K’ADDARA CE CHAPTER 9

 K’ADDARA CE CHAPTER 9

Wajen k’arfe goma kukan Ameerah ne yatasheta daga baccin da take, custard ta dama mata tabata tasha domin a ynz Ameerah duk abunda za a mata indai mai ruwane toh tana sha sosai.+

Bayan ta gama bata ajeta tayi domin tayi wanka.

Shiryawa tayi cikin less d’in da Aunty khairat tabata sky blue ta yi kyau sosai sannan tashirya Ameerah itama.

Gyara d’akinta tayi takunna turaren k’amshi nan da nan k’amshi ya gauraye ko ina, d’auko Ameerah tayi tanufi d’akin baba mairo da sallama tashiga lokacin baba mairo tana breakfast cikin fara’a ta amsa mata, waje tasamu tazauna tagaishe da babah mairo tare da yi mata ya jiki,

Murmurshi babah mairo tayi tace jiki ya yi sauk’i nagode sosai, sannunki Amina yau kinsha aiki Allah yasaka da alkhairi,

Lah babu komai babah ai yi ma kaine kun can-canci fiye da haka wlh, bari inje mugaisa da su mummy kafin daddy yafita,

Toh shikenan nagode sosai,

Main parlour tanufa dasallama tashiga lokacin su mummy suna dining area suna breakfast ita da daddy kasancewar su fatima suna school, wajensu tanufa dasallamarta cikin fara’a suka amsa mata Ameerah miko hannu take ta yi alamun mummy ta d’auketa, kar6anta mummy tayi tace oyoyo kishiyata kasancewar haka mummy take ce ma Ameerah

Murmushi Amina tayi tare da duk’awa k’asa cikin girmamawa tace daddy ina kwananku dafatan kun tashi lafiya,

Cikin sakin fuska suka amsa mata, kujera tajawo tazauna itama tayi serving d’in kanta,

Kallonta mummy tayi tana Murmushi tace gaskiya breakfast d’innan ya mana dad’i muna ta santinsa Allah yasaka da alkhairi kinsha hidima,

Murmushi Amina tayi tace bakomai mummy ai ba wani aiki bane.

Daganan shuru yabiyo baya suka cigaba da breakfast d’insu daddyne yafara ture plate d’insa sannan yakalli Amina yace mummynku ta yi min maganar karatunki nima daman ina da burin haka daga wane mataki kika tsayane,

She hung her head cikin girmamawa tace daddy tunda naga secondary school ban cigaba,

Yace toh masha Allah insha Allahu zan biya miki kud’i kizana exam tunda ance next 3 months za a fara kema kinga sai kiyi daganan sai asamo miki admission kiyi joining tunda zaman bai yuwuwa hakanan.

Zan samo miki text books kidinga dubawa kafin asamo miki wanda zai dinga miki lessons b4 tym d’in exams d’in.

Amina ta ji dad’i sosai saboda daman tana da burin taga ta yi karatu ummah ce tahanata, godia tashiga yi ma su Abbah da addu’o’in alkhairi,

Daddy yace ai bakomai ke da su fatima duk d’ayane kallon mummy yayi da taketa murmushi  itadai Amina tana burgeta sbd she is a frank girl, dat’s y take burgeta sosai,

yace toh ni zan wuce tashi mummy tayi tamik’a ma Amina d’iyarta sannan tabi bayan daddy dan tayi mashi rakiya, Amina tace Allah yakiyaye hanya daddy Allah yabada sa’ar abinda akaje nema Allah yamaidoka lafiya

Cikin Jin dad’in addu’an shi da mummy Ameen Amina, lumshe idonta tayi da tatuno addu’an da takeyi ma abbanta kenan d’an guntun murmushi wanda bai kai zuciba tayi sannan tatashi tatattare kayan takai kitchen,

Girkin rana tad’aura masu, babah mairo duk yadda taso Amina tabari tayi ammah tak’i kan dole ta amshi Ameerah takoma d’aki tabar Amina tayi, shinkafa da miya tayi kasancewar akwai nik’ak’un kayan miya, nan da nan k’amshi ya gauraye gidan, kunun aya tayi mai dad’i tasanya madara tasaka a cikin freezer.

