RANA DAYA CHAPTER C KARSHE

 RANA DAYA CHAPTER C KARSHE

Nazeefah de bata da aikin da yafi kiran Safiyya kullum tana tambayarta mey Amal ta girka wa Afzal, shin idan ya dawo daga aiki mey sukeyi, suna yawan fita ne ko kuwa zama suke a gida suna wasa? Komai so take tana ji haka kawai tayita tada wa kanta hankali.

Kwana bibbiyu Afzal ya cigaba da yima kowaccensu, bada dad’ewa ba aka bud’e makaranta. Ranan da kwanan Amal ne kuma tana da early morning lectures tare suke shiri su fita se yayi dropping nata kafin ya wuce office haka ma idan kwanan Nazeefah.+

Yau Amal da Afzal suka cika wata d’aya da aure se kuma Allah yayi ranan ya fad’o a kwananta se rawa jikinsa yake he can’t wait to go back home. Itama Amal bata mance da wannan muhimmiyar rana ba, morning lectures nata na k’arewa wajajen sha d’aya driver’n da Afzal ya mata hiring ya dawo gida ta shiga kitchen yayinda Safiyya ke tayata aiki. Abinci kala-kala suka had’a da juices abin se wanda ya gani ga fruit salad ba abinda babu dam suka cika kan dining table d’in da kayan abinci. Dab ta fito daga wanka around three kenan Afzal ya buga mata waya.

“Halo my adorable Kitten?” Ya fad’a bayan da ta d’aga.

“Yes Habib Albi ya kake ya office?” Ta amsa.

“I’m soo missing you Baby” ya sanar da ita.

“I miss you too Habib Albi ai ka kusa dawowa.”

“Wani kusa? Kina ji wai muna da meeting.”

“Meeting kuma? Se goma zaka dawo kenan?” Ta tambayesa tamkar zatayi kuka.

“Ai nima ba iya jira zan ba I miss you so much Babe.”

“I miss you even more darling amma ya zamuyi?”

“K’arya nayi nace musu bakida lafiya zan kaiki asibiti so I’ll be back in a jiffy.”

“Awwwn Habib Albi se kazo toh Allah ya kare.”

“Ameen Kitten I love you.”

“I love you too darling” ta fad’a had’e da katse wayar. Nan da nan ta ciro wata had’ad’d’iyar purple blouse ta sanya da wani bak’in straight skirt ba k’aramin amsan ta skirt d’in yayi ba yadda yabi perfect curves nata. Zama tayi gaban mirror ta rangad’a kwalya yau harda yin lining saman idonta tasa mascara ta taje dogayen eye lashes nata sannan tasa maroon janbaki ba k’aramin kyau tayi ba gashinta da tayi stretching jiya a salon ta jik’a da mai sannan ta taje ta kwantar a jikinta ta feffeshe da turare tana cikin sanya d’ankunne se taji k’aran motan Afzal da hanzari ta k’arasa tasa bracelets nata ta d’aura agogo ta fita taransa. Dai-dai bakin k’ofan ta tsaya yadda yana bud’e k’ofan ze fara cin karo da ita.

Hannunsa a cike ya fito daga motan d’aya rik’e bouquet na flower d’aya kuma da ledan da ya yo mata shopping aciki. Yana bud’e k’ofan sega Damsel tasa tsaye tana mar murmushi.

“Dayyummm!” Ya furta yayin da yakasa koda kyafta ido se kallonta yake kaman ze hambuleta tsabagen kyan da tayi.

“Happy one month anniversary Habib Albi” ta sanar da shi ledan ya ajiye a kan wani stool dake kusa da bakin k’ofan sannan ya mik’a mata flower’n “Happy anniversary to you too Baby I love you” amsa tayi sannan yayi hugging nata yana mey shak’an daddad’an k’amshin turaran jikinta, sun dad’e a haka sannan ta raba hug d’in a hankali.

“You’re looking.. you’re looking fabulous Kitten, gosh you’re so beautiful” ya sanar da ita tun daga k’ark’ashin zuciyansa wani sa’in har mamakin kalan kyawawan yaran da Amal zata haifa masa yake tabbas idan zasu bi ta ba k’aramin kyau zasuyi ba.

“Thank you Habib Albi thank you for the roses too.”

“Don’t mention Darling” jakarsa ta amsa ya d’aga ledan suka k’arasa d’aki inda ya rage kayan jikinsa yabar nickers zalla.

“Baka ci abinci ai bako?” Ta tanbayesa tana zaune a gefensa.

“Bayan kince kar naci se kuma in ci Kitten? Yunwa nakeji kaman zan mutu.”

STORY CONTINUES BELOW

“Kar ka mutu kaji? Taho muje kaci abinci.”

“Wow” kawai yake furtawa lokacin da suka isa kan dining d’in kuloli sekace fiest za’ayi se sallama suke masa ga wani chocolate cake babba da aka rubuta caption na “Happy Anniversary Habib Albi” akai ajiye a gaban sa.

“Duka wannan kika girka Kitten?”

“Yes Habib Albi nida Safiyya.”

“Wow I’m impressed the cake is so beautiful.”

“Thank you Habib Albi shi catering nayi” ta fad’a had’e da yankan kad’an tayi feeding nasa da shi. “Mmnm” ya furta yana santi “Chocolate cake.”

“Your favorite right?” Kai ya gyad’a eagerly “Shin mey da mey da mey Kitten d’ina ta tanada mun haka?” Ya tambaya se tsinkewa miyaun sa yake.

“Kai de bud’e kaga” flasks d’in ya shiga bubbud’ewa daga na pepper soup na kifi sena ganda se fried rice da coleslaw ga su samosa dasu spring rolls da ta sa akayi mata bayan nan ga apple juice da su aldeb da zo6o abun de se wanda ya gani.

“Kitten isn’t this too much?”

“Ka manta kai d’an gata na ne?” bi tayi one-by-one tana d’iba mai a plate sannan tayi serving nasa. Yaci wai sam shi seda ita haka tayi joining nasa. A kan cinyarsa ya zaunar da ita haka ya bata yaci har suka cinye inda ta kira Safiyya da ta tattare wajen seta d’iba duk abinda ya mata itama taci idan ta gama se tayi wanke-wanke. Safiyya se washe baki take taga pepper soup har kala biyu ga cake.

D’aki su Afzal suka dawo inda da k’yar Amal ta sanya sa ya watsa ruwa wai sam shi seda ita zeyi, ita kuwa tace bazata goge wannan kwalyan nan duka ba. Bayan ya fito ya sanya nickers nasa sannan ya iso ya zauna a gefenta “Here this is for you Wifey” ya fad’a yana mik’a mata ledan d’azu cike da jin dad’i ta amsa ta shiga fiddo da kayakin da suke ciki. Waya taga sabuwa pil k’irar Iphone X aciki, seda wasu shoes and bags kala biyu da wani purple doguwar riga voile me combination na colors a jiki wanda ko ba a tambaya ba ansan mey d’ankaren tsada ne k’arshe kuma seda wani photo album wanda ciki hotunansu ne da dama wanda suka d’ad’d’auka a waya yakai aka wanke masa.

“Omg Habib Albi this’s too much” ta d’ago kai tana kallonsa yayinda idanunta suka ciko da hawaye tsan-tsan farin ciki.

“Oh Kitten not again” yayi maganan yana matse ta a jikinsa, kukan farin ciki ta shiga yi yayinda ta kasa 6oye farin cikinta. “Please don’t ruin this beautiful moment Love” ya buk’aceta yana shafa gashin kanta sannan a hankali ya d’ago ta daga jikinsa yana share mata hawayen nata da babban yatsansa.

“I’m sorry I just don’t know how to react Habib Albi banida bakin yi maka godiya, wallahi ban san ta ina zan fara ba, I know thank you won’t compensate for this but thank you so much Habib Albi, Allah saka da alkhairi ya k’ara maka bud’i I love you soo much.”

“Masha Allah Kitten ameen kuma nagode, I love you even more. I don’t think I can survive without you, in fact my life has no subtle in the absence of your love Amal, duk yadda nakeso in nuna miki how deeply in love I am with you bazan iya ba because no words can describe the love I have for you, not even feelings could show Kitten, one thing I’m sure is that there’s no ME without a YOU” ya k’arisa yana mey rik’o k’ananun hannayenta cikin nasa tare da placing gentle kiss akai.

Hawaye sosai Amal take dan farin ciki sau dayawa takan zauna ta tambayi kanta shin mey ta ta6ayi wa Allah da ya bata miji mey kyautatawa kaman Afzal, mijin da burinsa bai fi yaga ya sanya ta farin ciki, mijin da be ta6a k’untata mata ba a iya zaman da sukayi, mijin da se abinda take so yakeyi mata. Gani take kaman bata cancanci mutum kamansa ba, shin anya zata iya rayuwa idan ba shi?1

STORY CONTINUES BELOW

“I can’t leave without you Habib Albi wallahi I can’t” ta rushe da kuka rungumarta yayi yana shafa gashinta a hankali sun d’au tsawon lokaci a haka sannan a hankali ya d’agota bayan da kukan nata ya lafa “Cry nomore okay? I love you so much” Kai ta gyad’a tare da kwantar da kanta a k’irjinsa “I love you more Habib Albi.”

****

Bayan sallan Isha suka shirya tsaf suka fice wajen shan ice cream se hoto Afzal yake tayi mata tun tana ce mai ya bari bata so chan itama da abin ya isheta ta d’au sabuwar wayarta ta shiga d’aukansa tana mai video, shak’atawa suka tayi abinsu suka bar Safiyya kad’ai a gida. Ita kam ta samu TV se fata take kada su dawo ita bata k’i ma su kwana a waje ba saboda tayita kallon series abinta. Haka har wayanta ya gama ringing bata ji ba se a karo na biyu tsabagen yadda hankalinta ya duk’ufa kan kallon.

“Assalamu Alaikum Aunty ina yini?”

“Ina kika ajiye wayanki ina kiranki Safiyya?” Nazeefah ta kurareta.

“Kiyi hak’uri kallo nakeyi.”

“Ya uwar d’akin naki? Meya faru yau?”

“Hmm Aunty baki san meya faru ba.”

“Gayan mey?” Ta tambaya cike da rashin hak’uri.

“Kinga abincin da Aunty ta girka wa Uncle kuwa? Wallahi sunyi kala ashirin pepper soup babu irin wanda batayi ba ga juice d’innan da su meat pie.”

“Kai! Wai meke faruwa?”

“Wallahi wai ani.. ani– ani wallahi na mance sunan abun amma tace wai yau ani wani abinsu ne shiyasa ta mai wannan girke-girken kuma baki ji yadda komi yayi dad’i ba.”

‘”Yar k’auye anniversary? Yau anniversary’nsu?”

“Yauwa wallahi shi! Anibasari haka tace.”1

“Innalillahi!” Ta furta cike da tashin hankali yayinda wani irin kishi da haushin Amal taji ya rufeta kup, shekaranta uku a gidan Afzal amma bata ta6a celebrating anniversarin su ba sega Amal da ta shigo na wata d’aya tayi hakan taya Amal zata fita kaifin tunani? Inaaaa baze yuwu baa! “Yanzu ina suke?”

“Sun fita tun d’azu tun bayan sallan Isha.”

“Basu dawo ba har yanzun?” Ta tambaya had’e da zaro ido tana duban agogon bangon d’akinta.

“Eh.”

“K’arfe goma fa! Ina sukaje ta fad’a miki?”

“Cemun kawai tayi zasu fita.”

“Innalillahi wallahi hawan jini ya kusan kamani ‘yar nan zata sace mun miji, na shiga uku ke wawiya meyasa baki k’ok’k’ona mata girkin nata ba?”

“Bata bari na ko kusa da cookan nata iyaka in yanka mata su albasa ko in daka mata maggi.”

“Wawiya ki bud’e kunnenki ki saurareni kina jina?”

“Eh Aunty.”

“Anytime ta sake saki yi mata jajjage ko kuwa daka maggi kiyi excess ki k’ara naki akai yadda abincin zeyi rad’au yayi yaji ya rud’awa Ya Afzal ciki ya kasa ci kinji? Haka ne kawai zesa abincinta ya fita masa a rai.”

“Aunty toh ai zata gane.”

“Banza ce mata zakiyi bakiji adadin da tace ki d’iba ba.”

STORY CONTINUES BELOW

“Amma fa ita take d’iba ni kawai bani take in daka ko in yanka.”

“Ki jini, nan gaba idan kuka shiga kitchen tun kafin ta d’iba mikin kice zaki d’iba da kanki seki tambayeta nawa, anan seki k’ara da naki akai idan ta tambayeki kice baki ji da kyau bane kinji?”

“Toh Aunty an gama.”

“Yauwa bayan nan se meya sake faruwa kingan shi ya saya mata wani abun?”

“Toh wallahi ban san wannan ba dake ina cikin d’aki ya taho.”

“Bance kullum kina jin k’aran motansa ki fito ba kiga meya shigo da shi?”

“Aunty na shiga ba ne.”

Aikin kenan kullum mstww wallahi ina da tabbacin ya mata sayayya shima soko d’aya ya cigaba se ‘yar shuwan nan ta tsiyatar da shi tukuna yanzu kinsan mey nakeso dake?”

“Sekin fad’a.”

“D’akinsu zaki shiga ki duba mun kiga koya sai mata wani abun.”

“Aunty-“

“Bade tsoro kikeji ba?”

“Aunty idan suka dawo ina cikin d’akin fah?”

“Wawiya idan baki cire tsoron nan ba ya zaki yi mun aiki toh? Ko bakison extra dubu goma akan albashinki k’arshen watan nan?”

“Ina so.”

“Good jeki lek’a mun d’akin nasu.”

Mik’ewa tayi ta nufi d’akinsu Amal cike da fargaba ta gwada bud’e k’ofar sede a kulle ta tarar. Koda wasa Amal bata ta6a fita bata kulle musu d’aki ba not that tana zargin Safiyya na sata se don gudun abinda shaitan ze iya raya wa mutum wataran. “Aunty a rufe” ta sanar da ita.

“A rufe de!”

“Eh wallahi.”

“Amma ‘yar nan shegiya ce wallahi barta watan cin ubanta ya kusa kamawa wallahi da ikon Allah sena koreta daga gidan nan Ya Afzal is mine alone.” Nan ta kashe wayan cike da takaici, safa da marwa ta shiga yi a d’akin nata yayinda hankalinta ya mugun tashi ji take kaman zatayi hauka. Wai taya ma shawaran celebrating anniversary be ta6a bugo mata akai ba? Shin hakan na nufin Amal ta fita iya tarerayan miji? Mstw! Wayanta ta bud’e ta shiga date tana neman yaushe 25th zeyi itama anniversary’n ta ya kewayo, dubawa tayi taga next week ne, nan ta shiga irgawa tana fatan Allah yasa ranan ya fad’o a kwanan ta, da ikon Allah kuwa se ya fad’a a kwanan nata. Toh ma auren nasu shekara uku da wata nawa ne? Ana March yanzu sun yi auren a December that is 3 years three months, perfect!

Jira tayi har ranan da anniversay’n nasu ya kewayo itama ta shirya gaggarumin girki, ba abinda bata had’a ba sauran abubuwan ma catering tayi dam ta cika kan dining itama. Tasha lalle da kitso ba dama ta sanya sabon d’inki. K’arfe biyar da rabi Afzal ya baro gidan Amal zuwa na Nazeefah, tun daga bakin gate k’amshin turare ya ke tashi gashi tunda ya gwada mata yadda ake sa turaren wutan ta koya takeyi itama. Tun daga gun parking lot taje ta taresa.

“Welcome home Ya Rouhi” tace da shi had’e da pecking nasa a kumatu.

“Wannan kwalya fa Rabba’atul Bait?” ya tambaya yana kallonta admiringly ba k’arya tayi kyau gashi unlike Amal da bata yin heavy makeup Nazeefah idan ta tashi yin kwalya yi take wane makeup artist ce ta zana mata fuska.

“Naka mana Ya Rouhi” ta amsa tana amshe mai jakansa.

STORY CONTINUES BELOW

“You look awesome Babe.”

“Thanks Baby” nan suka k’arisa ciki “Wai wai wai kulolin nan fah daga ina?” Ya tambaya yana bin dining table d’in da kallo.

“Happy anniversary Babe.”

“Wow!” Kawai ya iya furtawa yayinda kansa ya rud’e “Happy anniversary Dear” ya miyar mata had’e da brushing light kiss a lips nata “But wait I thought a December mukayi aure yau kuma March ko ba haka ba?”

“Yes Ya Rouhi yau 25th march which marks 3 years 3 months of our marriage ko ka manta?”

“Yeahh right” yayi reasoning da ita “Thank you Babes.”

“Muje ka watsa ruwa se mu ci abinci ko? Ina ba a k’oshe kake ba?”

“Ai ko a k’oshe nake ya zama dole inyi creating space wa delicious d’in Rabba’atul Bait d’ina” sosai taji dad’in amsansa. A tare suka k’arisa d’akin nan da nan ta had’a mishi ruwa ya shiga ya watsa fitowansa ya nufi wardrobe dan ciro wandon da ze sanya se cin karo yayi da wani k’aramin pack da akayi wrapping da wrapping sheet cike da mamaki ya d’aga ya bud’e wani had’ad’d’en designer agogo ya tarar mey d’ankaren tsada aciki, gefensa kuwa wani happy anniversary card ne daya sha k’amshin turare. Da murmushi kwance a fuskansa ya karance, a ko da yaushe godiya yake yi wa Allah da ya shiryar mar da Nazeefar sa har sukayi sorting out differences nasu suke zaman lafiya yanzu. Baya jin ze iya rayuwa ba ita, a hankali soyayyarta ya ginu a zuciyansa. A da be ta6a kawowa koda kusa da mafarki cewa wataran ze auri mata biyu ya zauna da su kuma ya sosu duka ba se yanzu da hakan yake faruwa. Ya sani son Amal daban yake a zuciyansa amma kuma Nazeefah na da wani gur6in da ta mamaye a zuciyansa, gur6in da ba me iya mamayewa se ita.

“Rabba’atul Bait?” Ya kewayo yana kallonta cike da soyayya.

“Yes Ya Rouhi” ta amsa had’e da takowa zuwa inda yake.

“Is this for me?”

“Yes Ya Rouhi Happy 3 years anniversary I love you so much” ‘yar kunkuminta ya kama had’e da matso da ita kusa dashi sannan yayi owning lips nata kissing her so gently with thousands of emotions and gratefulness. A hankali yayi pulling out “Thank you Nazeefah, this means alot to me Allah miki albarka.”

“Ameen Ya Rouhi you deserve alot morethan this.”

“Kin san ina sonki ko?” Kai ta gyad’a masa a hankali tana mai murmushi “Ko zaka sake sanar dani?”

Murmushin ya miyar mata sannan yace, “I love you Nazeefah ni kaina mamakin kalan soyayyan da nake miki nake ban ta6a kawowa kusa da raina that I’ll one day love you like I’m doing, Allah ne kad’ai sheda akan kalan soyayyan da nake miki, I just pray it continues to grow and never fades away, Allah bar min ke Rabba’atul Bait ya miki albarka kuma.”

“Ameen Ya Rouhi I love you even more gani nake kaman idan ba kai bazan iya rayuwa ba. Ka sani ka riga ka zama 6angare daga jikina wanda idan aka cire bazan iya rayuwa ba, please never leave my side.”

“We’ll forever remain together Nazeefah in shaa Allah har mu mutu sannan kuma mu cigaba da soyyayar namu achan Jannah where we’ll reunite.”

“In shaa Allah Ya Rouhi. I’ll choose you a million times if I were given the chance to, muje kaci abinci ko?” Kai ya gyad’a mata sannan ya zaro wandonsa ya sanya dining d’in suka k’arisa inda tayi serving nasa sannan ta zauna gefensa tana masa hirar soyayya har ya gama ci. Sosai ya yabawa girkin nata ranan. Washegari tun k’arfe sha biyu ya dawo daga office ya watsa ruwa se wajajen uku Nazeefah ta dawo daga school sannu da zuwa yayi mata ya sirka mata ruwa ta watsa sannan yajata dining da taci abinci. Bud’e flask da zatayi kawai ta tarar da kwalin waya ciki k’irar Iphone X sak irin na Amal fari itama.

STORY CONTINUES BELOW

“Omg! Ya Rouhi!” Tayi exclaiming had’e da d’agowa “Ya Rouhi an iX!”

“Yes Rabba’atul Bait this’s my anniversary gift to you I hope it’s not too late?”

“It’s never too late Ya Rouhi thank you soo much Allah k’ara bud’i I love you endlessly.”

“I love you too darling so ki shirya muje muci abinci nima yunwa nakeji.” Nan da nan suka shirya suka fice Nazeefah dad’i kaman ze kasheta sede jikinta se bata yake Afzal ya sai wa Amal itama iphone X d’in, da ta tuna da hakan se ranta ya 6aci she can’t wait ta fitar da ita daga gidan. Washegari bayan Afzal ya dawo daga office ya shiga tattara wasu documents nasa da ze buk’ata idan ya tafi gun Amal kasancewar yau kwanan Nazeefah ya k’are. Tunda Nazeefah ta shigo d’akin ya karanci mood nata sam ba walwala a tattare da ita.

“Rabba’atul Bait?” Ya kirata.

“Uhmm?” Ta amsa had’e da d’ago kai tana kallonsa a maraice.

“Lafiya?” Ya tambeyeta kai zalla ta gyad’a mar sede be yarda ba yana gama tattara documents nasan ya sanyasu cikin briefcase nasa ya k’arisa gefenta ya zauna. “What’s going Dear?”

“Ya Rouhi…” kawai seta rushe da kuka cike da tashin hankali ya rungumeta a jikinsa yana shafa bayanta a hankali yana bata hak’uri kukan ta cigaba da yi chan da kukan nata ya lafa ya d’agota yana share mata hawayen nata. “Ya isa kinji?” Kai ta gyad’a masa a hankali sannan ya tambayeta meya faru a cewan shi gabad’aya mutuwa akayi mata.

“Ya Rouhi I can’t do this anymore.”

“Talk to me Nazeefah I’m here.”

“Ya Rouhi muje asibiti.”

“Why? Meya faru? Bakida lafiya ne?” Yayi saurin jero mata tambayoyi.

“Ya Rouhi shin baka tunanin ko ina da wata matsala?”

“Matsala kaman ya kenan Nazeefah?”

“I don’t think I can conceive (bana jin zan iya haihuwa.)”

“Subhanallahi meyasa kika ce haka?”

“Ya Rouhi it’s been three years.”

“Se mey? Meya kawo maganan nan?”

“Ya Rouhi k’awayena da akayi auransu bayan namu duk sun haihu wasu kuma suna hanya amma ni shiru ko miscarriage ban ta6a yi ba, yanzu Asma’u ta kirani wai she’s pregnant Asma’u da last two months mukayi bikinta” se ta fashe da wani kukan. Hugging nata yayi a hankali yana mey cigaba da bata hak’uri, sosai ta basa tausayi be saketa ba seda ya tabbata kukan nata ya lafa.

Fuskanta ya rik’o cikin hannayensa a hankali ya fara ce mata, “It doesn’t matter Rabba’atul Bait it doesn’t matter saboda wanda kika rigasu yin aure sun riga haihuwa ko makamancin hakan remember kowa da lokacinsa a duniyan nan, we weren’t born together, we shall die alone and so shall live our lives differently. Kisa a ranki kema naki lokacin na nan zuwa kuma koda ma baki haihu mun bama ni banida matsala da hakan, dai-dai da RANA D’AYA Ummi bata ta6a cemun meyasa taji shiru ba har yanzu saboda tasan shi haihuwa yin Allah ne yau shekaranta nawa ita da Abba amma ta ta6a haihuwa ne?” Kai ta kad’a a hankali “Good kuma Abba yak’i ta don hakan ne? Har yanzu suna tare and deeply in love so ki kwantar da hankalinki bazan ta6a k’in ki ba wai don baki haihu mun ba a gidan nan kuma duk wanda ya goranta miki da hakan zan tabbata na mishi ba dad’i ke bakisan matsalar ma ze iya yuwuwa daga ni bane?”

STORY CONTINUES BELOW

“Ai kaima kasan ba daga kai bane Ya Rouhi ba haka ranan wata tace mun wai dan bana haihuwa ne ka k’ara aure ba, I’m very sure kwanan nan zamuji Amal tana d’auke da cikinka.”

“Subhanallahi! Don’t you ever say that Rabba’atul Bait kin de ji rantsuwa ko? Wallahil azeem ban auri Amal wai saboda ke bakiya haihuwa ba, Nazeefah ban ta6a d’aukan rashin haihuwan mu a matsayin damuwa ko matsala a zamantakewan auren mu ba kuma bazan ta6a ba saboda nasani haihuwa yin Allah ne. Kuma da kike maganan kwanan nan za aji Amal na d’auke da juna biyu se mey? Ai d’an Amal kaman d’anki ne kaman yadda kema d’anki yake matsayin nata. Ke baki san duk mun zama abu d’aya ba yanzu? Kuma ki sani dan Amal ta haihu kafin ke doesn’t mean anything, it won’t change the fact that kece Rabba’atul Bait d’ina and that I love you so much. Saboda haka nakeson ki kwantar da hankalinki mu cigaba da addu’a Allah kawo mana nagari masu albarka ko bakisan sometimes Allah yana hana bawa haihuwa bane saboda ya ga yaron ze zo ya zame mai matsala?”

“Na sani Ya Rouhi.”

“Toh sekiyi aiki da hakan kisa a ranki koda baki haihu ba bawai Allah ya k’i ki bane inda haihuwa wani abu ne da duk duniya ba wanda ze kai Aisha R.A yawan yara amma kuma mey? Ko miscarriage bamu ta6a jin tayi ba haka kad’ai ya isa ya kwantar miki da hankali Rabba’atul Bait.”

“Thank you so much Ya Rouhi I’m so lost without you, wallahi bansan ya rayuwata zata kasance idan ba kai ba, ban ta6a neman abu na rasa a k’ark’ashinka ba please forgive me if I’ve every wronged you.” Ta fad’a jikinsa tana kuka, rungumarta yayi yana shafa bayanta a hankali.

“It’s okay Darling kibar kukan haka kinji? Ita kuma Asma’au Allah ya inganta ya raba lafiya.”

“Ameen Ya Rouhi.”

“Smile toh in san ranki ba a 6ace yake ba.” Ya fad’a had’e da d’ago ta. Murmushin ta sakar masa kad’an “That’s my girl bari in gama shiri toh.”

“Zaka koma gun Amal ko?”

“Eh.”

“Akwai abinda kake so in tayaka da shi?”

“Kawai ki daina damun kanki bana son in sake jin kina maganan rashin haihuwar ki a gidan nan kinji?”

“In shaa Allah Ya Rouhi yauwa se kud’in fees na Islamiyya na kasan mun shiga sabon term dukda yanzu ba kullum zanna samu ina zuwa ba saboda boko.”

“Alright zan miki transferring shikenan ko akwai wata matsalar?”

“Babu bayan nan thank you.”

“Don’t mention” tayasa gama shiri tayi sannan ta rakasa har waje ta dawo ciki bayan ya sallameta.

***

Kasancewar Nazeefah ta cika masa ciki da abinci koda ya isa gidan Amal be buk’aci abinci ba se chan wajajen tara, serving nasa tayi ta zauna a gefe kasancewar macaronin be gameta ba yau. Cokali d’aya ya kai baki ya harar take.

“Subhanallah Habib Albi!” Tayi exclaiming a rud’e. Goran ruwan dake gefensa kawai ya bud’e ya shiga kwankwad’a seda ya kusan shanye duka ya cire. “Habib Albi lafiya?”

“Kitten mey kikasa a abincin nan haka?”

“Kaman ya mey nasa kuma Habib Albi? Wani abu ne?”

“Kinji gishiri da barkonon da yake ciki? Baki san bana son yaji bane?”

“Barkono da gishiri kuma Habib Albi?” Ta tambayesa da mamaki a iya saninta attarugu biyu tasa gishiri kuwa kad’an maggi ma tafi bawa k’arfi a girkin, mey Afzal yake cewa toh?

STORY CONTINUES BELOW

“Yes” ya jaddada mata tare da k’arar da ruwan goran plate d’in taja don d’anawa sede be barta ba yayi sauri yaja “Don’t mind bazaki iya tasting ba.”

“Wallahi attarugu biyu kacal nasa.”

“Maybe yana da zafi ne.”

“Toh gishirin fah? Har dana kusan sauk’ewa ma fa na d’ana kuma banji yayi rad’au ba please ka bani in ta6a inji.” Plate d’in ya tura mata spoon d’aya takai itama ta harar gora ya mik’a mata da wuri nan ta kur6e itama. “Kinji?”

Mamaki ne ya cikata shin ya akayi haka? Abincin se kace an d’ibo ledan gishiri ne aka juye a ciki ga wani d’an banzan borkono “Habib Albi I’m so sorry wallahi ban san ya hakan ya faru ba believe me har dana kusan sauk’ewa ma na d’ana and everything was okay ka kira Safiyya ka tambayeta kaji.”

“Haba Kitten me yayi zafi harda tambayan Safiyya? It’s okay kinji? Karki damu ina Safiyya kirata tazo ta zubar da abincin don ko almajirai ban jin ya dace a basu abincan.”

“Habib Albi dan Allah kayi hak’uri I’m very sorry.”

“Ohh Kitten” yayi maganan had’e da dafe hannunta dake ajiye kan table d’in “It’s really okay just be careful next time okay?” Kai ta gyad’a hankali har cikin ranta bata ji dad’in hakan ba, sam ta rasa ya akayi hakan ya faru koda wasa kuma bata kawo a ranta wai Safiya zata iya zuba mata borkono da gishiri cikin girki ba.

“In dafa maka indomie toh?”

“Karki damu.”

“Habib Albi kayi fushi dani ne?” Ta tambayesa tamkar zatayi kuka.

“Meyasa zanyi fushi dake Kitten kinsan mey?” Kai zalla ta kad’a mar. “Sanya hijabinki muje muci abinci a waje.”

“Hab-“

“Shhh not a word” da kansa ya kira Safiyya ta zubar da abincin sannan ya sanar da ita zasu fita. Suna fita ta d’au wayanta ta kira Nazeefah a karo na farko ta d’aga. “Aunty ina yini?”

“Lafiya ya kike?”

“Lafiya k’alau Aunty yau baki san meya faru ba.”

“Meneh?”

“Hmmm abinci Aunty ta ke girkawa da ta shiga d’aki na saci idonta na shiga kitchen d’in na barbad’a borkono da gishiri akai gashi yanzu Uncle ya dawo ya kasa cin abincin k’arshe ma cemin yayi in zubar.”

“Kai Safiyya!” Tayi exclaiming cike da jin dad’i.

“Wallahi Aunty.”

“Wow kinci kyauta, aikinki yayi kyau yanzu ina suke?”

“Naga sun fita amma de kam beji dad’i ba da be tarar da girki mey kyau ba har a fuskansa naga hakan.”

“Haka nakeso ki cigaba da gashi Sofin gaye niko na miki alk’awain sabon atamfa harda d’inki.”

“Godiya nake Aunty.”

“Yauwa se anjima aikinki na kyau” da haka sukayi sallama.

*****

Haka tun daga ranan sede Amal batayi girki ba se Safiyya ta zagaya ta zabga mata gishiri ko yaji aciki gashi koda wasa Amal bata ta6a zarginta ba saboda yadda ta amince da Safiyya ta rik’eta da zuciya d’aya bayan nan ga yadda it Safiyyan da kanta take nuna mata girmamawa da k’auna. Gashi kaman dagaske duk sanda girkin ya 6aci ta rink’a nuna damuwa. Abun daya sake d’aurewa Amal kai shine se idan Afzal ze zo mata ne girkin yake tashi 6aci idan ba haka ba girkinta me kyau takeyi idan baya nan amma da zaran ya dawo se gishiri da borkono su fara zarcewa. Abu kaman wasa seda Afzal ya ya tattare borkono da gishirin ya kulle a storeroom, attarugu kuwa ya kyautar don kar girkin nata yana 6aci sede aikin banza yayi. Muddin Amal tayi mai girki toh se gishiri da borkono yayi yawa. Sosai abun ya d’aure masa kai. Amal kam har kaman ta fara samun ta6in hankali ne tsan-tsan tashin hankali. Ba aikinta se kuka a gidan, ace wai yanzu Afzal nata baze iya cin girkinta ba? Hakan ba k’aramin k’ona mata rai yake ba. Gabad’aya ta fita daga hayyacinta barin ma yanzu da Afzal ya fara zancen hanata yin girki kwata-kwata don tun baya nuna damuwa abun ya fara damunsa. Ya rasa gane meke faruwa. Tunani ya fara kode iskokai ne suke mata wasa da hankali? Sede be san ta ina ze fara sanar da ita hakan ba, shi kansa ba wai ya amince da hakan bane, be ta6a ganin mace mey son addini kaman Amal tasa ba har taya iskokai zasu ci nasara akanta? Kullum suka fita seta tuna masa yayi addu’an barin gida haka idan suka dawo, na shiga bayin nan bata wasa da shi ko ruwan d’umi zata zubar setayi istihaza toh tayaya aljanu zasuyi nasara akanta? Sede kuma ba wanda yafi k’arfin jarawaba.

STORY CONTINUES BELOW

Kuka take sosai tana rantse mishi akan cewa lallai-lallai bata sa gishiri da attarugu ko d’igo ba cikin girkin amma ga abincin nan rad’au da uban borkono. Yau kusan sati biyu kenan suna abu d’aya.

“Kitten it’s okay kibar kukan haka.”

“Habib Albi please believe me.”

“I do believe you Kitten I do” ya amsa yana share mata hawayenta amma ina se zuba sabi suke.

“Wallahi ban bud’e storeroom d’in na ciro gishirin ba kana iya zuwa muje ka gani ko kuwa ka tambayi Safiyya, a kulle d’akin yake wallahi ban bud’e ba” hannunsa ta kama da niyyan jansa storeroom d’in akan yaje ya gani sede yayi saurin tsayar da ita ta hanyan rik’e ta.

“Shhhh it’s okay it’s okay” ya fad’a yana k’ok’arin calming nata. “Calm down okay? I believe you, I do believe you Kitten nasan baki bud’e d’akin ba amma ai kinji amount na gishirin da yake cikin abincin ko?”

“Wallahi ban sa gishiri ba Yaya.”

“I know Kitten and I do believe you, kinsan mey nake so da ke? Ki huta na kwana biyun nan kar ki sakeyin girki duk abinda kikeso zan siya miki ko kuwa Safiyya ta girka miki amma ke karki sake aza tukunya a gidan nan hala stress na school ne yake damunki you need to rest.”

“Har zuwa yaushe Habib Albi? I don’t need to rest ba hauka nake da shi ba wallahi ban sa gishiri cikin girkin nan ba you have to believe me tunda ka tattare gishirin ka rufe a store ban sake yin girki da shi ba, taya zakace kar in sake aza tukunya a gidan nan Habib Albi?”

“It’s just for some time Kitten please stop crying” Ya amsa yana share mata rushing tears nata had’e da rungumarta “Kiyi hak’uri kibar girkin na kwana biyu until everything is okay kinji?” Jikinta ta janye daga nasa “Kai kuma fa Yaya? Wa ze na maka girki? Wa ze na dafa maka abinci? Shikenan bazaka sake cin girki na ba?”

“Wayace bazan sake cin girkin ki ba Kitten? It’s just for the mean time okay? Zan na ci a restaurant kafin nan kin huta kema I’m sure stress ne ya miki yawa.”

“Yaya wani irin stress? Wallahi ba wani stress dan Allah kar ka hanani yi maka girki I beg you please Yaya” kuka take sosai tana rok’ansa. Hannayensa ya kama acikin nata.

“Kitten dan Allah kibar kukan nan haka bawai hanaki yi mun girki nake shirin yi ba its just for the meantime.”

“Yaya please I beg you, I promise daga yanzu zanna sa hankali maggi baze sake zarce mun ba please kar ka hanani yi maka girki.”

Kuka take sosai shi kansa ya rasa mey yake ciki shin ya kira malami a yi mata ruk’iya ne? Kokuwa likitan mahaukata ze nema? Shin meyake damun Kitten tasa? He don’t want to believe ta6in hankali ne ke shirin kamata, he can’t afford to lose her. Taya zata na rantsuwa bata sa gishiri da barkono a girki ba amma kuma ga abinci rad’au? Meke faruwa? Hugging nata yayi gam a jikinsa yana shafa bayanta har suka sauk’a k’asa akan gado. Be saketa ba seda ya tabbata bacci ya d’auketa. A hankali ya shimfid’ar da ita akan gadon ya rufeta da bargo sannan ya fito. D’akin Safiyya ya nufa yayi knocking bisa k’ofan take ta amsa ta fito.

“Sannu Uncle.”

“Safiyya?” Ya kirata “Na’am?” ta amsa tana kallon k’asa. “Meyake faruwa idan na tafi office?”

“Kaman ya Uncle?”

“Meyake samun Auntin ki? Meyasa girkinta kullum gishiri yake zarcewa bayan na tattare gishirin na kullesu a d’aki ke kike d’auko mata?”

“Wallahi ba ni bace Uncle kuma kaman yadda baka sani ba wallahi nima banida masaniya game da abinda yake faruwa ni kaina mamaki abun yake bani a ido na tayi girkin d’azun nan maggi da tattasai zalla tasa kuma har da ta kusan sauk’ewa seda muka d’ana mata amma da zaran ansa a flask se abincin ya 6aci.”

“Are you sure?”

“Na’am?”

“Nace kin tabbata?”

“Eh Uncle.”

“Bake kike yin gwaninta ki k’ara mata a bayan idonta ba?”

“Meyasa zanyi hakan Uncle? Allah ma shaidana ne.”

“Huhhh” nauyayyan ajiyan zuciya ya sauk’e.

“Ban so inyi maganan ba d’azu a gabanta sede ranan naga Aunty tana wani abin al’ajabi.”

“Abin al’ajabi?” Ya tambayeta cike da rashin fahimta.

“Eh uncle a kitchen ranan naganta tana magana da kanta haka jiya ma.”

“Tana magana da kanta kuma?”

“Eh Uncle ita kad’ai sekaga tana suratai dama Aunty tana da aljanu ne?”

“Aljanu kuma? Kina ganin aljanu ne suke mata wasa da hankali?”

“Toh ban sani ba amma da abun tambaya dan akwai wata k’anwar mamar mu a k’auye da aljanu suka tak’ura mata. Itama amarya take kaman Aunty amma sai dai bata d’aura girki ba baya nuna. Ko kwana kwanon zeyi akan murhu baze ta6a nuna ba daga k’arshe seda aka kaita gun Malami akayi mata ruk’iya sannan ta samu sauk’i.”

“Subhanallah” ya furta yana shafa sajensa “I’ll figure out what to do dan ko ni na fara zaton aljanun ne nima gashi de kema kince bata sa gishiri toh taya abincin yakeyin rad’au haka?”

“A gwada nemo malami yayi mata ruk’iyan ni kaina tausayi Aunty take bani wallahi se kaga kukan da takeyi d’azu.”

“Kiga koda wasa kar ki nuna mata munyi maganan nan kinji ai ko? Bana son kowa yaji maganan daga ni sai ke, kin gane?”

“In shaa Allah Uncle Allah ya bata lafiya.”

“Ameen” da haka ya koma d’akin nasu ya zauna a gefenta hannunta ya rik’o cikin nasa a hankali yana murzawa “Kitten what’s really going on? Meyake faruwa? Why is this happening to you?” Sosai ya tausaya mata he can’t believe aljanu na son haukatar masa da ita.

Kuka sosai Amal ta sha washegari da Afzal ya hanata yi masa breakfast yasa Safiyya. Ko makaranta tak’i fita ranan tun fitan Afzal ta rufe kanta a d’aki tana kuka, se hak’uri Safiyya ke bata kaman dagaske chan tace zata shiga bayi tana ficewa taje ta kulle kanta a d’aki ta d’au paper’n da Nazeefah ta rubuta mata lambarta ta zuba tare da danna mata kira.

“Assalamu Alaikum Aunty ina kwana?”+

“Sofin gaye ya kike?”

“Lafiya k’alau Aunty ya Hindu?”

“Hindu tana gida ni na fita school ya uwar d’akinki?”

“Hmmm Aunty ina da labari mey dad’i miki.”

“Kai Sofin gaye har ta gama haukacewan ne?”

“Gashi Uncle jiya yazo d’akina yana tambayata ko meke faruwa na tsara mishi labari kaman yadda kikace inyi yanzu haka yace ze nemo malami ayi mata ruk’iya don shima ya fara zargin ko aljanun ne.”

“Kin min dau-dai shin ta sake yi masa girki?”

“Ai hanata yayi yau gata chan a d’akinta se kuka take.”

“Bravo alaiki Sofin gaye tsaraban ki na nan na tanadar miki.”

“Toh amma Aunty yanzu idan aka kira Malamin ya duba ta yace lafiya fah? Za a iya gano ni ke k’ara mata gishirin fah.”

“Inji wa? Taya za a gane ki bayan duk malaman ruk’iyan nan kud’i kawai suke so? Da mutum nada ciwo da bashida shi muddin an kaisa gun su se sun bada magani dan abasu kud’i in return saboda haka ki kwantar da hankalinki in shaa Allah baza a kama ki ba kede ki cigaba da gashi.”

“Toh Aunty.”

“Mission number one complete muddin akayi mata maganin kar ki sake 6ata mata girki mu barta nan haka se idan an kwana biyu se mu fara mission number two.”

“Ohh kar in sake sa mata gishirin?”

“Eh mana baya riga ya hanata yi mai girki ba yanzu?”

“Eh.”

“Toh kinga idan akayi mata maganin seya zammana kaman dama akwai matsalar amma an samu an magance yanzu.”

“Nagane.”

“Yauwa jeki sameta kiyita bata hak’uri idan Ya Afzal ya dawo kice d’azu ma kin ganta ita kad’ai tana suratai.”

“Toh Aunty” da haka sukayi sallama. Wani irin dad’i maras misaltuwa Nazeefah taji burinta ya cika ta haukatar da Amal ta sa Afzal ya daina cin girkinta, ita taso ace ta6in hankali ma Afzal ya soma zarginta da shi bama aljanu ba yadda za a d’auketa akaita chaan asibitin mahaukata ta fara rayuwarta ta bar mata Afzal nata amma hakan ma be 6aci ba.

****

Da Azahar Afzal ya wuce restaurant yaci abinci daga chan ya biya gida gun Ummi kallo d’aya tayi masa ta gano akwai matsala.

“Prince?”

“Ummi” ya amsa a ksalance.

“Meke faruwa?” ta tambayesa.

“Ummi it’s Amal.”

“Subhanallah lafiya dai ko?”

“Ummi I don’t know na rasa gane ta6in hankali ne yake neman kamata ko kuwa aljanu ne suke mata wasa da hankali.”

“Subhanallahi meya faru? Wani abun tayi ne?” Labarin komi ya kwashe ya bata batare da ya skipping komai ba.

“Shine baka ta6a bud’an baki ka fad’a mun ba Prince? Allah sarki Amal gata mahadacciyar Qur’ani oh! kowa da tasa jarabawan amma anya kuwa aljanu ne? Ba ta6in hankali ba?”

“Ummi I don’t know I’m totally clueless kuka take yau seta yimun breakfast amma na hanata saboda ko tayi ba iya chi zan ba banda gishiri da borkono ba abinda yake cikin girkinta yanzu.”

“Kuma ba ita take sawa ba?”

“Gashi na tambayi Safiyya tace a gabanta Amal tayi girkin bata sa gishiri ba shiyasa nake zaton ko aljanu ne.”

“Kuma gashi yarinyan tace tana ganinta tana magana ita d’ai?”

“Har sau biyu ma tace.”

“Ikon Allah kode aljanun ne toh?”

STORY CONTINUES BELOW

“Shine nima ban sani ba mu fara kaita psychiatric hospital (asibitin mahaukata) ne su duba ta ko mu fara dana gargajiyan?”

“Toh nide gani nake kaman aljanu ne amma a fara kaita asibitin idan sun kasa gane kan abun se mu dawo na gargajiyan, akwai sanannen malamin dana sani yana ruk’iya sosai zan nemesa.”

“Toh yanzu ya zan fara sanar da ita zan kaita asibitin mahaukata Ummi? Wallahi bazata amince ba bayan nan kuma gani zatayi kaman naci amanarta ne ina danganta mata ciwon hauka kuma bana son su Mami suji maganan nan se idan abu ya gagara tukun zamu sanar dasu ko ba haka ba?”

“Tabbas kayi tunani Prince tunda de yanzu Amal responsibility’n muce.”

“Toh kinga…”

“Ka san yadda zaka sanar da ita Prince ai matarka ce zata fahimce ka in shaa Allahu.”

“Toh Ummi I’ll try, please karki manta kiyi wa Malamin magana.”

“In shaa Allah Prince kuma duk abinda akwai ka kira ka sanar dani Allah ya bata lafiya.”

“Ameen bari zan koma” rakiya tayi masa sannan ta dawo ciki. Yana isa gida Safiyya tayi mishi sannu da zuwa sannan ya k’arisa d’aki inda Amal ke mik’e akan gado amma ba bacci take ba ko da taji shigowansa bata juya ta kallesa ba Sallama yayi ta amsa ciki-ciki ba tare da ta kewayo ba. Kayan jikinsa ya rage sannan ya k’arisa gefen gadon ya zauna a gefenta.

“Kitten?” Ya kirata sede bata amsa ba. “I called you twice baki d’aga ba why?”

“Ban san inda na jefar da wayan ba” ta amsa ba tare da ta kallesa ba. Hannu ya mik’a ya mik’ar da ita zaune “How’re you feeling?” Ya tambayeta.

“Kaci abinci?” Ta mayar masa tunanin da take tayi tun d’azu kenan, shin yaci abinci, mey yaci? Ya k’oshi? It pains her alot idan ta tuna Afzal baze sake cin girkinta ba yanzu, sosai zuciyarta keyi mata k’ona.

Allah sarki sosai ta basa tausayi, bata ma damu da lafiyarta ba, ita burinta kawai taji yaci abinci ne, “Kefa kin ci?” Ya tambayeta.

“Yaya I really want to cook for you koda sau d’aya ne ka barni in sake yi maka girki please Yaya I miss feeding you” ta rok’esa yayin da idanunta suka shiga cikowa da hawaye.

“Kitten please cut it out, kibar kukan haka.”

“Then allow me cook for you and feed you one last time.”

“Baby” ya ambaci sunanta had’e da rik’o hannunta cikin nasa yana murzawa a hankali “Ba kida lafiya ki bari se in kin samu sauk’i kinji? I myself miss your cooking kinsan kece best cook d’ina ko?”

“Yaya can’t you see? I’m perfectly okay wallahi lafiyata k’alau ba abinda yake damu na” kwantar da ita yayi a jikinsa yana shafa bayanta a hankali “Zamu kaiki asibiti gobe su duba ki in shaa Allah idan kika samu sauk’i se kiyi resuming normal duties naki ki cigaba da yimun girki kinji?” cike da rashin fahimta ta d’ago kanta tana kallonsa “Asibiti Habib Albi?”

“Kitten I’m so sorry-“

“No” ta furta cike da tashin hankali tare da janye jikinta daga nasa.

“Kitten please understand me-“

“No Yaya” da sauri ta janye hannunta da yake k’ok’arin rik’ewa “Mey kake nufi da hakan? Ina da hauka?” Ta tambayesa cike da d’umbun mamaki.

“No Kitten ba haka nake nufi ba” ya amsa a rud’e shima, a rayuwa ba abinda yafi tayar masa da hankali kaman yaga Amal tana kuka, da zaran yace ze rik’e hannunta se ta ja da baya.

“Ni Mahaukaciya?” Ta ambata da mamaki yayinda hawaye ke bin k’uncinta.

“Kallon mahaukaciya kake mun Yaya?”

“Kitten please-“

“Yaya..” kasa cewa komi tayi kawai ta rushe da wani irin masifaffen kuka yayinda ta mik’e da hanzari dan bar mai d’akin. Hannunta ya cafko ya kwantar da ita a jikinsa had’e da matse ta gagam wane wani na shirin k’watar masa ita. Kokowa take sosai ya saketa amma yak’i hak’uri ya ta bata yana shafa bayanta a hankali har seda ya sauk’ar da temper’nta. A hankali ya d’agota yana share mata hawayen nata “Kitten please understand me bawai cewa nayi kina da hauka ba, bazan ta6a kwatanta ki da mahaukaciya ba but contrary to abubuwan da suke faruwa bakiya tunanin ko akwai wata matsala?”

STORY CONTINUES BELOW

“Yaya ashe Allah ze kawo ranan da zaka yi mun kallon mahaukaciya?” Ta tambayesa hawaye na bin k’uncinta.

“Kitten I will never refer to you as that kema kin sani I love you and I only want the best for you, dan za ki ga psychiatrist doctor (likitan mahaukata) bawai hakan na nufin kinada hauka bane, ze iya yuwuwa wani matsalan ne daban yake damun ki psychologically ko stress ko makamancin hakan.”

“There is no stress Yaya and I’m not losing my mind ni ba mahaukaciya bace kana tsammanin zansa gishiri acikin girki ba tare da na san nayi hakan bane? I told you ni bani kesa gishiri da attarugu ba, ba ni bace!” Sosai ranta ya 6aci taya upon all people Afzal baze yarda da ita ba? Taya za’a ce mijinta tilo yana yi mata kallon mak’aryaciya kuma mahaukaciya? Cikin tsananin kuka tace, “I thought you love me Yaya, I thought you trust and believe in me.”

“Of course I do Darling, I love you with every burning fiber in my soul and I do trust and believe in you than I do myself.”

“No Yaya inda har kana nufin abinda ka fad’a da baza ka fara tunanin kaini gun likitan mahaukata ba, da zaka yarda dani idan nace maka bani kesa gishiri da borkono cikin girkin ka ba.”

“I know Kitten nasan ba ke kike sawa ba shiyasa na fara zargin ko aljanu ne suke miki wasa da hankali.”

“Aljanu? Yanzu kuma mey kallon iskokai kake mun Yaya? Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” juyawa tayi da niyyan bar mai d’akin bata ma jin zata iya yi masa magana. Da sauri ya sha gabanta “Kitten please ki fahimceni ki sani lafiya nake nema miki wallahi na gaji da ganinki haka cikin k’unci da kuka kullum, kiyi hak’uri ki bari a magance miki wannan matsala please.”

“Ni bana tattare da aljanu I know how I feel saboda haka ba wanda zeyi mun ruk’iya, nasan kaina kuma na dogara da addu’o’in da nakeyi.”

“Kitten bawai ina jayayya da hakan bane ni kaina sheda ne game da yadda bakiya wasa da addu’o’in kariyan nan I’m aware of everything.”

“Toh mey kake nufi Yaya? Kallon mey iskokai da ta6in hankali fa kake mun how do you expect me to feel and react?”

“Darling I’m sorry but I’m just worried, ke da bakinki kika ce bake ke sa gishiri da borkonon nan ba kuma na amince da hakan I trust you Kitten amma toh wa yake sawa? Bakiya tunanin akwai wata 6oyayyan al’amari? Kuma baza mu ta6a iya gano inda matsalar take ba bale a magance miki se har idan kin amince kin bada had’in kai Kitten. I promise no harm will come to you, I’ve got you Baby, ba wanda yace kina da ta6in hankali I just need to find out what’s really going on. Please calm down everything is going to be alright in shaa Allah okay?” Ya k’are yana matso da ita kusa da shi. Cike da dabara ya kwantar da kanta a k’irjinsa yana shafa kanta “I love you so much” ya furta mata, a hankali yaji hannayenta a bayansa tana hugging nasa back “I love you too” ta furta. Washegari Afzal be fita office ba, wanka sukayi tsaf tare suka shirya, da kansa ya had’a musu breakfast sannan suka wuce psychiatric hospital inda aka duba Amal akayi mata gwaji da dama akan washegari su dawo su kar6i sakamako.

Washegari Afzal ya koma ya amshi results d’in shi kad’ai kasancewar daga office ya biya wajen sede da mamaki sakamakon ya nuna ba abinda yake damun Amal, hankalinta dai-dai yake dana mutane ba wata matsala. Hakan ba k’aramin d’aure wa Afzal kai yayi ba don haka kawai ya yanke hukuncin aljanu ne toh sukeyi mata wasa da hankali nan take ya kira Ummi yayi mata bayani dama ta riga tayi magana da Malamin yace koda yaushe suka shirya suje yana jiransu. Address kawai ta tura masa.

Gida gun Amal ya koma yaci ace ya koma gun Nazeefah dake kwanan Amal ya k’are amma baze iya barin Amal cikin wannan yanayi da iska suke wasa da hankalinta haka ba har se idan ya samo mata lafiya. Nazeefar yayi niyyan kira ya sanar da ita halin da ake ciki se ya sha’afa. Itako chan a gidanta ta gama girki ta gama komi jiran zuwansa kawai take amma shiru gashi har shida da rabi yayi. Jin shirun yayi yawa gashi be kirata ya sanar da ita dalilin hakan ba ta d’au waya kawai ta kirasa a karo na farko ya d’aga suka gaisa.

“Kin jini shiru ko?”

STORY CONTINUES BELOW

“Eh Ya Rouhi lafiya?”

“Amal ce bataji dad’i ba I’m afraid I can’t make it today ina fatan hakan ba matsala.”

“Allah sarki meke damunta?”

“Ermm… ermmm zazza6i ce” yayi mata k’arya haka kawai yaji baya son ya fayyace mata gaskiyan al’amarin. Amal na kwance kan cinyansa tana sauraransu.

“Ayyah ka gaisheta da jiki da Allah, Allah k’ara mata lafiya zan kirata in gaisheta.”

“Ameen in shaa Allah ba wata matsala ko?”

“Ba komai.”

“Toh seda safe I’ll call you tomorrow.”

“Alright take care” wata mak’irar murmushi ta sakar yayin da ta katse wayar. “Ai kad’an ka ga se zaman gidan chan ya gagareka you’ll see.”

“Nazeefah na gaisheki” ya sanar da Amal had’e da sanya hannunsa cikin gashin kanta yana massaging mata cikin kai a hankali, kai zalla ta gyad’a masa. “Kina jin yunwa?” Nan ma kai ta kad’a a hankali.

“I called Ummi earlier batun Malamin tace ta riga tayi mai magana so she sent me his address gobe zamu kaiki baki da wani test a school ai ko?”

“Babu” ta amsa ciki-ciki. Wace irin msuiba ce wannan? Tana ji tana gani ana dangata mata ciwon aljanu ciwon da tasan ba ta da shi. Kan nata ya cigaba da massaging mata chan ya dafa musu indomie bayan sun gama ci sukayi wanka sukayi sallah suka tofe addu’an bacci sannan suka kwanta. Washegari da yamma bayan sallan La’asar suka wuce gidan Malamin. A mota ya barota ya k’arisa ciki bayan sun gaisa yayi wa Malamin bayanin abinda yake damunta ciki harda ce masa da Safiyya tayi akan Amal ita kad’ai tana magana ya kuma buk’acesa da koda ya shigo da Amal d’in kar yayi maganan komai a gabanta. Bayan Malamin ya fahimce shi ya koma ya shigo da Amal karatu Malamin ya shiga yi mata amma ba alamun komai a tattare da ita, bayan ya k’are karatun yayi mata hayak’i nan ma ko alaman aljanu babu.

“Gaskiya bata tattare da iska sede ze iya yuwuwa shafanta sukeyi su barta amma bawai sun shiga jikinta ba.”

“Toh yanzu ya kenan Malam?” Afzal ya tambaya.

“Sede ince ta dage da addu’a ta kuma rage kalle-kalle da fita da kai a bud’e. Zan baku turaren almisky tana amfani da shi tana kuma shan man hul6a ta na karatun Al~Qur’ani sosai in shaa Allahu iskokan zasuyi nesa da ita.”

“Tana yi sosai wallahi Malam mun gode in shaa Allah zata kiyaye duka ababen da ka irgon.”

Almiskin ya d’iba musu da man hul6an Afzal ya biya kud’in. Tun shigansu mota har suka dawo gida Amal bata mai magana ba. Waje ya fita ya kira Ummi ya sanar da ita abinda Malamin yace.

“Ai Malamin ya iya aiki da ikon Allah zata samu sauk’i kuma shi ba ta kud’i yake ba kaga idan wani ne yanzu ya rink’a raina mana wayo kenan yana mana k’arya akan lallai akwai aljanun a jikinta ayita ruk’iya ana kashe kud’i ana bata wuya.”

“Hakane kam wallahi thank you so much Ummi.”

“Ya Amal d’in toh?”

“Lafiyarta.”

“Tana kusa ne ka had’amu?”

“Eh toh” nan ya bud’e k’ofan ya dawo ciki ya k’arisa ciki. “Kitten?” Ya kirata.

STORY CONTINUES BELOW

“Uhmm?” Ta kewayo tana kallonsa

“Ga Ummi tana son ku gaisa” ba gardama ta amsa suka gaisa sannan ta miyar masa. Ya so ya sake kwana mata amma baya son ya shiga hak’k’in Nazeefah dayawa dan haka ya shiga tattare abubuwan da ze buk’ata. Yana gamawa ya kewayo kan Amal dake mik’e kan gado “Kitten zan koma wajen Nazeefah” ya sanar da ita yana takowa inda take hannunsa ya mik’a mata kamar wacce bazata kama ba tasa nata ciki a nitse ya mik’ar da ita yana shafa fuskanta a hankali.

“Kina amfani da turaren kinji? Man hul6an kuma kina sha safe da yamma kaman yadda Malamin ya fad’a nasan kina karatun Al~Qur’ani sosai ba sena ce kiyi ba Allah baki lafiya Sweetheart I love you so much.” Kai ta gyad’a masa a hankali “Muje in raka ka” da sauri ya rik’o ta kafin ta ku6uta daga hannunsa yana mey zagaye hannayensa a ‘yar kunkuminta.

“Where’s my cheerful and loving Kitten please tell her I miss her so much and that I want her back” yayi maganan yana shafa kan lips nata a hankali da babban yatsansa. “Allah baki lafiya Kitten I can’t wait for you to get better, I love you so much.”

“I love you too Habib Albi” ta sanar da shi a hankali ya mik’a yayi owning lips nata kissing her gently and taking her fears away seda nishinta ya kusan d’aukewa ya saketa ya shiga shafa fuskanta a hankali “Take care of yourself okay? Duk abinda kike buk’ata ki fad’awa drivernki yaje ya siya miki idan kuma Safiyya zata iya seta girka miki amma kar ki sakeyin girki se kin samu sauk’i kinji?” kai zalla ta gyad’a masa. “Na ajiye miki kud’inki a gaban mirror ki kwanta ki d’an huta kafin Maghrib Sena dawo.”

“Thank you bara in raka ka.”

“A’a kiyi zaman ki I can manage” peck ya sauk’e mata akan goshi sannan ya fice. Koda ya koma gun Nazeefah hankalinsa gabad’aya na akan Amal ne minti minti yake d’aukan waya yana kirarta yana tambayarta ko lafiya se yanzu yake regretting meya hanasa amsan lamban Safiyya da ita zena kira yana tambaya ko lafiya baya son abin da tak’urawa Amal tasa, sosai yake missing nata ji yake shima kaman ba shida lafiya. He can’t explain how much he’s missing her giggles, laughs and smiles. Suna zaune a d’aki Nazeefah na masa tausa tayi gyaran murya “Ya Rouni?” ta kirasa cikin wani irin salo.

“Yes Rabba’atul Bait?”

“What’s wrong tun shigowanka jiya na ganka wani iri meke damunka?”

Be 6oye mata ba ya sanar da ita gaskiyan al’amarin “It’s Amal Rabba’atul Bait I’m worried about her.”

“Allah sarki zata samu sauk’i in shaa Allah muna kan mata addu’a.”

“Thank you Rabba’atul Bait.”

“Don’t mention love amma ciwon nata zazza6i ne kawai?”

“Wani abu ne?”

“A’a d’azu dana kirata ne take cemun wai abun nata harda iska-iska haka.”

“Ita da bakinta?”

“Eh” ta jaddada masa dukda kuwa tasan k’arya takeyi basu ma yi waya da Amal ba yau bale har wai Amal ya sanar da ita akan iskokai ne suke damunta.

“Malamin yace basu shige ta ba kawai sun shafeta ne amma ya bamu magani in shaa Allah zata samu sauk’i.”

“Allah sarki Amal, shin bata karatun Al~Qur’ani ne? Kasan ance aljanu basa kama me yawaita karatun Al~Qur’ani.”

STORY CONTINUES BELOW

“Tana yi kinsan shi jarabawa kowa da irin nasa, Amal mahaddaciyar Al~Qur’ani ce kullum seta d’au Qur’ani tayi karatu I guess wannan itace jarabawarta.” Haushi taji sosai Amal na da haddan izu sittin akanta ita tana nan tana fama da izu goman k’asa. Taya bazata tsani Amal ba bayan ta ko ina seta nuna tana son ta k’ureta.

“Allah sarki Allah bata lafiya toh” ta fad’a ba don tana so ba tana k’wak’ulo murmushin dole.

“Ameen” ya amsa.

****

Duk da kwanan Nazeefah ne hakan bai hana Afzal zuwa duban Amal da safe kullum kafin ya wuce office, da kwanan ta ya zagayo kuwa komi shi yake k’ok’arin yi mata, ba k’aramin kula da ita yake ba. Da yamma idan ya dawo daga office zasu d’au Qur’ani suyita karatu har zuwa Magriba. Tun ranan da suka dawo daga gun Malamin Afzal be sake gane kan Amal ba. Gabad’aya yanayinta ya canza a gidan sa6anin yadda suke zama suyi hira suyi dariya yanzu kam jugum sede shine ma yayita zuba ita befi tana amsa sa da eh ko a’a ba. Hakan ba k’aramin damun Afzal yake ba he can’t explain how much he’s missing her.

Yau sati biyu kenan tun dawowansu daga gun Malamin, cikin ikon Allah ta shiga sake sakewa da Afzal ta fara yi mai hira har suka koma zama yadda suke da. A hankali a hankali suka fara shiga kitchen tare suna yin girki har yazo ya fara barinta tanayi ita kad’ai. Afzal baze iya kwatanta irin murna da farin cikin da ya tsinta kansa aciki ba da Amal ta soma yin girki ba matsala yanzu, Ummi ya soma kira ya sanar da ita. A kullum son Amal dad’a k’aruwa yake a birnin zuciyansa, tabbas baze iya rayuwa ba ita ba.

Yau ya na tashi daga office ya wuce gida straight he can’t wait ya iso gida ya samu Kitten tasa. Fresh flowers ya tsaya ya saya mata a florist shop sannan ya k’arisa gida. Sede sa6anin kullum yau Kitten tasa bata fito ta tare sa ba k’arisawa ciki yayi amma Safiyya kad’ai ya tarar bayan ta mai sannu da zuwa ya tambayeta ko ina Amal take ta ce mai tana d’aki. D’akin nasu ya k’arisa sede be ganta ciki ba, kasa kunnen da zeyi yaji splashes na ruwa a bayan gidan don haka yayi knocking bisa k’ofan “Kitten I’m home.”

“Welcome home Habib Albi.”

“Mey kikeyi wanka?”

“Eh” ta amsa.

“In shigo?”

“Ka shigo Habib Albi” ta amsa tana murmushi, kayan jikinsa ya rage ya d’aura towel sannan ya d’au flower’n ya shiga bayin. “Here this’s for my adorable Kitten.”

“Awwn thank you Habib Albi” tace tare da amsa “I love orchids” ta sanar da shi “Don’t mention Love, matsa min toh in shiga” batayi gardama ba ta gyara masa ya shiga ya zauna had’e da riginginar da ita a jikinsa. Wasa suka tayi cikin tub d’in k’arshe suka wanke jikinsu suka d’aura alwala sannan suka fito. Sosai yaji dad’in kwana biyun da sukayi tare ba k’arya yayi missing delicious nata baze fasa yima Allah godiya ba da ya bawa Kitten nasa lafiya. Musamman ya koma gun Malamin da yayi musu maganin ya mishi kyautan kud’i. Kaman kar ya tafi yau da kwanansa ya k’are, yadda ta saba raka sa haka tayi ta kaisa har gun mota inda ya shiga kissing nata awajen be saketa ba seda ya tand’e jan bakin data shafan tas sannan ya sallameta ta dawo ciki. Yana isa gidan Nazeefah ta taresa da wani hot kiss nata itama bayan sun k’arisa d’aki seya karanci yanayinta ya sauya a lokaci guda.

“Rabba’atul Bait lafiya?”

“Ai kai zan tambaya Ya Rouhi” ta amsa tana turo baki

“Da nayi me Sweetheart?”

“Ba wani Sweetheart d’innan ai nasan inda ka ajiye ni.”

STORY CONTINUES BELOW

“Haba Darling meya faru haka?” tasowa yayi daga gaban mirron ya k’arisa inda take had’e da zauna a gefenta.

“Gaya mun waya ta6a mun Rabba’atul Bait d’ina.”

“Ba amaryarka bace.”

“Amal?” Kai ta gyad’a cike da shagwa6a.

“Me kuma tayi?”

“Cemin tayi kullm ka fita seka taho mata da flower ni dai-dai da RANA D’AYA ko yashi baka ta6a ibowa kace gashi Rabba’atul Bait wannan naki ne shin kana ma sona kuwa Ya Rouhi?” Mamaki da kunya yaji duka a lokaci d’aya. Be ta6a tsammanin hakan daga gun Amal ba. Wani irin abin kunya take shirin yi masa haka? Taya zata na fad’awa Nazeefah abinda yake mata? Meye riban hakan?

“Bayan nan kuma tace sede baka je gida mata ba baka bari ta zauna a ko ina se a kan cinyanka, ko abinci akan plate d’aya kuke ci ni duk baka mun ko d’aya Ya Rouhi” ta sanar da shi kar kusha mamaki komi nan Safiyya ne ke fad’a mata. Afzal baze iya kwatanta irin tsananin kunyan da yaji ba yayinda ya kasa daina mamakin dalilin da zai sa Amal tayi masa haka, shin mey ya buga mata kai? So take ta 6ata tsakaninsa da Nazeefah?

“Rabba’atul Bait I’m really sorry” ya furta cike da disappointment, a hankali ya d’agata ya zaunar da ita kan cinyoyinsa.

“Ba komai dama nasan kafi son Amal akaina ai.”

“Please don’t you ever say that nasan nayi kuskure amma kiyi hak’uri I’ll make it up to you in shaa Allah I promise.” Hannayenta ta zagaye a wuyansa “Can I count on you?”

“In shaa Allah Rabba’atul Bait, I love you so very much.”

“I love you more Baby” ta amsa fuskanta ya shiga bi yana kissing har seda ya kai kan lips nata.

***

Bayan sallan isha ya d’auketa a mota suka je suka ci abinci a waje daga chan suka wuce 3G inda ta kwashi jakukkuna guda uku masu kyau, tana jiran taji yace bari ya d’auka wa Amal kaman yadda ya saba fad’a ta ji yayi shiru yau kud’in kawai ya biya suka fito. Ai kuwa idan haka ne plan nata ya fara aiki kenan, da alama bai ji dad’in abinda tace masa Amal tayi bane shiyasa ko jakar ma yak’i sai mata, ai ko idan haka ne ta ringa 6ata Amal a gabansa kenan se tasa ta fita masa a rai gabad’aya. Zata sa Safiyya ta musu ido sosai tana d’auko mata rahoto.

***

Kamar yadda ta d’au alk’awari hakan ta cigaba da 6ata Amal gaban Afzal, duk abinda yayi ma Amal se Safiyya ta kwashe ta fad’a mata itako idan kwanan ta ya zagayo seta maraice fuska tace ai gashi-gashi abinda Amal ta kirata ta fad’a mata. Sosai abun yake k’ona ma Afzal rai be ta6a sanin Amal da halin nan ba se yanzu shin meye ribanta na fad’awa Nazeefah abubuwn da yakeyi mata? Sabida ta 6ata tsakaninsu ne take hakan kokuwa dan ta nuna wa Nazeefah a fili baya adalci a tsakaninsu? A kullum 6aci ransa yake idan Nazeefah ta irga masa abubuwan da yayi ma Amal wanda beyi mata ba amma dai-dai da RANA D’AYA be ta6a tunkarar Amal da maganan ba. A tunaninsa da kanta zata gano abinda takeyi ba dai-dai bane ta daina amma ina abun se worse yakeyi ko bathroom slippers ya sai mata be sai wa Nazeefah ba seya ji a bakin Nazeefah sosai abin ya isheshi har ya zamma ko tsinke ya daina saiwa Amal yana kai mata idan har ya sai mata abu to ya sai wa Nazeefah ne amma special treatment kam ya daina bata.

****

Yau ranan ya kewayo kwanan Amal wanka tayi tasha kwalya tasa sabon d’inki ba k’aramin kyau tayi ba sannan tayi zaman jiransa se after six ya iso shida kullum 5:30 ya shigo. Tun daga bakin parking lot taje ta taresa sede kaman zuwansa na biyu da suka wuce yau d’inma haka ya shigo fuskansa a d’aure, d’aure fuskan yau d’inma yafi na kowanne, ko attempting kissing nasa da ta gwada yi se taga yayi dodging abinda be ta6ayi ba shin meke faruwa? Jakansa ta gwada amsa nan ma ya hanata ya wuce gaba, cike da mamaki ta bi bayansa suka k’arisa ciki.

STORY CONTINUES BELOW

“Ya office?” ta tambayesa bayan sun shigo d’akinsu.

“Lafiya” ya amsa sama-sama ko kallonta beyi ba. Toh me tayi yake shasshareta haka?

“In sirka maka ruwa ko?” Ta tambayesa.

“Yanzun na yi a chan gida karki damu.”

“Toh muyi tare” ta sake fad’a duk don ya amince. “Maybe next time” ya amsa nan ma ko kallonta beyi ba. Wow! Shin meke faruwa? Ta tambayi kanta.

“Toh abinci fah?” Ta sake tambayansa a hankali, sosai jikinta ya mutu da irin short-short answers da yake bata.

“Nazeefah ta bani” ya amsata, amsan da a iya zamansu be ta6a bata ba.

“Habib Albi amma kullum fa kana ci idan ka dawo.”

“Bana jin yunwa Amal” taji ya kirata gatsau da sunanta. Tirk’ashi! Bata sake yi masa magana ba se chan wajajen k’arfe tara. A tunaninta wai ko stress ne daga office yake sanya sa yin abinda yake yi bari ta barsa ya huta. Bayan ta k’are karatun Al~Qur’ani ta d’an ta6a na bokon ta fito ta sami Afzal dake zaune a parlour yana kan tattara documents nasa yana sanya su cikin briefcase. K’arisawa tayi ta zauna akan cinyansa.

“Sekin yi hak’uri kin tashi na buge k’afa na d’azu zafi yake mun” yayi mata k’arya.

“Subhanallahi! Sannu shine baka sanar dani ba? Mu shafa maka man zafi ne?”

“Karki damu I’ll be fine” da haka ya sauk’eta.

“Baka ci abinci ba Habib Albi.”

“Bana jin yunwa.”

“Kana nufin yau abinci na zeyi kwante kenan?”

“I’m sorry but I guess yes excuse me” yana kaiwa nan ya d’aga briefcase nasa ya koma d’aki. Mamaki ne sosai ya cika Amal shin mey tayi wa Afzal yake shareta haka? A iya saninta de bata mai komai ba meyasa yake shareta haka toh? Safiyya ta kira ta tayata suka juye abincin suka sa a fridge sannan ta bi Afzal ta koma d’akin inda ta tarar da shi yana tu6e kaya da alama wanka zeyi. “Habib Albi wanka zakayi?” Ta tambayesa inda ya gyad’a mata kai zalla.

“Muyi tare?”

“Bacci nakeji Amal ki bari ko gobe” har cikin ranta taji zafin yadda yayi rejecting nata, ta rasa mey tayi yake yi mata haka amma tabbas tasan da akwai abu a k’asa amma bazata masa magana nan take ba zata yi masa uzuri halan wani abun ne yake damunsa. Haka tana ganinsa ya wuce bayin ya watsa ruwan ya fito ya sanya boxers nasa, bata ce da shi komai ba ta mik’e ta shiga itama fitowan da zatayi ta gansa da coke da cookies yana ci so ashe yana jin yunwa amma yayi mata k’arya wai baya ji don kar ya ci girkin ta. Mey tayi masa yanzu da baze ci girkinta ba? Hmm duk yadda ranta ya 6aci da kuma yadda taso tambayan sa dalilin da yasa yakeyi mata haka kwana biyu ta danne zuciyarta ta fasa. Wani shara-sharan rigan baccinta ta sanya tana ta zirga-zirga a d’akin duk don ta karkatar mai da hankali amma ko d’aga ido ya kalleta beyi ba bale yasan tana yi. Yana gama cinye cookies nasa yayi disposing goran da ledan ya haye gado ya kwanta had’e da juya mata baya. Addu’o’in baccinta ta tofe sannan ta samesa akan gadon ta gangaro da pillonta kusa da nasa inda yayi shiru kaman be jita ba.

“Habib Albi?” Ta kirasa shiru yayi kaman baya jinta. “Habib Albi I miss you” ta sanar da shi. “Please turn around” ta buk’acesa amma ko ya motsa bale tasan yanayi. A rayuwa baya son munafikin mutum mey yayi zafi da zata na kiran Nazeefah tana yi mata gulman abubuwan da yakeyi mata se yazo nan kuma ta tsaya tana maraice fuska tana acting kaman wata salihar k’warai.

STORY CONTINUES BELOW

Amal ta kasa bacci ranan se tunanin dalilin da zaisa Afzal yana shareta haka ta kwana tana yi, be ta6a dawowa be nemeta ba se wannan karan gashi ko da ta gwada nemansan ma yak’i ya kulata kuma sarai tasan ba bacci yakeyi ba lokacin.

Washegari ko da ta gaishesa sama-sama ya amsa, yana shiga bayi don yin wanka ta wuce kitchen ta shiga had’a masa breakfast sede da ya fito ko kallon kulolin nata beyi ba bale yayi tunanin ci. Yana cikin had’a black tea se gata ta fito don serving nasa.

“Karki damu bazan ci ba.”

“Bazaka ci ba kuma Habib Albi?”

“Eh” ya jaddada mata.

“Toh mey kakeso in girka maka?”

“Karki damu ina Safiyya? Safiyya!” Ya k’wala mata kira nan da nan ta fito daga d’akinta ta gaishesa sannan Amal.

“Zo ki soya mun k’wai biyu kiyi sauri I’m already late” Sandarewa Amal tayi wajen ko k’ala ta kasa cewa yayinda zuciyanta yakeyi mata k’ona sosai wato ya gwammace Safiyya ta soya masa k’wai da yaci girkinta? Hmm. Haka ba yadda iya ta koma d’aki ji take kaman tayi kuka.

Gashi tun da ya fita office ranan be dawo gida ba har wajajen tara na dare. Ba irin kiran duniyan da Amal batayi masa ba amma yana ganin calls d’in yak’i d’agawa a rayuwa baya son munafikin mutum taya zata na d’iban duk abinda sukayi tana kai wa Nazeefah kuma ya tabbata ba k’arya Nazeefah takeyi ba idan ba a bakinta ba a ina Nazeefah zata na jin dukkan abubuwan da suke faruwa idan yaje mata kwana? Ace wai har kayan abincin da ya siya ya kaiwa su Papi seda ta kira Nazeefah ta fad’a mata, dan kawai yana kyautata mata da iyayenta shikenan seta shiga neman 6ata tsakaninsa da uwar gidansa tana sanya sa looking maras adalci a fili, yanzu mey ze faru idan Nazeefah taje ta fad’awa iyayenta har magana ya kai kunnen Abba? Sam be santa da wannan munafikin hali ba kode k’awaye ne suke zigata? Toh ta cigaba shi de baze yi mata magana ba.

Amal na zaune a parlour tana jiran dawowan Afzal se taji k’aran gate. Agogo ta duba taga ana neman goma ko meya rik’esa se war haka yake zuwa gida? Yet she’s still grateful Allah ya dawo mata da shi gida lafiya. Da hanzari ta mik’e Afzal na bud’e k’ofar ta ruga taje tayi hugging nasa.

“Habib Albi where’ve you been? I’ve been trying your number but you weren’t picking up wallahi hankalina ya matuk’ar tashi.” Cike da tak’ura ya janyeta daga jikinsa “Meeting muka yi se yanzu muka tashi ni kuma ban sake duba waya na ba” yayi mata k’arya bayan gidansu Sultan yaje ya yini throughout.

“Bakada lafiya ne?” Ta tambaya tana shafa fuskansa.

“I’m just stressed out lemmi take a shower” yayi maganan yana sauk’e hannunta daga fuskansa.

“Kawo jakan naka in rik’e maka.”

“Bari karki damu” nan ya wuce ta ya k’arasa d’akin ji tayi tamkar tayi kuka bata ma iya ta bisa d’akin ba a parlourn ta cigaba da zama yayinda tunani ya mamaye mata k’wak’walwa ji take kaman tayi kuka ta rasa mey tayi masa yake bata wannan attitude. Se chan ta iya ta mik’e ta bisa d’akin. A kwance ta tarar da shi yana jin motsinta ya 6oye wayansa da yake ta faman chatting da Nazeefah k’ark’ashin pillow yana pretending kaman yana bacci. “Habib Albi?” Ta kirasa shiru yayi yak’i amsawa a hankali yakejin takunta har lokacin da ta k’ariso kan gadon ta zaune gefensa.

“Habib Albi bazaka ci abinci ba?” Nan ma shiru yayi mata sarai kuma tasan ba bacci yake ba. Hijabinta ta cire ta kwanta a d’an space dake gabansa had’e da kwantar da kanta a k’irjinsa tana mey zagaye hannunta kan cikinsa sannan ta ja musu bargo ta rufesu. “Goodnight Habib Albi I love you” ta furta a hankali bacci me wuya ya d’auketa chan tukuna shima Afzal baccin ya d’aukesa.

Kasancewar tana da morning lectures washegari se suka gama shiri kusan a tare, dukda cewan se shareta Afzal yake. Yau kwata-kwata ma k’in karyawa yayi wai ze fita da azumi. Gano itama school zata se yayi mata k’arya wai bazeyi ya kaita ba yana da meeting driver ya kaita kawai. Kud’in makarantar ta ya ajye mata ya fice ko kiss daya saba yi mata beyi ba yau haka ma jiya. Na matuk’a hankalin Amal ya tashi ta rasa mey tayi Afzal yake yi mata haka, Maamah ce ta karanci yanayinta a makaranta ta tambayeta ko lafiya.

“Babu” ta amsa.

“Taya zakice babu Amal? Tun d’azu fa na lura banda tunani ba a inda kike tayi mey ne?”

“Maamah it’s Yaya.”

“What about him.”

“Wallahi ni kaina ban sani ba, na rasa gane meke damunsa kusan sati kenan yau idan yazo baya sakewa dani seda yata d’aura mun fuska ko girki na baya son chi d’an tsaraban daya saba siyo mun idan ze dawo gida ma ya daina I don’t know why.”

“Subhanallahi Ya Afzal d’in?”

“Wallahi aka ce mun Yaya zemin haka wataran bazan yarda ba kinga tun da ya fita office jiya be dawo ba se kusan goman dare nasan sarai ba wani meeting da sukayi k’arya yake mun gashi ba kiran duniyan da ban masa ba haka yata ignoring calls d’ina maganan da nake miki haka yanzu ko nema na bayayi.”

“Ikon Allah this’s serious toh ke mey kikayi masa? Am very sure Ya Afzal baze fara shareki haka kawai ba dole da akwai sila.”

“Wallahi ban yi masa komai ba Maamah I can’t take this anymore bana jin dad’in yadda Yaya yake fushi da ni haka wallahi ko karatu na kasa yi jiya gashi muna da test gobe I can’t stop thinking about him, I miss him so much bazan iya rayuwa ba shi ba” ta k’are maganan idanunta na cikowa da hawaye.

“Ke kuwa kar kiyi kuka mana” Maamah tayi maganan tana kwantar da ita a jikinta “Yi hak’uri don’t cry komi mey wuce wa ne.”

“Har zuwa yaushe toh Maamah?”

“Kiga toh kiyi confronting nasa mana ki tambayesa mey kikayi yake shareki haka talk to him Amal silence is never a solution.”

“Maamah bana son hakan ya 6ata masa rai.”

“Toh haka zaku cigaba da zama ne? Har zuwa yaushe? Kiyi masa magana dole da akwai abu a k’asa tunda shi yak’i yayi confronting naki ai ke se kiyi hala wani laifin kikayi masa baki sani ba.”

“Bazan iya ba mey zan fara ce masa? Bana son yaga kaman rashin kunya nake shirin yi masa I respect him alot.”

“Ai ba rashin kunya aka ce kiyi masa ba Amal cike da kissa zaki tambayesa idan laifi kikayi masa ya yafe miki da haka har ze sanar dake abinda kikayi masa seku daidaita tsakaninku.”

“Okay I’ll try.”

“Yauwa yanzu tashi muje muyi karatu nasan idan kika je gida ba iyawa zakiyi ba in shaa Allah everything will be fine.”

