K’ADDARA CE CHAPTER 6

 K’ADDARA CE CHAPTER 6

Kujera tajawo wadda take opposite d’insa tazauna sannan tace yaya fahad ina kwana.

Ba tare da ya d’ago ya kalleta ba ya amsa mata.

Salma bataji dad’in hakan da yayi mataba ammah sai ta danne abun a ranta.+

Kowa shuru yayi aka cigaba da breakfast, salma sai satar kallon fahad take ta gefen idonta ammah ko da sau d’aya bai kallo inda taketa dole ta hak’ura tadaina kallonsa cikin ranta tace wannan mutumin ya cika miskilaci da yawa.

Fahad ne yafara tashi mummy tace ya dae ba dai har ka k’oshiba.

Murmushi yayi yace mummy wlh na k’oshi.

Bari inje gidansu mubarak yana jirana bai ma je wajen aiki ba jin na ce zan je gidan.

Mummy tace Allah sarki mubarak yaron kirki wlh ko da bakanan yana yawan zuwa ya gaishema.

Murmushi yayi yace ai daman mubarak haka yake akwai kirki bari inwuce mummy.

Ohk sai ka dawo kagaishe da mutanen gidan.

Toh zasuji mummy.

Fatima tace yaya fahad sai ka dawo, Toh my lil sis.

Salma ahankali tace yaya fahad adawo lafiya.

Batare da ya kalli inda takeba yace Allah yasa.

Bata ji dad’in yadda ya amsa mataba ammah babu yadda ta iya.

Bayan sun gama breakfast d’akinta takoma tafad’a saman gado duk takaici ya isheta tace wai wannan wane kalar mutum ne duk abinda nake saboda shi ammah ko kallona baiyiba bare yakula da hakan.

Tashi zaune tayi tace in ka san wata ai baka san wata ba yaya fahad muhad’u a karo na biyu.

wani wanka tacanza ganin tym d’in lunch ya kusa yasa tadawo parlour tazauna tana jiran dawowarsa ammah shuru.

Ahaka har suka fara lunch babu shi babu dalilinsa,

Ta ji haushin rashin dawowarsa ko da tagama bata koma room d’inta ba parlour tayi zamanta tana ta danna waya domin tanason ganin shigowarsa.

Sai wajen k’arfe biyar yadawo d’akinsa yawuce yayi wanka yashirya sannan yafito yanufi main parlour da sallama yashiga.

Salma da take kwance saman 3 setter dasauri tatashi zaune, kashe murya tayi tace sannu da dawowa yaya fahad

Kallo d’aya yayi mata yace yauwa mummy tana samane?

Eh tana chan.

Wucewa yayi tanufi d’akin mummy.

Ganin haka yasa salma tatashi tahad’o mashi abincinsa tanufi d’akin mummy tana murna.

Da sallama tashiga duk suka amsa mata.

Inda yake zaune tanufa ta aje kayan abincin a gabansa tace yaya fahad ga lunch d’inka.

STORY CONTINUES BELOW

Ta6e baki yayi yace bance miki ina jin yunwa ba ai koma dashi. 

Harararsa mummy tayi tace kaidai fahad wani lokacin bakada kirki daga ta taimaka maka sai kakushe ta.

Sorry mummy ba haka bane ke aje abincin kitafi.

Ajewa tayi tajuya tafita daga d’akin tana murna ko dai ba komai ya dai kalleta.

Haka suka cigaba da tafiya salma tana shisshige masa duk abinda taga zai burgesa shi takeyi ko da bakulata yakeba itadai bata damuwa da yadda yake mata,

shi kuma  duk haushinta yakeji ganin yadda take mashi rawar kai saisa yake yawan kushe abu indai ita tayi masa.

A haka har yayi kwanakinsa ukku yatattara yakoma india.

Salma ta sha kuka saboda bak’in cikin rashin samun nasara akansa,  a ranar saida ‘yan gidan suka rasa gane kanta sunyi tambayar duniya ammah saidai tace masu kanta yake ciwo dole suka hak’ura suka k’yaleta.