‘Dakinta takoma tayi wanka tashirya tayi sallar azahar sannan tafito tad’auki na babah mairo takaimata a d’aki lokacin ta tadda Ameerah har ta yi bacci, babah mairo tayi ta shi mata albarka.

Kitchen takoma tad’auko food flask d’in da tajuye ciki tanufi parlour nan tacikaro da su fatima tana murmushi tace ‘yan boko ashe kun dawo ban saniba sannunku y gajiya,

Murmushi fatima tayi tace yauwa gajiya ana ta fama, y zaman gida?

Murmushi tayi itama tace Alhmdllh, fatima takama mata kayan suka nufi dining table suka aje, sannan suka zauna

Salma ce tafito daga room d’inta itama tazo tazauna daidai lokacin mummy ma tasafko suka gaisheta sannan Amina tayi serving d’in kowa nan suka fara ci suna zuba santi ita dai dariya kawai take masu.

A gurguje bayan wata biyu Amina ta goge sosai ta k’ara kyau da kaganta ka san tana samun hutu sutura mai kyau take sanyawa, mayuka da turare masu tsada take using da su,

Ameerah ma ta yi wayau sosai dan ynz tana takawa babu inda ba ta zuwa, kowa yana mamakinta yadda ‘yar shekara d’aya ammah kamar ta shekara da watanni saboda wayonta tana magana da gwarancinsu na yara ga kyaunta yana ta k’ara fitowa kowa na gidan yanason yarinyar saboda tana da shiga rai duk miskilancin salma da rashin son mutanenta itama tana d’an d’aukar Ameerah, Fatima daman ba a magana dan duk anguwar da zataje tare da Ameerah take zuwa saboda Ameerah akwai son yawo.

Daddy ya samo mata wanda zai mata lesson yana zuwa kullum yana koya mata itama tana research da kanta da waya dan har waya mai tsada aka siya mata, ta maida hankalinta sosai wajen karatunta kasancewar lokacin exam d’in ya matso….

__________________

A chan 6angaren fahad shima karatunsa yake hankalinsa a kwance ya k’ara gogewa da kyau kamar daman hutu yaje ba karatu ba, ammah har a lokacin bai mance da yarinyarba kullum cikin tunaninta yake duk yadda yaso yamance da ita ammah ya kasa shidai yana ganin tausayinta ne yake d’awainiya da shi.

Dan ma bai faye zama shi kad’ai ba kullum yana tare da abokansa biyu (Kb da Bello su ma ‘yan Nigeria ne) saisa yake samun sauk’in tunanin domin baccine kawai yake rabashi da su,

Yana waya sosai da mutanen gidansu kusan kullum.

Yau ma kamar kullum bayan sun dawo daga practical d’in wata theatre da suka shiga  direct gidansu suka nufa suna shiga suka cire lab cut d’insu duk suka zube saman 3 seater d’in da take a parlourn na su kasancewar duk a gajiye suke,

Fahad yace wash gaskiya yau lecture d’in rohan ta wahalar da mu sauk’in ma munyita a practically dat’s y na fahimta ammah da ba dan hakaba wlh da babu abinda zan gane, murmushi kb yayi yace ai kai gifted ne handsome ai ni i can’t say ga abunda nayi understanding ba bakaga ko da muka shiga theater room d’inba baya nakoma nayi zama na ba,

Dariya bello yayi yace kace k’wara ni na fahimci many points d’in lecture d’in abunda ban fahimta ba some few ne, kuma na San ina tare da k’waro insha Allahu everything will be normal, kb yace nima ai dat’s y kukaga ban damuba.

Harararsu fahad yayi ku dai kuka sani daman ai kun saba tsokana na, mik’ewa tsaye yayi yace whatever ma dai we would try to do our best insha Allah,

Bari inshiga ciki i need some rest now, later sai muje library muyi research domin gobe akwai aikin biostatistics agabanmu,

Sukace ohk sai mun had’u domin daman munason more experience about it.

