɬɧɛγ )*

      _*GANI GA WANE….*_🌷

_*STORY & WRITING ~ BY*_

       _*AUFANA*_✍

_Wattpad@Aufana8183_

_*Devoted to – Maryam Abdallah and Maryam ( Mamu gee ) my granny’s*_

  _*PAGE 15~16*_

_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_

Hanyar k’asar yola ADAMAWA naga sun hau hakan yatabbatar min da cand’in suka dosa, yana driving naga yad’akko wayarsa yafara danne danne, wata number naga yai dialing nata sannan yak’ara a kunnensa cikin few minute’s aka d’aga wayar nan naji yafara magana cikin murya mai rauni kaman zaiyi kuka “Assalamu Alaikum Abbu na barka da warhaka” banji abunda aka fad’a daga day’an bangarenba sainaji kuma yacigaba da magana “Abbu na dan Allah dik inda kake kadawo gida ganinan zuwa nima ina kan hanya” daga d’ayan bangaren aka sake magana sai shima naji yace “toh shikenan Abbu ganinan nakusa k’araso insha Allah” yana gama fad’ar haka yakatse wayar tareda sauke wani nannauyan ajiyan zuciya yai shuru sannan yamaida hankalinsa ga driving d’inda yake,,,..

+

Kimanin 2hrs and 30mnts suka kwashe suna zuba tafiya sannan suka iso garin yola babban birnin ADAMAWA, kaitsaye wani babban titi naga sun hau wanda saida suka kwashi kilometers 130 sannan naga sunsauka daga kan titi suka kama wata hanyar,,,,…

Tafiyar 15mnts sukai sannan naga sun isa a gun wani matsakaicin gate mai d’aukeda matsakaicin gida, horn yai sainaga wani mutum yafito dattijo ne yabud’e gate d’in sannan shikuma yashiga da motarsa d’ayar motar ta asibiti ( AMBULANCE ) itama tashigo tai parking sannan ma’aikatan suka fito shima yafito,, fitowarsa tai dai dai da’isowar mutanen gidan ganin motar asibiti dakuma ma’aikatan asibitin yasa hankalinsu yatashi cikin sauro suka k’araso, d’aya daga cikinsu wacca naga alamar itace mahaifiyarsa naji tafara magana “Sunhanallah innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, Abdallah meke faruwa ne kamin bayani kohankalina zai kwanta dan Allah” cikin sanyin murya yabud’e baki zai fara magana saisukaji magana a bayansu “haba Amina miye haka dan Allah bazaki bari har kowa yasamu nutsuwaba sannan idanma zakiyi wannan tambayar kiyi” k’arasowa yai Abdallah yagaidasa sannan suka kama aka fito da KUBRAH daga cikin motar ta asibiti akawuce da’ita izuwa cikin gidan,,,..

Bayan anfito da’ita ne sai ma’aikatan asibitin suka tada motarsu suka wuce, bayan sun wuce ne sannan Abdallah da Abbun sa suka koma cikin gidan,, bayan sun zauna Abdallah yafara masu bayanin komai tindaga inda yabigeta har izuwa d’aukanta dayai yakaita asibiti dakuma bayaninda doctor yamasa,,,…

Kallonsa mahaifinsa yai cikin tausayi sannan yace “Wannan abun dayafaru K’addara ne kuma insha Allah zan taimaka maka domin ceto rayuwar wannan baiwar Allah zan taimaka maka da dika k’arfina dakuma abunda na mallaka koda kuwa zan rasa dika dukiyata ne” wani farinciki yaji yamamaye zuciyarsa cikin jin dad’i yataso yarungume mahaifin nasa yanamasa godiya dakuma kyawawan addu’oi,, haka itama mahaifiyarsa tabada goyon baya 100% takumayi alk’awarin kula da KUBRAH tamkar ‘yar cikinta,, dahaka suka watse Abdallah d’a mahaifinsa suka fita zuwa shirye shiryen tafiya da KUBRAH domin nemamata lafiya,,,..

1

Damisalin 2:00pm Abdallah yadawo gida amma mahaifinsa baidawoba hakan yasa yazuna yana jiran dawowarsa, saikusan 2:30pm sannan yadawo,, zaune suka a falour nan mahaifinsa yafara masa bayani komai yakammala tindaga kud’in aikin dadik wani abu daza’a buk’ata, mamaki ne yakama Abdallah sosai ya’akayi Abbun sa yasami wad’annan kud’in saboda dai yasan bashida su,,,…

Kasa jure mamakin nasa yai dan haka yatambayesa “Abbu ina kasamo wad’annan kud’in masu yawa haka bayan nasan bakada su” murmushi yai yashafi fuskar Abdallah sannan yace “yarona ai k’ofofin Allah na alkhairi a bud’e suke bayan nafita d’azu da damuwar wannan lamarin yazamuyi da wannan yarinyar kwatsam dabara tafad’o man naje nasiyarda wasu k’adarorina hud’u gidana wanda nake ginamaku kai da d’anuwanka dakuma adaidaita sahu na guda uku to anan ne nasami waennan kud’in  taimako zanyi ceton rayuwa zanyi natabbata kuma nasan insha Allah zansami lada agun ubangiji kuma shi zaisake bani dik wani abu dana rasa fiyema da wanda narasa d’in” wani murmushin farin ciki yai harda kwallan farinciki “Abbu na nagode sosai Allah i biyaka da mafificin alkhairi yasa aljannah ce makomarka” cikin jin dad’i suduka suka amsa da ameeen,,,…

Hannunsa yasaka a aljihunsa yaciro kud’i masu yawa yamik’awa mahaifinsa “Abbu nima nasamo kud’i bayan nafita, dana fita gidan magidana naje wanda motarsa take a hanuna nanemi yabani bashin kud’i cikin sa’a kuwa nasamu yabani naira dubu dari uku sai yadinga cirewa acikin kud’ina dayake biyana” shuru yai nawasu seconni sannan yace “to Allah yashige mana gaba itakuma yabata lafiya” nansuka amsa da ameen,,,..

        *****  *****  *****  ******

*WANENE ABDALLAH*

Cikakken sunansa ABDALLAH UMAR IBRAHIM haifaffen garin yola mahaifinsa malam Umar haifaffen k’asar KEBBI ne zamane yakawosa yola konace neman na halak saboda matarsa ma AMINA haifaffiyar k’asar KEBBI ce,, malam umar bafulatanine na’asali hakama matarsa Amina dikansu fulain garin ZAGA ne acikin jihar KEBBI,,,..

Malam Umar mutum ne mai neman nakansa maicin halaliyarsa wannan halayyar tasa akanta kuma yad’ora y’ay’ansa, d’an BOKO ne wanda har yanzu ake damawa dashi dan har yanzu BOKON yake kamar yanda dik y’ay’ansa bawanda baisakaba kuma dika sinayi,saisun dawo daga makaranta sannan sufita neman nakansu,,,..

Y’ay’ansa hud’u  sai d’aya wacca suka rik’o ‘yar k’anwar matarsa, ZINATU itace tafari sannan ABDALLAH sai AMMAR sannan SALMA wacca suke rik’o sai FATIMA saikuma ciki na biyar wanda baifi wata biyar ba,,,..

Dikkanin yaran nan kyawawa ne musamman ABDALLAH dik yafisu kyau d’an hasken fata kawai suka fishi ammafa yafisu kyau, Abdallah mutum ne mai sauk’in kai saidai miskiline nagaske sam bashi d’aukan raini agun kowa idan yafita waje kaman ba’itaba sanin miye dariya ba amma idan yana cikin gida tareda iyayensa zaiyita nishad’i da fara’ah ammafa tareda iyayensa kawai dan kannensa kam sam baya sakarmasu fuska acewarsa karsu rainashi,,,..

Abdallah mutum ne mai tausayi sosai sam bashison yaga wani acikin mawuyacin hali nantake tausayi zai kamasa, ahalin yanzu yakammala karatunsa na secondy har yafara karatu a jami’ah inda yake karanta BIOCHEMISTY yana a matakin 200level, Ammar kuma yana secondry ss3 Aunty Zinatu kuma tajima da kammala secondry School,sai Fatima da SALMA sukuma suna ss1 secondry suma,,,..

