KOMAI NISAN JIFA CHAPTER 8

 KOMAI NISAN JIFA CHAPTER 8

Tun daga wannan rana Atif yaci gaba da zama a gidansu Mubeenat har’i zuwa yanzu.

Shine mai kaisu makaranta ya kuma d’auko su,hakan baisa yabar Aisha ba duk haka yake hidima dasu tare da nuna musu k’auna sosai.

Haka kuwa zai kaita gidan friends nata koda biki akeyi ko wani hidima duk shine komai nata a yanzu,hakan yasanya Mubeenat sakewa da Atif kuma sabon shak’uwa ya k’aru a tsakaninsu wanda ita Umma harta fara tunanin ko soyayya ce,se daga baya ta gane cewa kawai soyayyace ta Yaya da K’anwa.

Gidan su Amal kuwa yau kusan sati biyu kenan amma Samira batayi batun tafiya ba,kuma Umman Amal ta samawa Sagir aiki yana samun kud’i har yayi clean.

Duk wani shiga da fice da Abban Amal yakeyi a wannan gidan akan idon Samira,har tana sha’awan inama da itace take auransa,dan gidan da tayi aure daga farko sam bataji dad’i ba.

Wata rana suna hira da k’anin nata Sagir inda yake cewa “Toke yanzu yaushe zaki tafi kiyi aure?”

“Kai dalla rufe min baki,kana nufin zan bar nan ne?”

“To dama anan zakici gaba da zama?”

“Wlh babu inda zani kana gani muna cin bulus mun huta da biyan haya ganka fa yadda kayi fresh ai wlh Sagir bank’i ace Abban Amal ya aureniba tunda dama mu k’awayene kaga shikenan zamuyi zaman lafiya kaima kuma ci gaba zata sameka kome ka gani?”

“Tabd’i! Lallai baki da hankali,yanzu har kina tunanin Mijin k’awarki zai aureki?”

“Eh mana inda rabo wlh sekaga abu ya yuwu”

“Hhhhh wlh kinban dariya,ki ganshifa ki kuma kalli k’awarki da ‘yarta duk sun fimu da komai.”

“Kaifa har yanzu baka gama wayewa ba Sagiru,ai inda kud’i ya zauna wlh duk clean zamuyi harma mufi ‘yan gidan,kuma kaima base ayi na gidaba da Amal gata kyakkyawa mai kama da mamanta”

Nanne Sagir ya washe baki “Amma fa kince wani abu,sedai kuma ni nfi son k’awarta Mubeenat kinga ita iyayenta masu kud’i ne sosai se muyi auren jari”

“Kai rufa min baki gara muyi dai-dai ruwa dai-dai tsaki ina kai ina wannan Mubeena take ko Mubeenata,wannan Yayan nata ma kad’ai ya isheka wlh kanaga koda yaushe suna tare karma ka fara ka rufa mana asiri Amal d’inma ai tafi k’arfinka dandai muna gida.”

Haka dai sukaita hirarsu suna tsara yadda za’ayi, “Sagir yace indai zan auri Amal kibar komai a hannuna sekin zama Amarya a gidan nan wlh”

“Yawwa d’an uwa shiyasa ai bana son rabuwa da kai duk lalacewa gara muna tare”

“Wannan haka yake,yanzu wani Malami zamu samu dazai mana komai cikin sauk’i”

“Kasha kuruminka ai dole ka koma k’auyenmu gun Malam na ruga kamishi bayanin komai sannan ka ajiye mishi kud’i shikenan an gama”

“Wlh kamar kina raina,gobe zanyi sammako inje in dawo da wuri,amma fa kema zaki kawo wani abu yanzu agurin ki”

“Karka damu mu had’u da daddare zan baka,ai kasan Abban amal d’in akwai kyauta hakama ita k’awar tawa duk tara kud’in da suke bani nake yi”

“Yawwa tose daren kenan.”

Haka suka rabu da wannan shawaran nasu washe gari da safe kuwa ya d’au hanya se gun Malam na ruga.

Bayan ya gama yiwa Malam na ruga bayanin komai shine Malam yace “Wannan abu ne mai sauk’i mazargin wandonsa kawai nake so ka kawo min akwai abinda zanyi dashi idan ya kwana d’aya aguna seka mayar ka kuma tabbata ba’a wanke mazarginba kafin yasa.”

“Bakomai dama tunda mukaje gidan nace ya dena kai wanki zan dinga mishi harda gugama ni nake mishi,dan haka zanje in kawo maka yau d’innan.”+

Sagir yana dawowa gida ya tambayi Umman Amal “Aunty nace kayan Alhaji bai taru bane in wanke?”

“Haba Sagir ka dinga hutawa mana”

“Ai dayake yau d’in ina hutu ne nace gara in rage wankin”

“To shikenan bari na fito maka dasu”

“To Aunty” sannan ta wuce ta d’ibo mishi kala biyar ne ta zuba a k’asa ya kwashe yayi gaba.

Seda ya gama wankin tas ya shanya sannan ya faki ido babu kowa atsakar gida ya zaro mazargin wando d’aya ya nufi k’auye segun Malam na ruga.

“Gashi Malam anyi dace”

“To shikenan kaje se gobe da yamma ka dawo”

“To Malam nagode”

Washe gari da yamma ya koma ya k’arb’o inda Malam yace “Ka lura dakyau duk randa yasa wannan kayan to a wannan ranan zakaga aiki tashi kaje”

“To Malam godiya muke sena sake dawowa.”

Sagir yana dawowa ya kwaso kayan yasa mazargin daya ciran sannan ya gogesu tas da dutsen guga yaje ya kaiwa Umman Amal,inda tace Amal ta karb’i kayan takai d’akin Abbanta.

  Bayan sati biyu dayin hakan kenan Abban Amal baisa kayan ba.

  

Acikin sati na Ukkun ne Abbi d’in Farhan da Ummin shi da Abdullahi d’an Yayan mamanshi se kuma Kakansu dashi kanshi Farhan d’in suka sauka a garin Abuja,daga nan kuma suka sake shiga jirgi zuwa Gobme inda su Abban Mubeenat da Yaya Musty da kuma Atif da Shureim sukaje tarar su.

Umman Mubeenat kuwa se kici-ciki sukeyi a kichine ita da Mubeenat da Amal suna had’a musu abinci wasu a parlour’n Umma akan daining wasu kuma acan parlour’n Abba.

