KWAI CIKIN KAYA CHAPTER A BOOK1

 KWAI CIKIN KAYA  CHAPTER A

                    BOOK1

Bilyn Abdull ce🤙🏻

*بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَـٰنِ الرَّحِيمِ*

Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai.

Ya rabbi ka bani ikon faɗar abinda zai amfanar da al’ummar MANZON ALLAH (A.S.W), ka tsare harshena da alƙalamina ambaton abinda zai cutar da ni da ku a duniya da lahira.😭🙏🏻

Ya ALLAH ka gafartama mahaifina masoyina da dukkan al’ummar musulmi da suka rigamu kwanta dama, ALLAH ka kawo mana ƙarshen wannan annoba ta corona virus (covid-19), domin rahamarka garemu😭🙏🏻.4

_____________________________________

BOOK ONE

Shafi na ɗaya

_____________________________________

………..Ko wacce kafar yaɗa labarai da ta yanar gizo labarinsu a wannan safiya ta laraba shine sace shahararren mai arziƙin nan *Alhaji Sadi kokino (ba giyar yaro ba)*.

A yanda labaran ke ta yawo an sace Alhaji Sadi kokino ne a daren jiya talata a filin jirgin sauka da tashi na babban birnin ƙasar. Abu mafi ɗaure kai ga wannan lamari shine ta hanyar da mutumin da yay garkuwa da shi ya ƙwamushe sa. Da yawan mutane da suka shigo jirgi ɗaya da Alhaji Sadi kokino sun tabbatar ma jama’a da lafiya lau ya sauka, harma ya gaisa da wasu tsirarun mutane da suka je tarbarsa. Sannan akwai wasu ƴan jarida guda biyu a filin jirgin da har suka ɗauki hotansa da gajeren bidiyo. Kowa ya shaida Alhaji Sadi lafiyar ALLAH ya shiga motar da ɗaya a masu gadinsa ya buɗe masa, sannan amintaccen direbansa yaja motar a gaban kowa. Sai dai a lokacin da motocin suka shiga harabar gidansa aka sake buɗe masa ƙofa dan ya fita sai yace ku ɗaukeni inda kuka ajiye, a taƙaice dai Alhaji Sadi kokino yayi ɓatan dabo a hanyar dake tsakanin filin jirgi zuwa gidansa.

Zuwa yanzu dai jami’an tsaro sun bazu ta ko ina nemansa, tare da buɗe kunnuwa da idanu ko za’aji wani abu da ga bakin wannan mai ƙwamushe da ba’a san ta yanda yay siddabarun sace Alhaji kokino ba…+

*____________________________________*

A yayin da masu yawun mai da yanda akayi ke kaikawo akan wannan ruɗaɗɗen labari suma talakawa ƴan bani na iya sai tofa nasu albarkacin bakin suke. Ko wane dandalin sada zumunta na yanar gizo ka shiga sai kace nace akeyi. A yayin da wasu ke jimamin lamarin wasu ALLAH ya ƙara suke faɗa, a wani gefen kuwa ma kai tsaye suke ƙaryata lamarin da dangantashi da farfaganda irinta manyan ƙasa ce kawai, ƙilama yana can kwance a gidansa lafiyar ALLAH.

Daga masu ƙaryatawa har waɗanda suka gaskata kowa yana da dalilinsa, dan kuwa a yanda ƙwamishen ya kasance dolene ya bada mamaki, musamman idan mukai dubi da jami’an tsaro da cctv cameras da ke zagaye da filin jirgin, ga haske ta ko ina tamkar rana.

Koma dai yaya abin ya faru lokacine zai bayyana mana hakan😟.

*___________________________________*

Kwance yake a bayan motar idanunsa a lumshe tamkar mai barci, lokaci-lokaci yakan ɗanja guntun tsaki tare da huro zazzafar iska daga bakinsa.

Duk da kasancewarsa gwarzo kuma jarumin mutum mai ƙoƙari da jajircewa a aikinsa kallo ɗaya zakai masa a yanzu ka hango tarin gajiyawa da ɗunbin kasalar dake tattare da shi.

Tsayuwar motar da buɗe murfin da akayine ya tilasta masa buɗe lumsassun idanunsa kaɗan tare da ɗago hannunsa ya kai dubansa ga agogon da ke ɗaure a tsintsiyar hannun, kaɗan ya yamutse fuska yana sake huro iska kaɗan kafin ya sauke hannun da maida dubansa ga ƙofar motar da aka buɗe.

Tamkar bazai motsa ba sai kuma ya yunkura a hankali ya ja baƙar rigar sanyinsa jibgegiya dake gefe ya zura kafafunsa waje.

Da sauri wanda ke tsaye a gabansa da alama shine ya buɗe ƙofar yay azamar kai hannu zai amshi rigar sanyin yana sake ƙamewa alamar girmamawa.

Kansa ya girgiza masa ba tare da ya bashi rigarba, ya matse idanu kaɗan saboda sara masan da kansa yake na azabar ciwo, ya sauke numfashi kafin ya fito gabaɗayansa yana tura ƙaramar bindigar hannunsa a aljihun bayan wando.

Idanunsa da ke jajir ya ɗago yana saukewa akan matasan samari biyu, cikin hanzari suka ƙame tare da sara masa. Hannunsa na dama ya dinƙule kawai yay gaba ba tare da suma yace musu uffan ba. bishin sa sukayi a baya suma ba tare da sheresun da yay ya damesu ba.1

STORY CONTINUES BELOW

Cikin nutsuwarsa ya iso wajen da ake buƙatar ganinsa, da ganin yanayin ɗakin zaka fahimci wajene keɓantacce na jami’an tsaro da sukan tattauna akan wani case ko shawarwarinsu idan sun tado musamman ta fuskar tsaro.

Ba tare da yay magana da kowa ba ya samu waje ya zauna, suma sauran waɗanda suka shigo tare wajen zama suka samu. Ɗakin yayi tsit, bakajin komai sai ƙarar AC da na fitar numfashi, sai kuma ɗan motsin da baza’a rasaba.

Wanda ke tsaye jikin allon bangon yana wani ƴan zane-zane ya ɗago fuskarsa a matukar murtuke yana kallonsu.

“Nasan kowa zaiyi mamakin wannan taron na gaggawa da muka kira, duk da dai dukkan tunaninmu zai iya tsayawa a waje ɗaya game da abinda muka wayi gari da shi na sace babban mutum irin Alhaji Sadi Kokino. Kamar yanda muka sani tun a daren jiya wasu a cikin jami’anmu suna a wajen domin binciko ainahin abinda ya faru, a yanzu hakama daga can muka tado ɗaya da ga cikinsu domin ya bamu bayanai dangane da lamarin, sannan musan mataki na gaba da zamu ɗauka kuma, dan yanzu dai ga agogo ya nuna ƙarfe 7:19am, na tabbata duk inda 8am tayi wannan labarin zai gama baje duniya ne, sanin kankune kuma mune jami’ai na farko da kowa zai maida hankalin ji da ga garemu, tun daga kan jama’ar gari zuwa ƴan jarida da iyalansa dama jama’ar dunaya baki ɗaya”.

A tare suka shiga jinjina kai alamar gamsuwa da bayaninsa.

Cikin gyara tsayuwa ya ke kallonsu, ya sauke idanunsa akansa da har yanzu hannunsa ke dafe da kansa, *”Jawaad!”*.

Jin sunansa da aka ambatane ya sakashi janye hannunsa tare da ɗago manyan idanunsa da ke a jajur ya sauke akan ogan nasa, cikin dakewar murya da ke tabbatar da shiɗin jarumine ma’abocin nutsuwa ya amsa da “Yes sir” tare da miƙewa tsaye yana ƙamewa.

Gaban allon ogan ya nuna masa da biron dake hannunsa.

Cike da kasala mai tare da nauyin jiki ya taka zuwa wajen, ya maido kallonsa gaba ɗaya zuwa ga sauran jami’an tsaron dake cikin ɗakin taron.

Cikin nutsatstsiyar muryarsa mai amo da saka razani ga abokin gaba ya fara faɗin, “Duk abinda zan faɗa game da wannan lamarin a taƙaice zai iya zama gaggawa, dan har zuwa yanzu da na baro filina jirgin da gidan Alhaji Kokino babu wani bakin zare da muka samu a kai sai surutai marasa makama, a cctv cemaras na Airport kuma lafiya lau Alhaji Sadi ya shiga mota tare da masu tsaron lafiyarsa. A ɗan nazarina ta wannan gaɓar ya nuna lallai mai satar yanada matuƙar wayo, kuma ƙwararrene mai aiki da ƙwaƙwalwa…”

Kowa jin jina kai ya shiga yi alamar gamsuwa da bayanin Jawaad da ke riƙe da kansa da ke ƙara ƙarfin sarawa na ciwo.

Wanine cikin waɗanda ke zaune a kujeru na musamman, alamun shima babbane yay gyaran murya tare da gyara abin maganar dake gabansa. “Wato bayanan JAY abin dubawa ne kam tabbas, amma ku wace shawara ce da ku a kan hakan?”.

Wani ne da ga can rukunin kujerun da Jawaad ya taso ya ɗaga hannu, damar magana aka bashi. Bayan ya miƙe ya ƙame sannan ya fara magana cike da girmamawa, “Yallaɓai ƙwarai maganar jay gaskiya ce, sannan ya kamata muma muyi shiri na musamman akan wanann case ɗin, dan inhar muka kuɓutar da Alhaji kokino ba ƙaramin daraja hukumar ƴan sanda zata sake samuba a idon jama’a”.

Tafa masa sukai, wanima ya sake ɗaga hannu aka bashi dama, shima goyon bayansa ya nuna akan maganar Jawaad. Bayan shi mutane biyu sun sake yin mubayi’a kafin wani ya tashi shikuma bayan an bashi izini, fuska a ɗaure yana wani hura hanci da fesar da iska yace, “Sam wannan shawarar tasa bata kan tsari, ya kamata ama ƙalubalancesa, tun a daren jiya bayan faruwar abin da mintunan da basufi goma ba aka turashi wajen shida wasu jami’an tsaro, amma ace babu wani bayani na cigaba da aka samu, bayan a ƴan mintunan da sukaje wajen bai kai nisan da za’ace shi mai ƙwamishen yayi nisa ba, kawai shi dai yace bazai iyaba sai a nema wanda zai iya kawai, inba hakaba ta silar wannan case ɗin to lallai hukumar ƴan sada tana tare da babbar barazana ta zubewar kima da sake saka shakku a zukatan al’umma a kanmu”.

Kowa kallonsa yake kawai, yayinda manyan suke jinjina masa kai da wasu a tsirarun sauran jami’an.

Jawaad kam ko motsi baiyiba balle ya kalli wanda ya gama bayanin, sai dai ya saki wani ƙasaitaccen murmushi da ya bayyana loɓar kumatunsa guda biyu kawai.

Ba karamin sukar zuciyar Qaseem Ali murmushin Jawaad yayi ba, amma ta wani ɓangaren ya ɗanji sanyi a ransa ganin maganarsa taso kawo ruɗani, dan sai ya zam kawunan jami’an tsaron yana neman rabuwa, wasu suna bin bayan Jawaad Abdul’aziz yusuf, wasu kuma suna bin bayan maganar Qaseem Ali.

Dan danan cece kuce ya fara yawaita a ɗakin taron har sai da aka tsawatar.

Murmushi Qaseem Ali ya saki ganin Jawaad ya dafe kai, sannan fuskarsa ta kuma ɗaurewa alamar ransa ya sosu, dama babban burinsa kenan.

Sai dai kuma sam tunaninsa bai sanar masa gaskiya ba, dan shi Jawaad surutun da ɗakin taron ya kaure da shine ya kuma saka kansa ƙarfin bugun ciwon da yakeyi sakamakon rashin samun isashshen barci da yay a daren jiya, ga ruwan sama da yay musu dukan tsiya jiyan da daddare, bayan dama ya koma gida a ƙurarren lokaci ne jiyan kafin ayi kiransa akan maganar sace kokino.

Tsitt ɗakin yayi bayan tsawatarwar da akayi, yanzu ma ɗaya daga cikin shugabannin ne yay magana.

“Duk wani kace nace bama buƙatarsa anan, kowa yasan wanene JAY akan ƙwazon aiki, ba wannan ne na farko ba da aka bashi irin wannan damar kuma ya magance ta, sai dai ko wanne irin case da ruɗanin da yake zuwa da shi, dan haka a wannan gaɓar mun naɗa Jawaad Abdul’aziz yusif matsayin wanda zai kula da wannan case ɗin, sannan mun saka Qaseem Ali matsayin mataimakinsa, kuna da damar haɗa rundinar jami’ai 30 da zasu taimaka muku, muna fatan zaku bamu gudunmawa ta haƙiƙa wajen fiddamu kunya ku kuɓutar da Alhaji Sadi cikin lokaci ƙankani da baza’a ga rauninmu ko gazawa ba”.

Tunda ya fara magana Qaseem yaji sunansa matsayin mataimakin JAY fara’ar fuskarsa ta ɓace ɓat, hakama magoya bayansa. Ga Jawaad kam bai ko ɗago kaiba balle musan yanayin da yake ciki.

Sun ɗan cigaba da tattaunawa kusan na awa ɗaya, wandda acikin awa ɗayarnan ba ƙaramin a takure Jawaad ya tsinci kansa ba, ana kammalawa ya nema izinin zuwa gida ya ɗan huta koda na awa uku ne.

Babu wani jan zance aka bashi dama, dan yanayinsa ya nuna buƙatuwa sosai na san hutun…..

*___________________________________*

Tunda Gimba yay fakin motar a harabar gidan ya buɗe idanunsa da suka sake masa nauyi da ƙyar, ba tare da ya jira Gimba ya buɗe masa murfinba ya buɗe da kansa ya fice, rigar sanyinsa ce kawai a hannunsa sai bindiga da ƙaramar wayarsa da ya fita da ita kawai.

A yanda ya shigo ya ga falon jiya yauma haka ya sameshi, yaja siririn tsaki yana haɗiye wani abu mai nauyi da ya tsaya masa a maƙoshi, zuciyarsa a matuƙar cinkushe ya ƙarasa sama inda nanne ɗakin barcinsa yake.

Kallo ɗaya yayma falonsa ya ɗauke kai, dan hatta da kofin da ya sha shayi a daren jiya yana a inda ya barsa, sam shi baima san wace irin mace ya aura ba, ƙazama ko ballagaza?. Takaici bai nemi shake numfashinsa ba sai da ya ƙarasa haɗaɗɗen bedroom ɗinsa ya sauke dubansa a kan lafiyayyen gadonsa da har yanzu take kwance, ta wani ƙudundune cikin lallausan bargonsa tana shaƙar barci. Tuni idanunsa sun sake kaɗawa sun koma jajur, yayinda jijiyoyin kansa suka sake fitowa raɗa-raɗa, yasan ko rantsuwa yay baza a bisa bashin kaffara ba akan Shuhudah batai sallar asuba ba.

Bai sake kallon gadonba ya jefa rigar sanyin akan sofa tare da zube wayarsa da bindigar saman tabirin dake shakanin kujerar da gado.

Duk da wani jiri-jiri da yake gani saboda yunwar da ke cin hanjinsa hakan bai hanashi nufar bayi ba dan ya samu ya watsa ruwa ko zai samo kan jikinsa……………✍🏻4

Ku kasance tare da ni Bilyn Abdull dan jin yanda wannan littafi mai suna a sama zai kasance, minene ma ma’anar *ƘWAI CIKIN ƘAYA!!?*, nasan wannan tambaya ce dake cikin zuciyoyin masu karatu baki ɗaya, wadda ni Bilynku kaɗai zan baku amsarta😚.

Zata iya kasancewa cikakken buk ɗin sai bayan sallah ƙarama zaizo muku idan munkai da rai, idan kuma na samu dama koda ba kullum ba zanyi wasu pages kafin azumi insha ALLAH

ALLAH ka gafartama iyayenmu4Bilyn Abdull ce🤙🏻

Ban yarda wani yaymin amfani da littafin nanba ta kowacce hanya, komin ƙanƙantarta, inkuwa hakan ta kasance ban yafe ba☹️.

Na sadaukar da wannan littafi a gareku auntys ɗina, dan kune taurarin da Bilyn Abdull ke kallo a duniyar rubutunta, da ku kuma zan cigaba da alfahari Aunty Fareeda Ado gachi & Aunty Rahama Abdul-Majeed (writer mace mutum), alkairin ALLAH ya kai muku a duk duniyar da kuke har gadon barci.😘👌🏻

+

_____________________________________

BOOK ONE

Shafi na biyu

_____________________________________

…………Motsin ruwan wankansa ne ya farkar da Shahudah, tunda ta yaye bargon da ga fuskarta nake tsarkake sunan ALLAH buwayi gagara misali da ya halicci wannan ƙyaƙyƙyawar baiwa tasa. Lallai Shahudah ƙyaƙyƙyawace wadda zamu iya sakata a jerin farko na ƙyawawan mutane, gata fara tas tamkar wata aljana.

Har lokacin bata yaye bargon da ga jikinta ba, kamar yanda alamu suka nuna bata da niyyar tashi ma.

Kusan mintuna arba’in da shigarsa bayin sai gashi ya fito ɗaure da tawul ruwan sararin samaniya, yayinda ya rataya ƙarami fari a wuyansa, ya kama can ƙarshen tawul ɗin yana goge gefen kumatunsa.

Shahuda da har yanzu take kwanci ta a hankali ta buɗe ƙyawawan idanunta ta sauke akansa, hakan yayi dai-dai da kai nasa duban gareta shima. Kuma tamke fuska yay yana kauda idonsa a kanta tare da nufar mirror kansa tsaye. Kamar yanda baiyi magana ba itama sai bata ce uffanba sai binsa da kallo da takeyi.

Duk da Jawaad naji a jikinsa kallonsa takeyi bai juyoba, amma yana kallonta ta cikin mirror, murya can ƙasan maƙoshi yace, “Kinyi salla?”.

Ɓata fuska tayi tana kuma narketa alamar son yin shagwaɓa, “Haba bb, kamun laifi maimakon ka lallasheni da ban haƙuri saika wani faramin tambaya”.

Duk da ya jita sarai sai ya share tamkar bai jiba, ya cigaba da shafa mansa yana lullumshe ido saboda ciwon da har yanzu ya keyi, sauƙinsa ma ruwannan da ya sakarma kan ya ji daɗinsa sosai gaskiya.

Ba ƙaramin ƙunar zuciya ta kama Shahudah ba jin Jawaad ya shareta, ta turo baki gaba tana yaye bargon da take ciki.

Masha ALLAH na sake ambata ganin haɗaɗɗun kayan barcin da take sanye a ciki, sun mugun mannewa da farar fatarta, tare da zama ɗam jikin surarta tamkar dan ita aka halicci figigiyar rigar barcin da kaɗan ta gota mazaunanta, siririyace sai dai jikinta a murje yake alamar hutu, ba kowa ne zai ga Shahuda ya yarda ta haɗa jini da HAUSA FULANI ba, dan komai nata yafi kama da na masu jajayen kunnuwa…..

Saurin janyeta yay da ga jikinsa jin ta rungumesa ta baya yana kuma ɓata fuska, a matuƙar harzuƙe ya juyo yana sanya jajayen idanunsa cikin fararen nata masu cikar gashi da gira baƙa wulik a sama. Sam bazata iya jurar kallon cikin idonsa ba, dan haka ta wani yi farr da nata cikin salo irin na manyan yara da ke taƙama da wayewa.

Hanya kawai ya nuna mata ba tare da yace uffanba.

Yanzu kam ranta yakai maƙura da haushin wulaƙancin Jawaad, dan haka ta yamutse fuska cikin tsiwa ta taka gaban gadon ta saka silifas ɗinta masu taushi ta nufi hanyar fita.

Sai da ta kama hannun ƙofar ne ta tsinkayo Jarumar muryarsa na faɗin, “Saura idan kinje canma ki sake kwanciya kar kiyi sallar”.

Harara ta watsa ma bayansa da ya juya mata ta fice tana ƙunƙunin da ita tasan mi take faɗa.

Bai sake bi ta kanta ba ya kammala abinda zaiyi a gaban madubin ya nufi Wadrobe ɗinsa ya saka boxer kawai ya fito falo. Kayan tea da ke ajiye saman D/table ya nufa, ya ɗauki kofi ya haɗa komai kafin yaje ga disfensa ya matso ruwan zafi dai-dai buƙatarsa. A haka ya koma bedroom ɗinsa yana juya cokali cikin kofin shayin da keta tururi.

Zama yay bakin gadon yana shan shayin a hankali, ko zafinsa baya ma damuwa da shi. A da can sam baya shan shayi sosai, ya kan sha amma ba ko yaushe ba saboda baya cikin abinda ya damesa, amma tun bayan auren sa da Shahudah suka ƙulla abota da tea, a yanzu baya da abincin da ya bama muhimmanci a rayuwarsa irin shayi, tun yana sha akan dole harya fara zame masa jiki, inma bai sha ba sam baya jinsa dai-dai, a baki sunan kawai yana da matane, amma a aikace ita da hotiho babu banbanci, dan babu wani abu na matan kirki masu daraja da Shahudah ta iya, banda tsagwaron son jiki da son hutu babu abinda ta tara, a ɓangaren gyaran jiki dai kam gwana ce, dan ƴar gayuce ta gani kasheni, sai dai sam babu tarbiyya mai birgewa da akasan ƴaƴan musulmai da ita, komai nata kwaikwayone daga jinin yahudu da nasara, salla wannan sai yayi mata jan ido take yinta, daga lokacin da yay nisan kiwo kuwa a aikinsa baisan wace wainar take toyawa ba a ɓangaren bautar ALLAH….

A hankali ya sauke sassanyar ajiyar zuciya yana ajiye kofin hannunsa saman durowan gefen gadon, magani ya ciro a ciki ya sha kafin ya haye gadon da ke manne da ƙamshin turarensu ya kwanta yana jan bargon ya lulluɓe har kansa.2

STORY CONTINUES BELOW

Koda Shahuda ta koma ɗakinta sam bataji gargaɗin Jawaad ba akan tayi salla, sai ma gado da ta faɗa tana ƙunƙuni wai baza tayin ba, a haukanta da gajeren tunani tunda Jawaad ya ɓata mata rai to itama saita ƙuntata zuciyarsa da ƙinyin sallar da yace tayi, dan haka tai kwanciyarta barci ya sake kwasheta saboda sanyin garin na ruwa da aka maka a daren jiya.1

ALLAH ya ƙyauta to, saikace kabari ɗaya za’a saki da Jawaad ɗin Shahuda?🤔 kokuma shike bada sakamako idan anyi sallar🤦🏻‍♀️?, ALLAH ka rabamu da wayewa mara amfani⛹🏻‍♀️.

3

★★★★★★★

Ring ɗin wayarsa ne ya farkar da shi da ga nannauyan barcin da yay nisa a ciki, ya janye bargon da ga kansa da ƙyar tare da miƙa hannu saman dirowan gefen gadon ya ɗauki ƙaramar wayarsa da ke vibration. Ba tare da ya duba wanene ba ya ɗaga kawai ya saka a kunne yana sake maida idanunsa ya lumshe. Tsawon seconds arba’in yana sauraren mai maganar da ga can, kafin ya furta “Ok sir” cikin nutsatstsiyar muryarsa da ke gauraye da barci. Ƙarƙashin filon ya tura wayar yana sake juya kwanciyarsa hankali kwance, sai faman ɓata fuska yake na jin takaicin katse masa barci da akayi. Sai da yaja kusan mintuna uku sannan ya ture bargon yana jan dogon tsaki, ƙaramin agogon dake gefen dirowan gadon ya kalla, ⏰11:29am, numfashi ya sauke a hankali dan sam baiyi tunanin barcin nasa yayi dogon zango haka ba, tashi yay ya sauka daga gadon gaba ɗaya.

Sosai ƙyanƙyamin bayin nan yakeyi, dan yakai kusan kwana huɗu kenan babu wanki, tun randa Batool tazo bai sake ganin gyara ba saboda tsabagen lalacin matar gidan.

A ɗarare yay abinda zaiyi ya fito ba tare da ya sake wanka ba, baƙar jallabiyarsa mai dogon hannu ya ɗauka ya zura kawai da silifas ya fice zuwa ƙasa.

Sai sha ɗaya saura Shahudah ta tashi a sabon barcin da ta sake komawa, sai faman ɓata fuska take tamkar ance ta tashi dole ne, rigar barcinta ta zame tare da sakinta a tsakkiyar ɗakin tai tsaye tsirara da ga ita sai pant wanda shi da babu duk ɗaya, hankalinta kwance ko tunanin bayan jinsinta akwai na aljanu da ido baya ganinsu a ɗakin batai ba, a haka ta nufi bathroom.

Tsawon lokaci ta ɗauka a ciki kafin ta fito ɗaure da wani mitsitsin tawul kalar ruwan hoda, shima tana zuwa gaban mirror ta sakeshi ƙasa, a haka ta shafa mai kafin ta buɗe Wadrobe ta ɗauki doguwar riga ɓaƙa ta saka, tare da naɗa ɗankwalin rigar ta ɗau abin salla ta shinfiɗa.

🤥tsantsar mamaki da al’ajab sun rufeni ganin sai yanzune Shahudah zatai sallar asuba, sha ɗaya da kusan ƙwata🤦🏻‍♀️.

Ina nan zaune ganin ikon ALLAH harta idar da sallar tata a cikin ƙanƙanin lokacin da bazai gaza mintuna uku ba. Rigar ta sake cirewa ta ajiye, ta ɗauki tawul ɗinta ta sake ɗaurawa tare da jan stool ta zauna aka fara tsara ƙwalliya ta garari.1

Kai tsaye ɗakin Shahudah Jawaad ya shiga, juyowa tai ta ɗan kallesa ta ɗauke ido ita a dole fushi takeyi da shi.

Shima sai da ya fara ƙarema ɗakin kallo kafin ya kai dubansa gareta, kallon kusan seconds goma yay mata sannan ya cigaba da takowa cikin ɗakin, jikin bangon da mirror yake ya jingina tare da harɗe ƙafafunsa waje guda ya tura duka hannunsa a aljihun jallabiyar.

Tsayuwar tasa sai ya zam tamkar sun fuskanci junane shi da Shahudah, hakan yasa ta sake ƙwaɓe face ɗinta tana cigaba da zana kwalliyarta.

Tsawon mintuna biyu suna a haka, babu wanda ya cema ɗan uwansa ci kanka, sai zuwa can Shahudah ta ɗago manyan idanunta da gashin ya sake jin maskara ya miƙe gazar-gazar fiye da da ta kallesa, “Nikam karka cinyeni dan ALLAH bb”.

Idanunsa ya janye a kanta yana sakin guntun murmushi da ya saka kumatunsa loɓawa, itama Shahudah sai tayi murmushin.

“Breakfast fa?” yay maganar yana sake maido kallonsa gareta.

Sosai ta sake zuba masa idanunta tana narke fuska, sai dai batace komaiba.

Hannayensa ya zare daga aljihu ya maida a ƙirjinsa ya harɗe, “Yanzu nan Hudah kina ganin wannan rayuwar itace ta dace da matar aure ta hausa fulani? Wata bakwai kawai da aurenmu amma matsaloli sunzo sun mana ɗaurin goro a cikin gida, wanda duk kece sanadinsu, shin ke wai bazaki taɓa canjawa bane?!…..” ‘Ya ƙare maganar a tsawace’.

Razana tayi matuƙa, dan haka ta zabura tana jan jikinta baya tare da waro manyan idanunta waje, “Wai ni bb ya kake so in maka ne? Kaifa nace a ɗakko kuku da wanda zaike mana gyara amma kace baka yarda ba, ta yaya kake tunanin zan iya aikin gyaran wannan ƙaton gidanne saboda ALLAH, kum….”

Haɗiye sauran maganar tata tayi tana ƙunƙuni saboda wani ɗan iskan kallo da yake mata, wanda ta tabbata yafara harzuƙa, idan ko ta bari ya kai ƙarshe zai iya ɓarota a kujerar ya haɗa kanta da mirror.

“Shahudah baki kai matsayin sakani yin abinda ban niyyaba, dan bazan taɓa kawo wani ƙaton banza gidana ba da sunan ma’aikaci, ki kama kanki kafin na raba shi da wuyanki a gidannan wlhy, stupid girl kawai”. Ya ƙare maganar da juyawa zai fita.

Cikin ƙunƙuni Shahudah ke faɗin, “Karka kawo ɗin, kata zama a gida tamkar tirken akuyiyin ƙauye kuwa, dan nikam ba ƴar wahala bace, kake wani cewa kamar ba matar hausa fulani ba, ALLAH ya rabani zama irinsu waɗannan kidahuman da basusan ko yanda zama su gyara jikinsu ba balle su san miye rayuwa, da ana canja yare ma da tuni na canja nawa anbar dangantani da wasu hausa fulani can mtsowww.

🤔tab, babbar magana, Shahudah anya kinada man kai kuwa? Matan hausawan ne bamusan abinda mukeba😨🤦🏻‍♀️? Rigiji gabji☹️.

Sarai Jawaad yaji abinda Shahudah ta faɗa, amma sai ya fice ko waiwayota baiyiba, bedroom ɗinsa ya koma ransa duk a jagule, ya ɗau babbar wayarsa da ke a kashe ya kunna, wata Number ya lalubo tare da danna mata kira, bugu biyu aka ɗauka.

Sama-sama sukai gaisuwa da wadda ya ambaci sunanta da Hibba, kafin yace, “Cikin yarannan wace a gida?”.

Bansan mi aka ce masa da ga canba, ya dai sake faɗin “turomin ita” kawai ya yanke wayar ya ajiye.

Tsaki yaja yana jingina da fuskar gadon tare da lumshe idanunsa ya afka duniyar tunani…………✍🏻

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭👏🏻7ƘWAI cikin ƘAYA!!

Bilyn Abdull ce🤙

SADAUKARWA:

Aunty Fareeda Gachi

Aunty Rahma A-Majeed

……….Zaman duniya da kayan cikinta buƙatar kowacce, amma waɗanda duniya ke buƙata da amfanuwa da kayan cikinta mutanene ƙalilan. A lokacin da wasu mutane ke bushasha da wani yanki na jin daɗin cikinta wasunsu kuka suke da kwankwaɗar ɗacin cikinta.

Yayinda idanun wasu ya bushe da ga kwaranyar ruwa mai amsa sunan hawaye, a lokacinne ijiyar wasu ke ambaliyar zubarwa da buƙatar abin gogewa koda ace ruwan hawayen bazai dakata daga malala ba.

Zuciyoyi duk iri ɗayane a suna, amma a aiyuka kowa da irin tasa. In dai zuciya zata kasance mabanbanta a ƙirazan mutane, to lallai dolene launin halayya da ɗabi’unsu ma ya banbanta. Sai dai wanda ya halicci duniyar da kayan cikinta, ya fika sanin miyasa ya banbanta ma’abota mu’amulantar ta da shawagi a cikinta harma da gudun zukatansu.

Kamar yanda duk ilimin ɗan adam bai isa ƙayyade numfashin da ke fita daga huhunsa zuwa maƙogwaro ya fita ta hanci ba, to lallai babu mai ilimin ƙa’idance ko banbance yawan jinsin ƙabilu da mutanen dake danƙare da duniyar nan sai wanda ya halicceta. A lokacin da fankama da tinƙahonka ke kwarzanta abincin tukunyar gidanka, da zaka leƙa ta gidan wani sai kaga ta fita abin kallo da kayan alfarma masu armashi.

Sai dai duk wannan ba shi bane tushen zancen, ba kuma shi bane abin dubi da hange ko burin riska, tsarin shine waiwaya can bayan bayanka ka hango waɗanda ko tukunyar ɗorawar basu da ita balle tunanin hura wutar da zata dafa musu.

Wani tun haihuwarsa ALLAH ya azurta tushensa ko zuri’arsa da rahamar fitowa cikin gingimemen hasken da ko baka mallaki komai ba a duniya sai shi to lallai ya gama maka komai, domin ya baka abinda ya fi komai tsadar tsada a cikin alfarmarsa. Sai dai abin mamaki da al’ajabi sai ka samu mafi yawan masu wannan damar sunyi wasarere da ita tare da mata riƙon sakainar kashi suna hange da gudun kamo wasu al’adu da ke da alaƙa da kishiyar nasu.

Zancen nawa a bayyane yake, sai dai fa fahimtarsa ba kowace kwanyace hasashenta zai kai canba, ba kuma toshewar basira ce zata kawo rashin fahimtar ba, sam ko kusa ba hakan bane, ɗunbin abin tarawa ne kawai kema ƙwaƙwalen jama’a yawa su gaza warware wani ƙullun igiyar a jikin gugar da takai kimanin dogon zamani ana cuɗanya da ita a rijiyar mai bakandamiyar alfarmar ruwa buƙatar kowa.

Shi wancan dama ya samu, amma rashin fahimtar hanyar da yake jefa ƙafa ta sakashi gaza fahimtar akwai waninsa da ke da buƙatar koda kwatankwacin tasa damarce shima ya shigo a dama dashi.

Gashi dai a cikin duniyar irinta wadda ke da damar a tafin hannu, ga kuma gangar jiki da fitar numfashi duk ALLAH ya haliccesa da ita shima, sai dai sam ba ƙofa ɗaya ya ke shiga da fita tsakaninsa da mai damar a cikin duniyar ba. Hakan yasa yake kallon tasa duniyar da ban a cikin duniya, ba dan baya ci ko sha ba kamar kai, hatta barci da kake domin hutu da dariyar farin ciki duk ALLAH shima ya azurtashi dasu, abin lurar shine kai duniyar rungumeta kayi tsam, itama ta tallafeka tare da sake cusaka jikinta kuna kwasar ɗumin juna saboda tsantsar buƙatarka da takeyi, Shiko waninka rakaɓe yake a jikinta tamkar hawainiyar da ke ɗauke da ciki ta ke jiran ranar haihuwa.

Bara dai mu ajiye duk wani dogon zance mu tsunduma cikin labarin ko mai karatu zaifi fahimtar gonar audigar da nake masa nuni da ita mai ɗauke da buɗaɗɗiyar kaɗa da gwaiduwarta ta fashe sumfut a filin gona.

Ni dai sunana *Bilkeesu* ɗiya ga malam Ado makaho, ƙwarai mahafina makahone da ko tafiya baya iya yi sai da ɗan jagora, Sai mahaifiyata Asiya.

A shekarun baya can mahaifina yana ɗan gani da ido ɗaya, amma da ga baya wahalhalun rayuwa suka ida rufe ɗayan idon yazam gaba ɗaya, mahaifiyata ma tana da nakasar ƙafa, dan kuwa gurguwace bata ma iya tafiya sai dai jan jiki.

A matsayin da iyayena suke kawai zai nuna muku ni ba kowan kowa bace ba, dan kuwa muɗin talakawane irin tiɓis ɗinan da a kullum sai an nemo za’aci. Abin da zai matuƙar birgeka a rayuwar iyayena shine sam mahaifina baya bara balle aje kan mahaifiyata, duk da baba baya gani bai yarda zama maroƙi ba, dan a ganinsa UBANGIJI ya masa dukkan gata da ya bashi rai da lafiya, idaniyar ganice kawai bashi da ita.

Sana’ar mahaifina itace sai da kayan ɗinki irinsu zare, allura, almakashi da dai sauran kayan nau’in ɗinki tsiraru dai-dai arziƙinsa, a gaba ɗaya jarin idan zaka dinƙuleshi waje ɗaya bazai wuce na naira dubu goma sha biyarba, wataƙil ma na zurma da yawa. Dalilin kamewarsa na janye kansa da ga ƙasƙancin bara ne ya ja hankalin mafi yawan telolin anguwarmu zuwa sayayyar kayan ɗinki a wajensa.

Sai mahaifiyata da ke saida kayan kuka, kuɓewa busashshe, kayan ƙamshi harda daddawa domin kare mana mutunci itama.

