RAYUWAR ASMAU CHAPTER 11

 RAYUWAR ASMAU CHAPTER 11

Zama yayi shima yai murmushin kawai.

Mami ce ta sauko. Hira suka dan taba sannan yai masu sallama ya tafi.

Zuciyar fal da tunanin Asma’u. Yana kaunar Asma’u son Asma’u yai masa wani irin kamu.

Asma’u kuwa tana shiga daki ta fada kan gado.

Ido ta lumshe ba wanda ya fado mata sai Yaa Aslam, Ta jima tana juyi duk ranta ba dadi sannan ta mike ta shiga cire kaya.

Tana gamawa ta fada bandaki wanka ta fara. Tana gama wa ta tayi alwala.

Sai da ta shirya cikin kayan baccin ta dogon wando da riga fare tas sannan ta tada sallah. Ta jima tana addu’a kan Allah ya kawo mata dauki sannan ta Mikewa jiki a sanyaye ta bude firij.

Lemo ta dauko ta koma kan gado ta zauna. Wayar ta ta dauka ta latsa number Yaa Buhari.

Da sauri ya dauka. Murya ta shagwabe ta ce,

“Yaya shine ka manta dani ko?”

Murmushi yayi ya ce,

“Tayaya zan manta dake Sis. Na ta neman number ki ke da wife ban same ku ba.”

Ajiyar zuciya ta sauke ta ce,

“To Yaya Ya hanya yasu Momy da Dady.”

“Suna lafiya. Ince kuma kuna lafiya.”

Kai ta gyada masa.

“Asma’u me yake dumun ki?”

Dan yaji muryar ta ba dai dai ba.

Damuwar ta tai kokarin kawar wa sannan ta danyi murmushin karfin hali ta ce,

“Ba komai.”

“Kin tabbata?”

ya tambaye ta.

Kai ta gyada masa. Yace

“To sai da safe.”

Sukai sallama. Kwanciyya tayi tana tunanin Sir Sabir kuma.

“To tinda na rasa Ya Aslam me yasa ba zan karbi duk wanda ya so ni ba. Sir Sabir bai da makusa. Yana da kyau ga ilimi ga addini ga nutsuwa me kuma zan nema bayan nan.”

Tayi juyi, ta kuma fadin,

“Duk da haka dai ina son Yaa Aslam ko ba komai Yaa Aslam yayanah ne,”

Hawaye ne ya zubo mata. Ta jima tana kuka sannan ya mike tayo alwala ta tada sallah.

Ta jima tana kai kukan ta gun Allah. Sannan ta hau karatun Alkur’ani.

Har akai sallah asuba tana kan sallaya. Wanka ta kara yi sannan ta dawo ta tada sallah.

Tana idar wa ta fada kan gado sai a lokacin wani bacci mai nauyi ya dauke ta.

Mami tinda ta tashi bata ga Asma’u ba ta leko ta tadda tana bacci ta sauka kasa kawai. Dan tasan ba zata aiki ba tinda bata sauko ba.

Aiki tayi ta hada musu break sannan ta yi wanka.

Har karfe biyu Asma’u bata sauko ba. Mami Ta hau sama ta dubo ta yafi sau uku amman bacci take kuma jikin ta ba zazzabi.

Wannan ne yasa Hankalin Mami ya dan kwanta.

Karfe biyu da rabi Zainab ta karaso gidan. Mami ta gani zaune a falo.

STORY CONTINUES BELOW

Har kasa ta durkusa ta gaishe ta cikin jin kunya.

Mami ta amsa cikin sakin fuska da soyayya.

Mami ta ce,

“Ki hau sama yau tana can ko aikin ma bata je ba.”

Zainab ta ce,

“Mami lafiya dai ko?”

Mami ta ce,

“Lafiya lau, ina jin dai abin ne ya fado mata kuma.”

“Allah sarki.”

Zainab ta fada tana mikewa. Ta ce,

“Mami addu’a dai xamu ta taya ta da ita.”

“Haka ne, Zainab Addu’a kuma kullum yi muke. Sai dai fatan Allah ya amsa.’

“Ameen!”

Ta hau sama. Asma’u na kwance ta daka mata duka. Da sauri ta mike tana sosa wajen da ta dake ta.

Tana mutsuka ido. Kallon ta Asma’u tayi ta ce,

“Zainab har kin zo?”

“Eh! Kinsan karfe nawa kuwa?”

Ta fada tana kallon idon ta da suka kumbura saboda kuka.

Asma’u ta ce,

“Uhmm wallahi bacci na sha ban sani ba.”

Ta fada tana mikewa tsaya, kallo Zainab tabi ta dashi har ta shige bandaki.

Kai ya girgiza, a rayuwar ta tana son Asma’u tana jin Asma’u kamar kanwar ta, duk abinda ya damu Asma’u itama damun ta yake.

Ta rasa tayaya zata shawo kan Asama’u har ta daina damuwa. Duk da tasan da wuya.

Mikewa tayi ta gyara gadon ta share dakin sannan ta koma ta zauna.

Tana zama Asma’u ta fito tana tsane jikin ta. Kallon dakin tayi ta kalli Zainab ta ce,

“Ke dai bakya gajiya wallahi.”

Ta zauna tana shafa mai, ta ce,

“Yau ina zamu?”

