KINA RAINA CHAPTER 5

 KINA RAINA CHAPTER 5

Dan sandan farin kaya kuma?” Maimunatu ta tambaya tana wanke hanunta a cikin bowl. Da sauri Rabi ta iso gabanta ganin tayi nasarar janyo hankalinta da labarin dan kowa ya san mutuncin dake tsakanin maimunatu da khalid.1

Cike da zumudi Rabi ta cigaba da bata labari “eh wallahi wai ashe badda kammanni yayi dan su kama alhaji wada saboda ana zarginsa da ajieye miyagun kwayoyi a cikin gidansa shine ya yazo ya kama kofar shagon saboda ya san shige da fice na gidan,ai kuwa ya aka yi ya aka yi muna zaune kawai muka ji karan jiniya ta ko ina a anguwan nan ai fa aka firfito kallo inda jami’an tsaro suka shiga har cikin gidan suka fito da alhaji wada tare da yaran da suke masa hidimomin kwayoyin ga kuma tulin kwayoyin da aka fito dashi har da hodar ibilis,shi kuwa me shago na tsaye hannunsa rike da bindiga sai turanci yake yi abin dai kaman a film gwanin ban sha’awa.” Rabi ta karasa maganan tana hadiye yawu dan tunda ta fara maganan sai lokacin ta samu daman hadiye miyau.2

Maimunatu kam banda mamaki babu abinda take yi wai Khalid ne SSS abin kam da mamaki kana tare da mutum baka san waye shi ba, shi yasa wulakanci bashi da amfani cos baka san inda mutum zai maka rana ba.1

Haka kawai taji ina ma zata ga khalid amma ta san hakan da kaman wuya tunda ya gama abinda ya kawoshi anguwarsu.1

Ganin tunani zai mata yawa ya sa ta sallami rabi ta nemi waje ta kwanta.

Maimunatu ta sha mamaki da har aka wayi gari momy bata hantareta ko ta goranta mata wani abu ba haka daddy ya sakko bai nuna mata akwa wani damuwa ba.1

A hankal rayuwar maimunatu ta fara dawo dai dai hatta ga tunanin marwan tayi kokarin hana kanta and alhamdulillah tana samun nasara akan haka ta cireshi a rayuwarta sai lokaci lokaci ya kan fado mata a rai.1

Sosai take mamakin halayar da namiji babu wanda zai taba cewa marwan yaudararta yake a yanda ya nuna damuwar sa da kulawarsa akanta ashe duk karya ce she was just helping him past time tunda gashi da zamarsa ya kare a kasar ya tafi ko waiwayan ta bai kuma ba ko da a ce irin na dan kwan biyun nan ne,no! Yanda ya bar kasar haka ya bar rayuwarta shiyasa itama ta bar duk wani abu da ya shafi rayuwarsa a cyprus sai abu biyu da ta kasa barinsu kuma ta kasa sanin dalilinta na yin haka.1

Agogon da ya bata ya na nan a cikin jewelry box dinta haka teddy bear din shima ta adana sa a cikin drawe dinta kullum tana kara godewa Allah da yasa soyayya bai rufe mata ido ta bawa marwan kanta ba lallai da ta tabbata kukan da zata yi me yawa ne.

Har kullum tana dana sani,da kuka hade istigfarin abinda suka aikata ita da marwan tana tir da wannan halim turawan da ta ara ta yafawa kanta tare gudunmawar marwan dan shinw ummul aba’isin lalacewarta marwan ya cutar da rayuwanta ya koyawa gangan jikinta abubuwa da dama wanda a halin yanzu in sha’awa ta motsa mata bata taba sanin yanda zata yi da rayuwarta.2

Ta kan tsinci kanta a matsanacin son kasancewa da marwan ko da kuwa kwamciya a jikinsa ne kawai.

In ta tsimci kanta a wannan halin sai dai tayi ta kuka tana aikawa da marwan Allah ya isa.1

Ganin zaman gidanta na yawa babu inda take zuwa tunda ba a resume school ba ya sa ta cewa daddy tana so ya kaita ziyaea danginshi da na mamanta sosai yayi murna dan dama shi daddy irin mazan nan da in ba wai kai ka nuna kana son abu ba hankalinshi baya kai mishi ayi.1

Ai kuwa a satin ya shirya mata tafiya ta tafi ziyara sosai danginta suka yi farin ciki da ganinta kowa sai nan nan yake da ita.1

Itama taji dadin shiga cikin yan uwanta ta sake da cousins dinta sun sharing numbers.1

Daga nan kuma gidan uncle sufyan ta tafi tayi kwana biyu mami matarsa kamar zata hadiyeta hakan yayi wa uncle sufyan dadi sosai,abinda take so shi ake yi a gidan. Haka kawai zai ce ta shirya ya fita da ita outing wurare dabban dabban sai hotuna suke yi a wayarsa kaman wasu couple tun tana jin kunya har ta sake.

Bata tashi dawowa ba sai da school aka resuming ta dawo ta fara karatunta ka’in da na’in sam bata kula shirgin maza duk saurayin da zai zo da sunan yana sonta zata fatattakeshi saboda nacin samari ta koma masifaffiyar karfi da yaji dan bata son sam abinda zai hadata da mayaudara a cewarta.2

In tace haka sai course mates dinta ko cousins dinta suyi ta mata fada suna cewa ai ba ko wani namiji bane mayaudari ko me take nufi? Aure ne ba zata yi ba kome kasancewar basu san marwan ba mutum daya ne ya san da labarin marwan ba kowa bace face jalila da zumuncinsu ya cigaba.2

Babu wanda ya san labarin marwan sai ita,ita kadai ta san irin kin da maimunatu take yiwa marwan dan ta tabbatar mata ko a lahira bata kaunar ganin ko me kama da marwan saboda ya cutar da rayuwarta marwan yayi mata miki me wuyar warkewa.1

A wannan yanayin ne maimunatu ta samu ta kamala karatunta inda ta samu BSc dinta akan kasuwanci sosai babanta yayi farin ciki da samun wannan ci gaban yayi kuma alfahari da ita a ranshi yana ganin  maimunatu zata tallafa masa a sha’anin kasuwancinshi ita kuma a nata bangaren sam bata sha’awar aiki a karkashin daddy dan ta san abinda zai kara hura wutan tsana a tsakaninta da momh kenan yanzu ta samu abu ya sassauta bata so abinda zai ballo mata ruwa,abin gabanta yafi karfin rigimar momy.1