Se yamma Amal ta dawo gida bayan sun k’are karatu da Maamah. Driver na sauk’eta ta zarce d’akinsu inda ta tarar da Afzal yana shirin komawa gun Nazeefah ko sannu da zuwa beyi mata ba hasali yi ma yayi tamkar be ganta ba. Itace tayi gyaran murya ta gaishesa tukun ya amsa sama-sama.
“Zan koma gida gun Nazeefah ga kud’inki ajiye a gaban mirror” ya sanar da ita.
“Habib Albi tun yanzu zaka tafi?” Ta tambayesa tana mey duban agogo dududu 5:17 ne amma yake zancen nan bayan se pass 6 yake tafiya kullum.
“Eh wani abu ne?”
“Habib Albi ko ka mance da alk’awarin da kayi mun?”
“Na mey fa?”
“Kace kafin ka tafi zamuyi wanka tare I miss bathing with you Habib Albi, I really do” tayi admitting abun tausayi. Kau da kansa yayi gudun kar tausayinta ya kama sa.
“Nata jiranki baki dawo ba Amal ni kuma sauri nake maybe next time.”
“Abinci fa kaci? Nasa Safiyya ta maka microwaving sauce d’in ta dafa maka white rice tayi?”
“A k’oshe nake karki damu na wuce.”
“Yaya” ta kira sunansa da sauri lokacinda ya shiga takawa chak ya tsaya had’e da kewayowa.
“Wani abu ne?” So take tayi masa magana kaman yadda Maamah tace da ita amma inaa bata jin zata iya, mugun nauyinsa takeji bata son a sanadin hakan yaga kaman rashin kunya take son yi masa don haka kawai tayi shiru. “Sauri nake” ya sanar da ita.
“Ermm nace Allah dawo da kai lafiya ka gaishe da Nazeefah idan ka isa.”
“Kaman dagaske” ya furta chan ciki-ciki.
“Na’am?” Ta tambaya kasancewar bata jisa da kyau ba.
“Nace naji” da haka ya fice Allah kare Safiyya dake sharan parlour tayi mishi sannan ya k’arisa.
Safiyya na ganin fitansa tayi hanzari ta kammala sharan nata da wuri ta wuce d’akinta inda tasa key ta danna wa Nazeefah kira bayan sun gaisa take ce mata, “Aunty bazaki amince da abinda nake shirin fad’a miki ba.”
“Mene meya faru?”
“Hmm yanzun Uncle ya bar gida toh kafin ya fito ina cikin share corridon d’akinsu naji su suna magana da Aunty.”
“Wai mey suke cewa?”
“Nide ban gane kan zancen nasu ba amma naji tana ce masa wai yayi mata alk’awarin zasuyi wanka tare se gashi kafin ta dawo daga makaranta har yayi wankansa ya gama shiri.”
“Wanka tare?!” Nazeefah ta tambaya da d’umbun mamaki “Wanka tare de?” Ta sake nanatawa yayinda ta kasa amincewa da hakan.
“Wallahi Aunty.”
“Kaiiii inaaaa! Baki ji su da kyau ba, wannan k’arya ne.”
“Wallahi na jisu da kyau Aunty kuma daman tun ba yau ba ina zaton hakan dan akwai ranan da abokin Uncle yazo Uncle Sultan se yace inje inyi ma Uncle magana toh dana k’arisa d’akin nasu sena tarar da k’ofan a bud’e nayita sallama amman shiru chan dana kasa kunne najiyo hayaniyansu acikin bayin.”
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un wallahi Amal mak’ira ce, shegiya ‘yar asiri toh dan ubanta bazeyi wankan ba kiji mun karuwanci fah! Wato har wanka ma sukeyi tare? Chab!”
“Hmm wallahi ko amma kuma kinsan tun dawowan Uncle wannan karan ko fita sau d’aya basuyi ba? Jiya kanma da tayi masa breakfast k’in ci yayi yace wai nice zan yi masa baya son nata. Bayan nan zama da sukeyi a parlour suyi kallo ma basuyi yanzu gashi banda d’ad’d’aure mata fuska ba abinda yakeyi yau tana da makaranta da safe amma yak’i kaita sa6anin kullum yace se de driver ya kaita shi yana da gun da zasa. Maganan da nake miki yanzu ko tsinke ban ga ya siyo mata ba tun zuwan sannan.”
STORY CONTINUES BELOW
“Ai kibari kad’an ta gani da izinin Allah se Ya Afzal ya tsani taka k’afa acikin gidanta kede kiyi k’ok’ari ki sato min littafin makarantar ta guda d’aya mu samu copy na handwriting nata, zata gani ba har wanka sukeyi ba? Allah kawo shi gida.”
“Zanyi k’ok’ari in samo miki bari in gudu ina kan aiki.”
“Jeki Safiyya aikin ki na kyau se anjima.”
“Toh se anjima” da haka sukayi sallama.
Fresh flowers Afzal ya tsaya ya amsa mata a florist shop sannan ya k’arisa sede har ya shigo parlourn bata mik’e tayi masa sannu da zuwa ba ko sallamansa ma k’in amsawa tayi. Da mamaki kwance a fuskansa ya k’arisa kan kujerar da take zaune ya zauna daga gefe.
“Rabba’atul Bait I’m home” ya sanar da ita.
“Sannu da zuwa” tace da shi zalla ba walwala tattare da ita.
“Rabba’atul Bait what’s wrong?” Hannunta ya gwada rik’ewa wanda tayi saurin wabcewa “Sweetheart please talk to me keda nake marmarin in dawo wajenki saboda ki cire min bak’in cikin da ‘yar uwarki ta cusa mun kuma kike haka? What have I done this time?”
“Ai mey hali bai ta6a fasawa amma nagode.” Cike da rashin fahimta ya tambayeta “Mey kike nufi Rabba’atul Bait please talk to me.”
“Ni de wallahi na gaji bazan iya ba da rashin mutuncin nan da tokari tunda baka sona kawai ka sallameni in tafi gida gun Mummy yaso ka cigaba da sha’aninka da amaryarka.”
“Wani irin magana kuma kike haka Rabba’atul Bait sanin kanki ne ina sonki kuma bazan iya rayuwa ba ke ba.”
“Wallahi baka sona Ya Rouhi” ta fad’a tana cika idonta da hawayen munafirci.
“Please don’t cry darling.”
“Ka daina kira na darling tunda ba sona har zuciya kake ba, idan da har ka d’auke ni da muhimmanci kaman yadda na d’auke ka da Amal baza tana kirana tana mun gori ba.”
“Amal?”
“Eh ita.”
“Oh Dear! Mey wancan ta kira kuma ta sake ce miki? Wallahi we’re not on good terms with her girkinta haka ban d’ana ba tun zuwa na, mey tace miki?” Ya tambayeta ransa na 6aci.
“Ni baza ka ji komai daga bakina ba har ga Allah bazan so in had’a kanku ba amma de ka cigaba wallahi ranan da komi ya isheni tattara kayakina zanyi in koma gida inyi ma Daddy magana asan ya za’ayi tunda gashi a fili ka nuna baka sona kuma baza ka iya yin adalci a tsakanin mu ba. Ka nunawa Amal ni ba kowa bace banida daraja a idonka idan ba haka ba taya zata na kira na tana gaya mun magana iya son ranta?”
“Nazeefah please calm down ke kanki kinsan I’ll never do this to you, I love and respect you alot, dan Allah ki daina magana haka kiyi hak’uri mey yayi zafi da zakice zaki koma gida? Believe me duk abinda Amal ta kira tace miki nayi mata wallahi k’arya take don ko tsinke ban sai na bata ma tun komawa na.”
“Ai idan da har ba kayi mata abubuwan dagaske da koda wasa bazata kira tace mun gashi ba nasan ba k’arya take mun ba.”
“Ni ke miki miki k’aryan kenan Rabba’atul Bait? Please tell me what is it that Amal told you.”
“Ka kirata ka tambayeta da kanka ni bazan had’a kanku ba.”
“Ita d’in ba so take ta had’a kanmu ba take kiran ki take miki k’arerayi a waya? Please tell me.”
“Dan tamun haka nima senayi mata? Ai ko addini cewa yayi karka sak’a wa mutumin da yayi maka sharri da sharri Allah ma shaida ne ni da zuciya d’aya na d’auki Amal amma ita kam ba haka bane.”
“Rabba’atul Bait wallahi ba k’arya nake miki ba I and Amal aren’t even speaking to each other ko tamun magana shareta nake saboda na gaji da kalan abubuwan da take yi miki, I’m tired.”
STORY CONTINUES BELOW
“I’m not buying any of your lies again Ya Rouhi zaka ce mun bakuwa magana da Amal bayan d’azun nan na kirata dan mu gaisa take ce min kana jiranta a tub zakuyi wanka tare.”
“Amal d’in?”
“K’arya zanyi maka ne?” wayanta ta janyo ta shiga call logs ta nuna mai wayan da sukayi da Amal d’in. Kuma tabbas ta kirata d’azu sun gaisa amma bawai Amal tayi mata magana makamancin haka ba.
“Innalillahi!” Ya furta cike da tashin hankali “Wallahi tallahi k’arya take yi miki Nazeefah-“
“A’a Ya Afzal” tayi saurin katsesa “Karka 6ata lokacinka, ba seka mun bayanin komai ba na riga na fahimceka na sani kafi son Amal akai na dama idan ba ni da shashanci bama taya zan had’a soyayyan da kake mun da wacce kake yima Amal ita da take matar so a gareka bayan ni auran had’i akayi mana? Ni abu d’aya nake buk’ata kawai ka sawwak’e mun in koma gida bazan iya ba da wannan walak’anci da cin fuska” ta k’are tare da rushewa da kuka. Sosai ransa ya mugun 6aci yayinda wutan tsanan Amal ke sake ruruwa a zuciyarsa. Gabad’aya ji yayi ta fita masa a rai, amma ko tana tattare da babban asara.
“Rabba’atul Bait” ya kira sunanta cike da tausayi yana mey k’ok’arin rungumarta sede tayi saurin janye jikinta yayinda ta cigaba da kuka.
“Nazeefah dan Allah kiyi hak’uri kibar kukan haka I’m dearly sorry.”
“Ka rik’e hak’urinka Ya Afzal ba laifinka bane don zuciyarka ta fi kwanciya da Amal akai na, ni kawai ka sawwak’e mun zey fiye mun kwanciyan hankali idan ina gida gun iyayena.”
“Please don’t talk like this wallahi k’arya Amal take yi miki you have to believe me” a hankali ya janyota jikinsa yana hugging nata “Idan kika tafi wa ze zame Rabba’atul Bait d’ina? Please stop crying I love you and you know it isn’t that all that matters Sweetheart? By Allah duk abinda Amal ta ce miki nayi mata k’arya ne ki yarda da ni” be d’agota ba seda tabar kukan munafircin nata. Hak’uri yayi ta bata ranan throughout chan dare da yazo yin wanka yace suyi tare Nazeefah tana so tana kaiwa kasuwa wai ita baza tayi ba. Lalashinta yata yi har seda ta amince suka shiga bayin wasa suka yita yi sannan sukayi wanka a k’arshe ya sanyata sukayi alwalan bacci kaman yadda Amal ke tunasar masa kullum. Da kansa ya sanya mata kayan baccinta sannan suka kwanta inda yata tattalinta yana mata wasu irin abubuwan da tuni yasa ta fita daga hayyacinta. Wani irin so na musamman Afzal ya shiga nunawa Nazeefah na d’an kwana biyun da sukayi, ji yayi kaman kada ya tafi da kwanansa ya k’are sam baya sha’awan komawa gun Amal gabad’aya ta fita akansa da abubuwan da takeyi.
“Ya Rouhi har six baka fara shirin tafiya ba ka manta yau kwanan ka ya k’are anan?”
“Ba se gobe ba?”
“Gobe kuma? Da Allah ka tashi ka shirya kar mu shiga hak’k’in Amal.”
“She can wait se bayan Maghrib zan tafi.”
“Ni baza ayi rashin adalcin nan da ni ba gaskiya.”
“Tashi ka shirya Ya Rouhi.”
“Zo ki d’agani toh.”
“Ni da kai wa ze d’aga wani?”
“We wouldn’t know until you give it a try so zo ki d’agani” bata sake musu ba ta k’arisa kan gadon. Hannun sa ta kama ta shiga ja sede ko motsawa baiyi a lokaci d’aya ya jata bata sauk’a ako ina ba se akan jikinsa inda sukayi gware.
“Awch!” Ta furta tana murza goshin nata “Ya Rouhi!” Tayi exclaiming.
“Toh ai na fiki jin zafi.”
“Tayaya?”
“Ba goshinki yafi nawa tudu ba.”
“Wallahi k’arya ne banida goshi” ta fad’a had’e da kai masa bugin wasa a k’irji.
STORY CONTINUES BELOW
“Mu gwada ne?” Yace yana mata dariya.
“Ban sanin ba ni ka sakeni” ta fad’a tana k’ok’arin mik’ewa, kankameta ya sakeyi a jikinsa tare da placing mata kiss a gefen baki hannu tasa ta dirje ita a dole tayi zuciya yace mata mey goshi at once yayi flipping position nasu ya zammana shi a sama ita a k’asa.
“Babe you’re the most beautiful girl I’ve ever seen.”
“Ba wanin nan nice mey goshi ba? Tashi ka barmun gida jeka samu amaryarka.”
“Haba Rabba’atul Bait idan kika koreni gun wa zanje?”
“Amal mana of course.”
“Nifa nace ki daina kawo mun magananta.”
“Nide d’agani.”
“Haba my beautiful Rabba’atul Bait” yayi maganan had’e da matso da fuskansa gab da nata yayinda ta zagaye hannayenta a wuyansa “I love you Babe” ya sanar da ita.
“I love you too Darling” a hankali ya sauk’e lips nasa akan nata ya shiga kissing nata yayinda take miyar masa da martani kaman wasa suka fara wuce gona da iri kafin su hankara har sun wula wani duniyan daban. Bayan sun gamsar da juna suka yi wanka tare Nazeefah na mik’e akan gado tana kallon Afzal cike da adoration da soyayya yayinda yake faman neman kayan da ze sa a wardrobe. Wayansa dake kan gado ne ya shiga ruri ko motsawa Nazeefah dake kan gadon batayi ba ina irin ita ba ruwanta da yi mai shisshigi d’innan shi da kansa yace “Who’s calling?”
“I don’t know” ta mayar masa tana gyara d’aurin towel nata.
“Duba” ya umarceta. Lek’awa tayi taga Kitten❤️💍🔐 na flashing akai ga picture’nsu da yayi saving contact natan dashi wani selfie’nsu ba hassada sunyi kyau.
“Amal ce” ta amsa tana k’ok’arin 6oye kishin daya rufeta lokaci guda “Ayya taji shiru.”
“D’aga kice mata idan nayi sallah zan shigo.”
“Ya Rouhi kana ganin yin hakan ya dace?”
“Toh ki bari seta ga shigowa na kawai” ya amsa tare da juyawa yana mey cigaba da neman abinda ze sa. Bada dad’ewa ba sega Amal na sake kira wayan ta d’aga tayi answering had’e da yin shiru.
“Halo Habib Albi?”
‘”Yar uwa Nazeefah ce” ta sanar da ita.
“Oh Nazeefah, ina yini?”
“Lafiya k’alau, kinji Ya Afzal shiru ko? Yana hanya abu ne ya rik’esa.”
“Ayya ba komai seya shigo toh.”
“Aha seda safe” da haka sukayi sallama sauk’e wayan tayi tana ma Afzal murmushi yayinda shima ya miyar mata yana mey mamakin hali irin na Amal ace duk yadda Nazeefah ke sonta har take kirarta da ‘yar uwa amma se tana kiranta tana irga mata ababen da tasan zasu 6ata mata rai. Seda sukayi sallan Maghrib sannan Afzal ya tafi yau har doubling kud’in daya saba ajiye musu yayi wa Nazeefah ita kam dad’i kasheta she can’t wait ta gama aikin ta akan Amal ta fiddata daga gidan finally.
Yana isa gida Amal ta bud’e k’ofa tayi masa sannu da zuwa tana cewa bari tayi hugging nasa yaja da baya. Dama a cike take dam tunda ta kirasa taji Nazeefah ta d’aga wayansa gashi yau se bayan maghrib ya shigo abinda be ta6a yi ba. Kuka kawai ta rushe da sede da mamaki taga ko d’aga kai Afzal beyi ba bale yasan tanayi. “Excuse me” yace da ita yana neman wuceta hannu tasa ta dakatar da shi.
“Yaya mey nayi maka haka ka za6i kana shareni kana wulak’anta ni a gidan nan? Idan wani laifin nayi maka dan Allah ka fad’a mun a shirye nake da in baka hak’uri” ta sanar da shi cikin tsan-tsan kuka. Shi dariya ma ta basa bayan duk rashin hankalin da take tafkawa still tana da bakin da zata tambayesa mey tayi? Lallai she thinks she’s smart. Kallonta kawai ya tsaya yi ko uffan bece mata ba.
STORY CONTINUES BELOW
“Yaya please talk to me I can’t do this anymore yau kwana nawa idan ka shigo mun sede kayita d’aura mun fuska, ka daina cin girki na, d’an gifts da ka saba siyo mun ka daina, ka daina kwanciya da ni yanzu ko jikinka kana neman hanani ta6awa baka tunanin hukuncin nan da ka yanka yayi tsauri dayawa?”
“Yayi tsauri fa kikace Amal? I’m truly disgusted at you I never expected this from you how could you stoop this low? Tell me mey kikayi benefiting da wannan abun kunyan da kikayi mun kika kuma yi wa kanki?” Ya tambayeta cike da tsiwa. Hawaye take sosai yayinda kanta ya d’aure shin mey yake fad’i? Wani abun kunyan tayi masa?
“Yaya wani irin magana kakeyi? Wani abun kunya nayi maka please talk to me ban fahimce ka ba.”
“Ai dama baza ki ta6a fahimta ta ba Amal you know what? I don’t have time for this idan kinsan k’arya zaki tsaya kina mun just forget it.”
“Yaya dan Allah kar kayi mun haka I beg of you wallahi ba k’arya nake maka ba” ta rok’esa cikin tsananin kuka.
“Ohhh itace take k’arya kenan?”
“Ita wa?”
“Seriously Amal? Har tambayana kike ita wa? Kin d’au magana baze zagayo kunne na bane? Kede ki cigaba.”
“Wallahi ban fahimceka ba Yaya bansan akan mey kake magana ba kuma a iya sani na ban yi maka wani abun ba sede ban sani ba ko a bisa rashin sani yet still zan baka hak’uri dan Allah kayi hak’uri ka rage wannan hukunci wallahi yayi mun tsauri dayawa Yaya can’t you see? I’m slowly losing my mind and going crazy fushinka a gareni ba k’aramin tashin hankali bane please kayi hak’uri ka gafirceni I’m dearly sorry.”
“Idan ba kiya son ina fushi dake se ki iya bakinki ki koyi rik’e sirrin gidanki ki dena buga waya tako ina kina irga wa mutane abinda mijinki yake miki, how could you Amal? I thought kina da hankali kuma kinsan abinda ya kamata ashe ba haka bane, wallahi ba halin ki bane ban san ki da halin nan ba.”
“Ni Yaya? Wa na kira na sanar dashi sirrin gidan nan? Wallahi ban buga wa kowa waya ba ko Mami.”
“Kiji I don’t have time to listen to your lies because a sane nake da komai don haka ba abinda zakice da zaisa in amince dake I’ve heard enough and I’m very disappointed with you ban ta6a sanin kina da wannan mumunan hali ba amma ki cigaba ni bazan miki baki ba sede inyi miki fatan shiryuwa idan ma k’awaye kike bi suke rud’anki suke d’aura ki akan gur6arcacciyar hanyan nan gara tun wuri kin rabu da su ina Safiyya!” Nan Safiyya dake lek’ansu ta koma cikin d’akinta a 360 seda ya sake kiranta a karo na biyu sannan ta fito tana wani hamma irin bacci takeyi ya kirata d’innan.
“Ina yini Uncle?” ta gaishesa.
“Lafiya ki dafa mun indomie biyu da k’wai biyu kiyi sauri I’m hungry.”
“Akwai abinci fah Rice and Stew Aunty ta girka.”
“Ina sane ai nace ki dafa mun indomin.”
“Toh” da haka ta wuce kitchen d’in wani pathetic look ya bawa Amal ya wuceta ya shige d’akinsu. Har k’asa ta sauk’a tana kuka wajen gabad’aya ta rasa mey ke mata dad’i sam bata da masaniya ga abinda Afzal yake cewa mey yake nufi da ta daina kiran mutane tana yad’a musu sirrin aurenta a ina tayi hakan? Ita da ko da iskokai suka shafeta ma bata kira Mami ta sanar da ita ba wani sirri yake nufin tana yad’awa idan akwai mutumi d’ayan da ta mar maganan aurenta itace Maamah kuma ta yarda da Maamah tasan Maamah baza ta ta6a ci mata amana ba. Kuka tayita sha wajen har zuwa lokacinda Safiyya ta gama abincin Afzal ta ajiye masa kan dining gun Amal ta k’arisa ta durk’usa.
STORY CONTINUES BELOW
“Aunty kiyi hak’uri dan Allah ga abincin Uncle yayi.”
“Kije kice mishi ya fito.”
“Da kaina?” Kai zalla ta gyad’a mata nan ta wuce bayan tayi mar sallama ta sanar dashi ta gama godiya yayi mata sannan ta dawo kan Amal tana cigaba da bata hak’uri kaman dagaske.
“Kije d’akinki Safiyya ba komai” haka Afzal yazo ya tarar da ita zaune a wajen, ko kallonta beyi ba ya k’arisa dining. Da k’yar ta tattara kanta ta koma d’aki Qur’ani kawai ta d’auka ta shiga karancewa shi kad’ai take jin ze iya rage mata wannan k’unci da bak’in cikin da takeji. Bayan Afzal ya gama cin abinci yazo shiga d’akin yaji sautin karatunta na tashi, na d’an lokaci ya tsaya ya saurareta sannan ya koma parlourn ya cigaba da zama be sake kewayowa d’akin ba se da ya tabbata tayi bacci wajajen sha d’aya kenan. Tsince akan gado tana bacci ya tarar da ita da alama karatu take bacci ne ya d’auketa don ga handouts nata baje a gabanta, Jallabiyan jikinsa ya tu6e sannan ya tattare handouts d’in ya ajiye a gefe ya gyara mata kwanciyan nata ya haura ya kwanta daga chan gefe shima had’e da kashe musu wuta.
Haka ya cigaba da d’aga mata kai yana shareta, washegari Amal tayi kuka har ta godewa Allah test da ta rubutan ma dukda cewan tayi karatu batazo ta gane mey ta rubuta ba saboda gabad’aya ba hankalinta a jikinta.
“Amal kiyi hak’uri haka kukan nan ba shida amfani” fuskanta daya kumbura tim ta d’ago daga kan benchi tana share hawayenta “Maamah a rayuwa ba abinda na tsana kuma yafi k’ona mun rai kaman banyi abu ba ace nayi fisabilillahi ko ke na ta6a sanar dake sirrin gida na ne in ba wannan karan da matsaloli suka yi mun yawa ba?” Kai Maamah ta kad’a mata a hankali cike da tausayi “Amma cemin yayi wai ba aiki na se buga waya wa mutane ina sanar dasu sirrin gida na harda wai ya d’au ina da hankali ashe babu duk na munafirci ne Yaya fa Maamah, Yaya yake kwatantani da wannan munanan kalamu” ta sake rushewa da wani kukan.
“Amal ki kira Mami ki sanar da ita kawai taya Ya Afzal ze miki haka ina laifin ma ya sanar dake laifin da kika yin amma haka kawai ya barki acikin duhu ai ba yi bane hakan.”
“So kike ya gama tsanata idan na sanar da su Mami? Ban kira kowa bana yace ina kiran waya ina yad’a sirrin gida na bale har in kira Mami? Hmm ashe ina tona kabari na da kaina kenan.”
“Toh ya zakiyi Amal? Ni anya kuwa ba kishiyarki bace take neman had’a kanki da Ya Afzal?”
“Nazeefah wai?”
“Sosai ma kiyi tunani mana mey yake nufi da yace miki ita take k’aryar? Nazeefah yake nufi.”
“Da wuya idan itace I trust Nazeefah bata da wani mugun hali kuma kinga ita bama zuwa gida na take ba bale ace taga wani abun taje tayi mai gulma.”
“Don’t get too confident trusting her Amal wallahi halin mutum se Allah idan ba haka ba waze shiga tsakaninki da Ya Afzal haka?”
“Maamah ban sani ba amma zan cigaba da addu’a har se idan Allah ya amsa kuka na.”
“Toh Allah taimakeki ya shige miki gaba Amal shi kuma Ya Afzal Allah sa ya gano gaskiya ya sani cewa idan mutum yayi laifi confronting nasa ake bawai a rik’e shi a zuci ana k’untata mai ba.”
**
Washegari kasancewar Amal tana iya kai har yanma a school ta yi girkin rananta tun da safe kafin ta fita. Abinda Safiyya zatayi kawai tayi wa Afzal microwaving ne idan ya dawo daga office that is idan ze ci ma kenan tunda yanzu ya k’aura daga cin girkinta. Tun k’arfe sha biyu ya dawo gida yana shiga ciki yaga cup da snacks haka akan table sekace anyi bak’o sallama yayi Safiyya ta fito tayi mai sannu da zuwa.
STORY CONTINUES BELOW
“Auntinki na gida ne?”
“A’a ta fita school.”
“Wannan fah?” Ya nuna cup d’in “Kinyi bak’uwa ne?”
“A’a Aunty ne ta shigo bada dad’ewa ba ita da wani.”
“Excuse me?!” Yayi exclaiming had’e da zaro idanunsa waje.
“Yanzu suka bar nan.”
“Ita da wa?”
“Ita da wani na miji suka shigo ta d’au wasu takardu suka d’an zauna se suka sake fita tace tayi mantuwa ne.”
“Amal ta kawo na miji gidan nan?” Sam ya kasa amincewa da hakan.
“Ni na d’au ma ko d’an uwanta ne yadda suka zauna a kujera d’aya.”
“A kujera d’aya!?” Ya sake tambaya idanun nan kaman zasu fad’o a k’asa dan mamaki. Dan yadda zuciyarsa ta shiga k’ona ko k’ala be sake cewa da Safiyyan ba take idanunsa suka kad’a sukayi ja. Cikin wani irin taku ya k’arisa d’akin nasu kawai ji Safiyya tayi ya buga k’ofan wane yana neman 6allesa, d’aki ta koma jiki na rawa ta kira Nazeefah.
“Aunty na aikata, kuma wallahi ya amince.”
“Kai haba!”
“Bakiga yadda yake ta nishi ba kaman zaki.”
“Kinyi dai-dai ai in shaa Allahu kwanan Amal a gidan nan ya kusa k’arewa aikinki na kyau.”
Amal baiwar Allah da tun fitanta k’arfe sha d’aya se biyar ta dawo bata san meyake jirarta ba a gida. A galabaice driver ya dawo da ita tana shiga parlour ta tarar da Afzal zaune kan kujera ko d’aga ido beyi ba bale yasan mutum ya shigo gidan se harkan gabansa kawai yake itama bata yi mai magana ba sanin ko tayi ba amsata zeyi ba. Da mamaki ya bita da kallo wato ma ko magana baza tayi masa ba lallai rainin har ya kai haka? Bayan ta kawo masa k’ato gida ta dawo kuma bazata iya ce mai sannu ba, wuyanta ya kai yanka. Da abinda zata sak’a masa kenan duk kalan halaccin da yayi mata a rayuwa? Wajajen goma ya koma d’akin kwance akan gado ya tarar da ita a galabaice.
“Kibar min d’akin nan kije ki kwana wani wajen” yace da ita zallah.
Da mamaki ta tsaya kallonsa ashe Allah ze kawo ranan da zeyi mata gori akan abubuwan da yayi mata a rayuwa? Ko k’ala bata ce da shi ba ta d’au pillonta da waya ta bar masa d’akin bayanta yabi yayi locking k’ofar sannan ya dawo ya kwanta yana mamakin wannan sabon d’abi’artan wato ma tsabagen tasan halinta ta kuma san mey takeyi shiyasa ko a bakin zaninta bale ta tambayesa dalilin da ze hanata kwana masa a d’aki ba. Toh ta cigaba.
Ta d’ayan fannin kuka Amal ta kwana tana yi bata jin zata iya da wannan walak’anci mey yayi zafi da ze koreta daga d’aki? Saboda bata kawo ko tsinke gidan ba? Da k’yar bacci yazo ya d’auketa. Kasancewar tana da morning lectures washegari bayan Asuba tayi wanka sannan ta wuce d’akin nasu dan d’auko kayan da zata sa sallama tayi jin shiru seta bud’e k’ofan amma bata gansa a ciki ba don haka kawai ta yanke hukuncin yana bayi ne. Wajen wardrobe ta nufa ta shiga fiddo da kayan da zata sa tana cikin hakan Afzal ya fito daga bayi ko juyawa ta kallesa batayi ba harkan gabanta ta cigaba da yi daga wajen wardrobe ta k’arisa gun mirror ta tattara man shafawanta da turare da sauran abubuwan da zata buk’ata ta fice. Binta da kallo yayi shima bece da ita ko k’ala ba. Tana gama shirinta tayi ma driver magana ko tambayan Afzal kud’in makaranta batayi ba sallama kawai tayiwa Safiyya ta fice. Yau ma kaman jiya Afzal ya riga Amal dawowa and thesame thing cup ya tarar a kan centre table da plate na abinci daya tambayi Safiyya still ta basa amsa irin na jiya akan Amal ce ta shigo da wani basu jima da tafiya ba. Na matuk’a ransa ya 6aci yau kam baya jin ze iya d’aukan rashin hankalin nata abun ya ishesa zama yayi a parlourn yana jiran dawowanta chan bada dad’ewa ba ta iso yau ma a galabaice. Kanta ta sunkuyar lokacinda ta shiga parlourn har ta kai ga wucesa ya kira sunanta chak ta tsaya had’e da kewayowa.
STORY CONTINUES BELOW
“Wa kika kawo mun gidan d’azu?”
“Mey kake fad’i Yaya?
“I’m not repeating myself Amal wa kika kawo mun gida d’azu?”
“Wa zan shigo maka dashi gida Yaya? A iya zama na da kai na ta6a shigo maka da na miji gidan nan ne? Why don’t you believe me Yaya? Na d’au ko da an fad’a maka hakan bazaka amince ba saboda a tunani na kafi kowa sanin hali na, a tunani na kafi kowa sanin abinda zan iya aikatawa da abinda bazan iya ba I’m so disappointed with you Yaya” ta tsaya ta numfasa yayinda hawaye yake ciko mata a ido “Ina soyayyar da kake ikirarin kana mun? Ashe za a iya fad’a maka magana akaina ka hau ka zauna akai ba tare da kayi bincike akai ba?”
“Stop acting like you’re the Amal I used to know saboda gabad’aya kin canza, I can’t trust you anymore Amal yau komin ya girman laifi yake aka ce mun kin aikata zan amince saboda I’ve lost my trust in you since the day kika fara d’iban sirrin gidan ki kina yad’a wa jama’a.”
“Allah ma shaida ne ban ta6a kwasan abinda kake mun a gidan nan na fad’awa kowa ba not even Mami” ta amsa tana share hawayenta.
“Ki bud’e kunnenki ki saurareni da kyau ban yafe ba idan kika sake kawo mun wani k’ato cikin gidan nan.”
“Yaya please idan wani abun nayi maka ka fito fili ka fad’a mun amma ka daina cemun nayi abinda ban aikata ba, yaushe na shigo gidan nan tun fita na bale har in shigo da wani?”
“Da ace ban shigo na tarar da ragowan snacks da drink da kikayi serving nasa bane se ki gaya mun maganan banza.”
“Drink? Wallahi ni ban kawo wani gidan nan ba ka kira driver ka tambayeshi ko ya dawo dani gida tun fita na da safe in ba yanzu ba.”
“You’re not as smart as you think you’re Amal and ki cigaba.”
“See Yaya idan gajiya dani ne kayi kawai ka fad’a mun I’ll understand you it’s too early for this, taya banyi abu ba ina ji ina gani zaka na mun sharri da fari kace ina kire-kiren waya ina baza sirrin gida na a waje yanzu kuma zargi na ka fara? Har kana tunanin kai na ya waye da zan fara kawo maka maza a gida? Wallahi a da koda wasa aka cemun zaka yi mun abinda kakeyi mun yanzu bazan amince ba amma ka cigaba dama nasani dole wataran zaka goranta mun tun da har ka iya ka koreni daga d’akinka jiya.” Bata jira jin mey zece ba ta wuce d’akin data koma a guje. Kuka ta shigayi daga haka har ta fara yin amai, bata tsaya ba seda ta harar da abincin cikinta tas har jiri na neman d’ibanta. Da rarrafe ta k’arisa d’akin ta kwanta ahaka har wahalallen bacci ya d’auketa. Next da ta tashi Safiyya ke ce mata Afzal ya riga ya tafi kai kawai ta gyad’a mata har ta tashi zata tafi seta kira ta.
“Na’am Aunty?”
“Mey kika cewa Ya Afzal jiya da bana gida?”
“Game da mey Aunty?”
“Kinsan mey nake nufi ai.”
“Wallahi ban fahimce ki ba dan ni magana ma be had’ani da Uncle ba.”
“Waya ce mishi na shigo da na miji gidan nan?”
“Na miji? Wallahi bani bace Aunty dan meyasa zan miki sharri? Wallahi bani bace.”
“Shikenan tashi ki tafi.” Chan bayan sallan Isha ta fito kitchen dan had’a custards ta sha sanadin wani irin yunwan da ya dameta. Tana tsaye a kitchen tana jiran ruwan ya tafasa Safiyya ta shigo zata dafa indomie.
STORY CONTINUES BELOW
“Ki d’au k’wai biyu ki soya” tace da ita.
“Toh Aunty nagode” jiki na rawa ta bud’e fride d’in ko ya akayi kawai d’aya ya ku6uce daga hannunta ya fad’i ya fashe.
“Subhanallahi! Ya akayi haka Safiyya?” Amal tayi saurin tambaya tana neman toshe hancinta.
“Aunty dan Allah kiyi hak’uri wallahi ban sa ya akayi ba bari in goge da wuri ina tissue” kafin ace mey k’arnin ya mamaye kitchen d’in gabad’aya gas d’in Amal ta kashe da wuri sannan ta juya sink ta shiga kwararo amai, amai tayita yi wane zata harar da hanjinta yayinda Safiyya ke bata hak’uri. Bakinta ta wanke Safiyya ta taimaka ta jata izuwa d’aki.
“Sannu Aunty kina buk’atan wani abun?” Kakkarwa take sosai ta kad’a mata kai “Ki had’a mun black tea kawai.”
“Toh ina zuwa” nan da nan ta had’o ta kawo mata.
“Shikenan kina iya tafiya.”
“Ba wani abinda kike buk’ata?”
“Babu kar ki damu.”
“Allah sawwak’e.”
Da k’yar Amal ta samu ta sha rabin tea d’in taji ta k’oshi zazza6i ne ya rufeta a lokaci guda ko makaranta ta kasa fita washegari ga shi jikin nata ya d’au zafi. Maamah ce da ta jita shiru ta kira dan tambayan ko lafiya.
“Wallahi zazza6i Maamah kaman zan mutu.”
“Allah sarki shafakillahu habibty Allah baki lafiya.”
“Ameen nagode.”
“Na yi miki assignment d’in na mana submitting.”
“Allah sarki Maamah kaman kinsan ina ta bi a raina wallahi nagode sosai Allah ya bar zumunci.”
“Ameen munyi waya da Ya Abdul ma yace in gaisheki.”
“Allah sarki ina amsawa.”
“Ya Afzal fah? Be kaiki asibiti bane?”
“Ya koma gun Nazeefah tun jiya ai.”
“Baki kira kin sanar da shi bakida lafiya bane?”
“Ko nayi mey zai mun? Kin manta ba wanda ya tsana kaman ni ne a duniyan nan yanzu?”
“Allah sarki Amal do you need anything? Wallahi Ya Afzal bai kyautawa.”
“Ba komai Nazeefah wataran se labari nagode” ta amsa hawaye na tsiyaya mata daga ido.
“Gobe zan shigo in duba ki in shaa Allah ki huta kinji? I love you.”
“I love you too sekinzo.”
****
Se wajajen sha biyu Amal ta samu k’arfin jiki a gida ta yini ranan ba inda taje, chan Maghrib nayi kuma zazza6in ya sake tashi ga amai idan ta fara kaman zata harar da kayan cikinta sosai Safiyya ta tausaya mata take kuma k’ok’arin kula da ita. Har anan Afzal be san mey ake ciki ba kaman yadda be kira Amal ba haka itama bata kirasa ta sanar da shi batun rashin lafiyarta ba ko Mami bata kira ba.
Bayan Safiyya ta tattare plate d’in ta fita dashi Amal ta janyo wayanta ta shiga calender tana counting yau kwana uku kenan da missing period nata anya kuwa lafiya? Kode? Subhanallahi it can’t be possible Allah yasa ba abinda take zargi bane inde haka ne ya zamo dole gobe taje asibiti ta tabbatar da koma mey amma fatanta Allah yasa ba abinda take zargi bane. Se sha d’aya ta fita washegari bayan da zazza6in nata yad’an sauk’a. A wani private clinic Driver ya sauk’eta inda ta k’arasa ta bud’e file tukun ta shiga ganin doctor tayi mata bayanin yadda takeji. Murmushi likitan tayi mata tace “Amma Amarya ce ke ko?” Kai Amal ta gyad’a mata cike da rashin fahimta.
“Shiyasa ai.”
“Ban fahimce ki ba Dr Sadiya.”
“Congratulations you’re pregnant Mrs Abdallah.”
“Pregnant?” Amal ta nanata cike da k’in yarda “Taya bakiyi mun gwaji ba bakiyi komi ba kice ina da ciki?” Murmushi ta saki kad’an “ni da aiki na kuma Mrs Abdallah ai ko ban miki gwaji ba idanunki kad’ai ma shaida ce kina d’auke da juna biyu.”
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” taji Amal ta furta.
“Lafiya?” Tayi saurin tambaya.
“Dan Allah kiyi mun tests d’in tukuna I can’t be pregnant at least not when babu jituwa tsakani na da mijina, I can’t be pregnant Dr please do something” ta fad’a cike da tashin hankali.
“Subhanallahi please calm down, taya zaki k’i kyauta daga Allah haka Mrs Abdallah?”
“Ba haka bane Dr matsaloli sunyi mun yawa and cikin nan will only add to it please help me.”
“That’s where you’re wrong wannan ciki sede ya warware miki duk wani matsalan da keda mijinki kuke fuskanta, ki yarda dani mijinki na jin wannan news ze sauk’o daga kowani irin temper yake kai, kede ki godewa Allah kawai” ta sanar da ita ta na wani rubutu jikin wani paper “Ga wannan kije next room zasu yi miki scanning mu gano sati nawa ne duk abinda akwai zasu sanar dake kafin ki fara zuwa pre natals naki, congratulations once more.” Jiki na k’yarma Amal ta amshi paper’n “Don’t be afraid Mrs Abdallah in shaa Allahu juna biyun nan shi ze zame sanadin shirya tsakaninki da mijinki.”
“Toh nagode Dr.”
“Sey kuma ga wannan magunan basuda k’arfi in shaa Allah baza suyi komi wa cikin ba, zasu rage yawan jin jiri da kuma yawan yin amai da zazza6in duka, Allah inganta.”
“Ameen Dr nagode se anjima.” Next room ta shiga inda akayi mata scanning cikin. Kwata-kwata ma cikin sati uku ne sede maimakon Amal tayi murna tun dawowanta gida take aikin kuka gabad’aya ta rasa meke mata dad’i bata ma san wa zata fara kira ta sanar da shi wannan labari ba abu d’aya da ta sani shine Afzal ne mutumi na k’arshe da zata kira ta sanar da shi. Tunda ya fara zarginta yanzu ai da k’yar ma idan ze amince cikinsa ne a jikinta, ya zatayi? Wannan musiba da mey yayi kama??
Ko makaranta Amal ta kasa fita washegari saboda yadda jikin nata ya tsananta, gashi de ta fara shan maganin amma ba sauk’i. Kaman yadda Maamah ta d’au alk’awari haka tazo ta duba Amal da soft drinks nata, Safiyya ce ta amsa ta sa a fridge sannan ta kai ta d’aki inda Amal ke kwance akan gado ta duk’unk’une kanta acikin bargo se kakkarawa take. K’arya ne mutum ya ganta be tausaya mata ba.+
   “Subhanallahi Amal!” Maamah tayi exclaiming cike da tashin hankali. “Amal dan Allah karki mutu” take idanunta suka ciko da hawaye tsan-tsan tausayi.
  “Amal mey kike yima kanki haka? Meyasa baki kira Mami ba? Meke damunki dan Allah?”
  “Maamah calm down ki kwantar da hankalinki.”
  “Ya jikin naki? How are you feeling?”
  “Da sauk’i zuwa anjima zazza6in ze sauk’a morning fever ne.”
  “Subhanallahi sannu ai baki fad’a mun zazza6in yayi tsanani haka ba what’s wrong?”
  “Maamah I’m pregnant” ta sanar da ita.
  “You’re what?!” Tayi exclaiming had’e da zaro ido waje.
  “Maamah ina d’auke da cikin Yaya” ta jaddada mata yayinda ta rushe da kuka. Hugging nata Maamah tayi tana kukan tare da ita sun dad’e a haka sannan ta janye Amal a hankali tana mey share mata hawayenta.
  “Amal I’m so happy for you, Allah ya inganta idan lokacin yayi ya raba lafiya.”
  “Ameen” ta amsa chan ciki-ciki.
  “Ya Afzal ya sani?”
  “Ke na fara fad’awa ko Mami ban kira na sanar da ita ba.”
  “Amal why? Ai Ya Afzal ya kamata ya fara sani ke bakisan wannan news shi ze zame sanadin shirya tsakaninku ba?”
  “Shirya tsakanin mu?” Ta tambayeta had’e da sakar da murmushin takaici “Maamah things just got worst kin san mey Yaya yamun?” Kai Maamah tayi saurin kad’awa.
  “Korana yayi daga d’akinsa shiyasa kika ganni anan bayan nan jiya yake ja mun Allah ya isa idan har na sake shigo masa da na miji gida Maamah zargi na Yaya yake, gani yake kaman duk zaman mu cin amanan sa nake.”
  “Innalillahi wa inna ilai raji’un the fuck is wrong with Ya Afzal? Ya yake abu kaman wanda baida ilimi? Ai yaci ace yasan abinda zaki iya aikatawa da abinda bazaki iya ba daga gun wani d’an jakar uban yaji wannan batu? Waya gaya mishi kina shigo da maza gidan nan?”
  “Wallahi ban sani ba Maamah kinsan zurfin cikin Yaya bayi ta6a fitowa fili ya fad’awa mutum abu.”
  “Amal dan Allah ki tattara kayakinki kibar mai gidan nan haka wannan walak’anci dame yayi kama? Se kikace mishi mey dayace kibar masa d’akin nasa?”
  “Mey kuwa zance masa? Pillow na kawai na ja na fice mey zance masa?”
“Hmm wallahi munafukar mey aikin ki d’innan nake zargi da ganin yadda fuskanta yake bak’i k’irin d’innan haka zuciyarta take in ba haka ba ina Ya Afzal zeji batun nan? Bawai zama yake a gida koda yaushe ba dole gaya mishi akeyi.”
“Na gwada mata magana tace ba ita bace banida lafiya ban so jan maganan ba nace kawai shikenan.”
  “Wallahi itace kinji rantsuwa ba kaffara ina gaya miki Nazeefah ba kishiryar arziki bace wallahi aiki suke tare da ‘yar nan dalilin daya sa tun farko ta kawo miki ita kenan. Wallahi aiki suke tare.”
   “Nazeefah kuma?”
  “Don’t be fooled by her kind gestures makashinka na nan tare da kai duk inda kake, kiyi tunani ita munafukar Safiyyan ce take kai wa Nazeefah rahoton komi a gidan nan ita kuma mak’irar seta ce ke ce kika kira kika sanar da ita.”
STORY CONTINUES BELOW
  “Maamah ni bana son abu da tashin hankali da tada magana idan ma aiki suke tare wataran dubunsu ze cika dukda cewan ban yarda da hakan ba I know Nazeefah baza ta ta6a yimun haka ba.”
  “Hmm Amal kenan ki bud’e idonki kisani yadda ka d’auki mutum ba haka yake d’aukanka ba ko a jinki kowa ne keda zuciya d’aya kamanki? Wallahi ba haka bane, balle wai har kice kin aminta da kishiyarki? Kishiyan da ba wacce take gaba dashi a fad’in duniya kaman ka? Ki bani izini inyi questioning mey aikin kin nan kawai.”
  “Maamah please ki barta bana son k’ananun magana” Maamah bata saurareta ba ta mik’e “Maamah dan Allah ki dawo” ficewa tayi ta dawo da Safiyya biye a bayanta “Bani wayanki” ta buk’aceta.
  “Waya na kuma?”
  “Eh wayanki.”
  “Lafiya?”
  “Wani abun kike 6oyewa ne?”
  “Wani irin magana kuma kike Aunty? Mey zan 6oye?”
  “Good then pass me your phone” hannu ta mik’a mata tana jiran ta sanya mata shi aciki bayan Saffiya ta d’au lokaci ta sanya wayan cikin hannun Maamah cike da fargaba.
  “Amal ya numban Nazeefan yake?”
“Maamah dan Allah ki bata wayanta ni bana son matsala.”
  “Mstw” wayan Amal taja ta bud’e ta latsa numban Nazeefah had’e da zubawa cikin wayan Safiyya sede da mamaki taga babu numban a wayan Safiyya how can it be possible? Ta tambayi kanta.
  “Babu ba?” Amal ta tambayeta kai zalla ta gyad’a “Ai na fad’a miki ba su bane dan Allah ki bata wayarta amshi Safiyya kiyi hak’uri.”
  Amsa tayi tace “Ba komai Aunty Allah k’ara miki lafiya” da haka ta fice.
  “This can’t be possible wallahi ina ji a jikina ‘yar nan munafuka ce.”
  “Maamah please enough gashi de kin gani ko lamban Nazeefah bata dashi kuma bataje boko ba bale kice ta haddace lamban ne akanta ranan lamban ta na tambayeta amma bata sani ba, babu yadda za’ayi kuma ace ta haddace na Nazeefah, na gaya miki ba had’in Safiyya da Nazeefah.”
  “Hmm toh mey gadin kine? Wallahi dole akwai wanda yake fad’awa Ya Afzal abubuwan nan ko kina tsammanin shi yake zama yake shirya zancen?”
  “I will not be surprised idan shi yake shirya komi Maamah saboda a fili yake nuna mun na fita a kansa baya sona ban ta6a tsammanin Yaya zemin haka ba watarana wallahi yanzu nake nadaman auransa da nayi nasan ko da wasa Ya Abdul baze ta6a yimun haka ba.”
   “Kar ki ce haka Amal Ya Afzal mijinki ne har yanzu.”
  “Maamah I miss Ya Abdul I miss him so much” hugging nata Maamah tayi yayinda ta cigaba da bata hak’uri.
   “Amal be kamata mu nad’e hannu mu zubawa koma wa yake miki wannan aika-aika ido ba we have to do something.”
   “Mey zamuyi toh Maamah? Ba muda hujja bamuda komai.”
   “Ido ya kamata ki sawa mey aikin kin nan wallahi ina ji ajikina itace munafukar lamarin nan.”
  “Nace miki ki cire Safiyya daga lamarin nan.”1
STORY CONTINUES BELOW
  “Hmm toh ke yanzu haka zaki cigaba da zama a gidan nan Ya Afzal na cusa miki bak’in ciki yana miki walak’anci har seya kasheki tukuna? Da wanne zakiji? Da laulayi ko kuwa da masifan miji?”
  “Maamah tunda nasan ni banyi masa komai ba ya cigaba da koma mey yakeyi tabbas wataran Allah ze wanke ni kuma shi zeji kunya, zan cigaba da kai kuka na wa Allah ai shi ba azzalimin bawa bane.”
  “Haka wannan yake amma ki kira Mami ki sanar da ita wannan k’aruwan da kika samu.”
  “I’ll amma ba yanzu ba saboda nasan one way or the other magana ze kai kunnen Yaya idan har na sanar da Mami abinda bana so kuma kenan bana son Yaya yasan ina da ciki.”
  “Amma ai ya kamata ya riga kowa sani tunda shine mahaifin abinda ke cikin naki, Amal you can’t do this on your own.”
  “Ki yarda dani idan nace miki Yaya yana iya denying baby’n nan yace ba nashi bane tunda har ya iya bud’an baki yace mun ina kawo masa maza gida.”
  “Wallahi Ya Afzal na tattare da babban asara tunda de kome aka gaya mishi hawa yake ya zauna akai ba tare da yayi bincike ba, sannu kinji?”
****
  Yini ranan Maamah tayi mata se wajajen biyar da rabi ta tafi. Seda Safiyya ta tabbata Amal tayi bacci ta dannawa Nazeefah kira lokacinda tasan Afzal bai gida ya fita masallaci.
  “Hello Aunty?”
  “Ya zaki kirani warhaka idan da Ya Afzal na gida fa?”
  “Aunty naga kaman lokacin isha yayi ya fita sallah ne.”
  “Idan da kuma bai fita ba fah? Ba nace se ya fita office zaki na kirana ba?”
  “Aunty kiran gaggawa ne.”
  “Meya faru?”
  “Wallahi Aunty ciki take dashi.”
  “Ci mey!” Nazeefah tasa wani d’ankaren ihu.
  “Wallahi ciki take dashi.”
  “Innalila..inna..innalila” dan rikicewa tama kasa k’arisa salatin yayinda cikinta ya d’au ruwa. Yau ga ranan da ta jima tana gudu. “Amal nada ciki kikace?”
  “Eh Aunty.”
  “Wayyo na shiga uku na lalace ya kika gane? Kinsan ba a wasa da zancen ciki ko?”
  “Wallahi ba wasa ba Aunty, tun rananda Uncle ya tafi ta ke zazza6i da amai d’azu wata k’awarta tazo sena ji suna tattauna wallahi ciki ne da ita.”
  “Yau na mutu na lalace taya Amal zatayi ciki gabani na? Wallahi baze yuwu ba koda sama da k’asa ne zasu had’u se na san yadda zanyi na zubar da cikin nan wallahi bazata haifesa ba.”
  “Aunty gashin be isa haka ba? Wallahi Aunty ta fara zargi na kokuma ince k’awarta, k’awarta ta fara zargi na d’azu harda amsan wayana ta zuba lamban ki aciki da ace nayi saving da shikenan sun kama mu.”
  “Wata mak’irar k’awarce take neman rusa mun plan bayan na kusan cimma burina?”
  “Wata wai Maamah.”
  “Safiyya aikin mu ya koma baya be kamata ace Amal nada ciki ba nashiga uku amma Ya Afzal be sani bako?”
  “Gaskiya da wuya kinsan basu magana.”
STORY CONTINUES BELOW
  “This’s the only opportunity I have ya zama mun dole in zubar da cikin nan kafin su shirya dan muddin suka shirya shikenan nawa ya k’are ya zamuyi? Be kamata mu bari Ya Afzal ya gano Amal na d’auke da cikinsa ba.”
  “Toh ya zamuyi Aunty ni Wallahi tsoro nakeji kar a kama ni, ko a haka muka bar Aunty ta sha wuya, ya isa haka please.”1
  “Wawiya ki saurareni gobe Afzal ze dawo mata inason ki taho mu had’u dake inda muka saba an gama rubutun zan baki seki je ki sa mun cikin wardrobe nasa ta k’ark’ashin kayakinsa kina jina?”
  “Eh Aunty.”
  “In shaa Allahu daga gobe zaman Amal a gidan ya k’are na tabbata idan Ya Afzal ya karance rubutun nan se ciwon zuciyansa ya kusan tashi daga nan seya buga mata saki ta tattara tabar gidan mu samu mu zubar da cikin kowa ya huta.”
  ***
  Ba k’aramin rama Amal tayi ba acikin wannan kwana biyu sosai cikin yake bata wuya d’an kumatun da take da shi ma tuni suka zube ta kuma yi duhu. Yau da yamma ana neman shida Afzal ya dawo gida sannu da zuwa Safiyya tayi masa sannan ya wuce d’aki ya rage kayan jikinsa ya bud’e wardrobe nasa ya sanya wasu files aciki ya sake kullewa sannan ya fito parlour.
  “Amal na gida ne?” Ya tambayi Safiyya.
  “Eh tana d’akinta.”
  “Batun maganan da kikayi mun ranan shin dagaske ne Amal ta shigo da wani gidan nan?” Har yau zuciyarsa ta kasa aminta masa da hakan.
  “Uncle meyasa zan fad’a maka abinda idanu na basu gane mun ba? Ni tasa na kawo masa drink da snacks wallahi ka yarda dani.”
  “In tambayi mey gadi? Kisani idan har sharri kikayi mata ina iya 6a6alla ki a gidan nan.” Sosai cikin Safiyya ya d’au ruwa yadda Afzal yake maganan sam ba wasa tattare da shi.
  “Kasan Malam Ahmad da zama a majalisa kuna fita shima yake fita se lokacin dawowanku ya ke shigowa da k’yar idan yana nan Aunty ta shigo in kuma baka yarda dani ba muje a gabanta ka tambayeni a idonta in shaa Allahu amsan dana baka zan sake nanatawa saboda ba k’arya nake yi maka ba.”
  Sajen fuskansa ya shafe cike da mamaki da kuma rashin sanin abunyi gabad’aya kansa ya d’aure. “Shikenan mey kuka girka?”
  “Babu Aunty bata ji dad’i ba kwana biyu so bata girka komi ba nima batace in girka komi ba kuma.”
  “Bata da lafiya?”
  “Eh.”
  “Meyake damunta?”
  “Toh nima ban sani ba gaskiya.”
  “Ina take?”
  “Tana kwance a d’akinta tana bacci nakega.”
  “Jeki ce mata ta shirya driver ya kaita asibiti.”
  “Toh” ta amsa ta fice sallama tayi bakin k’ofan Amal sannan ta shiga ta k’arisa ciki had’e da durk’usawa daga gefen gadon.
  “Wani abu ne?” Amal ta tambaya.
  “Uncle ne ya dawo.”
  “In yunwa yake ji seki dafa masa abinci kinsan banida lafiya ban iya nayi girki ba.”
  “Eh na sanar dashi.”
STORY CONTINUES BELOW
  “Rashin lafiyan nawa?”
  “Eh.”
  “Meya kaiki? Ni na aike ki?”
  “Kiyi hak’uri Aunty yanzu de yace ince miki ki shirya wai driver ya kaiki asibiti.”
  “Kice mishi nagode bana buk’ata.”
Sak abinda Amal ta fad’a mata taje ta fad’awa Afzal a fusace yace, “Ki ce mata ta shirya ba wasa nake ba.” Haka ta dawo ta fad’awa Amal inda Amal ta sake turata kice mishi “Nace bazan je ba.”1
  “Uncle wai bazata je ba” a fusace ya k’arisa d’akin had’e da bankad’e k’ofan na sosai Amal ta tsorata.
  “Ki tashi a kaiki asibiti nace.”
  “Nace bazan je ba nagode.”
  “In ta halin ki za a bi a jinki ko kallon ki zanyi ne a gidan nan? Karki 6ata mun rai Amal ki tashi driver ya kaiki asibiti.”
  “Nace bazan jeba Yaya ana dole ne?”
  “Rashin kunya kuma zakiyi mun? Ki cigaba Amal zamuga inda wannan banzan d’abi’ar zata kaiki” bata sake ce masa komai ba har yaja k’ofan ya fice. Wani irin masifaffen kuka ta rushe da, maghrib nayi ta mik’e tayi niyya bayan sallan Isha ta sanya hijabi ta fito waje takawa take wane wacce k’wai ya fashewa aciki har ta wuce Afzal dake zaune a parlour yana aiki akan laptop nasa, be ce mata komi ba itama bata ce da shi ko k’ala ba. Chan bada dad’ewa ba yana zaune kawai ya fara jin sautin amai daga kitchen besan lokacinda yayi wulli da laptop nasa ba ya nufi kitchen d’in inda ya tarar da Amal tsugune jikin sink tana ta kwararo amai. Na matuk’a ta basa tausayi kad’an ya rage beje ya rungumeta ba amma ya dakatar da kansa. Kallonta ya cigaba dayi har tagama ta d’auraye bakinta zamewa k’asa tayi don yadda bata da k’arfin ko sisi sosai Afzal yake ji ajikinsa duk yadda yaso shareta hakan ya gagara besan a lokacinda ya k’arisa ciki ya shiga d’agata ba.
  “Ka sauke’eni bana so I can take care of myself” ta fad’a a galabaice sede be saurareta ba ya d’agata sama chak be sauk’eta a ko ina ba se akan kujera a parlour “Safiyya!”
  “Na’am Uncle” ta amsa had’e da fitowa daga d’akinta.
  “Wuce ki d’auko mun key’n mota na.”
  “Ki dawo Safiyya nace maka bazan je asibiti ba” Amal ta fad’a a kasalance “Zo ki tayani in mik’e Safiyya” ta buka’ceta har Safiyya ta shiga takowa gun Amal Afzal ya dakatar da ita “Nace kije ki d’auko mun key’n mota na ko?”
  “Uncl-“
  “Bakiya ji ne?” Har ta shiga takawa zuwa d’akin nasu Amal ta tsayar da ita “Nace kizo ki tayani in mik’e baki jini bane?”
  “Uncle dan Allah ka bari in taimaka mata kayi hak’uri” ta fad’a tana kakkarwa.
  “Kije idan kika kashe kanki seki huta kowa ma ya huta” yace da Amal ko kallonsa batayi ba ta jira Safiyya ta taho ta taimaka mata ta kaita d’aki.
  “Sannu ko Aunty?”
  “Ki had’a mun black tea please.”
  “Toh Aunty” da haka ta fice nan da nan ta had’o mata tean tazo wucewa d’akinta Afzal ya kirata chak ta tsaya had’e da tsugunawa.
  “Na’am Uncle?”
  “Meyake damun Amal? Karki yi mun k’arya.”
STORY CONTINUES BELOW
  “Uncle wallahi ban sani ba zazza6i tace mun.”
  “Kin ganta taje asibiti?”
  “Gaskiya a’a tunda ka tafi ko makaranta bata sake fita ba” ta mai k’arya gudun kar ya gano gaskiyan al’amarin.
  “Ya jikin nata?”
  “Tace in had’a mata tea.”
  “Shikenan kina iya tafiya.” Yana kammala abinda yakeyi ya rufe laptop d’in ya koma d’akinsa towel yaja ya shiga bayi ya watsa ruwa fitowansa ya nufi wardrobe nasa yana neman shorts da ze sa k’ark’ashin wani wandon da yakeda niyyan sanyawa da fari Safiyya ta ajiye takardan da Nazeefah ta bata har ze janye wandon seya fasa ya hango wani a sama, zara yayi ya sanya sannan ya kwanta sede ya kasa yin bacci se tunanin Amal kawai yake tuna yadda take amai d’azu kaman wacce ke neman harar da hanjin cikinta. Shin meyake damunta? Ko da wasa k’wak’walwarsa be kawo masa ciki ne da ita ba.
   Washegari Amal ta d’an samu sauk’i don haka ta shiga shirin makaranta koda ta fito ta tarar da Afzal zaune kan dining yana karyawa bata yimai magana ba harkan gabanta kawai ta cigaba da yi. Sosai ya sha mamakin yadda ya ganta back on her feet contrary to yadda take jiya kaman wacce zata mutu. Sosai yake son tambayarta ya jiki amma ya kasa har yanzun haushinta yake ji na abubuwan data ringa yi masa tana gama abinda zatayi tayi ma Safiyya sallama yana jiran ko zata tambayesa kud’in makarantar ta yaga kawai ta fice.
   K’arfe biyu Afzal ya dawo daga office lokacin Amal ma har ta dawo tana zaune a d’akinta tana karatu, d’akinsa ya wuce bayan Safiyya tayi masa sannu da zuwa. Kayan jikinsa ya rage ya fad’a bayi ya watsa ruwa fitowansa ya nufi wardrobe nasa dan neman kayan da zaisa a garin haka takardan da Safiyya ta sanya a tsakankanin wandunansa ya fad’i hannu yasa ya d’aga tare da bud’ewa in da ya soma karancewa kaman haka;
  _To my most beloved soul on earth (Ya Abdul) I write this with a very heavy heart. Darling words cannot describe how much I miss you, I miss you terribly I wish I hadn’t sacrificed your love for Ya Afzal cause it’s true he doesn’t deserve my love, I regret the day I chose him over you, Ya Abdul I wish you were here to cry along with me and take my sorrows away, I wish you were here to fight for me and set me free from this miserable torture. If I were to be given another chance, I would choose you a thousand times over Ya Afzal. Ya Afzal is such a heartless demon now that I’ve thought of it I just realized it was never love he really felt for me but rather lust. All these while he’s been after my body and now that he’s gotten what he’s wanted he treats me more like a maid than his wife, Ya Abdul you’re the one I truly love and not Ya Afzal I’ll never love a heartless demon like him, I so hate him and I hate destiny even the more for separating me from you. My love for you will never die Habibi it’s still fresh like an open wound and I shall continue to hold onto it, I believe that one day you’ll come back to me, I will forever love you Ya Abdul. Life without you is so dull and colourless I need you to brighten up my world and wake me up from this horrible nightmare-_
   Afzal be k’arisa karancewa ba ya fad’i a k’asa bisa ga wani irin k’una da ciwon da zuciyansa ya shiga yi masa birgima ya shiga yi wajen yana rik’e dai-dai saitin zuciyansa yayinda idanunsa suka kad’a sukayi ja zir cike da wahala ya d’age carpet ya 6oye takardan aciki. Wayansa ya shiga lalima amman yayi masa nisa haka ya cigaba da birgima a wajen har seda ya sume chan Safiyya da ta gama had’a masa abincinsa tayi sallama bakin k’ofan.
  “Uncle na gama” takai minti biyu tana magana bakin k’ofar amma shiru dan haka taje ta samu Amal.
  “Lafiya?”
STORY CONTINUES BELOW
  “Aunty uncle ne yace in dafa masa farar spaghetti ya taho da sauce gashi na gama naje kiransa ina ta sallama bakin k’ofar d’akinsa amman shiru.”
  “Hala wanka yake ki jira idan ya fito.”
  “Toh” da haka ta fice bayan minti kusan biyar amma bata ji hayaniyan Afzal ba ta koma bakin k’ofan inda ta cigaba da yin sallama amma ba response d’akin Amal ta koma ta sanar da ita shiru fa har yanzu.
  “Safiyya kina damuna kije mana ki lek’a d’akin halan bacci yake.” Da haka ta koma d’akin ta bud’e k’ofan wani irin rikicaccen ihu ta k’urma bisa ga sumammiyar jikin Afzal da ta tarar a k’asa.
   “Auntyy!!!” ta k’urma wa Amal kira ba shiri Amal dake kwance ta zabura tana tambayan ko lafiya har ta iso bakin k’ofan inda Safiyya keyi mata nuni da cikin d’akin a rikice. Lek’a d’akin da Amal tace zatayi itama ta k’urma wani d’ankaren ihu had’e da k’arisasa da salati a guje tayi kan Afzal had’e da aza kansa akan cinyarta tana bubbuga fuskansa “Yaya? Yaya? Yaya please wake up” ba shiri ta shiga yin kuka “Yaya I’m terribly sorry dan Allah kayi hak’uri ka tashi na shiga uku Safiyya kije ki kirawo driver” a guje Safiyya ta fice Amal se kuka take a wajen yayinda take kakkarwa “Yaya dan Allah karka tafi ka barni I’m so sorry please don’t go.” Mik’ewa tayi ta janyo kayansa ta sanya masa sannan driver ya k’arisa ya cicci6esa sukayi mota duka har da Safiyya. Tunda aka shige da Afzal emergency room Amal keta safa da marwah bakin corridon gabad’aya ta rasa nutsuwarta tsabaragen yadda ta tsule ko Mami ta kasa kira bale su Ummi. Safiyya ce ta kira Nazefah ta sanar da ita, ita kanta Nazeefah bata d’au hakan ze tayar wa Afzal ciwonsa ba sosai ta rikice yanzu idan hakan kuma ya zame sanadiyan mutuwansa? Da ko itace da babban asara. Sarai tasan Afzal bayi so idan ciwonsa ya tashi iyayensa su sani amma da gan-gan dan aga laifin Amal ta kira Ummi ta sanar da ita akan Afzal ya samu attack ba shiri Ummi ta kira Abba ta sanar da shi.
   Kaman daga sama kawai Amal taga Nazeefah na shigowa bada dad’ewa ba sega Ummi har ma da Abba. Yau nata ya k’are ‘hasbunallahu wa ni’imal wakeel’ kawai take ta nanatawa. Kanta suka yo duka suna tambayarta meya faru Amal ta kasa magana se hawaye kawai daga k’arshe suka koma kan Safiyya.
  “Wallahi ban sani ba ya shigo gida yace in dafa masa spaghetti bayan da na gama naje nayi mai sallama amman shiru se nida Aunty mukayi zaton ko wanka yakeyi chan da shirun yayi yawa na sake duba shi bud’e k’ofan da zanyi kawai na tarar da sumemmiyar jikinsa a k’asa.”
  “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!” Ummi ta furta cike da tashin hankali.
  “Dole akwai abinda akayi masa” cewan Nazeefah dake ta faman kukan munafirci “Sanin mune nan duka ciwon Ya Afzal bai ta6a tashi kazai haka dole saida sanadi” Nan ta kewayo kan Amal da gaban hijabinta ya jik’e jak’ab da hawaye. “Amal mey kikayi wa Ya Afzal? Sanin kowa ne kece sanadin ciwon sannan mey kikayi masa?”
  “Nazeefah wani irin magana kike haka? Har kina tunanin zanyi wa Yaya abinda ze tayar masa da ciwonsa da gan-gan? Wallahi banyi wa Yaya komai ba wallahi ban mishi komai ba Ummi” ta sanar dasu cikin tsan-tsan kuka.
  “Taya zakice baki yi masa komai ba Amal bayan kinsan kece sanadin ciwon nasa? Bayan sarai kinsan da zaran kinyi masa abinda zuciyar bata so ciwon na iya tashi yet you still went ahead kika k’untata masa. Idan ban manta ba jiya kafin Ya Afzal yabar gidana seda yace kina yi masa abubuwan da baya jin dad’insu amma baze yi miki magana ba saboda yana gudun 6acin ranki meyasa ke bazaki mishi haka ba ki nisanci duk abinda ze 6ata masa rai?”
  “Nazeefah ki yarda da ni Ummi, Abba wallahi ban yi wa Yaya komai ba.”
  “Ummi wallahi ita ce ita ta janyo komi koda rasa ransa Ya Afzal yayi kisani kece sanadi Amal kuma bazan ta6a yafe miki ba idan wani abun ya samesa” nan ta fad’a jikin Ummi tana kuka.
STORY CONTINUES BELOW
  “Amal me kikayi wa d’ana? Mey kikayi wa Prince? A tunani na kece mace ta k’arshe da zata guji yi masa abinda zuciyarsa bata so meya faru Amal?”
   “Hajiya Mariam ya isa haka please mu jira likitan su fito tukuna” da haka Abba ya samu ya toshe wa Nazeefah da Ummi baki koda kowa ya nemi waje ya zauna Amal ta kasa zama se safa da marwah take a wajen chan globe na bakin k’ofan da akeyi wa Afzal aiki aciki ya mutu nan suka duk’ufa suna jiran fitowan Dr. Kusan a tare duk suka jefa masa tambaya.
  “Humm!” Dr’n ya sauk’e nauyayyan numfashi “Bazan 6oye muku ba ku sani by each attack da yake samu hakan na weakening rate and efficiency na heartbeat nasa ku magance masa matsala tun ba yau ba kun kasa kun zuba masa ido ranan da zuciyan ta buga gabad’aya shikenan se ku huta muma mu huta.”
  “Yanzu ya jikin nasa?” Abba ya tambaya.
  “Munyi masa abinda zamu iya sauran ku jira ya farfad’o d’ayan ku ya biyoni ya amshi list na drugs da za’a sai mishi.” Abba ne yabi bayansa ya rage su Ummi.
  “Ummi dan Allah kibar kukan haka” cewan Nazeefah tana share mata hawaye. “Amal kin de ji abinda Dr’n Ya Afzal yace ko? Rayuwan Afzal yayi depending akan ki ne dan Allah ki kiyaye k’untata masa idan baki damu da shi ba mu nan we love and care about him.”
  “Nazeefah-“
  Katse ta tayi da wuri “Ummi wallahi tun ba yau ba Ya Afzal yake mun complaining akanta gashi yanzu seda ta kwantar mana da shi.”
  “Nazeefah wallahi bani bace dan Allah ki yarda dani.”
  “Toh wa kikeso a zarga idan ba ke ba Amal? Ummi dan Allah ki sa baki.”
  “Amal dan Allah ba dan ni ba dan Allah nace kiyi hak’uri ki rufa mun asiri ki na yima Afzal abinda yakeso kin fi kowa sanin halin da yake ciki” Ummi ta rok’eta cikin kuka. “Na sani ba koda yaushe Afzal yake da dad’i ba amma dan Allah kina hak’uri da shi kina yi mishi abinda yakeso please Amal I can’t afford to lose him shi kad’ai Allah ya bani.”
  “Ummi dan Allah kiyi hak’uri I’m so sorry, please forgive me.”
  “Shikenan bari in shiga in duba sa” ta kai kusan minti goma aciki sannan ta fito har anan Afzal be tashi ba tana fitowa sega Abba nan shima ya dawo da magunan Afzal wanda ya mik’a wa Ummi. Bayanta ya bi ya shiga ya duba Afzal shima bayan ya fito ya buk’aci Nazeefah next da ta shiga, k’arshe Amal  ta shiga. A hankali ta k’arisa cikin d’akin ta zauna daga gefensa tare da sa hannunta cikin gashin kansa tana shafawa a hankali.
  “Yaya I’m so sorry dan Allah ka tashi ka fad’a musu bani bace” kuka ta shiga yi sosai a wajen a hankaki ta kwantar da kanta a k’irjinsa yayinda kukan nata ya tsananta “Yaya please wake up wallahi ban aikata ko abu d’aya daga cikin ababen da kake tokari na dasu ba wallahi wasu ne suke neman shiga tsakanin mu Yaya bazan ta6a aikata abinda nasan ze 6ata maka rai ko zubar maka da mutunci ba you have to believe me and stop bothering yourself I beg of you please” a hankali ta d’ago da kanta tare da had’a hannunsu gu d’aya “I love you so much and no matter what I’ll never leave your side” a hankali ta sauk’e light kiss akai. Har ta kai ga mik’ewa taga ya motsa yatsansa zamanta ta gyara ta shiga kiran sunansa har seda ya bud’e idonsa.1
  “Yaya you’re back!” Tayi exclaiming ba shiri tayi hugging nasa sede ko ta6a jikinta beyi ba gabad’aya ji yayi ta haramta masa tunda har yanzu Abdul ne a zuciyarta. A hankali ta d’ago daga jikinsa “Yaya what happened?” ta tambayesa had’e da zira hannunta cikin gashin kansa. Kan nasa ya shiga girgizawa da nufin baya so a hankali ta maida hannun nata “I’m sorry” tayi apologizing.
STORY CONTINUES BELOW
  “Su Ummi suna waje bari inyi musu magana su shigo” kansa taga ya kawar gabad’aya dan ko kallon ta baya sha’awan yi ko a mafarki akace masa Amal zatayi masa haka baze yarda ba kuma ba abinda yafi tsana kaman wannan munafikin halin hawainiyan nata, zatayi abu kuma ta zagayo kaman batayi komi ba tana proving innocence. Ko a ina yaci karo da rubutun chan yasan nata ne.
  “Yaya har yanzu fushi kake dani? Yaya wallahi ban aikata ko d’aya daga cikin abubuwan da kake tokarina dasu ba Yaya sanin kanka ne ina sonka kuma bazan ta6a yin abinda ze 6ata maka rai ko zubar maka da mutunci ba you have to believe me.”
  “Ki kira mun Ummi da Nazeefah” yace da ita zalla ba tare da ya kalleta ba hawayenta ta share sannan ta mik’e “Allah baka lafiya” ko ta kanta beyi ba har ta fice
  “Ya Afzal ya farfad’o Ummi.”
  “Ya farfad’o?” Ummi ta tambaya had’e da mik’ewa. Haushi Nazeefah taji wato seda Amal ta shiga ne ya ga daman tashi akan duk uban kalaman soyayyan da tayita fad’a masa? Duk su kwantar da hankalinsu soon enough ze saki Amal d’in.
  “Yana buk’atan ganinki da Nazeefah.”
  “Alhamdulillah! Alhamdulillah” ta mik’a godiyar wa Allah.
  “Abba fah?” Amal ta tambaya.
  “Ya koma” Nazeefah ta amsa. Tana ganin shigewansu ta kira Safiyya suka koma gida tunda baya buk’atan ta na mey zata cigaba da zama?
  “Prince!” Ummi ta kira sunansa had’e da hugging nasa “Prince dan Allah kayi a hankali wallahi likitanka na jiye maka.”
  “Ummi please it’s okay I’ll be fine.”
  “Welcome back Ya Afzal” Nazeefah dake tsaye akansa ta fad’a mai.
  “Thank you Rabba’atul Bait” ya amsa yana mata murmushi.
  “Prince meya faru? Mey Amal tayi maka?”
  “Amal kuma?”
  “Ka fara da zurfin cikin nan naka ko? Nazeefah ba ke kikace Amal ce bata kyautata masa ba?” Ido ya d’ago yana kallon Nazeefah da cikinta ya d’au ruwa tuni ta shiga rarraba ido.
  “Haka nace miki?”
  “Ya Afzal naga.. ermm… Toh ai sanin kanmu ne duka nan Amal ce sanadin ciwon naka Ya Afzal ko ba kai ka fad’a mun ba?”
  “Se kuma nace miki Amal ce bata kyautata mun?”
  “Toh waye ne?” Ummi ta tambayesa “Wayene idan ba Amal d’in ba?” Shiru yayi bece komai ba dan haka Ummi tayi tunanin ko bayi son yayi maganan a gaban Nazeefah ne. “Ermm nace mey kakeso kaci Prince Nazeefah ta girka ta kawo maka? Girkin waye ne acikinku?” Ta tambayi Nazeefah.
  “Girkin Amal ne amma ba damuwa zan girka in kawo masa mey kakeso Ya Afzal?”
  “Boiled potatoes da egg sauce” ya sanar da ita.
  “Toh bari inje zan dawo yanzu in shaa Allah.” Tana ficewa Ummi ta dawo da kallonta akan Afzal “Toh Nazeefar ta tafi gaya mun meke faruwa?”
  “Ummi babu” mari me zafi ta kai masa akan cinya. “Ummi please! Kin fa san hannunki da zafi.”
  “Ina tambayanka abu kana kallon cikin idona kana mun k’arya? Nace meya faru? Wallahi ka kuskura kayi mun k’arya toh ni da kai.”
STORY CONTINUES BELOW
  “Ummi misunderstanding muka samu.”
  “Fad’a kukayi?” Kai ya gyad’a mata “Amma mun shirya shigowantan nan.”
  “Ka tabbata?”
  “Eh Ummi.”
  “Ba senayi mata magana ba?”
  “Babu amfani komi ya wuce.”
  “Toh koma meye ne de ka daina bin komi da zuciya haka kasan yadda zuciyar taka take da rauni please Prince Abbanka ma na nan ai d’azun ya tafi.”
  “Allah sarki ku daina tada hankalinku please I’ll be fine.”
  “Zaka kwana ko zaka koma gida a yau?”
  “Kwana kuma? Na samu sauk’i se in kwana a asibiti? Nazeefah na kawo mun abinci naci zan koma gida.”
  “Kana buk’atan wani abu toh?”
  “A’a zaki iya tafiya Ummi thank you so much.”
  “Don’t mention my boy Allah baka lafiya ko?” Kai ya gyad’a tare da amsawa yanayi mata murmushi. “Bari inyi ma Amal magana tazo ta tayaka zama kafin nan.” Da mamaki ta nemi Amal bayan fitanta ta rasa ta dawowa ciki tayi tace, “Ban ganta ba fa, kode ta tafi ne?”
  “Ohh ban fad’a miki ba ko? Na ce ta koma kinsan itama kwana biyu bata ji dad’i ba zazza6i ya sata a gaba.”
  “Haba! Shiyasa na ga ta rame Allah sarki Allah shi bata lafiya.”
  “Ameen Ummi.” Zama ya cigaba dayi cikin d’akin har zuwa lokacinda Nazeefah ta kawo masa abincin ita da kanta ta basa bayan da ya gama tayi ma likitin nasa magana akayi discharging nasu. Kasancewar kwanan Amal ne har cikin gida Nazeefah ta kaisa sannan ta juya ta wuce nata gidan. Sannu da zuwa Safiyya tayi masa lokacinda ya shigo ciki.
  “Ina Amal?” Ya tambayeta.
  “Tana d’akinta” k’arisawa d’akinsa yayi ya zaro takardan d’azun had’e da ninkewa ya adana. Wayansa ya d’aga dan kiran Sultan inda ya tarar da missed call na Abba nan take ya kirasa back suka gaisa Abba yake mishi jaje. Suna k’are wayan ya kira Sultan.
   “Maza yane?”
  “Ba lafiya ba yanzu haka daga asibiti nake.”
  “Subhanallahi meya faru ciwon naka ne?”
  “Yes and alot has happened Sultan ka shigo gobe kaji?”
  “Toh sannu ya Amal ko gun Nazeefah kake?”
  “Ni seka shigo kawai” tun daga amsan sa Sultan ya gane akwai matsala “Allah kaimu goben toh.”
  “Ameen” Afzal ya amsa had’e da katse wayan. Zama ya cigaba dayi a d’akin chan bayan sallan Maghrib Amal tayi sallama cikin d’akin nasa shiru yayi yak’i amsawa dan haka ta bud’e k’ofan ta shiga kansa yayi saurin kawarwa.
  “Yaya-“
  “Get out Amal bana k’aunan sake ganinki a cikin d’akin nan in shaa Allahu burin ki ya kusan cika kiban lokaci kad’an.”1
  “Yaya mey kake nufi? Wani buri?”
  “Just get out Amal in kuma fitan ne bazaki iya ba ina iya bar miki gidan gabad’aya.”
STORY CONTINUES BELOW
  “Allah huci zuciyanka” tace mishi zalla ta juya ta fice d’akinta ta koma inda ta kwanta kan gado ta shiga kuka sosai.
  Washegari kaman yadda Sultan ya mar alk’awari haka yazarce gidan nasu daga office da Amal suka fara had’uwa lokacin tana zaune a dining tana cin abinci sannu da zuwa tayi masa tasa Safiyya ta kawo masa drink da snacks.
  “Kinyi wuyan gani amarya.”
  “Ji Ya Sultan nice amaryar?”
  “Amaryar amini na ma kuwa ke baki san yadda nake ji dake ba ko?”
  “Uhm haka de kace amma ka barni da makaranta yana ta bani wuya.”
  “Karde shiya ramar dake haka? Har kun fara tests ne?”
  “Ai mu kullum cikin tests muke Ya Sultan se a hankali.”
  “Allah sarki ba three kike ba yanzu? Kinyi mey wuyan ai Allah sa albarka.”
  “Ameen Ya Sultan yasu Umma?”
  “Lafiyansu k’alau Afzal fa yana gida?”
  “Eh ba motansa na waje ba?”
  “Na sani koya fita strolling ya jikin nasa?”
  “Toh Alhamdulillah de bari inyi mishi magana” nan ta mik’e ta nufi d’akin nasa sallama tayi amma be amsa ba dan haka ta bud’e ta shiga akan gado ta tsincesa yana bacci k’arisawa tayi had’e da tapping nasa a k’afa a hankali.
  “Yaya? Yaya ka tashi Ya Sultan yazo” a hankali ya shiga bud’e idonsa har ya bud’e su duka ganin ita ne yayi saurin kawar da kansa “Bance kar in sake ganin ki acikin d’akin nan ba?”
  “I’m sorry Ya Sultan ne yazo ya turo in kira ka” da haka ta juya ta fice. Brushing yayi ya wanke fuskansa sannan ya sanya shiry akan gajeren wandonsa ya fito ya sami Sultan. Bayan sun gaisa ya ce mishi su k’arisa ciki.
  “Meya samu nan d’in? Ko so kake mu koro Amal waje ita da gidanta?”
  “Bata d’akin come in” be sake musu ba ya mik’e suka k’arisa d’akin. Note na Amal ya d’au ya wulla wa Sultan akan cinya “Wannan fah?” Sultan yayi saurin tambaya.
  “Ka bud’e kayi observing handwriting dake ciki” yadda aka ce da shi haka yayi bayan ya karance rubutun ya d’ago kai “Ehen?”
  “Here take a look at this handwriting” yayi maganan yana zaro takardan d’azun daga inda ya 6oye “Handwriting na mutum d’aya ne ko kuwa?”
  “Of course na mutum d’aya ne mana” Sultan ya amsa bayan yayi comparing handwriting d’in.
  “Thank you ka zauna da kyau ka karanta content d’in.” Hankali ya miyar kai ya shiga karancewa yayinda mamaki ya mamaye mai fuska da zuciya.
  “Waya rubuta wannan maza?”
  “Ka duba sunan dake jikin littafin” Afzal ya umarcesa.
  “You don’t mean this!” ya furta bayan daya duba yaga sunan Amal rubuce a bangon littafin.
  “Yanzu zaka ga laifina idan na yanka mata ko wani irin hukunci?”
STORY CONTINUES BELOW
  “Ban fahimce ka ba Triple A kana nufin Amal ce ta rubuta wannan?” Ya tambaya da d’umbun mamaki.
   “Baka iya karatu bane?”
  “I’m just confused Triple A, Amal de? Har Amal ce zata rubuta wannan abu? Kode kafin kuyi aure ne?”
  “Kana ganin sabon paper sabon rubutu kana zancen kafin muyi aure?”
   “Amma meya faru? Meyayi zafi da har Amal zata rubuta wannan abu a matsayinta na matarka?”
  “Gata chan a chan d’akin kana iya zuwa ka tambayeta.”
   “Wow!” Ya numfasa totally speechless.
  “Maza ban san meyake damun Amal ba yarinyar nan ta sauya gabad’aya ta koma wani abun daban banda munafurci da had’a kaina da Nazeefah ba abinda takeyi ko tsinke na sai mata seta buga waya wa Nazeefah ta fad’a mata knowing right ba duka abinda nakeyi mata nakeyi wa Nazeefah ba sedan kawai ta 6ata ni idon Nazeefah tasa Nazeefah tayi mun kallon maras adalci hakan be isheta ba har course mates nata maza ta fara kawo mun cikin gidan nan suna zama a kujera d’aya.”
  “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un wacce Amal tukuna? Amal Amal naka da na sani?”
  “Ita de Amal ta cikin gidan nan.”
  “Maza are you sure of what you’re saying? Amal ce har zata shigo maka da gardawa cikin gidan nan?”
  “In kira maka mey aikinta ne ka tambayeta?”
  “Subhanallahi meya sameta?”
   “Waya san mata ne?”
  “Mey kake nufi kenan yanzu kana nufin kana zargin Amal kenan? Kana zargin tana ci maka amana?”
  “Nooo not at all nasan Amal baza ta ta6a cin amanan aurena ba, ko tunanin yin hakan ma baza tayi ba I know that.”
  “Toh mey kake nufi da tana shigo maka da maza gida?”
  “Yes ta daina shigo mun da coursemates nata saboda ba’a san abinda shaid’an ze iya raya musu ba wataran koba d’abi’arta bane wataran shi gardin ze iya kwad’aitar mata da hakan ko ba ka gane abinda nake nufi ba?”
  “Sosai na fahimce ka amma Afzal I’m still shocked Amal da muka sani ce ta sauya haka take yin ababen nan da ka irgo? Innocent Amal taka?? Na tabbata haka kawai Amal bazata sauya halayanta ba sede idan kai kayi pushing nata don’t you forget that for every reaction there’s an action.”1
  “Mey zanyi mata maza? Kafi kowa sanin irin son da nake yiwa yarinyar nan, Wallahi Amal bata ta6a neman abu a guna ta rasa ba komi ina yi mata da iyayenta amma ka kalli da abinda zata sak’a mun kuma abinda yafi bani haushi shine k’aryata komi da takeyi har yanzu ita bata amince da laifukanta ba bale ta nemi tuba mu sasanta tsakanin mu ni bazan iya ba, I can’t do this anymore I’m tired of her sick behavior.”
  “Mey kake shirin yi?”
  “Ba Abdul kowa take so ba? Seta je ta samesa.”
  “Wani irin magana kake haka Afzal? Da igiyan auranka akanta kake son taje ta auri wani?”
  “Sawwak’e mata zanyi.”
  “Mey?? Kana da hankali kuwa Afzal? Wani irin zafin kishi ne da kai haka?”
  “Toh mey kakeso inyi? Ba gara na sawwak’e mata ba taje ta samu shi wanda take son? Bazan iya zama da ita ba knowing zuciyarta na tare da wani gara na rasata gabad’aya dan idan har na cigaba da zama da ita toh zan cigaba da kallonta da abin ne wanda zuciya ta baza ta iya d’auka ba wataran sede ta har6a tabar aiki.”
   “Idan ka sawwak’e mata ta koma gun Abdul kai kuma fah?”
  “Na sani sena fita shan wuya bayan rabuwan nan amma ka gaya mun mey riban ajiyeta a wajena idan zuciyarta na tare da wani daban Sultan? I love Amal kuma har duniya ta nad’e bazan fasa sonta ba but this is not reason enough to keep her with me tunda gashi da hannunta ta rubuta bata sona tayi nadaman aurena. Kaji fa har cewa take wai dama tun fari tasan jikinta kawai nake so yanzu da na samu abinda nake nema gashi ina walak’anta ta. Ni fa Maza? Ni d’in da ko hannunta ban ta6a sha’awan rik’ewa ba… excuse me” tari ya shiga yi yayinda zuciyansa ya fara tashi yana yi masa k’una tsan-tsan takaici da bak’in ciki da 6acin rai.
  “Dan Allah kayi a hankali ba senun sake kaika asibiti ba it’s okay ya isa.”
   Gyaran murya yayi ya cigaba “So I think it’ll be better idan na barta taje ta samu shi wanda take so d’in ta huta kowa ma ya huta.”
  “Kai kuma fa Triple A? Ya zakayi da rayuwanka idan kuka rabu? Shin ka manta rayuwanka gabad’aya yana revolving ne a jikin na Amal? Shin ka manta idan ba soyayyarta zuciyarka bazata iya aiki ba? Shin ka manta idan ba ita a kusa da kai rayuwarka tana cikin gwagwarmaya? Ina ka mance da dukkan hakan Afzal har kake tunanin sawwak’ewa Amal? Besides ni ban yarda ma innocent Amal d’in da na sani zata iya aikata wannan munanan abubuwan da kake tokarinta da su ba. She’s too innocent to do all these I know Amal kuma na yarda da ita.”
“Ka san Amal kuma ka yarda da ita? Lmao” wani kalan dariyan rainin hankali ya saki “So kake kace ka fini sanin halin matata ko mey Maza?”+
  “I dunno but I guess yes saboda komin yaya nasan Amal bazata ta6a aikata wannan aika-aika ba.”
  “Mak’aryaci ne ni kenan? K’arya nakeyi maka? Is that it?”
  “Ba haka nake nufi ba Triple A amma da hankalinta kam Amal bazata ta6a aikata hakan ba, it’s either she’s possessed or something baka tunanin hakan?”
  “You mean you deny ba ita tayi wannan rubutu ba?”
  “Ba wai nace ba ita tayi bane it’s crystal clear rubutun tane amma waya sani ko wani mental illness ne yake damunta wanda idan ya tashi yake sanyata yin abubuwan nan daka irgo saboda a gaskiya bana tsammanin kan Amal ya waye d’inda har zatayi wannan abubuwa. Triple A kayi tunani mana kai fa da kanka kake yabawa da irin kyawun halatayyar ta.”
  “Mental illness? Gani kake kaman tana da ta6in hankali? Just so you know har asibitin mahaukata na kaita aka kuma duba ta and you know what likitan yace ba abinda yake damunta idan kuma tunanin aljanu kake nan ma na kaita gun Malami anyi mata ruk’iya shima yace bata tattare da komai lafiyarta k’alau so stop giving me lame excuses.”
  “Wow! But what’s really wrong? Ka sameta kayi mata magana? Kayi confronting nata? Maybe akwai wani 6oyayyan al’amari.”
  “Mey zance mata? Besides kasan ni ba d’abi’ata bane yima mutum magana idan yamun laifi idan shi hankalinsa be basa hakan ba ya nemi tuba ba sede a cigaba da zama hakan.”1
  “Kana nufin tunda abubuwan nan suka soma faruwa baka ta6a yiwa Amal magana ba?” Ya tambayesa da mamaki gaskiya ne mey hali baya canzawa ko shi yana iya tuna lokacinda suka kusan shafe term d’aya (k’imanin watanni uku) a makaranta shi da Afzal lokacinda suke boarding house basu magana a sanadin wasu maganganun da abokansu suka je suka shiryawa Afzal cewan Sultan ne ya fad’a. Shiko Afzal ba bincike ba komai kawai ya hau kan magana ya zauna akai. Kyat kawai Sultan yaga Afzal ya dai na yimai magana da k’yar suka zo suka daidaita tsakaninsu. Tun daga wannan rana ya karanci halin Afzal ko meye mutum yayi masa bayi ta6a tinkarar mutumin da maganar sede yayita kallon meshi da abun har zuwa lokacin da mutumin zey gano yayi kuskure ya nemi tuba. Bayan nan Afzal ya kasance d’aya daga cikin jerin mutanen da basu tsananta bincike game da duk wani abinda aka fad’a musu wanda hakan yake babban hatsari. Su komai aka same su aka fad’a musu d’auka suke su zauna akai ba bincike ba komai wanda sam hakan be dace ba musamman ma ga magidanci kamansa mey mata biyu. Tabbas yasan a banza Afzal yake hukunta Amal baiwar Allan da bata ma san mey tayi ba yanzu. Ashe dalilin da yasa ta zube tayi duhu kenan bak’in ciki ne da tashin hankali ba stress na makaranta kaman yadda tace ba. Allah sarki.
  “Maza that’s so unfair hukuncin nan da ka yanke yayi wa Amal tsauri dayawa kuma wallahi bazan 6oye maka ba ba haka ake ajiye gida ba, ba haka ake handling mata biyu ba. Afzal da dayanzu ba d’aya bane, yaci ace ka zubar da mumunan d’abi’ar nan naka na kallon mutum da laifi ka fara tunkararsa da laifin da yayi maka kaji mey zece, kuma be dace a matsayinka na mey mata biyu ace dan uwar gidan ka ta fad’a maka abu kawai ka hau ka zauna akai ba kamata yayi ka tsananta bincike ka zaunar da Amal kuyi magana kaji nata 6angaren labarin itama na tabbata akwai ababen da Nazeefah takeyi mata wanda bata jin dad’insu amma ta za6i ta had’iye wa kanta dan karta had’a kanku haba maza! Wallahi sam baka kyauta wa Amal ba.”
  “Naji nasan bana tsananta bincike kuma bana confronting mutum idan ya mun laifi amma wallahi akan Amal na fara yin hakan bayan da Nazeefah ta irga mun komai nayi mata magana.”
“And mey tace?”
  “K’aryata komi tayi abinda ya fi bani haushi kenan, tayaya Nazeefah zata na sanin abubuwan da suke gudana a cikin gidan nan idan ba wai kirarta ake ana sanar da ita ba? Ai abinda zaka duba kenan.”
STORY CONTINUES BELOW
“Wow! Ko ze iya yiwuwa hakan ne?”
  “Hakan kaman ya?”
  “Akan ba ita bace bata aikata abinda kake tuhumarta dashi d’in ba.”
“Are you kidding me? Ka zauna kayi tunani Sultan ko tsinke na saya mata a gidan nan se naji labarin a bakin Nazeefah how on earth Nazeefah zata san abinda ke gudana acikin gidan nan idan ba wai kirarta ake ana fad’a mata ba? Ko so kake kace tana da CCTV ne?”
  “No bawai haka nake nufi ba.”
  “Then tell me, tell me how exactly would Nazeefah know of everything da nakeyi wa Amal?”
  “You have a point amma still da kayi mata uzuri sanin kanka ne Amal yarinya ce, halan yarinta ke damunta ka sameta kayi mata magana kaja mata kunne I’m sure zata saurareka ta kuma daina.”
  “Yarinta ko rashin tunani? Wallahi da gan-gan takeyin komai, and you seem to be forgetting her actual age, Amal is 21 years old Sultan she’s nomore a child.”
  “Naji nan Amal bata kyauta ba tayi laifi, amma batun shigo da course mates nata maza cikin gidan nan fa? Ka ga hakan da idonka ne?”
  “A’a amma ai ‘yar aikinta ne ta fad’a mun.”
  ‘”Yar aikinta?” Yayi questioning nasa unbelievably ‘”Yar aikinta fa kace maza?”
“Yes ba ita take gida ba kullum ai tana sane da shigowa da fitan kowa.”
  “Amma Maza ka bani kunya, ban ta6a sanin kana da k’arancin tunani haka ba se yau ashe baka fasa halinka ba har yanzu wai tayaya ma zaka fara amincewa da abinda baka ji ba bale ka gani? Wallahi zato zunubi ne.”
“Ce maka akayi zato nakeyi? Clearly ‘yar aikinta tace sau biyu take ganin Amal na shigo da course mates nata har ragowan snacks da drink data basu ma na dawo gida na tarar ranan what else do you expect me to believe?”
  “Ka tambayi me gadinka ne? Ka tsaya kayi wa ita Amal d’in magana kaji labarin daga bakinta? You have to listen to both sides before taking a decision Afzal dole ne ka zubar da wannan halin naka kafin lokaci ya k’ure kazo kana nadama, tabbas duk wanda baya tsananta bincike yana tattare da babban hatsari bana son kazo kayi nadama daga k’arshe.”
“Kana tunanin Safiyya zatayi ma Amal sharri ne? Meye ribarta idan tayi hakan?”
“Kai kuma kana tunanin Amal zatayi maka k’arya ne da tace maka ita bata shigo da na miji gidan nan ba? Wai taya ma zaka fara amincewa da maganan mey aikinka akan na matarka ne Afzal? A ina aka ta6a yin hakan?”
   “A gaskiya ka bani kunya maza yadda kana ganin gaskiya kake takewa.”
   “Ma tukun a ina ka tsinci wannan paper?”
  “Cikin kayakina.”
  “Lmao cikin kayakinka? Wallahi ka bani kunya Afzal, it’s so unfortunate that you’re my friend. Har kana tunanin Amal zata rubuta wannan abu takuma sake ajiye maka shi acikin wardrobe inda ze fi sauk’in ka gani? A tunani na sede ta 6oye ba ta ajiye a inda zaka gani ba. Wallahi Allah this’s a trap.”
  “Har wani marasa aikin ne ze zauna yayi wannan aiki? Kuma har ya iya yayi irin rubutunta sak?”
  “The world isn’t a safe place and there are toxic people everywhere so zan baka shawara ka zauna ka bi diddigin lamarin nan idan ma da hali ka zaunar da Amal d’in da Nazeefar da mey aikin nata da mey gadin naku duk gabad’aya kayi musu tambayoyi ka kuma saurari both parties am very sure zaka sha mamaki da sakamakon da zaka samu” yana kaiwa nan ya mik’e “wannan kuma” yayi nuni da takardan hannunsan.
  “Duk da cewa rubutun Amal ne karara ajiki hakan baisa na yarda itace ta zauna ta rubuta ba kuma koda ma ita d’ince zan iya cewa tana da daman yin hakan tunda gashi a fili kake nuna mata rashin k’auna da adalci ta hanyan yanke hukunci ba tare da ka saurareta ba zan iya cewa abubuwan da kakeyi mata su suka tunzira ta har ta zauna tayo wannan rubutu, kai baka san the more kake k’untata mata the more kake sa take tunanin masoyinta Abdul take kuma kewon sa ba? Ko ka manta yadda kukayi auren nan ne Afzal? Yarinyar nan fa ba wani sonka take ba, lami lafiya suke soyayyansu da saurayinta suna building dreams nasu ka shiga tsakanin su haka dan ta ceto ranka ta sadaukar da farin cikinta da abin alfaharin zuciyarta. Kana ganin ta cancanci wannan walak’ancin da kakeyi mata? The earlier the better Triple A it’s time for you to make things right idan kuma har bakayi ba toh ni zanyi da kaina” yana kaiwa nan ya ajiye takardan ya fice.
STORY CONTINUES BELOW
Mugun d’aurewa kan Afzal yayi gabad’aya ya rasa meke masa dad’i what if duk abubuwan da suka faru set up ne kaman yadda Sultan ya fad’an amma ai kuma wannan rubutu is real ko a mafarki aka nuna masa rubutun nan yasan na Amal ne. Amma kuma idan har ita ta rubuta ai baza ta ajiye a open place inda ze gani ba sede ta nemi wani 6oyayyan wajen ta ajiye, ya Allah what’s really happening? Yini yayi gabad’aya ranan yana tunani ya kasa samun sukuni wajajen tara hak’urinsa ya k’are. Maybe is about time ya tunkari Amal suyita ta k’are.
D’akin ta ya nufa inda ya tsince ta zaune bakin gado tana karatu da mamaki ta tsaya tana kallonsa ba tare da tace komai ba. Takawa cikin d’akin yayi ya k’wace handout natan kafin tace zatayi magana yaja hannunta ya mik’ar da ita ya shiga janta waje.
“Yaya what’re you doing? Ka sakeni let me go” ko sauraranta beyi ba seda ya kaita tsakan d’akin nasu. Wardrobe ya nufa ya zaro takardan har anan kallonsa Amal take yayinda zuciyanta yake bugun d’ari-d’ari dan yadda ta tsure a tunaninta gabad’aya dukanta yake shirin yi. Takardan ya bud’e a idonta “rubutun waye wannan?” ya tambayeta?
“Rubutu na” ta amsa a takaice.
Sa mata yayi acikin hannu “here read it” d’agawa tayi ta shiga karantawa layi uku ta karance ta shiga kad’a kanta yayinda idanunta suka ciko dam da hawaye amma Allah ya isa tsakaninta da Safiyya da Nazeefah. Tun a asibiti ta gano Nazeefah ba sonta take har cikin zuci ba, tun anan ta gano Nazeefah ba da zuciya d’aya ta d’auketa ba. Tun anan ta gano Nazeefah is behind everything that has been happening to her barin ma yadda ta dage ta rink’a nunawa Ummi cewa lallai-lallai ita ce ta sa zuciyan Afzal ya buga. Ta sani ba wanda zeyi mata wannan d’anyen aikin se su, Maamah batayi k’arya ba da tace suna aiki tare idan ba haka ba tayaya Nazeefah zata san takai Afzal asibiti idan ba wai kirarta Safiyya tayi ta sanar da ita ba.
“Wallahi Yaya bani na rubuta ba” ta sanar da shi cike da tashin hankali.
“Ba ke kika rubuta ba?”
“Yaya wallahi bani bace wallahi bani na rubuta ba” rantsuwa ta shiga yi yayinda hawaye ya fara tsiyaya daga idonta.
“Can you even listen to yourself Amal? Aljani kike son kice ya rubuta ko mey? Ko kin k’aryata wannan ba rubutun ki bane?”
“Yaya you have to believe me wallahi bani ce na rubuta ba bazan ta6a yin abu haka ba” ta sanar da shi cikin tsan-tsan kuka ransa ne ya gama 6aci gabad’aya besan a lokacinda ya damk’ota ya shiga jijik’ata ba “Why do you have to keep on lying to my face Amal? Why!?” Ya tsawata mata kakkarwa take sosai yayinda hawaye ya shanye mata murya “I love you Amal, I love you morethan anything in this world amma da abinda zaki sak’a mun kenan? Duk kalan halaccin da nayi miki a rayuwa you think I deserve this from you? Har ni zakice jikinki kawai nakeso ba zuciyarki ba? Ni Amal? In ba da mukayi aure ba ko hannunki na ta6a sha’awan rik’ewa ne?”
“Ya- Yaya please believe me” ta ce dashi muryanta na d’aukewa “Wallahi bani na rubut-“
“Damn it Amal!” Ya katse ta. “You’re such a horrible liar, idan ba ke ba toh waye? Waye yake da irin sigar rubutunki bayan kanki? Answer me!” Ya sake daka mata wani tsawan da gabad’aya yasa jikinta rawa fiye da na da. Ita tsoronta ma kar gabanta ya cigaba da fad’i abu ya samu d’an cikin nata ne tunda de bawai cikin babba bane abu kad’an yana iya zubar dashi.
“Wallahi bani bace-“
“When will you stop lying to my face? When Amal?” tureta yayi kad’an ya rage bata sha k’asa ba “Stop lying to me already just admit it, confess all your crimes a shirye nake in yafe miki mu fara sabon rayuwa all over again Amal just admit it.”
Cikin tsananin kuka tace, “I have nothing to admit Yaya saboda bani bace wallahi ba ni na rubuta wannan abu ba.”
“You’re still not telling me the truth.”
STORY CONTINUES BELOW
“You have to believe me wallahi ba k’arya nake yi maka ba-“
“You’re lying! Just admit it, admit it already.”
“Yaya I have nothing to admit ya, taya kake tsammanin zan amince da laifin da bani na aikata ba? Wallahi bani bace wallahi bani na zauna na rubuta wannan abu ba, kana tsammanin har zan rubuta mumunan abu haka kuma se in ajiye a inda nasan idonka ze kai?”
“Fvck it!” Yayi growling yayinda yake wani irin nishi kaman zaki. “Amma rubutun waye ne?”
“Yay-“
“Just fvcking answer me!” Ya katseta cike da rashin hak’uri.
“Rubutu na ne amm-“
“Shhh!” Ya katse ta “Abinda nakeso inji kenan” hannu ya mik’a ya amshe paper’n “You’ve really hurt me Amal, you’ve hurt me so badly, kin karya zuciyan da take mutuwar sonki kin yasar, bazan ta6a mancewa da wannan abu da kikayi mun ba I might forgive you someday amma bazan ta6a mancewa dashi ba.”
Cikin sautin kuka ta kira sunansa “Yaya-“
“Just get out” ya sanar da ita a hankali.
“Yaya dan Allah ka saur-“
“I said get out!” Ya daka mata tsawa a raunane ta tsaya tana kallonsa sannan ta shiga takawa a sanyaye ta bar mai d’akin. Tana isa d’akinta ta baje akan gado ta shiga raira kuka. Kuka take wane zata cire ranta har seda ta fara jin k’warnafi. Bayi ta fad’a ta shiga kwararo amai kaman ba gobe seda ta harar da duk wani abunda yake cikinta sannan ta lalla6a ta fito. Yanzu ta tabbata da abinda Maamah ta jima tana fad’a mata. For all these while Safiyya amanarta ta rink’a ci ita ta ringa zuba mata gishiri da borkono a girki, ita ta rink’a kwasan abinda Afzal ya keyi mata tana kaiwa Nazeefah, ita ce ta fad’a masa tana kawo maza gida, ita ta kira Nazeefah ta sanar da ita suna asibiti bayan da ta ajiye masa wannan takarda ya karanta. Wow!
Meyasa ta kasa gane gaskiya tun farko? Meyasa bata gane Safiyya ce behind everything ba? Tabbas ta tafka sokanci gaskia ne da Maamah tace mata yadda ka d’auki nutum da zuciya d’aya yanzu shi ba haka ya d’aukeka ba. Ko da wasa bata ta6a kawowa a ranta cewan Safiyya zatayi mata abinda tayi ba. Bature beyi k’arya ba da yace “Trust No One” tabbas da tun farko bata ajiyeta kusa da zuciyarta ba da tun kafin abu ya ta6ar6are haka zata gano gaskiya. Tsakaninta da Nazeefah kuma sede tace Allah, Allah kad’ai ze sak’a mata yabi mata hak’k’inta. Chan ta mik’e taje ta samu Safiyya a d’akinta.
“Sannu Aunty ya jikin naki?”
“Safiyya a iya zama na dake ban ta6a cutar dake ba, ban ta6a tokararki ba, ban ta6a tauye miki hak’k’in kiba a matsayin k’anwa ta ta jini na d’aukeki da zuciya d’aya shiyasa har yanzu na kasa gane dalilin da zaisa kiyi mun abinda kikayi mun.” Cike da d’aurewan k’wak’walwa Safiyya ta tsaya kallon Amal yayinda cikinta ya d’au ruwa lokaci guda bade Amal ta ganota ba? Yau kashinta ya bushe ta shiga uku ta lalace.
“Mey na miki da kika za6i ki k’untata mun acikin gida na ki hana ni sakat? Mey na miki da kika za6i ki shiga tsakani na da mijina kisa har ya fara zargina akan ina ci masa amana? Mey na ta6a yi miki Safiyya? Amma ba komai ki kira uwar d’akinki ki sanar da ita cewan ta kwantar da hankalinta saboda burinta na rabani da Ya Afzal ya cika koda Yaya be sakeni ba ni zan tattara kayakina in bar gidan nan tunda kun riga kun juyar mishi da kai kunsa yana mun kallon munafuka, mak’aryaciya, annanimiya wace bata da aiki sena gulma. Ba gidan kukeso ba? Zan tattara kayakina in bar muku ita” bata jira jin mey Safiyya zata ce ba ta juya ta fice. Bayi Safiyya ta shiga a guje ta juye fitsarin da ya matseta a lokaci d’aya sannan ta fito ta d’au wayarta dan kiran Nazeefah se kakkarwa take yayinda jikinta yayi la’asar da irin kalamun da Amal ta fad’a mata sede sam layin Nazeefah yak’i shiga.
STORY CONTINUES BELOW
****
Babban akwatinta ta janyo daga d’akin da ta tarasu aciki ta nufi d’akinsu da Afzal sallama tayi sannan ta shiga ko kallan Afzal dake mik’e akan gado batayi ba ta zarce direct wajen wardrobe, da mamaki ya mik’e zaune yana kallonta sede bece da ita ko uffan ba. Kayakinta yaga ta shiga tattarewa na matuk’a ta basa mamaki shin mey take shirin yi? Tafiya? Tafiya zatayi ba tare da ya bata takarda ba? Ido ya cigaba da zuba mata yana ganin iya gudun ruwanta. Kayakinta ta cigaba da tattarewa tana had’awa tana gamawa da fannin kayakin ta zarce gaban mirror ta d’ibi mayukan shafawanta da turare da makamancin haka sannan taja akwatin ta fice har anan Afzal beyi mata magana ba. Handouts nata da littafafai da sauran muhimman abubuwan da zata buk’ata ta tarasu cikin wani akwati daban shima.
Na sosai Afzal ya kasa kunne yana jiran jin k’aran engine na mota inda ze tabbatar da tafiya Amal zatayi kokuwa kawai ta tare kayakinta ne ta k’aura izuwa d’akin da ta koma gabad’aya. Washegari da sassafe ko karyawa Amal batayi ba taja akwatinta ta fice. Ko da driver yace ze kaita inda zata hanasa tayi napep ta tsara a waje bayan d’an takawan da tayi ta wuce gida. Har bakin k’ofa ya sauk’eta sannan ta sauk’e kayakinta ta sallamesa ta k’arisa ciki.
Papi ta tarar a tsakar gida yana zaune yayinda suke hira da Mami dake kitchen tana shirya musu abun karin kumallo. “Baby!” Ya kirata da mamaki yana bin jakukkunan hannunta da kallo “Ya haka? Meya faru?” Ya jero mata tambayoyi. Ba shiri Mami dake kitchen ta sauk’e tukunyarta ta fito tana kallon abin al’ajabi. Ba k’aramin tsinkewa zuciyanta yayi ba ganin Amal da akwati haka, Allah de yasa ba abinda take zargi bane. Da sauri sukayi kanta suna tambayarta meya faru. Sede wane ‘yi kuka’ suka ce mata dan yadda ta rushe da wani irin masifaffen kuka, a rikice Mami ta jata jiki ta shiga hugging nata tana bubbuga bayanta yayinda Papi yaja akwatunan nata suka k’arisa ciki. Dan kukan da takeyi Papi ya rok’i Mami da tabar ta da tambayoyin haka ta bari se idan ta huta tukuna. Dan haka suka fita daga d’akin suka barta, kukan ta cigaba dayi har izuwa lokacin da wani wahalallen bacci ya d’auketa.
****
Wajajen tara da rabi Afzal ya tashi daga bacci bayan yayi wanka ya sanya shirt da shorts ya fito inda ya tarar da Safiyya na goge-goge. Cikinsu duka ba wanda yasan da tafiyan Amal banda mey gadi da driver. A cewan Safiyya har Amal ta irga wa Afzal halin da ake ciki ne don haka tayi surrender ta tsaya chak gu d’aya tana jiran sauk’an mari a fuska kawai setaji ya tambayeta “Ba gaisuwa ne?”
“Yi hak’uri ina kwana Uncle wallahi hankalina ya tafi wani gun ne” Ta gaishesa “Lafiya” ya amsa “Kiyi mun frying chips da two eggs.”
“Toh barin kammala aikin nan” instead ya wuce d’akinsa se yayi tunanin lek’a na Amal inda ya tarar da d’akin empty, shiga yayi ya zauna yana jiran fitowarta dan a tunaninsa gabad’aya ta shiga bayi yin wanka ne sam be kawo a ransa wai har Amal ta tafi ba. A cewansa tunda bata tafi jiya ba that means ba yaji zatayi ba kawai ta tattare kayakinta ne ta dawo dasu nan gabad’aya. Sede da ya duba gaban dressing mirror ya tarar dashi empty ko vaseline babu. Tirk’ashi! Ba shiri ya mik’e yayi knocking bisa k’ofan bayin, jin shiru seya bud’e ya lek’a ciki inda ya tarar da bayin empty a guje ya fito yana tambayar Safiyya ko ina Amal taje sede kaman yadda baida masaniya itama hakan ne. Waje ya fita yana tambayan mey gadi ko yaga fitan Amal.
“Tabbas naga fitanta Ranka shi dad’e nima na bud’e mata k’ofar.”
“Ina taje? Ita kad’anta ta fita ko kuwa da akwati?”
“Akwati har biyu.”
“Damn it! Meyasa baka hanata fitan ba kokuwa ka kirani ka gaya mun? Shin baka san aikinka bane? Mstww!” ciki ya dawo ya d’aga wayansa har ya danna kan contact na Amal don kiranta se kuma ya fasa yayi sauri ya katse wato shi be yi zuciya ya ce ya saketa ba be kuma ce ta tafi gida ba itace take da zuciyan yin hakan? Ita gata tana da gun zuwa wato, da kyau ta kyauta taje duk inda zata je.
STORY CONTINUES BELOW
*****
Wajajen goma da rabi Amal ta tashi inda ta fara duban wayanta saidai da mamaki taga ko message Afzal be tura mata ba bale ya kirata, lallai yau ta gane waye Afzal. Wannan walak’anci da mey yayi kama? Ace yana kallonta tana shirya kayakinta amma ko yayi mata magana bale yayi tunanin hanata. Yanzu kuma da ya tashi yaga bata gidan meya kamata yayi? Lallai yau tasan inda ya ajiyeta, yau tasan matsayinta a zuciyansa, yau ta tabbata Yaya baya sonta.
Masa me kyau Papi ya aika aka siyo mata ta karya da shi tasha magunanta alai sannan Mami ta shigo suka gaisa.
“Bakida lafiya ne?” Mami ta tambayeta tana bin magunan dake gabanta da kallo.
“Eh Mami ban ji dad’i sosai ba kwana biyu.”
“Allah sarki, Allah sawwak’e.”
“Ameen.”
“Ya baki ci masan ba sosai duka fa naki ne mu tun d’azun muka karya.”
“A’a Mami na k’oshi na d’an ci ai anjima ma ina da test.”
“Kai haba?”
“Wallahi around 1 haka.”
“Toh Allah ya bada sa’a Papinki na buk’atan ganinki.” Hijabinta ta sanya ta mik’e a sanyaye tabi bayan Mami bayan sun k’arisa d’akin nasa suka nemi waje suka zauna daga angles na d’akin. Gaisuwa suka fara yi bayan nan Papi yake tambayarta meke faruwa.
“Papi komai ma ya faru, ba abinda be faru ba ni kawai kar ku sake turani gidan Yaya dan Allah” seta rushe da kuka.
“Subhanallahi ya isa haka kinji? Ba wanda yace ze sake mai daki gidansa fad’a mun meya faru.”
“Nazeefah ba kishiyar arziki bace after all, yadda na d’auketa da zuciya d’aya ba hakan ta d’aukeni ba, ashe duk shiri ne bawai har cikin zuciyarta bane tana so na, son munafurci take yi mun….” nan ta kwashe labarin duk yadda akayi tun daga kan lokacin da Safiyya ta fara zuba mata gishiri da borkono a girki zuwa kan lokacin da Afzal ya fara shasshareta zuwa kan lokacinda tayi masa magana yace tana kire-kiren waya tana baza sirrin gidanta a waje, zuwa kan lokacin da Safiyya tace ta fara kawo maza gida har izuwa na takardan da suka sa wa Afzal cikin kaya bata 6oye masu komai ba illa labarin cikin da take d’auke da shi.
“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un” kawai Papi yake ta nanatawa da mamaki bayyane karara a fuskansa itakam Mami se tafe hannu kawai takeyi dan mamaki ko salatin ma ta kasa ambata.
“Kikace a idon shi kika tattare kayakin ki beyi miki magana ba?” Mami ta tambaya.
“Wallahi a idonshi Mami” ta amsa tana share hawayenta.
“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un” ta sa salati.
“Har yanzu kuma be kira ki ba?” Papi ya tambaya.
“Be kirani ba.”
“Kuma nima be kirani ba ko ya kiraki Jameela?”
“Sam” ta amsa tana kad’a kai.
“Tabbas Afzal zeyi nadama, ashe har za a fad’a mishi magana akanki ya hau ya zauna akai ba tare da ya tsananta bincike ba? Ashe har zega ayan tambaya akan tarbiyyan dana baki a gidan nan Baby? Har ke yake tsammanin zaki ci masa amana sabida ‘yar aikinki ta ce hakan? Baze tsaya ya tambayeki yayi bincike ba?”
“Wallahi Afzal butulu ne” cewan Mami “Ko a mafarki aka ce mun zeyi haka wa Baby bazan yarda ba, wannan sigan walak’anci da mey yayi kama? Ai ko a bishiya ya 6alloki be kamata yayi miki haka ba ni fa ba abinda ya fi ci mun rai kaman da ya koraki daga d’akinsa. Wannan wani irin gori ne?” Ta tambaya cike da tsiwa.
STORY CONTINUES BELOW
“Ya isa haka Jameela ki kwantar da hankalinki uwata ta shi kije ki huta ai ba makaranta yau ko?”
“Akwai ina da test.”
“Kinyi karatu?”
“Eh jiya nayi yanzu ma zan d’an ta6a kafin lokaci yayi.”
“Toh uwata Allah bada sa’a kinji? Ina son ki kwantar da hankalinki ki cire Afzal daga zuciyarki. Nasani abinda yayi miki da zafi amma hak’uri ya zama dole mamana, dan shi baza ki bari ki cutar da kanki ba, in shaa Allahu shi yake tattare da asara ba ke ba gashi ai da kika cigaba da hak’uri kina kai kukanki wa Allah, Allah ya bayyano miki da komai kuma batun cewa za mu miyar dake gidansa k’arya ne, baki komawa har se idan ke kika ce hakan bazan mayar masa dake ba koda yazo yin bikon ki Baby zan nuna masa cewa ba wanda ya kai ya walak’anta mun ke muddin ina raye so ki kwantar da hankalinki kinji? Ki cigaba da karatu Allah yayi miki albarka.”
“Ameen Papi nagode.”
“Tashi Mamana” da haka ta mik’e ta fice zuwa d’akinta ta cigaba da karatu. “Amma Afzal be kyauta ba wallahi” cewan Mami bayan ficewan Amal.
“Dama na sani wataran se ya gorantawa Baby shiyasa ban goyi bayan ka sanar dashi asalinta ba tun farko.”
“A gaskiya nima Afzal ya bani kunya yadda ba bincike ba komai ya yanke hukunci.”
“Ai walak’anci ne ba komai ba wallahi kuma kasan meya fi 6atan rai? Yadda tana tattare kayakinta a gabansa amma ko k’ala be ce ba irin bata da gata bata da gun zuwa d’innan kokuwa duk inda taje zata sake dawowa da k’afarta.”
“Ya isa Jameela ki kwantar da hankalinki in shaa Allahu ba shi ba Baby.”
“Ahtoh dan wannan rashin mutunci ne a fili saboda bata da uba yake ganin ze iya walak’anta ta toh wallahi yayi k’arya Baby nada gatanta.”
“Ki sauk’ar da muryanki kar Baby ta jiki dan Allah magana ya riga ya k’are muddin ba Baby ce tace zata koma gidan sa ba toh ba shi ba ita cin fuskan ya isa haka.”
***Sha biyu nayi ta shiga shiri sallama tayi wa Mami sannan ta fice, tana gama test nata sukayi sallama da Maamah. Dama yawancin ana samun napep na jiddari (unguwansu) acikin makaranta se yau kuma Allah yayi babu dan haka ta taka har wajen gate ta shiga nema. Tazo tsallake titi kawai kaman daga sama wani mota mey d’ankaren gudu ya d’auketa ya wuce ko kewayowa beyi ba. Nan mutane suka duk’ufa sukayi kan Amal da tuni ta sume a wajen yayinda kanta yake bulbulan jini. Mota aka shiga nema wanda zeyi gaggawan kaita asibiti ana cikin haka sega wani babban motan daya fito daga cikin makarantar ya faka a dai-dai inda abun ya faru. Daga ciki babban mutum da ake ja yace da driver’n sa “Iliya sauk’a kaje ka taimaka musu mu kai yarinyar asibiti.” Nan da nan aka d’auki sumemmiyar jikin Amal aka sata cikin motan inda suka wuce TH.
****
K’ofan ta rufe ta fad’a bayi a guje sannan ta d’aga wayan. “Hello Aunty?”
“Safiyya mission complete yau burina ya cika, na fidda Amal daga gidan Ya Afzal maganan da nake miki yanzu har mutanen nawa sun bigeta in shaa Allah se cikin ya zube.”
“Aunty meyasa kika sa aka bigeta? Kin fidda ta daga gidan nan bey isheki ba har sai kinsa an bugeta? Seda na ce miki ya isa haka amma kika k’i ji wallahi abunda mukayi wa Aunty yayi yawa ni nayi nadaman fara aikin nan da ke.”
“Mey kike cewa Safiyya? Bayan burin mu ya cika kike wannan banzan maganar? Kin manta da mak’udan kud’ad’en da na miki alk’awari ne?”
STORY CONTINUES BELOW
“Ban fad’a miki bane amma Aunty ta riga ta gane mu, ta gane muna aiki tare, kap abinda muka aikata ta irga mun jiya kafin tabar gidan nan.”
“Sai mey? Ba ta riga ta bar gidan ba?”
“Aunty duk da haka da bakisa an bigeta ba wallahi Aunty bata cancanci abubuwan da mukayi mata ba.”
“Kiji ni Safiyya wallahi idan kika kuskura kika 6ata mun aiki na sena tabbata na lahira ya fiki jin dad’i hello Safiyya? Safiyya? Hello?” Tuni Safiyya ta katse wayan. Tun tafiyan Amal yau ta kasa samun sukuni, sosai kalamun Amal suka ta6a ta suka sa duk ta tsani kanta. Bud’e k’ofan da tace bari tayi taga Afzal tsaye bakin k’ofan bayin yana wani irin nishi wane zaki ga yadda idanunsa suka kad’a sukayi ja zir, wai shin har yaushe ya shigo bata ji sa ba? Innalillahi ashe batayi locking k’ofar ba duk dan sauri ta d’auki call d’in Nazeefah kafin ya tsinke. Kafin ta hankara kawai taji ya fincikota da hannunta seda ya fiddo ta daga bayin.
Tsulewa tayi ta shiga yin kakkarwa yayinda idanunta suka ciko dam da hawaye.
“Da wa kike waya?” Ya tambayeta cikin wani irin salon da ya mugun sanyata jin fitsari. Kai zalla take iya kad’awa “Nace da wa kike waya?!” Ya daka mata wani irin tsawan da tuni ya sa ta shiga sake fitsarin da take ji tsabaragen tsoro.
“Uncle dan Allah kay-“
“Shut up you fool! nace da wa kike waya?” hannu ya mik’a ya fisge wayan nata tare da shiga call logs last numban da tayi waya da shi yayi dialing bada dad’ewa ba Nazeefah ta d’aga “Hello Safiyya? Hello Safiyya?” Wani irin rawa jikin Afzal ya fara lokacin da yaji sautin muryan Nazeefah acikin wayan. Kashe wayan yayi daga sama kawai Safiyya taji sauk’an mari a fuskanta tass! wani irin rikicaccen ihu tasa yayinda ta soma ganin stars suna bin kanta. Be bari tayi overcoming zafin marin ba ya k’ara mata d’aya kumatunta duka ta rik’e tana kuka.
“Abinda ta turoki gidan nan kiyi kenan ko? Ki shiga tsakani na da Amal is that it?”
“Uncle dan Alla-“
“Shut it!” Ya daka mata tsawa “wa kuka tura a kad’e?” Kai zalla take kad’a masa yayinda ta gama tsurewa “Nace wa kuka tura a kad’e?” Nan ma shiru “You fool I’m talking you” fincikota yayi had’e da kai mata wani marin again a rikice tace, “Aunty wallahi Aunty a ka kad’e ni bani bace.”
“What?” Yayi exclaiming cike da k’in yarda. “Kun sa a bige Amal? Bakuda hankali ne?” Turata yayi har jikin bango sannan ya shak’ure mata wuya take idanun Safiyya suka kad’a yayinda ta shiga yin tari kad’an ya rage Afzal be kasheta ba sannan ya saketa nan ta sauk’a k’asa tana wani irin tari.
“A ina kuka sa aka bigeta?” Shiru tayi se kuka kawai take wani ball yayi da ita da k’afa “Nace a ina kuka sa aka bigeta?” Cikin tsananin kuka tace “Wallahi ban sani ba tunda Aunty tace zata sa a bigeta nace kar tayi amma tak’i jina” wani ball d’in ya sakeyi da ita “K’arya kikeyi nace k’arya kikeyi a ina kuka sa aka bigeta?”
“Uncle wallahi ba k’arya nakeyi ba tace de daga makaranta za a bi Aunty amma wallahi ban san a dai-dai ina bane dan Allah ka yarda dani.”
“Wallahi tallahi kin de ji rantsuwa ba kaffara ko? Muddin wani abun ya samu Amal ki sani da hannu na zan kasheki” yana kaiwa nan ya fice daga d’akin makulli yasa ta waje sannan ya k’arisa d’akinsa ya d’au key’n motansa ya fice be tsaya ko ina ba se gidan Nazeefah. Tana zaune akan dining tana cin abinci kawai taga shigowan Afzal kaman diran yesu.1
“Ya Rouhi?” Ta kira sunansa had’e da mik’ewa dan yi mai sannu da zuwa. Peck ta mishi placing a gefen kumatu “Ya Rouhi mey ka shigo yi? Ba se gobe zaka shigo ba?” Ko amsata ya kasa yi yayinda zuciyarsa ke raya masa kawai ya had’a kanta da jikin bango ya shak’ure mata wuya se idan ta daina numfashi tukun ya saketa danne zuciyan nasa yayi sannan daga gefe yayi dialing lambarta ta wayan Safiyya.
“Excuse me” tace da shi tare da nufan dining dan d’aukan kiran, ba k’aranin har6wa zuciyanta yayi ba ganin Safiyya ke kira shin wai meke damun yarinyar nan ne haka? Rejecting call d’in tayi take nan Afzal ya sake buga mata har rawa jikinta yake ta kuma rejecting juyawan da zatayi taga Afzal gab a bayanta.
“Muje ka watsa ruwa ko? Bari in sirka maka ruwan.” Kafin tace zata taka k’afa Afzal ya rik’o hannunta “Who’s calling?” ya tambayeta.
“Ermm.. ermm Airtel ne Wallahi kasan su da kiran mutum anyhow.” Wayan Safiyya ya d’aga ya sake dialing lambar nata nan ya shiga ruri kafin tace zata katse yasa hannu ya hanata “Ba Safiyya ke kira ba? Ki d’aga mana.” Kakkarwa ta shiga yi a wajen bata san lokacinda ta sake wayarta a k’asa ba da ta hango wayan Safiyya rik’e a hannunsa. B’ari bakinta yake yayinda cikinta ya d’ura ruwa.
“Ya Rou-” wani irin zafaffan mari me rikitarwa ya zabga mata, wani irin rikicaccen ihu tasa bata hankara ba ya sake kai mata wani abinku da farin fata take fuskan nata yayi ja yatsun Afzal biyar suka bayyana akai.
“Ya Afzal dan Allah kayi hak’uri” ta furta cikin wahala da tashin hankali har wani kurma-kurma ta fara jin kanta tsan-tsan zafin marin.
“I can’t believe your guts Nazeefah, how could you? For all these while ashe wasa kike mun da hankali? Wace irin munafuka ce ke? Ma tukun mey Amal ta tare miki? Tell me mey Amal ta tare miki da kika za6i ki k’untata mata kisa in tsaneta ki shiga tsakanin mu haka? Baki tsaya anan ba har seda kika sa aka kad’eta? Are you forreal? So kike ta mutu?”
“Ya Afza-” wani marin ya sake kai mata dan yadda ko muryanta baya son saurara. Ihu Nazeefah tasa seda Hindu dake bacci ta fito daga d’aki a kid’ime ganin Afzal ne da kansa ta ja k’ofanta ta sa key.
“Mey ta tare miki nace?!” Hannunta ya damk’o yana yi mata wani irin rik’o tuni k’asusuwanta suka shiga yin k’ara “Ya Afzal dan Allah kayi hak’uri kar ka karya mun hannu.”
“Answer me then mey Amal ta tare miki?”
“Zan fad’a maka zan fad’a maka amma dan Allah ka sakeni wayyo Allah na” sassauta rik’on nasa yayi. “Speak up! Idan kika bari na sake tambayanki wallahi na lahira seya fiki jin dad’i, mey Amal ta tare miki nace?”
Cikin tsananin kuka da azaba tace, “Mene Amal bata tare mun ba Ya Afzal? Komi ma Amal ta tare mun, tamkar katanga haka Amal ta shiga tsakani na da samun soyayyarka, yadda kake sonta ba haka kake sona ba, yadda kake jin zaka iya sadaukar da rayuwanka mata ba haka kake ji da ni ba, komi Amal komi Amal, ko shopping muka fita seka tambayi ina na Amal, wayanka duk hotunan Amal ne aciki, girki nasani Amal ta fini iyawa, tafi ni iya tarerayarka, ta fini iya nuna maka soyayya, ta fini kyau ta fini fasali, ta fini ilimin boko da na islamiya gabad’aya komi da nake tunani Amal ta fini da shi. Gashi da shigowanta gidan nan dududu bata fi wata uku ba amma har ta d’au cikinka ni shekarana uku da watanni na kasa yin hakan-“
   “Amal na da ciki?” Ya katseta cike da k’in yarda.1
  Kuka take sosai ta gyad’a mai kai “Amal na d’auke da cikinka Ya Afzal bazan iya ba, ta ko ina Amal ta fini taya kake tsammanin zan iya yin kishi da ita. Ya Afzal I love you dan Allah karka ga laifi na wallahi son da nake yi maka ne ya janyo komai, akanka zan iya sa ayi ma mutum kallon me ta6in hankali ko ciwon aljanu, akan ka zan iya yin duk wani irin mak’ircin da kake tsammani, akan ka zan iya sa mutum ya zargi matarsa akan ka zan iya sa a bige mutum dan a illatamun shi, I love you Ya Afzal, akan soyayyarka kuma zan iya yin komai-” zuciya ne ya d’ibesa ya sake gaura mata wani marin, na hud’u kenan k’asa ta sauk’a yayinda ta shiga raira kuka.1
   “Kinsan Amal nada ciki kika sa aka kwa6eta saboda ki kashe ta ki kashe abinda ke cikinta Nazeefah?” Har yanzu ya kasa amincewa da hakan. “So it’s all been you these while, duk kalan mak’iricin da kika shuk’a har kika fitar da Amal daga d’akinta be isheki ba no har sai kin sa a kwa6eta? Ashe haukan naki har ya kai stage d’in da zaki iya yin kisan kai? D’ana kikeson ki kashe? Kuma a haka kike cewa kina so na? You’re insane Nazeefah, ki sani na tsaneki, na tsani duk wani mey k’aunar ki, I hate you Nazeefah.”
   “Ya Afzal dan Allah kar kace haka, Ya Afzal bazan iya rayuwa ba kai ba, a shirye nake da in hallaka duk wanin da yake da shirin shiga tsakani na da kai Ya Af-” zuciya ne ya d’ibesa ya shiga yin ball da ita a wajen. Belt nasa ya zare ya shiga zaneta ta duk inda zanan ya sauk’a dama gashi vest ne kad’ai a jikinta da wandon rigan bacci iya guiwarta.
   D’an banzan duka Afzal yayi mata sekace ya samu ganga ko jaki, dukan da tunda baabarta ta haife ta ba a ta6a yi mata irinsa ba seda yaga ta fara yin amai a wajen sannan ya barta se huci yake.
   “Ki bud’e kunnuwan k’ashin nan naki ki saurareni da kyau Wallahi tallahi kin deji rantsuwa ba kaffara ko? Idan abun ya samu lafiyan Amal mey hanani kasheki a gidan nan se Allah Nazeefah, da hannu na zan kasheki nace a dai-dai ina kika sa aka bigeta?” Nazeefah ba bakin magana banda kuka ba abinda take iyayi ga yadda jikin nata ya tashi nan take, belt d’in ya sake zabga mata “Ba magana nakeyi maki ba?”
 