Gidan da muke gidan hayane mai ɗauke da ɗakuna kusan arba’in, dan irin dogon gidannan ne da akan jeranta ɗakuna reras da ga farkon baranda zuwa ƙarshe tamkar gidan karuwai, ba wani faɗine da gidan ba, amma kowa iyakar mu’amularsa a ƙofar ɗakinsa ne da bazata gaza taku goma ba, babban kicinne guda ɗaya a gidanmu dake a farkon shigowa gidan wanda ya gama cuɗewar baƙi saboda mafi yawancinmu girkin icce mukeyi, masu arziƙin cikinmu ne keda lasisin dahuwar abinci saman gawayi, can da ga ƙarshen gidan kuwa banɗakine guda biyu, na kashi da wanka, wanda suka ɗaine duk yawan mutanen gidan ke shiga, shiyyasa mafi yawanmu zaki samu kowa da fo ɗinsa na kashi a ɗaki ko ƙaramin botikin fenti, da safe idan bakai azamar tashi kai wanka ba to fa ka tabbata ƙila sai dare ko goshin magriba zaka samu damar yinsa, shiyyasa da yawanmu mukan jera kwana biyu babu wanka.

Tunda na taso a gidan na ganmu, hakama mafi yawan waɗanda suke gidan haka na tashi na gansu, dan haka zuwa yanzu mun wuce ƴan zaman haya sai dai ƴan uwa.

Karku ɗauka ciranine ya kawomu garin har muka samu mafaka a wannan gidan haya mai kama da hotel, sam ba haka bane, mahaifina da mahaifiyata duk haifaffun garinne, kuma dukkan danginsu suna ciki suna rayuwa, hasalima akwai masu arziƙi a ciki. Sai dai kowa yasan halin zuciya irin ta wannan zamanin, inhar baka da shi to kaida banza duk ɗaya kuke, kai tsaye ma ake mantawa da kai a cikin dangi. To ballema irin iyayena da suka kasance naka sassu, inhar za’a iya mantawa da mai ƙafafu da hannu da idanu saboda talauci ya masa katutu ta yaya kuke tunanin ba za’a manta da musakan iyayena da bayan rauni da ALLAH ya jarabcesu da shi na halittar jiki harda talauci?.

Ni kaɗai iyayena suka haifa a duniya, nima an jima ba’a sameninba, sai da ga baya ALLAH ya azurtasu da samuna matsayin ƴa ɗaya tilo a garesu, duk da talaucin iyayena da kasantuwarsu nakasassu ni ƴar gatace, dan gwargwadon iko iyayena tsaye suke a kan bani tarbiya, nakanje makarantar gwamnati kamar yanda sauran ƴaƴan gidanmu ke zuwa, hakama ina zuwa islamiyya. Sai dai aduk lokacin da aka buƙaci wani abu da ga makaranta da yafi ƙarfin ƙarfinmu hankalin iyayena kan tashi da ni kaina, wannan yasa da yawan lokuta karatun nawa ke kwan gaba kwan baya, dan kuwa ƴan ajinmu sunsha tsallakewa gaba su banni da maimaita aji saboda rashin kuɗin abu idan an buƙata tamkar ba makarantar gwamnati ba.

Badan bani da ƙoƙaru bane, a wannan ɓangaren ma ina sahun farko na gwarzayen yara masu ƙwaƙwalwar karatu da fahimtarsa, sai dai rashin kuɗi ke daƙileni a kulum.

A yanzu haka shekaruna sha takwas, amma har yanzu ss2 nake na makaranta, saboda matsalar komawa baya da naita fuskanta.

Bani kaɗaice budurwa a gidanmu ba, a ƙalla zamu iya kaiwa fin mu ashirin kuma duk yawancin sa’oin juna, sai dai kowa da gwaninsa (inji masayin taliya ƴar murji😆), dan kuwa kowaccenmu tanada abokiyar mu’amularta daga cikin ƴammatan gidan, dan haka muka kasance kusan nau’i uku zuwa huɗu a ɗaukar rayuwa.

A kwai sahun farko da suke ɗaukar kansu masu matuƙar aji da jin sunfi kowa hakama iyayensu sunfi na kowa arziƙi a gidan, a group ɗin sun tasarma su kusan bakwai, sai sahu na biyu da ajinsu bai kai waɗancan sahun farkon su sakasu a cikinsu ba, sai suma sukaja tasu zugar da zama abokan takarar waɗancan ta fuskar sumafa ba bayaba, sai kaso na uku da suka ɗau rayuwar saisa-saisa saboda ƙoƙari na tsawatarwar iyaye da gudun jefa kai a halaka, sai mu da ke karshe da muka kasance ba kowan kowa ba, hasalima mune akema kallon ƙarshen ƙasƙantattu marasa gata da galihu, ta kowacce fuska bamu da wani amfani sai tarbiyyar iyaye da ke jagorantar dukkan haƙurunmu da ɗaukar duniyar wajen maƙalewa kafin wa’adin barinta ya cika.

Ba wani yawane da muba gayyar ƙarshen, dan kuwa da ga ni sai Firdausi ne da take ƙawata jallin jal a gidan, dan kuwa matsayin iyayenmu kusan ɗayane, itama mahaifanta suna fama da ciwon talauci tamkar mu, sai dai su sunma ɗan ɗaramu, dan babanta nada sana’ar saida kayan miya itama anan ƙofar gidan, shinema ke taimakawa babana a tashi sana’ar idan anzo saya da idan za’a danƙa masa kuɗi, kuma ita iyayenta duk lafiyayyune, sai yazam har kwancen kayan sawa itace mai bani, dan saka sabbin kaya a gareni sai sallah, suma kala ɗaya ne da ƙyar ake ƙulla kuɗinsu saboda ƙoƙarin iyayena nason ganin sun sharemin hawaye a cikin tsarata.

Haka rayuwa ta zaɓar mana, badan wanda ya haliccemu baya sonmu ba, badan mun kasance masu saɓa masa ba, sai dan kawai haka ya tsara son ganin bayinsa a cikin duniyarsa dan yazama ilimi ga jahilai, izna ga masu wauta, rahama ga masu haƙuri, sake girmama mulkin ALLAH ga masu mulki.

Gidanmu wani irin gidane da bansan yanda zan fassara muku shi ku fahimta ba sam, dan duk wani mugun hali ya ƙunsa saboda jama’ar daya tara masu kalar hali iri-iri a zukata. A duk lokacin da kake barci to ka tabbata sai ka samu wanda ke maka munshari a gidan, hakama akwai masu kallo da ido ɗaya, akwai masu gani ta ƙeya kuma. Tsabar iya annamimancin gidanmu ko faɗa ba’a yawan yi, kasan kuwa duk zaman da ya haɗa jama’a irin na gidanmu kaga ba’a faɗa to lallai ka jinjina wannan zaman kuwa.

Ɗakinmu shine a can ƙarshe sai na su firdausi, hakan yasa baban firdausi samun damar yimana ƙaramar baca ta katako a ɗan lungun da ke gaban ɗakinmu wanda dalilin ginin banɗakuna ya fita. wannan bacar ce ta zama ɗakinmu ni da firdausi, dan ɗakunan gidan duk falle ɗai-ɗai ne, hakan yasa mafi yawan ƴammatan gidan daina kwana a ciki sai dai suje maƙwafta kwana.

Rana mafi muni da razani a rayuwata itace ranar da muka wayi gari mahaifiyata babu lafiya, tun a daren jiya amai da gudawa suka saukar mata, kafin safiya tayi ligif, lokacin da ɗaya daga cikin mazan gidanmu mai tuƙin a daidaita ke ƙoƙarin sakata a napep ɗin dan zuwa asibiti sai rai yayi halinsa.

Tashin hankali ba’a sa maka rana, dan kuwa yanda na tsinci kaina a cikima ai ɓata lokacine, har aka kai gawar mahaifiyata makwancinta ban san ina hankalina ya ke ba, sai bayan komai ya dai-daita har rana ta doshi faɗuwa sannan na dawo hayyacina.

Abinda ya daɗa harmutsa dukkan tunanina shine babu kowanne ɗan uwan mahaifana da ya zauna dan karɓar gaisuwa a gidan, tun bayan binneta da aka dawo sukai ɗan zaman awoyi uku zuwa huɗu sai kowa ya kama gabansa.

Nayi kukan da yafi na rasuwar innata a wannan lokacin kam, hakama babana da ruɗani ya maidashi kurman gaske bai uhm baya uh-uhm, dama gashi babu ijiyar gani.

Matan gidanmu sun ɗan tausaya mana a tsakanin nan, dan kuwa kullum sai an samu mai bamu abinci ni da baba, dama maman firdausi kullum saita bamu na rana da dare, dan mafi yawan jama’ar gidan basa abincin safe, kowa sai dai yaje ya siyo a waje, sai ƙalilan a ciki dake ɗanyi shima da risho a ɗaki gudun idanun masu ƙwalama.

Bayan kwanaki uku na makokin mahaifiyata akai addu’ar uku, sai aranar ne naga wasu tsiraru a cikin dangin iyayena, harma sukaimin gaisuwa. Ko da aka kammala addu’a sai kowa ya sake kama gabansa aka barni da ga ni sai babana kawai.

Rayuwa ta cigaba da shurawa duk muna fama da tabon rashin innata ni da mahaifina, dukda baba yana dannewa da aro jarumtar rashin inna a gabana har ya lallasheni, nasan shima yana a cikin wani hali. A haka kwanaki sukaita shuɗewa har inna ta cika watanni uku da rasuwa. Zuwa yanzu naɗan saki jikina, amma ba da kowa ba, dan dama can ni miskilace kamar yanda ake jifana da zagi a cikin gidanmu, (akance sai miskilancin tsiya tamkar ƴar wani da wata), idan naji hakan iyakata murmushi kawai, dan bani da abin faɗa.6

Kamar kullum na dawo da ga makaranta a gajiye yauma, dan dukda tazarar nisan da ke tsakanin makarantarmu da gidanmu kullum a ƙafa nake zuwa na dawo, idan kinga na hau napep sai dai idan baba ko innata sun sami rarar kuɗi a cikin sana’arsu, to shine za’a ɗan bani talatin na break, maimakon naci wani abun sai na maƙale kuɗin idan an tashi na hau napep, shima da ƙyar ake ɗakkoni, wataranma bana samun maimun alfarmar sai dai na taho a ƙafar dai dana saba. To yanzu ma tun bayan rasuwar innata sai komai ya sake taɓarbarewa, dan baba baya da isashshiyar lafiya, wataranma ko ƙofar gidan bai iya fita wajen sana’ar tasa sai baban firdausi ya takura masa.

Tunda na shawo kwanar anguwarmu gabana ya ƙara ƙarfin faɗuwa, dama tun daren jiya nakejin girata ta haggu na rawa, ci gaba nai da takowa tamkar kazar da ke shirin sakin ƙwai zunɓutu a ƙasa, matasan anguwarmu da dattijai zagaye da wani abu a ƙofar gidanmu, ga jini faca-faca a gefen titin wajen, dan gidan mu nakan titine sosai, kuma titin irin wanda ake yawan bi ne saboda shine babban titin anguwar.

Yanda wasu da ga mutanen suka zubomin idanune ya sakani sake komawa jan ƙafa, dan kallon yafi kama da na wadda ake tausaya mawa. Yayinda na iso daf da su sai naga an fara darewa ana bani hanya, mamaki ya sake kamani, dan kuwa basu tsaremin hanyar da zan shiga gidaba, suna da ga gefen jikin gidanne. Dubana nakai ga ƴar sirɗaɗen hanyar da suka ƙirkira sai karaf idanuna akan mahaifina kwance jikin jini. A hankali jina ya fara nisa, duhu ya mamaye ganina sai ga duniya na juyamin, kafin na gama fahimtar mike faruwa har na rasa komai da ga motsin jama’ar duniya, na koma wata duniya can daban mai nisan zango da ta mutane.

Yau ake yinta gobe sai labari ne ya sake riskar rayuwata a karo na biyu, dan kuwa na sake rasa mahaifina da lilin bigesa da mai motar akori kura yayi yayinda yake ƙoƙarin tsallaka titi. Kowa ya shaida baiga fitowar baba ba balle ƙoƙarin ƙetara titin da ya yi, ƙararsa kawai sukaji tare da mugun jan birki da mai akori-kuran yayi. Hakan yasa kowa yayo kan baba, ganin hankalin mutane ya raja’a kansa ne ya bama mai akori-kuran ƙofar samun hanyar guduwa, baiko sakkoba balle ya ga halin da ya jefa mahaifina ciki da ni tilon ƴarsa. Bakin babana ni yaketa ambata har aka ɗakkosa aka maido gaban gidan, faɗi yake a kira masa Bilkisu, a kira masa ɗiyarsa dan ALLAH, sai dai abin tausayi da yankewar rabon sake haɗuwa numfashinsa na tsayawa ina isowa ƙofar gidan.

A wannan karon nafi tsintar kaina a ruɗani fiyema da rasuwar innata, banbancin da aka samu zaman wasu a cikin dangin mahaifina tare dani har akai sadakar uku.

Randa akai sadakar uku kowa ya kuma kama gabansa, babu wanda yay min tayin na bisa, sai abubuwan ɗakin masu amfani da suka tsince duk suka tafi dasu, aka barni da ga ni sai tarkacen matattun tsunmokaran iyayena da ƙwanƙwatsatstsun kwanikan cin abincinmu……………✍🏻

4

Turƙashi, lallai bilkisu kin cancanci shinfiɗa dogon bayani a farkon labarinki kafin mu masu binki mu fahimceki, ko wace rayuwa kuma zata riski gobanki tunda gashi a yau ɗinki dukkan ginshiƙanki sun janye da ga rayuwarki, rayuwa kenan, lokacin da wani jin dadinta ke ruɗarsa yana baza shirme, wani rakuɓe yake a cikinta domin alfarmar mafaka kawai koda bazata buɗa masa wani filin yin rawar banjo ba😭, ALLAH ya fimu kusanci dake, ya fimu kuma sanin wace rayuwa ta dace dake, wane tanadi yay miki a gobenki harma da jibinki da zata iya zama amfanuwa da wasunki a dangi ko abokan zama, bamu saniba ko kece zaki zama ƙwai cikin ƙaya!! ɗin watan watarana.☹️🤦🏻‍♀️.

3

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭👏🏻2ƘWAI cikin ƘAYA!!

Bilyn Abdull ce🤙🏻

SADAUKARWA:

Aunty Fareeda Gachi

Aunty Rahma A-Majeed

🤣🤣😂🤣😂🤣😂Kunsan miya sakani dariyarnan kuwa? 😆wlhy kune, sam na fuskanci ba kowa yama fahimci sunan littafinnan ba, dan wasu ƙwai cikin kaya suke cewa🤣, 😂dan ƙari, bafa haka nake nufiba, ku kula akwai lanƙwasa a jikin Ƙ ɗin, sunan littafin nana ƙwai cikin ƙaya (Thorn), ƙaya dai ta gona mai tsini da haɗari idan an taka kota soki mutum a ƙafa, ina fatan kun gane yanzu kam😂.9

One luv my Sweet guys🥰🥰😉.

Gidan Jawaad

Jawaad Abdul-Azez Yuseef ɗane da ga. zuri’ar Alhaji Yuseef Tafida.

Alhaji Yusif talaka ne mai rufin asirin ALLAH, domin kuwa manomine kuma makiyayi, duk da a birni yake rayuwarsa da iyalansa to dukkan wani sabgoginsa na ƙauyensu, acan yake nomansa da kiwo, hakan yasa hankalinsa rabuwa biyu, harma zamansa a ƙauyensu ya so ya rinjayi zaman birnin.

Matan Alhaji Yusif uku ne cif, kuma kowacce a cikinsu ALLAH ya azurtata da haihuwa, matarsa ta farko hajiya Atika yaranta shida huɗu duk maza biyu mata, sai ta biyu badiyya yaranta huɗu itama, mata uku namiji ɗaya, sai amarya Rahina ke da uku maza biyu mace ɗaya.

Zamu iya cewa a gidan Alhaji Yusif tafida akwai tsaftataccen kishi irin na matan da da suka san kansu, dan kuwa baka taɓa jinsu suna wata hayaniya a tsakaninsu, sannan kowa na da ikon tsawatarwa ɗan kowa idan yaga yayi ba dai-dai ba, so rayuwar gidan dai akwai abubuwan birgewa.

Tabbas Alhaji Yusif nason ƙauyensa sosai, sannan shi mutumne mai bautawa zuminci iya iyawa, sam bashi da matsala, amma yanada zuciya idan aka kaisa maƙura.

Ganin rayuwarsa ta ƙauye tana neman rinjayar zaman maraya sai ya yanke shawarar ɗauke ɗaya a cikin iyalansa ya maida ta can ƙauyen. Amma yana tara matan nasa ya ambata musu wannan batu duk sai sukai tsale suka dire akan sam bazama ta saɓu ba, kowacce tace babu yanda za’ai ta koma rayuwar ƙauye bayan ALLAH ya tsamota da ga can.

Abin ya matuƙar ɗaure kan Alhaji Yusif, musamman idan yay dubi da cewar duka fa daga ƙauyen ya aurosu ya kawo birnin, dan shi bai taɓa sha’awar yin aure a bariki ba, duka matansa daga gida ya aurosu, amma gashi yanzu ƙiri da muzu sunce bazasu koma zaman tushensu ba.

Da farko sai ya kwantar da murya ya shiga lallashinsu da nuna musu muhimmancin komawar wata a cikinsu can ɗin, dan babu daɗi da girmansa ace bashi da mata a inda rayuwarsa tafi ƙarfi, kullum sai dai ake kawo masa abinci da ga gidan matan ƙannensa ko ƙannensa mata.

Ai sai tamkarma ya tunzurasu ne, dan kowacce sai ta sake sama akan bijirewar farko, ya kaɗa su danbu da taliya suka nuna sam bazasu yi mubayi’a ba. Ganin bazasu lanƙwasu cikin sauƙiba ya rufe ido ruf ya banbamesu da bala’i tamkar zai cinye naman jikinsu ɗanye, duk da sun razana da fusatarsa babu wadda taji zata iya sadaukarwa ta koma ƙauye da zama. Shima takalminsa ya buga yay gaba ba tare da ya sake bi ta kansu ba.

Tsawon lokaci bai sake tado musu zancenba, duk sun saki jiki akan yabar ma zancen kenan, sai gashi rana tsaka yazo musu da maganar ƙara aurensa, kuma zai auri ɗiyar maƙwafcinsu ne Alhaji Sunusi na Abba, yarinyar da ke yawan shigowa gidan matsayin ƙawar ƴaƴansu.

Wannan lamari ya harmutsa dukkan lissafinsu da jinsu harma da ganinsu, shiko yay tsayuwar sojan badakkare a kansu kan cewar duk wadda tai masa hauka zata ƙarasa zaman turu ne a gidansu ba da igiyar aurenta ko guda ɗaya ba a kansa. Wannan shine dalilin nutsuwarsu dan dole, kowacce ta shanye bala’in da kecin ƙahon zuciyarta zuwa maƙwallato sukabi yarima akasha kiɗa dasu.

Bayan an ɗaura aure kai tsaye ɗaukar amarya maryam akai zuwa ƙauyensu Alhaji Yusif. Duk da maryam a birni ta tashi taga iyayenta, annan aka haifeta har kawo girmanta, kusanma dukkan danginsu anan suke, hakan baisa ta bijire akan bazata koma rayuwar aure a ƙauyeba, sai tayi biyayya ga mahaifanta da kuma mijinta, ta zauna lafiya cikin ƙauyen tamkarma ta saba da rayuwa a cikinsa da can, ta saki jikinta da kowa danginsa da jama’ar gari, sannan tanama mijinta biyayya sau da ƙafa, ta tsaya tsayin daka wajen taimaka masa akan dukiyarsa da yake kiwo a kanta.

Shekarar maryam ɗaya cif ta haife ɗanta namiji san kowa ƙin wanda ya rasa, bakin Alhaji Yusif har kunne dan murna, sai kace yanzune akai masa haihuwar fari, ba komai ya girmama murnar tasa ba sai biyayyar maryam a garesa da ƙyautata masan da takeyi, (kunsan zuciya nason mai ƙyautata mata).

Sosai maryam ke ganin gata fiye da ta farko a kan wannan haihuwa wajen dangin Alhaji Yusif, dan kuwa hidima suketa mata da bajinta irinta mutanen karkara, tunda aka kawo maryam garin matan Alhaji Yusif suka ɗauke ƙafa da ga zuwa garin, dama ƴaƴansu ba zuwa sukeba sosai, amma wannan haihuwa yace musu tilasne su halarci taron suna daga su har yaransu. Badan sunso ba suka shirya ana gobe suna suka nufi ƙauye, kai tsaye kowacce gidansu ta nufa maimakon gidan mai jego, hakama yaran babu wanda ya nemi inda take, dan duk haushinta sukeji, musamman ma ƙawayenta su Atika.

Itama dukda taji sunzo sai bata kulaba, dan danginta da suka cika gidan sun share mata dukkan kukanta, ga kulawa ta dangin miji da jama’ar gari.

Washe gari yaro yaci suna Abdul-Aziz. Yanda hidimar suna ta gudana ma ɓata lokacine, amma Alhmdllh komai ya tafi cikin tsari, matan Alhaji Yusif basu shigo gidan sunanba sai da dare, koda sukazo sama-sama suka gaisa da dangin maryam suka ɗauki jariri suka ƙara gaba bayan sun ajiye kayan da suka kawo.

ALLAH sarki maryam ita kunyarsu ma taji sosai, domin dai kallon iyayenta take musu, gashi yanzu ta aure musu miji harda rabon ɗa tsakani, ta baza ido taga ƙawayenta su Atika sun shigo amma sai taji tsitt, bayan kuma ance dukansu sukazo, dama bata saka ran ganin su Yaya Naseer da sauransu ba, tunda su mazane.

Bayan suna kowa ya kama gabansa, Maryam ta cigaba da rainon ɗanta Abdul-Aziz da kulawa da mijinta.

Rayuwa ta shuɗa, dan har maryam ta yaye Abdul-aziz, gashi yana tafiyarsa ko ina ga surutu ko akku ta shafa masa lafiya, yaron akwai wayo na haƙiƙa, gashi kullum yana cikin yara idonsa na sake buɗewa.

A hankali duk wasu wahalhalu da yaran ƙauyen keyi Maryam bata hana Abdul-Aziz shigaba, kiwon dabbobin babansa ma shine ya koma bin yara daji yi, ko yabi zugar yara yo ciyawa, shine zuwa gona shuka ko kwaso amfani da kaka, yana girma wahalhalu na sake hawa kansa, gashi yanata zuwa makaranta anan cikin ƙauyen, dan da farko Alhaji Yusif yayi niyyar maida Abdul-Aziz birni ya samu ilimi tamkar ƴan uwansa amma sai Maryam ta hana, cikin hikima ta nuna masa ta fison Abdul ya tashi cikin wahalhalu irinna ƙauyen, hakan zai taimakawa rayuwarsa ta gobe harma wani ya amfani jibinsa. Badan ya soba ya barsa, itako ta cigaba da sakashi duk abinda ya dace, lokacin da Abdull yakai shekara goma sha biyar tsaf zai ja maka kunyar gona sama da ashirin a nome, faskare wannan yinsa yake, ragamar kiwon dabbobin gidan kam ya koma hannunsa baki ɗaya, duk safiya da an fito sallar asubahi yana makarantar allo, zuwa takwas suke tashi sai yazo yay shirin makarantar boko ya tafi, yana tasowa abinci kawai yakeci ya ɗebo ruwa ya zuzzuba a gidan ya ɓalle dabbobin gidan ya tafi jeji kiwo, bazai dawoba sai gab da magriba, da yayi wanka zaije sallah shi da babansa idan yana gari, idan yana birni wajen sauran matansa zaije shi kaɗai, baya dawowa sai tara da rabi, dan ana gama sallar isha’i yake wucewa makarantar allo again.

Sai rayuwar Abdul-Aziz tazam sam babu hutu, har wasu na ganin maryam ta cika tsauri aka sa, gashi shi kaɗai ALLAH ya azurtata da samu, tun bayan haihuwarsa bata sake koda ɓari ba, baza’a ce bata damuba kam, amma ta danne ta cigaba da harkokinta hankali kwance, tasan dai haihuwa ta ALLAH ce, kuma shine ke badawa ga wanda yaso a lokacin da yaso, guda ɗayanma ta godama ALLAH, fatanta ALLAH ya rayasa ya zama amfananne ga al’ummar musulmai da addinin musulinci.

Rayuwa haka ta cigaba da shillawa, Abdul-Aziz shine autan gidansu, dan suma matansa na birni babu wadda ta sake haihuwa, abinda zai birgeka shine zuwa wannan lokacin kuma duk sun saki jiki da maryam, komai ya wuce, yaransu kan ɗanje hutu wani lokacin wajenta, itama Abdul kanje wajensu dukda dai baya jimawa sabida ya saba da ayyukansa anan ƙauye, acewarsa canko sai dai aita yawon banza da barci da kallo bayan anci an ƙoshi, shiko sam bazai iya rayuwar lalaci ba.

Sauran ƴan uwansa sukan masa kallon mahaukacin da baisan ciwon kansa ba, shiko ko a kwalar rigarsa, har zuciyarsa yake faɗar abinda ke ransa ne.

Yayunsa mata kusan duk sunyi aure, mazanne dai babu wanda ya yunƙuro har yanzu, dukda kuwa a cikinsu akwai waɗanda suka isa auren.

Lokacin da Abdul ya kammala secondary ne wasu a cikin yayunsa sukai aure, shiko Alhaji Yusif yay masa zancen dawowa birni dole saboda cigaba da karatu, sam bayason dawowar, idan ta shine abarsa yayta harkar nomansa da kiwo yafi birgesa, secondary ɗinma da yaya ya gamata, gashi yanzu ne mahaifinsu yafi bukatarsa saboda kulawa da harkokinsa na kiwo da noma, dan ƙarfinsa ya fara karewa girma ya fara kamashi, gashi sauran yayyen Abdul babu mai son zuwa ƙauyenma bare su taimaka masa, su kawai boko suka saka gaba da burin samun daula ta birgewa suci duniyarsu da allura, kasancewar mahaifinsu manomi makiyayi ma takaici yake basu, a ganinsu ajinsu ya wuce ubansu ya ƙare a harkar noma da kiwo, bayan kuma da itace duk suka samu tallafin karatun nasu.

Sosai Abdull ke lallaɓa babansa akan baison zuwa makaranta, amma sam yaƙi saurarensa, yace dolene shima ya fita haƙƙinsa akan karatu tamkar sauran ƴan uwansa.

Babu yanda Abdul ya iya dole yay biyayya, amma koda yatashi karatun sai ya karanci fanin kiwo da noma, dan aganinsa yafi fahimtarnan ɗin.

Ƴan uwansa dariya abun yayta basu, dan aganinsa abunfa na haukar Abdull ya fara wuce makaɗi da rawa, yaro kamar tsatson ƴan rawar banjo. Sam baya kula zancensu, abinda yasa a gaba yakeyi, ga ƙwarin gwiwa yana sake samu da ga mahaifiyarsa da babansa.

Kammala karatun Abdull babu jimawa ALLAH ya ɗauke Alhaji Yusif a duniya, wannan mutuwa ta girgiza dukkan ahalinsa musamman maryam da Abdull, abin ya taɓasu masuƙa, ansha ruguntsumi da tashin hankali har komai ya lafa zukata suka dawo hankalinsu bayan haƙuri da dangana da ya riskesu bisa rahamar UBANGIJI.

Ranar da akai addu’ar arba’in a ranar aka ɗakko zancen raba gado, babu wanda yay jayayya wajen amincewa akai rabo, ita dai maryam bata da abin faɗa, dan ɗaya tilo ne gareta, ita babban tashin hankakinta ma ta yadda zata bar ƙauyen, dan tasan tilas zamanta ya ƙare kenan, gashi ta saba da kowa da komai na yankin.

Ilai kuwa hakance ta faru, dan a yanda rabon gadon yazoma sai da gidan sukayi, dukda Abdul yace abasa zai saya da ɗan kuɗinsa kakarsa ta wajen uwa mahaifiyar maryam sukace zasu cika masa kuɗin, amma tsabar mugunta aka hanasu saya, maryam da ta lura zamansune ba’a sonyi saita lallaɓa Abdull akan yayi hakuri yabar zancen, duk inda ALLAH ya sake ƙaddara zamansu suyi haƙuri su karɓa kawai.

Da wannan nasihar taci ƙarfinsa yayi biyayya, angama raba gado tsaf, ɗan filin gonar da Abdull ya samu ma bawata mai yawa bace, dan haka yay zuciya ya saida tasa, cikin yayyun nasa da aka haɗasu ya saye suna masa dariya akan ya gama wahala amma ya tashi babu tsuntsu babu tarko.

Abdul ma yanada haƙuri, amma lallai akwai zuciyar masifa idan aka kai haƙurinsa tunga, wannan kalmomi da aka jefesa da sune suka bashi ƙwarin gwiwar mikewa da ƙafafunsa ya shiga fafutukar neman na kansa, yayinda maryam ta koma gidansu ta cigaba da rayuwarta, dukda kuwa ana takura mata da batun tayi aure tunda bata wuce yinsa ba.

Abdul ya zage damtse wajen neman halalinsa, ya manta ma da wasu takardun kwalin shaidar gama karatu, kai gaba ɗaya yama manta kansa matsayin ɗan boko, dukda kuwa ga yayyensa sunaci da biro cikin sauƙi, 100% kuma shima ya goyi bayan mahaifiyarsa akan tayi aure, dan shine mutuncinta.

Maryam bata musaba tai aure anan ma cikin anguwar kusa da gidansu, ta auri wani bawan ALLAH da matarsa ta rasu ta bar masa ƴaƴa har huɗu duk mata.

Mama maryam mace ce da ta san kanta, ta kuma yarda ɗa na kowane, dan haka ta rungumi yaran a jikinta tamkar nata, ta kuma tsaya tsayin daka akan tarbiyyarsu musamman babbar da ta zama budurwa. Wannan dalilinne ya jefa ƙaunarta mai tsanani a zukatan yaran da mahaifinsu, harma da danginsa da na mahaifiyarsu. Shima sai ya sake jan Abdull a jikinsa tamkar shine ya haifesa, ya kuma sake nuna masa hanyoyin neman na kai masu sauƙi, dan shi ɗan kasuwane.+

STORY CONTINUES BELOW

A cikin amincewar UBANGIJI sai ƙauna mai ƙarfi ta shiga tsakanin Bilkisu ɗiyar mijin mama maryam da Abdul-Azez, duk da babu burin aure kusa a ransa sai gashi ta canja masa dukkan tunani da tsarinsa, ya rikice ya fara kafa manufofinsa a gareta, koda mahaifinta ya fahimta sai yayta murna, dan shikam dama halayyar Abdul na matuƙar birgesa, hakama mama maryam taji daɗi sosai, ga yaran akwai tarbiyya dama, sannan gasu ainahin ƙyawawa abin son kowa.

Abdul sam bai ɗakko maganar auren bilkisu ba sai da yasamu ɗan abin dogara wajen riƙeta, dan shima dai kudin farko da ALLAH ya albarkacesa dasu a kasuwa saiya koma ƙauyensu ya sai gona ya tsunduma harkar noma tamkar mahaifinsa, ga kuma ɗan kasuwanci yanayi na sai da dabbobi da abincinsu anan cikin binni, ganin yanada abinda zai riƙeta gwargwadon iko sai kawai aka saka biki, haya ya kama na ɗakuna biyu a wani gida, su biyune kawai suke haya a gidan, dan haka komai sai ya zam musu da sauƙi, dan matan nasu duk masu hankaline, babu mai rawar kai aciki.

A Ɓangaren ƴan uwansa kuwa kowanne yana fantamawa rayuwa, dan mafi yawansu duk da biro sukeci, matan kam ba laifi suna auren masu hali, arziƙin ƴan uwansa bai taɓa kwaɗarsa ba balle ya zame masa abin rikewa wajen yimusu hassada, harkar gabansa yake da iya gwargwadon abinda ALLAH ya hore masa, bai dogara su bashiba, bai kuma zauna damuwa da sunfishi ba. Suko kullum cikin kallonsa mafi ƙasƙanci a cikinsu sukeyi, suna ganin ya tashi a ƙauye, sun fishi karatun boko, sun fishi komai na rayuwa, ko tarkacen kwancen kayansu ko wani abu suka tashi saisu bashi, shiko ya amsa cikin murna da girmamawa, bai taɓaji a ransa dan ƙaskanci sukai masa ba, yasa a ransa da yarda sun fisa ɗin da gaske.

ALLAH mai alkairi, harkar nomansa nata bunƙasa, hakama sana’ar saida dabbobi da abincinsu, har lokacin bilkisu bata taɓa koda ɓatan wata ba, sai da suka shekara huɗu da aure ALLAH ya bata ciki, zo kaga murna wajen Mama Maryam da shi kansa uban gayyar da ƴan uwan bilkisu, ciki na kai wata baƙwai haihuwa tazo mata, aiko tasha wahala kafin ta haifi bakwaini biyu tagwaye, ɗaya ma baizo da raiba.

Sun karɓa hannu biyu kuma sunyi murna da jin tausayin kansu na rasa ɗayan, sai dai kuma hukuncin ALLAH shima ɗayan bai kai labariba ya koma.

Tun da ga nan Bilkisu bata ma sake samun cikiba tsawon lokaci.

*Komai na da sanadi*.

Wannan magana haka take, dan kuwa sanadin dam da akajema ƙauyen su Abdul ne ya zamar masa wani gagarumin alkairi, gonarsa ta kasance ɗaya da ga cikin gonakin da dam ɗin zai cinye, hakan yasa aka biyasu makudan kuɗaɗe gwamnati ta saya, shi kuma Abdul yana da ilimi, sai yazama shine ya tsayama jama’ar ƙauyen da duk abinda ya shafa har sai da aka biyasa haƙƙinsa, ya kuma basu shawarwarin su sake sayen wasu gonakin dan ga damar yin noman rani ya sake samuwa, ɗari bisa ɗari suka amince da shawararsa da ga manyansu har matasansu.

Turawan da sukazo wannan aiki sai al’amuran Abdul-aziz suka matukar birgesu, hakan yasa suka jashi jikinsu ya zama abokin hirarsu duk da kuwa ba ko yausheba, dan shima yanada harkokinsa da yakeyi.

Turawan ba cikin ƙauyen suke kwana ba, zuwa yamma suke tashi su koma cikin birni inda suke da masauki, hakan yasa suka sake jan ra’ayin Abdull har yasan mazauninsu, suma kuma sukasan nasa.

Kafin kace mi shaƙuwa ta shiga tsakaninsu sosai, halayensa na neman nakai da dattako na sake birgesu, gashi dai ba wani babba ba can amma akwai halayyar manya, kafin su kammala aikin ƙaton dam ɗinnan da ko Abdul baisan iyakarsa ba shakuwarsu ta wuce misali, dan har bilkisu ya kaimasu suka gaisa, sannan wani lokacin yakan sakata tayi abinci ya kai misu, acewarsu suna koyon cin abincin arewacin Najeriya.

Bayan kammala aikin nasune sukai haramar komawa, dukansu sun fuskanci halin kewa na tsantsar sabo, sai kowanne ya tsinci kansa a damuwa, lokacin da zasu tafi suka damƙa gidansu kacokan ga Abdull ƙyautar ALLAH, dama saya sukai dansu zauna harsu gama aikinsu, ganin sun kammala kuma sai suka bashi da zasu tafi, rasama mizai faɗa musu yayi dan susan yaji daɗi, dan gidane mai azabar ƙyau da tsari, kowa yasan dai yanda turawa suka amince da gyaran muhalli, to shima wannan ya ɗauki tsari na musamman, gashi a anguwar manyan mutane.

Duk sai da ya ɗauki ƴan uwansa ya kaisu suka sanya albarka da matan babansa, hakama dangin mahaifinsa dake ƙauye, mota biyu suka ciko sukazo suka tayasa murna. Sannan ya maida iyalansa can, harda mama maryam yaso amma mijinta da ita kanta suka ƙi, aganinsu yaya zasuje suyima ƴaƴansu zaune dukda dai gidan babbane. Dole Abdul ya haƙura amma ya ɗauke ƙannen Bilkisu biyu da suka rage ya maida gabansu, dan ɗaya a cikinsu itama tayi aure.

