DR SAMEER AMEER CHAPTER B KARSHE

 DR SAMEER AMEER CHAPTER B KARSHE

Safiya nayi bayan sunyi having breakfast dinsu a a mini dinning table dinsu ..breakfast ne na toyayyen kosai Wanda yaji hanta da Kwai da kuma haddaddan kunin shinkafa…mamee takalli DR SAMEER AMEER daya xage yana ta dura kunu da kosai tace SAMEER hope you like it?DR SAMEER AMEER yai murmushi like it..I love it mamee..thank you it’s being ages danai having breakfast da abincin gargajiya..every morning annoying breakfast muke having kullum soybean milk da lasagne.+

Mamee tai Daria amma it’s good for the body aiko??dr SAMEER yai murmushi of course soybean yana adding nutrients a body sosai,NEELAM dake gefe tai saurin daukar cup tashanye kununta sannan takalli agogon hannunta..Kai mamee Wlhy nakusa makara sannan ta mike tana gyara suit din jikinta dayake uniform dinnasu suit ne maroon Riga da skirt mini da leggins se longsleeve din ciki baki ne da kuma leggins din shikuma tie din multi color ne na maroon and black se turban black da covered shoe baki se ankle socks maroon..

Mamee takalli nata agogon tareda mikewa itama wai wallahy ban kula ba kinsan kosannanne ya makarar damu gashi hiran jia yasa mukayi lattin tashi..DR SAMEER AMEER yamike its all my fault gaskia ninenaxauna se xuba nake kaman radio..NEELAM tai murmushi a haba Yaya Kaiba radio bane nd bet you inna dawo school wannan puzzle din xamuci gaba.har kasa yarakasu sannan suka tsari cab har biyu daya Wanda xekai NEELAM dake schooling can maitama dayan kuma xekai mamee dake can wurarren garki market..

Har mamee tashiga mota ta leko da kanta ..SAMEER kakka mnta da gidan suhaylan please..DR SAMEER yai murmushi Kai mamee bakya mantuwa insha Allah xanje amma kuma ba yana office yanxu ba?mamee tace no tana gidah she’s off duty every Tuesdays..DR SAMEER yai nodding Kansa insha Allah mamee xanje but sena karbo kayana a airport saboda akwai handbag da shoe Dana saya mata Itama..mamee to angode semin dawo ..sannan yadaga mata hannu yakoma cikin gidah.

Yana xuwa cikin gidah ya xauna Akan kujera tareda daukar wayarsa yakira yaseer sannan yasa a handsfree ringing biyu yaseer ya dauka ..DR SAMEER yace yo dude I have being waiting for you..whr you dey??

Yaseer yai murmushi dude I dey airport..didn’t expect your call Ma na karbo mna kayanmuma yanxu haka kaganni ana saka kayan a cab.DR SAMEER yace dude jokes apart you serious?

Yaseer yace I’m damn serious Wlhy yanxu haka kaganni nama shiga cab expect me insha Allah nanda 20_30 mins..SAMEER yace thanks dude your one in a zillion till you come..sannan yai cutting call din yana murmushi Alhamdulillah dama xuwa airport dinnan ga nisa ga wiyar xama..

Minti 35 kacal yaseer ya iso gidansu DR SAMEER AMEER yasa gateman yatema ka mashi shigowa a luggages da irin traveling loads dinann katinkatin kaman Wanda yasaye mall din kaya..DR SAMEER yatayasu suka shiga da Kayan sannan suka xauna a parlor bayan yakawomashi lemo da ruwa..yaseer yakalli DR SAMEER dude Ina mamee and beautiful NEELAM?DR SAMEER yai murmushi mamee na office .beautiful NEELAM kuma taje school..yaseer yace dude NEELAM a wane class takene..SAMEER yace tana ss1..yaseer yasakecewa wanne field art or ours?DR SAMEER yai murmushi bros I’m tired of this annoying questions finally NEELAM tana art .sociologist xata xama ..yaseer ya mike tareda daukar gorar ruwa well nifa nayi kamu..Allah xanjirata tagama I’m serious ku ajeyemin ita sannan yakurba ruwan yana heading towards the door xe bude..DR SAMEER yace nide baxanwa NEELAM auren dole ba haka kawai batasankaba batai komaiba kace xaka aureta sanann ya harareshi da wasa beside gynecologist xata aura ba surgeon ba..nd dakake bude kofa Ina xakaje?

Yaseer yace for NEELAM’s sake Wlhy xan iya switching inkoma gynecologist,Kai bakasan love bane and kofa dana bude gidah xani mana dama Wlhy Dan NEELAM naxo kuma batanan xaman mexanyi?DR SAMEER yai murmushi aikwa da ansaka a Guinness world book of record..and tunda futa xakai jirani xanje wuse gurin aunty suhayla..yaseer yace aunt suhayla maman nawal??DR SAMEER yace ehh mamnta.Yaseer yace aikwa naga yarinyar a amigo taje shopping Ashe tagama karatu itama?DR SAMEER Yabata rai to Ina ruwana?yaseer ya kyalkyale da daria I thought you care for her?DR SAMEER yai tsaki why on earth shd I care me hadina da ita ?kai lemme tell you nifa wannan yarinyar she’s not my type wallahy tafiya iyayi and beside she’s rude tunmuna yara Wlhy takeda Hali haka..yaseer yace toh toh Allah yabaka type dinka

STORY CONTINUES BELOW

DR SAMEER yai murmushi sannan ya mike yabude wani mini akwati yaciro jaka da takalmi a kwali designer din yvsl(yev Saint lauren)sannan yasa a Ledah babba..muje .cab kowannensu yadauka yatafi inda xashi inda DR SAMEER yanufi wuse 2 gidan aunt suhayla…

Yana zuwa yakalli balarabe megadi sannan suka gaysa dayake sunsan juna balarabe megadi se dashe baki yake mutan toki(turkey)saukar yauhe??sameer ya kyalkyale da daria wallahy jia nadawo balarabe kace kananan da hausar nan taka bakadenaba bayan har alkawari kamin kace kafin nadawo hausar ka taxama tayan Abuja.balarabe yadan murmusa wallahy sameer naso hakan amma Ina nagayamaka kwakwalwar kifice dani har yau ban iya hausar habuja ba,wannan kauyancin de yananan sede in anyi sallah aringa tayamu da addu’a.DR SAMEER yace toh shikenan insha Allah yanxu de ga wannan sannan yaciro 1k yabashi kasha pure water sena futo aunty nacike ko?balarabe yakarbi kudin sannan yanunke kudin yasa a aljihu godia nake mutan toki ehh tanaciki hajia suna ciki harda rawal (nawal)itama Tana ciki..DR SAMEER yace toh nagode sannan yasakai yashiga zuciarsa se tukukwi take.

Yana shiga da sallamarsa parlor din morad yataho da gudu ya rungumeshi bros how far ina yini?DR SAMEER yace not too far sanan kuma lapia qalau..zaune suke akan 3 sitter meerah dakuma NAWAL se aunty suhayla dake gefe Tana murmushi sannu DR SAMEER AMEER morad tashi kabashi wannan kujeran.morad ya tsugunna har kasa yagayda aunty suhayla sanann yajuya yagaydah meerah tunda tagirmeshi kamar daga sama yatsunkayo muryar NAWAL Tana gaysheshi Ina yini DR SAMEER AMEER?saboda idan mutanen palor din yadan basar sannan yace lapia qlau NAWAL.ahakade sukai ta hirarsu shida aunty suhayla dakuma Meerah se jefi jefi NAWAL take magana dukkoda DR SAMEER AMEER dinbecika maida mataba.NAWAL ce tamike tanawata tafiya barin kawo maka drinks da snacks.DR SAMEER yace dama kinbasshi nagode I’m okay..aunt suhayla tace a’a ba ayi haka ba yaxakai kace a’a .aunt suhayla tace SAMEER kaxama DOCTOR kuma yabatin fara aiki kasamu asibitin daxaka dinga xuwane??DR SAMEER AMEER yace wallahy a’a dama da friends Dina mukace xamu zanklin hospital mutambaya to kumade bamujeba may be by next week xamu muji yadda xa’ai.

Aunt suhayla tace why not kuxo asibitin danake aiki dama muna bukatar qualified surgeons anan guraren gangis street maitama xaka Ganshi wani NOBLE MEDICAL CENTER.xantanbayi wani Doctor hammadi shine Nima yasamamin aikin insha Allah xaku samu.kaga akwai gida da akeba doctors kyauta dakuma mota ga foodstuff kyauta duk monthly.inka shirya jibi kaxo se narakaka gurinsa sekataho da qualifications Dinka I heard da first class kafutomako?DR SAMEER AMEER yace eh aunt.tace Yawwa kaga abu xexo dasauki Ma Allah de yashige mana gaba.DR SAMEER AMEER yace amin.yakai kusan 1hr sanann yamike tareda ajiye Ledar gaban aunt suhayla.gashi aunty wanann ba yawa nixanwuce gidah.aunt suhayla tabude Tana mamaki kaikai yvsl designer aiko nagode sameer kamar kasan akwai wani meeting daxami da Aisha buhari na future assured Akan wani cancer awareness.kaga se insaka abuna nagode nagode DR SAMEER Allah yakymu bikinka we go party and jolly like no gobe..DR SAMEER AMEER yace amin.NAWAL takarba jakan Tana kalla wallahy tayi Kyau gaskia nixan karbe.aunty suhayla ta fisge jaknta wannan kuma tsakaninki kedah yayanki.futayai shide harda saurinsa kar NAWAL tabishi amma sedah tabiyo bayansa shi har mamakin Ina shan kamshin da wanann daga kan yake oho.yadan kalleta toh se watarana kuma.NAWAL tadan marairaice tareda kashe murya watarana kuma?kana nufin baxaka sake dawowaba?DR SAMEER AMEER yai murmushinsa me kashe yammata tareda daukar hankalinsu okay toh jibi xance kenan ko?NAWAL tadanyi Daria kokaifa,pls kagaidamin da mamee dakuma NEELAM.shide nodding knsa yai sanann yafice daga gidan itakuma tai murmushi sannan takoma cikin gidah how sweet?.

   KANO:

Bayan sunje Kano ceo Muhammad mahmud shida FAREED a hotel din royal Tropicana suka sauka bayan duk sun gama harkokinsu na ranar.washegarin ranar ceo muhammad Mahmoud yasa FAREED yakaishi unguwar gyadi gyadi court road.dede wani plaza ceo yacewa FAREED yai parking wani medium office suka nufa sannan CEO yacewa FAREED yajirashi awaje.dama haka FAREED din yakeso Dan baysan shiga hurumun da banasaba gefe yakoma tareda Ciro wayarsa yana dannawa.sanann CEO yashiga cikin office din.wani dattijan mutum ne aciki me shigar kamala dakuma dattako kusan age mate din CEO ne.bayan sungaysa CEO Muhammad mahmud yakalli mutumin sanann naji yakirashi da AMBASSADOR IBRAHIM_KHALEEL.

