HANGEN DALA CHAPTER B KARSHE

 HANGEN DALA CHAPTER B KARSHE

👁️‍🗨️👁️‍🗨️ *HANGEN DALA*👁️‍🗨️👁️‍🗨️

       _Ba shiga birni ba_

©️®️ *Safiyya Abdullahi Musa Huguma*

Haske Writers asso 💡

*BABI NA SHA UKU*

*ZAKU IYA SAURAREN LITATTAFAINA A TASHATA TA (SAUTIN HIKIMA) DAKE A YOUTUBE,SAUQI GA MUTANEN DA BASU SON KARATU DA KANSU SAIDAI SAURARE,LITATTAFAN NAWA SUNE KAMAR HAKA*

*ALKAWARIN ALLAH*

*DAURIN BOYE*

*KUNDIN KADDARATA*

*MUTUNCIN MACE*

*DANGANTAKAR ZUCI*

_DA WASU SABBIN DA ZASU ZO MUKU NAN GABA KADAN DA YARDAR ALLAH_1

13

“Idan ita batasan tsarina ba,batasan qa’idar gidan ba aiku kun sani,saboda haka daga yau koda wata cikinku keda lalura ban yarda abarmin yara da yunwa ba,kada irin hakan tasake faruwa kunajina?” Mmn amir ce tasoma magana,cikin qanqan dakai da tausa murya

“In sha Allah irin hakan ba zata sake faruwa ba”, mmn ummi bakinta taja ta tsuke,duk da ranta ya mata dadi na fadan da yayi ma rufaidan,kuma wala’alla yaudin suyi kwanan takaici,daga haka mmn amir ta miqe tafice,mmn ummi  ma tarufa mata baya saboda shiga kitchen tadebo abincin.

+

Shima miqewa yayi yafice da ummi a hannunshi wadda taqi yarda ya ajeta,yunwa yakeji sosai don yau yajima akasuwa,abinci yake da buqatar ci,don haka yawuce dakin rufaidan kai tsaye.

Zaune yasameta a falo,qafarta daya kan daya,kallo daya ta daga kai tayi masa ta watsar dashi taci gaba da kada qafarta.

Falon cike da sautin waqa,baice da ita komai ba yasoma wucewa ya rage waqar sosai ta yadda ko tashinta bakaji kwata kwata sannan yadawo yazauna kan daya daga cikin kujerun falon yana dubanta.

Qwarai take bashi mamaki,batasan idan tayi laifi ta nuna tayi laifi ba bare ta bada haquri,kullum ita keda gaskiya,saita dauki fushi da kumbure kumbure,tsahon zamansu bazai iya tuna sau nawa tace kayi haquri ba,saiya kauda wannan tunanin yace

“Bani abinci” kai ta tada ta dubeshi kana ta dubi yarinyar hannunshi wadda tuni ya direta saman kujera ta kama kujerar tamiqe abinta tana ta tsalle,saikace shi yafi kowa yara a duniya,motsi kadan yaranshi bini bini yadebo mata yara yashigo mata dasu,ba shakka sai tayi maganinsu,ba zata dauki wannan abun ba wlh,a rubar mata da carfet da katifar kujeru tun bata haifi nata ba ina dalili?

“Saikamaida yarinyar tukunna sannan kaxo kaci abincin” ta fada taba gyara xamanta,yabita da kallo mamakinta yana sake kamashi,yana ganin abun kamar almara amma yaga yana neman wuce gona da iri

“Ki bani abinci kawai ba ruwanki da ita” yafada adan kausashe,saita sauko tanufi inda abincin yake tana qunquni qasa qasa,sarai yajita amma saiya danne kamar baiji ba.

Tun a idanun yaga abincin bai masa ba,uban mai saman miya,ga qamshin attaruhu tun baikai gaci ba,abinda sam baicikin tsarinsa,saboda basir da kuma yara da kowa yasan ba kasafai sukeson abincin mai yaji ba,matan gidan sun riga da sun saba ma,kuma itadinma yasan ta jima da sani din tun kafin suyi aure,har sukayi auren ma bai fasa gaya mata ba idan hira tashigo,to amma sai bai tanka ba,harta gama zubawar ta tashi,ya sanya cokali yasoma ci.

Lomar farko yasoma jin matsaloli game da abincin kala kala,na farko miyar tacika gishiri,sannan bata gama soyuwa ba,baya ga uban mai da yayi mata yawa,na biyu kuma ita ka ta shinkafar batayi laushi na,gatanan dai tayi tsage tsage,a haka yadaure yatafi loma ta biyu wanda anan yaji ya kaure kan harshensa,tilas ya dakata ya dubeta

“Bani ruwa” ya buqaceta da hakan,tunda tsurar abinci ta dire babu mahadi,dan qaramin tsaki taja bayan ta aje wayarta data koma charting dinta ta dora daga inda ta tsaya dazun,don a rayuwarta ta tsani adinga tashinta ana aikenta,ta isa qaramin fridge dinta taciro ruwan babu cup ta aje masa takoma tazauna abinta,baice mata komai ba yadauki kofin yabude yasoma sha.

1

STORY CONTINUES BELOW

Daga can dakin mmn ummi kuwa usman ne ya wurgar da cokalin hannunsa yana yarfar da hannun gamida dalilen yawu saboda azabar yaji,mubarak kuwa tuni idanunsa sun hada qwalla donshi yafi usman ma qin abinci mai yaji,dai dai sanda mmn ummi tafito ashirye bayan tayi wankan da masifa ta hanatayi daxu ta dubesu

“A’ah,wannan wanne irin iskancine wannan?,me haka?”

“Yaji umma” usman yafada yana shirin fashewa da kuma,saboda yunwar da yakeji yaso yaci abincin sosai amma babu hali

“Wanne irin yaji?” Ta fada tana zama gefansu,gamida daukar cokalin tayi loma daya ta dandana

“Um,um_um,umum” ta fada tana gyada kai

“Tabdi” ta sake furtawa,ita abun ya mata dai dai,domin kuwa tasamu hanyar cin zarafin rufaida a daren nan,zata qarasa huce takaicinta,saita dauki kwanon abincin tace

“Ina zuwa” fuuu tayi dakin rufaida.

“Garin yaya rufaida abincin nan yayi yaji haka?” Ya jefa mata tambayar yana kallonta,sauke wayar tayi ta dubeshi

“Yafi dadi ai,abinci babu yaji kamar na ‘yan ruwa?”

“Amma dai nasha gaya miki ba’amin girki mai yaji ko?,saboda ulcer da basir,ga kuma yara”

“To nidai gsky haka na iya girki na” kafin yace komai mmn ummi ta bankado labulen tashigo riqe da kwano a hannu

“Wannan wanne irin abincine haka?,bbn amir kaga muguntar da matarnan tashirya ashe ko?,to gashinan dai yara sun kasa ci,babu abinda suke sai kuka,wannan ai mugunta ce da rashin mutunci”.

Da sauri rufaida tamiqe rana aje wayar hannunta

“Ke maryam ki iya bakinki ki kama kanki,kibar ganin ina daga miki qafa wallahi tausayinki nakeji,banason hauka banason dabbanci kinji ko?,banson jahilci da qananun maganganu…..”

Sakin farantin mmn ummi tayi ya tarwatsewa rufaida a daki,ta daki qirjinta tana cewa

“Waye jahilin waye dabba?,wallahi yau saikin gayamin….”

Tsawa bbn amir ya daka musu wadda ta tsaidasu daga yunqurin da kowacce takeyi.

“Waiku wadanne irin mutanene da basu qaunar zaman lafiya sai tashin hankali” cikin raunin murya mmn ummi tace

“Nice bana qaunar zaman lafiya ko ita?,kana gani yautun safe da kalar wulaqancin da takeyi cikin gidan nan amma banga wata cikakkiyar tsawatar mata da kayi ba,yanzu wannan zancan danazo dashi shine rashin qaunar zaman lafiyar?”

“Da kika shigo baki ganni ba zaune?,me yasa baki mutuntani ba kin kawomin qara kigani mezanyi akai?”

“Meko zaka iyayi tariga tashanye ka tamallake ka,sai abunda taga dama takeyi”

“Ya isheni maryam,wuce ki koma dakinki” yafada cikin bacin rai yana nuna mata hanya da yatsa,ta fuskanci yana dab da kaiwa maqura,saboda haka ta juya tana cewa

“Ni duk wanda ya cuceni Allah ya isa wlh,kuma kuyi lokacinku ne,akwai ranar qin dillanci ranar da hajar mai gari ta bata” da wadannan qananun maganganun tajuya ta fice.

Tsahon mintina falon yadauki shuru,saiya dauki ummi yafice,ya direta a qofar dakinsu ba tare daya shiga ba yajuya yafice daga gidan.

Da sauri rufaidan ta qarasa gaban kwanon abincin daya tashi akai tadauki cokalin tayi loma daya,saita hau zaro idanuwa saboda yaji da gishiri,itakanta batasan yajin da gishirin sunkai har haka ba,yaron daya kai mata markden dai yace tarage attaruhun tace haka takeso,yakai mata haka,saita koma tazauna tana jin yadda shinkafar ta tsaitsaya mata a maqogaro tana raba idanu,tare da da tunanin yadda zata nade tabarmar kunyarta.

Can bayan layinsu ya zagaya wajen wani maisaida fura da noni,gefansa kawai mai balangu,ya siya leda daya mmn ummin da yaranta,leda daya mmn amir don yasan bazata iyaci ba itama don bata qaunar yaji,leda daya tashi,yadawo gidan yashiga dakin mmn ummin,tana zaune ita daya,yana iya jiyo motsin yaran cikin dakinta,ya aje ledar yana dubanta

“Maryam,ki fita daga idanuna,banason fitina banason tashin hankali,ki kiyaye tun baki kaini bango ba” daga haka bai saurareta ba yafice yashiga dakin mmn amir.

Fuskarta ba yabo ba fallasa ta amsa sallamarshi,itama yamiqa mata ledar idanunshi nakan farantin dake aje gefanta tarufeshi da wani farantin,da alama itama tadebone ta kasa ci,ya tsammaci zatace wani abu,saidai batace komai ba har ya mata sallama yafito.

Cikin ranshi yadinga ganin qima da martabarta,har kullum kunya sake kamashi take idan yatuna abinda ya aikata mata a baya,sanda yana kan ganiyar neman aure da aurenshi da maryam,yakanji kamar yajawo baya yagoge duk abinda yafarun a baya,saidai babu damar haka,saidai danasani da hausawa ke cewa qeyace.

STORY CONTINUES BELOW

A baya idan tayi kawaici irin wannan yace munafuncine dason goga masa baqinjini wajen mutane,idan tayi magana yace tacika qorafi duk da ba maganar takeyi ba,duk wanda tayi bata tsira ba,sai a yanxu martabarta take sake fitowa muraran,darajarta take sake yauqaqa a idanunsa.

Wannan karon dakinsa yakoma,yayi shirin kwanciya abinsa kana ybude gurasa balangu da furar yasoma ci.

Baiyi nisa ba taturo qofar dakin cikin kayan barcinta tashigo dauke dai da kwanukan abincin,donta tsara abinda zatayi,dubanta kawai yake takaici yasauko masa,rigar barci ce transparent ana iya ganin pant da bressier dinta,amma ace haka ta ratso cikin gidan zuwa dakunanshi?,yanzu idan wani cikin yaran yaganta fa?.

Sai data aje abincin sannan ta bata rai sosai tana dubanshi,baqinciki biyu,yasiyo abinsa yanaci ba tare daya bata nata ba,sannan ga girkin datasha wahala akanshi baici ba

“Yanzu haka xakamin dear,wallahi na fuskanci an riga da an gama shiga tsakaninmu,randa nasoma girkina na farko ace kaqici ka bige dacin abincin kan titi?”saita fashe da kukan kissa wanda yadinga jinsa har saman kanshi,wannan matsaloli da yawa suke,daga ka toshe matsalar waccar saita waccar ta danno kai?,daga wannan sai wancan?.

Ganin kukan nata nayin yawa yasa dole bayan ya kammala cin abincin yakira sunanta,tadago da hawayen qarya tana dubanshi.

“Gaba daya rufaida kin bani mamaki,yadda na tsammata gaba daya ban tadda haka daga gareki ba,na zaci cewa zan sake samun wani nutsuwar da kwanciyar hankaline daga gareki,sai gashi kina neman bani mamaki,ina shirin ganin abinda ba haka ba daga gareki” fuska tadan yamutsa,saboda babu abinda zancan nasa suke mata sai bata mata rai,itafa arayuwa babu wanda ya taba mata kwatankwacin abinda jibril din yake mata yanzu,donko saurayi magana daya zai gaya mata yanzu ta sauyashi,bata lamunci a dinga gaya mata magaba kai tsaye ba

“Kaman yaya?”

“Kamar yadda nake gani” ya bata amsa shima kai tsaye

“Yanxu duk qoqarin da nakeyi kai baka gani,baka yabamin saima kusheni da kawo matsalolina,duk yadda nake haquri a gidan nan baka gani ba?” Ta fada cikin kuka,don ita harga Allah bata gano laifinta ko daya ba,sai tarin laifinsa dana matansa

“Tunda hakane saika fadi dame dame nake maka”.

Tiryan tiryan ya lissafo mata komai,saidai cikin zuciyarta tsaki take ja kawai,tanason maida masa wata zuciyar na kwabarta,saboda tana lissafe nan da rana ita yau zata amshi kudin ankon bikin qawarta,kuma taji daga bakin qawayenta masu aure,idan kika sake wani abun ya hadaku yana iya hanaki kema abinda kike buqata,saboda haka ta faki idanunshi ta yatsina fuska sannan tace

“Shikenan naji,xan gyara”

“Da dai yafi,saboda na auroki ne don dukkaninmu munason juna,na auroki don dukkaninmu muyi farinciki datarayyarmu da juna har lahira,abu nabiyu,irin wadan nan kayan banaso kina yawo dasu cikin gida haka,saboda yarana da sauran masu shigowa wadanda suke ba hurammanki bane,a qa’ida ta addini bai kamaci ace suna ganinki haka na,bugu da qari tarbiyyar yaran gidan,kinsan yaro da riqe abu da fahimta,bare kusan dukkaninsu sun riga dasun tasa,balaifi zaki iyamin ado dasu sanda muke daga ni saike,don Allah ki lura ki kuma  gyara” wani abune yasake tsaye mata a wuya,kusun uba,waime jibril yake nufi ne?,kwalliyarma da zata ringa da qananun kayan zai hanata,abinda taci vuri ta kashewa kudi,aqalla ita kanta batasan nawa ta kashe wajen siyan kayayyakin ba,gaskiya ba zata sabu ba wai bindiga a ruwa,bataga uban wanda ya isa ya hanata shigar datayi niyya ba cikin gidan,wannan shine babban abinda zata daina suyi galaba muraran a kanta,ba shakka dole ta rage mishi son yaran nan ba,idan ba haka ba ita za’a cutar da yawa,kuma akwai dambarwa ba ‘yar qarama ba,amma a fili saita cuno baki

“To naji” kai ya girgixa cikin mamaki,wasu lokutan halayanta kanyi kamanceceniya dana mmn ummi,mmn amir ce mace daya tak dakan saka gwiwoyinta a qasa ta bashi haquri a duk sanda tayi masa laifi.

Da wannan tasamu tasha kanshi,komai yawuce,don dama shi bamai daukar dogon fushi bane ko a baya,idan yayi dogon fushi to tabbas ka qureshi ne.

****    ****   ******  *****

STORY CONTINUES BELOW

Washegari hakanan badon taso ba tatashi da wuri ta dafa mishi shayi da chips,kamar xata fadi haka ta dinga ji saboda tashin wurin datayi,haka ta dinga aikin takaici nacin ranta,saboda tariga ta saba a gida bata tashi a irin wannan lokacin,suma sun sani ba’a tashinta sai sanda taci baccinta ta gyatse,ko aiki zaiwa mamanta kanta kuwa ba ruwanta,idan ta tashinma batason aikin wahala,zata karbi aikin da zatayi daga zaune ne,shima idan yadauki lokaci saita kawo wani uzurin da zata aje aikin ta barshi.

Bayan ta sallameshi saida ta koma takwanta din kuwa,bata tashi ba sai bayan goma na safe,yara tuni sun soma jin yunwa,tadora shayi a gurguje ta dora musu indomie,ta jibagata ta sauke sannan tashiga sharan gidan,wanda kafin tagama ta jigata ainun,haka ta dinga qorafi da surutai ita kadai,yaran kuwa duk wanda yayi kuskuren yin wani abu ba dai dai ba zaici gyatumarsa.

1

Mmn amir ce data fuskanta tayi hikimar tattare yaran a dakinta,don tasan tabbas idan mmn ummi ta fuska ta to yauma sai an raba abun fada,itakuwa sam batason tashin hankali,uwa uba kuma tasan hankalin jibril xai tashi fiye da jiya,abinda ita kuma bata fata kenan.

Haka taci gaba da karbar aikinta harna tsayin kwana biyu,wanda kafin sannan ta jigata qwarai,ta zaci abun akwai sauqi bata tsammaci haka ba,randa zata sauke girki tanason ta huta amma tana tsananin kishin miqawa mmn ummi jibril,babu yadda ta iya haka tasaki mmn ummi ta kama,saidai taci alwashi itama kafin mmn ummin tafita saita baro musu bacin rai.

Tunda gari ya waye ranar da zata karbi girkin take cikin walwala da farinciki,bini bini minti daya biyu kaji ta saki waqa wadda ke cike da habaici da baqar magana,sosai ran rufaida yabaci don ta gama yankewa da ita mmn ummi take,tayi qwafa ta quduri abinda zata mata ta huce yakai sau shurin masaki.

Mmn amir kuwa batasan ma me suke ba,tana kwance abinta tana duba wasu daga cikin litattafan marubuta masu ma’ana,sosai takejin dadin karatun,don tana qaruwa da abubuwa a ciki ba kadan ba.

Bayan yagama shirin fitarsa daga dakin rufaidan,yasoma leqa mmn amir din,tana zaune tafito da duka kayanta tana gyarawa da safen kasancewar bata da wani aikin yi,lemon siyarwar ma ta dakata dayi harsai ta sauka,sai ruwan pure water kawai da take saidawa yanzu,tanason bayan tasauka dinne tasake fadada sana’artata,ta qara wasu kalolin lemon da sauran abubuwan sanyi nasha.

Jin shigowarshi yasanyata fitowa falon nata

Kamar koyaushe suka gaisa ya tattambayeta jiki tace alhmdlh

“Idan nadawo ku shirya zamuje mu dubo hajiya bata jin dadi”

“Ashasha,me ya sameta?” Ta tambaya cikin nuna damuwa

“Ciwon qafarta ne yatashi”

“Ayyah,Allah ya sawwaqe ya bata lafiya”

“Amin ya rabbi” ya amsa yana sanya hannunshi cikin aljihunsa.

Dubu guda yaciro

“Kekam kawaicinki kamar yaso yayi yawa”batasan sanda murmushi ya subuce mata ba,kana tace

“Name fa?”

“Indai ba asibiti zakije ba,ko kin qure da yawa bazaki bude baki kice bbbn amir bani kaza ba,yanzu yadda baki girkin nan baki samun ‘yar biyar da ‘yar naira goma ya kenan?” Murmushi tasaki kawai ta kada kai,babu mutumin da zaice baison ace mishi ungo,to amma idan ya kasance bake daya bace wajen miji,sa’annan bani baninki tayi yawa to babu shakka zakifi kowa baqinji ne a cikinsu,bugu da qari Allah S W T ne kadai baya gajiya da roqo,wannan shine cikakken alfanun sana’a a wajen diya mace.

2

“Baka ganin ina saida ruwa da lemo?” Ta fada a tausashe

“Ah,kice hajjaju ce nan a gabana” yadda yayi maganar saiya bata dariya

“Duk da hajjajun ce dai ungo amshi wannan ki riqe,don nasan lalurorinku na masu ciki,kar a je a rugurguje ribar da jarin duka” hannu biyu ta amsa zata karba tana godiya saiga rufaida tashigo.

“Idan kagama inada magana” ta fada idanunta akan kudin hannun mmn amir da take niyyar ajewa,wani takaici ya kamata,ai ita datake kan ganiya ita yafi cancanta yadauki kyauta irin haka ya bata,wayasanima ko kullum sai ya bata?,shi yasa baya fashin shiga,kuma dakinta kullum yake fara shiga

“Ganinan zuwa muje” ya fada yana nuna mata hanya,yadda bata kula mmm amir din ba itama saita sake tsumewa,tayi kamar nata ganta ba,tunda aqa’idance ita yakamata tasoma gaidata,na farko ta girmemata a wajen miji,nabiyu kuma har dakinta ta taddata

“Shikenan saina dawo”

“Allah yatsare” ya amsa mata kana yafita.

Yana fitowa sukayi kacibus da mmn ummi wadda aketa gyare gyare tun safe za’a karbi miji,yayin da rufaida ke daga kitchen tana diban abincin kari,saidai duka kunnuwanta na tsakar gidan,gaisawa sukayi itama sannan yamiqa mata kudin cefane,ta amshe cikin walwala ta rakashi da addu’o’i,kana itama yashaida mata zasu duba hajiyan idan yadawo,wani murmushi rufaida tasaki,anzo wajen,plan dinta zai tafi dai dai kenan

“To Allah yakaimu” ta amsa ba tare data tambayi me zasuje yi din ba.

Fitowa rufaidan tayi daga kitchen din,itama gaya mata yayi

“To” tace kawai itama tayi gaba,ganin batayi magana kan nemanshin da tace tanayi ba saiya sanya kai yafice daga gidan,yayin da rufaidan tawuce dakinta tana waqar

“Ahayye sama ruwa qasa ruwa…” Tana wassafa tsiyar da zata tsula anjima.

*kuci gaba da haquri dai,duk sanda kukaji shuru ba shakka wani babban uzuri ne ya kawo tsaikon,sannu sannu bata hana zuwa,jigon ko manufar labarin dai daukar darasi da koyi da kyawawan halayen ciki*2👁️‍🗨️👁️‍🗨️ *HANGEN DALA*👁️‍🗨️👁️‍🗨️

       _Ba shiga birni ba_

©️®️ *Safiyya Abdullahi Musa Huguma*

Haske Writers asso 💡

*BABI NA SHA HUDU*

Sannu a hankali rayuwa tacigaba da garawa tsakanin wadan nan mata uku masu mabanbantan hali ra’ayi da kuma alqibla qarqashin inuwar miji guda daya,wanda ya koyi darasi daga kuskurensa nafarko daya tabayi a yanzu yake ganin ya gyara komai ba tare dayaci tura ba,saidai hausawa nace,tun ran gini tun ran zane,yariga daya dora maryam mmn ummi akan keken bera,ta sangarce ta tsammaci daga ita yarufe qofa,babu wata diya mace dazai sake aura a matsayin mata,tayiwa mmn amir duka cin kashin dataga dama,ta manta da cewa duk jisan jifa qasa zai fado,hakanan idan gemun dan uwanka yakama da wuta to sai kayi gaggawar shafawa naka ruwa,babu burgewa ga mace tashigo tasamu ‘yaruwarta cikin halin qunci da matsantawar miji tabuga tsalle da shewa taga saboda ita yake haka duka,a’ah fa,kamata yayi idan kemai zurfin tunani da hangece kiyi tunanin gobenki,kiyu tunanin ya zata kasance a dake duk sanda kika bude idanu kika ganki kan bigiren da ita waccar take?,ya zata kaya ke dake din?.

1

Wannan dalili na tunanin itace zata kulle mishi qofa yasanya duk sanda tabude idanu taga rufaida ranta ke bala’in baci,ta gaza boye kishinta,ta bada dukkan qofar raini,takuma bawa rufaidan gudunmawa wajen karantar abinda kw tunzurata da bata mata rai,ta bawa wannan bangaren himma.

Ta sashin rufaida kuwa duka yadda ta tsammacin abun sai taba wankin hula yana neman kaita dare,waishin ina duka tarin kalaman soyayya qauna lallabawa da bbn amir yake mata a waje?,ina duka tarin kalaman idan bake ba sai rijiya dayasha furta mata?,ina kalaman kinfi sauran mata suka maqale?,ina kambamatan da yakeyi?,ina dukka kudi da yake bata?,kanta yakan daure tamau da mamaki,kada dai ace *HANGEN DALA* take irin na wasu ‘yammatan wanda hausawa sukace *BA SHIGA BIRNI BACE?*,sam ko daya ba zata yarda tayi faduwar baqar tasa ba,qudurinta ko daya ba zata yarda ya salwanta ba,idan kuwa tabari haka ta kasance to tamkar ta zama lusara kenan,meye amfani meye kuma ribar auren me mata kenan?.

Ta sashin mmn amir kuwa tsuntsu biyu ta jefa da dutse guda,tafiyar yaranta zuwa gidansu ba qaramin taimaka yayi ba wajen bata sarari da damar tsara doro da bigiren da zata dora rayuwarta akai,ta sake karanta da kuma hasashen yadda rayuwar gidan zata iya tafi mata nan gaba,ta shiryawa komai bisa tsari da hikima irin na nagartattun mata masu tsaftataccen kishi,dimbin wayo da siyasa.

Ta bangare guda kuma kosau daya batayi wasa da addu’a da gayawa Allah yadorata kan dukkan wani wanda yake qin jininta ba,ya hasakakata idanun maigidan fiye da kowacce mace,ya sanya mata kwarjini da hasken fuska,lokaci lokaci takanyi waya gida tasa ayi wake da shinkafa koda nacij mutum biyar ne tace ayi mata sadaka.

Ta gama dukkan wani shirinta na haihuwa,ta karbi adashinta wanda tayi da ribar sana’ar da takeyi ta hade abinta tsaf,abinda duka bbn amir din yaga dama yayi mata bata da kaico,tunda tana sana’arta ta gama nata shirin,saboda batason cikin mata uku tafita zakka,ya zamana tahadu da tambarin bani bani wadda ke karya qima da darajar mace,ya kuma gusar da dukkan soyayyar mace a zuciyar mijinta,musamman a wannan zamanin da talauci yasoma qwanqwasa qofar jama’a da yawa,wasu mazan kuma zukatansu suka mutu,har wasu daga ciki suka yanki tikitin nade hannayensu matansu su dauki nauyin kansu su dauki nasu nauyin sukuma dauki nauyin ‘ya’yansu dukka a kafadarsu.

Raunannar kafada da annabi yace a killace,a tausaya musu,sa’annan yabada lambar yabon zamantowa mutum mafi alkhairi matuqar iyalanka suka maka shaida da cewa kaine mafi alkhairi a wajensu.

Duk da tasan ba haka jibril yake ba,tunda mutum ne jajirtacce,mai qoqarin sauke dukka nauyin dayahau kanshi,saidai Allahne kadai baya gajiya,kuma shine kadai baya buqatar taimako.

STORY CONTINUES BELOW

*BAYAN WASU LOKUTTA*

      Satittika qididdigaggu suka rage ma haihuwar tata,wanda tasan cewa tazarar dake tsakanin haihuwar da babbar sallah ba yawa gareta ba.

Yau ya kama ranar girkin rufaida ne,ta gama abincinta yadda tasaba wanda yazama alaqaqai ga jama’ar gidan da basu saba cinsa ba,bayan kaiwa dare da takeyi sai tsabar kura kurai cikin girkin nata,wanda kosau daya ita bata ganiba bare ya dameta tayi qoqarin gyarawa.

Qarfe bakwai na dare wansa tuni an idar da sallar magariba,dai dai lokacin da mmn amir ke zaune saman abun sallarta wadda ta gamafa azaune tana jan carbi,tanabin dakin nata da idanu tana duba meye bata hada ba.

Kayanta take kwashewa a hankali a hankali cikin satin tana dauresu waje guda ba tare da kowa yasan ma me yake gudana ba cikin dakin sakamakon sabbin kayan daki da zata sauya na haihuwarta,wanda wani cikin kudinta ta bayar,wani kuma lokacin bikin rufaida da bata siya komai ba ta adana abinta ta hada,cikin sati mai zuwa takeso a kawo mata takintsa komai koda haihuwar zata iya zuwa mata kafin cikar EDD dinta.

Sosai tasake sauya salonta,tasake zama mai sirri sosai fiye da sanda suna zaune ne itada mmn ummi,saboda ta karanci rufaidan macace mai shegen sanya idanu da bin qwaqqwafin abinda bai shafeta ba,shi yasa data karanci haka tasha maganin zama da ita,duk qwaqwwafinta sai mmn amir din taso take gane wani abu tattare da ita.

Sallamar mmn ummi yasanyata daga kai ta amsa mata tana dubanta,saitaga itama hankalinta naga dakin,da alama tana mamakin yadda komai yake a hargitse wani kuma hade waje guda.

Tana qoqarin zama bayan ta ture kayan tace

“Yausje kikayi wannan aikin mmn amir?,ko alama banji motsinki ba” murmushi tasaki kawai tana shafa addu’a

“Kinacan kina fama da yara”

“Mtsweew,wallahi bari kawai,kekam gashinan kin huta sosai abinki,babu mai saki bari bari”

“Wani satin suma zasu dawo ai,don na fahimci karar babansu tasona qarewa yasoma qananun qorafi”

“Yanzunma shi yace namiki magana yanason ganinmu”

“To Allah yasa lafiya”

“Da alama” tafada taba miqewa

“Yanzu zan fito” ta bata amsa bayan ta yunqura tamiqe,fitowarta kenan daga wankan dare,saita sake shigewa uwar dakin nata ta laluba kayan da zata sanya.

Duk da tsufan da cikinta yayi da rashin girki da batayi amma bata yarda tana zama haka wargazaza ba,shi yasa idan ba sanin mai tsohon ciki kayi ba kazo ka sameta a zaune haka zaka tsammaci ba ciki gareta ba,don hatta da jan lalle ciki baya hanata bare kitso,tariga tasaba ya zame mata jiki.

Doguwar riga tafitar ta wani yadi mai taushi ruwan hoda maidan turuwa wanda yahaska chaculet colour fatarta wadda tasake kyau saboda yanayin ciki,duk da dama kalar fatarta haka take,ko sau daya bata taba gigin gwada sanya mata man qara haske ba wato bleaching,bata da ra’ayi ko kadan,masu yima qyanqyami suke bata,dalili kenan daya sanya ba kasafai tafiya cin abincin rufaida ba,don tana taba shafa man duk da fara ce amma hakan bai mata ba.

Gashinta mai tsaho da laushi irin na baqaqen fulani ta tajeshi ta daureshi da qaramin ribbom tashafeshi da mai,ta maqala qananun dankunne fashion sannan tafeshe jikinta da turare bayan ta mutstsike jikinta da kuallacture mai qamshi,dauri tayi sosai daya sakeyi mata kyau tafito haka ba tare data damu da yafa mayafi ba.

