KOMAI NISAN JIFA CHAPTER 12

 KOMAI NISAN JIFA CHAPTER 12

What? Shi Atif d’in?”

“Eh wlh yanzu ta kirani pls kayi sauri ka tafi kar lokaci ya k’ure”

Cikin hanzari ya shige motarsa tare da barin gidan a 260.

Ita kuwa Mubeenat gudu takeyi suna zagaye gidan,tana bashi hak’uri amma sai dayayi nasanar kamota ya d’auketa cak sai d’akin su.

“Ya Atif lafiyan ka kuwa? Wlh bana so kasan halin da kake ciki so kake ka cutar dani ne? Kodai dama soyayyar k’arya ce kake min?”

“Ko d’aya Sis Mubee,bazan tab’a cutar dake ba har abada,amma kuma gaskiya bazan so in rasa kiba dan ina k’aunarki sosai Sis Mubee kema kuma kinsan hakan”

“Kaga Ya Atif kazo muje gida,baikama muci gaba da zama anan daga ni sai kai ba,sannan gaskiya ka fara bani tsoro.”

Mik’ewa tayi da niyan barin d’akin,amma sai ya janyota zuwa jikin shi yana son kissing nata da karfin shi.

Nan dai yafi k’arfinta dan haka har riganta yake k’ok’arin cirewa, dai-dai nan Farhan ya iso bakin gate d’in inda ya tsayar da motar shi daga waje ya nufi cikin gidan da sauri yana kiran sunanta “Sis Mubee!”

Daga ita har Atif d’in sunji muryar Farhan dan haka Atif yayi saurin sa key a kofan tare da cire key d’in yayi jifa dashi a cikin d’akin da suke.

Nanne hankalinta ya sake tashi sai kuka takeyi tana cewa “Ya Farhan dan Allah ka taimakeni yasa key a d’akin”

Nan Farhan ya koma motarsa ya d’auko wani key wanda ko wace irin k’ofa ce zai bud’eta dan daga madina ya taho dashi.

Atif ya rabata da riganta bra kake hangowa sai kuma dogon siket d’in jikinta na atamfa tana ta faman kokuwa dashi da dukkan k’arfinta duk da dai tasan k’arfinsu bazai zo d’aya ba.

Jin ana bud’e k’ofa ne yasa Atif saurin danne Mubeenat da dukkan k’arfinsa,ita kuwa kuka take fiye dana dah tana mishi magiya.

Hankad’owar k’ofa sukaji dukda hakan Atif bai fasa aikata abinda yayi niyan yiba.

Wani irin takaicine ya tokari Farhan har zuciyarsa baisan sanda yayi kan Atif ba ya hankad’a shi gefe tare da fara kai masa duka wane Ubansa.

Ita kuwa Mubee sauri tayi ta d’auki rigarta ta fice zuwa parlour,sai data kimtsa kanta sannan ta sake dawowa se fad’a sukeyi babu wasa sam a fuskar ko wannen su.

Mubeenat kuwa tama rasa me zatayi dan haka ta fara kuka tare dasa ihu kamar wanda wani abu ya sameta. Hakanne yasa Farhan barin Atif ya nufo Mubeenat a rud’e yana kiran sunanta tare da k’are mata kallo ganin ta zube a k’asa.

Sunkuyowa yayi yana kallonta tare dayin magana “Habibty are you okay?”

Jin sunan daya kirata dashi yasa ta bud’e ido tana murmushi tare da kai idonta gun Atif da yake shirin bugawa Farhan vas d’in flawer mai shegen nauyi. Jarumta tayi da dukkan k’arfin da Allah ya bata tayi sauri tashi zaune tare da hankad’a Farhan da k’arfinta ya fad’i a gefe sannan wannan vas d’in ya fashe a kanta nan ta fad’i sumammiya gefen kanta na fidda jini.

“Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un” Farhan da Atif suke furtawa a tare.

Nan suka nufota dukkansu kowa na kiranta inda shi Atif yake cewa “Sis Mubee i’m sorry”

Shi kuwa Farhan yana cewa “Habibty…”+

Nan haushi da takaici ya kama Atif dajin sunan daya kirata dashi,dan haka ya nufi Farhan da fad’a na gaske sosai.

Hmmm sai a yanzu ne Farhan ya nuna masa cewa shi yarone nan yayi masa duka alamu ya nunama ya karya masa k’afa dan ya kasa tashi sai ihu yakeyi yana saiya kashe Farhan.

A haka Farhan ya d’auki Mubeenat a hannushi bai tsaya ko inaba sai motar shi inda ya nufi asibiti da ita hankalinsa a tashe.

Tunaninsa na farko shine halinda Mubeenat take ciki,na biyu kuma mezai gayawa su Abba dan ya tabbata ya raunana Atif da gaske. Da wannaan tunanin ya kira Ahmad ya gaya masa komai ya kuma ce mishi yaje ya duba Atif.

Koda Ahmad yaje Atif ya kasa komai sai kukan takaici yake wai Farhan ya d’auki Mubeenat da hannayenshi kuma yana gani amma bai iya yin komai akai ba.

Nan Ahmad ya taimaka masa ya kaishi asibiti amma ba inda Farhan ya kai Mubeenat ba kamar yadda suka tsara shida Farhan d’in.