Shekara ɗaya kacal da faruwar hakan saiga turawannan sun dawo Najeriya, ashe zuwa sukai tafiya da Abdull, dan su dai yamusu har ƙasan zuciya, bayan ɗan kace nace da aka samu akan tafiyar tasa dai da ga karshe ALLAH ya amince su mama maryam suka barshi ya bi turawannan, sai dai yabar matarsa a nan gida Nageriya.

Wannan tafiya itace ta sake canja komai da ga rayuwar Abdul-Aziz Yusif Tafida, cikin ƙankanin lokaci ya bunƙasa, dan kuwa acan ƙasar turawannan ashe sun jashine akan harkar noma da kiwo irin nasu, suka sake wayar masa da kai, shima ya sake wayar musu da kai akan nasa sanin da ALLAH yay masa, dama su kunsan komansu da tsari, tamkar kamfani nasu yake, sai suka dirasa matsayin babba mai kula da komai, a duk bayan wata uku yake zuwa gida Nageriya yay wata guda ya koma can ƙasar, sannan anan Najeriya ma ya kafa jijiyoyi musamman a ƙauyensu, dan kuwa ya tallafa ma matasan ƙauyen da magidanta akan noman da kiwo, harma ya kwashi wasu acikin matasan suma sunacan turai ɗin tare dashi.

Rayuwa ta matukar sauyawa, duniya ta bama Abdul-Aziz babban filin fantamawa a cikinta, abin birgewa kuma yana amfani da damarsa sosai wajen gina kowansa, tamkar ƴan uwansa da abaya suke ganin sun fisa yanzu ya zamar musu runfa, dan kuwa dukkan dukiyarsa da ke Najeriya su ya ɗaura akanta, dukkan sirrinsa sun sanshi, duk abinda kaga bai sanar musuba to lallai sai dai sirrin da ya shafi matarsa ko mahaifiyarsa, wannan kam da ga shi sai su sai ALLAH, har zuwa yanzu kuma basu haihuba, kuma bai taɓa yunƙurin sake aure ba, hakama babu wanda yace masa ya sake auren ko za’a dace. Yana son matarsa sosai, dan haka bai taɓa nuna mata ya damu da rashin samun ƴayansu ba dukda yana kwaɗayin son ganin tsatsonsa a duniya.

Ba a cikin ahalinsa kawai yake taimako ba, hatta da mutanen gari ta kowanne fanni amfanuwa suke da tagomashin arziƙinsa, ya zama bango abin jinginar kowa, sannan runfa mai lulluɓe zafin rana ga kowa, dukda hakan kuma bai isa zama mai ƙyautata zukatan kowa ba, dan ko UBANGIJI daya hakicci ɗan adam baya iya masa…………✍🏻

1

Please mu haɗu page ɗin gobe idan ALLAH ya kaimu dan jin yanda zata kaya.😉

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭👏🏻ƘWAI cikin ƘAYA!!

                       Bilyn Abdull ce🤙🏻

SADAUKARWA:

Aunty Fareeda Gachi

Aunty Rahma A-Majeed

Shafi na biyar

………..A yanda Abdul-Aziz ke bautama al’umma da hidimarsa, sai ka ɗauka bai ma san ciwon dukiyarsa ba, kokuma a banza ya sameta ba da guminsa ya taraba. Abubuwa yake na bajinta ko tunanin kuɗin zasu iya ƙarewa bayayi, kafin kace kwabo sunansa ya zauna ɗam abakin mutane, ko yaro ƙarami ka ambatama sunan Alhaji Abdul-aziz tafida da gudu zai amsa maka harma yay maka sharhi gwargwadon fahimtarsa.

     

        Rayuwa ta ci gaba da shurawa, yayinda wasu da ga cikin jama’a suka fara kafa dandalin kiranye ga Alhaji Abdul-aziz zuwa ga siyasa. Duk da yana jinsu, kuma yana ganinsu, sai ya maida kansa makaho kuma kurma akan batun, dan shi sam siyasa bata cikin tsarin tafiyarsa ko burinsa.

       A na cikin wannan yanayinne ya fara ginin wasu katafaren gidajen gona guda biyu, amma a jihohi mabanbanta. Sai wani katafaren family house da zai haɗa dikkan ahalinsa waje guda, kuma kowa da ɓangarensa babu ruwanka da shiga sabgar gidan ɗan uwanka, Wannan aikinne ya kauda hankalinsa ga nacin jama’a na son ganinsa cikin siyasa.

        Lamarin kuɗi sai mai su, kafin kace wani abu gidajen gona sun kammala, hakama gidansu, matasa da yawa harma da magidanta sun samu aikinyi a ciki, abubuwan alkairi harsun fara fitowa ta gidan, sannan suma sun koma sabon gidansu shi da duk sauran ƴan uwansa da iyalansu, mama maryam ce kawai taƙi tunda dai aure takeyi, sai Alhaji Abdul-aziz ya sayi gida kusa da su suma suka koma.

     

      Duk yanda Alhaji Abdul-aziz ya so zamewa siyasa lamarin ya faskara, dan kuwa sosai ake masa bibiko da naci harta hannun aminan mahaifinsu da mama maryam kanta da mijinta.

       Rana ɗaya suka ware wajen ritsashi, dan gangami akai masa na musamman tare da manyan mutanen da zuciyarsa kejin kunyar bijiremawa. Ba da son ransa ba dole dole ya amsa da addu’ar ALLAH yasa haka shine mafi alkairi.

   Kowa ya amsa da murna da farinciki, tare da masa addu’oin na musamman wajen bashi nasarar jagorancin al’umma cikin sauƙi.

       Ƙyawawan halayensa ne yasa shi kasancewa mai kishin jama’ar sa, har suma sukeji a ransu zasu iya sakar masa ragamar rayuwarsu ya mulka, babu ɓata lokaci rana tsaka ya afka siyasa bisa jagorancin abokai da matsawar mutanen gari da suke ganin ya cancanci zama jagoran nasu.

     Koda ya tuntuɓi ƴan uwansa sai suka bashi goyon baya, dan duk ya riga ya gama siye zukatansu, zuwa yanzu ƙauna ta haƙiƙa suke masa da bashi kulawa wajen jansa jikinsu, (kowa yasan ziciya da son mai ƙyautata mata), dama kuma suna cikin waɗanda aka kama ƙafa dasu harya amince da batun.

      Mama maryam ma sai ta bashi goyon baya sosai, tare da binsa da addu’ar alkairi, sai dai sam Bilkisu abin bai kwanta a ranta ba, amma babu yanda ta iya tabi ayarin ƴan binsa da addu’a tunda taga kowa ya bashi goyen baya, bai kamata ita ta zama ƴar ta wareba a cikinsu.+

            Shekarar da Abdul’aziz ya shiga siyasa a shekarar Bilkisu ta sake samun ciki a bazata, ai farin cikin da wannan ahali suka tsinci kansu bashi da kwatankwaci sam.

      Bilkisu tanata rainon cikinta hankali kwance, ga kulawa tana samu ga kowa, watanta tara cif da wasu kwanaki ta haife ɗanta namiji sargaɗeɗe, inda ranar suna yaci sunansa *Jawaad*.

            Jawaad ya tashi cikin kulawar dangi da mahaifa, gashi yaro abin san kowa a zuciya, dan danan ya fara wayo, gashi da jikin girma masha ALLAH, shekararsa ɗaya da rabi Bilkisu ta yayesa, dan yana tafiyarsa ko ina, ga haƙora reras a baki, sai dai kumafa baya magana, dan har Jawaad ya kai shekara biyu da wasu watanni baya magana, bayama yunkurin yinta, hakan yasa kowa yake ɗauka ko bebe ne, dan sun tabbatar yanaji da kunnensa, tunda idan akai masa magana yana fahimta, bakinsa ne dai baya furtawa. Tunma Bilkisu na damuwa harta daina ta maida komai hannun ALLAH, dan koda Alhaji Abdul-aziz yace zai kaisa asibiti itace ta hana, acewarta a jira aga zuwa wani lokaci dai.

     Domin farin cikinta ne kawai ya so barin zancen sai dai kuma da ga baya saiya kasa hakan, dan abin na damunsa, ga dai Jawaad da wayau harma na tsiya, amma yaro bai da maraba da dutse a fannin faɗin albarkacin baki. Kuma zama yay ya lallaɓa bilkisu akan kai Jawaad ɗin asibiti, da kyar ta yarda dai aka kaishi, sai gashi kuwa an gano yana da matsala ne a ƙasan harshensa da maƙoshinsa, nan akai masa aiki yay tsawon sati uku yana jiyya kafin ya warke su dawo gida. Ba’aja wani dogon lokaci ba Jawaad ya fara magana, zo kuga murna ga wannan ahali, kowa na sake miƙa godiyarsa ga ubangijin al’arshi buwayi gagara misali.

         Babu daɗewa da samun lafiyar Jawaad, a cikin matan Alhaji Yusif ɗaya ta rasu, Wannan rasuwa ya mugun girgiza wannan ahali sosai, musamman ƴaƴanta.

         Bayan wucewar komai na rasuwar jama’a suka takura ma Alhaji Abdull akan ya fito takarar shugabancin jihar, sam ki yayi, danshifa dama bai shiga siyasa dan yazama shugaba ba, ya shigane kawai dan ya zama jagora da zai tsaya kan masu mulkin su tallafi talakawa kawai, amma badan yay mulkiba.

     Nanma dai caa aka sake masa, babu yanda ya iya sai ya amince kawai yabi ayarin ƴan takara.

     Abin zai baku mamaki idan nace muku komai yimasa akeyi, duk da talakawa sunsan yanada kuɗin da zai iyama kansa komai haka suka tattalafa da kansu sukai komai, acewarsu ai sune sukace yayi, dan haka sune zasuyi masa komai.

      Wannan lamari ya sake girgiza duniyarsa, dan yarasa miyasa jama’a suke masa irin wannan makahon soyayyar?1

STORY CONTINUES BELOW

Ni ko nace Alhaji Abdul ai masu iya magana kance (Nagari na kowa, mugu sai maishi).1

       Bayan kammala duk wani hatsaniya da ruguntsumi na kamfen akai zaɓe, tunma ba’ai nisa ba kowa ya fahimci Alhaji Abdul-aziza Yuseef ya bige abokin takararsa,  tunkan sakamako ya fito mutane har sun fara shagulgula, ana faɗa gari ya sake harmutsewa.

     Shi Alhaji Abdul-aziz ma ana faɗan yaci kuka ya kamayi, dan haka kawai yaji zuciyarsa ta karye ya shiga share ƙwalla.

      Lokacin Jawaad na jikinsa yana wasansa, sai ya tsirama mahaifin nasa ido yana kallo duk da baisan mike faruwa ba, murmushi Alhaji Abdull yayi ganin kallon kurilla da Jawaad ke masa, ya ja kumatunsa kaɗan yana faɗin “Haba ɗan sanda kallon fa na minene? Yau nauyi ya haye Abbanka mai girman gaske, kai min addu’a ALLAH ya bani ikon saukewa”.

       Duk da Jawaad baisan ma’anar maganarba sai ya ƙyalkyale da dariya shima yana jan kumatun abbansa kamar yanda yay masa.

     Murmushi Bilkisu da ke gefensu tayi kawai, dan batasan dalilin da yasa mijinta keson kiran ɗan nasu ɗaya tilo police ba, tun baima kai hakaba yake kiransa da suna JAY -P!, tunma bata fahimci ma’anar sunanba har dai ta tambayesa ya gaya mata.

    Ko a lokacin batai masa jayayya ba sai fatan alkairi yazama ra’ayin Jawaad ɗin kenan idan ya girma shima.

    Tun a lokacin ya fara amsa wayoyin taya murna har ma kansa ya nema fara ciwo.

         Bayan abubuwan da suka biyo baya dai a ƙarshe aka rantsar dasu, Alhaji Abdul ya koma gidan gwamnati shi da iyalansa, sai dai su mama maryam basu bisuba, sunce zasu rayu anan gidan da ya saya musu.

      Harkar mulki ta fara gudana, inda Alhaji Abdul yazoma duniyar ƴan siyasa da sabon salo mai ban mamaki, gaba ɗayan albashinsa ya sakashi a taskar gwamnati, an ware aiki na musamman za’ayi ma talakawa aiki da kuɗin, sannan ya dage tsayin daka wajen gyara jiharsa ta kowanne fanni, dandanan sunansa yay amsa kuwwa a ƙasar, komansa ya zama abin koyi da alfahari ga al’ummar da yake jagoranta, ya zama zakaran gwajin dafi sannan tauraro mai haskawa da zamaninsa.

     Gashi sam bashi da girman kai, kowa nasane, babu ruwansa da wani banbancin jam’iyya ko yare, tsakaninsa da ALLAH yake aikinsa cikin ƙwarewa da jagorancin UBANGIJI.

         Adadin shekaru na hawan farko suka cika ga duk waɗanda suke kan mulki, mai makon Alhaji Abdul-aziz ya koma sai jama’a suka nuna shugabancin ƙasar gaba ɗaya suke bukatar ya karɓa. Wannan lamari yaso gigitashi sosai. A fili ya nuna sam bazata yuwuba, amma ina jama’a sun tsaya kai da fata suna masa magiya da kai kukansu wajen ALLAH.

     To duk abinda ALLAH ya hukunta sai ya kasance koda bawan da abin ya shafa bayaso, kana nakane ALLAH yana nashi, nashiko shine gaskiya.

       ALLAH ya ƙaddara sai ya zama shugaban ƙasa, sai ga shi kuwa ya zama, dama wanda yake kai ya gamane gaba ɗaya.

     

      Zuwa yanzu Jawaad ya girma, dan shekarunsa bakwai a duniya, yaro mai wayo da ƙyawawan ɗabi’u, kamar yanda ƴaƴan talakawa ke makarantar gwamnati sai ga Jawaad ma a ciki, dan mahaifinsa yace ita shima yayi, a ma ƙauye, to ɗansa ma can zaiyi babu tantama. Aiko hakance ta kasance, dan sai ga ɗan shugaban ƙasa a makarantar gwamnati, abin ya burge jama’a, tare da jan hankali ga sauran masu mulkin suma duk sukaita maida ƴaƴansu can.

       A gefe kuwa Alhaji Abdul nata sake cusama Jawaad son aikin ɗan sanda, cikin amincin ALLAH kuwa sai gashi yayi tasiri a ran yaron, dan babu sunan da yake ƙauna a ransa kamar *JAY-P!* da Abbansa ke kiransa dashi, ma’ana *_(Jawaad Abdul-aziz Yuseef police)_*.

      Ko kayan wasan Jawaad duk zaka samu suna kamanceceniya ne da kayan jami’an tsaro, abin ya riga ya shiga yaron jini da ɓargo.

      Shekarar Alhaji Abdul-aziz ɗaya akan mulki ALLAH ya jarabcesa da ciwon da har ya kwanta, ashe hawan jinine bawan ALLAH, kwanansa uku kacal da wannan ciwo zuciyarsa ta buga yabar duniya😭.

     

     Tashin hankali kenan wanda ba’a saka maka rana, wannan lamari harma bansan a yanda zan musaltashi masu karatu su fahimta ba, dan kuwa ƙasarce baki ɗaya ta harmutse tare da komai na cikinta, mutuwar Shugaban ƙasa Abdull-aziz ba batun iyalinsa kawai akeba, maganar al’umma kawai akeyi, waɗanda sukeji basu taɓa gamo da rashi mai taɓa zukata da aiyuka irin wannan ba.

STORY CONTINUES BELOW

       Tunda wannan rasuwa ta gudana bilkisu ta rasa hankalinta, sam an kasa gane kanta, hauka take tuburan wanda ya kai ga har an rufeta a ɗaki ma.

     Mama maryam tsohuwa mai tawakkali da hakuri, baka ganin hawaye saman fuskarta sai dai na zuci kawai.

     Ƴan uwansa kam su kansu ka kalla abin tausayine, lamarin yay masifar ruɗasu, dan Abdul mai biyayyane a garesu tare da ƙyautata musu, suka tuna irin gwagwarmayar da yasha a rayuwarsa da bajintar da yay musu a rayuwa sai suji hankalinsu ya kuma ƙololuwa a tashi, sunyi kuka harsun godema UBANGIJI.

        ALLAH sarki Jawaad, duk da bai kai hankalin da za’ace ya fahimci komaiba ya ɗanyi kukansa ganin kowama yanayi, musamman ma halin da mahaifiyarsa take ciki na hauka, sai dai zuwa wani lokaci kuma sai ya saki ransa, yakan dai zo ya tambayi mama maryam ina Abbansa? Yaushe ne zai dawo?.

    Sam bata ɓoye masa, takan ce masa Abbansa ya tafi inda ba’a dawowa.

     Wani lokacin yayi kuka, wani lokacin kuma yay zugum yana tunani kafin kuma ya saki ransa ya koma wasa cikin yara sa’oin sa.

       A haka aka share wasu watanni, riƙon Jawaad ya dawo hannunsu mama maryam, bilkisu kuma ana cigaba da nema mata magani, dan bata ma ƙasar an kaita asibiti.

     Haka rayuwar ta cigaba da shurawa, an maido Bilkisu gida, kamar taji sauƙi sai kuma abu ya dawo sabo, lokacin har Jawaad ya fara wayo, yana shekara ta goma sha huɗu, ajin secondary js2, ranar wata juma’a sai aka wayi gari Bilkisu ta bar gida, nema iya nema anshasa amma babu ita babu dalilinta, lamarin ya girgiza mama maryam har itama ya zama sanadi a gareta.

      ALLAH yayma mama Maryam rasuwa sakamakon ɓatan bilkisun itama, wannan karon kam Jawaad yaji zafi sosai na rasuwar kakarsa da ɓatan mamansa, yayi kuka har abin ba’a cewa komai.

    Ƙanwar bilkisu taso riƙon Jawaad ya dawo hannunta amma dangin mahaifinsa suma suka ƙi, sai Abba Naseer babban yayansu Alhaji Abdull na farko a gaba ɗaya gidan ya amshe shi ya koma hannunsa da zama.5

        *★★★★★★★*

      Gata sosai Jawaad yake samu a wajen ahalinsa, dan a ganinsu  lokacin da zasu nuna jin daɗin ƙyautata musu da mahaifinsa yayi kenan, ɗan gatane ta kowanne fanni, riƙonsa ake tamkar yana gaban iyayensa, ƙilama idan sune bazasu masa wani gatanba irin haka.

     Kamar yanda marigayi Alhaji Abdul ya ajiye burinsa akan Jawaad na zama ɗan sanda sai ALLAH ya amince masa yasamu cikar burinsa ta hanyar cusa son aikin ƴan sanda a zuciyar Jawaad, sosai ya ke son aikin ɗan sanda, wannan shine burinsa, mafarkinsa, kuma fatansa. Lokaci ƙanƙani ya samu cikar burinsa kodan tsatson da ya fito, da dattako irin na mahaifinsa da baza’a taɓa mantawa ba.

*______________________________*

        Shekaru sun shuɗa, komai ya sauya, Jawaad ya zama abinda yay fata, ya girma ya zama babban mutum kamilallen saurayi mai aji da tarin cikar kamala da kwarjini na haƙiƙa, komansa na nagartattun mutane ababen koyi da dubi, gaba ɗaya halayen mahaifinsa sun dawo jikinsa, sam bashi da damuwa sai ta aikinsa tare da ƙyautatama jama’a.

    Mutum ne da bai damu da abinda bai shafesa ba ko ba’a sakashiba, abinda ke gabansa kawai yakeyi, idan har bakai ne ka sakashi a lamuranka ba bazai taɓa shiga ba, bashi da son hayaniya, bai da girman kai, bai da wulaƙanci, sanan sam ba miskili bane ba. Abu ɗayane yake yawo a jinin Jawaad da ke saka jama’a dangantashi da waɗancan ɗabi’un na sama, shine rashin sabo, sam baisan sabo ba, kana takashi zai shata maka dogon layi, tsautsayi ko rawar kai ya saka ka ƙetara to lallai kun ƙulla kenan, kuma ka ɗaura kanka a danja mai haɗarin gaske. Babu ruwansa da kai wanene? Ko kuma ina ka fito? Miye matsayinka a garesa duk ba’abin kallonsa bane.

     Jarumi ne ta fannin aiki da rayuwa, sannan gagararrene a duniyar tsagerun mutane, idan ya ɓalle sam bai san bari ba, duk abinda ya saka a gabansa sai ya cimma manufarsa yake yankan filin hutu.

      Waɗannan ɗabi’un nasane suka jawo masa abokan tsama ta fannoni daban-daban, a cikin hukumarsu da wajenta, harma da tsagerun gari. 

★★★★

              Shahuda ɗiya ce ga yayar marigayi Alhaji Abdull, wato Hajiya Humaira, tuni suna ƙasar Holland ita da mijinta, yaransu biyar suma, mata uku maza biyu, asalin sunan Shahuda *Sabeerah*, dan sunan mahaifiyar Abbansu aka saka mata, amma sai suke mata alkunya da suna Shahuda, ita ce ƴa ta huɗu a gidansu, ƴan gatane na haƙiƙa, waɗanda suka tashi da ɗabi’un turawa a cikin jininsu, sam basu san bari ba, dan bama a faɗa musu.

          Hajiya Humaira tana son Jawaad, shiyyasa lokuta da dama take matsa masa zuwa ƙasar Holland wajensu ya ɗan huta. To annan fa Shahuda ta ga Jawaad ta mutu a kansa, tun yana basarwa dai har shima ya zurma, dan Shahuda ƙyaƙyƙyawace ta haƙiƙa, saboda mahaifinsu bafilatanine ɗan asali mai asalin madarar ƙyawu, duk cikin yaran kuma Shahuda tafi biyosa, ga jin daɗi da suke ciki, saboda inda suka taso, wannan ya haɗu ya maida Shahudah son kowa ƙin wanda ya rasa.

      Jawaad yana son Shahudah, sai dai halayenta na bashi tsoro, dan kuwa dai irin yarannane da babu kwaɓa babu harara, idonsu ya buɗe da ƙazamar wayewa mai wahalar canja ra’ayi cikin sauƙi. Dan haka sai bai wani cika sake mata fuska ba, dama can yaran Family ɗin shakkarsa suke, dan bayan gaisuwa baya basu wata fuskar shiga huruminsa, sai dai fa yana ƙyautata musu akan bukatunsu, idan abu suke buƙata kafin su tambayi sauran yayyensu sun nema da ga wajensa, kuma inhar yana da halin yimusu yakan musu gwargwado.

 

         Aikin da ya kai mahaifin su Shahudah ƙasar Holland ya ƙare, dan haka ya tattarosu suka dawo ƙasarsu ta haihuwa, tunda suka dawo Shahuda ta dawo nan Tafida Family house ɗin su Jawaad ta tare duk dan shi. Ba zamuce baya kulata ba, sake mata ne kawai bayayi, wannan kuma badan hulaƙanci yake mata haka ba, rashin sakin jiki da jama’a halinsa ne kowa ya san haka, ita kanta sanin hakanne ya sata bata damun kanta da lamarin nasa, burinta kawai ta mallakesa matsayin miji, dan badan Jawaad ba bazata taɓa dawowa zaman ƙasarba sam, duk abinda ya shafi afirika ɓata mata rai yakeyi, a haukarta bayan aurenta da Jawaad saita ja ra’ayinsa sunbar yankin afirika gaba ɗayanta sun koma turai da zama. (😂🤣Babbar magana shahudah).

           *★★★★★★★★*

    Hankalin Hajiya Humairah ya tashi ganin tunda suka dawo ƙasar Jawaad yaƙi yay maganar aurensa da Shahudah kusan shekara uku, hasalima yafi maida hankalinsa ga aikinsa fiye da komai, ga Shahudah kullum cikin damunsu take akan batun Jawaad.

      Shiryawa hajiya humaira tayi ta nufi *Tafida family house* domin tattaunawa da ƴan uwanta akan batun auren, dama gashi lokacin meeting ɗinsu na family ya kusa. Koda takai kukanta akan zancen sai kowa ya bada goyon baya, aka kuma tuntuɓi Jawaad akan maganar.

        Haushi abun ya bama Jawaad matuƙa, dan sam bai shirin wannan auren nan kusa ba, so yay sai ya maida Shahudah cikin hankalinta da aƙidar yankinta da addininta, amma sam an wani zo an masa titsiye. Cikin ƙuluwar haushi akan zancen yace suyi duk yanda ya dace kawai.

          Wasunsu sun fahimci bai soba, amma sai suka watsar da fushin nasa aka hau shirin biki na ƴaƴan gata, dan dama babban burinsu suga yayi aure kamar sauran yaran gidan kodan su gujema zaginsu da jama’a keyi akan sunƙi sakashi yay aure.

           Sam ƙin bama bikin muhimmanci Jawaad yayi, hasalima hankalinsa na kan aikinsa, komai sai iyayensa keyi, sai da Shahudah ta sakashi gaba da kuka sannan ne yaɗan maido hankalinsa shima ba duka ba.

     Haka dai dangi sukaita lallaɓata akan ta manta da lamarinsa tunda kowa yasan halinsa ayi auren kawai, idan ta shiga zai bata kulawa insha ALLAH.

      Son da take masane ya sata yarda da shawarwarinsu akai biki lafiya aka tashi, sai dai a hidimar bikinma ta mugun shaƙar baƙin ciki, dan ƙin zuwa yay taro ko guda ɗaya har dinner ɗin da suka shirya bayan ɗaurin aure ta garari ta nunawa a gidajen tv saboda tsabar haɗuwarta, sam baijeba, a ranarma tsabar iskancin Jawaad a wajen aiki ya kwana, a washe gari kuma yaƙi yarda ya hadu da kowa a gidan saboda tsiyar da ya tsula musu.

        Shahuda kuma tace bazata tareba sai yazo ya bata haƙuri.

     Nanma sharewa yay kamar baisan sunayiba, sai da Hajiya Ummah ƙanwar mama bilkisu mahaifiyarsa ta kirasa tai masa faɗa sannan yaje, mai makon ya bata haƙurin sai ma ya sake gaggasa mata magana, ya kuma ce inma bata tareba baida matsala da hakan.

       Da yake su kaɗaine a ɗakin sai Shahudah ta ci kukanta ta share hawaye da burin sai ta rama amma a gidansa, ga sauran ƴan uwa kuwa sai ta nuna musu ai ya lallasheta ne itako tanata masa shagwaɓa (😂😝).

       Kowa ya yarda da batubta, dan an tabbatar Jawaad nason Shahudah, halinsa na nuna ko in kula da abu ne yake sakashi ɓoyewa, amma yanda ma yake ɗan kulata fiye da sauran yaran gidan zai tabbatar maka da yana sonta.

       Daga ƙarshe dai sai amarya ta tare a nan gidan sashin Alhaji Abdull mahaifin Jawaad, dama tun bayan tashinsu babu wanda ya shiga sashen, yanzu kam sai Jawaad yay masa gyara mai burgewa aka saka masa amaryarsa anan.

      A farkon amarci abin nasu ɗoɗa-ɗoɗa, amma son jiki da shegen ɗaukar dala babu gammo na ɗabi’un Shahudah ne ya zamarma auren nasu matsalolin da baibayi da sukai ma zaman nasu ƙullin goro. Tunda gashi har Jawaad na complain a kan auren watanni bakwai kacal🤦🏻‍♀️……….✍🏻

Mun dawo labari☺️

ALLAH ka gafarta na iyayenmu😭🙏🏻ƘWAI cikin ƘAYA!!

   Bilyn Abdull ce👌🏼

Shafi na shida.

……….A kullum duniya canjama bawa ajin karatu take, yau ɗinkace kawai zata tabbatar maka da hakan, musamman idan kaga ta banbanta da ƙaddarar jiyanka. Rayuwa mataki biyu ce, kowacce ka zaɓama kanka zaka isa zuwa makomarta, saɓanin shine kawai dace wajen banbance nagartacciya ko gurɓatacciya.

       A yau dai ga ni a matsayin marainiya, wadda babu ɗumin duka mahaifa guda biyu, sannan babu bangon jingina daga tsatson zuminci ko guda ɗaya. Rayuwata ta cigaba da tafiya a hannun mutanen kirki ahalin fiddausi, sun zamemin uwa da uba bayan ƙasa ta rufe idanun nawa, yanzu sune ci na sune shana da dukkan buƙatun rayuwa da aljihunsu sai iya ɗauka.

     Zuciyata na kewar iyayena, amma jarumtata na ɓoye hakan a koda yaushe, haƙuri kuma ya zamemin sandar jagora yayin tafiya ba tare da na lalubi hanya ba saboda makantar zuci.

    Tabbas rayuwar gidanmu ta canjamin ta kowanne ɓangare, dan a lokacin da iyayena na raye akanji shakkar min wani abun, amma yanzu kam ƙiri-ƙiri wasu kan nuna ƙyamata ko hantara ta ma kai tsaye, idanun maman firdausi ne kawai kan hana wasu cin zarafina koda da harara ne, amma da zaran babu ita a tsakar gidan to kare ma ya fini daraja.

        Matsala ta farko dana fara cin karo da ita a gidan mai ƙona zuciya da barin tabon da ba’a mantawa shine zuwan mai gidan Alhaji lado naira, koda iyayena suka rasu bana tunanin Alhaji lado yazo gidan gaisuwa sam, amma rana tsaka sai gashi danƙyas-danƙyas yazo koramin bayanin na kwashe kayana daga ɗakinmu zai zuba ƴan haya.

          Cikin ƙarfin hali da dogaro da kuɗin hayarmu na shekarar basuyi ko rabi ba na shiga kora masa bayani akan ai da sauran lokacin tashinmu.

      Alhaji Lado ya bankamin harara tare da watsamin yatsun hannunsa biyar cif alamar zagi (daƙuwa) “Kinci uwarki, kujimin lalatacciyar yarinya, yo ko yau kuka biya tunda wanda yay biyan ya tafi barzahu ai kuɗinku sunyi isfaya (expire) kuma, to dan shelen uwarki ma😱, gidan tsohonki ko nawa da har zaki zauna jamin sharaɗi. Maza tashi kiyo waje da komai tafe nake da mai fenti, ki zauna wannan bacar har kuɗin su kare, dan itama zaki fara biyan kuɗin hayane tunda yanzu ƙofar ɗakin wasune”.

     Kasare nai ina kallonsa tamkar wata wawuya ko sokuwa, wasu da ga jama’ar gidan ko dariya suketa tuntsurawa, ƙalilanne basu ji daɗin lamarin ba, amma babu wanda yace ma Alhaji lado baiyi dai-dai ba, dan sunajin tsoron ya shuka musu shika-shikan rashin arziƙinsa suma, kaɗanma da ga aikinsa yace kaima ka tashi ka bashi ɗakinsa. Baka da yanda zakai dashi kuma dolenka ka tashi, inba hakaba ya saka yaransa subi tsakkiyar rana ko duhun dare su naɗa maka na jaki🤦🏻‍♀️…….

      Tsawar da ya dakamin ce ta sakani zabura na miƙe tsaye, ya nunamin ƙofar ɗakinmu yana haɗe fuska tamkar kashin ƙato na farar safiya.

    Jikina na ɓari na nufin ɗakin, dan fuskar Alhaji lado tafi baƙin kashin shanu barazana idan ya murkite ta, ina shiga itama firdausi na shigowa, itace ta taimaka min wajen haɗe kayan muka ƙuƙƙulle ina sharar ƙwalla, sauƙina ɗaya ma kayan bawani uban yawane da suba, marasa amfanin ciki kuma sunfi masu amfanin yawa.

      Bayan mun gama haɗesu ta taimaka min muka fiddosu zuwa cikin bacar da muke kwana, wadda kayan suka mamaye kusan rabinta, dan dama bawani girman azo agani bane da ita.

     Alhaji Lado bai kuma bi takaina ba sai ma yaransa da suka shiga suka fara fente ɗakin da fenti mai ƙyau da ya bama kowa mamaki, dan duk ɗakunan gidan da farar ƙasa aka shafesu  maimakon fenti🤦🏻‍♀.3

            Da daddare munacin abinci a ɗakin su Firdausi innarsu ke bani haƙurin abinda ya faru da rana, dan ɗazun bata da sukunin nuna tausayina suma ta shafesu, shiyyasa sukai gum da ga ita har baba.

     Murmushi nai mai ciwo ina faɗin, “Babu komai inna, ALLAHN da ya bashi muma bai manta da muba ai”.

    “Hakane Bilkisu” inna ta faɗa tana murmushi, ta dafa kafaɗa ta tana ƙara nuna min muhimmancin haƙuri da amfaninsa.

    Naji daɗin bayaninta, dan naƙara samun ƙwarin gwiwar ɗaura ɗammarar zama jaruma akan kaina.

STORY CONTINUES BELOW

★★★★★★

       Faruwar hakan da kwanaki biyu kacal waɗanda zasu zauna a ɗakin suka tare.

      Abinda ya tada hankalin dukkan jama’ar gidan, shine wanda zai tare a ɗakin da muka zauna.

     Kusan sha biyun rana saiga ƙattai suna shigowa da kaya cikin gidan, waɗanda kallo ɗaya zakai musu ka fahimci addu’a kawai rayuwarsu take buƙata. Sune suka saka komai a ɗakin suka gyarashi tsaf, duk da bamu shigaba munsan dolene ya haɗu, dan kayan da akaita shiga dasu babu ma mai kwatankwacinsu a cikin gidanmu.

     Mun daɗe bamu da wutar nefa a gidanmu, amma sai gashi anzo a ranar an gyara, washe gari kuma sai ga masu gyaran fanfo tunda farar safiya.

     Irinmu da bamusan wanene zai tare a ɗakinba dai mamaki ya matuƙar kamamu, burinmu muga wanene zai zauna a ɗakin kawai.

       Da yamma gan da magriba mun dawo islamiyya mukaci karo da baƙon lamarin da sam ada babu kwatankwacinsa a gidanmu. Kana kusanto gidan kunnenka zai fara jiyo maka sautin kiɗa da ke tashi da ƙarar Janareto (Genretor).

     Kallon juna mukai ni da firdausi, dan munsan dai babu wani shagali da akeyi a gidan, koma anayi ba’a taɓa kalar wannanba.

      Badai muce komaiba muka shigo da sallama a bakunanmu. Fetal tsakar gidan yake tamkar babu wani mahaluki mai numfashi, gidanmu da idan ka shigo da yamma zaka ɗauka biki muke sai gashi tsitt, idanunmu suka sauka akan matasan samari da adadinsu zai kai goma sha uku acan jikin ɗakinmu da muka tashi, wanda bacar da muke kwana ni da firdausi take kallonsa, Mutum ɗaya ne zaune a kujera kawai yana zuƙar sigari, sauran kuma duk suna saman tabarna babba da aka shinfiɗa, wasu karta sukeyi, wasu kuwa zaune suke suna kallon masu kartar, sai ɗaya dake matsama na zaune saman kujerar ƙafa tamkar wani sarki.

        Kallon juna muka sake yi ni da firdausi, yayinda suma matasan samarin suka zubo mana idanu su duka.

      Gyaran murya da na kan kujerar yayne ya saka dukkan samarin saurin nutsuwa kowa yana sunkuyar da kai.

       Baice uffanba shikam, sai zuba mana idanu da yay yana ƙare mana kallo da ga sama har ƙasa duk da sanye muke cikin hijjabai har kusan ƙasa.

     Firdausi ce tai ƙarfin halin kama hannuna muka cigaba da takawa dogon tsakar gidan muna dosar inda samarin suke, dan ɗakin su firdausi shine jikin nami dama can, sannan bacarmu a tsakanin ƙofar su firdausi da ɗakinmu na da inda samarn suke yanzu take, hakan yasa samarin suke zaune har ƙofar bacarmu da gaban ɗakin iyayen firdausi.

        Duk da munga a yanayin da suke da bana mutanen kirkiba, ga kuma kiɗan dake tashi da bamu da tabbacin zasujimu, hakan bai hanamu gaishesu ba. A mamakinmu sai mukaji suna amsawa kuwa, wanda ke kan kujerarne kawai bai amsaba, kuma har yanzu idanunsa na kanmu.