Sanda tashiga yanacin abinci,idanunshi kanta yana sakin murmushi,hakanan duk sanda yaga haliman yakejin wani kwanciyar da nutsuwa na saukar masa,baisani ba ko tsananin biyyayarta da rashin sin hayaniya da rashun shiha duk wata kwaramniya ko tashun hankali shiya haifar da hakan?,rufaida na daga ciki bedroom din,a nutse tasamu waje tazauna tana ambatar sunan Allah

“Sannu halimatussadiya” myrmushi ya qwace mata,cikin fara’a tace

“Kai za’a yiwa sannu da kwaramniyar neman halal,Allah yasaka da alkhairi,yarufa mana asiei duniya da lahira” addu’ar ta masa dadi sosai,duk da cewa ma’abociyar addu’a ce ita

“Ameeennn ya rabbil izzati,Allah yayi albarka” ta amsa mishi da amin,dai dai sanda rufaida tafito daga dakin,sanye take da wando lages da riga tshirt wadda tadan sauko kadan,kanta sanye da hula data dace da kalar kayanta,fuska ta tamke tsam ganin suna magaba da juna da alama tattaunawa suke,hakanan tatsani taga yana hira da mmn amir din,wani lokaci harta gwammaci yayi da mmn ummi,saboda itadin batasan wanne malamine yake mata aiki ba,duk qanqantar magana sai taga tana tasiri har zuciyar jibril din,yanzu haka idan ba’ayi sa’a ba har gari yawaye yana cikin walwala,ko kuma yadauko wani labari na abun alkhairi data taba yi masa yahau bata,tayi fushin sunyi fadan yafi sau a qirga amma ya kasa dainawa,ta fuskanci wani lokaci ma baisan yasako mata zancanta ba,kamar ana tsirarsa yayi maganarta.

STORY CONTINUES BELOW

Bata taba tsammanin akwai wani abu da zatayi shakkarsa ba game da matar,amma yanzu tana shakka dari dari da tunani kan idan ta karbi girki kuma ya lamarin zai kaya?,tunda gashi yanzun ma suna nesa nesa da juna amman haka na kasancewa?,inaga ta shigo turaka?.

Har yau ta rasa meye yake baiwa mmn amir din haushi,canki canka take,ta gwada duk wani abu dake baiwa mmn ummi haushi akanta amma bataga wannan fushin ba kan fuskarta bare akai ga tankawa,hasalima ba wata hira suke tsakaninsu ba,sai magana ta kama sannan take hadasu,sai kuma gaisuwa da sallama,amma ba zata iya tuna sau nawa tazauna hira ba tsakaninsu,sabanin mmn ummi wadda da wuya rana tafito ta fadi basuyi ‘yar tankiya ba.

Kawai saita gwada sarar zama tasanya hannu cikin kwanon bbn amir itama tasoma cin abincin bayan tayi bake bake a gabanshi.

Itama macace kamar kowa,kishin hakan yataso mata,amma saita tuna cewa ba haramci rufaidan ra aikata ba,bugu da qari kuma itama matarsa ce kamar yadda itama take,don ita kanta tare suke cin abinci a sanda take girki,don haka saita soma furta YAHAYYU YA QAYYUMU BI RAHMATIKA ASTAGIS,ASLIH LI SHA’ANI KULLAHU,WALA TAKILNI ILA NAFSI DARFATA AININ,A’UZU BULLAHI MINASHSHAIDANIRRAJIM,hakan ya hana komai yin tasiri saman fuskarta,saima ta sanyo musu hira sukaci gaba dayi.

Sosai hirar ke sukar zuciyar rufaidan,cin abincin dai kawai takeyi,uwa uba ga turaren mmn amir din saya dumame falon nashi,wanda takejin kamar tatashi tafidda ita daga dakin,tun wata rana da wani abu yafaru tasake tsanar turaren.

Ranar taje gida,sai aka kawo mata kaya gugarta,mmn amir din ita ta amsa,mai wankin yace abashi dankwalin daya daure kayan a ciki,hakan yasanya bayan tabashi tasaka nata dankwalin tadaure mata,data dawo tasa mubarak yadauka ya miqa mata,ta amsa tadora saman kujerarta.

Ranar ita keda girki,bayan baban amir yadawo yazauna kan kujerar da kayan suke,kusa dasu yana danne dannen waya,tunda yazauna qamshin yadinga kai mishi ziyara,saiya daga kai koya waiga kadan kana yaci gaba da danne dannensa.

Dai dai sanda tashigo taji yace

“Haba,nifa ince” ta qaraso wajen tana tambayarsa

“Mefa?”

“Daa har zance ina kika samo irin turaren halima,ashe dankwalinta ne kusa dani” sak kawai ta tsaya tana dubanshi cike da kishi,shi kuwa baima kula ba yaci gaba da abinda yake,take ta warware dankwalin tacire kayanta,tafita tsakar gida saman igiya ta dora mata,sai data fito taganshi kana tadauki abinta.

Babu jimawa mmn ummi tashigo,daidai sanda yagama cin abincin yagyara zama yana dubansu

“Yauwa,inaso kubani aron hankalinku nan….dukkaninku nasan cewa kun sani halima da maryam,lokaci iwar haka na gabatowar babbar sallar cikin taimakon Allah nasiya abun layyata da kuma sitturunku kuda yara,to wannan karon al’amuran duka sunzo sai addu’a” shuru yadanyi kana yadora

“Duk da banso gaya muku ba,to amma kudin iyalina ne da babu wanda yakaiku kusanci dani,dadi da wuya ya kamata ace kunsani,na tattara kudaden hannuna da kudaden dakayan da muka siya a shago na bayar za’amin sari,to cikin hikima ta ubangiji jirgin ruwan daya dauko kayanmu igiyar ruwa takadashi wani waje wanda ba’asan nahiyar da yayi ba,kusan har yanzu babu labarinsa,duk sa cewa ana nan ana bincike to bazamu cire rai ba,saidai muyita addu’a da fatan Allah yasa muna da rabo”.

Cikin tausayawa mmn ummi ke kallonshi,ba shakka taga damuwa sosai tatare dashi,har tayanke tsakanin yau da gobe tatsaya ta bincika jin yaja bakinsa yayi shuru,ba shakka asara ba qaramin abu bane,kota sile biyarce bata da dadi bare ta maqudan kudade haka

“Subhanallah,ya salam,amma bbn amir shine kayi shuru da bakinka muna zaune abinmu munata walwala bamusan halin da kake ciki ba?”cewar mmn amir kamar zatayi kuka,don abun ya tabata,tasan cewa ba qananun kudi yazuba,tabe baki rufaida tayi,cikin zuciyarta tace

“Makira,indai pritending din nan ne kowa aiya iyashi,yau zakiga aikin makirci” murmushi baban amir din yayi,harga Allah yana yabawa da yadda take damuwa da lamuransa

“Banda abinki idan na fada aiba magani zaiyi ba,saima saku damuwa da zaiyi,musamman ke da kike wannan yanayin”

“Amma atleast ko a addu’a ma sanyaka ko?” Kaiya jinjina

“Gaskiyane,da wanann don wannan,to amma yanzunma ba’a makara ba aiko?”

Kaita jinjina

“Hakane,ubangiji ya bayyanasu cikin aminci,yasa rabonkune,yakaresu daga dukkan abinqi”

“Amin summa amin”

“Tofa,ana wata ga wata,to Allah ya bayyana” inji mmn ummi tana sanyawa ummi mama a baki,ta soma saqa tunane tunane iri iri a ranta.

STORY CONTINUES BELOW

Rufaida kuwa saitahau salati tana matsar hawaye,wanda hakan yaja hankalinsa zuwa kanta

“Yanzu dama a wanann halin kakeciki amma ba wanda yasani,ya Allah yadubeka,ga nauyin iyali gana iyaye,gashi kuma kowanne saikayi babu mataimaki sai Allah,ga hidima kala kala a gabanka” murmushi yasakeyi

“Babu komai,ai Allah yana tare da bawa kowanne lokaci,hidima kuwa wadda tasamu ai ita za’ayi,wadda tazama wajibi ba mustahabbi ba,shi yasa ma na taraku na gaya muku,wannan karon saidai kuyi haquri da layya,hakanan suma kayan salla,amma su kayan suna kaina in sha Allahu,da zarar komai ya warware zan biya bashi”.

Ai gaba daya sai wutar rufaida tadauke,tashin hankali,wannan wanne irin bala’i ne?,ita da taci burin wanna sallar?,qawaye da ‘yan uwa za’azo aci a raqashe a gidanta itama tayi aure?,sallar saura sati uku amma harta lissafa ya kama ranar suyar hanji da washegari duka ran girkinta ne,tabdijan.

Ta fannin mmn ummi ma sakato tayi tanajin wani dan takaici takaici na tabata,duka lissafin bogi da tayi zata qara ma bbn amir din kan qunshi da kitso da kudin dinki ya tashi kenan

“Haba bbn amir,ko wanda baisanka ba yaji wannan aiya sauke maka komai,bare mu da muke masu rufa maka asirine,shekara nawa ana abu,don yanzu kawai Allah yakawo wata lalura harsai ka taramu kabamu haquri?,kayi fata kawai Allah yawarware ya tsaga da rabonku koba haka ba?” Ta fada tana dubansu mmn ummi,don ita a tsammaninta suma haka yake cikin zuciyarsu

“Hakane” mmn ummi tafada a taqaice,rufaida kuwa kai kawai ta gyada na ganin ido,ji take kamar ta shaqo mmn amir tayita zabga mata mari,kawai don ya fadi hakan babu wannan dan boren ma na yayi qoqari yanemo saita wani kama ta sauke masa?,koda yake itace a cikin ruwa zundum ita da zata haihu,billhillazi sai tafi kowa jigata,itakam kod yage da fige saita samu wani abu jikinsa,bacin ranta kawai ace tana cikin amarci wai ace gidanta ba’ayi layya ba?,wannan shine babban tozarci,bayan ya gama sanya mata rai tun tana waje,ta gama baje lissafi,saboda ta sani dik shekara gidansa sa yake yanka musu,ita kuwa ba wanda yake najikinta sa baisan da wannan ba tun kafin suyi auren,don kasonta mai yawa yake kaimata a lokacin.

“Shikenan,na gode qwarai da fahimtata da kukayi,Allah yayi muku albarka yasake hada kanku,yakuma hore kafin sannan ayi duk abinda ya kamata”

“Amin amin” suka amsa kowa da abinda ke qasan ranta,kana yasallamesu suka tafi.

A daki mmn ummi haka abin yadinga mata qwaqur qwaqur arai,tadinga juya zancan cikin ranta,hakanan tadinga zancan zuci ita daya.

Ta fannin rufaida kam tsaf walwalarta ta janye,harya lura da haka,daya tambayeta tace kanta ke ciwo haka suka kwanta,saidai kafin bacci yadaukesu yajiyo maganarta

“Amma banda sakaci da wasa da dukiyar mutane jirgi sukutum da guda ace wai an rasashi ya harba wani gun?” Ya zaci zancanne yadameta kan asarar da suke gab da tafkawa,saiyace da ita

“Eh,hakan na faruwa idan ruwa yayi yawa,amma idan akwai rabo saikiga Allah ya bayyanashi”

“To Allah ya bayyanashi kafin nan da sallah,koda irin sallah saura sati dayane,komai ai zai iya warwarewa,saboda sallah ba layya aisai aslow” shuru yadanyi yana son shinshino inda ta dosa,sai kawai yabita da amin,saboda yanzu shiba wannan ne duka agabanshi ba.

*******    ******   ********

     Sati guda da faruwar hakan aka kammala mata duka kayan gadonta harda kujeru da showglass,sallah saura sati daya kenan,tayi waya aka turo mata salima da khadija da kubra ‘ya’yan qanwar innarsu sukazo suka tayata aka shirya kaya komai tsaf dashi,tsaffin kayan saita maida dakinsu amir wadanda ranar suma aka dawo dasu gida gaba daya.

Tunda aka shigo da kayan rufaida tagansu ta kasa zaune takasa tsaye,bacin rai kamar tasanya kuka,wato munafurtarta bbn amir yayi kenan?,yace babu kudi ga asarar da suke shirin yi amma ya narka mata kayan daki haka.

Bata iya jure bacin rai ba,saboda haka tadauki wayarta tahau kiransa,saidai ta buga babbar rashin sa’a duka layukansa switchoff,takai takawo cikin daki ita daya bacin rai yacikata,tanajiyo hayaniyarsu ita da yara da yammatan dake tayata aikin amma ko leqe,saima tasake sakin labule tunda dama girkin mmn ummine,don dole datagaji dakai kawon takwanta saman kujera taba wassafa yau tashin hankalin da zasuyi dashi,don wallahi da sake an baiwa mai kaza kai,wannan rashin adalcin dame yayi kama?,ya zagayesu yaje yamata kaya saboda zata haihu?,watafi cikin haihuwa,hakanan dai tawuni ita daya baqinciki fal zuciyarta.

Ta fannin mmn ummi kuwa duk da tasan cewa kudinta ne na sana’a da wadanda batayi hidima dasuba auren rufaida amma saidataji ranta yasosu,duk da ta dake tanata yaqe,takuma leqa dakin taga kayan,amma sai taji duk ta quntata,hakanan nata kayan dakin saita rainasu,taji itama babu abinda takeso irinta sauya.

Sai la’asar sakaliya suka gama komai tun safe,bayan sunci abinci suka soma shirin komawa,suna tsakar falon salima ta miqo mata kudi

“Ga kudin tsohon fridge dinki” murmushi tasaki tana irgawa

“Amma sun sayeshi da daraja,ban zaci zaikai haka ba”

“Ai mutumin yace duk yadda akai asalin mai firinjin tana da tsafta,shi yasa baiyi komai ba,don babu abinda ke saurin nakasta firinji bayan rashin kunnashi sai qazanta”

“Gaskiya ne” ta fada taba raba kudin biyu

“Wannan kikaiwa innarmu kice tasaka albarka” sannan tasake fidda wasu ta baiwa yaran saboda aikin da sukasha,sauran tasake miqa mata bayan takuma cire wasu

“Acika kudin firinjin dake wajen auwalu,freezer tana nan wajensa,yace idan aka cika sai adauko,don Allah gobe ko jibi a nemo masu kawomin,a hadamin da labulayena” dai dai lokacin da mmn ummi tashigo,taji komai kan kunnenta

“Mmn amir flask din shayinki zaki aramin in qarasa kwashe ruwan zafi” ta fada tana basarwa kamar batajimusu zance ba

“Miqo mata gashican khadija” mmn amir din tafada tana nunawa khadijan inda ta aje.

Koda ta karba tafita sai zancan ya tsaya mata arai itama,anya kuwa bbn amir bai zage ya baita wani abu ba?,wannan uwar hidima haka?,aiko sanda aka aurota bataga tayi wannan hidimar ba,komai sabo,kayan furniture harda kujeru,ga labulaye da freezer ana maganarsu?,take ranta yabaci,zargin bbn amir wanda baisan ma me ake cikin gidan na don bainan sanda suka shigo kuma bata gaya mishi ba yacika zuciyarta,a haka aquntace tagama aikin nata,takoma daki tazauna taba qwafa zuciyarta cike da zargi.👁️‍🗨️👁️‍🗨️ *HANGEN DALA*👁️‍🗨️👁️‍🗨️

       _Ba shiga birni ba_

©️®️ *Safiyya Abdullahi Musa Huguma*

Haske Writers asso 💡

*BABI NA SHA BIYAR*

*ZAKU IYA SAURAREN LITATTAFAINA A TASHATA TA (SAUTIN HIKIMA) DAKE A YOUTUBE,SAUQI GA MUTANEN DA BASU SON KARATU DA KANSU SAIDAI SAURARE,LITATTAFAN NAWA SUNE KAMAR HAKA*

+

*ALKAWARIN ALLAH*1

*DAURIN BOYE*

*KUNDIN KADDARATA*

*MUTUNCIN MACE*

*DANGANTAKAR ZUCI*

_DA WASU SABBIN DA ZASU ZO MUKU NAN GABA KADAN DA YARDAR ALLAH_

Dukka wadan nan abubuwan mmn amir batasan dasu ba,saboda tana cikin dakinta suna qarasa gyara kayansu amir a drower dinsu,bata ma sake ganin fuskar kowaccensu ba bare tasan da sauyin fuskarsu ba.

Baishigo ba kuwa dan halas sai bayan sallar isha’i,yaran sunajin sallamarsa gaba daya suka runtumo suna masa oyoyo,kowa ya maqalqaleshi,shima yayi mamakin ganin nasu,saboda baisan da dawowar tasu ba,hanifa ce cikin zumudi tasoma cewa

“Abba….zo kaga dakinmu yazama sabo,mama ta canza mana kayan daki” idanu yafiddo duk daya tsammaci quruciyarta ce kawai

“Kai haba hanifata,muje nagani” dai dai lokacin da rufaida tayi burum ta yaye labulenta tafito tana kallonshi

“Duk dakunan nan zaka wuce kasoma shiga nasu?” Waiwayowa yayi yana dubanta cikin mamaki,wannan bashine karon farko ba,sunsan tsarinsa,dakinta shine dakin da yake soma shiga duk sanda yadawo gidan,yayin da wadda keda girki kuma itace qarshe,daga ban zai wanka yaci abinci da sauran abubuwa

“Eh,ina nan shigowa bari nafito tukunna” daga haka yayi gaba zuwa dakin mmn amir.

Wani sabon bacin ran ne yasake taso mata,wato namiji dai munafuki ne,shi yabada kudin shi yasa yana shigowa gidan yasoma shiga dakin kenan don yaga irin kayan,banda haka ta yaya zai wuce dakunansu yashige nata?,haka tasaki labulen takoma kan kujera taxauna tana dakon shigowarsa,ta rantse yau sai tayi masa tas,saita wanke ciki dabai.

Yatsanta ta ciza tanajin zuciyarta na suya,waita yaya ma?,me yasanya yake nuna rawar qafa akan wannan tsohuwar matar tasa mai haihuwa hudu zatayi tabiyar?,bata taba tunanin xataga kwatankwacin haka daga gareshi ba,amma koma meye wallahi sai inda qarfinta yaqare.

Sanda yashiga mmn amir din na qasa a zaune,ta dora qafafunta da suka kumbura saman abu mai tudu donta samu kumburin yasabe,fuskarta a sake da fara’a ta amsa sallamarsa tana masa sannu da zuwa

“Iyyeee,shi yasa hanifata tace nazo nagani,ashe mamanta amarya tazama” yafada yana bin dakin da kallo gamida leqawa,dariya tasaki

“Da gaske dai halimatu kin zama hajjaju,eh lallai kudi basa magana” yafada cikin dalon tsokana,wannan karonma dariya yasake bata sosai

“Kai bbn amir,wani yaji wannan zancan saiya dauka da gaske kake,kawai kudin ‘yar sana’ata ne dana adashin dana shiga sai yanzu na dauka na hada duka da kudin tsaffin kayana,sai yaya mansur dayamin dan ciko”

“Ma sha Allah,ma sha Allah,Allah ya sanya alkhairi,yasa rai aka yiwa”

“Amin” ta amsa cikin jin dadi.

Biyewa surutun su amir da suka dan jima basa tare yayi,sunata bashi labarin gidan inna,har yadanja lokaci ba tare daya sani ba,saida mmn amir ta ankara sannan ta fiddashi cikin dabara,amma duk da haka saida hanifa da usman suka bishi.

Da sallama itama yashigar mata kamar yadda yasaba,tana zaune ta gama cika ta gama batsewa,daqyar ta amsa idanunta kamar xai fado akanshi,ganin yaran tare dashi yasake tunzurata,cikin tsawa ta zazzare musu idanu kana tace

“Me kukazoyi?!,ku fice maza kubani waje,da wasu idanunki guru guru kamar anyi barin qwai” tuni yaran suka tsorata,sai suka wuce sumi sumi suka fice daga dakin,yayin da bbn amir yabisu da kallp har suke fice kana yamaida kallonshi kanta,yafuskanci fushi a fuskarta,hakan yasanya ya mata uzuri saboda baisan meya bata mata rai ba.

STORY CONTINUES BELOW

Fuskar hanifa akwabe ta shiga tana duban mamanta

“Mama” tafada kamar zata saka kuka,daga kai tayi tadubeta

“Meye haka?,ke kuma dawa?”

“Anty amaryace,muna shiga ta shine tayi mana tsawa tace mufito mata daga daki,wai da idanunmu kamar…..”

“Shshahsh….” Maman amir ta dakatar da ita ta hanyar saka yatsanta akan lebanta

“Ya isa,basai kin gayamin ba,antynku batajin dadi ne,kuma idan kuka zauna surutu zakuyita sanyata da fitinarku”

“Wallahi umma bazamu mata fitina ba,aikinsan bama barna”

“Ya isa hanifa,samu waje kizauna,dauki jakankunan makarantarku ki goge muku ki baiwa yaya amir yakai muku daki” da haka takashe bakinta.

4

A nutse yasamu hannun kujera yazauna yana dubanta,sai huci take kamar wata macijiya

“Mun yini lpy” yafada yana duban tvn daketa aiki

“Wallahi kabani mamaki matuqa jibril,kuma sai yanzu nasake yarda da zancan hausawa dasukace namiji hankaka ne,niji tabarmar qashi,namiji qanin ajali” cikin mamaki yafidda ido yana dubanta

“Rufaida,lafiyarki qalau kuwa?,kinsan me kike fada?”

“Lafiya lau nake,ras nake,nakuma san me nake fada,kaine dai nake tunanin ba cikin hayyacinka kake ba,ka gama kallamemu da maganganun kana cikin rashi saboda kayanku da duka bace a jirgi,sai gashi ka kwashe kudi ka yiwa matarso kayan daki,ka canza mata komai da komai,mu muna zaune mun shanya baki dayake mata muka rako duniya”

3

Cike da tsantsar mamakin maganganun rufaidan yake kallonta,kana yanuna kanshi da yatsa

“Rufaida ni kike gayawa wadan nan maganganun?” Ya sake jaddadawa,ko daya batajin xata raga masa yau,saboda duk wani abu da take hange tattare dashi ashe HANGEN DALA NE ba shiga birni ba

“Kai nake fadawa,saboda kaima ka yaudareni,duk abubuwan dana gani a waje kafin na aureka ashe ba haka bane,idan kuma kana musu zan lasafta maka,na farko a waje koda bakazo zance ba inacewa ina da buqatar kudi kaza zaka turomin,na biyu kati baya yankewa a wayata,na uku duk inda kake nakiraka nace kazo inason ganinka ko zaka kaini waje kaza da gudunka kake zuwa,amma ko shekaran jiya da zanje gida sai keke napep nahau,sannan gaba daya a baya ka bani lokacinka,amma ayanzu ganinka saina kwana biyu,shima idan kana dakina saika kama ka kwasomin shirgin yara kuzo kucikamin waje,sannan wannan duka bai maika ba,so kake ka daidaita matsayina da matanka,harma kana neman wata daga cikinsu ta dara matsayina,wallahi nayi madamar aurenka,saboda ka gamamin romon baka gaba daya,ka nunamin cewa idan nashigo gidanka zan samu fiye da yadda nasameka a waje,amma me nasamu banda zallar baqinciki,da bautar girki da nakewa matanka,ka gayamin”.

Sosai ranshi yakai qololuwar baci,idanunsa harsun sauya kala yadubeta

“Zan miki gargadi na qarshe,kin fada basau daya ba basau biyu ba,kada bakinki ya qara kiran yarana da tarkace ko shara,domin kuwa bani da kamarsu,ku dukkanku zan iya rabuwa daku amma su har abada bazan sauyasu da wasu ba,matana dakike magana akansu sanda zan aureki na gayamiki na daina sansu shi yasa na aureki?,ko baki fada ba amsar itace a’ah,na aureki saboda inasonki kamar yadda nake sonsu,ba wulaqantattu bane a wajena,suna da qima a idanuna kamar yadda kike daita,sauran dukkan abinda kika lissafa kuwa idan baki sani ba ko kin manta bari na tuna miki,aure ibada nae,gidan aure filin bautar Allah ne,saboda haka dukkan wani aiki da mace zatayi ba’a banza zai tashi ba,tana da rubutuccen lada wajen Allah,kisan me zaki dinga fadamin,ni mijinki ne ba yaronki ba,sa’annan koda ni nayiwa halimatau kayan daki ban fadi ba,abinda kikaci a waje halimatu bataci rabinsa ba,koda tacin ma tare kika ganmu daga ke har maryam,kinsan fadi tashin da mukayi tare har muka kawo wannan bigiren?,kinsan haqurin datayi da abubuwan data shanye,to ki kiyaye wannan tun lokaci bai qure miki ba”daga haka yamiqe yana shirin ficewa daga dakin,sai itama tamiqe cikin fushi,cikin maganganunsa kaf yabon mmn amir da yayi yafi komai qona ranta

“Idan ban kiyaye ba saime?,me zai faru?,iyaka dai kace zaka sakeni,to wallahi donka sakeni ma ni gaba takaini,ban tsinci komai a aurenka ba,abokan aurena kowacce tamin fintikau,gaskiyace dai bazan fasa fada maka ba ko zaka haqa rami ka bunne ni,idan ma ba’a hayyacinka kake ba gwara ka dawo dai dai” kallo daya yayi mata kawai yasanya kanshi yafice daga dakin ba tare daya sake saurararta ba,saboda yana tsoron kada zuciya da shaidan su debeshi.

1

STORY CONTINUES BELOW

Bacin ran daya fita dashi yasanya bai shiga dakin mmn ummi ba,saiya tura usman ya gaya mata yadawo,tana zaune saman kujera saita girgiza kai

“Bazaidai fasa yimin rashin adalci ba wato kenan,tome zan masa daya dawo din?” Daga haka ta shareshi taci gaba da sabgarta,don takaicinsa take ji,tana ganin ya baiwa mmn amir wani abu a boye,sannan kuma yashiga dakin kowa amma banda nata saboda wulaqanci,harya gama wankanshi yashirya yazauna kawai yanajin dacin abinda rufaidan tayi masa babu mmn ummi babu dalilinta.

2

Tun hankalinsa baikai wajen dadewarta bata shigo ba har yakai din,saiya miqe yafita zuwa dakin nata.

Azaune yasameta dirshan abunta,yadanne fushinsa yayi sallama ta amsa a dage

“Usman bai gaya miki na dawo bane?” A yatsine tace

“Ya gayamin” kai tsaye,saiya jinjina kanshi,don itama ua shinshino wani abu

“Toki kawomin abinci tunda saina fada” yasaki labulen yajuya,sai idanunshi yasauka kan dakin mmn amir,suna ciki abunsu ita da yaran,yana iya jin muryarsu sama sama kamar tana hada musu kayayyakin makarantarsu ne waje daya,tana nunawa amir tare da masa bayanin idan sun tashi su shirya kawai kada wanda ya tasheta da sassafe,sai yaji ranshi ya quntata,babu qarya yasan yayi kewarta,kukawarta da iya mu’amala,sauqin kai da sanyin hali,take ya zargi kansa da me yasa ya barta ta aje girki?,ya hadiye wani yawu na takaici,harya doshi dakin nata saiya sauya akala,saboda sam bai kamata taga fushinsa ba,bayan batasan hawa ba sannan batasan sauka ba.

1

A qalla saida sake kwashe wasu mintuna goman sannan tashigo dauke da abincin,baice nata komai ba,saidai tuni har abincin yafita daga kanshi ba tare data sani ba,zuba masa tayi ta tura masa sannan takoma kan daya daga cikin kujerun tazauna tana hade gabas da yamma.

Jan plate din yayi yasoma tsakura,minti goma tsakani sannan tace

“Amm….ina da magana” dubanta yayi kana yace

“Bismillah”

“Dama cewa nayi na hada ‘yan kudadena na yiwa yaran nan dinkin sallah,to yanzu abinda yarage takalmansu da kudin dinkin,sai huluna,naira dubu goma ne nakeso kabani” tsaida cin abincin yayi cak sannan yakalleta cikin ido

“Maryam mantawa kikayi da yanayin da muke ciki?,wanda tuni ai nayi muku bayani ko?,sannan bayaga haka dukkansu da qaramar sallah dinki kala biyar biyar nayi musu,takalmi biyu hula biyu,shaddodinsu wankin inji nakai aka musu basu isa su sake sawa ba?”.

Bacin ranta yafito qarara a kan fuskarta

“Baka da kudi amma kayi wannan hidimar a gidan nan?” Cikin alamun tambaya yake dubanta,da yake ita ta gane saita dora

“Dama kowa yasan nice borar gidan nan,tun kafin na tambayeka dama nayi imanin bazaka bani ba,amma Allah yana gani idanma an zalunceni,shikenan kowanne juji da bola akaina,idan na rantse bazanyi kaffara ba cewa kana da hannu kan uban canjin da akayi yau a gidan nan a dakin uwargidanka,saboda rashin tsoron Allah yanzu sai kazo kawani ce wai baka da kudi,inataga kudin wannam aikin ita kadai?,shikenan koma meye Allah yana gani,kuma yarana ni bazasu saka tsaffin kaya ba bare su fito amusu dariya ba,Allah zai horemin” daga haka tamiqe fuuuu kamar zatayi fatali da abinda ke gabanta ta wuce.

3

Kasa cewa komai tayi sai binta da yayi da kallo baki sake,kiran sunan Allah yadinga yi,mamaki dukka yakamshi,wato kowaccensu abinda mmn amir din tayi ya tsone musu idanu suke ganin shi ya mata?,amma abun da mamaki,shekararsu nawa da maryam?,tunda ya aureta irin wannan situation din bai taba faruwa ba a gidan tsahon shekarun,kullum cikin wadata suke,amma yanzu da tsanani yazo shine zata rufe idanunta kamar bai taba mata alkhairi ba,lallai manzan Allah S A W yayi gaskiya da yace daya daga cikin dalilan daya sanya mata sukafi yawa a wuta shine *SUNA KAFIRCEWA MAZAJENSU* ma’ana:- rainuwa,da kuma idan irin wannan yanayin ya ratsa mace ta rufe idonta kamar baka taba yi mata alkhairi ba arayuwarta.

1

Ita kuma rufaida dame ya rageta?,dukkan wani naqasu da gazawarta yayi haquri dasu kan hakan,yadauka cewa saboda tana matsayin budurwa ne batasan kan abubuwa ba,ya rufe idanunsa yana mata uzuri amma ita sam bata gani na,sai  qoqarin dabbaqa da kururuta laifukansa take ba tare da tana hangen nata ba.

STORY CONTINUES BELOW

Ya aureta cikin wadata hakanan yakawo ta cikin wadatar ubagiji bakin gwargwado,ashe itama bata zama matar rufin asiri ba?.

Yana tsaka da wannan tunanin yadinga jiyo kukan hanifa,da kamar bazai fito ba saboda yanayin da jiki da zuciyarsa ke ciki,amma jin batayi shuru ba yasanyashi miqewa yafito zuwa dakin mmn amir.

Shigarsa dakin kawai ko a idanu da yanayi saiyaji ya banbamta da kowanne sashe na gidan,badon sabbin kaya dake ciki ba,a’ah,dabi’ar zuciya ce da binbini da nacin bigiren datake yawaita samu nutsuwa.

Tana zaune hanifan na zaune gefanta tana tsala kukan,yayi sallama tadago tana dubanshi ta amsa a nutse,kallo daya tayiwa idanunshi ta karanci akwai damuwa tattare dashi,yasamu hannun kujera yazauna yana miqawa hanifa hannun gami da cewa

“Meya sameta?,waya daketa” tsaki mmn amirdin taja tana zuge jakar ahmad data gama shirya masa litattafai

“Tsamigaye ne da inna tabasu nace taraba ta baiwa su mubarak,a’ah shine fa ita bazata basu ba nata ne ita kadai”

“To kuma shine kika daketa kenan” yadanyi maganar cikin kaushi kaushi wanda ke nuna zafin dake zuciyarsa,dan sak tayi tana dan karantar yanayinsa,ta fuakanci an fusatashi ne daga wani waje,bawai iya dukan hanifa ne kadai yasashi wannan furucin da kaushi ba,saita sassauta muryarta gamida sakeyin laushi tace

“Kayi haquri,Allah yahuci zuciyarka,amma ‘ya’ya amanar Allahne a hannunmu,itace tun yana danye ake tanqwarashi,idan ya bushe shikenan,tun daga wadan nan shekarun kake iya gyarawa yaro halayya da bata kamata ba zuwa wadda ta kamata,yan uwanta ne,raba abu tare dasu zai sanya yaro yatashi da zuciyar kyauta,da raba duk abinda yasamu tare dana kusa dashi,amma baza’a sake ba in sha Allahu” ta qarashe maganar idanunta a qasa.