Tana fara service zata fara raba cv dinta ko kuma zata yiwa uncle sufyan magana in lokacin yayi.1

Wata rana tana kwance tana karanta wani littafi ‘RUMASA’U’ a wayarta tana jinjina irin halin kuncin rayuwar da tauraruwar littafin take ci wayarta ta fara ringing dubawan da zatayi…………Murmushi ta saki tare da ansa kiran a hankali tace “uncle sufyannnn.” Limshe idanu yayi yana jin muryarta na ratsa kwanyarsa.1

“Munari! Munari kin k’i ki ban dama,why maimunatu?” Wani murmushin tayi tace “uncle sufyan kenan,ya su mami da sauran yan gidan?” Girgiza kai yayi kaman yana gabanta hade da zuba uban tagumi yace “as usual kina avoiding maganar nan maimunatu,na tabbata in har kika ban dama mami da kike tsoro will never be a problem na rasa tsoron me kike ji,ko ni ne dai ba kya so nayi miki tsufa?” Dariya tayi a nitse cikin kunya tace “ni wallahi umcle sufyan kana sa ni jin kunya.”2

Murmushi yayi yace “ke dai munari fadi gaskiya kawai ba wai mami ke baki tsoro ba nine nayi miki tsufa,daddynki fa ya girmeni,baki ganin sai yanzu farooq ya shiga jami’a ke kuwa duk da delays din da kika samu amma har kin gama,kinga ko ai ban kai daddyn mu shekaru ba.”6

Zuwa yanzu kam dariya take yi sosai dan ita dariya abin yake bata da mamaki wai uncle sufyan ke sonta har ma yake kokarin yaga ya burgeta ko da yake ba abin mamaki bane namiji ne shi su ba kunya garesu ba akan diya mace. Ba ta ce komi ba ban da “hmm uncle kenan.”1

Ya san ba zata taba bashi sahihin amsa ba ya san tana jin nauyin tace mishi bata sonshi ne and yet ba zata taba iya auransa ba,shi ya rasa dalilin da ya sa mata suke son haramta abinda Allah ya halasta saboda wata al’ada ya sani sarai in ya samu abdul da batun yana son diyar sa ba tarr da kyafta ido ba zai bashi ita but shi baya son yi mata dole yafi son on her own ta soshi ta yarda da auransa which he doubt hakan zai taba faruwa.1

“Uncle ya office daddy yace kwana biyun nan aiki yayi maka yawa, gashi muma mun kusan shiga camp.” Dan tattare gira yayi yace “oh haka ne fa i almost forget,ai ke kina Abuja abinki so baki da matsala, kinje kin duba company din da zaki yi serving kuwa? ” dan tabe baki tayi tace “uncle i thought kai zaka kaini.” Rolling idanunsa yace “sai kace wata baby? At 23 sai an raka ki? Its an official visit dole ki nuna jajircewanki akan abinda zaki je yi.” Gyada kai tayi kaman tana gabanshi tace “toh shikenan uncle insha Allahu zan yi kokari inje *moh interprises* in gabatar da kaina.”1

Kayataccen murmushi yayi yacw “good thats my girl.” Murmushi itama tayi tace “uncle kenan” da haka yayi ta jan ta da tadi tana amsashi sama sama dan ita sam bata son ta bashi impression din zata aureshi don ta san yanzu kowa maganan auranta ne ya tsone mishi ido tunda ta gama makaranta sam bata san ya zata yi ba.1

Ba wai ta rasa manema bane ah ah haka  kawai ba ta son abinda zai hadata da wani namiji marwan ya riga ya tambara ya’ya maza a wajenta yayi mata tabon da ya kasa warkewa,shine mutum na farko da ta taba so a da tayi tunanin khalid shine first love dinta sai da ta hadu da marwan ta gane ba son khalid tayi ba kawai a wajensa ne ta samu attension shi yasa.1

Murmushi tayi tuno da khalid for quite sometimes tana following dinsa a social media,yes yanzu tana da accounts da social media tana following dinsa on twitter,facebook,instagram da dai sauransu tana ganinshi amma shi baya ganinta.1

Yayi kyau ya kara zama well polished dan bafillatani tutor dinta sosai tayi missing dinshi ta san yanzu ma wata kila ya manta da ita.2

So tari ta kan attempting yi mishi magana ta dm but ta kasa sai dai kawai ta bi tweets dinsa da sauran posts dinsa ta liking ta sani ba zai taba tantanceta a cikin dumbin likes dinsa ba ita kuma bata taba commenting akan wasu abubuwan da yake sawa ba she doubt in ma zai wa comments dinta kallo biyu duba da yanda yammata ke throwing kansu a kanshi. Murmushi ta saki Khalid kenan me shago ta fada a fili ko rufe baki ba tayi ba wayarta tayi wani marayan kuka dariya tayi tunowa da tayi a zamanin da khalid kadai ke yi mata flashing lallai khalid ya kware wajen basaja. Yanzu kam ta san ba kowa bace da ya wuce Rabi yar aikinsu kuma abokiyar hiranta dan har yau maimunatu bata da wata shakikiyan  kawa in ka dauke Jalila itama da yanzu take shirin yin aure a dai dai lokacin da maimunatu take cikin camp kwarai tayi bakin cikin rasa bikin jalila toh amma ya bawa zai yi.1

STORY CONTINUES BELOW

Kiran number Rabi tayi da itama a halin yanzu tayi aure har da diyarta daya me sunan maimunatu suna kiranta hajiya karama murmushi tayi lokacin da rabin ta dauka tana mata karadi ta sani awan shan dariyarta ya kama.

1

A cikin kwanaki ukun nan Maimunatu bata samu sukuni ba sai shirye shiryen zuwanta camp take sai taje kasuwa ta dawo sai ta tuna tana buqatan wani abun haka tayi ta zarya tsakanin kasuwanni har dai ta samu ta kammala suka shiga camp

On the first day it was very hectic,check up,registration da sauransu. Bata samu ta gama registration ba sai bayan la’asr Maimunatu couldnt believe her eyes da ta ga kusan su rai ashirin zasu rayu a daki daya a hankali ta furtawa kanta sati uku ne kawai maimunatu.1

Wanka ta fara yi sannan taje neman abinda zata ci, da wuri ta kwanta saboda gajiya.

