HANGEN DALA CHAPTER A

 HANGEN DALA CHAPTER A

*Da sunan Allah mai rahama maijin qai*

©️®️ *SAFIYYA HUGUMA*

👁️‍🗨️👁️‍🗨️ *HANGEN DALA*👁️‍🗨️👁️‍🗨️

_Ba shiga birni ba_

Mallakar

*SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA*

*_Taqaitaccen labarine wanda ke dauke da kukan kurciya da kuma tsumagiyar kan hanya_*❗

*zaku iya sauraren litattafaina tsofaffi dama sabbabin da zan soma dorawa a dandalin youtube,a tashata ta SAUTIN HIKIMA*

*littafin ALKAWARIN ALLAH yanzu haka yana can nasoma dorashi gamai sha’awar saurare*

        Dai dai lokacin qarfe biyu saura na rana ne,tana zaune cikin madaidaicin falon nata wanda ya wadatu da tsafta,gefe guda kayan yaranta ne data debosu daga kan igiya bayan sun bushe tana ninkesu daya bayan daya tana tarawa a gefanta,gefe daya na zuciyarta cunkushe suke da tunani kala daban daban da taketa qoqarin kauda su.

      Idanunta tadaga sanda taji an yaye labulen,maman ummi ce ke shigowa hannunta dauke da qaramar yarinyarta da take goyo,idanu mmn amir(mamallakiyar dakin) tabita dasu tana karantarta,lokaci guda duka ta zabge ta rame tayi firgai firgai,haka taci gaba da kallonta harta samu kan daya daga cikin kujerun tazauna sannan ta aje ummi,wadda tana ajeta ta rarrafa tayi wajen mmn amir,yarinyar na qarasowa ta dauketa tana juyata gami dayi mata wasa yarinyar tasoma dariya

“Yanzu maman amir kina ganin zamanmu a haka yayi dai dai kenan?,munaji muna gani haka baban amir zai sake kawo mana wata cikinmu?,muna zamanmu muda yaranmu cikin kwanciyar hankali zai debo mana matsala?” Ta qarashe maganar wanda kana jin sautin muryarta kasan cewa ba qaramin tashin hankalo bane cikin zuciyarta,daga kai mmn amir tayi daga wasan da takewa ummi ta dubi mmn ummin,ba shakka kishi abune mai ciwo dacin zukata,kuma ita kanta zuciyarta kullu yaumin ba cikin dadi take ba duk da cewa ba wannan ne farau a kanta ba,amma ita kishiya kullum sabuwace a wajen mutum,saidai wannan ba komai bane idan aka kwatanta da sanda xa’a auro mata mmn ummin,banda Allah yasanya ta hadu da iyaye nagari,takuma yi yaqi da zuciyarta da wataqila yanzun hakan ba wannan zancan ake ba,cikin kwantar da murya tace

“To yazamuyi mmn ummi?,baban amir dai bamu muka haifeshi ba bare muce zamu hanashi abinda yayi niyya” kai take kadawa da sauri

“Zamu iya hanashi mmn amir indai zamu hada kai mu duka biyun muyi masa bore kamar yadda nakeyi yanzun,yanxunma abinda yasa haqata ta kasa cimma gaci saboda ni kadai naketa qoqarina kinqi kisa min hannu” qaramin murmushi ya subuce daga fuskar mmn amir tana duban mmn ummin,ta tuna wasu shekaru baya da suka shude,lallai wanzami baison jarfa

“Mmn ummi,abinda nakeso ki gane shine,dukkanmu qarqashin bbn amir muke nida ke gaba daya,duk wani abu da zamuyi don mu tashi hankali komu hanashi aure bamu da riba don Allah ne ya halasta masa,bugu da qari da haka nayi a baya da wala’alla nima bana bigiren da nake kai a yanzu,abinda dai na gayamikin shi zanci gaba da gaya miki,kiyita haquri ki kauda kai,komai yayi farko yana da qarshe,kuma babu wani abu dawwamamme sai ikon Allah,watarana sai labari,hakanan me haquri shike da riba” miqewa mmn ummi tayi cikin fushi da rashin gamsuwa,baki tadan tabe

“Munaji muna gani mmn amir wlh zamu zama ‘yan kallo idan bamuyi da gaske ba,ke kuwa kinsan yadda yarinyarnan ta mallake  baban amir?,hala bai taba waya da ita a gabanki bane saini daya raina?” Murmushi ta sake saki

“Ba rainakin da yayi,face ke da kokaqi tsayawa ki fahinci komai…”

“Mmn amir” mmn ummi tayi saurin dakatar da ita

“Wallahi wallahi yarinyar ban labarinta kaf yazomin kunnena,duk cika da batsewar unguwarsu babu tantiriyar yarinya mara kunya irinta,inata boye miki ina miki hannunka mai sanda amma na fuskanci baki gane ba,yana daya daga cikin abinda yasa hankalina yasake tashi kenan,bin malamai take kamar tashin hankali,ki fuskanta mmn amir muyiwa kanmu gata tun batazo ta fiddamu daga cikin yaranmu ba” tsai tayi tana duban yadda mmn ummi ta sake firgicewa,sai data gama sannan tace

“Zauna don Allah mmn ummi muyi magana ta qarshe dake” kaman bazata zauna ba,amma dole tazauna din don neman hadin kai da mafita take,sai data tattara dukka hankalinta akanta sannan tace

“Kin yarda da Allah mmn ummi?” Kaita gyada tana dubanta

“Indai haka ne to ki yarda da cewa babu wata halitta data isa ta cutar dake saoda yardar mahaliccinki,sannan matuqar zuciyarki a wanke take ba wani abu mummuna da xai sameki saidai idan qaddararki ce,duka wannan abun da kikewa baban amir bashi bane zai sanya ya fasa aurensa ba,saima qara nisanta kanki dashi da kike,idan kyautatawa na saka namiji ya qara aure da baban amir bai auroki ba,amma da lokaci yayi hakanan na haqura,na shanye duk abinda yabiyo baya na kama kaina na haqura,wannan abun da kike ba mafita bane,tashin hankali bazai qara miki komai ba sai wani tashin hankalin,ki nutsu don Allah ki sawa ranki haquri da salama” shuru mmn ummin tayi,wanda kafin takai ga cewa wani abu anyi sallama a tsakar gidan nasu,dukansu suka amsa suka zubawa qofa idanu don ganin wanda zai shigo.+

      Ba jimawa baquwar tayi sallama a qfar dakin mman amir din sannan ta daga labulen tashigo,cikin fara’a maman amir din tayi mata maraba duk da cewa baquwar mmn ummi ce,amma yanayin da mmn ummin ke ciki yasa ta kasa sakin fuska ko tarbarta,gaisawa sukayi sosai cikin mutunci sannan tadubi mmn ummi

“Lafiya kike kuwa maryam?” Baquwar tafada tana duban mmn ummi,shuru mmn amir tayi tana ci gaba da ninke kayanta ba tare data saka musu baki ba,ajiyar zuciya mmn ummi tasaki ba tare data bata amsa ba,saita waiwaya taba duban mmn amir

“Mmn amir lafiya kuwa?” Sai a sannan ta dubi baquwar,tasan cewa qawace sosai ga mmn ummi kuma makusanciyarta,don haka tasan da cewa tasan komai

“Kiwa maryam fada wala’alla keta yarda da zancanki,kan maganar qarin auren bbn amir,gaba daya ta daga hankalinta tafita hayyacinta,ba abinda ban gaya mata ba taqi ji,wai ai tasan halin yarinyar anxo an gaya mata”

“Eh fa,da wannan don wannan,yarinya fa kusan halinta a bayyane yake koni nayi bincike,mara kunyace ta qarshe,sannan ko a gidansu uwarta itake juya ubanta,sai abinda tace,bata ganin kowa da gashi” sosai gaban mmn amir ya fadi,amma saita ambaci sunan Allah ta kuna kauda tsoronta,donta tabbatar idan har hakan ya bayyana to kamar ta baiwa kanta dasu qofa ne

“Idan harka riqe Allah zai isar maka,yakuma tare maka abinda yafi qarfinka”

“Hakane,amma dole ku tashi tsaye,kuyi duk yadda zakuyi wallahi,don nikam ina jiye muku”

“Abinda naketason ta fahimta kenan amma taqi ta gane” mmn ummi tasamu bakin magana a wannan gabar

“Ahto dai” baquwar mai suna rashida tamiqe tana daukan ummi sannan tace

“Bari mu qarasa ciki”

“Toh” kawai mmn amir ta fada,jikinta a sanyaye saidai tana qoqarin qwararawa kanta gwiwa,mmn ummin tabi bayanta suka fice.

    **************

     Cikin nishadi da walwala ta kashe wayar,fuskarta washe fes tana jin wani farinciki na gewayata,ji take kaman ta mallako baban amir ta gama

“Gaskiya kina sha’aninki rufaida,kinacin duniyarki da tsinke,kin samu mutumin nan fa a hannu yadda ya kamata” dariya rufaida ta sheqe daita

“Wata abu takazar ubanma saina shiga gidan,kinsan Allah?,gaba daya tausayin matansa nakeji” wata muguwar dariya zahra’u tasaki

“Wallahi harkinsa na hango randa zan shiga gidan auwal,ni kaina matarsa tausaya mata nake” kai kawai rufaida ke kadawa cikin nishadi da gadara,tana hango yadda zata maidasu

“Na rantse da Allah duk saisun raina kansu,sainasa a karan kansu sunji cewa su gidadawane basu iya komai ba,sai baqinciki yakusa hallakasu saboda ganin zallar madarar soyayyar da xa’a dinga zubarwa a gidan,zasu gane kurensu,zasuyi danasanin hada kishi dani”

“Allah yakai damo ga harawa” zahra’u ta fada cikin qyaqyata dariya,sai a sannan fatima dake zaune gefe tayi magana

“Wallahi wallahi zahrau da rufaida kuji tsoron Allah gaba dayanku,haka kawai bayin Allah nazaune da mazajensu da yaransu cikin nutsuwa da kwanciyar hankali zaku je musu da mugun tanadi da baqin qulli na tarwatsa zaman lafiyarsu?,waishinma ce muku akayi matan nasu gazawa sukayi da yasa zasu aureku?”

“Gazawa sukayi mana!…..idan banda tsabar gazawa ta yaya zaki bari mijinki yaga wata harya aura,wallahi dani yasoma aura ko mace daya bazan bari yaqaro ba bare biyu,da basu gaza ba da basu nemu ba” cewar rufaida tana tafa hannuwa gami da jefawa fatima harara

“Kinga qyale wannan,batasan dawar garinba da Allah,ai babu cinyewa da nuna isarki,ki nunawa mace kurenta,ki kuma nuna mata cewa keba sa’arta bace,wutsuyar raqumi tayi nesa da qasa irin ki shiga ki taddata kiyo waje da ita”

“Shine qarshen magana” rufaida tafada tana tattare katin bikinta daya kawo mata dazun tanason tasoma rabo sati mai zuwa,kallonsu kawai fatima take tana kada kai,lallai wanda yayi nisa baya jin kira,ta tabbatar su rufaida sunyi nisa cikin kuskure

“Tashi don Allah tawan mu wuce,igbo road nakeso mu soma zuwa zan kwaso qananun kaya na tarwatsa zuciyar kishiya ya halakata saboda tsabar kishi,kin gansu nan dubu ashirince cif yakawominsu inje in siya” shewa suka saka bayan sun tafa

“Muje muje muje,mu zabi qarshen magana,amm fatima,don Allah idan kin gama ki gayamin saina sameki a gida” rufaida ta fada tana yada mayafinta cikin sauri,har suka fice fatiman bata iya sake cewa komai ba face binsu da kallo da takeyi.👁️‍🗨️👁️‍🗨️ *HANGEN DALA* 👁️‍🗨️👁️‍🗨️

    _Ba shiga birni ba_

©️®️ *Safiyya Abdullahi Musa Huguma*

*BABI NA BIYU*

       Bakwai da rabi na dare bayan sun gama sallar isha’i,tana tsakiyar yaran suna aikin gida da aka basu a islamiyya,yaranta ne guda hudu,amir,ahmad,hanifa da rabi’a,sai yaran mmn ummi guda biyu mubarak da usman,wanda da can baya sai da aka kai ruwa rana kan donme mmn ummin zata dinga yiwa yaran aikin makaranta?,ko cewa akayi itadin bata iyaba ko bata da karatun,saida suka kai ruwa rana ita da baban amir kafin ta sauko ta haqura.

      Tana daga gefe tana kallonsu,hannunta daya saman cikinta wanda yafara nauyi,kadan kadan tunaninta na tafiya kan zuwan hafsat shekaran jiya gidan,wanda hakan yasake sawa mmn ummin takumsa sauyawa,har ita kanta tasake sauya mata,dan hadin kan da rabarta da take tasake janyewa,wanda ita ko kadan bai mata dadi ba,tasani cewa dole sai sun wanzar da zaman lafiya a tsakaninsu sannan koma wacece xata shigo daga baya itama tayi koyi dasu.+

       Sallamar baban amir ita ta katse mata tunaninta,suka hada idanu sanda yaran ke rige rigen isa gareshi su rungumeshi gami dayi masa sannu da zuwa,ya qaraso dakin yanaji da sannu da zuwan yaran,tayi qoqarin qaqaro murmushi saman fuskarta tana masa sannu da zuwa,amsa mata yayi yana nazartarta,yanajin tausayi tausayinta yana kamashi,haliman taci sunanta qwarai shi kansa yasan da hakan,komai Allah shike tsarawa dan adam shi,auren maryam na cikin qaddararsa,haka rufaida da yakejin sonta cikin jikinsa,hakanan yana jin cewa tayi dai dai dashi ta kuma dace da ra’ayinsa,banda hakan babu abinda halima mmn amir tarasa,wanda daa a baya baisan da hakan ba,kafin ya auri maryam ganin gazawar haliman yake,gani yake kaman nata iya komai ba,akwai abubuwa da yawa da bata iya masashi wanda yake hasashen samunsa gurin wata macen,ashe Allah ya tsara masa auren maryam ne don ya fidda qima da darajat haliman a idanunsa,sai bayan ya auri maryma ne ya tabbatar haliman ba kayan banza bace,wannan dalili yasa yake matuqar ganin qimarta da qoqarin kyutata mata,gefe guda kuma yanajin kunya da nauyin abubuwan daya ringa aikata mata lokacin da idanunsa suka rufe yana neman auren maryam,wanda yayi imanin cikin kawaici da yakana ta halima haryau wani abun bata gayawa maryam shidin ya mata ba lokacin neman aurenta,sai gashi ayanxu yana samun sassauci da sauqi daga wajen haliman fiye da maryam,wadda ta bazawa idanunta kwalli,takuma shafawa fuskarta toka ta fitittike kamar basu taba wani abu soyayya ba kan auren da zai qara

“Sannu da zuww” haliman ta katse masa tunaninsa,ajiyar zuciya yasaki a boye

“Yauwa halima,kece da sannu,ya nauyin jikin?” Ya qarasa fada yana bude ledar daya shigo da tsarabar da yayiwa yaran nashi yasoma raba musu,murmushi kawai tasaki

“Alhmdlh” ta fada kawai a  taqaice,sai daya gama rabawa yaran duka tana zaune tana kallonsu sannan yacewa amir

“Jeka kiramin antynku,banji motsinta ba” aje kayan hannunsa yaron yayi yafita kiran kamar yadda ya umarceshi.

      Minti biyu amir din yadawo

“Abba,tace ba zata iya tasowa ba batajin dadi”

“Kace magana zanyi dasu,tazo injini” dakatar dasu mmn amir tayi

“A’ah,tunda bazata iya tasowa ba ka taddata can mana,yaukam batajin dadi sosai don tun daxun data gama aikima tana daki kwance” jim bban amir yayi,don yana tantamar hakan,don lokacin dayashigo tsakar gidan yana ganin sanda tashige dakinta abunta,ba tare data kula da sallamar da yakeyi ba,amma yasan mmn amir din taui hakane saboda akaucewa idanun yaran,saboda haka yace

“Shikenan,in zaki iya tasowa ki sameni a dakin nata” yafada yana miqewa yadauki manyan ledojin yafice.

        Sai data basu wasu mintuna sannan ta yunqura tamiqe tabi bayanshi

“Ai dama ko bakayi hakan ba nasani ba wani sona ko damuwa kayi dani ba,ta yaya ranar girkina zaka wani shige dakinta kuma ka aika wai naxo…..to wallahi bbn amir ni bazan dauki wannan ba,tun yanxu wallahi tallahi donma kasani” duk abinda take fada cikin kunnenta suka fada,amma sai tayi kaman batajiba tayi sallama tashiga,sallamar tata tasa bbn amir din bai maida mata amsa ba,saita samu waje tazauna tana yiwa mmn ummin sannu da jiki,zama yayi yasoma bude ledojin yafito dakayan ciki,yayin da take tsaye har yanzu taqi zama

“Gashinan,kayan fadar kishiyane,kowacce saita dauki leda daya” jiki a sanyaye mmn amir ta sa hannu tadauki leda daya tana cewa

“An gode,Allah ya amfana” tana daga tsaye tanajin kaman zata fashe da kuka,wani mugun kishi yana ratsata,wato dai da gaske yake bazai fasa din ba kenan,kai ta gyada cikin fada da bala’i tace

“Tabdijan,duk wani rashin adalcinka muraran yafito wallahi jibril,ka narkawa amarya kaya akwati akwati kalar wanda takeso,mu kuma shine zaka dubemu da wadan nan ‘yan tsirarun kayan da basu wuce kala goma goma ba?” Ta fada tana nunasu cikin rainuwa,kai ya daga ya kalleta

“Ke kin manta kala nawa akayimiki?,shine yanzu yazama laifi don an yiwa wata?”

“Au hakama zakace?,wato bban amir gidan nan bau shegiya banza kamarni,to idan haka ne ita mmn amir daka yi mata kai daya da nawa,nan da wata uku kazo kasake mata na haihuwa taci tudu biyu kenan ni tudu daya?” Bacin ran baban amir yaqi boyuwa,cikin fada da hargagi yace

“Ke malama kin fara isata fa kin soma kaini bango,uwatace ke da dai abinda kika tsaramin zanyi?,don kinga ina daga miki qafa ina qyaleki?,to na rantse da Allah ki shiga hankalinki,banason hauka da iskanci kinji ko?” Da sauri mmn amir ta dakatar dashi

“Don Allah kayi a hankali yara zasu iya jiyowa,indai kaya ne ni saina qara mata a nawan tunda ni xakamin na haihuwa idan Allah yakaimu da rai da lafiya”

“Bata isaba wallahi saidai idan kada ta saka” ya fada yanajin nauyi da kunya da tuna sanda ya hana mmn amir din ko tsinke sanda zai auro maryam din da sunan kayan fadan kishiya,a sannan yace mata bashi da kudi,bayan ba haka bane ita kanta tasani amma ta qyaleshi bata sale daga maganar ba,sai kayan fitar sunan ahmad ta saka

“Lallai samu yafi iyawa” mmn amir din ta fada a ranta itama tana tuna lokaci irin haka da za’a kawo mata maryam din a matsayin kishiya,tunda harya riga daya rabtse gaka ta tattara kayan nata tafito tabar musu dakin,don ta tabbatar yau din Allah ne kadai yasan wainar da za’a toya tsakaninsu,tayi imani cewa da maryam ce uta a wancan lokacin da tuni tajima da barin gidan,cin kashin da yayi mata lokacin aurenta dashi a yanzu ko rabinsa baiyi ba,tayi imani Allah baya barci,kuma duk abinda kayi sai an maka mafiyinsa,gashi tun ba’aje ko ina ba tana dandana irin abinda ta dandana itama,ashe nata salama ne tunda ta iya haquri da mallakar kanta.

STORY CONTINUES BELOW

        _WASHEGARI_

  

        K’arfe shida na sassafiyar ranar maman amir na kwance saman gadonta,tun bayan data idar da sallar asuba bata koma ba,idanunta biyu sai azkar da takeyi wanda idan tagama saita sake dauko wani.

       Daga bakin uwar dakin nata taji sallamar ahmad,kamar yadda ta koyar musu shigo mata daki sai sun tsaya sunyi sallama tabasu izini,kai ta daga ta amsa masa sallamar sannan yashigo,ya gidata duk da qananun shekarunsa ta amsa

“Umma,mama batayi mana wankan ba,kuma lokacin makaranta yana qurewa” shuru tadanyi,al’adarsu shine duk wadda keda girki ita zatawa qananun wanka sannan tashirya musu abinci naci dana tafiya makaranta,tunda taga haka tasancewa lallai jiyan anyi bacin raine ita da baban amir

“Shikenan,bari na taso nayi muku,duba min kettle din idan da akwai ruwa kazo ka gayamin”.

      Dai dai lokacin da yake duba kettle din abban nasu yashigo

“me kake anan?ina shirin makarantar taku?”

“Umma ce tace na duba ko akwai ruwa a ciki

” ba’ayi ma wankan ba kenan?”kai kawai yaron ya daga,sosai yaji ranshi yabaci,wato shi zata nunama iyakarshi kenan?,a fusace ya qarasa qofar dakin nata ya yaye labulen yashiga.

      Tana zaune gefan gadonta tana baiwa ummi nono,idanun nan a kumbure hakama fuskarta,gaba daya jin duniyar take ta juya mata baya,batajin dadin komai,kamar tafita tabar mishi gidan haka takeji,jiya kwana tayi kuka,har sanda mmn amir tafito ta daura alwalarta ta ka’ida takoma daki duk tana jinta.

      “Wadan nan yaran?,wa kika barwasu?,waye zai musu wanka?”wani kallo ta dago ta watsa masa

” oho,kaje ka kira wancan tantiriyar da zaka auro tayi musu,tunda mu bamu isar maka ba,kaga gwara mu zame hannuwanmu ita tazo tayi abinda mu muka kasa ko bamu dashi”yana sane yasaki murmushi

“Me kike ci na baka na zuba?,tana nan zuwa kuma zatayin,amma a yanzun dole ki tashi kiyi kafin nata lokacin” sosai maganar tashi tasake bata mata rai ta kuma dugunzumata,wato babu abinda zai fasa kenan gameda abinda ya niyyata,har yana ma mayar mata da magana,nan fa sa’insa ta kaure tsakaninsu,kowanne ranshi yabaci yasoma maidawa dan uwanshi da magana.

        Dai dai lokacin da mmn amir tafito tsakar gidan don hada kan yaran tayi musu wanka taji tashin muryoyinsu,gefe daya amir na tsaye fuskarsa cikin damuwa shida ahmad,kada yaran tayi dakinta sannan ta fada dakin mmn ummin

“Haba haba baban amir,bai kamata bafa,kuna abu kaman yara?,duk kunsa hankalin yara yayi kanku?,kiyi shuru mmn ummi mana haba”

“Kinga ba abinda yashafeki,ki qyaleni dashi wallahi,duk wani take takensa na gama ganeshi,tunda ke baki iya qwatarwa kanki ‘yanci ki barni nina qwaci ‘yancina”

“Don Allah kiyi shuru mmn ummi,haba mana”

“Qyaleta halima,barta tayi,dani take zancan na rantse da girman Allah,tunda aka tada zancan nan kin hana kowa hutawa?,saikace ke daya ce macw cikin gidan nan?,to kiyi duk haukar da zakiyi ki gama,aurene dai babu fashi sai nayishi”

“Ka fada duk abinda kakeso mana jibril,ai namiji kake,batulu,namiji ai dama hankaka ne,gabanka fari bayanka baqi,ka manta lokacin daka dinga daukarmin qawuran bayanni babu wata?,kamanta sanda kake neman aurena ido rufe kanason nashigo gidanka na haska maka shi na zamemaka fitila saboda gidan ya maka duhu acewarka a sannan?,shine zakayimin butulci a yanzu?”duk ya tuna,ya tuna komai,nauyi da kunyar mmn amir suka dabaibayeshi,gashi da alama mmn ummin tonon silili takeson masa,da sake tada husuma,tanasone ya rasa kwanciyar hankali da biyayyar da yake samu wajen haliman kenan?

“kinga maryam,tunda ke baki da mutunci,bakisan darajar mijinki ba to xama babu dole,ki tattara ya naki ya naki ki tafi,don bazan zauna kina haddasamin bala’i da masifa ba tun yanzu”

“Ashasha,haba baban amir haba?,wannan ma aiba zance bane” inji mmn amir duk ranta a jagule,baiko sauraretaba yafice abinsa,don tabarmar kunya yakeso ya nade dama da hauka kada ya baro wani zance daya shafi tsakaninsa da mmn amir din.

        Kuka sosai mmn ummin take,ta nemi gefan kujera taxauna tana ci gaba da kukanta,amir ta qwalawa kira tace yayiwa ‘yan uwan nasa wanka,ya saka musu unifoarm tan nan fitowa,sannan ta sake maida hankalinta ga mmn ummi

“Kinga irinta ko?,kinga irin abinda nake gaya miki,akan wata can a waje da batama kai ga shigowa ba har yanzu zaki girgide aurenki,ki fita kibar yaranki wanda baki da yaqini ko tabbacin yadda rayuwarsu zata kasance,yanzu wa gari ya waya?” Itadai batace komai ba sai kuka da take faman sheqa,mamaki duk ya cikata tana tuna soyayyar da suka zuba ita da baban amir,ko a mafarki bata taba tsammatar irin haka zata faru ba,shuru ya ratsa dakin kafin mmn amir tamiqe tana cewa

“Ba inda zaki,ina zuwa” ta juya tafice daga dakin da niyyar baiwa baban amir baki,saidai koda taje dakin nashi bainan,ahmad ya gaya mata yafita,saboda haka ta sauya akalar tata zuwa dakin girki ta dorawa yaran ruwan tea,tanayi tana tunani cikin ranta.

       ******************

“Haba don Allah dear,nifa banason ka dinga bata ranka a banza a wofi,yanzu kamar kai ace kana teburin me shayi wannan ai zubarmin da mutunci kawai kayi” jim tayi ma wasu mintina sannan tace

“Aini wallahi banga wani abu da xakayimin da har zai kaimu ga haka bama,nidai don Allah ka koma gida koka qaraso nan gidam anty luba na hada maka break,tunda su duka basu damu dakai ba nina damu dakai” sake shuru tayi kafin daga bisani tace

“Toh shikenan,i love you” daga haka ta aje wayar tana murmushi

“Uhmmm,rufaida kenan,ke naga ko a jikinki ma,da aketa jiye miki shiga tsakiyar mata biyu” dariya tasaki kafin ta tabe baki

“Mata biyu ko muna mata,nifa wallahi anty ko a jikina,wadan nan niban daukesu a bakin komai ba,kada madai uwar gidan nan tashi taji labari,wadda ko isasheshen ilim boko bata da,yadda kikasan matar ladar noma,gwara gwara ma ta biyun itace kawai nakega tafi fada a wajensa fiye data farkon,haba anty,me zanji,kamata?,nida nake da karatu har matakin degree dame zasu tsoratani?,wancan mai kwalin diploma din ko dayar da banda kwalin secondry bata da komai?,wucenan wallahi”

“K’nnnn,to ai shikenan,yanzu yaushe zaki shiga kasuwar?” Dan shuru tayi sannan tace

“Ina tunanin anjima kadan,don akwai wasu magunguna da zan siyo wanda yakamata ace nashasu tun last week amma ban samesu ba,to tayimin waya ta kawo nazo na amsa” baki anty luba ta kama tana dariya

“Lallai rufaida,kurman tanadi kawai akewa auren nan” fari tayi da idanu cikin jin dadi

“Kedai bari kawai anty,burina kawai nazama tafisu,duk da yanzun ma nasan tafisu dince” dariya tayi ta juya tafice tana cewa

“Idan kin tashi tafiyar kimin magana inada saqo”

“Tohm” ta amsa mata tana maida kanta tasake gyara kwanciyarta,tanajin dadin yadda take juya jibril son ranta,kamar sitiyari a hannun driver ba tare da wata matsala ba,hakanan ba tare data nemi komai ta rasa ba.👁️‍🗨️👁️‍🗨️ *HANGEN DALA* 👁️‍🗨️👁️‍🗨️

       _Ba shiga birni ba_

©️®️ *Safiyya Abdullahi *Musa Huguma*

*BABI NA UKU*

         “Adawo lafiya,Allah ya tsare” maman amir dake miqewa daga duqen gogewa baban amir takalma da tayi ta fada

“Allah yasa,shikenan babu wani abu?” Ya fada cikin sigar tausayi,har cikin zuciyarsa yana jin tausayinta,girmanta da qimarta na kuma daduwa cikin ransa,sai a yanzu ya gane ba qaramin haquri tayi dashi ba a wancan karon da yake fagamniyar kawo maryam gidan,gashi yanzun maryam din ta kasa daya cikin goman haqurin da ita halima tayi dashi,bayan shi a karan kansa yasan cewa bai mata kwatar abinda ya aikata ga halima din ba wancan lokacin

“Babu komai,saidai awo kawai da nakeso naje” baice komai ba yashiga laluba aljihunsa,yaciro naira dubu daya da dari biyar,cikin mamaki ta saka hannu ta amsa tana dubanshi,yadan saki murmushi

“Kije kiga likitan,sauran canjin ki riqe kya sayi wani abun a hanya” da mamaki saman fuskarta take juya kudin,ba kasafai yake mata kyauta irin haka ba,duk da cewa dama itadin ba wani damuwa tayi ba,don tana sana’arta tasaida ruwa da lemo da qanqarar yara,kuma ta rufa mata asirinta sosai,tana ciniki ba kadan ba,don ada firji daya gareta ta sake siyan wani ya zama biyu,daya tazuba ruwa zalla,daya tayi lemo zobo ginger da kunun aya da qanqarar yara,daya daga cikin abinda yasake kawo rashin jituwa da kishinta a zuciyar maman ummi kenan,don tana tsammanin bban amir din ke boyewa yana mata abubuwa ba tare datasan cewa guminta bane,da farko burga ta dinga mata na ita ta girmi sana’a,don miji ya tsaya mata,bata neman komai ta rasa,lokacin ludayinta nakan dawo,maman amir din takanyi murmushi kawai don tasan qarshen labari ko ba’a rubuta mata shi ba,itama tahau wannan siradin,sai a baya ta gane ashe duka kurace da fatar akuya,tadauki darasi ta kama sana’a tana bidar na kanta,sai gashi a yanxu bayan wasu shekaru abun yana neman zamewa maman ummin dan zani,ya fara tara iyali,hakanan mata biyu gareshi gata uku nan zuwa,tilas abubuwa da yawa suka soma sauyawa,wanda basuyiwa mmn ummin dashi kanshi dadi ba,suka dinga samun sabani,ta riga ta sangarce da saidai ta tambaya a bata,bata iya nema ba,hakanan take zaune,duk abinda mmn amir din tayi kuma ta zargi baban amir shiya mata,tun tana qoqarin fahimtar da ita harta tattarata ta watsar ta qyaleta,daga bisani idanuwanta suka gane mata.