STORY CONTINUES BELOW

Kasancewar kai kadai nayadda dashi a cikin duniar nan gabadaya sekuma yar dana Hayfa NASREEN.ksan cewar yan uwan damuke Uwa daya uba daya dasuma so suke yau nafadi namutu suci gadona.wani temako naxo kamin Dan Allah khaleel.AMBASSADOR IBRAHIM_KHALEEL yace subahanAllahi toh Allah ya kyauta menene temakon MM??dayake shorting din sunan suke In abbreviation saboda babban sunane..CEO ya goge hawayen fuskarsa sanann yadakko wasu document cike da files yatura agaban ambassador Ibrahim.wannan documents din files ne na accounts din Banks Dina sannan dasauran company dina tun last week nasa alkali naseer  yarabamin komi kashi biyu kashi dayada rabi goes to NASREEN while sauran rabin kuma na YAZEED ne saboda haka wanann document din Komi naciki na NASREEN ne Wanda ta gada na wajen mahaifiyarta dakuma Wanda ta gada nawa.wanann secret dinane tsakanina dakai kada kabawa kowa labarin wannan maganar damukai dakai not even NASREEN harse ranar aurenta .sannan sauran dukiya ta gaba daya naturata children fund dakuma orphanage sauran kuma nasa agina masallatai dakuma rijiyoyi.

Ambassador khaleel yakarba file din tareda xuge brief case din yasa aciki insha Allah xanyi yadda kace Allah kuma yabani damar cika wannan alkawari naka.sannan yace toh kuma NOBLE MEDICAL CENTER fa??ceo yace wannan tunda medical center ne incomes din daxa’asamu se aringa biyan ma’aikata dashi sannan kuma sauran profits din nasune kawai su biyu daga NASREEN SE YAZEED.da nayi niyyar sayardashi ko nai constructing dinsa namaidashi plaza hka senafasa ganin yadda marasa lapia sukai yawa ga kuma shine yafi sanuwa agarin abuja.hakade suka danyi hirarsu sanann CEO yaiwa ambassador sallama tareda doriyar yarike masa NASREEN amana .ambassdor khaleel yai murmushi toh naji insha Allah sekace mebada Wasiyya?ceo yace kasani ko ita nake bayarwa.ambassador yace toh insha Allah Ma ba ita kake bayarwa.ahakade har mota ambassador yaraka CEO sanann yamasu sallama yakoma ciki.

Sannan FAREED yaja mota se Abuja capital territory..bayan sun tsaya akaduna sunyi sallah sannan suka wuce abuja sunkasa shiga abuja ko ince sunshigama tunda sunkusa Zuma Rock wani me mota yafigo da gudu ga kuma me trailer a gefe shima yataho..CEO yakalli FAREED yace gyara masa yawuce muba sauri mukeba.matsawar da FAREED yai kenan trailer dinnan ta tafi da motar su FAREED tadaki wata bishiya wadda takaryo tafado kan motar tasu…….

                    •

Nan me trailer yai parking sannan ya fito ,nan mutane aka tafi wurin motar dakyar aka daga bishi yar danceto ransu anyi sa’a CEO da sauran ransa amma FAREED glass ya sokeshi ta wuya atake alokacin yace ga garinku nan.nande akai sa’a aka Kira ambulance akakaisu wani nearest asibiti kan tabbatar da FAREED rasuwayai ko dogon sumane?

Anci sa’a kowanne wayarsa ba code cikin mintina aka Kira YAZEED,NASREEN dakuma President Jameel awaya Wanda yaxo da matarsa dakuma HANAN.cikin mintinan da basukai arbain ba kowannensu yaxo dayake ba agaya masu kome akecikiba andesheda masu yin hatsarinde kawai.bayan ankarasa dasu asibitin kowannensu aka shigar dashi consulting room danganin me akeciki DR NAYRA dr din dake consulting FAREED dakuma CEO tafito Tana cire handgloves dinta Wanda YAZEED dake gefe yanata Allah Yasa mahaifinsa yarasu,dasauri suka karasa wajenta Doctor ya akeciki takallesu tareda doriyar tambayar suwaye iyayen Matashin ciki(FAREED)?presidnt Jameel yamatso gaba yana nuna kansa muryarsa se rawa take ni ni ne mahaifinsa,tagirgixa kanta kuyi hakuri Allah dayafi ku sansa yakarba abinsa sakamakon glass din dayacaki jijiyar wuyansa Wanda take inducing jini ta kwakwalwa Wanda yai relating to internal bleeding bata karasa fadaba suka jiyo shesshekar kukan HANAN dama nasani shysa Yaya yaketa Neman yafiyarmu yaketa acting strange Ashe Ashe sallama yake damu?kowa nagurin seda zuciarsa ta koka idanunwansu suka kawo ruwa..mahaifiyarsa kwa kasa tsayawa tai tafita waje tana nata kukan Banda president Jameel dake kukan zuci idanuwansa sunyi ja..

STORY CONTINUES BELOW

YAZEED dayaga kukan bana Kare bane yakalli dr nayra shikuma Dayan fa shima yamutu ko NASREEN taimai wani kallo sannan ta juya takalli dr nayra and the other patient ?dr nayra tace yes about the other patient shi ansamu da ransa sede he’s critically ill I mean situation dinsa is far beyond .da de da babban asibiti da kunkaishi beside kinga seda mukasamai oxygen yabugu sannan kuma ga karaya na backbone dinsa..NASREEN tasaki Wata Kara tareda Jan kukanta ga FAREED dinta yarasu ga kuma babanta rai a hannun Allah dama kuma mahaifiyarta tarasu komawatai gefe Tana kuka kowannensu Banda YAZEED kuka yake ba Wanda kebama wani hakuri..adole YAZEED yasa aka Kira ambulance akasaka mahaifinsu aciki domin maida shi can NOBLE MEDICAL CENTER .sannan akasaka gawar FAREED a mota aka nufi dashi can gidansu inda xa’a sallaceshi akaishi makwancinsa.

Ana xuwa a gurguje a kakai CEO vvip gurine na musamman na masu kudi ballantana shi da asibitin nasane (very very important person).likitoci faal akansa sannan aka samai oxygen tareda rufe kofar ,a kabar YAZEED dakuma NASREEN dake gefe Tana ta faman Rusa kuka,shikuma YAZEED na gefe yanata faman danna waya,NASREEN tadago ta kalleshi are you happy now mahaifin ka a gadon asibiti kwance gashinan kamar gawa amma ba abinda yashafeka sema danna waya dakakeyi? YAZEED yakalleta tareda watsa mata mummunan kallo ke Ina wasa dake kokuma renin dakikema ma’aikata har yaxo kaina yasaki Wata Daria idan har wanann abin yasa hannu tareda nuna mahaifinsu dake kwance ,idan har ya mutu Wlhy ki kuka da rayuwarki saboda xata xama cikin kunci dakuma danasani mark my words sannan yasakai yafice adakin,yabar NASREEN Tana hawaye lalle Dan uba bashida Kyau Allah kashiga tsakanin nagari da mugu Akan kudi jininka keneman lalata maka rayuwa yasaka ahalin nashiga uku NASREEN tadaga hannu sama Tana addua Ya Allah kashiga tsakanin nagari da mugu kaimin katangar karfe tsakanina da wannan Bawa naka kakawomin dauki ya Allah kakawomin Wanda ze fidda ni DAGA halin da wanann Bawa naka kesan jefani.sannan takare da neman lapiar mahaifinta Dama sauran marassa lapia.

EFAB ESTATE :

  mamee tace yanxu SAMEER har kaje Anya kuwa kunma gaysa da suhaylan?sameer yai murmushi wallhy mamee mungaysa sedah nadanyi hira Ma da ita har take cewa wai jibi xamuje wani asibiti datake aiki wani wai NOBLE MEDICAL CENTER suna Neman qualified surgeons tace wani dr hammadi daya sama ma mata shixe samamin.mamee tace ehh dr hammadi fa ,Wanda yaban aiki ogan suhaylan ne ai,Yawwa dakace NOBLE MEDICAL CENTER Seka tunamin Ma ni muna tare da dr hammadin yana bamu aiki aka kirasa awaya wai CEO din nasu na asibitin yayi accident shida wani Dan babban ma’aikaci shima shareholder ne a company din wai sunyi accident shi yaran atake awajen yarasu shikuma CEO din yana can asibitin a kwance ance critically bashida lapia.DR SAMEER AMEER yace Allah yabashi lapia shikuma Allah yajikanshi.

BAYAN KWANA BIYU:

  Dr hammadi yagama ganin qualifications din sannan ya aje agefe.tareda kallon suhayla I hope his well qualified..suhayla tace eh sosai Ma.sanann ya juya ya kalli DR SAMEER AMEER tareda doriyar Ina fatan xakai mana aiki tsakani da Allah kaga munada karancin surgeons kusan Ma mu uku ne kawai manyan surgeons anan asibitin ,DR SAMEER AMEER yace insha Allah kuma akwai sauran friends dinama suma duk sun kware a surgery in Ana bukata se in kawosu.dr hammadi yace ba matsala su nawane ?DR SAMEER AMEER yadanyi shiru Anya kuwa yai including kabeer kodayake nawa rayuwar takema?sannan yace su uku ne..DR hammadi yace to kakawosu by next week se su fara kaikuma gobe insha Allah sekazo kafara aiki.congratulations DR SAMEER AMEER kaxama qualified surgeon a NOBLE MEDICAL CENTER.

Godia DR SAMEER AMEER yaiwa dr hammadi sannan ya futo yana jiran aunty suhayla abakin kofa,BAYAN yan mintina kadan itama tafito tana murmushi tareda kallon DR SAMEER AMEER,Alhamdulillah mungodewa Allah .DR SAMEER yace Allah shine abin godia kuma dole nagode maki aunt suhayla hakika kincancanki godia tundaga karatuna gashi har xanfara aiki nagode Allah yasaka da alkairi.aunt suhayla tadan harareshi da wasa kaide kafiya magana abeg shut up kagodewa Allah kawai.Allah shine abin godia .sannan suka nufi surrounding din asibitin Tana nuna masa yadda abubuwa suke.

Se karfe kusan 9 nadare sannan yakoma gidah tired and exhausted yai sallama tareda xubewa Akan kujera Wlhy mamee nagaji,NEELAM tarunga Daria Tunkan kafara aikin lalle Yaya .mamee tace toh kuma ya akai?DR SAMEER yakwashe duk yadda sukai sannan yafadawa mamee,mamee tasanya albarka sannan takawomai abinci yafaraci harya gama sannan yakoma yakwanta Akan kujera yana kallon NEELAM daketa faman yin game a iPad dinta,NEELAM anmaki dialysis dinki nayau kuwa?? NEELAM tace eh mana tunda safe Ma daxu muka dawo Ma ai.sannnan yakalla mamee dake yanke farce agefe mamee yaushe xa’aiwa NEELAM dashen kodarta?mamee tace nanda Wata 3 yarage ai.DR SAMEER AMEER yatashi DAGA kwanciyar dayake 3months wai,Allah yakawo yadda xa’ai kafin nan.sanann mamee kifadawa friends dinki sena fara home calls (likitan da ake Kira gida)tahaka xami iya saving cikon kudin .mamee tace insha Allah .