  “Ya Afzal dan Allah kayi hak’uri na tuba.”
 
  “Aww bazaki amsa ni ba?” Bata hankara ba ya sake zabga mata belt d’in Nazeefah se ihu take tana kuka tana neman agaji amma ba wanda ze iya taimaka mata, ba mai gadi Hindu kuwa uwar tsoro tuni ta rufe kanta a d’aki se hasbnullahu wa ni’imal wakeel take ta nanatawa. “Answer me! A ina kika sa aka kad’eta?”
  “Wallahi a dai-dai bakin makaranta ne dan Allah kayi hak’uri na tuba Ya Afzal.”
  “No Nazeefah you’re never sorry and I swear to you, na miki imani da Allahn da raina yake hannunsa you must pay for this, you must pay for everything you’ve put Amal go through I don’t care if it costs you your life, sekin biya abinda kikayi wa Amal” yana kaiwa nan ya wuce kitchen ya kulle k’ofan da key ya zare sannan ya wuce d’akinsu ya tattara spare keys na gidan ya sanya a aljihunsa ya dawo ya d’aga wayanta ya fice ya kulle k’ofar ta waje yadda bata isa ta kira kowa ba bale tayi tunanin guduwa. A 360 yabar gidan nata ya wuce chan bakin unimaid ya shiga tambayan mutanen dake kusa batun hatsarin da akayi d’azu ina aka kai yarinyar dayawa suka ce basu sani ba da k’yar ya samu wani mai shagon da yace yana da tabbacin TH suka wuce tunda shine asibitin dake kusa da nan d’in. Be 6ata lokaci ba ya wuce TH d’in inda ya zarce emergency ward ya shiga neman d’akin da Amal take ciki.
STORY CONTINUES BELOW
******
   “Se anje an siyo jini ba jini a blood bank and the patient is losing so much blood” cewan likitan dake aiki akan Amal ma wata nurse. “Kuje ku nemo jinin yanzu type O- (negative)” a guje ta fito inda suka ci karo da mutumin da ya kawo Amal da driver’nsa.
  “Ya nurse? Ya jikin patient d’in?” Yayi saurin tambayarta.
  “I’m sorry sir amma patient d’in ta rasa jini sosai wanda dole se anyi mata transfusion se gashi anje blood bank kuma babu type nata.”
  “Wace blood group ce?”
  “O-” ta sanar da shi.
  “O-?”
  “Yes Sir.”
  “Idan ban manta ba nima blood group O ne.”
   “Sir O+ daban O- shima daban O+ ze iya receiving daga O+ kaman shi da kuma O- amma O- dole se O- kaga kuwa yanzu idan kai O+ ne bazeyi ka bawa patient d’in jini ba.”
    “I’m sure O- nake nima.”
   “Sir you have to be certain.”
  “Amma kun tabbata inda zakuje neman akwai blood group natan?”
  “Gaskiya bamu da tabbacin hakan sir se munje mu duba tukuna.”
  “Toh ai duk 6ata lokaci ne wannan ina kuma ace anje chan d’in babu blood group natan? Ai mun koma baya.”
   “Hakane kuma Sir.”
  “And mey ze faru idan ba ayi mata transfusion d’in da wuri ba?”
  “Based on tests da muka gudanar sakamako ya nuna tana d’auke da juna biyu toh muddin ba ayi supplying nata da jinin akan lokaci ba eventually zata iya rasa ranta da kuma abinda ke cikin nata.”
  “Muje ku gwada jinin nawa in irin nata ne se ku d’iba, bags nawa kuke buk’ata?”
  “D’aya da rabi Sir.”
  “Let’s go muje ku d’ibi nawa kusa mata da wuri kafin lokaci ya k’ure.”
  “Sir are you sure?”
  “Let’s go we don’t have time” haka kawai wannan Alhj yaji wani irin strong connection tsakaninsa da Amal duk da cewan bey santa ba, amma jinta yake a kusa da zuciyarsa. Nan da nan akayi d’akin d’iban jini da shi amma da fari aka gwada blood type nasa inda yayi matching dana Amal, bayan nan aka kuma wani gwajin don tabbatar da cewa jinin nasa baya d’auke da wani cutan zamani. Anan aka zuge leda d’aya da rabi kamar yadda nurse d’in ta fad’a sannan akayi masa recommending magunan k’ara jini da zena sha dan ya maido masa da jinin nasa.
   Godiya sosai mutanen asibitin suka tayi masa. Nan da nan akayi infusing wa Amal aka bata taimakaon gaggawa da ikon Allah kuma aka samu aka ceto cikin nata ba tare da wani abin ya samesa ba.
   Har anan su Mami basu da labari saboda ko waya Amal bata fito dashi ba bale a lalumo layin wayansu aciki, saboda acewarta test kawai zatayi ta dawo gida se bata damu ta fito da wayan ba.
   Har anan wannan Alhaji da ya ba wa Amal jinin jikinsa be tafi ba ya na nan yana jiran farfad’owanta. Tana farfad’owa nurses sukayi masa magana nan ya k’arisa cikin d’akin inda ya tarar da ita kwance akan gado da bandeji nad’e a kanta da k’afarta, da kuma wani a hannunta wanda aka nad’e mata shi tun daga wuya dan support da alama shima hannun ta samu matsala ne. Sosai ya tausaya mata barin ma da yaji tana da ciki.
  “Ga wannan shine mutumin da ya baki jinin jikinsa har leda d’aya da rabin da aka sa miki kyauta se kiyi masa godiya” nurse d’in tace da Amal. A hankali Amal ta shiga juyo da kanta har ta kai akan wannan mutumi. Mutuwan tsaye mutumin yayi lokacinda k’wayoyin idanunsu suka had’e. Ita kanta Amal seda taji wani iri a jikinta, tabbas bata mance fuska amma seji take a jikinta kaman ta ta6a had’uwa da wannan mutumi amma kuma ta rasa a ina. Shi ma on the other side kallon Amal yake na sosai ba tare da ya koda kyafta ido ba, ji yayi kaman sun ta6a had’uwa a wani gun amma duk yadda yayi ya kasa tuna a ina, da ya cigaba da kallon cikin idonta kuwa se gani yake kaman kansa yake kalla aciki there’s something about her eyes that reminds him so much of himself, he sees himself in her. Wani irin mumunan tsinkewa gabansa yayi yayinda rayuwansa na da ya fara taho masa.
STORY CONTINUES BELOW
  “Nagode sosai Allah sak’a da alkhairi Baba” tace da shi kai yayi saurin kad’awa had’e da sakar da murmushin dole “Ba komai ‘yata sannu Allah sawwak’e.”
  “Ameen” ta amsa da murya chan ciki-ciki.
  
   “Ya sunanki?”
  “Amal Abdallah” ta sanar da shi haka kawai yaji gabansa na fad’i jin sunan mahaifinta.
  “Mahaifiyar ki fah?”
  “Jameelah Muhammad” ido ya rufe na k’ank’anin lokaci yana k’ok’arin composing kansa. Baze ta6a mancewa da wannan suna ba, ko a ina yaji sunan nan yasan sunan Jameensa ce amma kuma ai ba ita kad’ai bace Jameelah Muhammad a duniya ba, ze iya yuwuwa wata Jameelah Muhammad d’in ce. Amma idan kuma itan ce fah? Can it be? Noo da sauri ya kad’a kansa yana d’auke wannan mumunan tunani it can’t be possible it can never be.
  Murmushi ya sakar wa Amal “Ko zaki bada lamban mahaifinki a kirasa?” Da biyu ya tambayeta hakan don jin mey zata ce idan har tace ‘eh’ ta basa that means ba shida alak’a da ita idan kuwa har tace ba na mahafinta se na mahaifiyarta that means zarginsa akanta ya tabbata kawai se yaji tace “Eh.”
  Wani irin ajiyan zuciya ya sauk’e had’e da yima Allah godiya tunda har tana da mahaifi toh ba abinda yake zargi bane barka. Nan da nan ya zaro wayansa daga aljihu Amal ta irga masa lamban Papi wanda ya kira take bayan sun gaisa ya sanar dashi abinda ke tafe da shi inda Papi yace yanzu haka ma suna hanyan zuwa asibitin ne mijinta ya riga ya kira ya sanar da su.
   “Iyayenki suna hanyan tahowa sunce mijinki har ya kira ya sanar da su” yace da Amal. A lokaci guda zuciyan Amal ya buga to the mention of Afzal’s name. Idan su Mami sunayi wa Allah kar su k’ariso nan da shi, bata k’aunan sake sanya sa a idanunta har k’arshen rayuwarta, baza ta ta6a mancewa da abinda yayi mata a rayuwa ba “Toh Amal barin je inyi settling bills naki in amso miki magunanki ko?”
  “Baba da ka bari ai kayi mey wuyan wannan ko iyaye na zasuyi handling dan Allah kar ka damu.”
  “Ba komai ‘yata kede Allah baki lafiya”
  “Ameen nagode Allah sak’a da mafificin alkhairi.” da haka ya samu ya fice inda ya tura driver’nsa ya biya komai aka amso magunan sannan aka mik’awa nurse ta kaiwa Amal.
  “Nurse?” Amal ta kirata.
  “Na’am kina buk’atan wani abu ne?”
  “How about my baby? Cikin na nan ko ya zube?”
  “Cikin ki na nan baiwar Allah, an samu an tsayar da bleeding d’in tun kamin ya isa cikin mahaifarki ya 6ata cikin.” Wani hamdala Amal ta sake “Thank you, k’afa na da hannu fa? Targad’e ne ko kariya?”
  “Targad’e ne duka biyu” Tasan zato zunubi ne amma tana da tabbacin Nazeefah is behind everything, na sosai ta duba kwalta kafin ta tsallake har yashe ne bata ga wannan mota mey uban gudu ba idan ba wai dama fakonta motan yake ba. Tana sake zargin Nazeefah ce behind this saboda duk yadda akayi taji batun tana da ciki ne daga bakin Safiyya shine take son rabata da abinda ke cikinta, k’arshe kuma idan har ba a bakin Nazeefah ko Safiyya ba ba yadda za’ayi Afzal yasan tayi hatsari.
  “Don’t mention” nurse d’in tace da ita tana me tsamota daga duniyan tunanin data wula “iyayenki sun sake yin waya anyi musu kwatancan d’akinki yanzun zasu shigo” kai zallah Amal ta gyad’a mata sannan ta maida kallonta ga jinin da ke kan shigewa jikinta ta canula. Mamakin halin alkhairi irin na mutumin nan kawai take, yadda be santa ba, be san wani nata ba, be san daga ina ta fito ba amma har ya d’ibi jinin jikinsa leda d’aya da abu ya bata gaskiya ne na Allah basu ta6a k’arewa toh Allah ya sak’a masa da mafificin alkhairi.
****
  Dab su Papi sun zo shiga k’ofan ward nasu Amal suka tarar da Afzal tsaye bakin k’ofan da tashin hankali bayyane karara a fuskansa yana ganinsu ya nufe su “Papi-“
STORY CONTINUES BELOW
  “Dakata Afzal” Papi ya tsayar da shi ta hanyan d’aga hannunsa “Bana buk’atan jin komai daga bakinka, ka kira mu ka sanar damu abinda ya samu Baby mungode Allah saka da alkhairi kana iya tafiya dan babu wata alak’a kuma tsakaninka da Amal yanzu.”
  “Papi dan Allah kar kayi mun haka dan Allah kar ka rabani da Amal I beg of you please.”
  “Miss” Papi ya kira wata nurse. “Dan Allah ku janye bawan Allah nan daga nan.”
  “Bawan Allah ba tun d’azu aka sallameka ba? Baka da appointment da kowa anan bazeyi ka shiga ba nan restricted area ne dan Allah kayi hak’uri ka tafi, yes Sir how can I help you?” Ta kewayo tana tambayan Papi bayan da ta gama da Afzal.
   Nan Papi yayi mata bayanin komai lamban wayansa ta amsa ta zuba cikin computer’n dake gabanta yana gama scanning ya nuna wayan da sukayi last da phone desk. “Bismillah kuzo in shiga daku.”
  “Mami? Mami please don’t don’t do this please” Afzal yace da Mami lokacin da tazo shigewa ciki “Please karku hana ni ganin Amal” ko kallonsa Mami batayi ba bale tasan yanayi ciki akayi dasu akayi directing nasu zuwa d’akin da Amal take yayinda aka bar Afzal tsaye a waje.
   Kuka wane d’an yaro Afzal ya shiga yi a wajen, yau ina ze sa kansa idan su Papi suka raba sa da Amal? Ya suke son ya rayu idan ba Amal a ganga da shi? Taya suke son ya fara neman tuba idan ko kallonta bazasu barsa yayi ba? Yau ina ze jefa kansa? Tabbas ya tafka babban sokanci na k’in saurara mata da yayi lokacin da take son yi masa bayani, tabbas ya tafka babban laifi na amincewa da maganan Safiyya akan na Amal da ta kasance matarsa, ta ina ze fara bata hak’uri? Ta ina ze fara nuna mata how deeply sorry he is and how badly he’s regretted everything he’s done to her? Tabbas ya tafka babban kuskure a rayuwansa na amincewa da duk maganan da aka fad’a masa ba tare da ya gudanar bincike akai ba. Tabbas duk mey irin hali irin nasa yana tattare asara, masifa da kuma nadama.
  ***
    Tunda Alhajin yaji isowan iyayen Amal ya 6oye kawai se basa jikin sa yake Jameensa ze gani. Ba k’aramin tsinkewa zuciyansa yayi ba lokacin da yaga ana shiga da Mami da Papi cikin d’akin Amal.
  “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un” kawai yake ta furtawa yayinda jikinsa yayi la’asar. Shekaru ashirin da biyu da suka wuce kawai yake tunawa, yau ina zai sa kansa idan gaskiya ta fito? Shikenan mutunci da girman da ‘yan unguwa suke basa ze rushe, shikenan reputation na family’nsa ze rushe. Shin da wani idon ze sake kallon Hajiya Surayya? (Mummy’n su Nazeefah) meke shirin faruwa da shi? Shin yanzu Amal ‘yarsa ce? Shin ciki ya shiga jikin Jamee bayan abinda ya faru a tsakaninsu? Wannan ne dalilin da yasa suka baro garin Askira? Duk da cewan blood group nasu da yazo d’aya ma babbar shaida ce akan cewa Amal ‘yarsa hakan baisa ya amince ba. He needs to carry out a DNA test. Test d’in da ze tabbatar masa da cewan Amal jininsa ce ko kuwa a’a.
   “Alhj yanzu PA’nka ya kirani batun meeting da kake da shi da deputy governor” Driver’nsa ya sanar da shi.
  “Ohh haka zamu tafi ko?” Ya amsa yana k’ok’arin composing kansa. 
  “Eh Alhj” daga haka suka kama hanya suka fice har anan Afzal na zaune bakin k’ofan akan wani benchi inda ya had’a kai da guiwa. Seda Alhj’n nan ya wuce Afzal ya d’ago kansa bisa ji da yayi an bud’e k’ofar a cewansa ma Papi ne yazo shiga da shi sede yaga ficewan mutum, zama ya cigaba da yi a wajen yak’i tafiya
****
   “Sannu Baby” cewan Mami. 
  “Ya kikeji? Ya jikin naki?” Papi ya tambayeta.
  Kai ta gyad’a musu a hankali “Da sauk’i” ta amsa.
  “Ya Nurse meya sameta?”
  Ta samu internal bleeding sannan tayi losing blood sosai bisa ga fashewan da kanta yayi bayan nan kuma ta samu targad’e a k’afarta da hannu amma ba abinda ya samu lafiyan abinda ke cikinta.” Da mamaki both Papi da Mami suka juyo suna kallon Amal da alaman tambaya bayyane karara a fuskokinsu.
STORY CONTINUES BELOW
  “Ciki?” Mami ta tambayeta “Baby kina da ciki?” Shiru tayi bata amsa ta ba.
  “Meyasa baki sanar damu ba Baby?” Papi ya tambaya nan ma shiru tayi “Kiyi magana kinji Mama na? Kar kiji komi.”
  “Papi, Mami kuyi hak’uri kar ku d’au na 6oye maku wannan al’amari saboda wani dalili ne k’wak’k’wara nayi hakan ne sabida gudun da nake kar kuce zaku miyar dani gidan Yaya saboda wannan lallura.”
  “Sam baza muyi miki haka ba Baby shin baki yarda dani bane dana ce miki se idan ke kika ce kina so zaki koma gidan Afzal zaki koma? Ki sani nida mahaifiyarki bazamu tilasta ki akan abinda bakiya so ba, sanin kanmu ne nan duka Afzal be kyauta miki ba so ki kwantar da hankalinki kinji? Allah ya inganta kuma.”
  “Ameen Papi thank you.”
  “Wata nawa ne?”
  “Sati uku ne kacal Mami” ta sanar da ita.
  “Allah inganta Mamana sannu Allah sawwak’e.”
 
  “Shin har ya aka bigeki Baby? Baki kalli hanya bane kafin ki tsallake kwaltan?” Mami ta tambayeta.
  “Mami na kalla kinsan shi tsautsayi baya wuce ranan sa” haka kawai taji ta rufa wa Nazeefah asiri saboda tasan halin Papi muddin yaji Nazeefah na da hannu acikin wannan al’amari abu baze zo yayi kyau ba saboda ba Afzal kad’ai ba har su Ummi da Abba da ze shafa ita kuma abu da tashin hankali ne bata so. Tun da de Allah ya raba ta da su yanzu sede tace Allah miyar masu da anniyarsu.
   “Ermm Nurse” Papi yayi ma nurse d’in magana.
  “Yes sir?”
  “Nace shin meyasa baku kai ta regular ward ba? Gani nayi nan VIP ne.”
  “Tabbas nan VIP ward ne.”
  “Toh ai kud’in zeyi yawa kuma kin dega ba k’arfi muke da shi ba.”
  “Kar ka damu da wannan sabida bawan Allahn da ya kawo ‘yarka asibitin nan ya riga ya biya kud’in d’akinta har na sati sannan ya saye mata magunan da duk likita ya rubuta.”
  “Subhanallah! Wannan wani mutumi ne haka?”
  “Bayan nan jinin nan da kake gani ma na jikinsa aka janye aka sawa ‘yarku leda har d’aya da rabi.”
  “Blood type nasu yaso d’aya?”
   “Tabbas duk O- suke.”
   “Alhamdulillah Alhamdulillah amma dan Allah waye mutumin nan? Nasan godiya kad’ai baze biya abinda yayi mana ba amma dole ne inyi masa godiya.”
  “Shigowanku ya tafi kuma bey ajiye mana wani identification card nasa ba yana biya ya tafi.”
  “Allah sarki Allah sak’a masa da alkhairi ya biya sa da gidan Al-jannah.”
   “Ameen” duka suka amsa “Tabbas na Allah basu k’arewa” fad’in Mami. “Amma Baby kinga mutumin ke?”
  “Eh Mami har nan ya shigo nima na basa lamban Papi.”
  “Allah sarki baki san sa ba?
  “Gaskiya ban san sa ba amma se gani nake kaman mun ta6a had’uwa da shi.”
STORY CONTINUES BELOW
  “Allah sarki Allah ya biya sa, zaki ji yunwa ai yanzu ko Baby?” Ta tamabayeta.
  “A’a Mami.”
  “Kaman ya a’a Baby? Kin manta zaki sha magani ne bayan nan kuma kinsan dole seda cin abinci yanzu in ba haka ba abun cikinki baze samu lafiya da k’wari ba ko dan shi seki hak’ura kina cin abinci.”
  “Bari inje da kaina cikin restaurant anan in sai miki abincin” fad’in Papi.
  “Toh Papi nagode.”
  “Allah ya baki lafiya shine babba uwata.” A bakin k’ofan ward d’in ya sake had’uwa da Afzal da har yanzu yak’i tafiya. Wucesa Papi yayi niyyan yi amma Afzal ya dakatar da shi ta hanyan shan gabansa cikin hawaye yace, “Papi dan Allah kayi hak’uri nasan nayi kuskure, nasan ban kyauta maku ba, na sani na ci amanar rik’on amanar da na d’au alk’awarin zanyi amma wallahi sharrin shaid’an ne Papi kafi kowa sanin yadda nake son Amal dan Allah kar ku rabani da ita I beg your pardon.”
  “Kana son Amal? Meyasa bakayi tunanin hakan ba kafin ka ci mata mutunci ka walak’anta ta haka? Ka sani Afzal Amal tafi k’arfin a walak’anta ta, Amal tafi k’arfin kace zakaci mata mutunci” ransa ne ya mugun 6aci ya shiga d’aga murya se tunawa yayi a asibiti suke “Kaga a asibiti muke bazan so in d’aga murya in shiga hak’k’in wasu ba so tun wuri kafin ka 6ata mun rai ka fice anan.”
   “Papi dan Allah kayi hak’uri, Papi I’m not asking for too much nasani abunda nayi muku will take much time to heal all I’m asking is ku barni inga Amal, dan Allah kar ku hanani ganinta please Papi.”
   “Baza ka ganta ba Afzal, ganin Amal ne nace baza kayi ba maza ka kama hanya kabar nan tun kafin insa a koreka.”
  “Bazan gaji da baka hak’uri ba Papi kuma koda kasheni za’ayi bazan fasa zuwa duban Amal ina baku hak’uri ba har se idan Allah ya huci zuciyanku” Papi be sake cewa da shi komai ba ya fice haka nan har Papi yaje ya siyo abincin wa Amal ya dawo Afzal be tafi ba. Se chan wajajen k’arfu hud’u da rabi ya mik’e yaje yayi alwala yayi sallah ganin ba mahalicci se Allah kuma ko min yaya ba barinsa su Papi zasuyi yaga Amal ba kawai ya d’ibi kansa ya fice. Police station ya wuce inda ya tattaro ‘yan sanda sannan yayi gida dasu inda aka d’au Safiyya aka sata a mota se kuka take tana had’a Afzal da Allah amma ina idan shima ze sha wuya toh se ya tabbata ita da uwar d’akinta sun d’ana wuyan da ze sha. Daga gidan Amal suka wuce na Nazeefah inda ya tarar da ita zaune akan carpet na parlour ta had’a taguni tana ganinsa ta mik’e tsaye yayinda jikinta ya hau 6ari. Kallonta yayi sau d’aya ya kawar da kansa dan yadda yayi mata jina-jina da jiki ko ina a jikinta ya kumbura yayi pink dan azaba ga shatin belt kaca-kaca.
    Takawa yayi yaje ya sameta cikin rud’ani tace, “Dan Allah Ya Afzal kayi hak’uri na tuba dan Allah kar ka sake ta6ani.”
  “I’m so sorry Nazeefah, I’m terribly sorry” ya bata hak’uri cike da d’aurewan kai tace, “Ya Afzal ni ya kamata in baka hak’uri please forgive me.”
  “A rayuwa ba abinda na tsana kaman inga na miji yana dukan mance, musamman ma inga magidanci yana dukan matarsa, tun da nake ban ta6a sha’awan d’aga hannu in mari ‘ya mace ba bale har in d’au abun zana in zaneta hasali duk mijin da naga yana dukan matarsa tsanansa nake sega yau kinsa na aikata abunda nafi tsana a rayuwata Nazeefah. It pains me alot ace yau na d’aga hannu na mari matata ban tsaya anan kad’ai ba har seda na zaneta ta tayar maga da jiki haka” yayi maganan had’e da d’aga hannunta yana shafa kan shatin belt d’in a hankali cike da tausayi “Kinsa na tsani kaina yau Nazee I so much hate myself for hurting you like I did amma kuma babban abinda kikayi yau shine na sanya ni tsanarki. I hate you right now Nazeefah, I hate the fact that I’m married to you, looking at you disgusts me right now. Na so ki Nazeefah, na so ki har cikin zuciyata son da bana tsammanin wani d’a na miji ze iya yi maki irinsa, akwai gur6in da ke kad’ai kika mamaye shi acikin zuciyata, gur6in da ko Amal bata isa tace zata mamaye sa ba amma se mey? Se keda kanki kika 6ata rawarki da tsalle kika sa na tsaneki tsanan da bana jin zan iya sassauta shi. Zaman ki a gidan nan ya k’are Nazeefah yadda kika rabani da Amal kema dole ne in rabu dake idan har zanyi ma Amal adalci, yadda kika fiddata daga gidan nan be kamata ace ke kin cigaba da zama ba.”
STORY CONTINUES BELOW
   “Ya Afzal dan Allah kar kace haka I beg of you dan Allah kar ka sakeni idan ka rabu dani ban san ina zansa kaina ba bazan iya rayuwa ba kai ba, Ya Afzal I love you, I love you so very much” ta sanar da shi cikin kuka.
  “Nima bazan iya rayuwa bake ba Nazeefah, batin duk abinda kikayi mun, batin yadda nakejin na tsaneki yanzu know that I still love you, kin riga kin zame ga6a a jikina Nazeefah amma bazan iya cigaba da zama dake a cikin gidan nan ba looking at you everyday remembering what you did to my innocent Amal, I can’t Nazeefah.”
  “Ya Afzal dan Allah kayi hak’uri I’m terribly sorry wallahi na tuba dan Allah ka yafe mun.”
  