Bayan sun gama kimtsa komaine suka wuce shiryawa dan duk sunyi wanka dama,Amal ma gida ta wuce taje ta shirya sannan ta dawo suna zaman jiran isowar bak’i.

“Wai haka zaku bar fuska fari sol babu ko kwalli?” Cewar Umma.

Dariya kawai sukayi batare da sunce komai ba suka wuce d’akin Mubeenat suna dariya.

“Nidai wlh bazanyi wani kwalliya ba sekace zamuje biki” cewar Mubeenat.

Amal ma dariya take “Dama nikam kunce natural face na yafi min kyau dan haka ke sekiyi d’an ado”

“Wlh babu abinda zansa” suna dariya se sukaji sallamar Aisha.

“Bak’in basu iso bane har yanzu?”

“Eh anje d’aukosu dai”

“Ina Umma?”

“Tana ciki”

“To bari naje mu gaisa tukunna karku isheni da surutu banje na gaisheta ba.”

Sauk’ansu kenan suka fito inda su Abba suka hangosu tun daga nesa,Shureim yace “Ya Atif wa’incan turawanne bak’in namu?”

“Hhhh ba Turawa bane Larabawane su.”

Da sauri su Abba suka nufesu cike da Murna suma kuma haka.

Tun daga nesa Farhan ya hango Shureim yana rik’e da hannun Atif,a hankali ya fara mishi murmushi tare da cewa “Shureim right?”

Murmushi Atif yayi tare da cewa “Yeah it’s him,you’r all wlcume”

“Thanks” cewar Farhan sannan ya kamo hannun Shureim yana mishi magana cikin harcen turanci,shi kuwa Shureim se bashi amsa yakeyi tare da k’ura mishi ido kamar zai had’iye shi.

Sanda sukayi musu sannu da zuwa sannan suka nufi gun moto suka wuce zuwa gida.

Gidansu Amal kuwa yau dai wannan kayan Abbanta yasa.

Kuma tunda yasa kayan se yaji wani iri kaha a jikinsa “Hajiya”

“Na’am Abba Amal harka shirya zaka fita kenan?”

“Eh zan fita ina Samira fa?”

“Samira kuma?” Ta tambaye shi.

“Eh ya kamata na ganta ai kafin na fita”

Mamakine sosai ya kama Umman Amal dajin abida yake fitowa daga bakin mijinta.

“To muje zuwa waje sena mata ganaga ko?” Cewar Umman Amal.

Nan ya fara washe baki yana cewa “To,to shikenan muje”

Haka suka fito tana gaba yana biye da ita a baya “Samira” Umman Amal ta k’wala mata kira.

“Na’am gani”

Nan Umman Amal ta kalli Mijinta “To gata nan Abban Amal”

Yaci gaba da washe baki “Dama cewa nayi a kiraki muyi sallama nizan fita”

Daga ita har Umman Amal mamakin jin kalamansa sukayi,amma acikin zuciyarta cewa tayi “Lallai aikin Malam na gura yayi kyau” a fili kuma se tace “To Abban Amal Allah ya kare,sannan ta mik’e ta wuce ciki yanata binta da kallo,ita kuwa Umman Amal aka barta da kallon mamaki “Tofa miye kuma hakan kenan ni Zainabu…?”