Wata wawuyar ajiyar zuciya yasaki wadda ke nuna lallai ba shakka yana cikin damuwa

“Hanifa bata da rowa,abinda kikayi kuma ba laifi bane,amma dai dukanne banso”

“Baza’a sake ba in sha Allah” tasake fada a tausashe,tare da qoqarin hakaito meya bata masa rai,bayan da wasa da dariya suka rabu yanzun babu jimawa,wala’alla ko duka zancan kayansunne da suka bata?.

“Kije fridge din dakina ki dauko muku qananun lemo kowa dai dai” da murna suka miqe suka fice,harya miqe zai bisu yatsinci muryarta

“Ka yawaita karanta la’ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin,Allahumma la sahla illa ma ja’altahu sahla,wa’anta taj’alil hazna iza shi’ita sahla,ya hayyu ya qayyumu bi rahmatika astagis,dukkan tsanani yana tare da sauqi,hakanan babu abinda ke iya sauya qaddara sai addu’a” wani sanyi ne yasaukar masa daga kalamanta,harsai daya fidda ajiyar zuciya,yakuma kasa daurewa sai daya dubeta yace

“Madalla da mace tagari,wadda annabi yace idan ka kalleta saita faranta maka,Allah yasaka miki da mafificin alkhairi”

“Na gode da wannan yabo dana samu daga wajenka”.

4

Cikin farinciki yafice daga dakin,wanda bai tsammaci samunsa a dan tsukukun ba,koda yakoma dakin bai bari bakinsa ya subuce daga addu’o’in ba,kafin wani lokaci duk wani qunci da yakeji sai yaji babu shi,harya kwanta mmn ummi bata dawo dakin ba,shima hakan bai wani dameshi ba,saboda yasan qarshenta idan tadawo din kwana zasuyi tana mita tana qorafi ta hanashi bacci a banza,saiya sakaya qofarsa yayi kwanciyarsa.

******************

     Washegari sai qarfe goma sha daya na safe yayi shirin fita yafito,bayan mmn ummi ta aika masa da break dinsa ba tare data koda leqashi ba bare ta gaidashi,shima a ranar babu wanda yaleqa cikinsu banda mmn amir,saboda yanajin ya kamata ya nunawa kowaccensu fushinsa.

1

Koda zai fita ma usman yabaiwa kudin cefane yakai mata,yayi hanyar fita saiya lura qofar dakin rufaida a kulle yake,cikin mamaki ya qarasa qofar dakin,ya jijjiga kulle kam take,mamaki yasake kamashi,shidai a iya saninsa yasan cewa bata tambayeshi zata wani waje ba,saiya juya zuwa dakin mmn amir ya tambayeta kota mata magana sanda zata fita.

Tana bacci ya tasheta,tuni yaran duka sun jima a makaranta,tace mishi batasanma bata nan ba,saiya zaro wayarshi yasoma kiran layukanta.

Har ta qaraci ringing ta katse bata daga ba,haka yayita maimaitawa kusan sau biyar amma babu amsa.

STORY CONTINUES BELOW

Cikin damuwa mmn amir ta debeshi

“To Allah dai yasa ba wani abunne yafaru ba ko a gidansu?” Ranshi adan bace yace

“Ko wani abunne yafarun bana cikin gidanne da bazata iya gayamin ba?,saita sanya qafa tafice?” Shuru mmn amir din itadai tayi batace komai ba,saiya soma kiran layin mahaifinta.

Da sauri mmn amir tace

“Don Allah karkace kana cigiyarta,ku gaisa kawai idan wani abunne zai gaya maka” baice uffan ba harya daga,suka gaisa lafiya lafiya,sukayi sallama ba tare dayace komai ba,tabbacin bataje ba,kuma komai lafiya yake a gidan,saiya sauke wayar daga kunnensa yana maidawa aljihun shaddarsa gamida furzar da iska daga bakinsa,kana yajuya yasoma tafiya yana cewa

“Saina dawo”

“Allah yatsare hanya” ta fada a sanyaye tana addu’ar Allah ya taqaita koma meye,sabida tasani babu abunda bbn amir din yafi tsana irin leqe da fita bada saninsa ba.

Dai dai lokacin da rufaidan ke cikin dan sahu,tana gab da qarasawa gidan mariya qawarta da suka hadu gidan lallen biki wanda sukayi waya kwanaki,daren jiya tayanke shawarar zuwanta gidan,don wala’alla tasake samun haske da dabarun raba jibril da matanshi tazama ita kadaice a zuciyarsa,donta fuskanci itakam tasamu yadda takeso ba kamar ita ba,don haka babu jinkiri takirata.

1

Koda tashaida mata zatazo ta amsa mata tace dama itama jiran zuwan nata take,ta tura nata adress,hakan ya yiwa rufaidan dadi,ta qiyasta wala’alla an samu sabbin hanyoyin mallaka ne.

Sanda tasauka qofar gidan ta biya dan sahun sai data tsaya ta qarewa gidan kallo,ba laifi yatsaru,ta tura gate din gidan tashige,saita tsaya a farfajiyar tana kwatsa sallama,saboda part biyune da gidan,batasan wanne ne sashen mariya ba.

Jin shuru yasanyata daukar waya tasoma neman lambar mariyan zata kirata tace mata tazo,dai dai lokacin da wata mace tabude daya daga cikin sasssan gidan tafito tana amsa sallamar da akeyi.

Kallo rufaida tasoma qare mata tun daga nesan,bata da tsaho za’a iya kiranta gajeriya amma bacan ba,kalar fatarta ruwan tarwada mai kyau da qyalli,tana da madaidaitan idanu da dogon hanci.

Tun daga nesa kana iya jiyo qamshin dake tashi a jikinta,sanye take da atamfa riga da skert da suka kamata ba wani can ba,amma sun fitar da sigarta gaba daya,tana da mazaunai da albarkatun qirji wanda hakan yasanya dinkin jikin nata yazauna mata das,tayi kwalliyarta mai kyau wadda tasake qawatata ta qara mata kyau matuqa.

“Baiwar Allah wa kike nema?” Sai data dan yatsina fuska sannan tace

“Mariya amaryar gidan nan” fuska ta washe sosai cikin fara’a tamkar tasan rufaidan sannan tace

“Ayyah,sannu da zuwa,gashi kuma tafita wallahi,amma ba damuwa muje falo saina kira miki ita,inajin ba nisa tayi sosai ba” kamar ba zata bita ba,sai kuma tabita din,don tanason kallon qwaqwaf,tana gaba tana binta a baya,tana qare mata kallo,hatta tafiyarta awani nutse take,da haka har suka qarasa sashen matar,wanda suka tadda yalwataccen falo wanda keta zabga qamshin turaren wuta da airfreshner,ko ina neat kamar bacci zai daukeka saboda dadin qamshi da sanyin ac madaidaici dake tashi

“Ga guri zauna,bari na dauko wayata” matar tafada cikin fara’ar dai tanayin ciki.

Ba’a dauki wasu mintuna ba tadawo dauke da tray da wayar a hannunta,kayan breakfast ne komai da komai akai,kama daga tea mai zafi da qamshi,lallausan biredi,gefe kuma farfesun naman kan rago ne ta aje gabata,dukkansu acikin kwano suke kuma ba’a rufe ba

“Bismillah,ga abinci ki karya kafin ta dawo,duk dadai nakirata amma bata daga wayar tawa ba,amma ke ki gwada kiran nata wala’alla ta daga” dukka tayi maganar ne cikin fara’a.

Da mamaki rufaida ke kallonta tanason tantance ita din wacece?,amma saita kauda duka wannan tunanin saboda qamshin girkin dake dukan hancinta yasanya yunwarta tasowa gamida kwadayin abincin,daga qamshin kawai tasan zaiyi dandano,duk yadda taso mazewa taqici abun yaci tura,saboda haka tajawo kayan tahau kaiwa baka.

Ta kuwa kama naman dakyau,don dama tunda aka shiga wannan yanayin bbn amir bai kawo nama gidan ba,kafin ta gama matar ta aje mata juice mai sanyi,duk da haka tanaci matar na janta da hira cikin fara’a da sakin jiki tamkar ta santa.

Bata kira rufaida ba saidatayi nak sannan takirata

“Kiyi haquri,nadan fitane,amma nan da rabin awa zan dawo,dole ce ta fiddani amma gani nan” haka tace da ita,duk sai haushi yakama rufaidan,tasan zatazo amma shine zata wani fita?,da haka matar taci gaba dajan rufaidan da hira,tun tana tsumewa harta sake ganin kirkin matar ya isa,sai nan nan take da ita kamar wata ‘yar uwarta.

A qalla saida rufaida ta rufa awa daya harda rabi sannan tadawo,a fusace tatur qofar falon matar gagaga,

“Yauwq,tun dazu taketa zaman jiranki,yanzu nake shirin sake kiranki tadan jima wallahi” cewar matar cikin murmushi,kallon banza mariya tayi mata sannan ta jefeta da harara sannan tace

“Munafuka algunguma,Allah ya fiki,qawata taso mutafi” lafazin saiya daurewa rufaida kai,du kirkin matar ta amsar mata baquwa irin haka amma takirata da wannan sunan,kodai bazata mata godiya ba bai kyautu ta jefeta da baqar magana ba haka,amma batace uffan ba sai tarin tambayoyi fal zuciyarta tamiqe tana saba jakarta,qarasowa tayi ta tattara sauran abinda rufaidan bata cinye ba tamiqa mata tana cewa

“Ki tafi da wannan din tunda yanzu tadawo,kyaci kafin a gama girikin rana ko?” Da sauri mariya ta figi hannun rufaida

“Da Allah taho qawata,makircinki yakusa zuwa qarshe wallahi”tafada tana nunata da yatsa.

“Wai meye haka mariya,bakiga karamcin datayimin ba?,ko bakwa shiri?” Rufaida ta tambayi mariya tana dubanta sanda mariyar ke qoqarin bude qofar bangarenta.

Wata muguwar qwafa kawai mariyan taja,idan tufaida ta lura dakyau qwalla ce tacika mata ido

“Muje ciki dai qawata tukunna zakiji komai” ta fada tana tura qofar sashen nata tasaka kai rufaida tabita a baya cikin xaquwa taji me mariyan keson gaya mata?.6👁️‍🗨️👁️‍🗨️ *HANGEN DALA*👁️‍🗨️👁️‍🗨️

       _Ba shiga birni ba_

©️®️ *Safiyya Abdullahi Musa Huguma*

Haske Writers asso 💡

*BABI NA SHA SHIDA*

*ZAKU IYA SAURAREN LITATTAFAINA A TASHATA TA (SAUTIN HIKIMA) DAKE A YOUTUBE,SAUQI GA MUTANEN DA BASU SON KARATU DA KANSU SAIDAI SAURARE,LITATTAFAN NAWA SUNE KAMAR HAKA*

*ALKAWARIN ALLAH*

*DAURIN BOYE*

*KUNDIN KADDARATA*

*MUTUNCIN MACE*

*DANGANTAKAR ZUCI*

_DA WASU SABBIN DA ZASU ZO MUKU NAN GABA KADAN DA YARDAR ALLAH_

“Wannan matar da kike gani rufaida ta bani mamaki,ashe dukka *HANGEN DALA* nayi ban shiga birnin ba sai yanzu?” Ta fada cikin sigar tambaya kamar tanason samun amsa daga rufaida.

Sai a sannna rufaida dakebin hargitsatsen falon mariyan da kallo tamaida idonta kanta tana cewa

“Kamar yaya?,yimin cikakken bayani”

“Hmmmm” tace tana gyara zamanta sosai

“Wannan matar bansan yazan fasalta miki ita ba,makira ce algunguma annamimiya,wannan matar rufaida ta rabani dakowa nawa ciki harda mijina,da shegen kisisinarta,kinga abinda tayi miki?,to kadanne akan abinda takewa dangina ko mamata idan tazo,rufaida,tabi ta karbe kowa ta kalallame kowa da kirkinta na munafunci da rashin tsoron Allah,kowa baya gani ganin laifinta,yanzu dana zagi hadiza gwara na fallawa kaina mari koda wajen ‘yan gidanmu ne,idan sukazo fa wajenta sukafi zama,wai zasu zabi abinda ransu keso ta girka musu,sannan falonta yafi nawa dadin zama,bata musu fada bata hantararsu,ke mamarmu rannan cewa tayi naje wajenta nakoyi yadda ake karrama baqi kijimin wani abun baqinciki” ta qarashe zancan da alamun abun ba qaramin qona nata rai yayi ba,sai rufaida ta gyara zama tanajin ikon Allah

“Miji kuwa wallahi rufaida idan hadiza tace wannan farin mayafin nawa baqinr wuluk to zancanta haka yake koda yafi nono fari,hadiza bata laifi a wajensa,koda baya ban tayimin abu qiri qiri ba donta cusa min haushi tayi idan yadawo na gaya masa saiya hau fada,wai tunda suke da hadiza bata taba kawo mishi qarata ba,saini da kullum bani da aiki saikai masa qararta,kuma koya kirata ya tambayi algungumar wallahi koni namata abu saita saki wanu munafukin murmushi tace aiya wuce,tasan bada gangan nayi mata ba,rashin sanine kuma zan gyara,rufaida,takai takawo hadiza dai ita kejan ragamar gida da dukkan abinda yashafi dangin auwal,na zama kamar wata ‘yar kallo sai abinda ta kasq zan dauka,idan kuma nayi qorafi ko gaban waye sai suce waina fiya kishi,ba’a taba jin hadiza ta nuna kishi ko tayi qorafi akaina ba,bata zancena,na raaa me take masa take dauke hankalinsa haka,kuma wallahi bata boka ko malam,ko kusa ko alama,tako ina rufaida na rasa mafita,na rasa yazanyi da ita,tasan komai na auwal kama daga dukiya abinda yakeso da wanda bayaso,amma wallahi kinganni haryau ban gama sanin danginsa bama bare wani abu,wannan wacce iriyar masifa ce?” ta qarashe zancan kamqr zata saki kuka

“Turqashi,yo ai wallahi dole kowa yabi jam’iyyarta,na farko idan kashigo gidan saika tsinewa kanka itace amaryar saboda tsafta da gayu,nabiyu ni kaina tunda nashigo bangarenki ko baqin ruwa baki bani ba,ita kuwa har qoqarin doramin girkin rana take idan baki dawo ba,na uku sashen mariyar kamar wadda tayi haihuwa goma,komai a watse babu kintsi ko kyakkyawan gyara,duka q zuciyarta take wannan maganar,amma a zahiri saita saki ajiyar zuciya

“amma matar nan ta shammaceki mariya,matar datake kiranka ada kusha hira kotasa mijinta ma yakiraki?”

“Hmmmm,idan ana salla ba’a magana,ashe duka cutata takeyi?,ta nunawa auwal ne sam ita bata kishina,shi yasa duk wani abun tashin shina idan yataso kowa ke doramin laifi,sai ace nice sila,saboda hadiza tun kafin nashigo bata kishina bare yanzu da muka zama daya,ni kuwa wallahi babu matar dazan boyewa kishinta da nake saboda ba tsoronra ai nakeji ba,rufaida…..hatta da abinci fa matar nan ran girkina saita tsiri dafa wani abu da tasan yana jarabar so,saitasan yadda tajashi sashen ta cikin dabara,acan zaiga abun,idan yace zaici saita hanashi,daga qarshe saita zuba a flask tarakoshi ban,fuskarta da dariya da komai zakiga ta ajemin flask din tana cewa

“babu ruwana ga mijinki nan nadawo miki dashi,yadage saiya ci mana abinci,ni kuwa bazan batawa ‘yaruwata raiba,kuma bazan bari yaci shi daya yabarki na,gashinan kwaci tare” tafada tana kwatabta salon magabar hadizar bacin rai nasake baibayeta

“Kuma wallahi rufaida a gabana zaicinye tas,daga lokacin nawa abincin saidai yakwana”aifa dole,irin wannan dabge haka?” Rufaida ta raya a zuciyarta sanda ta tuna da dandanon girkin hadiza datayi katari dazu dazu dashi.

“Yanzu fa haka siddan sai naji waya daga gida waita musu aike,mama tace na tayata godiya,shi kansa auwal din rabon daya siya singlet ko boxer ya manta,rannan fa haka tasiyosu set bibbiyu,tadauki set daya ta aikomin da daya waina aje yayi amfani dasu sanda yake wajena,don Allah kijimin wani cin fuska”2

STORY CONTINUES BELOW

Shuru rufaida tayi,tashiga dogon nazari,to indai ko har hakane tata matsalar salamace akan ta mariya,amma duk da haka a yanzu babbar fargabarta randa mmn amir zata karbi girki,batasan ya zata kaya ba,tasan cewa akwai bannar qura a gaba,a yanzu kusan itace damuwarta,donta mmn ummi dasauqi,tana ganin bata da ajin da zata wani zama damuwarta,zasuci gaba da bugawa a haka kawai,burinta ta karbi jibril a hannunta yadda ya kamata.

Itama nan ta gayawa mariyan komai,saita sauke ajiyra zuciya tace

“Amma mazan nan ‘yan abu ta kazar ubane,suzo suna fasa miki kai suna kambamaki,saikin gama dauka babu yake saikin shiga wasan yasha banban,wallahi rufqida ban taba daukan lamarin haka ba,ni da nasan hakane auren ma bazanyishi ba,idan ko nayi gwara na auri yaro irina dagani saishi babu abinda zai dagamin hankali,tunda suma nagidan ashe shegerune,kana musu kallon biri ne ashe suna maka kallon ayaba,yanzu jiya dana fita girki dasafe saida mukayi kaca kaca dashi,haka kawai yahanani barcin safe wainatashi na shirya masa abun kari,bayan kumaga bayan sallar asuba ya taramin gajiya nasamu bacci yadaukeni saboda rashin imani,wai saboda nayi banza naci gaba da barcina yatayarmin da hayaniya da gori,waishi tubda yake da hadiza bai taba cewa tayi ire iren wadan ba,kafin yace tayi tuni tahi,bai taba farkawa yasameta tana bacci ba idan ba bata da lafiya ba,danacemishi baida abinda yafaru ba yataramin gajiya ko wanka ban samu yiba waisai yace,hadiza sai nayi zagaye biyu,koda tana da tsohon ciki kuwa haka zata gyara jikinta takuma shiryamin komai,kinsan cikin maganganunsa maganar data tunzurani nafita neman mafita yau?”kai rufaida ta girgiza

“Cewa yayi,nifa dadin zama da ita yasa nayi tunanin akwai wata kamarta,bari na dado na rage mata wasu nauye nauyen,sai gashi ashe abun duka bige ne,qyalqyal vanza a waje” tana zuwa nan ta kasa daurewa sai ga qwalla.

1

Kai kawai rufaida ke girgizawa,ashe jibril yana da kirkinsa tunda bai tava gaya mata irin wannan kalmar ba duk iskancin da take masa?,to ai kuwa wallahi zata sake riqe wuta,bq zata yarda ma azo wanann bigiren ba,don duk sanda yayi gangancin gaya mata hakq saiya saki aurenta wallahi.

Rufaida riqe da habarta take kallon mariya sannan tace

“Turqashi,muna ruwa mariya,yanzu meye abunyi?” Saita goge qwallar tana dubanta

“Aini nayanke kawai zan nemi taimakon malamai masu zafi da aiki da sauri sauri su shiga lamarina,saboda na fuskanci abun bana qare bane,don wallahi da quruciyata dakyauna bazan zama baiwar namiji ba yadda ita tazama,nayi aurene don in sakata in wala,nayi aure don nasamu ‘yanci na shaqata,badon na takura kaina da bauta ba,shegiya gajeriyar banza,ko rabin kyauna bata kai ba bazan zauna wallahi tadinga juya komai da komai ba,bayan nice amarya niyafi cancanta nayi wannan mulkin ba ita ba,kuma wallahi da ba haka auwal yakemin ba” juya kai kawai rufaida take tana tunanin zancan mariya,idanma tace zatabi malamai ina taga kudi?

“Tunanin me kike?,koke bazaki shiga sahun ‘yan huce takaici ba,dama qawata tajima tana bani shawara wlh ninaqiji sai yanzu danaji uwar bari”

“Mariya,kudin da kake riqewa ada yanzu wallahi basa baka shi,akan dari biyu fa sai a titsiyeki ana tambayarki me kikayi da ita?,bayan ada sai a banki ninkinta koda watsarwa xakiyi babu mai tuhumarki” tabe baki mariya tayi

“Auke haka kika xauna?,tabdi to wallahi bari kiji,ke mazan nan matsiyata ne masu shegen romon baka,waisai ka tambaya kudi qiri qiri a hanaka?,da kuwa ko uwarsa zai saida saiya siyar yabaki kudin cas yadda kika buqata,ni dana masa zancan kudi da yadda naga hadiza na fantamawa waisai cewa yayi dama yataba cemin aina koyi sana’a tun a gida,saboda ita kanta hadizan sana’a take,duk abinda naganta dashi a kudinta ne take yiwa kanta,abinda yamana ta qara dashi,saina qyale banza,idan yadawo daga aiki daya rataye rigarsa xan lali na lala,idan bai dakina naji matsuwa saina bude store nazari taliya ko semo ko couse couse nakai shago nabugar subani kudina nayi gararin gabana,idan ba haka kamusu ba wallahi saikaji kunya koka mutu a tsaye,abinda kawai suka sani su ajema abinci,sus dinka maka kaya su baka” washe baki rufaida tahauyi saboda shawarar mariya ta wannan fannin da zata dinga samun kudi ta mata sosai.

2

Hira suka dingayi kala daban daban,kowacce na gayawa ‘yar uwarta sirrinta,wanda batabar gidan mariya ba sai data wuni sur,sun yanke cewa ita mariyan tasoma xuwa wajen maganin,idan tasamu nata kudaden kuma taga aiki yayi kyau saita rakata,da haka suka rabu.

Sanda tashiga gidan saota hade girar sama data qasa don kada kowa yamata magana,mmn amir kan dauke kai tayi saboda ba xamanta take ba,hakanan ba ita tayiwa laifin ba bare ace,yar neman magana ce mmn ummi tana girki amma tahau waqe waqe

“Kamota nan…..mai qafar tafiya ce….eh fa….mai qafar yawoce….ungulu kinsan gidan kowa” tajita sarai kuma taga ba zata iya tankawa ba,ta fito burum daga daki hannunta akan qugu,tayi tsaye kan mmn ummi tana cewa

“Dawa kike wadan nan waqe waqen naki?”,dagowa tayi ta jefeta da harara

“da wanda yatsargu”tsaki rufaidan taja

“Aikin banza,idan mutum ya isa yafito fili yafada mana”

“Dake nake,an gaya miki tsoronki nakeji,ko kedin wata tsiyarce?” Aikuwa bata rufe bakinta ba tasa hannu ta ingixa mmn ummin,takuwa qume qum a goshi da bango,itama kuwa tana waiwayowa takama rufaidan da komawa rikica.

Mmn amir na daki a sannan yaran suna islamiya,tiri tirinsu yasa tafito,saita kama salati cike da mamakin hauka da wauta irin nasu,dambe kamar wasu qananun yara,itakam bazata iya rabonsu ba suje su make mata dan cikinta,saita soma musu maganar kan su rabu,amma qememe sukayi kunnan uwar shegu da ita,ganin haqilon ya mata yawa saita koma daki takira bbn amir tashaida masa,yace tayi xamanta a daki,karta sake kula kowacce a cikinsu

“Amma abban amir sunata fa….”

“Haka nace kiyi ko kema musu zakimin?”

“Allah yabaka haquri” bisa umarnin bbn amir tayi zamanta a daki,haka sukaci suka gode Allah,kowacce tayiwa yaruwarta tabo,don kuwa mmn ummi bata haqura ba itama sai data kumburawa rufaida baki.

Afusace kowacce tazauna tana jiran dawowar bbn amir din yadauki mataki kan abinda ‘yaruwarta tayi mata.

Ranshi babu dadi yadawo gidan,ranar wuni sukayi sur maganar batan container dinsu.

Yana sallama tsakar gidan mmn ummi tayi hanzarin fitowa daga dakin,goshinta liqe da auduga,tana wani cika tana batsewa,ji take bazata iya jiranshi ya qaraso dakinta ba

“Gwara da Allah yadawo dakai,kazo kayiwa tufkar hanci indai kanason  zaman lafiya a gidanka,wallahi wallahi kayimin katangar qarfe….” Ai bata qarasa ba rufaida itama tafito fa kumburarren bakinta

“Ayimiki katangar qarfe dani koni ayimin katangar qarfe dake tun ban miki mummunar illaba,banza shashasha ballagaza,wadda tun kafin ashigo gida kike hauka da hayagaga da dabbanci”

“Ni kike cewa dabba….”sai tayo kan rufaidan,itama rufaidan tayo kanta,tsawa ka tasa musu sannan cikin fushi yace

“Kowacce tawuce tatafi gidansu”

“Subhanallah” mmn amir wadda tafito jin sallamarshi da sabuwar hayagagarsu ta fada

“Ko a jikina wlh”

“Oho tafi nono fari” haka kowaccensu tafada,duk da jikkunansu yayi sanyi sannan suka juya zuwa dakunansu.

A nutse mmn amir tanufi dakinsa,sanda tashiga yana tsaye kawai hannayensa cikin aljihu ya baiwa qofa baya,a sanyaye tace

“Don Allah bbn amir kayi haquri,bai….” Da hanzari ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu

“Karki sake kibani haquri,ki koma dakinki,banason tsaiwarki a nan” yanayin yadda yayi maganar ya tabbatar mata yayi matuqar fusata,saboda haka bata sake furta komai ba tajuya a sanyaye tafice a dakin.

Suna daki dukka shuru ita da yara,saidai su amir din kallo suke,yayin da ita kuma tashiga nazari,saiga usman da mubarak sun shigo dakin,da alama mmn ummin ta tafi kenan,su kuwa dayake yarane kuma akwai shaquwa tsakaninsu da mmn amir din sai basu damu ba,suka shiga sabgarsu dasu amir din.

👁️‍🗨️👁️‍🗨️ *HANGEN DALA*👁️‍🗨️👁️‍🗨️
       _Ba shiga birni ba_
©️®️ *Safiyya Abdullahi Musa Huguma*

Haske Writers asso 💡


*BABI NA SHA BAKWAI*
*har yanzu dai litattafaina nakan youtube,a tashata ta SAUTIN HIKIMA,shiga donki sauraresu kai tsaye*👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽

https://youtu.be/8LI1DTRwdaM

*Daurin boye*
*Alqawarin Allah*
*Mutuncin mace*
*Dangantakar zuci*

Cikin tausayi da qauna yake dubanta sanda take duqe tana goge masa takalmansa,gaba daya sai yakejin gidan sakayau kamar kadda yadawo dasu,har zuciyarsa tasoma raya masa meya kaishi ga qara aure aure bayan mmn amir din bata rasa komai ba?,qaddara da kuma *hangen dala* wanda yake *ba shiga birni* bane,a sannan ganin nawajen yake kamar zai samu fiye da abinda yake samu wajen mmn amir din,kamar suna da abubuwa da kuma qualityn da ita mmn amir din bata dashi,uwa uba da zugar abokai da suke ganin a yadda yakedin da yadda Allah yamasa budi lokaci daya a sannan yafi qarfin mace daya,ashe dukka kuskure ya tafka,amaimakon yayi taai da hankalinsa yayi dogon nazari,yakuma dora duk wani abu bisa doron doka da oda da kuna dacewa,sai yanzu yake ganin duka ashe ba haka bane.
+
Hannunta data motsa saman fuskarshi ya fargar dashi
“Tunanin me kake yallabai?,tunaninsu mmn ummi ko?,ko nima wlh kullum idan natashi sai naji gidam ba dadi,sabo turken wawa,ga yara idan naga sunyi wajen dakin ummansun wlh duk sai naji babu dadi,don Allah baban amir……”
“Toh….zaki fara ko?” Yafada yana dubanta,yasan kwanan zancen,baisan me yasa duka tadamu yadawo dasu din ba
“Wallahi ba haka bane….kawai”
“Kinga idan kin gaji da dawainiya danine ki fadamin,ni wallahi sai yanzu ma nake dana sani,bansan wanne tsautsayi bane yasa na yadda kika aje girkinki,sai yanzu na sake gane ashe cutar kaina nayi”
“Duka ba wannan ba bbn amir,don Allah kodon yaran kaduba mana” harara ya watsa mata,yana tsaka da morewarshi hankali kwance tanason dawo masa da tension.
Har yaqarasa abinda zaiyi yafita bai bata amsa ba,saita dawo tazauna jikinta a mace,itakam ko sau daya bata taba buri kishiya tafita tabar mata gida ba,saboda indai tashigo kuma magana ta gama qarewa ai,zata fita tabarmiki yara kiyita wahalarsu,ita ko uban ko jama’ar duniya ba lallai kowa yagani ba,wani ya yaba maka,wani yazageka koda bilhaqqi tsakaninka da Allah kake,sannan su kansu yaran babu yaron da zai girma yaso ganin mamarshi ba’a gidan babanshi ba,idanma babu yaran tafita ai tabar miki tabo,tunda ko ina za’aje za’ace tsohon mijinta ne,uwa uba yasanta tasanshi saidai kawai a kalli juna,idanma akayi rashin sa’a saisu sake dinkewa a waje,ke kina cikin gidan kina kwasar takaici da baqinciki.
Haka ta dinga shan kanshi yaje amma qememe yaqiya,duk da yasamu kira daga dukkanin gidajen rufaidan dana mmn ummi,amma baije ba sai da akayi kwanaki kusan uku bisa tursasawar mmn amir din.
Gidansu mmn ummi yasoma zuwa,aka saukeshi a soron gidan,bayan jin tabakin bbn amir aka saurari mmn ummi wadda dama keta son abata dama,don tanata tsomamasa baki yayanta yana kwabarta,sai kuwa tasaki kuka
“Wallahi ni dama bayasona,duk cikin matanshi ni yake nunawa banbanci da rashin soyayya qarara,zaluntata kawai yake….” Duka yayan nata yakai mata wanda yasanyata katse zancan,nan yahau bambamin fada yace ananma saikin nunamin halin naki,tashi kaje jibril sai tayi hankali kazo kadauketa.
Dama ba wani damuwa yayi tadawo din ba,saboda tasire masa da halayanta data nuna masa fes,tun daga neman auren rufaida kama yanzu,ba haka taso ba ita dinma,donta soma qosawa da zaman gidan,amma saita maze tayi cikin gida fuuuu.
Sashin rufaida kuwa itama tun tana zuba idanu da zaton zuwan jibril har taji dif,abun ya sosa mata rai da bata mamaki
“Lallai jjbril,ni zai wulaqanta,wato yakoremu yazauna da baqar matarsa kenan ko?” Sai mmn amir ta tsaye mata a rai,duk abun saiya soma damunta da bata mata rai,ta zaci daga zuwanta babanta zai kira jibril amma sai taji shuru,bai kira ba bai kuma yi zancanshi ba,sabida bayanan yayi tafiya,taci alwashin wallahi saita nunawa jibril kalarta,duk zaman haqurin da take da kauda ido amma bai gani ba,ita wallahi da tasan haka auren yakema ba zatayishi ba,ashe babu abinda yafi ‘yammatanci dadi?,kawai matsalarta bata son yadda komai ake hadata da qannenta ne,hatta da dakin kwana,hakan yasanya takan tuno dakinta da gidanta akai akai.
STORY CONTINUES BELOW