Anan aka tabbatar da cewa Atif ya samu karaya a k’afa.

Asibitin da aka kai Mubeenat kuwa Doctor ya d’an wanke gurin da spirit aka mata komai tare da tabbatar musu da cewa bakomai insha Allah karsu damu kansu.

Nanne hankanlin Farhan ya kwanta sannan ya kira Abba ya sanar dashi cewa suna asibiti da mubeenat.

Babu jimawa saiga Abba ya iso yana tambayar meya sameta?

Nan dai Farhan ya bashi labari cikin girmamawa bai b’oye masa komai ba.

Salati Abba ya shigayi tare da tambayar yanzu ina Atif d’in?

“Yana asibitin shima shida Ahmad”

“Dan Allah Abba kayi hak’uri ya k’urenine shiyasa”

“Abun baimin dad’iba Farhan,ban tab’a tunanin zaka biyewa Atif har kuyi doke doke ba”

Sunkuyar da kansa ya sake yi “Dan Allah Abba kayi hak’uri,insha Allah hakan bazai sake faruwa ba”

“Bakomai Farhan,Allah ya basu lafiya”

“Ameen Abba nagode”

“To bari naje can asibitin na duba Atif d’in,zan turo koda Umman tane saita zo ta zauna kaima ka huta”

“To Abba ai bakomai ma,inaga indai ta farka zasu sallamemu ma”

“To Allah ya kyauta”

“Ameen”

Bayan tafiyar Abba da kusan 30minit sai Mubeenat ta farka,har yanzu dai Farhan ne kawai agun yanata fama kallonta.

A hankali ta fara bud’e idonta tana kallonsa zaune yana yimata sannu.

“Kayi hak’uri Ya Farhan duk laifina ne har kukayi fad’a”

“Karki damu ai ya wuce,ya jikin naki?”

“Da sauk’i”

“Me yasa kika zab’i ki cutu akan ni?”

“Ya Farhan hakan shine irin kariyar da naketa burin in baka koda so d’ayane nima a rayuwata kamar yadda kayi min a baya da kuma yanzu,duk da dai nasan bazan iya biyanka abubuwan daka minba,amma inhar ina kusa da kai bazan tab’a bari a cutar dakai ba Ya Farhan”

Lips nashi ya lasa tare da kiran sunanta acikin wata irin murya mai cike da k’auna “Habibty thankyou”

“Na kuma godewa Allah daya tak’aita ya kare ki baki samu mummunan rauni ba,da bansan ya zanyiba Habibty”

Murmushi tayi tare da cewa “Ya Atif fa?”

“Shima yana asibitin”

“Asibiti kuma? Meya same shi?”

Mik’ewa Farhan yayi tare da shafar gashin kansa yace “Habibty na kasa hak’ura akan halin danaga kin shiga,zuciya ta d’ebeni harna raunana shi yana asibiti”

Tashi tayi zaune tana kallon sa cike da mamaki “Me kayi masa Ya Farhan?”

“Kiyi hak’uri Habibty,Atif ya samu karaya a k’afarsa a sanadiya ta”

“Haba Ya Farhan,kai da kanka kake fad’a min haka? Karfa ka manta da cewa shi Yayana ne,sannan duk abunda yakeyi ba’a sonshi bane damuwar da yake cikine ta haifar masa da hakan”

Kansa ya sake shafa tare da juya mata baya sannan ya sake juyowa yana kallonta har cikin ido itama kuma haka “Isbiri Habibty,ke kanki kinsan waye Farhan kinsan mezan iya yi kin kuma san me bazan iyayi ba,shaid’anne yayi nasara akaina wannan karon,amma ina tabbatar miki da cewa zanyi k’ok’arin kiyayewa insha Allah,musamman ma danaga ranki ya b’aci a yanzu” yana kaiwa nan ya fice daga d’akin ya barta a zaune kamar wanda ruwa ya daka…

