K’ADDARA CE CHAPTER 12

 K’ADDARA CE CHAPTER 12

+

Ta yi kusan minti biyar a tsaye daidai lokacin salma da fatima suka fito a tare, kallonta fatima tayi tana murmushi tace wow my sis kinyi kyau.

Itama Amina d’an guntun murmushi tayi tace nagode ku ma kunyi kyau sosai,

Fatima tace mutafi ko? Murmushi Amina tayi nan da nan dabara tafad’o mata tace daman zuwa zanyi infad’a miki ba zan samu damar zuwaba har na shirya sai k’awata murja takirani tace gatanan zuwa zata kawo min buk d’inta in ida note kinsan na ce miki ran Monday muna da test kuma ga note d’ina incomplete ne, itama kanta Amina ta yi mamakin yadda cikin k’an k’anin lokaci ta iya tsara wannan k’aryar.

Marairaicewa fatima tayi tace maimakon kizo mutafi, sai ta taddamu chan gidan?

A’a sis kutafi kawai wani lokacin zani je, Fatima tace gaskiya sis ki… Salma da take tsaye takaici duk ya cikata ganin yadda fatima take lalla6a Amina, takatse Fatima daga maganar da takeyi tace please my blood kizo muje ai ba dole bane sai taje, jawo hannunta salma tayi fatima ba dan ta so ba tabi bayanta, murmushi Amina tayi tace sai kun dawo kugaishen da ita, jikin fatima duk ya yi sanyi tace toh sis.

Amina d’akinta takoma tacire mayafinta ta aje sannan tafito tanufi d’akin babah mairo nan suka yi ta fira har ta mance abinda yafaru tsakaninta da fahad.

Tare da babah mairo sukayi girkin dare sannan Amina takoma d’akinta ta gabatar da sallar magrib,

Fatima ce takalli Aunty khairat tace Aunty magana ce mai muhimmanci mukeson muyi da ke, Aunty khairat tatattara hankalinta duka garesu tace ina sauraranku,

Fatima kallon salma tayi tace my blood kiyi mata bayani, sunkuyar da kai salma tayi tace sis kiyi mata mana, dariya Fatima tayi tace toh ai wak’a bakin mai ita ta fi dad’i, salma tace bakinki ma zatayi dad’i.

Kallonsu Aunty khairat tayi tace kuji min ja’iran yara idan ba zaku fad’aba intashi dan ni ina da abin yi.

Sowie Aunty daman salma ce takeson yaya fahad,

Cikin mamaki Aunty khairat takalli salma, salma cikin jin kunya ta sunkuyar da kanta k’asa, murmushi Aunty khairat tayi tace toh shi fahad d’in ya san da maganar,

Fatima tace a’a Aunty bai saniba,

Toh me zai hana kufad’a mashi,

Zaro ido sukayi gaba d’ayansu a tsorace salma tace Aunty ai zai iya 6a66allamu kinsan halin yaya fahad da dai ke kika yi masa magana, wlh Aunty ina sonsa sosai.

STORY CONTINUES BELOW

Dariya Aunty khairat tayi tace toh shikenan zamuyi maganar da shi, cikin jin dad’i sukayi mata godia sukace komai kenan zasuyi waya, daganan suka hau hira ba su suka baro gidan ba sai bayan magrib,

Kasancewar Ameerah na chan Fatima taso tatafo da ita gida Ammah tak’i binsu.

Bayan sallar isha’i fahad gidan Aunty khairat yaje domin yad’auko Ameerah bayan sun gaisa Aunty khairat takallesa tace my bro maganace nakeso muyi kabani hankalinka nan, fahad aje wayarsa da yake latsawa yayi yamaida hankalinsa wajenta yace ina jinki mmn jawahir,

Murmushi Aunty khairat tayi tace yauwa dan Allah inaso kad’au maganata da muhinmanci ammah shawara ce, shidai fahad zuba mata ido yayi dan jin me zatace,

Itama kallonsa take tace my bro tunda ka gama krt ya kamata ace ka fitar da mata munsha bikki, murmushi fahad yayi yasosa k’eyarsa cikin jin nauyin maganar, yace my sis insha Allahu zanyi inaso ne agama ginin asibitin idan kamai yazama ready sai inyi maganar auren.

‘Daga kai tayi alamun gamsuwa da maganarsa sannan tace toh me zai hana ka taimaka ka auri ‘yar uwarka salma, wuf Fahad yayi yamik’e tsaye d’aure fuska yayi yace god forbid, haba  me zanyi da salma gaskiya ni ba na sonta kuma ni na ce miki banda wacce nake so ne? Kawai inma wasa kike abar maganar,

Killonsa take cikin mamaki tace fahad karfa kamance salma ‘yar uwarkace.

‘Daga kafad’a yayi yace dan tana ‘yar uwata shine zan aureta? Ita ta ce miki batada wanda takeso ne?

ko ma tana da shi ai zata iya hak’ura kaga sai kuyi aurenku,

‘Daukar Ameerah yayi da taketa bacci yace nidai my sis na tafi gida tunda ke 6atamin rai kikeson yi.

Dariya yaba Aunty khairat tace my bro kenan kai dai kawai kace bakason maganar, tafiyarsa yayi bai tsaya bata amsaba,

Murmushi Aunty khairat tayi tace fahad kenan mai ra’ayin kansa.

Amina wajen k’arfe tara har ta yi shirin kwanciya sai taji anyi knocking d’in k’ofar, tana sanye da nyt gown d’inta iya cinya a tunaninta Fatima ko babah mairo yasa  bata d’aura zaneba taje tabud’e, ido hud’u sukayi da fahad duk saida gabansu yafad’i sonsane taji yana k’aruwa a ranta, fahad yana rungume da Ameerah da Ameerah da tayi bacci, Ida bud’e masa k’ofar tayi yashigo yakwantar da ita saman gado, Gefen gadon yazauna yakalli Amina da take tsaye bakin k’ofar tana jira yafita tarufe ta so tabashi dariya Ammah sai ya kanne, yace please kije kihad’o min coffee yunwa nakeji,

Amina sun6uro baki tayi ta mance da kayan da ke jikinta tana shirin fita muryarsa tajiyo yana cewa a haka zaki fita?

Sai a lokacin ta tuno komawa tayi tabud’e wardrobe d’inta tajawo zane tad’aura, shidai fahad binta kawai yake da kallo.

Bata fi minti biyar ba tadawo hannunta d”auke da cup tamik’a mai, kar6a yayi yafara sha, Amina chan gefen gado takoma ta kwanta, murmushi fahad yayi dan ya san fushi take ya hanata fita.

Saida yashanye sannan yajawo wayarsa yafara chart, Amina dai a k’agare take da yafita domin ganinsa ma kawai yana tado mata da ciwon sonsa, saida sukayi kusan 10 minutes a haka sannan fahad yace had’amin ruwa inyi wanka,

Juyowa Amina tayi takallesa a wulak’ance tace kaje d’akinka mana sai kayi da ni nake had’a maka idan zakayi?

Tashi fahad yayi yashiga toilet d’inta ba tare da ya k’ara yi mata magana, jiyosa tayi alamun wanka yake lumshe idonta tayi a hankali tace fahad kaine rayuwata, ban san wane hali zan shigaba idan narasaka tayi zurfi a tunaninta bata san lokacin da yafito sai jinsa tayi gefenta yana shafar fuskarta, a tsorace tabud’e idonta takallesa nan ma suka k’ara yin 4 eyes, murmushi yasakar mata yace my wife me kike tunani tun d’azun ina ta magana kinyi shuru, harararsa Amina tayi, dariya yayi yace wlh kar kik’ara min wannan kallon, murgud’a mashi baki tayi tace idan anyi fa komawa tayi takwanta tare da juya masa baya.