Sanda qawarta zahra tazo sunsha hira sosai(qawarta tun ashafin farko da take musu fada kan mummunan ra’ayinsu suke jin haushinta)zahra itama tayi aure,mai mata ta aura itana ikon Allah,saidai suna zamansu lafiya,don bata shiga da wani mummunan niyya ko nufi ba,haka itama matar bata da wani mugun quduri akanta,kallo daya zaka yiwa zahran kasan hankalinta kwance yake,harda ma yaron cikinta,suna tsaka da hira tadauki waya takira kishiyar tata
“Auntyn salama dame dame ma kikace nasiyo?” Rufaida naji tana lissafa mata,sai data gama sannan tace
“Me zakiyi da kayan fruit haka zahra?” Murmushi tayi tana aje wayar
“Maman salma ce zata koyamin wani abunsha da abban salma yakeso sosai,haba ni naga duk ran girkinta shi kadaine abinda yake shanyewa tas ashe yafisonshi ne niban sani ba inata masa wasu kalolin lemukan” tabe baki rufaida tayi
“Wace haka zata koya miki abu zahra?” Murmushi tasakeyi
“Abokiyar zamana mana” kama baki rufaida tayi cikin ta’ajjubi da mamaki
“Amma wallahi zahra bansan lalacewa ta sameki har haka ba sai yanzu,yanzu duk duniya ki rasa wanda zai koya miki abu sai kishiyarki?,wallahi kozan mutu da jahilci bqzan yarda kishiya takoyamin komai ba,wallahi kin fado zahra” murmushi kawai zahra tayi ta dafa rufaida
“Wato dai mai hali bai fasa halinsa,dawowarki gida rufaida ni nasan da walakin,bari na gayamiki wani abu da baki sani ba,macen data cika itace wadda ke jiran aikatawa da neman sani kan duk wata hanya da wani abu dazai sake daga darajarta wajen miji,dakuma qara soyayyarta cikin zuciyarsa,wannan abun da mmn salma zata koyamin ba wani abu bane ban kuma fado ba,abune da mijina yakeso ni ban sani ba,saboda nidin sabuwace cikin rayuwarsa,itadin tafini sanin komai nashi,iya abun dayi masa da zan dinga yi zai sake samamin fada cikin zuciyarsa,da zarar na iya an wuce wajen na kwashe ilim me yayi saura?,sai samin daukaka daga wajensa,wala’alla ma nazo nafita iyawa kona qara tawa fasahar akai,rufaida…bari kiji,duk wanda yariga kwana dole yarigaka tashi,babu yadda zamuyi qaddararmu ce auren mijin wata,mijin da suka dauki shekaru tare,tun bansan wayeshi ba,itace tasoma bude masa idanu da duniyar auratayya,ita tahoreshi kan abubuwa da dama wadanda ko uwarshi data haifeshi bai koya wajenta ba,ta dabi’antar dashi,to ta yaya keda kika shigo jiya ko yau zakice tashi daya saikunyi kafada da kafada da ita idan har ba kin samu banzar uwar gida ballagaza ba?,dole ki koyi siyasa da kwantar dakai bana cutarwa ba,wanda zaki zauna ki dauki darasin waye mijinku a wajenta,wanda ita tafiki shan wahal ke a bagas kika samu,tunda sanda tasoma zama dashi ba wanda yasan dukka halayensa na zahiri dana badini bare yagayamata ,bare takiyaye,sai dataci wuyarshi wala’alla kafin ta gama fuskantarshi a daidaita,ke kuwa ga satar amsa ga leakage kin samu,ruwanki ki kwantar dakai ki samu ilimi,ruwanki kita hauka darajarki na raguwa maimakon tayi sama,ba naki bane shiga da qafafa da nuna qarfa qarfa,bayan kedin cikin duniyar aure kamar jinjirin da aka haifane yau yashigo duniya,ta yaya zaice yafi dan shekara goma ashirin,ashirin da wani abu sanin kan duniya?,idan kabi komai sannu a hankali duka rayuwar bawata mai zafi bace” tabe baki rufaida tayi tana sosa qeya
“Me zafice ni a wajena indai akan kishiya ne,tunda gashi ita tayi sila da har wai jibril xai iya kallon qwayar idanuna yacemin nataho gida” ta qarashe zancan da alama abun na mata zafi haryau,nan ta kwashe komai ta gayawa zahra,murmushi kawai tasake yi
“Rufaida kenam,to wallahi na raina wayonki mayau,waya gaya miki ana dambe da kishiya?,ana harka ta masu aji meya kawo akuyanci a ciki?,ai yanzu kishin masu aji ake,mijin da kuke neman fada da matsayi a wajensu ku tsaya gabansa kuna dambe kamar awakin da aka sako sunajin yunwa?” Sai zahran tamiqe saboda ganin kiran maigidanta da tayi,da alama yana kan hanyar zuwa daukarta
“Ni wannan zancan wallahi kunya ma yabani wai dambe kamar wasu ‘yan nursery?” Saita kwashe da dariya saboda harta hango su suna kici kici da juna,harara rufaida ta watsa mata tana dariya dariya
“To ‘yar wulaqanci,awajenki ne wani abu,ni a wajena fidda raini ne wallahi,saboda na fusakanci yaren datafi ganewa kenan jakar”
“Towai ina uwargidan naku?,ita bata cewa komai ba abinda ke hadaku?”
“Uhmmm,rabu da wannan wadda haryau nakasa gane dame zan karya lagonta,kome nayi mata yi take kamar bata gani ba kobai bata mata rai ba,na rasa me zan mata ya tsaya mata a wuya”
“Dakyau,da alama tasan abinda takeyi”
“A hakan?,kishiya na maka amma ka nade hannu,wallahi ba’a haifi ‘ya ba”
“To ai kuwa kinga yanzu ta tsira da mutuncinta a idanun mijinta,tana dakibta asirinta rub a rufe” da wannan hirar ta raka zahran waje tawuce gidanta bayan ta mata nasiha duk da tasan ba lallai tadauka,tunda bayau aka soma ba.
2
STORY CONTINUES BELOW

Kwana uku tsakani saiga kakarsu,tunda taji sallamarta hankalinta yatashi,tasan halinta sarai,macace da bata daukar wargi ko raini,barema tasu tasake tsami tun randa za’a kaita data mata fadan tabi abokan zamanta su zauna lpy tamaida abun wasa,hakanan dai aka gaisa,tana ta mata fara’a da nan nan da ita don kada tayi wani ba dai dai ba.
Sai data gama hirarsu tamiqe zata fita sai tace
“Me kikeyi ne a gida,kamarma bayau kikazo ba ko?” Waigowa tayi,tayi wuqi wuqi da ita,suka hada ido da mamanta,saita dawo tazauna tana fara’a
“Banajin dadine,shine nazo,amma na warware,ina saka ran komawa ma da zarar abba yadawo” washe baki tayi sosai cikin fara’a
“A’ah,toko kishiya ko miji aka samar mana?” Dariyar jin dadi tayi na yadda qaryarta takarbu tace
“Uhmmm,to gamu nan dai”
“To Allah ya inganta” mamar na wajen natace komai ba,irin matan nan ne da basu da yawan magana,sanyi da shuru shuru,amma akwai shegen son ‘ya’ya,da dauke kai akan wasu kusakuran da suke da buqatar a gyara musu amma sai tayi biris.
1
Tunda tsohuwa harira tazo gidan rufaida bata da sukuni,addu’a kawai take Allah ya tattarata takoma inda tafito kafin abbanta yadawo gari,aikuwa addu’arta bata amsu ba,saboda kwananta uku saiga abban nata yadawo,wanda bayan yakirata sunyi magana bai shawarceta ba yanemi ganin jibril,hankalinta yatashi sosai bayan daya shaidawa baaba harira wadda take mahifiya ce wajensa,ranar kuwa anga sauka da hawa na masifa da bala’i
“Eyiii,yo baga abinda nake gayamiki ba,’yar bokon qarya,bokon asara,kin gama cika baki da tutiya amma baki iya zama da miji lafiya lau ba,aure duka duka watanni ba’a cika shekara ba amma gaki a gida,to billhillazi baki isa ba,ni bazan dauki kowanne iskanci ba,ki kuka da kanki idan yaron nan yazo naji akasin abinda kika fada” baki ta turo tana sake jin haushin ma yadda jibril din yayi burus da kiran da aka masa kwana biyu kenan
“Ni wallahi hajiya bazan zauna yana maidani tuwon cushe ba,yayimin matansa suyimin,mena qaru dashi ne a aurensa,can mata sun zira maka ido,ga hayagagar yara,baka huta ba ko kadan” duka takai mata aikuwa taci nasarar samunta a baya,ta gantsare saboda taji dukan,tsohuwar akwai qwari,sannan akwaita da zafi
“Haka kikace?,to muzuba nidake don ubanki,ni yaran wasuma saita musu sahu nake bare nawa”.
Kwana uku saigashi yazo,a dakin baqi dake soron gidan aka saukeshi,rufaida da mamanta na gefen hajiya harira,sai abba kusa da jibril din,kamar gidansu mmn ummi nan ma basu tauye kowa yafadi abinda  yasani ba,saidai rufaida kamar mmn ummin itama ta tsagalgale tadinga qarawa zancan armashi,wanda hakan yasa hajiya tayiwa jibril umarnin yatashi yayi tafiyarsa tun ba’akai ga qarqare zancan ba,dukkaninsu babu mai magana yatashi yamusu sallama yafuce abinsa kuwa kamar dai gidansu mmn ummi,shi kansa a hanya mamaki yadinga yi,abinda sukayi din sai suka sake sane masa arai,tunda har basa iya tausa harshe gaban manyansu ta yaya zasu iya zama da miji?,shi dinma kawai soyayyar da suke masa ne yasanya tun farko suka yiwa halayen nasu ado suka biye aibukansu.
Bai mantawa sanda akwai sanda yake neman auren mmn ummi,sabani yahadashi da mmn amir,a sannan yana tashensa da ganin rashun haquri da kishine yasa take abubuwa saboda zai qara aure,shi kuma babu uban daya isa ya hanashi,yaje yakai qararta,har gida wanta yazo yamata tas har kamar zai daketa ma,daga kai batayi ta kalleshi ba bare tamaida masa magana,sai qas da kanta da tayi tana sharar qwalla,daga ranar kuma bata kuma bari tayi abunda zaikai qarar tata ba,ajiyar numfashi yasaki,yana godewa Allah da shaidan da kuma ‘yan tunzura basuci nasara a kanshi yarabu da nagartacciyar uwargidansa ba.
“Nace ba,ajiya ai ba’a haka,dakin barta itama tagama fadar matsalarta duka sai a taru a gyara” cewar mmm rufaida,wata harara hajiya harira ta banka mata wadda tasanyata sadda kai qas
“Eh tabbas haka yake,tana da ra’ayi fa da ‘yanci,ke rufaida!” Ta qwala mata kira
“Ki hada kayanki tsaf gobe dake zan wuce gida” ita sai hakan yamata dadi,can gidan hajiyan babu yara,tana ganin acan din sai tafi sakewa,tunda babu yara aiba wani aiki mai yawa ba kamar gidansu ba,kana babu mai takura mata,saboda haka babu jinkiri tasoma hada kayan nata washegari tabita suka tafi.

STORY CONTINUES BELOW

****    *******   ******
Ganin yaje dukka gidajen biyu amma bai mata zancan kowacce zata dawo ba yasa dole ta sake tunkararshi da maganar
“Bbn amir,dadai kayi haqurin dai,duk abinda haquri bai bada ba,rashin haquri bazai badashi ba,kayi haqurin kadawo dasu,tunda kaga ni yanzu nasoma jin ciwo,wanda dagashi yana gaba gaba saina naquda fa,ka dawo dasu kodon ‘ya’yanka” shueu yayi bai tanka ba,yana nazari cikin ransa,idan akwai wadda zai dawo da itama yanzu bata wuce mmn ummi ba,itace yaran ke bashi tausayi duk da babu abinda suka nema suka rasa,asalima sunfi kyau wajen mmn amir din saboda kulawa da suke samu,saidai cikin satittikan nan tacika masa waya da saqonnin ban haquri dana nadama(meye amfanin aikata hakan?,duk abinda kikasan daga qarshe ke zaki fado qasa warwas kadama ki soma aikatashi),kira kuwa saidai yayita rejecting,shi kansa yasan halin yayan nata,baida sauqi,bazai qyaleta ba.
Sai da aka qara sati daya sannan yadawo da ita,a sannan sallah saura kwana daya ranar jajiberi da daddare,jinta tayi kamar a aljanna,ashe duk dadi  gidan uba idan ba dole ko mugun matsi cutarwa takura ko masifar dakan iya nakasta rayuwa ba gidan miji yafishi.
1
Ta sauke numfashi a dakinta sanda take tuna nasihar qanwarta jamila
“Tun baya dama mmn ummi aikin yaudari kanki,idan gemun dan uwanka yakama da wuta naka kake shafawa ruwa,duk macen dake da cikakken hankali wallahi bai cancanci kiyi murna ba saboda kina amarya ana fifitaki akan ‘yar uwaki ba ita ana wulaqantata ba,kuka ya kamata ka zauna kayi da hawayenka,ka kokawa kanka saboda watan watarana,abinda yaci doma bazai bar awai ba,toke ki godema Allah ma,bai miki abinda yayiwa mmn amir ba,kafin tashigo Allah yaganar dashi ya sauya halayyarsa,to saiki godewa Allah daya kawar miki da kwasar naki sakamakon,ki kuma sawa ranki haquri kan kishi,ki tuna haka mmn amir taji sanda zaki shigo,ke fiye da hakanma,saboda ita tasoma samunshi a farko,tana tsaka da rayuwarta daga ita saishi sai gako ciki,gwara ke kin taddata baki zauna ke kadai ba,amma saikika zauna kika biyewa zuciyarki,yanzu na tambayeki don Allah?” Shuru tayi tana kallon jamila,wadda take mamakin hankalinta wani lokaci kamar itace yayar ba maryam din ba
“Dake da mmn amir data kwantar da hankalinta ta iya allonta kuma taketa wankewa waye yafi wani samun kwanciyar hankali da riba?,banda samun qima a idanun miji?,kin taba tunanin meya siya mata dukkan wadan nan?,zaki iya tuna yaushe rabon da kuyi cacar baki ko cece kuce da ita?” Ta jefa mata tambayoyin da dukka bata bata amsar ko daya ba,bata jira amsar tata ba saita sake dorawa
“Ke abinda yake damunki indai ranki yabaci baki iya danne fushinki ba,baki iya cinye bacin rai ba,wanda hakan illane a wajen mace,bama mace ba,duk mutumin da bazai iya fin qarfin zuciyarsa ba to ba shakka bai cika mutum bq,kumq za’a yita tunzuraka saboda halinka a bayyane yake,kije kiyi tunani” da haka tabarta da wadan nan maganganun da suka sanyaya mata jiki,tana kade qurar dakin nata tana tunosu.
Daidai lokacin da rufaida ke zaune a tsakar gida tana famam gyaran uban kayan miya da hajiya zatayi tuwon sallar gobe,tattasai kwano biyu wanda tace duk sauta farke shi tacire ‘ya’yan,attaruhu rabin kwano,tumatir kwano daya,sai albasa qaramin kwando da uwar kabewa qwallo guda,iya gajiya ta gaji tubus,tunda tatashi take abu daya,kai tunda tazo gidanma bata taba sanya duwawunta ta huta na minti talatin ba,ita kanta tasan ayyukan qiriqrarsu kawai hajiyan keyi wasu,ga suyar kaji data dora suna tafasa wanda za’ayi miyar dasi,kuma ta fahimci ragunan layyar hajiyan guda ukune,wanda duk yaranta dama duk sallah kowa saiya mata rago guda.
Ta rintse ido kana taja tsaki sanda radadin tattasan yake ratsa faratan hannunta,wanda hajiyan tasa duka ta yankesu amaimakon tarasu da takeyi ada
“Wai hajiya duka wadan nan kayan miyar miya za’ayi dasu?,idan ba duka zakiyi amfani dasu ba mana abar sauran daga baya a gyara tunda dare yayi” tana daga kan tabarma tana shan furarta me sanyi tace
“A’ah baki isa ba,ni ma’abociyar jama’ace,saboda haka miya nake a wadace ban saba rowa irin taku na,a gyaremin su tsaf yanzu ana miqawa ladi komai yawansu zata niqemin su” fuska tahade tasoma guna guni qasa qasa,donta soma gajiya da gashin qumar da hajiyar ke mata,har wani qashi tayi,ga baqi datayi
“Toda da bana nan waye yakemiki wannan uwar bautar?”
“Ubankine,idan kin gaji ki aje saina kirashi shi yazo ya qarasa” tafadatana janyo wayarta,tilas tabata haquri taci gaba da aikin,saboda tasani kadan daga aikin hajiyan ta rattabo masa waya,kamar tayar da wuqar tazame awajen ta kwanta haka takeji,amma bata isa ba,aikin da tunda taje gidan jibril da za’a hada dukka ayyukanta ranakun girkinta haryau batayi kamarsa ba yau gashi rana daya duka akanta,tanajin alamun shigowat saqonnin watsapp a wayarta sake qarqashin filon hajiyan amma bata da damar dauka,rabonta da wayar tun bayan sallar asuba,gashi tabar mata data a kunne,tsoroma take kada ‘yar data din da take tattalawa ta qare,don bata da kudin saka wata yanzu,hajiya kuwa tasan koda mutuwa take yawo qwandala ba zata bata ba,kamar yadda ta hana abbanta da mamanta bata ko silai.
*_ALBISHIR A GAREKU MA’ABOTA KARATUN LITATTATAFANMU,GAFA DAMA TASAMU,JERIN GWANON LITTAFAN ZAFAFA BIYAR NA FARKO DANA BIYU WADANDA SUKA CIKA GUDA GOMA KENAN CIF 10,SUNZO A KAMMALE,MA’ANA DACUMENTS KAN NAIRA 1,000,JERIN LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*
*WUTSIYAR RAQUMI,GUDU DA WAIWAYE NA BILLYN ABDUL*

*K’AUNARMU & BURI DAYA NA MAMUHGHEE*

*IGIYAR ZATO & KAIMIN HALACCI  NA MISS XOXO*

*DAURIN GORO & SAUYIN QADDARA NA RANO*

*ALQAWARIN ALLAH & DAURIN BOYE NA HUGUMA*
GAME BUQATARSU DUKA GOMAN ZASU TURA KATIN MTN TA WANNAN NUMBER
09032345899
SAISU TURA SHAIDAR BIYA TANAN
09032345899
MASU TURAWA TA BANKI KUMA ZASU TURA TA WANNAN ACCNT DIN

0225878823
HAFSAT KABIR UMAR
GT BANK
SAIKI TURA SHAIDAR BIYANKI GA WANNAN NUMBER
08030811300👁️‍🗨️👁️‍🗨️ *HANGEN DALA*👁️‍🗨️👁️‍🗨️

       _Ba shiga birni ba_

©️®️ *Safiyya Abdullahi Musa Huguma*

Haske Writers asso 💡

*BABI NA SHA BAKWAI*

*_ALBISHIR A GAREKU MA’ABOTA KARATUN LITATTATAFANMU,GAFA DAMA TASAMU,JERIN GWANON LITTAFAN ZAFAFA BIYAR NA FARKO DANA BIYU WADANDA SUKA CIKA GUDA GOMA KENAN CIF 10,SUNZO A KAMMALE,MA’ANA DACUMENTS KAN NAIRA 1,000,JERIN LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*

*WUTSIYAR RAQUMI,GUDU DA WAIWAYE NA BILLYN ABDUL*

*K’AUNARMU & BURI DAYA NA MAMUHGHEE*

*IGIYAR ZATO &  NA MISS XOXO*

*DAURIN GORO & NA RANO*

*ALQAWARIN ALLAH & DAURIN BOYE NA HUGUMA*

GAME BUQATARSU ZASU TUNTUBI WANNAN NUMBER WAYAR

09032345899

Tsaye take a tsakar gidan hajiya hariran tazubawa sarautar Allah idanu,gabanta yayi mummunar faduwa sanda tagama irga kawunan ragunan da aka gama shigowa dasu,kai uku ras,kenan raguna ukun aka yanka duka?,kuma ita zata soya kenan?.

Bata gama wannan tunanin ba hajiyan tafito daga kitchen hannunta riqe da ludayin miyar da sai datayi kamar tamutu kafin tagama hadata

“La’ilaha illallahu muhammadarasulullahi,yanzu dama haka suka kwasheki suka kai mishi ke baki iya komai ba,yanzu duk yadda na tsaya kai da fata ina nuna miki yadda zaki hada miyar nan sai da kika tafka kura kurai?” Raita bata sosai,saboda itadai bata tabama qoqarin hada girki irin najiya ba

“Amma dai hajiya idan ba’acemin sambarka ba,ba’a tsinemin ba”

“Yimin shuru shashashar banza,daukomin ungurnu ta kwarara tun banjin kunya ba” gaba tayi kamar zata sanya kuka saboda azabar bacin rai,sai kuma ta dakata tajiyo tana kallon hajiyan

“Hajiya,wai dukka ragunan uku nakinne aka yanka kuma za’a soya?”

Sai data daga kai tayi mata wani kallo sannan tace

“Qwarai kuwa,an gayamiki nan gidan marowata ne?,duk wanda yashigo saiyaci yaqoshi,ban iya rowa irin taku ta yaran zamani ba” gabanta ne yafadi,wani gumi yasoma yanko mata,batasan ta furta

“Tashin hankali!” Ba,saiji tayi hajiyar tace

“Wanda ba’a sa masa rana ba” haka tagama tsaiwarta da sanyin jiki tanufi inda hajiyar ta turata.

Tun daga gyaran kashin dake cikin tumbi fa hanji ta raina kanta,haka takusa wuni bakin famfo quda yanata binta,ga baqi da hajiyar ketayi maza da mata cikin kwalliya,amma ita tana zaune tana bauta,ko abinci ta kasa kaiwa bakinta,ta qulu iyaka,baqinciki yakai mata wuya,ba ita tagama suyar hanjin ba sai sha biyu na dare,haka ta kwanta jikinta duka yana mata ciwo.

Washegari tadasa suyar nama,aitun ba’akai ko ina ba ta fuskanci bazata iyaba idan ba kasheta hajiyar kesonyi ba,saboda haka tasaki suyar tashiga bandaki tayi wanka tadawp daki tahau shafa mai.

Cikin masifa hajiyan tashigo tana dubanta

“Au sakarmin aikin kikayi?”

“A’ah hajiya fa,zafi nakeji nace bari nadan watsa ruwa sainafi jin dadi” saita sassauta fuskarta

“Saikiyi kiyi kigama ki koma kar wutar tamutu,don idan tamutu wani jidalin na sake kunnata yasameki”

“Wallahi saidai yasameki hajiya amma bandani” tafada cikin ranta.

Laqai laqai tadinga yi,harta saka kaya tana fakon hajiyar,sai data tada sallah sannan tadauki mayafinta ta yafa,dazu taga inda aka kawowa hajiyan barka da sallah,ya bankada tadauki dubu biyu a ciki ta zari takalmanta tafice ba tare da hajiyan tasani ba.

Bata tsaya ko ina ba sai gidan jibril,a sannan maman ummi na daki ita da qannenta biyu da sukazo mata,mmn amir itama na nata dakin akwance saboda ciwon marar da taketa dan fama dashi lokaci lokaci,wanda a yadda takeji a jikinta ba zata wuce satin ba zata haihu,itama tayi baqin yammata biyu daga gidansu da suka kawo mata tuwon sallah,sai cinyar saa daga yayanta,wanda jin basuyi layya ba wannan karon yasa ya aiko mata dashi,dakai da qafa na rago,yaran na tsakar gida suna wasa abinsu sukaga shigowarta,sai suka bita da kallo,sun bude baki suna niyyar mata sannu da zuwa ta watsa musu harara

“Duk wanda yayi magana saina yanke bakin” hakan yasa sukayi shuru,tabude dakinta tashige abinta ba  tare da kowa yasani ba.

STORY CONTINUES BELOW

Saida mmn ummi tafito da yamma zata dora abincin dare taji kusur kusur cikin dakin,hakanan qofar a bude,ta saka ido dakyau saitaga gilmawar rufaidan,gabanta yafadi,wani baqinciki ya qumeta,wato jibril shiya dawo da rufaidan bai shaidawa kowa ba kokuwa?,saita fasa abinda zatayin takoma daki da sauri.

Sanda tashigo jamila tadubeta

“Lafiya?”

“Rufaida nagani yanzu cikin dakinta yadawo”

“Tosai akayi yaya?”

“Bafa wanda yanunawa alamun zai dawo da ita fa”

“Zunubi ya aikata daya dawo da itan?,kokuma cewa akayi lallai saiya shaida muku kafin yadawo da ita?” Sai kuma tayi shuru jamilan tace

“Zauna” zaman tayi tana dubanta

“Idan kika fita koda kin ganta babu ruwanki da ita,kiyi sabgarki tayi tata,tunda kowannenku ba zaman wani yakeyi ba,don Allah karki biye mata”ajiyar zuciya tasauke sannan tace

“shikenan”tajuya tafita daga dakin.

Tayi kuwa qoqari,don sai tayi kamar bata ganta dinba tasoma hada girki,a haka har mmn amir tafito daura alwalar azahar.

Mmn ummin na ankare da ita itama sai data kalli qofar,amma sai taga sabaninta,ita tawatsar tayi gaba inda su usman ke wasa gaban cinyar san dake aje,wajensu ta qarasa tana cewa

“Ashshsha,mutumina zai bata kayanshi,abba yadawo baiga kwalliyarsa ba yace masa qazami,maza tashi kar jini ya bataka” saikuwa yamiqe tsam

Yana yarfar da hannunshi,alamun baison kayanshi su bacin,daga haka tawuce bakin famfo,bayan ta tari ruwa taja kujera ‘yar tsugune tazauna don daura alwala.

Ko gama wanke hannuwa batayi ba rufaida tafito da daurin qirji da kwandon wankanta tana qananun waqe waqe gami da girgixa,mmn ummi ta daga kai takalli mmn amir,sai taga tayi kamar batasan Allah yayi tsuron rufaidan ba,saboda haka sai itama taci gaba da ayyukanta ta watsar.

Shurun nasu saiya dada mata rai,take zuciyarta tafara raya mata kodai matan nan sun fara shayinta ne?,kai da alama,tunda gashinan habaice habaice take musu muraran,amma ko mmn ummin data saba tanka mutan suyi bata tanka mata ba,gwara mmn amir din dama tasan bamai tankawar bace ita,saboda haka taci gaba da waqe waqenta.

Aje kwandon wankan tayi tabude rijiya tahau jan ruwa,don tafi son yin wanka dashi akan ruwan famfo,dai dai lokacin da ahmad ya qaraso wajen,yasa hannu yadauki sabulunta yasoma saba da niyyar wankewa usman hannunshi daya baci,tana waigowa kuwa ta kwasheshi da mari gamida daka mishi tsawa,sosai marin yaratsa yaron,hatta da mmn ummi dake kitchen sai data saki abinda take tafito,,yasaki kuka sosai,duk daba yaronta aka daka ba amma ranta yabaci,ta yunquro zatayi magana mmn amir ta mata inkiya da hannu kan ta dakata,saita qarasa a hankali ta janye hannunshi,ta yiwa salima dake tsaye bakin qofa wadda itama kukan nashibya fiddota inkiyar takaishi daki,kamar zata hadiyi zuciya salimar saboda haushi haka ta kama hannunshin tana jifan rufaidan da harara,wanda tabbas da mmn amir din bata wajen dasaita nuna mata iyakarta,ba haka taso ba,so tayi wani ya tayata atada balli,tasamu abinda zata laqewa idan bbn amir yadawo,wanda hakan zaisa bazaibi ta ba’asin dawowarta ba,sai gashi mmn amir din kamar mai duba taqi bi ta kanta,saboda haka saita dora da fadin

“Wani yabani sabulun da zakazo kasanya min hannu saboda ka rainani?,to wallahi nasake ganin hannunka akao,bakai bama ko waye,aikin banza,yara kamar ‘ya’yan beraye” sai datakai zuciyarta nesa kana ta shareta tashige daki abinta.

Salima dake tsaye ta dubeta

“Anty wannan kauda kan naki gskiya yayi yawa,haka take muku wannan iskancin amma ku gaza daukar mataki a kanta” murmushi kawai tayi,batace mata komai ba sai data idar da sallah sannan ta dubeta

“Inajin zafi salima kamar kowa,saidai duk abinda mutum zaiyi ya sanya hankalinsa gaba da komai din nan,rufaida yau ta dawo,wanda duk da tsakanin miji da mata sai Allah amma na tabbata bbn amir baisan da dawowarta ba,saboda babu nacin da ban mishi yadawo da itan ba amma yaqi,kinga kenan bamusan dame tadawo ba,meta taka wannan duka sai Allah,bayaga haka tsayawa fadi in fada da kishiya babu abinda ke qarawa sai zubda qima da mutuncinki,don zata iya gayamiki maganar da duk bakinki bazaki iya maida mata kamarta ba,kinga taci riba dake,sannan kun haifar da rashin zaman lafiya cikin gidanku,wanda hakan kuma shike saukar da talauci da qunci cikin gida,ki duba mana,ko qasa ce ake fama da rikici zakiga sakamakon shine,tattalin arziqinsu kanyi qasa,su fada cikin matsi da talauci,abu na uku kuma,ko ta yarda ko bata yarda ba,ko tanaso ko bataso ahmad danta ne,donta dakeshi bai kamata na tsaya ina kulata ba don ni na haifeshi,kawai dai kowanne laifi akwai iya limit na hukuncin daya dace ayima yaro,nasan da gayya tayi,kuma neman matayi take donta fanshe bacin ran dake ranta,nikuwa bata isa nayi da ita bq,kuma naji dadi da mmn ummi data saba tayatan bata kulata ba,kinga basai taci kanta iya ita kadai ba?kawai dai abinda nasani shine,ni akaran kaina bata isa ta shiga hurumina,bata isa kuma tamin kanta tsaye ba,nawuce wannan fagen,itama kuma tasani” Kai salima ke girgizawa,ba shakka mmn amir din tana da zurfin tunani,sanin ya kamata da dora komai bisa muhalli da gurbinsa.

STORY CONTINUES BELOW

Awa daya tsakani saliman zasu tafi mmn amir tamusu rakiya tadawo,daidai lokacin da rufaidan tasake fitowa,tagama wankanta tasheqa kwalliya cikin riga da skert na atamfa wadanda suka matseta tsam kai kace kayan qanwarta ta sanya

“Kai kai,ashe babanku yayi yanka,ah lallai yau akwai dabge,amma shine akabar naman haka wasarere,to duk baqincikin mai baqinciki wlh sainaci nawa,saboda nasan jiya an soya hanji anci kuma ba’a bani rabona ba,bari na fanshe wallahi a tsoka” tafadi tana shiga kitchen,mmn amir dake kwashe shanyar da salima tayi ta kayansu hanifa data wanke mata tana jinta batace mata ta tafas ba,har sai data dauko wuqar tafito tanufi naman gadan gadan sannan cikin kakkausar murya dake nuna gargadi tace

“Akul…..kada ki kuskura ki tabamin kayana,saboda ba hurumin wanda kike tunani bane,don haka karki soma” saita tsaya can din kuwa,kunya ta kamata,don idan da tasan kayantane ba zata ko kallesu ba bare ajinta yazube,saita kama qugu tana qanqance ido

“Idan kuma na taba din fa?”