Kowa d’akinsa yanufa domin yahuta kasancewar kullum idan sun dawo sai sun huta bayan sallar la’asar suke zuwa library….

Wayarsa ce tashiga ruri dakyar yajawota batare da ya bud’e idonsaba yayi receiving d’in call d’in cikin muryar bacci yayi sallama, muryar bello yaji yana cewa lallai fahad kar dai kacemin ynz katashi muna nan muna ta jiranka ynz haka ko sallar bakayiba har 4:30pm dasauri yabud’e idonsa yasafkesu saman clock d’in da take manne a bangon d’akin yace subhanallah kashe wayar yayi yatashi yanufi toilet wanka yayi sannan yad’auro alwallah.+
Agurguje yashirya sallah yagabatar da ita sannan yajawo wayarsa yanufo parlour inda yatadda su K.B suna jiransa ba tare da ya tanka masuba yawuce yanufi k’ofar fita,  basu damuba bayansa sukabi kasancewar sun san halin mutumin nasu miskiline na sosai bai faye son magana ba.
Ko da suka isa library d’in mutanen da ke cikinsa basuda yawa, checking d’in books d’in da suke buk’ata sukayi sannan suka samu waje suka zauna suka fara dubawa.
Wasu ‘yan matane guda biyu suka shigo kowace daga cikinsu ta sha riga da wando wad’anda suka matsesu sun bazo gashinsu a baya wajen kyau ba bayaba da ka gansu ka san hausawa, d’aya daga cikinsu sai yatsine fuska take tana kad’a key d’in mota, duk library d’in idanuwan mutane suka dawo kansu.
Duk’owa K.b yayi daidai saitin kunnen fahad da baima san abunda akeba domin hankalinsa duk ya tafi wajen buk d’in da yake searching akansa yace handsome ga fa mutuniyar taka,
‘Daure fuska yayi yace wacece kuma mutuniya ta? Dariya kb yayi yace kad’ago kakalleta mana gatanan na san kai take nema, ta6e baki yayi yace batakai wannan matsayinba ko ma wacece, kai fahad humairah ce fa, tsaki yaja yace koma dai wacece ix not my own benefit saninta.
Daidai lokacin humairah ta iso wajen kujerar da take kusa da ta fahad taja tazauna tana cika tana batsewa, ganin bai ko kulataba bata damuba saboda ya saba mata haka yasa ta d’auke buk d’in da yake gabansa tace just sau d’aya kawai kad’ago kakalleni there ar more important things to talk about
daure fuska yayi tare da mik’ewa tsaye yace waike meyasa kikeson takura ma rayuwatane na fad’a miki ba na sonki ya kamata ki fahimceni u ar not my type, karatune kawai yahad’ani dake ko da da k’wayar zarra babu sonki a cikin zuciyata hope you understand me.
Tunda yafara maganar take kallonsa cikin mamaki itama mik’ewa tayi tamatso daf dashi har suna jin numfashin juna tace fahad tun ranar da nafara d’aura idona akanka natsinci kaina a cikin wani kalar yanayi i know i feel in love you, ya kamata ka fahimceni kuma ai abun alfaharine duk girman school d’innan kaduba kagani different tribes wajen kyau akwai wad’anda suka fika sosai ammah babu wanda naza6a sai kai meyasa kake wulak’antani? Dan kaga ina sonka toh wlh baka isaba…
Ke dakata kar kisaki kice zakimin rashin kunya, ba zan sokiba domin bakikai matsayi ko darajar da zan sokiba kije kinemi wanda yake sonki pls don’t ever show me your face again, I told u earlier I hate you completely, please let me stay in peace don’t give me more worries, bai jira abinda zata ceba yabi ta gafenta yaficce daga library d’in,