      Wanda ke zaune saman ƙofar su firdausi ne ya matsa mana fahimtar da yay kamar nan zamu shiga, cikin sassarfa muka faɗa ɗakin kuwa da hanzarinmu ko sallama babu.

      Maman firdausi dake zaune ta miƙe zumbur tana nufomu, hannunmu ta kama zuwa tabarma jikinta har rawa yake.

    Mamaki ya sake kamamu, mun buɗe baki zamuyi magana tai azamar mana nuni da muyi shiru. Shirun kuwa mukayi muna cigaba da binta da kallo.

         Haka mukai kwannan yau babu wani sikuni ga jama’ar gidan, kowa ya maƙure a ɗakinsa yana tsoron fitowa, mu kanmu yau a ɗaki ɗaya muka kwana da iyayen firdausi, baba ya hanamu zuwa bacarmu.

MAFARIN MATSALA

         Baƙon dai da ya tare a ɗakin da na taso tun ƙuruciya na ganni a ciki matsayin namu, ɗan Alhaji Lado Naira mai suna Jazuli (Jazuuuga) ne ya tare.

      Jazuli ko nace Jazuuuga ɗane na huɗu ga Alhaji lado, shine namiji da aka fara haifa masa a gidansa, yana matuƙar ƙaunar yaron tun yana ƙaraminsa, hakanne yasa ya tashi a sangarce, sam Jazuuuga bayaji tun bai kai girma ba, tun yana secondary sukul ya haɗa dabarsa, yana da yara masu take masa baya da haɗarinsu ya sa ake matuƙar tsoronsa, duk yanda kuke tunanin takadaranci irinna Jazuli abin ya wuce gaban nan, bayan ya kammala sakandire dinne kuma baban nasa ya ƙarama sheɗancin nasa armashi ta hanyar fiddashi karatu can kudancin ƙasar, acewarsa zaifi samun ilimi acan.

       Karku tunanin ilimin Jazuli ya nema koda yaje can ɗin, sam yama manta karatune ya kaishi, ya shige cikin manyan marasa jin magana yay kane-kane yana ɗaukar nasa karatun acan, tsawon shekara biyar iya abinda ya ƙaro ilimi a kansa kenan, idonsa ya matuƙar sake bushewa, ya zama jan wuya na sosai.

      Abinda ya maido Jazuuuga gida kuwa kashe oga kwata-kwata na ƙungiyarsu da yay ne, hakanne ya sakashi gudowa ya dawo gida dan yasan dai idan yazo nan ya tsira.

     Duk da hankalin Alhaji Lado ya tashi akan halin da ɗansa ya sake ƙwarewa a kai hakan baisa ya daina masa gata ba, saima ya ninka, a cewarsa ai hakanne zaisa ya shiryu.

    Ɓarin kuɗin da Alhaji Lado kema Jazuli ne ya bashi damar jan ra’ayin yara takadarai irinsa, wasuma abun nasu ƙaramine, amma saiya horar dasu matsayin sojojinsa, ya haɗa ƙungiya mai matuƙar haɗari da barazana.

      Akwai dalilin da yasa Jazuuga ya dawo gidan hayar na mahaifimsa, dukda gidansu kuwa yaci uban wannan sau fiye da goma, ga kayan alatu da morewar rayuwa a cikinsa, amma saboda son samun cikar burinsa shine ya cema mahaifinsa nan yakeson zama, babu ɓata lokaci kuma Alhaji Lado ya zo ya tada Bilkisu da ga ɗakinsa aka gyarama Jazuuuga…………✍4ƘWAI cikin ƘAYA!!

Bilyn Abdull ce👌🏼

Shafi na bakwai

JAWAAD

…………Cikin ƙunar zuciya da ɗacin da ya keji akan halayyar Shahudah yay shirin fita a gaggauce domin komawa Office. Bai bawani ɓata lokaci ba ya fito cikin shigar ƙananun kaya sai zabga ƙamshi yakeyi.

        Shahudah na a falon kwance cikin kujera, ga kiɗa mai taushi ya na tashi ta cikin sifikun da aka ƙawata falon dasu, sanye take cikin wando da riga masu azabar ƙyau kalar ruwan hoda, kasancewar kayan robane sunyi mugun bin jikinta tamkar da fatarta aka haliccesu, wandon iyakarsa gwiwa, sai rigar da bata rufe mata ko cibiya ba, dan ƙyau tayi ƙyau sosai, dolene ka kalleta ka sake kallo.

     Gaban ɗayan imaninta nakan waya ɗinta da take cheating, gefe ɗaya tana sauraren waƙa.

        Har Jawaad ya gama sakkowa bata sani ba, sai da mayen ƙamshin turarensa ya bugi hancinta ne ta ɗan lumshe ido tana zuƙarsa kafin ta buɗe ta yunƙura ta tashi zaune, ƙyawawan fararen idanunta a kansa.

         Shima idanun nasa na kanta, dan kwalliyar tata ta masa ƙyau, sai ya ji kaso mafi yawa na haushinta ya ragu a zuciyarsa, sauran cake ɗin da taci ta rage da kofin da ta sha tea ya kalla ya kauda kansa, kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa yana sake haɗe fuska.

         Murmushi Shahudah da ke kallonsa tayi, dan sam ita bata da riƙo, dama ko faɗa sukai zai ta shareta, itako mintuna kaɗan ta manta sai kuma an sake wani.

    Yanzu ma dai hakan ita harta huce, hakanne ya sata tasowa ta shige jikinsa tana magana cikin shagwaɓa.

         “Oh My BB kayi ƙyau sosai”.

       Shiru yay mata, bai kuma rungumetanba shi.

       hakan yasa ta ɗago tana kallon fuskarsa, ta kai lallausan hannunta tana shafa fuskar tana murmushi, “BB kamin murmushi mana”. ‘Ta ƙare maganar da sumbatar laɓɓansa’.

        Duk da saƙonta ya shigesa hakan bai hanashi ture hannunta ba daga fuskarsa yana ƙoƙarin janyeta a jikinsa, amma sai ta ƙankamesa tana bubbuga ƙafa cikin shagwaɓa.

          Iska ya ɗan huro da ga bakinsa, a daƙile yace, “Wai mikikeyi haka kamar wata tata Hudah? Ki bari karkimin Squeezing kaya”.

          “Sai ka sake fuskanka to” ‘ta sake faɗa a raunane’.

       Kansa ya girgiza kaɗan yana riƙota sosai jikinsa, hakan ya saka Shahudah ɗago fuskarta cike da annuri ta kallesa, shima kallonta yake cikin ido yana kuma narke idanunsa dake ƙara tsundumata a ƙaunarsa.

       “Idan kinaso ki sameni yanda kike buƙata Hudah ki canja kamar yanda nima nake buƙata”.

      Yay maganar a hankali tare da sauke laɓɓansa akan nata da keta walƙiyar janbaki, ya sumbata.

     Kafin ta samu zarrar magana ya cireta a jikinsa ya nufi hanyar fita yana saka baƙin Eyeglasess ɗinsa a ido ba tare da ya sake koda kallonta ba.

         Murmushi Shahudah tayi tana wani juya idanu, tabbas tana ƙaunar Jawaad fiye da hasashen mai tunani, dan shine namiji da ta fara so a rayuwarta, so kuma na haƙiƙa mai cike da tsagwaran sadaukarwa, kuma tana fatan ƙare rayuwarta da ƙaunarsa. Matsala ɗaya da ke tsakaninsu shine banbancin ra’ayi, Jawaad ɗan gayune mai aji da cikar haiba, duk yanda kake tunanin haɗuwarsa ya zarta nan, amma tana mamakin yanda kansa yake a tukunya game da rayuwa irinta manyan yara, ta ɗan taɓe bakinta tana komawa cikin kujera ta zauna, tasan canjawarta ta koma ra’ayinsa abune mai matuƙar wahala da iyawarsa a gareta zaiyi wuya, su dai tafi a hakan kowa da ra’ayinsa zaifi basu zaman lafiya, kan ya matsa sai ta canja ɗin dai-dai da buƙatarsa.

+

★★★★★★

         Ya isa Office ɗinsa da ya ƙawatu da kayan more rayuwa, sai ƙamshi mai daɗine ke tashi a ciki, ya zauna cikin kujera yana mai miƙa hannunsa domin karɓar takardun hannun wanda suka shigo tare. Shafin farko da ya buɗe ya maida ya rufe yana ɗago razanannun idanunsa, “Ina na farkon?”

     Ya faɗa cikin karsashi.

          Cikin ɗan ruɗewa da tambayar bazata Aminu ya shiga kame-kame, “S…o…so…sorry sir!, dama Sir Qaseem ne ya karɓa, sai yace na kawo maka waɗannan”.

      Gira ɗaya Jawaad ya ɗage sama, ya janye idanunsa da ke neman fara canja launi ba tare da ya tankama Aminu ba, cikin nuna halin ko in kula ya mai da hankalinsa ga Computer ɗin da ke saman desk ɗin gabansa.

     Tsawon wasu mintuna da basu gaza biyar ba Aminu na tsaye, babu abinda jikinsa keyi sai tsuma, zufa ta hudo dukkan ƙofar gashin da ke jikinsa.

    Jawaad dake aikinsa ya kallesa ta wutsiyar ido yana faɗin, “Tsayuwar ka zaɓa ko komawa dasu, idan ka karɓo waɗancan ka haɗa ka kawo min?”.

       Sosai tsantsar firgici ya kuma bayyana a fuskar Aminu, ya sharce gumin da ya tsatstsafo masa a goshi tare da gyara tsaiwa zaiyi magana…….

      Wani mugun kallo Jawaad dake ƙoƙarin miƙewa ya watsa masa, ba tare da yace uffanba ya zagayeshi ya fice da ga ma office ɗin gaba ɗaya.

        Da tsantsar sassarfa ya biyo bayan Jawaad da ko kallonsa baima sake yiba.

STORY CONTINUES BELOW

             Mutanensa biyar na amana suka take masa baya zuwa Office ɗin boss ɗinsu, yayinda Aminu ya bi hanyar da zata sadashi ga ubangidansa Qaseem Ali.

           Yardar dake gareshi ga manyansa sam ta hana masa shamaki da neman izinin shiga ofisoshinsu, kansa tsaye yake shiga ba tare da jiran iso ba. Sai da yay masa sarawar girmamawa tamkar yanda al’adar jami’an tsaro take, kafin ya zauna a ɗaya da ga kujerun gaban ƙaton tabirin.

           “Jay!”.

“yes sir”.

      “Ko kasan maganar sace Alhaji kokino tana neman  shigo da shugaba ƙasa a ciki”.

      Cikin rashin fahimta Jawaad yace, “Sir! Kamar ya kenan?”.

       Shiru ogan yayi na wasu sakwanni, kafin ya ɗago kansa daga wayar da yake dannawa ya maida kallonsa ga Jawaad, wayar ya miƙa masa yana faɗin, “Ɗazun  nai magana da shugaban ƙasa kai tsaye babu shamaki kowa a tsakaninmu”.

     Idanu sosai Jawaad ya zaro waje, “Sir, miya ce?”. ‘Jawaad yay maganar a hankali, mai nuna alamar tsorata’.

         Kaɗan Sir Ahamad barewa ya buga tebirin gabansu yana huro iskar bakinsa, ya miƙe tsaye tare da maida dukkanin hannayensa baya ya goya, sai da yay taku biyu zuwa uku kafin ya juyo ga Jawaad, “Jay! Adadin lokaci, lokaci shugaban ƙasa ya bamu na gaggauta samo Alhaji Sadi kokino, abinda ya bani mamaki annan yanda ya tsaurara, mika fahimta?”.

       Jawaad dake bin ogansa da kallo kamar ya samu magiji ya sauke numfashi, tare da taɓe bakinsa yana murza yatsun hannunsa da ke bada ƙarar ɗas-ɗas a hankali, zuwa kusan sakon goma sha biyar sai kuma yaɗan zabura, cikin ƙanƙance idanu mai nuni da na tuno, yace, “Sir  sai naga kamar yana tunanin ana zarginsa da hannu a ciki….”

     “Exactly my dear!, nima wannan shine tunanina, Jay kana da ƙwaƙwalwa, shiyyasa a komaina nake sonka a gaba” ‘Sir Ahmad ya ƙare maganar yana komawa a kujerarsa ya zauna’.

      Jawaad dake murmushin jin daɗin yabon da ogan nasu yay masa, ya sauke numfashi yana gyara zama, “Sir inada shawara”

       Sir Ahmad dake kallonsa yace, “ita mukafi buƙata ai ayanzu Jay”.

      Jawaad ya lumshe idanunsa tare da buɗewa a lokaci ɗaya yana jinjina kansa, “Zan turo maka a rubuce Sir”.

         “Okey babu damuwa Jay, yaya maganar zaɓin haɗa runduna?”.

       “Sir zanje na zauna dasu Asim yanzu insha ALLAH, zuwa yamma zamu aiko da jadawalin sunayensu”.

     “Okey, amm……”

Maganar Sir Ahmad ta kakare dalilin Knocking ƙofa da akayi, haɗiye maganarsa yayi ya bada izinin shigowa……..

_____________________________________

                BILKEESU

_____________________________________

              Sakamakon tashi da hayaniyar yaran gidanmu a kowacce safiya, sai yau muka tashi da hayaƙin sigari a gidanmu.

       Gashi rashin samun isashen barci ya saka mafi yawancinmu makara sallar asubahi. Hakanne ya kawo go slow ɗin shiga banɗaki. A ɗarare kowa ke komai saboda dokar rashin yawan motsi da yaran Jazuuuga suka kafa mana, a cewarsu yana barcin safe, duk wanda yay ƙwaƙwƙwaran motsin da ya tashi to lallai sai yaji a jikinsa, kuma komai tsufarsa basu ɗaga masa ƙafa.

         Hakanne yasa mafi yawan mazan gidanmu ficewa da ga gidan da wuri ba tare da ko wanka sunyi ba, wasu kuma suka ɗauki kayan wankan zuwa gidan wanka.

      Mukan dama maman firdausi ta mana dabara, wani tsohon bokitin ƙarfenta da hannun ya ɓalle tuni ta koma saka kayan tarkace a ciki ta ɗakko mana, a ciki mukai alwalarmu, bayan mun kammala muka fita muka zubda ruwan. Hakama da zamuyi wanka saita yi dabarar saka labule jikin murfin ƙofa da bango tace muyi cikin ƙatuwar bahonta. Muna kammalawa shirin makaranta nayi, babu zancen zaman karin kumallo, baba ya bani naira ɗari akan idan naje makaranta sai na karya, dan ita firdausi ta gama secondary tuni. Godiya nai masa na amsa na fito cikin fargabar waɗanan shaiɗanu da suka wargaza mana farin cikin gida a cikin kwana ɗaya kacal.

       Sosai gabana ya faɗi, dan kuwa ina fitowa da Jazuuga na fara tozali, yana gaban fanfo tsaye, daga shi sai gajeren wando, hannunsa riƙe da brush alamar baki zai wanke, sai yaronsa ɗaya a gefensa riƙe da kofin ruwa.

     Nai ƙasa da kaina, yayinda nakeji har lokacin shi nasa idanun na yawo a jikina. Tamkar munafuka naɗan risina kaɗan ina faɗin “ina kwana”.

    Ban jira amsarsa ba nai ƙoƙarin wucesu.

       “K zonan!”

Naji an faɗa cikin wata sautin murya mai ban tsoro, sosai ƙirjina ya shiga sama da ƙasa, na rimtse idanu ina karanto *Hasbinallahu wa ni’imal wakil.*

        “K dan ubanki kurma ce?!!”

     Aka kuma faɗa cikin sautin da yafi na farko razanarwa.

    Juyowa nai garesu, nazo gabansu na tsaya kaina a duƙe, dan bazan iya kallonsa haka babu rigaba, duk da kasancewar gidanmu gidan haya ne bamu saba ganin haka da ga mazan gidanba.

     Shareni yay tsawon lokaci yana cigaba da brush ɗinsa, yayinda idonsa ke kaina ko ƙyaftawa bayayi, sai da ya gama tsaf ya raɓa ta gefena ya wuce yana faɗin, “biyoni”.

      Ba ƙaramin firgici na tsinci kaina a ciki ba, dan marata wani ƙugi tayi kafin ta ɗaure tamau tamkar zata fashe. A cikin zuciyata kuwa ina tunanin na bisa nai masa mi? To. Ban gama samo amsar data dace da tambaya taba naji an fisgi hannuna, duk iya ƙoƙarin tirjewata da magiyar roƙonsa ya sakeni da nakeyi bai saurareni ba, sai da ya kaini har cikin ɗakin nasa sannan ya wurgar dani saman lallausan kafet ɗin da aka shinfiɗa yana huci.

     “K kin sanni kuwa? Kinsan wanene ni? Dahar zaki ringa sakani maimaita miki magana!!”.

      Jikina na rawa naja da baya dajan ɗuwawu ina girgiza masa kai, ga hawaye na gudu a fuskata tamkar fanfo, ya kuma zaromin manyan idanunsa jajaye, cikin nunani da ɗanyatsa tamkar zai tsokale idona yake faɗin, “Karki bari na tsaneki a gidannan, inba hakaba wlhy saina fatattaka rayuwarki, tashi maza ki gyaramin ɗakinnan”.

      Cikin rawar jiki nake amsa masa da “to” na ajiye jakkar makarantana na fara gyara ɗakin, duk abinda nake yana tsaye a kaina tamkar wani dogari, niko sai hawaye nake zubarwa ba tare da samun zarrar gogewa ba.

        Cikin mintuna ƙalilan na kammala gyaran ɗakin, dama ba wani datti yayba. Ba tare da na kallesa ba nake ƙoƙarin magana, duk da nasan shi ni yake kallo, “N…na..gama”.

         “Saura shara” ya faɗa yana juyawa ya fita.

     Tsintsiya na ɗauka nai sharar ina cigaba da kuka, ina gamawa na fito daga ɗakin, ALLAH ya soni ya shiga wanka, yaransa kuma wasu sun fita sai mutum uku kawai.

        A gudu-gudu na fice da ga gidan, duk da naga mafi yawancin matan gidanmu na laɓe ta jikin labule suna kallona, wasu kuma ta Windown ɗakinsu.1

          A yau kam inhar nace na fahimci wani karatu a makaranta to nayi ƙarya, abinda ya faru tsakanina da baƙon gidanmu ya tsayamin a rai, babu abinda nake sai fargabar komawa gidan ma, malamin mu na Geography har buguna yayi akan yana darasi ina duniyar tunani. Dai-dai da yunwar cikina ban tuna da itaba har aka tashi, haka na nufo gida cike da tsoro dan bani da inda nake dashi da ya wuce gidan, kuma dama can ban saba da yawo ba, da an tashi daga makaranta gida nake nufa, shiyyasa yanzu ma naji can kawai nake buƙatar zuwa dukda kuwa tsoron dake cike fal raina…………….✍🏻

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻2ƘWAI cikin ƘAYA!!

Bilyn Abdull ce👌🏼

Shafi na takwas

…………Shigowata soron gidanmu yaɗan sakamin nutsuwa kaɗan, dan yau babu mahaukacin kiɗannan, sai da nai addu’a kafin na shiga da sanɗa tamkar wadda tazo yin sata.

    Wata sassanyar ajiyar zuciya na kuma saukewa ganin ƙofarsa a rufe, sannan babu kowa a cikin irin yaransa, sai wasu a tsirarun matan gidanmu dake ƴan aiyuka a tsakar gidan.

        Abinda ya bani mamaki yanda duk suka zubamin ido kamar wata baƙuwarsu, ni dai sannu nai musu na wuce ɗakin innar Firdausi kai tsaye.

      Sannu Firdausi da inna dake zaune sukaimin, na amsa ina ƙirƙiro ƴar fara’a akan fuskata tare da bin tarin kayanmu da aka jibge gefe da kallo.

    Kafinma na tambaya firdausi ta fara min bayani,

     “Bilkeesu kayanmu ne baba yace mu kwaso da ga baca mu maido nan, dan babu dacewa zamanmu acanɗin saboda canjin da gidan ya samu”.

       Murmushi nayi sosai wanda ya bayyana farin cikina yanzun kam, na zauna kusa da Firdausi ina faɗin, “Amma inna idan mun dawo nan baba fa?”.

       “Karki damu kinji Bilkisu, babanku zai cigaba da kwana a bacar shi, kwananku acan babbar barazanace a garemu da mutuncinku, waɗannan yaran sam zukatansu basusan yaren tsoron ALLAH ba, abinda ransu keso kawai suke ji da gani a gaba ɗaya duniyarsu”.

        “Hakane inna, babu abinda zance daku nidai a wannan duniyar, ALLAH ya yalwata rayuwarku da dukkan farin ciki har cikin aljanna, kun haska fitila a rayuwata lokacin da tsatona suka kashe domin hana kansu ganin hanyar da zasu riskeni, kuɗin masu zinariyar zuciyace mai haske fiye da ta dayimon (diamond), na…….”

      Katseni inna tayi saboda kukan daya sarƙe harshena, ta jawoni jikinta tana bubbuga bayana alamar lallashi

     “Ya isa haka bilkisu, kema ɗiyarmu ce tamkar Firdausi, ki daina kallonmu a waɗanda sukai miki alfarma, muna yin abinda ya dace muyine kinji”.

       Kaina na jinjina mata ina sharce hawaye.

     Kusan tsawon mintuna uku tana lallashina, kafin na miƙe na cire Uniform ɗina naje naɗan watsa ruwa, bayan na dawone na iske Firdausi ta ajiye mana abinci.

       Munacin abinci inna na zaune gefe tana ƙullin kayan sana’arta, Firdausi ta haɗiye abincin bakinta tana faɗin, “Bilki akwaifa matsala”.

        “Tsayawa nai da ga ƙokarin kai abincin bakina ina kallota a tsorace”.

        Inna ta harari Firdausi tana faɗin, “K Firdausi bana son ƙirƙire-ƙirkire fa, ya zaki ɓata mata zuciya? Wannan ai shirmene”.

          “Kiyi haƙuri inna” Firdausi ta faɗa a sanyaye.

     Kallon Inna nayi nima a raunane, “Inna dan ALLAH karki hana ta sanarmin, da inji a wani waje ai gara naji daga gareku, dama tunda na shigo naga matan gidannan namin wani kallon ƙurullah daya tsoratani”.

     Murmushin takaici Inna tayi tana girgiza kanta, “Suma son zuciyane ke ɗawainiya dasu, dan abinda ya shafi kowane a gidane ai”.

       “Dan ALLAH Inna miya faru?”.

        “Karki tada hankalinki Bilkisu, baƙon gidanmu ne ya tara taro ɗazun bayan fitarki makaranta, ya kafa sharuɗa ne a gidan, wai bayason hayaniya, sannan kafin ya tashi barci a share tsakar gidannan a wanke tare da bayi, lokacin da zai fito kuma karyaga kowa sai…….”

    Tai shiru cikin haɗiye wani takaici daya zame mata ƙululu a maƙoshi.

    Cikin ƙaguwa da tsorata nace, “Inna sai me?”

     Shiru tai ta kasa bani amsa, sai Firdausi dake sharar hawaye tace, “Wai sai mu ƴammatan gidan kawai, kece zaki ringa masa gyaran ɗaki, ni kuma kai masa ruwan wanka, su Aina’u ma kowa da aikinta, kinsan miya bani takaici Bilkisu?”.

     Kaina na girgiza mata saboda hawayen da suka fara gudu a kumatuna. Ta goge nata itama tana cigaba da faɗin, “Bayan wannan dokokin harda sharaɗi mai barazana ga duk wanda yace zai bar gidannan ko zai sanarma hukuma, wai amma dukda wannan ruɗanin sai su Zee ke murna, harma suna ƙokarin yin kwarkwasa a gabansa”.

      Kasa cewa komai nayi, sai tsame hannuna danai daga abincin da mukeci na koma gefe, hakama Inna da Firdausi kowa yay shiru yana cuɗawa da kwance abinda yakeji a ransa.

+

STORY CONTINUES BELOW

★★★★★★★

        Kamar yanda Jazuga ya kafa dokoki a gidanmu haka kowa ke bi, ba komaine yasa hakanba sai tsoro, dan ba gidanmune kawai ke tsoron Jazuga ba, gaba ɗaya layinmu a tsorace suke dashi da yaransa, babu wani mai sukuni, dan yaran Jazuga sun addabi kowa a anguwar, gashi sai ƙara jan yara matasa ya keyi masu rauni cikin tawagarsa.

     Abinda zai baka mamaki Police kansu tsoron shigowa anguwarmu sukeyi, ballema muyi tunanin zasu iya kamashi ko ƙwatar mana ƴanci daga mulkin mallakarsa.

       Tun ina damuwa da bautar gyaran ɗakinsa har abin ya zame min jiki, ƙa’ida kullum sai na gyara sau uku, safe, rana, yamma.

       Abinda kawai ke damun rayuwata dashi shine kallo, duk motsina a gidan idonsa na kaina inhar yana gida, duk da kuwa a koyaushe cikin Hijjab muke ni da Firdausi inhar zamu fito tsakar gida.

     A cikin ƴammatan gidanmu kuwa wasu sai dai addu’a, dan kuwa sosai ake zargin Jazuga na lalata dasu yana basu kuɗi, hakanne ke ƙara tada hankalin iyayenmu.

        Muna cikin wannan halin ne kuma saiga ɗan uwansu Firdausi wanda yake matsayin zaɓin iyayenta yazo daga can asalin garin su Firdausin, canjin daya tarar a gidanmu ne ya tayar masa da hankali, dan haka ya roƙi baba akan kawai a saka musu ranar aure.

       Na taya Firdausi murna, sannan na taya kaina kuka, dan kuwa koba komai itakam ALLAH ya tsameta, niko da ko saurayi ban taɓa yibafa? Kunsan samarinma sunfi son ƴammatan masu ƙyale-ƙyale, niko bani cikin jerin masu shi, wadda suturar sakawa bata wadaceta ba ina taga kayan ƙyale-ƙyalen burge saurayi.

        Saurayin Firdausi bai bar garinba sai da aka tsaida maganar aurensa da Firdausi wata biyu kacal..

             Rayuwa a gidanmu ta cigaba da tafiya a ƙuntace, komai yabar mana daɗi saboda su Jazuuga, abu mafi ɗagamin hankali shine saka idonsa a kaina fiye da kowa a gidan, wani salon iskancima da ya ɓullo dashi shine danaje gyara masa ɗaki shima zai shigo ya zauna yana kallona kamar wata tv, narasa miyake kallo tare dani, ni dai sam baza’a sakani a jerin ƙyawawa ba, dan kuwa baƙace ni, bani da dogon hanci, bani da kayan ƙawa na ado da zasu fidda ƙyauna ga kowa. Shiyyasa lamarinsa ke ban mamaki da al’ajabi.

          Babban abinda na riƙe shine addu’a, dan itace babban makamina a gareshi.

     Yauma kamar kullum na tashi da wuri saboda zanje makaranta, dukkan abinda ya dace muyi ni da firdausi munyisa, hatta da aikinta da Jazuuga ya bata nakan tayata, saboda ni nawa saiya tashi barcinsa na ƙaddara da ko sallar asubahi bana tunanin yanayi.

     Shirin makaranta nayi, na dawo ƙofar ɗakinmu na zauna tamkar yanda sauran ƴanmata gidan suka fito, wasu sunci kwalliyarsu saikace wasu matansa, sai binmu da kallon banza suke, dan a ganinsu bamukai matsayin haɗa kafaɗa dasuba.

     Sukan bani dariya da mamaki, dan inda son samunanema wlhy ni namu aikinma duk ya haɗa ya basu.

      Banfi mintuna goma da zamaba sai gashi ya fito, kamar yanda ya saba da ga shi sai gajeren wando, kallo ɗaya nai masa na duƙar da kaina.

      Shiko inajin yanda idanunsa ke yawo a jikina tamkar kullum.

     Hazbilannahu wa ni’imalwakil na shiga ambatowa a kan laɓana, kamar yanda na fahimta a duk sanda nake karantata ko kallona yake saiya kauda idonsa sai naga yanzu ma yazo ta gabana ya gitta.

      Inajin yanda su Aina ke masa gaisuwa cike da kwarkwasa da salo, tausayinsu ya kamani, dan kuwa ni nafi ɗaukarsu a jerin masu karancin tunani, da wannan takaicin na miƙe na nufi ɗakinsa, kamar yanda na saba a gaggauce na shiga gyarawa, dukda nasan bazai shigoba sai yay wanka, kafin lokacin kuma insha ALLAHU na gama nama fice abina zuwa majaranta.

         Abinda na gani a ɗakin yauma ya tayarmin da hankali, dan haka na fice jiki na rawa ko shara banyiba, saboda tsantsar tsoro da firgici dake sake tasirantuwa a gareni game da tsagerancin Jazuga.

     Ranarma dai ko’a makaranta daka ganni kasan babu nutsuwa a tare dani, haka dai aka tashi na nufo gida, ashe nabar baya da ƙura akan rashin shara da banma Jazuga ba…….😭

2

*____________________________________*

*_JAWAAD_*

*____________________________________*

              Izinin shigowa aka bashi, ya turo ƙofar ya shigo, cikin risinawa irin ta girmamawa yake faɗin, “Sir! Ƴan jaridar nanne suka sake dawowa”.

        Shiru Sir Ahmad barewa yay yana kallonsa na tsawon sakwanni, kafin ya sauke numfashi da masa alamar yaje.

     Bayan fitarsa ya maida kallonsa ga Jawaad dake kallonsu ba tare da ya fahimci komai ba.

        “Jay! Rayuwa na bani mamaki, bansan miyasa a duk lokacin da case irin wannan yazo ba  hankalin duniya yafi tashi akansa, shiyyasa talakawa har abadan bazasu daina ƙalubalantar manyan ƙasa ba komai gaskiyarsu”.

       Murmushi Jawaad yayi irin na takaici, yaɗan lumshe ido yana faɗin, “Kuskuren daga mu yake Sir”.

       “Jay miyasa kace haka?”.

       Murmushi ya sakeyi mai ciwo, “Abun a bayyane yake muma mun sani sir, mubar wannan maganar kawai bata da muhimmanci a yanzu”.

      Kai Sir Ahmad ya jinjina kawai yana cije baki, sai dai acan ƙasan ransa maganar Jawaad tai mugun sukarsa, ba komai ya sa hakanba sai sanin tsantsar gaskiyar Jawaad, amma wasu dalilai bazasu bar muryoyinsu ɗaguwa ba har suyi kururuwar da duniya zataji, ta gaskatasu cikin jerin jami’an tsaro masu gaskiya da son shinfiɗata..

     Ya sauke numfashi mai zafi yana maida hankalinsa ga Jawaad, “Jay waɗanan ƴan jaridane, tun safe suke jera mana kira domin sonjin mi’ake ciki, inaga yakamata kaje garesu”.

     “Okey Sir”

Jawaad ya faɗa yana miƙewa, gaba ɗaya fuskarsa ta canja launi, sam babu ɗigon fara’a ko sauƙi a cikinta, sai tsumamman fushi mai gauraye da takaici irin mai zafafa zuciya.

        Harya fice Sir Ahmad na binsa da kallo, yana ƙaunar yaron saboda nagartarsa, duk da mahaifinsa yay suna irin na zama wani shi sam baya alfahari da hakan, ko yaushe tunaninsa akan talaka yake, da ace yanda Jawaad keda zinariyar zuciya haka sauran jami’an tsaro suke da tuni ƙasar ta canja daga yanda take yanzu.

                Koda Jawaad ya fito sai ya samu Qaseem tare da ƴan Jarida, kallon ido cikin ido sukaima juna. Jawaad ya janye nasa yana sakin wani lallausan murmushin daya soki zuciyar Qaseem.

             Office yay wucewarsa, ransa na susa akan shirmen Qaseem, baisan miyasa sam jininsu bai haɗuba.

      Cikin kujera ya shige yana mai lumshe idanu da faɗawa duniyar dogon tunani.

       Damuwa tai masa ɗaurin gori, saboda sabgogin aiki, ga matsalar gida na halayyar matarsa da taƙi ta zama irin kowacce mace, waje zafi, gidansa ƙunci, babu uwa ko uba da zasu fuskanci matsalarsa kai tsaye balle su taimakesa koda da shawarane.

       Ina zaiga mahaifiyarsa? Shin tana raye ne kokuwa shiɗin marayane gaba ɗayansa? Wasu hawaye masu ɗumi suka gangaro a kumatunsa, bai damu daya sharesuba, haka ya barsu suna kwarara. (Haka yake dama, aduk lokacin daya tuno iyayensa yakanyi kukansa ya ƙoshi).

Ya rabbi ka gafartama iyayenmu baki ɗaya😭🙏🏻.

5

       Sai da yasha kukansa ya more sannan ya share hawayensa.

        Nutsuwa yay ta musamman domin yin nazari akan wannan case da aka damƙa a hannunsa, dolene idan yanason aikinsa ya tafi dai-dai sai ya nemo abokansa, aminansa sun dawo kusa dashi, kuma insha ALLAH zaiyi komai da kula yanda bazai ƙara bada wata ƙofa da za’a farraƙasu ba koda na a awoyine.

      Bai ɓata lokaci ba a take ya rubuta takardar neman izini tare da shawarar da yay alƙawarin badawa kamar yanda sukai da Sir Ahmad……………✍🏻

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭iyayen

ƘWAI ciki ƘAYA!!

Bilyn Abdull ce👌🏼

Shafi na tara

…………Tun ƙarfe huɗu na maraice garin ya fara haɗa gagarumin hadari, wanda alamominsa suke nuna zai zubda ruwa mai yawa.

        Duk da yana a office hakan bai hanashi fahimtar canjin da garin ke cikiba, miƙewa yay zuwa jikin window ɗin Office ɗin ya leƙa, tabbas hadarine mai ɗauke da alamomin iska kuma, ya kalli agogon dake a tsintsiyar hannunsa yana huro iska a bakinsa, yana da sauran ayyuka, gashi bayason ruwannan ya samesa a waje.

     Barin Window ɗin yayi ya koma gaban desk ɗinsa, wasu takardu ya haɗa waje ɗaya kafin ya fito da ga office da hanzarinsa irinna masu cikakkiyar lafiya.

         Kai tsaye Office ɗin Sir Ahmad ya nufa, dan tun kusan mintuna goma baya ya aiko kiransa, bai fita bane saboda wani ɗan aiki da ya sakashi yakeson ƙarasawa ya kai masa gaba ɗaya.

       Sallama yay a ƙofar Office ɗin kafin ya shiga, su uku ya iske a office ɗin, gaba ɗayansu kuma suna cikin manya-manyan ƴan sanda, gaisuwa yay irinta girmamawa a garesu, ya miƙama Sir Ahmad takardun yana faɗin, “Sir gasu na kammala, kayi haƙuri da lattin da nayi, na ƙarasa aikinne”.

     “Babu damuwa Jay, dama tunanina ya bani hakan shiyyasa ban damuba, duk da kuwa jiranka muke”.

         “Sorry Sir’s” Jawaad ya faɗa yana maida kallonsa ga sauran mutane biyun dake zaune .

         Ɗaya a cikinsu ne yay magana fuskarsa sam babu walwala, cikin tsare Jawaad da idanu yace, “Jawaad Abdul-aziz ko?”.

          Cikin girmamawa Jawaad yace, “Yes Sir!”

       Zama wancan ya gyara sosai yana fuskantar Jawaad, ya fara magana cikin dakiya da kuma tsuke fuska.

         “Jawaad kai ɗan sandane, ɗan sandanma (SAS) ƙwazonka da ƙwarewar aiki ke ƙara maka ɗaukaka ga kowa dake a cikin hukumarnan, kamar yanda muka baka yarda a baya yanzunma munason ƙara baka a kan wannan aikin, dan tabbas inaji a jikina zaka iya, saboda kanada NAGARTA irin ta jami’an tsaro na ƙwarai, bamason wannan case ɗin ya wuce sati biyu, ya kake ganin zaka iya kuwa?”.