“Maiyi baya fada,ki gwada din kigani” daga haka ta rungumi kayan yaran tayi cikin dakin ko waiwayarta bata sake yiba bare tabi ta kanta.

1

Tunani biyu ne sukazo mata lokaci guda,nafarko kada taje ta tashi ballin da bbn amir zai sake maidata gida yaudin,nabiyu kuma yanayin fuskar mmn amir din kawai ta isa ta gaya mata bada wasa take ba,batasan me zai farun ba,tunda irin hakan bata taba hadasu ba,saita buge da qananun maganganu

“Aikin banza aikin wofi,masu yunwar nama dai sunayi,nida nabaro shanu uku raguna uku,nafi qarfin cinyar sa wallahi” mmn ummi dake kitchen ta kasa daurewa sai data saki dariya kana ta waske abinta taci ga a da aikinta kamar bada ita take ba,hakan yasake qular da rufaidan,saita juya tashige dakinta tana jan qwafa.

Tsaye tayi a tsakar dakin riqe da qugu,tana mamakin waiya akayima tayi saken da matan nan suka rainata,itadai iya saninta basu fita da komai ba,amma matuqar qura taci gaba dacin tura to mafita shine kawai takoma wajen mardiyya tabi wancan hanyar data mata tallanta,amna dole saita tsaya tasamu kudi tukunna,wanda tayanke shawarar bin duka hanyoyin datasan zasu tara mata kudi a gidan.

Koda yadawo bbn amir din shi kanshi yayi mamakin ganinta,amma saiya shareta yafita batunta,yayi kamar Allah baiyi tsironta ba a gidan,hakan ya daga mata hankali ainun,don bata zaci haka daga gareshi ba,babban tashi hankalinta abokan zaman nata suna ganin duk abinda ke faruwa,tasha wahala qwarai kafin tasamu kanshi,wanda kafin hakan sai daya tarasu ya kafa musu sharudda da dokoki,wanda hakan yasa jikin mmn ummi sake sanyaya,ta dinga bitar kalaman nashi,duka kusan gugar zana yake musu ita da rufaidan,yayin da yake wanke mmn amir a fakaice,saita hada da kalaman jamila duka ta’aunasu a mizani,ba shakka babu wani abu da yayi saura dazai tserar mata da mutuncinta face tasoma koyi da kwaikwayon halayen mmn amir din,ta gwada itama tagani ko zata dace.

******    ******    ********

Tun cikin daren ranar taji sam batajin dadin jikinta,dukkan alamu kuma sun nuna mata haihuwa ce,da safen tana kwance tana jiyo mitar rufaida wadda duk kwanan duniya indai girkinta ne ita zata bawa yaran ruwan wanka,breakfast da kuma abincin zuwa makaranta tofa sai tayita,a haka a daddafe suka shirya zuwa makaranta,bbn amir yashigo ya mata sallama don daga kaisu zai wuce kasuwa ne,don yanzu ya qara matsawa da qaimi wajen nema,duk da abubuwan duka sai a slow,komai yaja baya sosai

“Amma fusakarki kamar baki da lafiya fa sosai” murmushin qarfin hali tayi,don batason tsaidashi,taji jiya yana lisaafin fita da wurin yana neman kudaden dazai biyawa yara kudin makaranta,yanzu tana cewa bata da lafiyar zai dakata daduk abinda yakeyi

“Dama mai tsohon ciki ina taga lafiya?,ai har sai sanda Allah yaraba”

“To Allah yaraba lpy”

“Amin adawo lpy” da haka sukayi sallama yafita,daga ita sai amir wanda yatashi bayajin dadi sosai saboda haka baije makaranta ba.

Tana daga zaune tasa amir yadauko mata komai inda take,kasancewarsa yaro mai hankali da nutsuwa sosai,ya tarbiyyantu qwarai wajwn mahaifiyarsa,donkoshi bbn amir din naji da yaron sosai,duk da bata nuna wata alama dazai gane wani abu ba amma saiyaji duk tausayin mmn nashi ya kamashi,daya gama saita turashi can harabar gidan tace yaje can yayi zamanshi karya shigo saita kirashi,harya fita tadawo

“Idan kaje kayita karanta rabbi yassir wala ta’asir ba adadi”

“Toh umma” yafada yana ficewa.

STORY CONTINUES BELOW

Gidan babu kowa sai rufaida,mmn ummi tun safe da wurwuri tafita kai ummi asibiti tana kashin haqori,sam kuma batajin zata iya kiran rufaida kan haihuwarta,sai tacigaba da ambaton sunan Allah yakawo mata sauqi.

Ganin wasu lokuta sunshude shuru yasanyata miqewa ta qwalawa amir kira,ashe baiyi nisa ba saigashi,ta sanyashi yataro adaidaita,yadauki kayana yasanya ciki,sannan ta yaye labulen rufaida ta leqa,tana kwance saman doguwar kujera tana ta baqin ran aikin yaran data gama,idan akwai abinda ta tsana a duniya ranar girkinta ta hidimtawa yaran,duk sa hannunta wayarta ce riqe tana chart

“Zamu wuce asibiti” saitadaja iska sannan ciki ciki ta amsa da

“Saikin dawo” ba tare data daga kaima ta dubeta ba bare tabi ba’asin tafiyarta asibitin,a matsayinta na mace mai tsohon ciki,itama bata damu ba tasaki labulen tayi gaba,dama ta fada matan ne kawai saboda fita haqqin musulunci,sai data shiga takira lambar bbn amir amma akashe,hakan yasanya tace sutafi kawai,a hanya takira qanwarta guda daya mai aure dake kusa da asibitin,kafinma su qarasa tarigasu isa.

Da kudade a hannunta sosai,saboda haka ita tabiya kudin komai,don tasan cewa koda bbn amir yana nan basu wasu kudade masu yawa a hannunshi,cikin ikon Allah bata dauki dogon lokaci ba da shiga labour room tahaihu lafiya,tasamu sankacecen yaro namiji,yaron kuwa tabarkalla dashi qosashshe,asibitin akwai kulawa,saboda haka nan danan nurses din suka gyarasu bayan da suka tabbatar da lafiyarsu ita da yaron.

Sai bayan awa biyu da haihuwarta tasamu lambar bbn amir din,tana gaya mishi duka yarikice

“Me yasa sai yanzu kike gayamin halima,kidaina wasa da lafiyarki fa” murya a tausashe tace

“Kayi haquri,ban samu wayarka bane”

“Ganinan” ya fada a hanzarce yana kashe kiran.

Yayi tsammanin xai taddata da rufaida ne,saiya sameta da hannatu qanwarta,sai data gama ganin baby sannan yace

“Ina rufaidan?”

“Tana gida”

“Amma tana gidan ki taho asibiti daga ke sai amir?”shuru tayi itadai batace komai ba,tunda batasan amsar da zata bashin ba,kai ya jinjina haushi nasake quleshi,yasoma kaiwa bango da halayen rufaidan,don wasu sabbin halayen iska tasake tsira ma,idan taso iskancinta yanzu ko kwanciyar aure sai tace saiya bada wani abu,ga kudinsa da idan yashigo dasu kullum sai yaga gibi babu wani abu a ciki,saboda yanzu ba kamar da bane da yakan shigo da kudade da yawa har baisan iya yawansu ba,duk da yayi amanna tsakanin mmn ummin ko mmn amir ba wanda ya taba dauka masa sisi ba tare da saninsa ba.

“A ina za’a biya charges na asibitin?” Ya tambayeta bayan ya qiyasta sauran kudin dake aljihunsa

“Na riga dana biyasunma” saiyadan tsuke fuska

“Waye yasakaki?”

“Ara maka nayi dama aiba kyauta ba” tayi saurin fada,donta lura kamar zaiyi mita ne,murmushi yasaki ba tare daya shirya ba

“Allah ya sanya kiyita haifamin yara masu irin halayyarki halima,na tabbatar duk namijin da yayi katarin samunsu a natsayin mata,ko macen datayi katarin samunsu amatsayin miji tagama morewa kamar yadda namore,Allah yabiyaki da gidan aljanna” ya qaraaa fada yana kissing goshin babyn daketa bacci abinsa,idanu ta lumshe tana amsawa,taji dadin addu’arshi qwarai.

Tana cika awa shiddan ta na qa’ida suka bata sallama ganin komai har sannan lafiya,shiya kwasosu a motarshi zuwa gida,amir na qanqame da yaron,yabata kallonshi yana santinsa,sai daya tsaya a hanya ya siya mata nama gashin mai ruwa ruwa dayaji albasa,sannan yaqara gaba yatsaya qofar wani shago,zai fita ta kalleshi

“Ina zuwa kuma?”

“Zan siya miki kayan tea ne ko?,don nasan kafin mu isa gida na unguwarmu sun shiga sallar magariba”

“Karka wahal da kanka,tuni inada kayan tea dina” saiya waiwayo yana dubanta,ranshi yasake masa wani sanyi,duk wani lamuranshi halima na kula dashi kenan,kamar tasan rashin kudinsa nasake daduwa shi yasa wasu abubuwan tayi dabara tarage,saiya jinjina kai kawai ba tare daya iya cewa komai ba yatada motar suka wuce.

1

Suna shiga gidan mmn ummi na fitowa daga kitchen dauke da kwanukan abincinta,wanda har yau girkin rufaidan kawai dai ana cine da haquri

“Lalalaaaaa….kada dai ace dama asibiti kika tafi” mmn ummi tafada cikin mamaki tana dubansu bayan ta tsaya cak,murmushi mmn amir tayi

“Wallahi,kina fita ciwo yataso”

“Ma sha Allah” tafada tana aje kwanon hannunta,ta isa wajen amir tana amsar yaron daga hannunshi

“Kice korani kawai kayi bawan Allah,kuma dana dawo babu wanda ya gayamin,nayita kiran layukanki akashe tunda naga ina zakije da tsohon ciki haka?,babansu ma wayarshi a kashe” taqarasa maganar tana nufar dakin mmn amir din data baiwa amir key yaba bude musu,murmushi mmn amir tayi,tanajin dadi gamida mamakin sauyin mmn ummi,hakan yamata dadi qwarai,donta fuskanci ta rage abubuwa sosai,kuma ta karanci ita akaran kanta tanajin dadin hakan,don tsakaninta da bbn amir zuwa yanzu babu wata matsala sosai,an samu zaman lpy sosai.

Aikafin sukai ga shiga tuni mubarak usman hanifa da rabi’ah sun cika tsakar gidan da hayaniya da murnar sunyi sabon baby,kowa so yake ya daukeshi amma mmn ummi ta hanasu,kai tsaye bayan fitowarta daga dakin gawayi ta aika amir yaje yasiyo gawayi,tahura a babban kurfeti tadora musu ruwan wanka sannan tawuce daki don taci abinci zuwa sabda zaiyi zafi.

Duk hayaniyar dake tashi rufaida na daki a zaune tana jinsu,bata motsa ba sai dataji ana batun haihuwa kana tatashi da sauri ta isa bakin window ta daga labule tana kallosu,duk da bata iya hango babyn,baki ta tabe ganin yadda bbn amir keta fara’a,taja dogon tsaki

“Saikace yau aka masa haihuwar fari,aikin banza kawai”tasake sakin tsaki takoma inda tatashi ta kwanta abinta,gaba daya ranta a dagule yake,gani take qimarta tayi qasa warwas,gani take kulawa da nuna jin dadin xamantakewa da yake nunawa matansa ita baya nuna mata,bayan tafisu da komai,itace amarya,ita yafi cancanta tasamu dukka wadan nan abubuwa(hmmm,ba’a nan take ba wai an dannewa bodari kai,ta manta da cewa ita zuciya a halicceta dason wanda ke kyautata mata,dakuma qin wanda ke munana mata,ko shekara dubu ma’autara sukayi da aure qarin soyayya dajin dadi ya ta’allaqa ne ga yadda kowannensu ke qoqarin ganin ya kyautatawa dan uwansa da zuciya daya,kuma bilhaqqi da gaskiya).

1

Yana dakinsa yana sauya kaya amma mamakin rashin ganin wulgawa ko giftawar rufaida yake,bayan yasan cewa iya hayaniyar yaran kawai ta isa ta gaya mata meke faruwa,sai daya sauya kayanshi sa’an nan yafito zuwa dakinta,a kwancen ya taddata tana kallo,yayi sallama ta amsa masa gamida ci gaba da abinda take bayan tatashi tazauna,haka kawai take ganin baqinsa,sam haushinsa takeji,gaba daya tagama tsara rayuwar aurenta ta gama tsara burikanta amma babu guda daya daya cika,komai datake tunani zato da hasashe tattare dashi dukka ashe ba haka bane

“bakisan halima ta haihu bane?” Saita daga kai cikin wani kallo tace

“Wace halima?”

“Halima nawa ce a gidan nan?” Dan shuru na sakanni kana ta yatsina fuska

“Ban samu labari ba” saiya samu waje yazauna sosai yana fuskantarta

“Rufaida,saurareni da kyau,bana goyom bayan rashin kyautawa ko rashin kirki,lokacin da halima zata fita zuwa asibiti na tabbatar nakumayi imanin bazata fita bata gaya miki ba,amma ta yaya zakibar mace tana halin naquda tafita daga ita sai yaronta?,baki ko tsoron wani abu yafaru da ita?”

“Tsoro kuma?,tab” idanu yazuba mata cikin mamaki,ganin haka sai tace

“Aini bata gayamin haihuwa zatayi ba,datasan haihuwa zatayi saita gayamin tacemin nazo na rakata” cikin mamaki ya jinjina kai

“Au harsai tace miki zata haihu kizo kuje?”

“To haka kawai saina tafi gayyar sodi,matar da bata son ana shiga sabgarta”

“Yayi kyau” yafada cikin bacin rai,saiyamiqe yafice daga dakin.

**************

Cikin kwanakin gidan cike yake da ‘yan barka,kasancewar mmn amir din badai dangi da ‘yan uwa ba,duk ran girkin rufaidan kowa iskancinta kawai take zubawa,fara damai zatayi tazarce tun rana har dare,sannan abincin da baqoshi akeyi ba,da bbn amir ya mata magana bata gyara ba saiya qyaleta,amma sam tadaina jin dadinsa,babu wata walwala datake samu daga gareshi,ita kuwa mmn amir bata isheta kallo ba,girkinta take awadace tazuba akula kai daki,duk baqon dayazo mata barka yaci yaqoshi,bata dorawa bbn amir nauyi ba,saboda tasan cewa yanzu bashi da wani abu,duka lallabawa ake.

Hatta da wasu tsarabe tsarabe na masu jego kafin ya ankara tayi wani abun,hakan ba qaramin sake daga datajarta yayi a idanunshi ba,tare da faranta mishi rai qwarai da gaske.

Masu karatu aci gaba dayimin afuwa dai da uzuri,sabgogin rayuwarne sai godiyar Allah,ina godiya sosai,amma kunsan me?,leqo qasa kiga wani abun alkhairi👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽

😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊

*SUN IYA SUN HUTA*

*Nasan zakuce yada murmushi haka?,eh mai karatu,abunne bansan yazan wassafamuku shi ba,saidai wadda bata shiga taje an dama da ita ba toba shakka an barota a baya*

*ina magana ne akan RAHA COMPUTER INSTITUTE,makarantar koyar da ilimin sarrafa kwanfuta fanni daban daban*

*karki dauka dai dai take da sauran makarantun kwamfuta,a’ah,wannan ta dabance kamar yadda malamanta suke na daban,duk yadda zan wasafa miki/maka bazaku gane ba,amma zaku gasgata zancena idan kuka zama daya daga cikin dalibanta,suna gab da miqa shaidar kammala karatu ga daliban BATCH A,zasuyi diba nabiyu,a yanzu haka sun soma saida foam na shiga makarantar ga daliban da basu iya komai kan computer ba da kuma masu neman shaidar DIPLOMA zuwa sama*

*_AKWAI KYAKKYAWAN TSARI NA RAGIN KASO HAMSIN CIKIN DARI NA ABINDA AKE BIYA_*

*don neman qarin bayani kai tsaye tuntubesu akan wannan lambar wayar*

1

08033990209

👁️‍🗨️👁️‍🗨️ *HANGEN DALA*👁️‍🗨️👁️‍🗨️
       _Ba shiga birni ba_
©️®️ *Safiyya Abdullahi Musa Huguma*

Haske Writers asso 💡


*BABI NA SHA TAKWAS*
*_ALBISHIR A GAREKU MA’ABOTA KARATUN LITATTATAFANMU,GAFA DAMA TASAMU,JERIN GWANON LITTAFAN ZAFAFA BIYAR NA FARKO DANA BIYU WADANDA SUKA CIKA GUDA GOMA KENAN CIF 10,SUNZO A KAMMALE,MA’ANA DACUMENTS KAN NAIRA 1,000,JERIN LITTATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*
*WUTSIYAR RAQUMI,GUDU DA WAIWAYE NA BILLYN ABDUL*

*K’AUNARMU & BURI DAYA NA MAMUHGHEE*

*IGIYAR ZATO &  NA MISS XOXO*+

*DAURIN GORO & NA RANO*

*ALQAWARIN ALLAH & DAURIN BOYE NA HUGUMA*
GAME BUQATARSU DUKA GOMAN ZASU TURA KATIN MTN TA WANNAN NUMBER
09032345899
SAISU TURA SHAIDAR BIYA TANAN
09032345899
MASU TURAWA TA BANKI KUMA ZASU TURA TA WANNAN ACCNT DIN

0225878823
HAFSAT KABIR UMAR
GT BANK
SAIKI TURA SHAIDAR BIYANKI GA WANNAN NUMBER
08030811300
*_AFWAN BISA DOGON JIRA FIYE DANA BAYA_*🙏🏽🙏🏽

Rungume da yaronta ta shiga dakin bbn amir din da sallama,fuskarshi wadace da murmushi yadago ya amsa yana dubanta,itama ta maida masa kafin yamiqa hannu ya amshi yaron,gefansa tasamu tazauna tana masa sannu da zuwa ya amsa yana tambayarta ya suka wuni
“Lafiya qalau” ta amsa mishi.
Ya bude baki xaiyi magana tsulum rufaida tashigo tana rarraba idanu,dauke fuska mmn amir tayi kamar bata ganta ba,fuskarta a dinke taci gaba da dubansu,tana daga tsaye take duban bbn amir din,shima ita yake duba ganin yadda tayi musu tsaye aka kamar wata bodyguard
“Dan bamu guri xamuyi magana” tafada cikin salon dakewa shima fuskarshi a dinke
“Kamar yaya nabaku waje?,ka manta yau ranar girkina ce?” Wani banzan kallo ya watsa mata
“Don ranar girkinne kuma shine me?,sai akace bazanyi magana da kowa ba sai da izininki keme girki?,ki bani waje nace” takaici haushi da baqinciki suka cikata,ita zai yarfa gaban mmn amir din,ita zai ciwa fuska?,saita ja tsaki ciki ciki ta juya zatabar falon tana maganganu
“Duk dai wanda ya zalunci wani Allah bazai qyale ba,koma meye mutum kuma yayi lokacine akwai ranar qin dillanci,ranar da hajar me gari ta bata” ba wanda ya kulata acikinsu,bbn amir nema yayi kamar zaiyi magana sai kuma ya danne bacin ranshi suka soma maganar da ta sanya yakirata wanda yashafi abun yanka ne ne na suna
“Naso raguna biyu na yanka mishi kamar yadda aka saba,amma wannan karon saidai haquri abubuwan” murmushi tayi
“Haba saikace yau aka fara?,duk wanda yasanmu yasanka ai yasan uzurine,wanda ba wanda yawuceshi,babu komai,albarka kawai muke nema”
“Hakane,Allah yashige mana gaba”
“Amin summa amin” ta amsa mishi
“Sai zancan taron suna,shima inajin halima wannan karon saidai ayimin afuwa” kaita girgiza
“Dama aiba dole bane shi,bare anyi basau daya ba basau biyu ba basau uku ba har hudu,kuma ni yarjewarka kawai nake nema,na gama komai” shuru yayi yana dubanta,ba shakka ba qaramin baiwar mace Allah yayi mishi ba wanda shi kansa baisan da hakan bai yanzu yake sake gani,Allah yasoshi da rahama ya kuma taimakeshi da bai barshi ya rabu da halima ba,ba shakka daya tafka babban kuskure kuma babbar hasara,don yayi imani,ya kumayi yaqinin tsakanin maryam ko rufaida bashi da guarantee akansu kan zasu iya kwatanta hakan,har gwara maryam din da yake yana ganin sauya sauye da dama tattare da ita.
“Allah yayi miki albarka halima,ubangiji ya albarkaci rayuwarki” cikin jin dadin addu’o’insa take amsawa da amin,har cikin ranta takejin dadin yadda haquri juriya da kawaici suka jawo mata babban matsayi a wajen mijinta,duk da haqurin dakau dakai ba qaramin aiki bane,amma hakanan tayi yaqi da kanta da zuciyarta taga tabi komai bisa tsari da kuma dacewa.
STORY CONTINUES BELOW

******   ******   *******

Ranar sunan tun safe gidan yasoma cika da jama’a,kasancewar mmn amir din ‘yar dangice tako ina,suna da yawan family,duk da ba masu kudi bane amma dukkaninsu suna da rufin asiri dai dai gwargwado.
Mmn ummi ce tashigo dakin dauke da qaramin botiki da aka zuba hanji,tunda aka soma zurga zurgar da ita ake komai,tayi qoqari qwarai ta kwatanta abinda mmn amir din tasha yi mata,wanda ita bata taba gwada yi mata ba sai wannan karon,takuma ga jin dadi sosai kan fuskokinsu daga ita har bbn amir din,wanda daga qarshe harsai daya yaba mata,yakuma dauki wasu kudi duk da basu da yawa ya bata yace tasha maganin ciwon jiki.
Zata iya cewa wannan shine karon farko da irin hakan tataba faruwa tsakaninta da mijinta,taji dadi ita kanta,abun ya faranta mata,saita dinga qissima halinta nada dana yanzu,sam babu hadi,babu kuma riba ko misqala zarratin,face qarawa kai qunci takaici da baqinciki,saboda tana lura da rufaida tunda aka soma sabgogin babu abinda take sai qunci da qananun maganganu,hakanan ta lura dasabani da suketa samu da bbn amir din,sannan tunda aka soma saboda baqin hali take kulle adaki,jiyane ma kawai data amshi girki akaga wulqawarta a tsakar gidan,haka kawai ta takura rayuwarta,ta sanyawa kanta mugun kishi da baqin hali,wanda bai kai mutum ko ina face kogin takura qunci da rashin sakewa.
Mmn amir tamiqawa botikin tana cewa
“Ungo riqe mumun gama namu,wanka nakeson naje nayi kafin gidan yasoma cika” murmushi mmn amir tayi
“To aike zaki ajiye wajenki,ni nan ina naga wajen ajiya?,kuma ma zaku diba naku keda  yara da babansu”
“Ok to shikenan,hanifa riqemin ummi yanzu nayi wanka nadawo” tafada tana kunce yarinyar daje bayanta tamiqa hanifa dake zaune,wadda taci kwalliya cikin shadda iri daya da sauran ‘yan uwanta duka su shidan da babansu,wadda mmn amir dince ta dinka musu dukansu,yayanta ne yakawo mata ita da kudi a matsayin barka saita bar musu.
Mmn ummin na fitowa daga dakin hajiya mahaifiyar bbn amir dasu jidda sukayi sallama gidan,hakan yasa mmn ummi dawowa har suka shiga dakin maijegon,suka gaisa sannan tafita tahada dan abinda aka gama na abincin sunan ta aiko musu dashi sannan tasake wucewa daki donta shirya.
Dai dai lokacin rufaida na daki,sanye da wata tsohuwar doguwar riga ta material,wadda tun a gidansu take amfanarta,sarai taji shigowarsu,sai taja tsaki tana gyara daurin dankwalinta takoma tayi kwanciyarta cikin ranta tana ayyana
“Aikin banza aikin wofi,munafukan banza da wofi,anzo a takura mutane a sanya musu idanu,baza’a bar mutum ma da baqin talaucin dake damunsu ba,saikace wata tsiyar dan nasu ya aje a gidan” da wannan tunane tunanen tayi kwanciyarta taja wayarta tahau charting.
Hira suke sosai abinsu da mmn amir din hajiyar dasu jiddan,hajiyan nata mata godiya kan qoqarin da take
“Aiya gayamin komai,halima saidai Allah yayi miki albarka,ba qaramin dace bane gamo da matar rufin asiri,a zamanin nan samun macen da zaka shiga talauci tarufa maka asiri aiba qaramin dace bane” murmushi mmn amir tayi cikin surukuta tace
“Hajiya an riga da an zama daya koda babu zuri’a a tsakani bare akwai,ba abinda abbansu baiyi mana ba sanda yake dashi,kinga ko koda yanzun bai mana ba aiba abun damuwa bane,Allah dai ya warware yaci gaba da rufa mana asiri”
“Amin ‘yar nan,amin” hajiyan tafada cikin matuqar jin dadi,da sake ganin qimar haliman,su kansu su jiddan kallonta suke suna jin dadi cikin ransu na yadda take zaune da dan uwansu.
Cikin hirarsu taji kamar suna batun za’a yiwa jidda kishiya,itadai tana saurarensu,amma bata furta komai ba tunda basu sanyata cikin maganarsu ba,ta fahimci jiddan ta rame sosai,kunnuwanta najin dukka abinda suke fada,sai abun ya bata mamaki yakuma so bata dariya yadda suka wani haqiqance kan kishiyar da za’a yiwa jiddan kowa da abinda yake cewa,saita tuna lokacin da za’a auro mata mmn ummi da rufaidan,yadda su jiddan suka zaqalqale,suka shiga suka fita,sukayi uwa sukayi makarbiya,jira ake a sannan aga gazawarta ko kasawarta,rashin haquri ko juriyarta,sai Allah yasa duka ba’a gani ba,wato su mata a sanda yaruwarsu zata shiga gidan mai mata murna suke,a sanda dan uwansu zai qaro aure murna suke,amma asanda za’a qarawa ‘yaruwarsu abokiyar xama sunfi kowa shiga tashin hankali da zaqewa,to wai shin ita wadda zasu kaiwa qanwarsu ba mutum ba?,koshi dan uwansun matarsa da zaiwa abokiyar zama suke murna itadin ba mutum bace?,koba mace bace ita?,tambayoyin data dinga yiwa kanta kenan.
STORY CONTINUES BELOW