Rayuwa suke kamar kowa cikin rufin asiri Malam umar bamai kud’i bane amma yanada rufin asiri, gidansa gida ne mai d’aukeda d’aki uku kowanne d’aki yana daukeda toilet sai falour d’aya had’e da kitchen d’aya, a wajen gida kuma d’akin mai gadi sai shuke shuken flower’s masu kyau,,,…

_Wannan kenan_

       *****  *****  *****  *****

Aranar dai komai suka kammala natafiya 6:00pm dot jirginsu yad’aga izuwa k’asar INDIA a babban birnin New Delhi,, 11:00pm dot jirginsu yasauka a katafaren filin jirgin k’asar Taxi suka hau tawuce dasu masaukinsu,,,…

Abdallah da Abbu ne sai Aunty Zinatu sukazo,bayan sun iso masaukinsu sukai wanka Aunty Zinatu ta tsabtace KUBRAH tamata wanka sannan tacanja mata kaya harda d’an make-up tamata tafesheta da tirare, lokacinda ABDALLAH yashigo d’akin abun yabirgesa sosai dikda a kwance take idanunta kuma a rufe amma hakan baihana yahango tsintsar kyanta a fili,,,…

Dasafe bayan sun karya sukai wanka suka shirya sannan Abdallah yawuce hospital d’inda za’ayiwa KUBRAH operation, yajima sosai acan saboda y’an cike cikenda yai sannan yabiya kud’in aikin,, saikusan 2:00pm sannan yadawo gida yafad’awa Abbu komai ankammala jibi insha Allah za’amata operation d’in, Abbu yai murna sosai hakama Aunty Zinatu tai farinciki sosai,,,…

Ranar Monday itace ranarda za’ayiwa KUBRAH theater danhaka tin ranar Saturday suka tare a hospital anajiran ranar tazo,,,,…

Kula akebama KUBRAH sosai saboda acan sunsan aikinsu sosai sam basa wasa da kula da mara lafiya,, yau takasance Monday tin 6:00am dasukai sallah suketa faman hidimar shirye shirye, 8:00am dot akashiga da KUBRAH theater room Abbu da Abdallah kuwa suna a k’ofar shiga Aunty Zinatu kuma tanacan tana nafiloli da addu’oi naneman nasara….

#/Vote

#/Share

#/Comment

”’AUFANA for life ”’

   *I.W.A*🖊_Page 17~18_

Karku damu da tyaiping error ba lokacin editing

Abdallah yakasa zama sai zarya yake a k’ofar d’akin yaje yadawo likitoci kuma sai kai kawo suke acikin d’akin hakan ne yake d’agawa Abdallah hankali azuciyarsa kuwa sai jero addu’oi yake ubangiji yasa aci nasara sam bayasan wannan yarinyar tarasa komai nata a dalilinsa,, yana cikin wannan zancen zucin sai yaji wayarsa tai k’ara k’ararce tadawo da hankalinsa a jikinsa,,,,..+

Cikin sanyin jiki yad’akko wayar ganin mai kiran yasa yai saurin d’aga wayar yakara a kunnensa sannan yafita,, kusan 15mnts dafitarsa yadawo fuskarsa d’auke da fara’ah da murmushi yakalli mahaifinsa yace “Abbu maigidanane yakira yanzu nai waya dashi, yace yaturoman kud’i har naira dubu d’ari” cikin jin da’din abunda yafad’a masa yai murmushi yakallesa yace “masha Allah to Allah i biyashi yasaka mashi da alkhairi gaskiya Abdallah bawan Allah nan yana dawainiya dakai sosai yana k’ok’ari akanka harma damu iyayenka Allah dai yabiyashi da mafificin alkhairi” hakane Abbu gaskiya yana k’ok’ari kam sosai a kullum ina adduah Allah yabani abunda zan sakamashi koda kwatan kwacin abunda yake man ne saboda nasan bazan tab’a iya biyansa tarin alkhairanda yakeman ba. Abbu yai murmushi yace “to ameen”,,,…

Kimanin 30mnts kenan dashiga operation d’in saiga d’aya daga cikin doctor’s d’in yafito fuskarsa d’auke da murmushi yatinkaro gunsu Abdallah, ganinsa yana tinkarosu yasa suma suka tashi a tsaye suka tarbesa,, bayan yak’araso ne yafara masu congratulation yana tayasu murna saida yak’are murnarsa sannan yamasu bayani anci nasarar aikin komai anyi ankwashe dik sauran jinin dayataru acikin kwakwalwarta sannan kuma an wanke ta tas saidai balokaci d’aya zatadawo normal ba ahankali ahankali zata fara dawowa normal,,,,…

Sunyi matuk’ar farinciki ba kad’an ba musamman Abdallah wanda harda sujudul shukru saida yai sannan yarungume likitan yana masa godiya hakama Abbu yaita yiwa doctor d’in godiya,, saida tad’auki tsawon 30mnts sannan suka maidata d’akin hutu anan dinma sunhana kowa shiga ma’aikatansu kawai suka bari sudinga kula da’ita saboda matsalar kwakwalwa babba ce shiyasa suke bama masu matsalar kula tagaske, ganin haka yasa su Abdallah suka koma masaukinsu saida dare sannan suka dawo amma har lokacin ba’abarsu sunganta ba, ganin dare yayi sosai yasa suka koma gida hargobe sudawo k’ila zuwa lokacin ta farfad’o tadawo hayyacinta, Abdallah yamatsu sosai yaga KUBRAH ta tashi,,,..

Kimanin kwana biyar dayiwa KUBRAH operation amma har yanzu Norse’s kekula da’ita Aunty zinatu koda tazo iyakacinta zama da kallonsu idan sunshigo dubata saboda time by time sukanshigo suga kodawata matsala ne,, Arana ta shida ne aunty Zinatu na zaune bayan tagama sallar isha taga KUBRAH tafara motsi har tanaso ta tashi zaune, dasauri ta tashi tashi tazo gunta tariketa fuskarta cike da farinciki “K’anwata yi ahankali kinji jikinki ba kwari bara nakira Doctor” nan tasake maidata ta kwantar sannan tafita,,,..

15mnts dafitarta tadawo tareda wasu manyan likitoci da norse’s uku a bayansu, bayan sunshigo sukafara dube dubenta da kanta dasuka aske sumarta ta gefe suka daure da bandage saboda anan ne suka yanka sukai aikin, sunjima sosai suna dubata saidai Alhmdllh bawata matsala abunda suka zata shine yafaru batai loosing memory ba sun fahimci hakan  ne ta tambayoyinda sukamata saidai bakomai nata yadawoba amma sannu ahankali zata wartsake,, bayan sungama dubata sannan sukafita tareda kafa dokoki akanta,,,..

Bayan sunfita ne Aunty Zinatu tazo gunta tazauna tana kallon kyakkyawar fuskarta tana kuma ganin yanda take juya dara daran idanuwanta tana kallon sama azaton Zinat watakil itace batason kallo danhaka ta kyaleta bata takurata ba,, jim kad’an dafitar doctor’s din saiga Abdallah da Abbu sunshigo cikin farinciki da murna Abdallah yazo gun KUBRAH yai tsaye akanta yana kallonta, azuciyarsa mamaki yake sosai ashe dama akwai wanda yafishi kyau dik tsintsar kyanda ake fad’ar yanadashi amma yanzu dayaga fuskar KUBRAH saiyaga kamar ma shi mummuna ne saboda komai nata yafi nashi tindaga idanuwa hanci d’an k’aramin bakinta faffad’ar fuska kuma mai d’an tsayi baram ma idanuwanta sunfi birgeshi gasu manya kuma gasu farare tass nacikin kuma bak’i ne wulik kunsan idan farin abu yahad’u da bak’i sukan bada colour mai kyangaske,, yayi nisa sosai cikin tinani da mamakin kyan KUBRAH jin sautin maganar Abbu ne yadawo dashi hayyacinsa,,,..