+

      “To na gode,Allah ya qara budi”

“Amin amin” ya fada yana sanya kai zai fice daga gidan,duk abinda ke faruwa mamn ummin tana bakin famfo duqe tana wanke kayan da yaranta suka cire,qasan zuciyarta tana jin kamar ra kama mmn amir ta daka,tana ganin duk ita ke daurewa baban amir gindi,har wani durquson goge masa takalma take da tsohon cikinta?,tana masa addu’a?,mutumin da zai musu kishiya aoba masoyinsu bane,kamata yayi su hada kai su yaqeshi harsai ya gaji don kanshi ya janye,amma tafi yarda da zancan hadixa data gaya mata idan ta tona zuciyar maman amir din qila fal take da farincikin za’a yiwa mmn ummin kishiya,tunda kishiya tabiyu tana bin wada kebi mata ne ba matar farko ba.

        Tana kallonshi amma qyashi take tace masa a dawo lafiya,har yakai soro wata zuciyar ta tunzurata,donme zai baiwa mmn amir kudi amma ita data aika yara jiya suka gaya mishi ya bata cikon kudin me takalmi yace bashi dashi?,wuf ta miqe ta rufa masa baya.

          Dab da zai fita ta rafka masa kira,da mamaki yajuyo yana kallonta,ta qaraso dab dashi fuskarta kamar tasowar hadari hannunta aqugu

“Wannan rashin adalcin da kake gwadamin ya isheni hakanan,jiya jiya nace ka bada cikon kudin takalmina kace babu amma yanzu ita ka narka mata kudi zataje awo,toni ka gayamin a wacce bolar ka auroni ne?” Sakato yayi kawai yana dubanta cike da dimbin mamaki,ta manta lokacin da yake bata ninkin kudin da ake buqata a asibitin,kuma yadauketa cikin motarshi ya kaita yadawo da ita,wani lokaci harda qwalama ta masu ciki amma mmn amir din koda ta nuna damuwa a fuska badai kaji abakinta ba,ta manta sanda take tsiro da ankon qawaye na babu gaira babu dalili ya dauka kudin ya bata ba tare da mmn amir din tace komai ba.

1

STORY CONTINUES BELOW

         Kafin ya furta komai kira yashigo wayarsa dake gaban aljihu,ya zaro yana duban me kiran,rufaida ce,murmushi ya subuce masa wanda ya tunzura mmn ummi

“Ina magana dakai kayi banza dani kana kallon waya kanamin dariya kamar wata tababba?” Daga kai yayi ya dubeta sannan ya maida kansa kan wayar yana shirin dagawa fuskarsa washe da fara’a

“Baki da amsa ne ai” kafin yakai ga kara wayara a kunne tasa hannu ta warce wayar cikin fushi da fusata tana duba me kiran,dama jikinta ya bata ashe kuwa itace,a cike take da ita dama,wancan kwanakin ranar girkinta data turowa baban amir din saqonni har guda biyu,wayar na kusa da ita tadauka ta karanta,ta mata reply na zagi itama ta maido mata,kafin ta sake maida mata baban amir ya karbi wayar,da sauri ta kanga wayar a kunnenta,kafin tace komai kalaman sun daki kunnenta

“Honeeeyyyyyyy” muryar rufaida ta ratsa dodon kunnenta cikin shagwaba

“Honey din uwarko kona ubanki,shegiya karuwa,masifa annoba,to bari kiji na gaya miki,wallahi sai kinyi danasanin shigowa gidan nan in gaya miki,banza shashasha kawai,ballazaga mebin mazan jama’a” ta qarashe maganar tana barin soron da sauri saboda amsar wayar da baban amir ke qoqarin yi,ta saka sakata a qofarsu ta tsakiya cikin hanzari,ma’ana ta rufe baban amir din daga can soron do ta samu damar cin karenta babu babbaka,wata dariya rufaida tasaki kaman taba kallonta ta tabe baki

“Tooo….yau kuma da haukar da aka tashi kenan?,bari na soma tambaya cikin gawarwarkin daya aje gidan wace ke a ciki,ta farkonce kome bi mata don insan yadda zan ciwa mace uwa dakyau”

“Ta uwarkice,nace ta uwarkice wadda bata ramin kanta saina wani stupid” dariya takuma yi saboda tunda taji ta jefo kalmar bature to ba shakka maryam ce

“Kice dai bama ramin kanmu saina wani,ina cewa kema saura kika tarar shi yasa zan shigo na tayaki muci tare,to bari kiji,ni bana fada a waya,ki tanadi duk wata masifa da bala’i da makamanki da bomabomai saina qaraso gidan,don waya tayimin kadan wallahi,wawuyar mace wanda batasan inda yake mata ciwo ba,saikin gane uwarki bata koya miki komai na game da yadda zaka mallake miji,ki jirayi shigowar rufaida zaki gane komai da babban baqi” daga haka ta kashe wayar qit

“Abu ta kazar uba,ni zata zagawar uwa?,wallahi yau saita gane shayi ruwa ne” mmn ummi tasoma kumfar baki tana banbami tare da qoqarin sake kiranta,cikin haka Allah ya bawa baban amir damar bude qofar wadda sabida sauri sakatar bata gama shiga ba dai dai bata sani ba,yana shigowa yakai hannu ya finciki wayarsa

“Ka bani,wallahi saina rama zagina”

“Bazan bayar ba ki qwata idan kina da qarfi”

“Allah ya isa ban yafe ba wallahi,da ita da wanda ya daure mata gindi,macuci azzalumi,aina haka mukayi dakaiba sanda kaje zaka auroni,Alla ya isa ban yafe haqqina ba,kuma zagina da tayi sai Allah ya mana hisabi dakai” juyowa yayi yana dubanta cikin matuqar bacin rai,zaiyi magana kiran rufaida yasake shigowa

“Kiyi haquri don Allah my rufeee….” Abinda yasona cewa kenan cikin kwantar da murya kana yayi shuru na wani sakanni,wanda hakan yabaiwa rufaida damar jiyo bambamin da mmn ummi wadda ke tsaye a bayanshi takeyi,murmushi yasaki yana cewa

“Yauwa dear….na gode” baiko waiwayeta ba ya saka kai yafice yana ci gaba da wayarsa da rufaidan,wanda tana sane tajanyeshi dama,hannu maman ummi ta dora aka ta zube a wajen,tana jin kamar zata tayar da bori,ita baban amir yayiwa haka?,mutumin dako bacin ranta baison gani shine a yanzu zai watsar da ita yawuce abinsa?.

    “Haba mmn ummi,wai sau nawa zan gaya miki wannan?,yanzu meye amfani ko ribar abinda kikeyi,maqota da masu wucewa duka sunajinki?,kafin a tsinewa baban amir sau daya an tsinemiki sau goma koda mala’iku kuwa” harara tayi kaman zata watsa mata saita fasa,cikin qunar rai da fusata tace

“Kome baban amir yayi yasamu goyon bayanki ne,tunda kinsan hannu daya baya daukar jinka,ba yadda banyi dake mutare abinnan ba amma kika qi bada goyon baya,yanzu kinsan muggan kalamai da alwashin da yarinyar takeci a kanmu nida ke?,to nida ke mu shirya kayanmu dukanmu gaba daya saita fitar damu” murmushi maman amir tasaki tana kada kai

“Kome ta gaya miki maman ummi kece kikayi babban kuskure,ina ruwanki da budurwar mijinki?,meye hadinki da ita?,kin fita kusa da mijinki,kin fita daraja koda ba haka bane to a wajen Allah haka ne babu kuma wansa ya isa ya kankare,koda tashigo gidan kuwa karki manta zata jima bata cimma matsayin dake kike kai ba,tunda ko banza kin rigata samunshi,kin rigata samar masa da diya,to me yayi saura?,me zai daga miki hankali?,maman ummi….” Ta kira sunanta cikin nuna da gaske zata furta mata maganar

“Inada yaqinin nafiki son abban amir,na kuma fiki kishinsa” saitayi jagale tana kallonta,magana takeson gaya mata kenan kome?

“Qwarai,ina tare da abban amir tun auren saurayi da budurwa,tun baida wani abun azo a gani,amma daga sanda yasoma neman aure na sanyawa kaina salama,inajin kishinsa kamar na mutu,ina kuka saboda kishi,ina kasa ci in kasa sha saboda kishi,amma dana fuskanci wanda nake abun saboda shi shi jin ransa yake kamar sallah saina sawa raina haquri da dangana,na kawo idanu na zuba akan duk wani abu da zaimin cikin sani ko rashin sani,wanda zumudi da rawar kaine ya sanyashi dama wanda yayi saboda radin kansa,yanzu gashi an wayi gari na barshi da kunyar abinda ya aikatamin a baya,na tsira da mutuncina da darajata a idanunsa saboda ban aikata duk wani abu da zai nuna rashin nutsuwata ba,babbar zubewar girma ko daraje a wajenki na matar gida budurwar miji ta zageki,bari na tambayeki…”shuru ta sakeyi tana dubanta

“Tunda kuke da baban amir har kika shigo gidan nan kin taba kiransa na daga wayar?,kona taba kiranki dai dai da rana daya?,kin taba jin muryata ko ganina?” Kai mmn ummi ta girgiza sannan tace

“Duka ban taba ba,amma Allah yagani ni mmn amir bazan iya koda rabin abinda kikayi ba,wayar dare,kiran dare amma ace duka baki nuna ko daukan mataki ba?,bazan iya ba wallahi,babu wata shegiya data isa ta takani wallahi ko wace saina maida mata,duk wadda ta nunani da yatsa saina karyashi” ajiyar zuciya mmn amir tayi tana kallon mmn ummin,shi yasa a rayuwa duk abinda kasan bakaso kada kayima wani,idan ba haka ba kuwa,watan watarana saiya fado a kanka,sai an maka,sai an ramawa wanda ka cuta ko ka cusgunawa koka zalunta.

“Shikenan,Allah yabada sa’a” ta fada tana miqewa gami da bar mata dakin.

    *******    ****   *******

     “Wai maman amir mu mmn ummi zata wulaqanta?,har ta ganmu ta dauke kai tawuce daki?haka ta koma?,to do n yaya zai qara aure shine me?,me za’a fasa?”

“Mtseweeew,kice fa kika damu wallahi,ni tayita kumburinta idan taso ma ta fashe,qarin aurene babu fashi sai yayishi ehe” murmushi kawai halima tasaki tana zama bayan ta aje musu kwanon abincin da ita da kanta tashiga kitchen tazubo musu,ganin mmn ummi dake da girkin bata da niyyar basu din,shuru tayi na sauraron qorafinsu da yadda kowacce ke zuba baqar magana kan mmn ummin,dubansu kawai take don bata data cewa,zuciyar musulunci da ilimin addini kadai daya ratsata yasanya taci gaba da mu’amala dasu,a shekarun baya babu tamkar ya maryam a wajensu,a sanda ya niyyaci qara auren babu abinda bata gani ba daga gunsu,basa boyewa har a gaban idanunta

“Na qagu wallahi maryam tashigo”

“Wai kinga matar yaya kuwa?,tabdi,wallahi yaya yayi zabe”

“Ke ai wannan kankat ce,tayi a rayuwa,ga ruwan mutunci zallarsa,bakiga yadda takesonmu muda umma ba”

“Kinga kyautar data aikowa umma da ita kuwa?,ke yaya kanshi fa yamato,donta iya soyayya”

“Nce gareta mafa,wallahi da yaya zai barta tsaf zata dinga fita aiki,amma tace masa ma ita tafison tazauna gida takula dashi” ire iren wadan nan maganganun dama wadansu wanda ba zata iya tunasu ba ba wanda basu fadi ba a gabanta,babu kara alkunya ko kawaici,sunsa qafa sun shure duk wani alkhairi nata kyautatawa da haba haba da take dasu,a lokacin ambaton Allah datake yawaita yi shi kadai yazame mata haske,uwa tagari kuma da take da ita tayi mata jagora,matakin farko data soma mata dannar qirji,ta kuma kwabeta,a yanzun taga alfanun hakan

“Wallahi maman amir ni yadda kike yafi komai burgeni” cewar jidda qanwar baban amir,sai a sannan tadago ta dubeta

“Kishi na hankali da nutsuwa ba irin nata ba na jakan mata,ai rannan rufaida ta gayamin komai,wallahi ta burgeni data rama abinda tayi mata” cewar jidda tana ci gaba dacin abincinta

“Indai rufaida ce dai dai da ita take,yarinyar da takejin quruciya da karatu akanta” dariya haula tayi

“Nifa harso nake naga ya zatayi idan rufaidan tashigo,gaskiya tana ruwa,maman amir kedai wallahi kinyi a rayuwa da kika iya kama girmanki,kaman baki da kishi” kai ta girgiza kawai tana fidda dan qaramin murmushi,sa’annan cikin nutsuwa ta dubesu

“Babu wata mace da bata da kishi,duk matar datace bata kishin mijinta toba shakka an samu matsala,kuma idan aka zurfafa bincike akwai wata a qasa,zan muku maganar daban taba muku makamanciyarta ba,abinda kawai zanja hankalinku akai shine,ku gane cewa dukkan mace macace,kuma ba’a cewa jifa idan yawuce kaina yafada kan uban kowa,koda baku da aure ke jidda kina dashi,kuma kuma wataran matan wasune,gidan wasu zaku je,cikin dangin wasu,Allah yasa kun fahimceni”

“Eh hakane,amma wallahi kawai dai duk wanda yadebo da zafine bakinsa,ni banga abun wannan kishi hakaba ina dalili?” Cewar jidda tana watsa hannu,sai kawai mmn amir din ta watsar da maganar tadauko musu wadda ta kawosun,wunin da za’ayi cikin gidan.

  *BAYANA AWANNI*

     Tunda ta kawo masa abincin ta tattarashi ta watsar,banda ma ‘yan nasihun da maman amir tayi mata da babu abinda zai sanya ta saurareshi,shima cike yake da ita,hakan ya sanya baibi ta kanta ba yaci gaba dacin abincinsa,yana wasa da ummi daketa sabgarta saman carfet,lokaci lokaci yana diban abincin yana bata da cokali harya kammala,yasha ruwa yadauke ummin ya karkade mata jikinta yadorata saman cinyarsa sannan ya dubeta

“Me dame kike da buqata keda yara,inajin saura baifi sati uku ko biyu ba tariya” wani kallo ta watsa mata,kishi na tokare mata a qirji,ta rasa ma me zatace masa

“Kaje ka qarawa amaryar inaga hakan yafi armashi”

“Ohkey” kawai yace ya saba ummi a kafada yafice,binsa tayi da kallo,watoma bashi da lokacin lallashinta kenan barema ya biye mata suyita ba ko zata samu sassauci cikin ranta.

      Kai tsaye dakin mmn amir yanufa,tana kwance saman doguwar kujera sanye da doguwar riga mara hannu,yaran duka na zaune qasa suna kallon tv,sallamarsa yasa kowanne maida hankalinsa bakin qofar yana fadin abba,abba,miqewa tayi daga kwanciyar datayi tana gyara zamanta,bayan ya gama da yaran ya dubeta

“Sannu” yace da ita yana dubanta,murmushi tadanyi sannan tace

“Yauwa”

“Ammm….nace dame dame kuke buqata kedasu ahmad gaba daya dasu ummi” ganin ya bata dama yasa lissafa masa iya abinda take ganin tana da buqata din,aljihunsa ya lalubo ya qirga kudi ya miqa mata,hannu biyu tasa ta karba sannan tayi masa godiya,ya sake qirgo wasu ya miqa mata

“Wannan nasu ummi ne,a musu siyayyar duka abinda ya dace” hannu tajanye tana kada kai

“A’ah,ka bawa ummansu ina ganin ta fisu sanin me dame suke buqata”

“Karbi nan,nasan da itadin ai nabaki ko?,banason jan zance” haka tasa hannu ta amsa badon son ranta ba,ta sake masa godiya,ya dubi amir

“Dauki ummi ka maidata wajen mamarta ta soma bacci” ya miqe yadauki yarinyar,shima yarufa masa baya.

 

       Kudin ta irga,ya wucema yadda ta tambayeshin,tasan zai isheta tagama duk wata siyayyarta harda ma qari a sama,saita hada da kudinsu ummin ta adana da zummar gobe tasamu mmn ummin,da alama tamasa halin nata ne shi yasa ya watsar da ita shima.

*mrs muhammad ce*👑👁️‍🗨️👁️‍🗨️ *HANGEN DALA* 👁️‍🗨️👁️‍🗨️

     _Ba shiga birni ba_

©️®️ *safiyya Abdullahi Musa Huguma*

*BABI NA HUDU*

   Gidan babu kowa yayi shiru  kasancewar yaran dukka sun wuce makaranta maman ummi tana dakinta wanda tun sape bata gilmawarta ba itam tana nata dakin saidatagama kintsa duk abunda xatai na ayyukanta sannna ta dauko kudin da baban amir yabata sannan tanupi dakin maman ummi akwance ta tarar da ita  tana kallo ummi najin sallamarta tararrafo gunta tadauketa tana cewa xoki naushi dan uwanki na ciki yadda kikasaba sannann tai sallama takarasa parlourn tashi tai maman ummi tai tazauna fuskarta babu walwala maman amir takarasa  tasamu daya daga cikin kujerun parloun tazauna tanacewa muntashi maman ummi murya acushe ta amsa tanacewa lafiya lau to madallah tafada tana mika mata kudin dake dake hannunta amsa tai sannan tace wannan kuma namaye maman amir tadubeta tace kayan siyayyar yarane jiya baban amir yabasu”

“Jiya da yaushe?”

“Sanda kike can kina sake kashe kanki wajen mijinki,mmn ummi bakyajin magana,amma Allah yagani nayi iya abinda zan miki,shine shaida” daga haka bata jira taji me zata fada din ba ta miqe tafice a dakin.

+

     Da kallo mmn ummin ta bita takaici na cikata,wato kudin siyayyar ‘ya’yan nata ma yafi qarfinta?,yafi qarfin yabata da hannunta saiya kaiwa kishiyarta?,qwafa taja ta dauki kudin ta irga,saita rabasu biyu tana ayyana abinda zatayi dasu,rabi kawai zatayi musu siyayyar dasu,saura kuwa zubin adashinta zatayi dasu,ribar qafa kenan ta fada cikin ranta.

********   ******    *********

“Wallahi wallahi babu shegiyar da zanwa girki,girki?,ni nace ka qaro auren kenan,idan sunsoma su rube saboda basuci abinci ba” ta qarasa maganar tana kashe famfo gami da daukar botikin wankanta tashige bandaki ta banko qofar.

     Shuru ne ya ratsa tsakanin baban amir da mmn amir dake tsaye cirko cirko,bacin ran mmn ummi yana kamashi qwarai da gaske,cikin halayen datake masa bai taba ganin daya daga ciki mmn amir ta gwada masa ba,koda a sanda take neman auren maryam din,kunya duka ta dabaibayeshi,musamman daya tuna sanda babu kunya ba komai ya baiwa mmn amir kudin cefanen abincin ‘yan jeran mmn ummin a wancan lokacin,yace lallai ta girka,a sannan batajin dadi ta gaya masa amma yarufe idanu ya caccaba mata magana,yana ganin kamar tsabar kishi yasanyata tace bata da lafiya qalau take,baiso akai girkin gidansu ne,azo aga kamar bai isa da gidanshi ba,ko kan gidansa ba a hade yake ba,kasa magana ya motsa zaibar wajen

“Ka kawo kawai sai ayi kamar na wancan karon” yajuyo yana dubanta,farinciki ne qasan zuciyarsa,saidai yana ga bai mata adalci ba ayadda tayi nauyi haihuwarta nan da satittika ya bata abincin masu jere,ga wadda takw ziqau ma tace ba zatayi ba inaga ita

“Ki barshi kawao,zankai can wajen gwaggwo sai ayi a kawo musun” ko daya batason yakai wajen mahaifiyarsa kafa wata sabuwar maganar kuma ta bullo,tasan halin surukar tasu qwarai da zafin rai da fada,,wani sabon bacin ranne kawai

“Babu damuwa,tunda anyi wancan wannan ma bazai gagara ba” kai yake jinjinawa,qimarta da nauyinta na kamashi,a sanyaye yace tabiyoshi daki ta karba.

     Kudi ya irgo masu yawa ya miqa mata,ta amsa tana dubanshi tare da kallon kudin

“Sauran kiyi amfani dasu” ya furta yana kallon idanunta,godiya tayi masa kana ta miqe ta fito,sai data nutsu ta lissafa kudin da zai isa ayi komai,sauran canjin suna da yawa ba laifi,data lissafa taga sun kai mata kudin datake na cikon da zata sauya plasma dinta.

********   *****    ********

      Zaune take a falon qafafunta na amiqe,gefe wata matace wadda a qalla ba zata wuce shekara talatin ba,kana kallonta zakaga kamar da suke da mmn amir,hira suke jifa jifa har dayar ta jefo magana kan gidansu mmn amir din

“Yaushene tariyar amaryar taku ne?”

“Saura kwana goma inajin ko sati,don cikin satin nan masu jere xasuxo” baki ta tabe sannan tace

“Wannan karon kamar ba kishiya za’a miki ba anty halima,shi kuma mijinku haka Allah gada masa” itama nata bakin ta tabe

“To yaka iya da abinda yafi qarfinka?,idan fada yafi qarfinka ai wasa kake maidashi samira,wancan karon da hankalina yayita tashi me aka fasa?,meye kuma ya sauya?,tunda ya gingimo yakuma dauki aniya aisai ka tayashi da idanu da kuma addu’a ko?” Kai ta girgixa

“Haka yake,amma banga kina wani shiri ba” qaramin murmushi tasaki

“Nice kuwa me shiri,amma yanzu ta abinda yake cikina mu rabu lafiya nake tukunna,bama wannan ba,bari na dauko miki kudin plasma din nan ki tafi dashi,yanzu abinda ya rage kawai kiyi xancan labulayena da mutumin,kudin sun samu shi nake jira,yayimin masu kyau sosai don Allah kalar kujerun,zan dauko miki dinkunana ki tafi dasu duka ki ajemin”

“Amma dai anty halima aiko kala biyu kya dauka ko saboda zuwan amarya”

“Xan dauki uku ma,amma nikam yanzu batasu nake ba,ta lafiyata nake”

“Allah dai ya raba lafiya”

“Amin amin,don Allah idan baban abba zai barki kizo mana jibin ki tayani girkin ‘yan jeren,yaran duka suna makaranta kya tayani zama ma”baki samiran ta kama

” au wannan karonma keya hada da girkin?,bai baiwa waccar ba taji yadda kikaji?”

“To meye a ciki?,ko nayi ko banyi ba zaikai wani guri ayi,kuma a hadamu duka a zaga,sannan kuma babu wani abu da zai fasu,kinga ni mubar wannan xancan don Allah muje na lissafa abinda yarage na baki” daga haka ta yunqura tamiqe samiran ta bita tana sake jinjinawa juriya da qarfin halinta.

STORY CONTINUES BELOW

*********   *****   *********

      Tunda safiyar ranar bayan mmn ummi ta sallami yan makaranta tafito tasoma hada duka kayan girkin da zatayi amfani dasu,maman ummin nata shige da fice gami da sabgoginta,batace ma maman amir din kanzail ba,sai itama tadan bata iska don ta fuskanci yau a cike take fam,su kansu yaran sun daku kafin Allah ya taimakesu su wuce makaranta.

   Duk wasu kan kayanta ta hadesu tsaf,tsinkenta bata bari tsakar gida ba,duka mmn amir din ta ankare da ita amma bata tanka ba,hakan yasake qular da mmn ummin,a yanzun tafi yarda da zanxan hafsa datace ita tabaiwa baban amir goyon baya,kuma tabashi goyon bayanne saboda su quntata mata don tazo ta taras da ita itama a gidan,ta wuce yafi a qirga amma ta rasa dame zata takali mmn amir din da zance,har daga qarshe tace

“Hmmm,sannu da aiki” saita daga kai ta amsa mata kawai taci gaba da aikinta

“Kekam da daurewa qarya qarqashi kike,yanzu masu zuwa yiwa kishiyarki jere kikewa wannan hidimar,wallahi ko ‘yar sarkin santanbul ce bata isa ba” murmushi ya kubcewa mmn amir

“Ba saboda su nake ba,saboda mijina nake albarkacinsa sukaci,kuma wannan din ba komai bane ni a wajena,tunda ba yanzu na saba yiba” sai ta tabe baki

“To madalla,Allah ya taimaka” bata amsata ba taci gaba da aikinta,a haka samira ta cimmata ta kama mata sukaci gaba.

     Kafin lokacin isowarsu harsun kammala,tayi wanka ta sauya kayanta masu kyau wanda suka sake fito da ita dukda tsohon cikinta,tuni mmn ummi an dauki kwalliya kamar wadda aka gayyata wani babban taro,ta samu kujera ta dasa bakin qofar dakinta wanda yake fuskantar dakin amaryar,duk da yadda takejin zuciyarta kamar zata faso amma haka ta daure don tanason ganin tunqwal uwar daka,hakanan tanaso taga idanun kowacce shegiya da nasu salon.

     Mmn amir kuwa tana daki suna hira abinsu da samira,tana ta taya samiran aikin duwatsu na hannu da akewa kaya beadwork,ba’a wani jima sosai ba sallamar baqin ta ratsa tsakar gidan,gaban mmn amir yafadi,saita kira sunan Allah tana tattara nutsuwarta,mmn ummi dake tsakar gidan kuwa wayarta a hannu tana danne danne,tana jinsu har suka qaraci sallmarsu suka shigo babu wadda ta tankawa,sai sukayi turus ganinta a tsakar gidan suka hau kallon kallo a tsakaninsu,daya daga cikinsu ce tasake maimaita sallamar waiko ji ne batayi ba ganin kota dago ta dubesu,wannan karon dagowa tayi ta musu wani banzan kallo ta watsar,ganin haka daya daga cikinsu taja tsaki tana cewa

“Muyi abinda ya kawomu,don da alama dakunan a bude suke” sanda suka juya zasu shige din mmn amir tafito.

A mutunce suka gaisa,wanda mmn ummi taji kamar ta shaqota,suna gama gaisawa takoma daki abinta,samira ta gabatar musu da abinci da ruwa takoma daki sukaci gaba da sabgarsu ba tare dako sun kao hankalinsu ko sun damu da abinda ke gudana a tsakar gidan ba.

A hankali xaman qaryar datayi a tsakar gidan yasoma gundurarta,duk wani abu da aka shigo dashi idanunta akai yake,a zahirin gaskiya rufaidan ta fita yawan kaya nesa ba kusa ba ko sanda akayi nata auren bare yanzu da yara suka lalata wani itama ta lalata wani,sai taji hankalinta yayi mugun tashi,lallai dole tasan abunyi,dole ta sabunta komai nata,dole ta tattara takoma daki har zuwa sanda yaran suka dawo daga makaranta.

Yadda suka wuni jere haka tawuni yawo tsakanin dakinta da tsakar gida zuwa bandaki,ranar kuwa yaran sunsha duka sosai,gashi dama babu islamiyya bare su tsira,abu kadan yaro zai mata ta kamashi ta kila ta kila,kusan a kansu ranar ta huce,saida suka guji suka gudo dakin mmn amir,wadda tunda tasaki labulenta suna ciki ita da samira bata sake ma fitowa ba bare tasan wainar da ake tonawa,ko abune take da buqatarsa a tsakar gidan takan aika samira ko amir yadauko mata.