Washegari da sassafe DR SAMEER AMEER yashirya cikin English wears jar Riga polo da kuma Wando baki jeans skinny amma bekama Ma.ya bulbula turarensa tareda body spray futowayai parlor yana kallon agogo zaune su mamee suke da  alama shi suke jira ,mamee Ina kwana ?sannan yaja kujera ya xauna NEELAM dake cusa doya abakinta tai saurin hadiyewa Yaya Ina kwana ?lapia qalau baby sis ya jikinki?dasauki Yaya inajin sauki..agurguje suka gama breakfast din sannan kowannensu yahau cab bayan mamee tasamusu albarka.

Dasauri yashiga cikin asibitin yammata se kallonsa suma nurses mata marassa aure ba abarsu abayaba Dan yayi Kyau ba karya cikin English wears dinshi ga gashin Kansa ya kwanta luf barinma cyboc dinsa kamar wani balarabe,da sallama yabude office din Dr hammadi sannan yasakai yashiga.bayan sungaysa dr hammadi sannan hammadi yadago Kansa yana kallon DR SAMEER AMEER Yawwa SAMEER ko?dr SAMEER yadaga Kansa ehh nine..dr hammadi yace toh sameer dawuri xakaringa xuwa gaskia kaga yau kadanyi late and duk mexuwa late anacire wani amount acikin salary dinsa.karfe 7 yamaka anan xaka cike entrance mode Dinka sannan in kaxo fita Ma haka.+

Sannan babu xuwa wani bangaren sede innine nake round a wards kuma in har nanemeka kenan yazamana kullum kana surgical ward kagane ko?DR SAMEER AMEER yace nagane Doctor insha Allah baxanyi abinda kace karnayiba.dr hammadi yace Yawwa for now baxamu Baka office ba harse kacika 2weeks munga yanayin skills Dinka for now xamu barka a combine consulting room Wanda yakecin doctors kamar 4_5 haka .idan har kacinye duk exams din damuka gwada akanka toh xamu Baka office din kanka.DR SAMEER AMEER yace insha Allah.

Dr hammadi yabude baki xesake magana landline din dake office din tayi ringing,dauka yai kome akace masa oho yace toh ganinan sanann yamike tareda daukar Wata jaka agefensa bayan yadanyi dube dubensa sannan yace DR SAMEER Ina xuwa take care of my office yanxu xandawo duk Wanda yaxo kace naje round NA wards sanann yafice bejira cewar dr SAMEER ba.

Dr hammadi na futa yanata juyawa baya kowani yagansa sannan yanufi Wata kofa tare budewa a ahankali sanann ya shiga YAZEED ne xaune akujera se juyi yake da ita sannan wani danaji dr hammadi yagaysar da dr lawwali.sanann dr hammadi ya kwashi gaysuwa wajen YAZEED .both dr hammadi da dr lawwali kamewa sukai a tsaye danko duk basusan meke tafe da YAZEED ba,seda YAZEED yagama Shan yoghurt dinsa sanan yai jifa da roban tareda mikewa DAGA kan Kujeran yana zagaye office din.dr lawwali murya na rawa yake tambayan YAZEED sir da akwai matsala ne?

YAZEED yaja tsaki nikwa nakeda matsala kunsan cewa nine nan nasama maku aiki a medical center dinnan ko?dr hammadi yace kwarai kuwa kaine nan sir.yazeed yace toh gashi nima naxo da nawa favour din inason acikamin shi..dr hammadi yace komeye shi insha Allah baxefi karfin muba.yazeed yai murmushi tareda dafa kafadar dr hammadi,wannan maganr dakai bahar zuci take ba hammadi.well tinda kun amsa.bawani Abu bane inasan kwiwa CEO anesthesia guda 5 ajijiyoyinsa amma kafinnan kutabbatr da ambashi maganin atarax da Valium kafin kuyi masa.

Muryar dr lawwali Tana rawa yafara magana sir anesthesia kuda biyar kuma ajijiya?sir kasheshi fa kenan xamuyi sannan wannan magungunan daka fada ba ahadasu da anesthesia because tsinka hanji suke Wanda xeyi relating to internal bleeding sannan kidney din xeyi damage baxata iya excreting fitar da blood dinba..YAZEED yai murmushin kyashi kaga bahaushe amma Baka iya Hausa ba abinda nake nufi umarni nakebaku ai ba wai tambayar ku nakeba,inaso yai mutuwan dabaxa a zargi kowa ba.yanxu abinda nakeso kukaishi OR(operating room)sannan kwi abinda nasaku yanxu xanje gidah ni idan yacika seku Kira NASREEN kufada mata .nikuma xamu xo da ita alokacin kaga bawanda xe xargi wani abu kenan.yanxu kuje ku Kai shi OR din nikuma xanhada Dan meeting da kowa na asibitin kan wani ward daxa’abude kaga hankalin kowa bayagurinku kenan.kungane? Atsorace suka DAGA kansu sannan suka fice xuwa dakin da CEO yake kwance yake peacefully yana baccinsa ahankali dukkoda oxygen din dake bakinsa.

STORY CONTINUES BELOW

Seda suka Bari YAZEED yakira meeting sannan suka fita da CEO xuwa OR din ,kamar yadda YAZEED yafada haka suka aikata .dukkoda tarin tsoron dake zuciarsu.amma zunzurutun kudin dayai masu alkawari shiyasasu fitar daduk wani tsoro dake zuciarsu sannan suka daukeshi suka maidashi dakin dayake.bayan YAZEED yagama meeting dinsa yakoma gidah da wajen 1hr sannan dr lawwali yakira NASREEN kan taxo asibiti suna nemanta.lokacin da dr hammadi yakoma office yatarar da dr sameer yana karanta wani littafi na yadda ake operation na bladder,sannu sameer nabarka Kai kadai ,DR SAMEER yai murmushin dake karawa duk me kallonsa sansa,babu komai Doctor ai karatu Ma nake,dr  hammadi yace toh xanje round sekaxo mutafi .kasan dama xaka dinga xama anan office din nawa saboda aiki biyu nahada agabana ga ministry ga nankuma.hakade suka fita suna yan hira har sukaje dakin da CEO yake.kwance yake daka gansa kamar ka tasheshi yamike amma babu rai ajikinsa.

Suna shiga ciki NASREEN tai banging kofar tashigo Tana kallon dr hammadi Gani ya akai?dr hammadi yadan kalli dr lawwali ma’anar yai mata bayani dr lawwali yadanyi gyaran murya lokacin YAZEED yashigo tareda bude kofa yes dr hammadi naga kiranka meya faru?dr lawwali yace muna Baku hakurin abinda xamu fada Allah yayiwa mahaifinku alhaji Muhammad mahmud rasuwa awa daya dasuka wuce..bekarasa fada ba NASREEN tasaki Kara tareda faduwa akasa tabuga kanta da jikin karfen gadon tasulale sumamma awajen.YAZEED yasaki tsaki yabude baki xeyi magana dr hammadi yai gyaran murya da yana masa nuni da DR SAMEER AMEER.dasauri YAZEED yagano sanann yakalli dr SAMEER Wanda yatsaya yana kallon ikon Allah.dr hammadi yace DR SAMEER AMEER Dan Allah kaida nurse AFRAH kukai NASREEN wancan dakin Kai treating dinta wannan shine first examination Dinka..DR SAMEER AMEER yai saurin DAGA Kansa sanann nurses suka dau NASREEN suka sata agado tareda kaita wani special room shima na vvip..

DR SAMEER AMEER duk ya rude kan wani patient tasa,haka kawai yaji yana Jin tausayinta,ahankali yai treating inda tabuge akanta sanann yasa bandage yalike wurin bayan yamata Allura har sau biyu a hannunta.itade nurse AFRAH tsayawa tai Tana kallon ikon Allah yadda sabon surgeon din ya rude kamar kanwarsa ,sakin tsaki tai ahankali sannan tafice,tsayawa yai yana kallon NASREEN din ahankali tunda yake betavajin yadda yake jiba yanxu ba.wani bangare na xuciarsa kuwa raya masa yake kode SO ne?take ya girgixa kansa wanann ba SO  bane tausayine kawai.

Har karfe 9 dare SAMEER bekoma gidah ba ,mamee da NEELAM nata jiransa Dan basu iyacin dinner ko breakfast se dukknsu nanan.mamee takalli agogo karfe Tara har da minti 5 takalli NEELAM wadda ta takure waje daya da alama ciwon cikinne yatashi dama tunsafe take shiga tai fitsari yafi a kirga.mamee tace NEELAM cikinne ke ciwo ne?dasauri NEELAM tadaga kanta saboda ita kadai tasan azabar da gefen cikinnta keyi..ahankali tace mamee gefen cikinane ke ciwo dama tin asuba nake fitsari yellow kuma me xafi.

Mamee tace sannu yi hakuri insha Allah da safe xamuje asibitin.kinsha de maganin nanko??neelam tace mamee nasha nafara Jin normal damu duk weeks dinnan haka yakemin.mamee tace toh Allah yakara sauki barinkira SAMEER lapia najishi shiru haka?sannan mamee tadau wayarta takira SAMEER ringing biyu yadauka.slm/alykm SAMEER lapia najika shiru haka bekamata ace first day Dinka yaxama haka ba’ai ko ha NEELAM Ma ciwon ta yadawo yanxunnan kagantacan ba lapia a kwance dukdade dasauki jikin.toh shikenan seka karaso.

NOBLE MEDICAL CENTER:

DR SAMEER AMEER yana gama amsa wayan mamee yamike yana kallon fuskar kyakkyawar budurwar dabe San sunan tabama.kwance take Tana numfashinta ahankali dukda de bata farfado ba.yinsa yinsa kawai take ,damuwar hakan ta bayyana karara a fuskarsa,ganin yadda lokaci daya ta yanke tafadi haka da alama tension dama yanadaminta amma beka mata ace farar daya tashiga wannan yanayinba.to Ma wacece wannan din?

Gyara mata blanket din da aka lullbeta yai sannan ya rage sanyin air conditioner din dakin tareda kallon nurse AFRAH data xubamai Ido sekace mayya,dakyar yadaure yace kikula da ita please nixan wuce gidah ana nemana bejira cewarta yafice yanata sauri Jin cewar NEELAM ba lapia.yana fita yatsare cab ya wuce gidah.gudu gudu yahau stairs din tareda kwnkwasa kofar mamee taxo ta budemai.murmushi yai ganin mamee ce da sallama yashiga ganin NEELAM yai durkeshe jikin kujera da alama tanajin jiki.karasawa yai gurinta baby sis jikinne?neelam wadda tadan fara bacci tadago takalleshi Yaya seyanxu kadawo?DR SAMEER AMEER yace Wlhy yanxu nadawo baby sis wani abin ne yatsareni yajikin naki fadamin yakikeji..