        Jawaad dake tsaye a tsume fuska sam babu fara’a yay ajiyar zuciya yana sake tsuke fuskarsa, “Sir insha ALLAHU ina fatan hakan, sai dai bazan zama mai alƙawari akan abinda bani da ilimin sanin gaibu a kansa ba, ina dai muku albishir da koda ƙasa da kwanakin da aka banine zan iya yin hakan, alfarma ɗaya zuwa biyu nake nema a gareku, dan hakanne zai bani ƙwarin gwiwa akan nasarar da kuke fata daga gareni…”

        “Wace alfarma ce wannan?”.

      Ɗayan a cikin baƙin yay tambaya yana kallon Jawaad.

           Gyara tsaiwa Jawaad yayi yana satar kallon Sir Ahmad, Sir Ahmad da shima ke kallonsa ya jinjina masa kai alamar ya faɗa.

         Kai Jawaad yaɗan ɗaga masa, kafin ya maida hankalinsa sosai garesu yana cigaba da faɗin, “Alfarma ta farko itace inason a dawomin da abokan aikina tare dani, ina magana ne akan, Hafeez Umar, Aliyu S marwa and Jabeer Abdul-razaƙ. sai alfarma ta biyu kuma kununa ma abokan aikina cewar kun cireni da ga wannan case ɗin, a ɗora Qaseem Ali matsayin jagora, nikuma zanyi nawa aikin ne ta ƙarkashin ƙasa tare da abokan aikina ba tare da kowa yasan muna tareba”.

       Shirun da yayne ya basu damar fahimtar ya kammala magana, hakan yasa su duka suka sake zuba masa ido tamkar wani baƙonsu, kusan minti ɗaya da rabi kafin ɗaya a cikinsu ya miƙe, kafaɗar Jay ya dafa yana murmushi da fadin, “Jawaad tunaninka mai ƙyaune, kuma hakan yamin ɗari bisa ɗari, abu ɗaya nake tsoro da shakku akan dukkan bayananka”.

        Cikin izza da jin yakai jarumin na gaske ya ɗago kai yana kallon boss ɗin nasa, sai kuma ya sake wani lallausan murmushi da ya saka kumatunsa duka biyu loɓawa, “Sir! Miyasa kakejin shakku?”.

        “Gudun rashin samun nasara, ina gudun yazam ba’ai nasaraba akan tsarinka Jawaad, dan rashin nasara a aikinnan tamkar zubewar mutuncinmu ne, samun nasara kuwa kimace a garemu, sannan kowannenmu kuwa ribace a gareshi, kuɗi zasu jiƙamu, sannan zamu ƙara nagarta a idon duniya harma da shugaban ƙasa”.

       “Hummm” Jawaad ya faɗa a can ƙasan maƙoshi, kafin ya kallesu gaba ɗaya cikin takaici, “Insha ALLAHU zamuyi nasara, domin inaji a raina da NASARA AKE FARAUTO NASARORI a rayuwa, insha ALLAHU a karon farko da nake hangen samun damar farko zan sadaukar, badan komaiba sai dan farauto nasara ta gaske, abinda kawai nake buƙata a gareku goyon baya”.

     “Mun baka kuwa Jay”

Sir Ahmad ya faɗa fuska ɗauke da murmushi.

      Ƙamewa Jawaad yay tare da yin Salute nasu baki ɗaya.

         Sun bashi izinin tafiya, duk da kuwa maganarsa ta ƙarshe tai musu tsaye a zuciya, sam sun kasa fahimtar komai a kanta, domin dai hausace cikin hausa yayi.

           Da tabbaci na dawowar abokansa uku garesa a safiyar gobe ya fita, koba komai ransa yay masa daɗi idan ALLAH ya kaimu gobe iyanzu yana tare da aminansa, ƙashin bayan jarumtarsa.

          Duk bin ƙwankwantonka baka isa fuskantar yanayinsa ba, dan fuskarsa jarumar fuskace ma’abociyar adana komai, Office ya koma, cikin hanzari ya haɗa komansa.

        Yana fitowa Gimba ya ƙaraso gareshi, jikkan hannunsa ya amsa suka nufi mota.

         Kowa yasan Jawaad mutumin kirkine a hukumarsu, sannan jajirtacce akan aiki, sai dai sam baya ɗaukar wargi, yakanyi wasa da dariya da mutane idan yaso, amma kaɗan daga aikinsa ya birkice ka kasa gane kansa cikin ƙanƙanin lokaci.

         Gimba ya buɗe masa baya ya shiga, sannan ya koma ta ɗayan ɓarin ya ajiye masa jikkarsa a gefensa, mazaunin driver ya koma  yay bismillah tare da tada motar suka fice daga station ɗin.+

STORY CONTINUES BELOW

      Luff Jawaad yay kwance jikin kujera, ƙwaƙwaƙwalwarsa da zuciyarsa ne kawai ke faman aiki a lokaci ɗaya, hakan yasashi barin duniyar mutane ya koma zuwa wata duniyar ta daban.

                    Tun a shigowarsu farkon Layinsu ya buɗe idanunsa, da motar ɗaya da ga cikin kawunansa ya fara cin karo, ya tsurama motar ido tamkar yaune ya fara ganinta.

      Har aka wangale musu ƙaton gate ɗin family House ɗin suka shiga bai daina bin motar da kalloba.

           Sashin su Jawaad yana daga can ƙarshen gidan, hakan yasa saiya wuce dukkan sashin kawunansa kafin yaje nasun, umarni ya bama Gimba akan ya tsaya inda Kawu Nasiru yay fakin.

        Kusan a tare suka fito da ga motocin, fuskar kawu Nasiru washe da murmushi yana kallon ɗan ɗan uwan nasa.

       “A’a Jawaad har an taso aikin yau da wuri haka?”.

      Guntun murmushi Jawaad yay yana ɗan shafa kai, ya rissina a gabansa yana faɗin, “Eh kawu mun dawo, ina yini”.

       “Lafiya lau, Ja’iri kai dai kayi wuyar gani, muna a gida ɗaya amma sai mutum ya jera wasu kwanaki bai ganka ba”.

      “Ai min afuwa kawu, aikin namune sai addu’a, a koda yaushe mutum bashi da lokacin kansa, ni kaina inason kasancewa a cikinku a koda yaushe, amma hakan bai samuwa”.

        “ALLAH sarki karka damu, ai ka cancanci uziri ga kowa Jawaad, amma dai a rinƙa daurewa ana shigowa kaji, musamman ma tsofaffinnan kullum zancensu na gareka, a daure ana zagayasu akai-akai”.

         “Insha ALLAHU kawu zan gyara, zuwa anjima duk zan shiga na gaishe da kowa”.

      “To Alhmdllh, ka gaishe da baturiyar matar taka mai cika mana gida da kiɗa”.

       Murmushin kan laɓɓa kawai Jawaad yay yana miƙewa, ya buɗe mota da kansa ya shiga, Har gaban sashensu Gimba ya tsaya da motar, yazo da sauri ya buɗema Jawaad motar ya fito.

       Sai da ya rakashi da jakarsa har gaban ƙofar falonsu sannan Jawaad ya amsa yana ɗaga masa hannu ya shige.

             Idanunsa ya rumtse da ƙarfi saboda su Shahudah dake baje a falo ita da ƴammatan gidan, ga mahaukacin kiɗa na tashi a sifiku, wasu na rawa wasu na zaune wasu kuma a kwance cikin kujera.

      Sam babu wanda a cikinsu yaji sallamarsa balle motsin buɗe ƙofa.

         Taku yake a hankali har gaban kayan kiɗan yasa hannu ya kashe, tsitt falon yayi.

          Gaba ɗayansu a firgice suka maido kallonsu gareshi, kafin kace mi an fara ƴar reran gudu ta ƙofar kichin, wasu kuma ta ƙofar falon.

         Shahudah da ke kwance ta ɓata fuska tana masa kallon takaici.

       Koda suka gama fita baice mata uffanba, kallo ɗaya yay mata yay hayewarsa sama inda zai iske ɗakinsa.

           Tundaga hawowarsa step ɗin farko ya fahimci Batool ko Nabeelah wani yazo yay gyara, hakan saiya ɗan rage masa fusatar da yayi.

      Ɗakin barcinsa ya zarce kai tsaye, yana shiga ya maida ƙofar ya rufe tare da murza key dan karma Shahudah ta shigo.

     Ɗakin yay ƙal saboda gyaran da ya samu, sai ƙamshi mai daɗi ke tashi ga iskar hadari da ke bada ƙamshin ƙasa.

        Tamkar jira ake ya zauna ruwa ya fara sauka a hankali.

          Yana zaune a bakin gado yana zame takalminsa yakejin bugun ƙofar da Shahudah ke masa, baiko kalli ƙofarba balle tasamu darajar kulawa yay shigewarsa bayi bayan ya cire komai na jikinsa, sai ƙaramin wando da ya bari.

           Gaba ɗaya yarasa wane irin mataki ya dace ya ɗauka akan Shahudah ne ta dawo hankalinta, shi yama fara tunanin ko bata da isashshen hankaline, dan sam baiga abubuwan masu hankali tattare da ɗabi’unta ba, ko ada can yasan bata da kirrki sam, amma zaman watanni bakwai da sukai a tare ya sake fahimtar dashi sanin da yay mata a baya ƙaramine ashe.

         Rai a ɓace yay wankan harya gama ya fito, baiji motsinta ba, hakan yasashi gane tayi fushi, ya taɓe baki irin na rashin damuwa da hakan.

       Zuwa yanzu ruwa ake zugawa sosai, hakan yasa yay sallarsa ta magriba a ɗaki, bayan ya idar mai makon ya zauna tunani sai ya ɗauki Qur’an ya hau karatu cikin nutsatstsuyar muryarsa.

     Bai matsa a gunba har sai da aka kira isha’i, har sannan kuma ruwan saman ake zugawa.

       Wayarsa dake ring tun yana salla ya ɗauka, ganin Umma Bara’atu ce sai yay murmushi (Umma Bara’atu ƙanwar mahaifiyar Jawaad ce, karku manta a labarinsa ya nuna mana tana da ƙanne har uku duk mata).

       Cikin girmamawa ya gaisheta, da ga can ta amsa masa cike da kulawa.

        Bayan sun gama gaisuwarsu take tambayarsa koya ga abinci?.

       Murmushi mai sauti yayi, wanda har tana jiyosa, ya kwanta rigingine a gadon ƙafafunsa na ƙasa, “Yanzu nan Umma bazaki daina walar da kanki wajen aikomin abinciba kamar wani ɗan primary ”.

      Dariya tayi daga can, cike da son tsokanarsa tace, “Yo miye banbancinka dasu Jawaad, ni a gurina ai tamkar tata kake, bama ni na aiko da abincinba, ƴar uwarka ce tayisa shine tabama Nabeelah da taga zatazo tace ta kawo maka, sai kuma Nabeelar ta iske bama ka gidan ka fice”.

          “Ayya, ALLAH sarki Sister, na gode mata kuwa, ALLAH ya bata miji na gari wanda zai kulamin da ita, wlhy kiran gaggawa na samu da ga Office Umma shiyyasa na fice bata iskeniba”.

        “Aini wannan aikin naka dan banda yanda zanyine, amma da ga ni har Auta da Amina bama sonsa sam, sai dai muna maka fatan alkairi a cikin, tunda kullum baba shi baya ganin laifinka”.

      Guntun dariya Jawaad yayi, da gani kasan hirar ta sakashi nishaɗi, dan a ransa ji yake tamkar yana magana ne da mahaifiyarsa, “Karku damu Umma’s ɗina, addu’arku ita nafi buƙata, harma kinsa na tuna da Tsoho, insha ALLAH da safe asubanci zan masa naje shan saurar furarsa”.

          “Ja’iri, zaka fara ko? To sai anjima”.

      Sosai Jawaad ya ƙyalƙyace da dariya, ya shiga faɗin, “Haba Ummana karmuyi haka dake, tsaya kiji……”

      Ƙitt ta yanke wayar da ga can itama tana ƙyalƙyata dariya.

        

       Sumbatar wayar Jawaad yay a hankali yana kuma faɗaɗa murmushin fuskarsa dajin ƙarin ƙaunar ƙannen mahaifiyar tasa, masu ƙoƙarin share kukansa a koda yaushe.

2

_______________________

BILKEESU

________________________

        Naji daɗin shigowa gida na iske su Jazuga basa nan, ɗakinsa a rufe.

     Firdausi kawai na iske a ɗakinmu, Inna ta fita maƙwafta yin barkar haihuwa.

        Tagumin da Firdausi tayine na janye, ta ɗago a firgice tana kallona, ganin nice sai ta sauke sassanyar ajiyar zuciya.

      Murmushi nayi ina faɗin, “Matsoraciya kin zata waye da?”.

          “Ƴan ta’addan gidanmu mana, wlhy wannan rayuwar ta fara gundirata Bilkisu, nifa yanzu ko shakkar banzan nan banayi balle tsoro, dan nakula ibilis ne kawai ya rikiɗa a mutum ya shigo mana gida”.

      Ido na zaro waje ina waige-waige, a tsorace nake magana ƙasa-ƙasa, “Firdausi bar irin maganarnan dan ALLAH kar wani yaji”.

           Baki ta taɓe tana miƙewa tsaye, “Ai kunji tsiyar, wannan tsoron naku shike ƙara masa karsashi da jin ya isa, wlhy inhar a haka za’a cigaba da tafiya to lallai akwai babbar matsala, dan kuwa sai kunkoma bayinsa tamkar a ƙarnin farko”.

        Tsayawa nai kawai ina kallonta, dan na fahimci ranta a ɓace yake, hakan yasa nai shiru, sam banason zancen yay tsawon da har wani zaiji, duk da Jazuga baya nan za’a iya samun wani ɗan neman gindin zaman a gidan namu ya sanar masa.

         Itama jin nayi shiru sai taja tsaki ta fice ta barmin ɗakin, murmushi kawai nayi ina girgiza kaina, na cire kayana sannan na ɗauki abincinmu da nasan Firdausi bata ciba tana jirana na fita, nasan bazata wuce tana soro ba zaune.

          Ilai kuwa acan na isketa, dan haka na zauna kusa da ita ina ajiye kwanon tasar abincin a gabanta.

      Cikin sigar lallashi nake faɗin, “Haba dai tawan, wai fushi kikayi? To kiyi haƙuri kinji, taho muci abinci, dan da gaske da yunwa na dawo mai katse ƴan hanjin ciki”.

         Hararata tayi tana ƙokarin matse dariyar dake neman kufce mata, (haka muke sam bamu iya dogon fushi da juna).

          Munacin abinci muna ƴar hira jefi-jefi, sai ƙokarin kauda firar da Firdausi ke ɗakkowa ta Jazuga nakeyi gudun kar’a samu matsala, a haka har muka gama na sake ɗaukar kwanon abincin na maida cikin gida.1

           ★★★★★★★

    Kwanaki huɗu kenan cif Jazuga baya gidan, da alama dai yayi nisan kiwo, kallo ɗaya zakaima gidanmu ka fahimci akuyoyin ɗaure sun samu sake, dan harmun fara sakin jikinmu muna rayuwarmu tamkar ta baya.

          Sai dai kash a ranar cikon ta biyar murna ta koma ciki, ɓeraye suka koma wasan ɓuya da kuliya🤣, dan kuwa da yammaci kwatsam saiga Jazuga da zugarsa sun dawo, tsit kakejin gidan ya koma tamkar mala’ikan mutuwa ya shigo.

          A ƙofar shigowa soro ya tsaya, sai da ya karema gidan kallon kamar yau ya fara shigowa, sannan ya tako zuwa ciki, tafiya yake kamar zai tsinke saboda rashin ƙiba

         Dan sam Jazuga bashi da jiki, gaba ɗaya wiwi ta gama kalace dukkan wata tsokar jikinsa sai ƙashi data bar masa da fata

           Amma a hakan akejin tsoronsa tamkar mutuwa, ga jiki duk yabi ya zane da tatu, daka gansa kaga ainahin hatsabibi mai matuƙar haɗari da rashin imani, dan tsaf zai iya tsarwatsa kwalwar kanka da bindiga ba tare da ya damu ba……

ƘWAI cikin ƘAYA!!

Bilyn Abdull ce

shafi na goma

………..Wani siririn fito ya saki yana mai kallon kowacce kusurwa ta gidan.
      Hakanne ya saka yaransa fahimtar jama’ar gidan ya kema kiranye.
     Mai-tawaga, babban yaronsa ne yay magana cikin muryarsa mai kama da ƙattan farkon ƙarni, ga amo gata a matuƙar buɗe.
      Kafin kace mi jama’ar gidanmu sun fara yo waje da gudu-gudu.
        Muma dai ayari mukabi, duk da Firdausi taso yin tirjiyar ƙin zuwa, sai da inna tai mata magana sannan ta biyo bayanmu dan dole.
          Kowa tsaye yay a ƙofar ɗakinsa yana jiran ƙarin bayani, abunda zaisa kaji tausayinmu kuwa hatta da mazan gidan sun koma mata maza, dan kuwa suma sunzo sun jeru a cikinmu, bayan kuma mafi yawansu sun girmi Jazugan, harma da waɗanda zasu iya haihuwarsa.+

          Har yanzu yana a bakin ƙofar tsaye, yana jingine a jikin bango dukkan hannayensa na cikin aljihun wando three queater ɗinsa a zube, rigace armless mai zanen tutar ƙasar Amurika a jikinsa, hakanne yasaka bayyanar ƙaton bandejin da aka naɗe damtsen hannunsa dashi, tabbacin yaji ciwo a wajen kenan.
       Jajayen idanunsa ya ɗago yana kallonmu, sai kuma ya fara takowa yana wani rausayar layi irinta marasajin maganar gayu, fito ya fara rairawa yana cigaba da tinkaromu.
           A gabana yazo ya tsaya cak.
     Wata irin bugawa zuciyata tayi, tare da yin zallo tamkar zata fito, nai wuƙi-wuƙi da idanu kamar an tsamo zomo daga ruwa, addu’ar da nake ƙoƙarin haɗowa a harshena sam ta kasa haɗuwa……
         hijjab ɗin dake jikina ya cikuykuye ya maidashi iya wuyana, yakamashi a hannu tamkar zai shaƙeni ya jani zuwa tsakkiyar gidan yana cigaba da fitonsa, Saikace wanda ya sayo akuya a kasuwa.
     Duk da bansan warin giyaba inada tabbacin warinta ke tashi a jikinsa.
      Yanda jikina ke rawa ina hawaye da ƙoƙarin bashi hakurine ya sashi kallona cikin razanarwa, ya ɗora yatsansa saman bakinsa yana faɗin “Shiiiiii”.
       Duk da hawayen basu bar kwaranya ba dole haka na gumtse bakina kuwa.
     Ƴan gidanmu duk sun tsorata, innar Firdausi kam ta kasa kallonmu, saima naga kamar kuka takeyi.
           Ya gyara tsayuwarsa mai kama da zai ɓalle biyu yana dakama jama’ar gidan tsawa.
       “Kowa ya ɗago ya kalleni, dolene yau na nuna muku real jazuuli, ina son ku ɗauki darasi akan wannan mara kunyar yarinyar, yanzu ni har nakai matsayin da zan saka wani aiki a duniyarnan yaƙi min? Wato ɗaga ƙafar da nake mukune har take bama wasu lasisin bijiremin ma……..”
       “Kai wanenen da baza’a bijire makaba, wawa kawai sauran giya da wiwi, mikake takama dashine shin? Da har kake tunanin sai an bika dole? Ko ka ɗauka tsoronka akeji….”
     Firdausi ce a matuƙar hasale take wannan maganar tana nuna Jazuuga, takowa tai inda muke ta fisge hannun Jazuga daga hijjab ɗina a rikice..
     Gaba ɗaya jama’ar dake wajen babu wanda bai zaro idanun mamaki ba, sai dai saukar ƙarar marin da ɗaya daga cikin yaran Jazuga suka saukema Firdausi ya kuma sakamu sake firgicewa.
        Gaba ɗayansu sukai ribdugu akanta suka hau duka.
    Hakan ya sakani fashewa da kuka ni da inna mukayo kansu, amma ni sai Jazuga ya fisgi hannuna ya nufi ɗakinsa dani.
    Kuka nake ina tirjewa, shima yana jana a matuƙar fusace.
       Ai sai gidan ya kuma ruɗewa da koke-koke.1

          Inaji ina gani ya kaini ɗakinsa, babu ko tausayi ya hankaɗani kan gadonsa, ihu na shiga kwarawa iya ƙarfina, amma babu mai ceto.
    Inaji ina gani jazuga ya fara ƙoƙarin shiga mutuncina, UBANGIJI sam bai kasance azzalumin sarkiba, hakanne yasaka kawo wani haske a rayuwata, dan kuwa ina lalubawa sai ga ƙarfen da bansan kona mineneba, jawosa kawai nayi na maka masa akansa.
      Wata razanannniyar ƙara mai firgitarwa ya saki, kafin yay luuu zuwa gefe, jini kuwa tuni ya ɓalle har a jikina.2

      Ihun Jazuga ya saka yaransa barin dukan Firdausi data gama fita hayyacinta sukayo cikin ɗakin.
         Su duka kansa sukai suna kiran sunansa, da wannan damar nai amfani wajen fitowa da ga ɗakin da gudu, dukkan illahirin jikina rawa yakeyi, dan kuwa nasan tabbas na kasheshi.
         Ban saurari dukkan masu min magana ba cikin ƴan gidanmu, dan kuwa hannuna da gaban ƙirjina duk jinine, nasan mafita ɗaya ta ragemin shine nabar gidan. Hakan yasa na zaɓi ficewa ba tare da nasan ina na dosaba.

STORY CONTINUES BELOW

         Fahimtar Jazuga baya numfashi ya saka wasu a cikin yaransa biyo bayana suma a guje, ganin hakanne ya saka ƴan gidanmu suma fara guduwa zuwa wajen.
         Atake anguwa ta ruɗe, wasu gudu kawai suke amma basusan akanmi bane, wasu kuma azatonsu bomb ne ma.
    Ruɗewar da anguwarmu tayi baki ɗayane ta bani damar samun wajen ɓuya, dan kuwa wuuff nayi a cikin massalaci, nashige cikin mankarar dake jingine a bango taimin katanga.
     Dukkan ihu da anguwar ta ɗauka inajinsa, harma da ƙarar guje-guje, taimakon da ALLAH yaymin babu wanda ya shigo massalacin, dama kuma ban iske kowa a cikiba.
          Kusan mintuna talatin anguwar bata lafa ba, saima ƙarar jiniyar motar ƴan sanda danaji, ƙara tsurewa nayi da tsoro, nasan dai ni akazo kamawa ba waniba, kuka nake sosai, hannuna dafe da bakina, na jiƙe sharkaf da zufa har diga nake, duk mai imani ya ganni a wannan halin dolene hankalinsa ya tashi.
    Nai wujiga-wujiga na fita hankalina gaba ɗaya.

       
      Ɓangaren su Jazuga kuwa dai a tare dashi babu rai babu alamarsa, yaransa da sukabi Bilkisu tare da saka ƴan anguwa gudun dolene ya ankarar da ƴan sanda, hakanne ya sakasu zuwa dan suga mike faruwa.
       Har cikin gidan ƴan sandan suka shiga, kowa ya fice a gidan, innar Firdausi ce kawai tsigunne gaban Firdausi dake kwance itama babu rai a tsakar gidan, sai yaran Jazuga guda uku da keta kai kawo a kansa shima, harma sun fito dashi waje da nufin kaisa asibiti saboda jinin dake malala a kansa.
         Zuwan ƴan sanda yay dai-dai da zuwan Alhaji Lado naira, hankalinsa tashe ya hankaɗe ɗan sandan gabansa ya nufi wajen ɗansa yana ƙwala kiran sunansa.
      Atake nanma gidan ya kuma ruɗewa, dan mutane sunɗan fara shiga hankalinsu suna shigowa gidan suga mike faruwa.
          Bayan bayani da ɗaya acikin yaran jazuga ya shirya na ƙarya, da kuɗin da alhaji lado ya ɗebo a aljihu ya bama ƴan-sandan yasasu jiki na rawa suka kira Office ɗinsu, tare da shirya nasu tsarin akan Bilkisu ce tai kisan duk ita kaɗai, saboda Jazuga saurayintane, tazo ta gansa da ƙawarta Firdausi shine tayi yunƙurin kashesu ta hanyar kawo ƴan daba suka doki Firdausi, itakuma ta ƙwalama Jazuga abu a kai.
           Innar Firdausi dake kuka tana faɗin ƙaryane ƴan sandan suka kaimata duka, ɗaya a cikinsu yace a fiddata daga gidan kafin manyamsu suzo.
     Hakan kuwa akayi, dan an kulle innar Firdausi a ɗaki bayan an ɗaure bakinta.
    Koda ƴan sandan sukazo akan bayanin ƙaryar suka zauna, dan basusan minene gaskiyarba, an ɗauki Jazuga da Firdausi zuwa asibiti, bayan ƴan sanda sun rufe gidan saboda bincike, sannan wasu aka bazasu neman Bilkisu a anguwar tako ina.
1
😭innalillahi wa’inna ilaihirraji’un🤦🏻‍♀️.
_____________________
JAWAAD
_____________________
            Wani barcine mai daɗi ya sacesa take a wajen, gashi har lokacin ruwa ake zabgawa.
      Kamar kullum dai yauma dai mafarkinsa akan mahaifiyarsa yake, hakanne ya sakashi farkawa a firgice, sai da ya karanto addu’a kafin ya miƙe zaune sosai hannunsa dafe da kansa.
     Barcin nasama bawani nisa yayba, dan bai wuce mintuna ashirinba.
     Dukda abinda ke nuƙurƙusar ransa bai barsa yay tasiriba tamkar yanda ya saba, miƙewa yay yanata sauke ajiyar zuciya a jere-jare, falonsa ya fito, inda ya hango kulolin abinci saman D/table, takawa yay ahankali zuwa garesu, dan ɗan barcin saiya saukar masa da kasala, ga kuma sanyin ruwa da garin ya ɗauka.
       Kulolin yabi ɗai-ɗai yana buɗewa, yay ɗan guntun murmushi a kasalance, dan kuwa abincin da yafi sone a rayuwarsa, wato Masa, tayi ƙyau suɓu-suɓu, ga miyar taushe mai tsafta da tasamu ingantacciyar dahuwa.
         Sauka yay ƙasa inda ya ɗakko filet dama duk abinda zai buƙata ya dawo.
       Yana zama a kujerar dani ɗin Shahudah na fitowa daga ɗakinta saboda motsinsa da taji.
      Duk da yasan itace sai yay biris ya cigaba da hidimar zuba masar sa,
       Fuskarta da alamar damuwa taja kujera ta zauna kusa dashi gab, ta ɗora kanta jikin damtsen hannunsa ta kwantar tana lumshe idanu, tare da maƙalesa da hannayenta duka.
     Nanma bai motsaba, bai kuma kalleta ba, saima laumar masa da ya fara kaiwa bakinsa cikin zaƙuwa.
       Taunawa yakeyi a hankali yana wani luuu-luuu da idanu, ɗari bisa ɗari daɗinta yakai a yabama mai hidimar girkata.
      Shahudah ta ɗago kanta tana kallonsa da mamaki, sai faman ƙyaɓe baki take tana wani yamutse fuska saikace taga kashi, itafa sosai kyankyamin abincin gargajiyar nan takeyi lokuta da dama, ji wata irin miya dan ALLAH……
          “Wai dan ALLAH bb baka tsoron irin waɗanan abincin su sakaka yin nauyi da yawa?”.
      Banza yay mata kamar baijiba.
    Ta daki damtsen hannunsa kaɗan tana buga ƙafafu da turo baki cikin shagwaɓa.
      “Kai kaji tsiyarka riƙon masifa, ba nazo na baka haƙuri ba amma dan wula ƙanci ka kulle ƙofarka dan karna shigo”.
     Nanma ɗin banza yay mata.
     Tagumi tayi hannu biyu ta zuba masa idanu tana hawaye.
        Yi yay tamkar baisan tanaiba, yaci abincinsa yay nak, hannunsa ya wanke cikin ruwan daya ajiye, ya ciri tissue yana goge bakinsa da hannunsa. Duk dai Shahudah na kallonsa tana cigaba da kukanta.
      Miƙewa yay zai bar wajen ta miƙe itama a zafafe, sai ta faɗa bayansa ta zagayo hannayenta a cikinsa ta sakar masa kuka mai sauti.
            Cak ya tsaya bai motsaba, kusan mintuna biyu suna a haka, idonsa a lumshe yana sauraren sautin kukanta da saukar hawayenta a gadon bayansa.
      Hannu yasa ya cire nata dake akan cikinsa, ya tureta daga jikinsa yay gaba zai bar waje.
        Kuma kamo hannunsa tai da sauri tana fadin, “Haba bb, miyasa kakeson wulaƙantani ne? Kodan kaga inasonka da yawa haka? Nasan bakason a tara maka mutane a gida, amma nima ka dubi uzirina mana, kaji tausayin kaɗaicin da nake zama a ciki, ka hanani fita, dukda nasan ƴancinane na fita inda nakeso a lokacin da nakeso, amma nai haƙuri saboda kayi farin ciki, ya ka ke so na rayu dan ALLAH? ban saba da wannan rayuwar takuba, rayuwar ƴanci na taso a cik…….”
      Yanda ya juyo a zafafe ne ya saka bakin Shahudah rufewa akan dole.
      A tsawace tare da matsota kamar zai hadiyeta yace, “Ƴanci ko jahilci? Hudah ke wace irin daƙiƙiyace ne wai? Miyasa fitilar ƙwaƙwalwarki bata haska miki hanyar da zaki sanya ƙafa? Wlhy nayi nadamar aurenki, nadama irin wacce bama zan yafema kainaba, wawuya kawai mai koyi da toshewar basirar jahilai”.
           Shahudah dake tsaye tamkar wata gunki ta bisa da kallo harya shige ɗakinsa, duk da bagama fahimtar kalaman nasa tayiba sun girgizata, dan ita hausarma bakomai take ganewa a cikiba saboda ba yimusi akeba, ɗan dawowar tasun nanmane take ƙara fahimtar wasu abubuwan🤦🏻‍♀️(kaga turawa😆😝 ).
         Hawayen da suka sakko mata a farar fatarta ta goge, duk da kayan dake jikinta basu dace wani ya ganta da suba, haka ta fice daga sashen nasu, ga yayyafi har yanzu anayi ƙaɗan-kaɗan.
        Da gudu ta isa sashen tsohuwa Mama atika, (wato kakarta data haifi mamanta).
1
                 Zuciyar Jawaad a wuya take sosai, gaba ɗaya Shahudah ta sake ruguza masa dukkan farincikin da Ummansa ta bashi tare da ƴar uwarsa Batool.
       Haka yay shirin barci yanata sauke ajiyar zuciya, yanayin shafa’i da wutiri ya haye gado yay kwanciyarsa.
      Amma sai barcin yaƙi zuwa sam, haka yayta tunane-tunane har kusan ƙarfe uku, kafin barci ɓarawo ya sacesa.
        ★★★★★★

          Da safe haka ya tashi babu walwala, yana dawowa sallar asuba yay shiri ya fita wajen aiki batare da ya yarda kowa daga jama’ar gidan ya fito ya sameshi ba.

              Koda suka iso gimba ya buɗe masa motar ya fito.
       Da Qaseem ya fara cin karo, ya tara zaratan matasan ƴan sanda yana musu magana, da alama dai ya haɗa rundunane.
        Wani mugun murmushi yayma Jawaad yana kanne masa ido ɗaya.
    Waishi a haukarsa ai ya karɓi damar da Jawaad ɗin ke takama da ita.
         Shima Jawaad ɗin murmushi yay masa, tare da sumbatar yatsun hannunsa biyu ya nunama Qaseem alamar saƙo.
      Saikuma abin ya soki zuciyar Qaseem, tuni fara’ar fuskarsa ta bace ya koma bin bayan Jawaad da wani mugun kallo.
      Baima san yanayiba, dan tuni Jawaad yama shige sashen da zai kaisa Office ɗinsa.
       Yana zama da saƙo yafara cin karo.
    Zumbur ya miƙe ya fice tamkar zai tashi sama dan rawar jiki.
            A ƙofar Office ɗinsa yaci karo da Qaseem Ali, kallon mamaki Jawaad ke binsa dashi, amma baice komaiba.
     Qaseem yay wata dariya yana watsa hannaye gefe,
     “Yaya dai gwarzon ma’aikaci, yaya kaga wasan nawa? Ka shiga ruɗani ko? Aikin da kake takamar dashi an amshe cikin lokaci ƙankani an bani, nine zan jagorancesa yanzu, dama iyakar izzar taka kenan?”.
             Murmushi Jawaad yayi cikin ƙokarin katse Qaseem, buso iska yay daga bakinsa yana takowa cikin tsantsar takama da izzar jarumta irinta zaratan matasan da jini ke yawo ta kowace kafar jikinsu zuwa gaban Qaseem ɗin, ya dafa kafaɗarsa da hannu,
          “Na yarda kayi nasara my dear, ni kuma na faɗi, sai dai ina baka shawara akan ka kula kafin wani ya kula da kai, sannan ba’a cika baki da nasara kafin a nemota, nasara anan take Qaseem, (ya faɗa yana nuna saitin zuciyar Qaseem da ɗanyatsa), ina baka girma dalilin kaiɗin yayan matatane kuma ɗan uwana, sannan ogana a wajen aiki, karka bari zuciyata ta fara ƙoƙarin yin fito na fito da kai ko maida murtani. Nabarka lafiya, tare da fatan nasara jarumin ma’aikaci”.
      Ya ƙare maganar da salute ɗinsa, tare da zagayesa ya wuce.

            Harya shiga mota suka fice daga station ɗin Qaseem na tsaye kamar bishiyar giginya, zuciyarsa na tafarfasa da ƙuna, tare dajin tsanar Jawaad mai tananin gaske………………✍🏻

https://www.youtube.com/channel/UCl9IGLUXrqUtta-Tjmhoo7Q4

         *MANHA HAUSA NOVEL’S* takuce, maza garzaya domin bada gudunmawarka, danna Subscribing domin nuna ƙaunarka garemu🤩, kuyi  shiri na musamman domin samun daɗaɗan shirye-shiryenmu tare da nagartattun labaran novel’s masu daɗi da ma’ana nan da lokaci ƙanƙani, MANHA HAUSA NOVEL’S ta shirya tsaf domin baku farin ciki insha ALLAHU, ku garzaya kada ƙuda ya rigaku😂, Bilynku ma har taje tayi subscribing tun farar safiya, goyon bayanku shine ƙwarin gwiwarmu🥰🥰😉🤩.

MANHA HAUSA NOVEL’S
       (Ƙyautar ALLAH).

Ku isa da hanzari domin samun ƙyautar kuma, dan ALLAH a danna subscribing🙏🏻.

         Ga link ɗinnan a sama

ALLAH ka gafartama iyayenmu.😭🙏🏻3

ƘWAI cikin ƘAYA!!