*********   ******    *********

        “Yauwa nawa ne kudin lallen namu nida amaryar?” Zahra’u dake tsaye wadda tacire nata lallen ta fada

“Ku bada dubu da dari biyar harda baqin”

“Baji wannan amaryar ta musamman ce,ko nawa kikace a baki bayarwa za’ayi,angon ya tsaya mata,uwa uba gidan mutum biyu zata shiga itace ta uku,koba haka ba jama’a?” ta qarasa maganar dai dai sanda ta zaro kudin ta miqawa mai qunshi,kusan fiye da rabin dakin ‘yammata ne,amare da qawayen amaren,maganar zahra’un ta ruda dakin kowa da abinda yake fada,wata daga cikinsu dake zaune daga can gefe an gama sanya mata lallen ta tabe baki

“Mata biyu?,tabdi,wallahi saita tashi tsaye tayi da gaske,itakuwa meya kaita?,aini wallahi ban auren mai mata ma sam” wadda ke fuskantarta itama tata qafar da qunshin tace

“Hhhhh,lallai hajiyata baki hadu ba,ni nan da kike ganina wallahi idan bame mace bama bazan auri saurayi ba,kuma yanzu haka burin nawa zan aura,ai bari kiji na gaya miki…..” Ta miqe ta zauna sosai sabanin dazu da take kashingide

“Indai kin hadu kin cika mace,inda zaki nunawa duniya kedin kat ce,kiyi soyayya dame mata,ki guma mata baqinciki,tanaji tana gani halayen mijinta yasauya,ki karbeshi daga hannunta,ki morewa soyayya ya zama naki ke kadai,daga qarshe ki aureshi ki shiga gidan ki kafa sarautarki,ki watso taciki waje,idan kikaga wasa wasa ma ki hadota da yaranta”

“Shine magana!….” Rufaida ta fada cikin wani jin ixxa isa da ganin cewa tashiga layin wadanda suka cika mata

“Wannan dagani tafiyarmu zatayi kyau,badon lallene a hannuna ba damun tafa dake wallahi,amma bari nacire lallen ki sakamin number dinki,yaushe ne naki bikin”

“Cikin satin nan ne”

“Kash,naso ace akwai tazara daya yajewa dayanmu,amma duk da haka bata baci ba,kafin mu gama yaga amarcinmu zamu jone,zaki zomin koni naxo miki” dora bayani tayi

“Ke nifa tun kafin na shiga wallahi ta gama sanin matsayina a wajensa,ita kanta ta gama sallamawa,donko kishi dani bata isa ta nuna masa tanayi ba,ina kiransa duk sanda naga dama,wani lokaci ma ita zata daga,ta gaidani in amsa sama sama inashan qamshi,idan nasoma na datseta ince ta baiwa mamallakin wayar,ke wallahi saboda tasamu fada da soyayya a wajensa,data fuskanci saita kama qafa dani har kirana take tana gaidani,ta kuma bawa yaranta su gaidani,bari na taqaice miki zancan,ba yaranta ba har ita anty sama anty qasa take kirana dashi” dariya rufaida ta kwashe dashi,labarin ya mata dadi,har taji kamar dramer dinma tafi tata

“Dole muje dake wallahi,amma wannan matar tasa anyi jahila” dariya itama matashiyar me suna jamila tayi

“Kamar kuwa kin sani,daga primary aka liqa masa ita daga can qauyensu,tun bashi da komai har yayi arziqi,kinga kuwa yanzu dole yanemo ta gaban jirgi,kada babban abu ya tashi ta kwafsa masa” suka sheqe da dariya suda sauran wadanda kejin dadin hirar a dakin.

“Allah ya rufa asiri,amma dai kubi a hankali,bigiren da uwargida tahau wataran shi zaki hau kema,wala’alla tasu ma tafi taku kyau” wata mata dake tsaye tana zarowa me qunshi kudinta bayan ta cire nata ta fada,duk sai idanunsu suka koma kanta,

“Malama waya saka dake,nifa dama tunda na fuskanci kedin uwar gida ce ko zama kusa dake naqi,saboda haka ba ruwanki da sabgarmu,jeki ji da damuwarki”

“Sannu sannu dai bata hana zuwa,kuma *HANGEN DALA BA SHIGA BIRNI BANE*  daga haka ko waiwayowa ta dubesu batayi ba ta dauki diyarta dake bacci tafice,nan suka dasa yi da ita,wanda daga bisani suka watsar kuma sukaci gaba da sauraren labarin da jamila take basu,wanda baqaramin dadi yakewa rufaida ba da sauran masu ra’ayi irin nata.

_muje zuwa masu karatu_👁️‍🗨️👁️‍🗨️ *HANGEN DALA*👁️‍🗨️👁️‍🗨️

       _Ba shiga birni ba_

©️®️ *Safiyya Abdullahi Musa Huguma*

*BABI NA BIYAR*

       Aqalla ya kusa minti ashirin tsaye gaban mudubin yana dudduba kanshi yaga inda baiyi ba a jikinsa,shaddace ‘yar ubansu ya saka sky blue,ba abinda take sai sheqi da walqiya,hakan hular kansa itama babu abinda take sai daukar ido,komai na jikinsa daya sanya mai tsadane,kasancewar jin kansa da yake yaudin rana ce ta musamman,kuma yanason ya fitar da rufaida kunya ita da qawayenta ranar dinner din kamar yadda tace.

Wayarsa dake gefe ce tadauki burari,da hanxari ya dauka yaduba,rufaidan ce cikin hanzari ya daga ya kara a kunnensa,yayin da fuskarsa ta yalwata ta kuma wadatu da fara’a kamar wanda aka yiwa albishir an ‘yantashi daga wuta

“Dear…inata jira fa”

“Karki damu baby ina kan hanya,ganinan zuwa karki fushi don Allah,yanzu ba lokacin fushinki bane kinsan ya….” Maganarshi ta maqale sanda yaga shigowar mmn amir dakin.

+

Kanta tadauke kamar bataji abinda yake fada ba din na,shi yasa sam bataso ma shigowa dakin ba a irin wannan lokacin donta kaucewa ganinsa da kuma kaucewa ganin abinda zai motsa mata kishinta,saidai ba yadda zatayi Allah ya qaddara saitaji din.

Hakanan ya diririce,yar kunya ta saukar masa,saiya hau kame kame

“A’ah,mmn amir ba zaku bane?” Murmushin qarfin hali tasaki tana zama gefan sabon gadonshi sakamakon nauyin da takeji cikinta yayi,wanda ta tabbatar an sauya gadonne saboda amarya,saidai bata taba nuna masa ta gane hakan na,mmn ummi ce tayi qaura da kwana a dakin,tace dacan bai sauya saboda su ba saidon wata,to tabar kwanan dakin,tanajinsu amma bata saka musu baki ba

“A wannan yanayin da nake ciki hutu nafi buqata aiko?” Ta fada don ta baiwa kanta kariya,don tanajin koda ace lafiya lau take bataga abinda zaya kaita wajen bikin ba,kai yashiga kadawa

“Hakane kam,haka ne,Allah ya raba lpy”

“Amin,dama hajiyace tace kafin ka fita ka bada sauran kudin cefanen abincin wuni,saboda ba lallai ka kwana gida gobe ba ko saboda baqi,da sassafe kuma za’a je ‘yan kaba a siyo kayan miyan”

“Toh…ba damuwa” ya saka hannunshi cikin aljihu ya fito da sabbabin kudi wanda ya tanada saboda liqi wa amaryarsa ya irgo ya bata,hannu biyu tasa ta amsa kana tamiqe ranta na mata suya,zuciyarta na zafi amma tana qoqarin ganin ta danneta ta hana mata tasiri,a hankali ta juya tafice,saiya bita da kallo kunya da tausayinta na ratsashi.

      Dakin mmn ummi tawuce donkai mata kudin saboda ita hajiyar tace ta baiwa saboda ranar tafado ranar girkinta.

       Zaune ta can uwar dakanta,saman gefan gado tama fuskantar mudubi,saman gadon baje yake da kaya kala kala,daga na kwalliya zuwa na sakawa,da alama ta bajesu ne tana zaben wadanda zata sanya ne,ta kuma gama zaba din,don lace ne ta wareshi gefe hadi da mayafin da takalmi masu tsini,awarwaraye xuwa sarqa da dan kunne.

      Cikin mamaki mmn amir ya qarasa shiga dakin gamida sallama idanunta a kanta,daga kai tayi daga shafa jambakin da take tana amsa mata sallamar sannan ta sake maida kanta,ta mudubin mmn amir take kallonta,tasha makeup sosai wanda tajima rabonta dataga tayi kwalliya irin haka

“Da alama fita zakiyi ko?” Mmn amir ta tambayeta cikin shakku,da mamaki ta waiwayo tana dubanta

“Ya kike tambayata kamar bakisan meke faruwa ba,wai tsayama,ba zakije bane banga alamun kin shirya ba?” Kai mmn amir ta girgiza cike da mamaki,saboda abinda yafarun kafin yau bata tsammaci mmn ummi xatace zataje partyn ba.

Rufaida ce ta rarrabawa qawayenta number wayar mmn ummin suke kiranta suna zaginta tun randa sukayi hatsaniya da rufaidan ta wayar bbn amir din,a rana sai a kirata sama dasau talatin,data gane sune tayita mita har kunnen bbn amir din,toya danyiwa rufaidan magana,tace yace tana bata haquri,a hado da katin dinner guda biyu tace abasu tana gayyatarsu ai duka mijinsu ne.

STORY CONTINUES BELOW

Sam hakan baiwa mmn amir ba a nata tsarin,amma ga mamakinta saitaga mmn ummin yanzun na shirin zuwa

“Yanzu keda gaske kike zuwan xaki?” Sake waiwayowa tayi ta dubeta

“Qwarai kuwa,aiso nake naje naga shegiya da qawayenta,kuma na tabbatar zuwana zai quntata musu,ya hana bbn amir rawar gaban hantsi,sai naga tunqwal uwar daka”

“Kiga tunqwal uwar daka ko ko gano abinda zai tashi hankalinki ya hanaki barci?” Mmn amir ta fada cikin ranta,don tasan wanda yayi nisa bayajin kira,koda ta gaya mata baji zatayi ba,saboda haka ta aje ajiyar zuciya tana miqa mata kudin hannunta

“Allah ya kyauta,gashi inji hajiya tace zata kiraki” kudin ta harara kafin daga bisani ta amsa

“Nifa ku daina sakani cikin wannan sabgar taku,wadan nan sabbin kudinma da alama amaryar xai baiwa ya tsakuro a ciki ko?”

“Bansani ba wallahi,saidai idan kun hadu ki tambayeshi” baki ta tabewa mmn amir din sannan tace

“Yanzu ba zakije din ba?”

“Saikun dawo Allah yasa ayi lafiya a gama lafiya,amma ki dauki ummi kawai basai kinje da yaran ba bare su bata miki kwalliya”

“Kin kawo shawara kuwa” ta fada har cikin zuciyarta,ita kuwa mmn amir tayi hakanne saboda kada aje a tafka wani abun kunyar gaban yaran,batason duk wani abu da zai sakawa yaran negative tunani kan iyayensu ya dinga giftawa ta idanuwansu.

     A tsakar gida akayi clashing da bbn amir da mmn ummi,sai aka hau kallon kallo,kowa da abinda yake saqawa a ranshi,ran mmn ummi fal kishi take dubanshi,ko ran aurenta gani take baiyi kwalliya irin haka ba,yayin da gabanshi ya fadi,yayi tsammanin ba zataje na kamar yadda mmn amir tace,yanzu ya zaiyi kenan?,ga rufaida nacan tana jiranshi,duk saiya daburce,duka basirarsa tadauke

“Na shirya” ta fada tana tsareshi da idanu

“Toh….toh,ina zuwa” ya fada yana juyawa da sassarfa yafita daga gidan.

Daya daga cikin abokansa yakira ya gaya mishi abinda ke faruwa

“Kaga kasan ya za’ayi?,bari nazo na tuqaku,idan yaso sai aje a dauko rufaidan ka zauna dasu duka a baya nina kaiku wajen” dan jim yayi saboda yana tunanin yadda zata kaya,yasan yadda rufaida taci burin lokacin nan

“Yanzu hakan xa’ayi?”

“Kana da wata mafiyar ne bayan wannan?,idan akace za’akai wata sannan axo a dauki wata za’a bata lokacine kawai”

“Shikenan,sai kazo”

Cikin minti ashirin murtala abokinsa ya iso ya daukesu a motar,suka zarce gidan kwalliya inda tacan za’a dauki rufaidan.

Yana zaune a cikin motar yakirata yace gashinan ya iso ta shaida masa gata nan fitowa,a sannan anata kiciniyar rufe mata zip din gown dinta,saita aika qawarta ta sanya mata jakarta da kayan data cire cikin motar kafin tafito.

Da sauri xahra ta dawo

“Ke rufaida?,garin yaya,naga kamar bashi daya bane,shida wata mata ne harda yarinya a hannunta”

“Mata kuma?,yarinyar hannun tata macace?”

“Eh ba zata wuce shekara biyu ba” wani mugun ashar rufaidan ta lailayo ta maka

“Amma bansan matar nan jaka bace sai yau,zuwa zatayi wajen kenan?,lallai lallai yau zatasan da rufee take zancan,rabi’ah qyale rigar nan basai kin zugeta ba,shi zai qarasa zugewa da kansa” ta fada tana qwace jikinta,saita ciro wayarta daga jaka ta kirashi,bugu daya ya daga,ta narke masa sosai

“Kaga kasa qawayena sunatamin dariya wai bakaji dani tunda baka iya shigowa ciki mu fito tare” sosai ta rikitashi,saiya hau kallon mmn ummi dake qame a gefe ta gefan idanu

“Haba dai?,bari naxo to” ya fada yana kashe wayar

“Ina zuwa” kawai yace musu ya fito,saiya zagaya gefan murtala ya masa rada a kunne sannan ya wuce.

Tare suka jero shida ita,mmn ummi ta juya don gyarawa ummi xama a jikinta ta hangosu,wani abu taji yariqe mata wuya,ta zuba musu idanu sanda suke tahowar,sarai rufaida taga cewar ta gansun,hakan ya sanya tasaka hannunta cikin na bbn amir gami daci gaba da janye masa hankali har suka kawo bakin motar,idanunta nakan maryam din a fakaice,don babu laifi kwalliyar datayin ta mata kyau sosai,bata tsammaci ta iya ado yakai haka bama.

Shiya soma bude murfin motar yashiga sannan rufaidan

“Thanks my zuma” rufaidan ta fada tana kashe murya,murmushin yaqe yayi saboda mmn ummi dake motar,cikin tabara saikace qaramar yarinya soma tittirjewa

“Shine kayi shuru ba amsa?,wallahi kaci bashi,zaka sani”

“Yi haquri karki tasarmin yarinya” mmn ummi ta fada cikin matuqar tunzura,tanajin zuciyarta kamar zata fito,saita dan dago tana duban mmn ummi fuskatta cike da murmushin cusa takaici

“Au,ayyah antyna,kiyi haquri ai bansan kina ciki ba,ina yini?” Ta gaidata tana jefa mata wani kallon raini.

STORY CONTINUES BELOW

Lallai rainin hankalinta yakai,ita zata faki idanun bbn amir ta dinga jefawa kallon banza,sannan ta gaidata daga bisani,dauke kanta tayi tayi banza da ita,sai bbn amir din da baisan me ake ba ya waiwaya yana duban mmn ummin

“Ana gaidaki fa maryam” juyawa tayi ta jefawa  rufaidan harara da kuma kallon banza sannan tace

“Lafiya” sama sama cikin shan qamshi,hakan ya batawa rufaidan amma saita share saboda tasan cewa lallai zata fanshe.

“Zugemin dear don Allah,tun daxu muke fama amma yaqi” sai kuma ta dubi mmn ummi

“Ki haquri anty zan dan ari mujinmu xai rufemin zip” wannan qaton asharne yazo bakinta,amma wanzuwar murtala a wajen yasa ta kasa furtawa,don tana ganin mutuncinsa kamar yadda shima yake ganin mutuncinta,hakanan tanajinsa yana zuge mata zip din tana wani shagwaba gami da cewa

“Yimin a hankali dear da zafi”.

Maganar murtala yasanya mmn ummin taji kamar ta ciro zuciyarta

“Malama rufaida wannan shagwaba ai a bari mudan kauce ko?”fari tayi da idanu,maganarsa ji tayi kaman an qaramata qaimi ne

“Kai haba malam murtala,normal nefa,wannan aiba wani abu bane,na saba indai ina gaban dear,wani abun aisai an shiga daga ciki wannan kam ba wanda zaiji ba kuma wanda zai gani sai wanda yakai ido ko kunnensa”

“Hakane kam” ya fada yanason rufe maganar don ya fara shanshano wani abu.

Sanda suka fara tafiya qawar rufaida na gaba,hira suke ita da qawar tata suna kwasar dariya abinsu ganin kamar bbn amir din hankalinsa ya kasu kashi biyu,duk da tayi qoqarin janyr hankalin nasa donta cusawa mmn ummin haushi.

Suna gab da shiga wajen taron mmn ummin ta dora masa ummin datayi bacci saman cinyarsa

“Dan riqemin ita bari naje na kama ruwa nadawo” ta fada tana balle murfin motar tafice abinta,abun ya batawa rufaida rai sosai,don su kawai ake jira aga shigowarsu,ga qawayenta daga can qofa suna tsaye sun shirya kansu suna jiran shigowar tasu,sanda tasoma masa qorafin sunbar mutane na jiransu saiya dubeta

“Komu shiga ta tadda mu”

“Kan ubancan kayyasa” ta fada cikin ranta,a ranar auren nata,ranarta rana ta musamman kawai saiya wani sungumi ‘ya su shiga dakin taro da yarinya a kafada,dan hoton da zatayi na amarya a kafadar ango shikenan yasha ruwa yake nufi ko kuwa,sam ba xata lamunta ba.

Wayarta ta dauka ta turawa zahra dake zaune gaban mota tex,ba’afi minti biyar ba zahran ta juyo cikin nuna kulawa

“Ita kanta babyn kidan gurin nan zai tasheta,gashi da alama taji dadin baccin,ko zaka kawota na sami zani na goyata ta kwanta sosai?”hakan sai yaga kamar yafi,hakan ya masa,saboda haka zahra ta zagayo ta amshi ummi,yayin da su kuma sukabi ta cikin ayarin masu tarbar amarya da ango suka dunguma dakin taron.

Sai data tabbatar ta bata lokaci me yawa sannan tafito daga inda take boye,dab da zata wuce securityn dake wajen taji ance

“hajiya,ko wannan diyarki ce?” Da sauri ta waiwayo,saiga ummi kan kafadarsa tanata baccinta,wani irin bacin rai take taji ya sauko mata,ranta yabaci sosai,har wani daci daci takeji saman harshenta,qarasawa tayi ta amsheta tana tambayarsa wanda ya bashi ita

“Watace ina tunanin qawar amarya ce”

“Na gode” tace dashi tana amsar ummi,cikin bacin ta durfafi dakin taron tana qiyasta cin mutuncin da zata yiwa bbn amir da rufaidan ma gaba daya,ita zai wulaqanta?,ya bada ‘yarta kuma ‘yarsa ajiya?,yana nufin budurwarsa ta fita tafi ‘yarsa?,ashe haka bbn amir din yake sai yanzu ainihin kalolinsa suke dake bayyanar mata,lallai da gaske,bataga laifin matan da suke cewa duk wadda ta riqi namiji uba ta mutu marainiya,da gaskene namiji hankakane,gabansa fari bayansa baqi,ko a mafarki bata taba tsammatar haka daga baban amir ba,ta zaci ko a fuska kadai ta nuna batason abu ya barshi kenan har abada,ashe ita biqin jegon jaka takeyi.

Gab da xata shiga hall din daya daga cikin samarin dake gadin qofar yasa mata hannu

“Hajiya ina zuwa?” Daga kai tayi tana dubanshi cikin mamaki

“Ciki mana,ina zan shiga idan ba nan ba”

“Saidai ki koma gaskiya,an hana shiga”

“Kamar yaya?,kasan me kake fada kuwa?,kasan wace ni?” Dariya taga sun sanya gaba dayansu bayan sun hada idanu

“To hajiya ko wacece ke kuwa saidai ki haqura ki koma”.

Nan ta tsaya musu bayani amma suka watsar da ita a wajen sukaci gaba da hirarsu,abinda yasake bata haushi yakuma daure mata kai shine bayan ita wasu da yawa sun shige,ta musu magana sukace sudin ai an gayyacesune ansan da zuwansu,wani azababben bacin rai yadinga cinta,kunyar yadda suka tozartata ya kamata,saita koma inda suka aje motarsu,abin takaicin a rufe take,murtala kenan shima yana ciki.

Wayarta taciro a gaggauce tasoma kiran bbn amir,lallai ba shakka dukkansu saisun gane kurensu,da saninsa kenan za’a wulaqantata?,ta kirashi a qalla ya kusa sau ashirin saidai bai daga,kasancewar yawa da qarfin hayaniyar dake wajen ba zata barshi yaji ba.

Kamar zata saki kuka haka ta rungume ummi ta soma takawa zuwa titi donta samu abun hawa ta wuce gida,don ba zata iya zama har sai an tashi ba,bacin ran da takeji ita kadai tasan irinsa,inda Allah ya taimaketa da jakarta ta fita,da a cikin motar aka kulle batasan ya zatayi ba.

Kai tsaye dakinta tawuce ba tare da kowa yasan tashigo ba,yaran duka suna dakin mmn amir sunma yi bacci abinsu,kayanta tasoma cirewa tana watsarwa,jin zuciyarta take kamar anyi gobara,xani tasamu ta daura ta zauna jiran dawowar baban amir.

Awa guda harda rabi wayarra tasoma ruri,data duba saitaga baban amir ne ke kira,wani mugun tsaki taja,tanajin wayar harta gama rurinta ta katse,ya sake kira har sau biyu amma wayar bata isheta kallo ba bare ta daga.

Qarfe sha biyu da rabi na dare yashigo gidan,sanda yarufe qofar tana jinsa,miqewa tsaye tayi tana sauraren qarasowarsa.

A qofar dakinta yaga takalmanta,hakan ya alamta masa ta dawo kenan

Dakin mmn amir yashiga ya taddata sunyi bacci duka ita da yaran,yau duka yaranma na dakin,mazan na falo ita da matan suna uwar dakinta saman gadonta,saiya koma da baya ya rufe musu qofar yadda ya ganta ya durfafi dakinsa.

Yana tsaka da cire shaddar jikinsa ta bankado labulen tashigo,saiya daga kanshi yana dubanta tare da karantar yanayinta,har saman fuskarta takejin zafi saboda bacin rai,ta tsaya gabanshi tana dubanshi.

“Basai kayi haka ba zaka tabbatarmin da cewa kai namiji ne,lallai ka nuna halinku da ainihin kalarku,jibril kai munafiki ne maciyin amana da zakaci mutuncina,ku hada baki da budurwar da zaka aura ku wulaqantani,nayi nadama da danasanin aurenka,ba abinda zance tsakanina dakai sai Allah ya isa!” Ta qarashe fada cikin daga murya da zafin rai,daidai lokacin da wayarshi ta dauki ruri,hannu yakai zai dauka tayi hanzarin rigashi kana ta daga tasa handsfree ganin sunan rufaida

“Dear,na manta kayana dana cire a motarka”

“Allah wadaranki kwarkwasa fidda me giji,baqar daga qarshenki ya kusa zuwa” ta fada tana katse kiran,sannan ta daga wayar zata kwadata d qasa,duk kuwa da cewa tasan tsadarta sarai,da hanzari ya tsaidata

“Karki soma,bani wayata!” Ko kadan bata saurareshi ba ta daga wayar ta makata a qasa,take ta tawarwatse saman tiles din.

Cikin bacin rai ua durfafota,zaginsa da fasa wayar suka hadu suka masa zafi sosai

“Idan ka iso karka barni da raina” ta fada tana tsaye qyam tana jiran qarasowarsa,yana isowar kuwa ya dauketa da wani lafiyayyen mari daya sanyata sakin qara saboda yadda ya ratsata,take rigimar ta sake zama sabuwa,ta soma masa jaye jaye cikin dakin naduk abinda hannunta yakai tahau bannatarwa.

Wannan qarar ita tatashi mmn amir,cikin tashin hankali ta fito daga dakin  ta nufi dakin bbn amir din inda tajiyo hayaniyar tana tashi.

Daidai lokacin daya sake daga hannu xaikai mata mari mmn amir tashiga tsakani cikin hanzari,wanda kadan yarage yasameta

“Bban amir,meye haka?,meya sameka?”

“Ki qyaleshi ya aikata abinda yayi niyya,zai auro wata dama babu abinda bazai aikata ba!” Mmn ummi ta fada da madaukakin harshe,fuska jazur,saita waiwaya tana dubanta sanda bbn amir yace

“Idan bata ficemin a daki ba zan aikata duk abinda yazo raina” qin fita tayi sukaci gaba da sa’insa,harsai daya kusa sake kai hannu jikinta sannan mmn amir din tayi nasarar fitar da ita.

Cikin fushi yake furzar da iska me zafi,yasamu gefan gadonshi ya zauna yanajin yadda kanshi ke sake daukar caji.

Gefan gadonta ta zaunar da ita sai kuma mmn ummin ta fashe da kuka tana rufe fuskarta,ji take gaba daya duniya ta mata zafi,kamar duk wata qofar walwalarta da farinciki an tosheta,tsayawa kawai mmn amir tayi tana dubanta,tome xata gayawa maryam?,kome zata gaya mata ta jima da gaya mata shi,ita kanta tagaji da ganin wannan bala’in,tayi a qalla minti ashirin tsaye a kanta kafin tace

“Allah ya kyauta,ya sawwaqe” ta juya tafita daga dakin.👁️‍🗨️👁️‍🗨️ *HANGEN DALA*👁️‍🗨️👁️‍🗨️

       _Ba shiga birni ba_

©️®️ *Safiyya Abdullahi Musa Huguma*

*BABI NA SHIDA*

     Tunda safiyar garin asabar ta waye tasake shiga fita hayyacinta,tunda ta idara sallar asuba ta kasa komawa bacci,sai zirga zirga da take tsakanin tsakar gidan soro zuwa nata dakin,idanunta kacokam yana kan dakin baban amir,wani mahaukacin kishi takeji,yanxu nan da wasu awanni kenan yaxama nasu su uku?,tashin hankali,saita dora hannunta aka tana neman inda zata sanya zuciyarta da ranta taji dadi,wani irin radadi da zugi gamida qunci takeji cikin zuciyarta,saita dauki wayarta ta kirayi hafsat.

+

Bugu hudu ta daga

“Ya akayi mmn ummi,mun tashi lpy”

“Babu batun tambyar lafiya game dani,tunda kin san babu ita,yaushe zaki shigo,wallahi hafsat jin gidan nan nake kamar wata qiyamata ko lahira”

“Karki damu ina sallamar babansu minal zan shirya na taho”

“Don Allah karki dade”

“In sha Allahu” aje wayar tayi tana furxar da iska daga bakinta.

Wayar tatace tasake ruri,data duba sai taga lambar qanwarta ce,ba jinkiri ta daga sai taji muryar mahaifiyarta,kuka ta sanya

“Meye haka maryam?”

“Umma yaune daurin auren fa?”

“Sai kuyi haquri ai,haka Allah ya dora muku”

“Don Allah umma kixo,don Allah”

“A’ah,nikam bazanzo wannan gidan naku ba,zandai turo miki ruqayya da zakiyya,sai yayarku duka zasu taho tare”

“Toh umma”

“Zasu taho miki da saqo,saiki sawa ranki haquri,tunda haka Allah ya dora masa” daga haka sukayi sallama,saita danji sanyi da maganar da sukayi da ummantata.

Qarfe takwas tasoma jin motsin yaran a tsakar gidan,tun cikin satin suma yaran ta sallamasu gaba daya,mmn amir ce keta hidima dasu,hattasu abun ya shafesu,ita kuwa maman amir ko a jikinta,saboda kai kawon yaran da kula dasu da takeyi ya dauke mata hankali gami da debe mata kewa da bacin rai,idan tana tare da yaran sai taji ta manta da wasu abubuwan.

Miqewa tayi ta isa bakin window tana leqen abinda yake faruwa a tsakar gidan,mmn ummin ce zaune saman kujera ‘yar tsugunno,gabanta sabbabin shaddodine ruwan omo,saman cinyarta wasu daga wandunan yaranne tana saka musu tazuge,mubarak na tsaye a kanta da alama yayi wanka ya shafa mai yana jiran ta gama saka masa tazugen tabashi ya saka,yayin da mmn amir din ke aikin tana gyarawa  hanifa wankan da takewa usman.

Wani baqinciki da bacin rai ya kamata,wato har wani anko ya yiwa yaran na xuwa daurin aurenshi kenan,ita batama sani ba?,kafin tayi kowanne yunquri baban amir din yayi sallama yashigo gidan,hannunshi dauke da wata shaddar kalar ta yaran,da alama tashice ya amso.