Tun karfe ukunta fara jin hatsaniyar mutane ana tashi yin wanka saboda karfe hudu za a hura wistle na zuwa parade ground  ji tayi kaman ta daura hannu a kai dan sam baccin bai isheta ba gani take ko minti goma bata yi da rufe ido ba.

Haka rayuwa a camp ya kasance tun yammatan na jin ciwon jiki har suka ware tsakanin maimunatu da kowa gaisuwan mutunci ne da murmushi amma sam bata yarda tayi kawan da zata shiga jikinta ba dan dama ita haka take da mugun wuyan sabo.1

Wata rana tana zaune a mami market tare da wasu corpers din suna cin abinci taji wasu sojoji suna hiran wani captn moh daya daga cikin soldiar din ne yace  cikin broken english “na so ace captn moh ne imcharge of batch din nan,ban san ya yake yi su mishi abinda yake so ba.”1

Ba tare da dayan ya dago daga cin sakwaran sa ba yace “ni kuma naji dadi da ya tafi course din nan baka ganin yanda matan corpers din ke gwaking akan sa haushi abin yake bani shima sai kaga yana tafiya with full of grace irin shima wani shege din nan ne.”1

Hararansa dayan sojan yayi yace “kai banza ne kowa yaji ka ya san kawai kishi da hassada kake yiwa bawan Allahn da bai ma san kana yi ba,wawa kawai.” Daga nan kuma sai fada ya kaure tsakaninsu da haushi dayan ya tashi ya tafi.1

Dai dai lokacin maimunatu ta gama itama ta mike tana mamakin mutane da kirkiri basa boye bakin cikinsu,tabe baki tayi ta kama hanyan hostel.1

A kwana a tashi maimunatu har sun gama kwanakin su a camp suna shirin zuwa gida sosai kowa yake farin cikin tafiya gida sai kuma reporting to inda zasu yi serving sam maimunatu bata samu ta leka *moh interprises* ba kafin ta tafi which means zata sai ranan da zata reporting zata je.1

Haka kawai ta tsinci kanta da dokin aiki a *moh interprises* she wants to make a good impression who knows bayan service dinta su dauke ta a aiki cos Allah ya sani sam bata son aiki a karkashin mahaifinta duk da ta lura tskaninta da momy yanzu sai ido ko dan ta lura da yanda uncle sufyan ya damu da lamuranta ne ya sa oho.1

Murmushi tayi tuno da uncle sufyan,tab lallai da ta shayar da momy mamaki auran mijin yayarta dariya ta kyalkyale dashi hasko fuskan momy da tayi in taji labarin uncle sufyan na sonta.1

Sam bata mishi kallon nan har gobe a second mahaifi ta dauke shi mami kuma mahaifiya dan bata taba manta karamcin mami a wajenta lokacin sa take yarinya.1

Yau satinta guda da dawowa,sha’awan shiga cikin gari ne ya ratsata tsam ta mike tare da nufan closet dinta doguwar riga bubu ta dakko ta saka a rayuwarta tana kaunar gowns ko dan sun fi saukin sawa ne oho,haka marwan yana sonta cikin doguwar riga musamman in zata fita ko dan kar wani namijin ma ya kalle mishi ita.”1

Dan bata rai tayi tuno da marwan a hankali ta zura hannunta can  cikin closet din inda ta zakulo teddy bear dinta a hankali ta danna tsakiyan babyn “happy birthday miemie” teddyn yace in a tiny voice wani siririn hawaye ne ya zubo mata a hankali ta furta “marwan why?” Bayan hannunta ta saka ta goge fuskanta tare da wulla teddy din cikin closet ta koma gaban mirro tana kara gyara fuskanta,tare da fesa turare masu sanyin kamshi a jikinta.

A hankali take taku ta fito zuwa dakin momy dan knocking tayi sannan ta murda kofan ta leka da kanta “momy bari inje sahad pls.” Tabe baki momyn tayi tace “Allah kiyaye hanya.” Bata ce komi ba ta ja mata kofar ta barta da hararen kofa “shegiya yarinya ta gansame ko tunanin aure bata yi tafi son ta zauna ta hana mutum sikit shi da gidanshi mtssww.”1

Maimunatu key din karamar motan daddy ta dauka dan har yau daddy yaki ya bata mota tun lokacin da momy ta taba nuna mishi matsawar ya bata mota a matsayinta ma budurwa duk kudin namiji tsoron tunkararta zai yi dan zai ga kaman tafi karfinsa. Ajiyar zuciya maimunatu ta sauke tana sarrafa steering wheel momy kenan with her smart way inshaaAllah da kudinta sai ta siyawa kanta mota shi yasa sam bata son aiki da daddy dan kar ma ace da kudinshi take facaka dan kam she plan on spoiling herself da guminta (just like me😁) duk da ba wai daddy ya kasa bane tsab yana sauke hakkinsa dai dai gwargwado sai dai sometimes manuplating acts din momy na shiga mata hanci da kudundune.1

Tana wannan tunanin ta parking motan ta dauki purse dinta cikin store din tana tafe tana tunani bata ankara ba taji ta bangaji jikin namiji har ledarsa da yayi siyayya ta watse a kasan kafarsa da sauri ta dago tana bashi hakuri kalman hakurin ne ya makale a bakinta ganin fuskar da tayi arba da shi,shima da sauri ya zare farin glass din idonsa yana kallonta da mamaki……..

Da mamaki suke kallon juna can sai kuma ta saki murmushi tsugunawa tayi tare da tattara abubuwanshi da suka watse a kasan feet dinshi har lokacin bai ce komi ba bai kuma motsa ba sai kallon ta da yake yi kawai.2

Mikewa tsaye tayi tare da bawa mutane hanya kasancewar a dai dai entrance din suke tsaye wani ne ya dan matsar dashi daga hanya ganin bashi da niyyan matsawa sai a lokacin ya tattaro duk wani yawu da ya rage a bakinsa yace “maimunatu?” Ya fada ta sigan tambaya dan kara tabbatarwa kansa1

Dan baya ya koma tare da fad’in “wow! Oh My God! I cant believe this.” Hannunsa daya ya sa ya dafe bakinsa yayin da dayan hannun ya rike kugunsa dashi “my God! You have grown up and turn into a beautiful woman! Yah Rabb!” Dariya tayi tace “now that hurt kenan da bani da kyau.”