Cikin muryarsa mai taushi yafara mata magana “k’anwata sannu yajikinki…?” shuru tamasa bata amsaba saidai ta d’ago da fuskarta tana juya idanuwanta, cigaba yai damata magana “yanzu inane yake maki ciwo” nanma dai shuru bata bashi amsaba tacigaba da juya idanuwanta tanaso ta tino inda tasan mamallakin wannan muryar amma takasa, Abbu yakula sosai da yanda KUBRAH ke juya idanuwanta tamkar mara gani danhaka yamatso kusa da’ita yakai hannunsa yashafa fuskarta sannan yazauna akusa da’ita, ahankali yafara mata magana “Yarinya yasunanki” shuru tamasa bata amsaba yacigaba da kallonta dakuma kallon yanda take juya idanuwanta,, hannunsa yakai yadinga juyasa adai dai idanuwanta amma ko ko kiftawa bataiba alamar kenan batamasan abunda yakeba,,,..

Jikin Abbu yai sanyi akasalance yad’ago yakalli su Abdallah sannan yace “Abdallah yarinyar nan bata gani” cikin razana da kid’ima had’e da tsintsan tashin hankali Abdallah yazaro idanuwansa yafirfito dasu waje “Abbu bata gani kuma kardai sanadin wannan K’addarar ne tarasa ganinta innalillahi wa’inna ilaihi raji’un” yafad’a alokaci d’aya…..

#/Vote

#/Share

#/Comment

”’AUFANA for life ”’

   *I.W.A*🖊

_Page 19~20_
Cikin sanyin jiki Abbu yace “banazaton haka Abdallah amma komadai menene ubangiji shine mafi sani” Abbu wallahi inatausayin yarinyar nan sosai Abbu banasan nazama silar rusawa kowa rayuwarsa a kullum burina shine nayi taimako amma yanzu gashi wata zata rasa farincikinta a sanadina” Abdallah kowa yasan niyyarka mai kyau ce danhaka natabbata bawanda zai zargeka akan wannan lamarin fatanmu shine Allah yabata lafiya kawai.cikin sanyi jiki da sanyin murya suduka suka amsa da “ameeen”,,,,..
Dasafe bayan Aunty zinatu tai sallah sai ta tashi ta tada KUBRAH kasancewar yau anan ta kwana, bayan ta tadata tad’auketa tashiga toilet tamata wanka ta tsabtaceta tass sannan ta daukota tafito da’ita, mai ta shafamata mai k’amshin gaske sannan tasaka mata kayanda Abdallah yasiyo mata, riga da wando ne blue jeans and pink t-shirt sunmata kyau sosai,, bayan ta shiryata sannan tahad’amasu tea mai kaurin gaske sannan tazauna tabata dakanta tanasha har tashanye gabad’aya tasake zubamata kuma tashanye tana shanye wannan tabarta hakanan saboda kartacikamata ciki da ruwa kawai,,,..+
Bayan tagama bata sannan takwantar da’ita jim kad’an saitaga tarufe idanunta alamun tai bacci ganin haka yasa tazauna itama tasha nata tea d’in,,,…
Haka Zinatu kekula da KUBRAH kamar k’anwarta uwa d’aya uba d’aya hakan kuwa bakaramin dad’i yakeyiwa Abdallah ba,, kimanin sati biyu sukai a k’asar Hindi anabama KUBRAH cikakkiyar kula, aranarda tacika sati d’aya da kwana hud’u aranar ne aka sallami KUBRAH saidai sun kafa dokoki akanta, time by time zasudinga kawota anaduba lafiyarta, sannan batasan hayaniya sosai, kada adinga takurata akan abunda bataso, sannan akula da bata maganinta kan lokaci idan har aka kiyaye wannan to insha Allah zatawarke sumul kamar ba’itaba,,,,..

Kwana d’aya suka k’ara sannan suka tattaro nasu i nasu domin dawowa gida Nigeria, aranarda zasu dawo kuwa shirye shirye da gyare gyaren gida Mami tasaka yaranta da’ita kanta suka dingayi domin tarbansu Abbu, haka su Abdallah ke kiran iyayensu Abbu da Mami,, dikda cikinta amma baihanata zage dantse wajen shirya liyafar tarban uban y’ay’anta, 1:00am na k’asar Hindu jirginsu yad’ago amma sai 6:00pm sannan suka iso gida Nigeria bayan sun iso sannan suka tsayarda a dai daita sahu sukashiga KUBRAH na ajikin Zinatu harsuka iso gida, koda suka iso kuwa gidan yacika da murna da farincikin dawowarsu,,,,..
A falour dika suka zube anamasu barka da dawowa lafiya, Mami ce takalli KUBRAH dake mak’ale a jikin Aunty zinat tace “y’ata yajikinki fatan kinsamu lafiya” shuru KUBRAH tai tanacigaba da ware dara daran idanuwanta. Har Mami zata sakeyin magana Abdallah yai saurin tareta dafad’in “Mami na barta tahuta ai k’anwar tawa gimbiya ce” yafad’a cikin murmushi sannan yakalli Aunty zinat yace “Aunty zee kishiga da’ita d’aki kisauya mata kaya da’alamu tanabukatar hutu ”  toshikenan baramuje. Tafad’a tana mik’ewa tsaye tareda mikarda KUBRAH sannan sukawuce,,,,..
Bayan sunfita ne Abdallah yakeyiwa Mami bayanin matsalar KUBRAH dakuma rashin ganinta, Mami ta tausayawa KUBRAH sosai ganinta k’aramar yarinya kyakkyawar gaske amma kuma makauniya saidai itama tace insha Allah ba’asanadin wannan matsalar ne tamakance ba da’alamu tincan dama makauniya ce,, jin tinanin Abbu dana mami yazo d’aya yasa hankalin Abdallah yad’an kwanta akan tinanin da yake, Abbu ne yatab’ashi jin anamagana ammashi yai shuru. Murmushi yai sannan yace “Abbu ina tinani ne akan yarinyar bansan wacece itaba haryazu tak’i tai magana gashi kuma bata gani bansantaba bansan iyayentaba barekuma gidansu ko wani nata tak’i tai magana barenatambayeta wacece ita kuma namaidata hannun iyayenta idan tawarke” Abdallah ka kwantarda hankalinka mana insha Allah komai zaitafi daidai mujira kawai takara jinsauki. Cewar Abbu kenan, nannauyan ajiyan zuciya yasauke sannan yamik’e tsaye yanufi d’akinsu,,,..
Dashigarsu Zinatu tamata wanka ta tsabtaceta sannan tafito tad’ibo mata abinci takoma dakanta tadinga bata tanaci hartak’oshi sannan tabata magungunanta tasha sannan ta kwantar da’ita cikin k’ank’anen lokaci bacci yad’auketa,, around 9:00pm Abdallah yashigo d’akin ya tarardaita tana bacci Salma da fatima kuma suna zaune suna karatu, gaisheshi sukai yakarb’a cikin d’aurewar fuska sannan yace “kuyi ahankali karku tadata tana bacci” toh sukace sannan yafita, wani mugun kallo sukabishi dashi SALMA ce tace “kiji dan Allah wai karmu tadata tana bacci kaman wata ‘yar gold” dama salma da Abdallah basa shiri saboda dukanta yake idan tai laifi kokuma yadinga mata fad’a da hantara hakan yasa sam basashan inwa d’aya, fatima kuma rashin sakin fuskanshi agaresu dakuma dukansu dayake shiyasa basa shiri sosai itama yana d’an ragamata saboda batada rashin in da fitsara kamar salma,,,,..
Itama fatima wani mugun tsaki tai sannan tace “wallahi ni ma haushin yarinyar nan nake dubafa yanda kowa yake wani nan nan da’ita kaman wata gold sudai suka sani k’ilama aljanace wallahi” dariya salma tai tace kai k’anwata bakida damafa. Haka suka dinga kushe KUBRAH saboda Abdallah da kowa nagidan yana nuna kulwarsa akanta itadai baccinta take batamasan sunayiba,,,…
Dasafe bayan Aunty Zinat tashiryata itama ta shirya saita rik’o hannunta ahankali sukafito falour, koda sukafito kuwa suka tadda Abbu da Mami da Ammar nan Zinat tagaidasu sannan suka zauna KUBRAH kuma tak’i tasake zinat tana nan manne ajikinta, kallonta Abbu yai cikin murmushi yace “‘yata bagaisuwa” shuru tai tana ware dara daran idanuwanta tana juyasu kai kace tanagani, mami ma murmushi tai sannan tace “Abbu wallahi yarinyar nan jinta nake kamar jininace idan ina kallonta dakuma yanayinta sainaga kamar nasanta kokuma tanaman kama da wani wanda nasani sannan wallahi tinda nafara ganinta naji kaman nasanta ko wani nata” nima haka nakeji wallahi kaman jinina ce Allah dai yabata lafiya kinga idan tasamu sauki saitafada mana iyayenta mu maidata a hannunsu. “hakane toh Allah yabata lafiya” suka amsa da ameen,,,,..
Abdallah ne yashigo Ammar ya kallesa yace “kai kai kai brother wannan tsadadden wankan fa kaganka kuwa saikace wanda zaije tad’i ko neman aure” yafad’a cikin tsokana yana dariya, d’an dukan wasa yakaimasa yana fad’in “kaganka ko” a tsakanin Abdallah da Ammar akwai nisan shekaru amma dikda haka baihanasu wasa da junansuba kuma Ammar nabama Abdallah girmansa sosai,, k’arasowa yai yaduk’a cikin ladabi yagaida iyayensa sannan yayiwa Aunty Zinat barka da kwana takarb’a cikin fara’ah “barka dai d’an k’anena inakuma za’aje da wannan gayun haka kuma da wannan safiyar” murmushi yai yana shafa sajensa da sumar kansa batareda yabata amsa ba, akusa da’ita yazo yazauna tareda rik’o hannunta yataso da’ita cikin murmushi yace “k’anwata kintashi lafiya ya jikinki” inda taji sautin muryar nafitowa tabi da kallo kamar tana ganin mamallakin muryar hannayenta takai a fuskarshi tana shafawa, da tsinin hancinsa tafara cin karo sannan takai bakinsa daganan sai idanuwansa sajensa daganan kuma tawuce da hannayenta izuwa cikin sumarsa tana shafata tareda cusa hannayenta aciki,,,..
Wani yanayi yaji yafara bak’untarsa Shauk’i dakuma wani yanayi wanda who kansa baisan yazai kwatantashiba,, ahankali ya lumshe idanuwansa saboda yanayinda yakeji.jin abun nata nanema yawuce saboda jin hannunta dayai a k’irjinsa tana shafawa har takai ga kan nipples d’insa, dasauri yarik’e mata hannu yana k’ak’aro wani murmushi yace “k’anwata mekike so ne” shuru tai tareda komawa jikin zinat takwanta, Aunty zinatu ce tace “tahakane suke fahimta dakuma sanin mutane nima jiya haka taman daina tambayanta sunanta” murmushi yai yace “ok”,,,,,..
Juyowa yai yakalli su Abbu yace “Abbu inaso ne naje gunda nabige yarinyar nan nayi tambaya ko Allah zaisa nasamu nawanda yasanta” ok to Allah yasa adace. Abbu yafad’a  mami ma hakan tace hakama Zinat, Ammar ne yakallesa yace “bro idan balaifi zan rakaka” murmushi yai yace “je kashirya kasameni a mota inajiranka ” yafad’a yana mikewa tsaye yawuce shima yashiga ciki yashirya yafito sannan suka kama hanyar garin ZAGA….