Qurawa fuskarshi idanuwa tayi sanda yake qarasowa gaban mmn amir,fuskar da ada babu wata fuska da takeso da qaunar gani amma a yanzu babu fuskar data tsana take jin haushi da takaicin gani irinta

“Sannu da aiki maman yara” ya fada yana murmushi,har cikin ranshi kuma yanajin dadin yadda take shirya yaran zasu daurin auren tare dashi

“Yauwa” ta fada ciki ciki fuskarta sam babu wannan fara’ar daya saba gani,duk sai yaji jikinsa yayi sanyi,tayi qoqari matuqa kuma tana kanyi,yasani cewa baiwa Allah yayi masa da uwar gida,wadda ta tsaya kai da fata wajen ganin ta hade kan gidan waje daya,ya tabbatar da maryam ce uwar gidansa tofa sai abinda hali yayi,yasani sarai cewa suk maigidan da yayi rashin dacen uwar gida toya kade ya gama yawo,duk wadda zai aura daga baya mawuyacine idan batayi koyi da wasu dabi’u nata ba,uwar gida itace ginshiqin gida,itace kuma kamar turken mai gida da dukka wani ahu daya mallaka,idan ka dace a ita saika godewa Allah.

Yanayin dayaga fuskarta yasa ya gaza wucewa,saiya soma kame kame,inda daga bisani yac”wannan zaman bazaki gaji ba?,kawo tazugen na qarasa saka musu kije ki huta”kai ta kada

“A’ah,barshi kawai,aiba lokacin hutu bane yanzu koda naso na huta din” haka ya tsaya yana ci gaba da tayata gyara kayan yaran har kowa ya sanya nashi sannan ya shige dakinsa donya shirya shima,ta bishi da kallo tanajin wani bacin rai da kishi yana taso mata,ta dauke idanunta taba karanta “hasbiyallau la ilaha illa huwa,alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azim”.

STORY CONTINUES BELOW

Mmn ummi dake bakin window din tana kallonsu ta saki labulen cikin tafasar zuciya,wato ta fuskanci wani dama dama yake da mmn amir,itace banza kenan?,fushinta banza farincikinta banza?,anya ko matar nan haka ta zauna?,sai wani sashe na zuciyarta ya gargadera,don tunda suke da mmn amir din nata taba ganin wani abu guda daya tattare da ita daya sata shakka ba,abu dayane tasan cewa tana da yawan azumi kamar ma bata damu da abinci ba,hakanan tana da yawan tashin dare harta dinga zargin ada wani abu take cikin daren,saita gane sallar dare ce.

Sai data zauna saman kujerar sannan ta qwalawa yaran nata kira da sunayensu daya bayan daya,usman ne ya soma shigowa

” gani umma”cikin dakinta ta nuna mas”shiga ka cire wadan nan kayan ka samu wasu cikin kayanka ka saka”dum yayi yana dubanta sannan kuma yace

“Amma umma,wajen daurin aure zamuje”

“Iyee,ni kake gayawa wajen daurin auren kishiyar uwarka zakaje?,to shiga kayi yadda nace maka tun ban tashi na zazzabga maka mari ba” hakanan yaron yashige ciki sum sum,ya sauya kayan yafito,zai fita ta tsaidashi ta nuna masa saman kujera

“Zauna nan” ta fada tana dubanshi,haka yakoma yazauna,yayi lakur saman kujerar har zuwa sanda usman yashigo.

Cikin murna yana nuna mata shaddar jikinsa

“Umma,kalli sababbin kayana zamuje unguwa mu dasu abba dasu ya amir”jawoshi tayi da sauri sannan tahau tube mishi kayan,saiya riqe rigar da hannunsa yana kallonta

“Nidai umma karki ciremin,karki batamin kwalliyata,mama ce ta sakamin unguwa zamuje”

“Unguwar ubanka ko?,maza ni kama min bakinka a nan” yaro da baisan hawa ba baisan sauka ba,ganin tacire kayan da gaske kuma tana niyyar sanya masa tsofaffi saiyahau kuka da ihu harda tsalle,haushi ya cikata,ta janyoshi tahau duka,tanajin mmn amir dake tsakar gida tana tambayarta lafiya amma tayi banza da ita tashiga takoma saman kujera tayi zamanta tana baiwa ummi da kukan usman ya tasheta nono.

Bai gaji ba yazauna dirshan yaci gaba da kukanshi,har bban amir yagama shiryawa,ya gaji dajin kukan saboda haka ya daga lebulen yashigo yana kallonta

“Me aka yiwa yaron nan ne wai?” Sai idanunsa ya fada kan ahmad dake zaune kan kujera yana rarraba idanu

“A’ah,kai kume me kake a zaune duka ‘yan uwanka sun shirya?,ina kayan naka?” Sai daya saci kallon uwar yaga ta maka masa harara sannan ya maida kallonshi ga uban,usman daya dakatar da kukan ganin shigowar uban shiya bashi amsa

“Abba umma taciremin sabbabin kayana” daga kai yayi ya dubeta,bai tanka mata ba yasanya kai cikin dakin ya debo kayan kayan yaran yadawo yasanya musu

“Karka fitarmin da yarana,babu inda zasu gayyar arna a idi” dai daya kada kansu tana rsaye a bayanshi tana yada magana sannan ya juyo yace

“Idan ‘ya’yankine saiki hanani zuwa dasu ai”

“Ai wallahi kaima kanka kasan na fika iko dasu ehe,kuma ba’a canzawa tuwo suna duk juyin da zamani zaiyi sunanshi tuwo” taci gaba da daga murya tana zazzaga ruwan masifa harya yaran zuwan ‘yar farfajiyar dake gidan wanda anan yake aje motarshi.

Surutun duka suka damu mmn amir,wanda itama kanta a quntace take,ga hayaniyar baqi tasoma jiyowa maza ‘yan daurin aure,wanda ta tabbatar ba za’a rasa mata masu shigowa ba,saita saki abinda take tabar tsakar gidan ta hada ruwa tayi shigarta wanka.

      Tana bakin madubi tana kwalliya taji shigowar maqotansu su biyu,a gurguje ta gama shiryawar tafito ta samesu,suka gaisa sannan sukace sun shigone koda wani aiki

“Ai kuwa akwai,samira naketa jira ta iso,gasu innarma har yanzu basu qaraso ba” abinda za’a rarrage ta nuna musu,sannan tashiga taci gaba da shiryawa.

    Duk da cikin jikinta amma tayi kyau,kwalliyar ta dace da ita,ba jimawa samira ta iso,ita da qanwar ummanta da qannenta biyu da yaransu,nan suka shiga cikin maqotan akaci gaba da aiki.

      Ba’a jima ba innar jibril ta iso itama da qannenshi duka mata,da kanta mmn amir ta tarbesu,tayi musu duk wani abu daya dace sannan sukaci gaba da sabgarsu,kafin wani lokaci gidan yadan soma cika da tashin hayaniya,awa daya da wasu mintuna da zuwan innar hafsa ta iso ita da qannen maman ummi,saida suka soma tsayawa ga jama’ar tsakar gidan aka gaisa sannan suka nufi dakin mmn ummi,wanda tun dazun datashiga dakin ko leqe bata sake ba,kai kace babu dan adam cikin dakin.

STORY CONTINUES BELOW

    Jiddace ta waiwayo ta dubi mmn amir

“Tabdi,wai dama mmn ummi na gidan nan?”

“Abinda zan tambaya kenan nima” innar jibril ta fada fuskarta cike da tsantsar mamaki,sai mmn amir ta rasa amsar da zata basu

“Eh…me yiwuwa ko bataji zuwanku bane”

“Wanne irin bataji zuwanmu ba?,awata nawa zaune a nan,sannan duka yaran ai suna tsakar gida,idanma bataji zuwana ba ai bazata rasa jin muryar daya daga cikinsu ba,ashe duk abinda ake fada kan yarinyar nan na rashin arziqin da take tunda jibril yatashi aure da gaskene,ban gasgata ba sai yau” sababi sosai innar take,mmn amir na tausarta

“Kiyi haquri inna ki mata uzuri,ba lallai taji ba” shine abinda taketa fada tana fatan zata sassauto,bata da abin cewar daya wuce haka,saboda shekarun baya iwar haka ita ake tsinewa ake zaga sanda maryam din ke gab da shigowa gidan,bata da wani katabus bata da abin cewa,babu abinda zatayi tayi fari a idanunsu,sai gashi yau da yake ance duniya juyi juyi wai kwado ya fada a ruwan zafi maryam dince abar zagi

“Jeki kiramin ita” innar tace da jidda,saurin dakatar da ita mmn amir tayi tace

“Bari nayo mata mata magana dakaina inna” saboda tana tsoron kada jiddan tashiga ta tunzurata su raba abun fada,abu yazo ya kwabe,don ita kanta yau ta kanta take,ba zata iya daukar kowanne tashin hankali ba.

    Daga can dakin mmn ummi kuwa hafsa da jamila qanwarta ne suka sanyata tsakiya suna faman lallashi,yayin da taketa faman sharbar kuka duk sanda ta daga kai ta kalli agogo taga lokacin da aka sanya na daura auren harya gota,yanzu kenan abban amir din ya zama nasu su uku?

“Wallahi wannan abun da kikeyi bayi bane yaya,tun yanzu kin karaya gaba daya tun kafin anjima azo kawota?,baki ganin mmn amir ita saikace abun bai dameta ba?” Tabe baki hafsa tayi

“Uhmmm,kinga maryam,ki tashi ki shirya tun kafinma a gane a haka kike zaune”.

     Sallamar mmn amirce ta sanyasu yin shuru,tashigo fuskarta sake tana duban mmn ummi

“hala bakiji zuwan inna ba?”

“Naji,me zanyi mata?,nafito taga na damu ko ban damu ba?,to ta Allah ba tata ba munafuka” sosai maganar ta baiwa mmn amir mamaki,a nata tunanin furfura ko bata tsohonka bace ka girmamata,jamila ma kama baki tayi,daurewa mmn amir tayi

“Amma dakin leqo kun gaisa,kin san idan ba leqowa kikayi ba zata yita qorafine”

“Tayita yi,uwata ce?” Kai mmn amir ta girgiza,sai taga tafiyarta yafi alkhairi akan ci gaba da tsaiwarta,don kada tsautsayi ya debi mmn ummintace zata aikata wani lafazi naba dai daiba a kanta.

    Tabe baki hafsa tayi

“Kekam haryau baki da siyasa,tashi ki shirya din kije ku gaisa ki dawo,saime idan kinje?,gutsurarki zasuyi” da qyar suka lallabata tashirya din kana tafito,saidai duk wanda yakalli fuskarta yasan cewa babu walwala ko fara’a a fuskarta kona gamin gafara,haka ta dinga gaisawa da mutane daqyar harta isa dakin mmn amir.

      A daddake tagaida innar ta amsa itama tana mata wani kallo

“Wato ke isassa ba’a isa kizo ki gaida mutane ba kenan sai an kiraki ko?”

“Banji shigowarku bane,inacan ina lallaba ummi tana rigima”

“To ai yayi kyau” daga haka shuru ya ratsa tsakani,minti biyar taqara ta miqe abinta tafice.

      Da kadan kadan baqi ke zuwa wasu suyi Allah yasanya alkhairi su tafi,wasu kuma su zauna zaman wuni,ko sau daya mmn ummi bata sake leqowa ba tana cikin daki abinta,duk meson su gaisa saidai yashiga.

      Daga can sashen rufaida kuwa lokacin da angon yashigo gaida surukai bayan an gama daura auren idanunta a kanshi,wani farinciki takeji yana ratsata,yau Allah ya cika mata burinta,kunyar ragaggiya ce ko sanda akazo daukan hotuna tsakanin amarya da ango,style take badawa kala kala,har wata kakarsu ta ankara,daga bisani ma tabar tsakar gidan tashige daki ta zauna.

       Kusan duk hotunan da ake musu yaran saida suka shiga,usman da yake qarami yana hannunshi,tun bata lura ba harta lura,sai abun yasoma tsaye mata a wuya,data sake lura sosai saitaga hatta da shaddar jikinsu ma iri daya ce,qwafa taja can qasan ranta,wato bayan iyayensu suma akwai tasu qurar kenan?,zataji da kowa ta raya haka a ranta.

     Saida azahar abbansu yasaukesu a gidan,innarshi kawai ya gaida yafice daga gidan,mmn amir na falon sanda yashigo,saita dauke ido kawai taqi kallonshi tana jin wani kishi na taso mata,ta tsiri hira da mmn ja’afar matar abokinsa,shima daya dubeta saiyaga hankalinta bai kanshi don haka ya juya da hanzari yafice.

       Bangaren mmn ummi kuwa sanda yaran suka shigo ji tayi kaman ta kamasu ta gada da uban tayita duka,shaddar jikinsu ta dinga ganinta kamar daga wuta aka cirota,don haka ta korasu waje tace su bata waje.

*BAYAN AWA SHIDA*

        Tsaye take cikin dakin tana shiryawa cikin atamfa,kayan kwalliyane baje a gabanta tana makeup,zahara dake zaube tana miqo mata abubuwan da take buqata,dakin ya bade da qamshi kai kace barin turare akayi,ba abinda kakeji sai hira da shewarsu,a haka kakar rufaida hajiya kaka tashigo dakin.

      Cikin mamaki take duban rufaida daketa zuba baki rai rai batama lura da shigowarta ba

“Ke aku,samu waje ki zauna” sai a sannan ta waiwayo,ta dakata daga saka dan kunnen da takeyi tace

“Kefa tsohuwarnan kin iya takura wlh” tafadi tana samun waje ta zauna kamar yadda hajita kaka ta buqata,saita itama tasamu waje tazauna tana dubanta

“Duk fitsarar da kike da rawar qafar da kike ina lura dake,to bari na gaya miki gaskiya idanma uwarki bata gaya miki ba,wannan mu a wajenmu abun kunyane aga amarya tana haka,don haka ki kama kanki karkice zaki shiga cikin matansa kina musu wannan rawar kan,idan kikai hakan kai tsaye za’ace ba daga gidan tarbiyya kika fito ba” dariya rufaida ta bushe da ita ita da sauran qawayenta na makaranta dake dakin masu irin tunaninta

“To hajiya yanzu so kike naje nayi ta sussunne kai ina abu kamar banje makaranta ba ko kuwa yaya?,nifa auren soyayya mukayi da mijina,kuma babu wadda zanwa biyayya tunda yadda suke matanshi haka nake,haba hajiya nafa fisu da komai,idan ba’a bini ba ai kuwa bi ba’ace nabi mutum ba” ta fada tana juya idanu,sai hajiya ta kama baki ciki mamaki

“Ni tarasulu,ke rufaida akul ki shiga hankalinki,mu idan muka aurarwa mace miji kunyarta mukeji,mukan jima bama iyama hada idanu da ita saboda abune me nauyi da girma,hakanan abokiyar zamana harta rasu ke har yanzu da nake miki maganar nan ban iya fadar sunanta yaya nake ce mata,haka itama bata taba batamin raiba ko sau daya,suna na kuwa nima ban tabaji ta fada ba,saida nayi haihuwar fari take kirana da sunan dana” sake kwashewa tayi da dariya har suna tafawa da zahra

“In gaya miki gaskiya hajiya?,wallahi bazan iya wannan rayuwar ba,banma tanadeta ba ko a mafarki,kishiyar zan shiga ina kwantarwa dakai ina yiwa biyayya?,bayan nasan cewa na fita da komai?,ai tsakanina da ita kawai shine nasaita mata hanya ta bani waje na sarara nida mijina,matan nashi gidadawa kada ma uwar gidan taji labari” da yatsa hajja ta nunata

“Ke wallahi ki kiyayi kanki,mu dukka din nan da kukewa kallon gidadawa da haka muka fiku iya riqe miji,me bokon taku ta tsinana muku banda tabarbarewa lalacewa da rashin iya zaman aure?,iyee ki gayamin?” Shuru dukka sukayi saidai rufaida tasan halin mutuniyarta,saita hau lallabata

“Aikin banza aikin wofi,duk bokon da kuke haryau sunqi karanta muku iya zama da miji da kishiya lafiya lau,kunawa aure kallon abu mai sauqi,bayan bakusan cewa *HANGEN DALA BA SHIGA BIRNI BA* ne”

“Kiyi haquri hajja nima tsokanarki kawai nake,zauna ki gayamin ina saurarenki” ta fada don kada hajjan ta ballo mata ruwa,ita ta haifi babanta tasan kuwa yanzu idan zance yashiga kunnensa sai ya bata mata ranta,fur hajjan taqi zama tace taje tagwada bokon tata.

        Dariya sosai ta dingayi suna tayata sanda hajiyan tafita,haka tajuya taci gaba da diban kwalliyarta.

        Lullube amarya rufaida take cikin shigar atamfa da yalwataccen mayafi kamar yadda akasan kowacce amarya,tana riqe hannun qanwar mamanta wadda rafito da ita daga dakin mamarta zuwa dakin dakin da dangin ubanta suke don yi mata fada,qasa qasa tace da zahra dake kusa da ita

“Ke nifa na gaji da wannan qabli da ba’adin nasu,wai meye baka sani bane a auren nan da aketa damunka?,kwanciyar aurece kawai fa ta rage,kosu wlh saina koya musu wani abun,amma sun dameka da zantattuka wani sai haquri sai haquri suke cewa kamar ance musu anmin mutuwa” dariya zahra ta kwashe da ita cikin qunshe bakinta kana tace

“Salon bata lokacine kawai da al’adar da suka daukaketa,kedai kawai ki bisu a haka suyi su gama mu qara wuta” da wannan zancan aka qarasa dakin,sun mata nasiha daidai gwargwado,wanda wajen rufaida kallonta take a matsayin ita da babu duk daya,ta kunnen data shiga haka take fita ta dayan,har suka gama aka tattaro aka fito da ita don danganata da gidanta.👁️‍🗨️👁️‍🗨️ *HANGEN DALA*👁️‍🗨️👁️‍🗨️

       _Ba shiga birni ba_

©️®️ *Safiyya Abdullahi Musa Huguma*

*Haske Writers asso*💡

*BABI NA BAKWAI*

     “Allah ya kawo mu gidan gimbiya rufaida,lokaci yayi,gamu gidan rufaida,mata mai cikakken iko a gidan jibrila” wata zabiya dake cikin tawagar amarya taketa faman fada tana sake nanawatawa,gami da hadawa da guda mai shiga tsakar ka,su kansu wasu daga cikin ‘yan uwan amaryan basusan wace ita ba,suna dai biye ne,har suka wuce farfajiyar gidan zuwa babban tsakar gidan,wanda ke dauke da varender da dakuna manya a jere.

+

“Allahumma la sahla illa ma ja’altuhu sahla,wa’anta taj’alil hazna iza shi’ita sahla” mmn amir take maimaitawa sanda takejin wata faduwar gaba da fargaba na saukar mata

“Uhummm,sun iso kenan” daya daga cikin matan qannenta ta fada

“Da alama” samira ta fada tana dawowa kusa da mmn amir din,qoqarin kauda duk wani surutun masu shigowa da amaryar take daga kunnuwanra,da kauda duk wani furuci da zaya iya fitowa daga bakinsu.

“Na shiga uku,hafsa sun kawota,wallahi gasunan” mmn ummi ta fada tana dora hannuwanta saman ka,hawaye yana balle mata,da sauri hafsan ta sauke mata hannun tana cewa

“Haba don Allah mana maryam,ki nutsu,a haka kikeso su shigo su taddaki?,haba don Allah” hafsan ta fada tana sauke mata hannun data dora din aka,jamila tamiqo mata mayafinta tace ta yafa,don wala’alla suce zasu shigo da ita nan din.

“Ku fara shiga da ita dakin uwar gidan” yayar maman rufaida ta fada sanda taga suna yunqurin shiga da ita dakinta,wani takaici yacika rufaidan,taji kaman ta dakatar dasu,saidai ba yadda ta iya haka tanaji tana gani aka sauya akalarta zuwa dakin mmn amir.

A mutunce suka amshesu,sannan suka gabatar da itawa mmn amir din gamida danqa amanarta a hannunta kamar yadda al’ada ta tanada,cikin matuqar dakiya da nuna juriya mmn amir tace

“Toh,amana abune mai nauyi,amma duk da haka muna fata da addu’ar Allah S W T yabamu ikon riqewa,yashige mana gaba ya kauda fitina” dukka suka amsa da amin cikin yabawa da halayyar mmn amir din.

Ta cikin mayafin rufaida ke tabe baki sanda mmn amir din ke karanto addu’o’i suna amsawa,qaramin tsaki taja qasa qasa cikin ranta sannan ta furta

“Bagidajiya,kawai zata batawa mutane lokaci” sai data kammala suka shafa sannan suka miqe da ita suka fice zuwa dakin mmn ummi,har cikin zuciyarta taji sanyi na sauka sanda take shafa addu’ar,ta saki sassanyar ajiyar zuciya gami da sake maida kanta cikin sabgogi ta hanyar sallama da maqotanta wadanda suka soma haramar komawa gida ganin an kawo amarya.

Idanunta qir a kansu sanda suke shigowa dakin nata,baqiqqirin take ganinsu,kallon da take musu tamkar ganin abokan gaba ne a sansanin yaqi.

1

Wani irin tafasa zuciyarta take,kaman ta tashi ta koresu,amma dole tazauna tanaci gaba da dubansu,saboda maganar da jamila tayi mata tun kafin su shigo.

Yadda sukayi bayani dakin mmn amir haka sukayi mata,zuciya ta ciyota,taga zallar rainun wayonsu,ita za’a baiwa wani amanar kishiya?,duk yadda taso ta danne tayi shuru saita kasa

“Dacan baku bata tarbiyyar zaman gidan miji ba da bazata iya ba har sai kun bada amanarta?” Da mamaki suke kallonta,idanunta qyar akansu tana jiran wata ta tanka musu,ware idanu rufaida dake cikin mayafi take,inama daga ita sai ita tafadi wannan maganar,lallai wannan matar saita gane kurentq,dama tana sane da ita sarai,bata manta daduk wani cin fuska data mata ba kafin shigowarta gidan ,ta kuma ci alwashi ta lashi takobi saita rama,saita bada mata yaji a rayuwarta mai radadi

“Ikon Allah,to adai dinga haquri” yayar umman tata ta fada,sai duka suka miqe tare da rufaidan don barin dakin

“Da ba’a haquri ai da ba’a kai yawar haka ba,da bata shigo bama” ta fada ranta na mata zafi.

Dubanta jamila tayi bayan sun fice

“Gaskiya baki kyauta ba mmn ummi,abu na ‘yan mintina ki barsu suyi su gama su fita shine kika kasa shuru,nikam gida zan wuce” ta fada tana miqewa ta dauki jakarta ta rataya

“Madalla,Allah ya raka taki gona,tunda na taba qanwar umma uwarmu” bata tanka taba tafice a dakin,ta leqa dakin mmn amir da tuni baqinta suka yoye saura ‘yan qalilan suma daketa hada karonsu zasu wuce,sai qanwarta salima da zata kwana gidan donta tayata hidimar gobe ta gidan.

STORY CONTINUES BELOW

Zuwa awa daya gidan ya yoye babu kowa,hatta da amarya sai ita kadai,don qawayen nata duka angon yasa an kwashesu an maidasu gida,don yace bazaiyi wani siyan baki ba,saboda yana bala’in jin nauyi da kunyar mmn amir,bazai iya tsayawa yayita wannan yarintar ba da qawayen amarya ana jinsu,duk da hakan bai yiwa rufaida ba,amma haka ta haqura suka tafi suka barta.

Dukka yaran mmn amir ta sanyasu suka canza kayansu,salima ta gyara musu wajen da zasu kwanta tasaka su sukaje suka kwanta,hatta dasu usman basu kalli qofar dakin mamansu ba,don sunsan qarshen zancan wala’alla kafin bacci ya daukesu sai sunci na jaki.

Dai dai lokacin da amarya rufaida take kewaye dakinta tana dubawa,ba laifi komai yayi mata yadda takeso,duk da tasan cewa data yarda bbn amir din ya raba musu gida to dakin nata sai yafi haka,saidai sam ita bata da sha’awar wani raba gida,tafi sha’awar a hadesun yadda zataji dadin nuna musu cewa ruwa na sa’an kwando bane,wannan ma hakan ya mata.

Babban falo ne mai hade da bedroom,sai wajen dining wanda kusa dashi kuma qofar toilet ne,duk da ita kitchen taso a mata a wajen,duka sauran falukan matan nashima haka yake,gini ne mai kyau wanda yasha tiles da fentin mai kala biyu,kalar da kowacce cikinsu ita tazaba da kanta.

Tana zaune tun dazun inda take,ba inda ta motsa,jikinta gaba daya ya mata nauyi,ga wani ciwon dako ina na jikinta ke mata,hakanan zuciyarta sam babu wani sauran karsashi ko qwarin gwiwa tattare da ita.

A haka taji shigowar baban amir din gidan,tanason ta tashi tabar falon amma ta kasa,a haka harya shigo gidan,sai daya tabbatar ya kulle ko ina sannan yashigo tsakar gidan bakinsa dauke da sallama,shuru tsakar gidan yake,saidai a kacame yake,ko baqone kai zaka tabbatar cewa lallai anyi wani sha’anine cikin gidan.

Idanunsa kan qofar dakin rufaida,wanda yake tarwai da haske kamar yadda dakin mmn ummi yake,sabanin dakin mmn amir da nata hasken baikai nasu ba,da alama ta rage qwayayen dakin nata.

Kai tsaye dakin mmn amir din yanufa,ya yaye labulen bakinsa dauke da sallama,amsa masa tayi a sanyaye bayan ta daga kanta da niyyar kallonshi,saidai ta kasa,saboda wani abu daya takore mata wuya,hakanan taji cikinta yasake nauyi

“Sannu da zuwa” ta furta daqyar tana kuda kanta gefe,idanunshi a kanta yana karantarta ya amsa mata

“Kun yini lpy ya yaran duka?”

“Sunyi bacci” ta bashi amsa a taqaice,shuru daiya ratsa tsakaninsu,hakanan yadinga jin nauyinta,yana tuna wancan shekarun da suka shude a rana irib wannan,kusan hakan tayi masa,yaga zallar kishi da bacin rai a fuskarta amma tazabi yin shurun kamar wannan lokacin,duk sai yaji nauyin tashi yafita din,yana ganin kamar ya cutar da ita a rayuwa har sau biyu,cikin son nade tabarnar kunya yace

“Na tsammaci zuwa yanzu kin kwanta,don nasan kunsha kujiba kujiba ko”

“Yanzu nake shirin tashi” ta fada tana yunqurawa da qyar

“Yi a hankali” ya fada sanda tadan koma baya kamar xata zauna sai kuma ta sake miqewa,ledar hannnunshi yamiqa mata ganin tana niyyar shigewa uwar dakinta

“Babu wani abun da kuke da buqata?” Ya tambayeta yana kallon bayanta sanda take dab da shigewa dakin nata

“Babu komai” ta fada bayan ta dakata ba tare data waiwayo ba

“Haka akeso” sai yasake yin shuru na wasu sakanni sannan yace

“Halima…..don Allah ki kwanta kiyi baccinki sosai kodon abinda yake jikinki,karki sakawa ranki damuwa don Allah”kai ta jinjina tana qoqarin hadiye abinda ke taso mata sannan ta sanya kai cikin dakin.

Kusan sakan goma sannan ya taka ya juya yafice yana jin tausayinta sosai cikin ranshi,ta nuna dukkan wata jarumta da haquri,ba shakka haliman baiwa ce da Allah yayi masa na macen da ba kasafai ake samun irinsu ba,maryam kawai ta zame masa ishara.

Daga nan dakin mmn ummin yashiga,itama da sallamar yashiga,tana tsakar falon tana kai kawo goye da ummi a bayanta wanda ta jima dayin bacci,fuskarta kawai zaka kalla kasan bala’i da tashin hankalin da take ciki.

Dauke kanta tayi sanda taga shigowarsa,qirjinta yaci gaba da zafi,ko sallamar ma bata da lokacin amsa mishi

“an yini lpy” ya fada itama yana zama hannun kujera,banza tayi dashi,saima tasoma tattare kayan dake zaune d’ai d’ai tsakar falon kamar batasan Allah yayi ruwanshi ba,qoqarin danne bakinta take ta hana kanta ruga masa ashariyar daketa yawo saman harshenta,data gama saita wuce dakinta tarufe qofar tabarshi nan zaune.

STORY CONTINUES BELOW

Yasan cewa lallai anzo gabar da duk dauriyarki dole gazawarki ta bayyana,saboda haka baiyi qasa a gwiwa ba yanufi qofar dakin yasoma qwanqwasa mata

“Bude mana maryam”

“In bude inyi uwar meye?,jibril kafice min daga daki wallahil azim idan nafito ba zamu kwasheta da dadi ba,maciyin amana kawai,Allah dai yayimin sakayya” saita rushe da kuka sosai mai fidda sauti,kanshi kawai ya girgixa saiya koma da baya ya aje mata ledar ya juya yafice zuwa sashen rufaida.

Cikin so da qauna ta taryeshi,cike da nuna wayewa da sanin me rayuwa take ciki,hakanan ya biye mata,saidai can qasan ranshi yana mamaki kadan kadan idan tayi wani abun,sabida ko maryam daren farkonsu batayi ba bare halima,daga bisani saiya share shima,komai ya kauce daga ranshi ganin cewa ba wani abu daya tadda tattare da ita wanda ba dai dai ba ko zai saka zuciya ko rai cikin zargi.