   “No Nazeefah, you’re never sorry, you’re never sorry na sani tuban muzuru kikayi ba dan wai kinyi nadaman abinda kika aikata ba, hungo” yayi maganan had’e da janyo hijabinta dake kan couch “Amsa kisa” ba gardama ta amsa tasa “Na taho da ‘yan sanda sunzo su d’aukeki.”
  ‘”Yan sanda?!” Ta nanata yayin da gabanta yayi wani irin mumunan tsinkewa ‘”Yan sanda fa kace Ya Afzal? Dan Allah ka rufa mun asiri Ya Afzal dan Allah kar kayi mun haka” jikinsa ta fad’a had’e da zagaye hannayenta a bayansa tana kukan tsuma zuciya “Ya Afzal dan Allah kar ka bari su tafi dani bazan iya kwanan cell ba Ya Afzal I beg of you please don’t do this idan tuban Amal kakeso in nema na amince zanyi hakan amma dan Allah kar ka bari ‘yan sanda su tafi dani” shi kansa seda idanunsa suka cika da hawaye dan yadda ta rik’esa gam take kuka take kuma had’asa da Allah. Na sosai ta basa tausayi shima har cikin ransa beso hakan ba amma hakan ne kad’ai hanyan da ze iya sak’awa wa Amal abubuwan da Nazeefah sukayi mata. Hannu ya sa na k’arfi da yaji ya raba ta daga jikinsa “Securities!” Ya kira su Nazeefah bata tashi rikicewa ba seda taga matan polisawa suna dosan inda take wani irin rikicaccen ihu tasa had’e da fashwwa cikin wani irin kuka mey tsuma zuciya “Ya Afzal dan Allah kar ka bari su tafi dani Ya Afzal I’m deeply sorry please don’t let them take me wayyo Allah Mummy na dan Allah kizo ki taimakeni Ya Afzal please don’t let them take me wayyo Allah na.”
   “Take her away” yace da polisawan hawaye na tsiyaya daga idanunsa hannu yasa ya share da wuri. Ihu da bori Nazeefah ta cigaba da yi bata kuma fasa kiran sunansa ba tana da had’a sa da Allah sede he’s mind is already made up, ko juyawa ya kalleta beyi ba se hawaye yake ta zubarwa shima kaman ba na miji ba haka yana ji yana gani aka janyeta waje aka sata mota d’aya da Safiyya sukayi police station.
   Ga shi nan yau ba Nazeefah ba Amal daga kansa se kansa sauk’a yayi a wajen ya zauna kan kujera sannan ya shiga yin kuka tsakaninsa da Allah, kukan da ya rasa akan wa yake yi, akan Nazeefah ne ko akan Amal ne. Daga k’arshe ya gane kuka akan dukansu biyu yake. Kuka yake akan zafin rabuwa da Amal da kuma abinda yayi wa Nazeefah a matsayinta na matarsa. Be ta6a tsammanin Allah ze k’addaro masa da ranan da zeyi wa matarsa jina-jina kaman yadda yayi ma Nazeefah ba har yanzu zafin hakan yakeji, sannan kuma har ya sake turata kwana a cell tabbas yau rana ne da baze ta6a mancewa da shi ba a rayuwansa.
     Yunwa yake ji amma baya jin ze iya sanya komi a bakinsa tuna Amal nasa na kwance a asibiti rai a hannun Allah, ruwan zafi kad’ai ya iya sha ya watsa ruwa sannan ya kwanta. Da ya rufe idonsa se ya tuna da abinda mey shagon d’azu ya fad’a masa akan cewa kan Amal ne ya fashe acikin jini aka d’auketa aka sanyata cikin motan da ya yi agaji. Wayansa ya d’auko ya lalimo lamban Amal sannan ya shiga kiranta.
  ***
    Tana rigingine jikin gadonta Mami na bata abinci wayanta ya shiga ruri a hankali take juya kanta ta kai kan wayan gani tayi Habib Albi🌹💍🔐 na flashing akan screen d’in da hotonsa wanda tayi saving contact d’in da shi. Silencing wayan tayi ta bar shi ya cigaba da ruri, be dad’e ba Afzal ya shiga kira again kafin tayi silencing Mami ta tambayeta “Wa ke kira? Afzal ne?”” Kai zalla ta gyad’a.
  “Amma baida kunya shin mey ze kira ya fad’a miki?” Wayan na tsinkewa Afzal ya shiga kira again kashe wayan Amal tayi gabad’aya yanzu. “Kin san kuwa d’azu yana nan? Tun kafin mu shigo yake nan amma nurses suka hanasa shiga saboda restricted area ne nan d’in, haka har seda Papinki yaje d’ibo mana kayakin mu sannan ya tafi.”
STORY CONTINUES BELOW
   “Mami dan Allah kibar yi mun maganansa I’m not interested.”1
  “Shikenan Baby yi hak’uri yi sauri ki cinye mu kwanta ki huta.” Wajajen goma da rabi ta d’au wayanta ta kunna da sak’on Afzal ta fara cin karo ko bud’ewa batayi ba ta goge baza ta ta6a mancewa da kalan walak’ancin da yayi mata ba, in shaa Allahu ba abinda ze sake had’ata da shi idan ta samu sauk’i zatayi ma Papi magana a amso mata takardanta dan muddin Nazeefah na cikin gidan chan bazata ta6a komawa ba.
  *****
   GIDAN ALHJ ABDALLAH.
  “Khaleefah d’auko mun glasses d’ina a d’aki” fad’in Daddy lokacinda suke zaune duka a kan dining suna shirin karyawa. Mik’ewa yayi ya wuce d’akinsa ya d’auko masa sannan ya dawo yana zama wayan Mummy dake kan dispenser.
   “My phone Khaleefah” ta sanar da shi kaman wanda zeyi kuka ya mik’e a rayuwa ba abinda ya tsana kaman aike. “Wa ke kira?” Ta tambaya.
  “Number ne” ya amsa yana mik’a mata, swiping tayi ta d’aga “Halo Mummy?”
  “Nazeefah?”1
  “Na’am Mummy.”
  “Ina kika ajiye wayanki? Tun jiya ina trying numban ki switched off.”
  “Mummy dan Allah ki taimaka mun.”
  “Meya faru?”
  “Mummy a cell na kwana.”
  “A cell! Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!” chak Daddy dake karanta newspaper ya tsaya haka Khaleefah ma dake shan tea.
   “A cell? Meya faru? Ina Afzal?”
  “Mummy shi ya kawo ni.”
  “Innalillahi mey ke faruwa me kikayi?”
  “Mummy dan Allah kizo police station na Damboa road muke.”
  “Toh gamu zuwa” tana sauk’e wayan Daddy yayi saurin tambayarta “Ya meke faruwa?”
  “Nazeefah ce wai Afzal ya kaita police station a chan ma ta kwana.”
  “Police station?” Daddy Yayi exclaiming “Dalili?”
  “Nima bata fad’a mun ba kawai cewa tayi muje mu sameta achan Damboa road take.” Breakfast da basuyi ba kenan duk suka mik’e suka duk’ufa cikin mota se police station.
   Suna isa akayi dasu 6angaren da su Nazeefah suke kuka tasa lokacin da ta gansu haka Mummy ma. “Nazeefah meya faru? Meyasa Afzal ya kawo ki nan? Mey kikayi masa.”
  “Mummy dan Allah kuyi hak’uri Mummy I’m so sorry.”
  “Meya faru Nazeefah?” Daddy ya tambaya.
   “Ya Nazeefah?” Khaleefah da har yanzu ya kasa amincewa da abinda idanunsa ke gane masa kirata.
  “Daddy laifi nayi masa, laifin da ni kaina ina jin kunyan sanar daku please help me out Daddy dan Allah kar ka barni in sake kwana acikin nan.” Waya Daddy ya zaro ya kira Afzal bada dad’ewa ba ya d’aga.
   “Ka taho inda ka kawo Nazeefah yanzun ina jiranka.”  Bacci yakeyi lokacin da Daddy ya kirasa yana sauk’e wayan ya koma baccinsa seda ya k’ara baccin kusan minti talatin sannan ya mik’e ya d’aga wayan nasa sak’o ya tura wa Amal ya miyar da wayan ya zarce bayi yayi wanka ya fito ya karya da corn flakes ya koma d’aki ya shirya tsaf sannan ya fito. Isansa police station d’in ya tarar da su Abba da Ummi har su Daddy sun kira su. Saidai ko alamun tashin hankali babu tattare da Afzal dalili kuwa yasan shine da gaskiya. Binsu yayi duka da gaisuwa sannan yasa aka fito da Nazeefah daga cikin cell d’in jikin Mummy ta fad’a tana kuka sosai yayinda Safiyya ta la6e a lungu tana kuka itama. Breakfast da ya siyo musu ya mik’a aka basu nan da nan suka karya a wajen sannan Abba ya tambayeshi meya faru.
   “Baki fad’a musu abinda kikayi bane?” Ya tambayi Nazeefah da jikinta keta k’yarma har yanzu. “Magana nake miki Nazeefah confess your crime, crimes if possible” sede ta kasa magana gyaran murya yayi “Tunda bazaki fad’a ba ni zanyi hakan. Mutane tayi hiring tasa aka kad’e Amal yanzu haka Amal na kwance a gadon asibiti rai a hanun Allah duk wai a sunan kishi.”
  “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” salati kawai kukeji yake tashi a wajen. “Nazeefah?” Mummy ta kewayo tana kallonta “Da hankalinki? Yaushe kika fara kisan kai?”
  “Mummy dan Allah kiyi hak’uri wallahi sharrin shaid’an ne.”
  “Sharrin shaid’an? Sharrin shaid’an?” Mari me kyau Mummy ta zabga mata cike da 6acin rai, wannan wani irin haihuwa ne? Taya zaka haifi d’a amma d’a ya gagareka? Ashe duk kalan nasihar da takeyi wa Nazeefah a wajen take ajiye mata abinta? take Ummi ta shiga tsakaninsu tana bata hak’uri.
   “Tarbiyyan da na baki kenan? Da abinda zaki sak’a mun kenan nida Daddy’ki? Wannan wace irin rayuwa ce?” Tuni ta shiga yin kuka yayinda Ummi ta cigaba da bata hak’uri.
   “Afzal kayi hak’uri” cewan Daddy “Dan Allah kayi hak’uri.”
  “Hak’uri nayi Daddy amma Nazeefah must pay for what she did” har a nan Abba bece komi ba yana bayan d’ansa d’ari-bisa-d’ari saboda akan gaskiyansa yake.
  Wayan Nazeefah Afzal ya zaro daga aljihunsa ya kunna “Gashi da hannunki zaki kira mutanen da kika sa suka bige Amal kice musu suzo su sameki dai-dai bakin junction d’innan justice must be served for Amal.” Amsa Khaleefah yayi ya mik’a mata nan ta lalumo lamban d’aya daga cikinsu tayi kaman yadda Afzal ya umarceta se kakkarwa take. Har anan mamakin ta Mummy take, sam ba irin tarbiyyan data bata ba kenan, kunya take ace ita ta tsuguna ta haifi gagararriyar ‘ya kaman Nazeefah idan a d’an shekarunta zata iya sa a bige mutum gaba mey zatayi kenan?
   Yaran suna isowa bakin junction d’in sukayi mata waya nan Afzal ya d’au ‘yan sanda uku a motansa suka fice tare da ita Nazeefar a gaban mota suna isa wajen ya umarceta da ta sauk’a tayi musu magana achan aka kamasu aka k’ariso dasu cikin police station d’in. Mummy se kuka take Ummi da Khaleefah suna bata hak’uri.
   “Officers ku hukunta mun su hukuncin dake dai-dai da attempt nayin kisan kai” Afzal yace da polisawan yana nuni da yaran da Nazeefah tayi hiring samari guda biyu. “Wad’an nan biyu kuma” yayi nuni da Nazeefah da Safiyya “Ka miyar dasu cikin cell ka kulle mun su I’ll speak with my lawyer in shaa Allah justice must he served for Amal nan gaba ko akan mey bazasu sake yin ganganci ta6a lafiyar wani ba bama Amal kad’ai ba.”
   Yana kaiwa nan ya juya ya fice kiransa Daddy yake amma ko ya juya bale ya sauraresa motansa ya shiga ya basa wuta.
   Kaf wajen ba wanda kansa ya mugun d’aure yake kuma cikin tsananin tashin hankali kaman Daddy da yaji Afzal ya ambaci sunan Amal a matsayin wanda Nazeefah tasa aka kad’e. Shin wata Amal ce wannan? Amal da ya tsince ta a bakin makaranta jiya ya kai asibiti ne? Shin Amal Abdallah ce kishiyar Nazeefah Abdallah ‘yarsa? yau wani irin k’addara ne wannan? Wani irin fallasa ne yake shirin afkuwa masa? Wani irin badak’ala ne wannan? Ta inda Allah ze kamasa alhak’in Jamee da ya d’auka kenan? Fatansa d’aya ne Allah yasa Amal Abdallah ta asibiti ba ‘yarsa bace idan kuwa har hakan ya tabbata ‘yarsa ce nasa ya k’are that mean ‘ya’yansa biyu suna auran miji d’aya kenan. Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un.”Ina securities?” Daddy ya tambaya “Nawa ne kud’in bailing nata?”+
“Ranka shi dad’e ai baze yiwu kayi bailing nata ba saboda ‘yarka is accused of an imprisonable offense wanda hukuma take tsoron saketa gudun kar ta sake tafka wannan laifi dan haka kotu ya nemi a ajiyeta under close supervision idan har ba wai wanda yayi filing case akantan bane ya buk’aci a saketa that is idan yaja baya da case d’in” d’aya daga cikin securities d’in yayi masa bayani.
“Alhj Amin dan Allah kayi wa Afzal magana yayi hak’uri duk nan mun san Nazeefah bata kyauta ba amma yayi hak’uri yaja baya da filing case d’innan hannun mutum baya ri6ewa ya yasar komin munin halin Nazeefah bazan so ta k’are a gidan yari ba kuma tabbas idan Afzal ya kai k’aranta kotu tunda tana da laifi chan zasu kaita, ni bazanyi fighting against Afzal ba saboda shike kan gaskiya. Amma dan Allah ba dan ni ko ita ba kayi wa Afzal magana yayi hak’uri, kai kad’ai keda ikon hanasa aikata hakan please.” Hannu Abba ya dafe a kafad’ansa “Karka damu Alhj Abdallah zanyi masa magana in shaa Allahu za a sake Nazeefah.”
“Nagode nagode sosai.”
“Toh bari mu wuce Hjy Mariam mu tafi ko?” nan sukayi sallama suka fice. Har anan kuka Mummy keyi.
“Yanzu mey riban wannan abin kunyan da kikayi mana kika kuma yi wa kanki Nazeefah? Ki gaya mun mey riban hakan? Kiga yadda Daddy’nki ke rok’an Abban Afzal kaman mey maula yanzu hakan ya miki kyau?”
“Mummy dan Allah kiyi hak’uri, Daddy I’m sorry” ta amsa cikin sautin kuka.
“Wace wacan?” Mummy ta tambayeta tana nuni da Safiyya.
‘”Yar aikin Amal ce.”
“Mey tayi ita kuma?”
“Mummy please forgive me.”
“Ki bud’e bakinki kiyi magana ana tambayanki!” Daddy ya tsawata mata.
“Daddy dan Allah kayi hak’uri wallahi sharrin shaid’an ne.”
“Am asking you for the last time idan har baki amsa tambayan da Mummy’nki tayi miki ba wallahi tallahi kin deji rantsuwa ba kaffara ko? Zame hannu na zanyi acikin wannan al’amari Afzal yayi duk abinda yaga dama da ke tunda ke kince bakida hankali.”
“Daddy wannan itace ‘yar aikin Amal Safiyya wacce nayi amfani da ita na fidda Amal daga d’akinta.”
“Kika fidda Amal daga d’akinta?” Mummy ta tambaya da d’umbun mamaki. “Kina nufin kinsa Afzal ya saki Amal?”
“Be saketa ba yaji tayi.”
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un Nazeefah! Is this how evil you’ve become? A iya shekarunki kike wannan mak’irci? har kinsan ki raba aure ki shiga tsakanin miji da mata? Wallahi ba tarbiyyan dana baki ba kenan Allah ma shaidana ne” ta k’are maganan tana neman fara sabon kuka. “Duk kalan wa’azi da nasihan da nake yi miki ashe shiga kunneki kawai yake ta dama yana fita ta hagu ashe a wajen kike ajiye mun magana na, wallahi ba abun in ja miki Allah ya isa ba.”
“A’a Hjy Surayya kiyi hak’uri duk bey kai ga haka ba” Daddy yace da ita yayin da Khaleefah ya cigaba da bata hak’uri yana shafa bayanta a hankali. Shi kansa mamakin halin ‘yar uwarsa yake.
“Mey da mey kika rink’a sanya yarinyar nan yi haka har kika sa Amal tayi yaji iyyeh?” Tisata Mummy tayi a gaba seda ta irga dukkan abubuwan da ta aikata “Wallahi Alhj idan har baka bari an hukunta taba an yanka mata watanni ko shekaru a gidan yari ba uba kage ga ‘yar nan ba, ni da kaina zan kira Afzal in k’arfafa masa guiwa in shaa Allah sekin biya abinda kikayi wa baiwar Allahn nan, har kisa mijinta ya zargeta? Zargui fa Nazeefah! Innalillahi wa inna ilaihi raji’un.”
“Mummy dan Allah kar kiyi mun haka Daddy na tuba dan Allah karka saurari Mummy.”
“Kin bani kunya Nazeefah, na d’au kinyi hankali dagaske har nake alfahari da hakan ashe halin nan naki na nan har yanzu, yaudara na da Mummynki kawai kikayi kika nuna mana kin shiryu, wallahi ban ta6a tsammanin hakan daga gareki amma bazan biye miki ba, Hajiya Surayya kiyi hak’uri hanun mutum baya ri6ewa ya yasar komin mey Nazeefah tayi har yanzu a matsayin ‘yarmu take hakan baze ta6a canzuwa ba. Kuma ko kema fad’a kawai kike baza kiso ace an kai ‘yarki gidan yari ba hak’uri ya zama dole dama acikin ‘ya’yanka dole akwai wanda ze gagareka saidai mu a matsayin mu na iyaye muyi hak’uri mu cigaba da yi musu fatan shiriya.”
STORY CONTINUES BELOW
“Hakane Alhj” ta amsa tana kewayowa kan Safiyya “Ke kuma Safiyya kike ko wa kinga abinda kwad’ayi ya janyo miki ai ko? Shin a ina ma kika samota tun farko?” Ta tambayi Nazeefah.
‘”Yar mey aikin Su Rumaysa ce k’awata wallahi tun farko ita ta fara bani shawaran nan.”
“Ke kuma dake dabbace Allah beyi miki hankali ba kika biye mata ko? Ai kinga ni da idonki kinga yadda ta kaiki ta baroki.”
“Mummy dan Allah kiyi hak’uri wallahi na tuba.”
“Tashi mu tafi Khaleefah.”
“Mummy please don’t go Mummy I’m sorry Daddy dan Allah ka bata hak’uri.” Ko sauraronta Mummy batayi ba ta fice “Alhj muna jiranka.” Juyowa yayi ya kalli Nazeefah ba shida bakin yi mata horo saboda abun kunyan da ta aikata kad’an ne a ganga da nasa, tausayi ta basa sanin duk abinda takeyi shi ya janyo komai, ko dan alhak’in Jameela daya d’auka yaci ace Allah ya basa gagararriyar ‘ya kaman Nazeefah.
“Nazeefah kiyi hak’uri in shaa Allahu zan nemi Afzal inyi masa magana bazaki sake kwana cikin nan ba.”
“Daddy kaima tafiya zaka yi? Dan Allah kar ku tafi ku barni.”
“Mummy’nki na jira na a waje se anjima idan na dawo” kuka take sosai tana kiran sunansa amma haka ba waiwaya ya fice shima, nan aka sake miyar dasu cell ita da Safiyya, ba abinda take nadama kaman fara bin shawaran Rumaysa da tayi. Gashi yanzu tana chan tana morar rayuwarta a k’ark’ashin AC ita tana nan tana shan wuya. Tabbas duk duniya bakada abokiyar shawarar da ta fi mahaifiyarka, itace kad’ai zata baka shawarar da bazata cutar da kai ba amma idan ka biye wa k’awaye musamman na banza irin su Rumaysa da Suwy da ta so sata aikata shirka toh tabbas kana tattare da k’alubale. Yau ta gane bin shawaran k’awa bala’i ne musamman irin nasu Rumaysa. Tayi nadama, tayi nadama matuk’a.
Mummy ta kasa hak’ura suna isa gida takira maman Rumaysa bayan da suka gaisa take irga mata halin da Rumaysa ta jefa Nazeefah aciki. Atafir maman Rumaysa tace ita sharri ake yi wa ‘yarta, ‘yarta baza ta ta6a aikata haka ba. Itama Rumaysan munafukar kanta bayan da Mamanta ta kirata tayi mata maganar bushe ido tayi tace ita bata ma san da wannan zance ba iyaka abinda ta sani Nazeefah tace ta nemo mata yaran aiki guda biyu d’aya nata d’aya na kishiyarta.
***
Afzal kam yana fita daga police station d’in ya kama hanyan TH dan duban lafiyar Amal tasa, saidai kaman jiya yau ma nurse dake bakin k’ofan ta hanasa shiga. Ba irin rok’an duniyan da beyi mata ba amma ta hanasa shiga acewarta bashida appointment da kowa. Ana cikin haka sega Mami ta fito be 6ata lokaci ba yaje ya tareta. “Mami ina kwana?” Kaman wacce bazata amsa ba tace “Lafiya wani abu ne?”
“Mami ya jikin Amal?”
“Da sauk’i idan abinda ya kawo ka kenan kana iya kama hanyanka ka koma.”
“Mami dan Allah kar kiyi mun haka, Mami nasan ban kyauta muku ba amma kuyi hak’uri ku bani wani daman, d’an Adam ajizi ne kuma na gane kuskure na please forgive me.”
“Ka 6ace ka bani waje Afzal, duk kalan walak’anci da rashin mutuncin da kayi wa Baby har kana da bakin cewa a sake baka wani daman? Saboda ka kuma walak’anta ta? Toh wallahi kayi k’arya Afzal dan kuwa Baby tafi k’arfin a walak’anta ta shiyasa nake son tun kafin raina ya 6aci ka fice anan kar insa securities su ja mun kai waje” tana kaiwa nan ta bi gefensa ta fice. Kad’an ya rage Afzal beyi kuka ba a wajen, gu ya nema ya zauna ya had’a tagumi haka har Mami tazo ta wuce sa da bak’ar leda a hannunta da alama breakfast ta siyo musu anan restaurant bata yi mai magana ba, ko kallon kirki bata k’are mai ba. Mik’ewa yayi ya fice inda ya wuce gidan madara ya siyo kayan tea da dama wanda a hanyan sa na dawowa Abba ya kirasa, connecting wayan nasa da car Bluetooth yayi sannan ya d’aga.
STORY CONTINUES BELOW
“Halo Abba?”
“Na’am Prince kana ina ine?”
“Na d’an fita cikin gari ne Abba.”
“Ko zaka iya biyawa tanan? Ina son muyi magana.”
“Toh Abba ba matsala.”
“Ya jikin Amal? Wani asibiti take kaga ya kamata nida Umminka muje mu dubata ai.” Gabansa yaji ya fad’i yasan komin jimawa da dad’ewa gaskiya ze fito su Abba zasu gane Amal tayi masa yaji, daga nan kuma ya san nasa ya k’are har hango kalan masifa da fushin da Abba zeyi masa yake idan ya gano cewan Amal tayi masa yaji bisa ga rashin kyautatawan da yake yi mata.
“Prince?”
“Eh a TH aka rik’eta” ya amsa cikin sauri.
“Toh in ka taho se ka kaini da Umminka muje mu dubata ko?”
“Eh Abba sena shigo.”
“Yauwa Allah ma albarka.”
“Ameen Abba” sannan ya katse wayan. Ajiyar zuciya ya sauk’e sannan ya k’arisa asibitin nurse d’in dake gadin bakin ward d’in still yaje ya sameta.
“Bawan Allah wai baka gajiya ne? An fad’a maka bakada appointment da kowa baze yi ka shiga ba.”
“Nurse na sani, na sani kuma bawai na dawo dan hakan bane” ledan daya ciko da gongonin madara da milo da kwalin sugar da su biscuit da cookies irin masu tsadan nan da kuma sauran kayan tea ya d’ago ya ajiye akan table natan.
“So nake in biya bills na drugs nata da kuma na d’akinta na kwana bakwai I’m sure kafin nan an sallameta.”
“Karka damu da hakan, bawan Allahn daya kawota asibiti jiya ya riga ya d’auke nauyin komai.”
“Ko waye shi?”
“Ya 6oye identity nashi.”
“Allah sarki Allah sak’a mishi, ga wannan toh ina son ki kai mata amma nasan idan kikace in jini ne bazata amince ta kar6a ba.”
“Inji wa zan ce toh?”
“Kice mata inji mutumin da ya kawota asibitin jiya.”
“Toh zan sa akai mata kar ka damu.”
“Kice ina gaisheta dan Allah.”
“Karka damu amma ince inji wa?”
“Kije inji Habib Albinta.”
“Habib Albi? Toh zan fad’a.”
“Thank you and one more favor please.”
“Don’t you think you’re asking for too much?” Ta tambayesa had’e da zuba mai ido.
“Dan Allah ai nace.”
“Ma tukun mey had’inka da patient d’innan? Kai mijinta ne?”
“Yes.”
“Then meyasa iyayenta suke korinka haka?”
“Matsala muka samu har tayi yaji ta koma gida shiyasa nake son ki taimaka mun dan Allah, I really love my wife, I love her soo much.”
“Fad’i abinda kakeso.”
“I want to know ko abu ya samu lafiyan cikin dake jikinta bayan hatsarin jiyan.”
“Toh ni bani muka mata aiki ba jiya ‘yar uwata ce sukayi mata kaga ko bazan sani ba.”
“Please call her and ask I really want to know ko babyna na nan har yanzu.” Shiru tayi bata ce komai ba tana contemplating. Hannu Afzal ya sa a aljihunsa ya ciro wallet nasa tare da irga dubu biyu ya ajiye mata. “Ki sa kati da wannan but please ki kira ‘yar uwar taki ki tambaya mun ita.”
Ba makawa ta d’au wayanta ta yi kaman yadda ya buk’ata.
STORY CONTINUES BELOW
“So?” Eager Afzal ya tambayeta bayan data sauk’e wayan.
“Your baby is still safe, tace ba abinda ya samu lafiyan cikin.”
“Alhamdulillah” wani kalan ajiyan zuciya Afzal ya sauk’e. “Alhamdulillah! Thank you so much I really appreciate.”
“Lallai da alama kana ji da wanan d’an naka, d’an fari ne ko?”
“In shaa Allah” ya amsa ta yana murmushi yayin da ya kasa 6oye farin cikinsa.
“Ayyah Allah ya sauk’eta lafiya toh.”
“Ameen thank you bari zan koma anjima zan dawo.”
“Toh seka dawo.”
“Please make sure kin isar mata da sak’o na.”
“Kar ka damu” da haka sukayi sallama yana ficewa ya bi ta gida inda Abba ke tsammaninsa.
“Ka hau kujera ka zauna mana sekace wani bak’o” Abba yace dashi.
“A’a Abba kar ka damu nan d’inma yayi mun.”
“Batun Nazeefah ne dama, hukuncin da ka yanke yayi dai-dai Prince kuma nida Umminka muna bayanka d’ari-bisa-d’ari” ya sanar dashi yayinda Ummi dake gefensa take gyad’a kai cike da goyin baya.
“Thank you Abba.”
“Tabbas duk wanda ya zalunci wani shima be kamata a barsa haka ba sai dai Allah ma muna yi masa laifi kuma idan muka nemi tuba yana yafe mana shine nikeson kai ma ka duba kayi mata hak’uri, Nazeefah matarka ce har yanzu Prince, nasan abinda tayi da zafi amma kayi hak’uri.”
“Abba kasan evil acts da yarinyar nan ta rink’a yi kuwa? Inda ka sani baza ka ce a tausaya mata, ban so in irga abubuwan da tayi mun bane saboda darajan iyayenta amma abinda Nazeefah tayi mun ta kuma yi wa Amal yaci ace na rubuta mata takardan ta yanzu haka.”
“Subhanallahi me tayi haka?” Kwashe komi yayi ya fad’a musu abu d’ayan da ya 6oye shine yajin da Amal tayi da kuma cikinsa da take d’auke da shi.
“Nazeefan de?!” Ummi tayi exclaiming.
“Ita fa Ummi.”
“Subhanallahi yarinyar da nake cewa tayi hankali ta rungumi k’addararta? Toh inde haka ne head na Amal da aka d’auke ma ranan bikin dinner ku ita ce.”
“Sosai ma kuwa Ummi kika barni har rushe cake d’in da yarinyar chan tayi ita ta turata.”
“Kai amma yarinyan nan akwai ta da sharri, ace a iya shekarunta haka take wannan mak’irci? Allah sarki Amal baiwar Allah ya jikin nata?”
“Alhamdulillah da sauk’i.”
“Bataji ciwo bade sosai ko?”
“Toh Alhamdulillah de” be isa yace eh gashi ba saboda shi kansa be san iya ciwon nata ba banda fashewan kai da mutumin shago ya fad’a masa.
“Gaskiya Nazeefah bata kyauta ba kuma koda nine a position naka abinda zanyi kenan amma Prince kayi hak’uri ko dan iyayenta kayi mata hak’uri kar ka kai maganan nan kotu dukanta da kayi da kuma sata kwanan cell da kayi ma kad’ai ya ishi ya sata nadama kayi hak’uri kaja baya da maganan dan Allah.”
“Abba-“
“Dan Allah nace Prince wallahi rok’ana Abbanta yake dukda shima bawai ya ji dad’in abinda ta aikata ba amma sedon ‘yarsa ce kasan hannun mutum baya ri6ewa ya yasar, yaso ko anyi releasing nata se iyayenta su d’auke ta su tafi da ita chan gidansu kai kuma idan kaji ka huce zaka iya dawo da ita d’akinta se kayi bikonta.”
“Toh shikenan Abba amma dan Allah ka bari ta sake kwanan cell d’in yau yaso gobe se na sa a saketa abinda tayi wa Amal zafi yake mun.”
STORY CONTINUES BELOW
“Ko ya kace Prince nide kawai kar akai maganan nan kotu.”
“Toh Abba in shaa Allahu.”
“Nagode Allah ya cigaba da yima albaraka.”
“Ameen” shi da Ummi suka amsa.
“Toh Hjy Mariam kije ki shirya Prince ya kaimu muje mu duba Amal, seki d’iba mata fruit juices d’innan biyar ko shida haka da carton na ruwa d’aya, duk dey yadda kika ga ya dace.”
“Toh Alhj” nan ta mik’e bayanta Afzal yabi izuwa sashinta yayinda yake tunanin ta ina ze fara sanar da ita cewan Amal tayi masa yaji. Shi kad’ai ya zauna a parlourn yayinda ta shige d’akinta dan canza kaya sede har ta fito ta zauna gefensa be sani ba tsan-tsan yadda yayi nisa a tunani.
“Prince?” Ta ambaci sunansa had’e da tapping nasa akan cinya a firgice ya d’ago kai yana kallonta “Lafiya? Tunanin mey kake haka?”
“Urhmm.. Babu.”
“Yau kuma? Gaya mun menene? Tunanin Nazeefah kake?”
“Ummi no.”
“Yaya ne toh? Feel free to talk to me kaji?”
“Ummi it’s Amal.”
“Innalillahi!” Haka kawai taji gabanta ya tsinke. “What about her? Bade wani abun bane ya sameta dai ko?”
“Ummi dan Allah kar kiga laifi na wallahi zafin so da kishin da nakeyi mata ne ya janyo komai, sanin kanki ne ina son Amal, son da ni kaina wataran har tsoro yake bani.”
“Tabbas ina sane da hakan Prince, meya faru? Tell me already.”
“Ummi Amal tabar gida.”
“Tabar gida kaman ya?”
“Tayi mun yaji kwana biyu kenan yau.”
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un kana nufin Amal bata gidan ka ma da Nazeefah ta tura aka kad’e ta?” Kai zalla ya gyad’a.
“Meya faru ta tafi? Akan abubuwan da Nazeefah keyi mata ne?”
“Kusan hakan.”
“Prince ka bud’e baki kayi mun magana mana mey kake cewa?”
“Ummi ni ne, ni janyo komai tun da Nazeefah ta fara kawo mun k’aran Amal ban ta6a d’aukan mataki akai ba haka nan na cigaba da kallonta da shi har ya zammana ko magana ba ma yi, ana cikin haka kuma Safiyya tace mun wai Amal ta fara shigo da maza cikin gidan-“
“Kai kuma ka amince?” Tayi saurin katsesa.
“Ummi wallahi kishinta da nake ne ya jan-” mari me rai ta kai masa a k’eyarsa “Amma ban ta6a sanin kai soko bane Prince se yau” rai ya had’e yana susa k’eyan nasa bisa ga zafin marin.
“Har za’a ce Amal tana kawo maka maza cikin gida kuma ka amince ba tare da kayo bincike ba? Ai bama abin bincike anan daga ji an san sharri ne da k’azafi.”
“Ummi ni wallahi ba zarginta nake ba.”
“Toh mey kakeyi? Ai de idan ance mutum na kawo maza gida kwana dasu yake kenan.”
“Wallahi ni ba haka nake nufi ba, I know Amal nasan baza ta ta6a cin amanata ba.”1
“Toh da aka fad’a maka se kayi mey seka sameta kace mata kana zarginta?”
“Ni kawai ce mata nayi ban yafe ba idan ta sake shigo min da maza gida.”
“Wallahi kai ka sayi yin yajin Amal da hannun ka lallai ashe baka fasa halin nan naka na amincewa da duk abinda aka fad’a maka ba, yaushe zakayi wayo Afzal? Ace kaman ka amma ba bincike ba komai da an gaya maka abu ka d’auka ka zauna akai?”
STORY CONTINUES BELOW
“Ummi I’m sorry.”
“Kai ka sani ai yanzu kam, bakin da ya sa Amal tayi yaji shi zeje ya dawo da ita d’akinta.”
“Ummi please don’t talk like that please help me get Amal back wallahi I can’t do without her.”
“Kaje ka samu iyayenta?”
“Jiya muna tare a asibitin amma ko sauraro na ba su son yi bale in samu daman basu hak’uri, duk fushi suke dani ko ganin Amal sun hanani d’azu ma naje amma fushi suke dani har yanzu.”
“Ai daidanka kenan nan gaba ko d’an akuya ka gani cikin gidanka akace maka na Amal ne zakayi bincike ka ji bakinta kafin ka amince.”
“Ummi please don’t do this.”
“Toh ya kake son inyi? Kai shikenan kullum bakada aikin da yafi ka ringa tafka shirme ka barni da Abbanka da bada hak’uri da neman alfarma?”
“Ummi I’m sorry wallahi bazan iya rayuwa ba Amal ba.”
“Zaka koya kar ka damu ina Abbanka in sanar dashi wannan rashin hankalin da ka tafka” kafin ta mik’e ya zaunar da ita.
“A’a Ummi please karki fad’a masa kibari se idan mun dawo na koma gida, kema kika mun surutu wallahi na Abba bazeyi kyau ba.”
“Ashe kasan kayi ba dai-dai ba kenan har Amal ce za ace maka tana kawo maza gida ka yarda? ‘Yar da har yau ban ta6a ganin k’wayan idonta ba tsan-tsan kunya.”
“I’m sorry.”
“Ai ita zaka bawa hak’uri ba ni ba.”
“Kema zan baki dan Allah karki sanar da Abba.”
“D’agani ni kam mutum ga shekaru ga hankali amma bayi aiki dasu nan gaba zakayi wayo ai.” Hannunta ya sake kankamewa “Please don’t tell Abba Ummi dan Allah” ya sanar da ita tamkar zeyi kuka.
“Kuka zakayi mun ne?” Kai yayi saurin kad’awa “A’a.”
“Aikin banza kawai duk nabi na 6ataka ka zama wani abun daban.”
“Ita Amal d’in fah? Ka samu kunyi magana da ita tun tafiyarta?”
“Nata kiranta jiya amma bata returning calls d’ina tana matuk’ar fushi dani please help me out Ummi” hararansa tayi ba tare da ta sake cewa komai ba.
****
Haka har suka isa asibitin bata sanar da Abba ba. Tunda su Mami ba son ganinsa sukeyi ba ko k’udurin shiga ciki Afzal beyi ba gudun kar a garin hakan magana ya fito Abba ya gano gaskiya ya kuraresa, yafi son se idan har ya sauk’e su ya koma gida tukun Ummi ta sanar da shi komin yaya dey yasan ba kiransa Abba zeyi musamman yace ze mai masifa ba.
“Ermm Abba wayana ba credit ko zaka kira Papi kace mishi mun iso?” Ya k’irk’iro k’arya sanin ko ya kira Papi ba lallai ne ya d’aga ba.
Ba gardama Abba ya kira Papi ya sanar dashi isowansu.
“Toh gani fitowa.”
“Ya wai?” Ummi ta tambaya.
“Yace yana fitowa.” Jin haka se Afzal ya shafe aljihunsa “Omi’god!” yayi exclaiming da gan-gan.
“Ya lafiya?” Abba yayi saurin tambaya.
“Nayi mantuwa a mota ina zuwa Ummi d’an rik’e wannan please” yayi maganan yana mik’a mata ledan soft drinks da suka d’ibo wa Amal had’e da tura mata carton na ruwan gefenta. Sarai ta gane kan plan nasa, so yake ya gudu gudun kar asirinsa ya tonu. “Ummi” ya kirata a hankali through gritted teeth yadda Abba baze ji ba, yana mey mata ido kai ta kad’a sannan tasa hannu ta amsa da sauri ya bar wajen kafin Papi ya fito.
Har su Ummi suka mik’a gaisuwansu Afzal be dawo ba se chan daya hangosu daga nesa sannan ya k’arisa lokacin har Papi ya rakasu ya koma ciki.
“Kai kuma daga d’auko abu se ka k’i dawowa?” Abba yace da shi.
STORY CONTINUES BELOW
“Ermm” yayi maganan yana susa gefen kansa “Mun had’u da wani abokina na ne matarsa ta haihu shine naje nayi mata barka.” Ita de Ummi banda ido ba abinda take bin Afzal da shi. Tun yana yaro haka nan yake da d’an banzan halin nan ba yadda batayi da shi ba amma ya kasa canzawa, mutum zeyi masa lefi baze samesa ya fad’a masa ba se aukin zurfin ciki bayan nan gashi duk maganan da aka fad’a masa ba bincike ba komai yake amincewa gashi ai yanzu inda banzan d’abi’ar tasa ta kaisa a banza ze rasa mafi son halittar rayuwarsa.
“Allah sarki Allah raya abinda aka haifa.”
“Ameen mu tafi ko?”
“Ba zaka je ka duba matar taka ba yaso mu jira ka? ko kuwa?”
“Zan dawo anjima Abba bazan so in ajiye ku waiting ba ai.”
“Toh shikenan mu tafi” nan suka koma gida.
***
“Ya na d’au ai zaka koma?” Abba ya tambayi Afzal dake k’ok’arin sauk’owa daga mota. “Zan ci abinci ne tukuna.”
“Toh ni na wuce site d’ina zan shirya ma ina da meeting” daga nan Afzal ya bi bayan Ummi suka zarce site nata.
“Nifa banida abincin da zan baka” tace da shi bayan da suka shiga ciki.
“Badan hakan nake nan ba Ummi I just wanted to ask you ya jikin Amal.”
“Da sauk’i” ta amsa shi sama-sama.
“A ina taji ciwon?”
“Kanta ne ya fashe ta gefe sekuma targad’e da ta samu a hannu da k’afa.” Har cikin ransa yaji wa Amal yayinda yake sake tsanan Nazeefah ji yayi kaman kar ya ja baya da kai zancen kotu sa’an ta d’aya Abba ya sa baki da kuwa seta ga abin mamaki. “Allah sarki I wish I could see her.”
“Toh kana iya komawa gida tun da na sanar da kai abinda kake buk’atan ji.”
“Ummi kema fushi kike da ni?” Ya tambayeta a maraice.
“Taya bazan yi fushi ba da kai Prince akan wannan rashin hankali da tausayi daka tafka?”
“Ummi I’m so sorry Amal na fushi da ni, Papi da Mami suna fushi dani ke ma kina fushi dani a ina kikeson insa kaina? Dan Allah kiyi hak’uri.” Se kuma ya bata tausayi.
“Shikenan mey kakeso kaci?”
“Ni bana jin yunwa abu d’aya nakeso ki daina fushi dani dan Allah.”
“Shikenan na daina Allah ya bawa Amal lafiya.”
“Ameen” ya amsa tare da rungumarta she’s the only one he has left ba Amal ba Nazeefah yanzu. A hankali ta zagaye hannayenta a bayansa tana bubbugasa “Zan yima Abbanka magana in shaa Allahu Amal zata dawo a gareka amma da sharad’i” ta sanar da shi had’e da janyesa daga jikinta.
“Muddin muka samu muka dawo da Amal a gareka ka sake ka kuskura ka ci zarafinta zanyi fushi da kai sosai Prince fushin da komin yaya bazan sake sauk’owa ba.”
“Ummi na amince in shaa Allahu bazan sake zaluntar Amal ba, wannan d’in ma sharrin shaid’an ne amma daga yanzu nayi hankali bazan kuma sake ba.”
“Yauwa.”
“Ummi?” Ya kirata.
“Wani abune?”
“Ummi Amal is pregnant.”
“Iyyeh? Kace mene?” Ta tambayesa had’e da zaro ido.
STORY CONTINUES BELOW
“Amal is pregnant jikanki na hanya.”
“Prince wasa kake kokuwa?” Ta tambayesa yayinda ta kasa 6oye farin cikinta. “Kasan fa ba a wasa da irin maganan nan.”
“I’m serious.”
“Masha Allahu, Alhamdulillah Alhamdulillahi ashe de akwai rabo nima watarana zanga jika na kai amma nayi farin ciki, wayyo Amal baiwar Allah. Yarinyar nan ta ko ina tayi ne Prince ga kunya, ga nutsuwa, ga hankali da ladabi, bugu da k’ari kuma gashi yanzu tana d’auke da jika na, wata nawa ne?”
“Nima ban sani ba a bakin Nazeefah nakeji ashe dalilin da tasa a kad’e Amal kenan dan ta samu ta raba Amal da abinda ke cikinta.”
“Oh! Wallahi ko a mafarki ban ta6a sanin Nazeefah bata da hankali haka ba se yanzu. Yanzu saboda Amal ta rigata d’aukan cikinka shine har zata sa a bige baiwar Allah?”
“Wallahi Ummi shiyasa ban so Abba ya amince wa Daddy ba, na so ya barni in kai k’ara kotu saboda a hukunta mun ita.”
“Kayi mata hak’urin kawai Prince ai ko a haka ma ta horu. Allah ma kansa yace yana tare da masu hak’uri da yafiya, kuma kaga wala Allah ma idan ka yafe mata kai ma Amal da iyayenta su yafe maka.”
“Haken kam Ummi toh bari zan koma gida in d’an huta.”
“Bazaka jira kaci abinci ba kace?”
“No need Ummi thank you.”
“Toh Allah kare.”
Gidan Amal ya koma ya mik’e akan gado se tunanin ta yake ya kasa daina yin hakan chan ya d’ago wayansa ya shiga kiranta missed calls kusan 5 yayi mata amma ba wanda Amal tayi returning aciki, da ya gaji kawai seya tura mata sak’o daga k’arsge kaman jiya yau ma ko karancewa batayi ba ta goge.
“Sannu ko?” Mami tace mata.
“Sannu da hidima Mami sakillahu bil jannah.”
“Ameen wannan k’awarki Maamah na sonki wallahi, Allah yabar zumunci.”
“Gaskiya sede ince Alhamdulillah.”
“Kawai de Allah ya sanya rabo ne tsakaninki da Afzal in ba haka ba da Abdul d’inki kika aura na tabbata wancan baze walak’antaki yadda Afzal yayi ba.”
“Hakane Mami ko nima saida nayi tunanin hakan, idan da Ya Abdul ne na tabbata ze min uzuri amma Yaya baya wa mutum uzuri kuma ace kamata har ze amince zan shigo masa da maza gida?”
“Kede barsa shike tattare da asara da alama ma be fad’awa iyayensa kinyi yaji ba shi kansa kunyan abinda ya aikata yake.”
“Tunda Allah ya fitar dani kam ai sede inyi masa godiya, Yaya baya sake samuna bale har ya walak’anta ni yadda yayi a baya.”
“Kina nufin kun rabu kenan?”
“Toh Mami a dalilin mey zan koma masa tunda zargi ya shiga tsakanin mu, ai ko Allah ma ya haramta zaman da zargi ya shiga.”
“Hakane kam Baby amma-“
“Mami please bana k’aunan maganan da ya shafi Yaya.”
“Toh shikenan, nace kayan tea d’in chan fa? Daga gun wa?”
“Oh wannan? Wata Nurse ce ta shigo min dasu d’azu wai inji mutumin daya biya min kud’in asibitin ne.”
STORY CONTINUES BELOW
“Allah sarki wannan bawan Allah dagaske yake a neman aljanah idan da haka duk masu kud’i suke ai da talaka yaji dad’i Baby.”
“Sosai ma kuwa wallahi Mami Allah sak’a mishi da alkhairi dey kawai.”
“Ameen kina jin yunwa ko?”
“A’a d’azu na sha tea.”
“Tea abinci ne Baby? Yanzu fa bake kad’ai bace dole kina cin abinci sosai dan lafiyan abinda ke cikinki.”
“Toh Mami.”
“Gashi kuma baze yi ana siyo miki abinci ba kullum kinsan halin da muke ciki dey amma bari yanzun inje gida in dafa miki duk abinda kikeso akwai nama akwai komi mey kikeso?”
“Banida matsala da hakan Mami dama Papi ne yayi insisting ni kwad’ayin kuka da brabisko ma nike, tun da nayi aure ban sake ciki ba Yaya baya so se bana yi.”
“Allah sarki bari inje in hura wuta toh muyi miki alwala tun yanzu tunda azahar d’in ya kusa ko?”
“Gaskiya kam kika tafi ba wanda ze tayani.” Bayan Mami ta taimaka mata tayi alwala tayi mata sallama ta fice.
Daddy na tasowa daga sallan Azahar yayo TH don duban Amal so yake ya samu koda tsillin gashin kanta ne da za a iya gudanar da DNA test da shi don ya samu ya gano ‘yarsa take koko a’a. Cikin sa’a kuwa daya isa asibitin ba Mami ba Papi, k’ofan ward d’in aka bud’e masa sannan ya shiga inda yasa driver’nsa yi mai gadi daga waje. Sallama yayi amma shiru ba amsa kasancewar Amal na sallah shi ko se yayi tunanin ko bacci take tunda nurse d’in tace masa ba kowa akanta. A hankali ya bud’e k’ofan ya tarar da ita tana sallah a zaune. Tsayuwa yayi daga bakin k’ofan yana jiranta yayin da yake tunanin ta ina ze fara samun tsillin gashin kanta chan seya hango comb a gefen gadon nata wanda Mami ta taje mata gashinta da shi ta kuma manta bata yasar a bola ba. Wani hamdala ya sauk’e sannan a hankali ya k’arisa ciki ya d’au comb d’in had’e da zare gashin ya cusa a aljihu. Lokacin da yake ajiye comb d’in Amal take sallame sallar.
“Baba sannu da zuwa” tace da shi lokacin da idonsu ya had’u tana mey mamakin ko mey yakeyi a kusa da gadonta haka gano kaman tana suspecting nasa ne se ya wayence ya zaro envelope na kud’i a aljihunsa ya ajiye a gefen gadon “Dama nace bari in duba ki a hanzarce kafin in wuce sekuma na tarar kina sallah shine nace bari in ajiye miki kawai tunda ba abu bane mey yawa.”
“Allah sarki Baba baka gajiya damun d’awainiya haka? Naga kayaki da dama d’azu nagode Allah saka da alkhairi” dukda cewan bey fahimci wani kayakin take nufi ba se kawai ya amsa “Ameen ‘yata ba komai Allah k’ara sauk’i ina fatan jikin naki da sauk’i?”
“Alhamdulillah Baba ina samun kulawa sosai.”
“Toh madallah barin koma ina da gun zuwa.”
“Allah sarki nagode sosai Allah ya saka da alkhairi gashi kazo yau ma iyayena basu nan suna ta son suyi maka godiya.”
“Ba komai kice musu kar su damu, toh na wuce se na sake zagayowa.” Nan yayi mata sallama ya fito. A gurguje suka bar asibitin gudun kar su had’u da Mami ko Papi. Wani private clinic suka nufa inda ya sanya gashin kan Amal acikin wata farar leda sannan shima ya tsinke kad’an daga cikin na gemunsa ya sanya a leda daban ya mik’a wa driver’nsa tare da yi masa kwatancan likitan da yake son ya kai masa.
“Har ka kai masa?”
“Eh Alhj yace results ze fito nan da kwana uku.”
STORY CONTINUES BELOW
“Toh madallah se mu wuce office ko? Ina da appointment da wasu.”
***
Da yamma Daddy ya dawo gida sede har anan beji labarin an sako Nazeefah ba wayan Afzal ya kira inda yaji switched off dama da gan-gan Afzal ya kashe wayan nasa sanin Daddy ze nemesa da misalin k’arfe shida sabon layi ya kira Mummy tana d’agawa taji muryan Nazeefah.
“Mummy dan Allah ku taimaka mun Mummy bana son in sake kwana anan dan Allah kuyi hak’uri.”
“Ba daga mu bane Nazeefah Daddy’nki yayi wa Abban Afzal magana shima yace zeyi wa Afzal d’in magana amma shiru har yanzu an kira Afzal d’in ma layinsa a kashe.”
“Innalillahi dan Allah ku kira Abbansa please help me out Mummy.”
“Naji Nazeefah ki k’ara hak’uri” anan ta katse wayan.
“Alhj ko zaka kira Alhj Amin d’inne kaji daga bakinsa?”
“Kar yaga kaman mun tak’ura masa Hjy Surayya.”
“Amma ai ze iya yiwuwa ya mance beyi ma Afzal maganan ba.”
“Da wuya mu jira de zuwa gobe.”
“Yanzu a cell d’in Nazeefah zata sake kwana kenan?”
“Toh ya muka iya Hjy Surayya?”
“Wallahi Nazeefah ta cuci kanta duk mey hali irin nata yana tattare da asara.”
***
Rok’an alfarma Nazeefah ta sakeyi gun securities d’in akan a sake ara mata waya ta kira Afzal sede wayan nasa a kashe, private numbernsa ta kira nan ya shiga a karo na biyu ya d’aga.
“Halo?” Ya soma da cewa.
“Ya Afzal” ta kira sunansa.
“Nazeefah?” Take ya gano muryarta.
“Ya Afzal I’m sorr-” katse wayan yayi nan take ta sake kira haka yana gani yak’i d’agawa daga k’arshe ma kashe wayan yayi gabad’aya. Kwana Nazeefah tayi tana kuka ranan yayinda take nadaman biyewa Rumaysa da tayi. Washegari Afzal yayi resuming office, wajajen k’arfe tara Daddy ya sake gwada layin Afzal se gashi ya shiga, sede har ya tsinke Afzal be d’aga ba instead seya tura masa sak’o akan cewa wai yana meeting ne idan ya fito ze biya police station d’in ayi releasing Amal.
Da misalin k’arfe sha biyu da rabi Afzal ya wuce TH dan duban Amal sede yau ma nurse d’in tak’i barinsa ya shiga, rok’anta yatayi kaman ba gobe har seda ya samu ya shawo kanta.
“Naji zan yi maka hanya ka shiga amma daga yau se yau.”
“Thank you so much I couldn’t ask for more ita kad’ai ce aciki?”
“Eh d’azun mahaifiyarta ta fice.”
“Papi fah?”
“Shi tun safe yazo ya lek’a su ya koma dama shi ba a nan yake kwana ba.”
“Okay.”
“Muje in kai ka” bayanta yabi ta kaisa d’akin Amal. “Seka yi sauri” kai ya gyad’a mata yayinda ta juya ta fice. A hankali ya bud’e k’ofan yana lek’an ciki, akan gado ya tarar da Amal tana kwance, ciki ya k’arisa ya maida k’ofan inda ya tabbatar da bacci takeyi. Kujera yaja ya zauna a gefenta yayinda hawaye ya ciko masa a ido he can’t believe yau kwana uku kenan be sanya ta a ido ba. Hannunta ya d’aga ya sa acikin nasa yana murzawa a hankali “I’m so sorry Amal, I’m terribly sorry” ya shiga bata hak’uri har anan baccinta take ba makawa. Strands na gashin da ya fad’o mata akan fuska ya shiga miyar dasu cikin hulan dake kanta sannan ya soma shafa fuskan nata a hankali yayinda gobaran sonta da tausayi yake ruruwa acikin zuciyarsa. A hankali ya sauk’e hannunsa akan cikinta yana feeling presence na baby’nsa. Gani yake kaman a mafarki, wai Amal na d’auke da cikinsa, oh he can’t ask for more.
Ya kai kusan minti goma zaune akanta yana kallonta da hannunsa manne akan cikinta har anan. Cikin bacci Amal ta d’an motsa hannunta dake kan gado ta d’aga dan ajiyewa akan cikinta inda ya sauk’a akan hannun Afzal. Gagam ta rik’e hannunsa yayin da ta cigaba da baccinta minti biyar a gaba Afzal yayi tunanin komawa gudun kar Mami ko Papi suzo su iskesa. Hannun nasa ya shiga janyewa amma ya kasa dan yadda Amal ta k’ank’amesa. Gashi baya son ya tayar da ita, ya zeyi? Hannun nasa ya cigaba da k’ok’arin cirewa amma ya kasa wanda daga k’arshe seda Amal d’in ta farka. A hankali take bud’e idanunta har ta sauk’e su akansa ba k’aramin razana tayi ba ganinsa da tayi akanta. Kad’an ya rage bata sa ihu ba, shin har ya akayi ya shigo ciki? Ta d’au nan restricted area ne se idan an san da zuwan mutum ake barinsa ya shiga how comes toh?
“Amal” ya kira sunanta a hankali cikin wani irin salo hannun nasa ta sake da wuri ta shiga kalle-kalle cikin d’akin tana neman Mami.
“My adorable Kitten” yake sake kiranta lokacin da ta kawar da kanta gabad’aya daga kallonsa. “Amal please turn around and look at me” saidai kaman ba da ita yake ba.
“Amal I’m terribly sorry, please forgive me for doubting on your faithfulness, I’ve realized the truth nagane Nazeefah da Safiyya ne ke bayan komai dan Allah kiyi hak’uri maganan da nake miki yanzu haka na mik’a su ga hukuma a hukunta munsu, I can never forgive them for what they did to you, yau kwanansu biyu kenan a cell.” Mamaki sosai kalamunsa suka sanyata, akanta har ya kaisu police station? Sede tayi shiru bata ce dashi komai ba.
“Amal I felt horrible when I found out Nazeefah ce tasa aka kad’eki however I’m grateful for the fact that you still chose to be alive and didn’t leave me all by myself. Bazan iya rayuwa ba ke ba Amal, kinfi kowa sanin hakan, you’re my necessity and everything I need to complete my life please don’t leave me” hannunsa ya d’au ya ajiye akan cikinta hakan ne kawai yake tunanin ze sata yin magana ai kuwa ba shiri ta cire “Don’t you ever touch me Yaya” ta sanar da shi ba tare da ta juyo ta kallesa ba.
“Thank you for speaking to me Kitten, at least yau zan iya bacci tunda na saurari muryanki thank you so much” nan ma shiru tayi masa “Baby why didn’t you tell me? Meyasa baki fad’a mun kina da ciki ba?” Mamakin yadda akayi ya gano tana da ciki take, waya sani ko nurses d’in ya tambaya suka sanar da shi.
“Kitten gani kike kaman in kin fad’a mun zanyi denying baby’n ince ba nawa bane? Amal I’ve never and will never accuse you of cheating on me, I know who you’re nasan bazaki ta6a cin amanata ba kuma koda nace miki ban yafe ba idan kika sake shigo mun da maza cikin gida bawai ina nufin wani abu bane course mates naki nake nufi kuma Wallahi ni ban san shirin yaji kikeyi ba da na baki hak’uri na hanaki, senayi tunanin ko so kike ki tare zuwa d’ayan d’akin gabad’aya ban san lokacinda kika tafi ba se washegari dana lek’a d’akinki naga bakiya nan.”
So take ta ce masa meyasa be kirata ba toh bayan da yaga bata nan d’in se taga kuma ba amfani tunda ba komawa agaresa zatayi ba.
“I got so mad shiyasa ban kiraki naji daga gareki ba amma bawai hakan na nufin bana sonki bane ko kuwa nayi hakan dan in nuna isa ko dan in walak’antaki ba, Amal sanin kanki ne bazan ta6a yi miki haka ba, I love and respect you alot please come back to me abinda ya faru ya riga ya faru nasan ni mey laifi ne, nasan nayi kuskure, na san ban kyauta miki ba na k’in miki uzuri da nayi da kuma k’in baki dama kiyi bayanin kanki Wallahi duk sharrin Nazeefah ne, she manipulated me please forgive me Amal Yaya is so sorry.”
“Amal why aren’t you saying anything?” Ya tambayeta a maraice bayan dogon shirun da tayi, shirunta a garesa ba k’aramin tashin hankali bane but he really can’t force it ya zama masa dole ya hak’ura ya bata space da take buk’ata har izuwa lokacin da za ta huce.
    Tabbas mutum ya guji fushin mey hak’uri koda wasa be ta6a tsammanin Amal zatayi masa fushi haka ba saidai bai ga laifinta ba ko d’aya saboda shi ya turata har bango, idan da wata ce da tun ranan da ya korata daga d’akinsu zatayi mai fushi amma dukda hakan bata fasa yi masa ladabi ba, he’s sure with time she’ll come by.+
Envelope da ya tanadar mata ya zare daga aljihunsa ya ajiye mata a kan gadon daga gefenta sannan ya mik’e “I have to go now, Allah k’ara miki lafiya I can’t wait to see you back on your feet I love you so much my adorable Kitten” badan yana so ba ya mik’e ya fice juyawanda Amal zatayi hawaye ya tsiyaya daga d’ayan idonta. Tabbas har yanzu tana son Yaya amma idan ta tuna da abinda yayi mata se taji gabad’aya ya fita mata a rai, she never wished for things to turn out bad between them two like this, amma ya ta iya? She can’t change the past only can she make the future better. Gyara kwanciyanta da tace zatayi taji k’aran paper, a hankali ta miyar da idonta wajen nan taga envelope da ya ajiye mata da hannunta d’aya ta d’aga ta zazzage inda ta tarar da kud’i da dama aciki, sabin dubu d’ai-d’ai. Da hannunta d’aya ta irga taga dubu ashirin ne sannan ta miyar ta ajiye a gefe.
***
  Koda Afzal ya shiga cikin mota ya kasa kunna engine d’in, be hankara ba kawai yaji hawaye na tsiyaya masa daga ido yau ina ze sa kansa? Ya ze rayu idan ba Amal a kusa da shi? Gani yake idan har bata dawo a garesa ba ze mutu saboda zuciyarsa bazata iya jure rashinta a kusa da shi ba da k’yar ya iya kunna motan ya koma office. Hud’u nayi ya tashi. Gabad’aya ya mance da labarin Hindu se yanzu ta fad’o masa a rai, gidan Nazeefah ya biya inda ya sameta kwance a d’akinta tana bacci, tashinta yayi sannan ya kira driver’n Amal da ya kaita gida bayan sallamarta da yayi. Tana isa gida Ummansu ta rungumeta tana kuka tun jiya take kuka har zuwa d’azu da taje ta duba Safiyya. Dama tun farko ita bata goyi bayan kawosu birni ba dan gudun sharri irin wannan. 
   Se k’arfe shida Afzal ya wuce police station d’in yayi magana akayi releasing nasu Nazeefah. Da gudu ta fito ta fad’a jikinsa tana kuka “Ya Afzal dan Allah kayi hak’uri ka yafe mun na tuba bazan sake ba” hannunsa yasa ya janyeta “Don’t misinterprete my intention, ba wai don ina so nasa akayi setting naki free ba Nazeefah se don Abba ne ya buk’aci hakan, idan da ta ni ne da se kotu ta yanke miki hukuncin da yake dai-dai da laifin da kika aikata sannan zanji dad’i because I want you to change, canji na tsakani da Allah bana muzurun da nake da tabbacin kikayi ba. Bazan 6oye miki ba Nazeefah, da abinda kikayi kinsa na tsaneki kaman yadda Amal ta tsaneni yanzu, ko k’aunan gani na Amal bata so a haka kike cewa kina sona? A tunani na idan kana son mutum har abinda yake so zaka so, kin san ina son Amal but you still went ahead and hurt her I’m still mad at you Nazeefah I might forgive you someday amma bazan ta6a mancewa da abinda kikayi wa Amal d’ita ba let’s go home.” Driver’n Amal ya kira yazo ya d’auki Safiyya itama kud’in sallamarta yabata sannan ya buk’aceta da idan ta isa gida ta tattare ina-inata tabar masa gida yayinda shi da Nazeefah suka koma nasu gidan suma.
   Babban akwatinta ya d’auko mata “Here start packing your clothes ki bar min gida bana k’aunan ganinki anan Nazeefah as long as kika cigaba da zama anan zakina sani tunawa da munanan abubuwan da kika rink’ayi wa Amal d’ita wanda hakan ze sa in sake tsanar kine kawai so its better ki koma gida gun su Mummy.” Kuka take sosai ta k’arisa inda yake tsaye had’e da sauk’a k’asa akan guiwarta “Ya Afzal dan Allah karka mun haka, dan Allah don’t send me home I’m terribly sorry please forgive me wallahi na tuba bazan k’ara ba dan Allah kar ka sakeni Ya Afzal bazan iya rayuwa ba kai ba please don’t divorce me” ta k’arisa cikin tsananin kuka. Hannu yasa ya d’agata “Bazan sake kiba Nazeefah saboda despite everything I still love you and I cherish the moments we spent together, I just need some space and alone time anytime I’m ready zan dawo dake but you really have to go now.” Rungumesa tayi tana kukan cire rai “Please don’t send me away Ya Afzal I can’t live without you dan Allah kayi hak’uri ka yafemun please don’t send me home I’m so sorry” kuka ta cigaba dayi ajikinsa na sosai ta basa tausayi shima bawai dan yana so ze korata gida ba dan kawai bayida wani option ne saboda zamanta acikin gidan nan kawai sake sanyasa tsananta zeyi shi kuma baya son hakan saboda idan ya tsani abu ya tsanesa kenan no turbing back, so it’s better ta tafi gida kawai. A hankali ya sauk’e hannayensa a bayanta hugging her back sun d’au tsawon lokaci a haka sannan ya janyeta na k’arfi dan yadda ta kankamesa kuka take sosai tana kad’a masa kai “Please don’t do this Ya Afzal please don’t.”
STORY CONTINUES BELOW
  “I’m so sorry Nazeefah I’m really sorry I wish there’s something I could do you have the next one hour to pack your belongings zan sa driver’n Amal yayi dropping naki a gida” yana kaiwa nan ya juya. Ihu Nazeefah ta k’urma tana kuka tana kiran sunansa amma ko waiwayawa beyi ba ya fice rushewa tayi a wajen tana kukan tsuma zuciya yau ina zata sa kanta? Ya zatayi da ranta? Ya zatayi da masifaffen son Afzal dake cikin zuciyarta? Bazata iya rayuwa ba shi ba, da ta rasa sa gara ta rasa rayuwarta gabad’aya, soyayyan sa ya riga ya zame mata jinin jiki, idan ba shi baza ta iya rayuwa ba. Tafi minti goma a wajen tana kuka sannan da k’yar ta iya lalla6awa ta k’arisa wajen wardrobe nata yayin da ta shiga tattare kayakin nata, tana yi tana kuka haka har ta samu ta gama tattare kayakin nata ta ja akwatin ta rufe sannan ta fito da akwatin parlour ganin ba Afzal a gurin se ta k’arisa waje nan ma bata gansa ba ashe acikin motansa ya 6oye yana kallonta daga mirror. Waya yayi wa driver’n Amal nan ya k’ariso ya ja mata akwatin nata cikin mota se kewaye take tana nemansa amma ko alamansa babu ga kuma motansa na nan a fake, haka ba don tana so ba ta k’arisa motan ta shiga har driver ya kaita gida tana aikin kuka. Ba k’aramin hamdala su Mummy sukayi ba ganinta ta dawo gida, text Daddy ya turawa Afzal yana yi masa godiya, kwana ranan Nazeefah tayi musu tana kuka, kukan zafin rabuwa da Afzal shima Afzal har hawaye seda ya zubar bayan tafiyan ta, yana sonta amma baze iya cigaba da zama da ita muddin Amal bata dawo a garesa ba toh baze iya dawo da Nazeefah ba, wannan haka take.
****
     GIDAN ALHJ AMIN
Seda Ummi ta jira Abba ya gama cin abincinsa sannan tayi gyaran murya. “Alhj?” Ta kira sa.
  “Yes My dear?” ya amsa had’e da d’ago kai yana kallonta.
  “Dama wata magana nake son yi maka amma sena ga jiya kaman a gaje ka dawo yau kuma throughout baka yini a gida ba.”
  “I’m sorry schedule d’ina ne kwana biyun nan is so tight se a hankali.”
  “Ba komai dear Allah taimaka ya k’ara arziki da bud’i.”
  “Ameen Hjy Mairama ta so what is it you wanted to discuss?”
  “Batun Prince ne dama.”
  “What about him?”
  “Amal tayi masa yaji” bata tsaya yin corner-corner ba ta sanar da shi gaskiya kai tsaye.
  “What?!”
  “Amal tayi masa yaji yau kwana hud’u kenan.”
  “Kina nufin har mukaje muka gaisheta dama ba a gidansa take ba?”
  “I’m sorry but yes.”
  “Kuma kin sani?”
  “Dear I’m sorry.”
  “Meyasa baki fad’a mun ba?”
  “Alhj ina gudun fushin da zakayi masa ne already matsaloli sunyi masa yawa kaga idan kaima ka k’ara da naka abun zeyi masa yawa.”
  “Wow! Meya faru har tayi masa yajin? Batun abinda Nazeefah tayi ne?” K’arya taso yi masa tace eh amma tuna idan aka je yin sulhu gaskiya na iya fitowa taji kunya se kawai ta fasa ta irga masa gaskiyan al’amarin.
  “Afzal d’in?” Ya tambaya da mamaki shi kam da ba a bakin Ummi yake jin labarin ba se yace sharri akeyi wa d’ansa.
  “Unfortunately abinda ya faru kenan amma yayi nadama yanzu wallahi Alhj dan kad’an ya rage beyi kuka ba da yake ban labari kayi hak’uri kayi masa uzuri sharrin shaid’an.”
STORY CONTINUES BELOW
  “Nadama? Bega komi ba tukuna kuma ki daina kawo zancen sharrin shaid’an wannan ganganci ne da rashin mutunci da kuma rashin tunani da rashin aiki da hankali a fili har ‘yar yarinyar nan ne zeyi zarginta? Mey ta sani?”
  “Alhj yace shifa ba zarginta yake ba.”
  “Maganan banza amma ai abinda ya nuna mata kenan kuma abinda zata fad’awa iyayenta kenan.”
  “Alhj kayi hak’uri tabbas Prince yayi kuskure amma baza mu iya canza hakan ba kayi hak’uri a had’a kai ayi masa bikon yarinyar nan yaso yayi hakan da kansa amma abun ya gagara ko ganin Amal iyayenta sun hanasa yi wallahi yaron nan na cikin tsaka mey wuya ace cikin matansa biyu ba ko d’aya a wajensa.”
  “Ai daidansa kenan ko nine bazan barsa ya shiga yaga min ‘ya ba tunda ya walak’anta ta haka, iyayen Amal sunyi mun dai-dai ko a babu yanzu ze san matsayinta, ma wannan wani irin rashin hankali ne? Wallahi wasu abubuwan in ance min Prince ya aikata se inga kaman sharri ake yi mishi ban ta6a sanin sa da wannan banzan hali da rashin wayo ba.”
  “Alhj kayi hak’uri ze gyara.”
  “Kibar 6ata miyan bakinki kina bani hak’uri Hjy Mariam ba dani za’ayi abin kunyan nan ba in kinga na taka k’afa gidansu yarinyar nan toh takardan sakinta na kai mata dan nasan koba jimawa da dad’ewa iyayenta zasu nemi a kai musu takardan ‘yarsu bayan nan ba abinda ze kaini gidansu, rashin hankalin Afzal ya isheni haka.”
  “Alhj dan Allah kar kace haka kafi kowa sanin ciwon Afzal, kafi kowa sanin raunin zuciyarsa da kuma abinda rashin yarinyar nan a kusa dashi ze haifar, ina fatan baka mance da abinda likitansa yace ba.”
  “Ai idan ma mutuwa yayi shi ya siya mutuwan nasa da kansa kawai dan yarinya na da hak’uri shikenan seya walak’anta ta? A idonsa yarinya ta tattare kayakinta amma dan gadara yak’i koda yi mata magana bale yayi tunanin hanata? A ina aka ta6ayin haka? Saboda yana ganin gidansa yafi gidan iyeyenta gata ko mey? Sannan kuma dan rashin kunya da rainin wayo yace wai bey d’au shirin yaji take ba? Kinga I’ve had a stressful day I’m very tired in kina da niyyan kwanciya bismillah in kuwa a’a ni seda safe.”
  “Alhj please kar kayi haka wallahi mune da asara idan muka rasa Afzal kaman yadda Daddy’n Nazeefah yace hannun mutum baya ri6ewa ya yasar toh muma fa hakane komin yaya baza mu k’i Afzal ba kuma kaima fad’a kawai kake wallahi baka gansa kwance akan gadona asibiti bane fighting for his life” ko amsata beyi ba ya k’arisa d’aki abinsa ba tare da ya kewaya ba. Ita kanta bawai taji dad’in abinda Afzal yayi bane kokuwa tana goye masa baya kawai gudun halin da yake iya fad’awa ne idan ba a dawo masa da Amal a garesa ba sanin raunin zuciyarsa. Bazata gaji da basa hak’uri ba tasan zuciyansa yana da saurin fushi amma kuma hak’uri kad’an aka basa ze sauk’o.
***.        ****.           *****.          *****
Kaman yadda likita ya d’au alk’awari bayan kwana uku ya tanadar da results na Daddy. Da yammacin ranan yaje ya amsa da kansa ko da driver be nema ya rakasa ba. Ba k’aramin tsinkewa gabansa yayi ba bayan da ya karance results d’in yaga komi positive yake nunawa, ma’ana Amal ‘yarsa ce kad’an ya rage beci tuntu6e ba dan yadda ya razana se hailala yake yana maimaita innalillahi wa inna ilaihi raji’un.
   Yanzu Amal ‘yarsa ce? Ashe dagaske ne ciki ya shiga jikin Jameensa bayan abinda ya faru a tsakaninsu, yau ina zesa kansa? Ta ina ze fara sanar da mutane wannan badak’ala? Wai wannan a duniya ma kenan Allah yake neman tozarta sa haka ina kuma ace a lahira? Wannan wace irin k’addara ce taya yaransa biyu zasu auri miji d’aya? Shin haka Allah yake kama duk wanda ya d’au alhak’in wani? Shin haka duk wanda ya aikata aikin banza yake fara ganin sakamako tun anan duniya ba ma se anje lahira ba? Shin ashe komin yaya mutum yaso 6oye laifi ko zunubi ta inda baya tsammani Allah ze tozarta sa a idon jama’a? Yau yana cikin wani yanayi ta ina ze fara sanar da Amal shine mahaifinta? Ta ina ze fara sanar da Hjy Surayyarsa yana da shegiya a waje? Ta ina ze fara sanar da Nazeefah Amal ‘yar uwarta ce? Da wani ido yaransa zasu sake kallonsa? Da wani ido amininsa da kuma manyan abokansa zasu sake kallonsa harma da ‘yan unguwa da masu aiki a k’ark’ashinsa? Shikenan k’wan da ya jima yana gudun fashewansa ya tsage yanzu k’iris ya rage kuma ya fashe ya zube. Kansa ne ya mugun d’aurewa gabad’aya ya rasa mey ke masa dad’i. Allah ne de kawai ya kaisa gida ranan saboda yadda ba hankali a jikinsa yake tuk’i tunda ya isa gida ya rufe kansa a d’aki yayi k’aryan migraine ne ke damunsa baya son a tak’ura mishi, tunanin ta inda ze fara 6ullowa al’amarin nan yake amma ya kasa tabbas acikin yaransa biyu dole se d’aya ta zama bazawara dan bazeyi Afzal ya cigaba da zaman aure da dukansu biyu ba tunda jini d’aya suke. Annabi beyi k’arya ba da yace idan kayi me kyau me kyau ze bika idan kuwa kayi na banza na banzan ne ze bika tabbas yaga hakan yanzu. Yanzu da ace aikin alkhairi yayi a baya sede ‘ya’yansa suci riban hakan, amma daya shuk’a tsiya ba shi kad’ai ba harta yaransa seda hakan ya shafa.
STORY CONTINUES BELOW
  ****  
  Nazeefah bata fasa turawa Afzal sak’o tana neman tubansa ba safe ba dare tun tana kiransa baya d’agawa har ta hak’ura ta daina yau kwanan ta biyu kenan gabad’aya ta fita daga kamanninta dama ba k’iba bane da ita akan raman nata ta sake ramewa ba aikinta se kuka da tunani kullum, gashi ko makaranta ta shiga bin ta da kallo ake Rumaysa duk ta bazata a gari mijinta ya kaita cell sekace ba ita ta d’aurata akan gur6arcacciyar hanyar ba.
  ***
  Afzal na zaune a office amma hankalinsa gabad’aya akan Amal tasa yake kullum haka yake yini da tunaninta ya kuma tashi da shi gashi tun ranan be sake sanyata a ido ba, koya kirata bata d’agawa sak’o ma ya tura mata bata replying nasa, whatsapp messages ma ko reading batayi he can’t explain how much he’s missing her. So yake ya sake ganinta kafin a sallameta daga asibitin dan yaji daga bakin nurse d’in cewa yau za a sallameta jira yake lokacin lunch yayi yaje ya dubata wanda kafin nan ya d’au wayansa ya kira Ummi jin shiru tun ranan da sukayi magana har yau bata sake nemansa ba. Seda wayan ya kusa tsinkewa ta d’aga bayan sun gaisa yake tambayarta ko sunyi magana da Abba, bata 6oye masa komai ba ta fad’a masa yadda sukayi da Abba yadda ya nuna komin yaya shi bazesa hannu cikin wannan al’amari ba na sosai zuciyan Afzal ya karye.
  “Halo Afzal are you still on the line?”
  “Yes Ummi” ya amsa cikin wani irin salo ko daga jin muryarsa Ummi tasan zuciyarsa ta mace.
“Don’t lose hope Afzal ka cigaba da addu’a nima bazan fasa bawa Abbanka hak’uri ba in shaa Allahu ze sauk’i aje ayi maka bikon Amal kaji? Amal zata dawo a agreka da izinin Allah.”
  “Ta yaya Ummi? Ko jiya naje na samu Papi amm he’s not willing to talk to me in the case of Amal it’s worse ko magana bata yimun Ummi I’m slowly dying I can’t do without her.”
  “Ka kwantar da hankalinka Afzal.”
  “Ta ina hankalin nawa ze kwanta Ummi ina shirin rasa Amal? I’m definitely going to die.”
  “Subhanallahi wai bazaka bar magana haka ba? Bazaka mutu ma kuma in shaa Allah Amal zata dawo a gareka kar ka gaji da bata da iyayenta hak’uri nima zan taimaka maka zan samu Mami inyi mata magana.”
  “Thank you Ummi, I know I can always count on you thank you so much Allah sak’a miki.”1
  “Ameen ka kwantar da hankalinka kaji?” Kai ya gyad’a tamkar tana gabansa “Se mun sake waya zan kuma cigaba da bawa Abban ka hak’uri nasan ze sauk’o even though ba yanzu ba amma definitely he’ll.”
  “Thank you so much Ummi” da haka sukayi sallama. Azahar nayi bayan ya idar da sallah yaci abinci ya wuce TH sede yana isa ya tarar da sad news na cewa an riga an sallami su Amal har sun koma gida, tamkar yayi kuka haka yaji dama yaso yayi wa driver’nta magana yazo ya d’aukesu ya kaisu gida, a cewansa gabad’aya se yamma zasu tafi ashe ba haka neba. Be gaji ba washegari da yamma bayan ya taso daga office ko gida be je ba ya zarce gidan su Amal sallama yayi Mami ta amsa sannan yasa kai ya shiga ya nemi gu ya tsuguna. “Bismillah hau kan tabarman mana ka zauna” Papi yace da shi.
  “A’a Papi nan ma yayi nagode. Ina yini?”
  Gaishesu yayi duka cike da ladabi da biyayya inda suka amsa ba yabo ba fallasa har hakan yaso d’aurewa Afzal kai a tunaninsa gabad’aya zasu koresa yau idan ya shigo sekuma ya tarar da sa6anin hakan.
  “Papi ya jikin Amal?” Ya tambaya afterwards.
  “Da sauk’i Alhamdulillah.”
  “Jiya naje asibiti na tarar har an sallameku kun dawo gida dama driver naso turawa ya dawo daku gida.”
  “Ayyah karka damu mungode.”
STORY CONTINUES BELOW
  “Papi bazan gaji da baku hak’uri ba dan Allah kuyi hak’uri ku dawo mun da Amal, nasan nayi kuskure amma kuyi hak’uri ba yadda banyi da Abba ba ya sa baki ya tayani baku hak’uri amma yak’i saboda shi kansa fushi yake dani akan abinda nayi wa Amal, dan Allah kuyi hak’uri wallahi sharrin shaid’an ne.”
  “Tabbas d’an Adam ajizi ne amma a gaskiya bazan 6oye maka ba Afzal abinda kayi wa Baby ya ci mun tuwo a kwanu. Ban ta6a tsammanin hakan daga gareka ba Baba na, atunani na ko a bayan raina zaka kula min da Baby ka rik’e min ita amana se gashi tun a ido na ka soma walak’anta ta kodan gani kake bata da uba bata da gata?”
  “Wallahi Papi ba haka bane, sanin kanmu ne nan duka Amal tafi k’arfin a walak’anta ta kuyi hak’uri wallahi sharrin shaid’an ne.”
  “Tafi k’arfin a walak’anta ta amma harda korinta daga d’akinta Afzal? Saboda ko tsinke bata kai gidan ba?” Mami da tayi shiru tun d’azu ta tsoma baki.
    “Mami Wallahi ba don haka bane sharrin shaid’an ne amma in shaa Allahu hakan baze sake faruwa ba.”
  “Tabbas saboda Amal baza ta sake komawa gidanka ba, haka tace kuma ina biye da ita d’ari bisa d’ari.”
  “Mami dan Allah kar kiyi magana haka Mami keda ya kamata ki tayani shawo kanta kuma kike cewa haka? Mami kin fi kowa sanin yadda nake son Amal kin fi kowa sanin yadda rashin ta a kusa dani yake babban hatsari da tashin hankali a gareni dan Allah kar kiyi mun haka.”
  “Ina sane da hakan Afzal, shiyasa kai na ya d’aure na rasa gane dalilin daya sa kayi mata abinda kayi ko dan gani kake bata halacacciyar hanya aka sameta ba dan haka bata da wani k’ima da daraja? Kake ganin kaman alfarma kake mata saboda ka aureta hakane Afzal?? A jinka idan da anyi shawara da ita zata so ta kasance hakan ne? Ko a jinka ni d’in inda nasan sharrin dake jira na a yinin ranan zanje in sami azzalumin mutumin daya cuceni d’in ne?” Ta k’are maganan idonta na cikowa da hawaye, dama rana mey irin ta yau take gudu shiyasa bata goyi bayan Papi ya sanar da Afzal asalin Amal ba tun farko, ai ga irinta nan yanzu tun ba ayi nisa ba ya soma walak’anta ta.
  “Subhanallahi Mami dan Allah kar kice haka, Mami please don’t ever talk like that ni wallahi in ba da kika d’auko maganan ba ma yanzu gabad’aya na manta da ita wallahi ban ta6a goranta wa Amal akan asalinta ba idan k’arya nake muku ku kira ta ku tambayeta wallahi bazan ta6a yin haka ba please forgive me if you felt that way I’m terribly sorry.”
  “Ya isa Jameelah yi hak’uri ki koma ciki ni da Afzal zamuyi magana karki d’aga muryanki Baby ta jiyoki yi hak’uri ki koma ciki” batayi musu ba ta mik’e ta shige d’aki inda Papi da Afzal suka cigaba da tattaunawa.
   “Shin meya faru Afzal? Naji 6angaren labarin daga gun Amal kaima zan so inji naka 6angaren.”
  “Papi kunfi kowa sanin yadda nake son Amal, wallahi sharrin abokiyar zamanta ne, ita tayi manipulating mind d’ina ta shiga tsakani na da Amal, Papi komi na saiwa Amal harta tsinke idan na koma gun ‘yar uwar nata senaji a bakinta taya zan san wai ta had’a baki ne da ‘yar aikin Amal tana kai mata rahoton duk abunda ke gudana a cikin gidan namu?” bayanin komai dalla-dalla yayi wa Papi.
   “Tanan kam kayi gaskiya ko ni ne zan fi yarda da Nazeefah akan ita Baby saboda wannan shaida k’wwak’k’wara amma batun shigo da maza cikin gidanka fah? Ka ko san Allah ya haramta auren da zargi ya shiga? Ashe har Allah ze kawo ranan da zaka yi kokonton tarbiyyan dana bawa Amal?”
   “Wallahi Papi ni ban ta6a zargin Amal ba, itace bata fahimce ni ba dan ko da ‘yar aikinta ta gaya mun cewa sau biyu tana shigo da maza cikin gidan tunani na gabad’aya akan course mates nata ya k’are ba wai kwartaye ba, wallahi sam ni hankali na be kai ga chan ba saboda nasan da wata irin mata nake zaune. Kuma ko da na tashi yi mata magana ce mata nayi kar ta sake shigo mun da coursemates nata cikin gida ba wani abun ba, itace tayi mun mumunar fahimta dan haka nake sake baku hak’uri, kuyi hak’uri.”
STORY CONTINUES BELOW
  “Na fahimce ka, amma batun kana ganinta take had’a kayakinta baka hanata ba baka kuma yi mata magana ba ba fa shin hakane?”
  “Wallahi Papi ban zata wai shirin yaji takeyi ba, dama tunda muka soma samun matsala na turata d’ayan d’akin kowani safiya takan shigo d’akin namu ta shirya toh ko da naga tana shirya kayakin nata senayi tsammanin ko zata tare chan gabad’aya ne washegari kawai na tashi na tarar bata gidan wallahi ban san lokacinda ta tafi ba.”
   “Idan har haka ne meyasa baka nemeta ba bayan faruwan hakan? Da ace a ranan kazo bikonta ka deji rantsuwa ko? Wallahil azeem komin ya girman kuskuren da aikata yake zansa maka Amal a mota ka koma da ita gida saboda ka nuna tanada muhimmanci kenan amma bakayi hakan ba Afzal, ni kake tunanin zan kiraka ince maka naga Amal ta taho gida lafiya?” Kai ya kad’a a hankali cike da nadama “Abinda ya 6ata mun rai kenan, banzan da kayi da ita kak’i ka neme ta kak’i ka neme ni ko mahaifiyarta, anan ka nuna baka damu da ita ba, anan ka nuna ita ba kowa bace kasan komin jimawa da dad’ewa zamu sata a mota mu miyar maka da ita mu baka hak’uri tunda de gidanka yafi gidan iyayenta gata ko ba haka ba?”
  “Subhanallahi dan Allah Papi kayi hak’uri wallahi ni ba hakan a zuciya na nasan nayi kuskure kamata yayi in kira Amal idan banyi hakan ba kuma in kiraka ko Mami, amma d’an Adam ajizi ne kuyi hak’uri ku gafirceni in shaa Allah hakan baze sake faruwa ba wallahi fushinku a gareni babban tashin hankali ne especially in the case of Mami bana son ku d’au bana son Amal wallahi ina sonta, I really do love her kuma se inda k’arfi na yak’are zan cigaba da baku hak’uri har se Allah ya huci zuk’atan ku.”
  “Ni ba fushi da kai nake ba Afzal nayi maka hakan ne dan ka gane kuskurenka ka kuma san k’ima da darajar Baby bayan nan kuma don in tabbatar da kalan soyayyar da kakeyi mata kuma na tabbatar da hakan yanzu don idan da wani ne da tuni yayi zuciya kodan irin abinda nida Maminta muka rink’ayi maka a asibiti amma haka baka fasa zuwa ba kullum dukda tokarin da muke maka. Hakan ya nuna mun dagaske ne komi ya faru bisa kuskure ne amma  kana son Baby kuma ina alfahari da hakan sosai Afzal tabbas se mey sonka ne ze so wani naka akan Baby kuma na tabbatar da cewa kai masoyin mu ne na hak’ik’a.”
   “Godiya nake Papi, ba k’aramin farin ciki kalamunka suka sanyani ba kuma hak’urin nan shi zan cigaba da baka da Mami kuyi hak’uri duk sharrin shaid’an ne.”
  “Shikenan Babana ya wuce Allah yasa mu dace.”
  “Ameen Papi godiya nake, Allah saka da alkhairi.”
  “Ameen.”
  “Shin yanzu zan iya dawo da Amal d’akinta? Dan Allah kar kace a’a Papi, alk’awari na d’auka bazan sake k’untata mata ko yi mata ba dai-dai ba bi iznillahi.”
   “Na yarda da kai Afzal amma nima ba daga ni bane, bazan iya tilasta wa Baby akan cewa lallai-lallai se ta koma maka ba iyaka inyi k’ok’ari in shawo maka kanta.”
  “A hakan ma godiya nake Papi, Allah sak’a da alkhairi yabar zumunci.”
  “Ameen ba komai ana tare ai.”
  “Kuma dan Allah ka sake bawa Mami hak’uri ni wallahi sam ba hakan a raina.”
  “Karka damu.”
  “A kuma gaishe mun Amal da jiki nasan koba don tana bacci ba bazata amince ta fito mu gaisa ba.”
  “Zan gaisheta in shaa Allah.”
    “Godiya nake barin koma yamma nayi” hannu ya zira a aljihu ya zaro envelope daya tanadar da 20k aciki ya mik’awa Papi akan a sai wa Amal abinda take buk’ata sede sam Papi yak’i amsa daga k’arshe ajiyewa kawai yayi ya mar sallama ya fice. Mik’ewa Papi yayi ya d’au kud’in dan kai wa Amal a d’aki dukda cewan yasan bacci takeyi.  Bud’e k’ofan da yayi ya tarar da ita tsaye dai-dai wajen ta jik’e jak’ab da hawaye. Salati yasa ba shiri bade taji dukkan abubuwan da suka tattauna akai ba? Bade taji labarin asalinta ba?
STORY CONTINUES BELOW
  “Baby?” Ya kirata cikin mucacciyar murya, d’ago kan da tayi zata kallesa kawai ta zame k’asa a sume.
  “Baby?” Kumatun ta ya shiga tapping amma ba response. “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Jameelah! Jameelah! D’au waya ki kira Afzal beyi nisa ba Baby ta sume.”
  Da gudu Mami ta fito ta fad’a d’akin Amal inda tasa ihu had’e da k’arasawa da salati “Abba meya faru? Na shiga uku!”
   “Ki d’au waya ki kira Afzal” da hanzari ta d’auko wayanta ta sanar da Afzal halin da ake ciki akan ya juyo, yana isowa ya d’au Amal ya kaita mota inda Papi ya zauna a gidan gaba Mami kuma a baya tana rik’e da Amal. Emergency ward akayi da Amal lokacin da suka isa asibitin.
  Cikinsu duka uku ba wanda ya iya ya zauna se safa da marwah sukeyi a waiting room d’in, Mami se kuka. “Abba meya sameta?” Ta tambayi Papi.
  “Ban sani ba Jameelah tsoro na d’aya Allah yasa bata jiyo abinda muka tauna akai ba, ina zaton taji komai saboda tsaye a bakin k’ofan d’akinta na tarar da ita tana kuka lokacin da na bud’e k’ofar.”
   “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” Mami tasa salati “Yau na shiga uku Abba ya zanyi dan Allah? Mey zancewa Baby yanzu? Shikenan abinda nake gudu ya faru.”
  “Ya isa haka Jameela ki kwantar da hankalinki in shaa Allahu Baby zatayi miki kyakkyawan fahimta.”
  Bada dad’ewa ba likitocin da suka duba Amal suka fito nan su Papi suka duk’ufa suna tambayansu ya jikin nata.
  “In shaa Allahu ba wani abu serious bane kawai a bisa fad’in da tayin ne ta kusan fama ciwon nata amma Alhamdulillah achan Allah ya tsayar babu internal bleeding ba komai, ta ma riga ta farfad’o kuna iya shiga ganinta.” Hamdala dukansu uku suka sauk’e a wajen sannan suka duk’ufa cikin d’akin, Amal na ganinsu ta shiga zubar da hawaye.
  Hak’uri Papi ya shiga bata Mami kam banda hawayen da take zubarwa ta kasa yin komai.
  “Kukan ya isa haka Mamana ko ta halal aka sameki ko kuwa ta haram kaf nan bamu damu da hakan ba saboda ba abinda ya isa ya canza matsayin ki a idanun mu da kuma yadda muke sonki a zuk’atan mu Baby, kece Amal nan da muka sani muke kuma so har yanzu.”
  “No Papi” ta amsasa tana kad’a kai “Bakuwa sona idan da har kuna sona da bazaku min k’aryan asali na ba har na tsawon shekara ashirin da d’aya, I can’t believe you and Mami could do this to me.”
  “Baby dan Allah kar kiyi haka sanin kanki ne ni da Maminki ba wanda muke so sama dake.”
  “That’s not true Papi how could you do this to me? Har ku sanar da Yaya asalina amma ni ku hanani sanin gaskiya? No one deserves to know the truth above of me no one Papi” ta sanar da shi had’e da rushewa da wani kukan.
  “Baby dan Allah kiyi hak’uri” Mami tasa baki “Wallahi ni da Papinki mun so sanar dake gaskiya lokacin aurenki amma Afzal ya hana saboda baya son hakan ya jefa ki cikin wani hali.”
Mamaki sosai kalamun Mami suka sanya Amal, har Afzal ne yace kar a sanar da ita gaskiya kuma akan wannan dalili? Wow! She’s speechless ita kanta tasan batada masoyi sama da shi bayan su Mami shiyasa har yau ta ke mamakin kanta na kasa yafe masa kuskuren da yayi mata. Kai ta d’ago a hankali ta sauk’e idanunta akansa murmushi ya sakar mata kafin tayi sauri ta kawar da kanta.
“Meya faru Mami? For all my life you made me believed inada Abba akan cewa mutuwa ce tayi mana yankan k’auna ashe ba haka bane, ko a mafarki aka cemun keda Papi zaku yi mun k’arya haka bazan ta6a yarda ba, why do you have to lie to me Papi? Why Mami?” Kuka take sosai duk ta basu tausayi a wajen.
“Baby kiyi hak’uri” Papi yace da ita “Bawai mun 6oye miki gaskiya bane don son kai kokuwa makamancin haka munyi hakan ne saboda muna sonki.”
“Papi ba haka so yake ba, idan da har kuna so na bazaku ta6a 6oye mun wannan muhimmiyar maganar ba.”
“Ya isa kukan haka Mamana ya isa dan Allah karki k’ara wani ciwon ma kanki.” Kewayowa tayi kan Mami. “What happened Mami? Meya faru? Na tabbata bazaki cuceni haka kawai ba seda k’wak’k’warar dalili, na tabbata koma waye ne mahaifin nawa shi ya cuceki.”
“Tabbas ‘yata, sanin kanki ne ba wanda nake so sama da ke a fad’in duniyan nan kuma idan da har Allah na shawara da bawa kafin ya k’addaro masa da k’addara da na hana afkuwan wannan mumunar k’addara, kin fi kowa sanin bazan ta6a sha’awar kawo ki duniyan nan ba uba ba Baby ko dan nayi miki tsari daga tokarin ‘yan unguwa da kuma yara ‘yan uwanki. Sai dai kaman yadda Allah ya fad’a a Qur’ani _fa inna ma’al usri yusrah_ kowani wuya da musiba na tattare da sauk’i. Acikin ikonsa da sassauci se ya kawo mun sauk’i ta hanyan bani uba mey tausayi kaman Papinki, ubanda ze iya sadaukar da rayuwansa dan farin cikin ‘yarsa, uban da yayi playing role na mahaifinki a rashin asalin mahaifinki Baby, ba abinda zance da Papinki sede Allah ya sak’a masa da mafificin alkhairi ya basa gidan Aljannah. Tabbas k’addarata mumunar k’addara ce wanda bazan yi fatan irinsa wa mutum ba koda kuwa mutumin ya kasance mak’iyi na” ta tsaya ta numfasa nan Afzal ya mik’e “I’m sorry let me excuse you” yace dasu duka.
“A’a Afzal” Mami tayi saurin tsayar da shi “Ka riga ka zamo na gida tamkar d’an cikina kuma nakeji da kai, kaman yadda Baby zata ji wannan labari kai ma zanso ka zauna kaji komai” ta buk’acesa sede du da hakan Afzal beji ya cigaba da zama a d’akin ba gani yake kaman ya musu invading privacy.
“Karka ji komai Baba na ka zauna” Papi ya jaddada masa lokacinda k’wayan idonsu ya had’e numfasa yayi sannan ya dawo ya zauna inda Mami ta fara daga inda ta tsaya…
_Labari na ya fara ne lokacinda na had’u da Abdallah wanda ake kira da Khaleefah, lokacin ina matakin form 5 (ss2) da karatu a Government Girls College dake garin Askira inda muke da zama a da kafin muka dawo nan. Umma (mahaifiyata) ta kasance mey buri akaina kasancewar ni kad’ai Allah ya azurta ta da, tunda ta haifeni har ta koma ga mahaliccinta ko 6atan wata bata sake ba. A dalilin haka ta d’au burin duniya ta sauk’e akai na, na cewa se mey kud’i ko d’an wane zan aura. Lokacin da samari suka fara lek’o kai suna nemana se Umma ta hanani kula kowanne daga cikinsu acewarta se mey kud’i. Duk yadda Abba yaso ya ganar da ita cewan shi fa miji na gari ake nema ba se mey d’ankaren kud’i kaman yadda take buri ba hakan ya gagara, acewarta taya ‘yar shuwa kaman ni zan fara auren d’an talaka. Dan inyi ladabi a gareta se na hak’ura ban kula kowa duk wanda yazo guna da sunan zance se in ce masa ni an riga anyi mun miji ana cikin haka ne na had’u da Khaleefah watarana a hanyana na dawowa daga Islamiyya. Acikin duk manema na ba wanda ya ta6amun ya kuma burgeni ya kwanta mun a rai kaman Khaleefah, duk yadda naso sharesa lokacin da ya fara mun magana hakan ya gagara kawai na tsinci kaina ina mishi fara’a, har gida ya rakani ranan na basa lamba na a karo na farko da ya tambaya. Khaleefah saurayi ne kyakkyawa san kowa k’in wanda ya rasa, lokacin da muka had’u yana matakin part 2 ne a karatu a wata jami’a a chan k’asar waje inda ya samu scholarship. Khaleefah ba d’an babban gida bane amma saurayi ne mey zafin nema saboda tun a lokacin yana d’an sana’a haka, kafin ya koma makaranta soyayya me k’arfi ya shiga tsakanin mu amma ban ta6a nunawa Umma ba sanin bazata ta6a amincewa dashi ba. Ko da yazo ya koma makaranta hakan bey hana mu cigaba da gudanar da soyayyar mu ba, ze kirani mu wuni muna waya nima ranan da nasamu kud’i kuma nakan sa kati in kirasa muyi hira. Ana cikin haka ne d’an Alhj Iro Chairman na Askira ranan da suka zo makarantar mu kawo ziyara ya ganni yace yana sona ni kuwa ban basa fuska ba nace masa ina da wanda nakeso dukda haka be saurareni ba seda yazo har gida ya samu Abba ya sanar da shi k’udirinsa akaina da kuma abinda na fad’a masa na cewa ina da tsayayye. Umma naji ta hau ni da surutu akan bata yarda in kula kowa ba se Faisal d’an Alhj Iro. Niko a lokacin ba wanda na tsana kamansa, daren ranan na kira Khaleefah na irga mai halin da ake ciki inda ya rok’eni da in kwantar da hankalina idan ya dawo next hutu zeyi ma Abbansa magana ya turo magabatansa. Na sosai na tsaya da addu’a dan kar Faisal yayi gaggawan turo magabatansa cikin ikon Allah se har wani hutun ya sake zagayowa Faisal be turo ba. Lokacin ina matakin ss3 da karatu har mun soma rubuta WAEC._
   _RANA D’AYA ina cikin waya da Khaleefah Umma ta jiyoni, fisge wayan tayi ta jawoni tsakar gida tun daga d’aki sannan ta shiga duka na tana huci._
  _”Ban ce ba ruwanki da wani d’a na miji a gidan nan ba se Faisal?”_+
  _”Umma dan Allah kiyi hak’uri” na shiga bata hak’uri cikin tsananin kuka._
  _”Rufa mun baki maras kunya kawai ce miki akayi ban san mey nake bane da nace se Faisal zaki aura? Ana neman miki sauk’i da jin dad’i anan gaba kina shashashanci.”_
  _”Umma dan Allah kiyi hak’uri wallahi bana son Ya Faisal ni Ya Khaleefah nakeso.”_
   _Zazzafan mari ta sauk’e mun a fuska. “Ina fad’a kina fad’a? Mey za’ayi da talaka da talauci idan ba Allah ya d’aura ma mutum ba? In ba rashin wayo irin naki ba ma taya a matsayin ki na ‘yar shuwa zaki hau auran talaka? Kin ci sa’a har d’an chairman yace yana sonki amma kike sokancin nan? Naira na kiranki kina cewa baki so? Jakar ina ce ke? Wallahi idan har kinga kin auri Khaleefah yake kowa toh a bayan raina ne. Ma tukun waye shi? D’an gidan waye ne?”_
  _”Umma kiyi hak’uri.”_
  _”Tambaya nake miki waye shi nace?”_
  _”D’an gidan Malam Ilu ne.”_
  _”Wani Malam Ilu? Na bakin titi?”_
  _”Eh shi.”_
  _Wallahi ban ta6a sanin bakida wayau ba se yau, ashe rashin wayon naki ya kai matakin da har zakiyi sha’awan aure a wancan matsiyacin gidan.”_
STORY CONTINUES BELOW
  _”Amma Umma ai nagari ake nema ko musuluni bece se mai kud’in bala’i ba bale ma fa yana karatu bazamu rasa na rufin asiri ba.”_
  _”Uwarki da karatun da kuma rufin asirin nace, chin kwalin degree d’in zakiyi kokuwa, kuma ni zaki gaya ma musulunci? Toh naji musulunci bece se me kud’i ba amma ai al’adar ki bata amince ki auri talaka ba.”_
  _”Umma amma-“_
  _”Dakata idan kuma kina ganin ya akayi na auri Abbanki kike bayan bayida komai kisani Abban ki d’an uwa na ne, auran had’i akayi mana kuma nima muddin zaki amince ki auri wani nawa koda baida kud’i zan amince miki amma muddin bare zaki aura toh wallahi se mey na hannu kiji ki sani.”_
  _”Umma bana son Ya Faisal dan haka bazan aureshi ba” na sanar da ita cikin 6acin rai. Amsana ba k’aramin tunzirata yayi ba, kafin in hankara kawai naji ta rufe ni da d’an banzan duka ana cikin haka ne Abba ya dawo daga kasuwa ya kar6eni. “Haba Awatif! Meyayi zafi haka zakisa yarinya a gaba kina dukanta kaman ganga? Meya faru?”_
  _”Yo ba gara gangan ba dama an san ba mutum neba bale yayi wayo, kuma ba ruwanka Malam wannan tsakani na da ‘yata ne ehe! Bana son shisshigi.”_
  _”Shisshigi fa kikace? Ni da ‘yata kice shisshigi?”_
  _”Eh shisshigi ne mana kana na miji ina ruwanka da harkan daya shafemu.” Abba be sake kulata ba ya juyo a gareni “Yayata ta kaina yi hak’uri” ya shiga bani hak’uri “Mey ya faru?” Bayanin komai na mishi Umma na tsaye tana hararata cike da takaici._
  _”Haba Awatif! A ina akace se mey kud’i za’a aura? Tunda yarinyan nan tana son yaron nan kuma yana da shirin turo magabatansa me zey hana muyi mata abinda takeso?”_
  _”Aww biye mata zakayi kai ma? Toh wallahi kunyi k’arya dukanku ‘yar nan bazata auri matsiyaci ba se Faisal mu zuba daku mu gani” tana kaiwa nan ta janye hijabin ta daga kan igiya ta fice. Kuka na cigaba da yi a wajen Abba yana ban hak’uri._
  _”Abba dan Allah ka bawa Umma hak’uri Abba bana son Ya Faisal bana sonsa.”_
  _”Yi hak’uri Jameelah zanyi mata magana in shaa Allahu zata sauk’o kinji? Kukan ya isa haka.”_
  _Haka nan Umma ta k’wace mun waya ta hanani waya da Khaleefah ko fita ta hanani in ba Islamiya ko boko ba kullum ina rufe kup a gida gashi duk yadda Abba ya so fahimtar da ita gaskiya hakan ya gagara saboda Umma ta kasance mace mey zafi ko Abba wani sa’in tana fin k’arfinsa daga k’arshe Abba yace sede in hak’ura inyi yadda takeso saboda yayi-yayi ya ganar da ita gaskiya amma tak’i fahimta niko nak’i amincewa da hakan, ranan paper’n mu na k’arshe bayan mun gama naje na samu Khaleefah na sanar da shi cewa Faisal ya kusa turo magabatansa da yayi ma iyayensa magana su riga sa turowa idan har akayi haka toh dole Umma ta yarda amma sai dai shima koda ya kai maganan gida iyayensa suka k’i amince mai acewansu ya bari seya gama makaranta tukun. Na sosai na shiga wani irin yanayi bani da wata sana’ar data fiye na kuka acikin gida. Ba waya gashi ko fita Umma bata bari na inyi kusan sati biyu kenan banji daga Khaleefah ba rana d’aya kwatsam kawai mukaji ana sallama, amsawan da Umma tayi sega Khaleefah. Da fari da bata gane waye shi ba ta kar6esa da fara’a ta k’arisa dashi ciki bayan ya zauna yayi mata bayanin kansa ya fayyace mata k’udurinsa akaina Umma ta ci mai mutunci tayi mai koran akuya a idona ta kuma nuna masa ni Faisal zan aura. Ranan na kasa bacci dole washegari da yamma na saci idonta naje duban Khaleefah. Wannan yini shine mafi munin yini a rayuwa na, ban ta6a tsammanin Khaleefah ze iya mun abinda ya mun ba, ashe abinda Umma tayi masa ya mugun ci masa rai dan haka yayi tunanin k’untata mata ta hanyan 6ata mun rayuwa, yana ganin idan ya cuceni kaman ya cuceta ne, a tunaninsa Umma na sona d’inda har idan abu ya shafeni zata shiga damuwa saidai ba haka bane. A yinin ranan ne Khaleefah ya mun fyad’e ba irin rok’o da hak’urin da ban basa ba amma haka seda ya aikata abinda yayi niyya ba ko d’igon imani tattare da shi had’e da taimakon abokansa k’waya biyu. Bayan faruwan abun ban sake sanin inda nake ba se bayan kwana biyu dana farka na tsinci kaina a gadon asibiti. Abba na fara tararwa nan take na shiga zubda hawaye yana bani hak’uri shigowan Umma ta shiga zagina na tana kira na da ‘yar iska. Duk yadda Abba da likita suka so ganar da ita fiyad’e akayi mun tak’i amince tana ganin gaskiya amma ta take. Ba irin sunan da bata kirani da shi ba harda ja min Allah ya isa. Har aka sallameni daga asibitin kuma bata sake koda lek’oni ba, Abba ne ya zauna akaina har aka sallameni. Ranan da muka dawo gida Abba ya shirya zuwa tinkarar iyayen Khaleefah akan abinda d’ansu ya mun dan k’watan mun hak’k’i amma haka mahaifin Khaleefah ya bushe ido yace sam shi d’ansa be aikata wannan mumunan abu ba sharri kawai ake son yi masa. Shima Khaleefah koda aka kaimu gaban mey unguwa rantsuwa ya ringa yi shi ba abinda ya ta6a had’amu ko sani na ma beyi ba haka muna ji muna gani aka tauye mana hak’k’i. Faisal kuwa tun da yaji wannan magana ya d’auke k’afa daga gidan mu hakan yasa Umma ta sake tsanata, dama chan nasan ba sona yake har zuci ba, kyau da jiki na kawai yake bi. Bayan wata biyu da faruwan abun ne kwatsam rana d’aya na tashi da zazza6i da amai. Ko kallon kirki Umma batayi mun ba, ina cikin aiki a kitchen da rana kawai amai yabi kaina na fito na shiga kwararowa a tsakar gida ana cikin haka Umma ta dawo gida daga unguwa, salati ta shiga yi tana tafe hannu amma ko agaji bata taimaka mun da ba seda na gama na kishingid’a jikin bango sannan ta tako ta shiga dubata._
   _”Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Ciki! Wayyo jama’a! Shikenan tayi cikin shege” ihu ta shiga yi tana kururuwa seda ta tara mana jama’a a gidan kafin ace mey magana ya zagaye gari akan cewa ‘yar Malam Muhammad tayi ciki alokacin kuwa har Khaleefah ya koma makaranta, koda nazo na samu waya na kirasa layin nasa bai shiga ba shakka ya canza. Tun daga ranan da aka tabbata ina da ciki Umma ta sauya mun a gidan tokari na safe daban na yamma daban tamkar ba ‘yar da ta tsuguna ta haifa ba haka ta tsaneni take kuma gaba dani. Sau dayawa nakan zauna in sha kuka ina kokonton anya kuwa Umma ce asalin mahaifiyata? Se daga baya Abba yake sanar dani dalilin daya sa ta tsane ni. Tun farko bata so ayi mun takwaran Baaba Jameela ba yar Abba wacce jininsu sam be had’u ba, sam babu jituwa a tsakaninsu tun ma kafin ta auri Abba, bayan auran nasu kuma se abun ya sake lalacewa tamkar annabi da kafiri haka suke ji da juna, toh tunda aka samun sunan Baaba Jameela Umma ta tsaneni. Shima Abba bawai yaso yasa sunan bane sedon mahaifiyarsa da dama akayi niyan yi mata takwaran tace ta yafe ayiwa Baaba Jameela kasancewar tunda tayi auri sama da shekara ashirin ko 6atan wata bata ta6a ba, dalilin da yasa aka sa min sunanta kenan._
STORY CONTINUES BELOW
   _Ba yadda banyi da Abba ba da ya barni in zubar da cikin amma yak’i acewansa yin hakan haramun ne bayan nan kuma nima ina iya rasa raina ta dalilin hakan. Ko fita ban isa inyi ba haka ina ji ina gani na daina zuwa islamiyya bayan nayi nisa sosai a karatun, shima Abba kaman wasa duk inda yaje se an ringa binsa da kallo ana nuna sa da yatsa, harta kasuwa gun aikinsa. Umma ce kad’ai ke fita freely ta dawo gida bawani fargaba ko tashin hankali saboda ko zagi na ake seta tsaya ta sa baki ayi da ita. K’arshe de haka zaman garin Askira ya gagaremu amma Umma ko a bakin zaninta hasali itama ke yad’a wa mutane nayi cikin shege. Alokacin da Abba ya gir6e gonansa lokacin cikina na wata hud’u ya kawo shawaran mubar garin Askira idan ba haka ba ko nazo na haife cikin nawa ba bar min d’an za’ayi ba shi kuma abinda yake gudu kenan, baya son laifin Khaleefah ya shafeki Baby._
  _Koda Abba ya sanar da Umma cewa zamu bar Askira ita tace ba inda zata tunda ba ita ta turani inyi abun kunya ba. Ganin Abba dagaske yake ko ba ita shi zeyi tafiyarsa yasa ta amince ta biyo mu. Gidan mu da komai da muka mallaka Abba ya siyar muka dawo nan Maiduguri bada sanin kowa ba dan ko Umma ma Abba be sanar da ita inda zamu ba kawai ganin kanta tayi anan cikin garin Maiduguri. Mun dawo bada dad’ewa Umma ta kamu da ciwon nono wato breast cancer, ina da shekara sha tara na haifeki Baby, bamu ta6a neman abu gun Abbanki mun rasa ba, komi yi mana yake, damuwa na tun kafin in furta yake yaye mun. Tamkar ‘yar cikinsa haka ya d’aukeki yake kula da ke. Kina da shekara biyu mutuwa yayi halinsa ya tafi da Umma sede har ta mutu bata ta6a rik’eki a hannu ba. Tsanan duniya gabad’aya ta d’au ta aza mana ni da ke ko kallon arziki ban ta6a ganin tayi miki ba, batun Khaleefah kuwa har yau ban sake ji daga garesa ba. Sau dayawa manyan ‘yan kasuwa masu aure harma da samari su kan nuna suna son su aureni amma tun kan abinda Khaleefah ya mun naji na tsani na miji a rayuwata shiyasa kika ga har yau ban sake yin aure ba, dan kuma gudun kar wataran yaran dana haifa su nuna miki banbancin ‘yan uba, bana son abunda ze ta6a farin cikinki Baby, bana so”_ ta k’are cikin tsananin kuka.
    Kuka sosai Amal take itama, Afzal ma na sosai jikinsa yayi sanyi yana mamakin rashin imani irin na Umma marigayiya da kuma wannan Khaleefah mahaifin Amal.
  “Baby kiyi hak’uri na 6oye miki wannan sirri da nida Papinki mukayi dan Allah kiyi hak’uri.”
  “Kibar bani hak’uri Mami, ni ya kamata inyi hakan na rashin fahimtar ku da banyi ba keda Papi please forgive me.” A hankali Mami ta rungumeta yayinda suka cigaba da kuka shima Afzal seda k’walla ya ciki masa a ido dan tausayi. Be dad’e ba aka sallamesu Afzal ya dawo da su gida chan dare da Mami tashigo kawo wa Amal abinci Amal ta tsayar da ita.
  “Mami alfarma nake nema.”
“Fad’i ko mey kikeso Baby.”
  “Mami ku raba aure na da Yaya.”
  “Subhanallahi meya faru Baby? Wani abun ya sake miki ne?”
  “Mami sanin kanku ne kun cuci yaya tun farko da kuka san asali na be kamata ku had’a mu aure ba.”
  “Baby wani irin magana kuma kike? Ya kike magana sekace mun zalunce shi? An fa fad’a mishi gaskiya kuma a hakan yace yana sonki Abbanshi ma na wajen.”
  “Kina nufin Abba ma yasan asalina?” Kai Mami ta gyad’a mata a hankali.
  “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un” ta furta cike da tashin hankali yayin da hawaye ya shiga ciko mata a ido. “Bayan su se suwa kuka sake sanar dasu asalina?”
  “Wallahi babu Baby daga su shikenan.”
  “Nide na fad’a muki kuyi ma Yaya magana kawai ya bani takarda na bazan iya cigaba da zama da shi ba, zaluncin ya isa haka.”
  “Baby dan Allah kibar magana haka, ya kike magana sekace laifinki ne kika kasance haka? Karfa ki manta wannan k’addararki ce haka Allah yaso ya ganki kuma ba wai yayi hakan dan baya sonki bane se don ya gwada k’arfin imanin ki.”
STORY CONTINUES BELOW
  “Na sani Mami shiyasa nake son Yaya ya sauwak’e mun, Yaya be kamanci shegiya kaman ni a matsayin matarsa ba-“
  “Baby dan Allah kibar magana haka ki daina kwatanta kanki da wannan mumunar kalma” Mami tayi saurin katse ta yayinda ta saki murmushin takaici “Akwai k’arya ne acikin hakan Mami? Ko ba shegiyar bace ni?” A hankali Mami ta jata jikinta “Dan Allah ki bar fad’in haka, Baby tunda muna sonki mijin ki na sonki mey kuma kike nema? Wannan abu ya riga ya faru ba abinda zamu iyayi mu canza ko a tunaninki ni d’in dad’i nakeji na cewa bakida uba? Wallahi Baby na fiki takaici da zafin hakan shiyasa ni da Papinki muka d’au burin baki tarbiyya da ilimin boko da na islamiyya duka dan ki banbanta daga sauran ‘yan matan da suka tsinci kansu acikin hali irin naki masu yawo akan layi suna barikanci saboda ganin da suke ba ta hanya madaidaiciya aka same su ba, Baby idan ba wai fad’a akayi ba bawanda ze miki kallon shegiya dan Allah ki daina fad’in haka” cikin kuka ta d’ago kanta daga jikin Mami tana share hawayenta “Godiya nake da ilimi da tarbiyyan da kuka bani Mami amma ban cancani miji kaman Yaya ba da yake da asali da mutunci da ma komai ba bayan ni inada akasin hakan, dan Allah ku mishi magana ku kuma basa hak’uri na zaman da mukayi tare.”
  “Baby cikinsa da kike d’auke da shi fa? Ya zakiyi da shi? So kike ki haifi d’an shima ba uba?”
  “Sam Mami amma k’addara tariga fata cikin nan kuma zan raineshi, yadda Papi ya tayaki rainon cikina na tabbata ze tayani rainon wannan har zuwa lokacinda zan haifa in mayar masa da d’ansa.”
  “Kekuma fa Baby? Haka kikeson ki k’arisa rayuwarki cikin k’unci da takaici ba miji kaman ni?”
  “Ya fiye akan in zauna da wanda nake ganin kaman ina cutansa ne Mami, wallahi gani nake Allah ma baze yafe mun ba.”
  “Subhanallahi bayan shi yace kar a fad’a miki gaskiyan al’amarin ko bayan da yaji komai? Da ace mune muka 6oye mai gaskiya da seya zama yadda kike fad’an amma fa da saninsa da kuma amincewansa kafin aka d’aura muku aure.”
  “It still doesn’t matter Mami, Yaya deserves someone much better than me, he’s way out of my league bazan iya cigaba da zaluntarsa ba.” Duk yadda Mami taso fahimtar da Amal gaskiya hakan ya gagara ita sam hankalinta yak’i d’aukan maganar ita kawai Afzal ya sallameta, game da soyayyar da takeyi masa kuwa zata rok’i Alah ya cire mata shi daga zuciyarta du da cewan tasan hakan ba k’aramin abu bane. Da k’yar Mami tasamu kukan nata ya lafa ta sata taci abinci ta sha magunanta sannan tayi mata sallama ta janye k’ofar taje ta samu Papi take irga mai yadda su kayi da ita. Na matuk’a Papi ya tausaya wa Amal dama ranan da ya jina yana gudu kenan, ranan da zata gano gaskiya ta tsani kanta.
  Tana mik’e akan gado tana kukan zuci wayanta dake kanta ya shiga ruri dubawan da za tayi taga Afzal ke kiranta ba shiri ta 6arke da kuka. Tunda take a rayuwarta bata ta6a tsanar kanta da kuma k’yamar kanta ba kaman yanzu, gabad’aya ji tayi batada mutunci bata da daraja, bata jin zata sake iya sa Afzal ko Abbansa a ido waya sani ma ko sun sanar da Ummi hala itama Ummin ta sanar da Nazeefah. Amma ko idan da har Nazeefah tasan asalinta ta tabbata da ta yi mata gori da shi. Shin meyasa Afzal be bari an fad’a mata gaskiya ba? Ai idan da ta san gaskiyan al’amarin tun fari da bazata soma auren sa ba ma. Haka tana gani wayan ya tsinke bata d’aga ba har a karo na biyu ma k’arshe kawai seya tura mata sak’o. Sa6anin yadda ta saba goge sak’onninsa anytime ya tura mata yau se tayi tunanin ta bud’e inda ta fara karancewa kaman haka;
   _My Adorable Kitten please don’t let what you found out earlier ruin you, you’re still the beautiful, charming, elegant, intelligent, clever, and amazing Amal that I know, my wife and mother to my unborn kids. I love you regardless have a peaceful night rest, I’m missing you and our little one down here. Xx_ 😘
STORY CONTINUES BELOW
   Tana gama karancewa ta shiga wani sabon kukan haka ta kwana tana yi se kusan Asuba bacci mey nauyi ya d’auketa. Wajajen goma ta tashi bayan tayi wanka Mami ta kawo mata breakafst nata taci sannan Papi yayi sallama cikin d’akin nata. Zama yayi ya mata nasiha sosai amma inaaa Amal ta riga tayi making up mind nata ita sam bazata komawa Afzal ba. Daga k’arshe Afzal d’in Papi ya kira ya sanar da shi halin da ake ciki yana tashi daga office ya biya gidan nasu. Ba yadda Papi beyi da Amal ba da ta fito daga d’akinta Afzal yazo wajenta amma tak’i ta rufe kanta a d’aki se kuka take. Na sosai zuciyan Afzal yake k’una gabad’aya ya rasa ina zesa kansa. Kwana uku ya jera yana zuwa duban Amal amma ko yaje baya samun su had’u gashi koya kirata bata d’agawa, messages nasa ma bata replying tamkar sabon mahaukaci haka Afzal ya koma. Su Papi ma sunyi mata magana har sun gaji amma tace sam bazata cigaba da zama da Afzal ba tana cutansa, acewarta zalunci ne ace yadda yake d’an halak ita ko ga ta inda aka sameta ace sunyi aure. Tun sha biyu ya baro office yau yaje ya samu Ummi a gida kallo d’aya tayi masa ta gano yana cikin matsala.
   “Meya faru kuma Prince? Amal d’ince har yanzu bata sauk’o ba?”
  “Ummi things just got worse.”
“Subhanallahi kamar ya?”
  “Ummi kiyi hak’uri na 6oye miki wannan sirri da nayi nasani ko ba dad’ewa da jimawa gaskiya ze fito shiyasa nake son sanar dake yanzu.”
  “Speak up already meya faru?”
  “Ummi gab lokacin da na kusan auren Amal iyayenta suka bayyana mun da Abba wani 6oyayyan al’amari wanda na buk’aci Abba da kar ya sanar dake bawai dan ban yarda dake bane se don ina gudun kar hakan ya canza miki ra’ayi akan Amal.”
   “Ina jinka.”
  “Ummi Amal batada asali.”
  “Asali kaman ya kenan?”
“Amal ba ta halatacciyar hanya aka same ta ba.”
  “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un kana nufin Amal shegiya ce?”
  “I’m sorry but yes.”
  “Kuma ka aureta Afzal? Baka da hankali ne?”
  “Ummi ki tsaya ki saurareni mana bawai abinda kike tsammani bane, k’addarar fyad’e ne ya fad’o akan mahaifiyarta.”
  “Haka suka ce maka? Kuma ka yarda?”
  “Yes Ummi saboda ba k’arya sukeyi ba idan da har k’arya ne da bazamu ta6a jin sirrin nan daga bakinsu ba amma fa Papi da kansa ya sanar da ni da Abba.”
  “Toh ai wayo suka maku saboda sun san ba a iya 6oye abin kunya ne.”
  “Ummi kibar cewa haka, just calm down and listen to me ita kanta Amal bata ta6a sanin gaskiyan ba se last week.”
  “Ita Amal d’in?”
  “Yes nida Abba suka fara fad’awa akan daga nan se su sanar da ita amma na buk’aci da a cigaba da 6oye mata gaskiyan saboda nasan halinta muddin har ta gano gaskiya toh zata iya k’in amincewa ta aureni gashi yanzu ta gaano gaskiya tace ita sena sauwak’e mata tana cewa she don’t deserve to be with me I deserve someone better.”
  “Ita Amal d’in? Ya akayi ta gane gaskiyan yanzu?”
  “Shine ai nake kaiki, ranan da naje gidansu muke sulhu ne taji komai” labarin duk yadda sukayi ya kwashe ya bata, Ummi can’t help but to remain shocked. Tausayin Amal ne ya kamata na matuk’a.
STORY CONTINUES BELOW
  “Toh yanzu ya kenan? Zaku rabun?”
  “Kema kinsan bazan iya rabuwa da Amal ba Ummi.”
  “Toh ya zakayi Afzal tunda iyayenta ma sunyi su ganar da ita sun gagara.”
  “Even stil Ummi I’ll continue to try my best.”
  “Ko kana so inyi mata magana?”
  “Nooo bana son tasan kin sani.”
  “Toh Allah baka ikon shawo kanta wallahi tabani tausayi matuk’a yarinya ga haddan Al~Qur’ani.”
  “Ummi bakiga yadda take kuka ba ranan da gaskiyan ya fito.”
  “Allah sarki Amal ‘yar nan jarabawanta a duniya dayawa suke Allah de bata ikon cinyesu.”
  “Ameen Ummi.”
  “Ya batun Nazeefah fah? D’azu Mummy’nta ta kirani muka gaisa when do you plan on bringing her back?”
  “Ummi muddin Amal bata dawo mun ba bazan iya dawo da Nazeefah ba.”
  “Zata dawo in shaa Allah Prince zan tayaka da addu’a.”
  “Thank you Ummi barin wuce gida in huta idan Abba ya dawo ki gaishesa.”
  “Bazaka jira lunch ba sauran kad’an fa.”
  “I’m not hungry Ummi thank you.” Rakasa tayi har gun mota sannan ta dawo ciki.
   Afzal be fasa zuwa duban Amal ba a rana na shida ne da yaje ya tarar da Mami kad’ai itama tana shirin fita, tana gama cin abinci ta basa hak’uri kan zata shiga nan mak’ota yin barka akan ya jira Papi shi ma ya kusa dawowa.
  “Ayya ba komai Mami sekin dawo zan jirasa.”
  “Yauwa toh barin wuce.” Bayan ta fice ya mik’e had’e da zaro wayansa daga aljihu sannan ya taka har izuwa bakin k’ofan d’akin Amal dai-dai gun ya tsaya ya shiga buga layin nata sede yana ji daga ciki yana ringing amma bata d’agawa.
  A hankali ya gwada bud’e k’ofan sa6anin kullum ya tarar da k’ofar a bud’e da mamaki ya bud’e mik’e akan katifarta tana bacci ya tarar da ita a tunaninsa gabad’aya tana ganin call d’inne kawai tak’i d’agawa ashe bacci take even though yasan koda idonta biyu ma ba d’agawa zatayi ba. Cikin d’akin ya k’arisa ya tsuguna a gefenta. A hankali ya aza hannunsa akan cikinta yana shafawa a hankula.
  “Kitten?” Ya kirata da k’aramin murya. “Kitten wake up it’s me Afzal” ya sanar da ita kaman a mafarki take jin sautin muryansa, a hankali ta shiga bud’e idonta har ta sauk’esu akansa ba k’aramin razana tayi ba ganinsa da tayi akanta kad’an ya rage bata sa ihu ba.
  “Shhhhh it’s just me calm down” ya buk’aceta. Kanta ta kawar ba tare da tace da shi komai ba.
  “Amal?” Ya kirata nan ma bata juya ba a hankali ya kewayo da fuskarta. “Babe please come back to me, dan Allah kiyi hak’uri mu koma gida I terribly miss you.” Shiru ta mai ba tare da tace komai ba hakan yasa ya cigaba.
  “Amal fushi kike dani har yanzu da bazaki mun magana ba? Please forgive me I’m sorry, I’m terribly sorry.”
  “Why did you do it?” Ta soma da tambayarsa tare da kewayowa.
  “Did what Sweetheart?” Yayi saurin tambayarta.
STORY CONTINUES BELOW
  “Mesa ka hana su Mami sanar dani gaskiya Yaya? Meyasa ka aureni bayan kasan yin hakan kaman ka zalunci kanka ne, sanin kanka ne iri na da bamuda asali bamu cancanc-” da sauri ya katseta ta hanyan aza hannunsa kan dry lips nata. “Please not a word Amal, I married you because ba laifinki bane da kika kasance haka, I married you because I love you Amal, I don’t care koba ta halatacciyar hanya aka sameki ba and above all I married you because it’s been destined you’re going to be my wife and the mother to my kids Amal saboda akwai rabo a tsakaninmu” ya k’arashe maganan had’e da aza hannunsa akan cikinta. “Please come back home with me Baby please don’t say no.” By now kuka take sosai “I can’t Yaya, I really can’t” ta sanar dashi cikin tsananin kuka had’e da kawar da kanta.
  “So dagaske ne da Papi yace kince in baki takardanki?” Ya tambayeta cike da k’in yarda. Kai zalla ta gyad’a masa.
  “Lily ya kikeson in rayu in ba ke? Taya kike tsammanin zan iya rayuwa idan ba ke a kusa dani please don’t punish me like this, by Allah my heart can’t take it dan Allah kar kiyi mun haka taya kike tsammanin zan iya rubuta miki takardan saki wallahi koda wuk’a a wuya na bazan iya ba yaushe ne zaki gane cewa kece rayuwa na Amal idan kuma ba ke bazan iya rayuwa ba? When will you realize that?” A hankali ta shiga juyo da kanta tana mey mamakin kalan tashin hankalin daya bayyana a fuskansa tausayinsa kawai taji ya kamata har yanzu ta rasa gane soyayya ne ko kuma wani ciwon yake damun Afzal ace yasan asalinta amma be k’yamace taba bayan ita da kanta k’yamar kanta take.
  “I’m sorry Yaya I’m terribly sorry” ta basa hak’uri hawaye na tsiyaya daga idanunta.
  “I don’t want you to be Amal just come back to me please ko ba dan ni ba dan wannan” ya fad’a yana sake mayar da hannunsa kan cikinta. Hannunsa tabi ta aza nata akai “Yaya you don’t deserve me at all, you deserve someone better.”1
  “Dan Allah kibar cewa haka, I deserve no one other than you Amal please come back.” Shiru tayi bata sake ce dashi komai ba.
    “Kinji? Dan Allah kiyi hak’uri kibar cewa in sawwak’e miki.” Kai ta gyad’a mar a hankali. “Kin yarda zaki dawo?” Ya tambayeta eagerly nan ma kai zalla ta gyad’a mishi. Wani irin farin ciki Afzal ya tsinci kansa a ciki, hannunta ya d’aga had’e da placing soft kiss akai “Thank you Amal, thank you so much.”
  “Yaya meyasa kake so na haka?”
  “Kitten ni kaina ban sani ba all I know is my love for yu knew no bounds a jinin jikina yake.”
  “Yaya shin baka k’yamata ne?”
  “Subhanallahi Amal wace irin magana kike haka? Dan Allah kar ki sake cewa haka kinji?” Kai ta gyad’a mishi a hankali “Thank you” mik’awa yayi a hankali yayi kissing kumatunta “In shirya miki kayakin ki mu koma gida yanzu?”
  “A’a Yaya” tayi saurin cewa.
  “But Kitten why? Baki hak’ura ba har yanzu?”
  “Ba haka bane, I was never mad at you I was just angry.”
  “Toh yaya ne?”
  “Yaya ai ni nace zan dawo kar ka damu nafi son in had’a kayakin nawa da kaina.”
  “Toh ai bazaki iya ba hannunki da ciwo har yanzu.”
  “Mami will help me kar ka damu.”
“Har yaushe kenan?”
  “Yaya don’t you trust me?”
  “I do Amal morethan I do trust myself I just can’t wait to see you back home.” Murmushi kad’an ta sakar masa “You should go, Papi ya kusa dawowa kar ya tarar da kai anan.”
STORY CONTINUES BELOW
  “Sure” ya amsa yana duban agogon dake d’aure a tsintsiyar hannun sa. “Kafin nan baki fad’a mun how many months is my baby ba Kitten” Wani kunya taji ya rufeta take ta kawar da kanta wanda hakan ya sanya sa murmushi “Kunya na kikeji Kitten?” Shiru tayi bata ce komai ba “Tell me kinji? In soma counting.”
  “Yaya da saura fah.”
  “Toh how many months ne?”
  “D’aya ne fa kacal” ta sanar da shi cike da kunya.
  “Wow! In conclusion saura mana 8 months kenan we have a long way to go don’t we?”
  “Yaya ka tafi kar Papi yazo ya tarar da kai please.”
  “Kori na kike haka Kitten?”
  “Yaya please.”
  “Ba kiss ba komai kike son in tafi Kitten? Do you know how terribly I miss your sugary lips?” Bata kai ga juya mai baya ba ya rik’o hannunta “I can’t wait to have you back Kitten” ya sanar da ita kafin ya matso kusa da kunnenta “Sena biya bashin duka kwanakin nan da muka d’auka bamu tare” kunya ne ya rufeta gabad’aya kawai ta matse idonta. Murmushi ya sakar sannan yayi pecking nata a kumatu “I’ll call you later I love you” yana kaiwa nan ya ajiye mata envelope daya tanadar mata sannan ya mik’e ya fice ko jiran dawowan Papi beyi ba ya koma gida cike da farin ciki.
  Chan misalin k’arfe tara ya kira ta seda ya kusan tsinkewa ta d’aga.
  “Alhamdulillah I can’t remember when last kika d’au wayana Kitten thank you for picking up.”
  “You’re welcome Yaya.”
  “So how’re you and my baby?”
  “Duka lafiya shine ka ajiye min kud’i d’azu Yaya?”
  “Take care of yourself Kitten I love you.”
  “Thank you” ta amsa tana murmushi.
  “Yaushe zaki dawo toh?”
  “Zan dawo karka damu.”
  “Toh shikenan zanga ko zan iya cigaba da jirarki nayi kewarki Kitten, there’s no one to run to after coming back from home, no one to bath with or sleep together with ni kad’ai na na rage pity me and do come back soon please.”
   “Nazeefah fa?” Kawai ta tsinci kanta da tambayarsa.
“Bata nan.”
  “Tana ina?”
  “Na ce ta tafi gida Kitten muddin baki  dawo ba bazan iya dawo da ita.” Mamaki tasha na sosai amma tayi shiru akanta ya tura Nazeefah gida? Wow!
  “Kitten are you there?”
“Uhmm” tayi mumbling.
  “Kiyi ki dawo kinji? I miss you so much.”
  “Toh mun gaisa I’m sleepy ina son in kwanta.”
  “I can’t ask for more Kitten, kwanta kinji? Sleep like a baby I love you.”
  “You too seda safe” bata jira jin me zece ba ta kashe wayar. Murmushin dake d’auke akan fuskan Afzal ya kasa gushewa he can’t wait to have his Amal back. Be kai ga ajiye wayansa ba sak’on gaisuwan Nazeefah ya shigo na goodnight bayan ya karance yayi replying nata da _Thank you I love you too_ 😘💕
STORY CONTINUES BELOW
   ****
   A kullum jira Afzal yake Amal tace masa ta shirya yazo ya d’auketa sede shiru ko yayi mata maganan kuma setace tana kan shiri ne gabad’aya ya k’osa ta dawo bayan kwana hud’u da yamma yana zaune a parlour yana kallon sports sega call nata yana shigowa hannu na 6ari ya d’aga baze iya tuna yaushe Amal ta d’au waya ta kirasa ba.
  “Halo Kitten?”
  “Yaya kana gida ne?”
  “Yes Kitten.”
  “Zaka iya zuwa ka d’aukeni ko se gobe?”
  “Gobe kuma? I’m on my way right now.” Wurgi da wayan yayi ya mik’e ya sa sabin kaya red buttoned sleeves shirt  me adon bak’i da black trouser sanin yadda Amal ke son red color. Combing gashin kansa yayi sannan yayi wanka da turare ya fad’a bayi ya wanke bakinsa da mouthwash ya fito ya d’au key ya fice. Nan da nan ya isa gidansu Amal yana k’arisawa ciki ya tarar da su zaune a tsakar gida Amal tayi wanka tsaf abinta ba bandeji ko d’aya d’aure a jikinta se yanzu ya gane dalilin da yasa tayita jan dawowa a garesa ashe so take se ciwonta ya warke. Masha Allah.