“Ke dai ki sauri zamu je, madobi fa.”

Kai Asma’u ta gyada.

Mai kadai ta shafa ko powder bata shafa ba ta mike ta saka wata doguwar rigar Atamfa. Mai A shape. Tana da dogon hannu. Mayafin after dress ta yafa ta dau wayar ta da mukullin mota ta ce,

“Muje ko?”

Zainab ta ce,

“Kin karya ne?”

“A’ah muje zan dau Maltina ta ishe ni ma.”

Mikewa tayi tabi bayan ta.

Mami tana falo tana ganin su ta saki murmushi ta ce,

“Kun fito.”

Asma’u ta ce,

“Eh! Mami ina kwana?”

Mami ta amsa, da

“Lafiya lou kin tashi lafiya?”

Kai ta gyada ta mike ta nufi firij din falo ta dauki Malt guda biyu ta ce,

“Mami mun fita zamu je Madobi wajen yan ajin mu.”

Mami ta ce,

“To a dawo lafiya. Allah kiyaye hanya.”

Suka fita. Suna fita suka ci karo da Sir Sabir zai shigo.

Wajen sa suka karasa suka gaishe shi cikin girmamawa. Amsa yayi yana bin Asma’u da kallo. Bai taba ganin ta da irin wannan shigar ba.

Zainab ya kalla ya ce,

“Amare ina zaku ne?”

Asma’u, Zainab ta kalla ta ce,

“Wallahi kati zamuje rabawa daga nan mune har madobi.”

Kallon su yayi ya ce,

“Madobi da kanku. A’ah muje na kai ku. Daman Buhari yai min maganar zuwa Madobin.”

Asma’u, Zainab ta kalla ta ce,

“Sis kinga Sir Sabir ya rage miki aiki.”

Asma’u dake danna wayan ta, ta dago ta kalli Zainab sannan ta kalli Sir Sabir da ya zuba mata ido.

Murmushi ta dan saki ta ce,

“Da ka huta ai.”

Dan Hararar ta yayi ya ce,

“Ku shige muje.”

Ya bude mata gidan gaba. Zainab dai kallon su ta tsaya yi tana cewa Allah yasa Sir Sabir ya so Asma’u dan ba karamin dacewa sukai ba.

Ga wani kallo da taga yana binta da shi.

Da haka ta shiga gidan gaba. Zainab ta shiga cikin gidan baya.

Maltina ta mikawa Zainab sannan ta mikawa Sir Dabir dayar ta hannun ta.

Bai amsa ba ya ce,

“Ke fa?”

Murmushi tayi ta ce,

“Na koshi.”

Ya ce,

“Ban yadda ba sha ki rage min.”

Zata ce A’ah ya ce,

“Ki sha ki ragen in ba rowa zaki min ba.”

Fasawa tayi ta sha kadan ta mika masa, hannu ya kawo zai amsa ya hade da hannun ta.

Kallon sa tayi ya kashe mata ido daya. Kai ta dauke ta cigaba da kallon titi.

Shiru tayi sai Zainab da Sir Sabir da suke hira.

Sai dai shi da yake dan tabo ta, in anyi abu ya ce,

“Ko Husnah?”

Da haka har suka karasa gidan su Hafsat.

Anan suka dan jima dan shima Sir sabir suna tare da Baban Hafsat.

Har abinci suka ci sannan suka taho, ranar shi ya dinga yawo dasu daga can zuwa can.

Har magariba sannan ya kai Zainab gida. Ana sukai sallah magariba sannan Asma’u tai mata bankwana suka taho.

A mota kuwa kowa shiru yayi shi yana tunanin taya zai kara cusa kan sa awajen Asma’u dan ya tabbata Asma’u baza ta ki shi ba sai dan kawai tana son Yaa Aslam ne.

Itama a zuciyar ta rokan Allah take Allah yasa kar yai mata maganar dan bata so.

Can ya dago ya kalle ta ya ce,

“Kin fadawa Maryam bikin ne?”

Kallon sa ta danyi sannan ta kawar da kai ta ce,

“Na fada mata, ta ce, next week ma zata zo.”

Kai ya gyada ya ce,

“Oh yanzu dai kun zama friends ko?

Murmushi ta dai yi kawai ba tare da ta bashi amsa ba.

Ya ce,

“Yaushe za muje ki gaida Mamah?”

“Ko yaushe ma!”

Ta bashi amsa.

“Da gaske?”

Ya tambaye ta.

Kai ta gyada. Kallon ta yayi ya ce,

“Ko yanzu ne?”

Kallon jikin ta tayi ta ce,

“A’ah dai.”

“Saboda me?”

Ya tambaya.

“Kalli jiki na fa?”

Ta fada tana kallon kan ta.

Murmushi yayi ya ce,

“Me jikin naki yayi?”

“A’ah dai.”

Ta fada tana tsare shi da idanun ta.

Da yake shima ita yake kalli take yaji motar na neman kwace masa. Saboda idon ta da suka ruda shi.

Da kyar ya kamo motar ya cigaba da tukin.

Daga haka bai kara cewa komai ba, har suka kara sa gdn.

Suna zuwa gida ya dire ta ba tare da ya fito ba ya ce,
“Ki gaida Mami. Dare yayi zan je wani waje ne.”

Kai ta gyada masa, ta ce,
“Mungode. Allah huce gajiya.”