Wanka mmn amir tasamu tayi cikin bandakinta sannan tasauya kaya,ganin idanunta yasoye,tunani yana neman hanata bacci,saita dauko qur’aninta da dama kullum bai rabo da gefan gadonta,ta bude wasu shafuka tasoma karantawa,babu jimawa taji bacci yazo mata,idanunta har rurrufewa suke,tasamu ta maida qur’anin batayi wata wata ba taja filo ta kwanta.

Mmn ummi kuwa a iya cewa kwanan zaune tayi,sai zirga zirgan shiga bandaki data sameta saboda tashin hankali,tayi kuka har batasan iyaka ba,haka tazauna tasaka agogo a gaba tana kallo,duk daqiqa daya da zata wuce tana lissafawa gamida qissima yanzu abu kaza baban amir din yake,yanzu yaci ace yayiwa rufaidan abu kaza,saita sake rushewa da kuka,haka takusan kwana,kafin wani lokaci kuwa kanta yadinga ciwo,da qyar gefin asuba tasamu bacci yayi awon gaba da ita cike da tarin baqinciki da quncin zuciya.

Qarfe biyar da rabi yashigo dakin,a lokacin tana zaune saman abun sallarta tana jan carbi,duka yaran sun gama sallarsu sun koma baccin,itama jira take ta gama addu’o’inta takoma ta kwanta din kafin gari ya qarasa wayewa,saboda tasan gidan a kacame yake sosai,gashi yaudin tanason zuwa awo ranar da zata likita ne.

Kallo daya tayi masa ta dauke kai,saidai abun ya bata mamaki,batama tsammaci shigowarsa ba adai dai wannan lokacin,don kuwa zamanin maryam bataga idanunshi ba sai goma na safe.

Shi yasoma gaidata har taji abunma bambarakwai,saita amsa kawai,ya tambayi yaran tace sunyi sallah sun koma

“Sannu da qoqari,Allah yayi albarka”

“Amin” ta amsa tana ci gaba da jan carbinta ba tare data sake tanka masa komai ba,tana kallonshi ya gama kame kamensa sannan ya juya zai fita

“Idan gari ya gama wayewa zanje naga likita” waiwayowa yayi cikin kulawa

“Au…lafiya dai ko?”

“Qalau,lokacin komawa awona ne yayi tun wancan satin ban samu zuwa ba saboda hidima”

“Me yasa zaki fashin zuwa ganin likita?,wannan ai sakaci da lafiya ne,ki shirya da wuri ki barma mmn ummi sauran ayyukan,idan kin gama saiki sanarmin” zataso ya sallameta ne kawai a lokacin basai ta tsaya wani binbinin nemanshi ba,amma batason doguwar magana a yanayin da take ciki,saboda haka tace masa to kawai

Qarfe bakwai ta tashi salima suka shiga gyaran gidan,ita kuma tashiga kitchen tadora abin karin safe,don tasan idan tabiye ta mmn ummi bataqi ranar gidan yakuma yini a haka ba,hakanan uban kowama cikin gidan yawuni da yunwa ba damuwarta bane.

Duk zirga zirgar mmn amir din kan idanun mmn ummi,don tunda tafarka qarfe shida tayi salla bata koma ba,saita koma saman kujerarta dake bakin qofar dakin tazauna ta yaye labulen tana ganin duk wani abu da zai gitta ta tsakar gidan,tunanin abinda zata qirqira kawai take wanda zai fiddo bban amir daga dakin rufaidan da farar safiya,yadda zata cusa mata haushi da takaici.

Ranta a bace takebin mmn amir dake kai kawo tsakar gidan tana hidimominta,ji take kamar ma farinciki mmn amir din keyi da wannan lamarin,qwafa taja haushinta na sake cikata,ita ko wani dan bacin rai bata karanta saman fuskarta ba,kamar ma ba matarshi ba,shine zata wani tashi da sassafe tahau aiki,itakam baiwar Allahn batasan ma tanayi ba,don abinda ta iyakancewa ranta zatayi komaine don saboda yaran da kuma karan kanta.

Sai data gama abun karin yaran sukayi wanka gaba dayansu suka karya,tabar saura a kitchen saboda sauran mutanen gidan,ta kintsa tsaf,tana daga zaune tana karyawa don karta zalunci abinda ke cikin nata,saboda jiya batasamu damar sanya komai a bakinta ba,tunanin yadda zata aika yaran kiran abban nasu take,batason shigarsu dakin

“Amir miqomin wayata” ta fada tana kai kofin tea bakinta,dakinta yashiga yafito mata da wayar ya miqa mata,tasa hannu ta amsa sannan tafara laluben number abban amir din,sau biyu tana kira bata shiga,saita aje wayar taci gaba da karyawarta.

Bayan ta gama ta duba jakarta,taga akwai sauran kudade,saboda haka ta zura hijabinta ta miqe tana duban salima

“Zanje,don Allah ki kula dasu,karki barsu suje ko ina,tunda akwai wuta ga cartoons can dana ware musu wadanda duke kalla ki saka musu,kiyi zamanku a daki,tunda mmn ummi nanan zata kula da sauran komai”

“To saikin dawo” daga haka tamusu sallama tafice ba tare data tsaya neman bbn amir din ba.

Qarfe sha daya nasafe tashiga bandakin dake falonta ta silla wanka,sannan taxauna gaban mudubi ta tsara kwalliya tagani ta fada,ta zabi riga da skert da suka kaamaata cikin kayanta tasanya,ta tura daurin dankwalinta gaba goshi sannan ta dawo falo inda tabar bbn amir zaune yana kallo.

Wani fari ta sakar masa gamida sauya takun tafiyarta,ya buda mata hannayensa yana sakar mata murmushi gamida fasa mata kai kan yadda tayi kyau,ta narke ajikinsa sosai tana zuba mishi shagwaba shi kuma yana tambayarta daren jiya

“Yunwa mafa nakeji dear,su mutanen gidan nan basu iya adana baqonsu ba?”

“A’ah na tabbata akwai abinci a kitchen,may be basason matsa mana shi yasa ba wanda suka aiko,bari naje na duba miki sweet,amma ya kamata ki fita ki gaisa da mutanen gidan”fuska ta yatsine tana jin abun wani banbarakwai,don bata tsammaci zaice haka ba

“amma ai nice baquwa,niya cancanci a gaisar” kai ya kada

“Eh,amma idan kika duba ai kece qarama ko?,keya kamata ki dinga zuwa gaidasu” kan ubancan,yo koshi ita yau bata gaisar ba ballantana wasu gajarabul din matanshi,batason bata plan dinta saboda haka tace mishi

“Ba damuwa,amma yunwa nakeji,bari na qoshi tukunna”

“Karki damu,bari na duba gidan”murmushi ta sakar masa

“kayi sauri kadawo,akwai wani daddadan labari dana tanada maka”

“An gama gimbiya” daga haka ya juya yafice,wani wawan tsaki taja tana yatsuna fuska,gaida matanshi kamar wani a qauye?,koko zamansu take?,itakam ba zata juri wannan iskantar ba wlh,duk wadda ta matsu da ita tashigo ta gaidata.

Dakin mmn ummi yanufa yana don yasan aikin gidan kamata yayi ace yana hannunta,tana zaune tun safe yadda tatashi da kayan jikinta,ita daya cikin dakin daga ita sai ummi itama data gaji da zaman ita daya,tana ta ‘yan qananun rigingimu tana neman wanda zai dauketa ya fita da ita.

Aiko yana shigowa tagudu daga wajen uwar tayo wajen,ya dauketa yana cillata sama yana mata wasa,ko ummin ba’a yiwa wanka ba bare uwarta tasamu yi tana zaune tana dacin rai,sosai ta qureshi da idanu kamar zata gani sauyawar wani abu daga jikinsa,sai kuwa taga kamar walwalarsa ta dadu,fuskarsa ta qara kyau,wani abu ya tokare mata wuya,tsantsar tsanarshi da haushinsa kamar tatashi ta rufeshi da duka haka takeji

“An gama abincin kari ne?” Wata uwar harara ta watsa masa,ta masa kallon sama da qasa

“Na maka kama da wadda zata zauna tana muku girki kuna ci?,toni ba jaka bace nasan inda yakemin ciwo” daga haka tashige daki abinta,baiso kulata bare subar wani abun fadan,saboda haka yajuya yafice zuwa dakin mmn amir.

Suna zaune yaran a nutse duka suna kallo cikin tsafta,ya tambayesu ina mmrsu,usman ne ya amsa mishi data tafi asibiti,saiya juya yana neman qarin bayani wajen salima,ta gaya masa cewa takira wayarshine taqi shiga,shuru yayi kana yasoma qoqarin fito da wayarshi daga aljihu yasoma kiranta,saidai wayar taqi shiga,maidata aljihu yayi yana rayawa cikin ranshi,kishinne yamotsa itama shi yasa taketa shakulaton bangaro da shi,saidai koma meye baiga laifinta ba sam,tayi namijin qoqarin da sai an tara mata dari ba’a samu wadda zatayi abinda tayi ba

“Kuzo muje ku gaida antynku” bbn amir ya fada sanda salima ta gaya masa kayan abincin yana kitchen.

Kowa yasan yaro da zumudi dason amarya,sai suka miqe kuwa dukkansu suka bishi,sai salima kawai tarage,ya soma biyawa ta kitchen ya diba abincin ya baiwa amir yadauka suka nufi dakin rufaidan.

Tana zaune sosai tana shaqar iska dai dai,jiran dawowarshi kawai take tana tsara yadda yau zata haramta kowa ganinsa da kuma walwala cikin gidan,sai taji sallamar yara,ta daga kai da sauri tana dubansu,take duk wata fara’ar dake fuskarta ta bace bat

“Meye hakan?” Take tambayar kanta cikin zuciyarta,zuciyarta na wani iri zafi ganinshi tare da tarkacen yaranshi duka.1

👁️‍🗨️👁️‍🗨️ *HANGEN DALA*👁️‍🗨️👁️‍🗨️
       _Ba shiga birni ba_
©️®️ *Safiyya Abdullahi Musa Huguma*

Haske Writers asso 💡

*BABI NA TAKWAS*

     Amir ne ya qaraso ya dire tire din dake dauke da kayan abincin,ya duqa har qasa ya gaidata,ta bishi da wani kallo tana amsawa da qyar kamar wadda aka cusawa tsumma a baki,tana jin zuciyarta na mata daci,takaici ya cikata.
Duka yaran suka qaraso cikin falon suma,da daya da daya suka soma gaidata,daqyar take iya amsa gaisuwa daya tak,duka tana qare musu kallo a kaikaice,sai taga kowannensu yasamu waje ta zauna.
Dubanta ta maida kan bbn amir,tayi tsammanin zai musu magana su tafi,sai taga sabanin hakama shima wajen zama yake nema dauke da ummi a hannunshi,hakanan dukka hankalinsa yana kansu yana musu tambayoyi kan abinda ya faffaru jiya a gidan.
+
Dif tayi yana shaqar wani baqinciki da takaici,ummi tasoma daga mata hannu taba bangala mata dariya,amma saita dauke kai kamar bataga yarinyar ba,saida babanta ya kula ne yace
“Antynsu,so take ki dauketa fa,kinsan ummi dason yawo kuwa dason a dauketa” yaqi tayi tana qoqarin sakin fuskarta amma sam ta kasa,don bata saba da hakan ba tun asali,bata fiya iya biye abinda kecin zuciyarta ba
“Ki sauko muci abincin,usman ku matso maza aci abinci” ya fada yana saukowa qasan carfet gami da janyo farantin abincin gabanshi yasoma bubbudewa,amir ne kawai yace yaqoshi
“Abba suma bamu dade da gama karyawa ba,tun kafin umma tafita ma” ya fadi kasancewar dukka yafisu hankali da wayo
“Qyalesu suci,kasan hali ai ko sunci abinci idan sukaga zanci sai sunci ko abikaina?” Suka saka dariya duka harda yara matan.
Waiwayawa yayi da zummar sake cewa rufaida tasauko suci abincin sai yaga wayam ba ita a wajen,abinda bai sani ba tun sanda yasoma tattaro kansu suci abincin tamiqe tabar falon
“Ikon Allah,ina antyn taku?” Ya fada yana duba falon
“Tashiga daki abba” hanifa ta fada,saiya dire ummi yace yana zuwa.

Zaune ya sameta gefan gado qafarta daya kan daya tana cika tana batsewa,cikin kwantar dakai da kwantar da murya yace
“Haba amarya wadda bata laifi,ya zaki taso ga yaranki sun shigo gaidaki,ga kuma abinci can bakici ba?” Taso boye fushinta amma saita kasa,taga idan taboye abinda ke ranta kamar ta cuci kanta ne
“Ai gwara nabaku waje kuci sosai ko?” Dan jim yayi cikin mamakin me kalamanta ke nufi,bai gama wannan tunanin ba tadora
“Ta yaya ina amarya ranar farko a gidana zanci abinci da mijina kawai saikaje ka debomin tarkacen yara suxo su cikamin daki,fusabilillahi haka ake?,niwa nayiwa gaka duk cikinsu?” Mamaki sosai ya kamashi,don bai tsammaci jin wannan furucin daga bakinta,sakamakon a baya yadda take haba haba da yaran,har gidansu take sawa yaba kai mata su,sannan idan baizo dasubama zatasa yakira gida da wayarshi a bata yaran su gaisa,saisu kusa cinye masa kudin waya ma suna hira.
“Yanxu rufaida yaran nawa na cikina kika gayawa haka?,ko kunyar idanuna bakyaji?”dubanshi tayi,taga alamun maganar batayi masa dadi ba,amma sai ba zata iya bashi haquri ba,don a ganinta ita akaiwa laifi,maimakon haka ma saita soma qanqanun gunguni,ta maida kanta saman filo ta kwantar
“Nidai bawani mummunan abu nake nufi ba,saidai idan kaine ka fahimci haka”.
Ganin da gaske ba zataci abincin ba yaga bai kamata tun ranar farko haka ta faru tsakaninsu ba,saboda haka ya juya ya fice daga dakin,ya debo mata abincin ya aje mata
“Gashinan saikici anan” miqewa caraf tayi daga kwanciyar ta kamo hannunshi,cikin narkewa kamar maishirin kuka tace
“Wato baka ma damu dani bako?,to wallahi ba inda zaka fita anan zaka zauna kaima muci tare” hakanan yazauna din kodon abinda yafaru daren jiya yana ganin dole ya haqura ya lallabata.
“Ya kamata kije ku gaisa da mmn ummi,mmn amir bata nan tafita asibiti,in yaso zuwa anjima saina ganku kuma gaba daya ko?” Kamar ya soka mata wuqa a qirji haka taji,wanne irin taje ta gaidata don tsabar son ya siya mata raini?,ina laifi ma ita ta leqo?,amma batason wani dogon jayayya muma da abinda zai bata mata amarcinta yadda ta tsarashi,sabida haka tana hadiye bacin ranta haka tamiqe ta isa gaban mudubi tana sake goga hoda,zaya fita tace ya tsayata su fita tare,yace ta taddashi a falo.
1
STORY CONTINUES BELOW

Sai data sake kwalliye fuskarta sannan ta feshe jikinta da turare,ta ciri chewing gum cikin wanda tazo gidan dashi ta jefa a bakinta ta turo daurinta gaba sosai sannan tafito.
Tsaki taja qasa qasa tanajin takaicin ganin har yanzu yaran suna nan,haka suka dunguma gaba daya suka fice.
Tana nata falon tana tsintsince kaya zata soma shara,ranta cike fal da qunci da daci,musamman lokacin data fuskanci yaran sun shiga dakin amarya ne,ta qudira a ranta yau saitayi musu dukan tsiya,ta kuma zauna ta karanta musu kada tasake ganinsu dakinta,idan maman amir tasake to ita tabbas ba zata sakeba bare ta rainata,idanma basuyi wasa ba ko dakin mmn amir din sunbar zuwa bare su shiga dakin wata amarya.
Shine a gaba dauke da ummi,sai rufaida a bayanshi da sauran yaran daga bayanta,tsayawa tayi da ninke zanin goyon ummi wanda ta kwantar da ita dashi dazu saman kujerar tana dubansu.
Rufaida ta hango daga bayanshi,tana qarewa mmn ummin kallo,wadda ke sanye da t.shirt nai kwala harda aljuhu a gaban rigar,a tsaye t.shirt din take babu shape da alamu ta maza ce,sai zanin atamfa sungul wanda daya daga cikin zunnuwan goyon ummi ne.
Murmushi rufaida ta saki tana danne dariyar dake cinta,wani raini na musamman game da mmn ummin ya taso mata,ba shakka dukkan yadda tayi hasashensu haka suke,ta bangaren mmn ummi kuwa kunya da takaici suka cikata,ko a mafarki bata taba tsammatar rufaidan xata shigo dakin nata ba,dako da wasa ba zata taba yarda tazauna ta ganta a haka ba,hannu tasa ta amshe ummin tana cika tana batsewa,yayin da rufaida tazauna hannun kujerar mmn ummin tana qarewa falon kallo,babu wata qazanta tattare dashi,saidai da alamu bata damu da gyaran dakinta da sassafe ba a matsayinta name yara
“Mun tashi lpy mmn ummi” rufaidan ta fada tana murmushi wanda ita kadai tasan manufarsa
“Lafiya”
“Ya kwanan yara kuma?” Takuma fada da wani salo na daban
“Qalau” ta amsa mata tana cirewa ummi wandonta daya jiqe da fitsari.
Bbn amir ne yajuya zai fita rufaidan ta miqe
“Tsayani mana dear,bacci fa nakeji” daga haka tabi bayanshi,wani abu yatsaya mmn ummi a ranta,tabusu da kallom harara da ashariya cikin zuciyarta,sai usman yamiqe yana cewa
“Abba tsayani zani” finciko usman din tayi da hannu daya,ya saki qara kuwa saboda yaji zafi sosai
“Dakin uwarka ne kona ubanka?” Ta fada tana zarewa yaron ido,yaji ihunsa hakan yasa yadawo,hannu yamiqa masa
“Taho” da hanzarinsa yatashi,hanifa matace zata koma,haka suka sake binsa su ukun.
1
Tana shirin miqewa kan kujerarta tana tsara tadda zasu wuni tare saigashi tare da yaran,qugu ta riqe kawai tana kallonsu,ranta yasoma suya,ya aje usman yana shigewa daki saita bishi.
Sanda ta isa taras dashi tayi yana kira a waya,don haka ta tsaya tana kallonshi har computer ta shaida masa is not reachable,yasauke wayar tana sakin tsaki
“Taqi shiga” ya qarashe maganar yana duban rufaidan
“Dear,gaskiya bacci nakeji,kuma yarsn nan kasan bazasu barni nayi ba,niban saba da bari bari ba,infact ma bacci ni nakeji,tunda farfajiyar gidan nada yalwa ai zata ishesu wasa ko?” Bai samu sararin bata amsa ba kira yashigo wayar tashi,saiyaga mmn amir ce,da hanzari ya daga har hakan yaja hankalin rufaida tasoma son sanin waye yakirashi haka har yake zumudin dagawa cikin kulawa.
“Test test ne yanzu likita yarubutamin,kuma kudin hannuna danazo dasu duka sun qare,idan ba damuwa ko zakamin transfer ta accnt dina saina tsallaka nan titin asibitin akwai atm na cire?” Ta fada bayan ta gaidashi,hakanan yaji duka babu dadi
“Ke zakije ma ki cire kudi da kanki?,wayace ki tafima baki gayamin ba bayan nace ki shaidamin idan kin gama shiryawa?,kuma inata kiran wayarki a kashe?”
“Babu network ne inda nake din,sai yanzu dana fito” dan shuru yayi shima sannan yace
“Jirani ina zuwa” daga haka ya sauke wayar,saiya dauki agogonsa daje gefan gado yasoma daurawa.
Tsuke fuska rufaidan tayi,donta fuskanci dawa yake wayar
“Ina kuma zakaje?”
“Zan duba mmn amir ne a asibiti,tana buqatar wasu kudi zan miqa mata” idanu ta qanqance ranta nasake baci
“Amma inaji tace ai kayi mata transfer taje tacire da kanta ko?” Tsaiwa yayi da daura agogon dayakeyi yayi yana dubanta,ya tsammaci zata qarfafashi ne akan yaje dinma
“Matata da tsohon ciki a jikinta nabarta taje layin atm cire kudi?,yau qarshen wata anyi salary,kuma kema kinsan yadda wajen yake cika da masu cirar albashi duk qarshen wata ko?”
“Nidai gaskiya dear ban yarda ba,wannan wanne irin abune,duka yadda naso zama dakai hakan yaqi samuwa haba” ta fada cikin fushi tana juya bayanta.
STORY CONTINUES BELOW

Murmushi yasaki yana mamakin kamar batasan yana da iyali ba,amma dayake ance amaryace bata laifi saiya rungumota ta baya yace
“Haba sarauniyar mata,yanxu zanje na dawofa,abani aron lokacin baxan jima ba,afwa zamu samu lokaci har saikin gaji,kwana shidane dake fa nan gaba?” Wannan maganar ta sakata tadan sassauto,amma duk da haka fuskarta a hade take,zafin kishi takeji sosai idan tatuna wajen wadda zaije,musamman ma dataga ya dauki muqullin mota,mai yiwuwa ma yasakota agaban motar kuma duka da sunan matarshi,haka tana gani ya debi sauran kudinsa ya saka a aljihu yafice.
Sai dataji tashin motarsa ta tabbatar yafita sannan tadawo falon,yaran suna zaune suna kallo,ya sauya musu tasha zuwa mbc,cikin tsuke fuska ta dubesu
“Kai….ku tashi maza ku tafi dakin babarku ku kalla” ba musu suka miqe daya nabin daya suka fice,ta sauke labulenta sannan ta maida qofarta tarufe,tadawo tayi kwanciyarta bayan tasauya tasha tana kada qafa,haushin yaran yana cikata,haka kawai su zasu soma zame mata qarfen qafa babu gaira babu dalili?.
Zaune ya sameta cikin reception na asibitin,akwai fresh yo a hannunta me sanyi tana sha kadan kadan saboda wata sabuwar yunwa data taso mata kamar bataci komai ba kafin tafito.
Daura da ita yazauna yana mata sannu,sannan ya mashi dukka takardun gwaje gwajen
“Nan cikin asibiti za’ayi ko a wajene?” Ya fada yana dubanta,duk da fafur taqi dubanshi kai tsaye
“Sunce duk wanda yafi”
“Zauna anan naje lab din na tambaya wanne ne yafi saurin amsar result” daga haka yawuce xuwa lab na asibitin.
Bai jima ba yadawo
“Muje suyi mikin,sunce duka daya ne” daga haka suka wuce,tana gaba yana biye da ita a baya,da alama cikin yasoma mata nauyi sosai fiye da baya,don d’ai d’ai take daga qafarta har suka isa.
Ko lokacin gwajin ma yana tsaye bisa kanta,yana janta da hira lokaci lokaci,saidai duka bata fiya bashi wata cikakkiyar amsa ba,hakanan takejin haushi haushinsa,bakinta kuma takeji ya mata nauyi kamar me ciwon baki.
Basu bar asibitin ba saidaya tsaya aka kammala komai suka miqawa likitan,ya duba duka sakamakon sannan yadaga kai ya dubesu.
“Ba wata matsala bace mai yawa yadda na zata alhmdlh,saidai duk da haka tana buqatar hutu da kuma ci gaba dacin abubuwa masu gina jiki,jininta yahau kadan amma wannan ba matsala bace in sha Allahu,taci gaba dashan magungunanta”
“Toh likita,in sha Allahu” ya miqa masa hannu sukayi musabaha yana mishi godiya suka fito.
Da kansa yabude mata motar gidan gaba tashiga sannan ya zagaya shima yashiga nashi bangaren,ya tada motar suka fice daga asibitin.
Har suka hau kan kwalta sosai batace dashi uffan ba,sai daga bisani yadan dubeta kadan sannan yace
“Meye damuwarki?,me kike da buqata?” Itama duban nashi tayi kadan sannan ta dauke kai tana mamakin ma’anar tambayarsa da maqasudinta
“Babu komai” kawai tace dashi,numfashi ya aje
“Duka cikin amir da yake na fari,hanifa ahmad da rabi’a duka ba wanda jininki yahau sai wannan?” Sake dubanshi tayi kana tadauke kai
“Kowanne ciki da irinsa,hakanan ba lallai mace tayita samun yanayin cikkunanta yazana iri daya ba” sai yayi shuru duk da bai gasgata maganarta ba,zuciyarshi tana bashi kawai shine sila,hakanan yakejin duka ranshi babu dadi.
Bai sake magana ba har suka hau titin zooroad,wanda nata gane ina zai kaita ba saida suka kai bakin gate  din gidan zoo,yayi horn masu gadi suka bude yabiya kudin shiga suka bashi ticket yashige.
Maimakon ya dakata a inda aka saba parking sai taga yayi ciki,tafiya kadan sai gasu a wani garden na daban,ya tsaida motar ya dubeta
“Fito muje” da mamaki ta dubeshi
“Me zamuyi anan?,bafa yara muka kawo ba?” Kai ya kada
“Na sani,ke na kawo kisha iska ki huta kadan”dan shuru tayi kana tace
“Amma kasani na baro yara a gida,sannan ana iyayin baqi yaudin”
“Yara ai basu kadai bane,akwai mutane a gidan,baqi kuwa duk wanda yazo akace masa kina asibiti ai yasan lalurarki” bata sake cewa komai ba ya dafe mata murfin motar tafito,nan ma yasake wani pyment din suka shiga.
Sosai wajen taji ya sanya mata nutsuwa,saboda yanayinsa dake luf luf da shuke shuke masu bayar da sanyi da iska mai dadi,hakanan babu hayaniya kai kace ma ba’a gidan zoo din kake ba.
Sai da sukayi awa guda cikakkiya ya tabbatar data sake samun nutsuwa da hutu sannan yazauna yana fuskantarta,dukka hannayenta yakama yana duban qwayar idanunta bayan yakira sunanta,kasa amsa mishi tayi,sai zuciyarta tayi rauni,duk wani nauyi data rinqa daukewa a qirjinta taji yau yana neman ya rinjayeta,cikin murya mai taushi yace
“Nasani cewa kinyi qaqari matuqa,kinyi jajircewa da tsaiwar daka,hakanan kin nuna sadaukarwa da kuma kara da karamci irin naki,tunda lamarin nan yataso bama yanzu ba tun zamanin maryam zuwa yanzu,ina mai matuqar miqa godiyata a gareki da kika zamemin abun dogaro cikin gidana,kika amsa kuma wannan sunan da hausawa ke baku na UWAR GIDA RAN GIDA,babu shakka kedin ran gidana ce halima bawai ganin idanunki ba,Allah shine shaidata,na gode qwarai halima,ubangiji yaci gaba da baki juriya da qarfin hali,ya kuma saka miki da aljanna madaukakiya” idanunta yarausayar taba son qarfafawa kanta gwiwa ta amsa addu’arshi,sannan ya dora
“don Allah inason wata alfarma awajenki halima game da gidana”
“Allah yasa bazata gagareni ba” ta furta a sanyaye”
“In sha Allahu,na yarda da nagartarki halima,inason aduk sanda nayi kuskure a tsakanin kuku ukun kiyimin uzuri,sannan karki qyaleni ki sameni ki nusashe dani,ki dorani kan hanya” idanunta tawaro waje har hakan yaso bashi dariya
“Baban amir,gaskiya ka doramin aiki mai girma da nauyi,dukkaninmu matanka ne,hakanan kana qaunarmu ka auremu,ta yaya zan dinga bin diddigi kan lamuran kowaccenmu ina gyara ko kwaskwarima akai?”
“Ashe bakison kada nashiga wuta kenan ko halima?”da sauri ta girgixa kai
“a’ah,’a’ah,ko kadan,zanyi iya abinda naga zan iya dai,kuma shine daidai wanda zan fita haqqin addinina” kai ya kada shima
“Ko hakanma na gode,Allah ya saka da khairan” amin ta amsa mishi tana kallon yatsunta da suka dan tashi kadan fiye da dada kafin tasamu ciki.
“Amma kamar fa fushi ake dani,tunda kwana da kwanaki ko kallona ba’ayi” a hankali ta daga kai ta dubeshi
“To meye damuwarka tunda kana da sabuwar tauraruwar da idan ta kalleka koda ban kalleka ba ta isar maka?” Dariya sosao ta kamashi amma ya danneta,wato kishin dai,kishi kumallon mata,idan yataso sai an amayar dashi,kai ya kada
“Ko kusa ko alama babu wata tauraruwa da zatayi dai dai dake halima,ke din ta dabance,yadda kika zama ta farko a zuciyata da rayuwata haka kike ta farko har yanzun,matsayinki bazai taba dai dai dana kowanne mace ba,kece kika fara sanin waje jibril,ke kika fara shiga rayuwarsa,kikasan dukkan wani sirri nashi,kika zauna dashi a yadda yake tun a lokacin,tota yaya matsayinki zaiyi daidai dana wata?,ummm?” Sosai taji wani sanyi yana sauka cikin zuciyarta,bata taba tsammanin cewa har yanzu tana da wannan matsayin da martabar a zuciyar jibril ba,ta dauka tuni an mata overtaking komai nata daga gareshi,ashe batasan akwai wata qima daraja da martaba da ita kadai ta mallaketa ba daga wajensa
“Sarautarki ta dabance ai halima” dole murmushi ya qwace mata,ta dinga jin wani nishadi da farinciki yana ratsata.
Sai da sukayi sallar la’asar anan sannan suka baro gidan zoo din.
A hanya ya dinga tambayarta me takeso?,to kusan bataga abinda takeso din ba harsai da suka baro hanya sosai sannan taga rake tace tanaso,ya tsaya ya siya mata mai yawa kuwa sannan suka wuce gida.
Bayan ya aje motarshi a muhallinta tana gaba yana biye da ita riqe da ledar raken,dai dai sanda zasu shiga dogon soron dazai kaisu ga tsakar gidansu amarya rufaida ta rako nata baqin zata juya sukayi kacibus,tabi mmn amir da kallo wadda ke tafe a nutse,sanye da doguwar rigar atamfa budaddiya sosai,kanta yafe da mayafin daya dace da atamfar,qafarta plate shoes ne sai qaramae jaka ta maqalewa a hannu data sanya wayarta da tarkacen magungunanta.
Ta ganeta sarai,amma banda bbn amir dake bayanta riqe da leda niyya tayi tayi shigewarta da sunan bata gane wacece ba,ledar hannunsa tabi da kallo,wani baqinciki na tokareta,wato saboda ya raina mata wayo daga cewa zaikai mata kudi shine yaje yayi zamansa harya buge da riqo mata leda kamar wani almajirinta?,dukka kwalliyar datayi da tanadin datayi masa saidaya goge ya salance?,ganin irin kallon datake musu yasa ya mmn amir yin sallama wadda ra maidota hayyacinta,saita dan dake tana amsawa ciki ciki,saidai fuskarta babu fara’a sam.4👁️‍🗨️👁️‍🗨️ *HANGEN DALA*👁️‍🗨️👁️‍🗨️

       _Ba shiga birni ba_

©️®️ *Safiyya Abdullahi Musa Huguma*

Haske Writers asso 💡

*BABI NA TARA*

   Dukkanin idanun rufaida nakan bbn amir tana dubanshi,ranta a bace yake sosai saboda bata tsammaci zai mata haka ba,ta yaya zaice mata zaije yanzu yadawo amma kawai saita ganshi da matarshi?.2

   Saita maida kanta ga mmn amir tana qare mata kallo,wannan baqar matar ma zatafi mata sauqin gamawa aiki,saita zarce da qaremata kallo,saidai bayan baqin bataga wani abu na kushe tattare da ita ba,duk da cikin dake jikinta yasauya wasu daga cikin halittarta,amma mmn amir din black beauty ce ciki ya sanyata baqi,tana da idanuwa da hanci mai tudu na wani siriri mai tsini bane can,cikin dai yasanyashi budewa,duk da cikin jikinta batayi wata qiba ta azo a gani ba,duk da ta qara kauri,bata tsaho hakanan ba gajeriya bace,tana da yalwar gashin gira.+

     “Sannu amarya” mmn amie ta fada saboda yadda taga rufaidan ta xuba mata idanu,saita dan basar sannan murya ciki ciki tace

“Yauwa sannu” ta fada kamar batasan fuskan mmn amir din ba,bata kulaa ba hakanan bata damu ba tasoma qoqarin rabeta tawuce tana cewa

“Ya kwanan baqunta?”