#/Vote
#/Share
#/Comment

”’AUFANA for life ”’
    *I.W.A*🖊® *INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION~I.W.A*📚

    *( ơŋщąγɖ ɬơɠɛɬɧɛγ )*

    _*GANI GA WANE….*_🌷

_*STORY & WRITING ~ BY*_

      _*AUFANA*_✍

_Whattpad@Aufana8183_

_*Devoted to – Maryam Abdallah and Maryam ( mamu gee ) my granny’s*_

  _*PAGE 21~22*_

_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_

Aranar kusan wuni sukai wajen neman wanda yasan KUBRAH ko wani nata kokuma gidansu amma shuru basusamuba, abun yad’agawa Abdallah hankali bakad’an ba kuma ransa baimasa da’di ba yaso yagane iyayenta saboda yamaidata hannunsu, haka suka gaji da yawo suka dawo gida ran Abdallah a b’ace,,,…

Bayan sundawo yafad’awa iyayensa basu sami wanda ko yasan iayayen KUBRAH ba mutum d’aya ne akace shi k’ila yasanta wani mai shago a bakin titi saidai ance yaje k’auyensu kuma ba’asan lokacinda zai dawo ba,, cikin hikima dakuma dabara irinta mai shekaru Abbu yadinga kwantarwa da Abdallah hankali karya damu sucigaba da yimata addu’ar samun sauk’i idan har tawarke ai ita dakanta zatafad’i ko wacece ita,sannan kuma yai masa alk’awarin zasu tayashi rik’on amanarsa har izuwa lokacinda zai maidata a hannun iyayenta,, jin zantukan mahaifinsa sunmatuk’ar kwantar masa da hankali nan yayiwa mahaifinsa godiya dakuma yimasu fatan gamawa da duniya lafiya,,,,..+

Cikin murmushi Abbu yakalli Abdallah yace “Abdullahi to dawanne suna zamu dinga kiranta dashi kamin komai nata yadawo” hmm….!!! Yasauke nannauyan ajiyan zuciya sannan yace “RAIHAN inaso mucigaba da kiranta da raihan” to shikenan ai Raihan sunane mai da’di kuwa to Allah yabata lafiya yakuma tayaka rik’on amanarka. Nan dik suka amsa da ameeen,,,,…

Haka rayuwa tacigaba da tafiyarwa KUBRAH wacca tadawo RAIHAN yanzu, tanasamun cikakkiyar kulawa sosai abinci nakwarai wanda ma bata tab’a tinani ko zaton zataciba,, aranarda tacika sati biyu da dawowa aranar Abdallah yadauketa tareda aunty zinat sukaje kasuwa yamata siyayyar kayan sakawa harda kayan make-up da dai komai dik wani abu wanda mace zata buk’ata saida yasiyamata shi,, dasuka dawo kuwa su Salma sukaita dariya wai makauniya ce za’asiyawa kayan make-up to dawanne idon zatayi kwalliyar, suna fad’a suna kyalkyala dariya,,,..

Aranarda tacika wata biyu sukaje wata babbar hospital d’inda ke cikin garin aka ciremata bandage d’inda akasakamata aka daure gunda akayanka, Alhmdllh sunduba aikin yai kyau sosai nan suka sake rubuta mata wasu medicines d’in Abdallah yasiyo had’e da injection wad’anda za’acigaba dayimata, bayan yasiyo sannan suka d’orata akan wasu na’urori suka duba cikin brean nata sukaga bawata matsala sannan suka sauketa Abdallah yadawo da’ita iga,, haka yakeyi dik bayan wata biyu saiya kaita anduba lafiyarta ganin komai Alhmdllh lafiya sai k’aruwa take yasa sukamaida zuwan nasu dik wata uku ko hud’u kuma dik sukaje saisunga ansami cigaba,,,,,..

Zaune take itakad’ai  acikin lambu tanashan iska a gefenta kuma sandarta ce wacca Abbu yasiyomata, wajen yai tsitt iska mai dad’i nahurowa tsintsaye na kuka mai d’aukeda sauti mai dad’in ji, tai shuu kamar tana nazarin wani abu kwatsam saitaji sautin wata sarewa mai d’an karen dad’i sautin ta gefenta na dama yake hurowa da’din sautin tamkar kanari wanda sautinsa yafi kowanne sauti da’di, cikin sauri tamik’e tsaye tafara bin inda takejin sautin nabugowa tamkar ta tab’a jin sautin,,,,,..