STORY CONTINUES BELOW

Bayanta fahad yakwanta tare da rungumota, lumshe idonta tayi tana jin wani irin yanayi, hannu fahad yakai yafara shafar fuskarta ita dai Amina batayi gigin hanasaba ahankali yazage mata zip d’in rigarta yacigaba da shafar k’irjinta ture masa hannu Amina tayi, cikin muryasa da tafara dishewa duk yafara fita hayyacinsa yace please my wife kibarni, cigaba yayi da shafar ko’ina na jikinta cikin dabara yarabata da rigarta nan yafara kissing d’in wuyanta zuwa k’irjinta, bud’e baki tayi dakyar tace please yaya fahad kadaina banaso, had’e bakinsu yayi yacigaba da tsotsa cikin salonsa da yarikita Amina batasan lokacin da ta bada kai tabiye masa ba takai hannu tadafe kansa itama tana mayar mashi da nata salon cikin so da k’auna,

Dukkansu sun fita hayyacinsu kissing d’in juna kawai suke ahankali fahad yaxare bakinsa daga nata itadai Amina tana rungume da shi cikin wani kalar salo nasa da shi kanshi baisan ya iyaba ya cigaba da kissing d’in sauran part na jikinta, saida yaga tayi lik’is ko motsin kirki bata iyawa alamun ta zo hannu sannan……..

Fahad rungume yake da Amina itadai sai k’ara tura kanta take a jikinsa saboda wata irin kunyar abinda tayi da takeji, shidai murmushi yake yana shafar kanta, bakinsa  yakai saitin kunnanta yace nagode my wife kin shayar da ni zumar k’auna Allah yabiyaki,

Itadai sai k’ara sunne kai take tana murmushi, fahad ma murmushi yayi yace Amina ina sonki meyasa kike 6oyemin son da kike min? Ko da kin 6oye a fuska toh jikinki yana nunawa, meyasa ba zaki bani damaba innuna miki irin son da nake miki? lumshe ido Amina tayi tabbas tasan fahad baiyi k’aryaba itama kanta tasan tana sonsa son da take tunani zata iya rasa rayuwarta idan tarasa fahad,

Cigaba da magana yayi yace Amina kidaina tunanin su mummy nasan zasu fahimcemu kar kimance da *K’ADDARA CE* tahau kanmu kuma babu wanda ya isa ya tsallake k’addararsa na yi miki alk’awali babu wanda zai rabamu zan baki kulawa bakin gwalgwado, Amina kece farin cikina ki amince da ni inzama abokin rayuwarki zan nuna miki k’auna zallah zan baki farin cikin da ba kowace mace take samun irinsa a wajen mijintaba sai macen da takasance ‘yar gata a wajen mijinta.

Amina k’ara rungumesa tayi hawaye suna zuba daga idonta jitake sonsa yana k’aruwa kamar zai fashe k’irjinta yafito.

su6ul da baka tayi tace yaya fahad ina son….. shuru tayi takasa k’arasawa, murmushin jin dad’i fahad yayi yace dagaske kina sona? Shuru Amina tayi duk sai taji haushin kanta, k’ara rungumeta yayi yace kidaina 6oyemin sonki Amina domin a cikin idanuwanki na ga sak’on da yake cikin zuciyarki,

Dakyar tabud’e baki tace yaya fahad ina sonka, dasauri fahad yad”agota daga jikinta suka fuskanci juna suna aikawa juna sak’onni ta ido, cikin jin dad’i yace dagaske kike Amina kina sona? Murmushi tayi hawaye suna zuba daga idonta d’aga mashi kai tayi alamar eh, dakyar tabud’e baki tace ina tsoron su mummy surabani da kai ban san yadda zanyi da kainaba idan muka rabu, yaya fahad *KAINE ZA’BINA* na mallaka maka zuciyata, share mata hawayen fuskarta yayi cikin Jin dad’i yace nagode sosai Amina kin faranta min, kin ban  kyautar da kud’i ba zasu iya siyaba, kifad’amin duk abinda kikeso ni kuma insha Allah zan baki, murmushi Amina tayi tace ina so kamallaka min zuciyarka, dariya fahad yayi cikin jin dad’i yace tuni na mallaka miki ke kad’aice a cikinta, lumshe idonta Amina tayi tare da jan numfashi tace nagode sosai yaya fahad. Saidai ina tsoron rabuwarmu ba zan iya rayuwa babu kai ba,

K’ara matseta yayi a jikinsa tare da yin ajiyar zuciya yace babu mai rabamu da ke sai Allah kidaina fargaba kar kimance da *HA’DIN ALLAH NE* kinga kenan babu mai iya rabani da ke sai Allah.

Nan suka cigaba da fad’a ma junansu sirrin da yake cikin ransu, daganan fahad yad’auki Amina bai direta ko inaba sai toilet cikin bathtub shi yayi mata wankan sunayi suna wasanninsu na masoya, Amina ganin yana shirin wuce gona da iri yasa ta dakatar da shi nan sukayi wankansu suka fito,

Amina tana rungume a jikinsa sukayi bacci cike da k’aunar juna.

gab da Asuba Amina tafarka ahankali tad’ago kai takallesa taga baccinsa yake hankali kwance murmushi tayi takai bakinta tayi kissing d’in lips d’insa , bud’e idonsa yayi yasafkesu akanta Amina murmushi takeyi masa tace  yaya fahad katashi katafi kaga asuba ta kusa,

kallonta yake yace ina zan ta6i? Cikin shagwa6a tace d’akinka mana, jawo d’an k’aramin bakinta yayi da take ta turowa, ‘yar k’aramar k’ara tasaki cikin shagwa6o tace Allah ban yadda shine kaji min ciwo, dariya yayi yace sowie my wife, mak’e kafad’a tayi tace ban yadda sai na rama, dariya yayi yace toh kirama, bakinta takai tana shirin cije masa lips dasauri yacafke bakinta yafara kissing d’inta saida yaga ta fara fita hayyacinta sannan yajanye bakinsa daga nata ya janyeta daga jikinsa yasaka kayansa yatashi yaficce daga d’akin yana dariya dan shi har mamaki take basa yadda bata da wahala wajen kar6ar sak’o.

Murmushin jin kunya Amina tayi sannan tatashi tajawo towel tad’aura tashige toilet.

Wajen k’arfe goma duk sun hallara a dining table suna breakfast, Fahad da Amina suna ta aika ma junansu sak’onnin so ta idanuwansu, chan yajawo waya yatura mata message, jin alamar message ya shigo yasa taduba number fahad ce tagani d’ago kai tayi takallesa, nuni yayi mata da kansa alamun taduba,

Bud’e message d’in tayi _kinyi kyau my wife_

Murmushi Amina tayi tamaida mashi reply

_kai ma haka ka yi kyau my dear_

murmushi shima yayi yatura mata reply _ammah ban kaiki ba my wife_

_ka ma fini dan sai kace wani ango_

_Toh ai angon ne tunda sai yanzu nasan menene aure_

‘Dago kai tayi takallesa yakashe mata ido d’aya, Murmushi kawai tayi tacigaba da cin abincinta,

Wajen k’arfe sha biyu tana kitchen tana masu girki saboda babah mairo ba ta jin dad’i yau, yanka albasa take lokacin Fahad yashigo kitchen d’in zai d’auki ruwa tsaye yayi yana kallonta yanata murmushi ita dai ta juya baya batasan da shigowarsa ba ahankali yatako ya iso inda take kawai sai ji tayi an rungumeta ta baya, Amina tsorata tayi k’amshin turarensa da ta shak’a yasa tagane shine, murmushi tayi cikin shagwa6a tace yaya fahad har ka ban tsoro, dariya yayi tare da kwantar da kansa saman kafad’arta yace sorry my wife, wane delicious kike had’a mana, murmushi tayi tace in na gama zaka gani,

Kissing d’in wuyanta yashiga yi, marairaicewa tayi tace please yaya fahad kadaina kaga fa aiki nake kuma kar ashigo aganmu, batare da ya daina abinda yakeba yace sai me dan anganmu ai matatace, Amina ta bud’e baki zatayi magana kenan kawai sai sukaji tafiya alamun annufo kitchen d’in dasauri fahad yasaketa yabud’e fridge itakuma taciga da aikinta, mummy ce tashigo kitchen d’in tana murmushi tace sannu my daughter kina ta aiki, itama Amina murmushi tayi tace yauwa mummy, kallon fahad tayi da yake tsiyaya ruwa a cup tace my son ashe kana nan daga room d’inka nake naga a rufe yake,

Saida yasha ruwan sannan yace yanzu nashigo mummy fridge d’inane babu ruwa shine nazo nan insha, mummy tace idan ka gama kazo zan aikeka,

Yace toh mummy

fita mummy tayi takoma d’akinta.

