FARA YAR SHEHU CHAPTER C

 FARA YAR SHEHU CHAPTER C

Ban taba jin gidan mu ya isheni ba se wannan karan, seda naji inama nayi zamana a dutse ban dawo ba. Tunda nan din dana dawo dan samun relief kwatakwata abin ya gagara, se ma karin wani tension din da na samu.

Washegari, babu kowa gidan dukkansu sun tafi hakan yasa na fito da wurwuri na shiga kitchen dan hada breakfast se na samu Asiya ta fara hakan yasa nayi joining dinta muka kammalla. Ina cikin wanke hannu na cikin sink naji maganar Abba da Yaya Halifa, cikin sauri na fito dan ranar nake tunanin zuwa gidan shi. Suna zazzaune na samesu, gaishesu na fara yi sannan na tambayeshi su anty Zannira yace min dukkansu suna lafiya. Munata hira yawanci shi da Abba ne sede nayi ta dariya a haka Ummaah ta same mu. Gefen Abba ta zauna suka gausa da Yaya halifa sannan na gaisheta nima, amsa min tayi normal kamar ba jiya ta tara min jamaa ba. Nayi tunanin inama wani yayi min abinda Ummaah tayi min, inaga nida shi har abada amma Ummaah Ummaah ce tafi gaban komai, everything she said I consider it as frustration.

Key Abba ya miko min yace

“Auta yau shekararki ashirin da shida, Allah yayi miki albarka. Ga gift dina”

Gaba daya na manta da wai yau birthday dina, tabbas girma ya hau kaina I couldn’t believe cewar I’m 26 years already. Kallon key din nayi na mota ne, ai wani ihu na buga ina fadin

“Abba mota? Abba nagode Abba Allah ya saka maka da mafificin alkhairi”

Na juya gurin Ummaah data tsira min idanu tana kallona, da murana na mika mata key din nace

“Ummaah kinga gift din Abba”

Maimakon ta karba se cewa tayi

“Haba Sir…”

Dake haka take kiranshi a matsayinshi na tsohon dan sanda

“…ta yaya zaka siya mata mota? Mu da muke son ta kawo miji tayi aure”

Gaba daya se naji murnar ta dauke min, dukkan mu muka saka mata ido muna kallonta da mamaki, nidai inajin anya Ummaah ta ce kuwa? Is she really my mom ko wani ke zugata haka? Abba yayi murmushi yace

“Madam, meye hadin siya mata mota da samun mijin aure? I see nothing”

“Dama baza kaga komai ba amma ai wannan maza tsoron tunkarar ta zasu dinga yi, gata likita ga mota”

Dariya sosae Abba yayi sannan ya dubi Yaya halifa kafin ya kara kallonta fuskarta a hade kamar hadari, yace

“Halifa, kaji zancen mamanka fa. Can you imagine? What if ta dalilin motar zata samu miji. Kema mutane sun fara miki wannan hudubar? Aure ai nufin Allah ne kuma ko shekara arba’in Asmau ta kai babu miji bazan takura mata ba, saboda abu daya na sani everything lies on it timing!”

Daga wannan maganar abin mamaki Ummaah ta fara kuka wai Abba ya fada mata magana sannan wai shi yake daure min wani guri shiyasa naki bada hankali nayi aure. Gaba daya hankali na yayi masifar tashi, na dinga bata hakuri ina lallashi amma ko kallona batayi ba, se na fara kuka nima naji gaba daya tamkar an kifar min da duniyar da nake ciki. Yaya Halifa yasa ni muka fita yana ta bani baki tareda nuna min komai zai wuce.

Da yamma naji gidan ya isheni, kamar ana hadamin wuta haka na dinga ji, babu sauki naje nace da Ummaah zanje gurin Adda Sa’ada, bata hanani ba se cewa tayi

“Gwara ki dinga fita ko kya samu mashinshini.”

Har na tafi ina mamakin Ummaah, mota ta kirar peugeot 206 blue na bude nayi addua sannan na tafi. Adda Sa’ada tayimin murna sosae, da muka kebe na dinga fada mata abubuwan dake faruwa , tayi ta bani hakuri akan lokaci ne sede I’m frustrated na gaji hakanan, bansan yaushe ne har laolacin zai zo ba.

Da daddare bayan na idar da sallar ishai na tafi parlon Abba dama seda na tabbatar Ummaah na dakinta sannan naje. Yana zaune ya gama cin tuwo na shigo tareda zama inda ya nuna min. Shiru nayi na rasa me zance masa saboda nauyinshi naji. Can yace

“Asmau ya akai ne?”

Kaina na girgiza nace

“Abba gobe zan koma dutse sa…”

“Saboda me? Ba kince min two weeks zakiyi ba, is just five days kawai fa”

Se na rasa me zance masa tunda ni dai I’m not used to karya amma bana son ce masa pressure Ummaah ce ke damuna tunda dazun naga sun samu sabani akaina.

“Asmau, Rukayya ce ko? Ita take damunki akan aure ko? Kada ki damu kinji ko komai lolaci ne, kada kiji haushinta nata salon kilawar ne. Kibar tafiya dutse ki kara hutawa kinji.”

Kaina na gyada nayi mishi godiya sannan na tafi nayiwa Ummaah sallama. Har naje bakin kofa se naji tace

“Asmau zo nan”

Jiki a sanyaye na koma na zauna kan carpet, gaba daya mun zama sirikai nida ita , idan ina tare da ita se naji wani irin nervousness na damuna. Drawer ta janyo ta fito da wata leda ta aje batace komai ba haka nima se shiru nayi ina fidgeting da hannuna. Asiya babu jimawa ta shigo da wani kasko cikeda ga garwashi, ajewa tayi a gurinda babu carpet saboda kar ya kone. Tana fita Ummaah ta mike tareda min alamar na bita, hakanan babu yadda zanyi na bita, wasu itatuwa ta ciro a ledar ta watsa cikin garwashin take kuwa wani mugun hayaki ya tashi, seda gabana ya fadi. Haka tasa Na tsugunna ta samu wani thick towel ta lulluba min. Na dinga tari ga mugun gumi da ya dinga karyo min Amma Ummaah seda nayi more than 10 minutes a haka sannan ta yayeni.  Dana mike se layi har seda ta rikeni sannan ta hada min ruwan wanka shima wasu magunguna ne a ciki amma ko uffan bance ba haka nayi, ina fitowa ta bani mai na shafa sannnan ta sallamrni na tafi.

Seda na jera kwana biyu kullum se anyi sau biyu kafin wani lokacin na fita a hayyacina, na rame na lalace nayi duhu. Babu arxiki na cewa Abba tafiya zanyi dan bazan iya zama ba. Shima duk abinda ake ya sani dan tuntuni na fahimci maganin farin jini ko na samun miji akemin, i cant afford losing my iman saboda hakan.

Da naje yiwa Ummaah sallama tace min

“Asmau akwai bikin Amratu, ina fatan zakizo”

Kaina na gyada amma deep down nasan wallahi bazan zo ba dan na rigada na rantse bana son zuwa na zama topic of discussion.

Da motata na tafi, wannan shi ne karon farko dana fara tuki me nisa and alhamdulillhi naje lafiya. Dakin kyaftun na wuce bayan na tsaya na zubarda magungunan da Ummaah ta bani cikin incinerator sannan na shiga. Tana zaune ta gama girki kenan na shigo nayi wujigawujiga dani kamar an jefoni. Tace

“Twin meye hakan? Me yake damunki?”

Zama nayi nace

“Bani abinci kede”

Babu musu ta zubomin shinkafa da wake da kifi se dressed salad da zobo, nasan gandar kyaftun hakan yasa nace

“Kinyi Bako ne?”

Fuskarta ta kwabe tace

“Dr Lamin ne yayi lunch a gurinna”

Kallonta nayi for some minutes kafin na cigaba da cin abinci na , seda na gama tas nayi wanka na dakko zani daga cikin wardrobe dinta na daura hade da top na dawo na zauna nace

“Twin, meye tsakanin keda lamin abin yafi karfin kawance sede wani abin”

Murmushi ta fara kamar na mata albishor tace

“We’re dating har yaje Bama”

Idanuna a waje , se kuma na saki murmushi nace

“Alhamdulillah, yafi muku ai kun zauna da kuna raina mana hankali”

Hakanan mukai ta hira har ta shirya zata tafi night duty sannan taga motar dan bance mata da ita nazo ba da dauki bazai batta muyi hirar ba.

Chromic din hannuna na aje sannan aka miko min gauze na rufe muka rufe da plaster sannan na kalli kowa tareda sakin murmushi bayan na cire google din idanuna nace

“Alhamdulillah, nice job everyone!”

Dukka team din murmushi sukaimin kowa yana kokarin karasa abinda ya kamata, Apron na cire na wulla cikin bin, fitowa nayi tareda cire mask din dake fuskata na danyi mika sannan na tafi lounge dinmu dake cikin OT bayan na karba patients folder a gurin chief anesthetist naje na zauna kan cushion ina documenting aikina. Koda na kammalla banida wani aiki daya rage min hakan yasa na zauna tareda lumshe idanuna kamar wadda take bacci amma ba baccin nake ba, ina naga idon bacci? Matar da ko da daddare se nayi da gaske baccin ke daukeni balle yanzun ido na ganin ido, da dinma guri na samu amma yanzun babu halin hakan, dan damuwar da nake ciki kadai ta isa ta samin insomnia. Bansan adadin lokacin dana dauka a hakan ba se naji an bubbuga min kujerar da nake kai hakan yasa nayi firgigit na bude idona da sukai ja. Dr. Fadima ce tana tsaye ta zubamin ido, zama na gyara tareda kirkiro murmushi nace

“Doctor yaushe kika shigo?”

Zama tayi kujerar dake facing dina se center table dake tsakaninmu, coke ne a hannunta chilled dan kadan ya rage yayi kankara. Tunda nake ban taba ganin coke addict irinta ba, kullum muka hadu se nayi mata fada amma sede tayi dariya kawai tace ai ina exercise ko kuma ace min inada glucometer. Haka dai take tana da kirki tare mukai medical training dinmu a Bayero.

“Dr Shahada, me yake damunki?”

Dan murmushi nayi nace

“Me kika gani? Am I looking terrible?”

“More than”

Ta fada tana hararata, murmushi na kumayi nace

“Kinsan yadda rayuwa take, mutum baa rabashi da matsala sede addua kawai”

Gyara zama tayi tace

“Amma naki ya fito da yawa, kowa ya kalleki yasan kina cikin damuwa. Kinga yadda kika koma kuwa? Idanunki are all sunken, you hardly concentrate.”

Dan runtse idanuna nayi sannan nace

“I’m trying”

Shi kadai ne abinda ya fito daga bakina, kanta ta gyada tace

“Anjima ki shirya tunda baki komai se mu fita, you need a fresh air”

Kaina na gyada nayi mata godiya sannan muka koma hirar aiki anan take bani labarin MD ya kusa retire, duk se naji babu dadi dukda bansan shi personally ba amma mutumin yasan me yake, i happened to attend a seminar dashi.

Da yamma kuwa muka fita wani hanan hangout, mukai ta hira da ita sannan muka ci abinci danni ko lunch banyi ba, dama kyaftun ke takurani naci, to taje off se ni daya. Sahad mukaje mukai shopping sannan muka koma asibiti. Se naji tamkar ta bani therapy ne. Washegari saturday, kuma shi ne ranar daurin auren Amratu, tun jiya akai kamu da mothers’ eve dama bazanje ba, koda su Ummaah suka kirani nace ai aiki ya cabe min bazan iya zuwa ko ina ba, Ummaah tayi fadan ta tareda jadadda min akan next weekend na tabbatar naje kwalam bikin wata neice dita, wannan nasan bazan tsallake ba, dole ne naje idan kuma ba wani problem nake son karawa kaina ba.

Ranar sunday muka hadu, Dr lamin, Dr Hafiz, Dr fadima, Dr Habiba, kyaftun dani muka shirya zuwa rock climbing. Tunda na tashi da asuba nayi wanka nayi mana toasting bread sannan na daukar mana drinks. Cikin leggings da knee length top maroon na shirya, nasa hula maroon se nayi rolling veil karami sannan nasa wani black canvas na tsaya a meeting point. Anan na tarar da Lamin da Habiba. Muka gagaisa sega kyaftun da fadima. Dr Hafiz ne ma yadan yi delaying har muka so makara. Garu mukaje inda zamu wani mutumi yazo danyi mana rakiya , tunda muka fara hawa dutse na fara ihu saboda abin ba na wasa bane, a daddafe wani lokacin se an ja hannunmu sannan muke iya hawa a haka dai muka kai karshen gurin. The amazing veiw ever. Aerial view din was wow mukai ta hotuna, nayi farin ciki, nayi dariya wadda take from the bottom of my heart bawai yake ba kamar yadda na saba yi. A wannan lolacin na manta cewar inada damuwa na manta da duk wasu matsalolina na kalla sama saboda yadda nake very high se naga kamr zan taba gajimare. I was so happy.1

STORY CONTINUES BELOW

Wajen sha daya muka koma prison dinmu, kowa ya tafi dakinshi, ina zuwa na cika bath da ruwan dumi na shiga da towel na gasa jikina, ina fitowa na sha pain reliever naci pasta sannan n kulle dakin na fara bacci, God so kind period nake bani Na tashi ba se wajen biyar da rabi shima knocking ne ya tadani. A kasalance na mike tareda tambayar waye amma babu amsa hakan yasa kawai na wuce toilet na sake wanka sannan na shirya.