Sai data shiga daki sauya kaya saiga jidda tabita
“Kiyi haquri anty halima kinga nabiyoki ko?,wlh magana naketa so muyi dake”
“Babu damuwa inajinki” sai data zauna gefan gadon sannan tace
“Bakiji muna magana ba daxu,wai abban madina ne yakeson yayimin kishiya ina zaman zamana mmn amir?” Taqarashe maganar hawaye nason sakko mata,kamar dariya zata subucewa mmn amir data tuna baya amma saita danne tayi murmushi kawai sanda take zuge zif din rigarta tace
“Shine kika tada hankalinki haka kika rame kika qanjame kamar qwarangwal?” Tana qoqarin maida qwallarta tace
“Haba mmn amir,abunfa da ciwo fa”kaita gyada
“qwarai kuwa,ni zan gaya miki haka,dukka haka mukaji amma muka danne,yanzu ba gashi kamar ba’ayi ba?…..” Kafin ta qarasa aka leqo kiranta,hakan yasa ta dubi jiddan
“Matakin farko kiyi qoqarin cire damuwa a ranki,don tunda yadauki damara babu abinda ya isa ya hanashi fasawa,ki samawarwa kanki nutsuwa da salama ta hanyar addu’a,saikiga komai yazo miki da sauqi,zan samu lokaci muxauna dake”
“To mmn amir na gode” tafada tana maida hawayenta.
“Wai matar gidannan unguwa tafita ne ranar suna?” Hajiyan jibril ta tambaya bayan ta idar da sallar azahar bata wulgin rufaida ba
“Wacce hajiya?” Mmn amir ta tambaya don bata tsammaci rufaidan bata shigo ba
“Amaryarku”
“Ohoo,tana nan mana hajiya….ke hanifa jeki kira antynku,kice tazo zasu gaisa da hajiya”sosai hajiyan taqule amma batace komai ba,don tuni ta fuskanci iyashegen da rufaida ke tatawa,qanwar jidda ce ta tabe baki
“Wai kamar hajiya sai an aika mata tazo ta gaisheta?”
“Uhmmm,Allah yakyauta dai kawai,amma dukka wanda ka goyadin daga baya sai kaga ba ‘yan goyon bane” yayarsu jidda ta fada,itadai jiddan babu bakin magana,don ta kanta kawai take yanzun.
“Anty wai kizo inji umma ku gaisa da hajiyan abbanmu” tashi tayi tazauna sosai tadubi hanifa kana ta watsa mata daquwa
“Hajijiya ba hajiya ba,tafi ki bani waje!” Ta daka mata tsawa,dasauri yarinyar tafice takoma dakinsu
“Umma,cewa tayi hajijiya ba hajiya ba,waina taf…”
“Ya isa,banson shirme” mmn amir tayi saurin kwabarta,saidai tuni autarsu bbn amir din taji,don haka tamiqe ba tare data saurari kowa ba ta nufi dakin rufaidan.
“Me kika kira hajiya dashi?” Ta tambayi rufaidan tana tsaye akanta,saita miqe tazauna tana kallonta
“Zuwa kikayi ki dakeni na gaya miki ko kuwa?”
“Idan dukanma ya kama aisai adakekin qaramar mara kunya” miqewa tayi tana dubanta sama da qasa kana ta kwashe da dariya
“Ke baki isheni yi ba,jeki turo manyanki,bazan zauna baqincikin dan uwanku da naku ya halakani ba wallahi,gaisuwa ce bazanje na gayar da ita ba sai me?,bajin dadin danta nima nake ba saboda haka ba wanda zai sake jin dadina nima wallahi”
“Au haka kikace!…..mara…” Muryar hajiya data daka mata tsawa ya tsaidata niyyar wanke rufaidan da tayi
“Fito mata a daki kixo wuce mu tafi” haka hajiyan ta tasa ta gaba,wanda daga haka ma tattarawa tayi sukabar gidan sunan gaba daya,zuciyarta cike fal da mamakin sauyawar rufaidan,yarinyar da kusan kullum kafin suyi aure saita kirata taji yata kwana yata tashi,hakanan kusan duk qarshen wata saita mata hasafi,biyayya kamar ta ahri jibril,har take ganin duk kirki da kyautar halima rufaidan ta shafeta,ashe baka sanin haqiqanin halayyar mutum saika zauna dashi.
Basusan ya akayi labari yakai kunnen bbn amir ba,a daren daya dawo ya tada ballin babu matar data isa ta wulqanta masa uwa ta zauna lpy,lallai sai rufaida tabar mishi gidanshi,mmn amir ita tashiga tafita tagayawa hajiyan me ake ciki,takira jibril din taja masa kunne kan karya kuskura yace tatafi gida,abun yamasa ciwo,dole ya haqura yabi umarnin hajiyan ba bisa son ranshi ba,amma rufaidan tasake ganin sauyi sosai tattare dashi.
Abun itama ya baqanta mata,ace kamar ita mmn amirce zata zama jagaba wajen zamanta a gidan,lallai saita tashi tsaye ba shakka,don ita bazata zauna zaman kwaikwayon kishiya ba kamar yadda tafuskanci mmn ummi tanayi ba.
******   *******   ********
Cikin tsari tsafta gamida sanin abinda takeyi taci gaba da jegonta da rainon yaronta dayaci sunan mahaifinta,wanda cikin wasu satittika tayi bul bul tayi kyau ita da yaronta gwanin sha’awa.
Tun suna da kwana ashirin bbn amir yasoma murda kambunsa kan lallai shifa tunda yanzu tasauka ta amshi girkinta,murmushi tayi taba dubanshi cikin salon tsokana
“Haba abban amir,aina tsammaci saimunyi arba’in biyu sannan zamu koma turaka” hularshi yadauka yadora saman kanshi bayan yamiqe sannan yabata amsa
“A’ah,arba’in dubu zakuyi ba biyu ba” yana qarasa fada yafice yabarta da qyalqyaltar dariyar yadda yayi kicin kicin yana fadin gaskiyarsa,wanda dariyar tata ta fada kunnen rufaida datazo wucewa,girkinta ne,kuma sarai taga ficewar bbn amir daga dakin,gakan yasanyata qulewa.
Tunda ta fuskanci da gaske yake saita koma girki da zarar tayi arba’in saita sake qara qaimi wajen gyaran kanta cikin hikima da sirri,yadda babu wadda zata gane cikin abokan zamanta,dama tunda ta haihun ba hakanan tazauna ba,bata wasa da ruwan zafi da fruits,madarar ruwa,kunun aya,kwadon zagale me qwai,kwakwa da dabino hakanan turarukan tsuguno bayan jini yadauke,dasu kanunfari da sauransu.
Saura sati ta amshi girki sauran gyararrkinta yasoma bayyana,duk da batayi gaban idanunsu saboda gujewa motsuwar kishinsu,da kuma iya taku,amma duk da haka saida rufaida ta sanya idanu tagane komai,saboda hadin qwai da madara da wata dilka da ruwan dumi da mmn amir din kewa jikinta yasanya fatarta ruwan chaculet ta qara sheqi da sulbi.
Take hankalin rufaidan yatashi matuqa,lokacin da taketa tunanin zuwanshi gashi zai iso,nan tashiga itama hade haden magungunan mata da duk kudin data tara wanda tayi niyyar zuwa gidan mardiyya takaita wajen malaminta ne,sai taga bari ta soma kashe wannan wutar gaban nata kafin taga kamun ludayin lamarin.
Mmn amir din ta lura da duk abinda take,amma saitayi murmushi kawai tayi kamar bata gani din ba,saboda abun nata babu wani sirri ko kamun kai a ciki,duk masu tallar magungunan mata turo mata su ake daga sabbin qawayen maqwabtan da tayi,da sunyi sallama dama zasuce wajen rufaida aka turosu,haka zaga danqara ba ruwanta da duba komai nashi,herbal ne kona bature ne,yadace tayi amfani dashi ko baidace ba,indai wata ta bata lbarin ta taba amfani dashi ya mata aiki shikenan anzo wajen ita a wajenta.
Haka ranar girkinta xataita zubda kwalaye babu kyan gani,saidai mmn amir tayita biyan almajirai suna zubda sharar gidan akai akai saboda gudun idanun yaransu kada suga wani hoton banzan dabe dace ba jikin kwalin.
Randa zatakai abba(jaririn)allurarshi ta arba’in,tabiya gidan yayanta,matarshi nabude gumaman kayan bacci masu kyau,takuwa taki sa’a ta zabar mata azababbu,wasu ma sababbine fil,ta amsa tasake zabar wasu kana tawuce gida.
Kafin ranar da zata amshi girki sai data tabbatar ta tsara komai nata,hatta kayan sawar abba da zasu dinga tafiya turaka dasu ta zabesu ta kammalesu,yaranta kuma ta gama tsara musu yadda zasuyiwa kansu wasu abubuwan,hakanan ta fannin girki hadin spices da maggi tayo kala kala,ta sassauya wasu coolers nata da sauransu.
Hatta mmn ummi wannan karon ta ankara,ta fuskanci wani abu,duk da tana qoqarin gyarawa da kwaikwayo amma sai data danji kishi,don bata taba tunanin tayi haka ba ita bayan ta haihu zata koma turaka,amma saita danne itama tadauki damarar sake gyarawa.
Ana ya gobe zata koma turakar taje aka yarfa mata qananun kizo da jan lalle,wanda wuni sukayi sur ranar a waje,don haka a gajiye ta dawo ranar,mmn ummi tadauki abba tana masa rawa
“Yau kunsha wunin waje abba,irin wannan shiri abba da kuke sai muja baya ko?” Murmushi kawai mmn amir din tayi tabar mata abban a hannunta tawuce daki,ta sani kishine wanda yana nan cikin zuciyar kowacce mace,kuma yana iya motsa miki aduk sanda yaso,so dole tayi mata uzuri,don mmn ummi na iya bakin qoqarinta wajen ganin ta caccanza abubuwa marasa kyau zuwa masu kyau,shi yasa ma bata damu ba.
Abban yana hannunta har tayi wanka tasauya kaya,saita dauki wani yankan salatif data siyo musu agidan data gani ya mata kyau
“Ko zaku saka keda ummina,acan gidan nagani yamin kyau” tafada tana amsar abban gamida miqa mata salatif din,fuskarta a sake ta amsa
“Kai amma kuwa yayi kyau,to muma madan sabunta,an gode” murmushi tayi tana riqe da hannun ummi data sake wayo sosai tana gudunta ko ina suka fice zuwa dakinta.
*Har yanzu makarantar nan taku ta koyon ilimin computer wato RAHA COMPUTER INSTITUTE(RACI) naci gaba da saida foam dinta ga dalibai a matakin farko,da kuma masu neman certificate na DIPLOMA,babu shakka sai an gwada akansan na qwarai 😊😊,makarantar ta bambanta da sauran makarantun koyar da komfuta da kuka sani,idan a birnin kano da kewayenta kake/kike,k’wararrun malamai ba ‘yan kuci ku bamu ba,zan iya cewa kinyi sake indai kika bari wannan babbar damar ta subuce miki/maka,maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number*

08033990209

👁️‍🗨️👁️‍🗨️ *HANGEN DALA*👁️‍🗨️👁️‍🗨️
       _Ba shiga birni ba_
©️®️ *Safiyya Abdullahi Musa Huguma*

Haske Writers asso 💡

*BABI NA SHA TARA*

*_NEW UPDATE_*

   
     Ana ya gobe zata koma turakar taje aka yarfa mata qananun kizo da jan lalle,wanda wuni sukayi sur ranar a waje,don haka a gajiye ta dawo ranar,mmn ummi tadauki abba tana masa rawa
“Yau kunsha wunin waje abba,irin wannan shiri abba da kuke sai muja baya ko?” Murmushi kawai mmn amir din tayi tabar mata abban a hannunta tawuce daki,ta sani kishine wanda yana nan cikin zuciyar kowacce mace,kuma yana iya motsa miki aduk sanda yaso,so dole tayi mata uzuri,don mmn ummi na iya bakin qoqarinta wajen ganin ta caccanza abubuwa marasa kyau zuwa masu kyau,shi yasa ma bata damu ba.
+
Abban yana hannunta har tayi wanka tasauya kaya,saita dauki wani yankan salatif data siyo musu agidan data gani ya mata kyau
“Ko zaku saka keda ummina,acan gidan nagani yamin kyau” tafada tana amsar abban gamida miqa mata salatif din,fuskarta a sake ta amsa
“Kai amma kuwa yayi kyau,to muma madan sabunta,an gode” murmushi tayi tana riqe da hannun ummi data sake wayo sosai tana gudunta ko ina suka fice zuwa dakinta.
*Har yanzu makarantar nan taku ta koyon ilimin computer wato RAHA COMPUTER INSTITUTE(RACI) naci gaba da saida foam dinta ga dalibai a matakin farko,da kuma masu neman certificate na DIPLOMA,babu shakka sai an gwada akansan na qwarai 😊😊,makarantar ta bambanta da sauran makarantun koyar da komfuta da kuka sani,idan a birnin kano da kewayenta kake/kike,k’wararrun malamai ba ‘yan kuci ku bamu ba,zan iya cewa kinyi sake indai kika bari wannan babbar damar ta subuce miki/maka,maza garzaya ki tuntubesu ta wannan number*

08033990209

      Tun  a safiyar ranar gidan yasamu gagarumin sauyi,shi kansa da ace yana magana tozai tabbatar da cewa lalle yau akwai sauyin dake shirin faruwa,don tunda ta idar da sallar asuba bata zauna ba tasoma qalqale waje waje na gidan wanda tajima tana jin haushinsa saboda yadda akayi sakaci ya lalace.
      Girkin rufaida ne ranar kuma ranar zai fita daga dakinta yadawo dakin mmn amir din,don haka hatta shirin makaranta na yara ita tayi musu bata tsaya jiran tashin rufaida ba,wanda dama yawanci yaran duk ranar girkin nata sai sun makara a makaranta,koda basu makara din ba basa samun wani kulawa yadda ya kamata haka suke haquri.
      Bakwai da rabi yaran sun gama shirinsu tsaf,daidai lokacin da me adaidaitan dake kaisu yaiso,hanifa tadubi mmn nasu
“Umma…abba bai tashi yabamu kudin break ba,naje na tasoshi?” Sam ko kadan ba al’adarra bace,hasalima bata yadda ko barin yaranta na shiga dakinsa ko dakin daya daga cikin matanshi idan acan yakwana da niyyar tashinsa ko zuwa karbo wani abun,hanasu take harsai sanda yafito,idan kuma ita tana dashi ta sallamesu kawai,wannan karon ma hakan ce ta faru
“A’ah,haba hanifa,lunch box dinku duka da abinci,har lemo fa na saka muku,me kuma zakuyi da kudi?” Langabe kai tayi
“Umma don Allah ko biyar ce”
“Uwar wayo,a baki takeso ta saka fa umma” cewar ahmad yana dubanta,harara ta galla masa
“Ina ruwanka?” Tafada tana tura baki
“Shikenan ya isa,amir” ta qwala mishi kira daga dakinsu sai gashi ya iso
“Ina kudin dana baka ajiya shekaran jiya?” Haka take musu lokaci zuwa lokaci takan dauki kudi da zummar batasan ma nawa bane ta basu ajiya don gwada amanar ‘yaran nata,bata taba kuma ganin ba dai dai ba
“Suna can qasan kayana”
“Debomin” ya amsa mata yana komawa dakin nasu,ba jimawa yafito dasu yamiqa mata,tasa hannu tana amsa gami da cewa
“Nawa ne kudin?”
“Dari hudu da hamsin da biyar” haka kudin suke cas tasani,tana sane tasake tambayarshi,saita warware ta baiwa manyan naira goma,qananun biyar biyar dukansi,sai usman da ba’a sashi makaranta ba dake tsaye yana zaro ido suna masa gwalon shi badan makaranta bane ai,zai sanya kuka shima tabashi biyar din ,saiya shiga murna.
STORY CONTINUES BELOW

         Sai data tabbatar sun shiga adaidaitan sannan tadawo tsakar gidan,daidai lokacin da mmn ummi ke sanya silifa dinta dake qofar daki,takalli tsakar gidan tana kama baki
“Tabdi,sannu da aiki mmn yara,yanzu duka yaushe kikai wannan aikin ina can ina bacci?” Yar qaramar dariya mmn amir tayi sannan tace
“Ai gwara ku huta,kunsha aiki da yawa,wata kusan hudu ko biyar aiba wasa ba”
“Gaskiya kin aikatu sannu” tasake fada tana duban yadda marbles din gidan yayi wani haske na daban.
       Gaisawa sukayi sannan kowacce tawuce inda zata,mmn amir dakinta takoma donta gama duk abinda zatayi a tsakar gidan,ta sake kintsashi duk da amir da ahmad kansu wuce makaranta bayan sallar asuba suke share mata shi tas,sun kuma iya saboda ta horesu bata qyalesu ba wai don suna maza,idan suka mata shara sai ayita mamaki,zaki tsammaci macace tayi,a sannan abba yana bacci,saboda haka bayan tagama tasirja ragowar ruwan zafin data yiwa yan makaranta wanka tasanya a bandakin falonta tashiga tayi.
       Tsaf tashirya bayan tafito cikin atamfa riga da zani,ta bulale jikinta qamshin turarukanta data yiwa tanadi saboda wannan lokacin,koda bata jego bata wasa da turare bare tanayi,qaryarka kadauki yaronta kaji yana qarni tsami ko hamami iyakar sanin da zakayi mata,ganin akwai wutar nepa saita jona burner dinta tacika ta da turaren wutarta tadawo falo tazauna tahada tea mai kauri tasoma sha kafin abba yatashi ya tsotseta,don bata dafa abun kari na gidan ba,iya na ‘yan makaranta tayi tunda ba girkinta bane.
       Cikin qaramin lokaci saqon qamshinta ya gauraye ilahirin gidan harda maqota,ya hadu da ragowar sanyin safiya yabada wani yanayi mai dadi,haka qamshin yacigaba da kutse har cikin hancin bbn amir dake kwance yana bacci,saiya soma bude idanunsa a hankali yana tuna a inda yasan wannan qamshin.
        Sassanyan murmushi yasaki yanajin wani madaukakin farinciki yana ratsa zuciyarsa daya tuna yau kwanan halimatussadiya ne,saiya tashi yazauna sosai saman gadon,yawaiwaya gefansa saiyaga rufaida na sheqar bacci abinta,da sauri yakalli agogo,tara saura,yara fa?,waye yashiryasu zuwa makaranta?,yayiwa kansa tambayar,cikin hanzari yasoma tashinta.
       Sai data gama miqa sannan tamiqe tazauna cikin ranta tana mita,tana kishinsa amma wani lokaci takan gwammace ba kwananta bane,saboda tafiyin baccinta ta more yadda ranta yakeso.
Tsaki taja ciki ciki bayan tasauke hamma sannan tace
“Lafiya?” Agogo ya nuna mata yana shirin sauka daga gadon
“Yauda makaranta,yara ba abinda aka dafa musu bare a shiryasu,yi maza ki tashi don Allah” yafada a gurguje yana dage labulen bedroom din yafice daga dakin,wata muguwar harara tabi bayanshi dashi sannan taja matsiyacin tsaki,cikin qunquni tasoma saukowa tana maganganu ita kadai
“Wai yara,ina ruwana dasu,kada Allah yasa suyi karatun ma,auren mai iyali auren jaraba auren masifa,baya ta taka kullum sune a ransa,kafin ya ambaceka ma ya ambacesu,baka haifa ba amma ka qare a bauta” ta dura ashariya sannan taja zaninta tayi daurin qirji kafin tafito falonta.
     Da mamaki yake duban tsakar gidan yadda yake fes fes kamar wani lokaci can baya,saiya kauda wannan yanufi dakin mmn amir don yaji baiji ma motsin yaran ba.
       Sallamarshi da lumshe idanunsa duka lokaci guda yayisu sabida qamshin daya mamaye hancinsa wanda yayi kewarsa fiye da tunani,sanda take amsa masa sallamar samun kansa yayi da zuba mata idanu,wani irin kyau tayi masa gamida daukar hankalinsa ba kadan ba,ga qamshinta daya cika mishi hanci,ita dinma ta lura da hakan,saboda haka tasaki murmushi,tasan cewa tun rana ta dana tarkonta,lallai yau zai wuni ne da tunaninta,hakanan dokinsa zai sake ninkuwa.
      Amshe gaisuwar da take mishi yayi
“Ina yara?” Dan juya idanunta tayi
“Yara kuma aisun tsufa a makaranta” ajiyar zuciya yasauke
“Ina can ina na rude naga lokaci yawuce na zaci basu tafi ba”
“Haba kai kuwa abban amir,kawai saimu zauna jira bayan zamu iya sallamarsu” murmushi yasaki
“Hakane,amma wannan aikin nasan na halimatussadiya ne” yafada yana mata wani irin kallo,saita saki murmushi kawai tadan sadda kai alamun kunya,wanda hakan ya qayatar dashi sosai.
STORY CONTINUES BELOW

      Ta bangaren rufaida kuwa tunda tafito tasaki baki galala tana duban yadda gidan yacanza gaba daya kamar bashi ba,gabanta yayi mummunar faduwa data tuna cewa yau baqar rana ce a wajenta,wato ranar da mmn amir din xata amshi girki,tana nan tsaye tana jimami har mmn ummi da tun sassafe ta saka lalle da salatif din da mmn amir ta bata tafito cirewa saboda yayi awannin daya kamata yayi,bata kalli rufaidan ba tawuce bakin famfon tawanke abinta,duk akan idon rufaidan
“Cabdijan,wai suna nufin kai zasu hademin,ita taje an mata lalle itama ta saka,kan uban nan kayyasa”.
      Sanda mmn ummi tazo gifatata sai tahau yada waqar habaici,duk daba daidai take waqar ba
“Kayan aro abun banza ne……dole wataran kadawo naka” ita dariyama tabaiwa mmn ummin,bata isheta kallo ba ta wuce dakinta ta turo qofarta tabarta anan a tsaye,don a yanzu ta girmi wannan abun,bata sake ganin wautarta bama sai dataga yadda mmn amir din ke komai cikin aji da hankali.
      Abun saiya tsayawa rufaidan a ranta,ita daya atsakar gida,ta kasa wucewa kitchen dinma bare tadora abinda zata dora,tana shirin shigewa saiga bbn amir yafito daga dakin mmn amir din,fuskarsa dauke da murmushi,don iyakar ganin da yayiwa haliman ya tabbayar yau a ango yake sak.
      Da idanu ta tsareshi,zuciyarta kamar tafaso qirjinta tafito saboda kishi,taci gaba da kallonshi harya wuce dakinsa batare daya kula ma da abinda take ba.
     Wannan bacin ran yasanyata ruwan tea kawai ta dafawa a gidan tsurarsa,tunda kowa nada bread dinsa a daki,yawanci da daddare yake shigowa dashi yabaiwa kowacce nata.
      Tayi hakanne dabiyu donta batawa bbn amir din rai,abinda bata sani ba ko a qasan silifas dinsa,yasan yaudin ko babu komai zai huce duk wani bacin ranshi,yashirya abinsa ya biya dakin mmn amir din tana zaune tana baiwa abba nono yabata kudin cefane hade da muqullin dakinsa
“Rufaida tana ciki,idan tafita kya kulle” ya gaya mata,kyawawan addu’o’in data saba tayi masa,ya amsa cikin walwala kana yafice.
       Sai data gama bawa abba nono sannan ta goyashi tafito,don tana son gyaran dakin bbn amir din,shi kadaine bata gyara ba saboda bata da dama a sannan,don girkin mmn ummine data gama ta baiwa rufaida,batason tashiga haqqinsu,ko baya ga haka ma batason tayi gyaranta wata ta bata mata.
     Ga mamakinta har yanzu rufaida na cikin dakin,ta gane hakanne ba tare data shiga,takalmanta data gani kawai ya shaida mata,saita qyale bata shiga din ba,takoma ta hada ruwan wanka tayiwa abba,tashiryashi ta sake goyashi sannan takuma fitowa taduba ko zuwa yanzu tafita daga dakin,saidai har yanzu tana ciki,a karo na ukune data ga bata da niyyar fita ta yaye labulen falon kana tawuce uwar dakin,don tanason gamawa da wuri tadora abincin rana saboda yara ‘yammakaranta da zasu dawo.
     Shame shame tasameta saman gadon,daga ita sai kayan bacci masu shara shara sosai,wayarta a hannunta tanata charting,ta daga kai suka hada idanu,sai mmn amir din ta gintse kamar bata ganta ba tasoma tattare labulen bedroom din don so take ta sauya mishi wani data siya duk da mai sauqin kudine amma suna da kyau.
      Harta gama cire labulayen bata motsa ba,don haka cikin dakiya dashan magani tace mata
“Ina buqatar space zan kintsa dakin” wata miqa tayi tana tashi zaune sosai
“Oh sorry…..wallahi….jikinane duk ciwo yake,a gajiye nake,kinsan halin maigidanne haqurinsa kadanne,baida wasa ta wannan fannin” juyowa tayi sosai tadubeta yadda taketa wani yatsina,murmushi mmn amir din tayi duk data motsa mata kishinta amma bata bari tagani ba koda saman fuskarta kuwa
“Qwarai kuwa,nizan bada labarin haka,ai Allah ya taimakeki ma da kikazo a qarshen lamarin,kina da mataimaka masu karbar miki shi ki huta,ni a lokacin da nake amarya ni kadai dagani saishi,dukka soyayyarsa babu wajen da zai raba ya rageta ni kadai nake tallafarta ai ansha gwagwarmaya,kice da kece bazaki iya ba,ashe nidin ba qaramar jaruma bace,shi yasa kinga yara hudu cas ga goyon na biyar a baya,banda jarumi wazai haka?” Dum rufaida tayi,saboda ta fuskanci bayan maida mata magana datayi harda habaicin bata mori soyayya ba ita kadai,don haka ta figi mayafinta ba tare data ce komai ba tafice a dakin
“Mara kunyar banza da wofi,mu zuba,nida ke shege ka fasa” taja qaramar qwafa taci gaba da aikinta.
STORY CONTINUES BELOW

     Gyara tayiwa dakin na haqiqa komai saida tabi ta kanshi,hakan yadan ja mata lokaci,inda Allah ya taimaketa mmn ummi da taga bata komai saita tayata da gyaran su kayan miya da sauransu,tana bakin qofar sunayi suna taba hira,zuciyar rufaida kamar tafito,haka tadinga leqensu ta window dinta abun yana nata ciwo,daga qarshe data rasa yadda zatayi tahau group dinsu ba watsapp tasoma bawa qawayenta labari tana tsinewa su mmn ummin da basusan me ake ba,suka tayata suka zagesu tas,kana kowace tahau bata kalar tata gurguwar shawarar.
      Tana da zafin aiki ba laifi,don haka tana kammala girkin baifi da minti biyar ba yaran suka shigo,a sannan qamshin miyar data sauke bai gama tafiya ba wanda taji spices din data tanada tun randa tayi siyayya,aikuwa suna sallama kowanne yasoma cewa yunwa yakeji,mubarak kuwa yaron mmn ummi dayaga itace akitchen saiya riqe cokali yahau rawa
“Yau zamuci girkin umma” haka Allah yayishi duk dabai wuce shekara goma ba amma yanason abinci mai dadi,yakuma san umman tasu ba baya bace,ko jallop ta sarrafa saikaji taste din har tsakar kanka.
     Abinci tayi mai kyau ba kamar wanda mmn ummi kanyi ba koda yaushe da rana basa wuce dafa duka saboda gandar dora sanwa biyu,uwar gayya rufaida kuwa tunda tazo girkin rana fara da maice,maici yaci,mara ci ya haqura,ta hadawa mazan daban matan daban,tasa amir yadaukowa kowa lemo a fridge dinta,nan fa baki ya gaza yin shuru,sukayita surutu wanda idan kakula dakyau santi suke.
      Mmn ummi na daga falonta wanda labulenshi ke a dage tana karantar taran,farincikin da suke da yadda suke enjoying abincin kawai ya isa ya gaya maka abunda ke cikin zukatansu,sai a sannan tayi picking wani kuskuren nata wanda tunda suke da mmn amir din batama taba fuskantar yadda suke zumudin abincinta ba sai yanzu,tasan dai yawancin lokuta zataga mmn amir din idan zatayi miya tana daka wasu abubuwa tazuba wanda ita a wajenta bata daukesu a bakin komai ba,hasalima ganin qoqarinta take idan tazauna tana yiwa miya dake dake,takance
“Bayan zaman bare maggi saikin wani zauna wani aikin bare bare na wasu abubuwa daban?,ai miya indai maggi da mai yaji shikenan an wuce wajen”.
      To ita kanta ayau datake cin abincin ranar tana cine tana karantar banbance banbance,babu qarya abincin ya mata dadi harta taya yaran suma.
      Rufaida kuwa tun tana daki qamshin ya isketa,saita dinga tunanin daga maqota ne,amma sanda tazubo abincin saita gane daga ina ne,sanda tazauna tasoma ci taso taci da yawa saboda taste din yayi masifar kama mata harshe,amma data tuna shawarar da daya daga cikin qawayenta ta bata ba banzatar da abinci da yawan qorafi gaban maigidan kan girkin mmn amir din saita dannan babbar loma a matsayin lomar qarshe tamiqe da kwanon a hannunta ta isa kitchen.
       Takuwa taki sa’a mmn amir din tana ciki tana kwabin wainar shinkafa,ta aika amir kan suwuce islamiyya cikin kudinta yasiyo tantaqwashi donta sake burge bbn amir din
“Nifa gasky qamshin dake cikin miyar nan yahanani cin abinci,don wallahi niban saba jin irin wannan ba,saikace an zuba mata turare,komai gauuuu a ciki,gasky bazan iya jurewa ba don ban shirya zama da yunwa ba wlh” ta dangwarar da plate din ta tsaya tana jiran taji me zatace.
       Saidai banza mmn amir din ta baiwa ajiyarta,idan tukunyar dake kitchen din ta nuna tasan rufaidan tashigo to mmn amir tanuna tasan da shigowarta,saita maida kanta ga hanifa dake yanka mata alayyahu tana gyara mata yadda ake jerashi kafin a yanka,don yawancin yanzun tare suke shiga kitchen ranakun da babu makaranta,ko idan aiki yacabe mata kamar yau kafin lokacin shiga islamiyya yayi,tunda sai uku da rabi suke tafiya.
      Ganin taqi ko dubanta saita buga tsaki
“Bari shi jibril din yadawo,yasan matakin dauka wallahi” tafice faran faran daki,haka ta haqura tacika cikinta da ruwa tana jiran dare sadda maigidan zai dawo.
       **********
      Kafin magariba ta gama komai,gidan yadauki harama,hatta iskar gidan kamar an canzata saboda qamshi take bayarwa,tayi wanka hade da alwala tashige uwar dakanta,bayan ta baiwa su amir dake assigment riqon abba,ta tura qofar tarufe saboda idanun yara,kana tasoma kintsawa,duk wani loko da saqo na jikinta tayi mishi abinda ya kamata kafin lokacin bacci yayi,ta duba cikin kayanta ta fidda riga da skert na atamfa da dinkin ya mata cas yafidda kowanne komada ta jikinta tashirya kanta a ciki.
STORY CONTINUES BELOW

      Bata fiya damuwa da sanya qananun kaya ba idan ba gown haka ba ko skert budadde saboda yara,tayi imanin cewa basai kin saka kayan da qirjinki zai fito koya kasa rufe miki cibiya,koya shaqe miki wuya ko hannu sannan zaki kyau ba,a’ah,shi ado da kwalliya iyawa ce,saidai duk sanda tayi shigar wala atamfa ko gown takanyi wani kyau,saboda kowanne lokaci takanyi duba da yanayin da kwalliyar zata dace dashi.
      Sosai tayi ruwan tararewa kanta,sannan taduba wata after maikyau cikin kayanta tadora saman kayan saboda sundan matseta,amaimakon ta bata mata kwalliya saita sake qawatata,kamar baqar balarabiya,ta yafa qaramin mayafin after din tafito zuwa dakin bbn amir donta aje wasu kayyaki da zata iya amfani dasu a kwana biyun da zatayi,dazun saboda idanun mutane yasa bata shiga da komai ba tabari sai duhun magariba yashiga.
      Kusan a idanun rufaida kome yake wakana,don tunda tazauna bakin window dinta takasa tashi,addu’a kala daban daban tadinga yi,har bata qaunar taji sallamar bbn amir yau cikin gidan.
2
      Fes ta hangi mmn amir din saboda akwai wutar nepa,qirjinta yahau suya da wani irin kishi,harta shiga tafito idanunta yana wajen.
      Haka kawai yaji yau bazai iya shiga gidan hannunsa haka ba duk da babu isashshen kudi a hannunsa saboda har yau basu fita daga matsalar batan kayansu ba,kawai dai ana jalauta rayuwar cikin rufin asirin Allah,dama kuma jibril din ba baya bane wajen riqo wani abun yashigo gida dashi,ba kasafai yake shigowa gida haka ba.
       Kifi ya tsaya yasiya musu mai kyau mara qaya ragon ruwa kana yawuce gida.
      Yana sallama dukka yaran dake dakin mmn amir suka fito suna masa oyoyo,kasancewar sunfi zama a can har yaran mmn ummi,basu wani damu da dakkn mmn nasu ba sosai,don mmn amir din tafi dadin sha’ani,hatta da ummi da yanzu tasoma wayo tafison tafiya can,wani lokaci saisu bar mmn nasu ita kadai.
      Ummi dake itace qarama yasoma dagawa sauran yana shafa kansu yana amsa sannu da zuwar da sukeyi masa,dai dai lokacin da rufaida ke labe bayan labule tana kallonshi gabanta na faduwa,kishi fal ranta.
     Tunda yashigo yashaqi qamshin gidan gaba daya hankalinsa ya karkata wajen mmn amir din,amma dole yayi adalci yadda yasaba,mai girki dakinta ne qarshen shiga,wannan karon mmn ummi ce a matsayin babba,don haka yanufi dakinta.
       Tana zaune a falonta tana goge kayan yaran yashigo,fuskarta ba yabo ba fallasa ta aje gugar tana masa sannu da zuwa da tambayarshi ya kasuwa kamar yadda taga yawanci mmn amir din nayi,ya amsa ciki jin dadin yadda take sake sauyawa,yana addu’ar Allah ya dorar da ita,yana kuma qara ganin qimar halima don ya tabbata kusan itace silar wannan nasarar data fara samuwa.
       Saiyadan zauna mata nadan wani lokaci donya faranta mata,kana ya fice zuwa dakin rufaida usman rabi’a da ummi suka bishi.
       Tana ganin tahowarsa takoma takwanta rigingine tabaiwa qofa baya,da qyar ta amsa sallamarshi yaqarasa shigowa idanunshi kanta
“Lafiya dai ko?” Ya tambaya ganin yanayin nata,saita yatsine fuska tana wani gyara kwanciya daqyar
“Tunda kafita bani da lafiya ne” tayi maganar tana hararar yaran ta qasan idanu,saboda takaicin hawar mata kujera da sukayi
“Ayyah,Allah ya sawwaqe,kin sha magani ne?” Saita kada kai,anzo wajen,dama kudi take nema daga wajensa,tana so tacika kudaden da take fafutukar hadawa don ta yaqeshi shida matansa gaba daya
“Asibiti nakeso naje gobe” shuru yadanyi don yasan kudin hannunshin yanzu basufi suyi masa lalurar gobe ba,inda yasan zata buqaci zuwa asibitin da ya haqura da siyan kifin,amma yasan goben Allah bazai hana yadda za’ayi ba
“Ba komai,Allah yanuna mana goben,duk da babu kudi hannuna amma Allah bazai hana yadda za’ayi ba zuwa goben” wani qarin takaicine yacikata sanda yamiqe zai fita yana mata sallama,na farko ta tsammaci yadda taketa juye juye zai tsaya ya bata lokaci sosai wajenta fiye da yadda ya bata yanzun,nabiyu kuma baqincikin yadda kullum babunsa take qara gaba take,ta zabeshi cikin manemanta ganin duk yafisu abun hannu,ashe zata bare da ita,taja wani matsiyacin zaki tana kashingida gamida zaro wayarta,a sarari ta furta
“Mtswee,tsautsayin takaba auren shidadde” saita koma grp dinsu tana duba chart din da aka gama dazu,ana hirar wani dan grp dinsu da yake buga wani game,yayi kudi lokaci guda sanadiyyar hakan,harma ga motar daya siya nan falleliya an turota group.
STORY CONTINUES BELOW