Bilyn abdull ce👌🏼
Shafi na goma sha ɗaya

………….Mama Atika tsohuwa mai ran ƙarfe dake zaune a falonta tana jan cazbaha ta ɗago tana kallon Shahudah data shigo a guje kamar an korota, ga jikinta harya fara jiƙewa da yayyafin da har yanzu akeyi, sai da ta ƙarema guntun wandon jikin Shahudah da bai gama zuwa koda rabin cinyartaba kallo da riga mara hannu, wadda inda zata ɗaga hannu sai anga cibiyarta.
Janye idanunta tayi daga barin kallonta sannan ta girgiza kanta.
Ƙarasowa Shahudah tayi ta zauna a jikinta tana kumbura fuska ga hawaye na kwarara.
Mama Atika ta shafa addu’a tare da maida hankalinta ga Shahudah.
“Kekuwa Sabirah miya jamiki fitowa a haka cikin wannan ruwan? Ko ɗankwali ma babu fa a kanki, baza dai kibar wannan shigar ta bayyana jikinki ba ko?”.
“Ni ki daina cemin Sabirah, idan bazakice Shahudah ba basai kin kira sunanaba, Wlhy hajiya nagaji da abinda Jawaad kemin a gidansa, ni gaskiya ku kirasa kuyi masa faɗa”.
Mama Atika tace, “Hummm, yauma tsiyar kuka sakeyi kenan? Waishi wannan yaron wane irine? Ni abindama ke ƙaramin takaici dashi kokin kawo ƙarar tasa an kirasa sai yace shi baki masa komaiba, narasa irin wannan rikitaccen zama naku”.
Kuma fashewa da kukan shagwaɓa Shahudah tayi, sai kuma lafewa jikin tsohuwar takeyi.
“K yanzu yasan kin fitone?”.
Mama Atika ta tambayi Shahudah.
“Ni ban sani masaba, dan fitowata kawai nayi bayan yamin wulaƙancin”.
“Hummm, to shikenan, yanzu tashi ki koma, da safen zansa iyayenku su nemeku”.
“Ni dai anan zan kwana, dan inason ya gane kuransa yau”..
Murmushi irin na girma mama Atika tayi tana gyara zama, “Shikenan, tashi kije ki sauya waɗanan shiɗanun kayan ki kwanta muga idan zai biyoki, idan bai zoba ai iyayenki zasuzo gaisheni da Asuba zan sakasu kiransa ayi zama yau, dan bazan yarda da irin wannan halin na wulaƙanciba, sai dai yasan mai yuwuwa”.
Jin hakan da Shahudah tayi saiya sake kai kanta sama, ta shige bedroom din ƴar tsohuwar da aka narkama dukiya ta kwanta abunta.+

Tun mama Atika na zuba idon ganin ko Jawaad zai shigo a daren harta fidda, dan har tagama cin abinci da duk abinda ta saba yi kafin ta kwanta, har lokacin kuma babu Jawaad babu labarin.

Da safema koda suka tashi bai zoban, harta gaƙaraci mitarta akan Shahudah da bata tashi tai sallaba tai shiru, sai kuma ta koma kan Jawaad.
Da mitar Jawaad ɗin a bakinta su baba Usman suka shigo suka sameta, bayan sun gaisheta take sanarmusu komai.
A take suka aika a kira musu Jawaad, amma sai akai rashin sa’a aka iske ya wuce aiki abinsa.
Takaicin hakan ya hanasu motsi har saida suka fara jiyo kakarin aman Shahudah daga bedroom ɗin Mama Atika.
Itace ta shiga ta isketa duƙe tanata amai cikin banɗaki, mamaki ya kamata, amma saita ajiye mamakin ta taimaketa harta gama sannan ta bata ruwa ta wanke bakinta suka fito.
Sannu taketa jera mata da tambayarta komi taci haka daga tashinta?.
A galabaice Shahudah ke faɗin, “Ni banci komaiba Hajiya, dan rabona da cin wani abu tunma jiya da yamma, bansan miyasaba kwana ukunnan kullum da amai nake farkawa da safe, narasa mike damuna”.
Tsiramata ido mama Atika tayi ba tare da ta iya cewa komaiba, tsawon wasu sakanni tana a kanta tana nazarinta, sai kuma ta fice daga ɗakin a hanzarce tare da wani irin ɗoki akan fuskarta.
Shahudah kam kanta ta maida ta kwantar barci ya kuma kwasheta.

Albishir ɗin da tsohuwa takaima ƴaƴan nata ne ya sakasu miƙewa zumbur a wani irin razane.
Kowa na ambaton mama da gaske?.
Dariyar jin daɗi tayi tana zama, “Ƴaƴannan mizaisa na muku ƙarya nikuwa, sam bakwa bina bashin rantsuwa akan wannan maganar haka take. Amma danku tabbatar a kira likita ya gwadata yanzunnan”.
Duk da sun yarda da batun mahaifiyar tasu haka suka nemo Doctor domin sake tabbatarwa a aikace.
Jikin Shahudah rijib da zazzaɓi zuwa yanzun, haka dole Mama Atika ta tasheta, tambayoyi likitan yaymata tare da bata tsinken gwaji saboda ba’a buƙatar jan lokaci.
Gwajin farko ya tabbatar akwai ciki, tuni falon ya ruɗe da wani irin murna, kowa fuskarsa a washe saɓanin ta Shahudah dake a rikice.
Ciki kuma? A wannan shekarun natane zatayi ciki? Kai da sakal wai anbama mai kaza kai, sam babu tsarin ɗaukar ciki a gareta a nan kusa, yaushema sukai auren da har tagama morarsa da za’ai batun ciki a jikinta, so ake ta ragwagwgwaɓe da wurima kenan tamkar wata matar Afirika, ina wannan shirmen bamai yuwuwa bane, dolene Jawaad yazo asan abinyi, dan bazata haifi wannan cikinba koda za’a tada yaƙin duniya na ukune.
STORY CONTINUES BELOW

😱😱hummm ashe akwai kallo, dan inba’a tada yakin duniya na uku ba to lallai Shahudah za’a tada na ƙarshe akanki🤣🤣, yanda naga cikin yazama burin mutane da yawa aiko yagalgalaki zasuyi harma da Fans din ƙwai cikin ƙaya😆😂.
★★★★★★★★

Ya isa ƙofar kurkukun (Jail) da abokansa uku kuma aminansa suka tsinci kansu a ciki dalilin ƙaddara, dan kuwa shekarunsu na biyu kenan a wajen bisa sharri da akai musu dan a durƙusar da Jawaad ɗin, yayi iya bakin ƙokarinsa a lokacin ganin sun kuɓuta amma sai hakan ya gagara, dankuwa ƙulline mai cike da ruɗani a ka ƙulla dan kawai a dakusheshi tunda ansan abokansa suna cikin manyan abinda ke ƙara masa ƙwazo da ƙarfin gwiwa, duk yanda yaso gano wanda ya aikata masa hakan kuma bai samu nasaraba, shiyyasa ya tattara komai ya maida hannun ALLAH, sai gashi a yanzu cikin sauƙi ALLAH ya kuɓtar dasu.
Shigarsa wajen ta saka ma’aikatan gidan yarin bashi girma na musamman, dan sunsan wanene shi da matsayinsa, tunda dama jail ɗin bana kowa da kowa bane, jami’an tsaro masu laifi kawai ake sakawa a ciki.
Bayan shigarsa Office ɗin shugaban wajen na wasu mintuna aka kammala komai, yana nan zaune aka fito dasu.
Idanu suka tsurama juna da ga shi harsu, tuni idonsa ya kaɗa yay jazur tamkar an hura barkono, jijiyoyin kansa sunyi wani irin fitowa ruɗu-ruɗu, ya miƙe ahankali yana tunkararsu tamkar yanda shima suke nufoshi cikin wani irin yanayi na kewa da farinciki, dan shekaru biyun da suka ɗauka a rufe sam an hana Jay ganinsu.
Rungume juna sukai su huɗu, dukda yanda jikinsu yake baiji ƙyamarsuba, kowanne hawaye masu raɗaɗi suna kwarara a idanunsa.
Su dai ma’aikatan wajen kallonsu kawai sukeyi.
Kusan mintuna uku suna a haka, kafin su ɗago kowanne yana ƙokarin sharema ɗan uwansa hawayensa, sai kuma suka sake rungume juna suna dariya saikace wasu zararru.
Nanma kusan sakwan arba’in suka ɗauka kafin suyi haramar fitowa ba tare da ko bakin ɗayansu ya saɓa ba wajen furtama juna magana.
Gimba dake jikin mota tsaye ya hangosu suna fitowa daga cikin Jail ɗin a yanayin da yasansu a baya, jarumai kuma aminai, sannan ƴan uwan juna masu ɗaukar kansu JINI ƊAYA.
Cike da wani irin ɗoki yake washe musu baki har kunne, lallai yau farin cikin boss ɗinsa sun dawo, yanzu sauyi zai sake zuwa a hukumarsu, hannunsa ya dunƙule waje ɗaya yana cigaba da washe bakinsa, yama kasa magana saboda tsabar farinciki.
Suka dafashi a kusan tare suna dariya suma.
Da ƙyar ya iya furta, “ALLAH mun gode maka, yau ga basawan boss sun dawo gareshi, tarkon da makiya suka kafa ya buɗe”.
Jawaad da fuskarsa babu walwala ya girgiza kai kawai ba tare da yace komaiba ya buɗe mota yana musu nuni dasu shiga.
Basu ɓata lokaciba suka bar wajen zuwa gidan Jay ɗin dake Empty babu kowa ciki, gidan yayi ƙyau sosai, gashi anguwar da yake babu yawan hayaniya.
Suna shiga gidan dukkan farin cikinsu da suka danne da kewar juna sai ya bayyana, dan sake rungume juna sukai a tare kowa na faɗo yanda yay kewar ɗan uwansa.
Tsawon lokaci suka ɗauka a haka har Gimba ya dawo da ledojin abinci ba tare da sunsan zaiyi wannan ɗawainiyarba.
Godiya sukai masa duk da kuwa yana ƙasansu, ya nuna musu hakan ba komai bane tare dajin daɗinsa na murna da sukai, ya jajanta musu da addu’ar ALLAH ya kiyaye gaba.
Wanka suka shiga su duka a mabanbanta banɗakin dake cikin gidan, sun ɗauki tsawon lokaci, dan Jawaad ma harya fice zuwa wani kiran gaggawa daya samu daga office ya barsu akan kafin ya dawo su tabbatar sunci sunsha sun huta…….
______________________
BILKEESU
______________________
………Har dare babu labarin bilkisu a cikin anguwar, ga kuma ƴan sanda ta ko’ina an bazasu nemanta, sai kuma yaran Jazuuga dasuma ke aikinsu domin taya ƴan sandan.

Ina cikin mankarar har dare, tun ina kuka da hawaye da murya harna koma na zuciya kawai nake iyawa, hankalina bai gama tashiba sai da na farajin motsin mutane masu shigowa sallar magriba, kuma nutsuwa nayi a wajen duk da ƙarfina ya ƙare, hannuna dafe da bakina gudun kar wani mai ƙarfin ji ya iya jiyo fitar numfashina.
ALLAH ya aramin wannan lokacin har akai sallar magriba aka kammala.
Sosai ƙarfina ya gama ƙarewa, na gaji da tsaiwar, burina kawai na zauna nahutama raina, ƙafafuna sunyi nauyi tamkar ba’a jikina sukeba, gashi wasu suna a massallacin basu gama ficewa ba, sun zauna har sai anyi sallar isha’i.
Haka na cigaba da dauriya a wannan yanayi mai wahalar musaltawa har lokacin sallar isha’i yayi ya wuce, mutane sun fara barin massallacin, inda akabar tsirarun da suka koma fita ɗai-ɗai.
Wani da ya fita na ƙarshe shida abokinsa naji suna faɗin ƙarfe goma da rabi na dare, bana a hayyacina zuwa lokacin sosai, amma bayan fitarsu da wasu mintuna saina leƙo kaina cikin massalacin, babu kowa sai mutum ɗaya dake barci, da gyar na tattaro ɗan sauran ƙarfina na janye mankarar na fito, tafiya nake tamkar bugaggiyar da tayi mankas da kayan maye, ni kaina bansan a ina nake jefa ƙafaba, tafiya kawai nake tamkar bahagon raƙumi.
Ƙwaƙwalwar kaina sam bata aiki da zuciyata, ni kaina na fara manta wacece ni?.
Ƴan sanda biyu dana hango gabana suna tunkaroni yasani firgicewa, nai saurin komawa baya na maƙale jikin bangon wani gida, ta gabana sukazo zasu wuce suna magana wadda na fahimci akainace.
Ɗaya a cikinsu ke faɗin, “Oga kana ganin Alhajin nan zai bamu maƙudan kuɗinnan kuwa daya faɗa inhar aikinnan ya kammala yanda akeso?”.
“Hhhh bayarwa kuwa zaiyi ɗan sambo, bakaga yanda yake a firgiceba, bashi da burin daya wuce akama yarinyar, sannan ɗansa ya kuɓta, shiyyasa nima nace muyi ƙaimi, dan inada tabbacin tana cikin anguwarnan bata fitaba, sai dai idan wani munafikinne ya bata mafaka a gidansa”.
“Shegun ba, ai zamu kamatane, idan kuma har kuɗinan suka tabbata lallai lokacin ƙara aurena yayi kenan, dan wlhy zama da kubra kawai nafi ƙarfinsa”.
“Hhhhhhh!! Wato ɗan sambo shiyyasa nake sonka wlhy, kai abokin neman arziƙine, idan kana abu sainaji daɗi saboda lallai kana kan tsarina, saikace uwa ɗayace ta haifemu”.
Dariya suka kwashe da ita tamkar wasu mahaukata su duka biyun, da wannan mahaukaciyar dariyar suka wuceni batare da ɗayansu ya hankalta dani ba.
Numfashi na sauke cikin gajiyawa, sai da na tabbatar sun ɓacema ganina sannan nacigaba da tafiya ina zirar da hawaye, wace irin ƙasa muke da ita hakane? Masu bada tsaro da kariya sune suka koma masu ɓata tsaro da zalunci?.
Ta yaya har muke tunanin samun shugabanni adalai bayan muma talakawan azzaluman junane?.
Nacigaba da tafiya ba tare da namasan ina nakeba, abinda na sani kawai shine nayi nesa da anguwarmu kam tabbas, sannan ina buƙatar zama na huta, sai dai tsoro da fargabar kar azo a kamani sun hanani damar samun wajen yada zango.

Nayi tafiya mai nisan gaske, wadda sam banida nutsuwar ƙididdigeta koda da ƙiyasine, tun ina gamuwa da mutane da kallon motoci a titi har garin ya fara ɗaukar shiru, bakaji koda ƙarar mashin, ƙafa tafara ɗaukewa, hakama motoci, lokacin da garin ya gama ɗaukar shiru babu abinda kakeji sai haushin karnuka.
Da ƙyar na iya kawo kaina wani wajen da nakeji sautin kiɗa na tashi, duk yanda naso samun dauriyar matsawa daga nan na kasa, cikin rashin kuzari da ƙarewar ƙarfi na zube jikin wata bishiyar mangwaro dake a gaban gidan, mashina ne birjik a wajen duk an faka, sai jefi-jefi na mutane dake fitowa daga wajen mace da namiji ko mata zalla.
Tun ina kallonsu har na gazama hakan, idanuna da sukai nauyi jingim saboda kukan da nasha na lumshe a hankali, badai barci nakeba, bakuma ina tare da duniyar mutane bane sam.
Tsawon lokaci ina a wajennan ba tare dana fargaba, sama-sama naji ana tadani, na buɗe idanu da ƙyar ina saukesu akan ƴanmata biyu da bazasu gaza sa’annina ba, sai namiji dake gefe yana faɗin, “Ƙila tasha abinda kanta ya gaza ɗaukane ko?”.
Ɗaya a cikin ƴanmatan da ke ƙokarin taimakamin na tashi tace, “Anya ma wannan kuwa bamma santa ananba sam, dan inaga baƙuwace”.
Kaɗan ɗayar ta ɗan haskani da fitilar wayarta rakani kashi, ta kautar da hasken daga fuskata tana cewa, “A gaskiya baƙuwace, dan nima bamma taɓa ganintaba a gidan wasannan”.
“Da wannan surutun da kuka tsaya da kamata kukai mukaje da ita gida, dan tabbas tana bukatar taimako” namijinne yay magana cikin nuna kulawa.
Basuce komaiba sai taimakamin da sukayi na miƙe tsaye sosai, ni dai ban iya cemusu uffanba, suka kamani a kafaɗinsu mukabi wani lingu.
Banwani damu da inda suka kawoninba, duk dama gidan tsitt yake alamar duk anyi barci, namijinne yasa key ya buɗe ɗakin suka shiga dani ciki.
Sun kwantar dani a katifar ɗakin wadda halin danake ciki baisa na fahimci komai akantaba.
“Ƴar daɓas kunna risho a dafa mata ruwa tasamu tai wanka, dan a halin da take ciki na fahimci bazata iya jin daɗin barciba”.
Da to wadda aka kira ƴar-daɓas ta amsa, cikin mintuna kalilan aka haɗamin ruwan wanka mai matsakaicin dumi, yanzuma da taimakonsu na shiga banɗakin dake a cikin ɗakin.
Ban cutar da kainaba na daure nayi wankan, naji daɗin hakan sosai, bayan nagama na ɗauki doguwar rigar da aka ajiyemin na saka sanann nayo alwala na fito, dan yin wankan yasa naɗan fara dawowa a hayyacina.
Zaune na iskesu sunacin nama, na ɗan kallesu na duƙar dakai ina faɗin, “Dan ALLAH ku taimakeni da abin salla da hijjab”.
Ganinai sun kalli juna a wani irin yanayi na shakku, ni saima na fara tunanin koba musulmai bane…….
Ɗayar ta katsemin tunani da faɗin, “ƴar uwa samun abin salla a ɗakinnan lallai babban abune, ke ama gidannan gaba ɗaya zance, amma dai ga ɗankwali idan zaki iya maneji dashi, hijjab ma inaga za’a iya samun wanda nazo dashi a farkon zuwa gidanan, tunda kuma na ajiyeshi ban sake waiwayeba”.
Ban fahimci zancen nasuba, bankuma tambaya ba, inadai tsaye aka bani hijjab da ɗankwalin, shinfiɗawa nai na tada salla, sai da nayi sallar la’asar da banyiba da magrib sannan nai isha’i, harma da shafa’i da wutiri, hannuna na ɗaga sama ina addu’a hawaye masu zafi na kwarara saman kumatuna, nakai tsawon lokaci ina kaima ALLAH kukana, kafin na miƙe.
“Wai, wannan salla taki akwai tsawo, zokici abinci muɗan kwanta, dan gari gab yake da wayewa”.
Yunwa nakeji, hakan yasa banyi musuba nai zaman cin naman da sukaci suka ragemin, sai fura mai sanyi wadda naji daɗinta sosai.
Ina kammalawa suka nunamin wajen kwanciya.1

Sai a yanzune dana samu nutsuwa komai ke iya dawomin dalla-dalla, wasu hawaye ke sauka saman fuskata a gurguje, koyaya Firdausi take? Inna da baba da sauran ahalin gidanmu, na ɗago hannuna ina kallo zuciyata na wata irin suka, ni Bilkisu yau nice matsayin wadda tai kisan kai, wai ni na kashe mutum?….
Kuka mai ƙarfi ya ƙwacemin, nanfa na shiga rairashi babu mai lallashi, dan masu masaukin nawa bansan ya akai daga kwanciyarsu barcinsu yay nauyi irin hakaba, na daɗe ina kuka har aka kira sallar asubahi a kan kunnena.
Tashi nai cikin layi da nauyin jiki nayo alwala, nazo ina ƙokarin tashinsu amma sam babu wadda tai motsin kirki balle na saka ran zasu tashi, haka na haƙura saboda jin zan rasa sallah.
Koda na idarma na sake gwada tashinsu amma basu tashinba, nanma haka na haƙura, sai dai zuciyata na mamakin irin wannan nauyin barci haka?, nima ban fargaba barcin ya kwasheni a wajen.
2
★★★★★★

A daren ranar yaran jazuga suka dawo gidan da taimakon ƴan sandan nan, duk wani makami da sukasan sun ajiye gidan harda wanda Bilkisu ta gani da yawa a kwali randa ta kasa masa shara duk suka fitar dasu, kayan shaye-shayensu da duk abinda za’a iya kalubalantarsu dashi saida suka fitar dashi.
Hakama innar Firdausi sun fito da ita, asibiti suka kaita inda baba yake cikin wani yanayi da baki bai iya musaltawa.
Innar Firdausi ta fashe da sabon kuka saboda ganin halin ruɗani da mijinta ke a ciki, gefe yaran Jazuga sukaja baba da inna, suka shinfiɗa musu dokoki tare da gargaɗi mai tsoratarwa.
A tsorace baba da inna suka amince kodan son tsira da ransu.
Alhaji Lado yace, “Zamu baku ƴarku mu canjata da gawa, munaso kuyi nesa da garinanma gaba ɗaya, koda sau ɗaya naga masu kama daku na rantse saikun mutu dukanku, bayan na gama gallaza muku azaba mara musaltuwa, sannan koda wasa kuka taimaki yarinyar data kashemin ɗa wlhy kuma saikun mutu, dan daga yanzu dukkan motsinku zai cigaba da gudana ne a kan idona”.
Cikin kuka baba da inna suka amsa.
A munafurce aka fiddo firdausi da taimakon likita da shima aka toshe bakinsa da kuɗi, tare da yaran Jazuga da ƴansandan nan.
A wata mota aka sakasu harda Firdausi da har yanzuma bata farfadoba, sai dai raunikan jikinta duk sun sami kulawa.
A wannan tsohon daren aka nufi asalin ƙauyen su baban Firdausi dasu, sunaji suna gani, suna kuka da ɗunbin tausayin Bilkisu da tunanin tana cikin wane haline? Wane kuma hali zata iya shiga daga nan zuwa safiyar gobe………….✍🏻

https://www.youtube.com/channel/UCl9IGLUXrqUtta-Tjmhoo7Q
MANHA HAUSA NOVEL’S

Maza garzaya domin bada gudunmawarka kaima, dan ALLAH a danna mana subscribing, tare da bibiyar shirye-shiryanmu masu ƙayatarwa a koda yaushe, harma da tsaftatattun littatafan hausa masu ƙayatarwa da zasu dinga zuwa muku a Audio, yanzu haka ƘARAYAR ARZEEƘI ya fara sauka, garzaya kar ayi babu ku😉🥰🥰🤝🏻.

ALLAH ka gafartama iyayenmu

ƘWAI cikin ƘAYA!!
Bilyn Abdull ce👌🏼
Shafi na goma sha biyu
…………Tun a farkawar da nai a wannan barcin safe da yay nasarar saceni na fahimci lallai ƙaddarar rayuwa ta sake jefoni wani rukunin ajin karatun, dan kuwa babu tantama gidan nan na karuwaine. Wasu hawaye masu ɗumi suka gangaro saman kumatuna, ban damu da sharewa ba na barsu suna cigaba da kwarara tamkar an buɗe fanfo…..
           “Baƙuwarmu kina ganin kuwa kukan nan bai isa hakaba?”.
     Ɗaya daga cikin waɗanda suka taimakeni ta faɗa tana janye hannun da nai tagumi dashi.
     Idanu na ɗago na kalleta, ƙyaƙyƙyawace, sannan yarinya shakaf da shekarunta bazasu gaza kamar nawa ba, banbancina da ita kawai jikinta a murje yake alamar akwai jin daɗi tattare da ita, na sauke ajiyar zuciya ina kauda idanuna daga gareta ba tare da na ce uffanba.
      Ɗayar data shigoce ta katsemu da faɗin, “Sweet gafa Laran gabas can nayi dake akan wasan jiya”.
       Ƴar daɓas ta kwashe da dariya tana zama a bakin katifar, “Bar shegiya kinji Sweet, itadai ai bariki iyawace, kowa kaga yazama wane ya iya allonsa ne, idan ta isa itama ta iya wanke nata”.
      “Kamar kuwa kin shiga zuciyata Sweet, dan nima haka nace mata”.
        Kusan a tare suka taɓe baki, Nazy ta juyo indomie daga cikin tukunya tana ajiyewa gabana, “Sorry bakuwarmu mun barki da yunwa, kinga abincinki nan tun ɗazun tsumayen tashinki mukeyi, kinfa sha barci, saikace wadda bata samun isashen barci daga inda ta fito?”.
      Murmushin yake kawai na mata, sai dai ban iya cemata komaiba itama.
       Ƴar daɓas tace, “Nikam badan jiya kinyi magana ba da nace kodai ke kurmace, ki daure ki amsa mana tambayoyinmu kafin Uwargida ta shigo gidan nan, dan in bata fara samun wani bayani daga garemu ba zamu fuskanci matsalane akan kawoki, kodai kema rayuwace ta nuna miki hanyar zaɓar ƴancin kankine?”.
       “Neman ƴancin kai kuma?”.
      Cikin tsagwaron mamakin daya mamaye fuskata nake jefa musu tambayar tawa.
       A tare suka ɗagamin kai, Nazy ta washe haƙora tana cewa, “Ai duk macen da kika gani a gidan nan tazone domin samun ƴancin kanta, sai dai kisamu banbancin dalilan da suka nuna mana hanyar hakance nasararmu”.
        “Wata sabuwa kenan”. na faɗa a fili batare dana saniba.
       Atare suka maimaita abinda na faɗa ɗin, suka ɗora da faɗin, “Miyasa kikace haka? Kina ganin hanyar da muke bata dace da tsarinkiba kika fito da ga gidanku?”.
       Murmushi nayi ina lumshe ido, wasu hawaye suka sake ziraromin, hannu na saka na sharesu a karo na farko, na kallesu sosai cikin matuƙar tausayawa kanmu, “Ni ba wannan harkar nazo yiba, ƙaddarar rayuwace kawai ta kawoni cikin taku ƙaddarar”.
     Shiru duk sukayi suna kallona, nima ban sake cewa komaiba na zame na kwanta ina cigaba da kukana, tsawon loakaci muna a haka babu wanda ya sake cewa komai, sai zuwa can ƴar daɓas tace, “To ki daure ki tashi kici abincin, sannan idan bamu shiga rayuwarkiba dan ALLAH ki bamu labarinki”.
       Shiru ban motsaba, bankuma iya cewa da ita komaiba, babu abinda ke sukar zuciyata sai halin dana bar ƴar uwata Firdausi a ciki tare dasu Inna, saiko kisan Jazuga danai da hannuna, na ɗago hannuna ina kallo, wasu sabbin hawayen suka sake ziraromin, jinake inama ni Jazuga ya kashe, dana huta, koba komai zan kusantu da iyayena, na rushe da kuka mai sauti ba tare da nasan muryata tayi ƙarfi irin hakanba.
       Akusan tare sukai kaina suna tambayata lafiya?, yanzunma dai basu iya samun amsaba daga gareni har wata mata ta shigo.
     Barina sukai duk suka juya gareta, cikin matukar ladabi da girmamawa suka shiga gaishe ta.
      Amsawa take a dake, yayinda idanunta ke a kaina ko kyaftawa batayi, batare data ce musu komaiba ta nunani da ɗan yatsa.
      Nazy ce tai saurin faɗin, “Uwargida baƙuwace da jiya muka taimaka a ƙofar gidan wasa, Babu ne kuma ya bamu ƙwarin gwiwar hakan, yakuma sanar mana zai faɗa miki da safe”.
         Shiru bata amsa ma Nazy ba, sai takowa da tayi zuwa gabana, da hannunta taimin alamun na miƙe zaune, babu musu na tashi danni tsoro ma ta bani, gata garjejiya da tsaho da ƙiba, kaina a ƙasa murya na rawa nace, “Ina kwana?”.
     Karon farko naji muryarta ta amsa mini, sai dai kallon ƙurullar da takemin ne ya sakani jin na takura.
        “Ya sunanki? Mikuma ya kawoki nan?”.
     Shiru kamar bazance komaiba, wani wanda bansan dashiba ya daka min tsawa, hannu ta ɗaga masa alamar ya bari, niko da naketa rawar jiki sai ta tsugunna gabana tana cemin, “Kinga nutsu faɗamin”.
        Tamkar zan haɗiyi zuciyata na mutu dan tsoro nace, “Sunana Bilkisu, ƙaddarar rayuwace kuma ta kawoni nan ɗin”.
         Batace komaiba ta cigaba da kallona tsawon sakwanni, sai kuma ta miƙe tana faɗin,  “Ƴar daɓas ku bata dukkan kulawa, tana bukatar hutu koda na kwana uku ne, amma zuwa dare kuzo da ita gidan wasa”.
     Da to suka amsa mata cike da ladabi, itako ta fice tana ƙara jin kanta sama.+

STORY CONTINUES BELOW

         Tun daga hakan babu wanda ya sake tambayata komai har dare, sune suka sani yin wanka tare da bani kayan sakawa, amma ganin wando da rigane nace musu bana sakawa su bani zani, Har Nazy zatai musu, sai ƴar daɓas ta hanata, siket da riga na wani yadi mai ƙyau suka bani, ba musu na amsa na saka, danni burina daga wannan fitar bazan sake dawowa ba.
        Kusan ƙarfe goma na dare muka fita, tsakanin gidan wasan nasu dana kwanta a ƙofar jiya da gidan babu wani nisa, duk wanda yazo saiya saka kuɗi yake shiga, amma mu sai aka barmu muka shige bayan kawai su Nazy sun saka sunansu a wani littafi.
     Ƙaton wajene da aka jerama kujeru tamkar aji ko gidan kallon wasan ball, sai ko dima-ɗiman sifiku na kiɗa, ƴammatane bila adadin cikin shiga mai tada hankalin duk wani mai aƙidar tarbiyya, sai maza dake ƙalilan a wajen,
      Muma wajen zaman muka samu muka zauna, ni dai sai baza ido nake ina kallon ikon ALLAH. bamufi zaman mintuna talatinba wasa yafara gudana, ni dai sam bammaga abin birgewa a wajenba, amma su sai ihu da sowa sukeyi, wasu suna fita suna liƙa kuɗi.
          Abinda yafi bani mamaki shine yanda manyan mata ƴan gayu keta shigowa ɗai-ɗai wajen suna ɗaukar ƴammata, suna fita.
    “Mikenan?”
Na faɗa a zuciya ba tare da nasan maganar ta fito fili ba.
     Nazy dake gefena tace, “Akanmi kike magana Balki?”.
     Kallonta nai da tabbacin maganata ta fito fili kenan, banyi nauyin bakiba nace, “Akan waɗanda naga ana ɗauka ɗai-ɗai ana fita dasu nake magana”.
     Murmushi Nazy tayi ta ɗauke kanta tamkar bazata amsa minba, kusan mintuna uku harna fidda ran hakan sai naji tace, “Duk wanda kikaga an fita da ita tayi kasuwane, a tsarin gidan wasannan yaune ranar baje kolin haja, wasu daga wannan ɗaukar da za’ai musu sun tafi kenan, dan kuwa sunzama hajiyoyi na gaske masu ƙazaman kuɗi, duk wata hajiya dakikaga ta shigo nan mai ɗunbin dukiyace, acikin abinda zata jiƙaki dashi idan ta ɗaukeki bazai tsunkuli koda kashi ɗaya a cikin goma na dukiyartaba…….”
     Maganarta ta katse sakamakon zuwan wata hamshaƙiyar hajiya wajen namu, yanda ta kafeni da ido tamkar wata mayyane ya sani jin faɗuwar gaba, saurin fara karanto “Hazbinallahu wa ni’imal wakil” nayi ina janye idona daga shashensu.
      Batace komaiba tai murmushi tana maida kallonta ga ƴar daɓas da tun ɗazun na lura ranta a jagule yake, dan sam bata da walwala ko sukuni, duk wadda tazo kuma inda muke saita ɓata fuska.
        Murya a yangance hajiyar ke faɗin, “ƴar daɓas wannan karonma bazaki sallama minba? Na ƙara ruɓanya kuɗin wancan karon sau biyu, harma da ƙyautar mota”.
      Shiru ƴar daɓas bata ɗagoba, bakuma tace komaiba, Murmushi naga Nazy tayi tana matsawa jikin ƴar daɓas ɗin sosai, ta ɗago tana kallon hajiyar cikin fari da idanu, “Hajjaju sweetyna ba kuɗin kowa bane a gabanta, nikaɗai nasan yanda nake sarrafa kayata har take ganin babu mai iya matan sai ni, kibar ƙwaƙwa da wahal da kanki a kan kowaccenmu, ɗakin wasannan cike yake da ƴammata masu aji kuma kyawawa, kizaɓi duk wadda tai miki zaki samu da taimakonmu, dan zamu shige miki gaba wajen Uwargida”.
        Ajiyar zuciya Hajiyar taɗan sauke tana sake maida kallonta gareni, ina kallonta taima Nazy nuni dani cikin wani salo.
       Dariya Nazy tayi, har ƴar daɓas ta ɗago tana kallonta, nima dai kallonta nayi, taimin kallo ɗaya tana ɗauke kanta da faɗin, “Hajjaju mutan makka, banƙi zaɓinki ba, sai dai fa wannan *ƙwai cikin ƙaya* ce, sabuwar hajace da batasan kasuwar da take cikiba, tana buƙatar lokaci kafin a buɗeta Uwargida ta saka cinikinta bayan tamata sabis, kinsan duk abinda Uwargida bata ɗanɗanaba baya shiga a hajar saidawa”.
      Wani shegen ƙayataccen murmushi hajiyan tayi, ta ɗaga yatsunta uku da sukasha gwala gwalai tana kaɗawa, “Zan zauna da Uwargida, sannan ku na hannun damartane, inaso ku tayani barbaza manufofi, dan inason samun sabuwa dal a leda wannan karon, a ɗaki zan sakata dindin saboda tsaro, idan har nasamu wannan hajar naimuku alƙawarin kuɗade masu nauyi da ƙyautar mota, tareda kaiku duk ƙasar da kuke buƙata Honeymoon”.
          “Zamu gwada, ki bamu kwanaki bakwai kacal”.
      Nanma murmushi tayi, ta zaro kuɗi masu yawa a bag ɗinta tabasu.
     Sagadada nai da baki ina kallonsu, danni sam ban fahimci dukkan zaurencensu ba, jin an kamo hannuna sai nai firgigit na dawo hankalina, hajiyarce dai, bangama dai-daitaba ta kuma tsunbula tunanina a ruɗani, dan kuwa hannuna ta sumbata tare da kashemin ido ɗaya cikin wani irin salo”.
     Ko motsi kasayi nayi, na bita da kallo harta fice riƙe da hannun wata yarinya.
       
         Dariyar su ƴar daɓas ce ta sani maida kallona garesu, Nazy tace, “Ƴar daɓas da alama fa Balki hajiya ta fara kaita network, irin wannan suman zaune haka”.
     Dariya suka sake kwashewa dashi suna taɓawa.
         “Dan ALLAH kumin bayani mana?”.
     Cikin dariya ƴar daɓas tace, “bakya bukatarsa a yanzu Balkisu, ki kwantar da hankalinki zaki fahimci komai, mudai fatanmu ki riƙe wannan harkar, dan harkace mai cike da ƴanci, babu ruwanki da wulaƙancin wani banza shi namiji, jinsin dake kallonki a ƙasƙance, ya aureki ya kaiki gidansa yana wulaƙantawa, bakida wani muhimmanci saina haifa masa ƴaƴa da gadin gida, wannan kuwa gashin kanki zakici, sai kinso wata ta saka miki zoben mallaka ma”.
       Nikam sunma ƙara ruɗar dani, hakan yasa nai shiru ban sake tambayaba.
      Muna nan zaune sai da gidan kusan kashi biyu bisa ukun mutanen gidan suka fice, tsurarun mazan wajenma sun ɗauki ƴammata sun fice, muma tashi mukai muka fito domin komawa gida……..
4
STORY CONTINUES BELOW

_______________________
JAWAAD
_______________________

    ……………A yau Jawaad bai koma gidaba, bai kuma nema Shahudah ba, dan tun fitowarsa ya fahimci bata kwana a sashen nasuba, hakan ba wani sabon abu bane a wajensa, dan abu kaɗanne zai haɗasu taje takai ƙararshi.
          A wannan daren suka tsara abubuwa masu yawa shi da su Hafeez Umar akan kubutar da Alhaji Sadi kokino (ba giyar yaroba), yanda tsarin nasu yazo komai ya gamsar dasu, dan haka suka kwanta cike da farinciki bayan sun gamawa Jawaad tsiya akan yatashi ya tafi wajen matarsa.
     Murmushi kawai yayi, danshi mutumne mai yawan zurfin ciki, bai yarda kowa yasan matsalar gidansaba komai kusancinsa da kai, shiyyasa ko kararsa Shahudah ta kai, idan aka kirasa abinda kawai suke iyaji daga bakinsa shine (ba komai), har ƙannen mahaifiyarsa su Umma bai taɓa zama ya sanar musu matsalar Shahudah ba, sai dai ƴan gidan su Jawaad su kawo musu gulmar.
         Jabeer dake gefensa yace, “Boss mufa da gaske mukeyi bazaka kwanar mana ananba, kaje wajen amarya taimaka tausar gajiyar da ka sha yau, mun yafe mata”.
     Harara Jawaad ya watsa masa, yaja filo yana kwanciya saman Sofar dake cikin ɗakin tare da zungurin Jabeer da kafa, tashi Jabeer yay a kusa dashi yana dariya da riƙe gefen ƙugunsa da Jawaad ya shura.
     Cikin danne abinda ke sukar ransa yace, “Waini korata kukeyine? To babu inda zanje, itace ai tace muyi hirar yaushe gamo”.
         Carab Aliyu ya amshe da cewa, “A lallai Shahudah, amaryar tamu mai haƙurice wlhy, mun kwa gode mata, kuma tunda mun fito sai an sake mana sabon biki da bamu ganiba”.
      Duk dariya sukayi banda Jawaad daya ɗauke kansa tamkar baisan sunayi dashi bane…..
        “Alhaji kayi shiru?” cewar Jabeer yana zungurinsa da biron hannunsa da suka gama rubuce-rubuce”.
      Baki Jawaad yaɗan tabe, sai kuma ya tashi zaune yana faɗin, “Kunga kubar wannan shirmen malamai, ya kamata gobe fa kowa yaje yaga iyalansa koda a ɓoyene, kafin komai ya dai-daita”.
        Dukansu kallonsa suke da murmushi a fuskarsu, ƙaunarsa na sake shiga musu rai, Aliyu yay karfin halin amsa masa,
       “Amma kana ganin babu damuwa Jay? Da kawai an haƙura munbi dukkan sharadin nasu yanda suka faɗa”.
         Ajiyar zuciya Jawaad yayi, yace, “Aliy dokarsu ni bata wani dameniba, kawai abinda ya cancanta nake dubawa”.
        Kansu duk suka jinjina masa saboda gamsuwa da maganarsa, Hafeez ya miƙe tsaye ya dawo kusa dasu, sai da ya zauna yana kallonsu kafin yace,
        “Anya kuwa Jay kana ganin mahaifin Surayya zai bani damar ganinta ita da Suhail?”.
         Shiru sukai su duka, kusan sakwan goma Jawaad ya ɗago kansa, guntun murmushi yayi yana dafa kafaɗar Hafeez ɗin, “Karka damu Broth, namaka alƙawarin zan kawo maka Surayya har gidannan itada Suhail, kuma Aliyu da Jabeer hakan inaga ya dace muyi”.
      Bai jira amsarsu ba ya tashi ya shige bayin dake cikin ɗakin, duk binsa sukai da kallo a wani irin yanayi mai wahalar fassara.