Su kb da tunda aka fara dramar suke kallonsu suma tashi sukayi sukabi bayansa basuyi mamakiba domin sunsan halin gogan nasu baidamu da kula mataba,
Humairah saboda kunya kamar tanitse ganin yadda yatsinkata cikin mutane kasa d’aga k’afarta tayi saidai k’awarta pinky tajata suka ficce daga library d’in ko da suka shiga mota hawayen bak’in ciki suka zubo mata tace pinky wlh ko da fahad ne autan maza na hak’ura da shi,
murmushi pinky tayi tace hakan ai zaifi dan banga amfanin son wanda yatsanekaba just kicerasa from ur mind hakan nakega zaifi,
dogon numfashi humairah taja tace zan kwatanta hakan domin shine mafita agareni daina sonsa….
****    *****   ****    *****
Achan 6angaren Amina karatunta kawai take domin ynz saura kwana ukku sufara exams, zaune take d’akinta ta baje buks saman gadonta duk ta tattare hankalinta tana ta nazari, gefenta Ameerah ce take bacci,
mummy ce tashigo da sallama amsamata Amina tayi tana murmushi,
Mummy tace lallai d’iyata na lura dagaske kike karatun nan gaskiya naji dad’i Allah yasa ayi a sa’a, murmushin jin dad’i Amina tayi tace Ameen mummy,
Mummy kallonta takai ga Ameerah da taketa bacci tace a’ah kishiyar bacci taketayi kenan ai d’azun na jiyo kukanta,
Eh wlh mummy 6arna tagama yi dan anhanata shine take kuka daga nan tayi bacci.
Mummy tace ina ruwan Ameerah sarkin hidima, yauwa daddynku ne yayi maganar uniform d’inki, kishirya idan mukayi sallar la’asar zamuje kasuwa asiyo tunda saura 3 days kufara kinga k’ara tun ynz atanadi komai dawuri,
Toh mummy nagode Allah yasaka da alkhairi Allah yabiyaku.
Ameen mummy tace sannan tafita daga d’akin…..
Ko da sukaje kasuwa basusha wahala ba wajen samo uniform d’in set biyu mummy tasiya mata sannan tasiya mata atamfa kala ukku masu kyau, itama Ameerah aka siya mata set goma na kaya masu tsada da takalma kala biyar.
Amina tace mummy hidimar ai tayi yawa ko lokacin da tacika shekara d’aya kun siya mata kaya set sha biyu kuma ynz ba afi wata d’ayaba kun k’ara siya wlh hidimar ta yi yawa da dai kala d’aya aka d’auka.
‘Daure fuska mummy tayi tace ni nasa kaina yi kuma ma wannan Alhajine yace asiya maku  wlh raina yana 6aci idan naji kina cewa hidima ta yi yawa kenan yadda muka d’aukeki ba haka kika d’aukemuba domin mu wajenmu duk d’aya kuke ke da su fatima.
Duk’ar da kanta k’asa tayi kwallah ta cika mata ido tace mummy wlh na d’aukeku a matsayin iyayena a ynz kune dangina dan Allah kiyi hak’uri kiyafemin idan maganata ta 6ata miki rai.
Murmushi mummy tayi tace bakomai Amina Allah yayi muku Albarka.
Ameen mummy Allah yak’ara bud’i, Ameen.
Akwana atashi yau  Amina tafara zuwa school kasancewar yau za’ fara WAEC,
Wajen babah mairo tabar Ameerah, daddy dakansa yakaita ko da taje har anfara arranging d’insu, exam card d’inta tanuna aka gano mata number d’in sit d’inta,
Exam d”in batayi mata zafi ba kasancewar biology suka fara.
Ahaka sukacigaba da exams d’insu hankalinta a kwance ko da ana d’an taimaka masu ammah hakan baisa tayi k”asa da gwiwaba wajen ganin itama ta k’ok’arta ta yi fiye da rabin questions d’in by her brain.
Tun daga ranar malam idi driver yacigaba da kaita school d”in kasancewar daddy bayanan ya yi tafiya kullum 1k mummy take bata ammah ta yi-tayi da mummy tarage  ammah tak’i ganin mummy tana shirin fushi da ita yasa tahak’ura tacigaba da k’ar6a ko da ba ta iya cin sama da 500 a rana shima sai idan ta shiga restaurant d’in da yake a school d’in