Sati na kamawa ranar Friday, muna gama rounds na dauki hanya zuwa kwalam. Lokacin da naje zanyi sallama da kyaftun seda ta cemin nayi hakuri duk abinda zan tarar. Tabbas nasan ba wani abin arziki zan tarar ba, banda tsangwama da kuma nuna ni da zaa dinga yi. Anan sakkowa a massallacin jumaa ina shiga garin. Straight Cikin gida na wuce nidai nasan ba tarbar dana saba gani zan tarar ba a gurin Inna amma dukda haka na rugada na saba, indai nazo kwalam da dadi da babu dadi to gurinta nake zama saboda ko me inna zatayi min bazan taba manta alkhairin ta akaina ba. Wannan rikon da tayi min ma kadai ya isa balle yadda ta fifita ni akan sauran jikokinta.

Acan gefe nayi parking sannan na ciro trolley ta na rataya hand bag dita a kafada na doshi gidan. Muna dan gaisawa da mutane har Ikram yarinyar Adda Habiba da Badar yarinyar Yaya Hauwa sukazo suka karba kayan nawa muka shiga ciki. Gidan a cike yake anata kidan kwarya wasu na rawa, gefe ana sauke abinci a haka na kutsa kai ina gaida mutane wasu su ganeni wasu suce ai na girma duk kammani na sun canja, nidai nawa murmushi kawai.

A dakin inna na tarar dasu Adda da wasu daga cikin cousins dinmu, sunata shiri zaaje gurin kamu banma shige ciki ba na zauna cikinsu munata gaisawa yawanci na jima banga mutane ba kowa se cewa yake na zama babbar mace nayi kudi aure kawai ya ragemin. Sede inyi murmushi kawai. Adda Maryam ita ta tayimin ankon so gurinta na karba nawa na saka ko Inna bamu hadu da ita ba na tafi.

Wajen sallar ishai na dawo a gajiye seda na biya ta gida na gaida Ummaah sannan na taho. Nanma banga Innar ba, babu mutane sosae hakan yasa nayi shirin bacci bayan nayi wanka nazo n haye gadon cikeda kewarshi. Rigingine nayi ina kallon roofing din gadon tareda tuna rayuwar da nayi akan gadon, lokacin i was living peaceful banida wani tashin hankali daya takura min amma yanxun wace ni. Wayata na janyo na bude wani Emdex application ne na drugs, na cigaba da studying magungunan. A hankali bacci yayi gaba dani ba tareda na sani ba dama nayi addua kafin na fara karatun.

Na jima da yin baccin kamar daga sama naji ana tashi na, da kyar na bude idona raina duk a jagule saboda i hate it idan aka katse min baccin dare. Inna ce a tsaye tana kallona hakan yasa na tashi daga kwancen da nake tareda gyara zaman hular kaina nace

“Inna an wuni lafiya? Ya taro?”

“Lafiya lau”

Ta bani amsa sannan tace

“Asmau wannan gadon da kika kwanta akai ki sakko ki dawo kasa”

Kallonta nayi da rashin fahimta nace

“Ai zai ishemu mu kwanta ni dake, se kace nayi kiba”

Kawar da kanta tayi tace

“Kinga Amina da Nusaiba ne zasu kwanta akai saboda kinga su ciki ne dasu, kuma me aure bai saba kwanciyar kasa ba”

Kallonta nake sosae, maganar ta dakeni idan tacemin sakko Asmau wasu zasu kwanta saboda ciki, ni ai ba hauka nake ba nasan me ciki need something comfy babu yadda zaayi me ciki ya kwanta dandaryar kasa but meye se ance me aure bai saba kwanciyar kasa ba wato dole se an nuna min ni din banyi aure ba kenan. Kaina na gyada nace

“To ni ina zan kwana kenan?”

Tabarma dake gefe ta nuna min tace

“Ki sakko ki shimfida ta”

Wani mugun takaici ya kamani nace

“Inna, kinfi kowa sanin bana bacci akan tabarma, ina laifin waccan katifar”

Na nuna mata extra katifar ta da take jingine, a hasale tace min

“Ke sakko daga gadonnan, idan baki son tabarmar kina iya tafiya wani gurin. Yarinya se tsirin masifa da ruwan ido, dole ki kasa aure”

Yadda nake kallonta seda yasa ta dauke kanta naji haushi sosae yadda har bazan iya fada ba, kaina na girgiza tareda sakkowa daga gadon na finciki hijab dina da wayoyina nayi waje amma se na dawo har lokacin tana tsaye bance mata ci kanki ba na janyo trolley na da hand bag dita na nufi kofa se ta biyoni tana fadin

“Matsalata dake kawata zuciya, meye abin hada kaya?”

Juyowa hawaye ya cika min idanu nace

“Aure Allah yake sawa ayu, idan lokacina yayi zanyi, gorinku da duk wani tsangwama ta bazai saka nayi ba.”

Kafin na gama tuni wasu daga cikin mutanen dake parlor sunzo suna tambayata me ya faru babu wanda na kula nayi ficewata Allah yasa bankai motata gida ba hakan yasa na bude motar na shiga tare da kifa kaina jikin steer wheel na fara kuka, a raina ina rokon Allah ko aron wucin gadi ne yasa nayi, ko ma wanene kawai Allah yasa nayi aure na huta. Seda na gaji da kukan sannan na kira Adda zannira akan ta bude min gida ina nan tafe. A takaice dai acan na kwana, juyin duniya Yaya Halifa yayi akan na fada masa meye matsalata naki suka hakura suka kyaleni.

Washegari ban fita ko ina ba ina daki ina jinyar zuciyata bansan waye yace ma Inna ina gidan ba se gata tazo da kwanuka wai na kari nace mata ni na koshi bazan ci ba, ta kada ta raya naki, ko ji tayi abinda tayimin bai dace ba oho mata dai. Da yamma kuma sega Ummaah itama abin mamaki lallashina ta dinga yi har ta tsareni naci abinci sannan ta tafi. Da daddare mamansu Rahina taxo biko akan na koma can gurin inna amma nace ni sede wata kuma, ba dai aure bane to nayi alkawarin ko dan cocaine ne yace yana sona aurenshi zanyi, na gaji da wannan masifar har ina?