Ta daga masa hannu. Shima daga mata yayi ya tada motar yai gaba.

Ciki ta shiga, Mami na falo ta same ta. Kan ta ta fada ta ce,
“Mami na gaji.”

Murmushi Mami tayi ta ce,
“Sannu ai fa ku da ku huta sai bayan biki kuma.”

“Uhmm Mami kinji Zainab wai sai naje na kwana. Bayan ni ba iya kwana zan ba wallahi.”

Mami ta shafa kanta ta ce,
“Sai ki san me zaki ce mata.”

“Kuma fa Mami har da Maryam yar Sir Sabir ma xata zo nan ta kwana fa. Mami zan ce mata kawai zan na zuwa da asuba.”

“Kwa san yadda zakuyi dai.
mikewa tayi ta ce,
“Mami me kika dafa ne.”

“Tuwo ne miyar agushi.”
mikewa tayi ta shiga kitchen ta hado abinci ta zauna tana ci.

Tana gamawa ta yi sama. Wanka tayi ta saka kayan bacci ta sauka kasa.

Akan kafar Mami ta kwanta tana kallo. Ta ce,
“Mami, kinga Yaa Buhari yaki ya dawo.”

Mami ta ce,
“To ai ke kkika tsayar dashi. Sakon ki Momy ta ce, ya tsaya gobe ya taho dashi.”

Murmushi tayi ta ce,
“Sakon me?”

“In ya kawo kya gani. Dazu ta kira ta ce, bata samu layin ki nace mata ai kin canja layi ne.”

Asma’u ta ce,
“Mami ba sake layi nayi ba. A office na bar waccen wayar ne shiyasa. Kuma aiki yasa bana kiran ta amman gobe zan kira ta.”

“Allah ya kaimu.”
“Ameen!”

Sun jima a falo kafin su mike kowa yai dakin sa.

Tana kwanciyya taji wayar ta na kara. Dauka tayi taga Sir Sabir ne.

Jiki a sanyaye ta dau wayar ta kara a kunnen ta. Ta yi sallama cikin sanyin murya.

Amsawa yayi yana sauke ajiyar zuciya. Shiru yayi kafin ya ce,
“Husnah na kasa bacci. Husnah da na rufe ido na ke nake gani, Husnah baki ji yadda nake ji ba.”

Husnah da tasan dadi da dacin soyayya sosai ta tausayawa Sir Sabir.

Shiru tayi, idon ta ya kawo kwalla dan itama ya fama mata ciwon dake cikin zuciyar ta.

“Husnah kina ji na?”
Jin sheshekar kukan ta ya sa ya firgita.

Ya ce,
“Dan Allah kiyi  hakuri in nai miki wani abun da baki ji dadi ba. Wallahi damuwata na fada miki bansan ta zata bata miki rai ba amman bazan kara ba. Husnah kiyi hakuri dan Allah ki daina kukan.”

Sosai ya rikice yana lallashin ta. Sai da tayi kukan ta mai isar ta sannan ta ce,
“Ni ba kai ka sani kuka ba Sir, tuna min kai da irin abinda nake ji game da Yaa Aslam ne, Nasan dadin soyayya, wacce ban taba zaton zata kare min ba. Na zata za ta zan dauwama da ita ashe ta wani lokaci ce. A lokacin da ina shan soyayya ban taba jin wani abu mai dadin ta ba. Haka nan bani da damuwa sai farin ciki da annushuwa a koda yaushe. Lokaci daya na fara rasa soyayyar Dady na. Ashe bayan ita zan kara rasa wata soyayyar wato soyayyar Ya Aslam.”

STORY CONTINUES BELOW

Ta goge hawaye ta ce,
“Haka nan nasan dacin soyayya wanda har yanzu nake kan jin dacin ta. Dacin ta ya kasa fitar mun daga baki na. Sir ba komai ne ya sani kuka ba sai sanin halin da kake ciki. Dan nasan zafin yadda kake ji. Amman ka sani wallahi ni ba kinka nake ba sai dai ina tsoro ne, sannan kuma ina son Yaa Aslam duk da abinda yai min. Kaji dalili nah.”

Sabir da yai shiru yana jin ta ya rasa me ke masa dadi. Tabbas shima akwai mata da yawa dake son sa, kenan haka suke ji.

Ba wacce ta fado masa sai Nusaiba kawar Maryam yarinyar da ta mutu a son sa.

Bata da buri sai na ta sa shi farin ciki. Duk yadda take shishige masa ya kasa amsar soyayyar ta kuma itama ta kasa daina son sa.

Kenan haka take ji. Tabbas in ana so kawai ana so ne. Haka nan in ba’a so shima ba a so ne.

To shi ba son Nusaiba ne ba yayi ba. Kawai ya rasa sanin feeling din da yake ji akan ta ne.
Dan Kyau Nusaiba kyakyawa ce ta karshe dan ita fara ce ma. Doguwa, kuma tana da diri mai kyau. Haka nan idanun ta manya da ga hanci. ga  gayu ga ilimi ga arziki. Hankali nustuwa duk tana dasu bare ace tana da aibu. Kawai dai shi ya kasa gane me yake ji game da ita,
Yasan tin da ya hadu da Asma’u yake jin abinda bai taba ji ba game da mace sai dai ya kasa gane mai yake ji.