NEELAM tace da sauki fa Yaya,kawai de da cikina ne yake ciwo to yanxu gefen cikinane yake ciwo har kashin bayana ta gefe sannan bowel(fitsari)Dina Ma yellow ne gashi me zafi nake yinsa.shikenan kawai,DR SAMEER AMEER yai murmushi NEELAM bakyajin magana sau nawa inace maki bakowane abinci xakiciba nafada miki duk me ciwon kidney kowane Iri ne ba’ason patient yadinga cin abinci kowanne Iri,amma bakyaji yanxu keda xa’ama kidney transplant(dashen koda)nanda 3month meye na xuwa kici wani abu yanxu gashi daga yadda kika fada Kidney stone yanxu kika jama kanki yanxu .kince kinci abinci me infection ko ince Ma food poisoning wannan fitsarin mexafi da ciwon gefen ciki duk symptoms dinsane you are even lucky da aka gane da wuri Ma da bansan yaxa’ai ba.

Mamee takalli NEELAM wadda tai tsuru tsuru da idanuwa tasan tabbas ita tatashi taci danwake da mai da yaji harda lemu irin Wanda ake hadawanann kuma na road side,sau nawa Inace maki kidena wasa da lapiar ki NEELAM bakowane abinci me ciwon kidney yake civa,yanxu gashinan bayan weekly dialysis da ake maki gashi xa’amaki kidney transplant ga kidney stone duk ke kadai de dubi yadda kika xama yau daya jiyadda kika rame Idonki yashige ciki,Allah de yasawwake.ameen SAMEER yace sannan yamike yashiga daki tareda dakko Wata jaka cike da magunguna da allurori.daukar Allurai har biyu yai sannan yahada yaiwa NEELAM duka a jijiyoyin hannunta sannan yabata magunguna Tasha bayan anhada mata qoaker oats tasha.daki mamee takaita ta kwantar da ita Dan maganin bacci yake sawa.

Mamee takalli SAMEER daya dafe haba yana cin abinci da alama kuma tunani yake,mamee tace SAMEER meyafarune yau a aasibitin naga kamar kanacikin damuwa,SAMEER yadan kurbi ruwa sannan yace mamee Wlhy patient Dina nake tunani naga kamar bugu war datai bekamata ace tashiga doguwar suma haka even though Tana numfashi amma hardly yake futa sannan kwata kwata batako motsi.mamee tace toh Allah yabata lapia amma ya akai ta bugun?DR SAMEER AMEER yace Wlhy mamee nide munfita da dr hammadi xuwa wani dakin patient da yarasu toh inaganide baban yarinyar ne toh da fadin hakan shine tai wannan faduwar sanann akwai Wanda sukaxo tare Ina tunanin Dan uwanta ne I think akwai wani Abu a tsakaninsu Dan kwata kwata bexo yaduba jikin yarinyarba harna Baro dakin bawani nata dayaxo.mamee tace toh Allah ya kyauta rayuwar yanxu ai se ahankali kowa da abinda yadameshi may be major stress ne ke damunta ko tanada aure ko ya’ya!mamee nafadin haka gaban DR SAMEER AMEER yafadi insha Allah Bama tada aure da yardar Allah.ahaka badan ya koshiba sedan abinda mamee Tafada yaji wani makokon tarin bakin ciki ya tsaya masa a wuya amma koma wacece insha Allah xegano awajen NURSE AFRAH.

KANO:

Alhaji AMEER IDRIS da abokinsa alhaji hamman Bala xaune suke agidan na alhaji AMEER bakomai cikinsa setarin kura da datti kamar badan Adam ne acikin gidan ba.hawaye ne fal cikin idon alhaji AMEER(mahaifin DR SAMEER AMEER)sannan yaxaro handkerchief cikin alhajihunsa sannan yagoge hawayensa tareda sa tissue ya goge majinar data gangaro masa!+

Alhaji hamman Bala yataso yadawo gefensa tabbas AMEER kayi kuskure kuma nasha Gaya maka babu wani abu waishi FARAR KAFA!babu shi,Allah shi kadai ke bayarwa shike hanawa,shike rayawa kuma shike kashewa,shine me daukar Wanda yafi kowa talauci kuma yamaidashi me arziki.sannan shike maida me arxiki yaxama talaka.amma bakaga ganewa yau Dan kawayi gari wani kaso daga cikin arxikinka babu shi bekamata kadau butulci Kadora akan matarka ba amatsayin wai Tana da FARAR KAFA ba.superstition(camfi) ne kawai Wanda mu hausawa mukadauka kuma muka yadda dashi kuma kasan aksari abinda mutane sukai believing yakan xama gaskia.

Saboda haka inaso kasan Hajia zuhra(mahaifiyar DR SAMEER AMEER DA NEELAM)batada wani Abu wai FARAR KAFA Kai babu macen dake da haka adunia,sede ga Wanda yai believing.inaso Kai disbelieving hakan ka fawwalawa ALLAH al’amuranka ,Alhaji AMEER yashare hawayen dake gangarowa a fuskarsa wallahy na yadda nakuma San rashin fawwalawa Allah al’amurana shiya janyomin xargin danaiwa matata zuhra wadda tadauki ragamar So da SHAKUWA tadoramin takuma yadda dani tabar kasarsu tabiyoni ni yanxu abinda yafi damuna matata zuhra dakuma ya’yana SAMEER DA NEELAM.bansan awane hali suke cikiba abinda yafi damuna ma Wlhy rashin lapiar NEELAM ce.yanxu ko anmanta kidney transplant din Allah kadai yasani,Alhaji AMEER yasake goge hawayen dake gangaromai Wlhy sonake ingansu innemi yafiyarsu.alhaji hammani yace to tunda kayi amending mistakes Dinka kagane kaine kajanyo wanka halin dakake ciki.sede inaso kafin naimaka wani albishir shin tsakaninka da Allah sanda kasaki Hajia zuhra medakinka kanacikin mayene kokuwa lapia qalau Kai sakin?

Alhaji AMEER yai shiru tabbas besha giyar daya Saba shaba se bayan yayi sakin da dadddare hakan tafaru,,dakyar yaseseta Kansa tareda doriyar gaskia Ina cikin hankalina hakan tafaru amma lokacin Ina smoking cigrette ita batacikin Kayan mayen?alhaji hammani yai Daria lalle agaysheka AMEER to kasani hadisi ingancacce shine yanuna cewa da de ace kana cikin mayene kasaki matarka to bata sakuba tunda alokacin hankalin mutum ya gushe amma deyanxu Kai da zuhra matarka maidota dakinka harse tasake wani auren tukunna Kuma idan har mijinta yasaketa saki 3 Wanda shine babu kome sannan batin smoking cigrette wannan kuma bata hunhu yake(lungs)sanann dama ace ba saki 3 bane kuma tayi idda agidanka kafin fitar iddanta xaka iya maidota dakinka..amma kariga kamata saki daidai har 3 sannan tagama fita daga iddah shekaru dayawa dasuka wuce zuhra yanxu bamatarka bace ya’ya de SAMEER da NEELAM sune ya’yanka..muryar Alhaji AMEER narawa yake fadin to ayanxu Ina xangansu inemi yafiyarsu?alhaji hammani yace yanxu kadawo xance Hajia zuhra tarike maka ya’ya tsakani da Allah,kusan guri Daya suke aiki da medakina Habiba amma tafita matsayi Dan zuhra na grade 6 Habiba na grade 4.ya‘ya kuma NEELAM Dinka ss1 inaga shikuma SAMEER yaxama surgeon yanxu yana aiki a wani babban asibiti NOBLE MEDICAL CENTER yaxama DR SAMEER AMEER.abinda yasa tinda banfada maka nagabakayi nadamar abinda ka aikata bane amma tinda yanxu kagane abinda kayi kuma karoki Allah gafara kuma kana neman yafiyar iyalanka idan kashirya gobe semuje can Dan gobe xankoma gidah..godia sosai Alhaji AMEER yaiwa alhaji hammani.

NOBLE MEDICAL CENTER

DR SAMEER naxuwa bayan yayi signing entry yaduba office din dr hammadi arufe Kai tsaye yawuce dakin da kyakkyawar patient dinnan take.harya sa hannu xebude kofar yaji alamin mutane adakin kuma ana magana ahankali.tsayawai yana shawarar yashiga koya tsaya yatsinkayo muryar dr lawwali dakuma dr hammadi sekuma muryar dayaji jiya nawannann mutumin (YAZEED)kasa kunne yai yanaji Dan dama beyadadda dashi ba.

STORY CONTINUES BELOW

YAZEED yai gyaran murya yana kallon dr lawwali Idan baxakuyiba consider yourselves fired,bama kora kawaiba wani abin daban xe iya biyo baya,yanxu abinda nakeso daya daga cikinku yai inducing wannan allurar aciki daxe sata yin bacci har na kusan sati biyu harse angama raban gado kamar yadda aka binne CEO bawanda yasan da hannumu aciki naji elders(manya)na maganar Wanda xexama wakilin baba kuma kasan inhar wannan Tana raye ita xasuba heiress Wanda ni baxanyadda da hakaba.sannan da ace tanada miji ne Ma well da shi xexama wakilin ta acan amma tunda nikadaine jininta nikeda iko da komai nata,inason kumin alkawarin hakan akwai babbar kyauta da karin girma da kowannenku.

DR SAMEER AMEER najin haka seda hawaye suka xubo masa wannan wacce irin rayuwa ce Allah ubangiji yakaremu daga sharrin masu sharri,bejira karajin komi ba jiki a sanyaye yawuce yakoma combine consulting room dinsu yana tunanin mafita shin yamata allurar daxata bata kwarin jiki  ko kuma yatasheta yaji cikakkaken labarinta.

Washegari da sassafe mamee da SAMEER suka tafi Kai NEELAM asibiti Dan condition dinta was beyond worst jikinta yayi xafi sosai NOBLE MEDICAL CENTER suka wuce da ita can DIALYISIS AND KIDNEY TRANSPLANT CENTER.cikin gaggawa doctors suka karbeta akawuce da ita daki dialysis din gaggaawa suka mata sannan Doctor din tafuto Tana kallon mamee da SAMEER sunyi jugum jugum..dasauri SAMEER ya nufi inda take yana tambaya rta Doctor Yaya ana bukatar wani abinne??

Dr fadeelah takallesu taga duk yadda hankalinsu yatashi bakomi its not that worst you need to calm down.yanxu muna bukatar jini amma fa 0+ saboda nanda 3 to 2 weeks mukeso mumata kidney transplants(dashen koda)and yanxu Tana bukatar jini saboda jikinta is weak damuka mata dialysis din..DR SAMEER AMEER yai shiru shi duk abinda yadameshi Ma yadda xa’ai mata dashen kodar gashi bayason yafada Ma mamee tun a Istanbul aka masa checkup Ashe kidney dayane dashi.gashi mamee kidney dinta baxeyi fitting Dana NEELAM ba.

Dr taji shirun yayi yawa tace naji kayi shiru bame 0+ acininku?inbabu munema koda akwai Wanda xeyi donating.dr sameer yace no no that’s not it,bahaka bane kawai inaso insan kidney kaman nata xeyi nawa in siya xami dr tadanyi shiru sannan tace yanakaiwa 1_2million.dr sameer yai nodding Kansa tareda kallon mamee dake hawaye agefe,sanann yanufi inda dr din take adebi nawa 0+ne sannan suka nufi dakin da NEELAM take kwance idonta biyu dukta rame abin tausayi DR SAMEER AMEER yai mata murmushi tareda mata sannu adayan gadon kusada ita ya kwanta sannan akafara dibar jinin nasa ana sawa NEELAM.