“Lafiya lau” tasake fada ckki ciki,batako waiwayo ba ba bare tasan meke wakana tashige cikin gida abunta.

      Da sallama tashiga tsakar gidan,tana iya jiyo surutun yaran daha dakinta,dakin mmn ummi labulenta na asake kamarma babu mutum cikin dakin.

     Sunajin muryarta yaran gaba daya suka fito suna mata oyoyo

“Kuyi haquri karku kayar dani” ta fada tana murmushi itama,sau tari yaran sukan debe mata kewa da sakata walwala,sun shiga ranta sosai har takan damu da lamuransu fiye dana jama’ar gidan,da yaranta dana mmn ummi kusan dukansu kamarsu daya,hakanan tana musu kallon yaranta,shi yasa kome zatayi musu tanayi ne kamar ita ta haifesu bata banbantasu da natan.

    Da qyar suka barta ta qarasa falonta,tazube kan kujera cike da gajiya,salima na mata sannu da zuwa ta amsa tana dubanta sannan tace

“Me aka dafa yau a gidan,yunwa yunwa nakeji” dan tabe baki kadan salima tayi sannan tace

“Babu abinda aka dafa,suma gari na basu suka siyo da kudin da kika barmin muka jiqa muka sha” cike da mamaki take dubanta

“Gari kamar yaya?,bayan store dinmu cike yake da kayan abinci”

“To mmn ummi dai bata girka komai ba,amarya ma snacks ta baiwa baqinta dasu alkaki na gararta” shuru mmn amir tayi,tana mamakin halayen maryam din duk da baqinta bane,amma daga bisani ta rage wasu da zama yayi zama,shine yanzu takeson dawowa dasu?,rasa abun fada tayi har zuwa wani lokaci kafin tace

“Allah ya kyauta yarufa asiri,tashi kijr kitchen din,ki jawo qaramin gas dina ki dora mana indomie”

“Yeeyy,umma dama yunwa nakeji tun dazu,nagayawa mamana tace naje abba yabamu abincin” cewar usman da bashi da wani cikakken hankali ko wayo,saita dora hannunta saman kanshi

“Ba haka take nufi ba kaji usmanu,yanzu za’a dafa muku indomie kuci” kai ya gyada mata,saita bisu da kallon tausayi,daidai sanda amir yashigo da ledar rake ya aje mata

“Ga kayanki inji abba”.

Jawo ledar tayi gabanta,ta bude ta rarrabawa yaran,itama tadauki wani tasoma sha ko zata rage yunwar da takeji,take kuwa dukkansu suka nutsu,kowa yasamu waje yazauna yasoma shan nasa sunata surutu.

     Fuuu rufaidan tayi dakinta,yabi bayanta bayan ya baiwa amir ledan mmn amir din yace yakai mata.

     Zaune yasameta kan hannun kujerarta rungume da hannyenta a qirji,ta cika tayi fam kamar zata fashe,dankwalinya gana goshinta,saiya zagayo yazauna kan kujerar da take zaune din,zumbur tayi zata miqe yacafke hannunta,ya kuma jawota ya riqeta gam,cikin fushi da bacin rai tace

“Sakanni jibril,aini wallahi ka bani mamaki,cikin kwana saya tal amma inata ganin abubuwan da ban tsammata ba daga wajenka,babu abu guda daya tal daka iya cikamin shi sai abubuwa kala kala,tun daga dare zuwa wayewar gari,daga wannan sai wancan”

“Haba mana amaryata uhumm?,kiyi haquri ki tsaya ki saurareni,nikaina bansan dukka abubuwan nan zasu taso haka ba,idan kin duba duka lalura ce,ni mutum ne me iyali dole nakula da haqqin kowa nakuma saukeshi,idan kika duba mmn amir kema wataran haka zata kasance akanki,zakiso nayi burus dake naqi bin lamuranki?” Saita kalleshi sosai

“Sai kuma akace ka dauki lokacina duka ka rabawa matanka da yaranka?” Shima sosai ya dubeta,duk da yanason shawo kanta ne amma hakan bai hanashi cewa ba

“Au…rufaida abunma babu kara,matana dai amma yara ai namune gaba daya ko?” Saita dan yatsina fuska tana jin takaici har cikin ra ta

“Sorry,ka fusatani ne,yaranmu to”

“Daga yau ba za’a sake ba kinji,haba amarya fushi baya miki kyau” ya fada yana lakace mata hanci,tanason jibril sosai,dole yasaki murmushi,sannan tashigar da qorafinta nabiyu

“Kuma sannan jibril baka isa da gidanka bane ko kuma dama haka ake zama da yunwa a gidanka?” Fuska yadan tsuke yanajin tambayar banbarakwai,tun tana gida dama yana dan fama da ita kan rashin iya magana,wani lokaci idan tayi wata maganar sai kaji kamar mecin kashi

“Kamar yaya?,wacce iriyar maganace wannan?” Gyara zamanta tayi sosai sannan tace

“Dole na fadi haka,yau babu abinda naci sai snacks da nazo dashi daga gidanmu,koda nayi baqima ka duba kaga abinda nabasu” tafadi taba numa mishi kwanukan da bata kwashe ba a wajen masu dauke da kayan gararta da lemo data bayar aka siyo mata a shagon layin

“Ba’ayi girki ba?,tome yaran sukaci?” Ya fada yana jeho mata tambaya,saita tabe baki wani takaici yana qumeta,wato bata ita ko baqinta yake bama,ta yaranshi yake?

“Oho” ta bashi amsa tana sake tabe baki

“Ina zuwa” ya fadi yana miqewa kana yafice,dariya tasaki tamiqe zuwa cikin bedroom dinta tana cewa

“Allah yasa ta kwabemusu,shegiya naga ta shegen daukan kai yau ai”.

STORY CONTINUES BELOW

       Kai tsaye dakin mmn ummi yanufa,baima kula da salima dake kitchen ba tana kunna wutar gas,ranshi ne kawai ke suya,taya za’ace yaranshi sun wuni basuci komai ba bayan za’a iya girki a gidan koda bai bada kudin cefane ba,tunda suna da komai.

      Wannan karon tayi wanka ta shafe jikinta damai,tana sanye da dovuwar rigar material me gajeran hannu,kwance take abinta saman doguwar kujera tana kallo hannunta riqe da remote,ummi ma nakwance gefanta tana bacci,da alama ta matseta ne ta sanyata baccin dole.

    Tunda ta amsa mishi sallamar bata kuma kallo shi ba taci gaba da abinda take,zama yayi hannun kujerar dake daura da ita sannan yace

“Lafiya kuwa yau kike?” Dubanshi tayi ta amsa mishi a taqaice

“Eh”

“Qalau kuma?”

“Ras” ta sake amsa mishi,kai yake jinjinawa,dama yayi tambayar ne don kada ya yanke hukunci bisa rashin sani

“Amma maryam don tsabar wulaqanci dason tozartani gidana akwai baqi ace an wuni ba’aci komai ba tun abincin safe?” Dama jira take yace wani abu,saboda haka tamiqe tazauna sosai

“Ka fito kafadi maganarka kanka tsaye mana,kace kawai ban girka na baiwa amaryarka da baqinta abinci ba,to bari kaji,wallahi wallahi dana dafa taci ita da baqinta gwara kowa yawuni da yunwa,kuma ni ai bamai aikinta bace dazan dafa mata tana zaune,aiba ita tafi kowa zane a duwawu ba,idan ta matsu maiya hanata shiga kitchen din ta girka?,aiba riqe mata qafafu akayi ba kuma qofar kitchen din a bude tawuni bare kace wani abu” daga haka takoma ta kwanta abinta,harya bude baki zai magana sai kuma ya fasa,yanajin akwai lokacin maganar,saiya miqe yafice daga falon ba tare daya sake ce mata komai ba.

      Bakin layinsu yafita yaje ya qaro cefane,sanda yadawo salima harta gama dafa indomie din tana juyewa,sannu ya mata ya aje kayan yajuya zuwa dakin rufaida.

       Itama kallon yataddata tanayi,ta sauya kwalliyar jikinta da wasu doguwar riga data matseta sosai,murmushi tasakar masa ya maida mata ya zauna yana cewa

“Ga kayan cefane can,kozaki taya yarinyar can salima ku gyara ta dora wani abun,don mmn amir ta gaji gsky,nasan tuni ta kama”

“Tashin balagar tsintsaye” ta fadi cikin ranta,amma a fili saita aje lemon hannunta

“Ina mmn ummin idan mmn amir ba zata iya ba?”

“Ajima zan ganku gaba daya,zaki ji koma meye” narke masa tayi sosai

“Yanzu dear jiya akawoni yau a ganni a kitchen?,idan nayi baqi suka gani aisai sucema bakasona” daga haka tasaki kukan qarya,lallashinta yasoma yi har aka bagarar da zancan,inda daga qarshe indomie yaje yasiyo musu da qwai.

“Anty bbn amir naga ya aje kayan cefane tun daxun,kuma naga ba wanda tafito bare ya taba” salima ta fada bayan ta aje musu indomie din sun soma ci,dubanta mmn amir tayi na wasu sakanni,ta gama gane abinda ke faruwa,ta kuma gama yanke hukunci na matakin da zata dauka

“Mu gama kuje keda rabi’a ta tayaki ku gyara ki kawo amir yakai markade,saiki dora koda shinkafa ce,ki dafa qwai ki hada salad”

“Tohm” salima ta fada tana ci gaba dacin abincinta.

     Tanacin abincin tunani na zuwar mata,ta soma gane inda kowa yadosa,zakuma tadauki mataki cikin kwanciyar rai.

     Suna gamawar kuwa saliman tayi yadda tace din,ita kuwa sallar la’asar kawai tayi wadda lokacinta yadan gota ma sannan tasha magungunata tashige dakinta takwanta donta huta,bata jima ba kuwa bacci yayi awon gaba da ita.

      Sanda tafarka anata kirayen sallar magariba,nepa sun dauke wuta amma har bbn amir din ya tayar da inji,wanka takesonyi,saita miqe a hankali tafito falon,babu kowa falon amma tana dan jiyosu daga tsakar gida,fes falon yake yana qamshin turaren wuta kai bakace da yara a dakin ba,kamar dai yadda saliman taga tanayi,tazauna saman daya daga cikin kujerun tana qwalawa saliman kira.

   Shigowa tayi da alama tayi alwala ne

“Gani anty”

“Kin gama ne?”

“Eh na gama,suna cikin coolers,na zubawa bbn amir nashi”

“Yauwa sannunki da aiki,yanzu ruwan wanka zaki doramin,idan kin dora din ki leqa dakunansu ki gaya musu abinci yana kitchen,kadan ruwan zai danyi zafi ki kowomin zanyi wanka”ta amsa mata da to ta juya tafita.

STORY CONTINUES BELOW

       Wankanta tayi sosai ta shirya cikin wata doguwar rigar material,wadda tayi mata kyau sannan ta fidda cikinta sosai,ta kuma haska choculet colur fatarta,ta feshe jikinta da turare kamar yadda tasaba,sannan ta dan goga hoda daman lebe tadawo falon.

    

     Suna falon amma zaune shuru sakamakon bitar karatun islamiyya da kowannensu yakeyi,saita samu gu tazauna ta jona dasu itama har aka sallaci isha’i,lokacin bbn amir yashigo,yaran suka tarbesu yariqesu kana ya qaraso,bai zauna ba ya shaidama mmn amir din yanason ganinsu a falonshi,ta amsa masa dato sannan yafice.

    Gyara daurin dankwalinta tayi ta sake feshe jikinta da turare sannan tasake fitowa,hanifa tayi sauri tace

“Zan biki umma”

“A’ah ki zauna da salima,yanzu zanje nadawo” daga haka tayi gaba.

     Shi dayane da alama sauran basu fito ba,tayi sallama tashiga falon,ya amsa mata yana murmushi kana ya dora da fadin sanda take shirin zama

“Sannu uwar biyu” murmushin itama tasaki,sai data zauna sannan tace

“Ni dayane a cikina,scanning ya nuna” baki ya kama yana murmushi

“Idan kuma Allah boye dayan yayi fa?” Dariya yabata sosai,wai duka yaran gabanshi basu isheshiba,kalen ‘yan biyu yakeyi

“Dayanma an godewa Allah,banda abinka bbn amir duk yaran dake gabanka?,ga wanda idan Allah ya nufa amarya zata haifa maka?”

“Dozen biyu fa nakeso” sosai dariya ta qwace mata ganin bilhaqqi da gaske yake

“Ina zakakai dozen biyu”

“Da gaske nake miki,yara ai rahamane” tana dairiyar take gyada kai,daidai sanda rufaida amarya tashigo.

     Sanye take da wasu matsatstsun baqaqen riga da skert da suka fidda dukkanin jikinta sosai,taku take d’ai d’ai tana taunar chewing gum tashigo da sallama.

     Kai tsaye kusa da bbn amir tazauna kamar zata shige jikinsa,dauke kai mmn amir tayi kamar bata gani ba

“Kin sha magungunan dai ko?” Bbn amir yakuma fada yana dan janye jikinsa ganin yadda ta matseshi sosai,fuskarta a sake tana murmushi kamar dai daxun tace

“Bamu jima da dawowa ba dukka nasha,shinema nadan samu barci”

“To ma sha Allah,Allah ya qara lpy”

“Amin amin,na gode” ta fadi tana maida hankalinta ga wasu jaridu dake kusa da ita ba tare data dubi sashen da rufaidan ko bbn amir din yake ba.

     Tanajin yadda rufaida ke janshi da hira irinta soyayya,amma sai tayi kamar batasan sunayi ba,ta maida hankalinta sosai tana duba jaridar,rufaidan rabin hankalinta nakan mmn amir din,so take taga sauyawar fuska ko yaya tattare da ita,saidai taqi bata dama,hakan yadan sosa mata rai,tasake bada qaimi,amma azahiri saikace ko a jikin mmn amir wai an mintsini kakkausa,duk da zuciyarta cike take da kishi fal.

      Ganin abun na neman wuce gona da iri saita rufe jaridar tana duban bbn amir

“Ko za’a yiwa mmn ummi magana ne?,inason in sha magani na kwanta dawuri”

“Eh to,to ayi matan” yana rufe bakinsa mmn ummi tashigo dakin dauke da ummi,mmn amir tasoma mata tafi tun kan su qaraso yarinyar tasoma daga mata hannu,suna qarasowa ta karbeta,tahau qyaqyata dariya kuwa,don yau duka basuga juna ba.

       “A ina zan zauna kenan?” Mmn ummi tafada fuskarta tsaf a dinke,duka suka dubeta shida rufaidan don basu gane me take nufi ba,shi yasoma magana

“Ko inama,ai akwai wajen zama”

“Amma ka kiramune don muzo mu ganta nanuqe da ita,toni indai irin wannan zaman za’ayi wallahi bazan zauna ba” sai sannan rufaida tagane me take nufi,saboda haka tasake shige masa tana duban idanunta

“Ayyah mmn ummi,aiga daya side din can saiki zauna na wani abu bane ko?” Ta fada tana fakar idanun baban amir ta watsa mata harara,sarai ta ganta,kuma itama batayi qasa a gwiwa ba ta maida mata,kafin tace wani abu bbn amir yadubi rufaida

“Koma can kema ki xauna” ya nuna mata kusa da mmn amir,ranta yabaci sosai,saidai duk da haka taci riba tunda ta bata ran koda iya mmn ummin ne.

      Cikin nutsuwa ya musu dukkan jawabin daya dace kowanne maigida yayiwa matansa,yaja hankalinsu kansu xauna lafiya,kuma kowa ya girmama na gaba dashi,kaf maganar bata yiwa rufaida ba,ta tsammaci xai bata wani matsayine na daban a gabansu cikin maganarshi,mamaki ita gaba daya take,kaman ma ba jibril dinta ba,duk wani fifiko datake zatan ta dara saura dashi bata ganshi ba cikin bayananshi,yana bayani kaman daya take da matanshi?,ya zama lallai ta nuna musu akwai banbanci,ba zata lamunta yazama tana hangen dala ba tana tunanin birni zata shiga ashe ba birni bane.

       “Sai zancan rabon kwanaki zai zama bibbiyu kamar yadda aka saba ko?,mai magana ko qorafi kuma bismillah kafin mu tashi” shuru dukka sukayi,kowa da abinda yake saqawa cikin ranshi,ganin haka sai mmn amir tagyara zamanta

“Nidai ina da magana ko qorafine zance” waiwaya yayi yana dubanta sannan yabata dama

“Yauwa,inajin gsky zan sadaukar da kwanakina da kuma girki zuwa hannun ‘yan uwana,saboda yanayin jikina,da kuma hutun da likita yabuqata na dinga samu” dukkaninsu suka zuba mata idanu,rufaida tayi caraf

“It means mu zamuna miki girki kina kwana da miji?” Ta fada ranta na mata zafi,kallonta mmn amir tayi sosai kana tasaki murmushi

“Wannan ba damuwa bace,nabarmiki bbn amir harsai na haihu,kiyi girki kuma ki riqeshi” can qasan ranta taji wani mugun dadi,a fili tasaki murmushi tana qiyasta bagidajiya a ranta,banda bagidajiya ta yaya za’ayi ki barwa kishiya mijinki?,ai idan itace ko naquda take ranar ba zata taba yarda ta barwa kishiyarta mijinta ba.1

      “Tabdi,to wallahi ni ban yarda ba,ta yaya zakiyi haka baki nemi jin ta bakina ba,kina nufin tayi kwana hudu nidata samu a gidan nayi kwana biyu,wallahi ko sama da qasa zata hadu ban yarda ba,da sake an baiwa mai kaza kai,saidai muyi uku uku” mmn ummi tafada tana kumfar baki,haushin mmn amir ya cikata taf,tana ganin kamar akwai maqarqashiya ko hadin baki tsakaninta da rufaida ko bbn amir,sun hada baki da kaine kawai don a zalunceta ko a cusa mata baqinciki”

“Kinga jimana maryam,kamar yaya?,kwana dai ba nata bane kuma tace tabarmin har saita haihu,tunda ba’a baki ba aisaiki saka na annabawa,kinata abubuwa na saka miki idanu daga jiya zuwa yau,shine yanzun ma dai dole kin saka nayi magana,ni banson aikin zubda aji gaban miji” ta fada tana kada idanu hadi da kada qafarta data dora daya saman daya.

     A zabure mmn ummi tamiqe tana nuna rufaida

“Ke dakata karkimin rashin kunya,wutsiyar raqumi tayi nesa da qasa wallahi niba sa’ar yinki bace” dariya rufaida tabushe dashi

“Ikon Allah,yanzu duk saboda ba’a baki……”

“Dakata ya isheni da Allah malamai haba!” Bbn amir yafada cikin bacin rai

“Wane irin abune wannan?,to ya isa,zata riqe kwanakinta,sannan ku zaku ci gaba da girki har Allah ya sauketa lafiya,ke maryam zaki riqe girki har kwanakin da rufaida zata karba,zakuci gaba dayin kwana uku uku” hakan yayiwa mmn ummi dadi,saboda tasani dama ita ko mmn amir duk wadda cikinta ya tsufa haka ‘yaruwarta ke amsar girki harta haihu,ko banza an soke kwanan da aka qarawa rufaida,saboda haka ita bata da damuwa,saidai girkin da zatayi har tsahon kwana shida tana basu sunaci bataji xata iya gaskiya,ta wannan bangaren ma kamar bbn amir din duka gidan ita yafi rainawa kenan,mata biyu kowacce nakwance zata dinga dafawa tana bata?,gaskiya da sake an baiwa mai zaka kai.

“Nifa gaskiya bazan mata girki har kwana shida ba,don ba baiwar wani bace ni” ta fada tana harare harare,mamaki ya cikashi,wato wanzan baison jarfa kenan,ya tuna sanda mmn amir tadinga mata girki kwana da kwanaki,harda qarin kwana uku tayi mata saidata cike kwana goma cif

“To shikenan,mu zuba nidake naga waye mai gidan”ya fada akusashe cikin bacin rai,fuuu ta amshe ummi daga hannun mmn amir tafice daga dakin,binta da kallo mmn amir tayi harta fice,saita miqe itama a tausashe

“Nikam ina neman alfarmar akarbi kwanan idan zaiyiwu don Allah,saida safe” daga haka tayi gaba,duka ranta babu dadi,taya mmn ummin zata bari daga shigowar matar tsakanin jiya dayau amma su soma irin wannan tataburzar,harta bari taga warginta da zata dinga fadi in fada da ita?.

     Itakam batasan ya aka kwashe ba,tunda tashige dakinta tadan zauna cikin yaran kana tawuce tayi kwanciyarta,bata farka ba saida asuba.

       Da safe ya leqosu kamar yadda yasaba,ta gaidashi a ladabce sannan tace

“Yau salima zata koma gida”

“Au,ai na zaci zata tayaki zamane harsai kin haihu” kaita kada

“Inna ba zata barta ba”

“Data qyaleta kuwa aida hakan yafi,shikenan,idan zan fita zan baki saqo ki bata”

“Tohm,sai alfarma da nake nema” harya soma takawa ya tsaya

“Wacce irin alfarma halima?”

“Yaran nan nakeso tawucemin dasu,saboda indai suna nan din bazan huta yadda nakeso ba,idan suka danyi koda sati ne sai adawomin dasu don Allah” ta fada atausashe,saboda tasan halinsa sarai,baiso ko yaya yaranshi su matsa daga kusa dashi,shuru yayi na wasu mintuna sannan ya amsa

“Banaso halima,amma yadda kike kyautatamin dole naso abinda kikeso,su bita din,babu damuwa”

“Na gode qwarai”

“Madalla” ya amsa yana ficewa.

        Saida saliman tayi mata duk wani gyara sannan suka shirya tsaf ita da yaran,sanda suke hada kayansu ahmad yashigo

“Umma inasu hanifa xasu?”

“Zaku anguwane,amma bazasu dade ba zasu dawo” nan kuwa ya narke kan saiya bisu,da dabara tasamu ta turashi dakin mahaifiyarshi,don tasanma babu batun mmn ummin tabarsu suje.

        Sai data rakosu har farfajiyar gidan sunata murna zasu gidan innar, taga tafiyarsu sannan tadawo cikin gidan,sai takejinta sakayau da suka tafi yaran,koba komai kafin su dawo tana saka ran lamuran gidan su daidaita tagama gane kan komai da yadda zata bullowa kowanne matsala da yadda zata fuskanci komai.

      Tana komawa ciki ta sakaya qofarta tayi kwanciyarta hankalinta kwance,tasan koma wacce matsala ce zata taso zata zo mata da sauqi,lokaci kadan kuwa bacci ya kwasheta .👁️‍🗨️👁️‍🗨️ *HANGEN DALA*👁️‍🗨️👁️‍🗨️

       _Ba shiga birni ba_

©️®️ *Safiyya Abdullahi Musa Huguma*

Haske Writers asso 💡

*BABI NA GOMA*

*zaku iya saurarar litattafaina a tasha ta ta SAUTIN HIKIMA dake youtube,litattafan sune kamar haka*

*Alkawarin Allah*

*Daurin Boye*

*Kundin Kaddarata*

*Mutuncin Mace*

*Dangantakar Zuci*

*_karku manta,nan gaba kadan acan zaku dinga samun ci gaban kowanne littafi nawa*🤫

     Tunda ta kwanta bata farka ba sai bayan sallar azahar,tamiqe tana ambaton sunan Allah ganin lokaci na neman qurace mata bata sallaci azahar ba,bandakin dake falonta tashiga ta daura alwala tazo ta gabatar da sallar azahar din,tana nan saman abun sallar tana tasbihin data saba bayan kowacce sallah me 33 taji yunwa tasoma sakadarta,duk da haka bata katse ba amma saita qara sauri harta gama,tashafa addu’arta tamiqe tana tunanin abinda xataci.

2

Bata qaunar fita ma tsakar gidan bare tasan meke faruwa,batasan yata qarke ba,saboda haka saita jona heater anan falon nata tazauna tana jiran ruwan ya tafasa,mintina kadan ya tafasa,ta duba cikin dakinta ta laluba cikin kayan abinci da lokaci lokaci wanta yakan bata,dayake gidan basu da matsalar abinci majority bayarwa take,na qarshen ne daya aiko mata dashi bata bayar ba ta aje din,a sannan bikik bbn amir yakusa,batasan me zaije yadawoba shi yasa ta aje din.

Kwalin taliya ne dana indomie,ta farke taliyar taciro guda daya ta karya taxuba,ta ciro miyar nama data saka salima tayi mata daga fridge ta dora saman botikin da take tafasa taliyar donta dumama,cikin mintuna kadan tagama,taxuba tazauna sosai taci ta qoshi,saidai tana cidin taba tunanin su usman,sam bataji motsinsu ba,kodon ta rufe qofarta ne?.

‘Yan halak kuwa tana gamawa saiga usman din yashigo,ta dubeshi sosai,fuskarshi qayau qayau da alama ma ba’a mishi wanka ba,ga jirwayen hawaye nan layi biyu kan fuskarshi

“Umma zanci” ya fada yana kallon sauran taliyar data rage

“Bakaci abinci bane?” Kai ya gyada mata

“Mama bata gama ba,tun daxu nakejin yunwa saita dakeni wai ba yanzu zata dora ba” mamaki ya kamata,wai wanne irin banzan haline mmn ummin ta tsiro dadhi,yaran nata take hadawa suda ubansu take musu horo gaba daya?,wannan ai shashancin banza ne da wofi,su yara me suka sani?,tana qara dasa rashin jituwa tsakaninta dasu bata sani ba,da alama bbn amir ya turasasata zatayi girkin ne,shine ta qulla muguntar qin dorawa da gamawa da wuri,banda haka gidan tunda mmn ummi tazo itama tasamu tsarin gama abinci da wuri saboda yara,haka tsarin mmn amir din yake,itama haka tazo tasamu ta dora akai,amma ace har uku na rana na neman gotawa amma ace ba’a gama girki ba?.