Dan komawa baya yayi yana kara kare mata kallo sai da ta tsargu yace “no baki gane then u were a kid bu now….. Wow! I cant say,i dont know whats hidden beneath this baggy gown but right now what i see is a grown up beautiful lady.” Sosai maganarsa ta daki zuciyarta so all thia while kallon yarinya yakr yi mata bai kalleta a matsayin mace ba sai yau?2

Murmushi tayi tace “dan Allah bari,wani in yaji ka sai yayi zaton rabon da ka ganni tun ina shekara 8 ne ba 18 ba.”1

Girgiza kai yayi yace “17” a dan cikin rashin fahimta tace “sorry?” Dan hadiye yawu yayi yana kallon kyakyawan fuskanta babu abinda ya canza sai dan kumatu da tayi “i mean kin tafi shekarub ki 17 not 18.” Dariya ta yi tace “toh naji almost all the same dictective dan fulani.”1

“Ahhh so kin san ni wanene?” Ya tambaya knowing the answer already waye bai san shi ba a arewa maybe da wasu sashi na nigeria

Dariya tayi tana gyada kai dan waige waige ya fara kafin yace “akwai wani coffee shop a kasan nan not very far from here ina ga mu karasa wajen because there are a lots of question i want to ask you,sai dai in ko kina da abin yi yanzu?” Ya tambayeta girgiza kai tayi tana mishi mirmushin da ya lura yanzu its always on her face unlike da, da kullum fuskanta a hade and she always looked distant.1

A hankali suka fara taka hannunsa sike cikin aljuhu yayin da nata yake rike da purse dinta tare da ledansa da taki yarda ta bashi.

“So yaushe kika dawo?” Ya tambayeta suna kokarin shiga cafe din daga kai tayi tana kallon farin fuskansa dake dauke da dogon hanci madaidaitan idanu tare da kwantaccen bakin saje tace “ai ina ganin ko shekara biyu ban yi a can ba na dawo.” Da mamaki yaje kallonta har ya ja mata kujera ta zauna shima ya zauna.

Sai kallonta yake yi not sure what to ask her next rufe fuskanta tayi tana dariya tace “wannan kallon fa?” Kyafta idanu yayi tare da kawar da kai yana murmushi bai son kallon yayi yawa haka ganin abin yake yi kaman a mafarki wai yau gashi ga maimunatu he never thought zai kara ganinta.

2

“Ai toh mamaki nake yi da kika ce wai baki yi shekara biyu a can ba,toh karatun fa?”

Daga kafadu tayi tace “na zo na karasa a nan yanzu haka ma service nake yi though ban fara ba sai monday”

Ta bashi amsa a nitse,relaxing yayi a kujerarsa yace “ahhhh kune batch din da suka fito daga camp kenan?” A hankali ta gyada mishi kai.

“So what happened?” Ya tambayeta yana kallon kwayar idonta kau da kai tayi sannan ta kuma dawo da kallonta kanshi tace “what happened what?” Daga kafadu yayi yace “what happened kika baro can kika karasa karatunki a Nigeria.” Tabe baki tayi tace “nothing really haka nan daddy yace in dawo kuma,you know how he can be.” Ta bashi amsa ba tare da taje details din abinda ya dawo da ita ba,there is no need of that.”1

STORY CONTINUES BELOW

Gyada kai yayi yace “yeah haka ne.” Amma deep down ya san akwai wani abu a kasa.”1

“So dictective dan fulani enough about me ya kake ya rayuwa,how is life treating you?”

Dan watsa hannu khalid yayi yan murmushi yace “as you can see life is treating me quite well.” Gyada kai tayi tana yarda da abinda yace tace “haka ne,ai ina following dinka ina ganin activities din da kake yi,kuna kokari sosai Allah ya kara taimakawa amen.”1

Kankantar da idanunsa yayi yace “maimunatu kina following dina on social media amma not once did u care to send me a dm?”  Dariya tayi tace “roh naga kai celebrity ne shi yasa ban san dms nawa kake recieving ba everyday so ba lallai bane ma ka gane nawa har ka kulani.” Shiru yayi yana kallonta yayin da maganarta ke ratsashi tabbas haka abin yake sosai kullum inbox dinshi ke cike da unread messages da bai san ta inda zai fara karanta su ba.1

“Toh keh why didnt you ever called tunda kin san bani da layinki na can na gwada asalin  naki like hundered times baya shiga i was sick worried wani hali kike ciki in a new place,tunda kika tafi babu labarin ki is as if you never exist, har kullum kina raina,i missed you…” Ya karasa maganan a sanyaye.1

Sauke kanta kasa tayi tana wasa da yatsunta yayin da idanunta ke kawo kwalla she did to him exactly what marwan did to her ta san yanda yaji cos she felt the same way da marwan ya tafi babu labarinsa even though shi da ita ba dating suke yi ba but they cared about each other,is she like marwan in anyway? Girgiza kai tayi tare da jan hanci tana kokarun mayar da hawayenta amma sai da suka zubo bayan hannunta ta saka ta goge a can saman kanta ta tsinci muryansa “ahhh now this is the maimunatu i know shagwababbiya me ocean of tears.” Dariya tayi wasu hawayen na zubo mata,bude purse dinta tayi ta fito da tissue tana goge fuskanta.2

Murmushi yayi ganin ya sakata dariya somehow ya san ba laifinta bane sa bata contacting din sa ba.

Sai da ta gama gyara fuskanta ba tare da ta kallesa ba tace “you fooled everyone har dani.” Gyada kai yayi yana sipping coffee dinshi da bata san yaushe aka kawo ba,ba tare da ya tambayi me take nufi ba ya bata amsa “i was just doing my job.” Gyada kai tayi tana kallon wayarta da tayi haske ta dauke ta san rabi ce dariya tayi tace “u were so mean har flashing kake min.” Dariya yayi yana tunowa har kati take saka mishi yana sonta because she have a very good heart a lokacin yana fata ya gama assignment dinsa ya gabatar da kansa sai abubuwa suka juya wannan karon duk da abinda yake shirin tunkarosa ba zai yi wasa ba.1

“Dole inyi duk yanda zanyi in badda kammani na ko mahaifana basu san inda nake ba a cikin garin abuja ba.” Gyada kai tayi cike da gamsuwa.