****    ****    ****   ****

Bayan sun tafi Amina tadawo tacigaba da hidimarta ita dai hajiya batayi mata maganar ba.

K’arfe tara kamar kullum suka kulle restaurant d’in kowa yakoma masaukinsa domin yahuta.

Washe gari tunda suka gama hidimarsu suka shirya sukayi breakfast d’akin hajiya suka je suka mik’a gaisuwa bayan sun gama gaisawa suka tashi zasu tafi.

Gyaran murya hajiya tayi tace Amina kizauna ina son ganinki.

Komawa tayi tazauna tana addu’a a ranta Allah yasa ba wani abu tayiba.

Kallonta Hajiya tayi tana murmushi tace na san kina mamakin kiran nan da nayi miki ko?

Toh bakomai bane magana ce nikeso muyi.

Numfashi Amina taja, murya chan k’asa tace toh hajiya.

Yauwa Amina daman maganar wani bawan Allah ne jiya da yatareni da maganar cewa yana sonki

Gaban Amina yafad’i dasauri tad’ago kai takalli hajiya tace ni kuma hajiya?

Ke mana Amina inba ke ba toh wa nake nufi.

Mutumin yana da kirki sosai kuma yana da kyaun hali,

Ya ce min ya yi miki magana ammah baki basu had’in kai ba shine suka biyo ta wajena ko ba haka bane?

Amina tana jin haka tagane ko su wanene hajiya take magana a kansu, 

Eh hajiya hakane.

Yauwa, wlh kin kyauta da baki kar6esu lokaci guda ba batare da ansan halinsuba.

Alhamdullillah gaskiya mutanen kirki ne kuma kinga yana da kud’i idan kika auresa za ki huta kema,  nasan zaki so Inda zaki huta kiji dad’i, ya kika gani ne?

Shuru tayi gabanta sai fad’uwa yake cikin ranta tace shikenan asirina yana shirin tonuwa kenan.  

Muryar hajiya ce takatseta tace kinyi shuru Amina bakice komai ba.

Cikin fargaba tace hajiya ina fa da yarinya kuma…

Hajiya takatsemata magana tace kar kidamu da maganar yarinyarki wannan ba matsala bane inma kina tunanin mijinki da yarasu kiyi hak’uri daman haka rayuwartake duk mai rai ai mamacine ya kamata kishiga wata sabuwar rayuwa.

Hawaye ne suka zubo daga idanuwanta domin ita har ga Allah ba ta son mutumin tace hajiya abani lokaci zanyi tunani.

Tunani kuma Amina?  Na d’auka za ki amince ko saboda jin yanayin mutumin nidai ina duba miki inda zakije kihuta.

Amina bataji dad’in maganar hajiya ba cikin ranta tace ta d’auka ni kwad’ayayyace ni da ace baban Ameerah za a bani ko da babu cin yau bare na gobe toh zan iya zama dashi.

Hajiya takatse mata tunani tace kije dai kiyi tunani duk abinda kika yanke zuwa gobe sai ki fad’a min ammah gaskiya kiyi tunanin da zai fisheki.

Kanta a k’asa tace toh hajiya nagode ahuta lafiya,  tashi tayi tafita daga d’akin.

Restaurant takoma sukacigaba da hidimarsu,

Ga abubuwa da dama sai damunta suke daurewa kawai take a ranar, sauk’inta ma Ameerah hannun baba salame take.

Yanayinta kawai zaka kalla kagane bata cikin walwalah duk tambayar da su baba salame sukayi mata dan jin damuwarta bata fad’a masuba saidai tace kanta ne yake ciwo.

Da daddare ko da takwanta juyi kawai take ta kasa bacci tunani take amsar da zataba hajiya gobe domin ita gaskiya bata shirya aureba a wannan lokacin k’arshe dai tayanke shawarar zata fad’a ma hajiya gaskiya.

Washe gari Aminace zaune a d’akin hajiya bayan sun gaisa hajiya tace dafatan dai kinyi tunani me kike ganin ya dace ayi.

Hajiya gaskiya ni yanzu ban shirya aureba kuma ni da banda komai ya za ayi inyi aure.