Shuru Mubeenat tayi tana tunanin kalamansa,ga dukkan alamu fushi yayi.
Ganin su Umma sunzo ne yasa Farhan komawa gida.
Mubeenat bata kwana ba aka sallameta ganin ta samu sauk’i sosai. Shi kuwa Atif yana can yana fama da nashi tare da jin haushin Farhan fiyema dana da.
Abba ya kirawo Farhan akan yazo ya maida su Mubeenat gida,koda yazo tambayarta kawai yayi yaya jikinta tace da sauk’i. Bayan nan bai sake ce da ita komai ba harya mai dasu gida yacewa Umma zai koma asibiti gurin Atif sannan ya fice.
Shima Atif kwanansa biyar aka sallamesu amma baya iya takawa saida wasu k’arafe guda biyu.
Doctors sun tabbatar da cewa zai samu lafiya da yardan Allah nan da wani lokaci.
Mum d’insa ce take kulawa dashi sosai a gida,amma duk ya rame saboda damuwa daya sawa ransa,ga rashin Sis Mubee ga kuma Farhan daya tsole masa ido.
Kullum k’ok’arinsa shine ya samu lafiya kamar yadda yake a baya dan a nashi tunanin zaije ya shawo kan Mubeenat.
Farhan kuwa tun maganan da Mubeenat tayi masa a asibiti saiya sauya mata kwata-kwata baya ma shiga harkarta iya kacinsu gaisuwa bayan wannan kuma shikenan.
Tun abun baya damunta har yazo ya fara damunta amma sam,bata nuna mishi saboda itama idda takeyi.
Yau tafiya ya kama Ahmad zuwa garin Zamfara wanda daga gurin aikinsu Ogansa ya aike shi. Suna zaune da Farhan yana gaya masa sai yace zai raka shi tunda kwana d’aya kawai zasuyi.
Suna zaune a parlour’n Abba ya shigo tare da sanar dasu cewa zasuje Zanfara shida Ahmad amma gobe zasu dawo insha Allah.
Sukai masa fatan alkhairi sannan ya fice suka tafi,zuciyoyinsu cike da k’una daga shi har Mubeenat.
A ko wace irin yanayine Farhan baya son abinda zai had’ashi da Mubeenat harma yayi baya-baya da ita,amma ya zama dole musamman ma yanzu da take cikin iddanta.
Kamar zata kirashi taji kosun isa lafiya sai kuma ta fasa domin ta tsare mutuncinta kar yaga kamar tana neman shishshige masa ne a nata tunanin.
Washe gari kafin su tasone Ahmad yaji kansa na tsananin ciwo,hakan yasa Farhan karb’an tuk’in ya kuma garzaya dasu asibiti mafi kusa dasu.
Bayan sunga Doctor an gama komai ne sannan aka bashi magunguna suka fito.
Dama Malam Buba ya kawo Umman Amal asibitin sakamakon ciwon ciki da yake damunta. Ai kuwa saita hango wata fuska daga nesa wanda ita dai tasan wannan fuskan a gidansu k’awarta wato Umman Mubeenat.
Nan ta tuna da cewa Farhan ne bak’in Madina,harsun shige mota suna shirin barin gurin sai tayi saurin sanar da Malam Buba, nan yayi saurin zuwa gun motar yana bubbuga da hannunsa ganin har sun fara tafiya.
Cak Farhan ya tsaya tare da cewa Ahmad “Lafiya kuwa,ina zuwa” sannan ya tsayar da motar tare da fito ya mik’awa Malam Bubu hannu suka gaisa.
“Bawan Allah ko kaine Farhan daga Madina wanda yake zaune a Gombe yanzu haka?”
Mamaki sosai Farhan yayi dan yasan shi bayida kowa a Zamfara.
“Eh nine,saidai ban ganeka ba?”
“Tabbas bazaka ganeniba amma zaka iya gane wannan matar?”
Juyowa Farhan yayi yana kallon Mahaifiyar Amal sosai. Nan yayita tunanin inda ya tab’a ganin fuskar,tabbas shidai bai santaba,amma ya tab’a ganin fuskar ta.
Nan ya tuno lokacin dasu Abba suke ta raba hotunanta harma a gidan TV.
Zare ido yayi tare da cewa “Umman Amal ce ko?”
Nan take ta fashe da kuka shi kuwa Malam Buba yace dashi “Kwarai kuwa ita ce”
“Allahu Akbar, Alhamdulillah” sannan ya juya da sauri ya koma gun motarsu tare da bud’ewa yace “Ahmad fito ga Umman Amal”
A firgice Ahmad ya fito yama nemi ciwon kan ya rasa yana bin inda Farhan yake da ido.
Tabbas wannan Umman Amal ce,dan kusan kullum saiya ga hotonta a wayar Amal. Nan ya sunkuya ya gaishe su cikin girmamawa suka amsa,sannan Farhan yace su shigo mota saisu k’arasa gida.
Haka kuwa akayi suka shige anata tattaunawa tun daga hanya yayinda suke ta mamakin bayanin da Malam Buba yake basu game da had’uwarsu da Umman Amal.
Zaune suke a tsakar gidan Malam Buba yana basu cigaban labarin har zuwa mafarkinta na shekaran jiya datayi. Yaci gaba da cewa “Dama yau zamuje garin Gomben,sai kuma ta tashi da rashin lafiya ashe kuma da rabon zata ganku ne”