Sun  kwashe fiye da awa biyu suna hira kafin daga bisani suka exchanging contact tare da yi mata alkawarin  zai kawo mata ziyara.

Ranan monday maimunatu ta tashi da doki ta yi shirin zuwa aiki.

Tsaye take a gaban mirror tana sanye cikin uniform dinta na NYSC sosai suka yi mata kyau dan curvy hips dinta ya fito a cikin wandon sosai yayin da karamin kugunga ya rike belt din da kyau.1

Ta dade tana kallon kanta dan ita da kanta tayi wa kanta kyau murmushi tayi ta saka mini hijab dinta yayin da ta cusa hular cikin jakanta.

A hankali take sauka daga stepa din fuskarta dauke da murmushi bakinta dauke da addu’ar fita gida, a tsakar palo ta sami daddy a tsaye da alama ita yake jira dan shi zai saiketa a *moh interprises* cikin farin ciki ta fara gaishe shi kallonta yayi shima fuskarsa dauke da murmushi yace “kaga corper!” Dariya tayi tare da hade hannunta a bayanta momy ce ta fito hanninta rike da brief case din daddy a nitse maimunatu ta gaisheta tare da yi mata sallama.

A hanyar su ta zuwa babu abinda daddy yake yi mata sai nasiha akan ta rike mutuncinta kuma ta zauna da kowa lafiya har su rabu na dan lokaci ne.2

Maimunatu tasha mamakim ganin girman company din a yanda ta samu labarin campany 50 story building ne wanda daga sama har kasa glass ne baki bude take kallon building tana mamakin yawan ma’aikatan da suke aiki a wajen ta san bata da chance din samun aiki a wajen sam bata ma sa rai ba zata yi service dinta kawai ta kama gabanta.2

STORY CONTINUES BELOW

Bakinta dauke da addu’a ta shiga companyn a reception din taga wata mata wacce ta dan manyanta zaune gaban wani kyakyawan table sai wani saurayi a ta can gefe shima.

Gabatarwa da matan kanta tayi da murmushi matar ta mata maraba sannan ta directing dinta to 15th floor nan office dinta yake.

Bayanin aikin da zata yi mata tayi.

Tayi mamakin matsayin da aka bata secretary na MD din company din zata zama kasancewar asalin secretary din nata tayi aure kuma ba a garin abuja take zaune ba.

Ko da ta haura 15th floor din maimunatu bata yi tsamanin ganin MD din a matsayin mace karama yar shekaru 25 sosai abin ya burgeta MD din tana zaune a hadaddiyar office dinta wanda furniture din ciki ma kawai abin kallo ne.1

“Wow” shine abinda maimunatu tace MD din nai suna Mubeena ba ilimi da matsayi kawai take dashi ba tana da kyau sosai black beauty ce fuskarta doguwa ce me dauke da dogon hanci da manyan idanu sai baki me dauke da jan labba she is just so beautiful.

Murmushi ta sakarwa maimunatu dan yanda maimunatu ke appreciating kyaunta haka itama take yabawa maimunatun kasancewarta baka me haske wato wankan tarwada shape din fuskanta oval shapr me dauke da karamin baki da madaidaitan idanu sai gashin gira da na ido cikakku she is naturally beautiful ta ayyana a ranta.1

Gabatar da juna suka yi sannan tayi maimunatu bayanin aikin da zata  inda maimunatu ta tabbatar mata zata yi kokarinta.

Mubeena akwai barkwanci nan da nan taji tana son maimunatu she treat her more like a frnd than an employee  duk da maimunatu har yanzu bata saki jiki da kowa ba kasancewar ta me wuyar sabo da mutane tsakaninta da yan ma’aikatan gaisuwa da murmushi.

Asalin companyn ko ince ma’aikatan company din yawancin yan uwa ne sai daidai ku irin su maimunatu me company Namiji ne yayin da president din company din ta kasance kanwarsa yar kimanin 30 a duniya  sunanta mufleeha tana da aure da yara biyu in ka ganta ba zaka taba cewa tana da aure ba balle ta kai shekarunta da ka ganta ka ga mubeena wacce ta kasance autar su sauran ma’aikatan kuma duk yawancin cousins ne sai family frnds.1

A yanda labari ya zowa maimunatu girma da arzikin company din bai dade da bunkasa ba har sai da ya shiga hannun moh family sosai suke kokarin gina arzikin family dinsu.

Wata rana maimunatu na zaune a desk dinta tana kokarin rounding up wasu ayyuka kafin ta khalid ya zo daukanta.

Karan takalmin mubeena da fita yanzu ne ya jawo hankalinta ta dago tana kallon mubeenan da ta tsaya tana kallonta fuskarta dauke da fadaddan murmushi kafin maimunatu tayi magana tayi carab tace “ga dan fulanin saurayin ki a waje yana jiranki.” Rolling idanu maimunatu tayi tare da dafe goshi tace “for the past 5 months ina kokarin fahimtar dake cewan khalid ba saurayina bane kin ki yarda.” Daga kafadu tayi tace “ko dai bai furta miki yana sonki kuna son juna,ku tsaya kallon ruwa kwado ya miki kada kina ce ba dan habibi dan tuntuni ban yi gaba da wannan saurayin naki ba.” Ta karasa maganar tare da kashe ido daya1

Girgiza kai maimunatu tayi tana tattara tarkacenta tace “maza kiyi haka kin ga sai mu cigaba da zama a moh interprises tare dake.” Zaro idanu tayi tana bin bayan maimunatu da ta shiga elevator dan sauka kasa tace “no way in hell,but on a serious note ina sonki da gayen nan shoot ur shot yarinya.” Girgiza kai maimunatu tayi tana murmushi tace “sai da safe ma’am a gaishe da habibi.” Dan fari da ido tayi na jin dadi kafin ta dagawa khalid dake tsaye jikin motarsa hannu itama ta shiga nata motan.1

Karasawa jikin motar maimunatu tayi tana murmushi ta bude ta shiga kafin shima ya shigo sai da ta relaxing sosai sannan tace “sorry i couldnt pick ur call ashe wayar na silent ban sani ba.” Gyada kai yayi yana yiwa motar key.

“Ya aiki?” Ya tambayeta a nitse.