Amman shi abu daya yake son yaji game da Asma’u shin tana son sa ne ko A’ah.

Ajiyar zuciya ya sauke ya ce,
“Naji Husnah. Kina tunanin in ba Yaa Aslam zaki iya rayuwar aure da ni. Ma’ana zaki iya aure na.”

Shiru tayi dan a zahirin gaskiya, baza ta ce, Sir Sabir bai.mata ba ko yana da wata makusa.

Kyakyawa ne ajin farko ga ilimi ga addini ga halin kirki ga nutsuwa. Anan zata iya cewa ba za ta iya tantance wa yafi wani addini da ilimi da nutsuwa tsakinin shi da Yaa Aslam.

Dan dai Yaa Aslam jinin larabawa ne dole kyan sa ya banbanta da namu hausa fulani.

Amman fa Sir Sabir shima akwai kyau da cikaken bafulatani.

Ba abinda ta tuna sai yadda Sir Sabir ya dinga dawainiyya da farin cikin ta har ya samu ya dawo.

Ta tuna zuwan sa makkah wajen su da yadda zai zauna yai ta sata farin ciki.

Ta tuna yadda ya ke takura kan sa yake taimaka mata a wajen aiki.

Ta tuna yadda yake damuwa da damuwar ta a lokacin da wanda ta aminta dashi ya juya mata baya.

Ya zata yi in har ba Yaa Aslam zata iya auren Sir Sabir sai dai me. Tana tsoro.

Ba wani tsoro bane sai na son Yaa Aslam da yake dankare a cikin zuciyar ta.

Tayaya zata fara cewa tana son Sir Sabir bayan ba haka bane akwai wanda take so daban.

Anya zata iya. Gaskiya da kamar wuya baza ta iya pretending ba.

Zata fada masa gaskiya dan gwara ya sani duk da yasan irin so da shakuwar dake tsakanin ta da Yaa Aslam.

Duk da haka tana tsoron halin Maza duk da tana tantama akan abinda Yaa Aslam yai mata.

Ta rasa dalilin sa na mata haka. Duk da tasan ita ba wani laifi tai masa ba.

Tana son tasan dalin da yasa ya guje ta har yai aure bayan duk alkawarin rikan da ya daukar mata.

Duk abinda yai mata sai wani son sa dake kara shigar ta. Tana son Yaa Aslam amman ya zama dole itama ta samu farin ciki kamar yadda Yaa Aslam ya tafi ya samu nashi.

Zata sanar da Sir Sabir komai duk da son sa take wa Yaa Aslam.

Ajiyar zuciya ta sauke, wacce har sai da Sir Sabir ya jiyo ta.

Jin shirun ta daman yasan Tunani take. Gyaran murya yayi, Ya ce,
“Ina jinki!”

“Sir amman kasan dai ina son Yaa Aslam ko?”
Ta jefa masa wannan tambayar.

Sai da yaji kirjin sa ya buga jin wacce yake kauna tana ambatar tana son wani. Duk da yasan tana son Yaa Aslam kuma ya cancanci ta so shi.

Mutumin da tin tana karama ta tashi dashi har girman ta dole ta kasance me son shi.

Kai ya gyada mata ya ce,
“Na sani.”

“Kasan Yaa Aslam dan uwa nane, baka ganin nan gaba zargi bazai shiga tsakanin mu ba in ka ganmu tare tin da kasan dan uwa nane kuma wanda na dauke shi kamar wana uwa daya uba daya, na dauke shi uba na.”

“Wane zargi Husnah?”
“Ko na aure ka, in ina tare da Yaa Aslam zanji shi kamar Yaa Buhari duk da nasan ba haka muke ba. zaka iya jurewa in na dauki damuwa ta nakai gare shi “

Sai da yayi jim kafin ya ba kan sa amsa. A ransa ya ce,
‘Bama zan barki da damuwar ba har da zaki fada masa ba.’

A fili kuma ya ce,
“Ba komai ai duk ya zama yayan mu ko?”

“Ina son Yaa Aslam. Kayi hakuri in ina fada nasan baza kaji dadi ba amman abinda yake cikin zuciya ta kenan. Ina son sa,”

“Ba komai Husnah, na miki alkawarin in har kika kasan ce tawa zan mantar dake Yaa Aslam sai dai ki kalle shi a matsayin Yaa Buhari, amman baza ki tuna da wata soyayya da kukai ba insha Allahu.”

Shiru kawai tayi dan ita yanzu dadin baki kawai take dauka duk abinda wani namiji zai fada mata.

Wanda batai zaton zai bar ta ba ya har ta bare kuma wani dan ya barta ai ba komai kuma.

Kamar yasan me take sakawa a ranta ya ce,
“Husnah kada kuma kiyiwa Samari gaba data kudin goro mana. Shima baki san dalilin sa na barin ki ba. Kuma kada ki manta duk abinda ya faru ga bawa mukadari ne, Allah ya riga da ya rubuta hakan zai faru. Ki mika komai naki ga Allah.”

Sanyi ta danji a ranta. A haka ya dinga kwantar mata da hankali har wajen sha daya da rabi.

Sannan sukai sallama. Mamaki sosai take dan rabon da ta kai sha biyu ido biyu ta manta tin suna tare da Yaa Aslam.