Cikin sauri harda sassarfa takeyin tafiyar saidai kash dikda saurinda take saida mai busar yatsereta saboda shi a waje yake itakuma a cikin filin gida,, tsaye tai tanajin haushin abun ji take kamar tatsere dagudu tacimmasa, cikin damuwar rashin sa’arda tai tajuyo tadawo tazauna, batafi 5mnts da zamaba taji dik wajen ya’isheta kawai tamik’e tawuce cikin gida kasancewar yanzu ko’ina tanakai kanta tasan ko’ina nacikin gidan, koda tashiga falour ta tadda Mami a zaune Salma namata tausan k’afafunta dasukayi k’aba saboda nauyin cikinta, mami naganinta tai murmushi tareda fad’in “aa ‘yar yayan ta andawo daga lambu” saida ta zauna kusa da mami sannan tace “Eh mami na nagaji da zamane shine nadawo ciki” ok ai hakan nadakyau adinga d’an motsa jini. Ananma falon bata wani jimaba tawuce d’akinsu Salma kuwa wani mugun kallo ne tarakata dashi har tashige ciki batasan mami takula da’ita ba,,,..

Da dare har Zinat tamata shirin bacci sun kwanta saiga Abdallah yashigo saboda dama al’adarsa ce kowanne lokaci yadawo tosai yazo yaganta yaga lafiyarta hakama idan zai fita da safe saiya shigo yaganta,  tana a kwance kanta na’acinyar aunty zinat yashigo cikin sallama aikwa tanajin muryarsa tamik’e dasauri a zaune tana murmushi k’arasowa yai shima cikin murmushin yazauna a kusa da’ita, cikin ladabi kamar yanda aunty zinatu takoya mata tagaidashi tareda yimasa barka da dawowa cikin fara’ah ya’amsa mata tareda shafa fuskarta “k’anwata yakike fatandai bawanda yatab’a man ke” murmushi tai sannan tace “yayana kasiyoman abunnan mai dad’i ko” dagashi har aunty zinat hardama su salma saida sukai dariya,ledarda yashigo da’ita yad’akko sannan yabud’eta yaciromata chocolate yaballemata sannan yabata tareda fad’in “to gashi k’anwata ai bazan tab’a mantawa da sak’on y’ar k’anwata ba” cikin jin dad’i tamik’o hannunta danufin takarb’a sai kawai taji yakaimata abaki aikwa nan taware hak’oranta tagutsura tafaraci tana lumshe dara daran idanuwanta, binta yai da kallo cikeda sha’awar yanda take tauna chocolate d’in kamar batasan taunasa gakuma dara daran idanuwannan nata datake lumshesu saboda dad’in d’and’anonda takeji,, saida tacinyeshi dika zaisake b’allamata wani aunty zinat tai saurin cewa “haba kabarta haka dawannan kayan zakin har gobe darefa yayi munaso mu kwanta” murmushi yai sannan yace “to anbari big aunt” yafad’a yana ajiye sauran kayan dayasiyomata agefenta sannan yagyara mata kwanciyarta yareda lullub’amata blanket  yatofeta da addu’oi sannan yamasu saida safe itama cikin fara’ah tace masa “ya Abdallah saida safe tafad’a tana d’agamasa hannu alamar bye bye” cikin jin da’din abunda tamasa yafita yana murmushi tareda janyo masu k’ofa yarufe,, dik abunda ake Salma da fatima nagani idonsu biyu basuyi bacci ba aikwa takaici kaman yakashesu Salma ce take fad’in “dan Allah duba yanda ya Abdallah ketawani faman dariya da wannan tsintacciyar magen amma idan mune yamana kaman baitab’a sanin wani abu waishi dariya ba” fatima kuwa tsaki kawai tai saboda ita takaici yama hanata magana,,,,..

Haka Abdallah ke matuk’ar kula da RAIHAN har tasaba dashi sosai komai zakiji tace yayana shima kuma haka k’anwata,,,, bikin Aunty zinatu ya tashi danhaka yanzu kullum acikin shiri Abdallah yad’inkawa RAIHAN kaya har kala biyar nabiki bayan kuma Abbu yamasu anko har kala biyu, saura sati d’aya afara hidimar bikin Mami tahaihu cikin dare a asibiti suka kwana sai 10:00am sannan suka dawo, tahaifi santalelen d’anta kyakkawa sosai,,,,..

Aranar suna kuwa bawani taro akayiba kasancewar Abbu yahana taron biki acewarshi tinda gawani babban bikin zaizo danhaka basai kowa yazoba ajira har bikin Zinatu,,,,..

Saida mami tai sati biyu da haihuwa sannan akacigaba da hidimar shagalin zinatu,, wata ranane da safe RAIHAN na’a d’aki itada aunty zinat tana murnar dinkunanda yayanta yayomata saitaji fatima nakiranta tace kuma tana a falour tazo,,,..

Koda tafito tana tafiya tana dogara ‘yar sandarta kwatsam saitaji ta taka wani abu yashigemata acikin k’afa, ashe su fatima ne suka had’a plan Salma tafashe kwalba tazuba a wajen itakuma fatima takirata akan tazo tad’ibo mata ruwa a kitchen,, jin wata k’ara mai k’arfi data buga saboda wani azababben zafi dataji a k’afarta yasasu Zinat da k’awayenta dake d’aki sukayi saurin fitowa musamman Zinatu saboda ita harda guduma take, su Salma kuwa wani tsallen jin dad’i sukai harda tafawa dan murna…

#/Vote

#/Share

#/Comment

”’AUFANA for life ”’

    *I.W.A*🖊® *INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION~I.W.A*📚

     *( ơŋщąγɖ ɬơɠɛɬɧɛγ )*

    _*GANI GA WANE….*_🌷

_*STORY & WRITING ~ BY*_

     _*AUFANA*_✍

_Whattpad@Aufana8183_

_*Devoted to – Maryam Abdallah and Maryam ( mamu gee ) my granny’s*_

_*My Blood Sister Naja’ert kínα rαínα ínα mαtuk’αr k’αunαrkí αrαínα kєtαdαвαn cє kє wαní в’αngαrє nє nαjíkínα wαndα ѕαídαѕhí zαn íчα rαчuwα, hαk’ík’α kє ‘чαr uwαcє tαgαrí ínα mαtuk’αr k’αunαrkí αrαínα ínα αlfαhαrí dαkє, much lσvє u mч вlσσd, í wíll nєvєr ѕtσp frσm lσvíng u mч ѕíѕtєr вcσzz u αrє mч вlσσd ínα k’αunαrkí mσrє, σnє lσv 💘🌷*_

+

    _*PAGE 23-24*_

_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_

Ahargitse kuma rikice Zinat ta’iso gunta koda ta’iso kuwa tafad’i a k’asa tana kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro tasaka hannayenta dika tarik’e k’afar, cikin kid’imewa tarik’ota tareda tambayar abunda ke faruwa itakuwa dikta kid’ime ganin jini yanazuba a k’asan k’afar, aunty zinat ma hankalinta yatashi saboda ganin jini a k’afar nan cikin sauri tad’ago da k’afar tanaduba gunda jinin kefitowa, tsagin kolbar tagani kafe a k’afarta nan tasaka hannu domin tacire sai RAIHAN tai wata iriyar k’ara mai sauti saboda zafinda taji,,,,..

K’ararda tai yasa tadakatarda cirewa, Abdallah dake fitowa yashirya zaifita neman halak d’inshi yajiyo sautin k’arar RAIHAN aikwa akidime ya’iso wajensu cikin tashin hankali yafara tambayar Zinatu abunda ke faruwa, ganin jinindake zuba a k’afar ‘yar k’anwarshi kuma amanarshi yasa yakasa tsayawa jin komai kawai yad’auketa yafita da’ita itakuma Zinat taje tafad’awa Mami abunda ke faruwa sannan itama tad’akko hijab d’inta tabi bayan Abdallah,,,..