Kwantar da kanta jikin seat din tayi tace “fun but hectic.” Mmmm shine kawai abinda yace dan bude idanu tayi tana kallonshi sai lokacin ta lura fuskarsa kaman akwai damuwa.

Cikin sanyin murya tace “me yake damunka na ga kaman kana cikin damuwa?” Kallonta yayi yana dan murmushi yace “sonki ne ya sani damuwa cos ban so ko kema kina jin abinda nake ji ba.”2

Dan zaro idanu tayi tare da bude baki tana rufewa kaman kifi amma kalma daya ya gagara fitowa cos bata taba expecting abinda zai ce ba kenan ta san yana nuna mata alamun yana sonta ta san sooner or later zai furta amma bata taba tunanin ta wannan sigar zai furta mata ba tayi tunanin something more romantic kaman yanda marwan ya mata.2

“No! Ba ta son yayi mata yanda marwan yayi mata marwan was just a fairytale he was never real shi yasa duk abinda yayi mata yaudara ce kawai ba soyayya gyada kai tayi tana yarda da kalmar yaudara sai dai me sai ta tsinci muryan khalid na cewa “i take that as a yes?” Da sauri ta rufe fuskarta tana murmushi he misunderstood gyada kanta as answer dinsa but yes ansa din iri daya ne.

1

Dariya yayi yana parking motarsa a kofar gidansu yana shirin magana wayarsa ta dau ringing da alama important call ne dan ta tsakankanin hannunta ta hango yanda ya bata rai kafin ya picking call din.

Ta tsakankanin yatsun nata take hango kyakyawan farar fuskarsa mai dauke da bakin saje juyowa yayi yana kallonta da sauri ta hade yatsunta tana murmushi rufe mouth piece din wayar yayi kafin yace mata pls excuse me think about what i said kafin in gama waya dan ba zan bar nan ba sai naji proper amsa.” Daga haka ya fita yana fita a motar ta sauke hannunta tana murmushi iskan bakinta ta fitar sannan ta dauko wayarta dake kife a kan cinyanta data dinta ta bude cos she have nothing to think about in akwai mutum daya a duniya da ba zai cutar da ita ba toh khalid ne.1

Abinda idanunta ya gano mata a saman wayarta a rubuce da hoton wanda ta gani rungume da wata macen shi rikita mata brain komi nata ya tsaya cak……….

A rikicd take bin rubutun dake rubuce ‘The famous dictective Dan fulani is getting hitch on 19/5/20’ cikin rawar jiki ta bude notifications dinta duk inda ta bi abinda yake threading kenan hotunan khalid tare da wata farar budurwa tsayuwa fadan kyan yarinyan ma b’ata baki ne fara ce kal da ka ganta kaga bafillatana usul.3

Hotunan gasu nan birjik in different styles da ka gansu kaga masoyan da suke son junansu.

Kur ta kurawa wani hoto da suke tsaye ya rike kugunta suna kallon juna suna dariya.1

Sam maimunatu ta kasa tantance halin da zuciyarta take ciki abu daya ta sani mamakin khalid ne ya cikata menene dabararsa na furta mata kalman so? Toh ko dai wasa yake mata ta dauki abin da gaske? Lallai kuwa da ya mayar da ita shashasha.1

Tana cikin wannan tunanin ya bude murfin motar ya shigo yanayin da ya ganta ya sha jinin jikinsa.1

Kwata kwata ba haka ya so abin ya zo ba,one thing with being famous kenan  abu daya na fita shikenan naka ya kare,ya so ace ya bayyanawa maimunatu soyayyar amma ya rasa ta inda zai fara fada mata yana sonta da aure amma sai ya auri y’ar uwarsa kafin ya aureta,amma me bayan ya ja kunnan Habiba sosai akan kar ta fitar da pre wedding pictures dinsu sai a week to bikin amma saboda kunnen kashi ne ta turawa laure kanwarsa ita kuma ta dora a stories dinta na social media daga nan kuma 1 to tell ten,10 to tell others.1

Wayarta ya leka ya ga hoton da take kallo take ya rintse ido yana addu’a ranshi,bude idon da zai yi ya ga idon maimunatu k’ur akan fuskarsa tana murmushi kafin yayi magana tace “congratulations Allah ya sanya alkhairi” daga haka ta sa hannu ta bude murfin motar tana shirin sa kafarta a waje ya rik’o hannunta tare da fad’in “wait!” Kallon hannunsa da yake rike da nata ta kalla sannan ta kalleshi abinda bai tab’a attempting yi ba kenan da sauri ya saketa ta fice.1

Cusa hannunsa yayi cikin kwantaccen  suman kanshi na asalin fulani yana cakudawa shi kam yanzu ta ina zai fara? Baya son ya rasa maimunatu a karo na biyu gaba daya yayi shirme da bai gabatar mata da maganan aure ba har maganar ya fito bai sani ba zata amshe shi a haka ko yaya?3

Ya san ba karamin sa’a yasha ba da bata kwasa mishi mari ba,dan ba ko wacce mace bane zaka gama gayawa kalman so kuma ta tsinci maganar aurenka a lokacin,ba ko wacce mace bacce za ta dauki abin da sauki da yawa zasu fassarashi a rainin wayo which shi gaba daya ba nufinsa ba kenan.2

Ya so ace bayan ya gama zayyana mata soyayyarsa sai ya fito mata da kalubalen da ke tunkararsu sai wannan wayar da ogansa yayi mishi ya katse masa hanzari har abubuwa suka jagule masa, wayarsa yake kallo kaman ya danna kiran layinta sai ya fasa “she needs space ya fada a hankali.” Da wannan tunanin ya ja motarsa ya bar kofar gidan

A bushe take jin zuciyarta tana jin ita kam inshaaAllah ta gama kuka akan wani d’a namiji just when she thought she is going to be happy boom sai ga pre wedding pictures dinsa ke yawo

Hhhhh toh ya aka yi ma bata taba zaton haka ba.1

Sam bata wani ji haushinsa ba,she did’nt expect after like five years da tafiyanta babu labarinta ya zauna babu wata a rayuwarsa yana zaman jiranta alhalin bai san zata dawo ko ba zata dawo ba and bama soyayya suke yi ba

Haushinta daya yana da daman fada mata hakan bayan haduwarsu  amma bai fada ba sai ma ya fito da wani salo wai yana sonta,yana sonta ya hadadu yake nufi kenan ko me? Lallai yana bori3

Kara juyi tayi akan gadonta tana latsa wayarta duk inda ka duba hotunansau kawai kake gani da wanda ya sani posting hotunan suke dan tabbas hotunan sunyu kyau sun dauku da yake an dace daga angon har amaryar kyawawane na bugawa a jarida who is she to compete with this damsel? Kara kallon smile din dake kwance akan fuskar yarinya mai suna Habiba tayi a fili tace “lucky you.”1

Message din Mubeena ne ya shigo wayarta ta status.