        ★★★★★★★

       Kamar yanda yay alƙawari washe gari da safe sai da ya cika, dan kuwa duk sai gashi da matansu da ƴayansu, Aliyu ne kawai matarsa bata haihuba, dan aurensu da wata uku abin ya faru, Jabeer kam da yarinyarsa ɗaya Fatima, sai cikin daya barta dashi ta haifi namiji aka saka masa sunansa.
       Hafeez kuma yaronsa ɗaya Suhail.
    Sunyi murna sosai da ganin juna, hartakai saida Jawaad yay musu hawaye, zare jikinsa yay shima ya nufi gida wajen nasa iyalin dukda yasan ba lallai ya tarar da abu mai daɗiba.
★★★★★★

         Zuwa tashin hantsi Shahudah ta koma normal kamar ba itace keta amai da safe ba, faɗan da mama Atika taimata ne ya tilastata saka doguwar rigar jallabiya baƙa a jikinta, amma sai ƙorafi take wai zafi yamata yawa.
       Tun mama Atika na tanka mata har tai banza da ita, a haka gayyar ƴan gidansu suka isketa harda mamansu.
    Rungume Shahudah tayi tana murna, takai hannu kan cikin Shahudah tana shafawa.
    Ƙwaɓe fuska Shahudah tayi tana wani turo baki, “Momy wai kema kina nufin son cikin kikeyine?”.
        Hajiya Humaira ta faɗaɗa murmushinta tana zama saman kujerar dake kallon ta mama Atika ba tare data bama Shahudah amsar maganarta ba.
        Mahaifiyarsu ta shiga gaidawa, mama Atika ta amsa, tare da faɗin, “Wannan lalatacciyar ƴar taku saikun saita mata zama akan wannan cikin, inba hakaba wlhy zata ɓata komai”.
      Wani guntun murmushi Hajiya Humaira tayima mama Atika, “Mama manta da batunta, zamuyi maganar daga baya, idan kuma bataso ai sai a zubar ko”.
     Kafin mama Atika ta bada amsa Shahudah tai carab ta cafke maganar, “Yauwa Momy na, ashe kin gane, dama nasan kekam zaki bani goyon baya, kuma zaki saka wancan uban taurin kan Jawaad ya yarda akan hakan, danni a tsarina saina shekara goma gidan miji zan haihu, shima ƴaƴa biyu kawai nake bukata, mace ɗaya namiji sun wadatar dani, idan son samunema na haifesu ƴan biyu kawai, kunga shikenan”.
     Babu wanda ya tanka mata a wajen sai Hajiya Humaira da tace, “Tsarinki mai ƙyaune mamana, kuma ni na amince dashi”.
      Wannan magana ta Hajiya Humaira taima Shahudah daɗi, saitaji zuciyarta ta samu nutsuwa, tunda mahaifiyarta ta bata goyen baya ko Jawaad bai isa hanata yin yanda tasoba.5

      Babu wanda ya sake tada zancen har washe gari, sundai aika kiran Jawaad da daddare aka iske bai dawoba, hakan yasakasu fahimtar bazai kwana a gidaba kenan.
        Yau ma Shahudah a sashen mama Atika ta kwana, duk da taso ta koma sashenta sai mama Atikar ta hana gudun kar Shahudah taje ta aikata musu ganganci akan yunkurin zubar da cikin, dan tunda ta ambata to zata aikata kuwa.

      Motar Jawaad na shigowa family house ɗin ana kaima mama Atika labarin dawowarsa, hakan yasa ta aika a kira matashi, amma saiya maido ɗan aiken da saƙon yana zuwa kawai.
        Sunta zuba idon ganinsa amma sukaji shiru, har kusan awa biyu da rabi sai gashi……….✍🏻

https://youtu.be/6YuGtf5lQF8
Maza garzaya domin sauraren cigaban littafin *KARAYAR ARZIƘI*  Na Bilyn Abdull a *MANHA HAUSA NOVEL’S*.

Ku danna Subscribing domin nuna ƙaunarku garemu, tare da ƙararrawar sanarwa dan samun shirye-shiryenmu a duk lokacin da muka ɗora.

MANHA HAUSA NOVEL’S (Ƙyautar ALLAH).

*takuce, kuma natane, ta hanyar kasancewa da itane zamu sake tabbatar da wanene yafi son wani😉👌🏻😻😻😍😍🥰💃🏻

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻

ƘWAI cikin ƘAYA!!

Bilyn Abdull ce👌🏼

Shafi na goma sha uku

………….“Alhaji akwai matsala fa”.
       Jikin Alhaji lado na ɓari yace, “Yallaɓai matsala kuma? Akan mi? Yarinyarce ta gagareku samune ko yaya?”.
       “Alhaji ba wannan bane, yarinya kam muna kan nemanta, insha ALLAHU kuma zamu sameta, matsalar danake faɗa akan ɗanka take, harbine a damtsen hannunsa, binciken likita ya tabbatar mana kuma jami’an tsarone suka harbesa a wajen, kuma da alama harbin anyisane bayan awa goma sha ɗaya kafin faruwar rigimarsa da yarinyar, lallai idan labarin nan yaje kunnen manyanmu reshe ne zai juye da mujiya, komai kuma zai iya ɓaci”.
      Zufar data jiƙa alhaji lado yasa hannu ya sharce, harshensa har sarƙewa yake yace, “Yanzu miye mafita?”.
        “Shine nima abinda na kasa haɗawa a raina gaskiya”.
       Alhaji Lado yay shiru yana kallon ɗan sandan, sai buga hannunsa daya dunƙule yake cikin ɗayan, cikin taune leɓe yace, “Ni ga tawa shawaran”.
      “Ina saurarenka Alhaji”. ‘Cewar ɗa sandan yana kallonsa’.
      “Mizai hana shi likitan mu ƙara masa kuɗi ya rufe zancen da dabarunsa, dan gaskiya inason a kamo wannan yarinyan, cikin abokansa sun tabbatar min akwai abinda yarinyar tagani a ɗakin my son kwana bakwai da suka shuɗe, kwana biyar kafin faruwar wannan abun kenan, sannan rashin kamata barazanane a garemu baki ɗaya”.
      “To Alhaji ka kawo shawara mai ƙyau, sai dai matsalar da nake hasashe kar yazam waɗanda suka harbi yaronka sun san fuskarsa ko wani abu dangane dashi, hakanne kawai zai kawoma shirinmu rashin tasiri”.
      Nanma shiru Alhaji Lado yayi, zuwa wani lokaci ya saki wani nishi da ƙarfi, gaba ɗaya ya rasa wane irin tunani kuma zaiyi, yana ƙaunar Jazuli, sam baya buƙatar rasashi, gashi dama har yanzu baima farfaɗoba cikin hankalinsa, dan sosai bugun da Bilkisu tai masa akai ya shigesa har can cikin kansa.
     Basu samo mafitaba a wannan zaman, hakan yasa Alhaji lado yace ɗan sandan ya bashi lokaci zuwa safiya zaiyi tunani akai.

+
_________________________
JAWAAD
_________________________
…………Da sallama ya shigo falon, Shahudah da mama Atika dake zaune duk suka zuba masa idanu, yana sanyene da ƙananun kaya farare tas gaba ɗaya, duk da bana kwalliya bane yayi ƙyau abinsa, ga wani annuri da cikar haibar kwarjininsa na fitowa a fuskarsa.
      Babu walwala a kan fuskar tasa, ya risina yana gaida Mama Atika.
    Cikin fara’a ta amsa masa tana tambayarsa ya aikin nasa, ta kuma ɗora da ƙorafin rashin zuwansa gaidasu a koda yaushe.
     Haƙuri kawai ya bata yaja bakinsa yay shiru, bai ko kalli inda Shahudah takeba, ita kuma ALLAH bai bata tunanin tako gaidashiba.
      Shiru falon ya ɗauka na wasu mintuna da basu gaza uku ba, kafin sallamar Uncle Uwaisu ta katse musu tunani.
     Yana zama Uncle Bashir shima ya shigo, dan haka Jawaad yay musu gaisuwa a tare cikin girmamawa.
         Sai da suka kammala gaishe-gaishen nasu, suma sukai masa ƙorafi akan rashin ganinsa akai-akai, kamar yanda ya saba dai haƙurin ya basu suma da tabbatar musu da yanayin aikinsane ya kawo hakan.
       Duk sun nuna gamsuwarsu akan hakan, shiyyasa suka saki wancan zancen suka tsunduma maganar data tarasu game da ƙararsa da Shahudah ta kawo.
       Hakan ba sabon abu bane a wajensa, shiyyasa baice uffanba har suka kammala, itama Shahudah aka sata ta maimaita komai daya faru.
       “Jawaad kaji abinda matarka tace, shin hakane? kokuwa akwai kuskuren fahimtarta a ciki?”.
        Guntun murmushi Jawaad yayi, cikin nutsuwarsa yace, “Uncle ni dai gareni babu komai, amma tunda ita na mata ba dai-daiba tayi haƙuri, akan rashin sanine”.
         Dukansu sagade sukai suna kallonsa, duk da dama a koda yaushe irin wannan zaman ya haɗa amsar da yake basu kenan sai ta yau tafi ƙona ransu, a ɗan fusace Uncle Uwaisu yace, “Jawaad ka daina mana wani ɓoye-ɓoye akan abinda ke faruwa tsakaninka da matarka, mu dai iyayenkune ku duka, bamajin daɗin yawan matsalolin dake kunnowa a cikin aurenku, gashi kai kullum akazo irin wannan zaman sai kace batai maka komaiba, anya kuwa gaskiya kake faɗa?”.
         “Uncle gaskiya nake faɗa, da tamin wani abu dana faɗa ɗin……”
      “Wlhy ƙarya kake bb, ban maka wani abuba kake cewa kayi nadamar aurena, wai harma bazaka taɓa yafema kanka hakanba”.
      Banza Jawaad yay mata bai tankaba, yayinda su Mama Atika suka zuba masa ido suga idan zaice wani abu, amma sai sukaji yaƙi cewa komai.
        “To kaji abinda tace Jawaad”.
     Uncle Bashir ya faɗa yana kafesa da idanu.
      Kamar Jawaad bazai amsaba sai kuma ya gyara zamansa yana kallon Uncle Bashir ɗin, “Uncle wannan zancentane kawai, ita tasan a inda ta samoshi”.
       Gaba ɗaya ba ƙaramin haushine ya turnuƙe zukatansu ba, musamman ma Shahudah da kamar zuciyarta zata babbake dan baƙin cikin murɗaɗɗen halin Mijin nata……
      Mama Atika tai ƙarfin halin haɗiye nata ƙududun tana ƙaƙalo murmushin yaƙe, “To shikenan yanzu duk abar wannan maganar tunda yace shi babu komai, sai kuyi musu nasiha suyi haƙurin zama da juna kamar yanda kowa ke zaune a nasa gidan, ni dai zan faɗi maka albishir mai gidana Jawaad”.
         Ɗago manyan idanunsa da suka sake girma saboda ɓacin rai yay ya kalli kakar tasu, sai dai baice komaiba.
    Ta faɗaɗa fara’ar ta tana cewa, “Matarkace ke ɗauke da cikin wata ɗaya da wasu kwanaki”.
        Kafeta da ido Jawaad yayi, sai kuma ya janye ya maida kan Shahudah, baka isa fahimtar farin ciki yayi ba kokuwa baƙin ciki…….
     Shahudah ta katse masa tunani da faɗin, “Nifa kuma bar lasa masa zuma a baki Hajiya, dan wannan cikin zan zubdashine, dan yazo ne akan kuskure, sainan da shekaru tara zan sake amsar waninsa, lokacin mun cika shekara goma da aure…….”
     Cikin Hanzari Uncle Uwaisu dake kusa da ita ya kai mata duka, kaucewa tai tana kumbura baki.
       “Wai miyasa baki da hankaline shin Sabira?, mike damun tunaninki ne?……”
         Murmushi Jawaad ya saki yana katse Uncle Uwaisu da faɗin, “Uncle barta, tanada gaskiyarta itama, haka muka tsara ba yanzune zamu haihuba saboda gudin karmu tsufa da wuri, “Hudah nawa kike buƙata dazai isheki ganin likitan da zai zubda cikin?”.
       A matuƙar razani duk suka kalleshi, banda Shahudah da daɗi ya lulluɓe, babu kunya ta taso daga wajen zamanta ta faɗa masa ajiki tana ƙanƙamesa, dukda yaji kunyar hakan saiya basar shima yaɗan rungumota yana bubbuga bayanta, ɗago kanta tai ta sumbaci goshinsa da laɓɓansa, tana niyyar kissing ɗinsa ya kauda fuskarsa da ɗan tureta kaɗan a jikinsa.
     Wannan abu yabama su Mama Atika matuƙar kunya, dan haka duk suka kauda kansu garesu, Shahudah kuwa ko a jikinta, neman ma ɗare cinyarsa take zata zauna yay mata gargaɗi da idanu.
       Matsawa tai tana wata siririyar dariya da faɗin, “Bb har yanzu baka wayeba, ai dai matarkace ni balle ace munyi abu mara ƙyau, tunda komai ku hausawa a wajenku baida ƙyau…….”.
         “Kinci gidanku Sabira”. ‘Uncle Bashir ya katse Shahudah cikin mata daƙƙuwa’ yaci gaba da faɗin, “Ke yanzu da ƙaniyarki a gabanmu kike faɗar wannan maganar?”.
        A hannun kujerar da Jawaad yake ta zauna tana dariya, ta maƙale damtsen hannunsa tana ɗora kanta ta kwantar jikin hannun.
     Ko motsi Jawaad baiyiba, ya kuma fuske abinsa kamar ba shi ta kwantama a jikiba.
        Rashin mutuncin Shahudah ya wuce dukkan tunanin su mama Atika, dan haka suka ɗauke kansu akanta.
       Mama Atika tace, “Kai yanzu nan Jawaad da hankalinka zaka biye mata ku zubda ƙyautar da ALLAH ya baku? Wane irin banzan aƙidane wannan? Ku ba’a haihuwa aka haifeku ne?”.
        “Kiyi haƙuri hajiya, ni karkuga laifina, Hudah itace mai ɗauke da cikinnan, sannan itace zata haifesa, ta rainesa, ta bashi tarbiya, to taga bazata iyaba ni mizaisa na takurata, bayan kuma ƴancintane zaɓama kanta duk abinda taga ya dace da ita, inhar batason ta haihu yanzu zan goya mata baya ta zubda cikin, idan kuma zata haifesa zanfi kowa jin daɗin hakan,duk shawarar data tsaida ta sanarmin”. Ya ƙare maganarsa da ƙokarin cireta a jikinsa ya miƙe, “Kuyi haƙuri bara naje, dan nanda awa biyu zan sake fita, inason naɗan huta kafin lokacin”.
      Babu wanda ya iya cewa komai sai Shahudah da tai tsigil tana faɗin, “Bb jirani mu wuce”.
       Tsayatan kuwa yayi, ta shiga ɗakin Mama Atika ta ɗakko wayarta ta fito, a gabansu Uncle Uwaisu Jawaad ya kama hannun Shahudah suka fice abinsu”.

STORY CONTINUES BELOW

       “Turƙashi”. ‘Mama Atika ta faɗa cikin sauke nannauyar ajiyar zuciya’.
     Daga Uncle Uwais har Uncle Bashir babu wanda ya iya cewa komai, dansu lamarin yafi ƙarfin tunaninsu.
         A wannan yanayin Hajiya Humaira ta shigo ta iskesu itama…..
★★★★★★

         Suna shiga Sashensu Shahudah ta maƙalƙale Jawaad tana dariya.
         “Nagode ALLAH da yau ra’ayina yazo dai-dai da naka bb na, ina sonka harma babu adadi”.
     Wani munafikin murmushi ya saki shima ya rungumeta, murya can ƙasan maƙoshi yake faɗin, “Duk abinda matata takeso nima shi nakeso, kuma tsarinki ya birgeni tawajena”.
        Da sauri Shahudah ta ɗago kanta ta manne bakinsu waje ɗaya, babu musu Jawaad ya amsheta hannu biyu, tun a falon labari yaso fara canja salo, da ƙyar ya iya ɗaukarta ido rufe suka haura sama.
😉ni dai a falo nai zamana gudun gano abinda malam ya hana😂⛹🏻‍♀️.

            Jawaad ya sumbaci goshin Shahudah dake jikinsa a lafe bayan lafawar komai, shi shaidane akan ƙoƙarinta na bashi dukkan farin ciki a makwancinsu, halayyarta da tsarintane kawai matsalarsa, dan ba mu’amular kwanciya kawai ya dace mace ta ƙware wajen mijinta ba, akwai wasu farin cikin dake girmama danƙon zaman lafiya da ƙarfafa soyayya ga ma’aurata, mafi yawancinsu a kula da gidan ma ake samunsu.
       Sake matseta yay cikin jikinsa yana lumshe idanunsa alamar sonyin barci……..
_______________________
BILKEESU
_______________________
………..Har muka shigo gidan zuciyata da tunanina basu gaza wajen cuɗanya game da gidan dana tsinci kainaba, kamar yanda na saba na ɗauro alwalar barci, har zan kwanta sai zuciyata ta bani ƙarfin gwiwar miƙa kukana wajen UBANGIJI, hakkane yasa na shinfiɗa ɗankwali na kabbara salla.
      Ƴar daɓas da Nazy basa ɗakin, bansan ina suka maƙaleba duk da tare muka shigo cikin gidan.
       Ina cikin salla naji shigowarsu, duk da hankalina ba a kansu yakeba kusan mintuna biyu da shigowar tasu sai nakeji wani nishi-nishi tamkar wasu mayu sunga nama.
      Koda nai sallamar sallata ban kallesunba, saina sake miƙewa na kabbara wata sallar, kafin na idar ne abin nasu yay ƙarfin da har waswasi ya fara min kutse cikin sallata, takaitawa nai nayi sallama dan son ganin wane hali suke ciki? Ni duk tunanina ko wanine baida lafiya a cikinsu.
          Cikin matuƙar razana da firgita na ƙwalla ƙara, kafin wani lokaci jina da ganina duk sun gushe.
    
     Ƴar daɓas taɗanyi ƙoƙarin janye Nazy dake mamuƙe da ita dan bama bilkisu ɗauki, amma sai Nazy ta sake matseta tana mata wani salon sheɗancin da ya sata maida hankalinta gareta, cikin narkewar murya Nazy tace, “Barta Sweet, ta firgitane kawai saboda bata taɓa ganiba, a haka harzata saba itama ta fara sha’awar abun a ranta” bata bari ƴar daɓas ta bata amsaba ta haɗe b…….

(Wa’iyazubilla) kaicon wannan mummunar rayuwa al’ummar MANZON ALLAH, yanzu waɗanan fa sune har suke iya bugar ƙirji su kira kansu cikakkun musulmai masu jiran samun aljanna😭, sune suke buƙatar addinin musulunci yay alfahari dasu matsayin al’ummarsa?😭 sune suke buƙatar ƴaƴa suyi alfahari dasu matsayin iyaye😭 ya rabbi ka wajabta mana tsoronka a zukatanmu, ka hanamu shagala da duniya da kayan cikinta, ALLAH ka rabamu da asararriyar rayuwa mara amfani😭😭😭😭🙏🏻🙏🏻.
7
★★★★★★
          Ban tashi farkawa ba sai da zafin rana ya fara dukan fuskata, na buɗe idanu da ƙyar, inda na ganni kwance ya sani tashi zaune a firgice saboda tuna abinda ya faru jiya, waige-waige na farayi a cikin ɗakin, ganina ni kaɗai a cikine ya sakani sauke numfashi ina share hawayen da ke ziraromin, abinda na gani a daren jiya ne kawai ke dawomin cikin idanu da zuciya……
       Shigowar Nazy ɗakin ya saka gabana faɗuwa, nai saurin duƙar da kaina saboda wata kunya data kamani, sukuwama da suka aikata ko a kwalar rigarta.
       Ina jiyo sautin murmushinta ta zauna kusa dani, “Oh Balkisa minene damuwarki? Idan abinda kika gani jiyane karya dameki Please, wannan shine ƴancin ai, ki gwada harkarnan zakiji daɗinta, uwa uba zakiyi arziƙi, ki zama hamshaƙiyar mace abar kwatance a duniya, dan yanda ALLAH yay miki jiki mai ƙyau ɗinnan wlhy abincin manyan hajiyoyi zaki zam…….”

       “Wa’iya zubillah” na faɗa a fusace ina zazzaroma Nazy idanuna da sukai jazur, ga hawaye na kwarara a cikinsu, cikin nunata da ɗanyatsa nake cigaba da faɗin, “Karki sake danganta ni da wannan shaiɗancin mai gusar da imani, ina roƙon UBANGIJI na ya shiryeku, kuma zukatanku su buɗe, tunaninku ya fara gudana akan bigiren gaskiya, kukuwa wace amsa harsunanku suka tanada wajen bama UBANGIJIN al’arshi aranar da gaɓɓai ne kawai zasu bada amsa ba bakuna ba? Wa kuke taƙama dashi da zai tsaya muku a ranar da rana take gab da ƙwakwalen mutane? Wani ƙwarin gwiwa kuke dashi na gujema makoma irinta mutanen ANNABI LUƊU da suka gushe akan wannan mummunar ɗabi’ar? Wace amsa gareku akan iyayenku da sukasha wahalar baku tarbiyya bayan ɗaukar ciki da haihuwarku zuwa ciyar daku har kuka kai wannan munzalin girman? Wace amsa gareku ga al’ummar daular musulinci da kuka fito a ciki? Tayaya kuke tunanin akan alfahari da MANZON ALLAH zaiyi daku kasancewarku al’ummarsa? Kaicon wannan Rayuwa ta dabbanci, kaicon wannan buri mara amfani, kaicon wannan duniya mara dorewa, kaicon dukiyar da zata zamewa mamallakanta dana sani, kaicon rufaffiyar zuciyar da bata banbance ƙyaƙyƙyawa da mummuna, kaicon sha’awar dake tunzura zuciya bisa ɗabi’ar aladu, inama na tsaya ƴan sanda sun kamani, da inada ilimi akan sanin tarar daku a ƙaddarata dana roƙi UBANGIJINA ya ɗauki ruhina kafin zuwana gareku…….”

Ta fashe da kuka mai tsuma zuciyar mai saurarenta, harshenta ya sarƙe ta kasa cigaba da magana.
       Kan ƴar daɓas dake bakin ƙofa tsaye da wasu ƴammatan gidan kusan su shida duƙe saboda wani irin rawa da zucikatansu keyi akan kalaman bilkisu, ita kanta Nazy tsigar jikinta sai tashi takeyi……..

       Da sauri suka waiga bayansu saboda jin gyaran muryar Uwargida, babu wanda bai ruɗeba a cikinsu da ganinta, dan ɓacin ran dake fuskarta kawai ya isa tabbatar musu da taji komai akan kalaman Bilkisu, darewa sukai biyu suka bata hanya, cikin takunta na izza da bushewar zuciya ta tura kai cikin ɗakin….
      Wani wawan mari ta sauke mani a fuska, na ɗago a razane ina kallonta, saukar wani na sakeji, kafin na dawo dai-dai an kuma saukemin wani, tun ina fahimtar adadin marukan har ruɗani ya sani gaza fahimta.
      Jinai kawai an sungumeni anyo waje dani, ina kuka da roƙonta amma taki saurarena, ta wata ƙofa dake a cikin gidan tabi dani, ashe gidane mai ƙyau a wajen, wanda shine matsayin sashenta.
     Ban damu da kawatuwar gidanba, burina kawai sauka daga jikinta na samu hanyar kuɓuta.
     Wani makeken ɗaki daya jiƙu da kayan more rayuwa ta kaini, ta jefani bisa bankeken gadon ciki wanda tashin hankalin da nake ciki bazai barni lissafa muku haɗuwarsa ba…………..✍🏻

       https://youtu.be/6YuGtf5lQF8
Maza garzaya domin sauraren cigaban littafin *KARAYAR ARZIƘI*  Na Bilyn Abdull a *MANHA HAUSA NOVEL’S*.2

Ku danna Subscribing domin nuna ƙaunarku garemu, tare da ƙararrawar sanarwa dan samun shirye-shiryenmu a duk lokacin da muka ɗora.

MANHA HAUSA NOVEL’S (Ƙyautar ALLAH).

*takuce, kuma natane, ta hanyar kasancewa da itane zamu sake tabbatar da wanene yafi son wani😉👌🏻😻😻😍😍🥰💃🏻*

ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏🏻
4

ƘWAI cikin ƘAYA!!

Bilyn Abdull ce1

Shafi na goma sha huɗu

…………..Kusan a tare suka farka da ga barcin da ya kwashesu, sai dai yanda Shahudah taci karo da fuskar Jawaad sai zuciyarta ta shiga yimata wasuwasi.
      Ya sauka a kan gadon ba tare da yace da ita uffanba, bayi ya shiga, ta miƙe da sauri tabi bayansa, sai dai a mamakinta ya rufe ƙofar bayin.
     Ɗan bugawa tai kusan sau uku, yanajinta lokacin yana ƙoƙarin haɗa ruwan wanka amma sai ya shareta kawai tamkar bai jiba.
       Dole ta haƙura saboda motsin fara wankanta da tajiyo.
      “Mike damunsa kuma?” ta faɗa a fili cike da mamaki, kujerar gaban mirror ɗinta taja ta  zauna, bayan wasu mintuna kusan ashirin sai gashi ya fito yana tsane jikinsa da towel.
        Yanzun ma dai fuskar babu walwala, bai kuma kalli sashen da Shahudah takeba ya wuce wajen kayansa, jallabiya ya ciro a drawer, ya juyo zai saka suka haɗa idanu da Shahudah data kafesa da idanu.
        Janye nasa idon yayi  kamar bai ganta ba, saida ya saka jallabiyar a jikinsane ya ƙaraso gaban mirror ɗin yana ɗaukar turare zai fesa.
     “K bazaki tashi ki wanka ba kizo kiyi salla?”.
       Shiru kamar bazata tankaba, sai kuma ta sauke numfashi tana miƙewa, gabansa ta matso kamar zata shige jikinsa, ya ɗan matsa baya kaɗan yanda zasu sami tazarar data matse.
     “Humm” ta faɗa cikin kafesa da ido, muryarta a raunane tace, “Bb yanaga ka canja daga tashinmu? Naga cikin farin ciki muka shigo gidannan”.
      Turaren hannunsa ya ajiye, ya juya zai tafi ba tare da ya bata amsaba, saurin riƙo hannunsa tayi, bai juyoba, sai dai a hankali ya furta, “Karki ɓatan lokaci salla zanje”.
     Dole ta sakar masa hannu saboda fisgar da yayi, harya fice tana binsa da kallo.3

         A tsakkiyar falon ƙasa ya tsaya, ba tare da ya kalli ko inaba a cikinsa yace, “K fito, idan kuma kika bari na fito dake wlhy saikin raina kanki”.
      
    Mamaki ya kamani, dan ni dai bilynku banga alamar mutum a falonba, amma maganar Jawaad ta sakani waige-waige, a raina ina tunanin ko aljani ya gano.
        kamar da wasa kuwa saiga ɗaya daga ƴammatan gidan ta fito daga ƙasan bene jiki na rawa.
        Fitowarta yay dai-dai da sakkowar Shahudah da tai tunanin Jawaad ya fice.
      Jikin Amrah sai ɓari yakeyi, dan batasan ta yaya Jawaad ya ganta a falon ba, tunda ta rigasu shigowa shi da Shahudah.
         Juyowa yay ya kalleta da rinannun idanunsa masu firgitasu, yay mata kallon sakwan biyu ya janye yana kallon Shahudah dake tsaye jikinta sai tsuma yake dan tsoro, dan batai tunanin Jawaad zai ga Amrah ba.
       Murmushin takaici ya saki launin idonsa na sake yin duhu, ya nuna kansa cikin ɗacin da yakeji a zuciyarsa yana faɗin, “Ni kika kirama wata taga yanda zanyi kwanciyar aure da ke Hudah? Saboda kawai ki burgesu akan ina miki duk abinda kikeso ko? To gata nan, saiki zauna kafin na dawo massalaci ki ida sanar mata duk abinda ya faru a cikin ɗakin da bata ganiba”.
       Ya maida kallonsa ga Amrah itama, tana tsaye tamkar zatai fitsari a wajen dan firgita,  “K kuma yanzu nasan kin yarda inabin dukkan abinda takeso ko? Tunda na amince mata ta zubar da ciki, ta kuma gigitani da salonta a gabanki wanda yasa nake koma mata soko” yay murmushi irin mai nuna tsantsar takaici ɗinnan, kasa cigaba da musu magana yayi ya juya ya fita zuwa massalaci.1

            Wasu hawaye masu ɗumi suka gangaro a fuskar Amrah, lallai taji kunyar abinda ta aikata yau, takuma yi nadamarsa, bata san miyasa ta biyena Shahudah ba, yanzu da ace Yah Jawaad ɗin bai farga da itaba ya kuma biyema Shahudah a falo ɗin tamkar yanda taso da ta kasance azzaluma, dan dafa sai taga komai na sirrinsu…….
       Dafa kafaɗarta da Shahudah tayine ya katse mata tunani, ta kalleta cikin takaici tana janye hannunta.
     A zatonta zataga nadama a idanun Shahudah akan abinda sukaso aikatawa, amma sai taga saɓanin hakan.
     Cikin dariya Shahudah tace, “Wai wannan faɗan nasa kikema kuka? Tab amma baki da wayo, mutumin da a gabanki ya komamin ƙaramin yaro shine mazuransa yanzu zasu ɗaga hankalinki, wlhy naso ya biyemin kiga abin dariya, ashe shegen idonsa ya hangoki, ni……..”
      A harzuƙe Amrah ta ɗagama Shahudah hannu, “Ya isheki haka malama, ni wlhy bamma san bakida wayoba sai yanzu dana dawo cikin hankalina, bansan miya lulluɓe ganina ba har na iya yarda naga abinda zan shekara dubu ina nadama, Shahudah wannan ba wayewa baceba, dan ALLAH ki dawo akan ƙyaƙyƙyawan tunani na mutanen ƙwarai masu riƙo da addinin ALLAH, yanzu dan kawaifa ki birgeni kika jawoni nazo na laɓe dan naga yanda kike maida Yaya Jawaad kamar ba shiba a shinfiɗa, sirrinku, innalillahi, na shiga uku ni Amrah, wlhy naso tafka kuskure kam yau a rayuwata” da gudu Amrah ta fice daga falon tana kuka.
          Shahudah da jikinta yaso yin sanyi, amma zuciyarta dake ɗorata a shawarar banza tai saurin bijiro mata shaiɗaniyar shawarar da take bata sai tayi dariya tana taɓe baki, a fili tace, “Sun wani damu mutane da maganar sirri-sirri, uwarmiye sirri anan? Waima shegiyarnan Amrah da BF yafi talatin a cikin wayartace take faɗar kallonmu ni da Bb zaisata na dama, Mtsoooww aikin banza kawai, ni wlhy dama nayi mamakin yanda ya biyemin cikin sauƙi, mutumin da idan ina bukatarsa sai ya gama yanƙwalani kafin ya bani haɗin kai, amma ɗazun dandanan sai gashi ya miƙa wuya kamar yau ya taɓa sanina, munafiki kawai”.
    Ta ƙare maganar da juyawa ta koma ɗakinta.4

STORY CONTINUES BELOW

      
……………………………………………

            Dukkan abinda ya faru tsakanin su da Jawaad sai da suka sanarma Hajiya Humaira mahaifiyar Shahudah, ba karamin tashin hankaline ya risketa ba jin wai Jawaad ma ya bama Shahudah goyon bayan ta zubar da ciki.
    To mi kenan? Mi yake nufi? Bayason ya haihu da ita ko kuwa haihuwarce gaba ɗaya baya so?.
    Basu da mai basu amsa, shiyyasa suka shiga dogon tunani wajen tattaunawa da juna, harma suna tunanin ko dai Jawaad raina musu wayo kawai yakeyi, anya kuwa baisan wani abuba game da shirinsu akan sa?.
      Gashi ALLAH ya basu lusarar ɗiya da bata fuskantar komai na rayuwa sai wawanci, dolene susan abinyi akan Shahudah kafin ta aikata zubar da cikin nan, su kuma sake taku akan murɗaɗɗen halin Jawaad da duk bin ƙwankwantonka baka isa gane inda ya dosa ba kai tsaye.1

………………………………………….