Dan yanzu inta kai sha biyu sai dai kuka ko karatu da sallah.

Yanzun ma alwala tayo ta kwanta tana tuna duk irin rayuwar da suka yi da Yaa Aslam.

Yau Yaa Buhari yana tashi ya fara shirin tafiya.

Mami taso ya kara kwana ki to amman ba lokaci, dole haka ta bashi sakon Asma’u.

Kaya masu yawa ta aiko mata sannan ta bata sakon tayi amfani da kayan laifen da aka hada mata.

Sunyi bakwana kan cewa nan da kwana biyar zata taho Kano ita ma.

Haka Yaa Buhari ya taho yana kewar ta, a ransa kuma yana sa ran sai komai ya gyaru dangane da Yaa Aslam.

Asma’u kuwa washe gari ta tashi lafiya sai dai damuwa dake damun ta sosai.

Da farko akwai damuwar ta, ta rasa masoyin ta sai kuma damuwar, da Sir Sabir, yake ciki.

Tasan matsalar so tasan halin da ake fadawa na rashin samun masoyi. Dan haka dole ta tausayawa Sir Sabir.

Ta sa a ranta zata aminta da Sir Sabir ko da bata son sane.

Da wannan shawar da ta yanke kuma ta tuna wane Sir Sabir wajen kyawun hali yasa ta dan ji dama dama a zuciyar ta.

Dan har waya sukai da Maryam ta ce, mata tare zasu zo da kawar ta Nusaiba.

Asma’u kam murna har tana cewa su taho cikin satin nan.

Sannan ta ce, ta aiko da measurement din su za’a kai dinki. Sosai Maryam tai murna ta ce, mata insha Allah ran juma’a zasu zo kafin sati biki kenan.

Suna gama Waya Mami ta sauko ta ce,
“Asma’u dawa kike waya ne haka?”

Asma’u ta ce,
“Mami da Maryam ‘yar yar Sir Sabir muke waya ranar juma’a ma zasu zo biki.”

Mami ta ce,
“To fa. Allah dai ya nuna mana bikin nan lafiya.”

Asma’u ta amsa da
“Ameen!”

Mikewa tayi ta shiga kitchen ranar ita ta shirya musu abincin rana.

Sannan ta shiga tai wanka ta ce, zata je ta kai musu dinkin dan har da Hafsat da Maimuna za akai dinkin.

Mami ta bata kudin dinkin isashe ta fita.

Zainab ta biya ta dauka sannan suka wuce Zoo road inda zasu kai dinkin.

Kayan ta bashi ta ce, zata turo masa da measurement din su ta waya.

Ta bashi kudin dinki suka wuce wajen da Yaa Buhari ya bada a bugo musu littafi da jaka da calender.

Har ya gama suka amsa suka nufi gida.
Ya Buhari sai Yamma ya dawo lokacin Asma’u bata gida.

Wanka yayi ya bawa Mami sakon ta sannan ya fice yai wajen Sabir.

Asma’u kuwa, suna dawowa ta kai Zainab gida tayo gida a gajiye.

Sabani suka samu da Yaa Buhari dan tana tafiya shi kuma ya nufi gidan su Zainab.

Asma’u na shiga taga motar Yaa Buhari cikin gida ta shiga da sauri tana kwala masa kira.

Mami dake falo ta ce,
“Oh Asma’u!”

Dariya Asma’u tayi ta ce,
“Mami ina Yaa Buhari nane?”

Mami ta ce,
“To ya fita kije ki wanka, kizo ga kaya can Momy ta aiko miki.”

STORY CONTINUES BELOW

Mikewa Asma’u tayi ta ce
“A’ah Mami kayan zan fara gani tukkunna.”

Tayi sama da sauri. Dakin ta ta shiga akwati ta gani babba ta bude.

Kaya ne masu kyau da tsada wanda Momy ta saba aiko mata dasu duk karshen wa.

Amman wannan kyan nasu yafi karfin wasa.

Kayan dai fitar biki ne, sai wata shadda da ta gani a dinke kala biyu da ta tata da ta Mami.

Da wani material shima iri daya amman dayan pink dayan kuma green.

Mai pink dine nata green din na Mmai.

Har da takalma da jaka duk da fashion dankunne da sarka.

Sosai taji dadin kayan duk da dinki nan da tayi.

Cikin akwatin ta mayar ta rufe ta zauna ta zuba tagumi,

Murmushi ta danyi ya ce,
“Allah sarki da yanzu muna tare da Momy. To Allah bai ba. Allah yasa haka ne mafi alheri.”

Ta mike tana maida kwalar da ta fito mata.

Dady ne kuma ya fado mata. Wanka ta shiga tana yi tana zubar da hawaye.

Har ta gama ta fito, ta shirya sannan ta gaye gado.

Dan bata da walwalar da zata iya sauka kasa dan kar ta dagawa Mami hankali.
Tana kwancen nan take zancen zuci ta ce,
“Ni kam wai haka rayuwa ta xata kare kenan ban da walwala banda farin ciki. In kuwa har haka ne, zancen Sir Sabir zai faru na, zan iya kamuwa da wani ciwon bayan kuma ina da masoyan da zasu damu dani.”

Juyi tayi ta rufe idon ta duk dan ta samu tayi bacci.
Asma’u sai karfe tara na dare ta mike, sallah tayi ta kara komawa gado ta cigaba da bacci.