“Allahu akbar,Allah mai girma da d’aukaka Allah maiyin yadda yaso a kuma lokacin daya so,Alhamdulillah gaskiya bansan wani irin farin ciki ‘yan Gombe zasuyiba na dawowarki Umma,musamman Amal kullum cikin kuka take wlh”
Malam Buba yace “Ai dole tayi kuka yaro,kuka ya zama dole,amma daga yau ai kuka ya k’are sai kuma kukan farin ciki”
“To yanzu yau zaku koma kenan?”
“Eh dama yau zamu koma,amma zamu bari sai gobe inyaso saimu tafi gaba d’aya daku” cewar Farhan.
“Toh ba komai Allah ya nuna mana goben”
“Ameen” sannan Farhan ya kira Abba ya sanar dashi wannan abun farin cikin,yayita mamaki tare da murna harma ya had’asu da Malam Buba suka gaisa tare da tabbatar masa da cewa zasu taho gobe dasu Farhan.
Nan Abba yayita godewa Allah tare dayin murna  ya kuma nasar dasu Umma.
Amal da take kwance a gida sai taga wayar Ahmad,take ta d’aga tana cewa “Kun taso ne?”
“A’a bamu taso ba sai gobe insha Allah”
“Amma kasan ba haka mukayi da kai ba ko?”
“I’m sorry ina kuma tayaki murnan dawowar farin cikinki wato Umma,gata ku gaisa”
Amal bata gane me yake nufi ba dan haka tace “Me kake fad’i ne?”
Muryar Ummanta taji cikin kuka tace “Amal?”
K’irjintane taji ya buga take ta mik’e gami da dafe k’irji tace “Ummana kece kodai kunnena ne?”
“Nice Amal ba kunneki bane,nice dai Mahaifiyarki Amal d’ita”
Nan take Amal ta fara kukan farin ciki tana magana da mahaifiyarta cike da so da kuma kewarta har ji take inama da itace suke tare a yanzu ba Ahmad ba.
Hmmmm Allah sarki duniya,babu wani abu da yake dauwama har abada indai mutum ne yayi ba Allah ba.
Dukiya,mulki,arziki,tak’ama duk zasu k’are,idan kuma basu k’areba tofa lallai kai daka ajiyesu ko kake gadara dasu zaka k’are ka barsu watan wata rana.
ALLAH KASA MUFI K’ARFIN ZUCIYOYINNU AMEEN…Samira kuwa ranar bata nan taje unguwa dan haka batama san abinda yake faruwaba,hakama shi Abban Amal ba’a sanar dashi ba dan baya nan kuma number’n shi baya shiga.
Atif kwance yake yanata kiran number’n Mubeenat amma bata d’agawa,dan haka yasa Aisha ta kirata shima k’in d’agawa tayi dan tasan duk shine. Amma a cikin ranta tausayinsa take sosai,dan takan tuna rayuwarsu na baya.
Wayarta ce ta sake yin k’ara,tana dubawa sai taga Ya Farhan ne da sauri ta d’aga tare da cewa “Assalam”
“Wa’alaikis salam”
“Ya Farhan ina kwana?”
“Lfy k’alau ya jiki yasu Umma?”
“Alhamdulillah kowa lfy”
“Na kira wayan Abba dana Umma duk baya shiga,ki sanar dasu cewa mun taso”
“To insha Allah,Allah ya kare ya kawoku lfy”
“Ameen Ahmad yace agaisheki da jiki”
“To nagode agaishe shi”
“To zaiji sai mun iso”
“Ya Farhan?”
“Na’am”
“Wai fushi kake dani ne?”
“Na isa? Ki bari idan muka tsaya zan kira”
“To shikenan dama na d’auka ko fushi kake,tunda ba haka bane ba komai Allah ya kawoku lafiya”
“To ameen nagode.”+
Dad’i Mubeenat taji dan ita duk a tunaninta fushi yake da ita.
Gun Umma ta wuce ta sanar da ita sak’on Ya Farhan,sannan suka tsunduma kichine domin shirya abinci.
5:12pm su Farhan suka iso har k’ofar gidan su Amal. Da gudu ta fito ta rungume Ummanta suna kuka,su Mubeenat ma ba’a barta a baya ba tazo ta rungumeta tare da ‘yar k’walla tace “Mun godewa Allah daya dawo mana dake Umma”
“Sannunku Mubeenat,baki da lafiya ne? Naga duk kin rame”
“Eh amma naji sauk’i” sannan ta d’auki kaya ta wuce dashi ciki.
Bayan an gama shiga da kayanne su Farhan suka koma can gida domin su d’an watsa ruwa kuma suci abinci,Ahmad dai yak’i zama dan haka ya wuce gida shima.
Mubeenat ta d’auki abincin su Umman Amal takai musu harda shi Malam Buba da aka sauk’eshi a parlour’n Abban Mubeenat.
6:00pm saiga Samira da Sagir sun dawo daga nasu damuwar batare da sun san abinda yake faruwa ba.
Ai kuwa suna shiga sai sukajiyo murya anata hira,wa zasu gani? Umman Amal ce zaune ita da Umman Mubeenat ga kuma Amal Mubeenat da Shureim ana zazzaune anata hira. Ai daga Samiran har Sagir sake matsowa sukayi dansu tabbatar da abinda idanunsu yake nuna musu,suna had’a ido Samira ta fad’i sumammiya wanda yayi dai-dai da shigowan Abban Amal dayake Abban Mubeenat ya kirashi yace lallai yazo gida yanzu.
Da sauri ya k’arasa ya d’ago Samira yana jijjigata tare da cewa Sagir “Tome ka tsaya kanayi yi maza-maza kabani ruwa”