Seda dr SAMEER yai bedrest na 1hr sannan yamike yanufi inda mamee take bacci yaga yadan dauketa kuma bayasan yatasheta,surgical ward yanufa office din dr hammadi ,da sallamarsa yashiga office din dr hammadi Wanda ya amsa ahankali sannan yamaida Kansa kan files din dayake cikewa,,dr hammadi yadago ya kalleshi dr SAMEER naje vvip din NASREEN banganka acan ba saboda munyi trusting Dinka nema shysa mukasaka aiki acan.dr SAMEER yai shiru azahirin gaskia besan WACECE NASREEN ba?ohh wannan kyakkyawar dayaji suna maganarta jia itace NASREEN?dr hammadi yace kayi shiru hakan yana nufin kayi hakane kana sane kenan?dasauri dr SAMEER yakada kanka no sir,actually banmasan hakan sunan patient din yakeba shysa.kuma abinda yadan xaunar dani banxo dawuri ba Wlhy munje dialysis center ne nakai little sister dina anmata dialysis kuma sundan debi jinina ankara mata kan nanda 2weeka xa’amata kidney transplant.dr hammadi yai saurin kada Kansa alamar jinjinar tausayi aiban saniba Allah yakara mata lapia.yanxu kajecan dakin NASREEN din akwai allura kawai inducing xakai acikin ruwan dake shiga jikinta Okay??dr SAMEER yace nagane sir sannan yatashi yanufi dakinda NASREEN take.

STORY CONTINUES BELOW

Kamar kullum nurse afrah Tana tareda ita se aika masa da sakon murmushi take,murmushin shima yamayar mata saboda neman hanyar daxesa ta fita waje yake danso yake yacanxa alluran da akace yama NASREEN.dr se yanxu ka iso I have being looking for you..tundaxu asibitinma duk ya isheni bawani dadi dry dashi,,dr sameer yai murmushi kamar kinsan Nima so nake nagama abinda nake naxo naga wannan beautiful face dinnaki,,nan take nurse afrah tafara wani blushing sewani fari take da Ido tadauka dagaske yake..

Dr SAMEER yai Daria azuciarsa ganin yadda take wani gyare gyare ,sanann yakara daurewa yakalleta why not kidanje ANKA YUMMYTREATS kimana reserving waje yanxu xanfito semu danyi having lunch peacefully nankinga bamu kadai bane yafada yanadan mata nuni da NASREEN ke kwance.da sauri afrah takada kanta sannan tafigi jakarta tai waje.dr sameer yai Daria tareda daukar ruwan allurar yaxubar sannan yadakko wani a aljihunsa ya xuba sannan yasaka a drip din dake hannunta.tareda sa hannu ya shafi gefen fuskar NASREEN dake kwance..insha Allah xuwa gobe xaki tashi sekidau revenge dinki akan duk wasu makiyanki but kafinnan senaji labarinki.sannan yafice yana tunanin yadda hakan xe kasance musamman da yalura yarinyar tanada dan girman Kai haka.

Yanaxuwa YUMMYTREATS din yatarar har nurse afrah tamasu reserving guri se sakon murmushi take aika Mai ,kujera yaja yaxauna tareda kallon menu din sannan yakalleta mexa akawo maki beautiful??nanfa afrah tasake rudewa tareda rage murya duk abinda handsome xeci shi xanci,DR SAMEER AMEER yai murmushi Wanda kyakkyawar hushiryarsa ta bayyana perfect couple kenan sannan yai ticking frozen yoghurt dakuma vanilla cake..

Seda suka danyi hira sannan dr sameer yace beautiful nikwa wannan patient din wacece ne??afrah tabata rai meyasa kake tambayana ita?sameer yai saurin katseta no don’t think negatively dear kawai inajin tausayinta ne Tana kama da Wata late sister na.afrah tace Allah sarki Allah ya jiknta,NASREEN itace heiress din noble group gaba daya sannan kuma majority na share din company din,itakadai ce wajen babanta CEO kenan sannan Yaxeed half brother dintane babansu daya dashi that’s all. Sameer yace no beautiful bakide karasaba nidake yanxu fa tube nd tyre ne baki ganin kamar akwai wani Abu a tsakanin NASREEN dashi YAZEED din?afrah tai saurin kada kanta Dan dr hammadi yamata warning kanhaka.no I knw nothing beside abinda nafada maka..sameer yace toh shikenan ganin a tsorace take kuma yasan tasan komai..seda sukagama cin komai sannan sameer yamike yana duba agogo okay see you later beautiful xanje inada patient a dialysis center bejira tayi magana ba yatafi wurinsu NEELAM danganin yajikinta.

Wadanda yagani a corridor din daxe sadaka da dialysis center sune suka tsaidamai da duk wani tunaninsa dukkoda sudin basu lura dashi ba suna magana tabbas mahaifinsa ne daya haifeshi dakuma aminin mahaifinsa wato alhaji hamman Bala sekuma mahaifinsa Alhaji AMEER.kotakansu bebiba saboda yadda xuciarsa ke azazzala yawuce dakin da NEELAM take ga mamee a tsaye Tana hada mata tea. Sameer yaja kujera ya zauna tareda dafe Kansa.why ?mesa muna rayuwar mu peacefully kaxo xaka Kara messing family dinmu off ,this is so not fair .mamee data gaji da bambamin masifar SAMEER,Dan Allah ya Isa kanata magana Kai kadai meya faru wai?waye xebata maku family ?sameer yadago idonsa dasuka kada sukai ja lokaci daya mamee waye kuwa Banda so called mahaifinmu,tass mamee tamari SAMEER yadafe kuncinsa da lokaci daya yafara mai ciwo,,,are you out of your senses SAMEER?mahaifin naka kaka fadin wannan maganganun akansa harda wani so called wato be Makai matsayin kakirashi mahaifi fi bakenan,

To Bari kaji ingaya maka iyaye ba abin raini bane akowane mataki kakai arayuwa,bakaji Hausawa Ma nafadin Wanda yarasa mafadi abin tausayibane,you are even lucky dakakedah both parent araye.ai hannunka baxe rubeba kace xaka yanke kayar.ballantana mahaifinka Wanda shine sanadin kawoka dunia,to kasani niba irin iyayen nan bace wa’enda suke barin yaransu suna raina nagaba dasu.babu ruwana karna sake jin wannan maganganun abakinka Ina abban naku yake yanxu?bata Ida fadaba Alhaji AMEER da alhaji hammani suka shigo.murmushinta yafadada na fuskarta sannan TA mike tana gyara mayafinta kamar babu wani Abu wai fada dayashiga tsakaninsu sannanku daxuwa alhaji Kai SAMEER tashi kabasu waje ,yanxu kwa NEELAM din tasamu bacci batasan abbanta xexoba..sakin baki da hanci Alhaji AMEER yai yana kallon Hajia zuhra wadda yagata canxa tayi Kyau kamar ba ita bace xuhransa ada.

Dakyar SAMEER yagayshesu sannan alhaji hammani yace yatashi yabasu waje..alhaji hammani yakalli hajia zuhra wadda tadakko ruwa ta ajiye musu agabnsu.tabbas Hajia kinmatukar bamu mamaki tayadda kika karbemu baki nuna komaiba dukkoda tundaxu muke jiran yadda xamu shigo mufuskanceku.

Hajia zuhra tai murmushi bakomai alhaji ,ai fadar manxo SAW cewa idan dayanku yadakko dutse yajefeku to ku dau fura ku rama da ita.ma‘ana ai fura ba sharp object bace kuma babu abinda xatai na karje mutum ko illatashi bama xata kaiga mutumin dakakesan ramawa ba xata farfashe tafadi akasa..kuma fadinsa ne cewa kuyi hakuri aduk abinda aka maku domin Allah yanasan masu hakuri.alhaji hammani yace kwarai dagaske toh Allah yayafemu gaba daya .yanxu de ga Alhaji AMEER yana Neman yafiyarku..Hajia zuhra tace nide kam nayafe bansan SAMEER ko NEELAM Ma amma suma dole xasu yafe masa saboda mahaifinsune amma yaxama dole muji tabakinsu tukun.

Alhaji AMEER ya kalli NEELAM dake bacci ahankali daka ganta kasan tanajin jiki,hawayene suka kawo ruwa a fuskarsa take yaji wani tausayi na yar’ tasa yakamasa ahankali yamike yanufi inda take yana gyara gashin kanta daya rufe mata Ido  sannan yajanyo hular kanta datai baya yana gyarawa Allah yakara sauki NEELAM.yakalli Hajia zuhra data kasa hada Ido dashi Sannan yadora da Yaya jikin nata dialysis din aka mata ne??hajia zuhra tace ehh Tana kokarin maida hawayen dasuke kokarin xubo mata muryarta narawa tace ehh  ammata dialysis din jira muke Doctor din taxo TA sallamemu nanda 3weeks xasu mata kidney transplant din.

Alhaji AMEER yai hammadalah da Allah yasa yana raye xa’amata dashen kodar.sannan yakoma wajen xamansa yaxauna ,inda massengers na asibitin suke TA shigo da Kayan dubia Wanda su Alhaji AMEER da alhaji hammadi sukashigo dashi inda Hajia zuhra tai godia daga bisani kuma tamike tabar dakin tafice waje.tana fita alhaji hammani yakalli Alhaji AMEER Wanda ke hawaye,sannan ya tausasa muryasa haba AMEER ba kuka yakamata kaiba,atleast you shd be happy Ma ai at long last kaga family Dinka Wanda kaskntar da kanka yakamata kayi kanemi gafara awajensu amma bakaita kukan da ba abinda xejanyo maka ba se ciwon kai kuma kasan kanada hawan jini (blood pressure)Dan Allah ya Isa haka yanxu mafita daya ce kacire kudi kabiya wa yar’ka NEELAM kudin kidney dinnan asamu amata kidney transplant dinnan.hakade sukai ta xanjensu harde Hajia zuhra tashigo abayanta kuma dr fareedah ce.

Da murmushi a fuskar Hajia zuhra takallesu tace ansallamemu,dr Fareedah tanufi inda NEELAM take sannan tadan duddubata tareda tashinta tamata allura sannan tamaida da takwantar,sannan takalli Hajia zuhra xaku iya tafiya ansallameku nadubata batada matsala Allah ybata lapia ,sannan tadanyi rubutu ajikin takarda tamikawa Hajia zuhra wanann medicine din daza’a siya mata ne akula pls da irin abincinta sannan into weeks time seku dawo xa’ai mata kidney transplant din..Allah yabata lapia sannan tasakai tafice .