Wayata na kalla a karo na barkatai ina kallon text din da Ummaah ta turo min kusan awa daya data shude , numbers ne har guda biyu na GLO da MTN a kasan an rubuta Barr. Ishaq. Kifar da wayar nayi kawai ina jiran inji kiranta dan tayi min karin bayani amma shiru bata kira ba, nima kuma ba kira zanyi ba saboda ina tsoron abinda zatace min, bana son hooking stuffs dinnan gwara no matter how bad a situation is gwara ace shidin ya fara ganinka yace yana so, dan bahushe yace matar cushe bata da kwarjini. I believe in that also.+
Hakan yasa na mike na cigaba da gyaran daki. Ranar call nake so yamma nayi Na shirya na dauki stethoscope da key din mota da wayoyina na fita. Call room naje Na zauna a gefe ina chatting a wayata ni kadai ce cikin dakin, se can aka kirani a Emergency hakan yasa na tashi na tafi na tarar da wani fatal accident. Tabbas aikin asibiti dole yasa ka kara gaskata iko da daukaka ta ubangiji, mutum ba komai bane a rayuwa duk wannan dagun kai da dagawa amma lokaci daya Allah zai iya reforming halittar shi muga ta karshen girman kai. Mutanen da sukai accident su goma ne cikin wata golf, i wonder yadda sukai squeezing kansu cikin wannan karamar motar.
Ina shiga na adana wayoyina da sauran abin amfani, O’C dake duty su uku muka hadu dasu dan ceto ran mutanen, amma uku seda suka mutu babu yadda zakayi, sede you will be contented kayi abinda ya kamata tunda duk munsan death is inevitable. Haka sauran bakwai muka sakasu cikin class din daya dace bamu muka zauna ba se bayan sallar ishai. A matukar gajiye mukai sallah sannan na dawo dan nayi documenting aikin, sannan mukai sallama na koma lounge anan na tarar da missed calls din Ummaah. Ina zama na fara kiranta ta dauka nace
“Ummaah inata aiki kika kira, ya gida?”
“Lafiya lau”
Ta bani amsa sannan tace
“Kinga numbers da na turo miki dazun?”
Seda gabana ya fadi nace cikin sanyin jiki
“Na gani Ummaah, inata son na kiraki”
“Ni dana matsu ai na kira, kinsan Hajiya Barira right?”
Kaina na gyada kamar tana ganina nace
“Eh, Ummin Kaduna ko?”
Kawar Ummaah ce irin childhood friend dinnan ce , kowa yasan yadda Ummaah ke ji da ita haka itama indai zatazo kano to se kin ganta tazo gurinta.
“Yawwa, wannan Ishaq din danta ne na uku zaiyi aure shine nake son ku daidaita kanku, kinga kema kya samu ki huta da gorin mutane”
Se nayi shiru tareda adduar Allah yasa ba nufinta in kirashi ba, jin nayi shiru yasa tace
“Baki jina je Asmau?”
“Ummaah to me zanyi yanzun?”
“Kiranshi zakiyi mana, me kike jira da? Come on ki kirashi kice kece wadda Hajia tayi mishi magna akai”
Se naji raina ya baci ni zan kirashi ma bashi ba, ok ya raina ni kenan. Ni na gaji da yadda Ummaah ke hadani da yaron kawayenta suna raina min hankali dan wannan shine third time ana hakan.
” Ummaah, dan Allah karki sani nayi haka, shi ku bashi number ta ya kirani mana amma hakan kamar irin neman kai akeyi dani ne?”
Baki bude Ummaah tace
“Oh da baki gane ba? Shi ai bashi yake nema ba mu muke nema so mu zamui proposing kingane?”
Kaina gaba daya se ya kume, I couldn’t think straight wanne irin ni nake nema ni zanyi proposing? Kawai se nace
“Shikenan”
Kafin muyi sallama ta tambayeni ni na tura mata kudi nace eh, tayi ta shimin albarka har naji dadi sannan na kashe wayar inajin wani abu ya tokare min kirjina, da kyar nake iya fuzgar numfashi na, idona yayi ja ina fatan Allah ya kawomin dauki a rayuwata, ya kawo min miji nayi aure. Dan nasan bani kadai ce a duniya nakai shekarun nan banyi aure ba amma kowa ya takura min an hanani zaman lafiya da kwanciyar hankali. Hannuna nasa na rufe fuskata nayi ta kuka kamar raina zai fita ina fatan as my tears cascade down my cheeks, all my worries will be gone and my pains will be ease!
Ina gama kukan lokacin already goma tayi ko lunch banyi ba balle dinner, yunwa nakeji amma bana tunanin inada nutsuwar zama naci abinci. Mikewa nayi na fito daidai shigowar kiran kyaftun ,  se naji wani sanyi cikin raina at least someone cares. Ina dauka ta tambayeni inda nake , ko minti biyar ba ayi ba se gata da basket a hannunta, tunda ta kalleni se naji jkinta yayi sanyi , zama tayi ta hadamin tea ta bani babu musu nasha sannan ta zuba min Arabian sphaghetti tasha vegetables haka naci sannan tace
“Wannan kuburin na ido me ya faru?”
Lumshe idona nayi ai kamar ance lacrimal glands su sake hawaye se suka wanken fuska, hannuna ta rike batace min komai ba se kallona da takeyi , se can tace
“Asmau menene akan aurenne?”
Kaina na gyada na fada mata komai daya faru, se cemin tayi
“Ki kirashi kinji”
Wani kallo nayi mata irin are you mad dinnan? Murmushi tayi tace
“Ummaah ce tafi karfin komai, just do it saboda haka Ummaah tace”
Haka na kwana ina tunanin yadda zan bullowa koda safe dana fadawa Adda Sa’ada cewa tayi nayiwa Ummaah biyayya hakan kuwa nayi dukda jikina a matukar sanyaye yake haka Na kirashi, tunda ya dauka ko sallamar da nayi bai amsa ba yace
“How may i help you?”
Duk se naji na muzanta amma haka na daure nace
“I’m Asmau shahada, ni ce wadda hajianka tayi maka magana akaina”
Maimakon naji tone dinshi ya canja se naji ya kara tamkewa yace
“Ya akai to?”1
Na kasa cewa komai se wasa nake da hannuna tareda jin mugun haushinshi kamar na shako shi haka naji, jin nayi shiru se cewa yayi
“Kinga idan kin shirya bayanin kanki kya kira but I’ve better things to do!”1
Kit! Ya kashe hannuna na rawa na ciro wayar ina kallonta da gaske yayi hanging, take nayi deleting numbers dinshi daga wayata baki daya inajin tamkar na shake kaina tabbas Ummaah ta gama dani. Da daddare ta kirani akan ko na kirashi na fada mata yadda muaki dashi, tsaki tayi tace na kyaleshi to wannan ya dan sayaya min rai.
1
Ana fara tafiya aikin hajji na tafi nima, i badly want to talk to Allah, lokacinda na ganni gaban kaaaba se kuka na rasa abin roka, se kankame jikina da nayi saboda yadda dukkn tsikar jikina ke tashi. Na jima sannan na samu nayi addua dake lokacin mune daukar farko i got the space. A wannan lokacin alkawarin Allah ya cika kyaftun ta auri Dr Lamin.
Bayan na dawo nigeria da hope akan nasan da izinin Allah kukana ya zo karshe. Nasan soonest alkawarin Allah zai tabbata kaina amma shiru har shekara take neman zagayowa, banma kara saurayi ba duk yadda nakejin nakai babu wanda ya kalleni da sunan yana sona, nasha tsayawa gaban mirror na kalli kaina, inga ina nake da makusa. Ni fara ce fari sosae har wani yellow yellow nake, idan nayi mirmushi bayan dimple dake lotsawa a both sides na kumatu na, akwai wata jijiya green dake fitowa rado rado a goshina. Idanuna normal suke kamar na kowa sede eye balls dina manya ne kuma deep chocolate orbs nake dashi. Hancina dogo ne bakina daidai ni da kaina nasan im a beauty, akaina na fahimci kyau baya kawo miji se lokaci yayi.
Pressure kam se wadda ban fada ba amma akwai lokacinda nayi wata hudu banje kano ba ina dutse saboda Ummaah kamar ta dakeni idan muka hadu ga inna kamar danni ta koma kano saboda girma, kullum gorin yau daban na gobe daban. So se na daina zuwa gidan gaba daya, sukai cigiyar duniya suka rasa. Ranar wata monday na shiga OT yin Appendectomy, ina fitowa straight dama daki nayi niyyar tafiya dan na shirya zanje wata seminar, da sauri na kalla office din Chief Anaestethist saboda jiyo muryar da Abba da nayi. Banma yi niyyar shiga ba haka na shiga and there i saw him sitting looking at me. Da sauri naje na rungumeshi nace
“Abbana”
Hararar wasa yayi min yace
“Nazo biko ne, tunda laifin wasu ya shafeni”
Dariya nayi tareda rufe fuskata , i cant remember ni ina dariya genuinely har haka ba. Ranar se dare ya tafi ko seminar bankje ba, tare mukai lunch a cafeteria se naji ina missing gida sosae. Lallashi na yayi yana nuna min komai zaizo karshe. Haka sati na kamawa naje kano se naga babu wanda ya takira min like always do.Hannuna na zura cikin aljuhun lab coat dita na ciro wayata saboda jin alamar shigowar message a wayata. Message dinne kuwa daga chief obstetrician dake last month na koma gynae team na bar surgical team na fara residency dina. Kallon metron din nayi nace mata
“Mummy, zanje meeting idan akwai matsala a kirani”
Kanta ta gyada tareda min fatan alkhairi, inason matar she’s mother figure, a dan zaman da nayi a ward dinta tana yawan bani shawarwari masu amfani tamkar tasan matsalata akan aure take kullum ni da sauran nurses dinta akwai topic din da zaayi discussing akai. Kuma baka isa kace ka zauna bakayi gaining wani abu ba. Office din Dr halima na wuce dake ita ce chief din tamu, na tsaya ni da Dr hafiz se gata ta fito in her usual outfit wato lace gown an daura lab coat akai, irin classy mutanen ne yar gayun gayu sosae. Da sauri na karasa inda take nace
“Maam naga message dinki gani”
“Yaawa nima yanzun nake shirin kiranki muje meeting zaayi na tarbar sabon MD”1
Kaina na gyada tareda bin bayanta munata dan hira jefijefi, a office din Dr Mahmud anan muka zazzauna akai briefing kowa akan washegari sabon MD da akai posting zai fara aiki , seda Dr Rashida ta ja mana kunne akan kowa yayi watching takunshi saboda baya wasa mutumin idan zaayi aiki ayi dan shi baya daukar kailula. Ta tsoratar damu sosae Amma banji komai ba dana nasan bana barin aiki Na unfinished. Haka muka gama se kuma muka koma office din Dr halima danyin meeting da sauran yan team dinmu. Kafin wani lokaci dukkan asibitin kowa ya shiga hankalinsa ko ward ka shiga se gyare gyare akeyi da fito da sabbabin linens a haka dai ranar ta kare na tafi gidan kyaftun.
Washegari da safe da wurwuri na gama shirina nayi breakfast dan nasan it will be a busy day i know. Hakanan na fito na shirya cikin coffee wando da riga na soft cotton yadi lab coat na daura ban mayi buttoning ba na rataya stethoscope dina a wuya sannan nayi rolling da karamin coffee veil. Kallon kaina nayi a jikin mirror babu laifi idanuna sun fara dawowa hayyacinsu, wannan zurmawar da yayi ciki duk yadan fito dan hankalina ya fara kwanciya na daina tsangwamawa kaina tunda nasan wannan bashi zai bani miji ba.
Gynae emergency na fara zuwa muka gaisa da staffs din gurin sannan aka bani patient din da zanyi reviewing. Ina cikin aikin Dr halima ta karaso mukai rounds sannan muka shiga labor room nanma stable babu wani damuwa sosae a ciki nan muka gama sannan nida ita muka fita. Ko ina cikin asibitin tas yake kowa ya shiga taitayimsa haka kowa yana post dinsa se naji zuciyata tana kwadayin ganin waye wannan sabon MD, naji dadi a raina saboda kowa zai dawo hayyacinsa kowa ya fahimci abinda ya taramu a asibitin.
Karfe goma dukkanmu muna tsaye a reception Doctors mu shida daga kowacce cader mutum uku muna tsaye dan tarbarshi, wayata tayi ringing na dauka Dr Ema ne wani house officer ne su na bari a labor room akan duk yadda ake ciki su kirani, seda muka gama magana dadhi sannan na fadawa Dr halima ta fadamin yadda zamuyi kawai se na juya na tafi, ina zuwa na tarar matar tana wani irin massive bleeding babu anyi anyi ya tsaya yaki hakan yasa nabi shawarar da sister ta bayar akan mu cire mahaifar kawai, dole muka tafi OT and that’s how i missed ganin sabon MD.
A wannan satin kowa ka kalla cikin asibitin kasan ya dawo hayyacinsa, aiki kowa yake ka’in da na’in nidai bamu taba haduwa dashi ba har yayi wata a asibitin. Kowa complain yake akan ya takurawa mutane, to dama hakane idan mutum yazo yana kwatanta gaskiya tabbas kowa zai tsane shi.
Ranar wata litinin nayi aiki na gaji daga nan na tafi Amenity unit wajen kyaftun, mun jima da ita muna hira sannan na tashi n koma lounge. Muna da yawa cikin lounge din masu cin abinci nayi haka wasu na research inda na saba zama naje na zauna bayan mun gaggaisa da Doctors din. Wata Dr hajja watching buddy dita ce ta kawo min wani romantic doctor korean film.1
“Shahada watch this film yayi kyau sosae fa”
Bakina na tabe nace
“Rabani da wannan romantic films din nasu, ana nuna soyayyar da bata existing gaba daya”
Dariya tayi tace
“Hooo Anty Asmau i cant wait naga wanda zaki aura, bama romantic din bane ba, surgeries ne kalakala a ciki zaki karu”
Da haka tasa na karba film din cikin flash dina, komawa na gyara zamana kan cushion din nayi na fixing wayata a charge tareda dan runtse idona a hanaklai bacci ya fara kokarin fizgata, dama gefena wasu house officers ne mata suna zaune Ina jin dayar tace
“Ke kinga sabon MD kuwa”
Bude idona nayi a hankali na kallesu amma duk saboda yadda suka zama engrossed ko effect din idanuna basuji ba, dayar tace
“Kin ganshi ne ke?”
“Sosae ma, though daga nesa ne, ban taba ganin mutumin da fada yake mishi kyau ba se shi, baya murmushi fa amma he’s so cute mashaaa Allah”
Ta fada tana rungume fuskarta da palms dinta, se grinning take, se suka bani dariya. Na dauka ni kadai nayi shashancin admiring maza da kuma one side love ashe inada yan uwa.
“Awnnnn I’m crushing him already”
Wayata ta katse min hanzari da ringing, kaina na kaudar da sauri, tareda sakin siririn tsaki sannan na janyo wayar wata sabuwar number ce, picking nayi tareda karawa a kunnena
“Dr Shahada, Dr halima ce”
Da sauri na gaisheta se tace min
“Kina jina ko? Akwai wata middle age woman a labor room kamar ta samu ruptured uterus, kije yanzun kiyi reviewing dinta in the next 20 minutes zakui mata aiki a OT keda MD”
Ambatar MD seda gabana ya fadi me yasa nida MD. Mikewa nayi na tattara kayana na fita cikin sauri, muryar Dr halima nayi min echo a kunnena
“Nasan zaki iya, i trust your skills amma ki kula sosae sannan kiyi komai da sauri amma with care, kada ki bari ya kamaki da wani matsala. All the best”
Ina shiga labor ward na karanta write up din matar naje nayi assessing dinta sannan na zauna aka shiryata daga nan na wuce OT nayi changing, ranar chief anesthetist din shi zai bamu anesthesia da kanshi sabida wannan shi ne first time da zaiyi aiki a OT tunda yazo. Cikin five minutes suka kammalla komai hakan yasa na kira Dr halima na sanar mata mun kammalla.
“Bara na turo miki digits dinsa ki fada masa kun shirya”
Idanuna a warwaje nace
“Kai dan Allah ki fada masa”
Dariya ta danyi tace
“Shima mutum ne kamar ni”
Daga haka tayi hanging, se na rike wayar sororo ina kallo, aikuwa sega pop din message nata ya shigo, Dr Kwaciddo nayi ta nanatawa kafin da kyar nayi summoning courage na kira shi, muryata a dan rikice nace
“Sir I’m Dr Shahada, muna jiranka a OT koami is set.”
Cikin stern voice yace
“Alright! I’ll be there inshaaa Allah”
Sauke wayar nayi tareda sakin ajiyar zuciya, se naji ya burgeni da yace inshaaa Allah. Ina nan tsaye baifi 10 minutes ba se naji shigowar shi. Dogo ne sosae dan idan na karu jikinshi Allah yasa zan kai aljihun gaban rigarshi, nima a mata bana cikin sahun gajeru amma this is to show how tall he’s. Ba siriri bane da ace bashida tsayi kibarshi se tafi fitowa amma dake yana da tsayi se ta shanye kibar. Shi ba fari bane yafi ga a kirashi baki sede not that dark, ga jin dadi se yasa fatarshi take glowing, smoothly tamkar mace kana kallon fuskarsa kaga ta bafullatanni ko ba usul ba amma an samu trait din cikin jini. Wannan shine MD or i can call him Dr Kwaccido.
Hannunsa ya tafa yana fadin
“Set?”
Kaina na gyada nace
“Set sir!”
Ciki muka shiga bayan mun jira yayi changing, yadda yake aiki will tell you shidin ba na yau bane yasan scalpel scapel tasan da zamanshi. I was extra careful akan aikin har muka gama muka stitching gurin sannan ya kalleni yace
“It’s nice working with you”
“Thank you sir!”
Kawai nace mishi ba tareda na bari kalamamsa sun shiga kaina ba, nasan I’m skilled person duk wanda yayi aiki dani komin yadda ya kware to tabbas se yasan nima na maida hankali. Cikin lounge yaje ya zauna aka kai masa folder yayi documenting sannan ya yiwa kowa bangajiya kafin ya tafi, wata nannauyar ajiyar zuciya na sauke sannan na fita baki daya daga OT. Ward na koma na karasa ayyukan da suka kamata nayi sannan na tashi gaba daya.
Washegari ranar friday, muna kammalla ward tounds dinmu na shirya dan tafiya kano a raina ina tunanin ya kamata yau ba se gobe ba na fadawa Abba kudirina. Misalin karfe uku na isa gida saboda na biya gidan Adda Maryam da nayi niyyar se yamma na koma gida amma ta bata min rai shiyasa na taho. Ina gidan kanin mijinta wani Nasir yazo, that wasn’t the first time dana hadu dashi a gidan sede baifi sau daya muka taba magana ta minti uku dashi ba kullum daga gaisuwa bamu karawa saboda naga dan raijin wayo me, ni kuwa bana cikin wannan class din. Tunda ya shigo muka gaisa naja mutuncin kaina na cigaba da kallona sunata hira shida Adda, can sega mijinta ya dawo, Yaya Mansur muka gaisa ya zauna yana ta jana da hira dake he’s very jovial to tamu ta zo daya dashi.
“Kina wuta fa matar nan, nazo kofar gidana naga wata benz, so inata tunanin wa muka samu? Seda na hango wannan ear piece din naku kafin na gane ashe kece”
Dariya nayi dan Na fahimci stethoscope yake nufi, nace
“Babu wani wuta fa Yaya, amfani ake da dama”
Murmushi yayi ya gyada kai yace
“Yeah! Allah ya kawo miji na gari”
Amin na bashi amsa ina murmushi, kallona Adda tayi tace
“Kamar gaske”
Ko kulata banyi ba  tashi tayi ta wuce ciki itada yayan, bata jima ba ta dawo hakan yasana wuce kitchen akan na duba abinci dan a daura wani, idan naje gidan sisters dina se nayi musu dinner nake tafiya. Kamar daga sama naji Adda Maryam na cewa Nasir
“Kaima kaki kayi aure kamar Asmau, ko baka da budurwa ne?”
Shiru nayi inason jin amsarshi se yayi dariya yace
“Kai time baiyiba, se an tara tukunna”
Gyara zamamta tayi tace
“Kaga Asmau shes 27 years yanzun, gata medical doctor, babu wani serious magana akanta, bana tunanin tana da saurayi gaba daya so idan tayi maka why won’t you tag along kuyi aure”
Idanuna na lumshe jikina har bari yake na rufe warmer da sauri zan fito kawai naji yadda gayen yake babbaka dariya hakan yasa na tsaya, naji yace
“Kina da abubuwan dariya Antinmu, ni wannan kanwar taki ai ta girmeni ma……in a mocking way ya fada, se naji kafafuna sunyi wani sanyi…..27 kikace? Tabdi! Beside ni fa bazan iya auran health workers ba ke wallahi ko a kafa aka daura min su se na kunce”
Tamkar walkiya haka na ganni a  parlon, wani irin mugun kallo na masa nace
“Ai ko maza sun kare nafi karfin na aureka, Adda na gode”
Daga haka na dauki jakata dama veil dina tuntuni yake a jikina nayi waje na barsu baki a sake, mota ta na bude na shiga se kuma nayi shiru ina ganin menene abin fushi har haka? Me yasa raina ya baci dan anyi talla ta, tunda auren yaki zuwa may be kilan ta hakanne zan samu miji. Zuciyata se ta kasu biyu wata na blaming dina wata na tafarfasa tana ganin an raina min hankali ajina ya wuce ayi kamar ana nanawa namiji yana kin karba.