Kallon Amina yayi yana murmushi yace kin tsorata ko?

Itama murmushin tayi tace sosai ma,

Hancinta ya lakuce yace sarkin tsoro kawai, bari inje inkar6i sak’on mummy akwai abinda kike buk’ata?,

Kallonsa tayi tace a’ah Allah yakiyaye hanya sai ka dawo, harararta yayi cikin wasa yace haka ake sallama da miji?

Tace toh ya za….

Bata ida fad’aba yahad’e bakinsu waje guda yafara kissing d’inta saida suka fara fita hayyacinsu ganin suna shirin zubewa k’asa sannan fahad yakyaleta, Amina kunya takamata ta sunkuyar da kanta k’asa,

Murmushi fahad yayi yace kinga yadda ake sallama da miji, sai na dawo, bai jira jin abinda zata ceba yaficce daga kitchen d’in yana murmushi,

itama Amina murmushin take sannan tacigaba da girkin ta……….

Ko da Amina tagama girkin d’auka tayi takai dining area tajera, sannan takoma d’akinta tak’ara wanka, shiryawa tayi cikin Pakistan white nd blue colour, tufke gashinta tayi sannan tayi rolling da gyalen kayan fari, simple makeup tayi ammah saida kyawunta yabayyana hijab tasaka tashimfid’a darduma tagabatar da sallar azahar, bayan tagama tana shirin tashi saiga Ameerah ta shigo dagudunta tafad’a jikin Amina, kallonta Amina tayi tana murmushi tace my dota ya dai? Had’e goshinsu Ameerah tayi tace mum kije Aunty tana kira, cikin gwarancinta tayi maganar dariya Amina tayi tace wace Auntyn? Uhm uhm Aunty, dariya Amina tasake yi tace toh sannan tatashi tacire hijab d’inta tanad’e pray mat, gyara rolling d’in gyalenta tayi sannan tad’auki Ameerah suka nufi parlour,

Mummy da daddyne sai fatima zaune suna jira cikin girmamawa tagaishesu, bata ji dad’in rashin ganin yaya fahad ba tana cikin tunanin sai tajiyo sallamarsa, Amina Ajiyar zuciya tayi tare da waigawa takallesa, suna had’a ido yasakar mata murmushinsa mai tsada,

Safke Ameerah tayi da taketa k’irk’irin tasafka daga jikinta, aikam dagudu taje wajensa, dasauri yad’auketa yad”aga sama yace oyoyoo my lil angel, kyalkyalewa Ameerah tayi da dariya, chocolate fahad yad’auko yabata.

Fatima tace lallai yaya fahad yanzu ka samu d’iya ni ka daina ji dani,

Dariya su mummy sukayi yace ke ai kin girma, cikin shagwa6a tace wlh ban girma ba takalli Amina da kanta yake sunkuye sai murmushi take tace Ko my sis?

Amina kallon fahad tayi taga shima ita yake kallo sannan tamaida kallonta ga Fatima tace aikam dai baki girma ba duka da mi kika d’an fi Ameerah, dariya su fahad sukayi, duka fatima takai mata cikin wasa dasauri tagoce.

Mummy tace wai ni ina salma ne? Fatima tace tana d’akinta na barota tana sallah, ohk kutaso muje muci abinci, Amina kije kikirata, toh Amina tace sannan tanufi d’akin salma,

Da sallama tashiga ta tadda salma kwance saman gado sai dannar waya take jin ba a amsa mata sallamarba yasa tak’ara yi, a wulak’ance salma takalleta tace lafiya zaki shigo min d’aki? Cikin rashin damuwa Amina tace mummy ce tace inkiraki kizo muci abinci,

Ta6e baki tayi tace kin iya tafiya ai ina sane, juyawa Amina tayi taficce, salma tarakata da harara.

A dining Amina ta taddasu har sun zauna Fatima tana serving d’insu, kujerar da take opposite d’in fahad tajawo tazauna tace mummy ta ce gatanan zuwa, mummy tace toh.

Daidai lokacin salma tafito daga d’akinta ganin Amina zaune opposite d’in fahad yasa tayi guntun tsoki tajawo ta gefensa tazauna suna had’a ido da Amina ta wurga mata harara, Amina bata damuba tacigaba da cin abincinta,

STORY CONTINUES BELOW

Sai satar kallon fahad take da yake ta feeding d’in Ameerah, d’agowar da yayi da kansa suka had’a ido dasauri Amina tasunkuyar da kanta cikin jin kunya,

Murmushi fahad yayi yajawo wayarsa, alamun shigowar message taji tana dubawa taga fahad ne, _kidaina jin kunya you have right kid’ago kikalleni ni  nakine my princess_

Kunyace takama Amina, tamaida mashi reply _Nifa ba kai nake kalloba Ameerah nakallah_

Murmushi fahad yayi sannan yamaida mata reply _ai na ganki kina satar kallona kinga d’an saurayi_

d’ago kai tayi takallesa yakashe mata ido d’aya, harararsa tayi cikin wasa sannan tacigaba da cin abincinta.

Amina had’a ido sukayi da salma, salma taharareta ita dai murmushi kawai tayi tacigaba da abinda take, akan idanun fatima taharareta duk sai fatima taji bata ji dad’iba.

Koda suka gama fahad fita yayi da Ameerah, Amina d’akinta takoma takwanta tajawo littafinta tana krtn C.A d’in da zasuyi gobe, ta ji dad’in tafiya da Ameerah da fahad yayi dan da tana nan da bata barinta karatun rigima za taitamata. Sai gab da magrib sannan tatashi tayo alwallah tilawar alk’ur’ani tayi har saida aka kira Sallah sannan tatashi tagabatar da ita ba ita tatashiba har saida tayi sallar isha’i. Fatima ce tashigo da Ameerah ta kwantar da ita ganin Amina tana sallah yasa tawuce.

Da tagama parlour takoma suka sha fira da fatima, nan fatima take bata hak’uri akan abinda salma tayi mata, murnushi Amina tayi tace ni bata min komai ba wlh, kibar maganar kawai muyi hirarmu daga nan suka cigaba da hira duk yadda Amina taso taga shigowar fahad bai shigoba har wajen k’arfe goma sannan tayi ma fatima sallama tatafi d’akinta,

Ko da takoma d’akinta wanka tashiga bayan ta fito daga ita sai k’aramin towel daidai cinya tsaye take gaban dreesing mirror tana tufke gashinta daidai lokacin fahad ya bud’e k’ofar ya shigo jikinsa sanye da kayan bacci yana rik’e da wata jakka mai d’an girma, murmushi tasakar mai sannan tacigaba da abinda take.

Ahankali yatako ya iso inda take, ta baya taji ya rungumota tare da sargafo hannunsa ya rik’e k”ugunta ta mirror d’in ya kalleta suka had’a ido nan suka sakar ma juna murmushi, hannu yakai kan gashinta da take tubkewa ya warware , ita dai kallonsa take ta mirror ahankali yarad’a mata cikin kunnenta kinfi kyau haka my princess please kibar min shi haka, murmushi kawai tayi, nan fahad yazira harshensa cikin kunnenta yafara lasa, Amina lumshe ido tayi tana jinta cikin wani irin yanayi, ahankali yadawo wuyanta yafara kissing d’inta, juyota yayi ya lalubi bakinta yafara tsotsa nan Amina tabiye masa, tsayuwa gagararsu tayi ganin suna shirin zubewa yasa fahad ya d’auketa yanufi saman gado da ita daga nan salon wasa ya canza.

Bayan komai ya lafa rungume abunsa yayi ahankali yace ga kaya nan na kawo na my dota ne,  cikin shagwa6a Amina tace toh ta gode Allah yak’ara bud’i, murmushin jin dad’i fahad yayi yace don’t worry my wife it’s my duty kema naki suna hanya gaban Amina saida yafad’i a tsorace tace nidai kabarsu bana so, dariya fahad yayi yace dole nane inkula da ku, toh kabarshi na yafe, murmushi yayi yace yarinya baki isaba indai nasa kaina babu wanda zai hana ni, gyara kwanciyarta tayi batace komai ba ahaka sukayi bacci cikin jin dad’i.