ONE HOUR LATER

Har sun isa gidah a motar Alhaji hammani,shiga ciki sukai sannan suka xauna inda Hajia zuhra tadau Waya takira SAMEER kan lalle yanxu yaxo tana nemansa..NEELAM datashi daga bacci alokacin ta tsaya Tana kallon bakuwar fuskar dakamar tasanta dukdade andau shekaru amma ai baxaka Taba mance fuskar mahaifinkaaba..tashi tai dakyar sannan ta kalli mamee ,mamee abba ne wannan?mamee tai murmushi abbankine baby doll tashi kije kigaysheshi kinji?neelam tanoke kafada Noo I dun want to see him again..shakera dayawa bexo wajenmu ba seyanxu after all muna missing dinshi always muna expecting call dinsa nd betaba kiraba sannan ta kalleshi why abba why hatred din har ya Kai haka?

Alhaji AMEER yamike yaxo inda take da nufin yarike ta tai saurin dakatar dashi don’t touch me,,abba don’t.hawaye yafara gangarowa a face dinta lokacin kuma SAMEER yashigo gidan fuskarsa a mirtike yanemi waje yaxauna,NEELAM tacigaba da magana tana hawaye abba you never care how muke samin shelter,schooling da sauransu duk kudin da mamme da Yaya ke samu a dialysis dina suke tafiya,kullum friends dina na tambayata Ina mahaifina?tun mamee nacemin kayi tafiya harna gane korarmu Kai daga gidanmu.and you even have the guts to come right in to our very own house sannan kace kayi amending mistake s Dinka how?sannan tasa hannu a bakinta dakuka yaci karfinta I will never ever for…bata karasaba Alhaji AMEER yarike ta yana kuka sosai Wanda xeba me karatu tausayi.itama Hajia zuhran kuka take har Alhaji hammani dayasa tissue yana gogewa.

Dan Allah SAMEER da NEELAM kayafemin Wlhy nasan nayi maku lefi tabbas wannan shine babban kuskuren Dana tafka arayuwata Wanda Wlhy tallahi idan har Baku yafemin ba narantse da Allah baxan sami rahamar ubangiji ba ballanatana aljannarsa megirma..kuma nasan kuma baxakuso yau nafadi na mutu ba da rashin yafiyar danai muku a kaina.Allah yanasan me yafiya kuma nasan xaku yafemin..

STORY CONTINUES BELOW

Tsakanin uba da ya’ya se Allah Alhaji AMEER betashi akan gwiwoyinsaba harse da ya’yansa SAMEER DA NEELAM suka yafemasa.

Ordering abinci Alhaji AMEER yasa aka masu a hotel duka suna xaune suna ci seda suka gama sannan Alhaji hammani yace ni DR SAMEER AMEER yaushene aurenka ne tunda kana aiki..SAMEER ya Sosa keyarsa baaba inade nema amma bamu dedetaba tukun .neelam tace Yaya wacece yasunanta amma Baka Taba fadaba ko Yaya NAWAL ce?dan naga Tana yawan xuwa gidannan kuma she likes you a lot..dr SAMEER yace sunanta NASREEN wannan ba NAWAL bace.alhaji AMEER yace toh Allah yasanya Alkhairi inkun dedeta kafadamin se aje ayi tambaya DR SAMEER AMEER.sameer yace amin .hakade sukai ta hirarsu kafin Alhaji AMEER da Alhaji hammani suyi masu sallama sutafi kan xasu dawo gobe.

Washegari da safe dr SAMEER AMEER yashirya cikin blazer dinsa Baka,Kayan cikin kuma(shirt)ash color ne sannan yasa covered shoe dinsa kirar hems(H)yasa turarensa medaukar hankali sannan yafita dinning inda sukai breakfast dasu mamee.ranar mamee baxata office ba tadau Hutu saboda rashin lapian NEELAM.shikadai yatafi titi yahau cab sannan yawuce asibiti.

Yana xuwa bayan yacike entry dinsa bebi takan su yaseer dasukafara aiki aranar ba Dan orientation yaga ana masu,wucewa dakin da NASREEN take yai sannan ya kwankwasa yashiga.kwance as usual take ita kadai amma wannan karen idonta a bude yake.karasawa yai yai sallama dakyar idanunsa suka sauka a kan idonta Wanda hawaye ke gangara ahankali wani Kyau yaga takara mai,sannu NASREEN bata iya amsawa ba illa kanta data gyada sannan yatemaka mata tareda jinginar da ita ajikin gadon.

Sannan yamike a hankali yasa key adakin dangudun kar wani yaturo yaganta,dakyar tabude baki muryarta na rawa take magana pls Ina rokanka kasakeyimin allura kamaidani baccin danakeyi tashina dakai bakaramin musiba xejanyo minba harkaidin daka tasheni YAZEED baxe barka hakaba.rayuwata tana cikin hatsari muddin YAZEED yaxo yaganmu ahaka I know right.kafin kajanyo wa kanka pls kasakemin duk abinda su dr hammadi sukamin sannan kabar asibtinnan naga alama bakasan Komi ba akan wannan asibitin.

Shiru DR SAMEER yai yana sauraron abinda take fadi dukkoda yasan abinda take fada gaskiane,ahankali yace meyasa kikace haka ?nasreen tai murmushi kona fada maka baxaka ganeba.yanzu de inasan inyi sallah ,se asannan SAMEER yatuno sannan yatemaka mata tashiga bandaki TA tsaftace jikinta sannan tafuto Tana Tama sallolin da ake binta.DR SAMEER AMEER yatsura mata ido yana kallonta bakaramar kyakkyawa bace gata daga ganinta tanasan addini,murmushi yai ganin yadda yadau keta Bama haka takeba.alhamdulillah Allah yabashi matar daxata kula masa da yara kan tafarkin addinin musulunci.

Tana idar da sallolinta tamike ahankali takoma kan gadonta TA kwanta sannan takalli DR SAMEER AMEER dake faman rubuce rubuce akan takarda ,yana yanayi da marigayi FAREED dinta.dago Kansa yai yaga Tana kallonsa dasauri tajanye idonta akansa ,murmushi yai sanann yamike ya fita,ba ajima ba yadawo da leda ahannunsa abinci ne yasayo mata yatemaka mata tafaraci ahankali sannan yabata ruwa Tasha.ita kanta tasan yunwa takeji sosai,seda takoshi sannan tace masa takoshi.tareda masa godia,ahankali tarufe idonta taname tunano RAYUWARTA wai Dan uwanka jininka shine me neman illata maka rayuwa Akan kudi daxasu Kai mutum su baroshi.sannan tajuyo takalli SAMEER tace Doctor inasan insan meyasa kake temakona dukkoda kasan tarin MATSALAR RAYUWAR daxaka shiga?

DR SAMEER AMEER yace toh sunana SAMEER AMEER,kuma surgeon ne ni anan asibitin,nasamu aiki ne tabangaren nurse suhayla Wanda dr hammadi yaban aiki sannan kuma bawai danwani abin bane yasa natemakeki a’a sedan inaganinki kamar kanwata ne Shysa.

STORY CONTINUES BELOW

  NASREEN tai murmushi Ashe nasamu brother kenan,toh nagode DR SAMEER AMEER.Allah yasaka da alkhairi.nande NASREEN takwashe tarihin rayuwarta kaf tabawa SAMEER labari.daga karshe tace masa Tana Neman Wata alfarma guda 1.

DR SAMEER AMEER yace inajinki kanwata insha Allah Nima kuma xancika maki wannan alfarma taki.

Takalleshi da idanuwanta da sukai ja saboda kuka Doctor inasan katsaya Kai defeating YAZEED,dukkoda nasan shidin yafi karfinka amma kaidin kanada abinda xakai kaci galaba akansa inaso kamin alkawarin xaka AURENI amma bayan angama Komi nadaga case Dina xaka sakeni saboda kaine xaka xama matemakina agurin YAZEED brother na,Yaya kakegani shin ka amince ko kwa?kodayake Kai shawara agidah tukun kar Kai abinda xakaxo kana danasi acikinsa,xabin iyaye shine.sameer yabude baki xeyi magana kenan akafara knocking kofa!!!!

Sunajin anyi knocking NASREEN tai sauri takoma wajen xamnta sannan sameer yamaida mata drip tareda gyara ko Ina sannan ya mike ya bude kofar.fuskar Wanda yagani jikin kofar shiyai matukar tsoratashi,YAZEED ne brother din NASREEN se dr hammadi dake biye dashi abaya.kofa yabude masu sannan suka shigo ciki YAZEED se kallon dakin yake kamar meson yagano abu.

YAZEED ya Matsa dede fuskar NASREEN yana kallonta yana murmushin mugunta,barin daya Taba hancinta yaji ba alamar numfashi besan duk hakan dayake NASREEN naganinsaba,ahankali ya rankwafo kanta hade da gyara bedsheet din,half sister NASREEN nanda kwana biyu xan amshe duk wani kadaranmu sannan xanxama chairman CEO na noble group.dr hammadi senuni yakewa YAZEED NA SAMEER dake gefe amma YAZEED ko ajikinsa ahankali ya tako har inda dr hammadi yake tareda xura hannunsa a rigarsa,inaso kafin dare kaida wannan likitan kucikamin aikina sannan yafice yabar asibitin dr hammadi yamai rakiya.

Sameer naganin dr hammadi yai saurin karasawa kusada NASREEN wadda idonta a rufe amma hawayene ke tsiyaya,bata bude idonta ba tafara magana ahnakli DR SAMEER AMEER,Dan Allah katemaka ka ceto rayuwata cikin matslar daxata shiga,DR SAMEER kasa cewa kome yai shikansa besan yaxeyi ya kubutar da itaba,musamman ma da YAZEED yahadu dashi Ido biyu,kasa cemata komai yai illah hakuri dayabata sannan yafice daga dakin.

Waiting area yanufa yaxauna tareda dafe Kansa dake baraxar fadowa,yaseer yaxo kusa dashi yaxauna DR SAMEER,Ashe kananan tundaxu muke nemnka dude haka wannan asibitin yakeda babes?omo kaga yammata kuwa kala kala Wlhy dakyar nai wani surgery daxu gaba daya Wata nurse tarikitani,DR SAMEER AMEER yai tsaki that’s your own business,I beg of you ,just keep quiet I’m not in the mood.yaseer yamike yana kallonsa I know ,right!naga alama ai Nina koma bakin aiki Allah yahuci xuciar DR SAMEER AMEER.bayan wasu yam mintina dukde dr SAMEER na gurin dafe da Kansa aka mai sallama,dakyar ya amsa don axatonsa yaseer ne yasake xuwa ko kabeer,wai bakai nama warning ba?mutumin dake tsaye yasami waje yaxauna tareda fadin pardon!se asannan dr SAMEER yadago da mamakinsa yaga badaya daga cikinsu bane,murya  a sarke yakeba mutumin hakuri,sannan yamika masa hannu suka gaysa.