Ina gama parking sega Yaya suleiman, tsayawa yayi yana kallona ni at first ban ma wani lura dashi ba kokari nake na bawa Baba me gadi key din ya shigo da kayan da nazo dasu. Ji nayi yace
STORY CONTINUES BELOW
“Ajhumma!”
Nasan shi daya ke kirana da wannan sunan hakan yasa na dago fuskata a sake na dubeshi nace
“Oppa”
Se naji na tuna da, kamar yadda oppa yake nufin Yaya a korea, yawanci suna fadawa saurayi hakan, tone din da suke using kadai kasan cewar bawai brother yake nufi ba aa sede something else. A wancan lokacin I’m feeling the same, lokacin dana fada se naji wani sanyi a raina but see me today, saying oppa plainly and emotionless rayuwa kenan. Yaya suleiman da naso na kaunace and so much badly wanted na zama mallakinsa amma ya dubi idanuna yace kawata yake son nayi hooking dinsu tare, i felt shattered. That’s then!
“Ya aikin? Kinyi kudi kin manta damu, kullum Nadia tana cigiyarki ko ziyara baki kawo mana”
“Aiki sede godiyar Allah. A gaida Nadia da yara”
Na fada saboda zancen babu ziyara ba mutum daya le zumunci ba both parties keyi, bantaba tunanin zan rabu da raihana da Nadia ba Amma yanzun ni ko numbers dinsu bani dashi. Duk yadda Yaya suleiman yaso na tsaya na nuna masa a gajiye nake dole hakanan yayi hakuri na shige gida. Ummaah Na parlor a zaune itada Asiya na shigo, Asiya ta rungumeni sannan ta bamu guri. Gaisawa nayi da Ummaah tace
“Ina kika tsaya? An shigo da kaya amma ke shiru”
“Nida Yaya suleiman na tsaya”
Bata kara cewa komai ba haka nima se na mike na wuce na tafi dakin Inna, tana zaune kamar kullum ana goga goro. Karba nayi kamar yadda na saba ina gurza mata muna dan taba hira abin mamaki. Hirar arxiki kuma wadda na jima bamui nida ita ba. Tana ta bani labarin ‘yan matancinsu ita da fara yar shehu
“Naso Asmau fara yar shehu ta rayu zuwa wannan lokacin ta ganki. Kawata ce wadda banda kamarta kuma ko bayan data mutu babu wanda ya maye min gurbinta, da yake ita mahaifiyar ta yar Mambila ce to dukkan mu tafi mu kyau, kyakyawa ce ta gaske hakan yasa tun muna shekaru tara aka sakata a lalle, naso kin biyo farin jininta da tuni kina dakinki, da kuma ace shahada da Saude sun barki hannuna da tuni baki shiga wannan kuncin ba.”
Dan murmushi nayi nace
“Inna lokaci ne”
Kanta ta gyada tace
“Da farko nayi tunanin laifinki ne shiyasa na matsa miki, amma a shekarunki na san kowacec so take ta ganta dakin miji. Ina fatan baki rikeni a ranki ba”
Rungumeta nayi da sauri ina dariya nace
“Waye yake fada da kawar shi? Sede idan kawancen bai kai zuci ba”
A wannan na samu sauki, ranar aka tuna da tare muka kwana, Abba nata tsokanar mu wai yau mun hada kai. Da safe nayi dukkan abinda ya dace wanda ya kamata sannan na koma bacci. Wajen sha daya nayi wanka nasan Saturday ce Abba bazai je gona ba, dan baya fita Friday da Saturday he always say they’re meant for rest. Kuma haka yake. Yana zaune shida Ummaah suna kallon Aljazeera, yau mun samu bakuntar yaran Yaya halifa dana Adda ummiey so suma suna parlon se kinji suke. Ina zama muka gaisa yaran suka gaisa se Ummaah ta fita naji dadin hakan sosae a raina dama bana son tana nan bazata bari nayi magana cikin nutsuwa ba.
“Nasan wannan zaman akwai magana, ina jinki”
Abba ya fada yana rage volume din, zamana na gyara nace
“Abba kayi hakuri dukda baka taba magana ba amma nasan kullum yana ranka, nima ba haka naso ba Abba na kai har lolacinnan banyi aure ba”
Murmushi yayi min yace
“Asmau! Ai bake kika hana kanki ba, shima Allah ba hanaki yayi ba he’s testing our faith kin gane?”
Kaina na gyada yace
“So, ki dage da addua Allah baya bacci. Ban taba miki zancen aure ba, bawai bana so kiyi ba ko kuma irin ban damu dinnan ba, ko daya I’m worried, sede ya zanyi idan na takura miki me zai canza?..”
Kanshi ya girgiza yace
“…Nothing my dear, ‘ya’yana takwas kowanne is educated islamically and western, bakwai sunyi aure kowanne peacefully, ke daya kika rage idan na kasa hakuri me nace da Allah? Ban gode bisa abinda yayiwa ‘ya’yana bakwai ba. Kinsan musulinci is wonderful, komai is open sede idan baka sani ba. Aure abu ne me girma, sunnah ce me karfin gaske sede mu bamu dauka sunna bace kawai aure wajibi ne idan bakai ba gani ake kaika jawo amma i know kinsan tarihin Nana Maryam mahaifiyar Annabi Isah A.S batayi aure ba amma sura kacokan sunanta ne, so bawai se kayi aure zaka samu yardar Allah ba kede ki tuna tarbiyar da nayi miki kawai, ki kare mutucinki da martabarki. I tried as much as i can na zama mutumin arxiki saboda ku, nasan ko bani da rai zaace wannan yaran CP Shahada ce, amma idan na zama mutumin banza akwai matsala abinda zai zama rightfully yours zaa iya denying muku.”
Se naji sanyi cikin raina saboda maganar shi tayi min dadi naji sanyi da farin ciki a raina. Gyara zamana nayi nace
“Abba na samu wata school a America, idan ka yadda ina son zuwa”1
Shiru yayi yana ta kallona har seda yasa na fara jin uneasiness, se yayi murmushi yace
“Zan iya yin tunani da shawara?”
Kaina na gyada nace
“Sure Abba”
“I’ll get back to you”
Ban kara ji daga gurin Abba ba akan tafiya ta states, shirun da naji ya tabbatar min it’s a no kenan. Hakan yasa na dangana ba tare da na kara masa magana ba. Wani sati na dawo na tarar da Ummaah ta cika fam kamar zata fashe dama wannan mood din kam ai na saba dashi. Tunda naga haka na kama kaina tareda jan mutumcina. Washegari inadakin inna muna hira ta aiko Asiya akan ta kirani. Ina zuwa na ganta a zaune gefen gado tana ta karkada kafa, zama nayi kan carpet nace+
“Ummaah gani”
Key din motarta ta mika min tace
“Dakko hijab dinki zamu fita”
Babu musu na mike hannuna rikeda key din na tafi dakina, dama atamfa ce jikina dinkin skirt da riga so kawai se na dauki hijab coffee dake atamfar da coffee jiki, shoe rack dina na duba na dauki wani flat milk vine se purse sannan na fito , ganin tana jirana yasa ko Inna banyiwa sallama ba kawai na wuce gaba tana bayana. Seda nayi warming motar sannan nayi addua kafin muka fita. Kallonta nayi tana ta danne danne a wayarta nace
“Ummaah ina zamuje?”
Dago idonta tayi ta kalleni, then ni kuma na rigada na maida hankalina akan titi tace
“Gidan Hajiya Zakiyya zaki kaini”
Seda naji kaina ya sara min baa taba matar da bana so a kawayen Ummaah ba kamar wannan matar, tana daya daga cikin masu zuga Ummaah akaina. Babu yadda na iya haka na dauki hanya amma bakina banda neman agajin Allah babu abinda nakeyi nasan shi kadai yasan abinda nake going through kuma shi zai kawo min dauki. A hanya na tsaya a filling station nayi mata full tank sannan muka karasa gidan. Ina parking nayi wining glasses din sannan muka fito, tana gaba ina baya muka shiga gidan, sunada kudi haka kishiyoyinta uku kuma ita ce ta biyu amma kana shiga zaka san ragamar gidan a hannunta take ita take juya kowa har shi mijin so bana son wannan kawancen. A katon parlonta muka zauna sannan yan aikinta suka cika mana gaba da abinci kafin taxo, tana shigowa tazo ta rungumeni tana fadin
“Daughter da bata zuwa gurin mamanta ko”
Dan murmushi nayi nace
“Aiki ke hanani wallahi amma ai bazan manta Mami ba”
Zama tayi suka gaisa da Ummaah ni kam na bude exotic na tsiyaya na sha bana son tace naki cin komai. Ina nan zaune inaji suna magana kasa kasa se kuma can Mami tace min
“Asmau jeki daki ki jiramu”
Mikewa nayi na tafi dakin tareda crashing akan gadon na dauki wayata ina random searching da ban masan me nake dubawa ba, baki daya hankalina yana parlon. Har nayi waya da kyaftun ta dan dauke min kewa sannan ta kara reassuring dina sannan naji hankalina ya kwanta. Wata Nannyyy ta shigo tace min nazo inji Ummaah. Mikewa nayi na gyara zaman hijab dina sannan na fito kwatkwata idona bai ma lura da mutumin dake zaune ba seda na zauna sannan na ganshi a zaune, mutumin yafi kama da boka gaba dayanshu a birkice yake gashi fal fuskarshi yana zaune se karkada kafa yake, ga wani wari dake tashi kuma nasan tabbas daga jikinshi ne, dan lokacinda muka zo parlon banda kamshin lavender babu abinda yake, i love the scent of lavender so duk inda naji shi se matar ta fado min saboda kamshin gidanta na dindin kenan.
Abu daya da bana tolerating duk kawaici na shi ne wari bana iya jurewa, ko minti daya ban cika ba kawai se naji cikina ya fara kadawa zuciyata tana tashi, i was completely nauseous. Kallon Ummaah nayi zanyi magana kawai naga mutumin yayo kaina gadangadan, fusace na mike tare da ja da baya ina muzurai, instead ya tsaya se naga ya nannada malum malum dinshi yana neman kai hannu jikina,
“Karka taba ni, Ummaah kina kallo?”
Kamar bai ji ba haka ya dinga bina har nakai bango, idanuna na runtse bakina yana ambatar sunan Allah kawai se naji hannunshi yana shafa fuskata, wata muguwar kara na saki tareda zubewa a gurin sumammiya. Bansan me ya faru ba i don’t even know, na dai san daga baya wai ashe me maganin aljanu ne aka dakko shi saboda ana tunanin aljanu ne suka kama ni shiaysa na ki nayi aure. A gado na sameni lokacinda na farka ni kadai, koda na tashi se na fara jin kaurin tukake, tashi nayi na zauna anan naga yadda hayaki ke tashi wai duk ni akewa turare, gaba daya zuciyata tayi min nauyi, kirjina banda zafi babu abinda yakeyi. Tashi nayi zan fita naji an maida ni gadon, se lokacin na lura da Ummaah da Mami da kuma bokan dan a gurina he’s never near Allah wannan mutumin tsubbu yake. Inaji ina gani haka ya kwara min wannan ya zuban wannan, idan nayi ihu se yace aljannun ne hakan yasa kawai nayi shiru. Haka ya gama ya bada wasu layu da itatuwa da saiwoyi da wasu kulle kulle da zaa binne. ita kuma Ummaah se godiya take mishi, kuka ne ya kwace min, kukan takaici, kukan bakin ciki, kukan tausayin kaina, kukan rashin madaga, se naji duk na sare naji kamar ni rahama ta sauka daga kaina. Nafi awa ina kuka tun Ummaah na cewa aljanun ne har naga hankalinta ya fara kaiwa kaina, ganin haka yasa Mami tace nayi wanka, kaina na girgiza ina cigaba da razgar kuka abuna.
Se laasar bayan nayi sallah sannan muka tafi, fuskata tayi jawur kada ma idanuna suji labari. Koda muka tashi tafiya kasa driving nayi saboda yadda jikina ke shaking. Dole haka mami ta bada driver ya kaimu gida sannan ya juya. Dakina na shige na kulle tareda saka key na datse, banma hau gado ba anan jikin kofar na silale a baki na dinga kuka kamar raina zai fita, ban taba tunanin haka ake bakin ciki ba, nayi ta kuka har bansan iyakar lokacin dana dauka a wannan gurin kuma cikin wannan halin ba. Time to time nakan ji ana min knocking amma ko a jikina banma ni da niyyar tashi.
Ban kara fitowa ba se washegari, dake na saba dama ba fitowa nake sosae ba tunda zaman gidan ya zama tamkar a living hell hakan yasa na koma zamana kawai sede aiki ya fitar dani. Ummaah tun daren take kirana a waya amma naki dagawa saboda bansan abinda zance mata ba. Seda nayi wanka sannan na zura wata purple abaya da stones a jiki se walwali take. Comb na dakko na taje kaina na tufike da karamin ribbon sannan na shafa balm a lips dina da yayi ja, kallon fuskata nayi har lokacin bata ware sosae ba ta kumbura saboda rashin bacci da kuka. Ummaah na zaune a parlor hankalinta dukka ta tattara shi akan kofar tawa, ina fitowa idanuna ya sauka a kanta, wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, gaisheta nayi ta amsa jikinta a sanyaye ni kuma na wuce kitchen. Ina cikin dama kunu naji shigowar t, kujera ta ja ta zauna sannan tace min
“Asmau kinada hankali kuwa? Kinsan yadda kika tsoratar dani ki shiga daki ki kulle ko a jikinki? Kinsan banyi bacci ba?”
Bance mata komai ba na cigaba da abinda nake, jin nayi shiru yasa ta dawo gabana tareda daka min duka tace
“Bakya ji ne ?”
Na kyafta ido se hawaye, raina a mugun bace nace
“Ummaah me zance miki? Ya kike so nayi? Nidai nasan this wasn’t my mother, uwata ba haka take ba wani ya canja min ke.”
Sororo tayi tana kallona kafin tace
“Saboda na kaiki gurin malami shiyasa zaki fadi haka?”
Kaina na girgiza nace
“Ummaah saboda banyi aure ba shi ne kike kokarin saida imaninki, ke kanki Kinsan wannan mutumin is never near malami, kawai dai kin bi son ranki ne….”
Wani bugu ta kaiwa bakina hakan yasa nayi saurin rufe bakin, fita tayi ni kuma na zauna na dasa sabon kuka.
A fragile heart was broken before, i don’t  think it could endure another pain, a piece of voice from deep inside that calling you to make you relaxed!
Wannan kwanaki biyun dana kara sun zame min kwanakin da bazan taba mantawa a rayuwata ba, tunda nake addua i was never specific sede nace Allah ya zaba min mafi alkhairi, a ganina hakan shi ne daidai amma tunda naga an fara haka yasa na dukufa adduar Allah yasa nayi aure cikin kankanin lokaci. Ana gobe zan tafi da daddare na dawo daga gidan yaya Halifa saboda gidan babu dadi, daga ni se Asiya se ummaah and I couldn’t, i was suffocating hakan yasa na tafi tun sassafe, Inna ade da Abba sunje umra , jikokin gidan kowa yana gidansu hakan yasa naji zaman ya isheni. Mun jima nida yaya Halifa ina kora mishi bayanin halin da nake ciki. To me zaiyi shi dinma Ummaah ta haifeshi, highest thing shi ne ban hakuri kuma shi din ya bani, ya nuna min Allah yana sane dani kuma komai kaga ya faru to da saninshi. Those words kept me going.
Kwana na biyu da dawowa daga kano, na koma aiki na saboda damuwar ma batada amfani. Da yamma ina kwance a daki ba call nake ba so bayan na gama abinda zanyi na fita kasuwa nayo cefane na dawo . Ranar i was craving for dambun shinkafa. Haka na zauna na daura a cikin steamer na koma na fara soya kazar da zanyi pepper chicken da ita. Ina nan zaune na saka wani chilled chapman a gabana ina sha se naji message ping, mikewa nayi da sauri na isa ga wayar tareda tapping message din
A 40year old null para with a diagnosis of ectopic pregnancy and ? Typhoid perforation. booked for ex-lap. Prepare for emergency ex-lap ASAP.
Na karanta yafi sau shida ina kara duba number data turon da mamaki, wannan ai aikin general surgeons ne kuma ma idan ance saboda ectopic dinne I’m not on call. Mikewa nayi na kashe steamer sannan na juye abincin cikin warmer se kadan nasa a plate na saka salad da naman na fara ci. Banma kara komawa takan message din ba saboda a tunanina mistake akai. Seda na gama na gyara dakin sannan naga call din Dr halima yana shigowa, hannuna na goge jikin towel na dauka, ko gaisuwata bata amsa ba tace
“Asmau bakiga message ya shigo wayarki ba?”
“Na gani, I thought mistake ne shiyasa na share”
Cikeda damuwa tace
“This is unlike you, kije yanzun patient din tana Female surgical ward kiyi reviewing dinta”
Kaina Na gyada nace
“Amma bani bace da call bafa”
“Just follow orders kinji, nima order aka bani”
Katse call din mukai inata bubbuga kafa da zumbura baki hakanan dai na samu na dakko kayana na kullum yau pink nasa wando da riga na soft cotton yadi na saba back pack dita na fita. A ward na sameta mugun restless, ciwo yana damunta hakan yasa nayi order a mata allura kafin na kira a kawo ta: daga nan OT na wuce, na samu sun shirya kawai jurana ake hakan yasa na kira dan a kawo patient din. Ana kawo ta na dubi scrub nurse din nace
“Sister, waye zamuyi surgery din dashi?”
Dariya tayi tace
“Baki sani ba dama”
Kafin na bata amsa naji wannan deep voice din tashi, dukda sau daya na taba ji amma hakan baisa na manta da ita ba.
“Evening everyone”
Juyawa nayi da sauri tareda bashi hanya nace
“Welcome sir”
Kanshi ya gyada min sannan ya bawa mazan gurin hannu sukai musabaha ya shiga ciki yayi changing sannan muka fara. Tunda na mika masa scapel yake min tambaya akan conditions din matar, God so kind nima book worm ce so yana tambaya ina amsa shi inda gyara yana min yana kara clarifying min abubuwa. Haka mukai almost 4hours muna abu daya, se bayan maghrub muka gama aka maida ita ward mukai sallah sannan yace  a kawo masa folder yayi documenting. Ni na kai masa yace
“Sit please!”
Zama nayi kamar yadda yace, idanunshi ya maida kan folder yana going through hx matar.
“What’s your name?”
Dagowa nayi na kalleshi amma bani yake kallo ba amma nasan dani yake tunda ni dashi ne kadai cikin office din
“Asmau Shahada”
Kanshi ya gyada yace
“A ina kikai training dinki?”
Shortly nace dashi
“BUK, sir”
“Good!”
Daga haka baice komai ba se can ya mika min folder yace nayi rubutun. Zama nayi yana kallo ina rubutawa yana kara guiding dina har na dan saki jikina. Muna gamawa yace min
“You’ve done a good job. We meet some other time”
Kaina Na gyada ya fita ni kuma na koma na zauna ina maida numfashi. Tun daga lokacin shi kenan indai zaiyi aiki kowa yasan I’m his partner tun abin yana damuna har na sake na saba.
Wata Wednesday mun gama ward round, banyi breakfast ba ranar saboda kadan ya rage ban makara ba hakan yasa na tafi cafeteria dan cin abinci. Tsirarin mutane na tarar suna cin abinci, wasu sun gama, seda nayi order sannan na dawo na zaune ina jiran a kawo min. Nayi nisa sosae a cikin wayata ina chatting naji alamar an zauna gefe na. Da sauri na dago wani mutumi ne in his mid thirties ya tsareni da idonshi, the gaze was so intense hakan yasa nace
“How may i help you”
Wani murmushi ya saki yace
“Finally, na samu ganin workaholic Dr Shahada. How far?”
Bansan amsar da zan bashi ba hakan yasa nayi shiru tareda maida hankalina kan wayata, i knew him somewhere amma na rasa a ina na sanshi. Shima bai kara cemin komai ba seda aka kawo min abincin se na maida shi akan ayi packaging ba anan zanci ba. Se naji yayi dariya yace
“Doctor, ya zaki ce ayi packaging?”
Dagowa nayi na kalleshi nace
“Ka takura min”
Murmushi yayi yace
“Tun yanzun, ai abinda zuciya ke so no way ta bar abinnan”
Mikewa nayi naje counter cashier na biya sannan na fice kawai, ashe yana bayana seda nayi nisa sannan yace
“Doctor, you shunning me?”
Tsayawa nayi nace
“Idan abu kake so ina ganin wannan is not right kazo ta haka, dan Allah idan wani abunne follow the right route”
Daga haka na juya zan tafi, to my utmost amazement kawai se ya ruko hannuna cikin sauri na juyo, mamaki kamar ya kashe ni, kafin nayi yunkurin cire hannun se ji nayi ance
“Asmau!”
A tsorace na dago idanuna only to see MD a tsaye ya tsareni da idanunshi da suka kada sukai ja, sunkiyar da kaina nayi tareda kwace hannuna, tuntuni idanuna sun fara kokarin kawo ruwa. Yana isowa gurin yace
“Meet me in my office yanxunnan!”