         Bayan an idar da salla ne Jawaad ya shigo gidan, kai tsaye ɗakinsa ya nufa, shirin fita yayi, bai wani jimaba ya fito riƙe da takardu guda biyu a hannunsa.
     Ɗakin Shahudah ya shiga da sallama a ƙansan maƙoshi, bata amsaba, dan dama can ita bama damunta sallamar tayiba, idan kuma anyi mata bai zamar mata tilas ta amsa ba.
       Tana tsaye cikin ƙananun kaya sket da riga masu ƙyau, yanda sket ɗin yake har ƙasa ne ya tabbatar masa da shirin fita takeyi, dan sam Shahudah batajin kunyar fita anguwa daduk suturar data tare gabanta, indai ka cire waɗanda tasan sunyi ƙananu da yawa, amma ita dan ta saka wando da riga ma ta yana ƙaramin gyale wannan ba damuwarta bane, a ganinta ai tayi shigar mutuntawa ma.
     Kallo ɗaya tai masa ta ɗauke kanta, dan haushin abinda yay mata gaban Amrah ya sata jin haushinsa.
     Shima halin ko in kula ya nuna a kanta, ya ajiye takardun hannunsa saman tebirin gaban gadon tare da biro a tsakkiyarsu.
    Dukda ta gani sai bata kula saba, jakkarta ta rataya a kafaɗa fuska a ɗaure tace, “Ina kuɗin zanje wajen Doctor, dan wannan cikin yau bazai kwana a jikina ba”.
       Bakinsa ya taɓe yana mata wani kallon banza, yay taku biyu gira ɗaya a ɗage yana jan tsakin da ya shigar mata har ƙasan zuciya.
       “A tunaninki nima wawane irinki? a haukarki na yarda a zubda cikin ne da gaske? To lallai har yanzu ke bagidajiyace inhar maganata a gabansu zaisa ki aminta da ni har haka, Hudah! gane ainahin Jawaad abune mai matuƙar wahala ga kowa, ko ke da kikai kusanci dani na kusan watanni takwas baki iya fara nazartar komai game daniba balle su, hhhh tunanin Jawaad kullum banbanta yake da na kowa, wannan takardun biyu, ɗaya ta cak ɗin kuɗi ce, ɗaya kuma babu komai cikinta tana jiran abincine. Idan har kina kan bakanki na zubarmin da ciki bazan hanaki ba, ki faɗi adadin kuɗinma da kike buƙata zan rubuta miki kije ki zubar, ammafa zaki zubar da shine bada igiyar aurena a kanki ba, idan kuma kin shirya barinsa ki haifa kinada lasisin cigaba da rayuwar aurene da Muhammad Jawad Abdul-Aziz yusif kenan. zaɓi ya rage naki, kafin na dawo sai naji bayani akai”.
    Yana gama faɗa yay ficewarsa ya barta tsaye tamkar wata gunki……..1

_________________________
BILKEESU
_________________________

     …………Hanunta da ya sauka jikinane ya saka duhu mamaye ganina.
    
     Yanda Bilkisu taja wani nannauyan numfashi lokaci ɗayane ya saka Uwargida dake a fusace kallonta, hannunta ta janye da ga ƙirjin bilkisun tana maidawa saman fuskarta, sam bata numfashi.
     Uwargida taja tsaki tana sauka a gadon, ruwa mai sanyi sosai ta ciro a ƙaramin firij ɗin dake ɗakin ta ɓalle murfin ta watsama Bilkisu.
       Nannauyan numfashi Bilkisu tayi.
  
      Na buɗe idanuna da ƙyar bayan fitar numfashi na daya fara nisa daga gangar jikina, akan Uwargida dake gabana tsirara na saukesu, nai saurin maidawa na rufe jikina na wani azabar rawa, jin motsin zata sake dawowa kaina ya sani tashi cikin azama ina matse jikina da kare ƙirjina da ta yaga rigar ya fita fili.
        Cikin muryarta mai razanarwa tace, “Wacece ke? Waya turoki cikinmu?”.
        “Wlhy babu wanda ya turoni gareku sai ƙaddadarar rayuwa, dan ALLAH kirufamin asiri ki barni na tafi, wlhy bana buƙatar aikata wannan abun a rayuwata, na miki alƙawarin har duniya ta tashi babu maijin sirrinku a bakina hajiya”.
       Wata dariya ta saki tana matsowa jikina, murya ƙasa-ƙasa tamkar mai raɗa take min magana, “Ƴammata waya gaya miki muna tsoron sirrinmu ya fitane? Hakan ba matsalarmu bane, kisa a ranki kamar yadda ƙaddara ta kawoki cikinmu itace zata wajabta miki zama damu, kina da sura mai ƙyau da zaki mori lokacinki, matana biyar dana aura, nakumayi alƙawarin daga su bazan sake auren kowaba, sai dai ɗanɗano, amma ganinki yasa naji alƙawarina bazaiyi tasiriba, dan tun jiya dana ganki kika kwantamin a rai, da tsantsar kwaɗayinki na kwana a daren jiya, ki kwantar da hankalinki zan jiyar dake daɗi, tare da mallaka miki dukiya mai tsoka da saikin wucema tsaranki. Sonki da nake na gaskiya zai hanani yimiki fyaɗe, duk da kuwa kin ɓatamin rai da maganganun da kike faɗama yarana, da watace bakeba yau ta aikata hakan wlhy saina kasheta, amma ke bazanyi hakanba, bakuma zanyi mu’amula dake ta ƙarfiba, zan biki a hankali harki saki jikinki dani kema ki soni, dan haka daga yanzu kin dawo zama sashena”.
        Rumtse idanuna nayi da ƙarfi hawaye masu zafi dana tara a cikinsu suna rige-rigen fitowa, ta janye jikinta daga gareni tana sauka, riga mai igiya naga ta ɗauka ta sakama jikinta, ta buɗe ɗakin ta fita tana faɗin, “Ki buɗe drawer ɗinnan duk nau’in kayan da kike buƙata zaki samu a ciki, karna dawo na sameki kina wannan kukan, dan na tsani kuka, sunana Uwargidan farin ciki, burina kullum na saka duk wanda ya raɓeni farin ciki kawai”.
       Harta gama ɓaɓatun ta ta fice ban kalletaba, na kwashi kusan mintuna goma ina kukan nawa tare da sambatun yanda kullum duniyata ke garawa da sabon salo mai saka ruɗani, maimakon haske kullum duhu nake sake gani, maimakon fahimta kullum toshewar basira nake sake gamo dashi, maimakon canji kullum tsanani nake sake gamo dashi, maimakon cigaba kullum ci bayane yake zoma rayuwata, shin haka rayuwata zata ƙare kenan?. Na sake fashewa da wani irin kuka mai cin zuciya, jinake tamkar nama kashe kaina kozan huta ne.
     
       Ban sake ganinta ba, dan bata sake shigowa ɗakinba, ni kaɗai na wuni a cikinsa, nayi yunƙurin fita amma naji an kulleni ta baya, sai wajen ƙarfe biyu wani saurayi ya kawo min abinci, ni bamma taɓa ganinsa a gidanba, baimin magana ba ban masaba, ya ajiye ya juya ya fita abinsa, inaji ya sake kulleni ta bayan.
       Ko kallon inda abincin yake banyiba, danni yanzu komai na gidan ƙyankyaminsa nakeyi wlhy, tunda nasan kuɗin siyen komai ta hanyar wannan ƙazantar suka sameta.
      Gadonma tuni na sakko na dawo ƙasa na zauna, amma sanyin tayis dake shigata yasa na kasa jurewa na miƙe na koma saman gadon na zauna.
         Yunwa da ƙishirwa duk sun gallaba mini, rabona da abinci tun jiya da safe da su ƴar daɓas suka takurani naci indomie ɗinsu.
    Babu abinda ke tadani zaune sai salloli, har zuwa dare kuma ban sake jin motsin kowa ba a gidan, sai bayan isha’i saurayin ya kuma kawo min abincin dare, ya ɗauki kwanikan rana zai fita dasu sai yajisu da nauyi alamar banci abincinba.
    Ya ɗan kalleni da mamaki, kamar zaiyi magana sai kuma naga ya share, ya ɗiba kwanikan ya fita abunsa..
     Na darenma da ya kawo ƙin ci nayi, haka na kwanta abina da yunwa, dan harna fara sallar dare rashin ƙarfin jiki ya sani komawa na kwanta, dan nakasa tsaiwar, na komayi a zaune shina saina fara ganin jiri, dole dai na haƙura gaba ɗaya na zube a tsakar ɗakin barci yay awan gaba dani badan na shirya ba.

STORY CONTINUES BELOW

        Da asuba dana farka da ƙyar na iya gabatar da sallar asubahi, ina zaune ina addu’a Uwargida ta shigo.
    Batace dani komaiba ta wuce ciki, a gabana babu kunya ta cire kayanta ta ɗaura tawul ta nufi ban ɗaki.
    Bani da damar fita a ɗakin tunda a kulle yake, hakan yasa na maida kallona ta inda bazan gantaba koda ta fito.
     Ta jima a cikin bayin kafin ta fito, “Babyna kin tashi lafiya” ta faɗa cikin salon yaudara.
     Ba ƙaramin ɗacine ya mamaye zuciyata ba, hakan yasa nai banza da ita ban amsaba.
     A mamakina sai naji  tayi murmushi mai sauti, tace, “Karki bar wata ƙofa da zatasaka raina fara zafi a kanki kinji, ina sonkine shiyyasa kike samun sauƙi da ga wajena”.
        Daga wannan maganar bata sake tankaminba, tai shirinta cikin shiga ta alfarma tanata zabga kamshi, sai kace ba itace shugabar sheɗanun nanba.
     Gaban kwanikan abincin jiya taje ta buɗa, ganin banciba ne ya sata faɗin, “Kai-kai wai bayan ƙuntata kanki harma horon yunwa kikema Kanki? Rufamin asiri kar wannan ƙyaƙyƙyawan jikin dana ɗorama buri ya lalace matata”.
     Babu shiri na juya na kalleta da tsagwaron mamaki akan fuskata, wannan matar lallai zuciyarta ta rigada ta gama bushewa, idanuna da sukai nauyi kawai naɗan lumshe na maida kaina na jingina da gadon.
           Ƙamshin turarenta da ya yawaita a hancina da motsinta ya sani tabbatar da tana a kusa dani, hakan yasa naƙi buɗe ido, ta kama hannuna tana murzawa cikin wani salo na shaiɗanci.
       “Haba gimbiyar mata, kiyi haƙuri haka nan, dan bazaki taɓa kuɓuta daga gareniba, na rufe dukkan ƙofofin da hakan zata iya faruwa ma, ki cire komai a ranki ki bada kai bori ya hau kinji, idanma tsoron shiga wuta kikeyi ai kafin tsufa yazo mana zamu bari ko”.
         A hankali na buɗe idanuna saboda jin furucinta na ƙarshe, ba tare da na shiryaba na sakar mata murmushi ina kaɗa kaina a hankali, banso mata magana ba tsawon zaman da zanyi da ita, amma a wannan gaɓar sai na kasa jurewa hakan, “Hajiya waya faɗa miki anama ALLAH wayone? Wakuma ya baki albishir saikin tsufa zaki mutu?”.
     Hannuna ta saki da sauri tana ƴar dariya ta mike, “Humm Ustazu sauri nake, ajiye waɗannan tambayoyin naki kinji, ki daure kici abinci zanje anguwa na dawo, dan gobe ne za’a mana baiko ni da ke, sai kuma a tsaida ranar da za’a ɗaura mana aure”.
       Da kallo kawai na iya binta harta fice, inaji ta sake kulleni.
    Sam na nema hawaye na rasa a idanuna, kuma ko kukan zuci ma na kasa yi, ina nan zaune niba mai tunaniba ba kuma gunkiba har hasken rana ya buɗe sosai, saurayin dake kawomin abinci ya shigo ɗauke da ture a hannunsa, yanzunma baimin magana ba ya ajiye tiren ya ɗauki abincin daren jiya ya fice abinsa.
      Nima kala bance masaba, dan maganar da Uwargida ta ambatamin akan baikon nan ta toshe dukkan tunanina, ni Bilkisu mace ƴar uwata take dangatani da aurenta?.
       “Hummm” na faɗa a fili ina maida kaina na kwantar a jikin gadon, yanda cikina ke murɗawar yunwa ya sani jin ya kamata naci abincin koda kaɗanne.
      Tiren da saurayin ya ajiye na jawo gabana, na buɗe kular farko farfesune na naman kai, sai ɗayar kuma soyayyar doya da ƙwai, sai ruwan shayi a ƙaramin filas, an zuba kayan shayin cikin kofi da aka ɗoro a tiren.
         Takarda mai rubutu da aka shinfiɗa akan tire ɗince taja hankalina.
     Na ja kular da aka ɗora ta lulluɓe kusan rabinta gefe.

ALLAH YASA KIN IYA KARATU?
       Kar kiyi abinda wani zai fahimta akan takardarnan, dan ɗakinnan akwai cctv a ciki

     Abinda na fara cin karo da shi kenan a rubuce, hakanne ya sakani nutsuwa, naci gaba da ƙoƙarin haɗa shayi a kofin ina bin sauran rubutun ƙasan ina karantawa.
      
    Na miki alƙawarin zan taimakeki, saboda baki dace da zama a wannan gidanba, Uwargida mahaifiya tace, inason ki saki jikinki da ita, duk abincin dana kawo miki kicisa dan wlhy bazan cutar da keba, insha ALLAHU gobe idan munkai da rai zan kuɓutar dake a wajen bikin baikon sheɗancin data ambata miki, dan inhar zaki cigaba da ƙuntata kanki bazata bari ki fito a ɗakin nanba, in kuma har kina a ciki bazaki samu damar barin gidan nanba, sakin jikin da zakiyi kamar kin amincewa buƙatartane kawai zai taimaka mana.1

        Bansan wani nannauyan numfashi ya suɓuce mani ba, na share hawayen da suka kwaranyomin, cikin sauri na zuba abinci naci kamar yanda ya shawarceni, nakuma tashi na shiga wanka, dirowan tata na buɗe na ɗauki doguwar riga baƙa na saka.
      Ina nan zaune kusan sha biyu da rabi saurayin yazo ɗauke da wani abincin, nayi mamaki, dan ba’a irin wannan lokacin yake zuwa ba, sai dai zuciyata ta bani yanason fitar da rubutun da yayo minne, tattare kwanikan safen yayi, cikin wani dabara yaymin magana da idanu dake tabbatar min da abinda ya rubuto.
     Yanzunma daya fita dai sake rufeni yayi, banci abincinba har saida nai sallar zuhur.
      Zuwa yanzu naɗanji ƙarfin jikina, na gama babu jimawa Uwargida ta shigo, sosai mamaki na karanto a fuskarta gani na ba’a yanda ta barni ba.
       Ta dire jakar hannunta tana faɗin, “Babie kece kuwa?”.
       Cikin danne ɗacin da nakeji na kalleta da murmushi a fuskata, “Nice hajiya, bayan fitarki nayi nazari akan maganarki, sai naga ma to idan na matsawa kaina barinku ina zanje?, na amince da bukatarki kawai”.
         Shiru Uwargida tayi kamar bata amince da magana ta ba, sai naga ta nufi wata ƙofa, ashe nan ma ɗakine, kusan mintunanta goma da shiga ta fito, babu tsammani naji ta rungumeni tana murna sosai.

★★★★★

       Tun daga haka sai Uwargida taita nan nan dani kamar zata maidani ciki, tanayin wanka taja hannuna muka fito falon, falon nan ya haɗu, haɗuwar da idan na zauna misaltashi ma ɓata lokacine.
      Zuwa dare na sake gaskata maganar saurayin, dan kuwa ta gama amincewa dani, harda zaunawa tana ƙara bani sirrikan arziki dake cikin harkar tasu, ni dai jinta kawai nake ina sake neman tsarin ALLAH da sharrinta a zuciyata…………..✍🏻
https://youtu.be/5xN4SGMIzME

Garzaya ka saurari littafin  SAUYIN ƘADDARA💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

   ALƘALAMI TV ta shigo gari, tasha mai ɗunbin abubuwan ilmi, akwai littatafai na soyhayya da zasu dinga zuwa muku bisa tsaftataccen karatu, sai kuma gudunmawar hanyoyin da amarya da uwar gida zasu gyara jikinsu hankali kwance daga cikin gida basai wata taci ko sisinki ba.

Shin duk wannan gara ɓasar ka yarda ayita babu kai?🙆🏻🤔.

Maza garzaya ALƘALAMI TV dake dandalin manhajar youtobe kajiyo abubuwan bukatarka a sauƙaƙe.

Na zaune baiga gariba masoyanmu🤤🤤😋⛹‍♀⛹‍♀⛹‍♀⛹‍♀⛹‍♀

A danna mana subscribing domin tabbatar da ƙaunarmu😍😍❤❤😘😻😻👌🏻
2
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻

ƘWAI cikin ƘAYA!!
Bilyn Abdull ce

Shafi na goma sha biyar

………..Washe gari ma dai naga gata wajen Uwargida, yanda na saki jikina da ita sai itama ta sake yarda dani ɗari bisa ɗari, dan har barina tai naje wajensu ƴar daɓas.
       Yanda suketa sinne kai basason mu haɗa ido sai suka bani mamaki, amma sai ban nunaba, dan na lura kunyata sukeji.
     Nima dai a kunyacen nake dasu, amma sai na dake tamkar baniba, nanko ƙasan zuciyata a matuƙar tsorace nake da kowa na gidan, nakan danne zuciyata bana kukan zahiri sai na zuci, tunanin iyayena dasu Firdausi yana sake gallabar zuciyata.
       Tun a yammacin ranar naga anata shigowa da drinks da wasu kayayyaki a kwalaye, tsoro ya sake kamani, danfa tabbas da gaske wannan sheɗaniyar takeyi, cigaba nai da neman tsarin ALLAH da sharrin kowannensu a zuciyata.
+
        ★★★★★★

Washe gari aka tashi da shirin baiko kamar yanda Uwargida ta faɗa, tun da rana manyan hajiyoyi suka fara isowa gidan, abin idan ka gani zat tashin hankali, sam banyi tunanin wannan ƙazantar tayi girma da yaɗuwar haka a cikin al’ummar musulmai jinin hausa fulani ba, wanda ma baka taɓa zato ko tsammani ba saika ganshi a wajen.
     Yara ƙanana ƴammata duk an tsundumasu wannan ƙazamar harka, mafi yawansu kuma saboda abin duniyane, gashi idan kana sauraren hirarrakinsu zaka fahimci sanadin waya suka haɗe da hajiyoyin a yanar gizo, bansan hawaye sun fara wanken fuskaba, sai da naji ɗigarsu akan hannuna, nai saurin gogewa ina haɗiyar rai.
        Kowa ya ganni sai ya yabama ƙoƙarin Hajiya, suna kurantata wai ta more, dan inada karuwan jiki, dukda ba wata ƙyaƙyƙyawa bace a fuska kuwa.
          Wasu mata kuwa su biyu sai hararata suke, ni ban saniba ashe wai matan hajiyarne, waisu nan kishina sukeyi.
    Kai jama’a, ALLAH kai mana tsari da asararriyar rayuwa dai.4

      Anmin wankin kai saikace wata amaryar data samu miji, sannan aka kawo mai kwalliyar da zatamin, bansan yanda zan musalta muku ɗunbin tashin hankalin da nake cikiba a wannan lokaci har aka gama kwalliyar.
      Duk wannan shiri da akeyi bikin zai gudana ne bayan sallar isha’i, amma abinda zai baka tsoro babu wanda naga yayi salla a cikinsu koma ambatarta a bakunansu.
      An kawomin wata riga mai ƙyau da zan saka, harda takalma da sarƙa da nake zaton ta gwal ce, dan ƙyawunta a ido kawai ya isa ka shaida hakan.
        Dakatar dasu nayi akan inason sai nayi sallar isha’i, da mamaki kuwa sai naga abun ya basu dariya, ni dai ban kulasu ba naje nai sallata, bayan na idarne na duba takardar da saurayinnan ya bani ɗazun da rana a ɓoye, bayanin danaga yayi a ciki ne ya sakani miƙewa da sauri, kaya na buɗe drawer ɗin Uwargida na ɗauka, na saka tare da gyara jikina tamkar ba niba, a yanda na fito inba sani kaimin na tsiyaba bazaka taɓa gane niceba, balle dama tunda akaimin kwalliyar babu wanda ya ganni a cikinsu har Uwargida.
         Cikin taimakon ALLAH na fito falon cikinsu ina taku da yauƙi, na saki jikina tamkar nima irinsu ce, duk da na fahimci wasu suna min kallon rashin sani, amma  harkar ta wayewace sai kowa ya amsheni ba tare da bincikeba.
        Uwargida ta miƙe akan zataje ta fito dani, hakan yasa wasu manyan mata suka bita ɗakin, suna shiga watar gidan na ɗaukewa baki ɗaya.
      Jikina har rawa yake na ajiye takalma da jakka tare da sarƙar danasa ta gwal ta uwar gida na fito da lalube, dan dama a hanyar ƙofar fita na zauna kamar yanda saurayin ya shawarceni.
     Ina fitowa kuwa ana kama hannuna, cikin raɗa yace, “Karki damu nine”.
       Bansan inda muke jefa ƙafa ba, kasancewar gidan babban gidane, maido wutar da akayine ya saka gabana faɗuwa, ni dashi duk mukaja birki ba tare da mun shirya ma hakanba.
      Surutai muka fara jiyowa wanda da alama ni suke nema, wasu na faɗin ta gudu, wasu na cewa ai da alama wata baƙuwace data shigo ta saceta kota kuɓutar da ita, dama su basu yarda da baƙuwar fuskarba.
     Cikin hanzari yaja hannuna muka faɗa ɗakin mai gadi dake a bakin gate, hawaye kawai nake jikina na rawa.
      Duk bidirin nemana da sukeyi muna jiyosu, wata naji tana tambayar Uwargida ko ina Sani?.
      Uwargida tace tun da rana ta turashi can wani ƙauye danya bar gidan ma tace ya kwana acan da safe ya dawo.
     Kallonsa nayi, dan da alama na lura shi ake nufi, kenan wasu sun fara zargin akwai saka hannunsa.
    Tun suna ɗaukar neman nawa wasa har abun ya fara caja musu kai, dan haka suka rabu, akabar ƙalilan a cikin gidan, ɗaukar kowa na fice, saboda sun iske gate buɗe.
     Saurayin ya ɗan leƙa ta Window, sai da ya tabbatar babu kowa kusa yay min nuni muje, hijjab ya bani na saka, ta bayan ɗakin mai gadin muka iske tsani, duk da tsahon katangar nan haka na hau tsanin nan ga tsoro na cina ga hawaye, da taimakonsa muka dira can baya, dayake ta canma ya saka tsani, kuma akwai abokinsa dake tsaye yana jiranmu.
     Duk naji ciwo a jikina, amma sam tashin hankalin da nake ciki baisa na damu da ciwukanba.
          Babu ɓata lokaci muka bar wajen, muna matsawa muka jiyo hayaniyar su Uwargida suna faɗin “tanan ta biyo” kugafa harda tsani, aiko tabbas akwai waɗanda suka taimaka mata ta gudu kenan. Buɗar bakin wata sai naji tace “kodai su ƴar daɓas ne”.
       Bamu jiyo amsar da Uwargida ta bata ba mai adaidaitar da suka sakani ciki yaja yay gaba.
      Na damƙe jakkar da saurayin ya bani a jikina sosai ina cigaba da yin hawaye, yanzu kuma ko ina zan dosa kenan?.
     Wata zuciya ce tace, “Bilkisu duk kibar wannan guje-gujen, kibi shawarar zaɓi biyu, kodai ki miƙa kanki ga ƴan sanda, kokuma ki nema gidan ƴan uwan mahaifinki ko mahaifiya kije ga wani, idan sun riƙeki shikenan, idan sun nuna bazasu iyaba sai kisan mafita”.
      Wannan shawara itace tai tasiri a raina, koda mai napep ya tambayeni batare da na shiryaba na faɗa masa anguwar da zai kaini.
    Ganinai ya tsaya da napep ɗin yana kallona, “Hajiya kinsan kuwa mi kike faɗane? Anguwar nan gaskiya tana da nisa, nikuma wanda ya bani ke ya cemin tashar mota zan kaiki”.
     Hawayen fuskata na share, murya na rawa nace ka taimakeni bawan ALLAH, kaga ni mace ce, tashar mota kuwa wajene mai haɗari musamman da daddare, amma anguwar da zaka kaini yanzu akwai wanda na sani, wajenta zanje kafin safiya idan ALLAH ya kaimu”.
      “Gaskiya Hajiya bazan ɓoye mikiba, a darennan bazan iya zuwa har canba, yanzu idan mun tafi sai mukai goma na dare bamu isaba, to yaushene na ajiyeki harna juyo nikuma na dawo gida. Ki dai faɗi wani wajen bayan wannan ɗin”.
         “Shikenan na gode” nai maganar cikin jan majina ina sharce hawaye, zuwa can wani tunanin ya sake faɗomin, bara naje gidan Inna zainaba, ko arziƙin kwana ɗaya tamin, da safe saina doshi gidan baba manu ɗin da nai niyyar zuwa, duk da dai bana zaton samun alfarma daga ko ɗayansu, amma zan gwada, karya zam na yanke hukunci akan gaibu.
     Sake faɗa masa anguwar da zamuje nayi, dan haka ya tada napep muka cigaba da tafiya, sai yake cemin to ai shima cannema anguwarsu.
     Wani daɗine ya kamani, dan dama dai bawani iya gane gidan inna zainaba ɗin zanyiba sai na haɗa da tambaya.
     Shiru mukai na wasu mintuna, lokacu-lokaci ina cigaba da sharar hawayena.
    Muryarsa na tsinkayo yana cewa, “Baiwar ALLAH kibar kukannan, ita rayuwa duk jarabawace, haƙuri kawai kesa a cimma buri, da alama dai wanda ya sakaki a keken nan mijinkine ko?”.
       Shiru na masa ban tankaba, jin haka shima sai ya tsuke bakinsa, mun ɗan ƙara tafiya na sake jiyoshi yana faɗin, “Dai-dai ina zan ajiyeki baiwar ALLAH?”.
        Muryata a dasashe saboda kukan dana sha nace, “Kace nan anguwar kake ai kaima? Dan ALLAH ko kasan gidan dogo kafinta?”.
     Da sauri ya juyo ya kalleni, bakinsa har harɗewa yake wajen faɗin, “Can gidan zakije?”.
      “Eh” na faɗa cikin mamakin razanar danaga yayi.
     Yace, “Kai, to ai babanane dogo kafintan hajiya? Dan ALLAH kozan iya sanin ke wacece?”.
      “Gidankune? To ko dai Yaya Shu’aibu ne?”.
     “Ikon ALLAH, tabbas kuwa kin canka dai-dai, Shu’aibu ne kuwa, wacece ke dan ALLAH? daga ina kuma?”.
      Murmushin yaƙe mai haɗe da takaici nayi, ganin yanda taɓarbarewar zuminci tasa ko juna bamu saniba dukda kusanci mai ƙarfi da muke dashi, shi kansa sunansa kawai nakeji a bakin Innata, amma ban taɓa ganinsa ba a ido, “Da wahala ka sanni, sai dai bansan ko kasan Asiya gurguwa data rasu kusan shekara ɗaya kenan?”.
       “Tabbas na santa, dan gwaggona ce ma ai, tunda ƙanuwar innatace”.
     Murmushi nayi mai ciwo, na maida kallona ga wata tukubar mai nama da muka tsaya dai-dai satinsa, mazane cike da wajen saboda mai shayi dake gefe, daga can kuma gabansu kaɗan mai doya da ƙwai, zaman masu wannan sana’a ne ya maida wajen dandali, harda masu suyar awara, gaddamar siyasa kawai kake jiyowa a wajen kamar zasu fara danbe, cikin share hawaye nace, “To ita mahaifiyata ce, ni kaɗaice kuma ƴarta tilo data bari a duniya”.
        Jinai kawai yanata jero salati da sallalami, na maida hankalina sosai a garesa, cike da tsagwaron mamaki yace, “Yanzu nan dama Gwaggo Asiya nada ƴa amma ban saniba? Har tambaya nayi wlhy a randa mukaje zana idarta sai akace ai bata haihuba, to kodai dama baƙya tare da ita?”.
      “Muna tare” kawai na iya cemasa saboda abinda ya tokaremin maƙoshi.
     Saurin tada Napep ɗin yayi yana faɗin, “Kinga yi haƙuri na tsareki da tambayoyi a titi, muje gida duk a yisu…………
STORY CONTINUES BELOW

________________________
JAZUGA
________________________

            Alhaji, ina baka shawara muyi amfani da maganat likitannan, gara ka ɗauke yaronnan ya koma yin jiyya wani waje, mukuma saimu fito mu sanarma duniya ya rasu, a ajiye wata gawar a maimakonsa kamar yanda mukai na yarinyarnan.
      Wlhy wannan sabon d.p.o ɗin baida mutunci, sannan baya amsar cin hanci, kaga dai yau kwanansa uku kawai da kawowa ko? To wlhy harya lalata wasu ɓoyayun cases guda huɗu da wancan d.p.o ɗin yaci ƙuɗi a kansu, to kaga kafin yazo kan bayanan case ɗin yaronka gara dai musan mai yuwuwa. Saboda tsaf zai gano gaskiya ta tashi mana mu duka wlhy”.
     Wani irin nishin damuwa Alhaji lado yaja, yace, “Zanbi shawararku, amma lallai naso ace burina ya cika an kama yarinyarnan, dan shine kawai zai kawo ƙarshen wannan case ɗin”.
      “Indai dan kamatane karka damu, zamu cigaba da ƙokari har sai mun ganta, kuma bazamu bartaba, tunda kaga yanzu kowa zai ɗauka yaronka ya mutune ai”.
     “To shikenan yallaɓai, nagode sosai da ƙoƙarinka, zan shirya mota a darennan abar asibitin da Jazuli, da safe kuma saiku bamu sabuwar gawar a maimakonsa”.
        “Hakan yayi Alhaji, na barka lafiya”.

    Bayan tafiyar ɗan sanda Alhaji Lado yata kai kawo akan zancen, tsarin likitan shima ya masa, amma fa yana burin a kama yarinyar kodan ya wulaƙantata, ya ɗaukama yaronsa fansa.
Nace, “Humm”.

     Duk yanda suka shirya haka aka tsara, washe gari saiga gawa a zuwan ta jazuga, mutane da yawa sunyi farin ciki, dan koba komai saji sakat, waɗanda sukaima wannan muwa kuma mutanene ƙalilan, suma na jikinsa, mutanen gari dai ko a fuska basa nuna jin kunyarsu akan gakan.
     Haka akayi zana idar gawa aka kaita makwancinta, yayinda acan bayan fage Jazuga ke cigaba da jiyya.

★★★★

     Haka abubuwa sukaita shuɗawa, jikin jazuga na samun sauki, sai dai da alama dukan da Bilkisu tai masa ya taɓa masa ƙwalwar kai, dan idan abun ya motsa haka zaita dukan kansa yana wata irin ƙara har sai an bashi maganin barci, idan kuma ya farka sai ka ganshi normal sai kuma ya sake motsa masa.
         Sunje asibiti akan matsalar, suma dai magani suka bashi, tare da tabbacin inhar yabi soka komai zai dai-daita.
      Dalilin sun sanarma duniya Jazuga ya mutu dole ya haɗa kayansa da yaransa suka bar garin akan sai komai ya lafa zai dawo.
     Wannan abu ya sake masa ciwo, tare da dasa tsanar Bilkisu mai tsanani fiye da farko ma a zuciyarsa, yakuma saka a ransa duk randa suka haɗu kasheta kawai zaiyi kowa ya huta.
😱🙆🏻‍♀️.

_________________________
JAWAAD
_________________________
                 Duk da ɓacin ran Shahudah daya fito dashi a rai, hakan bai hanashi zagewa ya maida hankali akan aikin da suke son farawa ba shi da su Aliyu abokansa.
       Duk suna zaune ne a cikin falon gidan da ya kaisu, Jawaad yace,
      “Tabbas a cikin satar kokino akwai lauje cikin naɗi, kuma tare dana kusa dashi akai hakan, bayanan dana samu yanzu haka sune, tare da amaryarsa suka dawo daga ƙasar Colonbia, kowa ya kasa gane yanda har aka sacesa babu wanda ya gani, hakanne yasakani ɗaura alamar tambaya akan wannan matar tasa, lallai tasan wani abu akai, dan a yanda tsarin saukarsa da baro airport ɗin ta kasance babu wani mahaluki dazai iya kutse wajen aikata hakan, kunsan a yanda tunanina da nazarina ya bani an sacesa?”.
      Dukansu kai suka girgiza masa cike da mamakinsa, duk da dai dama sunsan Jay mayene akan bincike da bin ƙwanƙwanto.
    Murmushi yayi yana komawa jikin kujera ya kwanta, sai kuma ya tashi zaune sosai fuska a haɗe yana tsaresu da idanu, “Tabbas lokacin da aka faɗi sacesa yana cikin gidansa ne, daga baya aka fita dashi acikin gidan”.
      “Kamarya kenan Jay? ALLAH ka sakamu a duhu, danni kam wannan case ɗin ban fahimci komaiba akansa, tayaya hakan zata kasance bayan kowa ya shaida Alhaji Kokino lafiya ya fita a jirgi, agaban kowa kuma ya shiga mota direbansa yaja shi, kuma basu tsaya ko inaba sai a cikin gidansa………”
     Cikin katsesa Hafiz yace, “Ni kasan mina fahimta Jabeer, kamar Jay kanason kace mana dai babu wanda ya sace Alhaji Kokino ko? Kawai matarsa tayi ƙarya da hakanne saboda wani dalilinta ko manufa ko?”.
       Kai Jawaad ya shiga girgizawa, ya miƙe tsaye hannunsa goye duka a baya, “Fahimtata tasha banban da taku, nakula kuma irin Fahimtar da sauran jama’a sukaima abin kukeyi a yanzu, “Tabbas an sace Alhaji Kokino da gaske kamar yanda zancen ya fita duniya taji”.
        “To waya sacesa kenan? Miyasa kuma ka kawo matarsa cikin zancen?”.
      Aliyu daya tsare Jay da idanu ya faɗa.
      Murmushi Jay yayi kawai ba tare daya amsawa Aliyu tambayarsa ba, ya taka a hankali zuwa gaban Window yana leƙa harabar gidan, kusan sakwan goma kafin ya juyo gasu Jabeer da suka zuba masa idanu kamar wani magiji.
       “Aliyu wannan shi nake so ku fahimta nima? Ni kaina inason nasan miyasa matarsa ta shigo cikin zargina”.
     Dukansu ajiyar zuciya suka sauke.
         Hafiz yace, “To yanzu dai saimu tsunduma aiki kawai, sai dai ina ganin Jay lokaci yayi da zaka yafema Rose ta dawo tare damu, kowa yasan amfaninta a cikinmu, bai kamata muyi sakaci da itaba ko a wannan lokacinma”.
     Gaba ɗaya fara’ar fuskar Jawaad ta ɗauke, sai dai baice komaiba ya tako ya dawo wajen zamansa ya sake zama.
     Maimakon ya taya zancen Rose da Hafiz ya ɗakko sai ya ɗakko wani maganar daban ma.
     Sunsan bazai tankaba, dan wannan salonsa ne idan baya buƙatar abu, suma duk sai suka ƙyalesa kawai akan zasu cigaba da lallaɓashi har itama Rose ɗin ta dawo tare dasu su koma su biyar ɗinsu tamkar yanda suka saba a baya…..

1
_________________________
SHAHUDAH
_________________________

          Tunda Jawaad ya fice tai tsaye a wajen, bata motsaba amma ta dasama takardun daya bari manyan idanunta.
      A wannan yanayin Hajiya Humaira tai sallama ita da ƙanwar Shahudah ɗin mai suna Aamila.

       Ko kusa bataji motsinsu ba, sai da Hajiya Humaira ta taɓata ne tai saurin juyowa a tsorace, dan tazata Jawaad ne ya dawo.
     Ajiyar zuciya ta sauke tana faɗawa jikin momynta ta fashe mata da kukan shagwaɓa…………✍🏻
https://youtu.be/5xN4SGMIzME

Garzaya ka saurari littafin *SAUYIN ƘADDARA*💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

*_ALƘALAMI TV_* ta shigo gari, tasha mai ɗunbin abubuwan ilmi, akwai littatafai na soyhayya da zasu dinga zuwa muku bisa tsaftataccen karatu, sai kuma gudunmawar hanyoyin da amarya da uwar gida zasu gyara jikinsu hankali kwance daga cikin gida basai wata taci ko sisinki ba.

Shin duk wannan gara ɓasar ka yarda ayita babu kai?🙆🏻🤔.

Maza garzaya ALƘALAMI TV dake dandalin manhajar youtobe kajiyo abubuwan bukatarka a sauƙaƙe.

Na zaune baiga gariba masoyanmu🤤🤤😋⛹‍♀⛹‍♀⛹‍♀⛹‍♀⛹‍♀

A danna mana subscribing domin tabbatar da ƙaunarmu😍😍❤❤🥰🥰😘😻😻👌🏻

Nayi Busy ne da yawa, shiyyasa baƙwa ganin posting sosai🤦🏻
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page