Washe gari kasancewar akwai school tun da wuri suka shirya idi driver yakaisu, wajen k’arfe biyu idi driver yaje yad’aukosu kasancewar yau su fatima sun ce ba zasu kai la’asarba,

wanka tayi sannan tayi sallah Bayan ta shirya tanufi dining nan ta tadda su fatima zaune suna cin lunch itama zuba nata tayi tafara ci, fahad ne yashigo yakalli Amina yace idan kin gama kikawo min nawa a d’aki sannan ina so zaki gyara min d’akina, karaf salma tayi tace yaya fahad kakawo ingyara ma, batare da ya kalletaba yace no ita nace tagyara min, haushi duk yakama salma, kallon Amina yayi yace kikayi shuru, ahankali tace toh.

Wucewa yayi yaficce daga d’akin cikin rashin damuwar abinda yayi, tashi salma tayi taharari Amina tace aikin banza taja tsoki sannan tawuce d’akinta.

STORY CONTINUES BELOW

Amina duk jikinta ya mutu bataji dad’in hakan da fahad yayi ma ‘yar uwarsaba kasa cigaba da cin abincin tayi, ta6ota fatima tayi tasakar mata murmushi tace karkidamu dear haka salma take, kuma kinsan halin yaya fahad Indai kana yi mashi aiki mai kyau toh bayason wani yayi masa sai dai kai.

Guntun murmushi Amina tayi cikin ranta tace ni da ban ta6a gyara mai d’akiba, kasa cigaba da cin abincin tayi dan haka tahad’a mashi nashi tanufi d’akinsa tana shiga ta tadda sa kwance saman 3 seater daga shi sai boxes a jikinsa murmushi yasakarmata d’auke kanta tayi daga kallonsa tazo ta aje masa a gabansa tazuk’unna tazuba mashi, batare da ta kallesaba tace gashinan tashi tayi zata fita, fahad yakai hannu yajawota tafad’o jikinsa kwallah duk tacika mata ido,

Kallonta yayi cikin mamaki yace kukan me kike? Share hawayenta tayi tace yaya fahad meyasa kake min haka cikin mutane? Batare da ya d’auke idonsaba a kanta yace me kuma nayi miki? Cikin shagwa6a tace ba kai bane salma ta ce zata yi maka shine ka yi mata tsawaba gabanmu,

Yadda tayi maganar ta so tabashi dariya yace toh kuma shine na yi laifi?

Harararsa tayi tace eh mana sai kaja sugano mu,

Uhm nidai bani abinci inci dan yunwa nakeji kikayi tafiyarki school kika barni,

Amina d”auko abincin tayi tafara bashi a baki yace kema na san bakici na kirkiba dan haka bari inbaki, Turo baki tayi tace na fa k’oshi, hannu yakai cikin rigarta yashafi jikinta yace banga alamar k’oshiba a tare da ke oya open ur mouth, Amina ba dan ta so tabud’e baki yasaka mata haka suka cigaba da ciyar da juna har suka k’oshi,

Yana zaune Amina tatashi tagyara mashi d’akinsa fes tafeshe da freshener takunna turaren wuta nan k’amshi yacika d’akin,

Da tagama ta so tatafi ammah fahad yahanata kwanciya yayi saman cinyarta itakuma tana shafa kansa suna hira cike da k’aunar juna.

A chan 6angaren salma tana shiga d’akinta saman gado takife kanta tadinga kuka, fatima ce tashigo d’akin ganinta cikin wannan hali yasa taji tausayin ‘yar uwartata dasauri taje tahau gadon tajawota jikinta tana rarrashi, dakyar salma tabud’e baki tace fatima me nayi ma yaya fahad ya tsaneni haka, menene narasa a jikina wanda zai sa yak’ini? Me waccan bazawarar yarinyar tafini? Rarrashinta fatima take tace kiyi hak’uri sis baki rasa komai ba, kidaina tunanin wani abu game da Amina ba fa soyayya sukeba mutunci ne kawai kuma kinsan halin yaya fahad da tausayi kuma kinga yana son d’iyarta sosai saisa yake shiri da ita.

Wani kalar kallo salma ta watsa ma fatima tace lallai na lura baki San komai ba, ba ki lura da yawan kallonta da yake kusan kullum a dining?

Fatima tace nidai ban lura da komai ba, na san yaya fahad ba ma zai so taba, kema kije kifad’a mashi kina sonsa dakanki,

Harararta salma tayi tace kina gani Aunty khairat tayi mashi magana ammah bai d’auki abun serious ba idan ni naje ai dukana zai yi, murmushi fatima tayi tace kar kidamu zamuyi magana da mummy,

Cikin jin dad’i salma tace yauwa my sis kin kawo gud idea, ammah sai na gyara ma yarinyar nan zama, zaro ido fatima tayi tace a’a sis kar kifara babu laifin Amina a nan.

Sai gab da magrib sannan Amina tasamu takufce daga wajen fahad tagudo d’akinta.

tun daga ranar kallon arzik’i bai had’ata da salma ita dai har ga Allah bata rik’eta a rantaba.

Fahad akwati daya yayo ma Amina na kaya dakyar ta amsa shima saida yanuna 6acin ransa.

Fatima ce tasamu mummy a d’akinta zaune tana kallon NTA News, kusa da mummy tazauna kallon d’iyarta tayi cike da k’auna tace ya dae autana daga gani na san da magana a bakinki,

Dariya fatima tayi tace mummy daman akan salma ne, tattaro hankalinta mummy tayi tace me yasamu salmar? Mummy babu abinda yasameta daman wai akan yaya fahad ne ita wai shi take so,

Mummy cikin mamaki tace ikon Allah yanzu ita salma tace miki tana son fahad?

Fatima tace eh mummy Allah tana sonsa, ajiyar zuciya mummy taja tace toh ta yi mashi magana? Fatima tace mummy mukayi mashi magana ai sai ya kashemu a gidan nan ke dai yakamata kiyi masa, mummy tace toh shikenan zanyi masa Allah yasa ya amince dan nima zanyi farin ciki da auren nan kinga sai ahad’a da naku ke da yusuf,

Cikin jin dad’i Fatima tace Ameen mummy, duka mummy takai mata abaya tace baki da kunya dagudu tatashi taficce daga d’akin.

Mummy ko da tayi ma fahad maganar haushi yakamashi yace shi fa a matsayin k’anwa ya d’auketa mummy tace ai ahankali zaka iya sonta.

Cikin takaici yace wlh mummy ba na sonta, kallonsa mummy tayi cikin mamaki tace kaje my son ko wane lokaci kaji kana sonta toh lafiya lau,  mummy ammah…… Please my son katafi kayi tunani akai

Tashi fahad yayi fuu yaficce daga d’akin, direct d’akin salma yanufa cikin fushi ya bud’e k’ofar lokacin salma tana kwance saman gado saida ta tsorata da tagansa,

Isowa fahad yayi bakin gadon tare da d’aura k’afarsa d’aya saman gadon fuskarsa a murtuk’e yace ke ni tsaranki ne yaushe nafara wasa da ke da zaki dinga zuwa kina cewa kina sona?

A tsorace salma ta girgiza mashi kai, tsawa fahad yayi mata yace bakida bakine?

Dasauri tabud’e baki tace a’a dan Allah yaya fahad kayi hak’uri, harararta yayi yace wlh idan nak’ara jin hakan zai na 6ata miki rai cikin gidan nan kina ji na?

Cikin kuka tace eh, wucewa yayi yaficce daga d’akin ransa a 6ace a ranar ko Amina bai bi ta kantaba.

Agurguje bayan wata d’aya Amina tana d’akinta tana saka kayanta a wardrobe kasancewar weekend ne  fahad yashigo kallonsa tayi tayi murmushi sannan tacigaba da abinda take,

Kusa da ita yamatso tare da rungumota jikinsa yace sannu da aiki ‘yan matana, cikin shagwa6a tace ‘yan mata ko mata? Dariya yayi yace ‘yan matan dai, ina my angel? Tace tana wajen baba mairo, lumshe ido yayi yace meyasa bakison kular min da ita?