Tamkar an daddatse min joint dina haka naji, ilahirin jikina yayi sanyi na rasa abinda yake min dadi. Lumshe idona nayi na dubi useless, unreasonable Ashole dake tsaye yana wani irin smirking, idanuna na lumshe raina a mugun bace kawai na juya na tafi. Once in a lifetime kowa yana experiencing such embarrassment, tunda nake ban taba jin kunya irin wadda naji ba. Tamkar anmin duka haka na tafi ina tunanin ta inda zan fara hada idanu dashi. Taya mutum zaiji ace mutumin dake ganin mutumcin ka ace yaga wani ya rike hannunka nasan Allah kadai zao fitar dani.1

Banyi gigin zuwa office dinshi ba saboda bansan wanne ido zan kalleshi ba kawai se na juya na tafi mota ta nayi mata key se gida, dukda hankalina yana kanshi Amma zuciyata gargadi na take akan kada fa na zake, tayi kuwa nasara haka na basar na tafi daki naci abinci sannan na kwanta, a raina ina fadin aikin ma na yau na fasa bazanyi ba.
Shikam acan a mugun fusace ya isa office dinshi, yana shiga yayi slamming kofar da karfi tareda fadawa kan cushion ya zauna, cushions ne guda hudu tsakiya center table ne me kyau covered with glass baki daya. Zama yayi ya daura kafafunshi akan table din. Wani zafi ne ke karyo masa se gumi yake ka rantse da Allah yana karkashin kwalleliyar rana ne, nan kuwa cikin niimar split yake har biyu a cikin office din. Coat dinshi ya cire ya aje gefe sannan ya sassauta necktie dinshi tareda kurawa kofar idanu yana expecting shigowar Asmau amma har awa daya ta shude babu Asmau babu alamar ta. Mikewa yayi ya fara pacing a cikin office din, me yarinyar nan take nufi dashi yace tazo sannan taki zuwa ta sameshi,  kanshi ya girgiza daidai knocking a kofar hakan yasa a sukwane yace