Hon d’in motoci dasu Mubeenat sukajine yasasu fitowa zuwa harabar gidan.
Tun daga nesa Farhan yake kallonsu dukkansu ukku yana tambayar kansa wacece Mubeenat acikinsu,dan rabonsa daya ganta tun tana 13 years.
Gun motar suka nufa cike da murna suna musu sannu da zuwa.
Bayan duk sun fitone Ummin Farhan tace “Where is Mubeenat?”
Matsowa Mubeenat tayi zuwa gareta tare da rik’e hand bag d’in hannunta tace “I’m here”
Kallonta su Farhan da Abdullahi sukayi suna mamakin girman ta.
“Mubeenat kece kika girma haka?” Cewar Abbin Farhan.
Cikin jin kunya tace “Sannu da zuwa Uncle”
“Sannu Mubeenat lallai semun sha bikinki kafin mu koma”
Nan dai aka sa dariya sannan Abba yace “Bismillah mu isa”
Mubeenat se bin Farhan da Abdullahi take da kallo tana sak’ar zuci “To waye Ya Farhan d’in a cikinsu?”
Haka dai suka wuce parlor’n Abba,su Ummin Farhan kuwa suka wuce parlour’n Umma.
Seda sukayi sallah sannan Atif yayi serving nasu,canma dai Mubeenat ce ta zubawa Ummin Farhan tare da kallon screen d’in wayanta dake ajiye a gefe,fuskar d’aya daga cikin maza biyun nanne ta gani akai dan haka Mubeenat tasan cewa lallai shine Farhan.+
Farhan ya kalli Abban Mubeenat yace “Uncle can i get a coffee?”
“Sure my Son” sannan ya kalli Shurim “Kaje kace Mamana ta kawo musu coffee”
“To Abba” sannan ya fice da gudu alokacin Mubeenat ta shiga toilet,dan haka Aisha taje ta had’a takai musu.
“Thankyou” cewar Farhan
“Wlcum” tace sannan ta fice.
Haka sukaita hira ana cin abinci daga nan kuma Atif yayiwa su Farhan jagora zuwa d’aya b’angaren da yake zaune dama akwai d’akuwana da toilet nasu masu kyau ba laifi dan gidan a tsare yake sosai.
Su Abba suna cikin hira a parlour’nsa shida Abbin Farhan da kuma Kakansu se Ya Musty. Sallamar Abban Amal suka jiyo,nan ya shiga suka gaggaisa sannan ya zauna anata hita.
Idanun Kakan Farhan gabad’aya akan Abban Amal yake,dan shi kanshi Abban Amal d’in se daya tsargu da irin kallon da yaga wannan tsohon yana binsa dashi.
Bayan an fito sallan magariba ne Kaka ya keb’e da Abbin Farhan yace “Wannan Mutum daya shigo waye shi?”
“Mak’ocin sune ana zaman mutunci sosai dasu ga gidansa nan babu nisa dasu” cewar Abbin Farhan.
“To akwai asiri a jikinsa”
“Subhanalillahi,asiri fa kace?” Abbin Farhan yasan lallai gaskiyane tunda daga bakin Kaka yaji,danba yau ya fara gane hakanba shiyasama ya yadda da maganan Kaka,amma kuma mamaki yaketayi a zuciyarsa to waye ya masa asirin?”
Kaka ya katseshi da cewa k’warai kuwa asiri mai muni ma kuwa,dama kuma ana haka sosai ne ta nan?”
“Wlh Kaka nidai ban saniba,tunda ban tab’a ganiba sedai naji wai-wai”
“To Allah ya wuce mana gaba”
“Ameen” sannan suka dawo gida.
Ya Musty yace “Abba mu zamu koma zan wuce da Aisha”
“To Mustapha mungode Allah ya kare a gaida Iyalai”
“Ameen Abba zasuji insha Allah” sannan yama sauran sallama suka tafi tare da Aisha.
Amal ma ta mik’e inda suka fito tare da Mubeenat zata rakata gida.
“Sis Mubee ina zakije?” Atif ya tambaye ta
“Zan raka Amal gida ne”
“Ok” sannan suka wuce suna hira.
“Mubee yau gamu ga larabawa”
“Hhhh wlh kina da abun dariya”
“Ke kuwa nidai a TV nake ganinsu se kuma yau gani gasu,gaskiya Allah yayiwa Mahaifiyar Ya Farhan kyau,kina ganinta kamar wata aljana,gaskiya Ya Farhan ma bai d’auko kyawunta ba wlh”
“Gaskiya dai kam nima se kallonta nakeyi bana d’auke idanuna fa”
Nan suka tafa suna dariya se sukaji muryan Sagir yana cewa “Amal ya kikayi dare haka yau?”
Cikin mamaki suka tsaya suna kallon shi.
“Kai kuma asu wa da zaka titseni da tambaya kamar na zama k’anwarka?”
“Haba Amal aidai naga a matsayin yayanki nake nima indai da kara”
“Tofa su angulu anyi takalmi,muje in rakaki kinji kima dena b’ata lokacinki kina sauraron shi.”
Cewar Mubeenat sannan suka wuce yana binsu da kallo.
“Kinga iya shegen nashi ko,ni wlh bansan meya ajiyesuba har yanzu sunk’i tafiya se shegen sa ido daga ita Yar tashi har shi”
“Hmmm dadai ina ganin laifinki Amal,ashe dai gaskiyarki ce wannan ai damuwa ne zuwansu”
“Nagode Mubee zan shigo gobe”
“Ai nice da godiya kinsha aiki ki huta gajiya”
“Kun jiki wani aiki,seda safe” sannan Mubee ta fito zuwa waje.
“Haba Mubeenat,ban tab’a tunanin haka daga gareki ba”
“Oh saboda ni k’anwarka ce?”
“Yanzu dan nayiwa Amal gyara laifi ne?”
“Laifi ne sosai ma kuwa,yanzu fa aka idar da sallan magrib,kuma ni wataran bana kaiwa isha’i ne agidansun da zakace wani tayi dare bayan ga gida ga gida kuma iyayentama sunsan tana nan d’in ai”
“To Allah ya baku hak’uri”
“Ameen!” Ta bashi amsa a tsawace sannan ta wuce gida.
Haka ta shigo gida rai b’ace su Abba suna harabar gida zaikai su Abbin Farhan gidan su dan sunce bazasu kwana anan ba su takura musu.
Ko tsayawa batayi a gunsuba ta wuce.
“Sis Mubee”
Cak ta tsaya donjin muryan Ya Atif ya kirata.
Juyowa tayi tare da takowa inda yake tsaye gasu Farhan daga gefe “Na’am Ya Atif”
“Lafiya kuwa?”
“Lafiya k’alau”
“A’a Sis Mubee kamar ranki a b’ace na ganki”
“Sagir ne”
“Wani Sagir d’in?”
“Wannan na gidansu Amal yasa mana ido dewa wai yanzu har cewa yake meyasa Amal tayi dare haka”