Da wadan nan tunane tunanen ta xuba ma usman abincin,tana zaune bayan tasha ruwa tana kallonshi yana cin abincin a yunwace hannu baka hannu qwarya,nan da nan yagama da abincin,ya nemi ruwa tabashi yasha,saiya bingire yahau bacci.

Ranar wuni tayi sur dakinta babu inda ta leqa,don bata da abinda zatayi a wajen,bata fito ba sai bayan sallar magariba,bayan tayi wanka ta sanya daya daga cikin dogayen rigunan atamfofinta,duk daba kwalliya tayi ba amma tayi kyau,tana ta qamshin turare,ta kama hannun usman wanda sai sannan yatashi a bacci,ya tsula fitsarinsa ta sake masa wanka saboda haka tayi nufin kaishi wajen mamarshi tasauya masa kaya.

Tsakar gidan nasu babu kowa sai hasken wutar lantarki,dayake haka unguwar tasu take akwai lafiyar samun wuta,sukanyi kwana uku da ita,shi yasa take cinikin ruwa da lemonta sosai,banda bikin nan da akayima da tuni ana sintitin zu siya,saidai tana tunanin gobe ko jibi zata koma sana’arta.

STORY CONTINUES BELOW

Duban tsakar gidan take adan kaikaice saboda yanayin tsaftarsa da tsarinsa bai mata ba,ba’a wani share yake fes yadda take masa ba,hakanan tawuce tana furta Allah ya kyauta,tadaga labule tashiga dakin mmn ummi.

Tana zaune falon tana shafa mai,da alama wanka tagama,ta daga kai fuskarta ba yabi ba fallasa ta amsa sallamar tana ci gaba da shafa manta.

Tana daga tsaye tasaki usman ya isa wajen mamarshi yaxauna yana gaya mata umma ce tayi masa wanka

“Wanne irin bacci kayi haka usman?” Ta tambayeshi tana dubanshi

“Ki barshi da yunwa ba dole yayi bacci ba,da kika hana yara abinci ke aisaiki hada kici” ta fada tana jefa mata harara,don sam ta kasa hadiye takaicinta,ta tsani a cuci yaro,shida bai gama sanin ciwon kansa bama bare na wani.

Dubanta mmn ummi tayi kawai batace komai ba tana ci gaba da shafa manta,itama saita juya tafice daga dakin,tana fitowa tanufi nata dakin tajiyo dariyar rufaida daga soro,saiga bbn amir na biye da ita,riqe take da hularshi,taci kwalliya da qananun kaya.

Sarai taga mmn amir na fitowa,hakan kuwa yayi mata dadi sosai,saboda haka ta tsaya anan tasoma shagwaba tana bubbuga qafafu kan saiya dauketa.

Shi sam baiga mmn amir din ba,saboda haka ya sungumeta,tahau kuwa qyalqyala dariya cikin jin dadi,bai ankare ba saidaya kusa da dakin rufaidan sannan yaga shigewar mmn amir dakinta da rufe qofarta,ya sauke rufaida da hanzari yana fadin

“Subhanallah,ashe matan gidan suna kusa” fuska ta turbune sannan tace

“Su waye matan gidan?,naga nima matar gidance,kuma kawai saboda wasu saika kama ka saukeni bayan baka qarasa dani ba” ta fada fuska kicin kici,cikin nuna fushi tayi gaba tashige dakin,yabi bayanta da hanzari yana kiranta.

Washegari mmn amir din tana zaune dakinta tana karyawa,yauma kamar jiyan bata leqa waje b,bbn amir din yashigo dakin cikin shirin fita kasuwa,ya kasa hada ido da ita saboda abun jiya,bayan sun gaisa yahau kame kame

“Kin zama hajiyar daka ko?,haka kawai kin koramin yara daga gida” kofin da take shirin kaiwa bakinta ta dakata ta dubeshi

“To ko aje a daukosu?” Ta fada cikin gatse gatse,don itasam bata sha’awar yaranma su dawo gidan nan kusa,saboda ta fuskanci take taken rufaidan,ko dazu tana jin ihunta daga daki,shima kuma yasan sarai sunji,abinda yasake sakashi kunya kenan,kuma ba wani abu yayi mata ba,kawai dan tsere ne haka da ba’a rasa ba na sababbin ma’aurata ya kamota shine tasaki wannan ihun,shi kansa abun yabashi mamaki don baikai tayi ihun ba

“Ni na isa,inna fa akai kaiwa su,aita isa damu gaba daya” shuru yadan ratsa don bata sake ce masa komai ba,sai kuma yayi gyaran murya

“Ni zan fita,ko akwai wani abun?” Kaita kada kawai tana ci gaba dashan shayinta

“Shikenan,saina dawo”

“Allah yatsare” ta amsashi a taqaice.

Har yakai qofa sai kuma tasake cewa

“Amm jimana” waiwayowa yayi yana dubanta,shi kansa sai yakejin wani shakka shakkarta yadda ta tsare gida,hakanan vabu wani abun magana da mutum xai tankata dashi,ta ga abubuwa amma kamar bata gani ba,taji amma kamar bata cikin gidan

“Don Allah kome zai faru kayi qoqarin kula da kiyaye tarbiyyar yaranka,don dukkaninsu sun taso,sannan kowanne da irin baiwa da kaifin basirar da Allah yabashi,so kome zai kasance yadinga zama cikin tsari da kiyayewa idanun yaranka” yasan magana ce tayi masa mai harshen damo cikin hikima da fasaha ba tare data kama sunan kowa ba,ya kuma fahimci inda tadosa,donko shidin yasoma wannan tunanin,saiya gyada kai

“Gaskiyane,nakuma gode da wannan tunasarwa uwar gida sarautar mata,Allah yayi albarka”

“Amin” ta amsa can qasan maqoshinta,saiya saka kai yafice daga dakin.

Daga nan dakin mmn ummi yanufa,don dama yakanbi girma girma ne,zaune yasameta itama ga abun karinta ta saka a gaba,saidai bata taba komai ba,sai usman da mubarak dake karyawa abinsu.

Qafarta na dore daya saman daya tana karkadata,kana kallonta sau daya zakasan akwai abinda ke cin zuciyarta kuma tanason ta amayar,da qyar ta iya amsa sallamarsa kamar wadda aka shaqe takuma bishi da banzan kallo,bai wani lura ba harsai daya gama biyewa yaranshi yana yiwa ummi wasa sannan ya dubeta

“Mun tashi lafiya” yasoma gaidata maimakon ita ta gaidashi

“Gashi nan kaga alama”

“To madalla” ya fada a taqaice,tunda yaga yanayinta da yanayin gaisuwarma yasan wani abune kuma na daban,bata rabo da qorafi sam a rayuwarta,kullum cikin matsala daga wancan sai wannan,shi yasa bai fiya jimawa a dakinta ba,hakanan ko ranar girkinta ba wani doguwar hira suke ba idan ba ita taso ba.

STORY CONTINUES BELOW

Da dafari sanda yake dokinta yana ganin tafi mmn amir iya komai saboda karatunta ya dara nata bai ganin illa da aibun dukka wadan nan halayen nata,saida tafiya tayi tafiya sannan ya tantance tsakanin aya da tsakuwa.

1

Yana dire ummi yace

“Xan fita,akwai wani abu?” Ya qarashe zancan yana dire mata kudin cefane,da harara tabi kudin kafin ta maida dubanta kanshi

“Wallahi wallahi kana bani mamaki jibril,bansan rainani dakayi dukka cikin matanka yakai haka ba,ku gama tiqa dariyar kaida waccar me zubin karuwan,kashig dakin mmn amir ka kusa kashe minti goma sannan nika shigo a wani tsaitsaye kabani kudin cefane,wato bauta itace aikina ko?” Yaran yaduba,baison wani cecekuce gabansu,wanda wannan dabi’ar mmn amirce takoya masa ita,da fari bai dauki hakan a bakin komai ba,sanda yake ganiyar neman auren mmn ummi yakan iya fadata da fada gaban yaran,koya caccaba mata maganganu,iyakaci tayi shuru,idan sun mata zafi da yawa tayi kukanta ta goge hawaye.

Sannu sannu sai Allah ya canzashi,wanda yasan ba komai bane yakawo hakan face addu’a data saka a gaba babu dare babu rana.

Yasha raba dare suna waya da mmn ummi suna kwance gado daya da mmn amir,baya shayi ko shakkarta,takan tashi ko kallonshi ba zatayi ba,tun a sannan bata da bandaki cikin falo sai tsakar gida,nan zata fito ta daura alwalarta ta koma falo tayi shinfida tahau sallarta,tabarshi shi kuma cikin dakin ya qaraci wayarshi har yayi bacci,wani lokacin bai sake ganinta sai zashi sallar asubahi.

Yakanyi mamaki idan washegari tatashi wasai tashiga sabgarta da yaranta,fuskarta cike da annuri,wanda duka hakan bai rasa nasaba da wannan sallar dare data kusa kwana yi.

“To tashiga hankalinta,idanma tanayine saboda muji n bata a gabana,saidai idan ita bata da tarbiyya mu muna da ita ehe” bai saurareta ba sai yunqurin danne zuciyarsa da yake,yasa kanshi yafice daga dakin.

Ya tabbatar da cewa kura ce tayi lafiya,ko kuma yakoma kan tarbiyyar mmn amir ne,inda ta sameshi a lokacin da yake a bbn amir dinsa bata isa ta gaya mishi wadan nan kalaman ba yana kallonta,koda bada shi take ba,saidai mmn amir ta zame masa mudubi,hakanan yakanji a karan kanshi bai kamata yayi wani abu naba dai dai ba,kobanza a yanzun iyali yake tarawa.

*****   *****   *****   ******

      Cikin kwanaki amarci sosai rufaida takeci yadda takeso,tasamu kusan duk abinda takeso daga wajen bbn amir din,don idan yadawo daga kasuwa babubinda yake sake fita yana tare da ita,hakan yakan mata dadi yana faranta ranta,takanyi kowacce shiga da take tunanin zata ja ra’ayinsa da hankalinsa,ta kuma samu yadda takeso,zub da habaici jirwaye da kamar wanka,dariya da darrarku na cusa haushi da takaici dukka ta baje abinta.

Babu wanda ke qunsar takaici irin mmn ummi,nafarko bata da wata sana’a da takeyi face zaman dabaro,zaman hira,zaman charting ko xaman kallo,uwa uba gaba duk wani motsi na rufaidan idanunta yana kai,kome take tana sane dashi tana biye dashi,hakan ya sanya tunda rufaidan ta fuskanci hakan saita qara qaimi,kullum burinta ta bullo da wani sabon abun dazai basu takaici.

Saidai ta bangaren mmn amir ko a jikinta wai an tsikari kakkausa,wasu abubuwan tana sane dasu itama,amma data fuskanci zuciya na neman janta saita dawo da sana’arta,nan da nan taci gaba da saida ruwa da lemonta,kasancewar ta iya sosai,ga uwa uba tsafta,hakanan idan bata komai takan zauna tayi tilawar qur’ani,idan ta gaji ta kunna kallo ta taba,dama ita ba charting take ba,idan tagaji da kallon kuma takan kunna karatun qur’ani yadda zai cika dakinta ya hanata jin motsin kowa da komai,yara kam har yanzu bata daukosu ba,don haka wuni takeyi daki abinta,idan dare yayine takan nemi izini wajen abban amir tadan fita tayi tattaki kadan tadawo gida,takan leqa wani sa’in gidan mmn laila maqociyarsu,kuma qawarta qwaya daya da take da ita,bata fiya shiga gidan tayi fitowar banza ba,takan qaru da ita ta fanni da dama,kusan halinsu yaxo daya,hakan yasanya suke abota sosai.

Abu biyu zuwa uku ke damun rufaidan,yadda ta fuskanci jibril din mutum ne mai son yara,uwa uba baya yarda da wulaqanta kowa cikin matansa,amma ta fuskanci kamar mmn amir din yafi kaffa kaffa da lamarinta akan mmn ummi,hakan yasanya tasake daura damara gamida cin alwashi.

Cikin haka kwanakin amarcin amarya rufaida sukaci gaba da turawa,har mmn ummi tagama girkin yazamana a yanzun rufaidan ce zata karba.

*******    ********    *******

      Karfe bakwai na safiya ya farka daga baccin daya daukeshi bayan dawowarsa daga sallar asuba,yazauna saman gadon sosai yana kallon rufaida daketa sheqar baccinta,donko sallar asuba batayiba kasancewar tana hutun sallah.

Hannunsa ya saka saman filon da take kai ya bubbuga yana tashinta,daqyar ta iya bude idanunta da sukayi jaa saboda bacci,mugun dadin baccin takeji sosai

“Tashi ki doramin ruwan wanka,saiki dafamin wani abu,zan fita daurin aure qarfe tara da rabi nakeso nafita” lumshe idanunta tayi tanajin wani yaji yaji na bacci,ta yaya tana baccinta me dadi zaice tawani tashi tadora masa ruwa da abinci?,ruwanne bai iya dorawa ba ko abincin ne dole sai yaci,itafa ba abinda tatsana tun a gida irin ka hanata baccin safe,daka hanata bacci da safe gwara kayi mata koma meye

“To” kawai tace dashi ta maida idanunta ta rufe,ya zaci taji,saboda haka yamiqe yafita falo yashiga bandaki don ya rage cikinsa kafin ruwan yayi zafi.

1

Saidai abun mamaki koda yafito wajen minti ashirin saiya sake samunta kwance abinta,babu alamun tatashi ma,sake tashinta tayi,ta dago kao cikin fusata,wanda har taja tsaki ba tare data tuna a inda yanzun take ba

“Wai meye?,nifa gaskiya bacci nakeji,kabari idan natashi saina dora maka mana” tana kaiwa nan tasake maida kanta

“Ya zakici haka,tashi da Allah,ina gayamiki zan fita ne qarfe tara da rabi fa” cikin qunar rai kamar ta kutuntuma ashar tatashi tazauna,fuskarta a dinke tsaf,bacin rai kamar tayi me?,ta kalli agogo taga takwas saura

“Haka kawai saboda rashin sanin muhimmanci mutum a akama a tasheshi,toko a gida ni iyanzu ina kwance,babu kuma wanda yake tashi na,sai kawai yanzu azo a hau tashin mutum” ta sake jan tsako bayan ta gama qunquninta.

A falo ta wuceshi fuuu ko kallonshi batayi ba,ya bita da kallo kawai harta fice,mamaki yadan kamashi,na meye quncin tashin?,wani lokaci kafin suyi aure iwar haka yana shirin fita waya na maqale a kunnenshi suna shan hira,kullun dawuri take tashi saboda shi,yanzun kuma na meye nauyin?.

A kitchen kuwa bayan ta dora ruwan wankan saita samu waje tazauna,bacci nacin idanunta kamar takifa,ba zata iya tuna yaushene tatashi iwar haka daga bacci ba a gida,idan ba rashin lpy take ba zata asibiti,ko wata lalura ta daban.

A daddafe tagama dafa ruwan tajuye masa tashiga dakin ta dire masa

“Yauwa,shayi xaki fara dafamin,saiki soyamin doya daqwai,ta isheni,idan ita zakuci kiyi duka gidan,idan kuma wani abun zaki dafa muku to” idanu ta fiddo,kusun uwa,bayan shayin ma sai an dafa wani abun na daban?,na daban dinma sai ta dafa da kowa cikin gidan?wallahi ba zata iya wannan tsiyar ba,ganin yashige bandaki sai kawai tajuya takoma kitchen din tadora shayin shima tana Allah Allah ya dahu,cikin zuciyarta kuwa haushi cike fal na hanata baccinta.

2

Tana gama juyewa ta dora ruwa,ta farke indomie ta tsumbulata cikin ruwan,ta farke maginta ta zazzage mata ta rufe

“Babu wani doya da qwai da zan iya da sassafen nan kamar wata ‘yar daudu,yaci indomie kawai,gwara dana hade mata kayan hadin bari naje na kwanta nadan sake matsewa kafin ta dahu,aikin banza,banson tashin safiyar nan” tasake yin tsaki tana ficewa daga dakin.

Gadonta tawuce tafada kai,ta sake jan bargo ta lulluba abinta,batayi minti daya cikakke ba baccin yasake awon gaba da ita.

7

Daure da towel yashigo dakin yana goge jikinsa,ga mamakinsa saiya sake ganinta kwance tana bacci

“A’ah” ya furta ranshi nadan sosuwa,bubbuga qafafunta yasoma yi

“Rufee,tashi mana ina abincin?” A zabure ta farka tana mutstsika idanu,yasake maimaita mata tambayar

“Au,tana wuta bari nazuba maka”

“Doyar?” Ya fada cikin mamaki,bata amsashi ba tayi gaba da sauri,saidai ina ta makara,sanda taisa kitchen din har mmn ummi da qauri ya isheta tafito tasauke tukunyar,wadda tuni taliyar ciki ta qone qurmus.

1

Turus tayi tana kallon tukunyar tana kuma kallon mmn ummi da tukunyar taliyar ke gabanta………

👁️‍🗨️👁️‍🗨️ *HANGEN DALA*👁️‍🗨️👁️‍🗨️
       _Ba shiga birni ba_
©️®️ *Safiyya Abdullahi Musa Huguma*

Haske Writers asso 💡

*BABI NA SHA DAYA*

*ZAKU IYA SAURAREN LITATTAFAINA A TASHATA TA (SAUTIN HIKIMA) DAKE A YOUTUBE,SAUQI GA MUTANEN DA BASU SON KARATU DA KANSU SAIDAI SAURARE,LITATTAFAN NAWA SUNE KAMAR HAKA*
*ALKAWARIN ALLAH*

*DAURIN BOYE*

*KUNDIN KADDARATA*

*MUTUNCIN MACE*

*DANGANTAKAR ZUCI*

_DA WASU SABBIN DA ZASU ZO MUKU NAN GABA KADAN DA YARDAR ALLAH_

Idanu suka hada da mmn ummi,sai kawai ta waske tana bata rai ta isa bakin tukunyar tasa hannu tabude murfin,ganin yadda tayi baqiqqirin saita saki tsaki,dai dai sanda bbn amir yashigo kitchen din saboda ya zaqu ya fita,yana neman makara ne
“Ina abincin?” Ya tambaya yana duban rufaida da tukunyar taliyar dake gabanta
Sautin dariyar mmn ummi ya karade kitchen din,wanda hakan yasanyasu dukka suka waiwaya suna dubanta,sai kuma ta gimtse kamar ba itace tayi dariyar ba,ta soma ‘yan waqe waqenta tana ciro wasu fulasanta tana sauya musu waje.
+
Sosai rufaida ta qulu,ta sani sarai da ita take,amma sata a gidan barawo rance ne,kuma duk wanda yaci tuwo da ita miya yasha,ba zata lamunya ba,kuma saita fanshe dariyar data yi mata din
“Ka ganta qonewa tayi wallahi” ta fada cikin salon shagwaba tana wani yarfe hannu,wanda hakan ya qular da mmn ummi wadda kunnuwanta suke kansu
“Qonewa kuma?,garin yaya zaki dora taliyar da bata wuce minti takwas ko goma ta gama dahuwa harta qone?”
“Na dora ne bacci yadan rinjayeni naje na kwanta kanta qarasa”.
Dariya mmn ummin tasake kwashewa da ita cikin salon waqa tace
“Kayan kitchen mama tasiya min,abinci dahuwar ‘yan gayu,wani kalarma sai an dandana,ayye sama mata,mata” daga haka ta sanya kai tafice abinta tana sheqa dariya.
1
Sosai rufaida ta qarasa qulewa,a zafafe ta waiwayo tana duban bbn amir
“Kanajin matar nan ko?,nifa take tsokana,wallahi kaja mata kunne niba sa’arta bace,idan ba haka ba nixan dauki mataki a kanta dakaina” nan take yaji ranshi yabaci,ita sam bata abinda zaici da barna da kuma bata mishi lokaci take ba,sam bashi ya dameta ba?,bacin rai ya hanashi magana,sai kawai ya rabeta ya isa gaban gas din.
Qwai uku ya dauka ya fasa ya kada,yana neman frying pan ta qaraso wajen
“Ina maka magana amma kayimin banxa kamar bada kai nake ba?” Ta fada itama ranta yana baci sosai,tana ganin kamar ya wulaqanta ko kuma yana bayan cin fuskan da mmn ummi tayi mata kenan.
Kai ya daga ya dubeta kawai,sau tari a kwanakin nan idan tana wanu abu sai yaga kamar ba rufaidanshi daya sani ba,kamar wata rufaidan ce ta daban,sai yaga kulata ma bata bakine,tunda ita batasan ya kamata ko bai kamata ba.
Har yagama soyawa yajuye yadauka yawuce tana tsaye,shurunsa saiya sake bata mata rai gamida kuma tunzurata qwarai,fuuu tabi bayanshi dakin,ta sameshi zaune harya soma karyawa da ruwan tea din data dafa mishi,da kuma qwan data soya.
Kanshi ta tsaya cikin bacin rai,don tana jin ya kamata tanuna mishi bacin ranta sosai
“Ni zaka wulaqanta jibril a gaban matarka?,ni rufaida ni zaka yiwa haka,na kawo.maka qararta amma kayi kunnen uwar shegu da qorafina,wannan shine kulawa ta musamman da kayi alqawarin bani,shine darajar tawa da kace zaka daukaka fiye data kowacce diya mace?,jibril tunda nashigo gidanka nake ganin abubuwa na cin fuska da wulaqanci,dama haka kake?,ina duka alqawuran daka daukarmin?”.
1
Kai ya tada ya dubeta
” ke bakisan kinyi ba dai dai ba?,bakisan abinda kikayi shi yafi cancanta ki maida hankali akansa ba ba wani shirmen banxa ba?,ga abinda yafi muhimmanci sam ke bashine a gabanki ba,kawai ta abinda aka miki kike na daukar miki fansa?,hakan shine dai dai a wajenki kenan?”ranta yasake baci,wato shi baima ga abinda akayi mata ba kenan,abinda aka mata din shine shirmen banza
“Amma dai aiko yaya kayi magana ko kodan saboda ta rainani,idan yaso mayi solving wannan issue din daga baya” shuru yayi yaba kallonta,wato bata fahimceshi ba kenan har yanzu?,sai kawai yamiqe daga cin abincin yana qoqarin danne bacin ranshi da mamakinsa,yadauki jakarsa da muqullin motarsa ya gewayeta yana fadin
“Saina dawo”
“Jibril” ta kirashi cikin bacin rai daya riqe mata wuya,amma saiya wuce baiko waiwayo ba.
1
STORY CONTINUES BELOW

Ganin ya makara da yawa ya sanya bai shiga dakin kowa ba yawuce,yayanke aranshi idan ya isa kasuwa yakira yaji lafiyar kowa,duk da yariga daya ga mmn ummi,mmn amir ce baiji motsinta ba,kuma ya kyautu ya leqata din kafin yafita kodon yanayin da take ciki.
Nan ta zube a kujerar falon nata ranta na mata suya,bata tsammaci zai bari mmn ummin tayi mata haka a gabanshi ba,kuma har tayi magana ya nuna ba wannan ne damuwarshi ba,damuwarshi wato cikinsa kadai?.
Ta jima zaune anan cikin bacin rai,tana saqa yadda zata rama abinda mmn ummin tayi mata,hakan yasanya har rana tasoma dagawa,lokqcin cin abincin yara da matan gidan yayi amma babu amarya babu dalilinta,kitchen wayam ba abinda aka dora,haka tsakar gidansu yana nan tun yadda yake daren jiya,baisamu arxiqin shara ba,wanda aikin amarya ne,kuma bata fito ba bare ta share din.
Dai dai lokacin mmn amir na daki kwance bayan ta idar da sallar walaha,bata wani jin yunwa sosai saboda tunda sassafe data tashi taji tana jin yunwar ta debi cake ta hada shayi mai kauri tasha abinta,tunda cikinta yasoma tsufa cin abincin nata ba wani mai yawa bane,shi yasa wanda tacin bai gama narke mata ba har yanzu.
Qarar wayarta yadauki hankalinta,tamiqa hannunta tadauko tana duba mai kiran,saita saki murmushi,din yanzun haka tunaninsa take taga bai shigo ba kamar yadda yasaba,har kishi yaso taso mata ko rufaida ce ta riqeshi?,sai tayi ta’awizi ta kori shaidan tayi istigfari,ta kuma gargadi kanta kan zato zunubi.
Sallama tasoma yi masa ya amsa mata
“Yanxun nake tunaninka,naji shuru yau babu motsinka nake cewa Allah yasa ya lafiya” ajiyar zuciya yasaki a boye,har kullum naya rasa samun wani abu dazai sanyashi farinciki daga bakin halimatunshi,kome yayi mata,kowanne yanayi suke ciki bata fasa nuna kulawa da damuwa dashi,daya daga cikin abubuwan daya sanya shima ko yaushe yakan qara qaimi wajen ganin yanuna mata kulawa kamar yadda take mishi,koda nashin baikai nata ba
“Nima kina raina,naso leqowa naga ya kika kwana keda baby,to na makara,ayimin afuwa” murmushi takuma saki
“Tunda naji shuru nasan babban lalurane ya tareka,babu komai yau da gobe sai Allah,ina kwana?”
“Lafiya lau,da fatan kin tashi lpy ke da babyn?”
“Lafiyarmu lau alhmdlh”
“To ma sha Allah,su amir basa nan bare na tambayesu,qiri qiri kin koremin yarana” murmushi tasaki kawai,don ita ason ranta ma yaran suyita zamansu a can,koda zasu dawo din gaskiya bata buqatar dawowarsu gida nan kusa,cikin nutsuwa da taushin harshe tace
“Ni na isa na raba yara da gidan mahaifinsu?,kawai dai nafi samun hutu da nutsuwa yadda ya kamata ne abban amir shi yasa,kuma nasan can din babu matsala,koda makaranta aka koma koda qafa suna iya takawa suje,tunda tamafi kusa dasu akan nan din” ajiyar zuciya yasauke
“Aishikenan,tunda anmin qarfa qarfa yana iya” murmushi tasaki mai sauti kadan
“A’ah wallahi,bankai wajen ba”
“Babu komai Allah ya raba lafiya dai”
“Amin ya Allah”
“Shikenan?,saina dawo?”
“To Allah ya tsare,ya bada sa’a,yayi jagora yakuma bada abinda aka fita nema”
“Amin ua hayyu ya qayyumu” ya amsa yana jin dadin addu’ar har cikin zuciyarsa,duk da wannan ba sabon abu bane wajen mmn amir din,abu daya dahar yau mmn ummi takasa koya daga wajenta,abu kadan xai hadasu tana kallo xai fita ma amma ba zata iya bude baki tace masa a dawo lafiya ba,ita a lallai saita nuna masa sai kuma yasan cewa taji haushi,abinda bai taba gani daga wajen mmn amir din ba,kome ya hadasu kome sukayi bata fasa ce masa a dawo lpy,ko Allah ya tsare.
1
Da wannan tunanin yakashe wayar yakira mmn ummi,ya kira wajen sau uku bata daga ba,tana gani kuma tana sane tayi dagawar saboda abu biyu,na farko tana jin haushi yafita bai leqo ba,gashi tana son amsar wasu kudade data shirya qaryar amsa daga hannunsa,nabiyu kuma batason ya mata magana ko fada kan dariyar data yiwa rufaida dazu,haka yagaji ya haqura da kiran tunda yafita haqqinta.
1
Har zai aje saiya tuna bai ajewa rufaida kudin cefane ba,amma sanin akwai kudi daya aje dakin yasa ya lalubi lambarta.
Dai dai lokacin tana kwance saman doguwar kujerar falonta,tasha tea da bread cup din yana aje gefenta,tunda yafita ko dakin bata samu ta gyara ba,tana miqe tana latse latsen waya abinta,charting take a grp dinsu wanda yake cike da qawayenta,tana ta basu labarin yanayin rayuwarta a gidanta,da kuma abinda yafaru dazu tsakaninta da bbn amir din,ashariya wasu ke qundumowa suna sake dorata bisa layin matakij da zata dauka,hirar tayi mata dadi,hakan yasanya zuciyarta yadan rage fushin da takeji.
1
STORY CONTINUES BELOW