  Sanye take da pitch hijab mey hula wanda ya mugun mata kyau bayan sun gaisa duka Papi ya yi musu nasiha sosai itama Mami ta d’aura nata akai da kansa ya janye akwatin nata yakai mota ya kuma bud’e mata k’ofar bayan ta shiga ya rufe. Har yanzu da k’ingishi take tafiya a sanadin accident d’in, hannunta ma ba iya aiki take da shi sosai ba kawai de da sauk’i ne. Sallama yayi dasu Papi sannan ya tada motan suka fice se gida. D’agata yayi chak a sama ya kaita har ciki yayinda yasa mey gadi ya shigo da akwatin nata.
  Mamakin yadda ko ina yake tsaf Amal take bayan nan ga k’amshin turaren wuta.
  “Kai ka kunna turare?”
  “Kin tuna lokacinda na tambayeki yadda kikeyi?” Ya tambayeta da murmushi.
  Kai ta gyad’a tana mayar masa da murmushin “I’m impressed.”
   “Let’s go in ki rage kayan jikinki” bata kai ga mik’ewa ba daga kan kujerar daya ajiyetan ya dakatar da ita. “Let me.”
  “Yaya kar ka damu I can manage.”
  “No My lady allow me assist you.”
  “Toh Yaya ai likitan ma kansa cewa yayi ina k’ok’ari ina taka k’afar idan ka cigaba da d’agani ai tsami k’afar zatayi.”
  “Naji amma ki bari na yau” bata sake mai musu ba ya k’arisa ya d’agata suna kai corridor’n d’akin nasu tace “Ka manta chan ne d’akina?” Ta tambayesa da gan-gan tana mai nuni da d’akin data koma bayan daya korata daga d’akin nasu.
  “Kitten da gan-gan kike ko? Ai sede ni in bar miki d’akin ba ke kibar min ba, it was so wrong of me to send you out of your own room forgive me okay?”
  “It’s okay Yaya” ta amsa tana mar murmushi, murmushin ya miyar mata sannan suka k’arisa ciki ya dawo ya ja akwatinta bayan ya sauk’e ta akan gado. Da kansa ya shirya mata kayakin acikin wardrobe nata. Ya so su fita cin abinci bayan sallan Isha amma ganin hakan ze bata wuya funda ga yadda take taka k’afara har yanzu se kawai yayi deciding ya musu girkin da kansa.  Kulleta yayi a d’aki be bud’e ba seda ya gama komai yayi arranging dining sannan ya d’auketa a hannunsa zuwa dining d’in yana bud’e flask d’in Amal taja wani numfashi “Hummm it smells so good.”
  “Wait until it is served” ya amsa cike da jin dad’i. Da kansa yayi serving nata spaghetti d’in, da fari yaso suci a plate d’aya amma tuna condition nata se be sake sha’awan d’agata ba dan kar ya bata wahala. Na sosai Amal taci abincin harda neman k’ari wanda hakan ya mugun yima Afzal dad’i. Wani sabon soyayyarta yaji yana shigansa, tamkar k’wai kuma haka yake jinta baya sake k’aunan abinda ze had’asu har wanda zesa ta sake yimai yaji. Shi kad’ai yasan kalan tashin hankalin da ya shiga a rashinta. Bayan sun gama yatattare wajen dukda cewan taso yi amma ya hanata bayan ya dawo ya zauna kusa da ita inda ta kira sunansa a hankali.
STORY CONTINUES BELOW
  “Nazeefah fah yaushe zaka dawo da ita?”
  “Soon” ya amsa.
  “Ina Safiyya?”
  “Na sallameta har gida nan Mahaifiyarta tazo ta bada hak’uri tace ta riga ta mayar da ita k’auye dama tun farko bataso kawo su nan d’inba.”
  “Allah sarki, Safiyya was innocent Nazeefah ce tayi manipulating mind nata ta kirani yayi sau uku tana bani hak’uri akan in yafe mata.”
  “Dukda haka be kamata tayi miki abinda tayi ba Kitten kodan yadda kike kyautata mata kayakinki nawa kika bata?”
   “Yanzu kam ai ya wuce.”
  “Nazeefah fa? Ta kiraki?”
  “Tace mun mey? Ba abinda ya sake had’amu.”
  “Kitten I’m sorry nasan abinda Nazeefah ta miki da zafi kuma nasan bata kyauta ba but I would appreciate it if you’ll find it in your heart to forgive her ni da kaina zan sa ta kiraki ta bata hak’uri.”
  “No need Yaya godiya nake da Allah ya tozarta mana ita ka gane halinta bale ta sake tunanin cutar dani kawai ka barta.”
  “But Kitten zan so ace you two are getting along ba abinda zefi min hakan farin ciki dan Allah kiyi hak’uri.”
  “Yaya it’s really okay” ta fad’a had’e da rik’e hannunsa. “In har Nazeefah ta gane kuranta ta kuma nemi tubana nikam me yafe mata ne kodan kai ma.”
   “Thank you so much Amal Allah yayi miki albarka.”
  “Ameen” ta amsa da murmushi.
  “Muje mu kwanta ki huta kinsan yanzu da da ba d’aya bane you’ll be needing alot of rest now kafin nan kuma sena kar6i hak’k’i na ko bazaki bani ba?”
  “Yaya” ta ambata tare dukar da kanta cike da kunya.
“Sarauniyar masu kunya toh wasa nake miki besides you’re still sick I can wait until you get better” murmushi kad’ai ta iya ta sakar masa “So let’s go bath” chak ya d’agata se a bayi ya direta inda ya fito ya d’auko musu towels nasu da kansa ya rage mata kayan jikinta. Bayan lokacin kansu da suka samu a bayin k’arshe ya tayata yin alwala dukda cewan tana iya yi da kanta amma yayi insisting shi zeyi mata. Daga nan ya tayata ta d’aure towel nata sannan suka fito tana rik’e a hannunsa. Kayan baccin ma yak’i ya barta tasa, bayan ya sanya mata yana cikin sa nasa ta mik’e a hankali ta nufi dressing mirror ta zauna ta shiga warware gashinta da hannunta d’aya ganin hakan ze bata wuya Afzal da ya gama sanya kayansa ya mik’a hannu ya rik’eta “let me help you” warwarewa ya k’arisa yi ya d’au comb ya shiga taje mata a hankali sannan ya shafa mata mai ya kama mata shi sakwa-sakwa yadda zataji dad’in bacci.
   “Thank you Habib Albi” ohhh how he misses her calling him with the name, baze iya tuna rabonta da ta kirasa da sunan ba. A hankula ya mik’ar da ita “Kikace?” Gano so yake ta sake nanata sunan se tace;
  “I said thank you” zalla.
“No ba haka kikace ba” yayi saurin kad’a kai had’e da zagaye hannunsa a ‘yar kunkuminta. “Yaya careful k’afana.”
  “Sorry so say the name again Baby.”
  “Wani suna?”
  “Kitten mana!” Ya had’e rai.
  “Ya Omri? Ya Amar? Ya Hayat? Mi Amor? Noorul qalb? Noorul ein? Wanne d’aya?”2
  “Damn! My kitten is such a lover girl, all these sweet names for me?”
  “Yes Habib Albi so wanne kafi so? I’m giving you a new pet name.”
  “Really why?”
  “Saboda we’re starting a new life all over again, wannan karan ba fad’a ba komai se zallan soyayya da kulawa kawai.”
  “Masha Allahuu I’m so proud of you Kitten Allah cigaba da yi miki albarka.”
  “Ameen Habib Albi so wanne kake so?”
   “I think ‘Ya Omri’ sounds great.”
  “Then you garrit Ya Omri.”
  “How about I give you a new name too?”
  “Really?”
  “Yes Kitten.”
  “Toh ina sauraranka” shiru yayi na d’an lokaci yana nazari, “How about Cherry? Peaches? Pearl? Flower? Rania? Snuggly? Cupcake? Which one?”
  “Cute names Ya Omri, Rania sounds arabic hakane?”
  “Yes Kitten it means Queen, my Rania my Queen” yayi mata bayani.
  “Uhmm na d’au Malikati ne My queen.”
  “Rania is another form of it so wanne kikeso? Malikati ko Rania?”
  “Rania it’s more fancy.”
  “Really?”
  “Yes.”
  “Toh shikenan starting today you’re My Rania.”
  “Thank you Ya Omri.”
  “All the time My Rania.”
  “So muje mu kwanta bacci nakeji.” Kafin tace zata juya ya sake kankameta yadda ko k’wak’k’waran motsi bazata iya ba “Ya Omri lafiya.”
   “I want to kiss you so badly Rania.”
  “Ya Omri..” ta kuma furtawa tana k’ok’arin dukar da kanta, yatsa yasa ya d’ago fuskan nata sannan ya shiga shafawa a hankali “May I?” Ya tambayeta yana gangarowa kan lips nata. Wani irin kunya taji ya rufeta kaman ta nitse a k’asa ba k’arya aciki ita kanta she misses his tasty lips and minty breathe.
  “Rania may I?” A hankali ta gyad’a masa kai “No Rania it doesn’t work like that answer me may I have a taste of this lips?”
   “Yaya mana” ta amsa a tak’ure tana kawar da k’wayan idonta daga nasa. “May I?” Ya sake tambaya yana mata murmushi “Yes Ya Omri you may kiss me” ta sanar dashi. Dad’i sosai yaji ya shiga matso da fuskansa kusa da nata a nitse seda ya had’e lips nasu, kissing nata ya shiga yi gently with tender touches yayinda take replying nasa itama a hankali dictating to him how much she missed him. Be bari numfashnta ya d’auke ba yayi breaking kiss d’in, a hankali ta sauk’e goshinta akan ha6arsa tana maida numfashi.
  “I love you Rania” ya sanar da ita yana shafe kan sajen fuskarta.
  “I love you too Ya Omri” daga haka ya d’agata ya kaita d’aki inda suka kwanta bayan ya kashe musu wuta.
  “Goodnight Raina I love you” ya sanar da ita had’e da sanya hannunsa k’ark’ashin rigarta yana shafa kan flat tummy’n ta.
  “Goodnight Ya Omri I love you too” ta amsa tare da sauk’e hannunta akan nasa.
 Da Asubah alarm na Afzal yayi ringing yana kashewa ya tashi ya shirya bayan nan ya tayar da Amal sannan ya fice masallaci, tana idar da sallan ta koma bacci ko jiransa ta kasa sa6anin yadda ta saba. Murmushi kawai ya saki ya tu6e jallabiyansa ya kwanta a gefenta sannan ya saita alarm nasa. Shida na bugawa alarm d’in ya shiga ruri sa6anin yadda Amal ta saba rigasa jin alarm d’in harma ta tashi ta kashe ta tayar da shi se gashi yau se baccinta kawai take, lallai nauyin baccin masu ciki daban yake. Mik’ewa yayi a hankali gudun kar ya farkar da ita sannan ya gyara mata kwanciya ya shige bayi yayi wanka, breakfast nasa ya had’a da kansa yaci ya shirya sannan ya komo kan gadon ya mata placing gentle kiss a goshi ya fice. Ba Amal ce ta tashi ba se chan wajajen k’arfe goma. A razane ta farke had’e da duban lokaci a fankacecen agogon dake manne a sentan gadon d’akin nasu.
“Subhanallahi!” Tayi exclaiming “Yaya you’re going to be late” ta furta cike da tashin hankali yayinda ta juya tana neman Afzal kan gadon sede wayam ba kowa. Mik’ewa tayi ta lek’a bayi nan ba shi wayanta ta d’au ta kirasa a karo na farko ya d’aga “Good morning My Rania” ya gaisheta yana mey barin duk wani abinda yakeyi focusing on the phonecall just.+
“Morning Ya Omri where are you?”
“At work” ya amsa nan take.
“Kana nufin kana office?”
“Yes Rania.”
“How? Yaushe ka tashi ka shirya? Baka sa alarm bane?”
“Kina bacci duk nayi hakan alarm kuma na kunna har ya gama ringing baki ji ba.”
“Omg! Ya Omri I’m sorry yanzu ka karya?”
“No harm done Rania I prepared breakfast myself.”
“Next time ka tayar dani in tayaka shiri kaji?”
“No Rania, you’re pregnant and still sick, kina buk’atan hutu sosai so karki damu kinji? I can manage.”
“Are you sure?”
“Yes Rania, yaushe kika tashi?”
“Yanzu ban san yaushe na soma bacci mey nauyi ba, daga cewa barin kwanta kafin ka dawo daga Masjid kawai se bacci ya d’aukeni ban kuma sake jin komai ba.”
“Dama chan haka baccin masu ciki yake.”
“Gaskiya bazamu shirya da baby’nka ba idan zena sani bacci kaman gawa haka.”
“Toh da mey zakiyi mishi?”
“Punishing nashi zanyi.”
“Ta yaya kenan Rania?”
“By starving myself.”
“So kike yunwa ya addabe min baby na?”
“Toh ba yana sani bacci ba.”
“Yi hak’uri Rania beyi zafi haka ba, ga breakfast a kan dining nasa driver ya saya miki je kici kinji?”
“O’o” ta amsa tana turo baki tamkar yana tsaye a gabanta.
“Yi hak’uri ko in dawo in baki?”
“Eh” ta amsa da gan-gan don jin mey zece.
“Toh shikenan I’m on way ki jirani.”
“Lol Ya Omri yanzu dagaske office d’in zaka bari dan ka taho ka bani abinci?”
“Anything for you Rania.”
“Wasa nake maka yi zamanka kayi aiki, zanci da kaina bari inyi wanka.”
“Are you sure ba sena zo ba Rania?”
“Don’t worry Ya Omri sekace wacce ba tada hannu.”
STORY CONTINUES BELOW
“Alright I’m waiting for your dope pictures in kinyi wankan ayi mun kwaliya na musamman a turo mun.”
“Anything for my Omri I’ll hang up.”
“Take care I love you.”
“I love you too” da haka ta katse wayan. Bayi ta fad’a tayi brushing sannan ta fito ta karya bayan nan tayi wanka ta sanya wata doguwar jallabiya mey d’ankaren kyau sannan ta zauna ta tsara kwaliya ta taje sumarta da k’yar da hannunta d’aya ta kwantar a bayanta ta shiga snapping pictures tanayi wa Afzal sending ta Snapchat. Ko aiki ya kasa yi ranan se kallon hotunan nata kawai yake. Da azahar bayan yaci abinci ya kira Nazeefah a karo na farko ta d’aga. Bazata iya tuna when last ya kirata ba, ko ta kira baya d’agawa ta sak’o kawai suke gaisawa.
“Ya Rouhi?” Ta kirasa.
“Na’am Rabba’atul Bait” ya amsa.
“Ya Rouhi you callled!” Ta fad’a cike da k’in yarda.
“Yes Rabba’atul Bait ya kike?”
“Ya Rouhi I miss you, I miss you so much.”
“I’m missing you too kina gida?”
“Yanzun na dawo daga lectures.”
“Inzo?”
“Eh?”
“Nace inzo?”
“Ya Rouhi zaka zo gani na?”
“Yes Rabba’atul Bait baki yarda bane?”
“Ya Rouhi you’re nomore mad at me?”
“Not anymore sweetheart so inzo?”
“Yes Ya Rouhi you’re always welcomed.”
“Alright I’m on my way” daga nan ya katse wayan. Kaman a kyaftawan ido Nazeefah ta fad’a bayi ta watsa ruwa nan da nan ta shirya cikin wani bak’in lace mey torches na pink. Na sosai d’inkin da shi kanshi lace d’in ya amshi farar fatarta. Light makeup tayi amma ta bala’in yin kyau kasancewar ta kwana biyu batayi applying makeup ba. D’auri irin na Zahra Buhari tayi ta cire gashinta ta k’asa sannan ta feffeshe jikinta da turare inda ta shiga zaman jiransa, chan bada dad’ewa ba Afzal yayi mata waya kan ya iso ta fito.
Mayafinta ta d’au ta yafa sannan ta fice daga gefen gidan nasu yayi parking motansa, wani irin sanyi ne ya ziyarci zuciyan Nazeefah na ganin Afzal kawai da tayi. Kishingid’a yayi daga jikin motan nasa yana sanye da black suits, sky blue shirt da red tie, ba k’aramin kyau yayi ba kaman a had’iyesa. Bata san lokacinda tasa gudu ta nufesa ba, hannunsa ya bud’e mata wide open inda ta fad’a jikinsa hugging him so tightly sun dad’e a haka sannan a hankali ya janyeta sede kawai yaga tana hawaye.
“Not the tears Rabba’atul Bait.”
“Ya Rouhi I miss you so much” ta sanar dashi had’e da sake fad’awa jikinsa tana hugging nasa be sake d’agata ba, tsam ya rik’eta yana shafa bayanta ba k’arya shima yayi missing nata na sosai. Da kanta ta d’ago daga jikin nasa tana share hawayenta hannunta ya sauk’e had’e da zaro hanky daga aljihunsa ya shiga share mata hawayen nata da kansa. “Cry nomore Sweetheart” ya sanar da ita. Kai zalla ta iya gyad’a masa.
“Kinga yadda kikayi kyau?”
“You too Ya Rouhi.”
STORY CONTINUES BELOW
“Toh ya kike?”
“Ka shigo ciki dan Allah.”
“No not today.”
“But ba kowa a gida dukansu sunyi tafiya sun tafi Umarah ni kad’ai ce se wata ‘yar uwarmu kuma ta fita itama.”
“Are you sure?”
“Yes Ya Rouhi please ka shigo.” Hannunsa taja ta kaisa har parlourn Daddy, da tayi yunk’urin kawo masa ruwa da abinci kuwa seya hanata akan cewa yanzun ya baro restaurant. A gefensa ya zaunar da ita yana kallonta tabbas yayi kewarta shima, yana cikin binta da kallo idonsa yayi tozali da wani shatin belt a hannunta wanda har yanzun ya k’i gushewa. Sosai yaji zafin hakan, duk lokacinda ya tuna ya d’au abu ya zaneta seyaji ba dad’i. Hannun nata ya d’aga a hankali yana shafa wajen “Rabba’atul Bait I’m sorry, I’m sorry for bruising you like this.”
“Please don’t be Ya Rouhi, you have no reason to be ni na jawo komai wa kai na and I’m sorry please forgive me.”
“I’ve forgiven you Rabba’atul Bait nazo ne don in jaddada miki ina shirin dawo dake d’akinki, zaki dawo?”
“Ya Rouhi zaka mayar dani gida?” Ta tambayesa cike da k’in yarda.
“Yes Rabba’atul Bait you’re going back to your home.”
“Ya Rouhi!” Ta ambata hawaye na ciko mata a ido yayinda ta fad’a jikinsa tana kuka, zagaye hannunsa yayi a bayanta yana calming nata “Ya Rouhi dan Allah kayi hak’uri na d’au alk’awari bazan kuma abinda na aikata ba please forgive me” a hankali ya d’agota yana share mata hawayen nata “Na fad’a miki I’ve forgiven cry nomore.”
“Thank you so much.”
“Baki tambayi ya jikin Amal ba.” Alokaci d’aya yaga yanayinta ya sauya.
“Nazeefah na d’au kinyi nadaman abinda kika yi wa Amal koba haka ba?”
“Ya Rouhi nayi.”
“Then why this reaction? In har Amal tana da niyyan yafe miki meyasa ke bazaki iya neman tubanta ba? Kinsan ko akwai hak’k’inta akanki? Kuma muddin baki nemi tubanta ba ta yafe miki Allah baze ta6a barin ki ba?”
“Ya Rouhi nayi nadaman abinda nayi mata, wallahi nayi.”
“Then ki bata hak’uri I want you to call her and apologize.” Shiru tayi bata ce komai ba tana tunanin ta inda zata fara kiran Amal ta bata hak’uri, wani irin k’ask’antarwa ne Afzal yake shirin yi mata haka?
“Bazaki iya ba?” Ya tambayeta yana mey tsamo ta daga tunanin da takeyi.
“Ya Rouhi ba haka bane” ta mai k’arya.
“Nazeefah yaushe ne zaki gane cewa Amal ‘yar uwarki ce ba abokiyar gabanki ba? Yadda kike ganin ina son ta kema fa hakan nake sonki, in kuma kina ganin kaman nafi son ta ne then you’re right saboda Amal na mun abinda zuciya na keso. Bata k’untata mun, bata sani surutu, kuma tana sonki saboda tasan ina sonki. Ta sani idan taso wani nawa kaman ni taso amma ke fah? You don’t love her single bit. Why Nazeefah? Do you even love me at all? I doubt so because if you really do zaki so abinda nake so kema ki so Amal.”
“Ya Rouhi dan Allah kar kace haka sanin kanka ne ina sonka, I do love you above of everything.”
“No Nazeefah, idan da har kina so na da zaki so Amal ki guji aikata abinda ze 6ata mun rai but no, you keep on hurting Amal which is technically like hurting me, ita kuma zuciya mey kyautata mata take so ko baki san da haka ba?”
STORY CONTINUES BELOW
“Na sani” ta ambata kanta a duke.
“Good saboda haka nake son ki soma kyautata wa Amal, kin fini sanin yadda Amal ta d’aukeki da zuciya d’aya, kinfi kowa sanin cewa Amal bazata ta6a aikata kwatankwacin abinda kikayi mata ba saboda tasan idan ta ta6aki kaman ta ta6a ni ne why can’t you do thesame? Yadda kike jin ni mijinki ne itama fa haka takeji you both have equal rights on me, I love you Nazeefah, I really do love you and bana son abinda ze sake shiga tsakaninmu but idan kika cigaba da wannan halin naki zakisa ki fita mun a rai kuma bana son hakan ya faru because I don’t want to hate you Nazeefah please change your ways. Kece fa uwar gidana komin yaya matsayin ki daban yake dana Amal a zuciya na da kuma ma a idon jama’a, be kamata ace ke kike yin wannan rashin hankali ba kamata yayi ace Amal ce keyi kina mata wa’azi, ke bakisan da wannan abinda kikeyi ba Amal zata iya k’wace miki martabarki?”
“Ya Rouhi I’m sorry.”
“Don’t be Nazeefah, I just want you to change ki sauya d’abi’un nan kiso ‘yar uwarki muyi zaman lafiya dukan mu please. Idan har kina sona zakiyi mun abinda nakeso.”
“Naji Ya Rouhi in shaa Allah kuma zan canza, ko mey kakeso I’ll do it.”
“Ki tuba ki bawa Amal hak’uri, that’s all I want.”
“Ya Rouhi sena bata hak’uri ne? Ai na tuba.”
“Toh bakiya son in dawo dake gida?”
“Ina so.”
“Then kiyi hak’uri ki sauk’e girman kan nan ki bata hak’uri I kow it’s not easy but do it for me okay?” Ya k’are had’e da d’aga hannunta ya rik’e acikin nasa.
“Naji zan bata.”
“And promise me bazaki sakeyin abinda zeyi hurting Amal ba, promise me ko na mayar dake bazaki sake tada wa kowa hankali a gidan ba, zaki bawa Amal dama kuyi zaman lafiya.” Hannunta ta aza akan nasa dake rik’e da d’ayan nata “I promise Ya Rouhi in shaa Allahu bazaka sake jin kaina dana Amal ba.”
“Thank you Nazeefah thank you so much.”
“Ni ce da godiya Ya Rouhi.”
“So yaushe zaki kirata?”
“Bana son muyi magana ta waya nafison inje in sameta har gida in nemi tubanta.”
“Masha Allah.”
“Yaushe zaka mayar dani gida toh?”
“Yaushe su Daddy zasu dawo?”
“Next week.”
“Suna dawowa zan zo in d’aukeki Rabba’atul Bait kinsan be kamata haka kawai in d’aukeki ba tare da sanin su ba.”
“Hakane kam toh in yi mishi magana ta waya?”
“Still hakan beyi fasali ba kibari su dawo d’in ai nan da next week kaman gobe ne.”
“I know Ya Rouhi is just that I miss you.”
“I miss you even more darling” ya rik’o fuskanta “And I can’t wait to have you back.” Murmushi ta sakar masa sannan ya mik’a a hankali yayi kissing lips nata na lokaci kad’an. “I should get going.”
STORY CONTINUES BELOW
“Tun yanzu Ya Rouhi?”
“I need to get back to work.”
“Zaka gun Amal de.”
“That is after I close from work.”
“Toh tashi in raka ka” har gun motansa ta kaisa inda ya d’auko wani pack k’arami daga cikin motan ya mik’a mata “This is for you.”
“For me?” Ta tambaya had’e da amsa.
“Open it” ya umarceta. Ba gardama ta bud’e wani Silver bracelet ne me bala’in kyau ta tarar aciki “Ya Rouhi this’s so beautiful.”
“Do you like it?”
“Alot, thank you so much Ya Rouhi.”
“Alright ki koma ciki se mun sake waya.” Da haka sukayi sallama ya koma office.
****
_9:36pm_
“Gobe zamuje muyi first baby scan namu ba? Ko bazaki iya zuwa ba?” Afzal dake kwance akan cinyan Amal a parlour ya tambayeta. Hannunta dake cikin gashin kansa tana wasa dashi ta cire “Mey ze hana Ya Omri? Allah kaimu.”
“Ameen, d’azu naje gidan su Nazeefah.”
“Oh how’s she?”
“She’s fine.”
“Yaushe zaka maidota d’akinta?”
“Zuwa next week su Daddy sunyi tafiya so sai sun dawo “
“Allah kaimu:”
“Ameen” ya amsa had’e da d’ago kansa “I wish Nazeefah will be like you Rania.”
“Meyasa kace haka?”
“Inda zata rage zafin kishinta ta sauk’o kaman ki ai kinga da mun samu zaman lafiya a gidan nan.”
“Why?”
“Because bakida kishi Rania.”
“Haka kake gani?” Ta tambayesa da murmushi kad’an.
“Yes Rania ban ta6a ganin kishinki ba.”
“Saboda ina 6oye wa ne gudun sanyaka cikin damuwa kaman yadda kake ciki yanzu.”
“Kina nufin kema kina kishi anytime na ambaci sunan Nazeefah?”
“Tabbas Ya Omri kawai dan ina 6oyewa ne ita kuma Nazeefah bata iya 6oye kishinta shiyasa kake ganin haka. If not ina matuk’an kishinka Ya Omri nakega fiye da yadda Nazeefah ma keyi, ma tukun tayaya ne ba zanyi kishinka ba bayan ina sonka?”
“Wow! So for all these while ranki na 6aci kema idan na kira sunanta?” Kai ta gyad’a masa “Amma bawai hakan na nufin na tsaneta bane saboda yadda nake jin inada iko da kai itama haka ne, we’re both your wives Ya Omri and we love you.”
“Rania you’re just different in a unique way, Allah sa Nazeefah tayi koyi da halinki.”
“Ameen” ta amsa tare da sakar da hamma.
“Baby na tana saki bacci ko?”
“Se kuma aka cemaka baby girl ce?”
STORY CONTINUES BELOW
“Toh mey ne da? Ai mace ce kyakkyawa kamar ki.”
“A’a na miji ne, handsome kaman ka.”
“Mu zuba mu gani.”
“Eh mu zuba d’in, nida abu ke jikina kawani ce min na mace ce? Na miji ne let that sink.”
“Wow ni kuma da nayi ajiyan kikeson kice bansan mey na ajiye ba?”
“Eh baka sani ba.”
“Shikenan time will tell ba se munyi musu ba” cike da dabara ya mik’ar da ita kan kujerar had’e da aza kansa dai-dai saitin cikin nata kaman mey son sauraron abu “I wish I can listen to its heartbeat Rania.”
“Not only will you listen to its heartbeat Ya Omri, one day zaka rik’e sa hannu” ta sanar dashi tana shafa kan nasa a hankali.
“Allah nuna mana wannan rana.”
“Ameen” ta amsa.
“I can’t wait have a replica of you calling me Daddy Rania, I really can’t.” Dad’i sosai taji ta sakar mar da murmushi “Thank you so much Babe.”
“Godiyan mey kuma kake mun Ya Omri?”
“For everything Rania, for trying to give me a family Allah ya cigaba da miki albarka.”
“Ameen Ya Omri everything for you yauwa d’azu ma Ummi ta kirani.”
“Ayyah ya take?”
“Lafiya k’alau ashe ka fad’a mata I’m pregnant.”
“A tunaninki zan iya yin shiru ne? Bank’i a buga a newspaper cewa kina da ciki ba Rania, you made me so proud and happy” hira suka ta6a sannan chan sukaje suka kwanta.
***
Lafiya k’alau suka cigaba da zama abinsu ba tashin hankali bale fad’a se zallan so da tsan-tsan k’auna amma kuma sey me? Kwana biyu zazza6in safe da na yamman nan ke son sake dawowa Amal, gabad’aya yabi yasata a gaba, kullum cikin amai take abin tausayi harta zube. Kaman kar Afzal ya fita office yau yakeji dan yadda jikin nata ya sake yin tsanani shi ya d’au sun riga sun wuce nan yanzu ashe rashin lafiyan mey tafiya ya dawo ne. Misalin k’arfe goma Maamah tazo dubanta. Ga laulayi ga targad’e a hannu da k’afan da be gama warkewa ba har yanzu.
“Sannu cikin nan na baki wuya Bestie.”
“Thank you, anata lectures bani ko?”
“Gashi next week muna da tests har uku na Mallam Auwal biyu da na Malama Binta.”
“Na shiga uku Maamah ko notes bani dashi gashi Malam Auwal baya bada handouts sede wani ikon Allahn kam in ba haka ba nasan inada carry overs wannan semester.”
“Karki damu na miki photocopying nawa notes d’in na Malama Binta kuma gashi na sai miki” tayi maganan had’e da zaro su daga jakarta tana ajiyewa akan side drawer.
“Maamah bansan ya zanyi in ba keba, thank you so much Allah yabar zumunci.”
“Ameen ba komai kede kawai ki samu time kiyi karatu in fever’n ya sauk’a. Ya Ya Afzal?”
“Ya fita office da k’yar wai ze zauna ya kula dani.”
“Ayya meyasa kika hanasa?”
STORY CONTINUES BELOW
“Toh ba amfani Maamah zuwa sha d’aya haka zazza6in ze sauk’a.”
“Ayyah ai ni na d’au kin rabu da zazza6in ashe da saura.”
“Wallahi ko nima na d’au ya k’are kawai shekaran jiya ya fara mun kaman wasa fa se amai, komi naci hararwa nake.”
“Sannu wata nawa ne yanzu?”
“D’aya fa da sati uku.”
“Allah sauwak’e toh in shaa Allah kina fita daga first trimester naki shikenan.”
“Ameen Maamah.”
“Na gaya wa Ya Abdul fa.”
“Mey d’in?” Amal ta tambayeta had’e da zaro ido.
“Batun kina da ciki mana.”
“Innalillahi!” Ta dafe goshinta “Baki da hankali ne Maamah?”
“Toh mey? Ba abun farin ciki bane?”
“God help me wallahi baki had’u ba taya zaki fara sanar da Ya Abdul ina da ciki dan Allah? Mstw se yace mey?”
“Ya taya ki murna of course yace in gaisheki.”
“Mstw wallahi ke banza ce wani sa’in ya yake toh? Se yaushe ze dawo?”
“Waya san masa ne kullum na tambayesa yace da saura da alama ya samu wata achan ne take d’ebe masa kewanmu.”
“Allaha yasa toh wallahi da sena fi kowa yi masa murna.”
“Wallahi ko, ameen deh.” Hira Maamah ta tayata da se wajajen uku ta tafi sanin Afzal ya kusa dawowa. Saidai har shida Afzal yau shiru dan haka Amal ta d’au waya ta kirasa don jin ko lafiya, saidai da ya shiga seya katse yin hakan sau biyu se tayi tunanin ko yana meeting ne bada dad’ewa ba kuwa sega sak’onsa.
_Sorry for not informing you, I’m in a meeting be home in a moment I love you._
Murmushi ta sakar ta furta “Allah dawo daki lafiya.” Sannan ta mayar da wayan ta ajiye.
Wajajen takwas Afzal ya dawo gida lokacin jikin Amal ya sake tashi se kakkarwa take k’ark’ashin bargo. Jakansa kawai ya ajiye ya nufi kanta yana shafa fuskanta a hankali “How’re you feeling Rania?”
“Sannu da dawowa” kad’ai ta iya fad’a masa.
“Kinci abinci?” Ya sake tambayarta inda ta kad’a masa kai.
“Rania why? Bakiji abinda Dr yace miki ba jiya?”
“Ya Omri ko naci hararwa zanyi yana tayar mun da zuciya.”
“I’m sorry kinji? Ko black tea ne ki dage ki sha bari in had’a miki.”
“Please no bana so.”
“Toh se mey? Bazeyi ki kwana akan yunwa ba Rania please.”
“Koko nake so, idan nasha bana hararwa shi Mami ke bani lokacin da nike gida.”
“Kokon dana sani kunun kamu?” Ya tambayeta da mamaki inda ta gyad’a masa kai.
“Toh Rania ina zan samu kamu? Ko da akwai ma ban iya had’awa ba kuma kinga dare yayi ba inda zan iya samu bale in siya miki.”
STORY CONTINUES BELOW
“Don’t worry zan sha ruwa kawai in kwanta gobe seka saya mun.”
“Rania don’t you get it? Bazan iya barinki ki kwana akan yunwa ba.”
“I’m sorry” tace da shi idanunta na kakkafewa. Wayansa ya zaro daga aljihunsa “Wa zaka kira?” Tayi saurin tambayarsa.
“Ummi to ask ko zata iya had’a miki se in amso tunda gida ba nisa daga nan.”
“Ya Omri ba seka sa Ummi aiki ba” saidai be saurareta ba ya kira Ummin bayan ta d’aga sun gaisa yake tambayarta ko akwai kamu a gida.
“Eh lafiya?”
“Ummi ban fad’a miki ba ko? Jikin Amal ya tashi.”
“Subhanallahi bade laulayin ba?”
“Shi Wallahi gashi ko mey taci hararwa take se koko kad’ai kuma babu a nan gida shi’e nake tunanin ko zakisa su Esther su had’a mata yi hak’uri dan Allah.”
“Kai kuma mey na wani bada hak’uri? Ai Amal ‘yata ce bari in had’a mata yanzun ni da kaina driver ya kawo muku.”
“Ko nima zan iya zuwa in kar6o kawai a had’a mata d’in.”
“No ka zauna ka kula da ita tunda ga driver.”
“Alright thank you Ummi.”
“Kayi mata sannu bari in yi sauri in had’a mata” nan da nan ta wuce kitchen ta had’a kokon da kanta ta cika masu a wani k’aton flask yadda har gobe Amal zata iya sha sannan ta had’a musu da d’anye incase zata kad’a in ta samu k’arfin jiki. Zama yayi akanta yana ta yi mata sannu ko kayan jikinsa ya kasa cirewa kunun na isowa ya d’iba a cup yasa sugar kad’an yadda baze tayar mata da zuciya ba ya koma d’akin sannan ya kishingid’ar da ita jikin gadon ya shiga bata, na sosai yayi mamakin yadda tasha kokon sosai gashi ko hararwa batayi ba sa6anin duk wani abinda takai baki.
Ai ko idan haka ne ya zama dole ya koyi dama kokon dan yana yi mata. Bayan ta shanye ya buk’aceta da ta watsa ruwa zata fi jin dad’in jikinta amma tak’i, ba yadda beyi ba tak’i wai yau Amal tasa me son wanka wane kifi ce ake had’a ta da Allah tayi wanka take k’i? Tun jiya rabonta da yin wanka haka k’arshe se da ya d’iba ruwan d’umi a bowl da tsumma ya mammatse mata jikin nata da shi sannan ya samu ya sata tayi bacci. Nan shima yaci abinci ya k’arisa aikin daya rage masa daga office ya fad’a bayi ya watsa ruwa yana cikin fesa turare wayansa ya shiga ruri dubawanda zeyi yaga Nazeefah ke kira be 6ata lokaci ba ya d’aga inda suka gaisa.
“Su Daddy sun dawo ne?”
“A’a se next week kuma wai.”
“Lafiya dai ko?”
“Lafiya kawai chan d’in ya musu dad’i ne.”
“Ayyah se mun k’ara hak’uri sun dawo kenan ko Rabba’atul Bait?”
“Ya Rouhi ni kawai kazo ka d’aukeni.”
“Bazeyi ba Rabba’atul Bait ki k’ara hak’uri kinji? Allah dawo dasu lafiya.”
“Ameen ya jikin Amal?”
“Gashi nan Alhamdulillah deh.”
“Allah sawwak’e toh.”
“Ameen thank you.”
“I miss you Ya Rouhi.”
STORY CONTINUES BELOW
“I miss you even more darling it’s late you should sleep by now.”
“Goodnight toh.”
“Sleep like a baby” nan ya katse ya gama abinda yakeyi yaje ya samu Amal suka kwanta. Duk yadda yaso kwantar da ita a jikinsa ya kasa sabida yadda jikin nata ya d’au wani irin zafi, sekace ba yanzu ya gama matse mata shi da ruwa ba.
Haka Amal ta cigaba da fama da zazza6in, da rana kad’ai take samu tayi karatu, ranan da zasuyi test d’in Afzal da kansa ya kai ta makarantar yayi magana da securities akayi cutting line aka shiga da ita ta gudanar da E-test suka komo gida. Haka duka sauran tests d’inma jiranta yake seta gama su taho gida tare. Kokon nan kuma shi kad’ai take sha ba tare da ta harar ba, da safe Afzal kafin ya fita office yake dama mata yasa a flask yadda da ta tashi sede tasha. Acikin sati Amal ta rame sosai tayi duhu sede jikin da sauk’i sosai yanzu zazza6in ya tafi se k’warnafi ko turare inba na wuta ko khumrah ba bataso, muddin tana d’aki Afzal be isa ya fesa turare ba se taji amai. Gashi sam bata son wanka yanzu, kwana biyu yau tak’i yin wanka matse mata jiki ma da Afzal yakeyi yau ta hanasa yi wai bata so. Alwala idan tayi na Azahar da shi takeyin La’asar wani sa’in har Maghrib. Shi de Afzal yanzu yake sake tabbatar da zancen cewa ciki nasa wasu matan k’aramin hauka.
“Rania yi hak’uri kiyi wankan kinji? Ni da kaina ma zan miki yi hak’uri.” Ko tankasa batayi ba taja bargo ta rufe kanta, sauk’e bargon yayi “Yi hak’uri kinji? Karfa zama da dottin nan yayi miki illa.”
“Wai wallahi inda kaine acikin halin nan ko alwala ma baza ka iya yi ba ka barni kurum in wari nake maka kaje d’ayan d’akin ka kwanta.” Dariya sosai ta basa, mutumin da banda k’amshin turaren wuta ba abinda ke tashi daga jikinsa ne wai ze ce yana wari shi kawai gudun abinda zama da dattin ze iya haifar mata yake ba don wai tana wari ba.
“Yi hak’uri Rania beyi zafi haka ba.”
“Toh ka barni in kwanta.”
“Toh shikenan seda safe Allah k’ara sauk’i.”
“Ameen” ta amsa tana rufe idonta sauk’an lips nasa taji a fuskanta “I love you.”
“Ina da dotti ka manta ne?”
“I’ll still kiss you Rania yi bacci kinji? Get well soon” Murmushi ta sakar masa sannan a hankali bacci ya d’auketa.
***
Da kwana hud’u Nazeefah ta kira Afzal akan su Daddy sun dawo, dad’i kenan he can’t wait ya dawo da ita gida ta bawa Amal hak’uri su fara shiri, it’s what he’s ever asked for. Yana zaune a office yana aiki around 2:30 wayansa yayi beeping alaman shigowan sak’o. Message yagani daga Amal from snapchat da hanzari ya bud’e wayan ya bud’e, hotonta yagani wanda yake da tabbacin yau ta d’auka. Tana sanye da wani dogon rigan roba armless ba ko d’igon kwaliya amma tayi bala’in kyau da gashinta kame a tsakiyan kanta jelan na lilo. Be 6ata lokaci ba yayi replying nata;
_Triple A💦;_ Iyyeehh😍😍 yau baby na yabar min Rania tayi wanka kenan._
Bada dad’ewa ba sega reply nata.
_His Rania👑; 🙈 na cika ka da wari two days ko?_
_Triple A💦; dama shuwa suna wari ne? Ai ban sani ba don ni kullum na matso kusa dake k’amshin turaren wuta da khumra nake ji._
_His Rania👑; 😩 Ya Omri you’re so sweeet_
_Triple A💦; 😁💕 Ya jikin naki toh? Da sauk’i?_
STORY CONTINUES BELOW
_His Rania👑; Alhamdulillah bakace nayi kyau ba😩😩_
_Triple A💦; Haba ‘yar shuwata kema ai kinsan kinyi kyau 😍😍, send me more._
_His Rania👑: O’o ai baka ce mun nayi kyau ba seda na rok’a😕_
_Triple A💦; Rania please😩😩😭 Ya Omri is sorry._
Seda ta gama waina sa sannan ta d’au sabi ta tura masa inda yata yaba kyanta, na sosai yaso posting hoton amma tuna Nazeefah kan iya gani seya fasa, baya son abinda ze sake had’a kansu.
Sa6anin kullum yana isa gida Amal ta taresa yau harda hugging nasa.
“Yau turare na baya wari?” Ya tambayeta dan kuwa sede be matso kusa da ita ba seta toshe hancinta wai turarensa wari yake mata. Kai ta gyad’a tana masa murmsuhi “Welcome back Ya Omri.”
“Jiki da sauk’i kenan.”
“Alhamdulillah.”
“You look so takeaway Rania.”
“Thank you Ya Omri.”
“Toh ya baby na? Kin bata abinci?”
“Mun sha kokon daka had’a mana kafin ka fita office har sau biyu.”
“Mashaa Allahu, ya rage ko a k’ara had’a wani?”
“Ka bari seka huta besides na fara aiki mafa da hannun nawa kaga” ta d’ago hannun nata mey targad’e tana juyawa a idonsa. “Alhamdulillah, My Rania is such a strong woman Allah k’ara miki lafiya Sweetheart.”
“Ameen Ya Omri mu k’arisa ciki” rage kayan jikinsa yayi ya ragar da shorts zallah sannan ya haura gado ya sameta inda take mik’i da handout rik’e a hannunta tana karantawa. Tamkar d’an yaro ya haye jikinta ya kwanta had’e da saita kansa dai-dai saitin k’irjinta da suka ciko tim. “Ya Omri zafi suke min kad’an gyara” tayi saurin sanar dashi.
“Ze daina Rania” yace da ita yana sake cusa kan nasa cikin k’irjin nata “Bacci nakeji na gaji daga aiki” murmushi ta sakar kad’an sannan ta zagaye hannunta a bayansa tana mey cigaba da karantunta, daga haka har itama baccin yayi awon gaba da ita. Da goshin Maghrib Afzal ya farka a hankali ya raba jikinsa daga nata ya fad’a bayi yayi alwala sannan ya tada ita itama.
Bayan da ya dawo daga sallan Isha ya had’a mata kokonta shi kuma ya had’a quarker oats yasha daga nan suka koma d’aki sukayi wankan su tare kaman yadda suka saba. Sede tun da suka kwanta Afzal keta tak’ura mata, itako tak’i barinsa chimma abinda yake da niyya se wani shusshuresa take shiko kaman maye ya kasa hak’ura.
“Ya Omri mana kana fa da office gobe.”
“Rania yanzu duk hak’urin nan da nayi baki gani ba? I need you today hak’uri na ya k’are.”
“Ni banida lafiya” ta amsa tana tattare bargon a jikinta.
“Na sani ai Allah k’ara miki lafiyan amma yi hak’uri ki barni kinji?”
“Ni gaskiya sena samu sauk’i.”
“Haba My Rania yi hak’uri kinji? Kad’an kawai shikenan.”
“Yimin wayo de” ta amsa tana cire hannunsa daya samu ya sak’ala cikin rigarta.
“Yi hak’uri kad’an nace I promise a hankali zan yi miki” rok’arta ya cigaba dayi har seda ya samu ya shawo kanta haka har suka gamsar da junansu. Tana rik’e a hannunsa bacci yayi gaba da ita. Shi kansa baze iya describing yadda yake son Amal yake kuma jinta a ransa ba, all he knows is that bayida irinta.
STORY CONTINUES BELOW
Kasancewar washegari Saturday ba aikin office se suka yini a gida abinsu, da safe sukayi breakfast tare, yau bayan kokon Amal har ta iya taci soyayyan k’wai da fries. Bayan breakfast ta rok’i Afzal da ya kaita salon ta wanke kanta. Shirayawa sukayi tsaf suka fice sede suka tarar da shagon a rufe, dawowansu Afzal yace ze wanke mata da kansa.
“Ya Omri yaushe ka iya wanke kai?” Ta tambayesa da mamaki.
“Da ke kike wanke min nawa?”
“Toh ai naka ba gashin kirki bane akai.”
“Kede kam kizo mana kiga.”
“A’a nikam gaskiya na yafe haka kurum ka jagwalgwala mun kai?”
“Rania I’m serious ki tsaya kiga in be wanku da kyau ba sekiyi complaining” wardrobe nata ya nufa ya d’auko mata vest da shorts “hungo sanya su.”
“Amshi mana Rania kinga fa La’asr ya kusa” amsan tayi ta tu6e ta sanyasu ya jata bathroom d’in. Daga bakin tub d’in ya ajiye mata kujera ta zauna akai ta mik’a kanta ciki inda gashin nata ya sauk’a har k’asan tun d’in. Tsoro yawan gashin nata ya basa shi kansa yama rasa daga ina ze fara wankewan, maganin mey kaud’i kenan.
“Toh Ya Omri ka fara mana” tayi maganan had’e da tattare gashin nata ta d’ago kai tana kallonsa yayin da yake tsaye a kanta.
“Toh ki mayar da kan naki mana ai nasani” ya fad’a confidently sannan ya zauna daga gefenta a bakin tub d’in. Hand shower ya bud’e ya jik’a gashin nata da shi jak’ab sannan ya tsiyaya shampoo akai ya shiga massaging kan a hankali dan dad’i har wani bacci-bacci Amal ta soma ji a gurin. Wanke mata gashin yayi mey kyau shi kansa be tsamman ze iya ba bayan ya wanke ya d’aure mata head towel suka fito ta zauna gaban mirror sannan ta kunce towel d’in tana tsiyaye ruwan.
“Ya Omri zaka iya taimaka mun da jakan hand driers d’ina?” Ta tambayesa politely.
“A ina?”
“A k’asan wardrobe d’ina.” Wajen ya nufa ya d’auko ya mik’a mata sannan ya cigaba da tsaye akanta yana ganin yadda take busar da gashin, na d’an lokaci shima ya gane yadda akeyi. Hannunta ya rik’e yana mey dakatar da ita. Da mamaki ta d’ago kai tana kallonsa “Kawo inyi miki.”
“Ya Omri ai kayi mey wuyan zan iya yin wannan da kaina karka damu.”
“No Rania kawo in miki” murmushi ta sakar masa sannan ya amsa ya shiga busar mata da gashin yana tajewa kaman yadda yaga tana yi har seda gashin ya bushe garau sannan ya jawo mai ya shiga shafa mata bayan nan yayi combing mey kyau sannan ya kama mata shi a tsakar kai sakwa-sakwa.
“Amazing Ya Omri you’re just incredible.”
“Yayi kyau?”
“Alot, thank you so much.”
“Don’t mention so you owe me big yanzu.”
“Meyasa?”
“Nima wataran se kinyi mun aski.” Dariya tasa na sosai “Ashe kuwa zaka ga disappointment har nice zanyi maka aski? Ashe wani ya kusa ya fara yawo da hula.”
“Lool” dariyan yake shima ‘”Yar k’auye ko rik’e clipper ma bata iya ba hala.”
“Toh akwai na miji ne a gidan mu da har zan koyan?”
STORY CONTINUES BELOW
“Ni d’in akwai mace ce a gidan mu har na koyi wanke kan?”
“Ai wanke kai da sauk’i yake akan yin aski barin ma irin naku na ‘yan gayu da se an gyara saje, gaban kan ma a cire wani shape, spare me please ni bazan iya ba.”
Dariya sosai ta basa amma ya cize, “Toh shikenan zan je Uni sex Salon (salon da maza ke zuwa mata ke zuwa) na Racheal tayi mun askin tunda ita ta iya.”
“Gun mace zaka je?” Ta kewayo tana tambayansa da mamaki yayinda kishi ya bayyana karara a fuskanta.
“Toh ba kince ke baki iya ba.”
“Toh ka je d’in zunubin ai ku biyu za a rubuta muku banda ni” ta sanar da shi had’e da juya mai baki sannan ta cigaba da harkan gabanta. Murmushin gefe ya saki nan da nan ya canza kayan jikinsa yasa wani bak’in half jamfan da ya mugun amsansa ya feffeshe jikinsa da turare ya zuba accessories nasa sannan ya d’au jakan askinsa ganin fa dagske yake ze fita Amal ta k’urma ihu kafin ya kai ga bakin k’ofan ta sa key ta k’wace.
“Matar Afzal ki bani guri in wuce.”
“Wallahi bazaka fita ba.”
“Harda rantsuwa?”
“Eh wallahi bazaka fita ba.”
“Toh ni da gida na?”
“Eh naji amma bazaka fita ba.”
“Askin ke zakiyi mun ne?”
“Ai gashin kama be yi wani tsawo ba fitina ne kawai.”
“Nide matsa min.”
“Seka rantse gun na miji zakaje tukuna.”
“Why?”
“Taya wata mace zata ta6amun kai? Wallahi Nazeefah kad’ai na yarda ta ta6a ka.”
“Really?” Ya tambayeta yana dariya.
“Sosai ma kuwa, bayan nan ga ‘yan mata cike kullum a shogon so kake su yi mun snatching d’inka?”
“Toh laifin waye? Ba ke kika ce baki iya ba.”
“Toh zan koya” dariya sosai ta basa amma ya moze. “Ni matsa min.”
“Zan koya Allah zan koya amma kar kaje shagon Racheal dan Allah.”
“Yaushe zaki koyan toh?”
“Ya Omri ai kasan ba a dare d’aya zan iya koya ba but zan sa kai.”
“Promise?”
“I promise” ta amsa tana gyad’a kai dad’i sosai yaji ya jata jikinsa had’e da zagaye hannayensa a ‘yar kunkuminta “Ashe kina sona haka dama?”
“Eh mana” ta amsa tana turo k’aramin bakinta. Bata hankara ba kawai taji yayi owning lips nata a hankali yake turata har suka fad’a kan gado ya shiga yi maya wasanni. Da k’yar ta iya k’watan kanta “Ya Omri yanzu na wanke kaina Allah bazan iya sake jure jik’asa ba.”
“Karki damu zanyi miki drying.”
“A’a Ya Omri da Allah kayi hak’uri ka bari” ko sauraranta beyi ba ya tu6e vest d’in daga jikinta. “Ya Omri stop wallahi zanyi maka ihu.”
STORY CONTINUES BELOW
“Kiyi d’in se muga mey k’watan ki” haka ya cigaba da sarrafa ta har seda ya kashe mata jiki lissss ya biya buk’atansa.
a_An hour later…_
Amal ce kwance jikin Afzal yana shafa dogon sumarta yayinda wayansa dake kan side drawer ya shiga ruri. “D’an mik’i mun wayana Rania” ba gardama ta juya ta d’ago “Wake kira?” Ya tambayeta.
“Nazeefah” ta amsa had’e da mik’a masa, niyyan basa waje tayi har ta janyo vest nata zata sa seya rik’e hannunta ya sake kwantar da ita a jikinsa tare da zagaye hannunsa a bayanta sannan yayi receiving call d’in.
“Halo Ya Rouhi?”
“Na’am Rabba’atul Bait ya kike?”
“Lafiya ya gida ya Amal?”
“Alhamdulillah lafiyanta.”
“Jikin nata da sauk’i?”
“Eh Alhamdulillah.”
“Su Daddy sun dawo d’azu.”
“Oh haba?”
“Eh.”
“Sun dawo lafiya?”
“Lafiya k’alau yaushe zaka zo ka d’aukeni Ya Rouhi?”
“Tunda yau suka dawo mu bari mana gobe? Su huta yau ko?”
“Ya Rouhi anya kuwa you miss me?”
“You know right I do Rabba’atul Bait ki shirya kayakin ki yau kinji? First thing gobe zanzo in d’aukeki.”
“Toh shikenan sekazo I love you.”
“I love you too” yace sannan ya katse.
“Rania?” Ya kirata kai ta d’ago a hankali tana kallonsa. “I’m sorry kinji?”
“Why? What for?”
“For everything I said to Nazeefah that made you felt jealous.”
“Karka damu Ya Omri, tunda nima kana fad’a mun daddad’un kalamu haka dan mey zanji haushi sabida ka fad’awa ‘yar uwata? Wannan kishi dole ne amma bawai hakan na nufin naji haushi bane, so karka damu kaji?” Dad’i sosai kalamunta suka sanya sa ya sake rungumeta tsam ajikinsa “I love you soo veryy much Rania.”
“So gobe zaka je ka d’auko ta?”
“Yes in shaa Allah har gida tace zata zo ta baki hak’uri.”
“Allah kaimu toh.”
“Ameen.”
“I’ll miss you for the 2-2days da zaka na yi mata.”
“I’ll miss you terribly too Darling” ya sanar da ita had’e da placing mata light kiss a goshi “Tashi muyi wanka toh muyi sallah kinga ana neman hud’u se muje muci abinci ba?”
“Sure Ya Omri.”
“Karde har kin mance?”
“Dame fah?”
“Seriously Rania?”
“Yi hak’uri ka tuna mun na d’an sha’afa ne.”
“Wato kin ma manta yau zamu fita first baby shopping namu ko?”
“Ya Omri beyi sauri ba?”
“Haka kullum kike cewa ai a hankali a hankali zamuna ragewa please don’t say no, I’m so excited.”
“Alright toh.”
“Kin yarda zamu je?”
“Anything for my Omri.” Nan da nan sukayi wanka sukayi sallah sannan suka shirya suka wuce shopping. Siyayya sukayi sosai, Afzal na kwasan kayan baby girl Amal na yin na baby boy se dariya masu shagon suke musu amma ko a jikinsu. Se after 6 suka dawo gida da goshin maghriba.
****
GIDAN ALHJ ABDALLAH.
Cike da jin dad’i da rawan jiki ta d’auko akwatin ta ajiye kan gado sannan ta shiga fiddo da kayakinta daga wardrobe tana jerasu aciki, taci rabin aikin Mummy tayi knocking bisa k’ofan d’akin. “Come in” ta amsa sannan ta bud’e ta shiga.
“Ya da shirya akwati haka ina zuwa?” Ta soma da tambaya.
“Mummy Ya Afzal yace gobe zezo ya mayar dani d’akina” ta sanar da ita cike da jin dad’i.
“Kai haba!” Mummy ta tambayeta unbelievably tana mey tayata murna.
“Wallahi ai tun last two weeks yaso mayar dani amman bakwa nan yace in hak’ura sekun dawo.”
“Allah sarki Afzal, toh Alhamdulillah yayi kyau sosai Allah kaimu.”
“Ameen Mummy” ta amsa delightedly.
“Kiga duk kalan rashin hankalin da kika tafka hakan be hanasa yafe miki ba har yake shirin mayar dake d’akinki. Sekiyi ma kanki fad’a Nazeefah ki kiyaye 6ata masa rai, kuyi zaman lafiya da ‘yar uwarki ba abinda hakan ze ragar miki.”
“Hakane Mummy in shaa Allahu komai ya wuce har gida zanje in samu Amal in bata hak’uri.”
“Masha Allah, Allah baku zaman lafiya duka.”
“Ameen Mummy.”
“Toh kinata hanzari haka ko gobe bazaki had’a kayakin bane?”
“Toh Mummy in kuma da safe zezo fah? Ai gara nayi na gama yanzu tunda ba abinda nakeyi.”
“Toh ki sauk’o muci abinci dinner is ready.”
“A’a nikam zan sauk’o daga baya sena gama had’a kayakin nawa tukuna.”
“Toh barin sanar da Daddy’nku.”
“Yauwa do please thank you” nan Mummy ta fice ta ja mata k’ofar. Bayan sun gama cin abincin tayi gyaran murya, “Alhj?” Ta kira Daddy.
“Na’am Hjy Surayya.”
“Errm batun Nazeefah ne daman, Afzal yace gobe zezo ya mayar da ita d’akinta.” Dummm! Zuciyan Daddy ya buga ko motsi ya kasa yi.
“Alhj lafiya?” Mummy data karanci yanayin da ya fad’a nan take tayi saurin tambaya.
“Lafiya ba komai.”
“Nace Afzal ze zo bikon Nazeefah gobe.”
“Bazata koma masa ba” ya fad’a zalla. Da mamaki Mummy ta tsaya kallonsa “Dalili Alhj?”
“Nace bazata koma ba zuwa zeyi ya bata takardanta zamansu ya k’are.”
Mummy ta kasa amincewa da abinda kunnuwanta ke jiye mata da mamaki tace “Alhj ka ko san me kake fad’i? Har mun samu yaron nan ze mayar da ita d’akinta kake cewa bazata koma ba? Ko kai zaman ‘yarnan a gidan nan haka na maka dad’i ne? Ko so kake ka mayar da ‘yar taka bazawara?”
“Nide na fad’a miki kije ki sameta kice mata ba inda zata” yana kaiwa nan ya mik’e ya nufi d’akinsa. Kai Mummy ta kewayo tana kallon Khaleefah da shima ya tsaya kallonta da d’umbun mamaki d’auke a fuskokinsu. Daga bisani ta mik’e ta je ta samu Nazeefah a d’aki, lokacin har ta gama had’a kayakin nata tana cikin tattare jakukkunanta da takalma.
“Nazeefah wani abun ya had’aki da Daddy’nku ne?” Mummy ta tambayeta bayan ta zauna bakin gado.
“A’a wani abu ne?”
“Gashi ina mishi maganan gobe Afzal zezo ya d’aukeki yana cewa ba inda zaki.”
“Ba inda zani kuma?” Nazeefah tayi exclaiming cike da k’in yarda.
STORY CONTINUES BELOW
“Haka yace wai zamanki da Afzal ya k’are.”
“Dalili? Ya Afzal yayi mishi wani abu ne?” Ta tambaya a rud’e.
“Anya kuwa? D’au waya ki kirasa muji” ba makawa ta janyo wayanta ta shiga kiran Afzal sede yayi ta ruri har ya tsinke be d’aga ba kasancewar ya riga ya kwanta. Three missed calls ta masa be d’aga ba ta hak’ura.
“Mummy he ain’t picking up.”
“Kode yayi bacci ne?”
“Might be amma meyasa Daddy ze hana Ya Afzal mayar dani d’akina?”
“Shine nima ban sani ba Nazeefah.”
“Mummy dan Allah kiyi mishi magana Mummy bana son abinda ze rabani da Ya Afzal please dan Allah Daddy ya rufa mun asiri.”
“Karki damu zanyi masa magana ki kwantar da hankalinki nake ga sun d’an samu sa6ani ne.”
“Please do Mummy.”
“I’ll je kici abinci kinga dare nayi.”
“Ni bana jin yunwa.”
“Toh kiyi sallah ki kwanta seda safe” da haka Mummy taja mata k’ofar ta fice taje ta samu Daddy dake mik’e akan gado ya zura wa ceiling ido. Sallama tayi amma ko amsawa beyi ba don yadda hankalinsa sam baya jikinsa.
“Alhj?” Ta kirasa bayan ta zauna a gefensa nan ma shiru k’arshe seda ta d’an ta6asa sannan ya dawo hankalinsa. “Alhj dan Allah ka tashi muyi magana.”
“Wace magana ce zamuyi? Na gaya miki ‘yar nan bazata koma gidan Afzal ba ko baki ji bane?”
“Naji Alhj amma-“
“Amma mey?” ya katseta a fusace “Ni da ‘yata kike son nuna mun iko akanta? Bazata koma ba bazata koma ba.”
“Bawai haka bane Alhj a tunani na koda sa6ani kuka samu da shi Afzal d’in be kamata ka hana sa miyar da yarinyar nan d’akinta ba tunda tana sonsa yana sonta-“
“Surayya dan Allah nace kiyi min shiru” ya katseta cike da rashin hak’uri “Idan kuma shirun ne bazaki iya ba ina iya bar miki d’akin.”
“Allah huci zuciyanka gobe zamuyi magana” Daddy be sake ce mata komai ba. Abinda ya kama daga kan shi harma Mummy da ita Nazeefar bawanda ya iya samun baccin kirki ranan barin ma Daddy da yake ganin asirin sa ya kusa tonuwa besan da wani idon ze sake kallon iyalansa ba.
****
Kiran Afzal ne ya tada Nazeefah daga bacci washegari ba shiri ta d’aga wayan.
“Good morning Baby” ya fad’a a karo na farko.
“Ya Rouhi” ta kirasa cike da tashin hankali.
“Yes is everything okay?” Yayi saurin tambaya.
“Ya Rouhi wani abu ya had’aka da Daddy ne?”
“Nop why?”
“Ya Rouhi cewa yayi wai bazaka miyar dani d’akina ba.”
“What?!” Yayi exclaiming had’e da dropping cup na tea da yake sha.
STORY CONTINUES BELOW
“Ya Rouhi please do something I don’t want to be separated from you.”
“Karki damu I’m on way now” daga haka ya katse wayan ya fad’a d’aki ya d’au key’n motansa. “Rania?” yayi knocking bakin k’ofan bayin.
“Yes Ya Omri?” Ta amsa daga ciki.
“Zan fita ina zuwa.”
“Toh seka dawo” be 6ata lokaci ba ya fice.
****
Mik’ewa tayi ta fad’a bayi tayi brushing ta canza kayan jikinta sannan ta sauk’o k’asa dan karyawa. Hayaniyan data jiyo ta gun d’akin Daddy yasa ta k’arisa gurin inda ta tarar da Mummy da Daddy se faman fad’a sukeyi.
“Haka kawai bazan zuba ido ka mayar min da ‘ya bazawara ba wallahi Afzal zezo kuma ze tafi da yarinyar nan” Mummy ta fad’a cike da tsiwa kaman ba ita ba.
“Idan ke kike iko da Nazeefar se mu gani” Daddy ya mayar mata.
“Daddy dan Allah kayi hak’uri” Nazeefah da idanunta suka ciko tim da hawaye ta tsoma baki “Daddy dan Allah karka rabani da Ya Afzal Daddy idan wani abun ya maka I’m sorry on his behalf please don’t separate us two.”
“Kiyi hak’uri Nazeefah amma rabuwa da Afzal ya zama dole” kuka ta shiga yi na hak’ik’a “Daddy dan Allah kar ka min haka dan Allah kayi hak’uri I’m so sorry” har cikin zuciyansa Daddy yaji ba dad’i ashe akan ‘yarsa Allah ze rama wa Jameelah abinda yayi mata, why not akanshi? Meyasa se akan ‘yarsa? Ashe anan Allah na nuna masa kamar yadda alheri yake d’anko shima sharri haka ne muddin baka shuk’a me kyau ba toh ‘ya’yanka ma bazasu ga mey kyau ba.
“Ki barsa” Mummy tace da ita tana mey janta jiki “Afzal d’in ai zezo se ya hanaki binsa muga” tana kaiwa nan taja Nazeefah d’akinta ta shiga lalashinta amma inaa Nazeefah se kuka. Ba’a dad’e ba sega Afzal ya taho yana isa ya kira Nazeefah inda ta tura Khaleefah ya shigo da shi zuwa parlourn Daddy sannan ya shiga daga ciki yayi ma Mummy magana. Mayafi ta yafa ta fito da Nazeefah biye a bayanta. Bayan sun gaisa take tambayarsa ko abu ya had’asa da Daddy.
“Wallahi ba komai Mummy kema kinsan bazan so abinda ze shiga tsakani na da Daddy ba kodan Nazeefah.”
“Hakane Afzal yanzu abinda nakeso da kai ka d’au Nazeefah ku tafi karka sauraresa.”
“Nace baze tafi da ita ba” suka jiyo muryan Daddy kaman daga sama nan take duk suka kewayo suna kallonsa.
Har k’asa Afzal ya sauk’a ya gaishesa amma ko amsawa beyi ba “Ka rubuta mata takardanta yanzun nan bazata bika ko ina ba.”
“Daddy ban fahimce ka ba.”
“Sakin ta nake so kayi yanzun anan” ya jaddada masa.1
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” ya sa salati “Daddy idan wani abun nayi maka kayi hak’uri amma karka rabani da Nazeefah dan Allah.”
“Baka ji me nace bane?”
“Daddy naji dan Allah kayi hak’uri.”
“Ai ni na rok’eka da ka aureta daman tun farko yanzu kuma ina rok’onka da ka sawwak’e mata zaman ku ya k’are.”
“But Daddy I love Nazeefah, ina sonta bana kuma son in rabu da ita.”
“Zaman ku ya k’are nace Afzal ka sakar min ‘ya.”
“Wai Alhj meke damunka ne? Haka kawai kake shirin shiga tsakanin yaran nan a ina aka ta6a yin hakan?”
STORY CONTINUES BELOW
“Hjy Surayya banyi magana dake ba saboda haka ba ruwanki.”
“Niko nake da ruwa acikin zancen nan taya zaka sa na dole miji ya rabu da matarsa?”
“Afzal ka rubutawa yarinyar nan takardanta nace” yace kaman wanda beji abinda Mummy ta fad’a ba.
“Daddy dan Allah kayi hak’uri” Nazeefah ta rok’esa cikin tsan-tsan kuka saidai ko kallonta beyi ba. “Idan kuma ranka ya 6aci ne game da dawo dani gida da Ya Afzal yayi kayi hak’uri amma bashida laifi, nice nayi mar laifi a matsayinsa na mey mata biyu kuma dole ya kwatanta yin adalci tsakani na da ‘yar uwata. Tunda ni nasa Amal tayi yaji na raba ta da gidanta nima dole a rabani da nawa. Amma ka duba yanzu da Amal ta dawo ba gashi yana son ya miyar dani d’akina ba? Kuma seka hana hakan Daddy? Please don’t.” Na sosai maganganun Nazeefah suka shige jikin Daddy suna masu samun mazauni a birnin zuciyansa. Ba shi kad’ai ba kowa seda kalamun nata suka ta6a sa a gurin amma haka na dole Daddy yayi banza da ita. “Afzal ba magana nake ma ba?”
“Daddy I’m terribly sorry idan mayar da Nazeefah gida da nayi na kwanakin nan ne ya 6ata maka rai kamar yadda Nazeefah ta fad’a. I had no option but please don’t be mad, I’m sorry and I do love Nazeefah.”
“Ka rubuta mata takardanta nace-“1
“Baze rubuta ba Alhj nace baze rubuta ba” Mummy da ranta in yayi dubu be 6aci ba ta katse sa.
“Afzal baka jina ne?”
“Daddy ina ji” ya amsa na dole.
“Ka rubuta mata takardanta nace.” Kuka Nazeefah ke sosai tace, “Please don’t do this Daddy, please.”
“Me kake jira ne har yanzu Afzal?” Daddy yayi kaman be jita ba “Biro ne ko takarda baka da ita? Khaleefah wuce d’akinka ka d’auko mar.”
“Daddy kayi hak’uri amma ka sani bazan iya rubutawa Nazeefah takardan saki haka kawai ba please understand me.”
“Daddy kayi hak’uri mana” Khaleefah da ya zuba musu ido tun d’azun ya fad’a.
“Daddy please don’t do this” Nazeefah ta kar6esa, “Please don’t Daddy, Afzal is sorry kayi hak’uri ka barni in tafi dashi.”
“Nazeefah kiyi hak’uri amma gaba kad’an zaki gane am doing this for your own good.”
“Which good Daddy? Kana shirin raba ni da mijina wanda yake sona nake kuma sonsa kake cewa you’re doing this for me? How? Mummy how is this going to be of help to me?” Ta jiyo cikin tsananin kuka tana kallon Mummy data janyota jiki.
“Zaman ki da Afzal ya haramta Nazeefah bazeyi ki cigaba da zama da shi ba dan haka ya zamanto dole ya sakeki ya sauwak’e miki.”
“Kaman ya zamansu ya haramta Alhj? Wani abun sukayi ne da zakace zamansu ya haramta?” Mummy tayi saurin tambayarsa “Dan na d’an wata ya korota gida kuma akan gaskiyansa se kace zamansu ya haramta? A ina ne idan mace tayi laifi akace miji baze hukunta ta ba? Tell me!” Tayi demanding.
“Nide na fad’i nawa zamansu ya haramta don haka ya k’are, Khaleefah yi maza ka d’auko mar paper da biro kar ka bari in nanata kaina.”
“Khaleefah zauna ba inda zaka” Mummy ta dakatar da Khaleefah daya zabura.
“Daddy I’m sorry amma bazan iya rubutawa Nazeefah takardanta ba” Afzal ya fad’a had’e da mik’ewa “I’ll get going ina zuwa amma.”
STORY CONTINUES BELOW
“Afzal! Afzal!” Kiransa Daddy yake amma ko kewayowa beyi ba. Gidansu ya wuce direct unfortunately Abba bayi nan yayi tafiya Ummi kad’ai ya tarar. Irga mata halin da ake ciki yayi inda ta sha mamaki na sosai.
“Toh yanzu ya zamuyi? Amma meya samu Alhj Abdallah haka?”
“Wallahi Ummi I don’t know and he seem so serious about it.”
“Subhanallahi meya buga masa kai toh? Kode koran Nazeefah gida da kayi d’inne ya 6ata mar rai haka?”
“Amma ai ba koran walak’anci nayi mata ba Ummi besides Nazeefah was at fault dole in hukunta ta kodan inyi ma Amal adalci.”
“Tabbas Prince kuma nima bawai nace kayi laifi bane am just surprised gashi Abbanka baya nan.”
“Se yaushe ze dawo?”
“Yau yace.”
“Toh kafin nan kije ki samu Daddy kiyi mishi magana please.”
“Ni kuma Prince?” Ta dafe k’irji.
“Eh Ummi I don’t want to lose Nazeefah please go” ya fad’a cikin tsananin tashin hankali.
“Prince ta ina zanje in fara yi wa Alhj Abdallah magana a matsayinsa na sirki na? Ai beyi fasali ba kade bari Abban naka ya dawo zuwa anjima.”
“Ummi please” ya rok’eta abin tausayi.
“I’m sorry Prince but I can’t” kafad’ansa ta dafe “Abbanka ze dawo anjima I’ll be the one to explain everything to him kayi hak’uri kaji? I’m sorry” kai zalla ya iya gyad’a mata.
“Ka karya ko tukuna?”
“Na karya” ya amsa.
“Toh ka kwantar da hankalinka, muyi fatan Allah dawo da Abbanka lafiya.”
***
Wajajen sha biyu Amal da ta ji shiru daga Afzal ta d’au waya ta kirasa lokacin har bacci ya fara d’aukansa zaune a kan kujera a parlour, ba makawa ya d’aga inda ta soma da “Halo Ya Omri?”
“Na’am Rania.”
“Ina ka shige? Shiru tun d’azu.”
“Rania akwai matsala” ya sanar da ita.
“Subhanallahi ina dey kana lafiya ba abinda ya same ka ko?”
“Not at all.”
“Alhamdulillah” ta saki ajiyar zuciya “toh meya faru?”
“Rania sena dawo gida kawai I’m on my way.”
“Toh Allah dawo da kai lafiya I love you.”
“I love you too” ya amsa sannan ya katse. Duban agogo yayi yaga pass 12 “Ummi!” Ya shiga kiranta chan sega ta tashigo. “Lafiya? Naji kana kirana.”
“Ummi se yaushe Abba ze shigo?”
“Zuwa anjima yace Prince bansan yaushe flight nasun ze tashi ba.”
“Ummi I don’t want to lose Nazeefah please do somethibg.”
“In shaa Allahu ba abinda ze faru kai de ka kwantar da hankalinka kaji?”
STORY CONTINUES BELOW
“Zan wuce gida idan Abba ya shigo seki kirani.”
“Toh shikenan Allah ya kare.” Be kai ga tada engine na motar sa ba sega Nazeefah na kiransa. Nan take ya amsa “Halo Nazeefah?”
“Ya Afzal…” ta kirasa kawai seta rushe da kuka.
“Ohh dear!” Ya ambata had’e da murza temple nasa “Rabba’atul Bait please kibar kukan haka ba shida amfani.”
“Ya Rouhi tayaya ne bazan yi kuka ba bayan Daddy yana shirin rabani da kai?”
“I’m not going to let that happen kinji? Abba is on his way idan ya dawo zezo ya samu Daddy yayi mishi magana in shaa Allahu ze sauk’o ya amince in dawo dake d’akinki okay?”
“But Ya Rouhi he seem so serious wallahi se rok’onshi muke tayi amma ko sauraron mu beyi I’m scared.”
“Don’t be sweetheart in shaa Allahu mutuwa ce kad’ai zata raba mu dan bazan ta6a aikata abinda Daddy ke cewa inyi ba because I love you okay?”
“I love you too Ya Rouhi promise me komin yaya bazaka rubuta mun takarda na ba.”1
“I promise darling” ya sanar da ita.
“Thank you Ya Rouhi.”
“Yanzu share hawayenki kibar kukan haka toh sena shigo anjima.”
“Okay take care” daga nan ya katse ya sa key ya wuce gida inda Amal ta taresa. Bayan ta kawo masa ruwa yasha take tambayar sa meke faruwa nan ya labarta mata komai inda itama tayi mamaki na sosai sannan ta shiga kwantar masa da hankali.
***
Se wajajen hud’u jirginsu Abba ya sauk’a driver yaje ya d’auko sa daga airport. Ruwa ya watsa sannan suka ci abinci da Ummi inda take basa labarin halin da ake ciki. Kansa ne ya mugun d’aure akan mey Alhj Abdallah zece a sakan masa ‘ya? Shin meya faru? Nan da nan ya kira Afzal a waya yake tambayarsa kode wani abun ne ya had’asa da Daddy amma Afzal ya nuna sam ba komai banda mayar da Nazeefah gida da yayi akan laifin da ta aikata. Take a lokacin Abba yaje ya samu Daddy saidai Daddy na kan bakansa har yanzu shi a sakar mishi da ‘ya ba yadda Abba beyi da shi ba, ba kalan hak’urin da be basa ba amma ya dage ina shi a sakar mishi da ‘ya kawai irrespective of abotakan dake tsakaninsu. Na matuk’a ran Abba ya 6aci be ta6a tsammanin haka daga gun amininsa ba, ai ko da ma ace laifi Afzal yayi masa be kamata yayi haka ba.
“Na d’au zamuyi magana man-to-man mu fahimci juna da kai Alhj Abdallah a matsayinka na amini na ashe ba haka bane.”
“Kayi hak’uri Alhaji Amin ko ni ban so abubuwa su kasance haka ba amma ya zama dole in raba auren yaran nan ne badan son ra’ayi na ba nima.”
“Sai don mey toh? Idan wani abun ne ka sanar dani mana kar fa kamanta aminin ka ne ni.”
“Ina sane da hakan Alhj Amin amma kayi hak’uri bazan iya sanar da kai dalili na ba ni kawai asa Afzal ya sawak’e wa ‘yata.”
“Kaine mahaifin Nazeefah kuma se yadda kace za’ayi amma a tunani na zaka sanar dani koma meye dalilin, in shaa Allahu zanyi maka kyakkyawar fahimta.”
“Kayi hak’uri Alhj Amin komin yaya naso sanar dakai bazan iya ba shiyasa nake sake baka hak’uri kayi hak’uri.”
“Shikenan tunda abinda kake so kenan Allah yasa hakan shi yafi alkhairi.”
STORY CONTINUES BELOW
“Ameen nagode da fahimta ta da kayi ina fatan hakan baze 6ata tsakanin mu ba?”
“In shaa Allahu ka gaishe da Madam.” Har bakin gate Daddy ya rakasa sannan ya koma ciki Abba ya k’arisa gida. Tun daga bakin k’ofa Ummi ta soma tambayarsa yaya.
“Yace shi a sauwak’e wa ‘yarsa” ya sanar da ita.
“Innalillahi! Toh Alhj ya zamuyi? Prince fa? Wallahi yana son yarinyar nan ina gudun kar hakan ya jefa sa cikin wani halin.”1
“Toh mahaifinta yace ga abinda yake so mun isa muce a’a ne?”
“Eh mana ai wannan bayi bane wallahi taya haka kawai ba k’wak’k’waran dalili se don an kora ‘yarsa gida akan laifin data aikata ze shiga tsakanin masoya biyu yace se an rabasu, rabawan ma wanda ba komawa?”
“Toh ya zamuyi Hjy Mariam?”
“Muko muke da abinyi wallahi mu kai k’ararsa kotu na tabbata bazasu goye masa baya ba.”
“Mey yayi zafi har da zuwa kotu Hjy Mariam? Shi prince d’in bashida mata a gida ne? Kokuwa Nazeefar ce k’arshen halittu?”1
“Ko d’aya Alhj amma ai zaka duba halin da d’an nan ze iya fad’awa cikine. Yaran nan yana son yarinyar nan haka kawai kuma a rabasu wallahi babban hatsari ne ga rayuwansa harma da ita d’in.”
“Ina sane da dukkan hakan Hky Mariam kuma idan da akwai wani hanyar da zanbi da na bi dan in dawo masa da matarsa amma gar-da-gar Alhj Abdallah yace shi a sakan masa ‘ya baya son jin komai mey kikeso inyi? Zancen kai k’ara kotu kuma ma be tashi ba idan dey mata ne Allah ya haliccesu dayawa ko a gobe yakeso yakan k’ara wani auren.”
“Hakane kam amma Alhj Abdallah bai kyauta ba ai ko dan abotakan dake tsakaninku ma be kamata yayi haka ba.”
“Zuwa gobe zan kira Afzal yazo anan ya rubuta mata takardanta a kai musu mu rabu dasu lafiya.”1
“Oh! Duniya, toh shikenan Allah ya kaimu bari in k’arisa site d’ina.”
“Alright.”
*****
“Ya Omri ka kwantar da hankalinka haka, everything is going to be alright.”
A raunane ya d’ago lumsassun idanunsa ya kafa mata.
“Rania I’m sorry” ya furta a hankali sam ba a son ransa bane ya nuna tsan-tsan damuwa akan Nazeefah a gaban Amal haka amma ba yanda ya iya ne abun ne yafi k’arfinsa.
“Why?” Ta tambayesa cike da rashin fahimta.
“For showing concern over Nazeefah like this nasan be kamata in nuna tsan-tsan damuwa akanta a gabanki haka ba but I just can’t help it, kaman yadda nake sonki haka nake son ta itama. Kuma kaman yadda bazan so abu ya shiga tsakanin mu dake ba ba ita ma haka ne Rania. I can’t afford to lose her, I just can’t” ya fad’a cikin raunannen murya.6
Baza tayi k’arya ba da fari taji haushi da kuma kishin yadda ya shiga matuk’an damuwa akan Nazeefah amma sanin yadda zafin rabuwa da masoyi yake musamman ma na dole irin wannan se taga ba laifinsa bane, ta tabbata idan da itane a position na Nazeefah zeyi haka ko fiye da hakan ma, toh kishin mey zatayi? Matsowa kusa dashi tayi sannan a hankali ta kwantar da kansa a k’irjinta tana mey shafe gashin kan nasa a hankali “Don’t be sorry Ya Omri, na fahimci yanayin da kake ciki and I’m here for you, feel free to cry in my arms I love you so much.” Hannayensa ya zagaye a ‘yar kunkuminta yayinda hawaye ya shiga tsiyaya daga idanunsa sun dad’e a haka har seda wahalallen bacci ya d’aukesa. Cike da dabara ta kwantar dashi kan gadon ta gyara mai kwanciya sannan tayi zamanta a gefe tana mamakin dalilin da zaisa Daddy ya aikata abinda yayi.
STORY CONTINUES BELOW
Chan wajajen Isha sega kiran Ummi da hanzari Amal ta mik’a wa Afzal kiran inda ya d’aga. “Ummi?”
“Na’am Prince.”
“Ummi ina kika jefa wayarki ina ta kira switched off?”
“Wallahi bak’i nayi d’azun suna ta game daga nan suka kashe min wayar suka yasar a lungu se yanzu na samu.”
“Ohh na d’au wani abu nema ya sameki ya Abba? Ya dawo?”
“Eh ya dawo” ta amsa a sanyaye.
“Yaje ya ma Daddy magana?”
“Eh ya mishi.”
“And???”
“Prince-” se kuma tayi shiru.
“Please speak up Ummi” ya fad’a cikin tsananin fargaba.
“An yi mishi magana amma he’s not willing to back out Prince yace lalle-lalle se ka sakar masa da ‘ya.”
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” ya saki salati “No Ummi.”
“I’m truly sorry Prince amma abinda yace kenan gobe da La’asr Abbanka na buk’atan presence naka. Seda safe ka gaishe da Amal” tana kaiwa nan ta katse wayar. Ko sauk’e wayar daga kunnensa Afzal ya kasa Amal ce ta tako daga gaban dressing mirror ta amshe wayan had’e da mik’ar da shi ta rungumesa tsam a jikinta tana basa hak’uri. Kaman d’an yaro ya zage yana kuka a jikinta ba makawa. A dalilin mey Daddy zeyi masa haka? No he can’t stand by it, baze iya jure rabuwa da Rabba’atul Bait tasa haka kawai ba sabida selfish interest na mahaifinta. Tunda yana sonta tana sonsa toh in shaa Allah ba abinda ya isa ya rabasu he don’t care koda maganan zata kai kotu. A shirye yake da yayi filing case akan Daddy, ya tabbata kotu zata dawo masa da matarsa.2
****
Washegari da safe suka shirya tsaf da Amal yayi dropping nata a school. Wajajen sha d’aya Nazeefah ta kirasa bayan sun gaisa ta buk’acesa da ya taho school a waje kaza yazo ya sameta. Be 6ata lokaci ba ya fice be tsaya ko ina ba se inda tace su had’un. Yana sauk’a daga motan ta ruga a guje taje tayi hugging nasa tana kuka har na fitan hankali. Rungumarta yayi tsam a jikinsa shima yayinda yake danne hawayen dake k’ok’arin ku6uce mar. Sun dad’e a haka sannan a hankali ya shiga raba jikinsa daga nata sede ina se sake matsesa Nazeefah ke da k’yar ya samu ya d’agota ya shiga share mata hawaye yana bata hak’uri yayinda take ta kad’a mar kai.2
“It’s okay calm down I’m here.”
“It’s not okay Ya Rouhi it’s not” ta sanar dashi cikin tsananin kuka.
“Look at me” ya buk’aceta “Look at me okay?” Cikin sanyi ta d’ago jajayen idanunta ta kafa mai. “Nothing in this world will ever seperate me from you except for death okay?”
“How Ya Rouhi? Tayaya? Abba ma ya mishi magana jiya yak’i ya sauraresa se kai ne ze saurareka?”
“I know it’s not possible just trust me.”
“I really want to but I’m scared, tsoro nakeji Ya Rouhi.”
“Kar fa ki manta nike da ikon rubuta takardan nan ko ba haka ba?” Kai ta gyad’a yayinda ya cigaba “Idan ban rubuta ba kuma Daddy be isa ya miki wani aure akan igiyan aure na ba ko ba haka ba?” Nan ma kan ta kuma gyad’awa “Excellent ni kuma ko da kasheni za’ayi sama da k’asa su had’u bazan rubuta miki takardan nan ba Nazeefah I’ll never do it.”
STORY CONTINUES BELOW
“I know Ya Rouhi amma kuma ko da hakan Daddy baze ta6a barina in koma a gareka ba ya gwammace in cigaba da zama a gida da igiyan auranka akaina daya amince ka miyar dani d’aki na.”
“I’m coming to beg him again later today idan har be amince ba zan kai k’ara kotu Rabba’atul Bait akan ki a shirye nake da inyi breaking rules and even worse saboda bana son rabuwa dake, da a rabani dake gara na rasa komi nawa dana malakka I love you Nazeefah, I love you so very much.” Kuka ne yaci k’arfinta ba shiri ta fad’a jikinsa tana kuka shima ba don ya danne hawayen ba da tuni ya jonata sunyi kukan tare. A hankali ya rabata daga jikinsa ya rik’o ‘yar fuskanta cikin hannunsa yana mey share mata hawayen nata “Your home will forever be here with me Darling” ya sanar da ita be hankara ba yaji tayi owning lips nasa kissing him so dearly. Kasancewar wajen ba mutane shima se be 6ata lokaci ba ya shiga sumbatarta in a soft demanding way. Sun dad’e a haka sannan yayi breaking kiss d’in daga bisani yayinda suka shiga mayar da numfashi.1
“Don’t cry anymore okay?”
“Okay” ta amsa tana gyad’a kai fuskarta ya d’ago yadda take kalon setin idanunsa “I won’t rest har se idan na dawo dake d’akinki Nazeefah you have my words.”
“I trust you Ya Rouhi and I love you so dearly.”
“I love you too Darling.”
“Ka koma haka nan nima I have a class to attend.”
“Alright se na shigo anjima da yamma okay?”
“Okay Allah kaimu.”*******
_3:47pm_
Yana cikin tattare kayakinsa da shirin kulle office sega wayansa ya shiga ruri dubawanda zeyi yaga Amal ke kira. Be 6ata lokaci ba ya d’aga “Hello Rania?”
“How’re you Ya Omri?”
“Alhamdulillah what about you?”
“Lafiya k’alau.”
“And my baby?”
“Itama lafiya.”
“Yau kika galabaitar mun da ita ko?”1
“Toh so kake inyi ta zaman gida ina tara wa kaina carrovers?”
“A’a Mummy’n Baby yi hak’uri kunci abinci?”
“Eh na dafa indomie.”
“Akwai wani abinda kike buk’ata?”
“A’a I’m just missing you yaushe zaka dawo?”
“Abba requested to see me so daga chan zan wuce gida okay?”
“Batun Nazeefah koh?”
“Yes.”
“Everything will work out fine in shaa Allah.”
“Thank you baby I love you.”1
“I love you too seka dawo.”
“Sleep until then sena zo in tada ke.” Da murmushi kwance fal a fuskarta ta amsa “Toh shikenan take care” nan ta katse. Be kai ga ajiye wayan nasa ba sega kiran Abba na shiga be hankara ba ya d’aga inda suka gaisa.1
STORY CONTINUES BELOW
“Ermm nace Umminka ta sanar da kai cewa ina buk’atan ganinka ko?”
“Eh Abba I’m on my way.”
“Alright Allah ya kare.”
“Ameen” da haka ya katse ya gama tattare kayakin nasa ya fice. Direct gida ya wuce inda ya samu Abba da Ummi zaune a parlour suna jiransa. Ba tare da 6ata lokaci ba Abba ya sanar da Afzal gaskiyan al’amarin inda yayi mar nasiha sosai akan cewa ba komi mutum yake so yake samu a duniya ba dole wataran se an k’ara da hak’uri amma ina Afzal tamkar kurma haka ya zame a wajen maganganun Abba kawai suna shiga ta kunnensa suna fita ta d’ayan ne shi bega abinda ze rabasa da Nazeefah ba bayan mutuwa.
“Saboda haka ga takarda nan da biro ka rubuta mata takardanta kuma saki ba d’aya ba, ba biyu ba yake nema saki uku yake so.”
“No Abba” ya sanar dashi ciki rud’ani “I can’t do this.”
“I know Afzal amma ya zame maka dole ba muke iko da Nazeefah.”
“Abba baka gane bane? Bazan iya rubutawa Nazeefah takarda ba I can’t.”
“Prince kayi hak’uri” fad’in Ummi.
“No Ummi I can’t zan je in samesa inyi masa magana in shaa Allah ze sauk’o.”
“Umminka bata sanar da kai cewa da kaina naje na samesa bane? Alhj Abdallah ya riga yayi making up mind nasa ba abinda zakayi da zaisa ya sauk’o.”
“I’ll still try my luck Abba idan kuma be hak’ura ba then I have no choice dole in kai maganan nan kotu dan idan ba mutuwa ba banga abinda ze rabani da matata ba.”
“Nima haka nace mu kai k’aranshi kotu tunda de ba zaluntar yarinyar nan kakeyi ba kotu zata tsaya maka ta dawo maka da matarka.”
“A’a Hjy Mariam seda na fad’a miki ki yasar da maganan nan kink’i akan mey zamu kai maganan nan har kotu? Nazeefar itace autar mata ko mey?”
“Ba itace k’arshen halitta ba Abba amma bazan iya rabuwa da ita haka kawai saboda selfish interest na Daddy ba.”
“Afzal kar ka manta Nazeefah ‘yarsa ce kuma bamu keda iko da ita ba.”
“No Abba, Nazeefah matata ce kuma nafi Daddy iko da ita shiyasa nake rok’onka da ka bani dama inje in samesa inyi masa magana.”1
“Afzal wai kam mey kakeyi haka? Akan rashin mutuncin da Alhj Abdallah yayi maka ya kuma yi wa mahaifinka ai yaci ace ka fita daga harkansa da ‘yartasa gabad’aya. Ka sani suke da asara ba mu ba, idan aure kake so ka k’ara ko a yau ka kawo mace gidan nan zan aura maka ita, infact ko uku kakeso ka k’ara zanyi maka komai balle ma kai da kake da mace a gida? Mene Nazeefah za tayi maka wanda Amal baza ta iya yi ma ba? C’mon man up.”
“Abba ba haka bane, baza ka ta6a ganewa ba Nazeefah and Amal are two different people dan Allah ka bani dama inje in sake basa hak’uri in shaa Allah he’ll come around.”1
“Alhj kayi hak’uri ka barshi yaje d’in hala rabonsa ya ratse” Ummi ta fad’a.
“Shikenan kaje amma ni ba ruwana na riga na fad’a maka abinda ya kamata.”
“Nagode” yace zalla had’e da mik’ewa “Ni zan koma duk abinda akwai I’ll let you know.” Da haka ya fice dai-dai gaban gidansu Nazeefah yayi parking ya k’arasa ciki.
STORY CONTINUES BELOW
“Ka kawo takardan nata ne?” Daddy ya tambayesa bayan gaisuwan da sukayi.
“Daddy ba abinda ya kawo ni ba kenan dan bazan ta6a iya rubutawa Nazeefah takarda ba haka kawai. Hak’uri nazo baka, dan Allah kayi hak’uri.”
“Shin mahaifinka be sanar dakai abinda nace masa bane?”
“He did Daddy amma bazan iya ba, wallahi ina son Nazeefah kuma bana k’aunan rabuwa da ita idan wani laifin nayi kayi hak’uri-“
“Dakata Afzal!” Daddy yayi saurin katsesa “Idan ba so kake ranka ya 6aci ba ka bani takardan ‘yata zaman aure ne nace bazaku k’ara ba.”
“Shikenan Afzal ka mik’e ka tafi zamuyi magana” Mummy dake la6e tun d’azu jikin garu tace.
“Mummy dan Allah ki basa hak’uri wallahi bazan iya rabuwa da Nazeefah ba.”
“Na gane Afzal just go zamuyi magana.” Ba dan yana so ba ya mik’e ya fice. Acikin mota ya zauna ya shar6i kuka kaman ba gobe.
Daddy da yaga dagaske Afzal yake baze iya rabuwa da Nazeefah ba ya shiga nazari, yasani koda kotu ya kai k’ara da k’yar su biye masa sabida bashida wata k’wak’k’warar dalili, da ace Nazeefar ne bata son auren da rabasa bazeyi wuya ba amma yasan komin yaya Nazeefah bazata ta6a amincewa ta rabu da Afzal ba. Ya zeyi toh?
Chan bayan sallan Isha Mummy na zaune a d’akin Nazeefah tana ta faman bata hak’uri Daddy yayi knocking bisa k’ofan ya shiga.
“Ermm Hjy Surayya ki tattaro min passports naku.”
“Passports? Kayi mey dasu?”
“Kede kam ki tattaro mun mana ina ruwanki?”
“So kake ka d’ibe mu kaje ka jibge mu a wani k’asan saboda selfish intrest naka?”
“Ba abinda na tambaya ba kenan ki bani passports naku.”
“Bazan bada ba.”
“Nazeefah ina passports naku?”
“Daddy dan Allah kayi hak’uri Daddy meyayi zafi kake shirin kaimu wani k’asan? A dalilin mey?”
“Saboda bana son abinda ze sake had’aki da Afzal.”
“Daddy da igiyan auren Ya Afzal akaina kake son inyi tafiya ba tare da izininsa ba?”
“Sau nawa zan fad’a miki Afzal ba mijinki bane? Zaman ku ya haramta.”
“Ya haramta kaman yaya wai? Idan wani abun ne ka fito fili mana ka sanar damu Alhj meye amfanin wannan 6oye-6oyen da kakeyi?” Mummy ta tambayesa.
“Ina jiran passports naku muddin Afzal baze sauwak’e wa ‘yar nan ba toh barin k’asar nan ya zama dole.”
“Daddy makaranta na fah? Khaleefah ma fa?” Nazeefah dake kuka ta tambayesa sede ko ta kanta beyi ba ya ja k’ofan ya fice. Fad’i tayi jikin Mummy tana kuka. “Wallahi wallahi kinji ko? Ba inda zamu. Iyayin Daddy’n naku ya soma isa na Allah kaimu gobe k’ara zan kai kotu akan mey dan na zuba masa ido ze tsaya yana yin son ransa a cikin gidan nan? Ki kwantar da hankalinki Allah kaimu goben.”.****
Chan wajajen goma Nazeefah ta d’au waya ta kira Afzal, ringing d’aya biyu ya d’aga.
“Hello Rabba’atul Bait?”
STORY CONTINUES BELOW
“Ya Rouhi please help me Ya Rouhi bana son in rasaka.”
“Wani abu ya sake faruwa ne?”
“Ya Rouhi Daddy na shirin relocating namu out of Nigeria gabad’aya.”
“What?!”
“Wai muddin bazaka bani takarda na ba zamu bar k’asar, d’azun yazo ya tattare passports namu Ya Rouhi please help me out.”
“Shhhh its okay don’t cry ina Mummy?”
“Mummy tace zata kai k’aransa kotu.”
“Ki kwantar da hankalinki kinji? Sena shigo gobe kibar kukan haka.”
“Please come.”
“I’ll, you should get some rest I love you.”
“I love you too” ta amsa sannan ya katse. Safa da marwah ya shiga yi a parloun yana nazari sannan chan yaje ya samu Amal a d’aki suka kwanta.
Washegari bayan sallan Azahar Afzal ya taho gidansu Nazeefah ba irin hak’urin da be bawa Daddy ba amma ina ko sauraronsa Daddy baiyi ana cikin haka Mummy dake sauraronsu tun d’azu ta sanya baki.
“Toh tunda de haka ne Afzal ni na baka dama kaje kayi filing case a kotu se muga idan kotun zata basa goyin baya ya raba wannan aure.” Wani irin har6awa zuciyan Daddy yayi tabbas idan ya bari maganan nan yakai kotu toh asirinsa ze toni kenan. Ya zeyi?
“Ni kike shirin kaiwa kotu Hjy Surayya?”
“You give me no option Alhj. Idan wani abun ne kake 6oye mana tell us we’re your family zamuyi maka kyakkyawn fahimta amma zancen canza mana gari be tashi ba.”
Kai ya shiga girgizawa “No Hjy Surayya bazaku ta6a fahimta taba, ba don ni ba dan Allah kuyi hak’uri a raba auren nan.”
“Trust me Alhj zamu fahimceka just tell us” a hankali ta shiga yi mai magana cike da kissa amma inaa Daddy ya kasa bud’e baki yayi magana se kad’a kai kawai yake.
“Toh inde haka ne mu ma bazamu amince mu bika koma ina ba kuma mayar da yarinyar nan d’akinta ba fashi.”
“Afzal ka rubuta wa ‘yar nan takardanta nace auren ku ya haramta!”
“A dalilin mey ya haramtan?” Itama Mummy ta mayar masa cike da tsiwa. Dai-dai lokacin Nazeefah da Khaleefah suke sauk’owa daga sama. A bakin stairs d’in suka tsaya suna sauraron iyayensu.
“Ya haramta nace kuyi wa Allah ku raba auren nan.”
“Mey sukayi da zaka haramta musu aure? A dalilin mey?”
“Ya haramta Hjy Surayya ki yarda da ni.”
“Na yarda da kai Alhj, just tell us ka gaya mana dalilin da yasa ya haramtan, muddin kaine da gaskiya na maka alk’awarin tayaka raba auren nan just tell us.”
“Bazan iya ba ku gafirceni.” Na matuk’a kan kowa ya d’aure a wajen, ba wanda ya fahimci inda ya dosa gashi duk sun k’osa suji dalilin da yasa yake cewa auren ya haramta.
“Alhj dan Allah kayi magana, ka fa sani rik’e maganan nan ba shine mafita ba, we’re your family komin yaya bazamu guje ka ba just tell us.”
“Ya haramta na fad’a muku ya kuke so inyi? Kar ku biye ma Afzal. Tunda baze saki ‘yar nan ba ku amince ku bini mu tattara mu bar k’asar nan shine kwanciyan hankalin mu gabad’aya.”
“Tayaya Alhj? Mene wannan abu da kake k’in gaya mana? Toh inde haka ne ina Nazeefah? Ku sauk’o mu bi Afzal mu bar mai gidan idan tayi tsami maji.”
“Hjy Surayya dan Allah karki tozartani a idon jama’a haka, kar ku tafi ku barni ku kad’ai gareni.”
“Fine seka sanar danu wannan magana da kake 6oyewa kokuwa mu tafi.”
“Ni koda zaku tafi ku amince a raba auren nan, na yarda ku tafin amma a raba auren yarannan tukuna.”
“Haka kawai ba gaira ba dalili kake son a shiga tsakanin masoya biyu? Toh wallahi kayi k’arya Alhj.”
“Sau nawa san gaya miki auren nan ya haramta?! Sau nawa!” Ya daka mata tsawa.
“Sau nawa nima zan gaya maka muddin banji dalili ba bazan yarda a raba auren nan ba?!” Itama ta mayar masa a tsawace.
“Ya haramta nace!”
“Mayar da aure ba fashi ku sauk’o mu tafi Nazeefah.”
“Kar ku tafi ko ina, auran Afzal da Nazeefah ya haramta saboda Amal da Nazeefah ‘yan uwa ne!” Ya sanar dasu a fusace ba tare da yasan yaushe ba.
“What??” Mummy tayi exclaiming cike da k’in yarda yayinda fuskokinsu duka ke d’auke da d’umbun mamaki barin ma Afzal da Nazeefah da suke jin lamarin kaman raha.+
“Ku gafirceni Hjy Surayya amma aure tsakanin Afzal da Nazeefah ya haramta, dole ne ya sauwak’e mata saboda Amal yar ta ce.”
“Innalillahi wa inna ilai-” Mummy bata kai ga idda salatin ba kawai suka ji k’aran fad’uwan abu a k’asa rigijib! Afzal kam dan mamaki bakin yin salatin ma ya rasa.
Atake duk suka maida hankalinsu game da k’aran inda suka ci karo da sumemmiyar jikin Nazeefah a k’asa. Kasancewar Khaleefah ne a kusa da ita seya rigasu fara yin kanta yana mey jijjigata amma ina ko motsi batayi ba shiri Afzal ya k’ariso ya d’agata yayi waje da ita se cikin motansa inda Khaleefah da Mummy suka zauna a baya da ita Daddy kuma a gaba. Nearby clinic Afzal yayi rushing inda akayi emergency room da Nazeefah. Tunda aka shiga da Nazeefah har Dr da nurses da suka duba ta suka fito kap acikinsu Afzal ba wanda Allah ya basa izinin sake yima Daddy wani tambaya as duk sun shiga cikin rud’ani. Jugum suka zauna daga lungu daban-daban kowa da abinda yake gudu masa a kai. Ita de Mummy har yanzu ta kasa aminta da komai haka ma Khaleefah amma banda Afzal da jikinsa ya soma basa tabbas Daddy ne mahaifin Amal in reference to labarin Mami da yaji. Duk yadda yaso k’aryata zancen Daddy ya kasa, yana da yak’inin cewa Daddy ne mahaifin Amal. Shin wani irin cakwakiya ne wannan? Taya za’ace yana auran wa da k’anwa? Innalillahi wa inna ilaihi raji’un.
Da wani idon ze sake kallon Nazeefah ya kalli Amal? Shin yanzu dukansu biyu sun haramta masa kenan ko ya? Yau ina zaisa kansa idan ya wayi gari ba Amal ba Nazeefah? Wannan wace irin k’addara ce? Ko a tatsuniya be ta6a jin inda abu haka ya ta6a faruwa ba. Wayyo Allah shi. Ana cikin haka likitan daya duba Nazeefah ya fito ya sanar dasu kan ta farfad’o suna iya shiga ganinta. Mummy da Khaleefah suka soma shiga sannan Afzal, daga k’arshe kuma Daddy da ya tsaya daga bakin k’ofa tsabaragen kunyan da yake ji ko k’arisawa ciki ya kasa. Jikin Mummy Nazeefah ta fad’a tana kukan tsuma zuciya “Mummy please tell me it’s a joke, Mummy it can’t be Mummy please.”
“Shhh ya isa haka” itama Mummy’n bata san lokacinda ta shiga zubda hawaye ba, ya rage Khaleefah kad’ai ke basu hak’uri. Duk anan kallonsu kawai Afzal yake bako uffan, yayi tsaye kaman gunki daga wani sashe. Daga bisani Mummy da Nazeefah kenrik’e a hannunta ta kewayo kan Daddy.
“Alhj meke faruwa? Shin kama san kuwa abinda kake fad’i?”
Nauyayyen ajiyan zuciya ya sauk’e sannan ya k’ariso cikin d’akin “Hjy Surayya ki gafirceni amma Amal kishiyar Nazeefah ‘yata ce.”
“Noo” Nazeefah ta shiga kad’a kai yayinda hawaye ke tsiyaya daga idanunta “Please don’t do this Daddy I beg of you.”
“I’m very very sorry Nazeefah-“
“Daddy ta yaya?” Tayi saurin katsesa “Taya Amal ta zamo ‘yar uwata? How Daddy?” Ta tambayesa tana mey rushewa cikin tsananin kuka.
“It’s a long story Nazeefah, fatana Allah yasa kin fahimci dalilin da yasa nake son ki rabu da Afzal ki kuma bani had’in kai.”
“No Daddy, bazan rabu da Ya Afzal ba idan ma akwai me rabuwa da Ya Afzal toh Amal ce not me.”
“Ya isa haka Nazeefah” Mummy ta dakatar da ita.
“No Mummy why will I be the one to pay for Daddy’s mistake? Balle ma ban yarda cewa Amal ‘yar uwata bace. Amal kishiyata ce she can never be my sister never!” Bori ta shiga yi wanda da k’yar Mummy ta samu ta lafa da ita. Hawaye na tsiyaya daga idanta ta d’ago kai tana kallon Daddy da jikinsa ya gama mutuwa ga kukan da iyalansa sukeyi har anan Afzal bece komai ba tsabagen state of shock da ya shiga, gani yake kaman a mafarki komi yake faruwa.
“Taya Amal ta zame yar Nazeefah Alhj? Ta yaya? I need answers.”
“I’m terribly sorry Surayya.”
STORY CONTINUES BELOW
“So kake kace mun kana da ‘ya a waje?” Shiru yayi dan kunya ko amsawa ya kasa ga yadda Khaleefah ya kafa masa ido. Da irin wannan abin kunya da wani ido ze sake yima ‘ya’yansa horo yanzu?
“Magana nake maka Alhj!” Ta tambayesa a fusace “I need answers we all need answers here!” Tayi demanding.
“Wallahi nima ban san da zaman Amal ba se lokacin da aka kad’eta.”
“Baka san da zaman Amal ba?” Mummy ta tambayesa unbelievably. “Baka san da zaman Amal bafa kace? A ina aka ta6ayin haka?”
“Wallahi ban san da zaman Amal ba se kwanan nan.”
“Taya ya zakace kana da ‘ya amma baka san da zamanta ba Alhj? Until when zaka daina yi mun da ‘ya’yana k’arya?”
“Wallahi ban san ciki ya shige jikin mahaifiyarta ba bayan faruwan abun.”
“Yanzu ko kunya baka ji kake k’arya a gaban sirinkinka da ‘ya’yanka Alhj? Wannan abu da me yayi kama? Ashe kana da ‘ya a waje na aureka ban sani ba? Kuma kak’i ka sanar dani har yau? Ashe da ba don wannan cakwakiya ba haka zan cigaba da zama da kai kana mun k’arya kana zolayata? Why Alhj?”
“Surayya wallahi ba haka bane ni kaina recently na san cewa Amal ‘yata cr, na so in sanar dake kuma amma tsoro nake, tsoron rana irin ta yau ki yarda dani Hjy Surayya.”
“K’arya kakeyi wallahi k’arya kakeyi” ta fad’i tana kuka.
“Idan da nasan yaran nan ‘yan uwa ne ajinki zan bari su auri Afzal ne dukansu biyu Surayya? Please believe me.”
“Shine kuma yanzu dan rashin adalci kake son ‘yata ta biya laifin da ka aikata? Toh kayi k’arya Alhj wallahi kayi k’arya.”
“Hjy Surayya dan Allah kiyi hak’uri ki bani had’in kai a raba auren nan.”
“Wallahi Allah ya isa nida ‘ya’yana Allah ya isan mana.” Har anan Afzal be ce komai ba. “Tashi Nazeefah tashi mu tafi.” Hak’uri Daddy ya shiga bata amma ko ta kansa batayi ba yana yunk’urin ta6ata kuwa ta fisge jikinta “Koda wasa kar ka sake yink’urin ta6ani mu tafi Khaleefah” har bakin k’ofa Daddy ya bisu yana basu hak’uri amma ba wanda ya kewayo ya kallesa acikinsu. Bayan sun fice ya juyo kan Afzal.
“Afzal da-“
“No Daddy” yayi saurin katse sa had’e da ficewa daga d’akin yayi gun motansa be ratse ko ina ba se gida. Yana bud’e k’ofa sega Amal ta taso yi masa sannu da zuwa hannunta ya ja ya jefata jikinsa had’e da rungumeta tsam wane wani na shirin k’watan masa ita. Wani irin rikicaccen kuka yasa wanda ya mugun d’aurewa Amal kai.
“Subhanallahi Ya Omri why’re you crying?” Se kuka kawai “Ya Omri please stop” kokawan d’agosa daga jikinta ta shiga yi amma ta kasa dan yadda ya damk’e ta. “Ya Omri cry nomore I’m here” bayanshi ta shiga bubbugawa a hankali tana basa hak’uri yayin da kukan nasa ya tsananta. Sun d’au tsawon lokaci a haka sannan na k’arfi da yaji Amal ta samu ta janyesa daga jikinsa yana mey k’ok’arin sake kankameta.
Kallo d’aya ta kaiwa idanunsa da suka kad’a sukayi ja nan take itama idan nata ya cika da hawaye ba shiri ta shiga tsiyayar da su tsan-tsan tausayi da k’auna. “Ya Omri what happened? Meyasa kake kuka haka?” Janta yayi ya sake rungumeta se chan ya saketa ya shiga share mata hawayenta har anan tambayansa take meya faru.
Hannunta biyu ya d’ago ya had’a da nasa yana murzawa a hankali yayinda ta k’ure masa ido tana shirin jin abinda ze fad’a mata. Bayan nishin da ya fisga ya kira sunanta “Amal?” Abinda ya jima beyi ba.
“Na’am Yaya?” ta amsa.
“Amal promise me.”
“Promise you what Yaya?” Tayi saurin tambaya.
“Just promise me.”
“I promise Yaya, everything for you.”
“Thank you, thank you so much.”
STORY CONTINUES BELOW
“Meya faru Yaya? Meyasa kake kuka haka? Batun Nazeefah ne?”
“Ko kad’an Amal, this is about you.” Na sosai kanta ya d’aure “Ni kuma Yaya? meya faru?”
“Promise me again Amal, ki min alk’awari koda mey ya faru bazaki ta6a tafiya ki barni ba.”
“Subhanallahi shin meya faru Yaya? Meyasa kake magana haka? Please talk to me.”
“Just promise me Amal please.”
“Yaya kafi kowa sani na bazan ta6a tafiya in barka ba because I love you, I love you so much.”
“Thank you Lily” nan ya jata jikinsa ya sake rungumeta. Na matuk’a kanta ya sake d’aurewa shin meke faruwa? Hannu ta zagaye a bayansa hugging him back. “Amal I’ve found your biological father” ya sanar da ita a saitin kunnenta wani irin mumunan fad’i gabanta yayi ba shiri ta janye jikinta daga nasa. “Ka samu asalin mahaifina?” Ta tambayesa cike a k’in yarda. Kai zalla ya gyad’a mata yana me rik’o hannayenta cikin nasa.
“How? When? Where? ” Ta jero mai tambayoyi nan take. Kafin ya amsa ta shiga k’aryatasa “No Yaya this can’t be true, har a ina ka sansa bale idan ka gansa ka ganesa? You’re mistaken Yaya koma waye ne mahaifin nawa nasan baya raye.”
“No Lily, not at all mahaifinki yana raye.”
“How? Taya kasan yana raye? Ya ma akayi ka sansa? Yaya please” kai take ta kad’awa cike da k’in yarda.
“Calm down Amal but that is not even the problem.”
“Yaya what’re you saying?” Seya bud’e baki ze sanar da ita seya kasa.
“Yaya please speak up what problem? Meyake faruwa?”
“Ki kwantar da hankalinki bana son abu ya samu lafiyan abinda ke cikinki.”
“Yaya just tell me.”
“Forget it, shikenan ma.”
Hannunsa tayi saurin rik’owa kafin ya juya “Please tell me Yaya what is going on?”
“Kiyi min alk’awari bazaki yi reacting ba, komin yaya bazaki tada hankalinki ba za kuma kiyi wa bak’on lamarin nan kyakkyawan fahimta.”
“Yaya ka fad’amun mana.”
“I have to know, bana son zuciyanki ya tsinke abu ya sameki ko baby’nmu so promise me bazaki tada hankalinki ba.”
“Okay I promise ka fad’a mun dan Allah” ta fad’a a k’ose.
“Amal you and Nazeefah are sisters” shiru kukeji a wajen ko motsawa Amal ta kasayi bale magana, k’ok’ari take ta fahimci inda ya dosa amma ta kasa. Daga bisani ta shiga kad’a kanta “Ni da Nazeefah?” Ta tambayesa.
“Yes Amal, Nazeefah k’anwarki ce” sulalewa k’asa tayi wanda da sauri Afzal ya tarota ya direta akan kujera yayinda idanunta suke shirin kafewa. Ruwa ya nema ya shiga yayyafa mata sede kaman sake kashe mata jiki yake tun yana iya ganin cikin idanun nata har ta rufesu. Ba shiri ya yasar da glass cup d’in inda yayi kaca-kaca a k’asa ya shiga bubbuga ta sede ina ko motsawa batayi. Dafe hannunsa da yace zeyi jikin kujeran kawai yaji abu kaman ruwa dubawanda zeyi ya tarar da jini wani irin rikicaccen ihu ya saki. “Amal? Amal? Please wake up Amal!” Se ihu yake yana kiran sunanta amma inaa ta riga ta jima da sumewa. Ba shiri ya kicicci6eta a hannu bema damu da jinin daze masa staining blue getzner’n dake jikinsa ba. A bayan mota ya sata ya shiga gaba se TH inda akayi emergency room da ita. Ko zama Afzal ya kasa gun se safa da marwah yake yana kuka kaman k’aramin yaro kowa yazo wucewa seya tsaya ya kallesa. Dan yadda ya rikice ko kiran Ummi ya sanar da ita halin da ake ciki ya kasa chan wata nurse ta jasa wani gu ya wanke hannunsa dake d’auke da jini har sannan ta tayasa goge kayansa sede jinin ya riga ya kama amma duk da hakan be damu ba. Bakin k’ofan nata ya koma ya tsaya yana jiran fitowan likitocin chan bada dad’ewa ba sega k’ofan ya bud’u. Ko daman yin magana be baiwa likitan ba ya shiga kwararo masa da tambayoyi.
STORY CONTINUES BELOW
“Calm down calm down” Likitan ya shiga kwantar masa da hankali sede is of no use saboda hankalinsa ya riga ya tashi.
“Please answer me how is my wife?”
“Your wife will be fine you don’t have to worry nan da ‘yan mintuna kad’an zata farfad’o.”
“And my baby?” Reaction daya gani a fuskan likitan kad’ai yasa k’asusuwan guiwansa sakewa yayinda cikinsa ya d’au ruwa. Ba shiri ya shiga kad’a kai “Please speak up Dr how’s the baby? Kun samu kun ceto cikin?”
“I’m very sorry Sir amma it was too late tun kafin ku iso nan cikin ya lalace an de wanke cikin yanzu anyi duk wani abinda ya kamata I’m very sorry zaka iya shiga ganinta.” Motsi wannan Afzal ya kasayi a wajen tun ficewan likitan da nurses d’in se hawaye kawai yake zubarwa yayinda gobaran tsanan Daddy yake ruruwa mai a zuciya. Ma shin meya kaisa sanar da Amal cewa ita da Nazeefah sisters ne? Da ya san abinda yin hakan ze haifar da be soma ba. Yanzu shikenan sunyi ban kwana da baby’nsu kenan? Baby’n da har ya gama imaging yadda kamanninta ze kasance d’aya da na Amal tasa? Baby’n da ya gama picturing rayuwansu da ita? Innalillahi wa inna ilaihi raji’un tabbas wannan rana a cike yake da masifa da k’unci. Guiwa na rawa ya dafe handle na k’ofan ya bud’e ya shiga ciki. Chak ya tsaya gun ya kasa k’arisawa tsan-tsan tausayi kawai, ta ina ze fara sanar da Amal cewa cikin nata ya lalace? Nooo baze iya ba. Jiki na rawa ya k’arisa ciki had’e da jan kujera ya zauna a gefenta. Kakkarwa hannunsa ke ya d’ago ya dafe nata da canular ke kai. “Amal I’m so sorry, I’m terribly sorry please wake up karki tafi ki barni you promised to stay by my side” kuka yake tamkar d’an yaro a gurin. Ba ma wai na zubewan cikin ba sena tsoro da yake zamansu na iya k’arewa shida Amal tunda dry gashi ita da Nazeefah ‘yan uwa ne. Baze iya rayuwa ba ita ba.
Kukan ya cigaba da yi ba fashi har seda Amal ta shiga bud’e idanunta. Mik’awa yayi had’e da sumbatan goshinta “Thank you for staying alive with me Rania” ya sanar da ita hannunsa na acikin gashin kanta yana shafawa a hankali.
“Rania why aren’t you saying anything?” Ya tambayeta bayan dogon shirun da tayi hannunta kawai yaga ta kai akan cikinta a hankali ya aza nasa akai shima.
“Is my baby still with me?” Ta tambayesa murya ciki-ciki. Rasa na cewa yayi kawai ya shiga yi mata murmushi saidai duk yadda yaso 6oye k’uncin da yake ciki ya kasa a hankali hawaye ya shiga ciko masa a ido.
“Ya zube ko?” Ta sake tambayansa itama idan nata na mey cikowa da hawaye. “Yaya please answer me idan zubewa yayi just tell me” ta k’are hawayen na tsiyaya daga idanunta.
“Amal I’m so sorry please forgive me.”
“Ya zube?” Ta kuma tambayansa kai zalla ya gyad’a mata yayinda ta rushe da wani irin masifaffen kuka. Gadon ya haye da wuri ya jata jikinsa ya shiga bata hak’uri amma se bori takeyi da k’yar ya samu ya lafa da ita. Tana kwance a jikinsa ta kira sunansa.
“Yes?” Ya amsa patiently.
“Meyasa se ita? Why not me?”
“Because you’re more precious Rania, saboda Allah ya tausaya mun yasan idan ya d’aukeki bazan iya rayuwa ba.”
“Yaya na kasa amincewa da hakan, dan Allah ka gafirceni.”
“Saboda mey Rania? Mey kikayi?”
“Na kasa rik’e amanan rik’on da ka bani Yaya I’m so sorry.”
STORY CONTINUES BELOW
“Ko kad’an ba laifinki bane Rania idan har akwai wanda ze nemi tuna toh nine, da ban sanar dake gaskiya ba da cikinki be zube ba, da har yanzu baby tana tare damu.”
“But for how long zaka ta 6oye mun gaskiya Yaya?”
“It doesn’t matter now, ni kawai ki daina blaming kanki, dama haka Allah ya qaddara baby bazata rayu damu ba, fatan mu Allah yasa mey ceto ce.”
“About what you said? Shin da gaske ne Nazeefah k’anwa tace?”
“Amal that doesn’t matter now lafiyarki ne a gaban mu yanzu.”
“No Yaya” ta d’ago kai a hankali tana kallonsa a raunane “It does matter, is Nazeefah my half sister? Shin dagaske ne Mahaifin mu d’aya ne da ita?”
“Amal I’m very sorry I never wished for things to turn out this way.”
“Just answer me.”
“Yes Amal, keda Nazeefah ‘yan uwa ne.”
“Ta yaya? Taya ma hakan ze zamo gaskiya?” Nan ya kwashe labarin duk yadda akayi ya bata Amal kam se kuka. Yanzu ma’ana kenan mutumin da ya taimake ta lokacin da Nazeefah tasa aka bigeta shine mahaifinta, mutumin da take ta fatan ina ma ace mahaifinta shine asalin mahaifinta? Meyasa taji ta tsanesa gabad’aya yanzu? Innalillahi wa inna ilaihi raji’un taya hakan ma ze zamo gaskiya? Tayaya ma ya gane ita ‘yarsa ce? Ashe de ba tsakani da Allah ya taimaka mata ya kuma kula da ita ba lokacin, shin tayaya ma yasan ita ‘yarsa ce? A iya labarin da Mami tayi mata ta nuna mata cewa shi mahaifin nata bema san an haifeta ba. How is this even possible?? She need answers. Kuka take Afzal yana bata hak’uri.
“Yaya baka gane bane Daddy baze ta6a zama mahaifina ba, baka fahimce sa bane.”
“Please cut it out.”
“No Yaya it can’t be possible idan da Nazeefah k’anwa tace da naji hakan a jikina please stop saying she’s my sister please.”
“Amal saidai muyi hak’uri amma bazamu iya canza k’addarar Allah ba.”
“Ya zamo dole mu hak’ura da juna kenan Yaya.”
“Saboda mey Lily?” Ya tambayeta a raunane.
“Bazeyi mu cigaba da zama ahaka ba Yaya, bazeyi muna jini d’aya da Nazeefah mu cigaba da kasancewa matayenka ba, zama damu ya haramta maka.”
“No Amal please don’t talk like that dan Allah kibar cewa haka, I can’t live without you kinfi kowa sanin hakan.”
“I’m sorry Yaya amma gaskiya d’aya ce rabuwa ya zamo dole.”
“No please Amal, dan Allah kibar cewa haka, kefa kika ce our love for each other is enough.”
“Not in this case Yaya saboda we can’t escape from the truth.”
“But you promised never to leave me.”
“I’m sorry I’m breaking that promise now.”
“Please don’t Amal there has to be a way.”
“What way Yaya?”
“I don’t know, zamuyi tambaya akai in shaa Allahu zasu san yadda zasuyi damu but please kibar cewa zaki tafi ki barni bazan iya rayuwa ba ke ba Amal I really can’t.”
STORY CONTINUES BELOW
“I’m really sorry Yaya I’m so sorry.”
“I dont want you to be Amal, I want you to stay please kiyi mun alk’awari.” Kai zalla ta iya gyad’a masa yayinda hawaye ke bin k’uncinta. Ita abun ma ya taru ya mata yawa ga miscarriage, gashi ita da k’anwarta suna auren miji d’aya. Wannan wace irin k’addara ce?
“Kayi ma likitan da ya dubani magana I want to be discharged.”
“But Amal you’re sick bakida k’arfi.”
“Ina son in tafi gida.”
“Wani gida d’aya? Har yanzu kina kan bakanki na tafiya? Please don’t leave me Amal please don’t.”
“Just take me home Yaya.”
“Promise me bazaki gudu gida gunsu Mami ma?” Kai zalla ta gyad’a masa amma abinda zuciyanta ke raya mata ba ta gudu ta koma gunsu Mami bane so take ta gudu ta shiga wani duniyan daban inda ba wanda yasan tarihinta. Cakwakiyan dake cikin rayuwanta ya isheta, abin kunyan yayi yawa. Haka Afzal yaje ya samu likita yace a sallamesu ba yadda likitan beyi dashi ba akan yabari koda zuwa gobe idan Amal ta d’an samu k’arfin jiki amma ina Amal tace ita sede yau za’a sallameta hakan kuwa akayi daga k’arshe. Magungunan da aka rubuta mata Afzal ya sai sannan suka koma gida inda Afzal ya d’auketa ya kaita ciki, a kan gado ya kwantar da ita sannan ya fad’a bayi yayi wanka ya sirka mata ruwan zafi bayan ya fito ya taimaka mata tayi wankan itama sannan ya shirya ta tsaf ya shirya kansa shima. Gabad’aya ya rasa nayi ga kukan da Amal take tayi masa tun d’azu da k’yar ya samu ta hak’ura ta daina. Wayansa ya d’aga ya kira Nazeefah amma layin a kashe yake cewa, na Mummy yayi trying nan ma switched off dama yasan za’ayi haka yasan Mummy zata kashe wayanta sannan tasa Nazeefah ma ta kashe nata don kar Daddy ya samu ya same su. Ummi ya kira next ya tambayeta ko tana gida inda ta jaddada masa eh. Key’n motansa kawai yaja ya k’arisa kan Amal da ke ta jan numfashi.
“Rania you’re sick, enough already please kukan ya isa haka.”
“Zaka fita ne?”
“Zanje gun Ummi zan dawo yanzun kinji? Akwai abinda kike buk’ata?”
Kai ta kad’a masa yayinda ya janye mata bargo ya rufeta da kyau, peck ya sauk’e mata akan goshi “Rest okay? I’ll be right back I love you” nan ma kai ta gyad’a masa sannan ya fice. Bada dad’ewa ba Amal ta mik’e zaune, a sannu a sannu take takawa ta d’auko akwatinta., bata da k’arfin ko sisi ta shiga fiddo da kayakinta tana shiryasu cikin akwatin nata bayan ta gama had’a kayakin nata ta sanya hijabi ta d’au wayanta ta fito waje. Kaman Afzal yasan abinda take shirin yi yasa key ya rufe k’ofan ta waje. Mey gadi na ganin ta fito yayi sauri ya je ya sameta.
“Hjy lafiya?”
“Ka tayani jan akwatin waje dan Allah.”
“Direba na gida ko in mishi magana ne?”
“A’a barshi kawai ka tayani kaja mun kayan nawa waje.” Amsan akwatin yayi sun kai dab bakin k’ofan suka iske a rufe ta waje.
“Ya lafiya?” Amal da har jiri ya soma d’ibanta ta tambaya.
“Hjy kaman Alhj ya rufe k’ofan ta waje.”
“Ya rufe k’ofa kaman ya? Bakada makulli ne?”
“Ya amsa kafin ya fita” ya amsa a takaice.
“Bakinku d’aya ko?”
“Wallahi Hjy ni Alhj be sanar dani komai ba face cewa da yayi in basa makulli na.”
STORY CONTINUES BELOW
“Ka bud’e min k’ofan nan.”
“Hjy wallahi ba makulli a hannu na.”
“Ka d’auko key ka bud’e mun k’ofan dan Allah ka bud’-” tana cikin magana kawai ta sulale k’asa saboda jiri. “Hjy!” Mey gadi ya sa ihu nan driver dake ciki ya fito mey ze gani jikin Amal kwance a k’asa.
“Adamu meya faru? Mey kayi mata?”
“Wallahi ban yi mata komai ba dan Allah ka nemo waya ka kira Alhj bai jima da fita ba.” Nan da nan Driver ya shiga neman Afzal a waya lokacin har Afzal ya isa gida an bud’e masa gate sauran kawai ya shiga sega kiran Driver ba 6ata lokaci ya d’aga “Alhj ka dawo gida akwai matsala, Hjy ta sume.” Ko amsa sa beyi ba yayi reverse, tuk’i yake kaman a sama yake tafiya. Nan danan ya iso gida yayi parking bakin k’ofa ya k’arisa ciki. Har anan su Adamu mey gadi basu ta6a Amal ba gudun da suke kar yin hakan ya haifar da wani matsala.
“Kan Amal ya k’arisa da sauri yana tapping fuskanta. Ashe ba sumewa tayi ba jiri ne ya d’ibeta. Be 6ata lokaci ba ya cicci6eta yayi d’aki da ita inda ya sauk’eta kan gado. Lamban abokinsa ya kira da ya turo masa family doctor’nsa bayan nan ya koma kan Amal.
“Lily meyasa bakiya jin magana ne? Seda na fad’a miki ba inda zaki amma kika k’i ji? Ina kike so kije?”
“Yaya zaman mu ya haramta” kad’ai ta iya ce masa cikin wahalallen murya.
“You’re not the one to decide Amal, so kike ki kashe kanki ne? Dan Allah karki sake yin haka stay here until you get better.”
“Just take me home Yaya.”
“Amal this is your home please.”
“No Yaya.”
“Ya isa haka just keep quiet bakida lafiya in kika samu sauk’i zamuyi magana.” Zama ya cigaba da yi akanta har seda likitan ya k’araso ya dubata inda ya d’aura mata ruwa yakuma jaddada wa Afzal cewa kar ayi wasa da magunanta sannan kuma tana cin abinci sosai bayan nan ya koyawa Afzal yadda ze sake sa mata ruwa idan ledan da aka had’a d’in ya k’are. Har waje Afzal ya rakasa ya sallamesa sannan ya taho ciki ya koma kan Amal. Hannu ya aza akan goshinta yana shafa kan gashin da ya sauk’o har kan wajen a hankali, “Yaya what of Nazeefah? Ka sake ji daga gareta?”
“Rania please, ki bar zancen Nazeefah forget about everything lafiyanki ne a gaban mu yanzu kinji?” Ba dan tana so ba ta gyad’a mar kai.
“Nasan kina jin yunwa mey kikeso kici?”
“Bana jin yunwa Yaya I lost my baby.”
“I know Rania and I’m sorry in shaa Allahu me ceto ne.”
“Yaya I lost my baby” kawai ta rushe da kuka. Hak’uri ya shiga bata amma takasa hak’ura, da k’yar ya samu ya shawo kanta kukan nata ya lafa “Yaya baka tunanin cikin nan ya zube ne saboda k’arshen zaman mu yazo? Acikin sauk’i zamu iya rabuwa da juna tunda babu rabo a tsakanin mu yanzu, Allah na sonmu ne shiyasa yasa cikin nan ya zube saboda guje mana abin kunya da yake, dan Allah ka kaini gida.”
“Rania har se zuwa yaushe ne zaki gane cewa kece ruhi na idan bake kuma bazan iya rayuwa ba?”
“Yaya I’m sorry amma ba abinda zamu iyayi, k’addarace rubucacciya dole mu rabu da juna.”
“Ina son da kike ikirarin kina yi mun Amal? Ashe har Allah ze kawo rananda zaki k’wad’aici rabuwa da ni? Ashe Allah ze kawo rananda zaki tafi ki barni?”
STORY CONTINUES BELOW
“Yaya ba haka bane, kai kanka shaida ne game da irin soyayyar da nakeyi maka but that still isn’t enough, taya zan cigaba da had’a miji d’aya da k’anwata? Shin akwai abu mafi muni irin wannan? Yaya idan har Nazeefah k’anwata ce da wani idon kake son in sake kallonta? Yaya wannan wani irin abin kunya ne?”
“I’m aware of all that Amal kuma idan har da akwai wanda zefi jin kunya acikin mu duka nan toh nine, ya Rabbi I married two sisters and slept with both of them ni nafi kowa abun kunya but I still don’t care as long as you’re willing to stay with me.”
“How Yaya? Wani 6angaren zaman mu ya haramta ne ka kasa fahimta har yanzu? Baze yiwu ba ni kawai ka kaini gida.”
“I don’t care Amal!” Ya sanar da ita a tsawace ba tare da yasani ba. A sanadin haka ta firgita se kuma be ji dad’i ba, hannunta ya d’aga ya rik’e acikin nasa “Look I’m sorry but please ki daina cewa auran mu ya haramta Amal I beg you please.” Hawaye na gangara daga idanta ta gyad’a masa kai “In had’a miki kunun ki kisha?” Nan ma kan ta kuma gyad’a masa “Kafin nan ka kira Mami ka sanar da ita banida lafiya.”
“Is this what you really want Rania? Ko so kike idan ta taho ki sanar da ita gaskiyan al’amarin dake faruwa saboda ta d’aukeki ta tafi dake?”
“Yaya-” katseta yayi da wuri “Please Amal don’t leave me, abinda yake faruwa already ya riga ya mun yawa, I just found out I’m marrying two sisters, after that kin samu miscarriage, mun rasa future’n mu, I don’t know ko addini na ze haramta min ku duka ko ze bani za6i in d’auki d’aya, I’m so confused akan hakan kuma kike son ki sake tafiya ki barni? Shin ya kike son in rayu Amal? Dan Allah ba don ni ba koda bana nan kar ki d’au waya ki kira Mami I beg of you.”
Na matuk’a ya bata tausayi, tasani tashin hankalin da take ciki kad’an ne a ganga da nasa amma saboda san zuciya se su take abinda Allah yace suyi zaman haramun? Tana sonsa, son da bata tunanin zata ta6a daina iya yi amma rabuwa ne ya zama dole. Ba don tana so ba sedon yadda ya bata tausayi ta gyad’a masa kai “I’m sorry.”
“I dont want you to be Rania, kawai kiyi mun alk’awari bazaki kira Mami ko Papi ba, idan lokacin yazo ni da kaina zan kirasu in sanar dasu komai da kaina I just need time to sort out things. Promise me okay?”
“I promise” ta amsa tana gyad’a masa kai. Peck ya sauk’e mata a kumatu sannan ya fice nan da nan ya had’a kunun ya kawo ya bata da kansa da ikon Allah kuma tasha sosai sannan ya 6allo mata magunanta ta had’iye ya sake miyar da ita ya kwantar da ita. Be bar wajen ba seda ya tabbata baccinta yayi nisa. Duban agogo yayi yaga Maghrib har ya wuce nan da nan ya idar ya shige mota ya fice gida bayan kunnen da ya ja wa mey gadi cewa komin yaya kar ya bar Amal ta fita ga k’ofa ya bar musu a bud’e saboda fita masallaci.
Sannu da zuwa Ummi dake ta jiransa tun d’azu tayi mai sannan ya samu gu ya zauna a gefenta sede kallo d’aya tayi masa ta fuskanci yana cikin damuwa ga fuskansa daya nuna cewa yayi kuka.
“Prince lafiya?”
“Ummi Alhj Abdallah ba mutumin kirki bane.”
“Ai dama sanda Abbanka ya fad’a maka ka sauwak’e wa ‘yarsa kawai a rabu dasu lafiya kak’i ji, shin yanzun mey yayi maka? ‘Yan unguwa ya tara suka ma duka ko mey?”
“Idan da dukan nema ai da da sauk’i.”
“Meyayi ma toh?”
“Ummi Nazeefah and Amal ‘ya’yansa ne they’re half sisters.”
“What?”
STORY CONTINUES BELOW
“Alhj Abdallah ne mahaifin Amal, Matana ‘yan uba ne Ummi shine mahaifinsu duka.”
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un shin Afzal ka san mey kake fad’i ma kuwa? ‘Yan uwa fa kace?”
“Ummi dan Allah ki taimakeni Ummi bazan iya rayuwa ba Amal ba.”
“Hasbunallahu wa ni’imal wakeel kace mey? Amal ‘yar Alhj Abdallah ce? Yau na shiga uku na lalace Prince! Ya akayi hakan ya faru? Ta ina Amal ta zama d’iyarsa?”
“Bana baki labarin Mami ba? Yadda akayi ta samu cikin Amal?”
“Tabbas.”
“Toh mahaifin Amal d’inne Alhj Abdallah shine yayi ma Mami aika-aika ya gudu basu sake ji daga garesa ba.”
“Yau wannan wace irin rayuwace? Wace irin mumunar k’addara ce wannan? Innalillahi yanzu Alhj Abdallah yasan yaran nan ‘yan uwa ne amma be ta6a yin magana ba se yanzu?”
“Cewa yayi shima recently yayi finding out gaskiya.”
“K’arya yakeyi idan ba haka ba har ya akayi yasan Amal d’in ‘yarsa ce.” Labarin komi ya kwashe ya bata Ummi kam se salati kawai take ta kasa yarda da komi da Afzal ya fad’a se gani take kaman mafarki ne. Ta ina zasu fara 6ullo ma wannan al’amari yanzu?
“Yanzu Amal ta sani?”
“Nayi kuskuren fad’a mata as a result ta samu miscarriage Ummi mun rasa baby’n namu.”
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un wai shin meke faruwa ne yau? Cikin Amal ya zube fa kace?”
“Ya zube Ummi yanzu haka tana kwance a gida likita yazo ya dubata ya sa mata ruwa akan hakan kuma take cewa zata koma gida, Ummi Amal na shirin tafiya ta barni ya zanyi da raina ba d’a ba Amal ba Nazeefah haukacewa kukeson inyi ne?” Ba shiri ya rushe da kuka. Hak’uri Ummi ta shiga basa yayinda kanta yagama d’aukan zafi itama, ta rasa ta ina zata fara 6ullo ma wagga al’amari ba abinda yafi k’ona mata rai kaman lalacewar cikin nan na Amal, amma kam Alhj Abdallah anyi mutumin banza. Ace duk zamanshin nan yana da ‘ya a waje?
“Ya isa haka Afzal crying is never a solution ka jira idan Abbanka ya dawo musan nayi.”
“I can’t wait for that long Ummi, Amal bata da lafiya she needs to be taken care of zan koma gida.”
“Afzal kayi hak’uri amma dole Amal ta koma gida.”
“Kema kin goyi bayan ta tafi kenan Ummi? Please don’t ku tausaya mun.”
“Bawai ina nufin ta tafi har abada bane Afzal, ina nufin taje gida na d’an lokacin nan ta samu kulawa mey kyau daga gun Mami saboda kaima ba hankali a jikinka yanzu bale ka iya kula da ita kai kanka kana neman kulawa.”
“Ummi I can take care of her, zan kula da ita ni kawai kibar zancen mayar da ita gida please.”
“Toh Prince amma dey kasani koda bata koma yanzu ba zata koma wataran ko?”
“Mey kike nufi Ummi?”
“Afzal har ka manta da cewa ya da k’anwa kake aura ne? A ina aka ta6ayin hakan? A ganina kaman yadda Amal ta sanar da kai hakan ne aure tsakaninka da dukansu ya haramta.”
“No Ummi please there has to be a way, zamu nemi Malami muyi tambaya in shaa Allahu ze san yadda zeyi damu.”
“Prince don’t get your hopes high.”
“”But Ummi I can’t lose both of my wives ko za6i akace inyi bazan iya ba bale kuma in rasasu duka. A tunani na idan suda kansu suka amince zasu cigaba da zama as kishiyoyi regardless they’re siblings se mu cigaba da zaman mu tunda a zamanin da ma ana had’a ‘ya’yan Annabi Adam da Hauwa’u aure.”
“Ya kake magana haka Prince? Kai yanzu baka ji kunya ba da gaskiya ya fito? An san ba laifinka bane amma ai da kunya Prince, wa da k’anwa ne fa. Kar ka bari son zuciya ya rufe maka ido ka aikata haramun, tun wani zamanin aka daina had’a jini d’aya aure? Kuma a tunaninka su d’in zasu amince au cigaba da zama tare ne yanzu bayan gaskiya ya fito? Wallahi a’a zafin kishi ma baze bar su ba.”
“Ummi ya zanyi toh? Wallahi muddin kuka bari aka rabani da Amal toh nima kuyi shirin rasani because I can’t do without her.”
“Nazeefah kuma fah?”