Cikin sauri Atif yayi waje ya nufi inda Sagir yake tsaye “Kai Sagir,ka mugun kama kanka kana jina ko,ina ruwanka dasu dazaka titsesu kana tambayarsu? Kaika isa ka hana Amal zuwa gidannan ne,ko kwana Amal tace zatayi a gidannan babu wanda zai hatana dan haka ina baka last warning karka sake shiga hidimarsu wlh inba hakaba zanyi maganinka a unguwan Allah.”
“To d’an gidan masu kud’i dama ida mutum yana da kud’i ai babu abinda bazai yiba”
Tasss kakeji saukar mari akan fuskar Sagir “Ni kake gayawa maganan banza,ko ance maka sa’an kane ni?”
Haba nan fad’a ya kaure tsakaninsu dama hankalin Mubeenat kaf yana waje da gudu ta fita taga dai fad’a sukeyi aise ta dawo da sauri “Abba Ya Atif da Sagir suna Fad’a”
“Fad’a kuma da Atif yau?”
Cikin sauri su Farhan suka biyo bayan Abba alokacin Atif yaji mishi ciwo a goshinsa su Farhan da Abdullahi ne suka rabasu inda Umman Amal da Samira da Amal d’inma suka fito zuwa waje.
“Atif meya had’aku da Sagir kuma?”
“Abba ya takurawa Amal ne da Sis Mubee dama tun ba yauwa ina samun labari akan dukkanin abubuwan da yakeyi ban tab’a mishi maganaba se yau,amma shine yake min maganan banza”
“Wani irin maganan banza na maka,yanzu dan nayiwa Amal magana akan tayi ba dai-dai ba laifine?”
“Me tayi maka na ba dai-dai d’inba?”
“Me kika mishi Amal?”
“Babu abinda na mishi,kawai munzo zamu wucene da Mubee shine yace wai meyasa nayi dare haka”
“Kaji ko Abba,a gidan bare take dazaka ce wani tayi dare,waye kaima tukunna da zaka titsesu kamar wani wanda yake da iko akansu? Wlh daga rana mai kamar ta yau karka sake shiga hidimarsu tunda ba wani abu daya kauce hanya sukeyiba.”
Yana kaiwa nan ya wuce gida.
Abban Mubee yace da Abban Amal “Dan Allah kayi hak’uri wlh ni bansan Atif da Fad’aba sam”
“Bakomai wlh shaid’an ne kawai”
Nan Samira tayi magana cikin b’acin rai “Amma kuwa aiba wani abu yayiba dazai kaiga duka,kawai zamu koma garinmu tunda naga kamar har mun fara damun ‘yan unguwa Sagir wuce mu tafi”
“Haba Samira meyayi zafi kuma haka da zakice haka,ayi hak’uri dai” cewar Abban Amal.
Umman Amal kuwa hannun Amal ta kamo suka shige gida inda Abban amal yakeba Abban Mubeenat hak’uri sannan ya wuce gida.
Abba ya kalli Mubeenat yace “Muje gida to”
Wucewa sukayi dama su Ummin Farhan da Kaka suna cikin mota basu fito waje ba.
“Habibi” shine sunan da take kiran d’anta Farhan dashi.
“Na’aam ya Ummi” sannan ya k’arasa ta gefenta ya rungumeta tare da bata peck a kumatunta kamar dai yadda sukeyi acan k’asashensu sannan sukai magana cikin harcen larabci Abdullahi ma yayi mata magana sannan Abbin Farhan ya zauna a gaba yayinda Abban Mubeenat yaja motar suka tafi.
Mubeenat taga daga ita se Farhan da Abdullahi a tsakar gida,hakan yasa tayi gaba batare da tace dasu komai ba.
“Mubeenat” ya kira sunanta da murya mai dad’i irin na larabawa.
“Na’aam Ya Farhan”
“Won’t you say anything to me?”
Se’a yanzu ta tuna da cewa basu gaisa ba. Ya sake cewa “Ko kin menta dani ne?”
Dariyar hausar nashi takeyi tare da cewa “Wellcome to Nigeria”
“Thanks,but why are you laughing?”
“Hausar kace taban dariya”
“To ai gyaramin zakiyi not laughing”
“I’m sorry”
“It’s okay”
“You say kokin manta dani ne,not menta dani”
“Hhhh sukayi dariya dukkansu sannan yace “OK manta right?”
“Yeah” tace dashi sannan ta sake cewa “Alright then good night”
A tare sukace mata “Good night” sannan ta wuce ciki suna dariya…Samira inaganin Sagir ne bayi da gaskya,dan tunda nake dasu anan Atif bai tab’a fad’a da kowaba se yau wlh”
“Ina ganin ya dena shiga hidimar Mubeenat kwata-kwata dan inhar ya shiga hidimarta to wlh Atif bazai bar shiba sunyita samun sab’ani kenan,dan basa son duk wani abu dazai tab’ata wlh tunda itama ba shiga hidimarsa takeyi ba.”
“Kiyi hak’uri dan Allah insha Allah zuwa gobema zamu tafi wlh.”
“Haba Samira hakan yana nufin fushi kikayi kenan? Wlh kowa zaiyi shaidan su Mubeenat a unguwannan bata da rashin kunya,basa shiga hidimar kowa zaman lafiya mukeyi dasu,amma yau gashi harda fad’a?”
“Kidaiyi hak’uri tunda shi bayida aiki se neman magana gara mu koma dukda dai bamu da gurin zama amma duniya tana da fad’i ba komai.”
Bayan ta fice ne ta wuce d’akin ta.
Shi kuwa Abba Amal masifa ya shiga yiwa Umman Amal ta inda yake shiga bata nan yake fita ba. Tass ya wanketa da fad’a sannan ya fita yaje gurin Sagir yana bashi hak’uri tare da cewa ya rarrashi ‘yarsa karya yarda su tafi.
Jin haka yasa Sagir jin dad’i sosai tare da niyan gobe da safe zai koma gun Malam na ruga domin ya sanar dashi aiki yayi kyau sosai.+
Washe gari da safe bayan anyi sallan asuba Umma da Mubeenat suka shige kichine sunata aikin abin karyawa na bak’i.
Zuwa k’arfe bakwai sun gama komai kowa ya wuce yayi wanka.
  Shirinta tayi cikin doguwar riga tas da ita babu ado a fuskarta ta nufi parlour’n Abba inda takejin muryansu suna hira.
“Slm Abba ina kwana?”
“Mamana an tashi lfy,ban gankiba da asuba”
“Eh Abba mun shiga kichine ne da Umma”
“To madallah”
“Ya Atif ina kwananku?”
“Duk suka amsa da lfy” sannan akaci gaba da gaisawa anata hira.
“Abba girman Mubeenat yaban mamaki gaskiya” cewar Farhan.
“Ai Mamana tana da gab’an girma ne sosai”
Kunya taji dan haka ta mik’e ta fice suna mata dariya. Harta fara tafiya se kuma ta dawo ta tsaya daga bakin k’ofa tace “Ya Atif wai inji Umma wai an gama abinci azo akaiwa su Ummi”