Kiran bbn amir din yashigo,takalli lambar taja tsaki,tayi minimizing kiran takoma kan watsapp dinta harta katse,wani kiran yasake shigowa sannan ta daga,murya a dake tayi masa sallama ya amsa
“Afwa na sha’afa ban aje kudin cefane ba,ki duba qasan kayana akwai kudi ki dauki dubu daya”
“Dubu daya?” Ta fada cikin izgili izgili a muryarta,ya tsammaci jine batayi  sosai ba,don haka yasake maimaita mata
“Eh dubu daya” tsaki taja yadda bazaiji ba ta kashe kiran,takoma grp dinsu tana gaya musu nawa ne kudin cefanen nasu,kasancewar kowa yasan yadda take cika baki da kurari kan bbn amir din sai sabuwar hayaniya ta barke,wasu na rainawa wasu suna babu laifi,kowa yashiga bata irin tashi shawarar,saita koma ta kwanta sosai tana sake duba saqonnin a tsanake daha bayan daya.
1
Dai dai lokacin da mmn amir tasoma jin yunwa,saboda haka ta katse carbin da takeja din ta yunqura tamiqe tafito daga dakin bayan ta aje hijabinta,kamar hadin baki mmn ummi tafito itama dauke da ummin tana magana ciki ciki a hade,da alamu mita take,usman na biye da ita yana kuka kuka
“A’ah,lafiya dan fodiyo?”mmn amir ta fada tana shafa kan usman din,ita kadai ke kiranshi da sunan wani lokaci cikin gidan,saiya maqe kafada cikin kuka sanda mmn ummi ta tura kitchen tashige
“yunwa nakeji”
“Bakaci abinci bane?,gashi har sha daya saura?”
“Inafa zaici abinci?,bayan babu abinda aka girka cikin gidan,zokiga kitchen din qwalam babu komai sai qonanniyar taliya” ta fada cikin daga murya ta yadda tasan rufaidan zataji.
“Toh,garin yaya?” Mmn amir tafada bayan taduba kitchen din ta tabbatar ba’a dafa komai din ba
“Oho,tsabar iskancine da iya shege,da kuma daurin qarqashi data samu wajen mai gidan,nina tabbata da nice yau a gidan na na kade idan na aikata haka,gwara ke da yake anayi dake tunda kin daure masa baya yayi yadda yakeso”
“Dakata,duk wannan bata taso ba,ko wani uzuri ne dai ya hanata fitowa,karki gaggawar hukunci” mmn amir ta dakatar da uta,don batason tasoma sakin zancan nan nata wanda idan kishin ya tsikareta kamar wadda aka dorawa wuta saman ka saita saukeshi
“Koma uban meye bari naje nagani” mmn ummin ta fada tanayin gaba xuwa dakin rufaida,da ido mmn amir tabita kawai tana addu’ar Allah ya kade fitina.
Sai data shige dakin sannan ta maido dubanta kitchen din,gaba daya yakoma wani irin tunda tasaki harkar girkin gidan,kamar yanzu da yake cike da kwanukan girki,saita duqa a hankali tana tattaresu waje daya.
Da qarfi ta bankada labulen dakin tayi tsaye tana duban rufaida wadda ke kwance dafa’an tana faman charting,ganin haske daya dadu a dakin yasanyata daga kai ta kalli bakin qofar,suka hada idanu kowacce ta tsuke fuska
“Ina abincin safiyarmu?” Ta jeho mata tambayar kanta tsaye,wani kallo ta watsa mata sannan tamaida kanta a charting dinta kafin ta bata amsa
“Ban dafa ba,don babu wanda ya ajiyeni”qarasa shigowa dakin mmn ummi tayi,wanda ada batayi niyya ba
“kamar yaya?,me kike nufi?,mu mugama dafawa mu baki kina lafe a daki keda miji kuci sannan yanzu kice mu bazaki dafa ki bamu muda namu yaran ba?”, sosai tatashi tazauna tana duban mmn ummin
“Kinga tsaya,karki cikamin kunne da hayaniya,abincine banga damar dafawa ba saboda haka ki samamin salama malama” sosai mmn ummi ta tunzura,ai kuwa cece kuce ya barke tsakaninsu,wanda hakan yaja hankalin mmn amir dake kitchen din
“Ya salam” ta fada tana miqewa daga durquson da tayi,bayanta ya amsa mata,tayi tsai donta huta tanajin kuma yadda harshe ke tashi daga dakin rufaidan.
A daddafe ta qarasa qofar dakin ta daga labulen tashiga
“Haba don Allah,meye haka?,saikace wasu qananun yara?,harshenku yacika gida?wannan aiba mutunci bane wallahi”
“Kinsan me wannan ‘yar rainin hankalin tace?” Mmn ummi tafada tana nunata cikin zafi,kafin mmn amir ma ta amsa ta gaya mata duka yadda sukayi,sannan ta dora da cewa
“To wallahi bata isa ba,yadda muka dafa muka bata itama saita dafa ta bamu”dariya rufaida ta sheqe da ita
“xakiga isar tawa kuwa,naga wanda ya isa yakaini kitchen”
“Zaki gamu da wanda kike ganin ya daure miki gindi kuwa” daga haka mmn ummi ta juya fuu tafice daga dakin tafada dakinta tasoma lalubar wayarta,yayin da rufaida tadauki wayarta tawuce bedroom dinta tana ci gaba da zagin mmn ummi gamida lalubar number bbn amir,tana ganin gwara tatareshi da zancan tun kafin yazo a rigata lauya maganar.
STORY CONTINUES BELOW

A falonta ta cimmata tazauna tanata huci gamida maimaita kiran lambar bbn amir
“Wa kike kira?”mmn amir ta tambayeta sabida sanda tafito ta fuskanci itama rufaidan bbn amir din take kira
“Shi wanda ya daure mata gindin nake nema yakwana da sanin abinda yafaru” kai ta girgiza tana duban mmn ummi,batasan sai yaushe zata soma gane dukkan lamura ba,idan rufaida farin shiga wadda batasan ciwon zamantakewar aure da ciwon jibril din gaba daya da qimarsa ba ita ta aikata,ita mmn ummi da yake uban yaranta kuma wadda tadan dauki wasu shekaru cikin mu’amalar aure,tasan ciwonsa yaci ace tayi?
“Yanzu abinda zaki aikata din kina ganin kinyi dai dai kenan?” Dubanta tayi cikin jin haushi tace
“Kamar ya?”
“Yanzu kinwa uban yaranki adalci kenan?,ya fita neman abinda zaici gaba da tufa miki asiri keda yaranki,amma ki rasa dame zaki saka masa saida kiransa ki daga masa hankali?,ke kina kira ita tana kira?”
“Auto,me kike nufi?,na qyaleta kenan tatakamu tabarmu da yunwa taci karenta babu babbaka?”
“Idan tabarku da yunwa baki da hannun da zaki sarrafa abinda zakici koda dai dai cikinkine?,ki jirayi dawowarsa idan yaso kya kai masa qorafin?”
“Au….to ko bakinku daya?” Da mamaki take duban mmn ummin harta gane hakan saman fuskarta,duk da tadanji nauyin abinda tafada din saboda ita kanta tasan ba hakan bane,amma da yake idanunta a rufe suke saita dora
“Idan ba haka bane toki qyaleni,don wallahi saina gaya masa yasan sa saninsa,ai dama duk qanda yasayi rariya yasan zata zubda ruwa,niba irinki bace dazan zauna inaji ina gani a cuceni na qyale,duk wanda ya cuceni saina qwaci haqqina koda tsiya koda tsiya tsiya ne ehe,tunda ya jajibo wata toya shirya tarbar duk wani qalubale”
“Allah ya bada sa’a” mmn amir din tafada tana miqewa tabar mata dakin.
1
Kitchen din takoma sharp sharp tayi jallop din taliya da tattasan leda,da yake gwanar girkice tayi dadi qwarai kuwa,ta diba tazubawa usman da ahmad tawuce da saura daki,donko gyaran dataso yiwa kitchen dinma saita fasa,hakaza tsakar gidan,takoma daki abinta ta sakaya qofarta.
Dai dai sanda kowacce cikinsu ta taqarqare tana zabga mishi kira,sam bai sani ba,wayar tana a silent kuma cikin aljihunsa yana fama da custumers,sai daya sallamesu sannan yasamu waje yazauna yaga kiran,hankalinsa yatashi ganin kira wajen sha biyar na rufaida da mmn ummin,saiya rasa ma wazai soma kira,hankalinsa ya tashi yana fatab Allah yasa ba wani mummunan abu bane yasamu iyalin nashi.
Yana cikin wannan taraddadin kiran rufaida yakuma shigowa,babu jinkiri yadaga
“Lafiya meya faru?” Shine abinda yasoma fada
“Mmn ummi tayi kiranka ne?”
“Me yafaru?,naga miscal dinta”
“Yauwa,kome zata gaya maka karka yarda da zancanta,idan kadawo gida zakaji komai” shuru yayi yana nazari,tunaninsa nason hasaso masa abinda ke faruwa,jin yayi shuru ya tabbatar mata bata fada masa komai ba,saboda haka cikin jin dadi tace
“Saika dawo,i lov you” ta katse wayar takoma ta kwanta abinta saman gado tana juyi hadi daci gaba da charting dinta.
Jin maganar da rufaidab ta fada yasashi jan mugun tsaki,ya gama hasashen komai,haushi yacikashi,wanne irin kira ne wannan haka na rashin tunani?,yana shirin maida wayar kiran mmn ummin yashigo itama,saiyaqi dagawa yamaida wayar yaci gaba da sabgoginsa,amma sai hankalinsa yagaza kwanciya,ya fiddo wayar yanemi mmn amir
“Lafiya lau,ba wani abu daya faru,kowa lafiyarsa qalau” tace dashi sanda ya tambayeta,don tunda taga kiran tasan bai rasa nasaba da daya daga cikinsu ta sameshi,jin amsarta ya kwantar masa da hankali,saiya sauke ajiyar zuciya yayu hamdala kana yace saiya dawo sukayi sallama,ta aje wayar tana lulawa cikin duniyar tunani da mamaki,daga bisani ta ture duk wasu guntattakin tunani taci gaba da lamuranta.
Hakanan taci gaba da kwanciyarta saman gadonta,batako motsa ba ballantana tafito,don ta riga data saba ko a gidan idan tahau online tasoma charting bata tashi saita kai intaha,kota cikinta batayi bare sauran lamura,tana baiwa wayarta da charting muhimmanci matuqa,koda qannenta suja dameta da hayaniya idan tana charting din takan iya makesu,shi yasa ba kasafai suke zama kusa da ita ba idan suka ganta ta sanya waya a gaba.
Har sha biyu da rabi na rana bata gyara dakinta ba bare gidan bare ayi batun girki,saida kamfanin wayar da take amfani dashi suka tura mata saqon data dinta yaqare sannan ta haqura tasauka,data duba balance dinta kuma na waya taga bazai isa ya siya mata data ba,anan taci karo da lambar wayar mardiyya(wadda suka hadu gidan lallen biki sukayi musayar number),rabonta da ita tun ranar dinner din mardiyyan dataje mata,sukaci dariyarsu ita da qawayen mardiyya na matar shamsudden din angon mardiyyan,kan taqi zuwa dinner din,suna ganin kawai tsorata tayi,tasan ba zata iya hada kanta da mardiyyan ba.
Yankewa tayi kafin tatashi bari takirata taji yaya ake ciki,don ita gata tana nan tana nata yaqin dasu mmn ummin,kuma tanajin a jikinta akwai nasara cikin abinda tasoma din,ba zata dauki wata wahala ko wani tsari ba,dole yadda takejin tafisu karatu,takuma fisu matsayi a gun miji to a harkar gidan ma tafita daban.
Bugu hudu ta mardiyyan ta daga wayar,cikin farinciki da walwala takama sunan rufaidan.
“Amarya,amarya” mardiyya ke fada cikin fara’a,dariya itama rufaidan tayi
“Amare dai,ya kike qawa,ya gida ya al’amura” cikin walwala tace
“Komai normal,al’amura suna tafiya yadda ya kamata,kefa?”
“To alhmdlhi” ta bata amsa a taqaice,duk da har yau ita abun bai mata ba,bata samu yadda take hasashe tasamu ba,kota samu sama da hakan ba.
1
Gyara zamanta mardiyya tayi sosai tana cewa
“Ai qawata duk matar da bata auri mai mace ba bata bata cika mace ba,ai ki shiga kawai inda za’a dinga takara,a goga dake kisam cewa eh yes kema macace kin isa,ke kinga yadda abubuwa ke tafiya kuwa?,fiye da yadda nake xato da tsammani?” Ta fada muryarta na cike da farinciki da kuma zumudi,gyara xama rufaida tayi cike dason jin lbarin
“Allah qawata?”
“Wallahi kuwa,ashe dai hasahenmu qawata haka yake,uwayen gidan nan idan banda gidadanci basu aje komai ba,sai uban haihuwa da tara yara,matar nan ban sake raina ajawalinta ba saida nashigo,kinsan wata biyu tabani?”
“Ke don Allah?” Rufaida ta fada cikin sigar tambaya da kuma mamaki,
“Wallahi nake gaya miki,tunda nazo gidan nan take bauta har nayi wata guda,bana komai kuma miji na wajena,yana hannuna sai yadda nayi dashi,ke ko bita kanshi ko kulashi ma bata fiya yi ba,kullum tana can tana dubgar aikin gida dana yaranta,idan zai kwana biyu bai leqa su ba bazata koda kira wayarshi ba bare ta nemeshi,idan yafito ma iyaka gaisuwa,ko zaman hira na minti goma batayi dashi,ni kuwa hakan yayimin na kame abuna tsaf,kullum muna qule a daka muna diban soyayya madararta” ta qarasa fada tana qyalqyalcewa da dariya,tayata rufaida tayi,tanajin lallai ashe ita tayi sake da yawa
“Waikinsan wani abu kuwa?”rufaida tasake fada
“Matar nan kamar babu zuciyar kishi a jikinta,kinga yadda take nan nan dani,saboda tasan saita hanyata zata samu fadar wajenshi,bari kiji wani rashin zuciya,randa nacika wata daya da sati biyu saura sati biyu ta amshi miji ko?” Kao rufaida ta gyada cikin zaquwa kamar mardiyya na kallonta
“Kawai shashashar saita tsiri tafiya garinsu,yanxu haka tana can,har kwanakinta sun shigo bata dawo ba,kota gajima tatafine gaba daya oho” ta sake sakin dariya,abun yaburge rufaida sosai,saita gyara zama itama ta bata nata labarin
“Tabdi,wallahi ki zage damtse,yaci ace matsayinki yafi haka,ki bude wuta kawai qawata” daga nan ta qara dora rufaida kan wasu shawarwarin irin nasu sannan sukayi sallama.
Aje wayar tayi tahau nazari,lallai saita sake bude wuta fiye da wadda tabude a baya,amma bari zata sake bude duk wani shafi nata,da wannan tunanin tasauko daga gadonta tasoma gyaran dakin tana duba agogo dake nuna mata qarfe daya harda rabi na rana.
1
_ina miqa fatan alkhairi a gareku,da kuma shuru da kukaji na tsahon wani lokaci,Allah ya zame mana jagora a duk lamuranmu amin_1👁️‍🗨️👁️‍🗨️ *HANGEN DALA*👁️‍🗨️👁️‍🗨️

       _Ba shiga birni ba_

©️®️ *Safiyya Abdullahi Musa Huguma*

Haske Writers asso 💡

*BABI NA SHA BIYU*

*ZAKU IYA SAURAREN LITATTAFAINA A TASHATA TA (SAUTIN HIKIMA) DAKE A YOUTUBE,SAUQI GA MUTANEN DA BASU SON KARATU DA KANSU SAIDAI SAURARE,LITATTAFAN NAWA SUNE KAMAR HAKA*

*ALKAWARIN ALLAH*

*DAURIN BOYE*

*KUNDIN KADDARATA*

*MUTUNCIN MACE*

*DANGANTAKAR ZUCI*

_DA WASU SABBIN DA ZASU ZO MUKU NAN GABA KADAN DA YARDAR ALLAH_

     Sai data kammala gyaran dakin nata sannan tafito tsakar gidan,batako damu da yanayin data samu tsakar gidan ba na rashin shara ba,saima harara data gallawa tsakar gidanbda qofofin dakinsu mmn amir taja tsaki,cikin quna quni tace

“Lallaima,rainin wayi,sunafa nufin girkina ne,nizan gwaggwafe nayi musu shara,toko tsakar gidan tsohona baxan iya tuna lokaci na qarshe dana share musu shi ba,idan sunaso suga gidansu dakyau saidai momiyo ko hasana su share(qannenta kenan)” daga haka tayi gaba tahau sabgarta.

1

Sanda almajirinsu yazo tabashi yamata cefane,taja kayan miyan ta aje takoma daki abinta,tana lissafi gami da tunanin me zata dafa da daddare,wanda bazata kunyata ba,sannan bazai wahal da ita ba,don itadin bawai ta wani iya kalolin girki bane ba.

1

Bata sake fitowa ba saida ana gab da sallar la’asar,tazo taja kayan miyan tahau gyarawa,aka kai mata markade tadora shinkafa da miya,wanda bata kammala ta ba sai da aka kira sallar magariba,akayi sallahr aka gama sannan tasamu gamawa,ta samu fulasai tazuba nata dana bbn amir,sauran tabarshi cikin tukunya,ba tare data yiwa kowa magana kan ta kammala ba ko suxo su diba,tashige wanka abinta,tana jin uwar gajiyar datayi saboda girkin,ko a gida idan ka ganta a kitchen tota baci,ko mamarta ta matsa mata saita shiga,ko babu kowa a gidan sai ita kuma an tafi anbar girkin.

Ranar Allah bai kawo dawowar bbn amir dawuri ba,sunyi baqi a kasuwa sun dan tsaidashi,hakan yasa harta kammala shirinta bai shigo ba,cikin wata doguwar riga streetgown wadda taba daga cikin qananun kayan data dinga siya tana adanawa saboda irin wannan ranar,riga ce mai hannun vest,wadda talafe tafidda duk wani tudu da kwari na jiki ta,hakanan daga bayan rigar an tsagata tun daga wajen agara har zuwa ramin gwiwarta ta baya,ta gyara kanta tafeshe jikinta da turaruka,sannan tadawo falonta tazauna tana kunna tv,cikin sa’a tashar tauraruwa sun saka waqa,saita qure sauti abinta,wanda yakarade gidan,takoma takwanta saman doguwar kujera tajawo wayarta tahau chartinga tana jin gajiyar aikin datake gani tayi yana ratsa qasusuwanta.

A qagauce take duba duka hirarrrakin da akayi bata nan,haushi tadinga ji,saboda ada tana daya daga cikin wadanda akeji dasu cikin duka grps din da take ciki,saboda yadda take particpating,amma sai gashi yanzu tana neman komawa kurar baya,sai ayita hira bata kusa sabida aikin gidan ko wani sanga ta babbn amir,haka tadinga jan tsaki tana maida amsa daya bayan daya tana wucewa,ba tare data lura da macene konamiji ne yayi magana ba,don duka grps dinta babu wanda tafita a ciki koda kuwa akwai maza,bare tayi tunanin sauya layin waya,sabgarta taci gaba dayi kamar yadda takeyi a baya sanda bata da igiyar kowa a kanta.

Kasancewar unguwarsu irin anguwannin da basa rabo da wutar nepa ne,koda sun dauke mintina qalilan suke dawowa da ita,hakan yasanya mmn amir ke matuqar cinikin lemo da ruwa,banda yanzu data sanya qalula saboda yanayin ciki.

Yana sanya qafarsa a tsakar gidan yagashi wani iri ba yadda yasaba ganinsa ba,babu kintsi babu shara,mamaki ya kamashi,saboda abune mai wahala yadawo gidan yasameshi haka idan ba wani taro ko sha’ani akayi ba,duka daga mmn ummi har mmn amir suna da tsafta,kada ma mmn amir taji labari,donko ummi bata kama qafarta ba,don wani lokaci itake tashi ta gyare gidan har harabar,tasamu almajirai su gyareta tsaf idan iskancin mmn ummin yamotsa ta biyasu da kudi,batabi ta kanta ko kadan,to amma saiyau yaga sabanin hakan.

STORY CONTINUES BELOW

Dauke kanshi yayi daga wannan nazarin,sautuka biyu suka karade mishi kunne,na qarar kida dana kukan ummi,mamaki ya kamashi,don bazai iya tuna yaushe aka kunna kida kamar haka na qarshe ba cikin gidan,saidai duk da haka kukan yarinyar yafi jan hankalinsa,saboda haka yanufi dakin mmn ummi kai tsaye.

Goye yasameta da ummi tana fama jijjigata,gefe daya ga usman da mubarak saman kujera xaune a takure,fuskar mmn ummin kadai xaka kalla kasan cike take fal da bacin rai,yayin da yaran suma kana iya karantar akwai abinda ke damunsu.

Bata amsa sallamarshi ba,saiya jeho mata tambaya yana nufarta da zummar amsar yarinyar yana cewa

“Meya sameta haka taketa tsala kuka da daren nan?” Tofa,dama mai kuka ne aka jefeshi da kashin awaki,kamar dama jira take,kasancewarta mace wadda bata iya shanye ko danne bacin ranta ba,hakanan bata iya nuna abu na kara ko alkunya ba,idan batason abu ko bai mata ba kai tsaye take fadi kota nuna gaba gadi

“Eh,ai dole kasameta tana tsala kuka,tunda an hanata abincin gidan ubanta kuma wuni guda sur me yayi saura?,ai kawai abinda yarage kuma inaga shine rufaida tace mu tattara kayanmu mubar gidan shine inaga abu nagaba” ta fada cikin fada,hasala da haqiqancewa,kai kace shiyacewa rufaidan ta aikata,ko kuma yana da masaniya kan abinda ta aikata din.

Dubanta yake cikin mamakin abinda yafaru,dakuma mamakinta ita kanta,kamar tana magana da usman ummi ko mubarak,duk da kusan idan dasabo yariga yasaba,sam mmn ummi bata iya furta lafuzza mai taushi ba,sai lokaci lokaci idan taso hakan,ko kuma tana da wata buqata daga gareshi,bata iya controlling fushinta ko bacin ranta,duk sanda yazo mata saita amayar,har takan manta a gaban waye ma take wasu lokuttan sai bayan ta gama

“Abinci kuma?,wuni guda garin yaya?”

“Shina kiraka na gaya maka dazu,amma dayake nidin bani da muhimmanci,muma baka daukeni a bakin komai ba baka daga wayar tawa ba,kuma nasan billahillazi daga dazun zuwa yanzu dawowarka ko kaffara bazanyi ba kaga kirana,amma ka gaza biyoni saboda bani da muhimmanci,na rantse da girman Allah da halima ce ko rufaida saika bi kiransu,ba zaka iya shanyewa ba” ta qarasa fada kuka yana qwace mata,ranta na mata suya,kishi sosai yake cinta ga baqincikin abinda rufaidan tayi musu wunin yau din,tana tuna yadda ya tilastatata sai data amshi girki a sanda take cewa ba zata karba din ba,gani take kawai cikin duka matansa itace koma baya,hakanan yafi tsanarta fiye da kowa.

Shuru yayi ransa na masa suya shima,sai a sannan yadubi su mubarak da sukayi tsuru tsuru suna rarraba idanu a tsakaninsu

“Kuje dakin ummanku,daga nan kuce mata tazo yanzu ina kiranta” duka suka amsa dato suka sauka suka fice.

Yana jinta tanaci gaba da kukanta da qananun mitoci,saiya ciro wayarsa yakira rufaida

“Honeyy,baka shigo bane har yanzu?”

“Nashigo ina dakin mmn ummi”sosai ta bata rau,ta qanqance idanu kamar yana gabanta

“dakin mmn ummi kuma?”

“Eh,kizo yanzu inason magana dake” daga haka bai jira jin me zatace ba ya katse wayar.

Jin yakira rufaidan zuwa dakinta yasanya ta hanzarin goge fuskarta,kana tahau kalle kallen meye ba dai dai ba cikin dakin,saboda wunin yau sau daya tak tayi shara tun safe,bacin rai ya hanata,haka take,aduk sanda ranta ke a bace,haka yake mata tasiri ya hanata aiwatar da duk wani abun kirki,hakanan sai taji bacin rai yashafi kowa da kowama har yaranta,haka take fama dashi har zuwa sanda zai dusashe da kansa.

Balaifi dakin,saidai duk da haka ba neat yake sosai ba,lokaci yaqure ba abinda zata iya gyarawa,saboda haka tazauna tana ci gaba da kumbura,yayin dashi kuma yayi shuru saboda nazari daya fada,idanunsa sun dan sauya launi saboda bacin rai,ko almajirinsa baya yarda matan gidan su bari da yunwa,bare ace yau cikin gidansa aka wuni da yunwa?,harda yaran cikinsa?.

Mmn amir ce tasoma shigowa,tasamu waje tazauna bayan tayi masa sannu da zuwq,duba daya tayi masa tasan ranshi a bace yake,tasan dama hakan zai iya biyo naya,saitaja bakinta tayi shuru,idanunta kan tvn dake aiki volume can qasa,duk da itama rabin hankalinta yatafi ga tunani.

Tsayin mintina kafin rufaida tashigo dakin,hakanan tafito sanye da rigar,ba tare data nemi dan kwali mayafi ko hijab ta saya jikinta ba.

Tana shigowa mmn amir tadauke kai,ta sake maidawa ga tv kamarma bataga shigowarta ba,yayin da mmn ummi tazuba mata ido tacika tayi fam,ta dinga jifanta da harara,ji take kamar ta tashi ta rufeta da duka ko zataji sassauci cikin zuciyarta.

Kai tsaye ta isa inda bbn amir yake,niyyarta tayi hugging nashi duk da ummi dake hannunsa,amma kallo daya tayiwa idanunsa da fuskarsa ta fahimci cikin bacin rai yake,saboda haka ta gimtse,ta isa daura dashi sosao tazauna tana cewa

“Sannu da dawowa sweethert”

“Yauwa” ya amsa a gintse.

Sai daya tabbatar da kowa ya natsu sannan cikin dakakkiyar murya yajehowa rufaida tambaya

“Meya hana ayi girki yau duka a gidan nan?”duk da tasan wannan tambayar dama na iya biyo baya amma ba haka taso ba,taso ace yayi yadda tace ne ba tare daya titsiyeta a gabansu ba.

Ido ta zaro tana dubanshi

“waya gaya maka haka?,to nikam nayi girki don yanzu haka ma nasu yana kitchen,saidai idan basuje sun dauka ba kawai”.

Wani abu ya tsayawa mmn ummi iya wuya,harta kasa magana,tazubawa rufaidab idanu tanajin kamar tatashi tayita jibgarta.

Waiwayawa yayi yadubi mmn amir

“Anyi girki yau a gidan nan?”kai ta kada sannan tace

” gaskiya yau gaba day…..”bata qarasa ba rufaida ta tari numfashinta

“Banyi ba?,au hade kai xakuyi kuyimin sharri?,to aje a duba kitchen din agani idan banyi ba”.

” ya isa”bbn amir ya dakatar da ita,sannan yacewa mmn amir taci gaba,sai data aje numfashi cikin nutsuwa sannan tace

“Daga safe zuwa rana dai babu abinda aka dafa,saidai ban sani ba koda daren nan”.

Sake waiwayawa yayi ga rufaida ya kafeta da ido cikin bacin rai

“Kikace kuma kinyi girki” ciki ciki kamar mai guna guni tace

“Girkin dare ba,ai nayi”

“Meya hana ayi na safe da rana”

“Banajin dadine tunda kafita,hasalima ina kwance tunda kafita”

“Qarya take wallahi….dakaina nashiga namata magana ta gaggayamin magana yadda ranta yaso,shine dalilin daya tunzarani nakiraka kai kuma baka daga ba”

“Ha’an….ina ruwankine?,dake nake maganata?,ki bari a kasa dake saiki dauka ko?” Hayaniyace taso barkewa tsakaninsu ya tsawatar musu kafin kowa yakoma taitayinsa.

Fada sosai yarufe ido yayi musi gaba daya saboda barin yaran da yunwa,duk da mmn ummin ta gaya masa mmn amir tadafa musu wani abu,amma saiya hada duka,saboda dagashi har ita sunsan dasu su biyun yake,sai daya gama mai isarsa sannan yace yana duban rufaida

“Allaha yarufamin asiri saboda haka ban lamunci zama da yunwa ba a gidana,koda almajirin gidan nan banyarda a barsu da yunwa ba bare ku iyalina,qa’idane kowaccw mace ta gama abinci akan kari,daga na safe na rana zuwa na dare,idanma kinyi kan rashin sani to daga yau ki gyara kar in sake jin irin hakan takuma faruwa,koda baki da lafiya ki sanar musu,koki nemi daya daga cikinsu ta amsar miki girkin,kina jina ko?”.

Tabdijan danqari kan uba?,yau ita jibril yarufe ido yake mata masifa sabida shirgin yaransa da kucakan matansa?,da idanu take kallon mmn amir zuwa mmn ummi,baqinciki fal yacika zuciyarta,matan da take ganin basu kaita komai da komai ba,amma yau yazaunar da ita yana neman daidaita matsayinta da nasu,har yana mata fada a gabansu?.

1

Sai kawai tamiqe tana cewa

“Naji” sannan tawucw tafice fuu,mazaunanta na juyawa cikin matsatstun kayan jikinta,wanda su kansu sun bata ran bbn amir din,donme zata dinga irin wannam shigar tafito da ita har waje?,bayan tasani yana da yara wadanda suka fara tasawa,kuma kowa yasan yadda yaro yake da saurin fahimta da tsinkaye,dukkaninsu da idanu suka bita harta fice,yayin da gefe guda farinciki yacika zuciyar mmn ummi,tunda ko banza yau rufaidan tasha fada a gabansu,an kuma bata rashin gaskiya.

Waiwayowa yayi yana dubansu su biyun,duk da yadda ranshi ke masa suya tare da sake shiga mamaki kan sabbin halayen da rufaidan ta tsiro dashi,idanunshi akansu yace…….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page