Miss Mubeena :_”ke wai da gaske dama ba soyayya kuke yi da dan fulank ba?”_

Murmushi ta yi tare da bata amsa da

_”eh”_

Miss mubeena :_”yanzu naga prewedding shots dinsa a tweeter sai da gabana ya fadi.”_

Dariya maimunatu tayi ta replaying mata da

_”toh gabanki ya daina faduwa ba soyayya muke ba balle kice ya yaudareni._” taji kaman ta gaya mata abinda ya faru tsakaninsu sai taga rashin amfanin haka kun santa da zurfin ciki.

  Emojis na sad faces ta turo mata can kuma ta turo da

Miss mubeen : _”Allah ya sani na soki da bawan Allahn nan and fron the way he ia looking at you wallahi yana sonki and zaki ce na fada miki muna tare.”_

Shiru tayi taba kara nanata karanta message din mubeena dan tabe baki tayi tace “toh in ma yana sona sai dai ya hakura with the way they are looking happy ba zan zo in shiga ciki ba.”1

Shiru tayi tana tunanin yanda kawai ta hakikance khalid na sonta deep down tana jin shi zata aura she is just waiting for him to confess his love to her dan kaman yanda mubeena tace her love is written all over his face ba mubeena kadai ke fadan haka ba duk wani da zai gansu tare sai yayi maganan yanda yake nuna kulawa akanta.1

Call dinshi ne ya kara shigowa wayanta for the tenth time kife wayar tayi a kirjinta dan bata shirya yin magana dashi ba yau sai da ya gama ringing ta dago da wayar.

Haka tayi ta juye juye har kusan sha biyu tana shirin kashe data dinta taga mubeena tayi status,na farko ta bude

_happy birthday to best brother in the whole wide world._

Sai na gaba kuma hoto ne da yaki budewa saboda network a kasa an rubuta _yau kam i will post ur picture ko da na 5 mins ne_1

Haka nan taji tana son ganin hoton mamallakin moh interprises.

Kiran uncle Sufyan ne ya shigo wayarta murmushi tayi dan ta san tayi laifi ya bar kasan ko sau daya bata kirashi ba.

Picking call din tayi bakinta dauke da sallama.

Sun kwashe a k’alla mintuna sha biyar ita da uncle sufyan suna waya inda yayi ta mata korafin bata son kiransa dariya kawai tayi dan ita bata ga ta inda zata dau waya ta kira uncle sufyan ba,toh tace mishi me?3

A haka dai suka yi sallama,wayarta ta tsirawa ido tana tuno me take yi kafin kiran wayan uncle sufyan ya shigo,wani status din da mubeena ta kuma yi ne ya tuno mata da abinda take son gani da sauri ta shiga status din nata inda taga har ta cire hoton sai rubutu da tayi kamar haka

_lucky those that were able to see his picture before he blastered me lol._ haka nan sai maimunatu bata ji dadin yanda bata samu ganin the face behind *moh interprises* ba.1

Kashe data dinta tayi tare da fita daga cikin whatsappp din wani irin bugawa kirjinta yayi ganin date da time dake fuskar wayanta yau birthday din Marwan ya subhana! Da sauri ta kife wayar tare da rintse idanu kaman wacce take ganin fuskar marwan din a cikin wayar.12

“He turn 34 in har yana raye.” Ta fad’a fili lokaci guda kuma ta zaro idanu jin abinda bakinta ya furta in yana raye? Where does that thought come from?1

Innalillahi wa inna ilaihir raju’un ta furta tare da yaye bargon da ta rufu da shi ta mike tsaye tana sintiri hannu ta dora a kai idanunta na kawo kwalla “me yasa ban taba yin tunanin ko wani abu ne ya sameshi ba? Ya rabbi ka sa ba haka bane, Allah kasa marwan lafiya lau yake yana raye,Allah kasa yaudarata kawai yayi amma yana rayuwa somewhere else cikin kwanciyar hankali.” Ta fada tana rushewa da kuka she cant bear the thought of wai marwan bashi a raye ta gwammace ace yau yaudaranta yayi ya tafi amma yana wani wajen ya fara ajiye iyali.1

Kuka take yi tana addua wishing din marwan all goods of life,tsohuwar laptop dinta ta dauko ta kuna,wanda bata wani abu muhimmi dashi tun bayan dawowarta daga cyprus limshe idanu tayi tana kokarin hana kanta aiwatar da abinda taake shirin aiwatarwa har laptop din ya gama booting.1

A hankali ta bude idanunta akan system din ta fara shige shige har ta samo abinda take nema wani folder ne da aka rubuta M.1

Ta dade tana kallon folder din har dai daga baya tayi shahada ta bude ba komi ke kunshe a cikin folder din nam ba sai hotunan marwan da wanda yake shi kadai da wanda suka yi tare.1

Rabonta da ta bude wannan folder din tun da ta bar kasar cyprus da gaske take bata son ta dinga tuno Marwan cikin sand’a ta clicking sannan ya bud’e hoton farko ta bude marwan ne ke zaune kan iron bench yana dariya sosai idanunsa a waje dama gasu manya hannunsa daya rike da littafi dayan kuma ya kai zai ansa wayar da take shirin daukan sa hoton dashi.1

Murmushi ne ya subuce mata hawaye na zubowa a kwarmin idonta she can vividly remember that day yana koya mata karatu ne. A hankali ta furta “happy birthday to you.”

1

Next hoton taje hotonsu ne su biyu a cikin kasan ruwa, sai wanda tayi mishi yana kan doki a ranch din frnds dinshi. Haka ta kwashe lokaci me tsawo tana kallon hotunan wasu tayi dariya wasu tayi kuka.