Kai tsaye wata hospital yawuce da’ita yana isa kuwa aka karb’eta aka shiga wani d’aki da’ita saboda ganin jinindake zuba a k’afarta, saida sukamata wata injection takashe zafi sannan suka samu sukaciro wannan tsagin kwalbar, bayan sunciro sannan suka wanke wajen suka saka bandage suka daure sannan suka mata wata injection tabacci nantake kuwa bacci yai awon gaba da’ita,,,,..

Aranar dai baije ko’ina ba saboda sam yakasa samun nutsuwa haka yawuni acan saida Ammar yaje sannan yadawo gida shima dan yamatsa masa ne,, aunty zinat ke kwana acan Ammar kuma yawuni kasancewar shima yadawo hutun bikin Zinat ne, a d’an zamanda Ammar keyi anan gunta yasa tasaba dashi saboda sak halayyarsa irinta Abdallah ce saidai shi yafi Abdallah wasa da dariya gashikuma dasan raha da barkwanci sai yaita sakata dariya da barkwancinsa hakan yasa tasaba dashi sosai,,,,..

Yau kimanin kwanan RAIHAN hud’u a asibiti wanda kuma yai daidai da saura kwana d’aya agama shagalin bikin Zinat gobene za’ad’aura aure sannan amarya ta tare a gidanta da dare bayan kwana hud’u kuma suwuce k’asar Dubai kasancewar mijin d’an kasuwane any time yana wajen kasuwancinsa sam baya zama gida,, haka akasha shagalin bikin bada RAIHAN ba dikkannin d’inkunanda Abdallah yamata bawanda tasaka har agama komai, aranar Jumma’ah aka d’aura aure amarya ta tare a gidanta aranar assabar kuma kowa yawatse yakoma gidansa na nesa kuma suka koma k’asashensu kowa na kewar d’an uwansa,,,,..

Aranarda kuma zasu wuce saida tazo har asibiti tai bankwana da RAIHAN aikwa nan taita kuka dakyar akarabata da jikin zinat sannan suka wuce,, tausayinta ya mamaye zuciyarsa dama gangar jikinsa gabad’aya baisan lokacinda yajanyota jikinsa yarungume tareda cusata acikin faffad’an k’irjinsa sannan yasanya dika hannayensa yarufe, ahankali kakejiyo sautin kukanta shikuma yasaka hannunsa d’aya yana bubbuga bayanta alamar rarrashi, saida yaji sautin kukan nata yaragu amma kanajiyo sheshekar  kukan nata sannan yajanyeta daga jikinsa, d’an duk’o da fuskarsa yai dai dai tata fuskar sannan yai murmushi yace “kidaina kuka k’anwata kinji namaki alk’awari insha Allah zankaiki har gidan Auntyn ki zinat” jin abunda tafad’a yasa tai saurin d’ago da fuskarta tareda ware dara daran idanuwata kamar tana ganinsa tace “Allah yayana zaka kaiki gidan Aunty Zinat” cikin murmushi yace “Eh amma sai idan kindaina kuka” Allah nabari yayana. Tafad’a tana share kwallanda yazubo mata cikin dariyar yarintar RAIHAN yace “yawwa my k’anwatyy na to yanzu kinga jira har asallameki kik’ara warkewa dakyau sai inkaiki gidan Aunty Zinat” taji dad’i sosai nantaita murna tana tana fara’ah harda dariya shikwa sai kallonta yake saboda shi koda acikin b’acin rai take to birgeshi take kuma a kullum gani yake kamar k’aramata kyau ake musamman idan tana dariya fararan hak’oranta nabayyana masu d’aukeda wishirya had’e da doddoriyar juna wani kan wani, gakuma dimples beauty point d’inta yana lutsawa koda murmushi kawai tai saiyaji tausayinta nak’ara shigarsa,,,,..

STORY CONTINUES BELOW

Kimanin satinta d’aya da kwana biyu a hospital sannan aka sallameta ganin tawarke sumul ko’ina tana zuwa batareda anrik’eta ba, saidai tadawo amma kewar Aunty zinat tadameta danma ga Ammar yana sakata nishad’i Salma da fatima kuwa baruwansu da’ita kusan kullum saisun sami sharrinda zasu kullamata wani sucinasara wani kuma basuci haka tacigaba da rayuwa acikinsu Mami ce kekula da’ita sosai har karatun islama tana koyamata kamar yanda take koyawasu fatima kuma tanajin dad’i sosai saboda tafahimci RAIHAN akwaita da kaifin basira, ganin k’ok’arinta dakuma san karatunta yasa Mami tarok’i Abbu akan yad’auka masu malami wanda zaidinga zuwa yana masu karatu haka kuwa akayi acikin satin Abbu yasaka Abdallah yad’akko wani malamin islamiyyarsu Fatima mai suna Alk’asim malami ne wanda akejidashi sosai yakwari sosai musamman afannin hadda,,,,..

Ranar Saturday itace ranarda malamin zai fara zuwa yaukuma takasance Saturday danhaka tinsafe RAIHAN tafara shirin karatu saboda dama tanasan karatu wani lokacin har kuka take tanaso tabisu fatima islamiyyarsu amma sai mami tahana to yau gadama tasamu,,,..

A dai dai yanda aka tsara karatun shine ranakun karatu sune Saturday,  Sunday, Monday,  Tuesday, sai Wednesday,, za’ashiga da 3:00pm sannan afito za’ayi haddah a wannan lokacin idan 4:00pm tayi sannan afito ayi sallah akoma idan kuma aka koma sai ayi b’angaren fikhu,  hadisi, dakuma sirrah domin sanin nasabar manzon tsira idan 6:00pm tai sannan arufe saikuma gobe,, wannan tsarin yabirge Abdallah sosai hakama Abbu,,,,..

Tafe take acikin wani k’aton hijab blue colour har k’asa dikda ba make-up a fuskarta amma hakan baihana bayyanar tsintsan kyanta a filiba, tafe take a hankali tana dogara ‘yar sandarta tazo dai dai k’ofar fita sai sukai kicib’is da Ammar zai shigo cikin gida, baya baya tai zata fad’i dasauri yakai hannunsa yarik’ota tadawo tafad’o sai akan k’irjinsa, jin wani shook dasukaji a lokacinda gangar jikinsu tahad’u yasa yaisaurin sakin k’ugunta daga rik’onda yamasa,, cikin in ina saboda yaji abunda baitab’ajiba akan wata ‘ya mace yace “RAIHAN inazakine kike nema ki kadani haka” dariya tai saboda taji muryar abokin wasanta tace “La ya Ammar dama kaine Allah nad’auka yayana ne harnafara shirin bada hak’uri amma tinda kaine bawani hak’urinda zan baka saidai ma kai kabani” tafad’a tana dariya sannan tawucewa saboda batasan tai letti zuwanta nafarko,, shima d’in dariya yai yace “Ok hakama zakice koh yamaki kyau zaki dawone ai” tawuce abunta batareda tasake masa magana ba,,,,..

Satinsu biyu da fara karatu Alhmdllh suna fahimta sosai konace tana fahimta saboda RAIHAN ce kad’ai ketsayawa karatun sukuwa daga wannan tace zataje fitsari sai waccan tace zataje tasha ruwa idanma anje d’in baza’adawo dawuri ba gakuma rashin kunyarda sukeyiwa malamin, wataranar Monday dasafe Abdallah yad’auki RAIHAN yakaita wata had’addiyar makarantar makafi inda yacikemata form saida akaimata komai nashiga sannan yad’akkota suka dawo, bayan sundawo ne take tambayarsa inane yakaita saiya fad’amata makarantar BOKO ne zaisakata saboda itama tai ILimi kamar kowa, bud’ar bakinta saitace masa ita batasan BOKO. kamar a bazata haka yaji zancen nata cikin mamakin abunda tafad’a yace “k’anwata bakyason BOKO to meyasa bakyaso…?” shuru tai tarasa amsarda zata bashi sai kawai tace “haka kawai nidai banaso” shima shurun yai yana kallon fuskarta kamar yana nazarin wani abu can kuma yasauke nannauyan ajiyan zuciya sannan yace “habadai k’anwata gimbiyata nikwa inaso kiyi BOKO kishiga cikin mutane ‘yan uwanki mata kiyi gwagwarmayar rayuwa sannan kema kizama cikakkiyar mace kamar kowacce mace sannan inaso kizamo mace tauraruwa bar koyi kamar sauran mata taurari kobakyason adinga koyi dake…?” yafad’a cikin murmushi yana kallonta,,,,..