Mutumin yadan gyara xamansa tareda Bawa security dinsa dake tsaya akansa minti 5 yadan basu waje,toh nisunana Ambassador Ibrahim khaleel.sanann nan asibitin aminina marigayi mm(Muhammad Mahmoud CEO)Wanda Allah yamasa rasuwa kwanakin baya,inata Neman diyarsa NASREEN nasha wahala kafin aceman aitananan asibitin.dan Allah ko kasan inda take naji ance anan surgical ward take,naga kuma Kai kamar likitane Dan Allah xansamu ganinta.dr SAMEER yai murmushi shi duk aganinsa irin mugayen nanne da YAZEED ke turawa,ahankali yace a’a batasan ganin kowa gaskia,kuma ni banyarda dakaiba,kaje kacewa YAZEED din nahanaka shiga wajenta.sannan yamike xevar wajen ambassador yai saurin rike hannunsa narokeka kobaxa barni nashiga ba kace mata ambassador khaleel ne xanjira anan pls naji amsan daxata bayar.kada kansa SAMEER yai sannan yatafi.

STORY CONTINUES BELOW

Dakin NASREEN yakoma haryanxu Tana hawaye,handkerchief yaxaro yafara goge mata hawayen,haba kanwata kukan ya ISA haka Dan Allah,banasn wanann kukan!yanxu daga waje nake awaiting area na hadu da wani wai ambassador Ibrahim khaleel yace yanasan ganinki nide banyarda dashiba saboda haka nahanashi shi..be karasaba NASREEN TA amshe tareda mikewa Dan Allah kashigo dashi guardian dinane fa,Wanda xe share min kukana.wayeshi dr SAMEER yatambayeta?nasreen tace bamuda lokacin tambaya shigo dashi pls.

Futa dr SAMEER yai sannan yashigo da ambassador ,kamar NASREEN xata cinyeshi Dan murna shima hawayen yakeyi,yatambayeta meyafarune NASREEN naganki anan?nasreen tace it’s a long story uncle,YAZEED soyake yakasheni shine duk yai planing wanann abin.nashiga comma badanda bravery din DR SAMEER AMEER ba,daban Kai yanxu ba….shide SAMEER shiru kawai yai.

Ambassador yakalli SAMEER,Doctor yanxu yaxa’ai mufita da ita?

Idea ce taxowa SAMEER alokacin ,yace ambassador baxeyu nabiku ba dan muddin nabiku dole asan da hannuna aciki amma idan kuka tafi seni kadai ko xa’a xargeni bade sosai ba,ahankali yai dialing number yaseer sedata katse be dauka ba sannan SAMEER yace Yawwa,yanxu akwai emergency exit tabandaki wanda inkuka fita har titi kakira driver Dinka yaxo wajen.nikuma xan kwanta anan a kasa inkun fita xanxama helpless and merciless kaman duka akamin sannan akai kidnapping din NASREEN that’s the logic.ambassdor  yai murmushi I got the logic hakan yayi,sannan yakalli NASREEN good luck kanwata kakki manta nanda kwana biyu YAZEED xexama chairman.xa‘a raba maku gadonku a sharia court yaxama kina wajen dole and kixo da evidence dinki..

Da sauri ambassador da NASREEN sukabi TA exit din suka fice ,DR SAMEER AMEER yai murmushin yake ganin bata ko karba number dinsaba,I guess Dama nikadai nakamu da soyayyarki tunda kin kubuta yanxu de shikenan,Jiyai ana knocking kofar dasauri yakwanta akasan tiles din tareda sharar hawaye kamar Wanda akaiwa dukan tsiya.bugun kofar dr hammadi yake ba kakkautawa dayaji ba abudeba yakira security dasu balla kofar.

Securities ne suka balla kofar sannan dr hammadi yasa Kai yashiga,abunda yagani shiya birkita mai lissafi,DR SAMEER AMEER yagani rashe rashe akasa rai a hannun Allah,karasawa yai ciki ganin yana temakon gaggawa,sanann yakira emergency division nacikin asibitin sukadaukeshi..da sauri dr hammadi yajuya yana kallon  gadon ba kowa akai ,dafe Kansa yai how on earth haka tafaru?sannan yaleka cikin bandaki ganin emergency exit din a kabude shyasashi ja baya ,dagudu yafice yanufi office din dr lawwali.

Sir,ansamu matsala fa,dr lawwali yadago yana kallonsa matslar mekuma?murya na rawa dr hammadi kefadin sir na.nassrr..dr lawwali yasaki tsaki just go straight to the point ,dr hammadi yace sir NASREEN ce andau keta bangantaba,mikewa dr lawwali yai yana kallon dr hammadi ,Ina wannan likitan da akabawa ajiyarta?dr hammadi yace DR SAMEER AMEER sunmasa duka koma suwaye yana emergency unit.

Dr lawwali yace tab to nigaskia babu ruwana Wlhy ,yanzu idan YAZEED yaji maganr nan bansan iya hukuncin daxe daukaba,kaki rashi kasan yadda xakai Kai convincing dinsa ba hannunka aciki Dan baxe yadda ba,murya na rawa dr hammadi yakira YAZEED yasheda masa abinda yafaru,mintina kadan YAZEED yaxo asibitin afirgice gaba daya baya hayyacinsa Dan tsabar rudewa komai seya duba yana kiran sunanta hardasu daga bedsheet,idonsa yakada yai ja lokaci daya yajiyo yakalla dr hammadi dayake atsaye kamar sanda shima daka gansa kasan arude yake,inashi Wanda yake xama tareda ita?dr hammadi yace sunmasa duka akwnce akasa naganshi rai a hannun Allah yana emergency unit yanxu.yaxeed yamike yafice batare da yakara cewa Komi ba.

SAMEER bayan anbashi magani yafaki idonsu ya watsar,sannan ya shirya yace masu shi gida xashi,haka kuwa akai gidah yatafi..yafadawa mamee duk abinda yafaru.mamee tace amma SAMEER kayi Ragon azanci gaskia yanxu da ankama kafa ko aka gane ba abinda aka maka kaikadai kashirya hakan.sameer yace haba mamee aikinane fa babu yadda xasu gane ba ‘amin komiba sannan seda natabbar dr hammadi baya asibitin bayan nan su yaseer suna surgery .shysa na gwada kiran yaseer be daukaba Kinga xa’aduba da Wanda nai Waya last idan har andau mintina to lallle ninashirya abin kenan amma idan har nakira ba’adaukaba yatabbata nakirane axo aceceni.mamee tai Daria to agaisheka,Allah kuma yasaka da alkhairi ,wannan yarinya tanaban tausayi Wlhy..wai Dan uwanka yanemi yakasheka da hannunsa Akan abin Dunia.DR SAMEER AMEER yace Wlhy mamee sekin mata hawaye idan kikaji labarinta.

Mamee tace toh shikwa meyasa ya tsaneta haka ?ba yar uwarsa bace,SAMEER ko de rikonta ake agidan ne nifa abin yadauremin Kai ..DR SAMEER AMEER yace mamee Wlhy ubansu daya dakanta takeban labarin.tace da babansu da mamansu iyayensu Uwa daya uba dayane..ita mahaifiyar YAZEED din ai mutuwatai se babansu ya auri mahaifiyar NASREEN din inda tahaifi NASREEN din itakadai ,shima kuma YAZEED din mahaifiyarsa shikadai TA Haifa,to mamee kinaji se da babansu NASREEN din da mahaifiyar NASREEN din sesuka hada kadararsu wuri daya sukatada NOBLE GROUP OF COMPANIES AND ENTERPRISES.

To mamee acikin YAZEED da NASREEN wakeda largest share idan akaxo gado tinda Komi a rubuce yake dama sunyi Komi a written documentary evidence??mamee tai shiru sannan tadago tace gaskia NASREEN dole tafi share saboda kason mahaifiyarta natane ita kadai sede idan har mahaifiyar Tana da iyaye to suma sunada gado aciki suma idan basunan se kannensu ko yayyensu suma duk sunada gado aciki.komade meye NASREEN itace me largest share na company din,sannan na YAZEED yabiyo baya.

Hakade sukai TA magana har dare yai sannan mamee tanufi daki tai baccinta,shiko DR SAMEER AMEER ba abinda yake inbanda tuno kyakkyawar fuskar NASREEN da murmushinta medaukeda da annushuwa.

••••

Koda NASREEN da ambassdor suka tafi ba gidan su NASREEN suka nufa ba gudun kar abu yaje yadawo,gidansa dake Abuja dayake yanada mata acan can yakai NASREEN taxauna harse ranar da xa’aje court ai Rabon gado.dan jia da share holders suka xauna na company din basuga wani evidence daya nuna cewa YAZEED shine xerike company dinba,haka yahakura yakoma gidah Cike da tashin hankali.

BAYAN SATI DAYA:+

Abubuwa da dama sun faru kamar xaman da akai a company akace YAZEED becancanci zama chairman na Nobel group ba,NASREEN kanwarsa itatafi cancanta,seya daukaka kara inda yakai Supreme Court suma sukace becancantaba.adole yahakura yajira sharia court Dan Jin yadda Abu xekasnce.

Ranar laraba da safe itace ranar da aka aje dangin sharia dakuma raba gado tsakanin YAZEED da NASREEN dubban mutane ne suka xauna Dan sheda haka.su dr hammadi,dr lawwali da nurse afrah da DR SAMEER AMEER duk suna gurin .alkali yafuto yaxauna akan Kujera kiran farko yakira YAZEED Dan masa tambayoyi akan zarginsa da ake na neman kisan kanwarsa,yaxeed yafuto dauke da murmushi afuskarsa ganin ba alamar NASREEN agurin.

Ahankali YAZEED yafuto yatsaya akan stage,sanann lawyer dake Kare kararsa wato barr ibrahim yamike yana magana yame girma meshari’a nine lawyer dake Kare karar zargin da akema YAZEED.sannan Barr lubna itama tamike itace lawyer datake Ke karar YAZEED abisa xarginsa dasuke na Neman kashe kanwarsa NASREEN.bayan YAZEED yagaysheda da alkali ,alkali yafara magana ko xaka iya gayamana hakikanin gaskiya kaika keneman kashe kanwarka NASREEN shin zargin da ake maka hakan yake koko bahaka bane?yaxeed yashake murya yame girma me sharia hakika bani ne nake Neman kashe kanwata ba wannan xargin da ake min kazafine kawai naneman cinma Burinsu akaina..

Alkali yace toh tayaya kenan?yazeed yace toh lokacin da aka sanar mana da mahaifinmu yarasu tare mukaxo da ita asibitin ,Ana sanarmna yarasu tafadi tabige kanta tai doguwar suma Wanda likitocin dake wajen sunshaida haka,,alkali yace ko xan iya ganin su nan aka Kira dr hammadi da dr lawwali harda dr SAMEER.

Haka akaita gwagwarmaya a court din,Barr lubna tamike cikin fushi harda biga bench objection my lord,wannan abinda suka fada bahaka yake ba,alkali yace tafadi dalili nan taxayyano nata da lilin,alkali yai shiru sannan yace yana Neman NASREEN data futo TA baiyani inba hakaba toh YAZEED ne Mai gaskiya ,se wani murmushi yake yana kallon kasa,nan kotu aka dau murna ganin NASREEN tashigo cikin court din da saurinta.tabawa alkali hakuri sannan tafara zayyano bayaninta batabar Komi ba tareda doriyar YAZEED shiya kashe mahaifinsu CEO.kotu tadau surutu ,alkali yace ai shiru,ko xaki fadi su waye evidence dinki Dan kotu TA samu kwakkwarar sheda Akan hakan?DR SAMEER AMEER taiwa nuni da hannu ya fito,nan jikin dr hammadi yai la’asar yasan tabbas kashinsu yau yabushe.