Sagir kam ai sayya fara cewa “Shikenan,wlh shikenan komai ya lalace tunda ta dawo”
Cikin rashin fahimta Abban Amal yace wa kenan?”
Sagir ya nuna Umman Amal da yatsan hannu yace “Gata can,dama Malam na ruga ya fad’a min wlh indai ta dawo to komai ya k’are asirinmu ya tonu kenan”
Abban Amal saiya tsaya ganin Umman Amal kamar wani zombi.
Shi kuwa Sagir saiya hau fad’e-fad’e kamar an tambayesa ya basu labarin abinda ya faru tun daga farko har k’arshe.
“Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un” aketa maimaitawa agun. Duk daya gama basu labari saiya d’aura da cewa “Ganin bata samu cikin bane yasa na bata shawaran neman wani Namijin a waje domin ta samu ciki muce naka ne,shine ta had’u da wani saida suka gama duk abinda zasuyine yake sanar da ita cewa yana d’auke da cutar k’anjamau yanzu haka daga asibiti muke kuma an tabbatar da cewa tana d’auke dashi itama.
  Abban Amal dake rik’e da Samira a jikinshi ai saiya saketa a k’asa yana “Allah ya isa tsakanina daku bazan tab’a yafe mukuba wlh”
Umman Mubeenat ce ta mik’e tare da d’ibo ruwa ta yayyafawa Samir,cikin wasu mintina kad’an ta farfad’o tana zazzare idanu tare da binsu da kallo.
“Tashi ki tattara komatsanku kubar min gida na sakeki saki Uku Samira,sannan wlh Allah ya isa tsakanina daku bazan tab’a yafe muku ba azzalumai kawai kun cutar dani da mamata harma da ‘yata wlh dolema Allah ya d’aura miki wannan bala’in tashi ku fita nace!”
“Dan Allah kayi hak’uri nicefa Samiranka ka yafemin,idan ka koremu ina zamu je?”
Ai baima jira ta gama fad’in abinda take cewaba ya wuce ya d’auko wani igiya ya fara zuba mata kamar wani tsohon mahaukaci ita kuwa sai ihu take kamar jaka,shi kuwa Sagir d’aki ya wuce ya kwashi kayansa ya fita da gudu dan yasan idan ya shiga hannu tofa zaisha wahala sosai.
Umman Mubeenat ce taketa bashi hak’uri amma ina baya sauraron kowa duka kawai yake,ganin hakanne yasa Shureim zuwa gida ya sanar da Ya Farhan dasu Abba.
Ai cikin sauri suka shigo harda Malam Buba sannan fa aka samu aka ceci Samira data zama kamar wata mahaukaciya duk ta yaye kayan jikinta da birgima har pant nata ana hangowa gashi bulalan ya kwanta a jikinta rad’a-rad’a.
Mubeenat da Amal sai dariya sukeyi tare da cewa “Dama ai mun tab’a gaya miki Samira KOMAI NISAN JIFA lallai k’asa zai dawo,jifanki rayi nisa sosai wanda har muke tunanin kodai bazai fad’o bane,sai kuma gashi ya dawo.”
Sam babu wanda ya dakatar dasu saida suka mata tass! sannan suka wuce d’akin Umman Amal suna k’arasa gyare gyare da Amal ta fara bata k’arasa ba.
Abban Mubeenat yace su shiga daga ciki tukunna ayi magana,amma Abban Amal yak’i fur yace ai babu sauran wani abu tunda ya saketa. D’akinta ya wuce ya d’ibo mata kayanta dama a had’e suke dayake bata da gaskiya ko jera kayan batayi a wall drop suna cikin akwatinta dan haka ya fito dasu yace ta kwashe tayi gaba.
Kuka takeyi tana bawa Umman Amal hak’uri da neman yafiya,Umman Amal tace “Na yafe miki Samira kije can kiyita fama da abinda kike d’auke dashi,sannan daga yau ki manta da cewa kinsanni a rayuwarki barema har kiyi tunanin sake zuwa inda nake.”
Farhan ne ya fitar mata da kayanta har wajen gate sai ihu takeyi tana kuka kamar zararriya anan ya barta ya dawo cikin gida yayinda mai gadima yake zaginta iya son ran sa…A parlour’n Abban Amal suka taru dukkansu inda akacewa su Mubeenat su fita waje.
Bayan sun fitane Shureim ya d’auki kekensa ya fita, Mubeenat da Amal kuwa suna lab’e ta yadda baza’a gansu ba dan suma suna son jin me za’a tattauna.
Abban Mubeenat ya fara da cewa “Ba wani abu bane yasa na taho da Farhan saidan naga yana da ilimin addini,daga ku harni kowa zaiso sanin ya al’amarin zata kasance na aure akan aure,wannan shiyasa na gayyato shi domin ya sanar damu hukuncin hakan a addinance.”
Farhan ya maida dukkan hankalinsa garesu ya fara magana kamar haka “To gaskiya dai Abba ba’a aure akan aure,amma dayake ba’a hayyacinta takeba tunda ko kanta bata saniba sakamakon asiri da aka mata wannan bata da laifi kuma aure ya d’auru tunda anbi duk hanyan data dace,ina nufin an d’aura aurenne agaban shaidu da kuma sadaki  aure ya d’auru”