Taji da’din zantukansa hakan yasa taji tasakko daga dokin nak’in da tahau, cikin dariya tad’ago da fuskarta kamar tana ganinsa tace “inaso yayana na’amince zanshiga BOKO kuma namaka alk’awari sainazamo tauraruwa abar koyi ga kowacce mace” yaji dad’in kalamanta sosai hakan yabashi kwarin guiwar taimakon rayuwarta koda kuwa komai nashi zai k’are ne,,,,..

Acikin satin aka kammala mata komai nashiga makaranta nantake tafara zuwa primary 2 suka kaita saboda girmanta idan tai k’ok’ari sukarata idan kuma tai akasin hakan sumaidata baya ko subarta anan,, yanzukam RAIHAN balokacin zama wani tinani ko damuwa tin 7:00am idan taje School sai 2:00pm ake dakkota  idan sundawo kuma 3:00pm anshiga islamiyya saikuma 6:00pm sannan adawo haka rayuwa kecigaba da tafiya kuma tana maida hankali sosai,,,,..

Ahalin yanzu hizifi biyar ne akanta kasancewar dik karatin da hadda ake mata saboda ba idanunda zata duba takaranta, wani abun mamakin da Abdallah da Abbu ke gani shine dik inda tawuce kace takaranta yanzinnan  zata karanta harma da inda bakaceba bare kuma gefen fikhu fiye da rabin kashe kashen tsarki tasani wankan tsarki dakuma abunda kesakawa ayisa hukuncin jinin haidha dana nifasi,, abun yana matuk’ar basu mamaki k’aramar yarinya kamar RAIHAN amma tasan wad’annan abubuwan dako su Salma dasukai k’anwa da’ita basusaniba,, hmm nikwa nace yama za’ayi susani hassada tashiga acikin zukatansu tai kane kane,,,,..

Wata rana ne RAIHAN tafito daga kitchen tad’akko ruwa acikin fridge tana tafiya ahankali tana dogara y’ar sandarta kawai saitai kicib’is da Fatima tazo zata wuce, ruwandake a hannun RAIHAN sai suka zubar mata ajiki Cup d’in kuma yafad’i ak’asa,, cikin fushi da masifa taware hannunta tawanka mata mari har biyu a fuska sannan tasaka k’afarta tahankad’ata tafad’i a k’asa sandarta tafad’i tasake d’aga hanu zata mareta saitaji anrik’e hanun tabaya,,,,..

Juyowa tai cikin fushi domin ganin wanda yahanata sauke takaicinda tadad’e tanaji, Abdallah tagani a tsaye yasha kunu kamar ba’itaba sanin wani abu waishi dariya ba fuskarnan tasa kamar namijin zaki acikin dawa idan yananeman nakaiwa baki,, batareda yacemata komaiba yai baya da hanun nata sannan yai jifa da’ita a gefe sannan yawanketa da kyawawan marika marasa adadi sai wanka mata yake kawai can dayaga kamar hakan baiyiba kawai yazuge belt d’insa yafara zabga mata itakuma tanajada baya tana kuka mai sauti tareda neman yafiyarsa, baidaina dukantaba harsaida Mami dake d’akinta tajiyo sautin kukanta tafito dasauri,, ganin abundake faruwa yasa taisaurin zuwa ta tare Abdallah tareda daka masa tsawa akan yadaina dukanta, ganin Mami yasa yatsaya yana huci tamkar kumurcin maciji,,,,..

Cikin masifa Mami take tambayarsa abundake faruwa, dakyar yadaidaita kansa tareda tsagaita fushinsa sannan yafad’amata abunda yafaru dikda mami tasan halin fatima amma batace komaiba tadaibama RAIHAN hak’uri sannan tahad’asu dika tamasu fad’a tareda masu nasiha mai ratsa zukata,, jikin fatima yai sanyi sosai nantake tai nadamar abunda take tajuyo tabama RAIHAN hak’uri tareda neman yafiyarta itakuwa dayake dama mai sanyi halice nantake tace bakomai Allah ya yafemana baki d’ai suka amsa da ameeen,,,,..

Tindaga wannan lokacin Fatima tazubda makaman yak’inta tarungumi RAIHAN da hannu bibbiyu hakan kuwa bak’aramin dad’i yayiwa Mami da Abdallah ba, itakuwa Salma wani bak’inciki ne yadad’a kamata dakuma takaicin abunda fatima tai nankuma tak’ara tsanar RAIHAN tareda cin burin k’untata mata,,,,,…

_To jama’ah hausawa sunce waiwaye adon tafiya danhaka bara mu waiwayi mutan KEBBI muji ya’ake ciki ne_

        ******  *****  *****  *****

*KEBBI CITY…..*🌷

Ahalin yanzu asma’u rayuwa take cikin k’uncin da maraicin rashin y’arta dakuma rashin sanin a wanne hali take ciki shin tana raye ma ko bata raye dik batasaniba, rashin KUBRAH yazamo tamkar ma mutuwarta ce Amadi yazamo kamar maraya yai kuka yai kuka kamar ransa zai fita  hakama su inna da malam sunyi kukan rashin KUBRAH yanzukam sunbarwa Allah komai suncigaba da addu’oi suna kaiwa Allah kukansu,,,,..

Tabbas Allah maji rok’on bawansa ne…

#/Vote

#/Share

#/Comment

”’AUFANA for life ”’

  *I.W.A*🖊

® *INTELLIGENT WRITER’S ASSOCIATION~I.W.A*📚
    *( ơŋщąγɖ ɬơɠɛɬɧɛγ )*

    _*GANI GA WANE….*_🌷
_*STORY & WRITING ~BY*_
     _*AUFANA*_✍
_Whattpad@Aufana8183_
_*Devoted to – Maryam Abdallah and Maryam ( mamu gee ) My granny’s*_
   _*PAGE 25~26*_

_*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*_

Rashin KUBRAH yasa Amadi yakasa zama a garin ZAGA yashirya yakoma k’auyensu har saida yai kusan wata uku sannan yadawo yana taya malam tanimu kula da almajirai da d’alibai, adik lokacinda yatina da KUBRAH yakanji bak’in ciki wani lokacin ma har kuka yake yana zubda kwallah wani lokacin kuma sai yaita murmushi shi kad’ai idan yana tino da zamansu dakuma k’awancensu,,,,..+
Wata rana yana gyara kayansa saiyaga d’ayan a warwaronda yasiyamata ashe tamanta dashine lokacinda take zumud’in tafiya kasuwa, wasu zafafan kwallah ne suka zubomasa alokacinda yatina da ranarda yasiyomata su yasakamata da’irin murna da jin da’dinda tai, haka yaita kuka daga bisani kuma yabama kansa hak’uri,,,,..
Agun asma’u ma dai hakane kusan kullum tanarik’e da carbi tana kaiwa ubangiji kukanta Allah yahad’ata da ‘yarta koda a aljannah ne kai koda gawartace ma,, haka kullum taketa faman addu’oi danunawa Allah damuwarta,,,,..
       ******  ******  ******  *******

*YOLA ADAMAWA*

Rayuwa RAIHAN keyi mai cikeda jin dad’i da walwala tako’ina gata ake nunamata musamman Abdallah da Ammar dandai idan Ammar nagidan tofa ba’ita ba damuwa ko b’acin rai saidai Salma cedai har yanzu basushan inwa d’aya da’ita komai tai saitace baiyiba kokuma tamata fad’a ko tsawa dikda RAIHAN nasan Salma sosai amma dole takesa tadinga ja dabaya da’ita,,,,..
Karatunta kuma sai cigaba yakeyi tanajin dad’in School d’insu na BOKO harma tai k’awa maisuna Ruk’ayya itama makauniya ce mahaifinta mai kud’i ne sosai kuma itama tanada basira sosai shiyasaka ma zamansu yai da RAIHAN,, Ammar yakoma School yabar RAIHAN da kewarsa sosai dan harda kuka tai lokacinda zai tafi saida Fatima taita rarrashinta dan yanzu RAIHAN da Fatima anzama k’awaye Salma kuwa ko kallo basu ishetaba, haka yatafi yabarta cikeda kewarsa bayan sunwuce shi da Abdallah danshine zaiyimasa rakiya sannan suka dawo cikin gida,,,,..