“Ok” sannan ya mik’e suka wuce tare da Mubeenat.
  Dama an shirya musu nasu akan daining d’in Umma,dan haka ya kira su Farhan suka ci abinci suna santin girkin su Umma sannan aka fito dana iyayen Farhan zuwa gun motan Abban.
  Atif ne ke driving Abba yana gaba,daga tsakiya kuma Farhan ne da Abdullahi,baya kuma Mubeenat da Shureim sannan suka tafi.
Sagir ya nunawa Malam na ruga farin cikinsa sosai inda ya k’ara masa kud’i masu yawa.
“Malam so nake ayi abun cikin sauri kar wani abu ya biyo baya.”
“An gama me kuke so ayi yanzu?”
“Tabar gidan kawai ta shiga duniya a rasa gane inda take,sannan ya auri Yayata Samira”
“Hahaha! Tashi kaje an gama gobe komai zai wakana kaje ku zuba ido kawai”
“Nagode Malam seka sake ganina,dan dolene inzo godiya idan aiki ya sake yin kyau kamar yadda na farko yayi.”
Su Abba suna isa aka sake gaisawa aka zauna hira kuma.
Ummi ta kalli Mubeenat tace ta taso ta dawo kusa da ita.
Haka kuwa akayi anan taci abincinta Ummi kam.
  Bayan tsarabobinsu da aka basu masu yawan gaske sukaita godiya sanna suka fito waje domin rakiya.
Farhan ne ya janyo Umminsa yana tambayar ta “Ummi kina son Mubeenat sosai fa harna fara kishi”
“Ooh Habibi aikai daban ne,haka kawai naji yarinyar ta shiga raina wlh”
Murmushi yayi “Kina nufin kina son ta?”
“Na’aam Habibi,kodai zakayi aure anan Nigeria ne?”
Cikin jin mamaki ya dubi Mahaifiyarsa “Ummi aure daga zuwanmu,kuma ni ai bansa aure a gabana yanzu ba,sannan kuma wa kike nufi Mubeenat?”
“Na’aam Habibi tun jiya muke wannan zancen da Abbinka,sedai bamu san ra’ayinka akan hakan ba,amma karka sa damuwa a ranka zab’inka shine namu karka b’oye min inhar zab’inmu bai maka ba.”
“Ummi naga ai maganar bud’e company ne ya kawomu ba wannan zancen ba”
“Hakane Habibi,amma kai bakaga yadda ta girma bane,sannan yarinya ce mai hankali ga nutsuwa gata ‘yar Aminin Abbinka inaga hakan zai k’ara dank’on zumunci a tsakaninsu kuma shi Abbi naka ne yazo min da zance dayaji ina yaba girmanta jiya da dare bayan dawowarmu”
Shuru Farhan yayi kamar mayin nazari sannan yace “Ummi please mubar maganan yanzu zuwa wani lokaci”
“Dama na gaya maka ai,wannan namu tunaninne amma farin cikinka ai shine namu Habibi” ta shafi fuskarsa tana murmushi.
Shima murmushin yayi tare da cewa “I will think about it Ummi”
“Take your time Habibi,karkayi gaggawa sannan kabi zab’inka ba namu ba okay?”
“Sure Ummi” sannan ya rungumeta suka nufo gun mota.
Duk abinda sukeyi akan idon Mubeenat da Shureim.
“Sis Mubee,wai shine d’an autan ta?”
“Hhhh kai Shureim,shi kad’ai ne d’ansu bayan shi babu wani,sannan kasan larabawa suna k’aunar yaransu sosai komai girmansu a matsayin yara suke d’aukansu sabar k’aunarsu da suke yi.”
“Oh gaskiya abun ya burgeni sosai wlh”
“Hhhh ya isa haka shige mota”
Ba musu ya shige,zata shige kenan Abbin Farhan yace “Mubeenat bazaki zauna mana ba?”
Murmushi tayi “Uncle zan dawo anjuma da rana”
“To shikenan sekun dawo”
“Amma idan kika dawo kwana zaki mana,kinga seki koya min abincin k’asarku” cewar Ummi.
“Hhhh to Ummi bakomai” sannan ta wuce ciki suka wuce.
Tunanin maganan Umminshi kawai yakeyi a hanya har suka iso gida.
Anan suka tarar da Umman Amal da Amal sun shigo gaisawa da bak’i,nan aka sake gaisuwa sannan aka tab’a hira kowa ya kama gaban sa.
Hira sosai Umman Amal sukai da Umman Mubeenat inda take gaya mata irin abubuwan da Abban Amal yakeyi akan Samira abun ya fara damun ta.
Mamaki,sosai Umman Mubeenat tayi “To ai inaga gara ki sallamesu tun wuri,yanzu ai duniya ta lalace halin mutum se Allah.”
“Wlh kuwa,Allah dai ya rufa asiri kawai.”
“Ameen” sannan sukaci gaba da hira daga baya ta wuce gida tabar Amal.
Sagir kuwa ya gayawa Samira komai dan haka take zaman jira,Allah ya kaimu gobe susha kallo.
Da wuri su Umma suka gama abincin rana,inda Abba yace Mubeenat ta had’a kayanta taje gidan bayan anyi taro seta dawo.
Dama kuma su Farhan ma yaune zasu koma gidan,dan dama karane kawai sukayi suka kwana musu d’aya.
Atif ne zaune a parlour’n Umma suna magana da Mubeenat “Ya Atif dan Allah zaka dinga zuwa?”
“Insha Allah bayan na dawo amma”
“Ina kuma zaka je?”
“Zamuje yin wasa a waje,kuma jibi ne tafiyar tawa bana tunanin ina nan ma za’a bud’e company d’innan.”
“Eyyah Ya Atif zanyi missing naka wlh”
“Don’t worry 1week ne kawai zamuyi mu dawo,aiga wani Yaya ma kin sake samu na gaya mishi ya kulamin dake ina mugun sonki.”
Murmushi tayi “But zanzo jibin muyi sallama kafin ka tafi,kuma semunje yawo ka yadda?”
“Yeah bakomai”
“Thanks Ya Atif ka kulamin da Shureim fa”
“Baki da matsala sam”
“Thanks” sannan suka fito da abincin rana.
“Ya Atif bari naje gun Amal muyi sallama dan bata san zanje ba”
“Ok” cikin sauri ta wuce dan duk suna cikin mota.
Amal zanje gidan bak’innan da suka zo mana,zand’an yi kwanaki acan kafin in dawo,but jibi ma zanzo muyi sallama da Ya Atif zai tafi wasa a waje”
“Tofa,kice zaki koyo larabci kafin ki dawo,kije ki koyo muma kizo ki koya mana”
“Kedai akwai ki da shirme,ina Umma?”
“Tana sallah”
“Wlh gashi ni suke jira idan ta fito kiyi mata sallama please”
“Ok amma tsaya,ina larabawan biyu?”
“Kai Amal dukda su zamu tafi suma can zasu koma”