Washe gari tana tashi ta shirya cikin Wata bakar abaya wacce akai mata aiki da golding zare.

Sandal ta saka golding da jaka golding tai rolling kanta da bakin mayafin rigar.
Ba karamin kyau tayi ba duk da ba kwalliya tayi ba. Sai kamshi take tashi.

Dakin Yaa Buhari ta shiga ta tada shi yana bacci, fita tayi ta sauka kasa.

Mami na kitchen ta karasa ta gaida ta, sannan tai mata sai ta dawo.

Fita tayi ta dauki motar ta ta nufi wajen aiki, tinda taje take kwance ta kasa komai.

Tana kwance Sir Sabir ya shigo. cikin shigar sa ya saka bakar suit yayi kyau da shi.

Fuskar sa sai annuri take fitar wa da wani murmushi mai sanyayya zuciyar wanda akai dan shi.

Jin shigowar sa yasa ta Mike da sauri, kallon sa ta yi, tai kasa da kai ta ce,
“Ina kwana?”

Zama yayi a gefen ta, yana kallon ta kafin ya amsa da
“Lafiya ya kike?”

“Lafiya lou!”
Ta bashi amsa.

Shiru sukai, Jin shirun yai yawa yasa, ta jingina kan ta a akan kujerar da take zaune.

Ido ta lumshe kamar me bacci. Kallon ta Sir Sabir yayi. Ta kara kyau da ita.

Ajiyar zuciya ya  sauke, sannan ya ce,
“Bakya jin dadi ne?”

Kai ta girgiza cikin sanyin jiki tai masa murmushi ta ce,
“Lafiya kalou nake, kawai garin ne?”

“Garin ne?”
ya tambaye ta.

Kai ta gyada masa, murmushi yayi ya ce,
“Taso mu fita to!”

Mikewa tayi dan baza ta iyai masa musu ba.

Fita sukai suka dinga zagaye gari shine kai ta can shine kai ta can.

Duk wajen da yasan zai ta ji nishadi ya dinga kai ta.

Har la’asar suna yawo a gari. Abinda yake buri ya samu.

Dan sosai ta sake har hira suke. Daga nan ya dauke hanyar yayi hanyar gidan su.

Sai da suka shiga sannna ta kalle shi ta ce,
“Ina ne nan?”

Ido ya kanne mata ya ce,
“Gidan mune!”

Kallon sa tayi tai kasa da kai. Fita yayi ya bude mata.

Fita tayi tabi bayan sa. Gida ne mai kyau gashi kato.

Ciki suka shiga da sallama. Mamah na zaune kan kujera, tana kallon suka shiga.

Suna shiga Mamah ta mike tana cewa,
“A’ah wa nake gani.kamar Asma’u!”

Ta kamo ta. Sabir ne ya ce,
“Ba kama ba ce ita ce.”

A kan kujera ta zaunar da ita Asma’u ta zame ta zauna a kasa.

Gaishe da Mamah tayi cikin girmamawa da kunya.

Mamah ta amsa cikin sakin fuska tana tambayar ta, yasu mami da Buhari.

Ta bata amsa. Mamah da kanta ta kama Asma’u suka nufi daining tana fadin
“ince daga aiki kike zo muje kici abinci “

Sabir kallo yabi su dashi, ba karamin burge shi sukai ba.

Bayan su yabi ya cewa,
“Mamah ta samu Asma’u yau ta manta dani.”

Dariya Mamah tayi ta ce,
“Ai dole na kula da Asma’u na manta da kai.”

Suka zauna. Abinci ta zubawa Asma’u. Shinkafa ce da taloya da miya da taji naman kaji, sai hadin kabeji da lemon kwakwa.

Kasa ci Asma’u tayk sai juya cokali da take, sai da Mami ta mike, sannan ta fara ci a hankali.

Sabir kam ido ya zuba mata yadda take cin abincin ma daban ne.

Jin ido akan ta yasa ta dago. Ido hudu sukai, Cokalin ta ajiye ta daina cin abunci.

Da ido da hannu ya tambaye ta
‘lafiya’

Kai ta dauke kawai, murmushi yayi ya ce,
“To sorry Baby nah, kici na daina kallon ki”

Ya fada yana dauke ido daga kallon ta, abincin shi yaja gaban sa yana ci.

Itama ci ta cigaba dayi. Sai da suka gama sannan suka koma falo.

A gidan sukai sallah magariba sannan suka mike tanawa Mamah sallama.

Wani hadin turaruka Mamah ta bata, amsa Asma’u tayi tana godiya.

Gida suka tafi tare suka shiga ciki. Mami na ganin su ta ce,
“To kuna tare kenan!”

Kai Asma’u ta daga ta ce,
“Kinga kayan da Mamahn Sir Sabir ta bani.”

Amsa Mami tayi ta duba tana godiya ta kalli Sabir ta ce,
“Angode Allah saka da alheri.”

Murmushi kawai Sabir yayi ya zauna. Asma’u dake gefen Mami ta kalle ta, ta ce,
“Mami ina Yaa Buhari?”

Mami ta ce,
“Yana gun Zainab!”

Baki Asma’u ta tabe ta ce,
“Yaya ba a kara sauran kwana nawa ta koma gunsa gaba daya.”