Rayuwa natafiyarmata dai dai yayinda karatunta kuma keta cigaba yanzu takammala primary har tashiga secondry jss1 islamiyya ma tana maida hankali sosai dan yanzu hizifi shida yarage mata tahaddace Qur’an wanda yai dai dai da shekarunta gomasha hud’u  danma anamayarda’ita baya datini tajima da haddaceshi, fannin sauran littafai ma tana k’ok’ari sosai,,,,..
       *******  *******

*BAYAN WASU SHEKARU…..*🌷

Kwance take akan gado Fatima kuma na’agefenta rik’eda Qur’an RAIHAN kuma nakarantawa itakuma tana dubamata inda tai kuskure saita gyaramata, Mami ce tashigo rik’eda hannun autanta Ansar yanazuba shagwab’a tace “au nankuke naketa faman kiranku a falour” RAIHAN ce tace “Eh mami muna nan tilawa muke kan lokacin shiga islamiyya yayi” to ai hakan nadakyau amma kutashi muje kitchen kutayani aiki kan lokacin shiga islamiyyar yai.  “To” suka amsa atare sannan suka tashi fatima tarik’a hannun RAIHAN suka fita saboda idan dai har suna a tare toh fatima bata bari RAIHAN tadinga dogara sanda saidai tarik’a hanunta har suje dik inda zasuje sudawo inma kagansu kan hanya tobazaka san RAIHAN makauniya bace,,,..
Atare sukashiga kitchen d’in suka k’arasa girkin d’an aikinda RAIHAN zata iya dik sai fatima tabata tayi kuma tanamata explanation yanda ake had’a girke girke dakuma iya adadinda kayanda girkin yake buk’ata, haka suke dik lokacinda suke girki atare wannan yasa RAIHAN ta’iya girki daban daban kala kala danma Mami nahata shiga kitchen ne da har girkin saitayi wata rana,,,,..
Wata ranar Saturday ne kowa yana a gida saboda weekend ne su RAIHAN sundawo daga islamiyyar safe, zaune suke suduka a falour suna fira saiga Abdallah yashigo fuskarsa d’auke da fara’ah mara misaltuwa a d’ayan hannunsa kuma yana rik’e da wata takarda fara mai girma,, k’arasowa yai yazauna kusa da Abbu cikin fara’ah yace “Abbu dubakaga wani abun alkhairi dayazoman yanzu” shima Abbu cikin murmushi ya amsa yafara dubawa yana karantawa, bayan yagama yad’ago fuskarsa d’auke da murmushi yace “masha Allah Alhmdllh tabbas Allah shine abun godiya dik abunda kai hak’uri akansa to tabbas zakaga k’arshensa ba’abunda zance sai Allah yasanya alkhairi yakuma bada sa’ah kuma yatayaku rik’o” fad’ad’a murmushinsa yai sannan ya’amsa da “ameen” cikin rashin fahimta Mami tace “mufa kunsakamu a duhu meyake faruwa ne kufadamana mana muma mutayaku murna” dariya sukai sannan Abbu yace “Abun alkhairi ne yazomana kinsan dama maigidansa yakarb’i takardunsa tinda dad’ewa” mami tace eh. “toshine sai yanzu Allah yanufi da za’asamu aikin kuma Alhmdllh aikin maid’an tsokane (Custom Security)” gyara zamanta tai ta tashi daga zaunenda take cikin jin dad’i tace “kai masha Allah Alhmdllh amma wallahi naji da’di sosai Allah i sanya alkhairi yabada ikon kiyaye gaskiya dakuma gujewa b’ata shikuma wannan bawan Allah ubangiji yabiyasa da mafificin alkhairi” nan suduka suka amsa da ameen,,,,..
RAIHAN tamatuk’ar jin da’din wannan abun tai murna sosai harda tsalle kaman tarungume Abdallah dan murna shi kansa saida yai mamakinta ganin yanda takeyi yakasa cemata komai sai murmushi yake yana kallonta,, hakama fatima tanuna jin da’dinta sosai kuma tamasa Allah i sanya alkhairi tareda masa kyawawan addu’oi shim yaji da’di sosai, Salma kuwa tin lokacinda sukai masa Allah i sanya alkhairi batasake ko kallon inda yakeba shima kuwa bai damu da’ita ba danshi sam baidamu da sabgartaba barema yadamu dan bata nuna farincikinta ba,,,,..
Kwana uku dakawo masu offer suka fara shirye shieyen tafiya training, a ranarda sukai sati d’aya suka wuce k’asar OSUN wanda kuma zasu d’auki kimanin wata goma ana koyardasu yanda ake aikin,, lokacinda zai tafi kuwa har airport suka rakashi RAIHAN sai kuka take kaman ranta zai fita haka jirginsu yad’aga suna kallo sannan suka juyo suka dawo gida cike da kewarsa,,,,..

Dawowar Ammar daga School yakammala degree d’insa a FEDERAL UNIVERSITY dake k’asar KEBBI wato ( FUBK ) itace takauda kewar Abdallah da RAIHAN keyi any time indai ba school tosuna a tare saiko idan yafitane amma matuk’ar yana nan tozaka gansu a tare,, wata ranar Jumma’ah ne darana yad’auketa ita dasu fatima sukaje kasuwa sukai siyayya anan ne yasiya mata wani tsadadden zobe had’adden gaske ba gold bane amma idan kagansa zakarantse da Allah zoben gold ne aikwa taita murna tana tsalle, bayan sungama siyayya sannan suka dawo gida, bayan yasaukesu ne yafita saigashi yadawo tareda wani abokinsa nan suka wuce d’akinsu, basufi 15mnts dashigaba saiga RAIHAN da fatima sunshigo kawo masu drinks nan suka gaida Aliyu abokin Ammar sannan suka fita,,,,..
Bayan sunfita ne Aliyu yakalli Ammar yace “friend wacce daga cikinsu kakeman bayani” cikin murmushi yace “tagefen hagu wacca take sanye da hijab red colour” wata dariya yai sannan yace “gaskiya friend dole kaji kanasan yarinyar nan dan wallahi nima naji tamun bcoz she’s very beauty and tanada saurin shiga rai nima badan kafadaman ba danace inaciki kodayake yanzuma ai zaniya hawa sahu” wani kallo Ammar yamasa na kama rainani shikuwa saiya kyalkyale da dariya tareda kaimasa dukan wasa, saida yatsagaita dariyar sannan yasake cewa “Amma meyasa bazaka fad’amata ba yanzu tinda nagadai tagirma” aa not now. Kallonsa yai yace “Whay… Naga dai tagirma karfa kaje kai Saki zari kama tozo” dariya yai yace “wallahi kaban dariya insha Allah ma hakan bazata faruba” hmm.. to Allah yasa.yace ameen sannan suka wuce wannan zancen sukacigaba da harkan gabansu,,,,..
  Alhmdllh su RAIHAN ankammala jss har anshiga ss girmanta kuwa sai k’aruwa yake ahankali cikar budurci ke b’ub’b’ugo mata, wata rana ne tana School k’awarta Ruk’ayya tazo class d’insu koda tazo saita tararda’ita kwance sai murk’ususu take tana kuka, cikin damuwar sanin abunda yake damunta tafara tambayarta “RAIHAN lafiya meke damunki…?” rasa tai mema zatace yake damunta saboda wani azaba datakeji, dakyar ta’iya fad’ar “cikina”….
*kuyi manage kuma kuyi hak’uri da tyaiping error balokacin editing gashi kuma rubutun sauri ne*👏
#/Vote
#/Share
#/Comment
”’AUFANA for life ”’
    *I.W.A*🖊

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page