Kar kidamu zaki samu komai babu abinda ba za mu kaimaki ba, fatana dai ki amince.

Shuru tayi takasa cewa komai,

Hajiya ganin kamar ba za ayi nasaraba yasa tace kije zasuzo yau kikula su Amina dan Allah banda wulak’anci ko da na san ba halinki bane kar kidamu ahankali za ki ji sonsa ya shigeki.

Nan cikin gida zasu shigo bayan azahar kafin lokacin sai kishirya.

Toh hajiya na gode, tashi tayi tafice daga d’akin ranta a 6ace.

Har lokacin zuwansu yakusa ammah bata shiryaba saida hajiya tayi mata magana sannan tabar restaurant ranta a 6ace taje tayi wanka tashirya ammah batayi wata kwalliya ba, wani tunani tayi sai kawai tayi murmushi tace zan samu mafita

Tana d’akinta hajiya talek’o jikinta sai 6ari yake tace Amina kifito gasunan sunzo suna d’akina,  ammah dan Allah kid’an shafa ko da powder ce, kiyi mana godia wlh sun cikamu da kayan arzik’i bakiga kayan abincin da suka kawo manaba gaskiya mun taki sa’a.

Murmushi Amina tayi wanda yafi kuka ciwo tace toh Hajiya, powder tashafa tatashi tanufi d’akin hajiya tana murmushi

sallama tayi suka amsa mata suna zaune bisa kujera duk ancika masu gabansu da kayan abinci,

Ta6e baki tayi tazauna bisa kujerar da take opposite d’insu.

Tunda tashigo yatsareta da idanuwansa yana jin sonta yana k’ara shigarsa.

Cikin sakin fuska tagaishesu,

Sunyi mamakin yadda yau tazo tana fara’a sukayi tunanin ko dan sunga kud’i ne.

Alh Abdul yace Amina dafatan munsameki lfy, batare da dogon zanceba na san dai kinsan abinda yake tafe damu hajiya ta yi miki bayani,

Murmushi tayi tace na san komai saidai wani hanzari ba gudu ba bansaniba ko abokin naka zai iya xama da karuwa wadda tahaifi d’iya da cikin shege.

Su dukansu kallonta suke mamaki k’arara a fuskarsu,  Alh faruk yace Amina kinsan abinda kike fad’a kuwa?  Hajiya fa ta yi mana bayanin cewa kin ta6a aure mijinki ne yarasu ya barki da yarinya ‘yar 6 months meyasa kike son 6atama kanki suna ne?

Murmushi tayi a karo na biyu tace ni ban ta6a aure ba d’iyata ba da aure na haifetaba a yawon karuwanci nayo cikinta. ………

A yawon karuwanci nayo cikinta nima kaina bansan ainahin wanene mahaifin Ameerah ba,

idan har za ka iya aurena a haka toh bismillah sanin cewa a neman aure ba a son 6oye-6oye saisa nafad’a maku gaskiya domin kar sai nan gaba kagano.

Ya kake gani game da hakan shin za ka aureni?

Alh faruk tunda tafara maganar kallonta yake hankalinsa a tashe wani irin haushi da kishinta yaji a zuciyarsa,  cikin ransa yace lallai na d’auko ma kaina babban aiki da har nabari zuciyata tafad’a tarkon son karuwa,

Toh waima yanzu ya zanyi da sonta da sha’awarta da suke d’awainiya da ni? 

Toh ko dai AUREN SHA’AWA zanyi (na maman ilham) in yaso daga baya sai in saketa dan ba zan iya zama da karuwa ba nida nakeda mata kamila nitsattsa a gida,  ko kuma ba sai na aureta inmaidata karuwata…..

Dafasa da yaji anyi shi yasa yadawo daga duniyar tunanin da yake. 

Alh Abdul yace ya dai ka yi shuru bakace komai ba,

Numfashi yaja yajuyo yakalli Amina da tatsareshi da idanuwanta tana jiran jin amsar da zai bata.

Murmushi tayi tace bari inbaku waje kuyi shawara kuyi shawara duk yadda kuka yanke sai ku sanar dani,

Tashi tayi har ta juya za ta tafi sai kuma tajuyo tace am kufa ci abinci please,  sannan tawuce tayi tafiyarta.