Murmushi Mami tayi ta ce,
“Asma’u daru.”

Mikewa tayi tai sama tana cewa,
“Bari naje nai wanka. Nai sallah.”

Tayi sama.

Cikin ikon Allah satin biki ya kama. Yau Momy ta taso.

Asma’u kuwa an kara zama busy ba lokacin zzama.

Dan tinda Yaa Buhari ya dawo basu zauna ba.

Sai dai ya shigo ita zata fita ko ta shigo shi zai fita.

Haka nan Sabir sai kara cusa kansa yake a wajen Asma’u.

Tinda Momy tazo suka tare da Asma’u. Hira suke ta yaushe rabo.

Duk da taga Asma’u ta dan canja daga yadda take sakin jiki da ita.

Kuma tasan hakan bazai rasa nasaba da abinda yya faru tsakanin su da Aslam ba.

To itama Momy ba yadda zatai dan da ta cewa Mami a daura auren kawai Mami cewa tayi A’ah a bar kowa ya auri rabon sa.

Momy yanzu bata fitar da Aslam da Asma’u baza suyi aure ba.

Yau Laraba tin lokacin zasu je a gyara musu kai ai musu lalle.

Wanka tayi ta shirya cikin wasu pakistan riga da wando.

Hijab ta dauka ta daura sannan ta dau mota ta nufi gidan su, Zainab.

Daga nan suka wuce gidan su Sir Sabir dan dauko su Maryam da Nusaiba.

Suna zuwa suka tadda Sir Sabir a compound din gidan

Fita tayi daga motar sa sukai wajen sa. Durkusawa sukai suka gaishe shi.

Amsawa yayi yana bin Asma’u da kallo. Kasa tayi da kai.

Zainab lura da irin kallon da yake mata yasa ta shige ciki ta barsu nan.

“Baby nah!”

Ya kira ta.

Dagowa tayi ta kalle shi. Murmushi yayi ya ce,

“Kinga wani kyau da kike sai kace ke ce amaryar.”

Murmushi tayi, ta ce,

“Sir tsokana dai.”

Daga haka ya dinga jan ta da hira. Ganin su dibi kusan rabin awa, yasa ta cewa,

“Bari na shiga na gaida Mamah,”

Tayi ciki tana murmushi. tana shiga ta tadda Maryam da Nusaiba sai Zainab a falo.

Da sauri Maryam ta tashi ta rumgume Asma’u.

Hugging nata Asma’u ita ma tayi tana murmushi.

Zama tayi ta kalli Nusaiba, wacce take cika tana batsewa ke kya ce an mata wani abu.

Murmushi Asma’u tayi ta ce,

“Lah Sis waccan ce Nusaiban?”

Kai Maryam ta gyada. Asma’u ta ce,

“Sannu Nusaiba ya hanya?”

Kamar baza ta amsa ba ta amsa da

“Lafiya Alhamdulilah!”

Kallon ta Asma’u tayi ta dauke kai ta ce,

“Kin zo wajen wallahi. Dan dai bikin mu kika zo ne.”

A ranta tai maganar.

Maryam ta kalla ta ce,

“Ina Mamah?”

“Tana dakin ta.”

Maryam ta bata amsa.

Hannun Zainab, Asma’u ta kamo ta ce,

“Taso muje mugaida ta mu tafi ko?”

Suka haye sama. Mamah na ganin su, ta saki fara’a ta ce,

“A’ah Amare ne ashe!”

Asma’u tayi murmushi. Zainab kuma tai kasa da kanta suka gaishe da ita.

STORY CONTINUES BELOW

Mamah ta ce,

“Kunga su Maryam din ko?”

Kai Asma’u ta daga ta ce,

“Eh tafiya zamuyi ma zamu lalle da gyaran jiki.”

Mamah ta ce,

“To a dawo lafiya.”

Mikewa Asma’u sukai Mamah ta kira su. Komawa sukai Mamah ta dauko kudi ta mika musu.

Kallon ta Asma’u tayi ta ce,

“Me za a siyo miki?”

Mamah ta ce,

“Kuyi lallen da shi.”

Murmushi Asma’u tayi ta ce,

“Haba dai Mamah wallahi muna da kudi mun gode Allah kara budi.”

Duk yadda Mamah taso su amsa ki tayi suka sauko.

Maryam Asma’u ta kalla ta ce,

“Muje ko?”

Mikewa sukai, suna fita Asma’u ta shige mota.

Nusaiba kuma tayi wajen Sir Sabir tana masa wani kwarkwasa.

Baki Asma’u ta tabe, ta shige mota. Zainab ta shiga gidan gaba, Maryam ta shiga gidan baya suna jiran Nusaiba.

Sabir ne ya taho ta biyo bayan sa. Gefen da Asma’u take ya karasa ya ce,

“Har kun fito?”

Kai ta daga masa, ta ce,

“Eh kar muyi rana.”

Kudi ya dauko ya mika mata. Kallon sa tayi ta tambaye shi da ido.

Murmushi yayi dan yana son maganar da take masa da ido.

Ido ya kashe mata ya ce,

“Kuyi amfani da su.”

Dariya tayi ta ce,

“Kada ka manta nifa hajiya ce, bayan nan kuma ango ya bada kudin lallen mu.”