DR SAMEER AMEER yafuto sannan yahau kan abin tsayawa ya tsaya.alkali yace toh amatsayinka na Wanda xebamu kwakkwarar sheda Akan zargin da akema YAZEED da sahannunsa akashe mahaifinsa mexaka iya cewa akai sannan kakka mnta nan court din musulunci ce kafadi tskaninka da Allah.nan DR SAMEER AMEER yai shiru sannan yafara magana ya megirma me Shari’a tabbas da kunnena naji YAZEED yayan NASREEN yana fadawa likitocin mahaifinsa dasu cigaba da xuba allurar da xata sa kanwarsa bacci harna sati biyu harse angama Rabon gado yaxama chairman a company din Nobel group tareda doriyar musu tilas Akan hakan sannan yamasu wasu alkawura masu tsoka da fadin aikin dasukai yayi tunda ba agane da hanunnsu akashe mahaifinsu ba,TA yadda sukai TA masa allurorin anesthesia da kwayoyin ataraxs.

Alkali yai shiru sannan yace yanasan ganin wanann likitocin su fito dr hammadi da dr lawwali suka fito jiki se rawa yake,alkali yatambayesu shin abinda yafada gaskiane ko ko bakayakeva idan bahaka bane toh su fadi akasin hakan,idan kuma hakanne sukai shiru toh su kuka da kansu idan yagano gaskiar al’amari.sukai shawara ajunansu sannan suka fadawa Alkali haka abin yake kuma tilastasu YAZEED dinyayi tareda furucin ba korarsu kadai xeyiba akwai mummunan al’amari daxe faru dasu.alkali yagama rubuce rubucensa sannan yadago Kai yana kallon jama’ar gurin.to wannan kotu me albarka tagama duk wani bincikenta Akan wannan sharia.sannan kamar yadda akasani Rabon gadon wa’innan yan Uwa mahaifinsu yaruga yagama rabashi dakansa inda amintacccrn abokinsa yanuna mna,sannan Abu nabiyu kotu TA wanke NASREEN da xargin da YAZEED yake mata xe biyata tarar kudi Wanda xa’afada nan gaba.

STORY CONTINUES BELOW

Sannan kotu tayankewa YAZEED daurin rai da rai tahanyar rataya bisa kamashi da hannu dumu dumu da akai nakashe mahaifinsa dayai tahanyar rataya kamar yadda yaxo a hadisai dakuma kundun tsarin kasa(constitution)sannan wa’innan likitoci guda biyu tunda bara’ayin kansu sukaiba kudi yabiya dakuma mummunan furucin daya ambata xe masu kotu tayanke musu shekaru 10 dukkansu a gidan kaso (prison)babu Tara(money)sannan kotu na maiwa wanann likita godia bisa jajir cewar dayai yafadi gaskiar al’amari.da wannan muka Kare shari’ar mu tayau na sallameku,nan aka mike gaba daya tare fadin COURT.
          130_135
BAYAN SATI DAYA:
Xaune suke a parlor dukansu ,mamee da NEELAM ,DR SAMEER AMEER dakuma abbansu se abokinsa alhaji hammani.NEELAM tanufi freedge tadakko ice cream Yaya aixan iya shako tinda anmin kidney transplant din?DR SAMEER AMEER yai murmushi lokaci daya yarame yai baki kamar bashi ba.yace NEELAM kibari yai Melting tukun seki sha kamar milkshake yanxu inkasha haka baxeyi digesting dawuri ba xexama stomach upset.
alhaji hammani yace ka iya aikinka son,Allah de yakara budewa i heard anbaka gidah da mota ko naji ance Ankara maka matsayi ma?sameer yace ehh uncle ankaramin Wlhy yanxu nine director incharge of Nobel medical center gaba daya!!alhaji hammani yes that’s very good,keep it up the sky is your limit.aikayi babban Abu Allah yasaka da alkairi ,sede haryanxu kukan kake ne naga kayi baki karame Kai dole se yarinyar nan NASREEN dabata damu dakaiba,anriga anhadaka da Wata sekayi hakuri kuxauna lapiya kaima iyayen ka biyayya.abba yace karma yayi gobe de daurin auren tashi kabamu wuri Allah yasanya alkhairi.
bayan SAMEER yatashi mamee tace nikwa da gayamai gaskia akai ace da NASREEN din xa’daura yarannan yabi yatakura Kansa jibi yadda yarame ko abinci baici shiduk axatonsa nawal xe aura yar suhayla besan ita yarinyar abokinsane xe aureta ba wani kabeer.abba yai murmushi tare xa’afada da NEELAM ai xata auri yaseer abikin SAMEER yaran yadage sekace zaucacce,NEELAM tamike Tana biga kafa Allah mamee ni a’a I’m too small amin aure ynxu beside ko makarnta ban gamaba bafa.sanann tawuce daki ,abba yace ja’ira itamafa Tana sonsa,alhaji hammani yace ku kyaleta kunya ce ai anasan mace me kunya.bakaji hausawa sukace wai kunya adon mace,mamee tace hakane ai annazafatu minal iman.da haka sukai ta hirarsu de TA yada bikin xe kasance.
Rana bata kunya sede uwar diya taji kunya,yaune aka daura auren NASREEN MUHAMMAD MAHMOUD DA DR SAMEER AMEER Akan sadaki dubu 50cif,dubban mutane ne suka sheda hakan,inda aka dunguma aka Kai amarya gidanta dayaji Komi irin na masu farce da susa(rich)yammatan amarya suka watse inda akabar amarya ita kadai,cikin dare DR SAMEER AMEER yashigo da ledojin gado(kaxa da lemo)sanann ya aje agefen gado yasakai xefita bayan yace mata seda safe tunda shide besan kowaceceba Dan da’ake sanar da aurenma toshe kunnuwnsa yake waidan karyaji bakin ciki.
Kamar daga sama yatsinkayo muryar dabaxe taba mantata ba,muryar datake masa zugi akunne tareda dandano a xuciarsa.DR SAMEER AMEER tace masa,a sufane yajiyo yanufi gurinta da sauri tareda yaye mayafin bade gixo kikeman bako?bade na zauce ba?nasreen tai murmushi calm down angon NASREEN ba mafarki kakeba nicede NASREEN naxama amaryar DR SAMEER AMEER.hira sukashiga yi cikin so da kuma shakuwa sannan sukaci kaxa da lemunsu ananne SAMEER yai wanka yai alwala sannan itama NASREEN din haka,sallah sukai TA nafila tareda godewa rabbus samawati bisa wanann babban al’amari medadi dayafaru dasu.sannan yamata tambayoyi Akan addinin musulunci kuma TA amsa masa yadda yakamata,daukar abarsa yai sai gado inda yanuna mata cewar itakadaice abirnin zuciarsa to itama dinma hakane.ahakde SAMEER yamaida NASREEN babbar macace cikin kauna dakuma kulawa.
Koda safe dasuka tashi kasa hada Ido tai dashi wai ita kunya,shikwa yadauke abarsa yakaita bandaki yaimata duk wani Abu dayakamata sannan yadawo da ita daki,yana murmushi nafa gode baby boo dina dakika kawomin yancinki har gidana baki xubda mutuncinki a wajeba dukda nasan Ke dintadance nasamu babyboo dita dede nine namaida abata sabuwa sannan kika Maida angonnaki kema haka wato sabo da sabuwa kenan.Alalh deyasaka da alkhairi Dan yesterday was the happiest day of my life ,mekikeso arayuwa kome kikeso kifadamin pls?nasreen tai murmushi ba abinda nakeso illah mukasance kullum cikin farin ciki dauwamamme Allah yakara hada kanmu.
SAMEER yai Daria amin baby boo ammade dole sena kawo gift Dina sannan kitayani addua Allah yasade na jefa kwallona araga adede Allah yabamu healthy babies. Nasreen tace amin dearest one.sameer yace kinsan wani Abu kuwa?nasreen tace a’a,,yace kece first love Dina ban taba soyaiya ba se akanki kuma Kinga miracle kena aura. Nasreen tai murmushi Nima bantaba San wani da namiji kamar yadda nakesan kaba.danko marigayi FAREED bansoshi kamar yadda naso kaba,sedaga baya nakejin Ashe Ma mahaifinsa president Jameel yaso yai mugunta yasa yaran ya aureni yadda xexama chairman na company ,amma shi yana sona tsakani da Allah gashi kuma Allah daya fimu sansa yakarba abinsa.dahakade sukai ta hirarsu irinta ma’auratah wanda Sukesan junansu kuma suke Bawa soyayya hakkinta kamar larabawa.
BAYAN SHEKARA DAYA:
Gidanne acike da mutane kowa yaxo harda yan gayyar sodi.santalelen yaro mukaga ana yawo dashi inda ko Ina sekaga ana mika hannu anasan adaukeshi yaro yaci sunan Muhammad mahmoud wato mahaifin NASREEN inda xasu ringa kiransa da sultan.savouniers kala kala ake yawo dasu dasunan baby sultan.bayan anyi suna da daddadre SAMEER yashigo daki ganin matarsa dakuma baby sultan wanda ke gefe yana baccinsa.sameer yakalli dansa taredasa masa albarka.nasreen dake gefe se muzurai take,SAMEER yakarasa yajanyota jikinsa haba madam mekuma nai bayan Allah ya isah danaji kinayi a labor room?
Nasreen TA harareshi Allah ka iya mugunta dama haka haihuwan yake bayn duk wahalan danasha kalli yaronan wai gaba daya kamarka yadakko harta farcen kafarka. Sameer yai Daria a’a kema yana kama dake kalli sumar kansa gashinki yadakko fa haba madam nan gaba xaki haifo me kamarki kema ai. Nasreen tabude baki wa?ni Rufamin asiri ba yanxu ba Wlhy ,kasan wahalar danasha?sameer yace kakkimanta ninakarba haihuwarki a asibiti ,NASREEN TA xumburo baki niba wannan nake nufi ba ,SAMEER yadaga mata gira ohh nagane abinda kike nufi ai mijin naki bawasa shysa..itade NASREEN rufe Ido tai sannan SAMEER yamike tareda aje leda agabnta sannan yafice yana Daria bari inje yaseer na jirana awaje.bayan yafuta NASREEN tai murmushi tareda daga hannu sama ya Allah kabarni da DOCTOR SAMEER AMEER Dina ya ALLAH katemaki mijina ka karamai SO na aransa ka rayamana sultan. Sanann kajikan iyayena kasa suna aljannatul firdaus tareda daukacin musulmi dasuka rigamu gidan gaskiya.
ALHAMDULILLAH
  komai yai farko xeyi karshe nanmuka kawo karshen littafinmu mesuna DR SAMEER AMEER abinda mukai Dede Allah yabamu lada Wanda mukai kuskure Allah yayafemana muna fatan idan kunga kuskure kudauka duk yan Adam 9 suke ba 10 ba.kuma shi Dan Adam ajizine.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page