“Amma fa tun daga lokacin data gane kanta tasan cewa lallai ita matar aure ce a baya ma’ana dai muce lokacin da asirin ya karye harta dawo hayyacinta to aurenta da Malam Buba ya warware kenan koda ya saketa koda bai saketaba auren ya k’are, saboda idan tana a hayyacintane ai bazata tab’a yarda a sake d’aura mata aure da wani ba”
“Maganan dai shine yanzu babu aurensu da Malam buba”
Shuru Malam Buba yayi yace “To Amma tana d’auke da cikina yanzu haka”
Farhan ya sake cewa “Koda kun haihu da ita ne wannan abinda kuka haifan d’an halal ne,sannan yanzuma cikin na halal ne”
“To yanzu ni ya zanyi kenan Malam Farhar?” Cewar Malam Buba.
Farhan yace “A shawarce inaga kayi hakuri tunda kasan tana son mijinta,idan ta haifa maka abinda aka samu wannan kana da ikon zuwa ka karb’a duk dai yadda kukayi.”
“To shikenan dukda dai ance auren ya warware amma gara in tabbatar wa kowa, na sauwak’e miki.”
“Amma ina neman alfarma idan kin haihu abinda aka samu zanzo in karb’a daga baya”
“Farhan yace wannan tsakaninku ne ai,sannan yanzu Umma zakiyita zaman idda harse randa kika haifi abinda ke cikinki sannan iddarki zata k’are  ki koma gun Mijinki.”
Abban Amal yace mungode sosai Farhan,kai kuma Malam Buba kayi hak’uri dan Allah”
“Haba ba komai wlh wannan abu Allah ne kad’ai yafi sanin dalilinsa,dan haka bakomai wlh nine da godiya sannan kuyi hak’uri watak’ila nayi saurin auranta a cikin shekaru biyu kawai dan ba’a samu masaniya akantaba nayi saurin auranta.”
“K’addara ce ai,haka Allah ya tsara babu yadda muka iya” cewar Abban Mubeenat.
Itama Umman Amal godiya tayi tare da bawa Malam Buba hak’uri sannan Farhan ya fita ya basu guri.
  Kunya sosai Mubeenat da Amal sukaji alokacin da suka tabbatar Ya Farhan ya gansu ya kuma san lab’ewa sukayi.
“Sis Mubee?”
“Na’am” kanta a sunkuye dan kunya.
“Muje gida”
Ba musu ta kalli Amal tare da d’aga mata hannu sannanu tabi bayan Farhan.
Har saida ya shiga gida sannan ya tsaya tare da juyowa yana ganinta ita kuwa kanta sunye zata wuce shi sai kuma ta tsaya “Ya Farhan kawai muna son muji yadda aurensu yakene shiyasa muka tsaya agun”
“Ok but meyasa bazaku tafiba kamar yadda aka gaya muku,inyaso daga baya aisai ku tambayeni ko?”
“Bazamu sake ba insha Allah,kun dawo lafiya?”
“Lfy lau,shikenan kije”
Sannan ta wuce parlor’n Umma tare da shigewa d’akinta ta fad’a kan gado tanata dariya.+
Kwanan Malam Buba d’aya a gombe ya koma garinsu.
Ita kuwa Umman Amal gidansu ta koma domin rainon cikin dake jikinta da kuma zaman iddanta. Mubeenat tayi-tayi abar Amal ta zauna a gidansu amma ina,itama kanta Amal d’in tana son tabi Mahaifiyarta dan tayi kewanta sosai.
Ranan kuka sosai sukayi daga ita har Mubeenat d’in dan basa so su rabu da juna.
Tun bayan tafiyarsu Mubeenat ta nitsu a gida a kuma d’akinta bata ko fitowa inba Abba taje gaisharwaba da asuba.
Lamarin Atif kuwa abin tausayi ya rame sosai ya zama wani iri dan sam baya shan maganinsa,sai dai randa akayi sa’a idan Mum nashi tana kusa saita sashi agaba dolensa yasha. Idan kuma bata nan sai dai yace mata yasha alhalin kuma k’aryane.
Hakan yasa ciwon ya shiga jikinsa sosai idan ka ganshi dole ka tausaya mishi,gashi babban damuwarshi a yanzu bai wuce yaga k’afarsa ta warke ba ya koma gun Sis Mubee nashi ya kuma d’auki mataki akan Farhan.
Aisha batada aiki sai kuwa domin tausayawa Yayanta da takeyi,taje gurin Mubeenat harta gaji tana gaya mata irin halin da Atif yake ciki dan Allah taje ta dubashi kozai d’anji dad’i damuwarsa ta ragu amma sam Mubeenat tak’i dukda cewa kuma har cikin zuciyarta tana tausaya mishi dan wataran saita zauna tayita kuka Umma tayi mata tambayan duniya akan abunda yake sata kuka amma sam bata fad’a nan kuwa tausayawa halin da Atif yake ciki kawai takeyi.
Tana kwance a d’akinta saita d’auki wayarta ta kira layin Atif,ai kamar dama yana jira nan take ya d’aga tare da cewa “Hello Sis Mubee” cikin wata irin murya maiban tausayi.
K’wallan idanunta ta goge tace “Ina wuni”
“Please karki gaisheni Sis Mubee ki bari nina gaisheki,ina wuni Sis Mubee?”