Ido ya lumshe ya ce,

“Kar ki damu, ai dani da ango duk daya ne, nima na amaryata na bayar. Dan Allah ki amsa.”

Murmushi tayi ta ce,

“To mungode!”

Ta amsa ta ajiye akan cinyar ta.

Nusaiba dake jin maganar su ji take kamar ta shake Asma’u da kishin Sir Sabir.

Motar ta tada suka tafi, yana dago mata hannu.

Ranar dai karfe goma ta maida Amarya gida ita da su Maryam kuma sukai gida.

Duk yadda Asma’u ke burge Nusaiba amman ta kasa nuna hakan saboda kishin Sabir da take.

Dan tinda Zainab ta shiga ta ce, Asma’u suna tare da Sir Sabir take jin kishin ta.

Sai kuma maganar da taga suna yi. duk yadda ta dauke Asma’u ta wuce nan.

Dan yadda ta biya akai musu lalle ja da baki da gyaran kai, ya bata mamaki.

Komai suka gani in ya burge su ta dauka ta basu.

Haka nan da suka koma gida taga yadda gidan su yake duk yadda ta dauki kanta sai taga Asma’u tafi ta.

Haka nan da ta fito musu da kayan su, su gani shima abin sosai ya bata mmamaki.

Dan tasa kayan masu tsada ne kuma dinkin ma daga gani kasan an kashe kudi.

Kaya kala biyu kuma ko wanne da abin amfanin shi.

Take jikin ta yai sanyi tasan Asma’u ta fita komai.

Dan haka ita ba tsarar ta bace. Duk girman kai da share tan da take sai tayi dana sanin yin sa.

Haka da suka koma gida aka kawo musu abinci mai rai da lafiya.

Bayan sunci ta ce suyi wanka ta basu kayan bacci sabbabi sannan ta kai su suka gaisa da Mami da Momy.

Nan ma yadda taga ana musu sai kace yan gidan ya bata mamaki.

Suna komawa daki kuma sukai bacci.

Sosai Nusaiba tai da na sanin kallin hadarin kajin da tai mata.

Ita kuwa Asma’u bata san dalilin yi mata hakan ba.

Washe gari gidan su Asma’u ya cika da yan uwan Dady da suka zo kwana.

Ranar Alhamis akai Arebian Night. Inda sukai shigar dogayen riguna.

Sosai Asma’u tayi kyau kai kace Asma’u ce amaryar.

A lokacin Nusaiba sai kallon ta take. Ranar Sir Sabir shima yaje

Sunsha hotuna. Kowa yai kyau har Maimuna da tazo itama da yan makarantar su.

Bikin fa ya tara yan gayu da yan boko.

Washe gari friday akai Mother’s evening, ranar ne akai ankon wani tissue material yan matan sunyi kyau.

Asma’u kuma anko sukai ita da Mami da Momy. Mami da Momy kala daya na Asma’u kuma kala daban.

Asma’u ita taiwa Maryam da Nusaiba kwalliya har amarya.

Sannan ta zauna tayi tata. Sosai tayi kyau cikin wani pink material din ta.

Amarya kuma ta shirya cikin silver kaya ango ya saka Ash kalar shadda.

Sabir ma yai kyau cikin farar shaddar sa.

Ranar anci ansha an yi liki. Sosai sunyi kyau.

Duk Family din Dady sun hallaci wajen.

Washe gari Yaa Aslam ya zo daurin aure. daurin auren da ya hada manyan mautane abokan Dady.

Yaa Aslam ya je sun gaisa da Mami kamar yadda suka ssaba.

Zuciyar sa ba wanda take so ta gani inba Asma’u ba.

Asma’u kuwa bata gidan ma. Sai da angwaye suka je gidan su Zainab ana hotuna sannan suka ga  Asma’u ta fito cikin wata pink din shada ana mata aiki da brown zare da stones. 

Aslam kuwa yana ganin ta ya buya sai leken ta yake yana ganin yadda ta kuma kyau.

Sir Sabir kuwa sai kare ta yake yi. Sunyi huto na sosai dashi.

Anyi huto na sosai. Dan tana gefen Yaa Buhari taji an tsaya a gefen ta.

Bata kawo komai ba kamshin turaren da taji shi yasa tai saurin juyawa dan gani wane mai kamshin turaren Yaa Aslam.

Tana juyawa sukai ido hudu da shi. Wata faduwar gaba tayi dan ta firgita.

Baya kawai tayi da sauri Sir Sabir ya taro ta.

Cikin gida ya shiga da ita. Ya bata taimakon gaggawa numfashin ta ya dawo.

Tana farkawa ta fashe musu da kuka.

Sosai hankalin Zainab ya tashi ta hau lallashin Asma’u dan ita ma kukan take son yi duk da bata san me ya samu Asma’u ba.

Aslam kuwa sosai hankalin sa ya tashi dan daga nan ya koma Abuja duk da yana son sanin halin da Asma’u take ciki.

Shi yana mamakin me ya shiga tsakanin sa da Asma’un sa ne ma.

Da kyar Asma’u ta dawo normal dan sai da Momy tazo tai ta bata hakuri sannan ta dan sake.

Nusaiba kuwa take tausayin Asma’u ya kamata dan har tana jin a ranta zata iya sadaukar wa da Asma’u Sir Sabir.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page