Numfashi yaja yace toh Alh faruk ya za’ayi?  Kananan kan bakarta na aurenta ko ko zaka fasa?

Hmm Alh Abdul ya za’ayi in auri karuwa nida nakeda kamilar mata a gida nifa daman ba wani sonta nakeba sosai kawai sha’awarta ce take d’awainiya da ni ko da na aureta na san auren sha’awa zanyi ba na soyayya ba ya kake ganin za ayi?

kabani shawara please

Shuru Alh Abdul yayi na d’an lokaci yana tunani  sannan yayi murmushi yace yauwa ga shawara,

Mai zai hana tunda daman karuwa ce kaga sai kabiyata kud’i kabiya buk’atarka da ita inyaso daga baya sai ka rabu da ita tunda kaga saboda kud’in take karuwanci kaima fa ba bayaba wajen neman mata,  inma bata yaddaba sai ka yaudareta da sunan za ka aureta idan komai ya kankama sai kawai karabu da ita kamar yadda nike ma wasu matan.

Murmushin Jin dad’i Alh faruk yayi har saida hak’oransa suka bayyana yace lallai abokina ka iya bada shawara haka kawai za ayi ka san inganma shan mangwaro yadda k’wallon ake domin ahuta da k’uda.

Dariya sukayi gaba d’ayansu sannan suka zuba abinci sukaci.

Tunda tafita daga d’akin,  d’akinta takoma takwanta saman katifa zuciyarta tana mata zafi hawayen da take dannewa ne suka zubo mata tace yanzu shikenan na 6ata ma kaina suna yanzu kowa kallon karuwa zai dinga yi mani,

Meyasa na aikata hakan?   Meyasa na shegantar da d’iyata alhali da ubanta?

Girgiza kai tayi tace aganina hakan shine mafita agareni?

Toh kuma idan yace yana sona a hakan fa?

Dak’arfi tace No! ba zan ta6a yadda in auri wanda ban so ba, kuka tayi sosai har saida taji sanyi a ranta sannan tatashi taje tawanke fuskarta tashafa powder,

“Dakin takoma lokacin har sun gama cin abinci.

Da sallama tashiga tana fara’a kamar ba abinda yake damunta,  zama tayi bisa kujerar da tatashi tana murmushi tace dafatan kungama shawarar ya ake cikine?

Alh Abdul yayi murmushi yace eh mungama bari inbaku waje sai kuyi magana ina jiranka a waje inkungama.

Alh faruk yakalleta yayi murmushi yace Amina ina sonki a haka.

Gabantane yafad’i jin amsar da yabata,  fara’ar da take fuskarta takoma damuwa k’arara,  kallonsa tayi tace saboda mi ba zaka hak’ura da ni ba alhali na ce maka ni karuwa ce? Kuma ni har yanzu cikin karuwancin nake ban shirya aureba domin ko na yi auren toh ba zan fasa sana’a ta ba.

Murmushin jin dad’in maganarta yayi yace yauwa ta kwana gidan sauk’i nima kinga sai kimaida ni customer d’inki idan kud’i kike buk’ata zaki samu masu tsoka daga wajena domin zaki warke daga talauci.

Harara tawurga mashi tace a harkata ba kowane kalar mutum bane nakeba jikina ba,  komai kud’insa idan bai minba toh ba ya samun had’in kai na.

Kallonta yayi cikin mamaki yace kar kidamu ahankali zan koya miki yadda zaki amince da ni baby,

Tasowa yayi daga inda yake zaune yadawo kusa da ita yaxauna daf da ita yamik’a hannu zai ta6ata.

Dasauri tamik’e tsaye gabanta yana fad’uwa tace kar kasaki kata6ani.

Mamaki k’arara a fuskar Alh faruk yace haba baby minene abun tada hankali kefa ‘yar hannuce.

Ajiyar zuciya tayi ganin asirinta yana shirin tonuwa tace eh na san da hakan hakawai ba kowa nakeso yana ta6ani ba.