“Ya Salaam! I don’t know! I really don’t know Ummi amma bazan iya jure rashinsu duka ba because I love them both ko za6i akace inyi bazan iya ba.”

“Rabuwa da d’ayansu ko dukansu ya zama dole Prince kai kanka ka sani.”

“Bazan iya ba Ummi gara ni in mutu da in rasa d’aya daga cikinsu.”
Nauyayyen ajiyan zuciya ta sauk’e yayinda take tausaya wa d’an nata tabbas yana cikin tsaka mey wuya “Yanzu ka kwantar da hankalinka ka koma gida d’in kaje ka samu Amal tunda bata jin dad’i gobe in shaa Allahu zan shigo.”

“Allah kaimu” ya amsa.
“Yauwa nace su Mami fa ka sanar dasu?”

“Banyi ba tukuna but I’ll.”

“Ya kamata.”

“Ummi tsoro nake kar suce zasu rabani da Amal.”

“Baza suyi hakan ba in shaa Allah, kaide ka kwantar da hankalinka ka kuma sa a ranka cewa komin meya faru shine mafi alkhairi a gareka.”+

“Thank you Ummi bari in koma.”

“Muje in raka ka.”

“A’a ba amfani yi zaman ki” nan ya fice ya nufi motansa inda ya zauna ciki yana tunani, gabad’aya ya rasa mey ke masa dad’i. Wayansa ya zaro daga aljihu ya sake trying layin Nazeefah luckily seya shiga sede yana soma ringing aka katse cike da hanzari ya sake gwadawa wanda nan ma aka kuma katsewa. Kansa ne ya d’aure yana cikin nazari sega sak’o nan ta tura mai;
_I’m sorry I can’t pick up your call, don’t worry we’re all fine._
Take yayi replying nata da;
_Alhamdulillah then, where are you at?_
Cikin minti d’aya reply nata ya iso
_Mummy ta kama mana d’aki a hotel zamuyi magana gobe goodnight._
Ajiyan zuciya ya sauk’e atleast they’re safe, ko bey tambaya ba yasan Mummy ce ta hanata sanar dashi inda suke saboda gudun kar Daddy yayi saurin ganosu. Oh Allah!
Key yasa ya kunna motan ya dawo gida. Har anan bacci Amal ke, kayan jikinsa ya rage sannan ya duba ledan ruwan nata yaga da ragowa, gadon ya haye ya sameta inda ya kwanta a gefenta had’e da aza kanta a k’irjinsa wanda a sanadin hakan ta farka.
“Shhh go back to sleep it’s just me” ya sanar da ita yana shafa bayanta a hakan har ta sake komawa baccin. Shi kam se tuna abinda Ummi ta fad’a masa yake _Rabuwa da d’ayansu ko dukansu ya zama dole Prince kai kanka ka sani._
Wajajen tara da rabi ya farka bayan yayi alwala yayi sallah ya zarce kitchen ya kad’a wa Amal kununta sannan ya dawo ya shiga tayar da ita. Taimaka mata yayi ta wanke bakinta sannan ya bata kunun da kansa bayan nan ya 6allo mata magunanta ta had’iye.
“Wa zaka kira?” Amal data k’ura masa ido ta tambaya ganin ya d’ago wayansa.
“Ummi, tace in kin tashi in had’aku ta gaisheki da jiki” bata sake cewa komai ba har se lokacinda Afzal ya had’asu suka gaisa. “Mami fa yaushe zaka kira su?”

“Zan kira su Amal amma ba yanzu ba.”

“Se yaushe Yaya?”

“Meyasa kika k’osa in kirasu Lily? Didn’t we talked about this?”

“Yaya I’m sorry I jus-“

“Ya isa please you’re sick don’t stress yourself. Zaki watsa ruwa?” Kai ta kad’a masa zalla sannan ya mik’e ya ciro mata kayan baccinta ya taimaka mata tasa. Bayan ta kwanta ya d’aura mata sabon ledan drip d’in sannan suka kwanta. Washegari kaman yadda Ummi tayi alk’awari tazo ta gidansu da breakfast mey kyau da kuma kunun Amal da ta dama mata cikin flask. Har cikin d’aki ta shigo suka gaisa da Amal sannan suka dawo parlour ita da Afzal.
STORY CONTINUES BELOW

“Na sanar da Abbanka halin da ake ciki jiya.”

“Meyace?”

“He was also shocked and disappointed at his friend mun kuma samu mun tambayi Malamai har biyu mun kuma samu amsa iri d’ai daga garesu.”

“Mey suka ce Ummi? Zan iya ajiye su duka?”

“Kai ma kasan hakan ba mey yiwuwa bane Prince.”

“Innalillahi! Then mey suka ce? In rabu dasu duka?”

“Sunce ya zamo dole ka d’au d’aya ka saki d’aya.”

“What? So kuke in za6i d’aya daga cikin Amal da Nazeefah?”

“Yes Afzal.”

“Ta yaya Ummi? Taya kukeson in d’au d’aya in saki d’aya? Shin idan nayi hakan nayi adalc kenan?”1

“Abinda yazo a shari’ance kenan, so sakan d’ayan su ya zamo dole idan har zakayi abinda addininka yace.”

“No Ummi there has to be another way. Bazan iya za6an d’aya daga cikinsu ba I love them both yaushe ne zaku fahimci hakan? Is like choosing between air and lungs I can’t because I need both to survive.”

“Ya zama dole ka d’au d’aya acikinsu Afzal.”

“No Ummi I can’t!”3

“Yes you have to, dubi nan” wayanta ta bud’e ta shiga kan sak’on da malaman suka turo musu bayan tambayan da sukayi inda ya shiga karancewa tun daga farko kaman haka;

arfrur
8442: Is it permissible to marry two sisters from one father at the same time?
A man has 2 wives and from each wife he has 1 daughter. Is it permitted for someone to marry the 2 daughters at one time (who of course have the same father but different mothers)? I am aware that it is not permitted to be married to 2 blood sisters at the same time, but is the case mentioned above slightly different?
Published Date: 2000-05-01
Praise be to Allaah.
It is not permissible to marry them at the same time, because they are sisters, regardless of whether they share the same father and mother, or they have only one parent in common, because of the aayah (interpretation of the meaning):

“Forbidden to you (for marriage) are: … two sisters in wedlock at the same time, except for what has already passed” [al-Nisaa’ 4:23]

It was reported from Abu Hurayrah that the Messenger of Allaah (peace and blessings of Allaah be upon him) forbade marrying a woman then her paternal aunt, or a paternal aunt then her brother’s daughter, a woman then her maternal aunt, or a maternal aunt then her sister’s daughter, or an older sister then the younger sister, or a younger sister then the older sister.” (Narrated by al-Tirmidhi, no. 1045; Abu Dawood, no. 1768. Al-Tirmidhi said, it is hasan saheeh).

Fayrooz al-Daylami said: I came to the Prophet (peace and blessings of Allaah be upon him) and said: O Messenger of Allaah, I have become Muslim and I am married to two sisters. The Messenger of Allaah (peace and blessings of Allaah be upon him) said: “Choose whichever of them you want [i.e., and divorce the other].” (Narrated by al-Tirmidhi, 1048; Abu Dawood, 1915, et al.)

_A hausance_
[Shin ya halatta namiji ya auri mata biyu wadanda suka kasance ubansu daya a lokaci daya?]

[Mutum ne ya kasance yana da mata biyu kuma daga kowacce mace yana da d’ya guda d’aya da ita. Shin ya halatta namiji ya auri yaran nan da suke uba d’aya a lokaci guda? ( wad’anda suka kasance ubansu guda amma kowacce da mahaifiyarta)?

STORY CONTINUES BELOW

Bai halatta namiji ya auri mata guda biyu da suka kasance yan’uwan juna ba maana yan’uwa na jini da ya kasance ubansu guda]
[Sai dai idan case din da aka ambata yasha banban da wannan ne?]

[Allah ne mafi sani]

[Ya haramta ga namiji ya auri mata biyu da suka kasance yan’uwan juna na jini koda kuwa uwa kawai suka had’a ko uba kawai suka had’a ko kuma uwarsu d’aya ubansu d’aya saboda fad’ar Allah madaukakin sarki a cikin Al-Qur’ani mai girma.]

[An haramta maku (game da aure) ka auri mata biyu yan’uwan juna na jini a lokaci guda, sai dai abinda ya riga ya wuce na baya.
(Suratun Nisaa’ee 4:23)]

[An kar6o daga Abu Hurayrah daga manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace; an haramta ma namiji ya auri mace Sannan ya auri gwaggonta ta dangin uba, ko ya auri Gwaggon mace ta dangin uba sannan ya auri d’iyar k’ani/wanta.]

[Ko ya auri mace Sannan ya auri k’anwar innarta ta dangin uwa ko ya auri k’anwar inna sannan ya auri d’iyar K’anwa/yarta.]
[Ko ya auri Yaya Sannan ya dawo ya auri K’anwa.]
[(Al-Tirmidh N01045 da Abu Dawood N0 1678 ne suka ruwaito shi. Al-Tirmidh yace hadith ne mai kyau ingantacce)]

[Fayrooz Al-Dalaylami yace” Nazo wajen manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi sai nace “ya manzon Allah na musulunta amma kuma ina auren mata guda biyu yan’uwan juna na jini ( a lokacin daya auresu yana kafiri ne baisan hukuncin yin hakan ba) sai manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yace; “ka za6i wadda tayi maka a cikinsu sai ka saki dayar”]

[Abu Dawood N0 1915, Al-Tirmidth 1048 da sauransu suka ruwaito shi.]

“Kaga anan tunda kaima a bisa rashin sani ka auri Nazeefah tukun kazo ka auri Amal, se Malamai sukayi amfani da wannan hadisi sukace kai ma zaka d’au d’aya ne ka saki d’aya tunda ba ba tare da sani ba ka auresu ba, da ace da gan-gan kayi hakan saboda son kai se ya zammana duka biyu sun haramta maka. Amma tunda ba da sani bane se aka baka za6i, kaga fa ba’a ce lalle se ka saki Amal ka zauna da Nazeefah ba saboda Nazeefah ce uwar gida, kuma ba’a ce lalle seka saki Nazeefah ka zauna da Amal ba saboda Amal ce babba. Za6i suka baka kaman yadda Annabin Rahama ya bawa wancan mutumin shima.” Ummi ta sake yimar bayani.
Shiru yayi zaune a wajen yayinda zuciyansa yake yi masa wani irin k’una, ina ma ace ba a ta6a k’addaro masa da rana irin ta yau ba? Ina ma ace shi kam mutuwa kawai zeyi ya zamanto ba seya za6i Amal ko Nazeefah yabar d’aya daga cikinsu ba. Shin yanzu idan ya saki Amal yabar Nazeefah yayi wa Amal adalci kenan? Kokuwa idan ya saki Nazeefah yabar Amal yayi wa Nazeefah adalci? Wa ze d’auka wa kuma ze bari a cikinsu?

“I can’t do this Ummi dan Allah karku tilasta mun” ya sanar da ita daga bisani.
“Kayi hak’uri Prince kowa yasan da zafi da ciwo amma dole ne muyi amfani da abinda shari’a ya kawo mana saboda gudun 6acin ran Ubangijin mu kuma kasani fa inna ma’al usri yusrah, kowani musiba na tare da sauk’i. Take for instance yanzu ace duka Amal da Nazeefan ne suka haramta maka ya zakayi? Amma seka duba privilege da addininka yayi maka na halatta maka d’aya acikinsu kayi godiya wa mahaliccinka.”

“Hakane Ummi But wa zan d’auka wa zan bari?”1

“This is not my decision to make Afzal, ka zauna kayi tunani in shaa Allahu zaka samu amsa ga wannan tambaya, idan kuwa hakan ya gagara se kayi istikhara, babu sharri acikin za6in Allah duk wacce tafi kwanciya maka a rai itace za6in ka seka ajiyeta ka sauwak’e wa d’ayar, ba wanda zeyi maka mumunar fahimta. Batun iyayen Amal kuma ka tabbata ka kirasu yau kokuwa kaje ka samesu ka sanar dasu halin da ake ciki hak’k’insu ne su sani, Allah shige ma gaba.”

STORY CONTINUES BELOW

“Ameen” ya amsa da k’yar bakinsa yana rawa.
“Ni bari in koma se anjima” bayan ficewanta Afzal da kowani ga6a da sassan da suke jikinsa sun mutu sunyi lis ya mik’e a kasalance, a corridor’n d’akinsu ya tarar da Amal tsaye wajen se kuka take shark’af-shark’af. Wani irin tsinkewa gabansa yayi bade taji duk abinda shida Ummi suka tattauna akai ba? Innalillahi wa inna ilaihi raji’un.
“Amal?” Ya kira sunanta da hanzari ta juya mai baya ta k’arisa cikin d’akin bata kai ga rufe k’ofan ba ya hankad’e ya fad’a ciki. “Amal please stop crying” ya buk’aceta cikin sanyin murya yayinda yake k’ok’arin rik’o hannunta sede ta hanasa.
“Amal please enough ke baki san kukan nan rashin lafiya ze k’ara miki ba?”

“One of us have to go Yaya” ta fad’a tana mey share abinda yace mata.
“Amal-“

“Dole ka rabu da d’aya tsakani na da ‘yar uwata koba haka ba?”

“Am-“

“Just answer me Yaya na riga naji komai.”

“Yes Amal amma dan Allah ki kwantar da hankalinki.”

“Tayaya? Tayaya kake tsammanin zan iya kwantar da hankalina Yaya bayan ina shirin rasa mijina mafi son komai a rayuwata? Mijina wanda na d’au mutuwa ce kad’ai zata iya raba mu? Mijina da na d’au shine mahaifin yaran da zan haifa? Wanda farin cikin rayuwana ya dangana a jikinsa? Ta ina hankali na yaga ta kwanciya Yaya? I’m about to lose you, I’m about to lose the love of my life, my soul, my spirit, and my everything!” Kawai ta fashe da wani irin kuka. Tsan-tsan tausayi Afzal be san a lokacinda hawaye suka ciko masa a ido ba, ashe itama Amal haka take sonsa kawai bata nunawa ne? Ashe tana iya shiga damuwa idan har rabuwa ya shiga tsakaninsu? Ya d’au shi kad’ai ze sha wuya a rashinta ashe itama rayuwanta na iya fad’awa gwagwarmaya a rashinsa wow!

“Amal please enough kibar kukan haka.”

“Wa zaka d’auka acikinmu Yaya?”

“Amal please-“

“Just answer me Yaya” ta katsesa cike da tashin hankali “Just answer me please.”

“I don’t know Amal saboda I can’t choose, kaman yadda bazan iya jure rasa ku duka ba haka ma bazan iya d’aukan d’aya in bar d’aya ba. I love you both, I really do.”

“But one of us has to go, baka ji abinda Ummi tace bane?”

“I know I just… I just don’t know ni kawai kibar kukan nan.”

“Bazan ta6a iya daina kuka akanka ba Yaya because I love you, I love you so damn much shiyasa rabuwa da kai yake min zafi, gani nake kaman idan na rasaka nima ina iya rasa nawa ran” da sauri ya katseta “But Amal you’re not going to lose me bance Nazeefah zan d’auka in bar kiba.”

“I don’t know Yaya, ban sani ba ko Nazeefah zaka d’auka akaina but I just want you to know that my everything revolves around you, I don’t think bayan kai zan iya kwad’aita wa zuciyata son wani d’a na miji because my heart is with you Yaya, I can never stop loving you” ta k’are tana kuka. A nitse ya rik’o hannunta maras canular cikin nasa yana murzawa a hankali “And I can never stop loving you too Amal I’m not picking Nazeefah over you kema kin sani.”1

“But one of us has to go.”

“Se kuma aka ce kece zaki tafi? Kin manta cewa zuciyana baya bugawa se ya ji ki a kusa dashi? Kin manta cewa without you I’m nothing? kin manta cewa ke kad’ai ce hasken da nake buk’ata a rayuwa na da kuma Iskan da nake buk’ata dan in rayu? Kin manta da duka hakan ne Amal?”

STORY CONTINUES BELOW

“Not for once did I forget any of these Yaya saidai a wannan hali da muka tsinci kanmu yanzu nake ganin soyayyar mu ma tayi kad’an ta ceto mu daga cikinsa.”

“Meyasa kika ce haka Amal? I thought our love for one another was enough.”

“I’m sorry Yaya but it isn’t.”

“Amal it is because I’ll never leave your side, I came into your life to stay forever not just for some time because I love you, I love you Amal morethan anything you could ever imagine.”

“And I love you too Yaya, morethan life itself. Your love is incomparable amma rabuwa ce ta zamo dole.”

“Ba se mun rabu ba Amal dan Allah kibar cewa haka.”

“Dole ne in fad’i haka Yaya, dole ne mu cire son zuciya muyi abinda ya kamata.”

“Mey kike nufi?”

“Ina nufin Nazeefah. Nazeefah k’anwatace Yaya kuma komin yaya ina sonta komin mey tayi mun I’ll always want the best for her. Kai kanka kasan irin son da Nazeefah keyi maka, ka kuma san cewa akan ka Nazeefah na iya yin komai, bazan so ace a matsayina na ‘yar uwarta kuma yarta ba na shiga tsakaninta da masoyinta. I don’t care ko ita bata feeling thesame way I feel towards her, ban damu ko tana so na ko bata sona ba, ban damu koda nice mak’iyar ta a duniyan nan ba as long as she’s my sister I’ll love her and want only the best for her, this is why I’m giving up on you for her.”1

“Amal kin kuwa san mey kike cewa?” Afzal da mamaki ya rufesa ya tambaya.
“Yes Yaya, ina sonka amma hakan ba wai na nufin zan cigaba da mallakanka bane, na yafe soyayyar ka wa k’anwata na hak’ura ni ka sauwak’e mun ku kucigaba da zama tare, seeing my sister happy is enough to make me happy.”

“I can’t Amal” ya amsata a raunane “Bazan iya rabuwa dake ba, bazan iya ba.”

“Zaka iya Yaya, ni kaina nasan how hard life will be for me without you amma ba komai mukeso a duniya muke samu ba, wani sa’in dole muyi making sacrifices koda kuwa akan abunda muka fi so ne it is why I’m doing this. I love you but I have to let you go.”

“No Amal dan Allah kibar cewa haka, you’re not leaving me you’re not.”

“Yes I am Yaya, you have to let me go.”

“No I can’t I can’t live without you.”

“Idan baza ka iya rayuwa ba ni ba Nazeefah kuma fa? Mey zakayi da ita?”

“I don’t know Amal, but I can’t afford to lose you.”

“Kaman yadda kake jin bazaka iya rabuwa dani ba itama Nazeefah haka take ji Yaya, haka take jin bazata iya rabuwa da kai ba. Ka fini sanin yadda take sonka let’s do this for her kar mu bari sharrin laifin Daddy ya fad’a kanta.”

“Ke kin amince ya fad’a a kanki kenan Amal? Keda Daddy yafi cutarki da mahaifiarki?”

“Yes Yaya na hak’ura hakan ya fad’a akaina saboda InnAllaha ma’as sabireen I’m sure Allah will listen to my silent cries and see me through.”

“But I can’t Amal, bazan iya jure ganinki cikin bak’in ciki da k’unci ba kullum. Kece aka sameki ta haramtacciyar hanya, kece kika girma ba uba, kece kikayi girma cikin talauci bayan kaman yadda Nazeefah tayi girma cikin kud’i da kulawa da jin dad’i kema kin cancanci hakan amma haka akayi depriving naki, bayan nan kece kikazo aure kina ji kina gani aka rabaki da masoyinki na asali aka sanya ki aurena na dole dukda bakiya so. For all your life you’ve never been happy-“

STORY CONTINUES BELOW

“But you made me happy Yaya” tayi saurin katse sa da murmushin takaici d’auke a fuskanta “zan iya cewa ranakun da na zauna da kai sune mafi farin ciki da murna a rayuwa na gabad’aya, the happy moments I’ve spent with you have erased every single bad day I’ve witnessed before and I’m morethan thankful to God, I cannot ask more for more. You gave me only the purest form of love, koda Papi ya sanar dakai asalina baka k’i ni ba, baka k’iyamace ni ba infact sema k’ara nuna mun so da kayi. You loved me as if your life depended on it, ka bani kulawan da bayan Mami da Papi ba wanda ya ta6a bani irinsa, your love was simply enough for me Yaya so karka damu dani, I’m morethan satisfied.”

Be iya ya sake cewa komai ba kawai tuna kalaman Nazeefah yake da take cewa _No Daddy, bazan rabu da Ya Afzal ba idan ma akwai me rabuwa da Ya Afzal toh Amal ce not me_ shi kansa ya sani baza a ta6a had’a halatayyan Amal dana Nazeefah ba, they’re two different people. Idan akwai kalma d’ayan da Nazeefah ta sani wanda Amal bata sani ba shine ‘Son Kai’ ko shi baze iya yin abinda Amal tayi ba yanzu. Janta yayi jikinsa kawai ya rungumeta yayinda ta kuma rushewa da wani kukan tsuma zuciya. Kukan ta cigaba da yi ajikinsa yayinda ya rik’e ta tsam a jikinsa, seda tayi mey isarta sannan ya d’agota ya shiga share mata hawayen nata inda ya jata bakin gadon ya kwantar da ita had’e da sa mata sabon ledan ruwan. “Rest okay?”

Kai zalla ta gyad’a masa be kai ga mik’ewa ba wayansa dake aljihu ya shiga ruri dubawanda zeyi yaga Nazeefah, ba tare da 6ata lokaci ba ya d’aga “Nazeefah?”

“Na’am Ya Rouhi ina kwana?”

“Lafiya ya kike? Ya su Mummy?”

“We’re all good.”

“Wani hotel kuke? I need to see you.”

“Deribe Hotels” ta sanar dashi.
“I’ll come pick you up okay? Tell Mummy ni nace zan zo in d’aukeki.”

“I’ll seka zo.”

“Yauwa ba-bye.” Nan ya katse tare da kewayowa kan Amal data k’ura masa ido. “Zanje gida gun su Mami domin sanar dasu halin da ake ciki okay? Daga nan inje in duba Nazeefah.”

“Allah ya kare.”

“Ameen I love you” ya sanar da ita had’e da sauk’e mata peck a goshi sannan ya mik’e ya fice bayan ya ja wa mey gadi kunne akan cewa komin yaya kada ya bar Amal ta fita. Daddy yayi ma waya yace yaje ya samesa a gidan Nazeefah sannan ya wuce Deribe hotels yaje ya d’auko Nazeefah inda suka nufi gidansu Amal. Nazeefah da bata san ina yake kai su ba se tambayan sa take ina ne nan, shi de iyaka ce mata yayi ze d’au wasu mutane ne shikenan. Ciki ya shiga suka gaisa da su Papi inda yake sanar dasu cewa Amal tayi 6ari bata da lafiya yazo ya d’aukesu ne suje su dubata. Cikin k’ank’anin lokaci suka shirya suka fito, sanin halin Nazeefah ba lallai ne ta yarda ta koma baya haka kawai ba se yayi mata k’aryan cewa Papi d’an uwansa ne Mami kuma matarsa ce don haka tayi hak’uri su zauna da matar a baya se shi ya zauna a gaba. Batayi gardama ba ta samu Mami suka zauna a baya bayan sun gaisa.
Sude su Papi ko da suka ga Afzal ya d’au wani hanya daban bana gidan Amal ba basuyi magana ba. Ahaka har suka isa gidan Nazeefah suka k’arisa ciki. Fitowan da zasuyi daga motan Nazeefah ta hangi Daddy dake zaune akan varenda akan d’aya daga cikin kujerun da aka ajiyesu a wajen.
“Ya Rouhi meyasa ka kawo ni bayan kasan Daddy na nan?”

“Enough Nazeefah we’re here to sort out things.”

STORY CONTINUES BELOW

“Not when Daddy is around take me back to Mummy.”

“Ya isa Nazeefah I know this is not easy on you amma kiyi hak’uri magana kawai zamuyi shikenan.”

“Ni bana so banida sauran abinda zance masa tunda ya had’ani kishi da ‘yar uwata.”

“Nazeefah please” Afzal yayi mata ido wanda hakan yasa tayi shiru.
Na sosai Mami da Papi suka shiga rud’ani domin a iya saninsu de kaman yadda Afzal ya gabatar musu da Nazeefah ce musu yayi ita matarsa ce toh mey take nufi da cewa mahaifinta ya had’ata kishi da ‘yar uwarta? Shin Afzal d’in mata nawa ne garesa?
“Afzal lafiya dai ko?” Papi da ya kasa hak’ura ya tambaya cike da rud’ani.
“Yi hak’uri Papi mu shiga daga ciki Mami, Nazeefah let’s go in.” Har anan Papi da Mami basuga fuskan Daddy ba kasancewar bayan sa ne ke fuskantansu itama Nazeefah dan sanin da tayi masa yasa ta gane shine. Sun k’arisa corridorn kenan Afzal yayi gyaran murya inda Daddy ya juyo idanunsa wanda basu sauk’a a ko ina ba se akan na Papi da Mami. Daga kan kujeran amma sanda yaci tuntu6e kad’an ya rage kujeran be yasar dashi a k’asa ba yasamu ya tari kansa. A rikice ya mik’e tsaye yayinda idanunsa dana Mami suke a had’e har anan, ita kanta Mami dan mamaki ta kasa yin magana haka Papi ma se k’ura wa juna ido kawai suke. Daga bisani Daddy ya kira sunan Mami.
“Jamee?” Da mamaki Nazeefah ta tsaya kallonsa tana mey tambayan kanta ta inda akayi Daddy yasan ‘yan uwan Afzal ‘yan uwan ma ba dangin kusa ba. Tun ganinsu da tayi talakawa ta yanke hukuncin irin dangin nesa-nesa d’innan ne su.
“Khaleefah?” Mami ta ambaci sunansa baki na rawa. Yau shekaru nawa? Sama da ashirin, ashirin da biyu kenan. Ashe dey Allah ze sake had’asu. Ashe de zata sake sanya mutumin daya cuceta ya kuma 6ata mata rayuwa a ido. Nazeefah kam kanta ya gama d’aurewa yanzu se raba ido take.
“Afzal meke faruwa anan? Waye mutumin nan? Meyasa kuma ka kawo mu gidansa?” Papi ya kewayo yana kallon Afzal.
“Mu shiga daga ciki dan Allah zan sanar da ku komai.”

“Papi mu koma” cewan Mami had’e da juyawa. “Ba cikin da zamu shiga.”

Da hanzari Afzal ya sha gabanta “Please don’t walk away Mami, please kar ki tafi.”

“Na d’au cewa kayi Baby tayi 6ari bata da lafiya” Ido Nazeefah ta zaro waje cikin Amal ya zube? Shikenan bata da wata tsoro yanzu, dama cikin nan shine tsoronta, kar don cikin Afzal yace ze d’au Amal akanta. Amma yanzu da ya zube ta tabbata idan ma za6i aka basa acikinsu biyu inhar ma basu haramta masa ba kenan ta tabbata ita za a sanya sa na dole ya d’auka tunda itace uwar gida.
“Yes Mami and ba k’arya nake muku ba I intend to take you to her idan mun gama warware matsalar dake nan.”

“Wace matsala kenan?” Papi ya tambaya.
“Papi wannan shine mahaifin Nazeefah matata.”

“Mahaifin matarka?” Ya kuma tambaya.
“Eh Papi.”

“Ka san mey kake fad’i kuwa Afzal?” Mami da ta kewayo ta jefa mar tambayar “kasan kuwa wannan azzalimin mutumin shine mahaifin Amal?”

“Eh Mami mahaifin Amal kuma mahaifin Nazeefah.”

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” Papi yasa salati. “Jameela yaran nan ‘yan uwa ne” yace da Mami da tuni idanunta suka ciko da hawaye.
STORY CONTINUES BELOW

Nazeefah kam se raba ido take yayinda abun ya tsaya mata a wuya, yanzu Daddy ya rasa da wa zeyi barikanci ma seda irin Mami?
“Mey nayi maka a rayuwa da ka za6i kayi ta k’untata mun haka Khaleefah?” Tace da Daddy da har yanzu be kuma cewa komai ba idonta na tsiyayar da hawaye. “Duk kalan zalunta ta da kayi ka lalata mun rayuwa hakan beyi maka ba seda ka dawo kan ‘yata?” Anan kan Nazeefah ya sake shiga duhu aww wai dama ba karuwar Daddy bace? Tarketa Daddy yayi ya d’irka mata ciki? Oh Allah! Wannan abun kunya da mey yayi kama ace a gaban mijinta ana tuhumar mahaifinta da aikata zina. Ji tayi gabad’aya ya fita mata daga rai bata k’aunansa.
“Jamee-“

“Allah ya isa Khaleefah, Allah ya isa tsakani na da kai.”

“Mami dan Allah kiyi hak’uri mu shiga ciki muyi magana” Afzal yace.
“Wani magana zamuyi Afzal? Ya kama ya had’a ‘yan uwan jini kishi wani magana ne kuma za’a sake yi wanda yafi a sauwak’ewa yaran duka? A tunani na da gan-gan yayi hakan dan ya mayar mun da ‘ya bazawara.”

“Jameelah dan Allah kiyi hak’uri wallahi ban san cewa rabo ya shiga tsakanin mu ba-“

“Dakata Khaleefah” Papi ya katsesa “Bamu buk’aci jin komai daga bakinka ba, mu shiga Afzal muji abinda kake tafe dashi muje Jameela.” Ba don Mami na so ba ta bi bayan Papi suka k’arisa ciki inda Afzal ya bayyana musu halin da ake ciki tun daga kan lokacin da aka bige Amal zuwa lokacinda Daddy yagano gaskiya dama komai, daga k’arshe kuma ya sanar dasu tambayan da sukayi wa malamai da kuma amsan da suka samu. Na sosai hankalin Nazeefah ya tashi, acewarta baza a bawa Afzal za6i ba ita za’a sanyasa ya d’auk’a na dole ashe ba haka abin yake ba. Ita kam ma bata yarda ba. Zata nemi wani Malami tayi mar tambaya ta tabbata za a samu sa6ani tsakanin amsan da Afzal ya samu. In ba haka ba ina zata sa ranta idan Afzal ya za6i Amal akanta? Yau nata ya k’are.
“Tabbas wannan abu da kunya yake da kuma zafi ace ‘yan uba suna auran miji d’aya. Anan Allah yana nuna mana cewa komin yaya mutum yayi baze ta6a iya yi masa wayo ba kuma muddin kad’au alhak’in mutum baka nemi yafiya ba toh tun a duniya Allah ze fara kamaka ya nuna maka illan yin hakan. Saidai ina son ka kwantar da hankalinka Afzal kasani wannan k’addarar bata su Amal ce kad’ai ba no harda kai kaima. Ka kuma sani kai kake da za6i tsakaninsu, kuma duk wacce ka za6a bawanda ya isa ya tambayeka meyasa. In shaa Allahu duk nan zamuyi maka kyakkyawar fahimta mu baka goyin bayan da ya kamata Allah shige ma gaba” Papi yace.

“Ameen” Afzal ya amsa “Nagode Papi.”

“Se yaushe kenan zamu sake ji daga gareka?” Mami ta tambaya.
“Wannan ba abu neba mey sauk’i Mami, ba abu neba da zan iya yinsa da kaina acikin k’ank’anin lokaci amma zan dey yi k’ok’ari inga ban ja lokaci ba.”

“Gaskiya ya kamata saboda kowa yasan inda ya tsaya, ba yaran kad’ai ba harta mu manyan ma” Papi ya amsa.

“Tabbas Papi saidai ban san wa zan d’auka wa zan bari ba acikinsu don gudun yima d’ayarsu rashin adalci, shiyasa na yanke hukuncin yin istikhara duk za6in da Allah yayi mun shi zan bi dafatan idan nayi hakan both parties bazasu ga kaman anyi musu rashin adalci ba zasu kuma fahimceni.”

“Ai zancen rashin adalci ma bai taso ba Babana, za6i naka ne ba wanda ya kai ya tilasta maka.”

“Nagode sosai Papi idan ba abinda zaku sake fad’a semu wuce gida kuje ku duba Amal.”

“Babu mu tafi” Mami ta amsa cike da hanzari.
“Papi dan Allah kayi hak’uri nasan abinda nayi muku is unforgivable nasan banida right na baku hak’uri amma dan Allah kuyi hak’uri ku saurareni wallahi tallahi ban san rabo ya shiga tsakani na da Jameelah ba, ban ta6a sanin Amal ‘yata bace se lokacin da tayi hatsari. Meyasa zan so in had’a ‘ya’yana biyu kishi? Dan Allah ku saurareni.”

STORY CONTINUES BELOW

“Jameelah kina da abin cewa?” Papi ya juyo had’e da tambayan Mami.
“A’a Abba mu tafi” ta amsa tamkar bataji abinda Daddy ya fad’a ba. Nan suka mik’e duka “Ermm Ya Afzal can I have a word with you? Papi ku d’an yi hak’uri dan Allah” fad’in Nazeefah.
“Ba komai muna jiranku a waje.” Hannun Afzal taja izuwa d’akinsu sannan ta rufe k’ofan.
“Ya Rouhi za6a zakayi tsakani na da Amal kenan yanzu?” Ta tambayesa a maraice.
“Nazeefah I have no other option inda ta nine da saidai in cigaba da zama daku duka because I love you both.”

“Nasan Amal zaka d’auka akaina I know.”

“Please don’t talk like that.”

“Ka k’aryata hakan ne? Ka k’aryata cewa ba Amal zaka za6a ka sauwak’e mun ba?”

“Nazeefah please-” yana yunk’urin ta6a hannunta ta ja da baya. “For all my life, I’ve loved you Ya Rouhi, banida burin da yafi inga na kasance tare da kai na sanya ka farin ciki. Duk wani abinda nayi da abaya wanda ya 6ata maka rai kasani nayi ne because I love you, saboda nafi son in mallakeka ni kad’ai. Dukda auren biyayya mukayi I’ll still choose you to be my husband if I were to be given a second life. Lokacin da na fara jin dad’in aurena kawai ka auro mun Amal out of the blue. Amal da na tabbata kafi sonta acikin zuciyanka fiye dani saboda ita za6in zuciyarka ce nikuwa za6in mahaifinka ne.”1

“Nazeefah-“

“Ba seka k’aryata komai ba Ya Rouhi hakan ne kuma nima na sani. Kafi son Amal a kaina wai tayaya ma bazaka fi sonta ba bayan she’s fertile wataran zata haifa maka yaran da kata mafarki kake so ni kuwa mey zan iya baka? Babu saboda ga dukkan alamu juya ce ni.”2

“Nazeefah enough please ke kanki kinsan ba haka bane, ke kanki kinsan ke ba juya bace.”

“Then explain to me why shekarana sama da uku a gidanka amma ko 6atan wata ban ta6ayi ba.”

“Saboda kowa da lokacinsa ne Nazeefah” ya sanar da ita a hankali yana mey d’ago hannayenta yana had’asu da nasa. “Saboda Amal ta rigaki conceiving doesn’t mean ke bazaki ta6a iya d’aukan ciki ba. Ina kika mance da tarihin Annabi Ibrahim da matarsa Saratu? Shin kin mance a tsufansu suka haifi Annabi Isma’il? Haihuwa lokaci ne Nazeefah, saboda Amal ta rigaki doesn’t mean you’re sterile. I believe in you Nazeefah kuma ni koda ma bazaki iya haihuwa ba hakan baze dameni ba ai dama ba jayayya mukayi kafin mukayi aure cewa dole dole se kin haihu min ba.”

“Then pick me over Amal, idan har kana nufin abubuwan da ka fad’a ka d’aukeni ka saki Amal.” Da mamaki Afzal ya tsaya kallonta yayinda kalamun Amal suke dawo masa yadda ta cire son kai ta nuna lallai lallai ita ta hak’ura ya d’au Nazeefah akanta.
“Nazeefah shin bakiya tausaya wa ‘yar uwarki ne ke?”1

“Tausaya mata? Meyasa zan tausaya mata Ya Rouhi bayan tana shirin sace mun mahaifi da miji?”1

“Amal bata da niyyan hakan kema kin sani Nazeefah, k’addara ce ta riga fata ba ita ta za6i mahaifinku ya zama d’aya ba, ba ita ta za6i mijinta ya kasance d’aya dake a matsayinki na ‘yar uwarta ba, k’addara ce.”

“Amal ba ‘yar uwa ta bace Ya Rouhi duk wanda yake shirin rabani da kai ba d’an uwana bane. I love you Ya Afzal, kuma ba kai bana jin zan iya rayuwa. Nasani yadda nake sonka ba haka kake sona ba but for once please choose me over Amal. For once ka nuna min kana sona nima let me feel loved Ya Rouhi. It has always been Amal, komai Amal komai Amal let it be this time, let it be Nazeefah. Please choose me over her I love you Ya Rouhi so much.”
STORY CONTINUES BELOW

“Nazeefah I love you too, kema kin san hakan.”

“Then choose me ka d’aukeni ka saki Amal.”

“But I’m not the one to decide Nazeefah. By Allah ko wuk’a aka sa min a wuya bazan iya za6an d’aya acikinki da Amal ba. It’s not as easy as it seems.”

“I know it’s Amal you’re going to pick dukda hakan I want you to know that I’ll never stop loving you Ya Rouhi, koda ka d’au Amal akaina hakan bazesa in daina sonka ba saidai in tsani Amal na shiga tsakani na dai da tayi. I love you so much Ya Rouhi” ta k’are idanunta na cikowa da hawaye. Janta yayi jikinsa ya rungumeta tsam yayinda take k’ok’arin k’watan kanta.
“Just let me go Ya Rouhi” ta fad’a tare da k’watan kanta daga jikinsa, idanun nan sun kumburo sun kad’a sunyi ja “Muddin ka za6i Amal a kaina bazan ta6a yafe maka ba Ya Rouhi, I can never forgive you for causing me this so much pain” tana kaiwa nan ta bud’e k’ofan ta fice yayinda Afzal yake ta kiran sunanta. Daddy taje ta sama a parlour tace ya kaita gun Mummy. Jiki na rawa ya mik’e suka fice dama so yake yasan inda suke.
Afzal kam kansa ya gama d’aurewa, gabad’aya tausayin Nazeefah yabi ya mamayesa shi kansa yasan bey kyauta mata ba idan har ya saketa. Shi kamsa shaida ne gamey da irin son da take nuna masa. Toh Amal fa? Ya zeyi da ita itama? Haka nan ya fito sam babu walwala tattare da shi yaja su Papi suka wuce gida inda suka duba Amal.
“Mami nida N-” tuna Afzal ya mata kashed’i se tayi shiru.
“Na riga na sani Baby, Afzal ya sanar damu komai” Mami ita sanar da ita. “Allah na tare de ke kinji? Karki tada hankalinki Allah k’ara lafiya.”

“Ameen” so take ta ce mata ita zata bisu gida amma dan ganin idon Afzal se tayi shiru, yana ficewa kuwa ta sanar dasu tana son ta bi su.
“Kema kinsan hakan ba me yiwuwa bane Baby. Bamu keda iko akanki ba, baze yiwu kina matarshi mu tafi dake haka kawai ba tare da izininsa ba. Ki k’ara hak’uri nan da d’an lokaci zamu san ajin da muke ciki.” Lokaci kad’an su Mami suka k’ara sannan Afzal ya mayar dasu gida. A hanyansa na dawowa ya kira layin Nazeefah sede har ya tsinke bata d’aga ba. Ba kuma wai bata kusa da wayan bane d’agawan ne baza tayi ba.
****
Koda Daddy ya sauk’e ta bakin hotel nasun yak’i tafiya se rok’an ta yake da ta kira Mummy yana son ya ganta yayi mata magana. Itama dake a cike take shi, seta k’i gani take shine silan komai. Da tun farko be tarke ‘yar mutane yayi mata ciki ba da duk hakan be faru ba. Ita se yanzu take sake gane dalilin da yasa yayi mata auren wuri ashe tsoro yake kar yadda ya lalata ‘yar mutane shima a lalata masa ita. Se gashi da Allah ya tashi kamasa ya kamasa ta inda baya tsammani. Haka nan tak’i k’ira masa Mummy tayi shigewarta ciki. Mami kam koda taji abinda ake ciki bata sa ran Afzal ze d’au Nazeefah akan Amal ba sabida kaman yadda Nazeefah ta gaya haka d’in yake, idan ba ikon Allah ba da wuya ya d’au za6in mahaifinsa akan za6in zuciyarsa. Hak’uri tayita bawa Nazeefah yayinda take sake tsanan Daddy na jefa mata rayuwan ‘ya acikin k’unci. Nazeefah yini tayi ranan tana kuka gashi ko Afzal ya kira bata d’agawa.
Cikin dare Afzal ya tashi ya gudanar da raka’a biyu yana mey neman kariya da haske daga Allah. Washegari ya cigaba da kiran Nazeefah amma haka tana gani bazata d’aga ba. Har hotel d’in yaje ya kira Mummy yana rok’anta da ta turo Nazeefah yana son yi mata magana amma haka ‘yar nan tak’i fitowa. Ta 6angaren Daddy kuwa shima ya tak’ura wa Afzal da kire-kire yana rok’ansa da ya basa address nasu Mami dan yaje ya bada hak’uri amma Afzal yak’i akan cewa in bada izinin Papi ba baze kaisa gidan ba.
Amal kuwa da ikon Allah take samun waraka, na sosai jikinta ya warware. Tamkar bak’in juna haka Afzal da Amal suka zame wa juna. Kamar yadda bata shiga harkansa shima haka baya shiga nata, in ba wai abinda ya zama dole ba se su yini basuyi ma juna magana ba. Deep down inside their hearts kuwa ba k’aramin missing how open and free they’re to each other suke ba. Na kwana biyun nan acikin d’ayan d’akin yake yini se bacci yake kawosa d’akin nasu.
Istikharan kwana uku yayi sannan ya iya ya amince da sakamakon daya samu saidai ya kasa d’aukan mataki a kai bale ya gudanar da abinda ya kamata. Rufe kansa yayi a d’aki yinin ranan yayita kuka tamkar ba d’a na miji ba. Baze iya jure rabuwa da ita, besan ya rayuwarsa zata kasance ba ita a kusa da shi ba. Jin shiru Ummi da yayi mata alk’awarin a yau ze sanar da ita sakamakon da ya samu ta d’au waya ta kirasa domin ji daga garesa. Kaman wanda bade d’au wayan ba ya d’aga a last ring d’in.
“Halo Prince?” Ta soma da cewa.
“Na’am Ummi?”

“Prince ya shiru? Tun d’azun nida Abbanka muke jiran kiranka lafiya dai ko?”

“Lafiya ya jikin Amal?”

“Alhamdulillah da sauk’i.”

“Ya naji muryanka k’asa-k’asa haka?”

“Babu.”

“Bade kuka kake ba Afzal? Meya faru?”

“Ummi I can’t do this” ya sanar da ita tsakaninsa da Allah. “Wallahi bazan iya ba.”

“Meya faru? Ka gama istikharan ne?
Hello Afzal?” Ta sake da cewa bayan shirun da yayi. “Afzal?”

“Na’am” ya amsa murya ciki-ciki.

“Ya sakamakon? Wace zaka d’auka? Wace tafi kwanciya maka a rai?”

“Ummi I can’t bazan iya sakanta ba she’s been through alot bana son yin hakan ya zame kaman na zalunce ta.”

“Wacece? Amal ce?

“Ummi ina tausayawa rayuwar da zata fad’a bayan mun rabu bazan iya rabuwa da ita ba.”

“Ka sanar dani mana Afzal? Amal ce?”