K’ara shigewa tayi jikinsa tace ina fa kula da ita da ban kula da ita ai da batayi wannan girman ba, dariya yayi yace toh ai har ynz bata girma ba, d’ago kai Amina tayi takallesa yad’aga mata gira, murgud’a mashi baki tayi bata tanka shi ba, k”ara rungumeta yayi yace my wife yau kushurya zamuje anguwa, zaro ido tayi tace karufa min asiri babu inda zan je,

Yadda tayi ta so tabashi dariya yace gidan Aunty khairat fa zamuje,

Turo k’aramin bakinta tayi tace su mummy fa kar sugane mu

Kar kidamu na san abinda zan ce musu, janye jikinsa yayi daga nata yace kishirya my dota itama tare zamuje, wucewa yayi yaficce daga d’akin bai jira jin abinda zata ce ba.

Murmushi Amina tayi sannan tacigaba da aikinta.

Bayan sallar la’asar Amina tashirya cikin shadda purple colour wadda tasha aiki da farin zare, farin veil tayafa tasaka fararen takalma sannan tad’auki hand bag fara, shirya Ameerah tayi cikin wata doguwar riga red colour wadda daddy yasiyo mata daga dubai tad’aure mata gashinta abunka ga fara nan da nan kyawunta yak’ara bayyana…..

Daidai lokacin fahad yakira wayarta tana d’auka batare da sallama ba yace kifito fa ina jiranki a parlour,  marairaicewa tayi kamar zatayi kuka tace su mummy fa,

Ke ni kifito kar ki6ata min lokaci baijira jin abinda zata ce ba yakashe wayar dan yasan idan baiyi da gaskeba ba zata fito ba.

Rik’o hannun Ameerah tayi talek’a d’akin baba mairo tace mata zata tafi anguwa, babah mairo tace Allah yakiyaye hanya adawo lfy.

Parlour tanufa kamar wacce kwai yafashe mawa a ciki dakyar tabud’e labulen d’akin tayi sallama mummy ce sai yaya fahad kawai a d’akin kasancewar su fatima sunje anguwa,

Cikin fara’a mummy ta amsa mata tace masha Allah my dota wannan kyau haka, murmushi Amina tayi tasaci kallon fahad ta gefen ido, sanye yake cikin farar shadda ya yi kyau sosai, dannar wayarsa kawai yake?

Mummy mik’oma Ameerah hannu tayi tace zo kishiyata inganki ammah dai bakiyi kyau ba dariya Amina tayi tace mummy kina kishi daddy ya ce sabon jini yake so, gidanku mummy tace, dariya su Amina sukayi. Mik’ewa tsaye fahad yayi yace toh mummy za mu wuce,

Leda mummy tamik’o ma Amina tace gashinan sai kikai ma mejegon su fatima na mance suka fita ai da tare zakuje, kinga ba dad’i ace ba wanda yaje saisa fahad yace ko ke kad’ai ce sai yakai.

Kar6a Amina tayi tace toh mummy, mummy tace sai kun dawo, d’aga ma mummy hannu Ameerah tayi tace bye, mummy tace dawo ba a zuwa da take, mak’e kafad’a tayi tarik’e fahad, dariya yayi yad’auketa.

Gaba fahad yayi Amina tana biye da shi a baya, inda motarsa take suka nufa yabud’e yashiga Amina ma shiga tayi sannan yamik’o mata Ameerah, babu wanda yatanka ma d’an uwansa, Amina lumshe idonta tayi tana jin wani irin yanayi ina ma ace aurensu mai d’aurewane suke tare haka saidai kash ba ta tunanin haka.

Hannunta fahad yarik’o ahankali tabud’e idonta tasafkesu akansa, tuk”i yake hankalinsa kwance batare da ya kalletaba yace kinyi kyau my princess, murmurshi Amina tayi tace kaima ai haka, kallonsa Amina tayi tace my husby wai ina zamuje ne haka? Ka ce min gidan Aunty khairat kuma na ji mummy tana maganar gidan maijego,

Murmushi fahad yayi tare da matse hannunta da yake rik”e da shi yace matar abokina ce tahaihu yau ake suna shine zamuje kugaisa kiga baby in yaso daga baya sai muje gidan Aunty khairat d’in,

Cikin jin dad’i Amina tace toh yaya fahad, daganan kuma duk sukayi shuru Ameerah ce kawai take ta wasanta.

Gaban wani gida yayi horn maigadi yafito yabud’e masu  kasancewar ya gane fahad, a parking space yayi parking sannan yakira waya yace Abdul kafito gamu mun iso, ohk sai ka fito.

Wajen duk cike yake da ‘yan suna daga ni kasan shagali ake a gidan sbd mutanen da ke shiga da fita a gidan, bud’e motar yayi yafito itama Amina tafito suka jingina jikin motor matan da ke wucewa wajen sai kallonsu suke musamman ma ‘yan mata da suke zarya ta gaban fahad ko zai taya, itadai Amina saboda kishi ta cika ta yi fam,

STORY CONTINUES BELOW

Shidai fahad danna wayarsa kawai yake bai san abinda akeba, daidai lokacin Abdul ya fito daga sitting room d’insa nan yamik’a ma fahad hannu suka gaisa yace abokina ashe dagaske kake ai da ba zan fitoba dan na san halinka ina iya fitowa inga baka zo ba, Amina gaishesa tayi ya amsa mata cikin fara’a, tace ansamu k’aruwa Allah yaraya, Ameen, kar6ar Ameerah yayi yace abokina wannan fa? Fahad dannar wayarsa kawai yake yace ina ruwanka, Abdul yace ba fa ruwana bari inkira ashiga da ke wajen Aisha, waya yakira ba a fi minti ukku ba sai ga wata mai kama da shi ta fito da ka gani ka san k’anwarsa ce, nan suka gaisa da su Amina, yace zinatu kishiga da ita wajen Aisha kice ga surukarmu ta wajen fahad, wani mugun kallo fahad ya watsa mashi batare da ya yi magana ba yacigaba da abinda yake, dariya Abdul yayi yace uban ‘yan miskilanci sarautar ta motsa kenan.

Ko da suka shiga wani had’ed’d’en d’aki suka shiga wajen wadda take zaune saman gado ta sha ado suka nufa ta sha ado daga gani itace mai jegon, nan Zinatu ta gabatar da Amina, cikin fara’a suka gaisa aka bata jaririyar tayi masu barka abinci kala-kala da drinks tasa aka aje ma Amina, ba a fi minti goma fa fahad yakirata yace tafito sutafi.

Kayan da mummy tabada tamik’a mata tare da yi mata bayani, godia maijego tayi, tasa aka cika leda da kayan suna har bakin k’ofa Aisha tarakota sannan sukayi sallama tace agaishe da su mummy,

A mota tasamu fahad yana jiranta nan sukayi sallama da Abdul yad’ebo kud’i dayawa yaba Ameerah yace tasha sweet, godia Amina tayi masa sannan tashiga motar, bankwana sukayi da fahad sannan suka kama hanya.

Ko da suka fara tafiya babu wanda yatanka ma d’an uwansa, kallonta fahad yayi yaga ta jingine kanta a murfin motar kamar tana tunani hannunta yarik’o tad’ago kai takallesa murmushi yasakar mata itama tamaida mashi, yace my princess me kike tunani?  Tace ba komai, yace really? ‘Daga mashi kai tayi, maida hankalinsa yayi wajen tuk’i, saida yabiya wani moll yayi masu siyayya sosai sannan yawuce gidan Aunty khairat.

Aunty khairat saboda murna tarasa inda zata sa Amina bayan sun gaisa tace k’anwata daga ina haka? Na San dai ba hakanan kika wanki k’afa kika zo ba dan rabonki da gidan nan har na mance,

Dariya Amina tayi tace hakanan nazo gaisheki Aunty khairat zumunci zamuyi yau har dare, daidai lokacin fahad yashigo d’auke da Ameerah cikin fara’a Aunty khairat ta amsa masa tace ashe tare kuka zo? Fahad yace eh Aunty khairat tace haba nidai na san Amina ba ta wanko k’afa tazo min,

Nan suka gaisa da fahad  daga nan suka hau hira,

nan fahad yatafi yabar Amina suna ta hirarsu da Aunty khairat, Girkin dare ma Amina tayi mata, sai bayan sallar magrib fahad yazo yad’auketa yamaida su gida, tsaraba sosai Aunty khairat tacikasu da shi.