Tunda taje k’awarta d’aya itama sit mate d’intace, Amina Al’ameen abokai barkatai daman basu gabanta kasancewar daman tun chan baya ta saba ummah bata barinta tayi abokai,
itama kasancewar halinsu ya d’an zo d”aya dukkansu basu da surutu sosai kuma exams d’ince takawo su school d’in basusan kowaba cikin ‘yan kwanakin da sukayi suka saba da juna domin meenat Al’ameen sau biyu tana zuwa gidansu Amina ammah ita bata ta6a zuwaba  duk kallon da meenat takema Ameerah a matsayin autarsu Amina ce mummy ta haifeta tana son yarinyar sosai, ita dai Amina bata yi gigin fad’amata d’iyarta bace domin tana ganin kamar tona ma kai asirine.
Bata ta6a kawo ma ranta Ameerah diyar Amina bace itama Amina bata fad’a mataba,
STORY CONTINUES BELOW
akwana atashi yau su Amina suke gama exams d’insu tunda suka isa makarantar zaune suke gaban hall hira kawai suke kafin time d’in shiga exams d’in yayi domin yau sai 10:00am zasu shiga duk wanda kakalla a wajen sai kaga jikinsa ya yi sanyi domin suna jimamin rabuwa da abokansu,
tunda Amina tafito daga paper d’in wajen bishiyar da suka saba zama taje tazauna tana jiran meenat tafito duk jikinta ya yi sanyi tana jin babu dad’i a ranta saboda rabuwar da zatayi da k’awarta bata dad’e da zama ba saida meenat ta fito tanufo inda Amina take tafiya take very slow jikinta itama duk ya yi sanyi itama waje tasamu kusa da Amina tazauna tare da k’ok’arin boye damuwarta tace friendy ya exam d’in?
murmushi Amina tayi tace Alhmdllh yau dai mungama sai ayafi Juna, kallonta meenat tayi tace Allah yayafe mana gaba d’aya ammah nidai har ga Allah zamana da ke Amina baki ta6a 6atamin ba ko da sau d’aya inma kin min to wlh na yafe.
hawayen fuskarta da take dannewa ne suka zubo tace Amina next week zan bar kaduna zan koma gidan iyayena da ke Abuja daman wajen Auntyna nazo garin nan exam ce takawoni kuma Alhmdllh mun gama tun jiya mummy take waya in mungama inkoma gida dan Allah ko da sau d’ayane kizo gidanmu mugaisa kiga Auntyna kafin intafi.
numfashi Amina taja tace toh insha Allah zan zo na yi miki alkawali, murmushin jin dad’i meenat tayi tace nagode sosai friendy Allah yabarmu tare.
fira suka shiga yi kowa yana jin babu dad’i a ransa dannewa kawai suke har driver d’in meenat yazo ammah tace ba zata tafiba sai anzo d’aukar Amina basu dad’eba sai gashi anzo d’aukar ta duk yadda sukaso su6oye damuwarsu ammah suka kasa sai da sukasha kuka sannan suka rabu da Juna kowa yanajin babu dad’i a ransa.
ko da ta isa gida su mummy murna suka shiga taya Amina nan da nan tafara mancewa da damuwarta. daddy ma sai da yakirata a waya yatayata murna.
Bayan kwana biyu Amina whatsApp tabud’e daman saboda exams yasa bata bud’eba group d’in girke-girke tashiga domin daman ita a rayuwarta tana son girki, duk wanda taga anturo intaga bata iyaba tana k’ok’arin gwada yinsa su mummy suna jin dad’in hakan domin sunsan Amina wajen girki ba bayaba bare yanzu da tazama expect,
yanzu kusan duk ita take girkin gidan dan ko ranar da daddy zai dawo kusan ita tayi mai girkin tararsa shima saida yajinjina ma girkinta, ya yi masu tsaraba sosai kowa ya ji dad’in tsarabar da yasamu.