Nan take taji hawaye yana bin kan fuskarta wanda ta kasa tsayar dasu.
“Ya jikinka Ya Atif?”
Nan ya fahimci cewa kuka takeyi dan ya baiyana a muryarta.
“Yanzu naji sauk’in jikina Sis Mubee,dama kinsan kece samun lafiyata”
“Allah ya baka lafiya”
“Ameen ya naki jikin?”
“Alhamdulillah ka dena damuwa dani ka damu da kanka Ya Atif,kana shan magungunanka kuwa?”
Shuru yayi dan yasan baya sha saidai idan Mum tana kusa.
“Ya kayi shuru? Hakan ya nuna baka sha kenan? Meyasa Ya Atif? Ina alk’awarin daka min na cewa baza kayi missing nashan maganinka ba?”
“I’m sorry Sis Mubee,amma daga yau nayi miki alk’awarin bazan sake missing ba”
Dad’in hakan taji har cikin ranta “Alk’awari fa kace Ya Atif?”
“Yes Sis Mubee,and i mean it,zaki iya tambayan Aisha domin ta zame miki shaida”
“Karka damu Ya Atif,nida kaina zanzo in tabbatar dan naji Umma tace ka rame sosai babu dai yadda kake,idan har zaka fara taking drogs naka yadda ya dace ka kuma tabbata kana cin abinci sosai to ina tabbatar maka da cewa zan dinga zuwa dubaka kullum,zan kuma dinga d’aukan wayarka wannan alk’awarine”
Dad’i sosai yaji har cikin ransa “Thankyou so much Sis Mubee,dama rashin jinki da banayi shine kad’ai yake ramar dani,amma yanzu komai yazo k’arshe insha Allah zakiji labari mai dad’i akaina”
Murmushi tayi mai d’an sauti tace “Thanks too Ya Atif saika sake jina”
“Alright,but please Sis Mubee pick my call”
“No Ya Atif,ai munyi magana dakai dan haka zan d’aga wayarkane inhar naji ance kayi jiki ka fara komawa yadda kake kafin na d’auki wayarka kuma na dinga zuwa ina maka hira kullum”
“To shikenan,thankyou Sis Mubee”
“Don’t mention Ya Atif byeee” sannan ta katse wayar tana share k’walla.
Shima Atif wani sabon farin ciki yake ji ayau da Mubeenat ta kirashi har kuma yaji tana kuka. Maganinsa ya janyo dama yayiwa Mum k’aryan yasha dan haka yasha tare da zuba abinci yaci sosai sannan ya kwanta yana tuna kalamanta…Ahmad da ‘yan gidan su ne gayya guda suka tafi gidansu Umman Amal domin taya ta murnan dawowa.
Nan dai suka sake gabatar da D’ansu wato Ahmad a gun Umman Amal. Dad’i taji sosai tayi  addu’an Allah ya tabbatar da alkhairi.
Atif dai baya wasa da shan magani da kuma cin abincin duk akan lokaci yakeyi yanzu,Mum da Aisha har mamakinsa sukeyi. Cikin ikon Allah harya fara maida jikinsa matsalar dai yanzu na k’afan sane dan sai ya d’auki watanni uku zuwa hud’u kafin ya zama normal.
Farhan kuwa yayi shirinsa tsaf na tafiya Madina domin yaje ya dubo iyayensa da abokan arziki.
Abba ne da Umma zaune a parlour’ suna tambayarsa inya tafi yaushe zai dawo?
“Eem gaskiya Abba inaganin zaikai 3 to 4 month kafin na dawo insha Allah”
“To Allah ya nuna mana Allah ya kare”
Ameen nagode sannan ya fice.+
Watan Mubeenat d’aya kenan da fara iddanta tafiyar Farhan yazo.
Dama can ba wani had’uwa sukeyi sosai ba dukda suna gida d’aya,dan haka ko labarin tafiyar nasa bata dashi dayake Umma bata gaya mata ba.
Amal ce take gaya mata cewa “Ashe Ya Farhan zai tafi Madina?”
Mamaki sosai Mubeenat tayi tare da cewa “Wlh to nidai ban sani ba sai yanzu danaji a bakin ki,yaushe zai tafi?”
Ita kanta Amal tayi mamaki tace “Kamar ya baki sani ba,jibi fa zai tafi”
“Amal kinsan dai bazan miki k’arya ba,wlh ban saniba ban kuma ji labari ko’a bakin Shureim ba,kinsan na gaya miki haka kawai naga ya fita harkata shiyasa nima kawai naja baya banama yadda ko had’uwa muyi wlh.”
Murmushi Amal tayi tace “Lallai kam kome dalilin hakan?”
“To waya sanine,nidai nasan ban mishi komai ba,wata k’ila kodan yaga Ya Atif ya sakenine kuma dai yasan bana d’auke da irin cutar Ya Atif bare ma ince ko k’yamata yakeyi,k’ila dai a tunaninsa zanyita rawan jikine dan soyayyarmu na dah ta dawo shi kuma baya ra’ayina a yanzu shiyasa yake k’ok’arin kauce min”
“Haba Mubeenat ke kanki kinsan Ya Farhan bazaiyi haka ba”
“Hmmm Amal kenan bakisan namiji bane,idan ba haka bane tome dalilinsa? Kinsan ranan yana cin abinci a parlour’n Umma wlh ina fitowa daga d’aki kawai naga ya mik’e ya d’auki plate d’in yayi waje batare daya cemin komai ba abun ya dameni Amal,shiyasa kawai nima na b’oye kaina ta yadda ma bazai ganniba harya bar inda nake.”