Ko da Amina tashiga gidan a parlour ta tadda mummy da fatima zaune suna hira da sallama tashiga suka amsa mata, dasauri fatima tazo takar6i Ameerah tace oyoyo my lovely daughter ina kika je kika barni, itadai Ameerah dariya kawai take, fatima tace sannu da hanya sis, murmushi Amina tayi tace yauwa fatima, mummy tace sannunku ‘yan suna, tace yauwa mummy, zama tayi kusa da mummy tace mummy barka da gida, cikin fara’a mummy tace yauwa my dota ya gajiya? Mummy ba gajiya, nan takawo tsaraba taba mummy, d’iba mummy tayi tabasu sauran suka raba.

‘Daki Amina tawuce tabar Ameerah wajen fatima, Amina bayan ta gama sallar isha’i zaune take saman pray mat  tana azkhar, kawai sai ganin salma ta yi ta shigo ranta a 6ace ko sallama batayiba kallon Amina tayi a wulak’ance  tace miye tsakaninki da yaya fahad?

Cikin mamaki Amina take kallonta tace salma ya za ayi kishigo min d’aki babu ko sallama ni babu komai tsakanina da shi, tsawa salma ta daka mata tace  kar kimaida ni mahaukaciya duk wani shige da ficcenki babu Wanda ban saniba, dan haka ina so kisan cewa yaya fahad ya fi k’arfinki nawane ni kad’ai, me zaiyi da bazawara bagidajiya irinki daman ku talakawa baku iya samun wuriba inkuka samu sai ku nemi kununa zak’ewa,

STORY CONTINUES BELOW

Ran Amina in yayi dubu ya 6aci ga tsananin kishi zuciyarta taji wani iri, cikin d’aga Murya tace ke! Ya isheki haka akan me zaki shigo har d’akina kidinga d’aga min murya na ji ni bazawarace ahaka aka ganni akace ana so aka bar budurwar, ina so kisan cewa k’addara ce kawai takawoni gidanku inda ba dan hakaba wlh baki isa ko kallon banza kiyi min ba, na gaji da wannan cin fuskar da kike min kuma idan fahad ne toh nan gani nan bari tsakaninki da shi,

Idanuwan salma saboda kishi suka rine sukayi jawur hannu tad’aga zata mari Amina daidai lokacin fatima tashigo sa6e da Ameerah da tayi bacci a kafad’arta mutuwar tsaye tayi, cikin zafin nama Amina tarik’e hannun tace kar ki saki ko da sau d’aya hannunki yata6a fuskata, dasauri fatima ta iso wajen tace minene haka kukeyi da girmanku? Kallon salma tayi tace salma wannan wane kalar kishine yakulle miki ido haka? Harararta salma tayi tace fatima kibarni in nuna ma yarinyarnan hankali a cikin gidan nan wlh bata isaba tashiga tsakanina da yaya fahad ba akansa babu abinda ba zan iya yiba,

Dariyar rainin wayau Amina tayi tace luk at you, aren’t you ashamed to say that, wannan ai abun kunyane mace kamarki ace tana fad’a kan namiji kuma mutumin da baisan tana yi ba.

Hannu salma takai zata cacumo Amina dasauri fatima tashiga tsakaninsu tace waiku wane kalar haukane haka kukeyi wlh zan je infad’a ma mummy,

Murmushi Amina tayi tace kar kidamu sis ni ba fad’a nake akan namiji ba ammah wlh ba zan yarda tak”ara cin mutunci na ba wlh na gaji da rainin wayon da salma take min ko dan taga ina kyaletane, wucewa tayi tahaye saman gadonta takwanta tare da runtse idonta.

Fatima kallon salma tayi tace please kiwuce kitafi d’akinki sis.

Salma wucewa tayi fuu tafita daga d’akin,

fatima saman gadon tahau tare da dafa Amina ahankali tabud’e idonta da sukayi ja tasakar ma fatima murmushi, jikin fatima duk ya yi sanyi tace kiyi hak’uri dan Allah sis, dakyar Amina tabud’e baki tace kar kidamu fatima komai ya wuce kije kikwanta,

Tashi Fatima tayi tace sai dasafe, Amina tace Allah yakaimu, fatima tana fita Amina  tace na shiga ukku wannan wace kalar k’addara ce kukane yaci k’arfinta, fahad ne yadinga kiran wayar Amina kusan 5 missed call ammah bata d’agaba haushi yakamasa yawurgar da wayar cikin 6acin rai yace har ta isa inkirata tak’i d’auka? Ko dan taga na damu da ita, tsaki yaja yace zata gane kuskurenta, komawa yayi yakwanta ransa a 6ace.

Salma tana shiga d’akinta tafad’a saman gado tafashe da kuka fatima tana shigowa tsayawa tayi tana kallonta cikin mamaki tace haba sis meyasa kike ma baiwar Allahn nan haka? Me tatsare miki, tsawa salma tadaka mata tace akan me zata dinga shige ma yaya fahad ba fa ajinta bane shi wannan bazawarar yarinyar, dasauri fatima tadad’e mata baki tace ya isa haka please sis kar mummy taji, ynz dai kikwanta kiyi bacci sai dasafe, fatima fita tayi tajawo mata d’akin sannan tanufi d’akinta.

Tun daga ranar kallon arzik’i bai had’a salma da Amina, Ko a mota idan zasuje school kowa sai yaita shan k’amshi fatima tun tana masu nasiha har ta gaji ta kyalesu, hatta shi kansa fahad Amina ta fita harkarsa duk inda tasan zasu had’u bata bari taje wajen ita burinta sonsa yafita daga ranta tunda saboda shi ake mata wulak’anci, fahad tun yana mamakin canzawar da Amina tayi har yahak’ura yakyaleta.

Bayan sati biyu dasafe Amina ta gama shirinta zata je school fahad ne yashigo d’akinta fuskarsa a d’aure itama Amina d’aure fuska tayi dakyar tabud’e baki tagaishesa ciki-ciki batare da ya amsaba  yace kihad’a min kunun gyad’a shinake buk’atar sha ynz, batare da ta kallesaba tace ba zaka samu hakan ba saboda school zanje, harararta yayi yace dole ne kiyi min abinda nake buk’ata in ba hakaba karatun da kike tak’ama da shi zai watse,

Kallonsa tayi yanayin da taganshi tatabbatar dagaske yake, wucewa tayi tanufi kitchen dan tad’aura mashi, shi kuma yakoma d’akinsa yana mamakin canjin da Amina tayi.

Fatima ce tashigo kitchen d’in zata d’au lemu, mamaki tayi ganin Amina tana girki dakyar tabud’e baki tace sis me kuma kike dafawa baccin zamuje school? Shuru Amina tayi bata tankaba, fatima tace Wlh yau 9 o’clock muke da lecture duba kiga ynz 8:40 dan Allah ki aje girkin kizo muje,

Murmushi Amina tayi tace kuje kawai sis idan nagama zan tafo kar kidamu, fatima tace toh shikenan sai kin tafo.

Amina tana gamawa, fitowar da zatayi daga kitchen suka had’u da mummy kallonta mummy tayi cikin mamaki tace ya akayi bakije school ba? Murmushi tayi tace yaya fahad ne nahad’a ma kunun gyad’a ammah ynz zan tafi,

Cikin fushi mummy tace kice masa nace yafito ya kaiki school yanzu, wannan ai zancen banza ne idan bai cin abinda aka dafa toh yabarshi mana,

Ganin ran mummy ya 6aci yasa Amina takwantar da murya tace kiyi hak’uri mummy bamuda lecture ne sai 10 dat’s y  nayi masa shima saida yace indai ina ganin da matsala intafi nace babu dan ko munje saidai muyi ta zama har sai 10 tayi,

Numfashi mummy taja tace toh shikenan Allah ya taimakeshi, kuma kice masa na ce yakaiki school idan ya gama kar yabari kimakara, Amina tace toh mummy.

Mummy tace bari ma zan kirasa, nan Amina tawuto mummy tana waya da fahad,

Dasallama tashiga d’akinsa daidai lokacin da ya gama waya da mummy, gabansa ta aje masa tace gashi nan, kallonta yayi yace kije kishirya idan na gama sai in kaiki, batace komai ba tafito tanufi d’akinta ta ida  shirinta tazauna jiran yaya fahad dan ta san ba zata samu lecture d’in first period ba kuma gashi 11 tana da C.A da sai tafasa zuwa,

sai wajen 9:30 yakira wayarta yace tafito suje, a mota ta sameshi nan tabud’e tashiga batare da ta kallesa ba murmushin mugunta yayi sannan yatada motar suka tafi babu wanda yatanka ma wani.