“Eyye,abun zaiyi kyau zamuyi suruki kwanan nan kenan” ta k’arasa maganar cikin zolaya.
Kafad’arta Mubeenat ta daka sannan ta wuce “Nina tafi kyaji dashi ai” tana dariya.
Abdullahi da Shurim ne a gaba,yayinda Farahan ke zaune a baya,haka ta wuce ta shiga dan a motar Atif zasu tafi kuma motar one door ce.
Babu wanda yace komai in banda Atif da yake amsa wayarsa.
Farhan kuwa wayansa yake dannawa yayinda Abdullahi yake hirarsa da Shureim cikin harcen turanci.
“Sis Mubee zanyi missing naki wlh” cewar Atif
“Kana so ka sani kuka ne ko Ya Atif?”
“A’a maganar gaskiya nake miki,musamman da dare yau Shureim ne kad’ai abokin hiran nawa”
“Ai zanzo jibi da wuri muyita hira”
“To Allah ya kaimu jibin”
“Ameen” tun daga nan babu wanda yace komai har suka isa.
Bayan Atif sun gaisa dasu ne yayi musu sallama shida Shureim sannan Mubeenat ta rakosu ita da Farhan hargun mota sannan suka tafi.
Tsaye take tana bin motarsu da kallo tak’i shigewa ciki.
“Mubeenat,or let me say Sis Mubeenat right?”
Murmushi tayi tare da d’aga mishi kai alamun “Eh”
“Ok muje ciki ko?”
“To” tace sannan suka tafi ciki a tare…Mubeenat”
“Na’am Uncle”
“Zoki zuba mana abincin ko?”
“To Uncle” sannan ta zuba mishi shida Ummi da Kakansu,Farhan suna binta da kallo daga nan suka wuce ciki.
Hira sosai Mubeenat sukeyi da Iyayen Farhan,ta saki jiki dasu sosai ganin yadda suke sonta.
Farhan ne ya fito da waya a hannunsa “Abbi”
“Yes Son”
“Kasa a kawo maka motan ne?”
“Na’aam suna kawowa,zakuje wani guri ne?”
“Abbi ina son mota ne dan zamu fita da Atif anjima domin muga guraren”
“Ok Son bari idan an kawo min motan seku fita kaima ka sayi naka ko?”
“Ok”
“Ya Farhan mota zaka saya?”
“Yeah,ko kina saida motan ne?” Ya tambayeta cikin zolaya.
Dariya tayi “A’a akwai dai wanda Abba yake saya agunsu ne zanso ka saya agunsu suna da kirki sosai”
“Ok kinsan gurin?”
“A’a but Ya Atif ya sani,nidai ban tab’a zuwa ba sedai su sukan kawowa Abba mota har gida indan zai saya”
“Ok zanyiwa Atif magana se muje”
“Ok thanks”
“You’r wlcum” sannan ya kalli Ummin shi tare da kashe mata ido d’aya yana murmushi.
“Habibi ta’ali”
Dawowa yayi yace “Im here Ummi”
“Zauna anan” ta nuna mishi kujeran dake kusa da Mubeenat.
Bayan ya zauna ne seya ajiye wayarsa,idon Mubeenat yakai kan screen nashi inda taga hoton sane yana sanye da shert yellow mai dogon hannu tare da wata yarinya tana sanye da pink d’in top da kuma bak’in suwaita akai sunyi kyau sosai musamman shi Farhan d’in.
“Ya Farhan zan iya yin tambaya?”
“Sure!”
“Kaida waye a hoton nan?”
Wayarsa ya kalla sannan yayi murmushi “She’s my Sister k’anwar Abdullahi ce”
“Tamin kyau sosai”
Murmushi yayi tare da cewa “Thanks” yana mai kallon fuskarta se kallon hoton takeyi.
“Zan had’aku k’awance kina so?”
“Da ni?”
“Yeah indai kina so”
“To nagode” tana murmushi baisan yana binta da kallo har haka ba seda Ummin shi tace “Habibi”
Sannan ya cire idanunsa akan Mubeenat wanda ita kamma bata san yanayi ba.
“Na’aam Ummi”
“You are my Habibi,and she’s my Habibty” cewar Ummi
Kallon Ummin nashi yayi cikin mamaki,ita kanta Mubeenat wani irin kunya taji dan tasan Habibty dai masoyiya ne.
Farhan ya kalli Mubeenat yace “Habibty?”
Itama kallonsa takeyi tare da saurin sauke idanunta zuwa k’asa.
“Yes Habibi,i love her so much”
Abbi ne yayi gyaran murya “Kunfa takura min Yarinya,kun sata jin kunya,Mubeenat tashi ki shiga ciki kinji?”
Kamar tana jira dama ta mik’e cikin sauri ta wuce d’akin Ummi dan anan Ummi ta ajiye mata kayanta.+
Bayan maganganu da sukayi da d’ansu Farhan ne sannan ya wuce gun Abdullahi a d’aki suna hira.
Bayan la’asar aka kawowa Abbi motar. Take Farhan yayiwa Atif waya yazo suka wuce dukkansu ba tare da Mubeenat tasan da zuwan Atif ba dan tana bacci a d’akin Ummi.
A hanya Farhan yake gayawa Atif maganar mota da Mubeenat ta mishi.
“Yeah muje gurin to”
Suna isa Farhan ya zab’i mota Camry 2015 ash colour had’ad’d’iya.
Ahmad ne yau ke zaune agidan motocin dan Yayansa baya nan ya wuce Umrah shiyasa yabar komai a hannu Ahmad d’in.
“Amma dai kai bak’o ne ko?” Cewar Atif
Ahmad yayi murmushi yace “Eh dayake bamu tab’a had’uwa ba,ni k’anin Lukman ne baya gari shiyasa na zauna anan d’in”
“Ok,toga d’an uwana sunan shi Farhan daga Madina suka zo kuma zaici gaba da zama anan ne baisan kowa ba dai a yanzu da fatan zaku zama friends?”
“Allah sarki,why note? Nice to meet you Farahan” cewar Ahmad tare da sake mik’a mishi hannu.
“Thankyou Ahmad” sannan sukayi exchenging number yayi mishi mobile transfer na kud’in motar sannan aka rubuta komai na motar aka basu suka tafi suna godiya.
Abdullahi ne ya hau sabuwar motar Atif da Farhan kuwa suna mota d’aya Abdullahi yana binsu a baya.
Yawo sosai sukayi yana nuna musu gurare har kusan magrib kafin suka dawo gida.
Lokacin Mubeenat ta gama musu abincin dare har tayi wanka sannan suka dawo.
Gaba d’ayansu suka fito domin ganin motar Farhan,nan sukaita mishi addu’a sannan suka koma ciki seda Atif yaci abinci suka tab’a d’an hira da Mubeenat kafin ya wuce gida.
8:45 Mubeenat ta shige d’akin Ummi ta kwanta akan gadonta suna chartn da Amal da Aisha tanata murmushi.
“Slm” taji sallamar Farhan
“Waslm” ta amsa tare da mik’ewa taje ta bud’e mishi k’ofar “Ya Farhan?”