“To Allah ya kyauta” cewar Amal.
“Ameen” Mubeenat tace tana mamaki dan Amal bata wani nuna damuwarta akan hakan ba.
Ana gobe Farhan zai tafi suna zaune da Shureim a d’akinsa Shureim yace “Yanzu Ya Farhan baza kama Sis Mubee sallama ba?”
“Uhum Shureim? Idan kaje saika ce mata zanyi tafiya gobe kaji?”
“Amma meyasa kai bazaka gaya mata ba?”
“Dani da kai ai duk d’ayane ko?”
“Eh amma ai zatafi jin dad’i,kasan jiya ta tambayeni wai da gaskene zakayi tafiya,nace mata eh sai tayi shuru.”
Murmushi Farhan yayi tare da mik’ewa yana duba takardun hannunsa yace “Idan kaje ka gaya mata sak’ona kaji ko?”
“To shikenan bari na tafi”
“To muje na raka ka”
Har parlour’n Umma ya rakoshi inda Shureim yayita k’walawa Mubeenat kira take ta fito tana cewa “Wai lafiyarka kuwa kake ta kirana… bata k’arasaba sukayi ido hud’u da Farhan.
Da sauri ya kauda kansa zuwa Shureim yace “Tona rakoka ko? Saida safe” yana shirin fita Shureim yace “To Ya Farhan ga Sis Mubee d’in ka gaya mata da kanka mana”
Kallon juna suka sakeyi sannan yace “Sis Mubee gobe zanyi tafiya insha Allah zuwa Madina”
Da sanyin jiki tace “Allah ya kiyaye hanya a gaida su Ummi” sannan ta juya ta koma d’aki suna binta da kallo.
  Shureim ya kalli Farhan yace “Ka gani ko,fushi tayi ai”
“Ba fushi tayi ba,kaje ka kwanta saida safe” sannan ya fice shima aka bar Shureim tsaye a parlour.
Washe gari haushi ya hana Mubeenat fitowa suyi sallama kuma tana ji ana mishi Allah ya kiyaye sam tak’i fitowa.
Umma ce tace “Shureim jeka dubo Mubeenat kodai bata tashi bane?”
“To” sannan ya wuce d’akinta tana jin shigowarsa ta rufe idanu kamar maiyin bacci.
“Sis Mubee2 wai inji Umma kizo kuyi sallama da Ya Farhan zai tafi”
Shuru tayi tana jinshi tak’i tashi dan haka ya koma yace “Umma bacci takeyi har yanzu”
“Bakomai Umma inta tashi agaya mata nina tafi”
“To Farhan Allah ya kare agai dasu Ummi da Abbi”
“Zasuji” sannan Ahmad yaja mota suka tafi.
Isar Farhan Madina akaita murna tunba Iyayensaba,sai shagwab’a shi Ummi takeyi shi kuwa yana biye mata son ranshi.
  Kowa yayi waya da Farhan dan yaji koya sauka lafiya amma banda Mubeenat,har saida Umma ta tambayeta kin kira Farhan kuwa kinji koya isa lafiya? Bayan tace mata eh ne sannan ta d’auki wayarta ta tura mishi da texs kamar haka
           Slm da fatan ka isa lafiya ka kuma sami su Ummi lafiya,masha Allah agai dasu.
Kodaya gani murmushi kawai yayi tare da tura mata reply kamar haka
Wslm! Alhamdulillah Shukran.
Koda ta gani sai abin ya sake mata zafi sosai harma tayi tunanin da bata tura mishi ba.
Tun daga wannan ranan babu wanda ya sake neman wani a tsakanin su,abin yana ta cin Mubeenat a ranta amma babu yadda ta iya haka kullum take cikin tunani harta rame.
Wata biyu kenan Farhan yayi a garin madina hankalinsa kwance domin Umminsa da Abbi sun gama had’a komai na bikin shi.
Washe gari suna zaune a parlour Farhan yanata damun Abbi akan lallai ya kira Abban Mubeenat.
Haka ya kira suka gaisa dukkansu sannan yace “Abokina ga D’anka nan kusa dani tun jiya yaso in kiraka amma nace ya hak’ura zuwa yau yana sake neman auran ‘Yarka Mubeenat a karo na biyu.”
Dariya sosai Abban Mubeenat yayi tare da cewa “Ka sanar dashi an bashi domin hankalinsa ya kwanta”
“To amma ka sanar da ita Mubeenat d’in,wata k’il akwai wanda take so daban kuma” cewar Abbi.
“Haba Abbi kai kake fad’in haka kuma?” Cewar Farhan.
Dariya suka saka dukkansu sannan Abbi yace “To mun gode sosai,kuma inda hali wannan karon zamu so muzo da komai namu lokaci guda dan D’an naka baya so abun ya  d’auki lokaci kunyarka yakeji sosai.”
“Hhhhh Allah sarki Farhan,bakomai insha Allah yadda yake so haka za’ayi”
Haka dai sukaita hiransu cikin raha dajin dad’i tare da sake taya D’ansu murnan dawowar Habibty farin cikinsa a karo na biyu.
“Abbi yaushe zamu tafi to?”
“Habibi ka kwantar da hankalinka insha Allah kaine Mijin Habibty kaji?”
“Allah ya amsa addu’arku Ummi” ya furta yana murmushi tare da rungume Ummin sa yana jin dad’i har cikin ranshi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page