“Ummi no, ba ita bace.”2
“Then wacece, Nazeefah?”
“Eh Nazeefah, Nazeefah ce Ummi.”
“Ni yanzu ka rud’a min kai, Nazeefah ce tafi kwanciya maka a rai kokuwa ita zaka saka?”
“Ummi hankalina yafi kwanciya da Amal.”7
“Toh Alhamdulillah in shaa Allah hakan shi yafi alkhairi.”1
“Ummi Nazeefah kuma fah? Shikenan yanzu semu rabu?”
“Toh ya zamuyi Prince? Rabuwa da ita ya zamo dole se inde zaka bijire wa za6in da Allah yayi maka ka saki Amal wanda nima ba barinka zan ba tunda har Allah ya riga yayi ma za6i.”
“I know Ummi kuma nima komin yaya bazan ta6a iya rabuwa da Amal ba but Nazeefah kuma fa? Na tabbata baza ta ta6a yafe mun ba, zan iya cewa soyayya na ne kad’ai ya bata wuya a rayuwa. Lokacinda ta soma jin dad’in aurena kuma na kama na k’ara aure nayi mata kishiya. Ban ta6a kyautata mata ba Ummi and now da abunda zan sak’a mata kenan bayan duk wannan wuya da ta sha? I need to treat her right one more time please ki taimakeni Ummi.”+
“Hak’urin nan de shi zan cigaba da baka Prince, nasan da wuya Nazeefah ta kar6i bak’on lamarin nan da hannu bibbiyu kaman yadda ka fad’a amma as time progresses zata gano cewa za6in Allah shine mafi alkhairi a gareku gabad’aya kuma ba kullum bane muke samun abinda muke so. Don yanzu koda ka bijirewa za6in da Allah yayi ma ka saki Amal kabar Nazeefah, ba alkhairin da ze biyo bayan hakan se ma sharri. Se ka ga ma rabon ya zame mata ajali, kuma zancen wai baka ta6a kyautata wa Nazeefah ba kaima kasan k’arya ne. Duk kulawan da ya kamata ace mace na samu daga gun mijinta kayi mata kuma itama ta sani, so just calm down and do what’s right Allah na tare da kai.”
“Thank you Ummi” da haka ya katse wayan yayinda kalamun Nazeefah suke ta yi masa yawo akai. Ji yayi gabad’aya baze iya sauwak’e mata ba. Dama seda ta fad’a mishi cewa tasan Amal ze d’auka akanta saboda baya sonta se Amal se gashi kuma Amal d’in ze d’auka yanzu. Sede ba don baya son ta bane kaman yadda ta fad’a se don Amal ce za6in da Allah yayi masa kaman yadda itama Yayi mata lokacin da zata aureshi. Tsoronsa d’aya kar wannan za6i ya sake 6ata tsakanin wannan ‘yan uwa. Dan kaman yadda Nazeefah ta sanar da shi ya tabbata muddin idan taji Amal ya bari ya saketa seta tsani Amal fiye da yadda ta tsaneta yanzu. Oh Allah shin ya zeyi yanzu? Idan da ace ze iya rabuwa da dukansu biyu da yayi dan hakan shi zefi wa kowa kwanciyan hankali. Gara duka su rasa sa da ya d’au d’aya yabar d’aya amma yaya ya iya? Zuciyarsa bazata iya jure masa rashinsu duka ba barin ma Amal tasa da yake ganin idan har ya rasata baze iya sake samun mace mey kyawun halatayya irin tata ba. She’s just different.2
Mik’ewa yayi a hankali yabar d’akin ya nufi nasu inda Amal ke kwance a kan gado se tunani take. Har ya k’arisa kan gadon bataji shigowansa ba. Seda ya kira sunanta tukuna.
“Rania?” Da mamaki cike da tsoro ta mik’e zaune tana kallonsa. Bazata iya tuna when last ya kirata da wannan suna ba, probably tun da ya gano cewa ita da Nazeefah ‘yan uwa ne. Ganin bata da niyyan amsasa seya mik’a mata hannunsa da nufin ta sa nata a ciki. Bayan dogon nazarin da tayi daga k’arshe seta mik’a hannunta ta sanya cikin nasa inda ya mik’ar da ita tsaye akan k’afafunta. Na matuk’a kanta ya d’aure yayinda zuciyarta ta shiga bugun tara-tara barin ma da Afzal ya rungumeta a jikinsa.
Shikenan ya tabbata ita zata tafi. Se bata kawai jikinta yake itace ze saka, tasani zamanta da shi ya k’are, ta sani Nazeefah ce tafi kwanciya masa a rai, ta sani Nazeefah ce za6in da Allah yayi mata. Tabbas tayi musu murna sedai kuma tayi k’arya idan tace bata ji zafin hakan ba because she loves him. No matter how hard she tried not to show how terrified she felt takasa saboda yadda take jin zafin rabuwa da shi. Kawai ji tayi hawaye na gangaro mata daga ido dai-dai wannan lokaci Afzal ya d’agota daga jikinsa da k’yar dan yadda ta kankamesa. Cike da mamaki ya tsaya kallon yadda take kuka sannan daga bisani ya shiga share mata hawayen nata “Please don’t cry Rania.”
STORY CONTINUES BELOW
“I should really start packing my clothes” ta sanar dashi tana mey hana k’wayoyin idanunta had’uwa da nasa. “I’m really happy for you two Yaya, Allah ya baku zaman lafiya mey d’aurewa.”
“Mey kike cewa haka Rania? Zaman lafiya tsakani na da waye?”
“Da Nazeefah.”
Murmushi ya saki kad’an “Meyasa kika ce haka? Why not you?”
“Saboda bani ce za6in da Allah yayi maka ba Yaya. I know I’ll be the one to leave and even though nima hakan ne ze fiye mun kwanciyan hankali I just can’t deny the fact that I still love you so very much and I’ll miss you so damn much.”
“But you don’t have to miss me Rania because you’re not going anywhere, this is your home anan kuma zaki cigaba da zama ba inda zaki.”
“No ba sekayi hakan ba Yaya, zanje in samu Mami a gida, chan d’in ze fiye mun kwanciyan hankali yaso ko haya ne se kasa a nan d’in.” Dariya sosai ta basa wanda ya kasa dannewa yayinda ta tsaya kallonsa cike da mamaki da takaici. Mey yake nufi da hakan?
“Rania listen to me, ba inda zakije nan ne gidanki kuma d’akin mijinki okay?”
“D’akin mijina? Nazeefah kuma fa? Karka bijire wa za6in Allah saboda son zuciya Yaya. Idan kuma tsoron abinda Papi da Mami zasuce kake then ka kwantar da hankalinka kasani duk zasuyi maka kyakkyawar fahimta kaman yadda nima nayi maka. We all know you love me Yaya, please don’t bother yourself.”
“Tsaya, kafin muyi aure mey kikayi? Kinyi Istikhara right?” Kai ta gyad’a masa a hankali cike da rashin fahimta sannan ya cigaba “Kuma bayan da kika gudanar se waye Allah ya za6a miki?”
“Kai Yaya” ta amsa a takaice.
“Kina ganin it is possible ace ni kuma nayi Istikharan yanzu se wata ta daban ta zame za6in da Allah zeyi mun bayan ke kuma ni Ya za6a miki?”
“But Yaya-“
“Ki sani Rania ko sau dubu mutum yayi Istikhara za6in Allah d’aya ne sedai idan shi yaso bijire wa hakan. Kaman yadda kikayi naki istikharan Allah ya za6a maki ni, nima haka ya za6a min ke yanzu. We two are meant to be Rania in shaa Allahu mutuwa ce kad’ai zata shiga tsakani na dake. Rania I love you so much kuma Allah kad’ai ne sheda game da irin son da nake yi miki, shi kad’ai yasan idan bake bazan iya rayuwa ba, shi kad’ai yasan muddin na rasaki bazan ta6a iya samun kamilar mace mey kyawawan d’abi’u da halatayya irin naki ba shiyasa ya za6an min ke ya sake bani daman da zan soki in kuma kula dake har ila k’arshen rayuwa na. I can’t do without you Rania and I can’t ask God for more da ya sake bani daman kasancewa mijinki, forgive me for all the times I’ve wronged you Rania, I’m terribly sorry please forgive me.”1
Kuka Amal ke sosai yayinda ta kasa amincewa da abubuwan daya fad’a mata. Se gani take kaman a mafarki komai ke faruwa tabbas itama bazata iya rayuwa idan ba shi ba. Gani take kaman duk yadda yake jin yana sonta ita tafi sonsa, don dai kawai ita bata nunawa ne. Daga k’arshe kuma bazata iya yima Allah godiya ba da ya sake bata daman kasancewa matarsa, sai dai kuma bazata iya duba irin rayuwan k’unci da tashin hankalin da Nazeefah zata fad’a ba a rashin Afzal. Se gani kawai take inda itace Afzal yace ze sauwak’e wa. Tasan duk kalan rashin tawakkalinta tana bayan Nazeefah. Tasan Nazeefah na iya yin k’aramin hauka akan wannan dalili, she knows this is not going to be easy on her shiyasa take tausaya mata sosai.1
“Rania?” Ya kirata bayan shirun da tayi, jikinsa kawai ta fad’ yayinda ta shiga yin kuka na sosai. “Bakayi mun komai ba Yaya don haka ka daina tambaya na yafiya I love you so very much.” Ba k’aramin dad’i kalamanta suka sanyasa ba, matseta tsam ya sakeyi a jikinsa tamkar ana shirin k’watan masa ita yayinda wani irin sonta yake sake shiga zuciyansa. Sun dad’e a haka sannan daga bisani ya janyeta daga jikinsa sede har anan hawaye Amal ke.
“Please don’t cry Rania.”
STORY CONTINUES BELOW
“I wish I could stop Ya Omri.”
“But there’s no need to.”
“There’s every need to cry Ya Omri.”
“Saboda ban barki kin tafi gida kaman yadda kikeso ba kike wannan kuka Rania? Saboda Allah ya za6an min ke? Ashe ba haka kika so ba, I thought you said you love me” Kai ta gyad’a mishi take tana murmushin takaici.
“Then meyasa kike kukan? A tunani na this is supposed to be the most happiest moment for us both.”
“Yes it is Yaya kuma hawayen nan da kake gani, hawayen farin ciki ne gani nake kaman a mafarki komai ke faruwa, I can’t believe that we’re still going to remain married to each other after hope has been gone.”
“I feel thesame way Rania, but tun farko tun kafin in gudanar da Istikharan nan nasan komin yaya akayi ni dake bamu rabuwa.”
“Ko meyasa kace haka?” Tayi saurin tambayansa cike da mamaki.
“Saboda Istikharan da kikayi kafin mukayi aure Rania, idan da har ace akwai sharri a auran mu da Allah baze za6a miki ni akan Abdul daya kasance masoyinki ba. Idan har na rabu dake kinga kenan babu amfanin istikharan da kikayi. Ko ce miki akayi shi istikhara temporal decision ne na d’an lokaci? Hankali na ya tashi ne gabad’aya saboda Nazeefah. Ina matuk’an tausayawa halin da zata shiga idan har ta gano cewa I chose you over her, shiyasa nayi coming up da plan na cewa zanyi Istikhara kinga idan har nayi ita da iyayenta bazasuyi mun mumunar fahimta ba, zasuga za6in Allah nabi ba wai na zuciya na ba. Sedai kuma yanzu bayan dana gudanar da hakan nakega still Nazeefah bazata amince ta kar6i wannan bak’on lamarin da hannu bibbiyu ba. Nasan komin tayaya bazata ta6a fahimtar cewa Allah ne ya had’ani dake ba, bazata ta6a gane cewa ba komi mutum yake so a duniyan nan yake samu ba, gani take komai laifinki ne Rania and that is what hurts me the more knowing who you really are. Bana son a sanadin hakan ta sake tsanarki, ita gani take komai laifinki ne, ke kika janyo bayan ba haka bane. I wish Nazeefah could see this kind and selfless side of you. Har yau kalaman ki na yinin ranan da na sanar dake cewa Nazefah k’anwarki ce suna kaina. Har yau na kasa mancewa dasu kuma bazan ta6a mancewa da su ba. Yadda kika cire son kai kikace kin yafe ni wa Nazeefah even though kina so na bawai bakiya sona ba se don cewa da Annabi yayi “La yu’minu ahadukum hatta yuhibbu li akhihi ma yuhibbu li nafsihi” [imanin d’ayanku baya cika har seya so wa d’an uwansa abinda ya so wa kansa] I get that you love me but you’re willing to let your sister have me and ba kowa keda irin imanin nan naki ba Rania ko ni nan bazan iya aikata abinda kikayi ba ranan saboda haka kuma naji respect naki ya k’aru a idona yayinda sonki ya sake k’aruwa a zuciya na.”
Murmushin jin dad’i ta sakar masa tana mey share hawayenta “Ka sani ko da nace maka hawayen nan na jin dad’i ne k’arya nayi because zuciyata tausayawa Nazeefah take, I can’t imagine the kind of hell she’ll go through Yaya don haka har nakejin kaman mu hak’ura da juna sedai kuma bazamu iya yin jayayya da za6in Allah ba.”
“Hakane Rania, let just pray for her in shaa Allah as time progresses zata fahimci komai ta kuma nemi gafararki ayi zaman lafiya gabad’aya.”
“Da kuwa ba abinda zefi mun hakan farin ciki da jin dad’i Yaya. Inspite of how Nazeefah disperses me wallahi I still love her kuma zan cigaba da sonta ina yi mata uzuri har zuwa lokacinda zata gane gaskiya.”
“Allah yayi miki albarka Amal ya baki yaran da zasu kula dake ranan da buk’atan hakan ya taso Rania, I’ll forever love, cherish and adore you.”
“Ameen Ya Omri I love you too.”
“Let’s eat out ai zaki iya fita ko?”
“Why not? Bari in shirya.”
***
Washegari…
Dai-dai gaban gidansu Nazeefah yayi parking sannan ya zaro wayansa ya kira Daddy a karo na farko ya d’aga.
“Halo Afzal ka iso ne?”
STORY CONTINUES BELOW
“Eh Daddy.”
“Toh bismillah mana ka shigo.” Harga Allah beyi niyan shiga ciki ba amma yaya ya iya? Gyara packing nasa yayi ya k’arisa ciki inda ya samesa a parlour ya gaishesa. Bayan sun gaisa ya zaro takardan daya ninke daga aljihunsa ya mik’awa Daddy “Kaman yadda nayi muku alk’awari cewa zanyi Istikhara, duk kuma wacce Allah ya za6ar mun ita zan d’au in sauwak’e wa d’ayan. Toh game da sakamakon dana samu bayan na gudanar da Istikharan na yanke wannan hukunci ba don son kai ko son zuciya ko makamancin haka ba, da fatan kai da iyalanka zakuyi mun kyakkyawar fahimta. Ga takarda nan na sakin Nazeefah, dafatan ze isa gareta zaka kuma bata hak’uri a madadi na ni zan wuce.”1
“Dakata Afzal kar kayi saurin tafiya. Kayi hak’uri ka bani dama in baka hak’uri na jefaka da iyalinka cikin wannan rud’ani da tashin hankali da nayi. Kuma ka sani wannan hukunci daka yanke shine dai-dai koda ma ace bakayi istikhara ba bazan bari ka saki Amal ba saboda abinda nayi mata da mahaifiyarta kad’ai ya ishesu takaici da jarabawa. Dole nima in gir6e abinda na shuk’a. Da fari na d’au zan iya yi wa Allah wayo, na d’au idan har na aurar da Nazeefah shikenan bani da wani tsoro kuma ashe ba haka abun yake ba, ashe ita zina bashi ce idan har ka cita dole komin ta yaya ne ka biya. Kuma muddin ba a kaina ze ramawa Jameela abinda nayi mata ba dole se akan wanda nakeso. Dukda cewan Amal da Nazeefah ‘ya’yana ne amma kaman yadda zanfi jin zafin sakin nan akan Nazeefah ba haka zanji ba idan da akan Amal ne saboda babu shak’uwan nan na uba da ‘ya a tsakani na da ita. Allah ya za6an maka Amal ne saboda ya koya mun da ‘yata darasi kuma saboda itama koda sau d’aya ne taji dad’in rayuwa. Ka sani wannan hukunci da ka yanke dai-dai ne kuma zanyi k’ok’ari in fahimtar da iyalai na, Allah ya baku zaman lafiya mey d’aurewa da Amal ya albarkaci rayuwanku in shaa Allah zan isar wa Nazeefah sak’onka.”
“Nagode sosai Daddy.”
“Ba komai, se kuma batun Jameela bazan gaji da rok’an kanka ba da kayi mun kwatance injeni gidansu in nemi tubarsu, idan ban samu sun yafe mun ba alhak’insu ya cigaba da bi na kenan, ka tausaya mun da iyalai na please Afzal.”
“In shaa Allah zanyi ma Papi magana karka damu.”
“Toh nagode sena ji daga gareka.”
“Ba komai ni zan wuce” ya fad’a had’e da mik’ewa “Ka gaishe da Amal ina da niyyan shigowa inzo in dubata nima in nemi tubarta amma ina son in d’an bata lokaci saboda nasan yadda zata ji ta tsaneni yanzu.”
“Zataji Daddy se anjima” yana kaiwa nan ya fice ya koma office har a yau idan ya gwada kiran layin Nazeefah bata d’agawa. Ba komai yasa yake son ya kirata ba se don so da yake ya bata hak’uri, baya son taga kaman baya sonta ne, har yau har gobe ze cigaba da sonta saboda akwai gur6in da ita kad’ai ce ta mamaye a zuciyansa. Ita ce macen da ya fara sani a rayuwansa, itace macen da ya fara sumbata itace macen da ya fara sharing wani abu nashi da ita. Shin har ze iya mancewa da ita a rayuwansa? He don’t think so.1
****
Daddy be samu ya kaiwa Nazeefah takardan nata a ranan ba se a washegari. Bayan ya dawo daga sallan Azahar ya d’au wayansa ya kira Mummy sedai kaman yadda ta saba ignoring call nasa hakan ma tayi yau don haka ya tura mata sak’o.
_Hjy Surayya kiyi hak’uri ki d’au wayan nan muyi magana. This is not about me it’s about our daughter Nazeefah, thank you._
Sak’on ya shiga bada dad’ewa ba Mummy ta karanta se contemplating take ta kirasa taji lafiya ne ko ta bari. Chan k’arshe de ta kira wanda ya d’aga a karo na farko. Bata basa daman yin magana ba tace, “Meya samu Nazeefan?”
“Hjy Surayya wannan ba maganan waya bane gani nan tahowa yanzu.”
“Karka 6ata lokacinka bana nan na fita.”
“We both know k’arya kikeyi zanzo yanzu please” bata sake ce meshi komai ba ta katse wayan. Cikin mintuna da basu kai ashirin da biyar ba sega shi nan ya iso. Waya yayi mata akan ta fito nan da nan ta sanya hijabinta ta fice.
STORY CONTINUES BELOW
Ba yadda Daddy beyi ba da su k’arisa koda reception ne su zauna suyi magana tak’i, tace ita idan har baze fad’i abinda yake tafe dashi ba zata koma ciki. Toh suje cikin mota su zauna nan ma tak’i. Yasan sam bey kyauta mata ba amma ba wai yayi hakan dan ya raina ta bane ko makamancin hakan, shi tsoron sanar da ita yake gudun kada ta gujesa kaman yadda takeyi yanzu.
Hannu yasa a aljihunsa ya fito da takardan had’e da mik’a mata.
“Mey wannan?” ta tambaya ba tare da nuna yunk’urin amsa ba.
“Kedai bud’e ki gani.” Kaman wacce bazata kar6a ba ta amsa ta bud’e had’e da karancewa.
_A ranan Laraba, goma ga watan Juneru shekara dubu biyu da goma sha takwas na saki matata Nazeefah, saki d’aya, biyu, uku saboda haramta mana zama da shari’a tayi a sanadin ta na kasancewa ‘yar uwar matata Amal na jini._1
Ajiyar zuciya Mummy ta sauk’e dama tasan za’ayi haka. Dama tasan Nazeefah ce Afzal ze saka kawai bata so ta nuna mata bane don kar ta tayar mata da hanaki amma tasan haka za’ayi dama kodan ma Allah ya kama Daddy yasa shima yaji zafin da mahaifiyar Amal taji sanda yayi mata fyad’e. Tasani dole ne wannan k’addara ya fad’a akan Nazeefah saboda itama Amal ta samu farin ciki koda sau d’aya ne a rayuwarta. Idan harda ace wannan saki akan Amal ya fad’a da Daddy baze ji zafi kaman yadda ace zeji yanzu da ya fad’a akan Nazeefah. Ta hakan ne kawai Allah ze sanyasa gir6e abinda ya shuk’a, ta hanyar mayar masa da ‘ya bazawara kaman yadda ya k’wace wa ‘yar mutane budurci.
“Shikenan ka huta ai yanzu Alhj, amma kasani nida ‘ya’yana bazamu ta6a yafe maka wannan abun kunya daka aikata ba.” Be bari ta shiga takawa ba yayi sauri ya rik’e k’asan hijabinta “Hjy Surayya bazan ma fara tambayan gafararki ba saboda nasan abinda nayi miki da ‘ya’yanki is unforgivable but atleast give me a chance to apologize and tell you sorry. I’m gravely sorry for hiding the truth away from you, wallahi bawai don bana sonki bane kokuwa don bana mutuntaki yasa na 6oye miki wannan al’amari, sonki da nakeyi ne ya rufe min ido, bana son abinda ze shiga tsakani na dake Hjy Surayya, bana son in rasa ki. Dan son zuciya irin nawa se naga idan har na sanar dake gaskiya zaki gujeni kik’i aurena shiyasa na rik’e komai wa kaina. I love you so much Hjy Surayya and I’ll never stop loving you, I’ll wait. Zan jiraki koda kuwa zuwa k’arshen rayuwana ne amma bazan gaji da baki hak’uri ba dan Allah kiyi hak’uri ku dawo gida.”1
“Babu wani abinda zaka sake fad’amun da zaisa in canza ra’ayina. Idan ‘ya’yanka kake so kana iya shiga ciki yanzu ka ebosu amma nikam takarda na nikeso. Kaman yadda ka shiga tsakanin auren yaran nan kasa Afzal ya saki Nazeefah saki ba d’aya ba, ba biyu ba har uku nima haka nake so ka rubuta mun nawa. Idan har ‘yata zata shiga k’uncin rayuwa ka tabbata kai m seka shiga ninki ba ninkin nata don haka ka rubuta min takarda na yanzun nan anan. Tunda rayuwan zawarci ka za6a wa ‘yarka tayi nima mahaifiyarta shi zanyi.”
“Dan Allah kiyi hak’uri Hjy Surayya nasan nayi miki laifi, laifi babba amma dan Allah kiyi hak’uri ki gafirceni. Idan kika tafi kika barni ya kikeson in rayu?”
“Bakayi tunanin hakan ba kafin ka danne ‘yar mutane kayi mata fyad’e? Se kaje chan ku k’arasa da ita mahaifiyar Amal d’in that is idan har zata iya yafe ma zaluntar ta da kayi.”1
“Kema kinsan bazan iya rayuwa da kowa ba bayan ke Hjy Surayya, kinfi kowa sanin yadda nake sonki tun ba yau ba.”
“Sam ba haka bane, I was a fool to believe you love me Alhj, yaci ace tun a lokacin chan na gane kud’in mahaifina kawai kake so ba ni ba. Wallahi Allah ne kad’ai ze sak’a mun. Duk kalan halaccin danayi maka na sa mahaifina yayi maka duk baka ga hakan ba you still chose to lie and cheat on me.”
“Dan Allah kiyi hak’uri bazan ta6a gajiya da baki hak’uri ba saboda nasan ban kyuata ba amma wallahi I love you Hjy Surayya I really do.”
STORY CONTINUES BELOW
“Shin anya ma kuwa labarin daka tsara min da iyayena na cewa kai maraya ne gaskiya ne kuwa? Shin anya kuwa ba k’arya ka shirya mana ba saboda ka samu kaci arzikin mahaifina Alhj?”
Shiru Daddy yayi gun ya kasa cewa komai. Tabbas yayi mata da mahaifinta daya kasance hanshak’in mai kud’i bahaushe daga Kano k’arya lokacinda yazo aurenta. Saboda gudun da yake kar a nemi iyayensa kowani d’an uwansa a garin hakan asirinsa ya tonu na cewa yayi ma wata fyad’e a k’auye Mummy ta fasa aurensa ko iyayenta su hanata. Tun bayan da abin ya faru ya samu ya dawo makaranta be sake d’aga wayan iyayensa ba, duk lokacinda yaga kiransu baya d’agawa har ta tsinke saboda yasan akan mey zasuyi masa magana shi kuwa bayida abin cewa. Daga k’arshe ma da yaga kiran ya soma isansa se kawai ya sauya lamban wayansa gabad’aya, tun daga nan be kuma sake ji daga garesu ba se…
“K’arya kayi mana ko? Why aren’t you saying anything Alhj?”
“Hjy Surayya yes, yes nayi miki da Abba k’arya batun iyayena amma wallahi ba don bana respecting naki bane se don tsoro da nake kar a garin hakan gaskiya ya fito in rasaki.”
“Wani gaskiya?” tayi saurin katsesa.
“Batun abinda ya faru tsakani na da mahaifiyar Amal.”
“Wane irin mak’aryaci ne kai Alhj? Mey nayi maka a rayuwa da ka za6i ka gina duk wani abinda mukayi accomplishing tare akan k’arya?” Ta tambayesa hawaye na saurin ciko mata a ido. “All I did was to love you Alhj I’m so disappointed in you na tabbata da Abba yana raye a yau da shima baze ta6a yafe maka ba.”
“I’m truly sorry Hjy Surayya amma abinda ya faru ya riga ya faru idan da zan iya mayar da lokaci baya da nayi dan in gyara komai amma bazan iya ba please give me a second chance idan kika tafi kika barni taya kikeson in rayu? Tabbas idan ba ke su Nazeefah bazasu amince su dawo gida a gareni ba please kiyi hak’uri.”
“Bayan k’aryan nan se kuma wani k’arya ka sakeyi mun?”
“Hjy Surayya a shirye nake da in sanar dake duk wani abinda kike buk’atan ki sani amma zaki galabaita tsaye a nan saboda labarina nada tsawo kiyi hak’uri mu shiga mota kokuwa mu k’arisa cikin reception.” Bata ce da shi komai ba kawai ta shiga takawa yayinda yake biye a bayanta, a VIP reception suka zauna sannan Daddy yayi gyaran murya ya soma kaman haka.
“A shekaran da na dawo hutun second year d’ina ne muka had’u da mahaifiyar Amal wato Jameela wacce nake kira da Jamee na. Jameela ta kasance itace mace ta farko da Allah ya fara sanya min soyayyarta a zuciya na, so kuma na aure bana lalata ba. We started off as friends amma cikin k’ank’anin lokaci soyayya mey k’arfi ya shiga tsakaninmu. Jameela was simply everything I could ever ask for, lokacin da muka fara soyayya kwata-kwata shekarunta goma sha shida ne, she was so beautiful, young and innocent. Tsaftacacciyar soyayya muka gudanar nida ita as ko zance naje wajenta iyaka muyi hira ba wani ta6e-ta6e bale makamancin hakan saboda Jameela yarinya ce kamila wacce take san addininta sosai take kuma k’ok’arin bin dokokin da ya kafa mata. Ahaka ne har nazo na koma makaranta wanda bada dad’ewa ba Jameela tayi mun waya cewa mahaifiyarta na shirin had’ata aure da d’an chairman na garinmu idan har ban hanzarta turo magabata na ba ana iya aura mata shi d’an chairman d’in. Hankalina ne ya matuk’an tashi se Allah-Allah nake session d’in ya k’are in dawo gida. Kasancewar a scholarship na samu karatun seya zammana banida gatan dawowa gida kowani hutu se shekara-shekara. Addu’a muka tsayar sosai nida Jameela cikin ikon Allah kuwa se har wata shekarar ta zagayo shi wannan yaro be turo ba. Na dawo bada dad’ewa ba na samu mahaifina nayi mishi maganan Jameela akan ina son a tura tambaya gidansu sede sam Abba yak’i amincewa akan cewa da baki na ne zan ajiye mata idan nayi aure yanzu ina karatu. Duk yadda naso fahimtar dashi cewa Jameela bata da matsala da hakan besides ma ina d’an yin business, makaranta kuma shekara d’aya ne ya rage sedai hakan ya gagara Abba yak’i ya amince ya bani goyin baya. A sanadin haka nida Jameela muka shiga tashin hankali sedai bamu cire rai ba, muka mik’a komai ga ubangiji. Ban san ya akayi ba de amma wataran mahaifiyar Jameela ta jiyota muna waya bayan kuma ita ta riga tayi mata miji a sanadin haka tayi ma Jameela duka tayi seizing wayarta sannan ta horeta da kada ta sake kulani. Kwana biyu na daina ji daga gun Jameela ko na kira layinta baya shiga gashi sun k’are makaranta lokacin bale inje mu had’u a chan d’in. Rana d’aya kawai na jajirce na jeni gidansu dan yadda shirun yayi yawa, dukda cewan ta haneni da taka bakin k’ofan gidnasu saboda yadda ta nuna mun mahaifiyarta bata sona. A farko da naje mahaifiyar ta kar6eni da fara’a kasancewar bata gane waye niba a lokacin da nayi mata bayanin kaina kawai ranta ya 6aci ta sauk’e duk wani haushin da takeji a kaina tayi mun koran kare harda muciyan tuwo ta bini waje. Hakan ba k’aramin 6ata mun rai yayi ba dan dole na hak’ura da Jameelah saboda a rayuwa na washi walak’anci na kuma d’au alwashin sena rama cin mutuncin nan da tayi mun ko ta yaya ne. Rana d’aya ina zaune kawai sega kiran Jameelah ban 6ata lokaci ba na d’aga inda take sanar dani tana son mu had’u. Chan na kaita bayan gari da siyasan cewa abu nake so in nuna mata, ina son Jameelah amma abinda mahaifiyarta tayi mun ya tsaya mun a wuya ko kallonta nayi se na tuna da abin. Haka kawai shaid’an ya soma raya mun in d’au fansa akanta sedai kuma sonta da nake yana rik’eni. Amma haka shaid’an ya rinjayi zuciyana ta hanyan raya mun ai tunda mahaifiyarta tana sonta idan na ta6a lafiyarta kaman na ta6a na mahaifiyar ne don haka idan na lalata mata rayuwa abun seya fi wa mahaifiyar zafi. Ana cikin haka ne sega abokai na guda biyu dana basu labarin abinda mahaifiyar Amal tayi mun nan suka sake k’arfafamun guiwa suka bani had’in kai nayi ma Jameela fyad’e ba tare da d’igon imani ba.”
STORY CONTINUES BELOW
“Koda mahaifinta ya kai k’arana dana mahaifina gurin mey unguwa k’aryata komai nayi na samu abokaina suka rufa mun asiri shima Abba ya goya mun baya saboda baze ta6a kawowa a ransa zan iya aikata abinda nayi ba. Acikin satin ko na gaba na samu na koma makaranta ban sake ji daga garesu ba. A karon chan ne na had’u dake Surayya, kika yi mun erasing duk wani bad memory’n dana bari da a k’auyen Askira. Tunda na sameki komai ya canza Surayya, soyayyar da kika nuna min ta dabance. Banida komai, Baki sanni ba, baki san wani nawa ba amma kika so ni kika kuma amince dani regardless. Ko a mafarki ban ta6a tsammanin cewa wataran zan iya mallakan ‘yar babbar gida kamar ki ba mey hankali da tausayi. Lokacin da kika ce mun muyi aure ne nashiga tashin hankali badon bana sonki ba se don banason hakan ya tono mun labarina dana bari a garin Askira. Ban san da wani idon zan sake kallon iyayena da na shafesu a doron k’asa saboda selfish interest d’ina ba na kusan shekara. Rud’ani na matuk’a na shiga yayin da na rasa ya zanyi gashi bana son in rasaki saboda da in rasa ki gara na rasa komi nawa koda kuwa raina ne. Don haka nayi miki da Abba k’aryan cewa ni maraya ne. A tunani na hakan ne kad’ai zaisa Abba ya amince ya aura min ke Surayya. Ba abinda Abba beyi mun ba bayan dana aureki, abinda ya kama kayan da zansa, gidan da zamu zauna, motan da zan hau harta sadakin ki shi ya biya mun, komai da na sani na mallaka a lokacin na Abba ne. Harta aiki shi ya samo mun bayan da ya biya mun kud’i na gama masters d’ina muka dawo gida nan Nigeria idan ban manta ba kina da cikin Khaleefah.”
“A lokacin da muka dawo ne bayan na tafi yin service d’ina na koma k’auyen Askira dan d’auko su Abba in nemi tubansu in basu hak’uri ake tabbatar min da cewa sunyi hatsari shekaru biyu da suka wuce a hanyansu na zuwa k’auyen Dambuwa. Shi Abba a take ya cika ita kuwa Umma tayi jinyan wata shida sannan mutuwa yayi halinsa. I felt hopeless and useless Surayya, iyayena sun mutu amma seda shekara biyu nake sani. Ji nayi kaman in soka wuk’a wa kaina in mutu wani irin d’a ne ni? Na sosai nayi nadaman abinda na aikata na d’au alk’awarin yin sadak’atul jariya da sunayensu Allah ya kai musu ladan kabari. Nasan rashin kyautatawan da nayi wa iyayena yasa nima Allah ya jarabce ni da gagararriyar ‘ya kaman Nazeefah.l
“Daga gida na wuce gidansu Jameelah inda ake sanar dani suma sun tashi sun k’aura sun bar garin gabad’aya. Ba wanda ya sanar dani cewan rabo ya shiga tsakani na da ita bayan faruwan abun shiyasa ban ta6a sanin Amal ‘yata bace se recently. Wallahi ba k’arya nake yi miki ba Surayya please believe me, taya zan so in had’a ‘ya’yan cikina kishi Surayya bayan na san yin hakan haramun ne?”
“Yanzu ina ita mahaifiyar Amal d’in take Jameelah?” Mummy data amince da duk wani abinda ya fad’a ta soma da tambayansa.
“Tana cikin garin nan da zama amma bansan inda take ba, rannan Afzal ya taho da ita da mahaifinta gidan Nazeefah inda mukayi magana duka akan yadda za’a 6ullowa al’amarin nan nasu.”
“Baka san inda take ba kace?”
“Wallahi ban sani ba Hjy Surayya ai kinsan bazan miki k’arya ba.”
“Bawai ina k’aryata ka bane Alhj I just want to be certain, tana da aure?”
“Wallahi banda masaniya akan hakan amma base on abinda Amal ta ta6a fad’amun kaman mahaifiyar nata bata da aure.”
“Ka aureta Alhj” ta sanar dashi. Da mamaki ya tsaya yana kallonta yayinda ya kasa amincewa da abinda tace.
“Eh?” Ya tambaya.
“Nace idan har Jameelah bata da aure kuma bata niyyan yin wani auran anan kusa ka aureta.”
“Hjy Surayya kin ko san abinda kike cewa?”
“This’s the only way zamu iya samu mu had’a kan yaran nan Nazeefah da Amal mu gyara zuri’ar mu. Ka fini sanin halin Nazeefah, yanzu da Afzal ya d’au Amal a kanta ba k’aramin tsanar yarinyar nan zatayi ba dama already ta riga ta tsaneta.”
“Toh mey auro Jameelah zeyi ya gyara wannan lamari Hjy Surayya?”
“Tabbas auro Jameelah zaisa Nazeefah ta shiga hankalinta ta nutsu ta sani cewa mu dasu mun riga mun zamo abu d’aya yanzu ta kuma sani cewa shi kishiya na akan kowa ne idan har da tanayin kwatance dani tagani toh yau nima gashi anyi mun kishiya.”
“Tabbas kinyi gaskiya Hjy Surayya amma bana son in had’a soyayyarki da kowa ke kad’ai nakeso.”
“Karka damu dani kuma ma ai nasan kana son Jameelar taka har yau ko ba haka ba?”
“Amma ba kaman yadda nake sonki ba Hjy Surayya ni tausayin Jameelah kawai nake yanzu.”
“Karka damu ai ni nace ka aurota.”
“Hjy Surayya nifa banga amfanin yin hakan ba. Ba sena auro Jameelah ba.”
“Ka aurota Alhj ni na baka dama karka damu.”
“Surayya-” hannunta ta aza akan nasa cutting him off “Don’t worry nima ai zama ni d’aya tal d’innan ya isheni ka kawo mun abokiyar zama tana tayani hira na tabbata kaman yadda Amal bata da matsala itama mahaifiyar tata haka ne.”
“Wannan ba sekin fad’a ba Hjy Surayya Jameelah sam batada hayaniya.”
“Toh kaga komi ya zo mana da sauk’i kenan, ka auro ta kaji?”
Hjy Surayya what can I say? You’re the reason behind who I am today and everything I’ve achieved, banida bakin yi miki da Abba godiya. Allah saka da alkhairi ya cigaba da sanya miki albarka a rayuwarki ya kuma ci gaba da kai rahama kabarin Abba.”
“Ameen Alhj tare da iyayenka kai ma.”
“Kin hak’ura zaki biyoni gida?”
“Har sena amsa tukuna zaka tabbatar da hakan?”
“Gani nake kaman mafarki nake Hjy Surayya, Allah yabar min ke tabbas irinku acikin mata d’ad’d’aiku ne.”
“Ameen Alhj na.”
“Mey hakan ke nufi kenan Hjy Surayya? Kin hak’ura kin yafe mun kenan?”
“We all make mistakes Alhj amma ba dukan mu bane muke gano kuskurenmu har ma mu nemi tuban wanda muka wa laifi, shin meyasa bazan yafe maka ba tunda har kai ka gane kuranka ka kuma nemi tuba? Na yafe maka Alhj Allah kuma ya yafe mana gabaki d’aya” ta k’arashe tana murmushi. Daddy baze iya kwatanta irin farin ciki da murnan da kalamun Mummy suka sanyasa ba. Da murmushi kwance fal a fuskansa ya mik’a hannunsa ya rik’o nata “Thank you so much Hjy Surayya I can say my life has never been better until I met you, Allah ya cigaba da miki albarka ya kuma barmu tare.”+
“Ameen Alhj you’re welcome.”
“Kinsan wani abu?”
“Seka fad’a.”
“I love you” yana sanar da ita bata san lokacin da ta fashe da dariya ba “Ji Alhj de, yaushe kuma muka fara wasan nan?”
“I’m serious Hjy Surayya saboda bana fad’a miki doesn’t mean I don’t love you, I love you like the day I just met you Hjy Surayya never forget that.”
“Thank you Alhj.”
“Thank you kad’ai? Ni bazaki cemin I love you in return ba?”
“Ka ga La’asar ya kusa gara ka tashi ka fice muyi niyya duka.”
“Yau kuma? Toh sekin fad’a min zan bar nan.”
“Lallai kuwa, nikam ka ga tafiya na” bata kai ga mik’ewa ba ya dakatar da ita ta hanyan kama hannunta. “Alhj ka sakeni mana!”
“Nak’i”
“Zan tara maka jama’a fah.”
“Ni d’in Hjy Surayya? Ni d’in naki?”
“Toh ka sakeni.”
“On one condition.”
“Name it.”
“Yaushe zaki dawo gida? Ina matuk’an kewarki.”
“Kai da zaka k’aro amarya kode ka manta ne?”
“Amarya daban ke daban so yaushe zaki dawo keda ‘yan’yan namu?”
“Zamu dawo karka damu.”
“Promise?” Kai zalla ta gyad’a mar sannan ya saketa “Toh se anjima ki gaishe mun da Nazeefah da Khaleefah.”
“I’ll semun sake magana.” Da haka ta fice ciki inda shi kuma ya mik’e ya yi tafiyarsa.
D’akinta da Nazeefah ta wuce direct inda ta tarar da Nazeefah mik’e kan gado kaman maciji ta zurfafa a cikin tunani ko makaranta tak’i fita. “Tashi ki zauna muyi magana” Mummy tace da ita bayan ta zauna a gefenta ta bakin gadon. Ba gardama ta mik’e ta zaune.
“Ina son ki saurareni da kunnen masu hankali a matsayinki na musulma me kar6an k’addara me kyau ko akasin sa.” Tun anan gaban Nazeefah ya fara bugun d’ari-d’ari dukda cewan bata fahimci inda Mummy ta dosa ba.
“Ki sani cewa komai na faruwa ne bisa dalili fatan mu kawai Allah ya sa hakan kawai shi ne mafi alkhairi a gareku gabad’aya.”
“Mummy ban fahimce kiba shin mey kike fad’i? Meya faru?”
STORY CONTINUES BELOW
“Ga wannan takardan ki ne Afzal ya kawo wa Daddy jiya yana mey baki hak’uri kuma” ta fad’a had’e da mik’a mata. Jiki na k’yarma Nazeefah ta mik’a hannu ta amsa had’e da bud’ewa sannan ta karance hawaye kawai Mummy taga na gangara daga idanunta ba makawa.
“Nazee-“
“Noooo!” Tasa wani irin d’ankaren ihu “Noo this can’t be happening, bani Ya Afzal yayi niyyan saka ba na tabbata munafukan chan ce ta tilasta mai ya rabu dani wallahi bani yayi niyyan saka ba Munmy.”
“Nazeefah ya isa” Mummy ta fad’a tana k’ok’arin shawo kanta saidai hakan sake tunzirata yayi. Zabura tayi tana kad’a kai yayinda hawaye ke ambaliya a fuskarta “Mummy wallahi bani Ya Afzal yayi niyyan saka ba ki yarda dani.”
“Nazeefah please-“
“Tsaya kiga ina key’n mota na inje in samesa kiji bani bace wannan takardan Amal ne ba nawa ba.”
“Wani irin banzan magana kike Nazeefah? Bayan ga sunanki nan boldly rubuce akai? Taya zakice ba naki bane na Amal ne?”
“Wallahi Allah ba nawa bane ina key’n mota na yake?”
“Shin wai ina zakije?” Ta tambayeta. “Zan je in samesa saboda bani yayi niyyan saka ba.”
“Nazeefah there is no point kiyi hak’uri ki rungumi k’addarar ki kowa yasan rabuwa da masoyi da zafi amma ba yadda kika iya.”
“Hak’uri? Hak’uri Mummy? Wallahi inde akan Ya Afzal ne bazan ta6a hak’ura ba.”
“Toh ya zakiyi? K’addara ta riga fata, the earlier kikayi accepting gaskiya the better.”
“How Mummy? So kike kice mun shikenan na rasa Ya Afzal a rayuwa na kenan? So kike kice in nad’e hannu in bar Amal ta sace mun miji ina ji ina gani?”
“Kema kinsan Amal baza ta ta6a yin hakan ba, Amal ba ita ta sace miki miji ba Nazeefah, Allah ne ya k’addara rabuwan ku.”
“No Mummy kinyi kuskure, idan ba mutuwa ba banga abinda ze rabani da Y Afzal ba” mayafinta ta sanya ta janye key daga gaban dresing mirror da niyan ficewa inda Mummy ta cafke mata hannu.
“Bada yawu na zaki fita ba Nazeefah.”
“Just let me go” tace da ita had’e da fisgan hannunta. Kaman a kyaftawan ido Mummy ta isa bakin k’ofa ta kulle da key had’e da zarewa ta rik’e a hannunta.
“Mummy ki matsa mun.”
“Ba inda zakije Nazeefah saki ne ya riga ya auku ba abinda kika isa kiyi da zeyi reversing case d’in sede hak’uri kawai, ki d’au komi a matsayin k’addara ki yi tawasalli.”
“Na gaya miki Mummy inde akan Ya Afzal ne bazan ta6a hak’ura ba har se sakin nan ya koma kan Amal, bazan rasashi ni kad’ai ba se inde mu biyu duka mu rasa sa so move out.”
“Ina nan tsaye anan ba inda zaki.” Dube-dube Nazeefah ta shiga yi a d’akin chan ta hango wuk’a a kan bed side drawer nan da nan taje ta d’auka ta saita dai-dai wuyan hannunta (wrist) “Ko ki matsa ko in yanke kaina in mutu” Baki Mummy ta hangame cike da mamaki da k’in yarda tana kallon Nazeefah, batayi tsammanin rashin sanin addinin nata har yakai matakin da za tayi tunanin d’aukan ranta da kanta ba.
“Nazeefah?” Ta kirata da d’umbun mamaki. “Da hankalinki?”
“Mummy banida wata amfani tunda na rasa Ya Afzal gara in mutu in huta kowa ma ya mutu.”
“Da hankalinki kike tunanin d’aukan ranki da kanki? Shin baki san hukuncin hakan bane a addinance?”
“I don’t care Mummy amma bazan iya rasa Ya Afzal ba I can’t because I love him, I love him so very much and Amal stole him away from me, what else can I do?”
STORY CONTINUES BELOW
“Idan kika hak’ura komi mey wucewa ne Nazeefah wataran se labari.”
“No Mummy I can’t move on, bazan ta6a iya son wani bayan Ya Afzal ba, I can’t do without him dan Allah ku bashi hak’uri ya mayar dani d’akina.”
“‘Yar uwarki Amal kuma fah? Ya kikeson ayi da ita?”
“Ki daina kwatanta ta da ‘yar uwata, idan da ta d’aukeni a matsayin ‘yar uwarta da bazata sace mun miji ba so ki matsa ko kuma in yanke kaina.”
“It doesn’t have to be this way Nazeefah” Mummy ta sanar da ita tana mey matsowa kusa da ita a hankali.
“Mummy stay away.”
“Nazeefah dan Allah kiyi hak’uri karki yanke kanki” ko kallon ta Nazeefah batayi ba ta sa wuk’an ta yanke hannunta wani irin ihu Mummy ta k’urma had’e da k’arisawa kan Nazeefah da ta shiga zamewa k’asa. Tarota Mummy tayi suka sauk’a k’asan atare tana mey bubbuga fuskanta yayinda idanunta suka cigaba da kakkafewa. “Nazeefah? Nazeefah? Innalillahi dan Allah ki tashi Khaleefah!” Ba shiri ta saketa ta d’auko wayanta had’e da kiran Daddy. A karo na farko ya d’aga, ko daman magana bata basa ba tace, “Alhj ka juyo ka juyo da wuri Nazeefah ta yanke kanta.”
“What?!’ I’m on my way” U-turn yasha nan take ya dawo ba tare da 6ata lokaci ba akayi da Nazeefah nearest clinic inda akayi emergency room da ita.
_53 minutes later_
Da wani irin gudu Afzal ya shiga haraban asibiti sannan ya nemi waje yayi parking ya fito ya k’arisa ciki. Tsaye a inda akayi mai kwatance ya same su da tashin hankali bayyane karara a fuskokinsu.
“Afzal?” Daddy ya kirasa yana mey mamakin yadda akayi yasan halin da suke ciki.
“Afzal waya sanar da kai muna nan?” Mummy ta tambaya.
“Mummy nine” Khaleefah ya amsa.
“How’s she?” Afzal ya tambaya. Shiru ne ya d’auki wajen se chan Mummy ta amsa “Muma jira muke likitocin su fito tukuna.”
15 minutes more sega emergency room d’in ya bud’u nan duk suka duk’ufa sukayi wajen kowa da abinda yake tambaya. Nan Dr’n ya musu bayanin komai yakuma tabbatae musu cewa cut d’in beyi affecting Radial artery nata ba in less than an hour zata farfad’o. Godiya suka masa sannan ya fice.
“Daddy, Mummy I’m so sorry I’m terribly sorry nasan duk laifi na ne.”
“Ko kad’an Afzal” Daddy yayi saurin katsesa “you’re not to be blamed for anything, idan har akwai mey laifi anan toh nine so kabar damuwa.”
“Mummy I’m sorry.”
“Don’t be Afzal mungode da kulawanka in shaa Allahu zan sanar da Nazeefah zuwanka.”
“Thank you Allah ya bata lafiya.”
“Ameen mungode Khaleefah ka rakasa” cewan Mummy.
“No don’t bother” Afzal yayi saurin amsawa sannan ya fice. Gida ya wuce direct sede tun shigansa Amal ta karanci yanayinsa wani iri. Bayan ta mar sannu da zuwa ta d’auko masa ruwa ta zauna a gefensa. “Ya Omri lafiya?”
“Babu” ya amsa sama-sama.
“Kaman ya babu Ya Omri? Tell me kaji.”
“Nagaji ne kawai barin je in watsa ruwa in huta” hannunsa tayi saurin kamawa” kafin ya mik’e “Please tell me Ya Omri nasan akwai abinda yake damunka.”
“Rania I’m sorry.”
“Why what for?”
“Rania it’s Nazeefah tana kwance a asibiti yanzu haka as we speak.”
STORY CONTINUES BELOW
“Subhanallahi meya sameta?”
“Yanke kanta tayi.”
“Nazeefan? Dalili?”
“Batun takardan ta, yanke kanta tayi in attempt to kill herself.”
“I want to go and see her Ya Omri.”
“Rania-“
“Please” tayi saurin katsesa “Ya Omri ji nake kaman duk laifi na ne, komin mey Nazeefah tayi laifi na ne.”4
“Kar kiyi magana haka Rania, in har akwai wanda za ayi blaming anan mahaifinku ne and he’s sorry mu taya Nazeefah da addu’a kawai Allah yasa ta gane gaskiya da wuri.”
“Ameen but I still want to go and see her please kar ka hanani Ya Omri.” Hannunta ya d’au ya rik’e a cikin nasa “Okay zanyi wa Mummy magana se muje.”
“Thank you.”
“Don’t mention so me kika girka mana? I’m hungry.”
“Spaghetti ne kawai nima ban dad’e da dawowa daga school ba.”
“Oh! Muje toh.”
****
Bayan Maghrib Afzal yayi wa Mummy waya inda ya tabbatar da cewa ba a sallamesu ba har anan sannan yace mata suna shigowa shi da Amal. Acikin k’ank’anin lokaci suka isa inda Mummy ta taresu ta k’arisa ciki dasu. Nazeefah na ganin Amal taji tsikan jikinta gabad’aya na tashi yayinda ta shiga yi mata wani irin tsananin tsana.
“Mey wanann take mun a d’aki Mummy? Send her out send her out!”
“Nazeef-“
“Bana k’aunan ganinta a kusa dani ku fitar mun da ita daga d’aki” ta katse Mummy da hanzari.
“Nazeefah please” Afzal ya sa baki. “Kiyi hak’uri.”
“Hak’uri Ya Afzal? Da abinda zaka sak’a mun kenan? Ashe for all these while k’arya kake mun? I never expected this from you, I thought you love me ashe ba haka bane, ka sani daga kai har matar taka bazan ta6a yafe muku wannan abu da kuka mun ba Mummy send them out.”
“Nazeefah dan Allah kiyi hak’uri” Amal tace da ita.
“Ko da wasa karki kuskura ki sake kiran suna na Amal saboda keba ‘yar uwata ba ce. You ruined my life, first you stole my father away from me and then now my husband, meyasa kike nok’e-nok’e? Ki fito fili kice kina son ki zama ni kina son ki sace nun rayuwa. Amal na tsaneki, na tsani duk wani mey sonki, ba kuma abinda ze fi mun nishad’i da jin dad’i kaman inga gawanki bana k’aunanki in har kina son kanki ki ficemun daga d’aki you have absolutely no right to speak to me get out.” Hawaye Amal ta shiga yi yayinda Afzal ya janyeta jikinsa “Ku fice mun daga d’aki bana k’aunan ganinku duka.”
“Nazeefah meyasa bakida mutunci ne?” Mummy ta tambayeta tana mey tsananin jin takaicin abinda Nazeefah ta aikata.
“Shikenan Mummy zamu koma” fad’in Afzal “Nazeefah Allah ya baki lafiya we mean you no harm” daga fad’in haka ya sauk’o da ganinsa akan Amal “Let’s go Amal.” Badan Amal na so ba ta amince ya jata waje se kallon Nazeefah take tana kuka itako Nazeefah ko sake kallon 6angarensu batayi ba.
“Meyasa baku barni na mutu ba Mummy? I hate my life I hate Amal.”
“Nazeefah it pains me as a mother ace ni na tsuguna na haifeki, Allah ma shaida ne ni ba tarbiyyan dana baki ba kenan, bansan a ina kika d’auko wannan banzan hali ba dan bazan ce na mahaifinku bane saboda koda wasa be ta6a gigin d’aukan ransa da kansa ba. Kuma Amal da kike gani kika raina wataran zaki nemata hannu bibbiyu ki rasata kuma ko kin k’i kin so ‘yar uwarki ce ba abinda zaki iyayi da ze canza hakan. Ki tashi ki ci abinci yanzu za’a sallameki zamu koma gida.”
STORY CONTINUES BELOW
“Wani gida?”
“Ban gane wani gida ba gida gida mana.”
“Meya samu hotel da muke zaune aciki?”
“Zamu koma gida gun Daddy’nku nide na fad’a miki.”
“No Mummy ni bazan koma gun Daddy ba, a dalilin mey? Bayan duk bak’in ciki da k’uncin da nake ciki shine sanadi.”
“So? He’s still your father nothing can change that.”
“Ni gaskiya bazan bi ku ba.”
“Ni na fad’a miki” tana kaiwa nan ta fice had’e da rufo mata k’ofan.
****
Tun da suka shiga mota har suka isa gida Amal take ta kuka.
“Amal it’s okay with time in shaa Allah Nazeefah zata fahimci komai kukan ya isa haka” Afzal yace da ita bayan sun k’arasa ciki yana mey share mata hawayenta.
“Yaya I feel so responsible for everything Nazeefah is going through, Nazeefah tana sonka har yau har gobe tana sonka she can’t ever stop loving you.”1
“And you too Lily, you love me don’t you?”
“I do Yaya amma Nazeefah kuma fah? Yaya har ranta fa ta so d’auka akan soyayyar ka.”
“Amal you matter to me more than anyone morethan Nazeefah kibar tada hankalinki kinji? I love only you” rungumeta yayi a hankali itama ta zagaye hannayenta a bayansa tana mey lumewa acikin rik’onsa yayinda kalamun Nazeefah suke faman yi mata wasa a kai.
****
Washegari…
Dawowan Daddy daga gidansu Mami kenan amma sam babu walwala tattare da shi. Yana shigowa Mummy da ta karanci yanayin nasa tayi mai sannu da zuwa.
“Tak’i amincewa?” Ta tambayansa a hankali.
“Hjy Surayya ko bani dama in nemi tubansu sun hanani bale in sanar dasu k’udurina, Jameelah tana matuk’ar fushi dani haka ma mahaifinta. Ban san ya zanyi ba muddin tak’i yafe mun, alhak’in ta ya cigaba da bina kenan idan da ma akaina kad’ai ze tsaya da da sauk’i amma har ku baku tsira ba, bana k’aunan sake ganin ku cikin k’unci Hjy Surayya bana son abinda ze sake raba kanmu yadda na samu da k’yar Nazeefah ta amince ta biyoki kuka dawo mun.”
“Ka kwantar da hankalinka Alhj.”
“Ta yaya Hjy Surayya? Ta ina hankalina yaga ta kwanciya bayan rayuwan mu duka yana cikin gwagwarmaya.”
“Ni da kaina zanje in samu Jameelah gobe muyi magana in shaa Allahu zata yafe maka komai ta kuma amince da k’udurinmu.”
“Keda kanki?” Ya tambaya yana mey kasa 6oye mamakin da ya sha.
“Baka yarda bane?”
“Hjy Surayya a ina aka ta6ayin haka? Dan Allah karki baiwa kanki wahala-“
“Kabar zancen nan Alhj” tayi saurin katsesa “Ai mun wuce haka yanzu try not to worry Allah kaimu goben.”
“Ameen Hjy Surayya banida bakin yi maki godiya, Allah saka ya biyaki da gidan Aljannah.”
“Toh kuma godiyan mey kake? Muje kaci abinci.”
“Ya jikin Nazeefah?”
“Da sauk’i tana kwance a d’aki tana bacci.”
“Toh madallah”.****
STORY CONTINUES BELOW
Tamkar mey ta6in hankali haka Nazeefah ta zame musu a gidan ko abinci tak’i ci tun dawowansu daga asibiti jiya da dare har izuwa yinin yau. Allah ma yaso ana sa mata ruwa. Banda kuka ba aikinta a gidan, Mummy tayi mata nasiha tayi mata fad’a amma ina tak’i ji haka zata kafa hotunan auransu da Afzal tayita kalla ba fashi. Washegari kamar yadda Mummy ta d’au alk’awari ita da Daddy suka jesu gidansu Mami inda ya tsaya daga waje ita kima ta k’arasa ciki. Sallama tayi yayinda take sa kai cikin gidan, Mami dake gida ita kad’ai ce ta amsa. Kallo d’aya tayiwa Mummy ta tabbata mahaifiyar Nazeefah ce saboda tsan-tsan kaman da sukeyi.
“Mahaifiyar Nazeefah?” Ta tambaya. murmushi Mummy ta saka had’e da gyad’a mata kai. “Bismillah ki shigo” tabarma ta shimfid’a musu inda suka zauna sannan suka gaisa.
“Bari in kawo miki ruwa.”
“A’a ‘yar uwa ba amfani.”
“Toh lafiya dai ko?”
“Lafiya k’alau batun Abdallah nazo muyi magana.”
“Kiyi hak’uri maman Nazeefah amma in har abinda ya kawo ki kenan saidai ki koma.”
“Nasani ‘yar uwa nasan abinda Abdallah yayi miki da zafi da ciwo amma abu ne ya riga ya faru ba abinda zamu iyayi da zai canza hakan saidai muyi gyara. Kiyi hak’uri ki yafe masa, shi yafiya ba kowa bane Allah yake basa iko da zuciyan yi amma na tambayeki ne saboda nasan zaki yafe masa saboda ko ban tambaya ba nasan a wajenki ‘yarki Amal ta yo gadon kyawawan d’abi’unta. Idan muka ce zamu biye ta zuciyoyin mu toh wallahi ba abinda zamu tsinana wa kanmu na arziki. Ko ban fad’a miki ba nasan kinsan irin tsanan da ke tsakanin yaran mu Nazeefah da Amal. Duk yadda Amal ke son shirya tsakaninta da ‘yar uwarta hakan ya gagara kuma ba wanda ze iya had’a mana kawunan yaran nan sama da ke.”
“Ban fahimce kiba Maman Nazeefah ta yaya zanyi hakan?”
“Ki amince ki auri Abdallah.”
“Iyyeh?” Mami ta zaro ido wuru-wuru waje. “Kikace?”
“Eh, ki amince ki auri mijina ta hakan ne kawai zamu iya gyara zuri’ar mu mu had’a kawunan yaran nan dan Allah ki amince.”
“Kiyi hak’uri Maman Nazeefah amma bazan iya cika miki wannan buri naki ba, bazan iya auran Khaleefah ba bazan iya ba.”
“Zaki iya ‘yar uwa muddin kika yarda da hakan, dan Allah karki bari tsanan dake tsakanin yaran nan yayi tsamari iche tun yana d’anyensa ake iya tank’warasa, muddin ba’a sa musu a jiki cewa mun zama abu d’aya ba yanzu toh wallahi gaba tsanan da zasu tashi dashi a cikin zuciyoyinsu baze so yayi kyau ba ki taimaka.”
“Maman Nazeefah tunda nake ban ta6a jin inda uwar gida tazo taya mai gidanta k’aro aure ba ko da kuwa a radio ne, saboda haka ban san abinda ke cikin zuciyarki ba keda mijinki, bansan mey kuke shirin yi mani ba amma koma menene kuyi hak’uri ku janye ni daga cikin matsalarku tunda na samu auren ‘yata be mutu ba Alhamdulillah koni na mutu a haka bazan damu ba.”
“Jameelah da zuciya d’aya nazo na sameki bada wata manufa ba, Jameelah har yau har gobe nasan Abdallah yana sonki, kema kin sani ba sena fad’a miki ba, ni kuma har ga Allah har cikin zuciyata tun cemin da Abdallah yayi bakida aure naji tausayinki ya shige min zuciya nasan ba komai ya hanaki yin aure ba illa idan kika juya baya kika ga abinda Adallah yayi miki, shi ya lalata miki rayuwa dan haka kuma shi ya tantanci yayi making everything right don haka na basa goyin baya na bashi shawaran ya auro ki. Kuma kinga ta hakan ne kawai zamu iya had’a kawunan yaran mu. Zan barki kiyi tunani anytime your mind is made up ga lamba na” ta fad’a had’e da ajiye mata wani gajeren paper data rubuta number’nta ajiki “Seki kirani, hope to hear from you soon ni zan wuce.”
STORY CONTINUES BELOW
“Toh bari in rakaki.”
“Ba amfani ‘yar uwa yi zamanki nagode da wannan lokaci da kika bani se anjima.” Tun fitan Mummy Mami ta shiga tunani, gabaki d’aya kanta ya d’aure se bata jikinta yake trap su Mummy suke shirin shirya mata in ba haka ba har a ina uwar gida ta ta6a aran bakin mijinta dan nema masa mata?
Daddy kuwa a gida ya sauk’e Mummy ya wuce gidansu Amal, yasani it’s now or never. Bayan mey gadi ya bud’e mishi gate ya k’arasa ya samu gu yayi parking sannan ya fito ya nufi entrane door inda yake ta knocking amma ba response kasancewar bacci da suke duka daga ciki. Ganin ba mahalicci se Allah kawai seya kira wayan Afzal. Kaman a mafarki Afzal ya soma jin ringing na wayansa dake ajiye akan side drawer’n kansa kafin ya mik’a hannu ya d’aga har Amal itama ta farka. Sorry go back to sleep” ya sanar da ita rik’e a hannunsa yana mey sake daidaita kanta a k’irjinsa sannan ya d’au wayan inda ya tarar da missed call na Daddy nan take ya kirasa back, “Halo Daddy?
“Na’am Afzal gani a bakin k’ofan gidanku fa amma shiru ko bakuwa nan ne?”
“Afuwan Bacci ne ya d’auke mu bari inyi ma mey gadi magana ya bud’e maka.”
“No already ina ciki ya riga ya bud’e mun ina bakin parlour ne.”
“Sorry bari ina fitowa yanzu” ya fad’a had’e da kashe wayan sannan ya sauk’o da kallonsa akan Amal “Rania bari in fita Daddy yazo yana waje.” Kai zalla ta gyad’a masa sannan ta koma gefe ta cigaba da kwanciyanta. Jallabiyansa ya sanya ya fito ya bud’e wa Daddy yana mey sake basa hak’uri. Ruwa da juice ya d’auko masa inda suka gaisa yake tambayansa ya jikin Nazeefah.
“Da sauk’i Alhamdulillah.”
“Toh Allah k’ara mata lafiya.”
“Ameen yaya Amal kuma?”
“Lafiyanta itama.”
“Ina sake baka hak’uri game da abinda Nazeefah tayi muku ranan, ni kaina I’m having a hard time with her kuyi hak’uri kuyi mata uzuri.”
“Ba komai Daddy duka nan mun san what she’s going through is not easy fatan mu Allah kawo mata sauk’i.”
“Ameen Afzal thank you.”
“Ba komai Daddy.”
“Yauwa dama batun Amal nazo ne Afzal, ina son muyi magana da ita in kuma bata hak’uri gameda duk wani abinda nayi mata, Afzal ka sani a addu’a I want to make everything right I want to marry Amal’s mother.” Mamaki da dad’i ne ya ziyarci zuciyan Afzal wanda ya kasa 6oyewa “Tabbas kayi tunani Daddy, Allah sanya alkhairi acikin hakan ya biya maka buk’atunka na alkhairi.”
“Ameen Afzal zan iya yi ma Amal magana.”
“Sure tana bacci bari in tayar da ita.”
“No no in tana bacci ka barta kawai ko gobe ina iya dawowa.”
“A’a don’t worry.” D’akin nasu ya koma yaje ya samu Amal ya shiga tada ita. “Rania?”
“Uhmmm?”
“Daddy yazo.”
“Uhmm?”
“Yana son ya ganki kuyi magana.” A hankali ta bud’e idanunta “Yaya I don’t want to face him ban san mey zance mishi ba.”
STORY CONTINUES BELOW
“I know Rania, I know kiyi hak’uri kije kiji mey zai ce miki.”
“Yaya-“
“Kar muyi haka dake kinji? Tashi hungo kayanki kisa” da kanshi ya mik’ar da ita zaune ya sanya mata kayan da hijabi suka fito suka zauna a kan two seater.
“Ina yini Daddy?” Ta durk’usa har k’asa ta gaishesa.
“A’a please Amal koma ki zauna Afzal ce mata ta zauna” duk da haka Amal tak’i mik’ewa seda ya amsa tukuna. Gaisawa sama-sama sukayi sannan ya fayyace mata dalilinsa na zuwa dan ya nemi tubarta.
“Nasan na cuceki a rayuwa Amal, nasan nayi depriving naki duk wani right da gatan da kika cancanta a rayuwarki, nasan ban kyauta miki ba ban kuma kyauta wa mahaifiyarki ba amma gani yau nazo neman tubanki” ya k’arasa had’e da sauk’a k’asa akan guiwoyinsa. “Daddy please ka tashi” tayi saurin cewa amma yak’i. “I’m dearly sorry Amal, kiyi hak’uri ki yafe mun I’m here and ready to take full responsibility for everything ki bani dama in cika aiki na a matsayina na mahaifinki, ki bani dama in kula dake in soki a matsayina na mahaifinki da jini na ke gudana a jikinki. Amal I’m so sorry” Afzal be ji tashin Amal ba kawai ganinta yayi gaban Daddy tana k’ok’arin d’agosa “Don’t be Daddy komai ya riga ya wuce ka kuma sani ni na riga na yafe maka komai da jimawa Allah ya yafe mana gabad’aya.”
Rungumeta tsam yayi a jikinsa cike da farin ciki yayin da duk suke zubda hawayen jin dad’i “Oh Amal thank you so much Allah cigaba da yi miki albarka bansan da wani bakin zan yi miki godiya ba.” Itama a hankali ta zagaye hannunta a bayansa “Ameen Daddy ka daina yimun godiya.” Se murmushi Afzal dake ganin komi kaman a mafarki yake faruwa, this’s all he’s ever wanted, ranan da Allah ze bayyana musu mahaifin Amal ya nemi tubanta su shirya se gashi Allah ya kawo musu ranan.
“Amal?”
“Na’am Daddy” ta amsa.
“Amal nasan kinsan yadda Mahaifiyarki ta tsaneni ko?” Shiru tayi bata ce komai ba. “Amal I need your help, Mahaifiyarki tak’i ta bani dama in bata hak’uri bale in nemi tubanta Amal a shirye nake da in auri Mahaifiyar ki in har zata amince.”
“Zaka auri Mami?” Ta tambayesa d’auke da d’unbun mamaki.
“In har zata amince, eh.”
“Mummy kuma fa? Bana son abinda ya faru tsakani na da Nazeefah ya faru dasu suma, in har Mummy bata goyi bayan zancen nan ba babu amfani Daddy.”
“Hasali Mummy’nku nema ta kawo shawaran nan Amal, Mummy’nku batada matsala da hakan idan har keda mahaifiyarki kun amince.”
“Kayi wa Mami magana ne?”
“Naso amma tak’i bani dama d’azu nida Mummy’nku mukaje tayi mata magana sede har yanzu bata shirya bamu had’in kai ba please help me Amal nasan bani da daman tambayan hakan daga gareki but Amal I love your mom, har yau har gobe ina sonta kuma ina son in aureta.” Na matuk’a Amal taji dad’i ta juma tana mafarkin rananda Mami zata shiga d’akin mijinta itama koda sau d’aya ne taji dad’i a rayuwanta. Inde hakane kuwa se inda k’arfin ta ya k’are inshaa Allahu bazata gaji ba seta shawo kan Mami waya sani ko da haka Nazeefah zatayi accepting nata ta bata chance suyi working out relationship nasu.
“Amal? Bazaki iya ba ko? Bakiya son mahaifiyarki ta kasance tare dani ko? Look I’m terribly sorry wallahi nayi nadaman abinda nayi muku please forgive me.”
“Ko kad’an ba haka bane Daddy hasali nayi murna da farin cikin wannan labari in shaa Allah kuma zan tayaka yima Mami magana.”
STORY CONTINUES BELOW
“Nagode sosai ‘yata Allah miki albarka sak’a miki da alkhairi.”
“Ameen Daddy.”
“Toh ni bari zan koma.”
“Da wuri haka Daddy?” Fad’in Afzal “kabari mana muci dinner.”
“A’a karka damu.”
“Please stay Daddy” Amal ta sanya baki.
“Tunda ‘yata tasa baki na isa ince a’a? Se in jira d’in.” Dad’i sosai both Amal da Afzal suka ji haka Daddy ya yini musu koda Mummy taji shiru ta kira ta tambayi dalili kuwa ce mata yayi se zuwa dare ze shigo, zeci dinner a gidansu Amal. Kafin su dawo daga masallaci Amal har ta gama tsara kan dining da had’ad’d’un dishes ta bi gidan da turaren wuta. Nan tayi musu magana suka k’ariso se yaba abincin nata Daddy yake Afzal na ta jin dad’i ana yaba girkin matarsa. Hira suka sha kaman ba gobe anan Daddy ya gano ababe da dama tattare da Amal, he’s in every way submissive to be a great Dad to Amal. Da yazo tafiya kuwa har wajen motansa suka rakasa sannan Amal tace a gaishe mata da Nazeefah.
Washegari…
Wajajen sha d’aya Amal ta dawo daga school bayan morning lectures nata ya k’are. Tana dawowa ta kama shara bayan ta gama ta aza tukunyan tuwo sannan ta d’au waya ta kira Mami wacce ta d’aga a karo na farko.
“Halo Mami.”
“Na’am Amal ya kike?”
“Ina yini Mami? Ya kike ya Papi?”
“Lafiya k’alau ya Afzal?”
“Yana office.”
“Makaranta fah?”
“Alhamdulillah ban jima da dawowa bama kinsan mun kusa fara exams.”
“Aww haba? Se part 4 kuma ko?”
“Eh in shaa Allah.”
“Toh Allah sanya alkhairi ya bada sa’a mamana.”
“Ameen Mami.”
“Ba wata matsala dai ko?”
“A’a ba komai.”
“Toh madallah.”
“Mami jiya Daddy yazo.”
“Wani Daddy d’aya?”
“Daddy mahaifin Nazeefah.”
“Kuma mahaifinki ba.”
“Eh” ta amsa tana murmushi “jiya yazo muka yini se bayan Isha ya tafi.”
“Allah sarki.”
“Yazo ya nemi tuba na.”
“Kin yafe masa?”
“Eh Mami.”
“Madallah toh yayi kyau.”
“Mami kefa?”
“Baby-“
“Mami kiyi hak’uri komi ya riga ya wuce Daddy yace min yana son ya aureki.”
“Baby ke kanki kinsan baze yiwu in auri mahaifinki ba ko?”
STORY CONTINUES BELOW
“Dalili Mami? Hasn’t it always been your advocate to get married someday?”
“Yes Baby amma ba ga mahaifinki ba.”
“Meyasa Mami? Didn’t you loved him? Dan Allah kar kiyi ma Daddy haka.”
“Baby bazaki gane bane.”
“Toh meneh Mami? Daddy yana sonki har yau har gobe kema kin sani.”
“Baby ba wannan bane matsalar.”
“Toh meye ne?”
“Mahaifiyar Nazeefah.”
“Mummy? Me tayi?”
“Baby bakiya ganin kaman wani muguntan suke shirin yi mun? In ba haka ba a ina ne kika ta6a ganin inda uwar gida tazo nema wa mai gidanta aure?”
“Gaskiya ba a ta6a yin hakan ba amma kuma I trust Mummy na tabbata Mummy baza ta ta6a aikata abinda ze cutar dake ba Mami.”
“Wai meyasa kike biye wa Mahaifin naki ne haka?”
“Because he loves you Mami and he’s sorry mey aciki idan kin yafe masa kunyi reconciling? Duk mun san abinda Daddy ya miki da ciwo da zafi amma yayi nadama Mami please kiyi hak’uri ki yafe masa ki sauraresa.”
“Baby-“
“Please Mami do this for me” rok’an kanta Amal ta rik’a yi amma ina Mami fa sam babu a ranta ta auri Daddy. Suna gama wayan Amal ta kira Papi ta irga masa komai mamaki yasha yadda har abu haka ze faru amma Mami bata sanar da shi ba. Chan dare bayan sun k’are cin abinci yayi gyaran murya had’e da kiran sunanta.
“Na’am Abba wani abu ne?”
“Tun shekaran jiya kika ce Khaleefah be sake shigowa ba?” Dum taji zuciyanta ya tsinke amma sam bata kawo a ranta har Amal zata kirasa ta sanar da shi komai ba dan haka se tayi masa k’arya “A’a wani abu ne?”
“Meyasa kike yi mun k’arya Jameela? Yaushe kika fara haka?”
“Abba-“
“Ashe har matarsa ya turo da ta baki hak’uri amma kika k’i sauraronsu?”
“Abba ba haka bane.”
“Dakata tukuna, shi fa d’an Adam ajizi ne kuma dukan mu nan ba wanda zece baya yi wa Allah sa6o amma kuma mey? Da zaran muka tuba kuma muka nemi yafiyarsa yana yafe mana ba wanda yace Khaleefah ya kyauta abinda yayi miki amma tunda ya gane kuransa yana son ya dai-daita komai meyasa bazaki basa had’in kai ba?”
“Abba ba haka bane.”
“Jameelah har yanzu ke yarinya ce shekarunki dududu nawa ne? Kin kai arba’in ne?”
“A’a Abba”
“Toh haka kikeson ki k’are rayuwarki ba aure? Bakiya son ki bar yaran da zasu yi miki addu’a bayan kin rasu? Ko gani kike Amal ita d’ai ta isheki? Kisani fa dan ba na nuna miki bawai hakan na nufin ina jin dad’in zamanki a haka bane, kiyi wa kanki fad’a ki dubi tuban mutumin nan ku rufa wa junanku asiri.” Shiru tayi batace ko k’ala ba “Ko baki ji ba?”
“Naji Abba.”
“Toh tashi ki tafi.”
“Toh seda safe.” Ko bacci Mami ta kasa yi ranan se tuna abunda Amal da Papi suka fad’a mata take gabad’aya ta rasa mey take ciki ita har ga Allah bata k’aunan abinda ze sake had’ata da Daddy saboda kasa mancewa da abinda yayi mata da take. Duk sanda ta kallesa se ta tuna da wancan mumunar ranan taji ta tsanesa. Amma ya ta iya yanzu tunda har Papi yasa baki? Bayan nan kuma kaman yadda Mummy ta fad’a ko ba dan tana so ba kamata yayi ta amince saboda su gyara zuri’a su had’a kan yaransu. Daga k’arshe de kawai ta yanke hukuncin yin Istikhara duk abinda Allah ya za6an mata shi zata bi.
STORY CONTINUES BELOW
_One week later…_
Cikin satin nan da aka shiga su Amal da Nazeefah suka fara exams har yau Mummy bata sake ji daga Mami ba shima Papi be sake yi mata magana ba as ya zuba mata ido yaga iya gudun ruwanta. Amal da Afzal suna zaune a parlour se faman kallo yake a laptop nasa yasa earpiece a kunne ita kuwa se karatu take kasancewar tana da paper k’arfe d’aya gobe. Wayanta dake gefenta ne ya shiga ringing dubawanda zatayi taga new number, without hesitation ta d’aga tare da yin shiru.
“Assalamu Alaikum” akayi sallama daga d’ayan 6angaren.
“Mummy?”
“Ashe ‘yar tawa zata gane muryan uwarta.”
“Mummy ina yini?”
“Lafiya k’alau ya kike ya gida ya Afzal kuma?”
“Alhamdulillah dukan mu lafiya.”
“Ya exams toh?”
“Alhamdulillah Mummy ya Nazeefah? Jiya ma Khaleefah ya kirani muka gaisa.”
“Allah sarki ya Mami?”
“Lafiyarta k’alau.”
“Kwana biyu shiru banji daga gareta ba nace ko zaki iya mun texting number’nta.”
“Sure Mummy bari in miki texting yanzu.”
“Yauwa ‘yata thank you Allah ya bada sa’an jarabawa.”
“Ameen Mummy seda safe” nan tayi hanging take tayi mata sending numban Mami, itama Mumny tana gani tayi replying nata da ‘Thanks.’
“Lafiya dai ko?” Afzal da ya zare kunnen earpiece nasa d’aya ya tambaya.
“Lafiya kawai tana son su gaisa ne.”
“Oh Rania I’m hungry.”
“Toh Ya Omri baga kitchen ba.”
“Aww ma ni zanyi girkin da kaina?”
“Toh Ya Omri karatu fa nakeyi” ta fad’a cike da shagwa6a.
“Ni o’o” ya fad’a harda doke kafad’a wanda hakan yasa Amal dariya. “Toh mey kakeso kaci?”
“Na fasa chin abincin ma I just want to sleep.”
“Tun yanzu?” Ta tambaya had’e da duban agogo “it’s just 9 O’clock.”
“Yes Rania na gaji kallon ma na fasa.”
“Toh sekaje ka kwanta ai seda safe.”
“Ni kad’ai?”
“Toh Ya Omri baka ga karatu nakeyi ba?”
“Nasani anan nake nufi” kafin ta karanci abinda yake shirin yi kawai taji ya sauk’e kansa a k’irjinta ita ta rasa damuwansa, ga gado amma yace shi se a jikinta ze kwanta adjusting kansa yayi ya kwanta da kyau a jikinta “Toh goodnight” tace da shi.
“Goodnight Rania I love you.”
“I love you too Ya Omri” ta amsa had’e da placing peck a cikin gashin kansa. Handout nata ta d’auka ta cigaba da karatunta haka har bacci ya d’auketa itama. Se chan wajajen k’arfe biyu Afzal ya farka se jin numfashin mutum yake a kansa shafawa da yayi ya gano Amal ce. Murmushi ya saki sannan ya rik’e kanta ya janye nasa a hankali. Handout na hannunta ya cire ya d’agata ya kaita d’aki suka kwanta.
STORY CONTINUES BELOW
Washegari Mummy da Daddy suka jesu gidansu Papi kaman yadda Munmy ta sanar da ita cewan zasu shigo sede bata ce da Daddy ba sam Mami batayi farin cikin zuwansu tare ba amma ya ta iya? Sannu da zuwa tayi musu ta shimfid’a musu tabarma sannan ta kira Papi inda duk suka gaisa.
“Toh ga Jameelah nan sama da sati kenan yau ina jiran ji daga wajenta amma shiru se jiya da daddare bayan da Surayya ta kira take fayyace mun cewa tayi Istikhara kwanaki hud’u da suka wuce za6i kuma Allah yayi mata” se kuma yayi shiru.
“Muna jinka Abba” Daddy da ya kasa hak’uri ya tambaya.
“Khaleefah zan d’auki amanar ‘yata in baka ba wai dan ka cancanta ba se don yin hakan ne ya kamata kodan mu samu mu had’a kawunan yaran nan. Kai ba yaro bane ka riga kasan komai ba sena sake nanata maka ba seka taimaki kanka kayi abinda ya dace wannan duka matanka ne ka kwatanta yin adalci a tsakaninsu Allah ya baku zaman lafiya gabaki d’aya batun yafiya kuma duka mun yafe maka Allah yafe mana gabaki d’aya.”
“Ameen Abba nagode sosai in shaa Alalhu zaka sameni mey rik’on amana Jameelah nagode Allah sak’a da alkhairi.”
“Ameen” duka suka amsa.
“Abba in ba matsala bana so a jinkirta auren.”
“Toh Khaleefah gaskiya seka d’an bamu lokaci mu shirya.”
“Wani shiri Abba? Ba shirin da zakuyi zan d’au nauyin komai da komai ni kawai kar mu jinkirta.”
“Toh madallah zamuyi magana duk abinda tace haka za’ayi.”
“Toh nagode, nagode sosai zamu koma.”
“Toh Surayya kekuma Allah ya sak’a miki da alkhairi ya baki riban hak’uri tabbas irinku acikin mata d’ad’d’aiku ne Allah ya baku zaman lafiya mai d’aurewa.”
“Ameen Abba nagode” ta amsa.
“Toh zamu koma ga wannan” Daddy yayi maganan had’e da zaro wani bak’in leda daga aljihunsa wanda yake d’auke da kud’i.
“Na mey kuma? Kaga kar mu fara haka da kai.”
“Abba dan Allah kar kayi rejecting mu tafi Hjy Surayya.” Duk yadda Papi beso kar6an kud’in ba seda ya kar6a saboda yadda Daddy yayita insisting.
Da Maghrib bayan Daddy ya dawo daga masallaci Nazeefah tayi sallama ta shiga d’akinsa inda ta tarar da Mummy aciki. “Ya Nazeefah lafiya?”
“Daddy ina son bayan graduation namu inyi proceeding masters program d’ina.”
“Toh masha Allah anan Unimaid zakiyi?”
“A’a a UK.”
“K’asar waje?” Mummy tayi sayrin tambaya.
“Eh Mummy.”
“Ko meyasa?”
“Achan nafi so inyi yafi sauk’i.”
“Toh shikenan se ayi making arrangements amma ai sekin jira results naku sun fito.”
“Zan tafi tun yanzu in results d’in ya fito seku amsa min a tura mun achan, Nagode” tana kaiwa nan ta mik’e ta fice. Bayanta Mummy ta biyo “Why the sudden decision Nazeefah? I thought ke kikace bakiyason fita k’asar waje karatu?”
STORY CONTINUES BELOW
“I changed my mind Mummy.”
“Saboda mey?”
“Babu.”
“Saboda kiyi nesa da Amal yeah???”
“Mummy Amal ba matsala ta bace bani da damuwa da ita I’m doing this for myself.”
“Ke Nazeefah bakiya tunanin mutuwa ne? Rayuwan ma nawa take da har kike neman gujewa ‘yar uwarki haka?”
“Amal ba ‘yar uwata bace stop referring to her as one.”
“Da kin k’i da kin so Amal ‘yar uwarki ce yanzu maganan da muke da Daddy’nku ma shirin auro mahaifiyarta yake Jameelah.”
“What? Wa d’in?”
“Mahaifiyar Amal, Jameelah.”
“Wannan wani irin abin kunya ne? Kuma kika amince?”
“Hasali ni na kawo masa shawaran ma saboda mun riga mun zama abu d’aya yanzu.”
“What? Mummy are you okay? Taya zaki amince Daddy ya k’ara aure, auren ma wai mahaifiyar Amal of all people? Wallahi baza ayi abun kunyan nan da ni ba.”
“Ya kika iya? The earlier the better Nazeefah just accept it mu da su mun zamo abu d’aya.”
“No Mummy bazan ta6a accepting su Amal as one of my own ba duk abinda kuke shirin yi count me out cause I’ll never welcome their kind into my family.”
“Yayi miki kyau.”
****
Acikin wata d’aya Daddy yagama had’a d’akin Mami, an sa rana nan da sati uku. Da ikon Allah kuma su Amal suka k’are exams nasu results yafito alhamdulillah duk sunyi passing. Ba yadda Mummy batayi da Nazeefah ba da tabari se bayan d’aurin auren tayi tafiyan nata amma tak’i. Ana saura sati d’aurin aure tabar Nigeria.
****
“Rania lafiya?” Afzal daya kasa hak’ura dan jin meke faruwa ya tambaya.
“Ya Omri” kawai seta rushe da kuka.
“Subhanllahi!” da sauri yayo kanta hugging her in his arms yana bata hak’uri. “Ya Omri ta tafi” ta amsa at last.
“Ita wa?”
“Nazeefah” ta sanar dashi yana share mata hawayenta.
“Ta tafi ina?”
“UK tabar Nigeria tace bazata sake dawowa.”
“What? Meyasa?”
“Ya Omri har yau Nazeefah takasa acepting d’ina da Mami tun kafin ma taji Daddy ze auri Mami tace ita zata wuce Uk tayi proceeding masters nata yanzu kuma dataji gaskiyan al’amarin jiya bayan sunyi landing ta kira Mummy ta jaddada mata cewa bazata sake dawowa ba.”
“Shhh it’s okay sooner ot later zata gano gaskiya in shaa Allah kuma da k’afarta zata dawo.”
“I really do hope so Ya Omri bana son Nazeefah tayi nesa da gida the more she stays away from us the more lost she’ll be.”
“I know but don’t lose hope okay? Nasan Nazeefah she’ll soon come around.”
“Thank you Ya Omri.”
“Anytime, still zamu fita d’in ko?”
“Yes.”
“Alright toh.”
***
Mami ce zaune a d’akinta ta baje zannuwa da dama a gabanta tana za6an wanda zata kai d’inki. Tana cikin haka sega wayanta dake gefenta ya shiga ruri dubawan da zatayi taga Daddy ke kira. ‘Yar murmushi ta saki sannan ta d’aga.
“Amarya bakiya laifi koda kin kashe d’an masu gida ne.”
“Haka de kace” ta amsa tana murmusawa.
“Toh ya kike?”
“Lafiya k’alau ya ‘yar uwata?”
“Lafiyanta k’alau yanzun tace tasan kanki yayi zafi k’ila ma kina jin yunwa amma ba hankalinki.”
“Ai kuwa wallahi ina ta sorting kayakin nawa.”
“Toh mey kikeso ayi miki ordering wai?”
“Laaa kace mata kar ta damu zan dafa taliya in ci.”
“A’a nikam kinga aikana tayi fad’a mun.”
“Toh inde haka ne kace mata duk abinda ya sawwak’a.”
“Toh shikenan ki gaishe min da Abba.”
“Zeji se anjima.”
“Yauwa” da haka sukayi sallama.
“Mey tace wai?” Mummy dake gefensa ta tambaya. “Cewa tayi akai mata duk abinda ya sauwak’a.”
“Toh se a sai mata fried rice and chicken ai ko ya kace? Ita da Abba.”
“Se abinda uwar gida tace.”
“Kai Alhj bana son zolaya fa.”
“Ai gaskiya ce.”
“Nifa har yau fushi nake da kai.”
“Afuwan in uwar gida na fushi dani a ina zan sa kaina?”
“Eh mana kak’i had’ani da ‘yar uwata a gida d’aya.”
“Ba wai nak’i bane Hjy Surayya.”
“Kak’i ne mana tun yaushe nake binka ayi a had’a ginin nan kak’i.”
“Ai kinga har yau aikin ake kan yi in shaa Allahu ana kammalawa zan dawo da ita nan chan d’in temporary ne.”
“Promise?”
“I cross my heart.”
“Toh Allah nuna mana .”
“Ameen Hjy Surayya nawa na kaina, bari in je in siyo ma ‘yar uwar taki abinci.”
“Gaskiya kam kar mu bar amarya da yunwa.”
“Toh a dawo lafiya.”
***
Ranar Asabar aka d’aura auren Alhj Abdallah da Jameela Muh’d akan sadaki dubu d’ari da sisin gwal arba’in. D’aurin aure kawai akayi da yammacin ranan aka kai amarya d’akinta. Se wani tattalinta Daddy yake, bayan sunci kajin amarcinsu Daddy yasa su sukayi raka’a biyu dan yima Allah godiya.
Washegari…
Hayaniyan da Daddy ya jiyo a kitchen ne ya sanyasa fitowa daga d’aki inda yake kwance. Mami ya tarar tsaye gun sink ko mey takeyi oho.+
“Jamee na mey kuma kike yi?” Ya tambayeta tsaye daga bakin k’ofan.
“Oh Alhj!” Ta juyo a d’an razane “Har ka tashi ne?”
“K’aran kwanukanki suka tadani” ya sanar da ita.
“Ayya yi hak’uri inzo in mayar da kai baccin ne ko zaka koma da kanka?”
“Ko d’aya tambaya nake mey kikeyi?”
“Oh! Doya nake ferewa Abba kasan bey karya ba.”
“Inji wa? Ai da kin tambaya, tare aka siyo mana breakfast d’in nasa mey gadi ya kai masa nasa se inde zaki site nasa ku gaisa.”
“Allah sarki nagode.”
“Jimin matan nan fa godiyan mey kuma kike mun? Dan na ciyar da Abban mu? Taho mu koma d’aki” ya k’are had’e da mik’a mata hannunsa murmushi cike da kunya ta saki sannan ta mayar da kayan aikin ta k’ariso ta mik’a hannunta ta sanya acikin nasa, janta yayi izuwa d’akinsu had’e da zaunar da ita kan gado. Cikin wardrobe nasu ya nufa ya d’auko wani package sannan ya dawo ya zauna a gefenta.
“Hungo” ya mik’a mata.
“Mey wannan?” Tayi saurin tambaya.
“Kede bud’e ki ga” ba tare da yin gardama ba ta amsa ta bud’e d’an kunne ta tarar aciki k’waya d’aya. “Ko na waye wannan Alhj?”
“Bazaki iya tunawa ba?”
“A’a gaskiya” ta amsa tana kad’a kai amsa yayi daga hannunta yace, “Kin tuna rana na uku dana fara d’auko ki daga makaranta muna tsaye a k’ark’ashin makeken bishiyan chan muna hira muna shan rakke chan kika ta6a kunnenki kikaji ba d’an kunne? Muka ta nema amma muka rasa?”
Murmushi take sosai cike da mamakin yadda akayi har yau Daddy be mance da wannan rana ba bayan ita da ba don ya tuna mata yanzu ba ta riga ta mance da shi shaf. “Toh ai bayan dana raka ki gida na dawo na cigaba da nema ashe ma ba a wajen ya fad’i ba tun a bakin makarantar ku ya fad’i.”
“Shine ka adana har yau Alhj?”
“Kamar yadda na adana soyayyarki a cikin zuciyata na tsawon shekaru ashirin da biyu.” Ya amsa nan take.
Mamaki ne ya mamaye Mami gabd’aya ta rasa na cewa chan ta kira sunansa inda ya amsa a take “Alhj idan har kana so na haka toh meyasa ka gujeni? Na fahimci kayi mun abinda kayi ne saboda ka rama abinda Umma tayi maka amma meyasa ka kujeni? Meyasa ka daina d’aukan wayana?”
“Duk da hakan ma be kamata inyi miki abinda nayi miki ba Jamee amma a lokacin shaid’an ya riga ya rinjayeni I’m terribly sorry.”
“Komai ya riga ya wuce Alhj ka daina neman tuba na.”
“Nagode Allah yayi miki albarka.”
“Ameen Alhj baka amsa min tambayan danayi maka ba.”
“Kinsan wani sa’in mutum baya sanin muhimmancin abinda yake da shi se idan ya rasa, da fari nak’i in amince da cikin Amal nawa ne saboda tsoro da nake kar in 6ata wa mahaifina suna acikin gari, kowa ya sani mahaifina sanannen malami ne ba k’aramin zubar masa da mutunci zanyi ba idan har na amince da cikin cewa nawa ne. Tsoro ne yasa na gujeki Jamee, na d’au bayan da nayi nesa daga gareki zan iya mancewa dake, na d’au yin hakan ne ze fiye mun kwanciyan hankali ashe sam ba haka bane. Tun bayan da nayi cutting off conact dake da duk wani nawa rayuwata ta dame, acikin k’unci nake kwanciya in tashi har seda Allah ya shigo mun da Surayya cikin rayuwata, wacce ta yaye mun duk wani bak’in ciki nawa take kuma bala’in tuna mun da ke ta kowani 6angare. Duk da hakan saide idan ban kwanta ba Jamee senayi mafarkin ki, lokacin da na fara neman layinki kuma se yayita cemun switched off.”
STORY CONTINUES BELOW
“Ba shakka nakega lokacin da muka bar Askira ne Abba ya buk’aceni da in yasar da sim card d’ina ze sai min sabo.”
“Tabbas ma hakanne, saide duk da hakan ban kariya ba kullum se na gwada layinki amma baya shiga, a wannan lokacin ne na tabbata da cewa guje miki da nayi shine babban kuskuren dana tafka a rayuwa na, a wannan lokacin na tabbatar da cewa akwai gur6in da kika mamaye a zuciya na, gur6in da se ke ne zaki iya cike mun shi. Lokacin da muka dawo Nigeria na koma Askira don nemanki inda ake tabbatar mun da cewa Allah yayi wa Abba da Umma rasuwa.”
“Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un Allah ya jik’an su da rahama a tunani na gabad’aya wanda ka kaini gunsu sune iyayenka.”
“A’a wan Abba ne da matarsa.”
“Allah sarki.”
“Daga chan se na wuce gidanku inda ake cemin kun bar garin Askira da dad’ewa kuma ba wanda yasan inda kuka dosa nayi cigiyarku har na gaji amma rana baya ta6a wucewa ban yi tunanin wani hali da yanayi kike ciki ba. Please forgive me Jamee.”
Hannunsa ta d’au ta had’a da nata tana murzawa a hankali “Alhj komai ya riga ya wuce wannan d’an kunne kuma zan cigaba da adana shi as a symbol of my love for you” Murmushi ya sakar yana mey jin dad’in abinda ta fad’a sannan ya janyo wayanshi “Bari in kira Hjy Surayya muji daga gareta.”
“Gaskiya ya kamata.” A karo na farko Mummy ta d’aga wayan inda suka gaisa. “Kun jini shiru ban kawo muku breakfast ba ko? Wallahi Khaleefah ne yamun tsiya na sa Alarm a wayana kawai ya saci ido na ya d’auke wayan sena makara.”
“Barka, dama waya aikeki? Karki damu mun riga mun karya.”
“Kai ina ruwanka? Idan na kawo se kar ka ci so ka fad’awa ‘yar uwata kar tayi wahalan yin girkin rana I’ll make it up to you guys.”
“A’a Hjy Surayya dan Allah karki sa kanki wahala.”
“Nikam ka had’ani da ‘yar uwata mu gaisa” yana murmushi ya mik’awa Mami wayar “Assalamu Alaikum” ta soma da cewa. “Amaryar mu” Mummy ta amsa.
“Kai ‘yar uwa bazaki bar zolaya bade ya kike toh ya Khaleefah?”
“Gashi se shiri yake ya kusan komawa school.”
“Allar sarki Allah kiyaye ya bada sa’a.”
“Ameen sena shigo anjima sauran kice zakiyi girki kuma.”
“Oh ‘yar uwa kar ki sakaltani dayawa fah.”
“Ba ga Alhj ba yasan yadda zeyi dake ai.”
“Kai ‘yar uwa.”
“”Ahtoh barin bar ku haka se na shigo anjima.”
“Toh muna godiya Allah kaimu.”
“Yauwa se anjima.”