kamar yadda Amina tayi ma meenat Alkawali bayan kwana biyu tashirya taje gidansu bata sha wahalaba wajan ganewaba sbd mijin Aunty rahma sananne a anguwar,
murna wajen meenat ba a magana domin kamar tagoya Amina saboda jin dad’i nan da nan aka cika mata gabanta da kayan ciye-ciye ita kanta Aunty rahma ta ji dadi sosai, ta dad’e a gidan suka sha hira sosai sai gab da magrib tabaro gidan, kaya nik’i-nik’i suka had’o mata, da zata tafi meenat har da ‘yar kwallarta haka sukayi bankwana kowa yana kewar d’an uwansa domin ynz sai dai idan meenat ta zo garin zasu dinga had’uwa.
bayan sati biyu Amina ce zaune d’akinta tana chart baba mairo ce tashigo da sallama cikin fara’a Amina ta
amsa mata tare da cewa sannu baba mairo ashe har kin dawo daga kasuwar murmushi baba mairo tayi tace eh wlh ‘yar nan na dawo tun d’azun ai kina d’aki saisa bamu had’uba ina jikalle ta take naga tunda nadawo ban ga giftawarta ba ga tsarabar da ta ce inyo mata nan na yo
kai baba mairo har da d’awainiya kuma?ni tun d’azu ma da tadameni da rigima nakorata kin san halinta da rigima dariya baba mairo tayi tace ina ruwan Ameerah ga chocolate d’in ki aje mata, tashi Amina tayi tace nagode sosai babah Allah yabada lada, nima ynz nakeso inje in dubota dan shurun nata ya yi yawa Allah yasa ba 6arna take ba,
parlor Amina tanufa taga Ameerah bata nan babu kowa parlorn direct d’akin Fatima tabud’e da sallama tashiga, kwance ta tadda Fatima a saman gado tana ta shagwa6a a waya ko ba a fad’a mataba ta san da wa take wayar, Ameerah kuma tana gefenta tana ta wasa, 
yadda take wayar yaba Amina dariya tatsaya a bakin Kofa tana kallon ta domin ta ga alamu Fatima bata san da shigowarta ba, cikin shagwa6a Fatima kamar zatayi kuka tace please my bro yaushe zakazo wlh munyi missing dinka sosai, daga can 6angaren fahad murmushi yayi yace kar kidamu my lil sis very soon zaku ganni har kugaji da ganina, ammah bro kullum haka kake cewa kuma shiru ka k’i dawowa toh kafad’a mana tym din,
kikwantar da hankalinki zan fad’a miki idan zan dawo murmushin jin dad’i Fatima tayi tace ko su mummy kar surigani sanin dawowarka, eh na yarda, yauwa my bro gaskiya na ji dad’i sosai juyowar da zatayi taga Amina a tsaye tana kallonta sai murmushi take itama murmushin tayi tace laahh sis yaushe kika shigo wlh banji shigowarkiba, bro please bari in d’an yi magana kar ka kashe wayar 2 minutes
harararta Amina tayi cikin wasa tace daman ya za ayi kisan dawowata kina ta waya da ya yasuf, laahh wlh sis bashi bane yaya fahad ne fa muke waya dashi kin san ina ji da wannan big bro d’in nawa,
hello yaya fahad, ina jinki my lil da wa kike magana? murmushi tayi tace da sis Amina ce gata ma kugaisa,
yamutsa fuska yayi yace wacece ita kuma.
kai yaya wadda fa nabaka labarinta tana zaune a nan, oh sry wlh na mance ne.  tashi Fatima tayi tanufo wajen Amina da take tsaye wajen bed d’in tana 6arema Ameerah chocolate tace tohm yaya gata ku gaisa,
mik’a ma Amina wayar tayi tace gashi kugaisa da yaya fahad, kallonta Amina tayi tace kai sis amma…
a kunne ta kanga mata wayar tace gaisawa zakuyi ba cinye ki za ayiba, murmushi Amina tayi tare da yin sallama shiru taji anyi tace hello nan ma shuru janye wayar tayi daga kunnenta tace sis ashe ta tsinke,