“Na’am bacci zakiyi?”
“Eh” ta bashi amsa
“Ok then ma’assalam”
“Murmushi tayi tace Bissalam” sannan ya tafi.
“Ummi bacci fa zatayi”
“To shikenan dama naga ita kad’ai ce shiyasa nace ka dubo ta”
Haka sukaita hiransu cikin harcen larabci tana jiyosu har bacci yayi gaba da ita.
Washe gari da safe bayan anyi sallah ta shige kishi ta had’a musu d’anwake dake Abbi ya sanar da ita cewa suna son duk wani abu daya shafi flour.
Gidan su Amal kuwa tunda Ummanta ta tashi bata ganewa jikin taba sakamakon mugayen aljanu da suka shiga jikinta nan take ta kira Amal.
“Gani Umma”
“Kije ki kiramin Umman Mubeenat”
“To” sannan ta fita tare da tunanin meya faru Umma zata aikeni da sassafe haka?”
Fitar Amal kenan itama Umman nata tasa k’afa ta fito,Mai gadi yayi mamakin ganinta ta fita da safe haka amma seya gaishe ta “Ina kwana hajiya?”
“Lafiya” kawai tace dashi sannan ta wuce ta kama hanya ba tare data san inda take dosa ba.
Wannan shine silar barin Umman Amal daga wannan gidan wanda har yanzu ba’asan inda takeba tsawon shekara biyu kenan yanzu.
Ita kanta Umman Mubeenat hankalinta a tashe ganin safiya ce kuma Amal tace Ummanta na kiranta,bayan ta sanar da Abban Mubeenat ne se suka wuce ita da Amal d’in.
Koda Amal ta shiga se bata ga Ummanta ba,ta kirata taji shuru,ta duba ko ina shuru saita wuce d’akin Babanta nanma yace da ita bata shigo ba.
Abu kamar wasa su Samira da Umman Mubeenat anata nemanta can mai gadi yace aita fita.
“Ta fita kuma? Amma aini bata gayamin zata fita ba” cewar Abban Amal.
Nanne hankalin kowa ya tashi amma banda Samira da Sagir da suka san abinda suka aikata wanda se murna suke acikin zuciyar su.
_ALLAH KA SHIGA TSAKANIN NA GARI DA MUGU,MASU HALI IRIN NA SAMIRA DA SAGIR ALLAH KA SHIRYAR DASU KASA MUFI K’ARFIN ZUCIYOYINNU AMEEN._
Abu kamar wasa aka kira wayanta se akaji yana ringing a cikin d’akinta,duk inda ake tunanin zataje duk an tambaya amma babu alamunta.
Take Amal ta fashe da kuka Samira tazo kusa da ita zata rarrasheta cikin sauri da kallon banza ta wuce gun Umman Mubeenat tana kuka sosai mai k’arfi.
Abban Mubeenat ne yace Umma ta shiga da ita gida bari su shiga cikin gari,nan suka fita shida Aban Amal d’in Atif ma yabi bayansu da motar shi se nemanta ake abu kamar a film mutum da girmansa anemeshi a rasa…
Abu kamar wasa k’aramar magana ta zama babba. Ko ina akaje babu labarin Mahaifiyar Amal.
Atif ne ya d’auki wayar shi ya kira Sis Mubee,lokacin tayi wanka harta shirya ta fito parlour suna zaune dukkansu tana zuba musu d’anwaken data dafa musu wanda ta yanka dafaffen k’wai nata ta yanka su slide ga tumatur ga cabage da lemun tsami.
Jin ringing na wayar tane yasa ta duba,sunan Sweet Bro ta gani a rubuce. Seda ta gama had’awa kowa nashi sannan ta zauna tare dakai wayan kunnenta “Hello Ya Atif”
“Sis Mubee kun tashi lfy”
“Lafiya lau Ya Atif ya kake yasu Umma ina Shureim?”
“They are all fine,Sis Mubee ko Umman Amal tazo tagun ku?”
Farhan dai ahankali yake bin Mubeenat da kallo,su kuwa Ummi se santin d’anwaken sukeyi waiya musu dad’i gobema shi zata musu. Sunata hiransu ita kuwa tana wayarta “Umman Amal kuma,bata zoba”
Shima kanshi Atif yadai tambaya ne kawai amma yasan batama san gidan ba.
“Ikon Allah” cewar Atif.
“Ya Atif meya faru ne?”
“Shikenan Sis Mubee ba komai se anjuma”
“No please wait Ya Atif” cikin sauri Farhan ya kalleta ya kasa d’auke idanunsa akanta. “Me yake faruwa ne Ya Atif dan Allah ka gaya min idan akwai wani abu”
“Sis Mubee Umman Amal ce ake nema tun d’azu tabar gida batare da ta gayawa kowaba har yanzu nemanta ake duk inda akaje babu ita,ki dai tayamu da addu’a byee.”
Take idanun Mubee ya kad’a “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un” ta furta sannan sauran suka amsa suka k’arasa atare.
“Mubeenat lafiya?” Abbi ya tambaya
Cikin sanyi murya tace “Lafiya Uncle” sannan tayi saurin cewa “Ya Atif yanzu ina Amal?”
“Tana gun Umma se kuka takeyi wlh”
Take k’wallan da Mubeenat ta b’oyesu a idanunta suka gangaro zuwa fuskarta “Ya Atif dan Allah ka rarrasheta nima zanzo yanzu”
“Ok byee.” Ya katse wayar.
A sanyin jiki ta ajiye wayar tana share k’walla “Uncle ina so inje gida gun Amal,tun safe Mahaifiyarta ta fita daga gida kuma bata sanar da kowa zata fitaba tun d’azun ake neman ta har yanzu babu labarinta”
“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un” suka furta dukkansu
“Uncle Amal tana cikin damuwa ina so inje in zauna da ita”
“Ok Mubeenat ki zauna kici abinci semu tafi tare kinji?”
Bazata iya mishi musu ba dan haka ta zauna amma sam ta kasa cin abincin.
Farhan kuwa duk idonsa akanta yake,inda su kuma suketa tattaunawa akan maganar.
“Sis Mubeenat” Farhan ya kira sunanta.
A hankali ta d’ago ta kalleshi batare datayi magana ba.
“Eat your food okay?”
Mik’ewa tayi tare da d’aukan wayarta tace “I’m not hungry” sannan ta wuce d’aki yana bin plate d’in d’anwaken nata da kallo.
D’auka yayi ya zuba mata kayan had’in d’an dai-dai sannan ya siyayi madara mai sanyi wanda suka taho dashi daga Madina ya d’auka ya bita dashi d’akin Ummin sa.
Da sallama ya shiga tana zaune tana wani sabon hawayen.