“Yes, come in please”

Kofar aka turo idanunshi a kafe yana jiran ganin wannan farar fuskar tata amma maimakon ganinta se yaga ashe Director Admins and finance ne, se lokacin ya tuna sunada magana dashi. Daidaita kanshi yayi cikin sauri ya koma seat dinshi tareda masa izinin zama, seda suka gaisa kafin ya bude file ya fara briefing dinshi amma rabin hankalin Dr Kwaccido baya gurin tunnainshi kodai mutumin da ya gani tareda Asmau ya gudu da ita ne? Kodai dama saurayinta ne cikin sauri ya matsar da wannan thought din a ranshi, it took him almost 2 months yana bincike a ciki da wajen asibiti akan Asmau, babu inda yaji tana da wani tsayayen magana a kanta….

“Sir, you’re not concentrating, ko mu hadu gobe?”

Kanshi ya dafe cikeda damuwa yace

“I’ll be glad, thank you”

Haka ya tattare kayan shi ya tafi shi kuma ya cigaba da jiran tsamanni amma har yaje azahar ya dawo bata zo ba, sau da dama se ya fara dialing numbers dinta da yayi storing dinsu a kwakwalwar kanshi tun ranar da Dr halima ta bashi ita amma ya kasa, baisan abinda zaice mata ba, zuciyatshi tasha gargadin shi akan wannan kallon ruwan da yake kada wankin hula ya kaishi dare. Ko kuma garin bari ya huce har ya zama rabon wasu, kanshi ya girgiza dan baya tunanin zai iya bari hakan ta faru.

Wajen laasar ya kammalla komai na ayyukan ranar, hannunshi rikeda briefcase da suit dinsa yana waya ya fito, messenger dinshi ya karba tareda kai mishi mota, godiya yayi masa sannan ya wuce cikin motar yana baza idon ganin ta inda zata bullo amma bai ganta ba haka ya tafi dik babu dadi, haka nan yaje gida. Kamar yadda ya saba ganin gidan it was so empty ya zaiyi tunda haka kaddra ta zabar masa kuma hakanan zai karbeta babu yadda zai iya. Straight bedroom dinshi ya wuce yayi wanka yayi alwala sannan ya zura jallabiya brown me gajeran hannu ya dawo parlor ya zauna. Babu jimawa yaji ana knocking wanda yasan ba kowa bae illa sabiu cook dinsa, sunyi waya yace masa ya fita dan yun wata gaisuwa. Shigowa yayi ya risina ya gaisheshi sannan ya wuce kitchen dan hada masa abinci, idanunshi ya lumshe yana bin parlon da kallo, ko ina a share yake, tiles din se kyallin mop suke amma kana kallon yadda komai Na parlon yake kasan babu mace a gidan. It’s obvious kana shiga zaka fahimci hakan, kanshi ya shafa yana jin lokaci yayi da zaiyi uncaging zuciyarshi hakanan, ya kamata ya fito daga dreadful past life dinshi ya cigaba da rayuwa, wannan zuciyar tana bukatar aboki, ya kara kallon katon parlon da hasaso gadon shi, yana bukatar living partner, he sure needs a soulmate.
STORY CONTINUES BELOW

Washegari ranar alhamis, kamar kowanne sati ita ce ranar da muke surgery ni da Dr Kwaccido. So ranar tunda nayi asuba na ko wanka banyi ba Na tafi Paediatric surgical ward, nan patient din yake. Yaron shekarashi biyar yana fama da umbilical hernia. Though condition din is a minor one amma a haka yayi mana booking. Ina zuwa anesthetist din tana zuwa, tare mukai reviewing dinshi kowa yayi documenting abinda ya samu sannan muka rabu. Gaba daya ji nake inama inada excuse din da zan bayar dan bana sam haduwa dashi kwata kwata amma ina na babu wannan, se goma na safe sannan na fito, fuskata tayi yar fayau tsabar fargaba da damuwar da nake ciki idanuna duk sun fada sunken in. Yanayi na ma kawai zaka kalla kasan akwai tambaya. Ina zuwa office na samu kan sofar dake gefe na dan kwanta ai bacci yace idan kaci bashi na se ka biya and it happen.
Bansan ashe har time ya tafi ba, se can naji ana knocking kofar office dina, ko kafin na tattara guntun karfin da ya rage na tashi, tuni kofar was flung open. Wannan kyakyawar fuskar tashi me cikeda haiba da kwarjini tasa nayi saurin tashi ina lalubar veil dina, wannan idanuna nashi that always shine me kamar an zuba musu mai cikinsu ya tsareni dasu, a take naji kamar anyimin duka, yunkurun da nake na daina se kasa da nayi da kaina ina jin an takura ni da yawa. Yana tsaye tareda harde hannyansa a kirjinshi shi bai zauna ba bai kuma nema gurin zaman ba. Kafin na kara yunkurawa naji yace

“Sleeping on duty?”

Da sauri na muskuta tareda girgiza kaina nace

“Sir, banida lafiya ne”

A take naga yanayin fuskar shi ya canja, shigowar shi tamkar wani zaki haka ya shigo ranshi a hade amma yanzun se naga damuwa ta dauke bacin ran dake ciki. Daidaita tsayiwarshi yayi cikin wata tattausar murya wadda babu wani da namiji daya taba amfani da ita wajen yimin magana yace

“Sannu, kinsha magani?”

Kaina Na girgiza nace
“I was about to, se bacci ya daukeni.”

Kanshi ya gyada se kuma ya fita, hakan yasa na sauke nannauyar ajiyar zuciya tareda lumshe idona, ni nasan banda lafiya amma a matsayina ta likita bana tunanin nasan me yake damuna, ban kuma san wanne irin taimako zan bawa kaina ba, nasan kilan tarin damuwar da nasa a zuciyata ce take neman kayar dani…..Soft knock akai jikin kofar, bakina a hankali na bude tareda bada izinin shigowa, shi dinne ya dawo sede wannan karan ya samu rakiyar head of medical department da kuma chief pharmacist. Inata kokarin mikewa ya hanani tareda bawa Dr Mansur damar ya dubani, BP na ya fara dubawa, kawai gani nayi ya cire glasses dinshi yace1

“Her BP is reading 70/40mmHg sir”

Yana fadar haka se naji tamkar an saukar da min symptoms, baice komai ba illa bina da yake da idanunshi me tuhumata akan Me ya faru? Nidai kasa kawai nayi da kaina ina jin ana min prescription sannan aka kira pharmacy suka kawo. Drip aka fara daura min yana fara shiga wani wahallalen bacci yayi gaba dani. Se can bayan wasu awoyi sannan na farka , ina office dina amma ba kamar dazun ba, ina bude idona da kyaftun na fara cin karo tana sallar laasar. Cikin sauri na yunkura inajin karfi a jikina ba Kamar dazun da nake jin jiri ba.
Toilet na shiga nayi alwala sannan nazo na zauna dan har lokacin jikina gashi nan dai, a zaunen nayi both zuhr da asr sannan na kwantar da kaina akan cushion ina lumshe idona.

“Ya jikin Twin?”

Bude idanuna nayi tareda yin kalar tausayi na dubeta har lokacin uniform ne jikinta alamu sun nuna kilan ko ward ba taje ba, ga Afeeyya ‘yar 5 months ta shimfidar da ita a yar corner se baccinta take peacefully.

“Twin Alhmdllh. Yaushe kika zo? Waye ya fada miki?”

Wani kallo tayimin wanda ta saba yimin idan gulma ta motsa, hakan yasa na cuna bakina ina dauke kai. Dariya tayi wadda tasa dole nima nayi sannan ta matso tace min

“Boss ne, da kanshi yazo har ward ya tafi dani, he left here not long ago.”

Kaina na gyada kawai ba tareda nace komai ba, dan bansan me zance din ba. Sake matsowa tayi kamar zata shige jikina hakan yasa na ture ta baya da dan guntun karfin nawa daya rage nace

“Ke munafuka ce”

Shrugging shoulders dinta tayi tace
“Oho! Baby bude baki zakiyi kimin bayani, me yake faruwa.  Kinga yadda ya rikice? Ni daya shigo ward dinmu I thought something terrible happened ashe Twin ce babu lafiya”

Hararata nayi nace

“Kede Allah ya sawwake miki, he’s none but my boss and partner aiki na”

Tsareni tayi da idanu irin she needs more, tsaki nayi nace

“Dan Allah ki bani abinci I’m starving”

Hakuri ta bani sannan ta hada min wani tea me kauri, yayi min dadi kodan ina cikin yunwa ne oho, seda na shanye tas sannan tace an tafi a kawo abinci. Bata kara min zancen ba tunda tasan da akwai wani abu da zan fada mata, tsakani na da ita babu boye boye so we still maintain the status. Tunda nayi shiru na fada tunani, anya yadda zuciyata ta adana Dr Kwaccido matsayin shugabana da kuma partner aiki? Ina tantamar hakan, duk wanda nayi aiki dashi zai nuna yaji dadi kuma zaiyi kokarin maintaining dina tun ina house job amma shi nashi salan caring din ya banbanta dana kowa. To amma someone like him…. Sallamar shi yasa nayi saurin bude idanuna, a hankali na amsa wanda iya bakina ne kawai ya motsa, muna hada ido ya sakar min wani murmushi. I swear seda tsikar jikina ta tashi, those eyes of his will definitely not allow me to live in peace sede idan kullum zan kasance ina kallonsu ne.
Gaisawa sukai da kyaftun sannan ya mika mata ledar hannunshi yace abinci nane, gefena ya dawo ya tsugunna yace

“Are you ok?”

Kaina na gyada nace
“Much better. Thank……”

Shush yayi min sannan yayimin murmushi yace

“Kici abinci zanje office”

Se na samu kaina da yi masa murmushi nace

“Allah ya bada saa”

Kanshi ya gyada ya dubi kyaftun dake rike da Afeeyya data riga ta tashi ya bata sallahun lallai naci abinci. Aikuwa yana fita ta fara tsokanata wai wallahi so na yake nidai ban kulata ba dan bazan saka abin a raina ba balle ayi back stabbing dina!

Ina kammalla cin abincin naji wani karfi yazo min, duk wannan kasalar babu ita, mikewa nayi na tattara gurin sannan nace da Kyaftun mu tafi gida dan ina son nayi wanka na canja kayan jikina. Babu musu ta tattara kayanta muka fita, bani da wani karfin da zan iya driving hakan yasa kyaftun karbar key din ita kuma Afeeyya na karbe ta, mun saba da ita sosae bata min kiwa dan wani sa’in se tayi ta kallona ni da kyaftun tana tantamar gurin wa zataje tunda kowa yasan nida mahaifiyar ta kama  muke sosae, banbanci na da kyaftun nafi ta haske ita kuma ta fini tsayi sannan ita ba a rame take ba, wadda tashin hankali da damuwa yasa na koma hakan.

Muna shiga na aje Afeeyya na shiga wanka, simple gown nasa ta wani pure cotton yard maroon, free gown ce se stones da aka mata ado dashi. Scarf milk na dakko Na daura sannan na murje jikina da turaren kullum La’eeqa da soft. Lumshe idanuna nayi na dawo na zauna inajin wani daddan yanayi a jikina. Kallon kyaftun nayi da take kokarin hada pap din Afeeyya,

“Ki kirashi kice kin dawo gida, let him not waste his time checking on you a office”

Dan bata fuska nayi tareda fadi

“Is there need for that?”

Kanta ta girgiza tana hararata tace

“Kina da matsala kinsan da hakan? How….?”