Kaman yadda Mummy ta d’au alk’awari bayan sallan Azahar ta shigo da abinci kala-kala se sauk’e kuloli kawai ake tayi daga mota. Yini Mummy tayima Mami se kusan Maghrib da Daddy ya kusa dawowa ta koma gidanta. Zaman lafiya maras misaltuwa Mummy da Mami sukeyi sekace ba kishiyoyi ba wane wasu ‘yan uwan jini, dai-dai da rana d’aya Daddy be ta6a jin kansu ba. Hasali har had’a kansu suke su biyu su waresa. Bayan ya k’are wa Mami kwana bakwai na amarchi ya soma yi musu kwana bibbiyu duka.
***
Haka kwanaki suka cigaba da shud’ewa yayinda zama yake k’ara yima wad’annan abokan zama dad’i. Labarin Nazeefah kuwa duk sanda ta bugi iska takan d’au waya ta kira Mummy amma dai-dai da rana d’aya bata ta6an d’aukan waya ta kira Daddy ba ko da shi ya kirata ma se ta ga dama take d’agawa.
STORY CONTINUES BELOW
9 months later…
Abubuwa da dama sun gudana, Amal hutu ya k’are sun koma makaranta har sun k’are first semester suna second semester yanzu. Maamah kuma an kai goron tambayan auranta, labarin dawowan Ya Abdul kuwa shiru har yanzu ko su Mama sunyi mishi magana se yace shi ba yanzu ba. Sultan ko har yau labarin aure shiru ya tsaya rawan ido. Labarin k’awar Amal Falmata kuwa tayi aure abunta tabar Maiduguri ta koma a Azare take da zama inda mijin ke aiki. Har Azare su Amal suka kaita suka dawo. Tun tafiyan Amal wane akan allura Afzal yake zaune, minti-minti yake yi mata waya yaushe zata dawo. Sam baya iya jure rashin ta a kusa da shi.
***
Amal ce zaune a d’akinsu da Afzal se faman karatu take gefenta kuwa plate ne cike da kayan k’walama ba abinda babu daga abinda ya kama kan tuwon madara, calanda, gullisuwa, tsamiyan biri, ba abinda babu ta d’au wannan ta d’au wancan. Haka kawai ta ke wani irin wawan kwad’ayi kwana biyu duk abinda tagani setaji tana so. Ba da dad’ewa ba wayanta dake ajiye a gefenta ya shiga ruri dubawanda tayi taga Afzal ke kira k’aramar tsuka taja ta cigaba da yin abinda ke gabanta. Yana tsinkewa ya shiga kira again nan ma tak’i d’agawa be dad’e ba sega sak’on sa.
_Please pick up Rania I’m sorry._
Tana cikin shawaran ta d’aga ne kokuwa sega call nasa again nan ma seda ya kusa tsinkewa ta d’aga had’e da yin shiru.
”Baby yi hak’uri mana.”
“Nifa ban ce kayi mun laifi ba.”
“Toh meyasa in na kiraki bakiya d’agawa?”
“Karatu nake bana son distraction.”
“Baby Ya Omrin na kine kuma yau distraction? Yi hak’uri kinji Yaya is sorry.”
“Shikenan ni kayi ta mun wasa da hankali kenan kullum, yau kace gobe, jibi kace gata dan kawai kaga ina missing naka.”
“Haba baby yi hak’uri wallahi sune suka k’i sakemu saura mana trips biyu amma de yanzu.”
“Toh nikam se yaushe zaka dawo?”
”Zuwa next week in shaa Allah.”
”Har next week Ya Omri?”
”I’m sorry.”
”Promise?”
”I promise Baby.”
”Toh Allah ya kaimu.”
”Ameen kin daina fushin?”
”Ba dole na ba.”
“That’s my Rania so ya kike? Should I FaceTime you?”
“Okay.” Nan ya katse wayayn ya yi mata video call inda ta d’auka suka cigaba da gaisawa. “Baby?”
“Na’am” ta amsa.
”Mey kikeci haka ba ni?”
”Oh tuwon madara ne.”
”Da kuma mey? Mey wancan bak’in abun?” Plate d’in ta d’aga ta matso da shi kusa ”Tsamiyan biri ne.”
”Rania yaushe kika fara wannan ciye-ciye?”
”Ba ka nan ma ban tsira ba ko?”
”Toh ya Mami? Sun dawo?”
STORY CONTINUES BELOW
”A’a wai daga chan zasu wuce Dubai.”
“Oh ayyah Papi fa? Yana nan k’alau?”
“Eh Mummy tana kula da shi.”
“Allah sarki toh yayi kyau.”
“Toh se anjima ko? Kaga karatu nake” tayi maganan tana nuna masa handouts nata.
“Wait Rania d’an tsaya.”
“Yaya wai yau kai kake hana ni karatu?”
“Not at all, Idona ne kokuma k’iba kika k’ara bayan tafiya na?”
“K’iba?” Ta nanata tana duban jikinta
“Eh mana kinga yadda kumatunki suka ciko.”
“Kai Ya Omri ka fa san bana son inyi k’iba.”
“Ai kuwa se kin fara slimming dan kin riga kin d’au hanya.”
“Omg! Dan Allah dagaske kake na k’ara k’iba?”
“Kije ki duba mirror kiga” katse video call d’in tayi ta ruga gun madubi tana matse kumatunta. Kuma fa hakanne da gaske ta k’ara k’iba toh kode? Kai da k’yar tayi sauri ta kad’a kanta. Koda tayi missing period nata last month bata damu ba cause tunda ta samu miscarriage date nata ya rikice wani sa’in se yayi wata biyu be zo ba atimes kuma sati biyu zuwa uku ya dawowa. Amma kuma ai tabar shan planning pills nata there’s possibility cewa tana da ciki. Toh amma wani irin ciki ne wannan ba laulayi ba komai? Ai wasu dama sunce cikin fari ne yafi bada wuya na biyu da sauk’i yake zuwa. Ta shigesu Allah taimaketa ba ciki take d’auke da shi ba in bahaka ba zatayi bayani gun Afzal da yace su jira ta gama makaranta tukuna su fara bearing children kasancewar yadda cikin farinta ya mugun bata wuya. Da na sani ta shiga yi shin meyasa ma ta daina shan pills natan ta kuma cire implant d’in? Har ga Allah ba don rashin ji tayi hakan ba illa dan so da take ta azurta Afzal da yara, so take yaga jininsa shima bayan hak’urin da yayi na shekaru kusan biyar ba haihuwa. Bata son ta shiga hak’k’insa dan wani personal interest nata. Ko ba a tambaya ba tasan Afzal na son yara yadda kullum idan suka je gidan wani abokinsa da suke mugun zumunci yake wasa da yaran tamkar ‘ya’yan cikinsa. Se kuma yanzu tsoro ya shigeta bayan alamomin juna biyu sun bayyana a jikinta, ji tayi gabad’aya dama bata cire implant d’in ba. Ita de zata jira zuwa nan da jibi idan har period nata be zo ba zata asibiti a dubata.
Washegari bayan lectures nasu ya k’are suka wuce restaurant dan chin abinci ita da Maamah sede Amal tak’i cin komai bayan kuma tana jin yunwan.
“Wai toh mey zaki ci?” Maamah da abun ya isheta ta tambaya.
“Ni wallahi ganda nake so.”
“Gan mey?” Maamah ta tambaya unbelievably.
“Ganda wallahi.”
“Ahh gaskia kin so nishad’i ganda? Da ranan nan kuma acikin school?”
“Wallahi shi nak so Maamah ki taimakeni.”
“Toh ya kikeson inyi Amal? Bawai ana siyar da ganda bane anan sede ki bari idan an tashi se driver’nki ya tsaya a kasuwa ya sai miki kije gida ki girka.”
“Toh ai yanzu nake so bazan iya jira har anjima ba.”
“Oh Amal! Ko mey sabon ciki sede hakan.”
STORY CONTINUES BELOW
“Nikam da Allah.”
“Kode cikin gareki?”
“Kaman ya ciki sekace bakisan ina planning ba?”
“Nasani ko kin cire.”
“A’a kam bayan Yaya yace kar incire.”
“K’arya kike.”
“Dagaske fah”
Mak’aryaciya rantse muji! idan ma cikin ne da ke in Ya Afzal ya gano zakiyi bayani.”
“Maamah dan Allah ki taimakeni.”
“Aww cikin ne dake dagaske?”
“Wallahi ban sani ba but ji nake kaman I’m pregnant jiya muna FaceTime da Ya Afzal yace wai na k’ara k’iba.”
“Ai gaskiyanshi kumatunki sun ciko.”
“Na shiga uku!”
“Ya gane amma?”
“A’a hankalinsa be basa ba.”
“Chab Allah ya taimakeki.”
“Da Allah ki daina tsorata ni nasan yadda zan sanar dashi idan har na tabbatar da komai.”
“Gara miki kam dan kinfi ni sanin halin ogan naki kikayi wasa se kunyi fad’a ma.”
“Kai Maamah ki daina razana ni.”
“Allah kuwa yadda seda ya ja miki kunne akan kar kije ki cire.”
“Nikam idan ba ganda zaki bani ba ki daina cika mun kunne.”
“Ganda kam sede unborn ya hak’ura dan babu inda zaki samu.”
“Ni bance miki ciki ne gareni ba” tayi maganan had’e da mik’ewa “Ina kuma zaki?” Maamah tayi saurin tambaya.
“Out of school zanje in nemi ganda.”1
“Lallai abu ya tabbata” Maamah tace cike da neman tsokana.
“Kanki akeji” Amal ta amsa had’e da galla mata harara sannan ta fita. Nan da nan ta kira driver’nta yazo ya d’auketa, haka suka shiga bin restaurant by restaurant suna tambayan ko akwai ganda har seda suka samu.
Na sosai hankalin Amal ya tashi bayan da tayi carrying pregnancy test a gida ya nuna mata positive sedai duk da hakan bata amince ba se da taje asibiti akayi mata tests da dama aka tabbatar mata da gaskiyan al’amarin cewa tana d’auke da juna biyu. Tirk’ashi! Yanzu mey abun yi? Tasan se sun haura sama idan Afzal ya gano gaskiya. Da fari tayi tunanin kwata-kwata ma kada ta sanar dashi amma kuma seta tuna idan har shi ya gano da kansa al’amarin zefi damewa. Yanzu what’s the way out??1
Haka tana ji tana gani har Afzal ya dawo daga tafiya bata yanke hukuncin ko ta sanar da shi kokuwa a’a ba. Gashi koda ta gwada tambayan Falmata da Maamah shawara duk suka sake tsoratar da ita.
“Rania k’iban nan naki lafiya kuwa?” Afzal dake mik’e akan gado ya tambaya yana mey k’ure mata ido yayinda take zaune akan kujera tana faman tsifan kanta. Zuciyanta taji ya buga, miyau ta had’iye sannan ta saki murmushin dole.
“Kai Ya Omri dan Allah ka daina razana ni.”
“Aikam da alama kinji dad’in tafiyan da nayi tunda har kika yi wannan k’iba.”
STORY CONTINUES BELOW
“Ni dama tayani wannan tsifa zakayi.”
“In dawo daga tafiya kuma ki sani aiki Rania?”
“Toh kayi shiru ka kwanta.”
“Zomu kwanta anjima in mun tashi se in tayaki.”
“Karatu nake so inyi anjuma.”
“Haba Baby na yi hak’uri mana.”
“Nikam barni inyi tsifa.”
“Toh zo kiji.”
“Mey?”
“Kekam kizo mana.”
“Meneh ka fad’e shi daga nan mana.” Ba salon da Afzal bebi ba amma haka Amal tak’i tasowa ta samesa gashi kuma baya son ya fito fili ya tambayeta saboda sarai yasan ta gane abinda yake nufi kawai bata son basa had’in kai ne. Mamaki ya sha sosai saboda wannan ne karo na farko da ya ta6a neman Amal tak’i basa had’in kai. Toh koma mey ne de Allah ya sa lafiya.
Yau kwana uku kenan da dawowan Afzal amma Amal ta kasa mustering courage ta sanar da shi cewa tana da ciki se tayi kaman zata sanar da shi seta fasa.
“Rania kiyi sauri mana I’m gonna be late for work.”
“Ermm ermm..” amma ta kasa yin magana se cin farcen hannunta take “Yaya”
Anzo gurin Afzal ya furta a ransa dama duk lokacinda ta kirasa da Yaya toh laifi tayi ko ne mey yanzu?
“Iyayen rashin ji mey kuma kikayi wannan karan?”
“Yaya” ta furta cike da shagwa6a.
“Rania speak up.”
“Kaga har past 7 hurry kar kayi latti.”
“Kin d’au na manta ne? Oya tell me what is it you want to tell me.”
“Dama so nake in ce maka I love you.”
Wani kallo ya watsa mata “We are not done Rania zamuyi magana idan na dawo.” Kai zalla ta gyad’a mar tana turo bakinta. Tun fitansa har dawowansa Amal ta kasa samun sukuni.
****
Fitowan Afzal daga wanka kenan ya nufi wardrobe nasa dan ciro kayan da zesa sede kap T shirts nasa Amal ta sanya tayi masa datti da su. “Huh! God help me Rania ina kika kai mun shirts d’ina?” Ya tambaya yana mey bud’e side na drawer’nta. Kaman a kyaftawan ido Amal ta mik’e dan dakatar da shi “Tsaya zan d’auko maka su da kaina kar ka d’aga chan” tayi saurin sanar da shi sedai ina tuni ya kai hannunsa wajen, paper ya ga wanda ya zaro waje. Hannu Amal ta mik’a zata k’wace amma ya janye “Yaya ka ba ni.” Ta fad’a tana k’ok’arin yin tsalle amma ina ko kusa da hannunsa ta kasa kaiwa.
“Yaya please dan Allah kar ka bud’e.” Gabad’aya ta tsure tasan idan Afzal ya gani nata ya k’are.
“Mey aciki?”
“Babu ka bani please.”
“Babu? Toh in babu bari in bud’e inga.”
“A’a please Yaya ka bani” se k’ok’arin k’wata take amma ta kasa.
“Dan Allah kar ka bud’e.”
“Mey aciki toh?”
“Ermm ermmm script na test d’ina ne wanda na fad’i please kar ka bud’e.” Dariya yasa “D’an tsaya toh muga zeron da kika ci d’in.”
STORY CONTINUES BELOW
“Yaya ple-” tana cikin yin magana ya bud’e sega pregnancy results na Amal da fari ma cewa yayi tun cikinta na fari ne sedai kuma da ya duba yaga data d’in ko sati be kai ba.
“Amal?” Dum taji zuciyarta ta buga dama anytime ya kira ta da asalin sunanta toh tana cikin big trouble nata ya k’are.
“Yaya-“
“Mey wannan?” Yayi saurin katse ta.
“Yaya-“
“Wait! Is this true?” Ya kuma katseta “Are you really pregnant?”
“Yaya-“
“Just answer me Amal!” Ya fad’a a tsawace har seda ta razana.
“Yaya yes amma kayi hak’uri I can explain.”
“Explain what exactly Amal?!” Ya kuna daka mata wani tsawan da ya mugun razana ta.
“Yaya dan Allah kayi hak’uri.”
“Cire implant d’in kikayi?”
“Yaya-“
“I’m asking you for the last time Amal cirewa kikayi?”
“Eh” ta amsa k’asa-k’asa.
“Wow tun yaushe?”
“Yaya-“
“Amal answer me!”
“4 months back.”
“Wow! Seriously? Ki ka kuma daina shan pills nakin?” nan kai zallah ta gyad’a.
“Why? Mey na ce miki amma?”
“Kar in cire.”
“Meyasa kikayi toh?”
“Yaya I’m sorry.”
“Ba abun da na tambaya ba kenan meyasa kika cire?”
“Yaya I’m sorry gani nayi kaman ina d’aukan alhak’in ka ne please don’t be mad.”
“Tayaya? Tayaya kike d’aukan alhak’i na? Ni na kawo shawaran mu fara planning d’in kokuwa?”
“Yaya kaine I’m sorry.”
“No answer me so kike kice kin fini sanin abinda nake so kenan komey?”
“Yaya dan Allah kayi hak’uri.”
“Ban san meyasa bakiya ta6a jin magana ba koda nayi miki, seda na ja miki kunne nace miki this is my decision komin yaya kar ki cire implant d’innan se idan kin gama school amma kika k’i ji kika je kika cire saboda ni bansan abinda nakeyi ba ko?”
“Wallahi Yaya ba haka bane I’m sorry.”
“Then yayane meyasa kika cire?”
“Yaya-“
“I’m not done” ya katseta “Answer me nace kin fini sanin ya kamata kenan ko mey? Kokuma ni da nace kar ki cire d’in bansan abinda nakeyi ba? Wanne d’aya?”
STORY CONTINUES BELOW
“Yaya ko d’aya I’m sorry.”
“I’m very upset with you Amal sanin kanki ne last year result naki beyi kyau kaman yadda ya kamata ba, kinyi passing amma duk series of D ne dalilin da yasa nace mu fara planning d’innan kenan saboda ki samu kiyi concentrating a karatunki ba tare da wani distraction ba.”
“Amma wannan be bani wuya ba Yaya ko sau d’aya banyi amai ba.”
“I don’t care Amal you’re still not safe, and no matter what dole cikin nan zeyi miki causing distraction daga karatunki, abinda bana so kenan ni kuma I want you to focus on your studies just. Ko nid’in a jinki bana son inga jini na ne nace mu hak’ura se kin gama school? Na fiki damuwa Amal but haka nayi hak’uri because thsit is what is best for you for us all” ya k’arasa a tsawace.
“Yaya I’m sorry bazan sake ba.”
“You’re never sorry Amal bana ta6a gaya miki magana ki ji sede kiyi abinda ranki yake so bans-” sautin kukan Amal ne ya dakatar da shi, kuka ta shiga rera masa tsaye a wajen.
Sedai Afzal be shiga yi ma Amal masifa ba kawai se ta yanki jiki ta fashe masa da kuka saboda tasan muddin ta fara kuka Afzal yana yin shiru. “Yaya I’m sorry” tace tana ta matso ‘yar hawayenta. Kallo ya watsa mata kawai yabi gefenta ya fice izuwa d’ayan d’akin inda ya kwanta. Kukanta tasha a wajen seda ta gode wa Allah sannan ta mik’e ta je ta samesa a d’ayan d’akin Allah ya taimaketa ma be sa key ba. Akan gado ta tsincesa yana bacci, sid’ak-sid’ak ta taka taje tasamesa, jikinsa ta shige ta kwanta akan hannunsa haka har itama baccin ya d’auketa.
Chan dab da goshin maghrib Afzal ya tashi se ganin Amal kawai yayi ajikinsa tana shar6an bacci. Ido ya k’ure mata yadda take ta baccinta cikin kwanciyan hankali da jurwayen hawaye a fuskanta. ‘Yar murmushi ya saki tuna anytime ya fara mata masifa se ta rushe masa da kuka sanin baya iya jure kukanta. Ya rasa wani irin d’an banzan shagwa6a ne da ita kodan chan a gidansu ba a saba mata da masifa bane kokuwa da gan-gan takeyi ne oho shide amma shagawa6an nata na burgesa duk lokacin da ta fara kawai se yaji ya huce. Hannu ya aza akan cikin nata. “I’m sorry I got mad at you earlier, Rania bana son a sanadi na GP’nki ya sake sauk’a, I only want the best for you” tsugunawa yayi tare da pecking cikin nata. Daga haka ya mik’e yaje ya kama ruwa yayi alwala bayan ya gama shiri ya dawo ya tada Amal, yana tayar da ita ya fice ba tare da yace da ita komai ba. Sallah tayi ta tofe add’u’o’inta sannan ta zarce kitchen ta dafa macaroni da minced meat aciki ta dawo ta shirya kan dinning. Tunda take girkin take tsammanin shigowan Afzal amma shiru gashi ko da ta gwada trying numbanshi taga wayar ma a gida ya barta. Haka se chan kusan tara ya dawo Amal tayi jiran duniya har ta gaji. Yana shigowa ta zabura, mayar da k’ofan yayi ba tare da nuna ra’ayin yi mata magana ba so yake yaga ko zatayi masa.
“Yaya sannu da zuwa” tace tana susan kanta yayinda ta kafe idanunta a k’asa.
“Sannu” ya amsa sama-sama sannan ya shiga takawa gabansa tasha da wuri “Yaya I’m sorry dan Allah kayi hak’uri” ta sanar da shi idanunta suna masu cikowa da hawaye.
“Ni ya kamata in baki hak’uri Rania I’m sorry kinji?” Cike da d’unbun mamaki ta d’ago kai tana kallonsa “Eh?”
“I said I’m sorry for shouting at you earlier ki gafirceni.”
“Yaya-” dan mamaki tama kasa cewa komai. “Yaya ka daina fushi dani?”
“Meyasa zan yi fushi da maman unborn d’ina? Na fahimceki Rania, and I appreciate your commitment to give me a family, to give us a family. Just know that I’ll always be here for you if you needed me okay?” Hugging nasa kawai tayi tsabagen yadda takejin dad’i. “I love you so much Ya Omri.”
STORY CONTINUES BELOW
“I love you too babe” a hankali ya janyeta daga jikinsa. “How many months is my baby?”
“Ko scanning banyi ba saboda tsoro da nake idan ka gano gaskiya zaka mun fad’a hala ma ka daina mun magana.”
“Be kamata in hau kanki da masifa ba d’azu Rania but I couldn’t help it bana son saboda ni ki sake komawa baya a karatunki shiyasa nace mu fara planning I love you so much my Amal.”
“And I love you more Ya Omri a shirye nake da in rasa komi nawa saboda farin cikin ka, I’m willing to sacrifice my life for you Ya Omri. I’ve seen the way you so much love and adore kids shiyasa nima nake so in yi maka fulfilling this one wish.”
“And I appreciate that so much Baby, I can’t believe I’m going to be a Daddy in anytime soon, Allah ya inganta ya cigaba da yi miki albarka.”
“Ameen Ya Omri.”
“So first thing gobe zamu je muyi scanning koba haka ba?”
“Duk abinda kace my King Allah ya kaimu.”
“Ameen.”
“Muje muci abinci tun d’azu na sauk’e ina jiranka.”
“Har girki kikayi?”
“Eh mana ba kayi mun fushi ba.”
“Yi hak’uri toh kinga ni bana son kina aikin wuya yanzu zan yi ma Ummi magana ta turo mana mey aiki d’aya daga gida.”
“A’a a’a nikam bana so bana so zan nayin komai nawa da kai na.”
“But Bab-“
“Trust me Ya Omri koda zaka d’auko mey aiki ma kabari ba yanzu ba maybe idan nazo nayi nauyi amma yanzu kam da k’arfi na bana so.”
“What baby wishes she gets, fine se a bari se kinyi nauyi d’in amma fa karki na aiki sosai bana son ki galabaita mun baby.”
“Toh shikenan let’s go and eat.” Abincin su suka ci cikin kwanciyan hankali sannan sukayi wanka abinsu tare suka kwanta. Washegari kaman yadda Afzal ya fad’i suka wuce asibiti sukayi scanning ashe ciki har na wata biyu da sati d’aya ne tattare da Amal amma bata sani ba. Afzal dad’i kaman ze kashe sa se buge-bugen waya yake yana sanar da mutane Amal tasa is pregnant. Se tattalinta yake wane k’wai, idan ba abu yafi k’arfinsa ba sam baya barin Amal tayi aiki se inde shi yayi haka ta zama lalacacciya a gidan ko d’aga tsinke batayi sede tayita ciye-ciye tace tana son wannan tace tan son wancan. Wani irin d’an banzan kwad’ayi ta sake koyowa amma Alhamdulillah ba amai ba jiri ba ciwo ba komai. Haka Afzal ya cigaba da rainon cikin nata, kullum tare suke zuwa yin scanning. Koda aiki yayi masa yawa ze buk’ace ta da ta jirasa seya dawo. Cikin na da wata biyar sukayi first semester exams nasu. Na sosai Afzal ya taimaka mata ta samu tayi passing with excellent results. Seda cikin ya kai wata bakwai tukun ya fara fitowa sosai acikin kaya, abinku da doguwar mace, tunda cikin ya fara fitowa Amal ta auri zama da hijabi a gida 24/7 saboda tsokananta da Afzal yakeyi sede bata cire hijabin ba seya nemi tsokananta. Har dan haka ma ta daina yin wanka tare da shi. Cikin nada wata takwas ya fito yayi k’ato tim, zama da k’yar tashi da k’yar kusan komai Afzal ne yakeyi mata. Haka kawi zata wayi gari rana d’aya tayita kukan banza in ya tambayeta dalili kuwa tace wai girman cikin ke bata tsoro.
Bayan nan ga wani uban masifan da ta koya abu kad’an ta hau surutu da masifa.
Da daddare wajajen goma Afzal na kwance yana bacci Amal ko se kuka cikinta yake sanadin yunwan da takeji, baccin ma ta kasa. Tun kafin su kwanta Afzal yake binta taci abinci amma tak’i saboda haushinsa da takeji har yanzu na hanata fita bikin sunan k’awarta da yayi. Shi kuwa dalilinsa wai saboda EDD nata ya kusa ne, it is more safe idan tana zama a gida kar labor yaje ya kamata acikin jama’a. Se harara take ta zuba masa shiko se baccinsa yake hankali kwance. Mik’ewa tayi da k’yar ta nufi kitchen ta bud’e fridge, jollof na shin kafa, macaroni, d’anyen awara, soyayyan kifi ta tarar a cikin fridge d’in sede duk ciki ba abinda ya gameta. Farin k’asa ta d’auko a inda take 6oyewa ta shiga tsotsa saboda Afzal ya haneta da sha tun lokacinda likitan ta tace musu abun baida kyau a jiki. Seda ta sha har biyu sannan ta koma d’akin, lokacin har goma da rabi yayi. Zama tayi daga bakin gadon tana tunanin ta yadda zata fara tada shi.
STORY CONTINUES BELOW
“Yaya!” Ta ambaci sunansa. “Yaya ka tashi!” Cikin bacci ya amsa. “Mey ne Baby?”
“Ni ka tashi” shareta yayi ya cigaba baccinsa.
“Yaya ka tashi mana!”
“Maman Baby na yi hak’uri mu kwanta kinga ina da office gobe yi hak’uri.”
“Toh ni yunwa nakeji.”
“Yaya ka tashi!” Tasa ihu, ba shiri ya mik’e zaune.
“Dan Allah mey kikeso Baby?”
“Ni pepper soup nakeso.”
“Toh ai akwai a fridge bari in miki micrwaving ko?”
“Ni ba na kaza nake so ba na kayan ciki wanda ba thyme aciki nakeso.”
“Baby fisabillahi a ina zan samu pepper soup na kayan ciki cikin daren nan? K’arfe nawa ne?” Ya tambaya yana duban agogo. “Baby sha d’aya fa ake nema, sha d’ayan dare.”
“Toh laifi na ne? Ba baby’nka bace se kayi mata fad’a ba ni ba.”
“Ni ba fad’a nake miki ba yi hak’uri ki bawa baby hak’uri kice mishi gobe da safe zanje in siyo mishi.”
“Ni baby na ba na miji bane baby girl
ce ka daina canza mata jinsi.”
“Toh naji yi hak’uri Maman baby girl ki bawa baby girl hak’uri.”
“Ni wallahi shi muke so.”
“God help me naji toh naji zanje in saya miki.”
“Kuma in da thyme aciki bana so.”
“Naji in shaa Allah ma babu.” Nan da nan ya canza kayan jikinsa ya d’au key. “Toh sena dawo.”
“Allah ya kare I love you.”
“Ameen maman baby girl I love you too.” Cikin sa’a kuwa a hotel na biyu da ya duba ya samu pepper soup d’in sede kuma da thyme aciki haka seda ya biya extra kud’i aka samu aka tankad’e masa romon aka yi getting rid of thyme d’in. Yana isa gida ya d’iba mata a saucer ya d’au mata ruwa. Sam bataji shigowansa ba kawai ji tayi karap an bud’e k’ofan. Kafin tace zata 6oye farin k’asan da take shan har Afzal ya gani.
“Uhm uhm fito da shi na riga na gani fito da shi.”
“Yaya” kame-kame ta shiga yi. “Oya mik’a mun.”
“Yaya please”
“Rania give it to me.”
Bata sake yin gardama ba ta mik’a masa.
“Ina sauran?”
“Babu wannanne na k’arshe.”
“One… Two…” ya shiga counting inda ta dakatar da shi da sauri. “Ka tsaya zan fad’a zan fad’a.”
“Oya a ina kika 6oye?”
“Baby na” ta maraice fuska.
“Three… four…”
“Yana cikin second cupboard a kitchen.”
“Kika sake saya se na kai k’aran ki gun Abba zance ko na miki magana bakiya ji ga shi zauna kisha an samu pepper soup d’in.”
STORY CONTINUES BELOW
“Na fasa sha ni awara nakeso.”
“Dan Allah kiyi hak’uri Rania bacci nakeji.”
“Ba zaka kai k’ara na gun Abba ba? Ni bazan ci ba.”
“Yi hak’uri wasa nake.”
“Nide wallahi awara nake so in ba haka ba inyi ma kuka.”
“Yi hak’uri Baby ta, ai bama haka dake kema kin sami, haba maman baby girl yi hak’uri ki sha mu kwanta ko? Gobe da kaina zan kaiki gidan k’awar naki kiga baby’n nata.”
“Daga baya kenan bayan an gama komai mey zanje inyi? Ni de awara nakeso.”
“Wannan d’in fa? In zubar?”
“Ka sa a fridge amfaninsa ze taso wataran.”
“God help me!”
“Ni de awara nake so.” Haka dan dolensa ya juye pepper soup d’in a fridge ya fito da d’anyen awaran daga fridge dama already a yayyanke ne soyawa kawai za’ayi har ya shiga soyawa ya tuna da gardaman Amal ze iya kai mata yanzu tace ita mey k’wai ajiki takeso dan haka ya koma d’aki ya tambayeta. Ai kuwa tace mey k’wai ajiki take so cikin mintuna k’alilan ya gama soyawa ya kai mata nan ne ta zauna tacinye tas shide Afzal tausaya mata yake tun cewa da likita tayi idan ta fiye cin abinci sosai toh baby’n nata zeyi girma in akayi wasa ma ta kasa haifa da kanta se anyi mata CS. Amma inaa ita Amal ko a jikinta se aukin ci kaman gara. Dam tayi sannan ta mik’e kan gado ta fara bacci. Se anan Afzal ya samu kansa ya kwanta shima.
Haka yayi ta fama da Amal har zuwa lokacin da haihuwanta yayi. Dama likita ta basu tsakanin 12th-15th on the 14th Amal ta tashi da wani irin ciwon ciki mey tsanani, dama Mami tace mata anytime taji cikinta na ciwo ko bayanta toh tayi mata waya. Aikam Allah ya taimaketa ranan asabar labornta ya tashi bata fita school ba saboda ba wani serious lectures sukeyi ba, shima Afzal na a gida saboda ba aiki, tana zaune a d’aki ta nad’e k’afa tana tsotsan tsamiyan biri tajiyo wani irin sharp pain a mararta. Tuni tayi watsi da plate na tsamiyan birin ta sauk’a k’asa, da cikin nata ya sake murd’awa ta sa wani d’ankaren ihun da seda Afzal dake parlour ya shigo ba shiri, kanta ya yo da wuri yana tambayarta ko lafiya.
“Yaya call Mami up I think I’m in labor.”
“Labor?” Ya sake nanatawa a razane. “Sure!”
“Yaya kayi sauri wayyo Allah cikina zan mutu” nan da nan ya kira Mami. Cikin mintuna k’asa da talatin ita da Mummy suka iso kafin nan ba irin yak’ushi da masifan da Afzal be sha ba. Amal se kuka da k’yar Afzal ya d’agata ya kaita mota Mummy ta biyo su da maternity bag nata duka suka yi asibiti inda akayi delivery room da Amal. Mutum d’aya aka buk’ata da ya shiga cikin d’akin da Amal nan su Mummy sukace Afzal ya shiga amma d’ankaren tsoro ne dashi atapir yace shi baze shiga ba sede cikin d’ayansu ita da Mami d’aya ya shiga. Baze iya jure ganin Amal tana kuka haka ba bayan ba abinda ze iya yi daze tsayar da azaban da take ji ba. K’arshe de Mami ce ta shiga, Amal se ihu take yi muryanta akeji ko ina a cikin asibitin Afzal ko zama ya kasa se safa da marwa yake a haraban d’akin yana mey rok’on Allah ya sauk’e masa matarsa lafiya. Bayan several pushes Amal ta samu kanta, ta haifo zankaleliyar ‘yarta. Ana gama kimtsa su akayi ma Afzal magana.
“Congratulations matarka ta sauk’a lafiya ta samu ‘yarta both the mother and the baby are in good health zaka iya shiga ganinta.” Dr ya sanar dashi da Mummy.
Wani irin sanyi Afzal ya jiyo a jikinsa “Alhamdulillah Alhamdulillah thank you so much Dr.” Ita Mummy dan farin ciki tama kasa magana.
“You’re welcome” daga fad’in haka yabi gefensa ya fice nan Afzal da Mummy suka k’arasa cikin d’akin. Wajen Amal tasa ya soma nufa had’e da placing mata peck a goshi. “Sannu da k’ok’ari my Rania, Allah yayi miki albarka sannu ko?”
“Ameen Ya Omri” ta amsa a galabaice tana mishi murmushin dole.
“Ga chan ‘yar tamu achan” Mami tayi masa nuni da crib da aka sanya baby’n aciki. Nan da nan yaje ya d’aukota, baze iya kwatanta irin farin cikin da ya ziyarci zuciyansa ba a lokacin da ya rik’e baby’n nasa a hannu. Se kaman Amal kawai ya rik’e, yarinyan ba abinda ya rabata da Amal wane kakinta Amal tayi. Se masha Allah kawai Afzal yake ta furtwa har izuwa lokacin da ya dawo ya zauna a gefen Amal. Addu’a yayi mata Mummy ta mik’a masa zamzam da aka jik’a dabino aciki ya bata.
“Rania she looks just like you” ya sanar da ita had’e da mik’a mata ita. Har kuka seda Amal tayi da ta rik’e yarinyar a hannu, yau Allah ya amsa mata addu’arta dan azaban data sha a labor room har cewa tayi ita mutuwa ma zatayi. Amshe baby’n Mami tayi ta mata addu’a itama sannan ta mik’awa Mummy itama tayi mata inda Afzal ya sake amsanta. “Gaskiya ‘yar nan ta d’ibo Amal dayawa” cewan Mummy.
“Nace miki kaman Amal kawai na rik’e a hannu ba abinda ya rabasu” Mami tace.
“Alhamdulillah” Afzal ya sake mik’a godiyansa ga mahalicci. Ya rasa wani kyauta zeyi wa Amal wanda zey sanyata farin ciki kaman farin cikin da ta sanyasa a ciki yau. “Rania?”
“Na’am?” Ta amsa mik’a mata baby’n yayi “Wani suna zamu sa mata?”
“Yaya nice zan bata suna? Ai kaine mahaifinta kai zakayi deciding.”
“Na baki wannan dama, ki sanya mata duk wani sunan da kika ga ya dace.” Shafe fuskan baby’n tayi a hankali had’e da placing mata kiss a kan hanci “Ina son mu sanya mata Nazeefah sunan k’anwata tilo.” Gabad’aya wajen seda sukayi mamakin wannan ra’ayi na Amal, barin ma Mummy. Ina ma ace yadda Amal ke son Nazeefah haka itama Nazeefah take son ta? Da kuwa ba abinda ze fiye wa Mummy farin ciki. Duk sunyi murna matuk’a barin ma Mummy da har hawaye seda ta zubar taso ace ta iya ta bawa ‘yarta tarbiyya kaman yadda Mami ta baiwa Amal, ta so ace Nazeefah tana da kyawun halatayya irin na ‘yar uwarta Amal. Amsan yarinyan Afzal yayi ya mata hud’uba. “Welcome to the family Nazeefah, Allah ya albarkaci rayuwanki.”1
“Masha Allah” fad’in Mami.
“Allah miki albarka Amal, Ya k’ara muku lafiya keda Nazeefar mu.”
Ameen duka suka amsa a gun.
“Toh kai Afzal haka akeyi ne? Ka rik’e ‘ya tun d’azu ka hana mu kakanninta rik’e ta?” Mami ta fad’a cike da wasa wanda hakan ya sanya su duka dariya a wajen.
“Mami sai de fa kuyi hak’uri dan wallahi duk yadda naso bayyana muku kalan farin ciki da walwalan da nake ciki a yanzu ba ganewa zaku yi ba, dan murna har gani nake kaman mafarki nake, I can’t believe that this beautiful here is my daughter and that Amal is her mother, Alhamdulillah Allah abun godiya.”
“Tabbas Allah abun godiya ne Afzal” Mummy ta sanya baki.
“Thank you Amal, Allah miki albarka.”
“Ameen Yaya” ta amsa da wahalallen dariya, tana wasa da canular’n dake hannunta.
“Toh shin za ayi wa Nazeefar tamu alkunya ne ko da Nazeefan zamu na kiranta? Naga ku iyayen zamani yanzu haka kuke yayi.” Mami ta kuma tambaya inda Mummy ta gyad’a kai in agreement.
“Yaya?” Amal ta kira Afzal da ya kafa wa ‘yar nasu ido ko kyaftawa ba ya yi. “Yaya?” Ta sake kiransa se anan ne ya amsa gabad’aya hankalinsa yayi nesa da shi.
“Na’am Rania?” Ya amsa yana d’ago kai.
“Baka ji Mami ba?”
“Sorry meney?”
“Za’ayi wa Nazeefah alkunya kokuwa?”
Murmushi mey alfarma ya saki sannan yace, “Rania ni ai se abinda kikace.”
“But Yaya I’m asking you now.”
“A’a nikam se abinda kikace, don baze yi ace bayan wannan gaggarumin kyauta da kika mun in sake cewa ga abinda nake so ba, this’s your moment live in it, idan kina son mu sanya wa Nazeefah alkunyan fine se mu nemi mey dad’i mu sa mata in kuma a’a we all good banida matsala.” Kewayawa Mummy tayi ta kalli Mami cike da jin dad’in amsan da Afzal ya bada, inda itama ta juyo tana kallonta suka sakar wa juna murmushi. A gaskiya Allah ya amsa mata addu’an da ta dad’e tanayi wa Amal tun tana ‘yar yarinya na cewa Allah ya bata miji nagari wanda ze darajata ya kuma kula da ita fisabilillah.
“Tuna mun wannan suna da kace yana maka dad’i.”
“Wanne d’aya?”
“Wannan da muka gani a cikin littafi ranan.”
“Wai NIHAL?”
“Yes shi why not muyi mata alkunya da shi you once said you like the name.”
“I really do but are you sure? In be miki ba, ba semun sa ba.”
“Of course Yaya duk wani abinda yake maka dad’i nima yana mun ko Mami?” Ta kewayo tana kallon Mami da murmushi d’auke a fuskanta. Murmushin Mami ta mayar mata had’e da amsawa “Eh Baby.”
“Toh kaga se mu sanya mata shi ko?”
“Thank you so much Amal, Mami har yau bansan da wani bakin zan yi miki godiya ba na tarbiyyattar da Amal da kikayi kika raineta har izuwa lokacin da na zo nayi muku wayo na d’auke ta” dariya suka sa sannan ya cigaba “Allah ya sak’a miki da mafi alkhairi da ke da Papi gabad’aya.”
Mami na murmushin jin dad’i ta amsa da “Ameen. So kun yanke shawaran kenan yanzu? Nihal zamu na kiran jikar tamu da ‘yar uwata?”
“Yes Mami” yayi saurin amsawa.
“Toh Abban Nihal baka sanar damu ma’anar sunan ba” fad’in Mummy.
“It means gratified; delighted; happy; prosperous; and a blissful person just like she truly is.”
“Masha Allah gaskiya sunan yayi ma’ana Allah d’ayyiba ya raya mana Nihal” ta kuma cewa inda duk suka amsa da ameen. Mami ta cigaba “Duk yadda zan so cigaba da zama anan in kula da Nihal hakan baze yiwu ba yau girki na ne ko tukunya kuma ban aza ba, ni zan wuce Mummy seta bi ki kin gane?”
STORY CONTINUES BELOW
“A’a baza ayi haka ba ‘yar uwa” Mummy tayi saurin katseta. “Jikar fari ce fah? Ku ku tafi ni se in koma gida in yi ma Alhj girkin karki damu.”
“Wayyo ‘yar uwa kin tabbata?”
“Kar kiji komai Allah ya raya mana Nihal.”
“Ameen ya Rabbi kai nagode sosai sakillahu bil jannah.”
“Ameen wa iyyaki kuje idan na gama girkin se na sa a turo muku naku had’e da kayakin ki kema kokuma yanzu ina zuwa in had’o miki kayakin se insa driver ya kawo miki, wanne kika ga ze fi?”
“Kinga dad’in da muke gida d’aya yanzu ko? In zaki iya had’a mun a yanzun nake ga zefi ga key na site d’ina nagode sosai.”
“Toh shikenan bari inyi sauri in had’o miki” ta amsa had’e da kar6an key d’in.
“Ermm Mummy?” Afzal ya kirata. “Na’am?” Ta amsa.
“Kiga ba sekin yi wani wahalan kawo abinci ba already munyi waya da Ummi tace zata kawo abincin so don’t worry.
“Ji min d’a, ladan ma se mahaifiyarka ce kake so ta samu wato ko?”
“Toh ai dukanku mummies d’ina ne Mummy” ya amsa yana dariya.
“Toh shikenan breakfast de gobe ni zan kawo ka fad’a mata na rigata.”
“Toh ba matsala Mummy thank you.”
“Yauwa barin wuce toh, mai jego sena shigo gobe ko?”
“Toh Mummy thank you ki gaishe da gida.” Har waje Mami tayi mata rakiya had’e da tuna mata kayakin da take so ta tattaro mata sannan ta dawo ciki. In less than an hour bayan kayan Mami sun iso aka sallami su Amal suka komo gida bayan tabbatarwa da likita yayi da ita da Nihal suna cikin k’oshin lafiya. Wanka me kyau Mami tayi ma Amal da kanta sannan ta had’a mata tea mey kauri ta sha dan samun ruwan nono. Afzal ko na zaune a parlour se pictures yake tayi wa Nihal chan idan ta fara kuka ya bata ruwan zamzam da suka tanadar.
Bayan Amal ta gama shiri Mami ta kira Afzal ya kawo Nihal dan a shayar da ita. Mutumiyar ku kam ta cire mama ta shayar da ‘yarta ta kasa se tayi kaman zata sa mata a baki seta fasa, kan Mami da Afzal ne ya gama d’aurewa.
Chan Mami da ta kasa hak’ura ta tambayi ko lafiya “Ya haka Baby?”
“Babu” ta amsa k’asa k’asa cike da kid’imewa.
“Toh ki bata mana baki ji tana kuka bane?”
“Zan bata.”
“Toh mey kike jira? In taimaka miki ne?”
“A’a zan iya zan iya” ta amsa cike da tsoro.
“Toh muna jiranki.” Setayi kaman zata sa mata a baki seta fasa. “Wallahi Baby zan sa6a miki me ke damunki wai?”
“Mami wallahi zafi zeyi, baki ji yadda yayi tsami ba, rik’e shi ma haka da nake zafi yake mun” Baki Mami ta hangame tana kallonta cike da d’umbun mamaki, Afzal da ya san kayansa kam se kad’a kai kawai yake. Ance aure na sa hankali toh ga har Amal tasa ta haihu amma shagwa6a da rashin hankalin nan nata na nan har yau, Allah taimake shi.2
“Dan zeyi zafi se baza ki shayar da ‘yarki ba? Ke d’in ba hak’ura nayi na shayar dake ba kema?”
“Toh ai Mami ke kina da dauriya.”
“Kinga bana son shashanci kiba ‘yar nan nono ta sha tunda ta shigo duniya fa banda ruwa ba abinda aka sake bata.”
“Ni wallahi zafi” ta sake cewa tana zum6uro baki yayin da ta shiga cika idanunta da k’walla.
“Ikon Allah toh wallahi inde haka zaki cigaba se Ummi tazo kuyi jegon tare na tabbata idan itace akanki zaki nutsu.”
“Ya Omri ina ruwanta a sake bata.”
STORY CONTINUES BELOW
“Ruwa?” Mami ta katseta kafin Afzal yayi magana. “So kike cikin nata ya fashe? Kai kuma Afzal kayi tsaye achan baza kayi mata fad’a bane?” Ta kewayo tana kallon Afzal dake rik’e da feeder’n Nihal a hannu.
“Zan yi mata Mami, Amal yi hak’uri ki bata kinji?” Ya ce da ita a hankali yana mey nufan inda take zaune.
“Aww ma hak’uri kake bata? Lalle kam banga laifin Baby ba kai kake d’aure mata gindi ko ka sata ta bawa yarinyan nan mama tasha ko in kira Ummi tayi mun maganinku duka” tana kaiwa nan ta fice daga d’akin. Se kuka Nihal take Amal na jijjigata, ta kuma bata maman ta sha ta kasa wai ita zafi. A nitse ya k’arisa ya zauna daga gefenta tare da dafe ta.
“Baby na?” Ya kirata, kai ta d’ago a maraice da k’walla cike dam a idonta tana kallonsa. Goshinta yayi pecking a hankali sannan yace, “Yi hak’uri ki ba Nihal ta sha kinji? Yi hak’uri.”
“Ya Omri wallahi yayi tsami ta6awa kad’ai nayi ma zafi yake mun” ta sanar da shi a shagwa6ance.
“I know sweetheart but kinga Nihal na kuka badan komai ba kuma se don yunwa help her out okay? I trust you na san ki da dauriya.”
“Mu sake bata ruwa zuwa gobe se in gwada breastfeeding nata nasan kafin nan tsamin ya d’an ragu.”
“Babe har zuwa gobe? Idan mukayi haka munyi ma Princess adalci kenan? Yi hak’uri kinji? I trust you I know you can do it” lalashinta yatayi yet still Amal ta kasa sawa Nihal mama a baki ita kuma da gajan hak’uri ta k’i yin shiru. Lalla6ata ya tayi har se da ya samu ta amince, rufe idonta tayi gam sannan shi da kansa ya saita kan Nihal ya ajiyeta, tana kama bakin Amal tasa wani d’ankaren ihun da ya mugun razana Nihal har da shi ma Afzal d’in. Sake nonon tayi ta shiga kuka cike da tsoro kaman ba gobe. Da hanzari Mami ta shigo d’akin a kid’ime se gani tayi Amal na hawaye, ita de ta na ganin shagwa6a yau, a hankali Amal ta mayar da bakin Nihal kai tashiga shayar da ita. Nihal bata yarda aka cire maman daga bakinta ba har seda tayi bacci.
Bada dad’ewa ba Ummi ta shigo da abinci, se rawan jiki take ta kasa zama gu d’aya da Nihal duk da cewan barci take, daga ta d’auketa suyi nan se suyi chan. Ita wai tunda take bata ta6a ganin fine baby ba kaman Nihal ba.
*****
“Ka ga hoton yarinyar?” Mummy ta fad’a had’e da mik’a wa Daddy wayanta across the table inda ya amsa. “Kaiii masha Allah Amal tayi k’ok’ari ita ta haifi wannan k’atuwar baby’n da kanta.”
“Wallahi ko Alhj da kanta, yarinyar tubarkallah k’atuwa.”
“Gaskiya Allah ya raya gobe in shaa Allahu zamu je mu dubata. Sun sa mata suna ko tukuna?”
“Eh sunsa Amal ce ma ta sa.”
“Masha Allah ya sunan?”
“Nazeefah, tayi wa ‘yar uwarta takwara amma za ana kiranta da Nihal.”
“Alhamdulillah Alhamdulillah Allah sarki Amal, Allah ya cigaba da yi mata albarka yasa ‘yar uwarta tayi koyi da ita.”
“Ameen Alhj wallahi addu’ata bata fin haka kullum.”
“Ya Nazeefar har yanzu tana kan bakanta na cewa baza ta dawo ba?”
“Eh tun d’azu ma ina trying line nata amma baya shiga.”
“Toh Allah sa de lafiya.”
“Amin.”
“Jameelah zata kwana achan kenan ko?”
“Eh kasan dake girkinta ne setace ni in taya Amal kwana amma ai kaga idan nayi haka ban kyauta ba tunda de jikarta ce ta farko shi ne nace suje ni zan kula da kai.”
STORY CONTINUES BELOW
“Hakan yayi Hjy Surayya Uwar gida a gidan Alhj Abdallah, Allah cigaba da yi miki albarka.”
“Kai Alhj ameen kayi ka gama muje ka watsa ruwa ko baka fad’a ba na san ka gaji.”
“Wallahi kuwa kaman kin sani meeting meeting baya k’arewa haka.”
Yana gama cin abincin ta sirka masa ruwan d’umi ya watsa suka kwanta. Washegari da sassafe ta tashi ta shiga had’a breakfast na nan gida da kuma wanda zata kai wa su Amal. Tana cikin aikin ne wayanta dake kan counter ya shiga ruri hannunta ta d’auraye tayi drying a jikin towel sannan tayi sauri ta d’aga duda cewan new number ne ke kira.
“Assalamu Alaikum” ta soma da cewa.
“Wa’alaikumus salam” aka amsa daga d’ayan 6angaren.
“Nazeefah?” Ta ambata had’e da sauk’e wayan tana mey duban lamban da kyau. “Nazeefah is that you?”
“Yes Mummy ina kwana.”
“Wani layi nake ganin kaman Nigerian number? Kin dawo Nigeria ne?”
“Eh Mummy ina Abuja yanzu haka, zuwa anjima zan shigo in shaa Allah flight d’ina by 2 ne.”
“Toh Alhamdulillah Alhamdulillahi sannu da dawowa Nazeefah sekin shigo.”
“Ya Daddy?”
“Lafiyashi k’alau me kike so in dafa miki?”
“Anything will do Mummy.”
“Don’t you miss my Eghusi?”
“I really do Mummy amma bana son saki aiki ne.”
“Karki damu Allah kawo ku lafiya.”
“Ameen Mummy se mun sake waya.”
“Erm Naz-” sede har Nazeefah ta katse wayan. Dama so take ta sanar da ita cewa Amal ta haihu kuma tayi mata takwara but then seta ga it’ll even be better idan Nazeefan ta shigo tukuna. She has a feeling everything is going to work out yanzu tunda yanzu ba tare da kowa ya mata fad’a ba ta duba taga ya kamata ta dawo gida. Ohh she can’t wait ita da Amal su fara shiri. Nan da nan ta kammala girkin ta kai musu nasu dining, ta kai wa Papi da sauran masu aiki nasu sannan tasa nasu Amal kuma a flask ta shirya komi tsaf sannan ta shiga bayi tayi wanka ta shirya. Har ta gama karyawa Daddy na bacci seda tazo fita ne ta tada shi “Alhj ni zan wuce yaso ko daga baya seka shigo.”
“Ina zakije da safen nan haka?” Ya tambaya yana k’ok’arin bud’e idonshi.
“Gidan Amal zan kai musu breakfast.”
“Ba munyi zamu fita tare ba? Ina Abba?”
“Ya na nan na kai mishi breakfast shima yana kwance yaso anjima seku taho tare naga baccin naka yayi nisa ne Alhj kaman stress yayi maka yawa.”
‘”Yata ce fa ta haihu.”
“Shiyasa ai zaka iya zuwa duk lokacin da yayi maka, nasani ‘yarka zatayi maka uzuri now go back to sleep idan ka tashi breakfast naka na jiranka akan dining ni na tafi.”
“Toh ki gaishesu.”
“Zasuji ba-bye.” Acikin mintina k’alilan driver ya sauk’eta gidansu Amal inda ya shiga da baskets d’in ciki. Kasancewar ba kowa zaune a parlourn seta wuce ciki, ta inda ta jiyo hayaniya ta dosa had’e da yin sallama bakin k’ofan kamin ta bud’e.
“Yanzu k’ara ruwan sanyi kikayi akan wanda na sirka miki Baby?”
“Assalamu Alaikum” Mummy ta sake yin sallama wanda se a nan sukayi noticing presence nata suka kewayo bakin k’ofan. “Ha’a ‘yar uwa yaushe kika shigo? Bismillah bismillah sannu da zuwa.”
STORY CONTINUES BELOW
“Ya nake ta jin hayaniya haka?”
“Ina kwana Mummy?” Amal dake d’aure da towel ta gaisheta tana mey k’ok’arin sauk’a k’asa.
“A’a ‘yata yi a hankali kinsan k’asan ki ciwo ne ba sekin durk’usa ba hakan ma yayi, ina kwana ya jiki?”
“Alhamdulillah da sauki’i ya daddy?”
“Lafiyanshi k’alau na barosa yana bacci akan cewa anjima shi da Abba zasu shigo, ya jikata?”
“Ayyah haka yace mun jiya Allah kawo su lafiya.”
“Ina Nihal tamu?”
“Tana gun Yaya a d’ayan d’akin.”
“Har anyi mata wanka ne? Sannu da k’ok’ari ‘yar uwa.”
“Sannu ‘yar uwa ai da ma baza kizo ki same mu haka ba sede kizo kiga kowa yayi wanka tsaf amma wannan yarinyar” tayi maganan tana nuna Amal da yatsa “Nakega sede ke ko Ummi ne zaku tayata zaman jegon dan ni kam ta raina ni bata ko shakka na.” Mummy na dariya ta tambayi meya faru inda Mami ta shiga irga mata, “yanzu haka ruwan dana sirka mata bayan nace kar ta k’ara na sanyi akai ta kama ta k’ara.”
“Toh Amal ai seda ruwa mey d’umi ake wankan ko so kike jikin ki yayi tsami ya rub’e shi ruwan zafin ai magani ne kar fa ki manta jikin naki du ciwo ne yanzu.”
“Mummy wallahi baki ji d’umin ruwan ba har fa hayak’i yake.”
“Rufa mun baki sangaltacciya kawai.”
“A’a ‘yar uwa ke kuwa ya zakiyi ma maman Nihal haka? Kinga maman Nihal yi hak’uri ki shiga bayin kiyi wanka bari in sirka miki da kaina nawa baze kai na Mami zafi ba.” Haka da k’yar suka samu Amal tayi wankan ta fito itama Mami ta shiga suka karya sannan Amal taje amso Nihal daga gun Afzal wa Mummy had’e da kai masa breakfast nasa. Sallama tayi bakin k’ofan bayan da ya amsa ta bud’e ta shiga. Tsince akan gado ta samesa da gajeren wando ajikinsa yayinda ya kwantar da Nihal akan k’irjinsa tayi tsit sekace ba ita ta fitinesu ta hanasu barci ba daren jiya.
“Toh kuma kinyi tsaye a wajen bazaki k’araso bane ko inzo in kar6e ki?” Yace da ita.
“Not at all Ya Omri I just can’t believe my eyes, like you two are the most cutest beings I’ve ever seen.”
“Look at you cute thing come in.” Murmushi ta sakar mishi sannan ta mayar da k’ofan ta k’arisa ciki ta ajiye abincin kan bed side drawer sannan ta zauna daga gefensa. “Good morning Ya Omri” ta gaishesa tare da kissing lips nashi a lokaci guda.
“Morning my sunshine” ya amsa “You’re looking spectacular se kace ba ke kika haihu ba jiya ba, such a strong girl.”
“Kai Ya Omri” ta amsa tana murmushi.
“I’m damn serious kinyi kyau and above all you smell sooo good.”
“Thank you Love kai kam dan k’azanta ko wankan ma bakayi ba anyways you’re still smelling good.”
“Aww dan ina mana raino kike so ki zageni?” Ya tambaya da d’aurarren fuska.
“Haba Sweetheart I was only kidding jazakallah kaji? Ya Nihal? Tayi bacci?” A hankali ya lek’a fuskan had’e da gyad’a mata kai “Sekace ba ita ta cika mu da kuka ba jiya.”
“Toh baku yi mata abinda take so ba ai dole.”
“Kaman ya ba ayi mata abinda take so ba Ya Omri? Ita wai kar in cire maman daga bakinta, a ina aka ta6ayin haka?”
STORY CONTINUES BELOW
“Oho de se kiyi hak’uri after all dama nata ne.”
“Toh kawota in kaita wa Mummy she’s so eager to see her.”
“Oh ayyah, ehemm before I forget, wai Mami yaushe zat tafi?”
“Yaushe tazo ko yaushe zata tafi kake tambaya?” Ta sa dariya.
“Babe wallahi jiya da k’yar nayi bacci I miss your legs wrapped around me.”
“Same here Ya Omri, I miss sleeping on your broad chest amma ya muka iya? Se na fita daga arba’in Mami zata tafi.”
“What!! Wasa kike amma ko?”
“Ka zauna anan.”
“Rania wallahi bazan iya ba gaskiya, if only you have an idea how I suffered yesterday alone.”
“Toh Baby ya zamuyi?” Ta tambayesa tana shafa gashin kansa a hankali “Kaman yadda ban iya wankan baby ba kaima na tabbata baka iya ba idan ba Mami wa ze nayi wa Nihal?”
“Toh ba se ki koya ba, in fact ni zan ma koya.”
“Wa d’in wallahi baza ka iya ba.”
“Toh ke ki koya mana Baby?”
“Ni wallahi tsoro nake gani nake kaman zan karyata idan na rik’eta ba kaya a jiki.”
“God help me is just that I miss you Rania.”
“Me too Ya Omri” ta amsa had’e da kwantar da kanta a gefen na Nihal a k’irjinsa.
“She’s so beautiful” ta furta tana wasa da ‘yar hannunta.
“Just like you” ya amsa had’e da zagaye hannunsa a bayanta. “Kinsan wani abu?”
“Tell me.”
“Kinsan kin mun wayo ko?”
“Da nayi meh?”
“Da Nihal take kama dake ke kad’ai mana, ina laifin ko ido nane ta d’an d’auka.”
“Toh yi na ne Ya Omri? If it was my way ai sede tayi kama da kai tunda de kafi ni kyau.”
“Inji waye na fiki? Besides I was only joking, darling you’re the most beautiful being I’ve ever known amma de ina son second child d’ina yayi kama dani kisan yadda zakiyi.”
“Wa ya fad’a maka ma zan sake haihuwa? Daga Nihal se Nihal.”
“Chab lalle ma! A dalilin mey?”
“Da nace ka shigo labour room ina k’i kayi?” Tayi maganan tana k’ok’arin mik’ewa.
“Sweetheart ba haka bane” yayi saurin fad’a yana k’ok’arin dakatar da ita.
“Toh yaya ne? Ni ban ta6a jin inda mata ta kira miji labor room yak’i shiga ba.”
“Shine kikayi zuciya?”
“Toh bazan yi ba?”
“Baby ba haka bane I was so scared bana son jin kukanki.”
STORY CONTINUES BELOW
“But I needed you in there sweetheart.”
“I’m sorry okay? Next time in shaa Allah tare dani zaki shiga.”
“Ba wani next time d’innan daga kan Nihal na gama haihuwa na se inde zaka auro wata.”
“Ba watan da zan auro ked’in de zaki haifo mun masu kama dani har goma.”
“Sannu toh kad’au haihuwan wasa ne?” Cike da dabara ya sake miyar da ita jikinsa “Yi hak’uri baby na yi hak’uri kinji?”
“Naji toh.”
“Then kiss me.”
“Dalili?”
“Dama nasan ni kad’ai ke kewarki?”
“Kaga bani Nihal in tafi nasan Mummy har ta gaji da jirana.”
Mik’ewa yayi ya zauna “you must kiss me first.”
“Or else?”
“Or else bazan bada Nihal ba.”
“lol ba se inje in fad’a musu ka hana ni ba.”
“Toh kije d’in” ganin ta mik’e dagaske yayi sauri ya cafke hannunta wanda hakan ya sata fad’i kan gadon. Nihal ya ajiye a gefe yayi sauri ya haye kanta yana mata dariyan mugunta.
“Yaya mey haka? Ka d’agani wallahi banida lafiya.” Wani killer’n murmushin dake tafiyar mata da imani ya saki “Let your dream boy kiss and take your sickness away baby.”
“Nikam ka d’agani Nihal dan Allah ki fara kuka.”
“Ai ita ‘yar arziki ce ba kaman ki ba.”
“Au nice ‘yar tsiya?”
“Ni ban ce haka ba” ya amsa yana dariya.
“Wallahi Yaya nasan maganin ka, nikam d’agani” bata hankara ba kawai taji sauk’an lips nasa akan nata. Kissing nata ya shiga yi a hankali yana mey tafiyar mata da imani. A sannu a sannu yake kashe mata duk wani sassa a jikinta, Amal bata san lokacinda ta shiga mayar masa da martani ba a garin haka har d’aurinta ya kunce. Knock da suka jiyo daga bakin k’ofan ne ya dawo dasu daga duniyan da suka fad’a a rikice Amal ta ture Afzal daga kanta ta mik’e zaune tana k’ok’arin mayar da d’an kwalinta. “Baby??” Suka jiyo muryan Mami.
“Ermm na’am Mami” ta amsa cike da tashin hankali.
“Kar6o Nihal d’inne har yanzu?”
“Ermm ermm na bata nono ne.”
“Ohh toh kiyi sauri Mummy na jiranki.”
“Toh Mami gani nan zuwa.” Juyowa tayi ta danna wa Afzal dake ta faman kallonta harara yana wani lasan le6ensa, daga bisani kawai ta kai masa pillow fuska. “God help me! Ni kuma mey nayi?” Ya tambaya yana mata dariyan mugunta.
“Ma tambaya na kake ko? Fisabilillahi wani irin abun kunya ne wannan Yaya?”
“Da nayi mey? Talking as if you didn’t enjoy it too.”
“Aww ma haka zaka ce? Zaka gani” kafin tace zata mik’e yayi sauri ya rik’eta “Shikenan ke Rania abu kad’an zuciya.”
“Ni sakeni in d’au ‘yata mu tafi.”
STORY CONTINUES BELOW
“‘Yarki ko ‘yar mu? Now that aside yi hak’uri Yaya is sorry.”
“Naji sakeni.”
“Kiyi hak’uri mana toh I said I’m sorry.”
“Nace naji.”
“Toh smile” murmushi cike da tsangwama ta sakar masa yayinda ya saketa ta d’au Nihal dake kwance a gefe, har bakin k’ofan yayi mata rakiya had’e placing gentle kiss a kan goshinta “See you around, I love you.”
“I love you too” ta sanar dashi sannan ta k’arasa wajen su Mummy. Bada dad’ewa ba Maamah, da sauran k’awayenta suka zo yi mata barka. Da Azahar Ummi da Abba suka kawo abinci inda Abba ya sawa Nihal albarka, sun kusan tafiya Papi da Daddy suka shigo suma. Wajajen 2:30 Nazeefah tayi wa Mummy waya kan sun iso dai-dai wannan lokaci Daddy suke shirin komawa da Papi dan haka suka ke6e inda take sanar da shi shigowan Nazeefah. Mamaki na sosai Daddy ya sha take suka wuce airpot suka d’aukota. Kuka sosai Nazeefah ta tsaya yi da suka had’u se faman neman tubansu take har suka isa gida. Bayan ta watsa ruwa ta sauk’o ta sami Mummy inda tayi serving nata abinci.
Abincin take ci amma gabad’aya babu hankalinta a tattare da ita.
“Nazeefah lafiya?” Mummy da ta karance ta na d’an lokaci ta tambaya.
“Ermm babu” ta k’irk’iro murmushin dole, miyan yayi dad’i I’ve missed your cookings.”
“Thank you, fad’i tunanin mey kike?”
“Babu fa kawai naga gidan ne ya canza site na waye wancan? Amaryar Daddy?”
“Eh na ‘yar uwata ce mahaifiyar Amal kuma amaryar Daddy’nku.”
“Oh” ta amsa sama-sama sounding not surprised. “Meyasa Daddy ya had’aku? Kuma harda mahaifinta suka dawo?”
“Eh we’re one big happy family down here, kuma ni na kawo shawaran a had’a mu.”
“Happy?” Ta nanata cike da rainin hankali.
“Nazeefah baki tambayi ya Amal ‘yar uwarki take ba?”
“Mey had’i na da ita? Please not this time Mummy.”
“Haba Nazeefah na d’au kin dawo saboda kin gano kuranki ne kina son ki gyara tafiyarki ko ba haka ba?”
“Wani kuskure Mummy? Mey na aikata? I’m not back because of that so called Amal I’m back because I’ve missed you and unless kina so acikin sati in koma in da na taho zaki daina mun maganan Amal bana son jin maganan da ya shafeta.”
“Uh well tunda kince haka dama ina son sanar dake cewan ta haihu ne jiya ta samu ‘yarta kuma tayi miki takwara.” Chak ta tsaya da hannunta da take k’ok’arin kai loman tuwo. “What???” Ta tambaya out of disbelief.
“You heard me right Amal ta haihu ta yi miki takwara.”
“Ni tayi wa takwara?” Ta kuma tambaya had’e da sakar da wani dariyan rainin hankali “You’re always good at telling jokes Mummy but not this time around.”
“Yaushe na zama playmate naki da zan na cracking jokes da ke Nazeefah? Amal ta haihu kuma tayi miki takwaraamma ita da Afzal sunyi deciing zasu na kiran ‘yar da Nihal.”
“Mummy kinsan mey kike fad’i kuwa?”
“Tabbas na sani kinga” tayi maganan had’e da d’ago wayanta kan pictures na Nihal ta kai had’e da mik’a mata “here swipe left ga yarinyar nan.” Hannu na k’yarma Nazeefah ta amshi wayan ta shiga kalla da fari ma taso k’aryata komai sekuma taga irin tsan-tsan kaman da baby’n keyi da Amal nan ta sake tabbata da cewa eh ‘yarta ce amma kuma se tayi mata takwara? Me ta ta6a yi mata mey kyau a duniya da har zesa tayi mata takwara? Shin Amal bata sane da irin k’iyayyar da tayi mata ne? Shin bata san cewa bayan shaid’an da fir’auna se ita tafi tsana fiye da kowa a duniya ba? Wow! Bata hankara ba kawai taji hawaye na tsiyaya daga d’ayan idonta wanda tayi saurin sa hannu ta goge had’e da mik’a wa Mummy wayanta sannan ta mik’e.
STORY CONTINUES BELOW
“Ya haka lafiya?” Munmy tayi saurin tambaya. Wanke hannunta tayi cikin bowl ta goge da towel ta shiga tafiya ko amsa Mummy batayi ba, tana kaiwa d’akinta ta fad’a ciki ta nufi kan gado inda ta kwanta. Kuka ta shiga yi kaman ba gobe tana mey tsanar kanta na d’aukan tsana da k’iyayyan duniya da tayi ta aza akan ‘yar uwarta wanda suka kasance jini d’aya da ita. Ji tayi kaman ta kashe kanta dan irin munanan ababen cutarwan da ta ringa yi wa Amal baiwar Allah. Shin masu halayya irin na Amal guda nawa suke a duniya irin tamu ta yanzu? Ace duk irin sharratayyan da bita dashi amma ita ta sak’a mata da alkhairi haka har ta d’auki sunanta ta sanya wa ‘yarta ta fari bayan ga mahaifiyarta dana mijinta a raye? Subhanallah ita kanta baza ta iya yafewa kanta abubuwan da tayi wa Amal ba bale ta soma neman yafiyanta. Gaskiya ne ta cuci kanta a rayuwa, da tun farko ta gane cewa idan abu rabon mutum ne ko ta yaya zai samu idan kuwa akasin hakan ne toh ko ta yaya ya buga baze ta6a samun abun ba koda ya samu ma abun baze yi lasting mishi ba. Da tun farko ta rungumi k’addaran cewa ita da Afzal are not meant to be da batayi hurting one and only sistee nata ba.
Tana cikin tsakiyan kuka Mummy ta bud’e k’ofan ta shiga da hanzari ta shiga share hawayenta.
“Nazeefah?” Mummy ta kirata had’e da dafe kafad’arta.
“Kukan mey kike haka? Tashi ki zauna muyi magana.” Ba gardama ta mik’e zaune cikin tsananin kuka tace, “Mummy I’ve hurt Amal so much, ta ina zan fara bata hak’uri? She really did not deserve everything I put her go through Mummy nayi nadaman abubuwan da nayi mata.”
“Inde Amal ce na tabbata ta jima da yafe miki komai Nazeefah tunda de har ta d’au sunanki ta sanya wa ‘yarta bayan ga mahaifiyarta a raye, inspite of everything Amal still loves you Nazeefah.”
“Abinda yafi ci mun rai kenan Mummy, meyasa zatayi mun takwara? Meyasa baza ta tsane ni ba kaman yadda na nuna na tsane ta? Meyasa bazata sak’a mun sharrin da nayi mata da sharri ba? Why is she making me feel like a bad guy?”
“She only did what’s right to reunite you guys.”
“Mummy I feel like a total crap ji nake kaman in kashe kaina Amal ta fini ta duk inda nake tunani” ta fad’a tana kuka sosai.
“Kar kice haka Nazeefah, life is a competition but we’re not competitions amongst ourselves, yadda kike ganin Amal ta fiki da wani abun itama haka take ganin kin fita ta wani fannin, you guys are sisters Nazeefah you learn from each other okay?” Fad’awa jikin Mummy tayi tana mey cigaba da kuka yayinda Mummy ke lalashinta.
**** Washegari…
“Har kin shirya ne?” Mummy ta tambayi Nazeefah dake sauk’owa daga kan stairs.
“Eh Mummy good morning.”
“Morning breakfast naki na kan dining.”
“Thank you Mummy ina Daddy?”
“Ya fita office just a while ago.”
“Ohh kakan Amal fah?”
“Yana nan zaki je gaishesa ne?” Kai ta gyad’a a hankali, dad’i sosai Mummy taji “sunansa Papi ba Kakan Amal ba kinji?”
“Naji.”
“Muje in raka ki toh.”
***
Bayan sunyi sallama Papi ya tashi ya bud’e musu k’ofa, a parlour suka zauna inda Nazeefah ta sauk’a har k’asa ta gaishesa. “Ina kwana Papi?” Na sosai Papi yaji dad’i ya amsa da fara’a “Tashi mamana, tashi ki zauna ya karatu? Ya k’are ko da saura?”
STORY CONTINUES BELOW
“Ya k’are Papi sauran graduation ne kawai.”
“Toh madallah Allah sanya alkhairi.”
“Ameen Amal tazo ta samu ‘yarta kuma.”
“Eh mun samu takwararki.”
“Haka Mummy tace, toh Allah ya raya ya d’ayyiba.”
“Ameen ameen.”
“Dama nace barin gaisheka kafin in wuce chan gida in duba Amal kuma in baka hak’uri game da duk wani rashin hankalin da na tafka da a baya, please forgive me.”
“Ba komai ‘yata nagode Allah sak’a da alkhairi ya miki albarka komai ya riga ya wuce kinji?”
“Ameen Papi, thank you so much.”
“Toh Abba bari mu koma” fad’in Mummy har bakin k’ofa ya rakasu sannan ya dawo ciki. Nazeefah na gama breakfast ta jira Mummy ta shirya suka fice. Tun da suka isa gidan gabanta ke fad’i shin idan sun had’u da Afzal zatayi mishi magana ne ko kuwa?
“Mummy I can’t do this” ta fad’a kafin su shiga ciki.
“Sure you can Nazeefah karki ji komai okay??” Kai zallah ta iya ta gyad’a sukayi sallama suka shiga.
“Ha’a Mummy sannu da zuwa” cewan Afzal dake zaune a parlour da Nihal rik’e a hannunsa yana mey k’ok’arin tashi. Mik’ewan da yace zeyi sukayi ido hud’u da Nazeefah ba k’aramin fad’i gabansa yayi ba for a second ya d’au ma ko hallucinating nata yake.
“Nazeefah?” Ya ambata bayan tsawon lokacin da suka d’auka suna kallon juna da sauri ta kawar da kanta daga kallonsa had’e da gaishesa “Ina yini Ya Afzal?”
“Nazeefah yaushe kika dawo? Bismillah ku shigo” waje suka nema suka zauna ita da Mummy yayinda ya cigaba da rik’e Nihal.
“Jiya-jiya ta shigo” Mummy ta amsa.
“Oh ayyah ya karatu? Ya k’are ko da saura?”
“Ya k’are Amal ta sauk’a lafiya?”
“Lafiya k’alau Alhamdulillah an samu takwararki” ya amsa had’e da mik’ewa dan kai mata baby’n, a garin mik’a mata ita hannunsa ya goga nata kad’an. Mutuwan tsaye yayi waien yayinda itama tayi freezing inda take zaune, ji tayi duk wani rayuwan da sukayi da a baya suna dawo mata, ta d’au by now tayi moving on, ta d’au koda ta sake sanya sa acikin k’wayoyin idanunta baza ta sake ji mishi wani abu ba ashe ba haka bane, har yau akwai ragowan soyayyarsa a cikin zuciyarta.
“Masha Allah she’s soo big” ta fad’a tana k’ok’arin 6oye bak’on lamarin daya ziyarce ta. “And soo beautiful ga shi kamanninsu d’aya da Amal.”
“Wane an raba kara” cewan Mummy. Bayan Nazeefah ta d’an rik’eta ta mik’awa Mummy sannan tayi gyaran murya. “Ya Afzal nasan komi ya riga ya wuce amma dan Allah ka yafe mun duk wani abinda nayi maka da wanda na sani da wanda bana sane da shi I’m really sorry.”
“Nazeefah there’s no need to, mun riga mun zamo abu d’aya yanzu, Allah ya yafe mana gabad’aya Amal will be so thrilled to see you bari inyi mata magana.” Knocking yayi bayan an amsa ya shiga a gaban dressing mirror ya sameta zaune tana taje sumarta.
“Ya Omri?”
“Ina Mami?”
“Wanka” ta amsa.
STORY CONTINUES BELOW
“Come there’s something you need to see.”
“Menene? Meya faru?” Lokaci guda hankalinta ya tashi a cewarta wani abu ne ya samu Nihal.
“Kede kizo.”
“Yaya please speak up menene ya faru? Nihal ce?”
“Just come” cike da fargaba ta mik’e tabi bayansa suna shiga parlour ya matsa gefe wanda hakan ya bata daman sanya Nazeefah a ido. Da fari ma k’in amincewa tayi, ta d’au ko wasa idanunta suke yi mata.
“Nazeefah?” Ta kira ta cike da k’in yarda.
“My sister” Nazeefah ta amsa idanunta suna masu cikowa da hawaye.
“Nazeefah kece??” Itama ba shiri idanun nata suka ciko da hawaye.
“Yes Amal ni ce” da gudu ta ruga taje tayi hugging nata inda suka fashe da kuka dukansu biyu. Mummy dake rik’e da Nihal itama bata san lokacinda idonta ya cika da k’walla ba.1
“Amal I’m so sorry please forgive me.” A hankali Amal ta janyeta daga jikinta sannan ta shiga share mata hawayen ta, “ki daina neman tuba na Nazeefah, har cikin raina na yafe miki komai duniya wa lahira kukan ya isa haka.” Sake rungumeta Nazeefah tayi tana mey sake tsanar kanta na duk wani cutarwan da tayi wa ‘ya uwarta.
“Amal ban san da wani bakin zan yi miki godiya ba” cewan Nazeefah bayan sun nemi waje sun zauna a gefen Mummy. “Amal you named your first daughter after me, duk kalan mugunta da bak’in halin da na miki hakan be hanaki aikata abinda kika fasa ba, da Mummy tace mun kin yi mun takwara na kasa amincewa sabida kasa gane wace irin mutum ce ke da nayi, instead ki sak’a mun da sharri kaman yadda nayita cutar da ke se kika gwammaci ki sak’a mun da alkhairi, alkhairin da ba kowa ne ze iya yin irinsa ba, Amal I hate myself for ever hurting you please forgive me.”
“Nazeefah komi ya riga ya wuce and I can’t tell you how happy I am right now that you’re back with us, addu’ata kullum bata fin Allah ya dawo mana dake cikin k’oshin lafiya and here you’re in good health and shape Alhamdulillah.”
“Amal thank you so much, thank you.”
“Don’t mention Nazeefah kuma dan Allah kibar kukan haka ya isa.”
“Allah ya raya mana Nihal gani nake kaman mafarki har yanzu wai kin yi mun takwara, ‘yar uwata guda tayi mun takwra it feels like a dream.” Murmushi mey k’ayatarwa Amal ta sakar wa Nazeefah “Ya karatu ya k’are?”
“Eh saura graduation.”
“Ayyah congratulations Allah sanya alkhairi.”
“Ameen, Naki fah?”
“Final year zan shiga nima.”
“Masha Allah Allah sanya alkhairi ina Mami?”
“Tana wanka nakega ta fito yanzu.”
“Muje ki raka ni in gaisheta.”
Da murmushi kwance a fuskanta ta mik’e “Oya tashi muje toh.” Afzal ya kasa daina murmushi, all he’s ever wanted is to see his Amal happy and ya san ba abinda ze kai mata shiryawa da Nazeefah dad’i se gashi yau Allah ya shirya tsakaninsu, he can’t ask for more.
Har cikin d’aki gun Mami Amal ta kaita inda suka gaisa sannan Nazeefah ta nemi tubanta na duk wani abinda tayi wa Amal wanda ta san yayi wa Mami zafi, a wajen duk sukayi reconciling. Kusan Azahar Mummy tace zata koma dan yin girki Nazeefah kam tace sam bata tafiya, se hira suke da Amal ta rik’e takwararta a hannu. Chan da zatayi sallah ta mik’a ta wa Amal dan yin alwala, tana cikin yin sallah ne wayanta dake gefen Amal ya shiga ruri lek’awa tayi dan ganin wake kira acewanta ma ko Mummy ce se gani tayi Baby❤️💕🔐 na flashing akan screen d’in da hoton wani kyakkyawan bawan Allah yana nan d’an bak’i da shi attatched to it. Murmushi ta sakar ta cigaba da rik’e Nihal har izuwa lokacinda Nazeefar ta idar.
STORY CONTINUES BELOW
“Wa ya kira?” Ta soma da tambayanta.
“Baby” Amal ta amsa.
“Oh!” Ta furta tana sunkuyar da kai.
“Baza ki kira shi bane?”
“Ba matsala ko anjima zan kira shi.”
“Wai kunya na kikeji ne? Kinga baza ki shanya mun in law ba haka kawai, d’au waya ki kira shi kice mishi sallah kike, gashi” Mik’a mata wayan tayi sannan ta cigaba da shayar da Nihal.
Kaman yadda Amal ta bui’aceta tayi ta kira sa back inda ya d’aga a first ring.
“Halo Babe?”
“Belle how’re you?”
“I’m fine Babe? Ya kake?”
“I also, just that I miss you.” So take tace she misses him too amma kunyan Amal take ji “Ermm Babe kasan wani abu? I will call you later okay? Se anjima” bata jira jin me zece ba ta katse. “Iyyeee so tell me who is the handsome looking dude?”
“Kai Amal kede kiyi focusing a abinda kikeyi kafin kisa nono ya bi mun kan takwarata.”
“Baki amsani ba waye shi?”
“Wani ne.”
“Your man?” Gira ta d’age mata as yes. “Wow ina kuka had’u? A UK?” Nan ma giran ta sake d’agewa.
“Awwn am so happy for you sister tell me about him mana.”
“Nak’i.”
“Pleaseeeeee.”
“Sa’anki d’aya saboda Nihal.”
“Haha naji ina sauraronki.”
“Sunan sa Ahmad A UK muka had’u naje yin masters d’ina whereas shi kuma PHD. He’s a Nigerian, yana zama a abuja yana da aure da yara biyu.”
“Wow I’m really impressed in ba wai kin fad’a ba mutum baze ta6a cewa yana da aure ba.”
“I know right ko ni da ya cemun yana da aure ban yarda ba, ashe wai harda yara biyu, ko da shike auren wuri yayi when he was 22, he had his first son at 24 and his second daughter at 27 he’s now 34 years old.”
“Impressive Nazeefah I’m so happy for you wallahi su Mummy sun sani?”
“Not yet ke na fara sanarda ina son se ya gama karatunsa ya dawo se in yi introducing nashi to the family.”
“Hakan yayi Nazeefah wallahi nayi miki murna sosai ya uwar gidan ta shi? Ya had’aku ko tukuna?”
“Ya had’amu, ai be jima bama suka je mishi hutu suka komo bari kiga pictures da muka d’auka da ya fita damu outing ranan” tayi maganan tana latsa wayanta “Here you go” amsa Amal tayi ta shiga viewing tana swiping “Goodness he’s got such a beautiful family wallahi, da ke da uwar gidan ban san waye gaba a kyau ba gaskiya gata itama very young.”
“Yes she’s 28 years old amma kika ganta wane tana early twenties nata.”
“Bata da wata matsala ko?”
“Sam wallahi yadda kika san kanki haka take tamkar ‘yar uwarta haka ta d’aukeni.”
“Such is life Allah ya baku zaman lafiya mey d’aurewa ya sunan yaran nasa?”
STORY CONTINUES BELOW
“Fawwas da Fauzah.”
“Masha Allah I’m sooo happy for you sis.”
“Thank you Maman takwara.”
****
Ba Nazeefah ce tabar gidan ba se bayan sallan isha. Haka kusan kullum tana gidan Amal, kafin suna kuwa ta samu ta had’a akwati mey set uku wa Amal biyu na baby d’aya nata. Amal ta samu kyautuka sosai sede ace masha Allah. Seda Mami tayi mata arba’in sannan ta koma gida.
Nihal na da watanni uku Amal ta soma shiga school so anytime zata fita school se ta biya gida ta kai wa su Nazeefah raino. Atimes kuma wa Ummi. Da Khaleefah ya dawo hutu kuwa se su had’u suyita fad’a akan Nihal cewa sam d’aya baze ta6a ta ba. Yarinya san kowa k’in wanda ya tasa, ga fara’a ga murmushi, gata very plumpy, gashin kan nan tabarkallah. Haka nan rayuwa ta cigaba da kasance musu cikin kwanciyan hankali da so da k’auna. Na sosai Afzal yake ji da Nihal sau dayawa yakan riga Amal dawowa gida daga office da ya tashi seya biya gidansu Mummy ya amshi ‘yarsa su dawo gida ya mata wanka yayi rainonta kafin Rania’nsa ta dawo.
Amal could not ask for more, this is indeed a dream she’s living. A perfect daughter, a perfect husband and a perfect family.
_7 months later…_
Ababe da dama sun gudana, da izinin Allah su Amal sukayi graduating bata da spill ko d’aya, ta d’ayan fannin ma Nazeefah har taje UK ita da Mummy anyi musu graduation nasu sun dawo. Shima saurayin nata Ahmad ya gama PHD nasa ya dawo gida har Nazeefah tayi introducing nasa wa su Daddy. Maganan da ake yanzu haka sa rana kad’ai ya rage. Kafin nan time to time yakan zuwa Maiduguri ya duba Nazeefah sannan ya koma, ko wani zuwansa kuwa da tsaraban da yake tanadarwa Nihal na musamman takwaran wife to be nasa. Na sosai yake son Nazeefah dan haka yake son duk wani nata tuni ya nemi Afzal suka k’ulla abotaka abinsu. Kullum sede be shigo gari ba se sun sa Sultan da ya kasa yin aure har yau a gaba. Maganan da ake yanzu haka Ahmad ya had’a Sultan da wata cousin tasa, abu kaman wasa wai Sultan ke soyayya. Na sosai yarinyar ta masa bayan ya kwana biyu haka yakan je Abuja ya duba ta. Afzal da Amal kuma sede abinda ya k’ari, soyayya suke zubawa kaman ba gobe sekace jiya-jiya aka d’aura musu aure even though suna d’an ta6a fad’ansu time to time amma hakan baisa sun daina son juna ba da kuma daina son farinta wa juna ba.
Yau ranan ta kama Asabar ranar da aka fi sani da ranar d’aurin aure.
Amal ce zaune akan dining table da Nihal dake da 10 months yanzu a gefenta tana feeding nata custards, tana sha tanayi mata wasa. Ba ruwanta ta sha nono ta sha madara ta ta6a custards gata nan k’atuwa gwanin sha’awa. “That’s girl” Amal tayi praising nata tana k’ok’arin sake kai mata wani spoon d’in baki “shanye se mu tafi unguwa ko? Muje dinner’n Aunty Maamah da na Ya Abdool, ai zaki je?”
“Dada” ta amsa wane taji abinda aka ce mata.
“Na Ya Abdool kikeso? Toh ai duka zamu je ko kin mance a venue d’aya za’ayi?”
“Dada!”
“Yauwa Princess d’ina shanye toh se mu tafi” Wayanta dake ruri ne tayi saurin d’agawa ganin Nazeefah ke kira tare da sawa a hands free.
“Mamman Nihal”
“Na’am sis yane?”
“Ina kwana ya kike?”
“Lafiya k’alau ya gida ya Ya Ahmad?”
“Yana nan d’an wahala yaushe ne ya tafi ba last week ba?”
STORY CONTINUES BELOW
“Amal na dariya ta amsa “eh wani abu ne?”
“Wai ze sake zuwa he’s missing me.”
“Shine zaki ce mishi d’an wahala?”
“Toh mey ne? Sekace baya son kansa dan Allah, shi bai tunanin stress ne ai nakega cewa Fareeda (matar Ahmad) zan kar ta barsa yayi wannan tafiya.”
“Ji min ‘ya! Ke baki san cewa garin masoyi baya nisa bane? Ko a tunaninki idan baya sonki zena zuwa ganinki akai akai haka ne?”
“Toh ai ni tausayinsa nake I don’t want him stressed out.”
“Ke bar shi ya d’an d’ana kafin ya kaiki gidansa, kinga fa da zaran kin shiga gidansa se yadda yayi dake.”
“lol toh uwar mugunta.”
“Eh mana enjoy your time while it lasts, kafin ya d’aukeki ya tafi dake.”
“Ya tafi da wa? Ce miki akai zan bishi Abuja?”
“Yo eh mana” ta amsa tana dariya.
“Lallai wallahi anan zan zauna kinsan ni bana k’aunan zaman Abuja, gara nayi zama na anan kusa da takwara ta.”
“Lol toh zamu gani de.”
“Ina takwara ta?”
“Gata nan ina feeding nata, Nihal ga Aunty Nazeefah kice mata hello.”
“Titi titi” ta soma cewa tana wasa wai Titi ne Aunty Nazeefah.
“My baby how are you?”
“She’s fine tana having breakfast.”
“Oh ayyah yanzu tailorn ya kawo mana gowns namu fa.”
“Haba yayi kyau?”
“Wallahi sosai barin ma na Nihal sekinga yadda d’inkin ya fita.”
“Yaushe zaki shigo toh?”
“Yanzu idan nayi wanka na karya.”
“Alright toh sekin shigo ki gaishe da kowa da kowa.”
“Zasuji ba bye.” Ta kai ga ajiye wayan kawai taci karo da 6arnan da Nihal tayi, goran ruwanta ta kwantar se tsiyaya yake tana kalla tana jin dad’i.
“Haba! Haba Princess shikenan ke ba a isa a baki abinci ba se kin miyar da wajen k’azanta?”
“Rania?” Afzal dake fitowa daga d’akinsu ya kirata, yana sanye da babban riga sky blue da ya sha aiki ya kuma mugun amsan sa ba shakka d’aurin auren Maamah da kuma na Ya Abdool zasa tunda se an d’aura na Ya Abdool za ayi na Maamah a different venue.
“Yes Ya Omri?” Ta amsa tana mey d’ago kai don kallonsa. “Dayyumm” ta furta a ranta dan wani irin kyan da yayi. “Kinga sabon cuff links da na siya last tafiyan da nayin nan? I’m running late” sede kaman ba da ita yake ba dan yadda hankalinta yayi nesa da ita. Nihal dake gefenta se faman kiransa take da “Dada” tana k’ok’arin mik’ewa daga kan kujerarta taje ta wajensa. Cike da tak’ama yake takawa har ya k’arisa dining aean, har anan binsa da kallo Amal take.
“Rania?” Ya kirata had’e da shafe gefen fuskanta wanda hakan ya sanya ta murmushi. “Ya Omri you look you look…” tama rasa abinda za tace.
STORY CONTINUES BELOW
“Handsome?” Ya d’age mata gira.
“Yes you look handsome, masha Allah” tsugunawa yayi had’e da pecking nata “Thanks Babe.”
“Dada Dada!” Nihal ta cigaba da kiransa.
“My Princesss” ya mik’a hannu ze d’agata “tukunah bari in d’auraye mata jiki kar ta 6ata maka kaya” murmushi ya sakar mata sannan ya ja kujera ya zauna daga gefeyana yiwa Nihal wasa har zuwa lokacinda Amal ta goge mata jiki ya d’agata. “So Kinga cuff links d’ina?”
“Wanda ka taho dasu last tafiyan ka?”
“Yep” ya amsa yana yiwa Nihal dake ta faman dariya wasa.
“Muje yana cikin wardrobe naka.”
“Na duba ban gani ba.”
“Kai dama ka iya duba abu ne? Yana nan a ciki muje.”
“Ni d’in ko? Muje zakig” d’akin suka nufa, Amal tayi gaba ta shiga neman pack d’min bada dad’ewa ba se gashi ta fito da shi. “Now tell me what is this?” Ta juyo had’e da tambayeshi. Shiru yayi na d’an lokaci “A ina kika samu? Bade a ciki ba.”
“Da a ina? Here of course” tayi nuni da cikin wardrobe d’in
“But I j-“
“Shhh literally Nihal is the only infant baby here but technically there are two babies tunda ko neman abu in ban sa hannu ba baka iya samu, here kar6i inje inyi wa Nihal wanka muma mu shirya.” Hannunta ya rik’e kafin ta fahimci abinda yake shirin yi ya janyeta seda ta fad’a jikinsa.
“Thank you for handling my crazy ass Babe I love you very much” ya sanar da ita looking deep into her eyes. It’s been almost 5 years but anytime Afzal ya sanar da ita cewa yana sonta se bugun zuciyanta ya dad’u. There’s no lying, she’s immensely in love with him.
“I love you much more my very own handsome” ta mayar mishi, adjusting height nasa yayi ready to kiss her, dai-dai lips nasa yazo sauk’a akan nata Nihal ta tsinka mata mari tas a kumatu
“Wayyo Allah Mami na!!” Amal ta sa ihu Afzal be san sanda yasa dariya ba ganin haka itama Nihal ta bi sa se dariya sukeyi wa Amal.
“Nihal kika mareni? Kika mari Mamma? Kai kuma Yaya maimakon ka mata fad’a se ka tsaya kana dariya ko? Wallahi da zafi” ta k’arashe tamkar zatayi kuka.
“Nihal tell Mamma sorry” itako se ta d’aga hannu da niyyan k’arawa Amal wani marin.
“Wallahi kika mareni ba ke ba shan nono yau.”
“A’a yi hak’uri beyi zafi haka ba Nihal and Dada are sorry yi hak’uri kinji sweetheart.”
“Ni kayi sauri kar ka makara Ya Abdool yace nice ban shirya ka da wuri ba?”
“Ko da nayi latti ma ai zey mun uzuri ko?”
“Dalili?”
“Because I have such a gorgeous wife.”
“Really?”
“Yes baby” da wayo ya sauk’e Nihal a kan gado sannan ya zagaye hannayensa a ‘yar kunkuminta yana mey sunkuyar da ita ta baya a hankali, “Now I really wanna kiss y-” bata bari ya k’are maganan da yake ba ta katsesa ta hanyan kissing lips nasa, a sannu a sannu har suka kai jikin bango suna manne da juna, chan Amal tayi pulling out, “Yaya you really have to go n-” shima nan be bata daman k’arisa abinda tayi niyyan fad’i ba ya kuma crashing lips nasa akan nata.
Warin da suka jiyo yana tashi ne ya dawo dasu daga duniyan da suka fad’a. “Humm Princess is that you?” Afzal ya kewayo yana kallon Nihal data d’age d’uwawu a sama.
“Nihal sannu ko?” Fad’in Amal “Ya Omri ka san mey za ayi yanzu? Bari in tayaka cire babban rigan nan ka wanke wa Princess taka pupu ko?”
“O my God Rania kiga it’s almost getting to 10 ina hula na kar inyi latti.”
“Now you’re trying to run away huh?”
“Take care of yourself okay? I love you, Nihal I love you too.”
“Dada!!” Juyowa yayi ya sakar wa Amal murmushi sannan ya nufi gaban mirror ya sa cuff links nasa ya cakkwala hulan Zannan nan ya kuma feffeshe jikinsa da turare “See you around Babe.” Murmushi Amal ta tsaya yi wa kanta admiring how gorgeous he is. “Be back safely, Allah kare mun kai Yaya.” Wajen Nihal ta nufa ta d’agata sukayi bayi inda ta wanke ta da kyau sannan tayi mata wanka daga nan itama tayi nata. Tana cikin shafawa Nihal oil a gashi Nazeefah ta shigo nan Nihal tafara kiranta da “Titi Titi!” Nan da nan Nazeefah ta amshi Nihal ta gama shiryata itama Amal ta samu ta shiga shiri. Ana cikin haka Maamah ta shiga kiranta a waya.
“Maamah zata kasheni gashi har pass 11 bamu tafi ba” ta furta tare da answering call d’in.
“Haba Amal it’s pass eleven already.”
“Amarya a gidan Mansoor yi hak’uri wallahi ankon dinner’n mu ne basu iso da wuri ba kinga yanzu da mun tafi se kuma bayan dinner mu dawo yi hak’uri we’re on our way.”
“Toh se kunzo send my love to princess.”
“I will bye se mun shigo.” Nan da nan suka gama shiri suka fita “Mamman Nihal wallahi kinyi kyau tsaya in d’aukeku da princess.”
“Sis bakiga munyi latti bane kam?”
“Pleaseee mana Mamman Nihal bakiya son in tura wa Ya Afzal ne? Mu d’an birkita masa lisafi a gun d’aurin aure?” ta k’are tana mata signal da gira.
“Alright pose d’aya kawai fa amma.”
“Eh eh naji” nan ta ciro wayanta yayinda Amal ta tsaya gyara pose nata dana Nihal nan Nazeefah ta shiga d’aukansu bata tsaya ba seda ta d’auki a k’alla ishirin “Yauwaaa sauran selfie yanzu” da sauri tayi joining nasu ta musu selfies. “Bari in nemi wanda yayi kyau in tura wa Ya Afzal” tayi maganan suna masu takawa gun mota inda driver ke jiran su. Suna shiga driver yaja mota.
“Yauwa kinga Ya Afzal yana ma online, tsaya kiga yana bud’ewa ze kiraki.” Cewan Nazeefah se kuwa tana mishi sending pics d’in yana bud’ewa in the next like one minute wayan Amal ya shiga ruri tana dubawa taga Afzal.
“Mena fad’a miki?” Nazeefah ta tambaya tana dariya itama Amal d’in dariya take sannan tayi swiping ta d’aga.
“Rania tell me I’m not dreaming how can you be soooo beautiful?? Masha Allah I have the most beeeyouteefull wife and daughter” se blushing kawai Amal take ko amsa sa ta kasa yi dan dad’i.
ALHAMDULILLAH Anan na kawo k’arshen wannan littafi nawa mey taken RANA D’AYA. Allah ya sa mu amfana da darusan da suke ciki inda nayi kuskure kuma Allah ya yafe mana gabad’aya. Ameen.1
With love Mariam Anas AKA Miemiebee.❤️💕

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page