ayya toh bari inkirasa a’a sis kibari mun gaisa wani lokacin mik’a mata wayar tayi tare da ficcewa daga dakin,
komawa Fatima tayi saman gadonta takwanta daidai lokacin wani kiran yak’ara shigowa d’agawa tayi tana murmushi tace yayanah, sry my lil sis wlh wayarce ta tsinke bata d’in mu gaisa, ayya yaya har ta fita daga d’akin ma ba ta kusa amman ga babynta ku gaisa, kanga ma Ameerah wayar tayi a kunne tace baby ce hello, dariya Ameerah tayi tacigaba da yi mashi gwaranci ko da baijin abinda take cewaba ammah maganar yarinyar ta burgesa sbd a yadda yaji maganar ya san yarinyar tana da wayau da surutu,
dariya kawae yake yi mata itama Fatima dariya take janye wayar tayi daga kunnen Ameerah tace hello yaya aikam nan Ameerah tasa kuka,  fahad yace yarinyar dai tubarkallah akwai surutu, Fatima tace kad’an ma kaji yaya, .
fahad yace kukan me takeyi ne.? wai dan na janye wayar shine take kuka, dariya yayi yace toh bata wayar, toh tace tare da kanga mata wayar a kunne, toh baby kukan ya isa haka nan,
jin muryarsa yasa tayi shuru tare da jan dogon numfashi,  murmushi yayi yace Aunty ce ta ta6aki ko?
uhmm tace
toh sry zan Zane Aunty Indai tana sa min baby kuka toh ya isa haka bani labari,
nan tacigaba da yi masa gwarancinta shidai dariya kawai yake yarinyar ta shiga ransa sosai sun dade suna waya sannan yakashe wayar daga nan kusan kullum sai ya kira ya ce aba Ameerah sun sha waya duk ranar da ko bai kiraba Ameerah sai ta damesu da rigima, ita dai Amina kallon ikon Allah kawai take……
Cikin murna tace oyoyooo my lovely bro u ar wlcm, cikin murna shima yace kedai fatima kin girma ammah har yanzu baki nutsuba,
Murmushi tayi tace yayana indai ina tare da ku ganina nake yarinyace a wajenku, dariya yayi yace mukuma kallon babbah muke, shagwa6e fuska tayi kamar zatayi kuka tace a’ah yaya.
Daidai lokacin su daddy suka iso wajen salma tace yaya fahad sannu da dawowa, murmushi yayi yace yauwa salma, kallon daddy yayi dasauri yajanye fatima daga jikinsa yarungume daddy cikin murna yace oyoyoo daddyna I really missed you, murmushi daddy yayi yace kaida baka zuwa kaganmu ai bakayi missing d’inmu ba.
Cikin shagwa6a yace daddy ai ynz gani nadawo har sai kun gaji da ganina, dariya daddy yayi yace haba my son ai ba zamu ta6a gajiya da ganinkaba, Let’s go home mummynku tana chan tana jiranmu kokuma inche tana jiranka,
Idi driver yazo yad’auki trolley din yasaka a mota sannan suka kama hanyar gida kowa yana ta murna.
Salma ko tunda taganshi hankalinta yak’ara tashi domin wutar sonsa da take dakonta a ranta ta tashi jikinta duk yayi sanyi satar kallonsa kawai take a mota,
murmushin jin dad’in ganinsa a k’asarsa ta haihuwa yake, ko da suka iso ganin gidan yayi duk ya chanza masa.
Tun kafin a ida yin parking yabud’e murfin motar yafito yanufi cikin gida  yana kwala ma mummy kira, dariya su daddy sukeyi masa, dasauri ya isa wajen mummy yarungumeta dariya tayi tace oyoyooo my son u ar highly wlcm back, I missed you so much. Murmushi yayi yace missed you more my lovely mum.