Se tayi shiru tareda daukar Afeeyya ta daura ta cinyarta ta fara feeding dinta, wayata dake gefena naji ta fara ringing hakan yasa na kai hannuna na dauka, Adda Sa’ada ce cikin sauri nayi picking dan ta rigada tasan banida lafiya, i texted her though ina tunanin se lokacin ta gani. Ina picking tace

“Fara what happened?”

Dan murmushi nayi jin muryarta duk da damuwa nace

“Ba wani abu bane kawai BP na yayi low”

Ai fa kamar famfo ta fara zuba, tana tamin fada akan tasan na takurawa kaina ne shiyasa hakan ta faru, seda ta gama fadan sannan ta dawo nasiha tana fadin

“Komai da kike gani is a matter of time, da ace tsangwama da takura kai yana sawa kayi abu, da tuni kinyi aure amma shi Allah is wonderful, he’s a perfect timer. Lokaci ne da zarar yazo zakiji it worth the wait!”

What will life be without Adda Sa’ada? Hell na ayyana a raina, bazan iya fadar abubuwan da matar tayimin a rayuwa ba amma she sticks around bata taba nuna min laifina bane da banyi aure ba, Anty Bintu, Yaya Halifa da Adda Meeyna. Banda kamar su. Ina aje wayar kyaftun ta mike tana fadin

“Kada ki zama kina manta alkhairi kuma kada ki bari a golden opportunity like this ya wuce ki. Zan tafi gida, se dare zamu dawo da Daddyn Afeeyya.”

Mikewa nayi a hankali dan bawai malaise din dake damuna ya tafi duka bane, yanzun ma jina nake kamar zan fadi dan dai ina daurewa ne. Hannunta na riko nace

“Ki fahimci abinda nake nufi, i can’t just throw myself on him kamar yadda nayi akan mukhtar (RIP) da kuma Suleiman. I was back stabbed kuma laifin waye? Nawa ne saboda ina ganin dukkan wanda yadan nuna kulawa akaina sona yake. Kina son na kara haka, repeating same mistake is nothing but foolishness”

Zaunar dani tayi dan taga alamar zan iya faduwa ta rike hannuna tace

“Ki fahimci abinda nake nufi nima, ba ina nufin you start chasing him, stalking him and stuffs. Kinsan dai ya miki abin kirki to ko thank you ne he deserves it.”

Kaina na gyada in agreement na dauki wayata and I sent him

Thank you, jiki yayi sauki. Na bar office ina gida

A gurina they were only a plain words amma a gurinshi yayi ta nanatawa saboda dukkan abinda zai fito daga gurina yana daukar abin me muhimmanci. Baiyi min reply ba har kyaftun suka kawo min abinci naci suka tafi na kulle dakin na kwanta tunanin rayuwata yayi min rubdugu, addua a bakina kan Allah yasa Ummaah ta fahimci rayuwa, ta fahimci cewar lokacin zai zo. Da wannan bacci yayi gaba dani se can cikin baccin naji vib din wayata, bansan yaushe rabon da naji an kirani past 10 so da mamaki na bude idona tareda mika hannu na cira wayar, take idanuna suka bude ganin number da take kira, Dr Kwaccido na ayyana a raina at this time, kifar da wayar nayi inajin yadda ilahirin jikina ya mutu, ina ayyana me yasa zai kirani, wata zuciyar tace just to check on you, kaina Na girgiza na ba tareda na yarda da uzurin da zuciyata ta kawo ba. Amma se na samu kaina da kasa nutsuwa, na janyo wayar na kalla 1 missed call, na danyi tsaki ina mitar har yaushe zaayiwa mutum call daya as if baa damu ba. Haka na gama yan mitocina na bude wayata ina kallon pictures dinsu Amalin Adda Habiba sunyi birthday itada Aarif last week. 

STORY CONTINUES BELOW

Washegari bayan nayi sallar asuba dake friday ce hakan yasa ban bar kan praying mat din ba har seda na karanta kahfi savoda nasan idan na bar gurin ba lallae nayi ba, ill be much occupied. Ina kammlawa na mike anan wayata ta katse min hanzari, ganin number seda zuciyata tayi fluttering, it kept jumping har hakan ya bani tsoro, but ya zanyi dole nayi picking call din saboda banda uzuri. Dauka nayi murya can kasa nace

“Good morning sir”

Manly muryar nan tashi me saka naji waves electrons cikin jikina ya amsa da fadin

“Morning Asmau”

I can swear akan ban taba jin wani ya fada Asmau so correctly kamar shi ba, kowanne harafi seda aka bashi hakkinshi, har seda naji ina bukatar nayi ta jin shi yana kiran sunan.

“Ya jikin naki?”

Dan murmushi nayi nace

“Yayi sauki, Alhmdllh”

“Alhamdulillah, zuwa karfe biyu zan wuce kano, ki zama ready zamu tafi tare”

Baki bude na tsaya ina tunanin abinda yace min, seda ya kara maimaitawa kafin nace

“Sir zan fara call gobe, so bazan samu damar zuwa ba and thank you”

“Na rigada nayi arranging yadda zaayi, ya kamata ki huta saboda ciwonki stress ne”

Se na kasa musa mishi haka mukai sallama bayan yace zai aiko min breakfast sannan nayi bacci kafin time din. Nidai na rasa tantance me hakan ke nufi na kuma kasa fahimtar inda zuciyata tasa gaba da kuma wanne tarba tayiwa alamarin. 8am na bugawa aka kawo min abincin, cikin basket aka jero shi, messenger daya kawo na bashi 500 yana ta godiya ya tafi. Chips ne cikin bowl se farfesun kayan ciki shima a bowl, tea me kauri cikin wani karamin flask. Gefe leda ce a aje na bude tareda ciro abinda ke ciki, rose flower ce hade da greeting card, mamaki sosae ya kamani na bude greeting card din naga na get well soon ne, a kasa yayi rubutu cikin rubutun da ban taba kawowa ya iya ba kasancewar kowa yasan handwritings din Doctors bashida kyau amma yadda yayi rubutun kamar calligraphy lettering style yayi amfani dashi.1

Come on, get back on your feet and continue that gorgeous smile of yours. Quick Shifaaa Cara Mia!

Shine abinda ya rubuta, zuciyata nasan dama is froze, dan tunda Salis ya betraying feelings dina shikenna na daskarar da ita, ga mamakina wannan kalaman nashi take suka raga raga da wannan kankarar, wani bugu da zuciyata ta shiga yi har seda nayi tsoron kada a samu over extension. Jikina yayi sanyi na kalla rose 🌹 din na shafa na shinshina a karshe na rungume ta a kirjina ina adduar Allah yasa daga shi ne. Greeting card na dauka na kara nanata rubutun ina bin kowacce kalma daki daki, komai na fahimta banda wannan cara mia din kuma babu me amsa min. Abinci kadan naci sega kyaftun tayi ta ihu tana murna tana fadin

“Yarinya kin saka yan maza a gaba fa, kinyi kamun full package”

Se na samu kaina da fara yarda da zancenta, kodai so na yake, ko dai……haka nayi ta tunanin kafin can bacci ya daukeni se wajen 12pm na tashi nayi wanka na hada kayan dazan bukata sannnan na yi sallah na karasa abincin da na rage na wanke na kife kafin na fara neman kaya. Ni dama ba maabociyar kwalliyya bace dan powder ma se kayi da gaske nake siya hakan yasa na zizara khol tareda shafa charpet kan tattausan lebena da ya fara bushewa har fata na neman dagowa. Dana kalla madubi se naga nayi kyau daidai yadda ya kamata. Wani lace na dakko me laushin gaske irin vapers dinnan ne. Background din Coffee ne se designs din suka tashi milk da zaren gold a jiki. Skirt da riga ne nasa na daura dankwali tareda dakko matching veil da takalmi, har na manta last dana nutsu nayi shigar arxiki. 1:50 daidai wayar shi ta shigo akan yana jirana, kara gyara zaman veil dina nayi sannan na dauki abinda zan dauka na fita. Yana tsaye gefen motar yayi shigar da ban taba gani ba, yana cikin farar shadda ta zarce ayi masa coffee aiki, kanshi sanye da zannan bukar yayi kyau very charming. Dake quarters din namu babu mutane yawancin an tattafi weekend masu aiki nayi yasa yake tsaye shi daya. Back seat nasa kayan sannan na shiga gefenshi danshi tunda na kusa karasowa ya koma ciki ya tashi motar. Tunda Na gaisheshi ya amsa ban kara ko tari ba haka shima se gudunshi da yakeyi, seda mukaje wudil ne ya tsaya karbar document ni kuma na samu saken kiran kyaftun na mata sallama. Yana dawowa ya kalleni tareda fadin

“You look disturbed, akwai abinda zan taimaka miki dashi?”

Cikin sauri na karkada kai alamar aa tareda lumshe idanuna ina shakar kamshin turarena nashi da kuma car freshner da ya saka, ga sanyin AC. Yanayin was so romantic. A hankali naji waka ta fara fita cikin speakers din, hannunsa yasa yayi increasing volume din tareda fadin

“Shirin yayi yawa, enjoy please”

🎶I’ve been looking for you everywhere, I’ve been asking god when I’ll found you dear? I know some times last days where you least expect. But I’ll be patient i go wait, wait for you my dear. wherever you are, you have my heart, my darling take me yes I’m. I’ll be loving you from now till i found you my love. I hope say you like me d way i be, i go dey wait for you day and night dear future wife. 🎵

🎤When I need you will you be there my dear? I’ll make silly mistakes please forgive me dear, we have a long a way to waka, hold my hands my dear. Wherever you are you have my heart my darling, I’ll wait for you day and night dear future wife.🎷

1

Tamkar kada wakar ta kare haka naji, idanuna na bude tareda kallon sadhin shi, murmushi ne kwance a fuskarshi wanda tsabar yadda ya kayatar dashi haka na bude baki, hanci ina kallonshi:

“Nayi kyau ne?”

Da sauri na janye idanuna daga kanshi inajin wata kunya ta rufenj kamar na tsaga kasa ta rufe dani.

Har kofar gate din gidanmu ya kaini, babu kowa a kofar gidan dama Abba nake tunanin zan samu kasancewar friday ce mostly da yammaci yakan fito da kujera ya zauna yana reading papers. Amma yau se babu kowa hakan yayi min dadi. Yana gama parking na kalleshi nace+

“Thank you so much sir, a gaida mutanen gidan”

Wani kallo yayimin wanda yafi kama da harara yace

“Shi bakinnan godiya kadai ya iya yi ne?”

Murmushi nayi tareda sunkiyar da kaina amma bance komai ba, shima murmushin yayi me sauti tareda fadin

“Monday very early zanzo mu tafi”

Babu amfanin musu dan Na lura baya son hakan, se kawai na gyada kaina kurum, daga nan na bude kofar na kara masa godiya nayi cikin gida inajin intense gaze dinshi a kaina da har suka so harde ni. Tundaga parlor na san tabbas yau munada baki dan kuwa ga hayaniyar yara nan, da sallama na shiga inajin yadda kaina ya sara, aikuwa yaran dukkansu suka yo kaina suna ihun murnar ganina, dan da yawansu na jima ban gansu ba. Dukda yadda nake ji haka na daure kowanne na bashi peck a kumatu kafin kuma aka karba kayana aka kaimin daki, ni kuma na wuce parlon Ummaah dan Na tabbatar itada ‘ya’yanta masu aure suna can. Ile kuwa dukkansu suna zaune banda Yaya Halifa.

Kowannensu ya amsa sallama ta tareda bina da kallo, wasu na mamakin ramar da nayi wasu kuma duhun da fata ta tayi. Gaba daya yadda kukasan an tsotse ni haka na koma wata yar fiyat dani. Gefen Ummaah Na zauna daga kan carpet a dadare nace

“Ummaah barka da gida”

Kaina ta shafa cikin kulawar da aka jima baa bani ba, baa nuna min irinta ba tace

“Yar fara kina kallon kanki a madubi kuwa? Kinga yadda kike rama kamar wata me AIDS”

Kaina na sunkuyar hawaye taf idanuna nace

“Bana jin dadi ne shiyasa na dawo nadan huta”

Dukkansu suka fara min sannu wannan ya rungumo ni tanan har seda hawayen da nake rikewa ya sakko kan kuncina, i can’t remember last time da naga haka.

“Ya A’isha da halima da me gidan?”