Amina ganin ya yi hanyar da ba ta school d’in suba yasa takallesa tace yaya fahad ba nan bane hanyar, ko kallonta baiyi ba yacigaba da tuk’insa.

Ganin haka yasa Amina takyalesa,

gabantane yafad’i ganin inda fahad yayi parking dasauri takallesa da mamakinta taga bai damuba, juyowa yayi yakalleta yace kifito muje,

Amina bata daina kallonsa ba tace yaya fahad baka ga inda kakawo ni ba mi zanyi a nan?

Kaduba fa kaga hotel kakawo ni, ni da zanje school wlh ina da test da anjima, me zamuyi nan?

+

Kallonta yayi yace ai bance ba zan kaiki school d’inba wlh kikai min gardama ba zakije ba, babu yadda Amina ta iya haka tabud’e motar tafito duk haushi ya kamata idanuwanta sun cika da kwallah,

Yana gaba tana biye da shi a baya har sukazo reception yabiya kud’i aka bashi key, ita dai mamaki kawai take,

Wani d’aki yabud’e mai kyau suka shiga yamaida k’ofar yakulle saman gadon yazauna, kallon Amina yayi da tayi tsaye ta tsaresa da ido ta so tabashi dariya ammah yadaure.

‘Daure fuska yayi yace kikayi tsaye kina kallona, Amina tace toh me zan maka? A wulak’ance yakalleta yace bakisan abinda zakiyi min ba? Toh hak’k’ina zaki bani, inkuma baki shirya ba toh sai ki hak’ura da zuwa school yau.

Takaici yacika Amina tace ammah yaya fahad duk gida bai isa ba har sai ka kawoni hotel? Kuma fa ina da C.A yau,

batare da yadamu ba yace nan nake buk’atar zuwa idan kin shirya toh bismillah idan Kuma baki shiryaba toh sai muyi ta zama a nan.

Ganin alamar da gaske yake yasa tanufi wajensa hawaye suna zuba daga idonta zama tayi saman gadon, yace baki shiryaba kenan.

Kallonsa tayi tace me kakeso inyi kuma? Yace hak’k’ina nace zaki bani, Amina ta ida k’ulewa cire kayanta tashiga yi nan fahad yajawota wulak’anci fahad yadinga mata duk abinda yakeso haka tadaure tayi masa mugunta yasa mata har saida yagaji dan kansa yakyaleta itadai batace komai ba,

Rungumeta yayi ganin baya da niyar sakinta yasa Amina tace yaya fahad please ina da C.A fa by 11, janyeta yayi daga jikinsa yatashi yashiga wanka, bayan ya fito Amina tashiga tayi cikin sauri tamaida kayanta ganin har 10:45.

Fitowa sukayi fahad yakai masa key d’insu a jikin motar ya hangota tsaye tana jiransa,

Wuta yaba motar ko da suka kama hanya kiwa shuru yayi babu mai yi ma d’an uwansa magana, Amina ta cika ta yi fam, ko da fahad yakalleta yaga tana ta had’a rai ta so tabashi dariya, cikin minti bakwai ya isa school d’insu har k’ofar class d’insu yakaita, ajiyar zuciya tayi ganin lecturer d’in bai shigaba, dasauri tabud’e motar taficce batare da takalli inda yakeba,

Saida fahad yaga shigarta class sannan yayi murmushi yaja motarsa yabar makarantar.

Ko da tashiga class d’in k’awarta murja tatisota a gaba tace wai ke ya akayi bakizo lecture ba d’azun? Kuma yanzu inda ace mlm sani y shigo fa kin sai dai saidai kiyi loosing d’in C.A d’insa kuma ina ta kiran wayanki bakiyi picking ba, murmurshi Amina tayi tace shikenan dai gani na zo, kyaleta murja tayi dan tasan halin k’awartata da rashin son yawan magana.

STORY CONTINUES BELOW

Ita dai Amina takaicin abinda fahad yayi mata duk ya isheta takaicinta d’aya dayakaita a otel, motsi kad’an sai taja tsoki,,Ita dai murja ta6e baki tayi tace kya ji dashi, ahaka har lecturer yashigo sukayi test d’insu sannan takama hanyar gida

Agurguje bayan sati biyu akayi walimar bud’e hospital d’in fahad an gayyaci manyan mutane dangi duk anzo anci ansha, ammah Amina bata samu damar zuwaba kasancewar ranar bata jin dad’i saisa mummy  tace ta zauna gids, ammah duk da haka ta kirasa a waya ta yi masa Allah yasa alkhairi.

Fahad ko duk inda zai je Ameerah tana biye da shi kayan ma da aka sa mata a ranar fahad ne yasiyo mata ita da jawahir d’in Aunty khairat, ko a wajen taron saida salma taso tayi masa iyayi nan yataka mata burki,

Abokan daddy dadama sunyi ma fahad tayin auren ‘ya’yansu ammah hak’uri yaringa basu yace yana da wadda yake so,

Su K.b ma ba a barsu a bayaba duk sunzo,

bayan kwana d’aya kasancewar mummyn salma ta zo itama, zaune salma take suna fira da mummynta da zata koma yola gobe nan salma take fad’a ma mummynta  ita fa babu wanda take so ta aura sai yaya fahad,

Mummyn salma ta ji dad’i sosai dan ta yaba da hankali da nutsuwar fahad kuma ko bakomai zumumcinsu zai k’aru,

Da daddare tasamu yayarta maman fahad take fad’a mata maganar da salma taje mata da ita.

Cikin jin dad’i mummy tace ina sane da maganar daman so nake yafara aikinsa sannan sai inyi ma daddynsu magana.

Cikin jin dad”i mummyn salma tayi ma mummy godia tare da sa albarka a Cikin had’in da za ayi.

________________

Yau kasancewar Ranar juma’a ne Amina dakyar tatashi tayi sallar asuba saboda wani irin ciwon kai da yamatsa mata ko azkhar batayiba ta lalla6a tahaye gadonta juyi kawai take saman gadon dan ma sauk’inta Ameerah tana d’akin babah mairo wajenta takwana, 

dakyar tajawo blanket ta lullu6e tana jin wani irin zazza6i ya rufeta. Ko da fatima taji shuru tashigo d’akin Amina tayi mata maganar zuwa school, ce mata tayi ba zata jeba school ba yau, fatima bata kawo komai ba a ranta dan ta d’auka duk bacci ne.

Paracetamol ta samu tasha nan taji Zuciyarta ta fara tashi dagudu tashiga toilet ta amaye sa, amai tayi sosai sai kace za ta amaye ‘yan cikinta, dakyar talalla6a tadawo takwanta.

Sai wajen 11 sannan taji yunwa duk ta isheta lalla6awa tayi tana dafa bango tafito tanufi kitchen tsakar gidan ba kowa, tahad’a tea mai kauri Tadawo d’akinta

Dakyar tayi kur6a biyu dagudu tashiga toilet ta amaye, nan da nan Amina tafita hayyacinta, ganin ta 6ata kayanta yasa tacire tayi wanka dakyar tasamu tasa kaya sannan tajawo wayarta number d’in doctor Halima family doctor d’insu ce mace takira,

Bayan sun gaisa dr halima tace Amina ya naji kamar bakida lfy, dakyar Amina tabud’e baki tace eh wlh ban jin dad’i shine nakira inji idan kina hospital d’inku sai inzo.

Dr Halima tace subhanallah me yake samunki?

Lumshe ido tayi jin yadda kanta yake sara mata tace zazza6i da ciwon kai.

Dr halima tace Allah yasauk’e Amina, saidai wlh ba na garin na je kano ammah bari inhad’aki da k’awata sister salaha sai kije chan hospital d’in taduba ki, idan nakirata waya sai inturo miki number d’inta idan kinje sai kikirata.

Toh Amina tace nan tayi mata godia.