Agefenta ya ajiye abincin sannan ya rik’e madaran a hannunsa yana kallon fuskarta “Sis Mubeenat” ta d’ago ta kalleshi “please eat”
“I’m not hungry Ya Farhan”
“I don’t believe you,beside you are the one that coked and it’s so sweet please eat,or do you wamme to say Habibty Mubeenat please eat?”
Kallonsa tayi har cikin ido shima kuma ita yake kallo tare da lumshe mata kyawawan idanuwansa yana mata murmushi.
“No thanks” ta fad’a tare da sunkuyar da kanta k’asa.
“Alright lemme feed you” ya fad’a yana k’ok’arin ajiye cup d’in madaran,ganin dagaske yakeyine yasata cewa “No Ya Farhan”
“Alright then eat” ya tsareta da ido.
A hankali ta d’auki spoon d’in takai bakinta tana ci kamar wata mara lafiya.
“Habibty tell me what you want”
D’agowa tayi da Sauri tana kallonsa “Take me home please?”
“Naji but sekin ci”
Ba musu taci kamar spoon biyar sannan tace dashi “I’m full now”
Madaran hannun shi yayi niyan kaiwa bakinta se kuma ya tuna da cewa bafa k’anwar sa bace ta Madina,nan ya fasa tare da ce mata “Take”
Karb’a tayi tahau sha tas ta shanye dan dad’in madaran dataji.
Cikin jin kunyarsa tace “Thankyou”
Murmushi yayi mata kawai sannan ya mik’e,itama mik’ewar tayi tare da d’auka plate da cup d’in da niyan fita dasu “Where are you going?”
“I will take it out”
“No let me” ya karb’a batare data soba ya fice tana binshi da kallo.
Gaskiyan Amal ne Farhan kyakkyawan gaskene gashi da tsawo ga wani k’amshi mai dad’i dake fitowa data jikinsa.
Murmushi tayi tace “Habibty kuma?”+
Bayan duk sun gamane Abbi yace da Faran ya kira Mubeenat su tafi.
Tana zaune tana kiran number’n Amal amma ba’a d’agawa sam.
“Slm Habibty let’s go” ya fad’a batare daya bud’e k’ofar ba.
“Ok” tace dashi sannan ta fito rik’e da wayanta a hannu. Kallon junansu sukayi tayi saurin sunkuyar da kanta k’asa shi kuwa murmushi yayi sannan yayi gaba tana binshi a baya.
Abbi ne ke driving Abadullahi yana gaba,Farhan da Mubeenat kuma suna baya yana ta kallon chartn d’in da takeyi kamar haka.
_”Slm”_
_”Wslm waye ne?”_
_”Wani masoyinkine”_
_”To nagode”_ sannan tayi blocking nashi duk akan idon Farhan dama Abbi nashi ya koma masa hausa da kuma karatun hausa dukya iya.
Wayarsa yasa a silent sannan yace da ita “Let me see your phone Sis Mubeenat”
Ba musu ta sauk’a a whatsapp d’in sannan ta mik’a mishi.
Yana karb’a yayi dailing number’n shi ai kuwa seya katse sannan yayi deleting number’n shi daga wayarta ya mik’a mata tare da cewa “Thanks”
Murmushi ta mishi tare da mamakin to meyayi da wayan nata dan ko dak’ik’ai biyu baiyiba a hannunsa ya bata.
Shi kuwa saving number’nta yayi da suna *HABIBTY MUBEENAT*
Har suka iso gida babu wanda ya sake yin magana a cikinsu,suna isa Amal ta fito da gudu,ta d’auka ko Abba ne tare da Abbanta suka dawo,ganin bak’uwar motace yasata sake fashewa da kuka.
Cikin sauri Mubeenat ta fito daga motar taje da gudu suka rungume junansu suna kuwa tare da wucewa ciki.
Atif ne yayi musu jagora har zuwa parlour’n Abba,sannan yazo ya sanar da Umma taje suka gaisa.
“Ashe kuma abinda aka tashi dashi kenan?” Cewar Abbi.
“Eh wlh,abu kamar wasa har yanzu dai shuru wlh” cewar Umma.
Nan dai ta bashi labari tun lokacin da Umman Amal d’in tace da Amal ta kira mata Umma.
“Ikon Allah,kuma babu wanda yaga fitarta?”
“Eh Maigadi yace yaga fitarta wlh,sedai baiyi tunanin wani abu ba shiyasama bai damu da yaga ta ina zata biba”
“Ikon Allah,to Allah yasa dai lafiya Allah ya bayyanata”
“Ameen” suka amsa gaba d’ayansu sannan su Farhan suka gaisheta cikin girmamawa.
“Bari a kawo muku abinci” cewar Umman Mubeenat.
“A’a wlh Alhamdulillah Mubeenat ta mana d’anwake ai Alhamdulillah wlh”
Dariya Umma tayi “D’anwake kuma,Farhan kun iya ci kuwa?”
Murmushi yayi “Munci sosai Umma ai yayi dad’i”
Nan dai sukai ta hira cikin dariya sannan Umma ta fito.
Fitarta bada jimawaba sega su Abba sun dawo,kowa ya fito cikin sauri dan jin ko an ganta amma sam ba’a ganta ba.
Hankalin Amal ya sake tashi fiye dana da,ba Amal kad’aiba duk wanda yake tsaye agun seda yaji wani iri kowa da iri tunanin da yakeyi a cikin ransa.
Abu kamar wasa yau kusan kwana uku kenan aketa faman nemanta harda gidan TV tare da nuna hotonta amma sam babu wanda yace ya ganta.
Amal ta rame bata da aiki se kuka,kullum idan Mubeenat ta gama abinci se su Farhan su kawota ta yini har dare kafin su dawo su d’auketa.
Yau sati kenan da b’atan Umman Amal amma haryau babu wani labari akanta. Su Samira kuwa suna gidan suna kukan munafurci tare da nuna damuwarsu sosai akan ta.
Lokacin taron bud’e company yayi hidima sosai akayi base na zaiyana muku komaiba, inda Mubeenat tace da Ummi zata mata kwalliya,ba musu ta amince dan yadda take k’aunar Mubeenat har cikin ranta.
Kwalliya d’an dai-dai tayi mata bamai yawa ba Farhan se yabawa yake da kyawun da Mahaifiyarsa tayi hakama Abbi nashi.
Soyayya sosai sukeyi ko agaban wayene basa kunya da yake haka suke dama su larabawa.
Kowa yayi kyau Amal nedai sam bata cikin walwala kuma dukkanmu munsan dalilin hakan,a haka aka nufi gun taron kowa Ummin Farhan yake kallo tare dasu Farahan da kakansu anata yaba irin kyawunsu ana cewa ai sune masu company d’in dama ba ‘yan k’asarnan bane su…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page