Aunty khairat ta iso tace mu tunda ba ayi missing d’inmu ba toh mu munyi naka sakin mummy yayi yace I missed you too my sisto, sorry ganin mummyna ne yasa namance da kowa dariya aka sanya mashi,
Mummy tace oya my son go an take a shower now then sai kafito kaci abinci.
Ohk mum
Daidai lokacin jawahir ta iso wajensa tarungumesa tace oyoyoo my uncle u ar wlcm back home, d’aukarta yayi yabata pick a kumatu yace thanks my lovely dota.
Kallon yarinyar da take tsaye tana kallonsu yayi yaga ta 6ata fuska ganin ya d’auki jawahir  kamar zatayi kuka 
masha Allah yace ganin ta ci kwalliya cikin doguwar riga antufke mata gashinta.
Sauke jawahir yayi yamik’a mata hannu yace common my baby, kamar ta san abunda yake nufi dagudu itama tanufo inda yake yad’agata sama yacillata yarik’ota nan tasa dariya, yarinyar yaji ta k’ara shiga ransa sosai kallon fatima yayi yace wannance babyna wadda muke waya da ita ko?
Eh yaya itace. Sai lokacin tatuna da Amina dasauri tanufi d’akinta tana kwala mata kira ganin d’akin tayi wayam, motsi taji a toilet alamun wanka take, fita tayi daga d’akin tace Allah ya soki ai na d’auka hakanan kika k’i fitowa ai, kuma sis idan kin gama kifito muna parlour.
Ameerah lik’ema fahad tayi dakyar fatima takar6eta daga hannunsa sannan yasamu yanufi part d’insa domin yakimtsa, ko da yashiga d’akin nasa yaga komai very need murmushi yayi domin ya san aikin
k’anwarsa ne.
Wanka yashiga yayi sannan yafito yashirya cikin k’ananan kaya yagyara sumar kansa sannan yafeshe jikinsa da turare shi kansa da yaduba mirror ya san ya had’u. Wayansace tafara ringing yana dubawa yaga mummyce murmushi yayi yad’auka yace ganinan mummy.
Koda tafito daga wanka simple makeup tayi tasaka atamfa black nd red colour d”inkin ya kar6eta sosai ta yi gwanin kyau d”aurin kallabi tamurza nan da nan tak’ara fitowa kamar wata amarya feshe jikinta tayi da perform Sannan tayafa veil black, flat shoes tazura sannan tafito tanufi parlour gabanta sai fad’uwa yake  tsaye tayi bakin k’ofa takasa bud’e labulen ta yi kusan minti biyar a tsaye hayaniyarsu kawai takeji,
Muryar mummy tajiyo tana tambayar fatima ina take ahankali tabud’e labulen da sallama tashiga amsa mata sukayi fatima tace kai sis wannan kyau haka? Aunty khairat tace masha Allah gaskiya kinyi kyau, mummy tace toh ya kukaga my dota, murmushi kawai Amina tayi ta isa tatsugunna tagaishe da daddy.
Tunda tashigo yaji muryarta gabansa yake fad’uwa tunani yashiga yi ina yasan mai wannan muryar ammah ya kasa tunawa sannan ba ya jin zai iya d’aga kansa yaga ko ma wacece latsa wayarsa kawai yake, itama bata lura dashi ba a parlourn saida fatima tace Amina ga fa yaya fahad nan kugaisa, batare da takalli inda yakeba tace yaya fahad sannu da zuwa ya hanya? dafatan andawo lafiya.
Lumshe idonsa yayi jin yadda muryarta tadoki dodon kunnansa cikin ransa yace duk yadda akayi nata6a jin muryarnan.
Maganar fatimace takatsesa tace yaya fahad ana gaisheka ahankali batare da ya kalletaba yace lafiya lou.
Ta ji haushin yanayin yadda ya amsa mata ammah ba yadda zatayi cikin ranta tace lallai wannan jin kansa ya yi yawa ji tayi tanason ganinsa d’ago kai tayi takallesa daidai lokacin shima yad’ago yakalleta had’a ido sukayi duk saida gabansu yafad’i………

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page