     Bata mantawa sa’idu na daya daga cikin masu sonta a sannan,amma saboda bashi da komai taga tafi qarfin ajinsa,me zatayi da saurayi wanda a yanzu yake fafutukar nema,mena sama waci bare ya baiwa na qasa,gwara dai ready made
“Allah dai yasa ba rabon wahala bane yake kirana,gudun qaddara guzurin taddata,Allah ya kiyaye” tafada bayan tagama duban hirar tasu.
       Sanda yashiga falon nashi komai ready yasameshi,hatta da cokali da tsumman dazai goge hannunshi,murmushi yadan saki saboda yayi missing irin wannan,gyaran falon kawai yasake kwantar mishi da rai,ya fuskanci kamar yaudin wani dan jan aji takeji dashi,don sanda yashiga da yaran dakin nata sai ya tadda tana bandaki wai,don haka yayi dakinsa cike da daukin ganin isowarta.
      Tana sallama yacira kai da sauri,ya amsa mata yana qare mata kallo,tana qarasowa dab dashi xatayi masa sannu da zuwa yayi caraf ya janyota cikin jikinsa,saiya sauke ajiyar zuciya yana jin yadda yayi rashinta da yawa,qamshinta yake sansana loko da saqo na jikinta yana lumshe idanu
“Yau an ‘yantani halimatu” dariya tadan kubce mata,kafin tayi magana yasake cewa
“Qamshi kike mmn amir,qamshi mai dadi,gaskiya na yadda yau ango nake” nanma dariya yabata,saita zame jikinta tana cewa
“Kasoma wanka tukunna bbn amir” ta tuna masa abinda yaso mantawa,don bayan barinta dakin babu wadda tadamu dawai yayi wanka bayan yadawo daga kasuwa,saidai wani lokaci shi a karan kansa idan yaji yana da sha’awar yin hakan.
       Kusan kome yake hankalinsa yana akanta,haryayi wankan yafito,sai yace sai yaje yayi sallar isha’i sannan zaici abinci,don haka ya hada kan yaran mazan suka wuce masallaci.
       Kafin yadawo ta gama da yaran,har abba dake bacci tabar musua dakinta,bayan ta kunna musu cartoon a mbc 3 bayan ta tabbatar da cewa basu da wani assigment na makaranta,saboda haka yana dawowa ta tattara mishi dukka lokacinta,wani sabon amarci sukeji dukkansu ita dashi,don a jikinsa take tana bashi abincin da kanta,bai sake sanin yayi missing komai nata ba sai daya soma cin abincin,lallai ba shakka yayi rashi mai yawa,ya rasa taste dinta na musamman
“A ina aka samu nama yau a miya?” Ya tambayeta sanda yaga nama a ciki,murmushi kawai tayi
“Allah ne yabamu yau” shima murmushin yasaki,yasan halinta tun ba yau ba,kusan takanyi hakan lokaci zuwa lokaci,musamman idan taga kwana biyu bai siya ba,koda yana da kudi,idan tayi hakan saiya zama kamar tuni ne a wajensa ba tare datayi magana ba,baya rufa kwana uku bai siya ba kuwa daga ranar,dukka hankalinsa yana kanta,musamman yadda dinkin ya fidda qirjinta dake a cike
“Nikam abban amir kada ka cinyeni mana,wannan kallon fa” tafada adan shagwabe kamar ba ita ta aje amir da ahmad ba,murmushi yasaki kana yace
“Ba zaki fahimta ba uwar gida sarautar mata” daidai lokacin rufaida ta turo qofar gamida yaye labulen,dukka suka maida dubansu gareta,sai sannan tayi sallama zuciyarta kamar zata tsinke saboda yadda tagansun ko ita a kwanakin amarcinta ba zata iya tuna sanda suka zauna kamar haka ba ita dashi
“Lallai matarnan ta cika qaramar karuwa” tafada a ranta.
       Janye jikinta mmn amir tayi gefe,saidai bata ko daga kai ta kalli rufaidan ba,hakanan bata tashi daga wajen ba,don zuciyarta da jikinta ya bata da gangan tayi hakan,bai kyautu tafado kai tsaye ba ba tare data tsaya daga bakin qofa ta nemi izni ba,tunda daga ita har mmn ummi haka sukeyi idan zasu shiga wajensa indai harda wata a ciki.
      “Lafiya?,qaraso bismillah” abban amir din yafada cikin mamakin ganinta,ya tsammaci ko jikinne,saidai sanda tazauna tana harhada rai,kishi na sake kamata,bata taba tsammanin haka mmn amir din keda kyan jiki ba,a yadda tasanta tana da ciki duk ciki ya bata yanayinta ta zaci a haka take,kota haihu ba zata canza ba,saboda tana jin labarin haihuwa tana lalata shape da kyan jikin mace,amma saitaga sabanin haka,uwa uba ma bata da rabin structure na jikin mmn amir din,tana ankare da kallon da take mata,saima tasake daidaita zamanta dakyau tana basarwa itama,qorafi tasoma cikin  bacin rai
“Qara nakawo maka jibril?”
“Qarar wa?” Ya tambaya cikin mamaki
“Wadda tayi girki yau,ni gaskiya ba’a kyautata min ba,ya za’a bani wani abinci duk qamshi,an cika abinci da abubuwa wanda ni na kasa ci bazan iya cin abinci mai qamshi ba”
“Qamshi?,wanne irin qamshi ne a girki halimatu?” A nutse tace
“Nima dai ban sani ba,amma gata nan ka tambayeta”.
      Bai sake cewa komai ba saiya daga waya yakira mmn ummi,babu dadewa tashigo ya tambayeta
“Qamshi kuma?,agirkin namu?,indai qamshi take magana saidai irin na wannan miyar da kake ci” tafada tana dora idonta ga rufaida
“Kasan dai yanayin girkin mmn amir din,qamshin girkinta daban yake” kai ya jinjina don yafi kowa sanin hakan
“Ai dama nasan baza’a gaya maka gaskiya ba,saboda ni aka tsana,anason hademin kai a musguna min,to nidai nawa abincin banda qamshi kamar na turare turare ko hoda babu abunda yake,saidai idan iya nawa kawai aka zuba saboda kada naci” dubanta kawai mmn amir tayi
“Ina zuwa” mmn amir din tafada tana fita,babu jimawa yadawo da farantin da rufaidan tasoma cin abincin,yana nan yadda ta maida kitchen din,hatta da cokalin bata cire ba,takuma ajene saboda abinda kaje yazo,sai gashi kuma abinda take zaton din ya tabbata.
     Gabanshi ta aje farantin tabude masa,kowa yakalli abincin yasan ba sabon zubi bane,an dade da zubashi kuma akaci kadan aka barshi
“Bismillah” mmn amir tace masa,saiya dauki cokalin ciki yayi loma har uku,baiji komai ba face qamshin spice dai irin na miyar da yake ci yanzu kamar yadda mmn ummi tace masa.
       “Indai kinci wannan miyar irin ta gabana to babu abinda yaraba taste dinsu,babu wani qamshi a cikinta daya saba”
“Ai dama nasan haka zaka ce,to miyar yau qashi daya tsoka daya aka bani saikace wata mayya”
“Ban bada kudin nama ba,adalcinta ne yasa tasiya tasaka muku” sai kuma tayi shuru,mmn ummi tamiqe tana danne dariya,saidai bata yiba illa cewa
“Uhmmm” datayi
“Allah kyauta,Allah yabamu alkhairi” tafada tana ficewa daga dakin.
     Gwiwa a sanyaye ta miqe tana qananun maganganu tafita itama tafita,sam ba haka taso ba,dukka yadda takeso bata samu ba,amma ba zata taba haqura ba,don abinda idanunta suka gani tattare da abban amir da bbn amir din bata taba tsammani ko a mafarki zataga kusanci da qaunar juna tsakaninsu haka ba.

*YAN BIYAR*🤚🏽🔥🔥🔥🔥🔥
      
*_RUMBUN FASAHA SUNAN WANNAN TAFIYAR_*🤙🏽🤙🏽🤙🏽
*WANNAN KARON TAFIYAR TA BAMBANTA DA SAURA*

*KOWANNE LABARI YADAUKI SABON SALO*
*SABON SALON DA BABU KWATANKWACINSA*
*ZAKI GASGATA HAKAN IDAN AKAYI TAFIYAR DAKE*
*BILLYN ABDUL*
_SARAN BAYA_

*HAFSAT RANO*
_ABINDA KE CIKIN ZUCIYA_

*HUGUMA*
_SIRADIN RAYUWAR BILKISU_

*MAMUHGHEE*
_MIN QALB_

*MISS XOXO*
_KIBIYAR AJALI_

_dukkan ruguntsumin gamayyar wadan nan litattafan zaki samesu kan farashi na_700

5 👉🏾700
4 👉🏾500
3 👉🏾450
2 👉🏾400
1👉🏾300

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun na banki👇👇

ACCOUNT NO-
*0812652655*
ACCOUNT NAME- *HAFSAT LAWAN GAMBO*
BANK NAME: *ACCESS BANK*

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇

0903 234 5899

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU

09033181070

Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO

TEAM#ZAFAFABIYAR

👁️‍🗨️👁️‍🗨️ *HANGEN DALA*👁️‍🗨️👁️‍🗨️
       _Ba shiga birni ba_
©️®️ *Safiyya Abdullahi Musa Huguma*

Haske Writers asso 💡


*BABI NA SHA ASHIRIN*

        Kafin ta kwanta Sai data tabbatar ta sallami yaran bayan ta sanyasu sunyi addu’a kowa ya kwanta,sannan tadauki Abba tawuce zuwa dakin bbn amir.  Cikin Pampers ta shirya Abba ta sauya Masa Kaya masu nauyi sa’annan itama tashirya cikin Daya daga cikin kayan baccinta,tun Tana shiryawar tagama tafiya da bbn amir din,Allah ya Sanya a lokacin abban yayi bacci,saboda haka ba Bata lokaci Suka Lula zuwa duniyar ma’aurata.     Fadar yadda Daren ya wakana man Bata bakine,kewa ce ta hadu da gyara,Sai bbn amir din ya tsinci kansa cikin wata duniya ta daban,zai iyacewa bai taba tsintar kansa cikin wanna situation din ba.    Koda asuba da Suka tashi salla bayan ta hada musu ruwa Mai dumi sosai sunyi wanka,saiya rasa me zayace Mata,Tana zaune gefansa Tana lazumi “Allah na gode Maka,na gode Maka Allah da baka barni na wulaqanta wannan kyauta Mai daraja daka yimin ba,halima…..Allah yayi Miki albarka sau babu adadi” sassanyar murmushi tasaki,wani farinciki itama Yana ratsata,ba shakka farinciki Miji shine farincikin duk wata mace tagari “Amma banjin zan sake gangancin barinki ki dauki hutu Koda ‘yan hudu xaki Haifa,na fuskanci wani horo kamar Kika yimin a fakaice”idanunta tajuya kawai Tana dariya,kusan zata iyacewa ya canka.
+
     A lokacin zuciyarta na cike taf da qunci da kuma kishinsa,Bata da wata hanyar da zata baiwa jiki da zuciyarta hutu a sannan Banda ta sallama musu Shi,ta gama karantar next level da rayuwar gidan nasu ta fada a nutse kafin tasan hanyar da zata bi ta magance komai, beside ma Tana da buqatar hutun na haqiqa a halin da take ciki Don tasamu ta rabu da cikin dake jikinta lafiya,alhmdlh koma meye kwalliya ta biya kudin sabulu dari bisa dari.   Hirarrakine masu Dadi Suka biyo baya tsakanin ma’auratan,wadanda Suka qara musu wata qaunar juna dakuma fahimtar juna din.
       Bayan wani lokaci bbn amir din yakoma yasake kwanciya kafin lokacin fitarshi,bata bari takoma ba saboda tasan akwai shirin yara makaranta da sallamar maigidan da gidan kanshi,don haka gari na qara sha tafita ta kama ayyukanta bayan ta tabbatar da duka yaran sunyi sallah
    Bakwai da rabi na safe kusan komai ya kammala,don yaran duka sun shirya kowanne kuma da abincinsa na tafiya makaranta,yau dinma mai adaidaitanne zai kaisu,saboda haka ta sallamesu suka wuce ba tare data bari sun tada bbn nasu ba,sai data gama dasu sannan tadawo ya kama sauran abubuwan da suka rage matan.
      Takwas da rabi rufaida tashigo kitchen din inda take wanke wanke tana raba idanu,kusan tun sassafen takula da cewa idanunta biyu,da alamu kuma baqin kishi ya hanata sukuni ne,kallo daya tayi mata ta dauke kai,idanun rufaidan kawai sun isa shaida maka bata samu isashshen bacci ba,kamar zata saki dariya saidai idan tayi hakan tasan cewa kamar ta siyawa kanta raini ne,don haka saita dauke kai taci gaba da abinda take.
     Qerere take tambayatta abun kari,bawai don zataci ba,ta tanbaya ne don tace bata gama ba ko babu kodai wani abun makamancin hakan ta tada bala’i cikin gidan wanda zai tada bbn amir din ba tare daya shirya ba,saidai kafin abun takaicin da hannu ta mata nuni da inda natan yake ba tare data dubeta ba,sanda ta isa daki taga yadda ta shirya break fast din sai baqinciki ya kamata
“Wai ita komai sai tayi wanda yafi nawa,duk yadda nake haqilo da qoqari amma saitayi wani abun daya wuce hankali,yanzu don Allah yaushe ka tashi ka sallami yara ka gyara gida kayi wadan nan soye soyen,bayan kitchen din ma dukka kayan abincin nasu yayi low sosai,saboda wannan yanayin na batan kayansu bbn amir din” haka tazauna tana cizon yatsa.
       To kusan dukka kwanakin da mmn amir tayi na girkinta babu abunda ta tsinta sai bacin rai da baqinciki,don a yanzun sam mmn ummi ma bata gabanta,mmn amir din tafi tsaye mata a rai,babu ma kamar ranar da bbn amir din yatashi babu ko sisi a hannunsa yasa mmn amir din tabata kudin cefanen abincin gidan gaba daya,ranar ji tayi ina wuta ta sanyata.
STORY CONTINUES BELOW

      Da fari ya tsammaci dokin komawarta dakin miji ne bayan ta gama jego yasa mmn amir yin duk abinda takeyi din,ta tsammaci da an kwana biyu zata watsar da komai,saidai ga mamakinta saitaga babu abinda ta fasa kota janye,saita daura damara itama tasoma bin sahu,da mmn amir din ta ankara sai abun yadinga bata dariya,saidai ko daya bata damu ba,tasan cewa abun alfaharine a wajenta tazama kamar wata makaranta abar koyi wajen kishiyoyinta,saidai da yake abun a jini yake,tun ba’aje ko ina ba ta watsar saboda gajiya da tayi.
      Lokacin da tafiya tayi nisa sai taji ba zata iya jurewa ba,kamar dukan yana neman yi mata yawa ne,ga mari ga tsinka jaka,bbn amir din nasake shiga rashi ga kuma mmn amir din data fuskanci itako a jikinta albarkacin sana’a,kusanma ma lokutta da yawa itake bada kudin cefane babu gori wariya ko nuna damuwa,wanda mmn ummi ma tuni ta kama sana’a da taimakon mmn amir din data ranta mata kudi tana juyawa,hakan yasanya ta yanke shawara,yanzun babu wata hanya data rage mata ko wani zabi da take dashi banda takoma gidan mariya qawarta ta rakata gidan malamin da tace mata tasamu,duk da babu wani cikakken kudi da take samu a aljihun bbn amir din,don shima bawani kudi yake shigowa dashi ba,amma kuma ta fannin kayan abincin da takewa dauki dai dai tana tarawa qasan gadonta tasan zuwa yanzu ta tara da yawa,hakanan idan ta saida zasu hada mata kudaden da takeso

*_SHUKA A IDON MAKWARWA_*
     A hankali cikin sanda tashigo dakin nata sanye da hijabi wanda ta boyo taliya guda biyu aciki,tun jiya da aka kawo cartoon na taliyar qwaya daya da aka baiwa bbn amir din kyauta idanunta suke kai,don tanaso ta cike taliyar data dinga zara da ɗai da ɗai ta cika cartoon itama idan zata fita anjima kan ta shiga gidan mariya tatsaya a wani shagon tasiyar,tasan idan ta hada da shinkafar data tara wadda a qalla takusa kwano goma da semovita wajen jaka goma shima zata samu kudaden da zasu isa a soma mata aiki kan bbn amir din da sauran matan gidan duka harda yaran ma idan ta kama.
1
        Tun sassafe tatashi da niyyar xata sallami ‘yan makaranta ne,anu ya baiwa shi kansa bbn amir din mamaki don yasan yadda ake daga da ita kafin ta shirya yaran amma yau gashi da kanta tayi tashin sammakon,bai tanka ba dai yakoma ya kwanta,tsam ta tsaya tana dunan bbn amir dake bacci gefan gadon nata,tana son ta tabbatar baccin yake ko idonsa biyu.
      Sai data tabbatar bacci yake sannan ta lallaba don kada ta tadashi,ta duqa qasan gadon ta jawo jakar datake tara kayan a hankali,ta zauna sosai qasan gadon tasoma irga yawan taliyar,sai data tabbar guda ashirin da biyu ce ashirin da hudu harda wadda zata saka sannan tasaki murmushi,taciro ta cikin hijabinta ta saka kana ta nannade bakin ledar zata tura ta mayar.
        Ga mamakinta sai ganin mutum tayi yatashi yazauna gefan gadon,wani irin xabura tayi sannan cikin rudani tasoma qoqarin maida ledar ta qarfin tsiya.
      Idanu kawai yazuba mata yana kallon yadda ta hautsine,tabbas yajima yana lura da yadda ake masa dauki dai dai a binci,kuma ba komai yajawo hakan ba da har yayi saurin fahimta face yanzu bashi dashi,kusan abincin kai da kai ake siyowa idan an samu ma,wani lokacinma sai sun irga zaikai musu kwana kaza kafin yaqare,amma abun mamaki sai a rasa na kwana daya,wanda inda sanda yake da wadata ne yake ajewa da yawa ba lallai ya fahimta ba,bai taba zargin kowa ba cikin matansa saidai kuma abun yana bashi mamaki.
      Hannu yamiqa yace “miqomin na tayaki irgawa” saita hau kame kame
“Menene?,me zaka irga?” Hannu kawai ya saka ya janyo ledar duk da yadda take qoqarin hanashi,ya zazzage dukka taliyar yana qare musu kallo,ba shakka kayan abincinsa ne,hakanan yaji bai gama aminta ba,saiya miqa hannunsa qasan gadon,sai gashi ya jawo ledar taliya da semo,semovitan da aka dinga nema harda buhunsa da yace su adana saboda idan an tashi siyan shinkafa azuba a ciki tunda buhun mai qwarine.
1
      Idanu ya daga yana dubanta,fuskarsa da zuciyarsa cike fal da mamakinta
“Rufaida?” Yadda yakiratan ya tabbatar mata akwai qura,kuma matuqar ta yadda ta amsa laifinta kota nuna karaya ko nadama to zata kunyata ce a banza a wajensa,donta lura qurar babu ce take bugunsa,zai iya sauketa akanta,gwara ta tsaya da qafafunta daga baya idan suka haura sa sauko,don haka sai tayi kicin kicin ta hade rantsa tsaf kanta tsaye kuma ta amsa kiran sunanta da yayin itama take duban tsakiyar idanunsa.
STORY CONTINUES BELOW

     Cikin sanyin murya dake nuna mamaki yace
“Rufaida diban kayan abincin mijinki?,kinsan ma’anar hakan?,sata fa kenan?” Ya fada cikin yanayin mamaki yana ci gaba da dubanta,zuciyarta ke gaya mata maza zuma ne sai an cisu da wuta,kuma tabbas idan tayi masa lako lako ita zata sha wuya,tabarmar kunya kuma da hauka ake nadeta,bugu da qari bataga illa ko aibu na abunda ta aikata ba,tunda tunsanda ta aureshi meta samu?,meta tsinta?,ba gwara rayuwarsu a waje ba sau dubun dubata,hannu ta daga masa cikin tsiwa dason nade tabarmar kunya
“Karka sake ambatarmin lafazin sata,don ni ba barauniya bace,don na diba kayan abinci naga na mijina ne ai,haka kawai kai baka iya morawa mutum komai ba,kullum gwara jiya da yau,sannan kuma ace mutum bazai yi wadda zata fishsheshi ba?,to wallahi niba barauniya bace,karkasa sake cewa nayi sata ehe” ta qarasa fada tana juya mishi qeya,sosai abun ya daure mishi kai,yasoma gajiya da rashin mutuncin rufaida,rabonshi da wani mu’amalar arziqi ta hadasu tun a waje lokacin da ake honey da darling,bata iya magana ba sam haka take,baga shi ba,baga matansa ba baga ‘yan uwanshi ba,har yau qannenshi basu shiga dakinta idan sunzo saboda ta yanko magana ta gaya mutun wannan ba damuwarta bane,yana sane da yadda take qananun maganganu kan halin babun daya shiga tundaga babbar sallar da basu samu layya ba har yau mita da gori take masa kamar shi ya dorawa kanshi,koda yake kuka da mmn ummi gwara ita sau dubu akan rufaidan,don ita takan qyara wani lokaci kodan mmn amir,amma banda rufaida,sannan koda bata so a kaso goma idan tayi masa halinnata zata bashi haquri koda kaso uku ne amma sam wannan banda rufaida,qoqarinsa har kullum a banza yake,kullum gajiyayyene shi a wajenta.
       “Ni wallahi nasoma gajiya,na gaji da wannan rayuwar,aure babu wani ci gaba?,haba da Allah,idan banda tsiya da talauci ma meye donka debi abincin gidan mijinka?”
“Ni kike kirawa tsiya da talauci rufaida a gaban idona?,nine matsiyacin?” Yafurta cikin mamaki
“Eh aiba qarya nayi ba,gidan nan kowa yasani mun fada cikin tsiya wallahi” kai ya jinjina ranshi yana wani irin baci,kowa yasani sautari wasu magidantan kan shiga depression idan suka shiga halin rashi ko babu,sukan muzanta su dinga tsargar kansu musamman mutumin daya sana hidimawa iyali yau a tashi bashi da abun basu saidai su su bashi
“Tsiyarma da takai ace matarka ce take cida kai,kishiyarki itake miki cefane?,haba wallahi munci baya” tsawa ya daka mata cikin zafin rai
“Ki iya bakinki” saita tafa hannu
“Wai meye na fada qarya ne a ciki jibril,nida aka cuta fa niya kamata na tuzura haka” ya fuskanci so take ta sanyashi ya aikata wani abun da zai sanyashi dana sani,saiya dauki hularsa ransa na suya
“Ki wuce gidanku,saina nemeki”
“Tafi nono fari,solobiyo karan mata” ta fada da qarfi har zuwa tsakar gida ana jinta,tana tafa hannu da kama qugu.
     Wani bacin rai yadinga bijiro mata,tadinga tuna wace ita,kamar ita rufaida da tayi tashen samari kala daban daban,kaf unguwarsu zuwa makarantarsu babu wanda baisanta ba,babu yarinya kamarta,bata mantawa a wata takan dinka sutura kala daban daban,sai wadda ta zaba,don duk saurayin datace mishi ga abinda takeso bai tsallake zancanta zai kawo mata,wani farinjini tazuba wanda har tayi aure ba’ayi kamarta ba,ta kafa tarihi,don rufaida indai matsala ta kudice bata da ita,vare katin waya da kana iya samun sama da dubu biyar credit na wayarta,abincin gidansu sai randa taso takeci,kayan qyale qyale da kwalliya a wajenta ‘yammatan unguwarsu suke aro,amma yau ace ita jibril yayiwa haka?,tafi qarfin wulaqanci namiji,kuma don tayi aure ba’ace tazauna adinga mata komai tana jan baki tana shuru kamar batasan ‘yancinta ko ciwon kanta ba.
       Sam su mmn amir basusan me yake faruwa ba,sunyi tsammanin kawai unguwa taje,saida aka kwana washegari taji suna waya da innarsa
“Duk da abinda tayimin inna bani nace tatafi ba,saboda nasani cewa da zarar nace taje gidan duk gaskiyata za’a ga don ina cikin babune yasa na aikata hakan” sai yayi shuru yana sauraren abinda innar take fada sannan yasake cewa
“Kiyi haquri inna,bazan iya binta ko zuwa bikonta ba,kuma su dinma babu wanda yacemin wani abu” daga qarshe yace
“To shikenan inna saina shigo”.
       Tun basu da niyyar yi masa magana har sai da suka masa kan rufaidan ganin lokaci na turawa amma yaqi batunta,ita mmn ummi ma cewa tayi uffan bazata ce ba,mmn amir ce tace
“ba wani abu bane mmn ummi,kodon ‘yan uwantaka ta musulunci aima tuntubeshi muji,ko meye rufaida tayi mana zamufi fatan gyaruwarta akan rabuwarsu”.
STORY CONTINUES BELOW

      Sanda suka masa maganar kuwa dukka saida ransu yabaci,don hakanan yaji yasamu wani inner peace tawani bangaren,damuwarsu ta ragu,babu wadda ke tada masa hankalin cikinsu don bai bata wani abuba sabida dukkaninsu suna sana’arsu,babu mai yada masa habaici saboda anci fara damai,babu mai uzzura masa saboda abinci babu nama,babu me daura masa lalurar da suka san bashi da ita,kowacce tayi haquri da yanayin da ake ciki,saima qoqarin sawwaqa masa da taimaka masa da sukeyi da sana’arsu
“idan kune kuka auromin ita tun farko saiku dawomin da ita,bani nace tatafi ba don haka billahil azim bazan taka qafata gidansu ba”.
       Ta fannin rufaida kuwa daga yayunta har kakarta suna sane suka mata dif sukaqi cewa komai kan batun dawowarta gida,hakanan sukaqi neman bbn amir din a wannan karon,tunda sun fahimci rufaidan halin tsiya ne kawai yake damunta,kuma iya bakin qoqarinsu sunyi kan ta zauna amma taqi,don haka suka dauke mata wuta suka fita batunta kamar basusan da zamanta a cikin gidan ba.
       Da fari itama rufaidan bata damu ba,a nata ganin yadda jibril yake sonta bazai iya barinta ba,bata san cewa halayenta sun wanketa tas daga cikin zuciyarta ba ta sire masa,daga baya ta fahimci akwai lauje cikin nadi,yadda tunda tazo baibi ta tata ba,hakanan agidan babu wani me ce mata komai,sannu sannu sai hankalinta yasoma tashi,saidai tana jin girman kan ta nemi jibril din,idan tayi haka kamar tafado ne ta zubda ajinta,don haka tadinga neman hanyoyin da zata karkato da jibril amma a banza,daga qarshe ta yanke zuwa gidan mariya,ta samu wasu daga cikin kayanta masu kyau ta saida ta hada kudin tayiwa gidan mariya dirar mikiya da wata safiya.
      Yanayin data iske mariyan ya bata mamaki qwarai,ta sameta ta kode ta lalace kamar ba ita ba,har tafi baya kyan gani,abun yadaure mata kai,saida suka zauna sosai take cewa da ita
“Matarnan kusan asarar kudina kawai ta sakani yi rufaida,na saida gwalagwalan da maigidan yasissiya mana nida ita,na dauki kadarorine da yawa na saida,har kayan lefena rufaida na taba,amma wallahi matar nan daga ita har yaran ko mummunan zazzabi babu wanda yatabayi,dukka malaman da nake zuwa wajensu cemin suke da gagga gaggan aljanu take aiki shi yasa muka kasa shan kan lamarin,amma naqaro kudi sai a gayyato manyan abokan aiki aljanu,ayimusu yanka suyi aikin,mutum daya tak ne yacemin tana da tashin dare,duk randa yake ba kwananta bane takan raba darenta ne tana sallah,hakanan ni shaida ce kan azumin litinin da alhamis dinta,kuma ni shaida ce kan yawaita jin karatun qur’ani da take”
“Rufaida na saida dukkan wata kadarata dana mallaka,yanzu bani da komai,dan abinda nasamu lokacin amarci sanda ludayina yana kan dawo duka sun salwanta,yanzu haka tafini da komai,shekaran jiya da doller tayi tsada ina gani tabaiwa abbansu yasaida mata gwalgwalanta tasamu ribar dubu daruruwa,daya nemi nawa nima yasaida min sai qarya na masa nakai gida ajiya amma zan amso nabashi….rufaida….gaskiya dukkan wata hanya da zanbi na lura babu riba tattare da ita,kawai na yanke shawarar zan jarraba sanya idanu naga yadda take mu’amalantarsa harta janyeshi haka,nima na gwada ingani ko za’a dace,don na fuskanci HANGEN DALA kawai na dinga yi daga wajen birni,tunda gashi har wankin hula yana neman kaini dare”.
       Haushine yacika rufaida,takalli mariya
“Karki bani kunya mana,kishiya zaki sallamawa kanki mariya?,kin manta mudin su waye da alwashin da mukasha sa’adda duk muka samu damar shiga kowacce mata?”
“Rufaida,gudun da babu tsira kwanciya tafishi,kuma idan an jarraba hagun taqi ai sai a koma dama,bawai ayita abu kullum jiya iyau ba,saika gwada wani hannun wataqila a dace”.
       Sam rufaida bata yarda da maganganun mariya ba,don itakam tariga ta sanya niyya,don haka ta kafe kai da fata kan babu gudu babu ja da baya,a haka dai sukayi sallama,daga nan cikin qawayenta ta lalubi gidan wata wai ita nusaiba,nusaiban batayi qasa a gwiwa ba ta hada rufaidan da irin malaman da takeso.
      Saidai duk yadda take narka kudadenta a banza wak an mintsini kakkausa,kome kama da bbn amir bata gani ba bareshi,harta kammala idda shuru maqatau wai malam yaci shirwa.
1
STORY CONTINUES BELOW

      Ta fanninsa shima babu abinda yaji,abinda kawai yadan sauya ma shine yawan fada da suka fuskanci yakoya,ita da mmn ummi suna zaune a wani yammaci suke tattaunawa,sai suka masa uzuri suka dora hakan kan lalurar halin babu dayashiga,don haka suka sake takatsantsan,da kuma sanyashi a addu’arsu ta kullum Allah yaye masa dukkan abinda ke damunsa,cikin qanqanin lokaci sai gashi yadaina.