Kyaftun take nufi da Afeeyya hakan yasa nace tanan tana gaishesu. Lokaci guda na ware anata hira dani muna kyalkyala dariya, naji wani sanyi cikin zuciyata hade da nutsuwa tareda fatan Allah yasa hakan ta daure na cigaba da ganin hakan. Bayan laasar naci abincin da khairiyya ta kawo min sega Yaya Halifa da Abba nan fa aka fara hira, a tsokani wannan a tskokani wancan se bayan sallar isha kowa ya hada kan iyalanshi suka wuce and i was left in my room all alone counting the numbers of boards that made up the ceiling. Na jima bacci bai daukeni ba inata tunanin rayuwa da yadda take juyawa da makomar rayuwata. Firgigit nayi da tuna ban kira bawan Allah daya kawo ni naji yadda yake ba, ba tareda wani tunani ba na janyo wayata na fara dialing tashi, tana shiga na kwakwalwata ta ankare da abinda nake ta tsayar dani se kawai na kashe wayar ina bubbuga kaina da jin haushin dalilin da zaisa na kirashi. Inata tura baki na tashi na tafi dakin Inna amma na samu tuni tayi bacci. Ina dawowa na tarar da wayar tana ringing and it was him calling, haka nan na karasa jiki a sanyaye na dauki wayar tareda karawa a kunnena nace

“Barka da dare Sir”

“Barka dai Asmau. Ya saukin jikin?”

Se dana kalla kaina kafin na amsa masa da sauki se kuma mukai shiru dan nidai bansan me zance msa ba kuma baya son godiya. Hakan yasa nayi shiru. Se can yace

“Kiyi bacci and ki tabbatar kinci abinci”

Kamar wata doluwa haka na shiga gyada kaina in agreement amma sede bama gani na yake ba balle, seda yace

“Huh! Asmau?”

Sannan nace

“Inshaaa Allah Sir”

STORY CONTINUES BELOW

Daga haka mukai hanging, wani irin raruma nayiwa wayar taredq rungume ta a kirjina inajin wani farin ciki marar misaltuwa. Murmushi kuwan from ear to ear kamar bakina zai yage. Can kuma na kashe wutar tareda yin addua na kara lula duniyar tunani a haka daddan bacci ya daukeni, it was peaceful dan ko mafarkan da nayi where of love. Dan haka da asuba dana tashi komai lafiya lau jikina ba wannan rashin kuzarin se ma wani karfi da nake ji. Hakan ya bani mamaki amma a kasan zuciyata nasan menene nasan dalili. Ina idar da sallah na janyo babban quran dina na fara tilawa a kalla nayi izu daya kafin nayi azkhar lokacin tuni gari ya waye hakan yasa na gyara dakina na shiga wanka. Ina fitowa na zura wata morning gown ta wani silk purple yadi. Kaina na zura hula sannan na tafi kitchen.

Na jima tsaye a jikin working surface ina karewa kitchen din kallo wanda a zahiri kenan amma a badini ina tuannin bidirin da aka sha a kitchen din, tun daga Yaya mukhtar down to Yaya Suleiman. Kowannensu it started at this very place. Ajiyar zuciya me nauyi na sauke ina kara kallon guraren tareda saka hannuna ina tattabawa wasu nayi murmushi a haka na kashe time din da bansan iya adadinshi ba. Se can dana fara jin motsin yan gidan sun tashi sannan na dukufa fara aiki. Na kusa gamawa Mama da Asiya suka zo muka karasa na wuce na gaida Inna sannan Abba da Ummaah. Muna kammalla breakfast na koma daki na dudduba wasu soft copy pages da aka turon akan Breast cancer da Cervical cancer. Ban wani dauki time ba na gama na janyo system dita na fara aikin da na saba wato kallon korean movies, wani Love In The Moonlight.

Gaba daya na sakankance ina kallona naji an turo kofar dakin, normally mun saba indai zaka shiga dakin koma waye seka yi knocking da sallama kafin ka shiga. Hakan yasa na dago da sauri tareda pausing film din, mamaki sosae ya kamani ganin  Nadia, its been long da naga kafafunta a cikin gidanmu kuma dakina. Mikewa nayi ina sakin murmushi nace

“Nads manyan mata, sannu da zuwa”

“Yawwa!”

Kawai tace min se ban wani damu ba tazo ta zauna nace

“Bari a kawo ruwa, yau akwai hirar yaushe gamo kenan”

Na fada ina kokarin tashi daga gefenta, hannunta tasa ta rike nawa, hakan yasa nayi saurin kallonta kafin nayi magana tayi beating dina to it tace

“Bashi ya kawo ni ba. Kina kallon yanayi na kinsan ba ruwa nazo sha ba. Gargadi nazo nayi miki, mijina Suleiman nawa ne ni daya kinganshi yafi karfin wadda tayi kwantai ta gama aiki cikin kartin maza irinki. Saboda kin kasa auruwa you decided kizo kimin snatching miji? Kul dinki!”2

I was dazed, confused and amazed! Tunda ta fara magana nake kallonta da tsananin mamaki wanda ya kasa boyuwa ya fit baro baro akan fuskata. Tana gama fada ta hankadar da hannuna ta mike da niyyar fita, nasa hannuna na riketa ina kallon idanunta wanda na rasa meye a cikinsu amma nawa firgici ne a cikinsu

“Ta yaya zaki fita baki fahimtar dani abunda maganar ki take nufi ba, Nadia ni ce fa”

Hannunta ta kwace kamar wata damisa, cikin daga murya tace

“Se me dan kece? Ai nasan ke dince shiyasa na sassauta miki, tunda bakiji kunyar kawancenmu kin kai idanunki kan mijina ba bazanji kunyar na miki gargadi ba. Me mijina zaiyi dake tsofe tsofe dake…..”

Ban barta ta karasa ba na wanka mata mari ina wani irin huci, i was boiling in,

“Kada ki kuskura Nadia…..”

Se na dunkule hannuna na kasa karasawa, zuciyata na fada min Nadia ce fa, wannan dinnan, kin manta ta? She doesn’t deserve this. Bana tunanin akwai circumstance da zai zo na manta matsayin rayhana da Nadia a rayuwata, sudai zasu iya mantua amma ni nasan alheri bana mantawa dashi. Ai tana ganin nayi shiru ta fara zage zage wanda ya janyo hankalin Inna da Ummaah dasu Mama, su basu san ta shigo bama dan kowanne na dakinsu. Ummaah tazo tana fadin

STORY CONTINUES BELOW

“Nadia me ya faru? Me ya hadaku?”

Wani mugun kallo tayiwa Ummaah tace

“Ki fada mata ta fita harkar mijina, mijina yafi karfin ta shi ba tsaranta bane, idan ba haka ba……”

Gaba daya har Inna muka tsaya muna kallonta da tsananin mamaki, kuma shirun da mukai mata baisa tayi shiru ba sema kara daga mirya da takeyi a haka Abba ya fito ya samemu a tsatsaye, Nadia tana ta wulakanci ita me miji. Kallonta yayi yace

“Kiyi hakuri ki koma dakinki, ni na miki alkawarin Asmau bazata taba auren mijinki ba, itama nata yana nan tafe da izinin Allah”

Kawai tana bude bakinta se cewa tayi

“Better!”

Ta juya ta fice, tana fita naji wani irin yanayi me wiyar na fada ya lullubeni, kaina kamar zai tsage gida biyu, idanuna da suke neman lumshewa na bude da karfin gaske nace

“Abba me ya faru”

Ashe yaya Suleiman ya samu Ummaah akan yana sona zai aureni tace masa aa kar ya manta abinda ke tsakanina da matar shi, bai jiba ya samu Inna ita kuwa kowa yasan yana daya daga cikin favorite jikokinta hakan yasa tayi naam da maganar. Kallon Inna nayi kamar zan daketa idanuna se hawaye ke zubowa, gaba daya na manta Inna bata jin turanci nace

“For goodness sake, Inna why will you do this? Danme? Kinsa yarinya yar cikinku tazo tayi muku fitsara. Saboda banyi aure ba, kun taba ganin macen da takai age dina bata damu tayi aure ba, in bai zo ba zan fita titi nayi shelar wa yake sona? Waye zai aureni…!”

Wani abu naji ya tokaren makoshi hakan yasa na juya dan tafiya daki amma wani mugun jiri ya kwashe ni se gani a kasa, dukkansu suka yo kaina dan tashina amma na mike seda Abba ya rikeni aka kaini har daki daidai shigowar yaya Suleiman a birkice, Abba yace baya son yaji komai kawai yazo ya dubani. Yana dubani ya daura min drip se na lumshe idona kamar me bacci hakan yasa suka fita dan na samu na dan huta amma maimakon na mutsu se kawai na tashi na hada kaina da gwiwa na dinga kuka, a raina ina ayyana yadda rayuwa ta juya, ni Nadia tazo har guda ta ciwa mutunci akan mijinta? Su Ummaah basu tsira ba. Asiya ce ta shigo ta sameni a hakan ta zauna tana ta lallashina har nayi shiru sannan ta dauki wayata dan nace duk wanda ya kira tace banda lafiya.

Misalin karfe bakwai na dare nayi sallar maghrib, na dan nutsu ba kamar da safen ba shima Abba da Ummaah suka zo sukai ta lallashina tareda nuna min haka rayuwar take, we must expect worst from life, it’s a trial which are never meant to be easy. Wannan ya karfafa min gwiwa har nasha tea sannan nayi wanka amma idanuna kadai zaka kalla kasan kodai ina cikin damuwa ko banda lafiya.

“Yar fara tashi maza maza ki canja kaya kizo parlor kinyi baki”

“Baki?”

Na maimaita ina kallon Ummaah data bude wardrobe dina da alamun kaya take nemo min kaya, mikewa nayi jin bata bani amsa ba nace

“Ummaah su waye?”

Juyowa tayi tana kallona kafin tace

“MD dinku ne”

Idanu na zaro cikeda mamakin abinda ya kawoshi, taba ni Ummaah tayi tace

“Tun dazun sukazo so kiyi sauri kisa wani abin kizo”

Idanuna Na lumshe ina jin wani mintsini da ale min a cikin zuciyata na farin ciki, kallon kayana nayi ba tareda daukar ko daya ba na rufe na nufi inda Abayas dina suke na samo wata simple royal blue abaya wadda egde dinta aka mata ado da wani silk blue material yayi kyau. Mayafin na yafa bayan na wanke fuskata na fito parlor Amma maimakon na ganshi se wata yar karamar yarinya wadda shekarunta bazasu wuce shekara biyar ba, sanye take da jeans se top an saka mata hula kalar top din. Wasa take da throw pillow din kan cushion din da take kai, gefenta wata middle aged mata ce tana zaune da waya a hannunta amma kamar da suke da wannan yarinyar ta baci. Hakan yasa naji hankalina ya kwanta daga tantamar da zuciyata take. A hankali na karasa inda matar take Na tsugunna a gefenta nace

“Barka da zuwa, ina yini?”

Da sauri ta dagani Na zauna gefenta tana ta murmushi kamar bakinta zai yage tace

“Mashaaa Allah, Alhamdulillah! Barka dai Asmau ya jikin naki?”

A kunyace nace

“Alhamdulillah!”

Dan yadda idanunta ke sparkling daga gani na kamar irin abinda kake jira dinnan shekara da shelaru ne yazo.”

“Yayi kyau, Raudha bakiga Anty ba, zo ki gaisheta”

Yarinyar tazo tayi hugging dina ta gaisheni , ina murmushi na zaunar da ita kaina naace

“Raudha”

Kallon Maman ta tayi tace

“Amiey, wannan ce Matar uncle Abbas din?”

Da sauri na kalli yarinyar dake shafa fuskata sannan na kalli uwar dake kallona with love a idanunta tace

“Inshaaa Allah”

Kunya ta kamani sosae, zuciyata wani irin bugawa take na kasa tantance a wanne yanayi nake ciki farin ciki ne ko mamaki. Kafin ta kara magana Ummaah da mama suka zo dauke da abinci akan tray, sannan ta zauna suka gaisa inajin tana fada mata su asalinsu iyayensu yan sokoto ne amma dukkansu a hadejia aka haifesu ta jigawa hakan yasa suke indigene tunda sun samu by birth. Nidai hankalina yana kan Raudha da nake feeding tana ta bani labarin Uncle Abbas. Can sega Abba ya shigo, har kasa Maman Raudha ta tsugunna ta gaisheshi ya kirani parlonshi. Tunda nasa kaina nasan Dr Kwaccido na ciki saboda kamshin turaraenshi daya baibaye ko ina Na parlon. Abba fita yayi so daga ni se shi se Raudha data biyoni tana ta tsalle tsallenta.

Cikeda damuwa yace

“Me yake damunki ne kin kalle ki kuwa? Nasa ki taho gida ki huta amma you are still falling sick. Y kike so nayi ne?”

Da sauri na dago kaina ina kallonshi, ya dage girarshi yace

“I care of course! My heart flutters whenever I see you or i remember you. Can you do me the favor of marrying a bachelor like me?”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page