Kallon kankantarta take yi a hoton she wonder ne marwan ya gani a tattare da ita lokaci,she was so young and neive ziciyarta ne ya bata amsa da shi yasa ya samu yanda yake so a tattare da keh,kuka ta rushe dashi tare da rife fuskanta da tafukan hannunta.1

Fadi take “why? Why marwan? Why? Me na taba yi maka da na deserving wannan ukuban me na taba yi maka mai zafi haka? Ban taba nufinka da komi ba sai alkhairi i did nothing but love you amma ka zabi ka banzatar dani i just hope and pray banzatar dani din kayi ba wani abu ne ya sameka ba sabida har gobe har kullum kana raina,nayi iya yina na kasa cireka a raina bani da buri da fata da ya wuce ka fita a raina ba but all in vein ko da yaushe kana raina.” Haka ta dunkule a kan gadonta tana rusa kuka.1

Bacci bai dauketa ba sai wuraren karfe uku inda ta dinga mafarke mafarken marwan da mr moh kaman yanda ta lakanawa moh din.

Exotic mafarki tayi wai marwan na romancing dinta a cikin dakinta na cyprus.1

Da matsanacin ciwon kai ta tashi a makare kaman ba zata je office ba taga in ta zauna a gidan ma tunani ne zai dameta tana balla buttons din dogon top dinta wayarta ta fara ringing ba kowa bane sai khalid har ga Allah tunowa da tayi da marwan ya mantar mata da batun khalid da matsalarsa.1

Kan dressing stool dinta ta zauna kafin ta amsa kiran da dasashiyar muryata.

Amsa mata sallamar yayi duk sai yaji babu dadi da ya ji muryarta haka ya san kuka tayi saboda ya sani tun kafin tafiyarta karatu tana sonshi yaki bayyana mata soyayyarsa a wannan lokacin saboda kar ya tabbatar da abinda daddy yake cewa na suna soyayya ne,ya san dole yanzu taji babu dadi musamman yanda a dan watannin da suka gabata babu abinda yake nuna mata sai zallan soyayyarsa da kulawarsa duk da kuwa bai taba furta mata ba sai a jiyan.1

Murya a sanyaye yace “munah ya kika tashi?” A hankali ta amsa mishi da “lafiya lau kai fa?”

Lumshe idanu yayi yace”alhamdulillah.” Daga nan kuma yayi shiru ya kasa cewa komi,tana shirin ce mishi tana shirin zuwa aiki ne yace “munah jiya sai kika ki sauraro na,why? Ban sanki da haka ba,me yasa ba zaki tsaya kiji uxuri na ba is not fair.”1

Murmushi me ciwo ta dan saki sannan tace “bana binka bashin bayani,ina ganin girmanka da mutuncinka bana son inji ka yi min bayani irin wanda kullum maza suke yiwa yammata ne.”1

Shima a gefensa murmushi yayi maimunatu ta bala’in dacewa da rayuwarsa da taimakon Allah sai ya mallaki maimunatu.

“Ba kya so kiji nace miki cousin dita ce ko? Ba kya so ince miki a gida ne aka ce in aureta ko?” Shiru tayi bata ce komi ba dan kaman ya shiga ranta ta sani sarai salon yaudaran samarin yanzu kenan.1

“Munah!quite alright Habiba cousin dita ce amma ba ayi min dole in aureta ba a gida aka ban shawaran auranta ni kuma nayi na’am dashi saboda tana da hankali sannan kuma…” Sai yayi shiru itama shiru tayi tana karasa mishi maganan a zuciyanta sannan kuma yana sonta.1

Numfashi ya sauke yace “anyway zan auri habiba sannan still ina so ki bani dama kafin ki yanke hukunci kar ki nesanta kanki dani kar ki yanke hukunci ba tare da kinyi zurfin tunani ba abinda nake so inyi ba haramun bane kin sani maimunatu kar ki haramta mana juna.”1

Dogon numfashi ta ja ta sake sannan tace “naji amma ka bani lokaci pls.” Gyada kai yayi kaman yana gabanta yace “ok,but pls karki kara yin kuka.” Murmushi kawai tayi a ranta tana fadin if only he knows kukan me ko na wa tayi

Sallama suka yi tana cigaba da shirinta,wani glass dinta ta dauko kato baki ta saka saboda ta rufe kumburin da fuskanta yayi na kuka..1

Ko da taje office da mubeena taga yanda fuskanta ya kumbura sosai hankalinta ya tashi dan duk a tunaninta saboda khalid ne.1

Suna cikin office din mubeenan ne maimunatu ta kai mata wasu files ta signing.

A hankali mubeena ta tashi ta nufi kan sofan dake can wani bangaren office din tayiwa maimunatu nuni da ta zo ta zauna.

A nitse maimunatun taje ta zauna,fuska cike da damuwa mubeena tace “sis kiyi hakuri da yanda rayuwa ta zo miki kowa da kalar tashi jarabawan,fatanmu da kokarin mu har kullum shine Allah ya bamu ikon cin jarabawan nan,na san da zafi ace ka rasa masoyin da kake so it hurts alot musamman ma ace ka rasa shi ne ga wata macen,sai ka fara questioning kanka ta inda ka kasa,my dear ba kasawa kika yi ba shi haka so yake mutum yake,beside wannan me zata nuna miki banda farin fata?”

Murmushi maimunatu tayi tace “ba komi nagode sosai da kulawarki amma ni damuwata ba na khalid bane kamar yanda nace miki ni da khalid ba soyayya muke yi ba fa.” Gyada kai tayi tace “ba soyayya kuke yi ba amma kina sonshi.” Shiru maimunatu tayi tana kokonton ta gayawa mubeena tana da wanda take sone ko zata barta da maganan khalid ko kuma yaya?1

“You see na gaya miki kina sonshi gashi kin kasa denying,ni dai hakuri shi zance kiyi sabo…”

“Eh ina sonshi amma zuciyata tana tare da wani.” Maimunatu ta katsewa mubeena maganarta ba tare da ta gama shawara da zuciyanta ba.1

Baki bude mubeena ke kallonta “ban gane kina sonshi amma Zuciyanki na wajen wani ba,me hakan ke nufi?”

Hannu maimunatu ta sa ta shafe fuskarta kafin tace “it means akwai wanda na so ya kasa barin zuciyata duk da kuwa ina jin son khalid amma son…son…m……….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page