***************
      Cikin watanta na biyar da komawa gida saiga qawarta tun ta ‘yammatanci ta kawo mata ziyara,suna zaune su biyun tadubi rufaida
“Ke kinga yadda kika koma?,wallahi ni kina bani mamaki rufaida,waishin me jibril yamiki ne,anya haka yabarki kuwa?,mu gamu da bamuyi auren ba fes damu munata cin duniyarmu da tsinke babu wani baqincikin da namiji dake damunmu,ta yaya zaki zauna da kyanki da quruciyarki da komai namiji yasaki a gaba da tarin bacin rai,maimakon ki miqe ki xama bazawarar zamani kishiga a dama dake,kusan kullum sai isma’il yayimin maganarki,yayi kudi yazama babban yaro,da alama har yau yana muradinki,banda haka bazai dinga tambayarki ba,ke kinga motar da yake hawa kuwa?,ke ba isma’il kawai ba,wallahi Allah duk tsaffin samarinki babu wanda bama haduwa dashi ba tare daya tambayeki ba yace kin gujeshi,to wallahi shawara daya zan baki,idan zaki yage jibril daga zuciyarki ki yageshi ,ki tashi kibi sahu,don babu wanda zai dubeki idan kika gyagije yace kin taba aure,Allah ya doka miki bargon suttura ma baki haihu dashiba bare a dameki”.
       Kwana tayi tana tunanin maganganun qawartata,mafi rinjaye na zuciyarta ya karkata kan tabi shawarar qawartata,don haka cikin qanqanin lokaci tasoma buga zawarci,nan da nan saiga tsaffi da sabbin samarinta sun soma dawo mata,cikin lokaci qarami kudi yasoma shigo mata,saita soma ganin baiken auren da tayi da jibril,ta dinga jin kamar wani kurkuru taje tadawo,nan tasoma dinka sabbin suturu duk da bata rasa ba,don ba qaramin lefe tasamu daga jibril din ba,tuni ta mance da igiyar dake kanta,ta manta da jibril gaba daya,abu daya take kiyayewa bata kawo kowa gaban gidansu,saboda tasan akwai qura.
      Ta fannin jibril kuwa inna data gaji da shurun shi game da rufaida tayi kiranshi,fada ta masa kan lallai lallai yaje yadawo da matarshi,koma meye aime wucewa ne,hakanan babu wanda baya kuskure,kuma ko meye tayi masa ai zamanta a gida zuwa yanzu ta gane kuskurenta.
       Shi kansa a yanzun zafin da yake ji game da rufaidan yaragu sosai,don haka baiyi mata gaddama ba ya amsa,kwana biyu tsakani suka shirya shida kawunnan shi da abokinsa suka isa gidansu rufaida.
     Kusan kowa yayi murna da zuwan nasu,suka kuma bashi haquri gamida nuna mishi nauyinsa ne yasa suka kasa nemanshi.
        Sanda aka kira rufaida sai labari yasha banban,sun zaci zatafi kowa murna amma saita qeqasa qasa tace ita sam ba zata koma ba,sosai hankalinta yatashi ma don bata zaci ma zai waiwayeta ba,sai gashi ba zato ba tsammani ya bata mata plan.
       Tana komawa tadauki waya ta nemi qawarta ta zayyana mata komai,cikin bala’i da masifa tace
“Tabdijan,wallahi kada ki soma yarda,ashe jibril dan baqinciki ne ban sani ba?,dan rainin wayo da hankali,sai yanzu da yaga kin soma wuce ajinsa zai wani lallabo yace zai maidaki,wato salon ya jaza miki asara kina ji kina gani,bayan isma’il da murtala duka sun miki alqawarin aure,kuma babu wanda bai ketawa jibril na,me zaki kuma kiyi a gidansa,me zakici dashi?”
“Aikima daina bata bakinki qawata,ni mahaukaciyar inace wai?,ai wallahi ko maza sun qare,ana aure don riba washin me na tsinta a gidan jibrin,banda bacin rai da qunci,da fifita tsofin matansa akaina?,nifa bansan juya miji ba,tun ina waje kafin nayi aure,bansan isa da mulki na mace ba cikin gidan,tsinanniyar uwargidansa ta tare komai,kai matarnan Allah ya zuba mata abu,wallahi qawata a waje kafin muyi aure idan akace min zanyi wata biyu ban fiddata daga cikin gidan nan ba zan qaryata,amma sai naga abun ashe ba haka bane,to koma meye suje su qarata dagasu har jibril din,amma haihata nida aurensa,gwara naje inda koda zanyi qunci zanyi cikin ac a gaban kwanon kaji” dariya tasanya itama tana tayata sannan tace
“Ai kawai ki shirya ki rakani naje har gidan tsohuwarsa nakai mata kashen ɗanta,taja masa kunne,babu ni babu shi ato”
“Kinyi tunani mai kyau kuwa,babu damuwa jibi sai muje” da wannan shawarar sukayi sallama.
STORY CONTINUES BELOW

       Cikin wata matsiyaciyar fitted gowan take baqa wadda tabi jikinsa,ta rataya jan mayafinta akafada,sai takalmi mai tsinin dunduniya data sanya,bayan tafkeken glass data sanya,bakinta dauke da chewing gum tana tauna qas qas,ta fannin qawarta itama kusan kalar shigar datayi kenan,a haka suka kutsa kai zuwa gidansu jibril.
      Innarce ita kadai zaune a tsakar gida tana baza barkono data shanya tanason yabushe zata dakawa jidda yajin haihuwa,jin sallamarsu yasa ya daga kai tana amsa musu,fuskarta a sake saidai akwai mamaki kwance qasan fuskarta na yanayin shigar rufaida.
    Miqewa tayi tana musu iso zuwa cikin falonta,rufaida ta dakatar da ita
“Kinga inna,ba shiga zamuyi ba,don ba zama ne ya kawomu ba”
“Auto,aiga tabarma” ta fada tana janyo tabarma ta shinfida musu,suna dai tsaye don kusan ita kadai tazauna saman tabarmar tata
“Inna” takira sunanta,a mamakance ta amsa tana dubanta
“Kashen jibril danki na kawo miki,kija masa kunne ki gaya masa cewa nidin yanzu ba sa’arsa bace,kuma ruwa ba sa’an kwando bane,bana aurensa a yanzu bana ra’ayi,karya sake tako qafarsa yazo gidanmu da niyyar neman wani banzan sulhunsa,niba sulhu nakeso ba”
“Haba ‘yar nan haba rufaida,sulhu aiduk inda yake alkhairi ne,hakanan da mutuwar auren da rashinsa ai zaman yafi alheri”
“A’ah walllahi…” Ta dakatar da ita
“Ba irin wannan auren dan naki ba da babu ci gaba saici baya,kullum jiya iyau,ban taba jin dadinsa ba,don yadda yadaukoni a waje ba haka yaci gaba da yimin ba,to wallahi inna bari kiji,dana koma gidan jibril gwara akai gawata wallahi na gwammace na mutu” baki innar takama mamaki ya gama kasheta
“Ba za’a kai gawarki ba,abun ai baiyi zafi haka ba”
“To idan baiyi zafi ba ki gaya masa tun muna shaida juna ya rubuta takardata yabani don babu abinda zanyi dashi”.
      Kasa daure maganganun da yakeji suna fita daga bakin rufaidan yayi,saboda haka yafado gidan kanshi tsaye,kallon kallo aka soma yi,cikin fushi da bacin rai yasoma cewa
“Nima babu abinda zanyi dake,matuqar zaki iya bude baki ki gayawa mahaifiyata wadan nan kalaman,koda kece autar mata na haqura dake har abada,na…..” Tsawar da inna ta daka mishi ita ta dakatar dashi
“Banson shirme ko sakarci,banason ka sake cewa komai jibril,wuce kawai” kamar zai shaqeta haka yabita da kallo,yayin da itama shi take kalla din cikin harara kamar idanunta zai fado tana jan hannun qawarta kana ta saki tsaki
“Idan baka qarasa fadin abinda zaka fada din ba baka haifu cikin uwarka ba” tana kaiwa nan ta sanya kai tafice,ba jibril ba hatta ina furucin ya tabata,dukka shuru sukayi bayan fitar tata kowa najin abun cikin jikinsa
“Inna,don girman Allah kibarni….” Kai ta girgiza
“Ban yarda ba jibril,bada amincewata ba” kawai saiya sanya kai yafice daga gidan don bazai iya ci gaba da zama ba,maganar ma dayazo gaya mata na an soma gano inda jirgin kayansu ya nufa duka bacin ran daya tarar ya hadiyeta gaba daya.
       Kwana uku abun yana ci masa rai,ta yaya zaici gaba da zama da auren mace irin rufaida a kanshi,a kwana na hudu ya yanke shawara ya rubuta mata takardar sarki biyu ya ninke,da kansa yaje gidansu yasamu waliyyanta ya danqa musu,kowa yaji mutuwar aurensu amma banda rufaidan da bayan ta amshi takardar takoma daki rawa tashiga yi,kana takira dukkan wanda take tunani zai tayata murna ta gaya mishi,daga qarshe takirayi samarinta da suka mata alqawarin aure ta shaida musu
“Mun zama free yanzu,don haka abinda yarage min idda kawai,iddar ma aina gama yinta tuni,sai kawai kasoma shirya mana yadda aurenmu zai kasance”
“Da wuri haka?,karki damu babe” amsar da kusan suka bata kenan.

      Ko kadan mmn amir bataji dadin sakin da jibrin yayiwa rufaida ba,saima tausayin rufaidan daya kamata sanda inna ke basu labarin abinda tazo har gida tayi musu,tasan ba shakka zallar quruciya ke dawainiya da ita,da kuma rashin cikakken hankali,tasan kuma tunda ta aikata haka jibril bai zama da ita,saboda girma da darajar innarsa tana saman komai da yake dashi a duniya,sai tayi addu’a Allah ya zaba musu abinda yafi alkhairi,mmn ummi kuwa cewa tayi
“Wai meye abun damuwa?,abinda ta shuka nefa ta girba,mu taso fiddawa Allah yaduba zukatanmu yaga bamu da haqqinta,ai indai a duniya ba zaka zama mai kwaikwayon aikin alkhairi ba saboda girman kai ko kana ganin kafi kowa to kana tare da wahala dakuma halaka”
“Gaskiyane” cewar inna,a fakaice tadinga yaba musu da qoqarin zama da yaronta da sukeyi duk da yanayin rayuwar da yake ciki hakan baisa sun juya masa baya ba kamar yadda rufaida tayi ba.
STORY CONTINUES BELOW

******************
*_MAHAƘURCI MAWADACI_*
      Cikin taimakon Allah da addu’ar iyaye da kuma dafawa da addu’ar nagartattun mata Allah ya qaddara jirginsu jibril ya bayyana,kuma aka samu dukkan kayansu,harda qarin wasu kudade masu kauri naban haquri daga kamfanin jirgin na akasin da aka samu.
       Cikin qanqanin lokaci rayuwarsu ta daidaita harma taso ta zarta na baya,don dama haka hukuncin Allah yake,a duk lokacin daya jarabci bawa yayi haquri da jarrabawar,to wala’alla yayi hakanne donya daukaka darajarsa yakuma maida masa mafiyin abinda ya amsa daga wajensa cikin kyautayi da karamcinsa,bai manta alkhairinsu ba,ya dunqule kudi da kansa ya baiwa kowa ta qara fadada sana’a da jarinta,don yaga amfanin sakarwa mace tayi sana’a qwarai da gaske.
      Tare suka zauna suka tattauna abinda zasuyi dinga yi,inda daga qarshe suka yanke su dinga saida atamfofi da laces pieces masu kyau,sai takalma masu sauqin kudi daga 2k zuwa qasa,wanda yayan mmn amir da yake zuwa lagos suka tattara kudin suka baiwa,yasoma saro musu masu kyau da sauqin kudi.
      Allah kuwa ya dafa musu,yasanyawa kasuwar tasu albarka,nan da nan sai gashi sun soma ganin sauyi,duk da haka mmn amir bata saki sana’ar saida ruwa da lemo ba,saita barwa yaranta mata suke hada lemon su gyara firjin su jera su kuma saida su adana kudin,aware riba su saka a asusu nasu ne,uwar kudin kuma a sake siyan kayan hadi,tayi hakanne don suma ta horesu da sana’a da neman na kansu,kuma alhmdlh tana ganin alfanun haka.
       Zuwa wani lokaci bbn amir ya rushe fiye da rabin gidan yamasa gyara na musamman aka maida musu ginin xamani,rayuwarsu taci gaba da juya musu cikin farinciki saboda kowanne ya fidda hassada qyashi da mugun kishi daga ranshi,kowa yana kiyaye abinda dan uwansa bayaso,sannan duk abinda yasan zai cutar dashi a karan kanshi bai yarda yayiwa abokin zamansa.
*************

     Mmn amirce tayi sallama a falon mmn ummi,mmn ummi dake kwance tamiqe tana amsawa tana yamutsa fuska da alamu bata da lafiya ne,sai da mmn amir ta aje kwanon gabanta sannan ta tsaya tana dubanta
“Dole kici wani abufa,ga alalan nan dan kadan nayi miki ma yadda zaifi dadi,amma karki soma cemin yafita daga kanki irin na dazu,in kuwa baki cinye ba agabansu mubarak xamusa bbn amir yamiki dura,yadda kike musu fadan basuci abinci idan basu da lpy kema suga haka kike,kinga bakya qara ba ko?”.
“Mmn yara,wallahi ji nake kamar yanzu na fara haihuwa,wannan cikin walahar dani kawai yake,haryau na kasa naji dadin jikina?”
“To ai dama kowanne da irin yanayinsa,aikin lada mukeyi,fatanmu Allah yabamu da sauqi yasa mu gama lafiya” tafada tana cire mata murfin kwanon,sosai alalan yayi mata don haka tasoma ci,ganin hakan yasa mmn amir tace bari taje ta qarasa girkin rana na yara suna gab da dawowa daga makaranta
“Mmn yara” mmn ummi takirata,saita amsa tana juyowa,cikin sanyin jiki da murya tace
“Don Allah ina neman afuwarki ki yafemin duk abinda na taba yi miki tun daga shigowata gidan nan zuwa yanzu,idan nazauna nayi bitar halayenki da zamanmu na yanzu duk sai naji kunya ta kamani da dana sani,ki yafemin don Allah don nasan na cutar dake a baya koda baki fada ba,nayiwa kalmar kishiya mummunan zato,na zaci saikin shigo da wuta da bala’i dakuma tsiwa sannan kike samun duk abinda kikeso,ki yafemin” murmushi tayi kana tadawo hannun kujera tazauna
“Ni a wajena tuntuni wannan yariga daya wuce mmn ummi,nasan cewa sharrin zuciyane dakuma rashin sanin dawar garin,dukkaninmu kuna kuskure daga amare har uwayen gida,yawanci ku amare kukan daukarma kanku wani abune,duk da cewa wata takan fara samun dama ne tun daga waje daga wajen wanda zata aura din,wala’alla shiya soma nuna mata matarsa ba wata abace bace,matarsa ta gaza dashi kodai wani abu makamancin hakan,wata kuma duka babu daya,abu daya take da tunani shine wannan mijin,burinta kawai ya watsar da matarsa da yaransa ya rungumeta,ta manta cewa itamafa wannan matar tasa macace kamar yadda take mace,itama tana da buri a zuciyarta,uwace tana da yaran da bazataso wani abu ya rabesu ba koya rabeta,tanason mijinta wala’alla fiye dake,saboda bakisan iya abinda ta hadiye tsahon xamansu ba,bakisan wacce wahala sukaci tare ba kafin sukai wannan matakin da kikazo kika samesu akai ba,kin manta cewa ya sameta ne kafin ke,ya sameta a sanda take zabi guda daya cikin rayuwarsa,tazauna dashi ta raineshi a duniyar rayuwar aure,tunda a sannan shidin cikin rayuwar auratayya tamkar jaririne sabon haihuwa cikin duniya,tafiki saninshi ciki dabai,maimakon kishigo da kyakkyawar niyya,saikiga Allah ya taimakeki ya miki maganinta koda tana da wani mummunan nufi a kank,amaimakon ta kwantar dakai tasan waye mijin ta hanyar kishiyar,tanutsu ta gane yaya gidan yake?,wacce rayuwa sukeyi,a’ah,duka saiki bata rawarki da tsalle,kice ke kin shigo da iyawarki ne,ki dauki labaran da wasu ke baki karance karance da kallace kallace kice dasu zaki hada kizauna da mijinki,bayan duka rayuwar wannan ta zahiri ce,tasha banban da duk yadda zaki hasaso koki tsarawa kanki,ki dinga takaici idan mijinki yana girmama uwargidansa,maimakon hakan yazame miki abun alfahari saboda kinsan cewa yacika nagartacce,kema aduk yayin da kika samu kanki a muhallinta zai mutuntaki ya darajtaki,sannan zaman lafiyarku cikin gidanku yafi komai kwanciyar hankali da riba a gareku gaba daya”
STORY CONTINUES BELOW

“Mu kuma iyayen gida namu kuskuren muma daban,kamar yadda kika dinga tafka kuskure alokacin kika baiwa rufaida dama ta rainaki tun bata shigo ba,sa’annan kika dinga qoqarin lallai saikin tilasta mijinki yafasa aure,bayan kin manta bayanke yana da damar sake qara wasu biyun ras,kina yunqurin ki haramta halas,ki soke fadin Allah,kiyi fito nafito da ayarsa,hasashenki na gaba kuma ki cutar da amaryar idan tashigo,kiyi amfani da jimawarki cikin rayuwar aure da rayuwar gidanki ki xalunceta,kisa miji ya qasqantata,ki dora mata dukkan laifi,ki hanata sakat,wasu daga cikinmu su bibiyi malamai su raba auren kamar yadda ake samun wasu amaren dake bibiyar malaman suma su raba uwargidan da mijinta da yaranta dakuma gidanta ma baki daya,gaba daya mata mun zama maqiyan junanmu,muke yaqar junanmu da haifarwa junanmu matsala,kullum damuwar itace,kishiya ta hanani zaman lafiya,uwar miji ta hanani xaman lafiya,qannen miji sun hanani zaman lafiya,faccala tasani a gaba,matan waje yake nema dukka dai matsalar  MATA ne matsalar yan uwansu mata,mafitar daya ce,kowa ya tsarkake niyyarsa,kowa yadora rayuwarsa bisa mizanin abinda Allah yace yakuma umarcemu,karka cuci wani kamar yadda bakason a cuceka,sai kowa yazauna lafiya,mu fita daga matsala,kakata ta taba bani labari,a baya idan aka qara miki kishiya kunyarki takeji,kunyar hada idanu take dake,saboda tana ganin ta aure miki miji,yayin da ke kuma a naki fannin uwargida kike riqeta hannu bibbiyu,kikemata kallon qanwarki,yadda zaki mu’amalanci qanwarki bazakiso ta cutu ba haka kike mata itama,to ayanzunfa?,haka muke?auren mai mata ba matsala ko kuma laifi bane,amma dole kisan cewa zaki ga banbance banbance,wataqila ma ki hadu da wasu ‘yan qalubale,hakanan dare daya bazaiyiwu kice zaki zama ita ba,kamar yadda itama ba zata taba komawa ke ba,kamar dan makaranta ne,a ranar daka shiga bazai taba yiwuwa kace so kake ka kamo dan aji shida kana aji daya ba,ko so kake kayi suna farinjini irin na dan aji shidan nan ba,komai na rayuwa mataki mataki ne,haquri kuma shine matakin dukkan nasara”cikin gamsuwa mmn ummi take kada kai
“Ba shakka muna kuskure kam,ko yaushe mune matsalar junanmu” mmn amir ta gyada kai
“Qwarai kuwa,duk da suma mazan suna da tasu mihimmiyar rawar da suke takawa,saidai mu namu mijin alhmdlh,yana bakin qoqarinsa tunda can bare a yanzu” hararar wasa mmn ummi ta jefa mata
“Eh mana,kyace haka mana,kullum dama ai bai laifi a wajenki” dariya tasanya tana miqewa
“To dama ta yaya,kema bai laifin ai wajenki” suna dariya dukka mmn amir tafice,mmn ummi tasaki ajiyar zuciya,tana godewa Allah daya ganar da ita da gaggawa,da ayanzun yadda mmn amir ke hidima da ita da taji kunya.
*_RUFAIDA FA?_*
       Tun daga lokacin data amsa takardarta sai tayi tsammanin zata sake bude sabon babin rayuwa ne,tayi aure da mutumin da bazai daina nuna mata qauna da tattali ba kwatankwacin yadda take samu a yanzu ba.
      Saidai kuma abu na farko daya soma bata mamaki shine yadda suke mata kauce kauce a duk sanda tayi maganar aure,kowanne saiya soma yi mata yawo da hankali,daga qarshe ma manufofinsu suka fito,kowanne so yake kawai suyi rayuwa a waje,data nuna qin amincewarta basu takura mata ba,saidai sun soma janye duk wani kudi da suke kashe mata da tallafi da suke bata,sa’annan sukaci gaba dayi mata goce goce kan turowarsu gidansu ayi maganar aure,sannu sannu sai suka soma guduwa daya bayan daya,da taga haka itama saita watsar dasu ta kama wasu,su dinma duk kanwar jace,abinda yakawo wadancan shiya kawosu,hakanan abinda yakori wadancan shi yakoresu suma,tun abun baya damunta harya soma damunta,tafi tafi sai maneman suka fara ja baya,saitayi kwana da kwanaki bataga walqin kowa ba,hakanan ba’a nemeta ba.
      Jikinta yafara sanyi sanda tasoma shiga zawarci dan gaske,don kowa ya zuba mata idanune,hatta da kakarta wannan karon tayi watsin tsiya da lamuranta,mmnta ma da take dan samun goyon baya daga wajenta yau dadine gobe akasinsa,don babu dana ta tambaya koda klien na wanki bare kudin kashewa zata hau fadan tagaji da hidima da ita,ta fidda miji tayi aure,to ina taga mijin ma bare ta tsaidashi?.
      Jikinta bai sake sanyi qalau ba sai ranar da taje asibiti batajin dadi zataga likita,mata babu wahalar sabo a tsakaninsu,kafin zuwan likita wajen zaman jira hira ta barke,ashe matan aurene da zawarawa,sai taji rabin hirar kamar da ita akeyi,maganar wata mata ta qarshe ita taja hankalinta
“Shi zaluncin aure tun a duniya Allah yake sakayyarsa,duk wanda ya cuci wani walau mata ko miji,indai kikace bazaki haquri ba auren zamani saidai kiyita fita ana irga miki aure,kowa haquri yakeyi,indai an sauke miki haqqoqin da duk Allah ya shardanta musu to duk abinda zai biyo baya mai sauqi ne,saidai idan an take dokar Allah ne ko akwai cutarwa mabayyaniya”.
1
STORY CONTINUES BELOW

    Duniyar tunani tafada maizurfi,tana nazarin iya zamansu da jibril,basu taba kwana sun tashi babu abinda zasuci ba,bai taba hanasu sutura sanyawa ba,hatta da ruwansha basu shan na fanfo saidai idan yaqare ne kafin yadawo daga kasuwa,ba zaki tambayeshi abu yana dashi ya hanaki ba,ta lissafa abubuwa da dama game da jibril din ita daya tana zaune.
      A hankali sai hankalinta yakoma gareshi,saidai duk wata hanya da zatabi don samun damar kowa gareshi lokaci yariga daya qure mata,ashe dama sau daya take zuwarwa mutum a rayuwa?,saimai matuqar sa’a ne yake samun dama ta biyu,koda ta fuskanci ‘yan gidansu da zancan babu wanda ya tsaya ya kulata,yayanta nema yace da ita
“Ban sake yarda baki da kunya ba sai yau rufaida,to bari kiji na gaya miki,kaf cikinmu mu muna da kunyar da bazamu iya tunkarar jibril ba,keda baki da ita to bismillah” kakarta kuwa duka takai mata,abun duka saiya taru yayi mata yawa.
         Tabbacin data samu cewa jibril yayi mata fintikau kuma ta rashi yasa tasoma koyawa kanta yadda zata fuskanci rayuwa,tasan cewa tagane kurenta a qurarren lokaci,don haka tasoma qoqarin gyara dukkan wani kuskure nata.
*_GASKIYA ƊAYA CE_*
      Hakanan tasamu kanta da shiryawa zuwa gidan zahra qawarta.
      Hannu bibbiyu ta amsheta amma tana mamakin ganin rufaidan a gidanta,saboda sam bata zuwa tunda ta fuskanci zahran na gaya mata gaskiya.
      Da kallo takebin zahran ganin yadda tayi qalau da ita,ko bata fada ba kasan bata nemi komai ta rasa ba,ta saka shuru sai data tanka
“Qiba kike kawai abunki zahra,kamar ba wadda ke gidan kishiya ba” murmushi tayi sanda take zuba mata lemo
“Ni ai ba kishiya gareni ba,abokiyar zama ce dani,kuma don kana da abokiyar zama saika dinga ramewa kaqi kumari?” Kaita juya tana murmushi itama
“Har yaudai kina nan da aqidarkin nan akan kishiya rufaida” tafada tana dan dariya
“Mun rabu da jibril fa watanni kusa tara” da mamaki take duban rufaidan,bata boyewa zahran komai ba ta gaya mata,dakuma wanda yanzun yafito yake neman aurenta wanda shi dayane yake da niyyar aure cikin manemanta,ajiyar zuciya mai nauyi zahra tasaki kana tace
“Tun farko ne rufaida tunaninki ya gurbace,kinsan ta ina?” Saita girgiza kai
“Da farko yadda kika tashi cikin unguwa wata ta musamman yasa kika dorawa kanki abubuwa da yawa,kika zauna kika tsarawa kanki yadda kikeso rayuwarki ta kasance,kina jin kamar dole hakan zata kasance miki,manemanki suna miki hidima sosai saboda kowa so yake ya kaiki gidansa,hali koda ba nashi bane ya ara ya yafa ma kansa duk don ya burgeki yaja ra’ayinki zuwa ga amincewarki,duka saikika dauka a haka,kikayi amannar cewa hakanne,baki taba sakawa ranki cewa wataqila ba haka yake ba,wataqila ya arane ya yafa don yasamu soyayyata,bari na sanyawa raina bayan munyi aure zan iya ganin canji iri daban daban,zan iya haduwa da qalubale,bari na cire tunanin zamu dore da mu’amalarmu ta waje,bari na sanyawa raina ibada zanje,bari na saka tunanin cewa zan iya haduwa da qalubale nau’i daban daban,soyayyar kadance,haqurin juriya da kawaici yafi yawa,qauna da tausayi shine zaici gaba da riqemu,saikika sawa ranki wannan halayya da dabi’a ta waje ita zata dore,dukkan abinda kika samu a waje a ciki ninkinsa zaki samu,baki taba tunaninma zaki samu dai dai da haka ko qasa da haka ba,daga sanda kika shiga kikaha komai ya canza sai a soma samun matsala,don baki tunanin faruwar hakan ba bare kiyi shirin tarbarsa,sai a soma samun sabani,saboda an lallabaki an kuma daukoki kamar sarauniya,kinyi tashe a media unguwa da makaranta,kina ganin kinfi qarfin daukan wulaqanci ko rashin kyautatawar namiji,saikiga kanku daya bai isa ba bazai kuma taba isa ba”
“Ta fannin matansa na gida da yawanmu sanda mai.mace yazo aurenmu,abu nafarko da mukesoma darsawa ranmu wanda shike kashemu shine,ta gaza ne,jaka ce,babu abinda ta iya,ta gaza hanashi kallon kowacce mace bare ya nemi qarota,mun manta cewa zukatan maza Allah ya haliccesu ne da qarfin ikon daukar soyayyar mace hudu,wai wasu suka ce,halin maza ‘yan china suka kalla sukayi waya mai sim hudu” sai suka danyi dariya gaba daya sannan zahran tadora
“sannan an qawata zuciyoyinsu da son mata,duk yadda kikagai ga qwarewa da iya komai na fannin rayuwa da zamantakewa baki isa ki hana zuciyarsa so ko kallon wata ba,jarrabawarmu kenan,yayin da kike yunqurin shiga burinki waccar ta tozarta ta wulaqanta,kin mata adalci kenan?idan qanwarki ce yayarki ko qanwar mahaifiyarki zakiso ta tozarta haka?” Kai rufaida ta girgiza cikin sanyin jiki
“To koda yaushe tunaninmu kenan,bama tuna cewa idan mune bazamuso haka ba,son kawunanmu ya mana yawa,munyi watsi da maganar ma’aiki faufau ta fannin kishi da yake cewa muso junanmu,musulmi dan uwan musulmi ne,kada ya cuceshi kada ya xalunceshi duka muna manta tarin hadisai da ayoyin muna gaban kanmu,shi yasa muketa wahala muna fagamniya a duhu,inda zamu koma bisa tsari da turbar koyarwar addini qafa da qafa da ayau munyi dariya munyi shewa kuma kowa ya rabu da matsalarsa,muna jahiltar rayuwar aure mazanmu da matanmu,muna kuma kaucewa turba”

“Kibar hangen gidan wata,duk matar da kika gani cikin gidanta tadauki wasu shekaru haqurine yakaita ga wannan bigiren,kyanki ko matsayinki ko nasabarki yabar rudarki ki dinga ganin cewa idan kika fita tarin maza suna jiranki ko suna sonki,a’ah sam,wadan nan din dakike gani duka na bogine,wallahi wallahi kika bari son zuciya yakaiki ga kashe aurenki kika zalinci mijinki ki guji ranar da Allah zai hukuntaki,ki godewa Allah dayasa kika samu daya ma daya zauna,abunda zaki dora shine istigfari kada Allah ya jarrabeki a sabon gidan aurenki sanadin kuskurenki na baya,ki rabu da dukka qawar da bazata baki shawara bisa turbar musulinci ba”.
       Sosai jikin rufaida ya ida mutuwa,takuma gano kurakurai masu tarin yawa data tafka cikin rayuwarta,kusan dukkan abinda zahra tafada hakane,koda can abinda ya rage kusanci da shaquwarsu da zahra fadan gaskiya irin na zahran,ita kuma a sannan duniya tana mata guda akai.
       Gidan zahran tawuni sai yamma sannan takoma gida,tana sake jaddawa kanta zata gyara dukkan wani kuskure nata don tayi kyakkyawan qarshe takuma rabauta kamae yadda sauran mata suke rabauta.
_ƘARSHE!_
_MARUBUCI a kullum tamkar kyandir ne da yake qona kanshi donya haskaka al’umma,a duk sanda marubuci yadauki alqalaminsa burinsa shine yayi rubutun da xai zama darasi ga al’umma,yasoma labarinsa yakuma kammalashi shida kansa,labarin yafi cizon marubuci fiye dakai dake bibiyar labarin,domin yakanji wani nauyi mai girma a tsakiyar kansa har sai sanda ya kammala rubutun yazama cikakken littafi_
_kyakkawar kalma sadaka ce,annabi S A W yace duk wanda bai godewa mutane to baya godewa mahaliccinsa_

_masulmin da yafi falala shine wanda musulmai suka kubuta daga cutarwar hannayensa da kuma harshensa(aikinsa da maganarsa)_

_mu’amalarka itake nuna waye kai?,daga wanne gida kafito?,wanne nau’in tarbiyya kasamu?,harshe yanzu zai daukaka darajarka yakuma sauke darajarka cikin qanqanin lokaci ya qasaqantaka,mu kula da harsunanmu_

_ka guji zalunci,saboda shidin duhune a ranar qiyama_

_littafin HANGEN DALA banyishi don cin mutuncin wani bangare ba,nayi ne don wayar dakai da samun daidaito da fahimta a garemu gaba daya_

_ina roqon Allah ya karba,yakuma datar damu_🙏🏽🙏🏽🙏🏽
_mu hadu a zafafa biyar da zasu fara zuwan muku a jibi in sha Allahu,litattafan namu sune kamar haka_

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page