Ba a fi minti biyar ba Dr halima taturo mata number d’in,

Tashi Amina tayi dakyar tajawo hijab tasanya tafito d’akin baba mairo talek’a tace xataje asibiti, salati babah mairo tahau yi tace daman kina gidan ashe baki lafiya ‘yar nan shine baki fad’a min ba?

STORY CONTINUES BELOW

Murmushi Amina tayi tace ai dasauk’i daman zazza6ine, babah mairo tace sannu Allah yasauk’e, kuma kina iya zuwa asibitin? Ko kikira fahad tunda shima abinda yakaranta kenan sai yadubaki.

Ita Amina shaf ta mance da  fahad ma doctor ne sai  lokacin,  daurewa kawai take dakyar tace babah mairo ai lafiya lau akwai likitan da zata dubani.

Baba mairo tace shikenan kau, Allah yabaki lafiya sai kindawo gashi hajiya basu dad’e da fitaba da Alhaji ba, ina ji bata san kina gidan ba,

Amina cikin zak’uwa da gajiya tace eh bata saniba gaskiya, babah mairo sai nadawo idan mummy d’in tadawo kice mata na je hospital d’in.

Ganin bata ga Ameerah ba yasa tatambaya tace Ameerah bata nan halan? Baba mairo tace eh d’azun da taga fahad shine talik’e masa ina ji suna chan d’akinsa.

Amina cikin rashin damuwa tace babah mairo sai nadawo.

Wucewa tayi ko da tabi ta hanyar part d’in fahad kulle tahangosa.

Tana fitowa taci sa’a taga idi driver nan suka gaisa take fad’a mashi asibiti zataje nan yace bari yakaita,

Tana shiga hospital d’in takira sister salaha nan tayi mata bayani tace tazo maternity tasameta, ko da taje suka gaisa nan tak’ara tambayarta me yake damunta,

Amina tace zazza6i ne sai ciwon kai da Amai, kallonta sister salaha tayi kamar tana nazari sannan tace kina jin tashin zuciya? Amina tace eh, dr salaha tace kina jin ciwo daga gefen cikinki? Amina tace a’a,

Hannu dr salaha takai ta danna gefen cikin, dasauri Amina tarik’e hannun saboda wani irin ciwo da taji,

Murmushi doctor salaha tayi sannan tarubuta mata test tace taje ynz tayo awon jini takawo mata.

Amina laboratory taje aka d’ibi jininta bayan minti 10 aka bata result d’in, office d’in sister salaha takoma takai mata lokacin tana shirin fita,

Sister salaha tana dubawa murmushi tayi tare da mik’o mata folder d’inta tace kije ANC, ko da Amina taje aka aunata akace tana d’auke da cikin wata d’aya da sati guda, zabura tayi tamik’e tsaye takalli sister d’in tace sister dagaske kike?

Murmushi sister d’in tayi tace dagaske  kin kusa zama mummy Allah yakawo masu albarka, complain of patient d’in sister taduba sannan tarubuta mata magunguna tafad’a mata lokacin da zata dinga zuwa awo.

Hankalin Amina in yayi dubu toh ya tashi office d’in sister salaha takoma ta tadda shi a rufe nan Hankalinta ya ida tashi dan ta so tasameta tataimaka azubar da cikin,

Waje tasamu tazauna saida tayi kusan minti talatin tana neman mafita domin ji take ina ma tamutu tahuta duk sai taji ta tsani fahad domin duk shine silar faruwar komai,

Dakyar ta lalla6a tatashi tanemi mai napep tafad’a mashi inda zai kai ta, ko da ta isa gidan direct d’akin fahad tanufa taci sa’a ko yana nan batare da ta yi sallama ba tafad’a,

Fahad da yake zaune laptop ce a gabansa, d’ago kai yayi yakalleta fuskarsa cike da mamakin yanayin da yaganta dakyar yabud’e baki yace Amina lafiya?

Wani irin kallo tawurga mashi tace lafiyar ce takawo haka fahad, takardar hannunta tawurga mashi tace duba kagani,

‘Dauka fahad yayi yaduba saida gabansa yafad’i ammah yadake yace toh kuma sai akai me? Allah ne yabamu kuma ina so,

Harararsa Amina tayi tace wlh fahad ka cutar da rayuwata sai Allah ya saka min, yanzu da wane ido kakeso inkalli su mummy? Kana tunanin ba zasu min kallon ‘yar iska ba? Toh wlh kasan yadda zakayi da cikin nan tun wuri kazubar min dashi.

Fahad da tunda tafara fad’an yake kallonta cikin mamaki yana tunanin daman ta iya fad’a haka? Jin ta ambaci zubar da ciki yasa ransa ya6aci tsawa yadaka mata saida Amina tafirgita domin saura kad’an tasaki fitsari, matsowa yayi kusa da ita yace baki isa kisa inzubar da shi ba domin cikina na halak ne ba na shegeba kuma ina so kisani duk wani rufe-rufe da nake miki yau ta k’are domin dole su mummy susan maganar nan daman dan azauna lafiya ne yasa nabiye maki ammah naga kamar baki da hankali kuma ciki dole sai kin haifesa da izinin Allah.

Cikin d’aga murya Amina da take kuka tace ya isa haka fahad, wlh baka isa kasani inbar cikin da bani so ba, yau nayi da nasanin had’uwata da kai har da nabari sonka yayi tasiri a zuciyata, yau nice kakira da banda hankali? Eh bakayi k’aryaba, banga laifinka ba *K’ADDARA CE* tahad’ani da kai fahad,

Fahad yakatseta yace kuma *K’ADDARA CE* tasa kika samu cikin kuma dole sai kin haifar min shi.

Harararsa tayi tace baka isa ba fahad wlh ba zan bar cikin nan ba ko da ace zan rasa rayuwata toh sai na zubar da..

Wani gigitaccen mari da fahad yayi mata yasa maganar ta mak’ale a bakinta,

Cikin mamaki tanuna kanta tace fahad ni ka mara?

Idanuwan fahad da saboda 6acin rai yasa suka canza kala, dafe kansa yayi yana jin haushin marin da yayi mata.

Girgiza kai Amina tayi sannan taficce daga d’akin,

Waje tafita hankalinta a tashe mai gadi magana yake mata ammah bata ma san yana yi ba, direct wani chemist da yake chan gaba da layinsu taje tayi sa’a ba kowa, nan suka gaisa da mai chemist d’in tace dan Allah taimako nakeso kayi min bawan Allah,

Mai chemist yace ina saurarenki, Amina tace maganin zubar da ciki nakeso kabani.

Zaro idon mutum yayi yace gaskiya a’a ba zan bakiba domin hakan bai daceba kima tashi kibani Waje,

Amina jakarta tabud’e tad’auko 20,000 ta aje masa, zaro idon mutumin yayi yace hajiya me za ayi da wad’an nan kud’in?

Murmushi Amina tayi ganin alamun samun nasara sannan tace dan girman Allah kataimaka kabani,

Kud’in mutumin yad’auka hannunsa har kyarma yake sannan yad’auko wani tablet yabata yace hajiya da kinsha yanzu zai miki aiki, cikin jin dad’i Amina takar6a tace yabata ruwa,

Ko da yabata ruwa tasha maganin mik’ewa tayi zata tatafi yace kizauna yabi jikinki, Amina tace no hakan ma ai ix ohk, godia tayi masa sannan tafito tanufi gida tana mai jin dad’in hakan da tayi,

Fahad tunda Amina tafita daga d’akinsa takaici da nadamar marin da yayi mata suka baibayesa, ammah kuma yana tuna maganar zubar da cikin da tayi duk sai ransa ya 6aci tsaki yaja saboda 6acin rai key d’in motarsa yad’auka yaficce daga gidan.

Amina da tunda tabaro wajen tafara jin cikinta yana murd’awa dakyar tamaido kanta gida tana cije le6e tana shigowa lokacin mummy tafito daga kitchen, duk yadda Amina taso tadaure ammah wani irin murd’awa da cikinta yayi yasa tacije le6e tare da dafe ciki, nan suka fara kallon-kallo da mummy,

Wani abu taji yana zuba ta k’asanta kallon k’asa tayi hankalinta yatashi ganin itama mummy abinda take kallo kenan ba komai bane face jini, wata irin k’ara Amina tasaki nan tafad’i k’asa a sume…..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page