Murmushi yayi yace gaskiya baby tsarinki yana burgeni,  kar kidamu indai kika amince min toh zakiji dad’in kasancewa da ni.

Kije kiyi shawara idan kin amince toh,  cikin aljihunsa yasa hannu  yad’auko wani k’aramin card tare da bandir d’in kud’i ya aje gabanta yace ga address d’in guest house d’ina nan sannan yatashi tsaye yace sai munyi waya, fitowa yayi daga d’akin yabarta tsaye ta kasa motsin kirki,

Zama tayi saman kujerar tare da yin ajiyar zuciya tace na shiga ukku yau na gamu da gamona…..Daidai lokacin hajiya tashigo d’akin da mak’udan kud’i a hannunta tana ta murmushin jin dad’i tace ya naganki haka duk kinyi zuru-zuru?+

Kinga irin sa’ar taki ko?  Kalli kud’in da yabani,  zaro ido hajiya tayi tace ashe kema ya aje maki, kai Allah ya gamamu da mutanen kirki gaskiya.

Dafatan dai kin amince mashi ko?

Bak’in ciki yahana Amina magana dakyar tabud’e baki tace munyi magana dasu ai hajiya.

Washe baki tayi tace yauwa ‘yar kirki Allah yayi maki albarka,  dan Allah kiyita latsar manasu muna samun kud’i domin mutanen nan daga ganinsu akwai kud’i dayawa,

Kema kanki kinfara warkewa dan Allah kirik’eshi hannu bibbiyu,

Takaici yahana Amina magana saidai tatashi tafice daga d’akin ba tare da tace ma hajiya komai ba.

Ranar hajiya murna tawuni tanayi saida kowa na gidan yasan tana cikin farinciki.

Dakanta tashiga d’akin Amina lokacin tana saman darduma ta gama sallar la’asar,

Tana murmushi tace ‘yar albarka ga kud’in sai kika baro baki d’auka ba,

Amina tace hajiya barmaki nayi ai,

A’a ba za ayi hakaba kinga nima anbani nawa na dai d’ibi na siyan Maggi, kema ai kina da buk’atarsu kinga kinsai ma kanki wani abun mai amfani dan haka ki aje wajenki.

Ba dan tasoba ta amshi kud’in, fita hajiya tayi daga d’akin tana ta shi ma Amina Albarka.

K’irga kud’in tayi taga 20,000 ta6e baki tayi tatashi tasakasu cikin jakkar kayanta tace ba zan ta6asu ba kar azo asamu matsala nan gaba.

Baba salame ce tashigo d’akin d’auke da Ameerah da tatashi daga bacci tana ta kuka,  kar6arta Amina tayi.

Tun daga ranar su Alh faruk basu k’ara zuwaba Amina ta ji dad’in rashin zuwan nasu hajiya dai ce take ta complain.

Bayan wata d’aya har ta mance da zancen wani Alh faruk, tana cikin restaurant suna ta sana’arsu d’aya daga cikinsu ce bilki tashigo tace Amina kije hajiya tana kiranki,

Toh Amina tace sannan tamik’a Ameerah hannun bilki tawuce tanufi d’akin hajiya dasallama tashiga,

Hajiya ta amsa mata tana murmurshi tace zauna mana,

Zama Amina tayi.

Daman Alh faruk ne yakira waya yakeson magana da ke ashe d’an albarkan yana dubai saisa mukaji shi shuru.

Daidai lokacin wani kiran yashigo murmushi hajiya tayi tace ga ma d’an albarkan nan ya k’ara kira,

Mik’ama Amina wayar tayi tare da tashi tanufi bedroom d’inta.

Saida wayar takusan tsinkewa sannan tad’auka tare da yin sallama,  daga chan 6angaren aka amsa mata.

Kwantar da murya yayi yace baby dafatan kina lfy kiyi hakuri tafiyace takamani zuwa dubai saisa ban dawo ba ammah fa I  missed you so much baby,

Please idan kin amince sai insa ayi maki visa sai ki taddani a chan,

Zaro ido tayi kamar yana kallonta tace wlh ba zan iya ba.

Marairaicewa yayi kamar zaiyi kuka yace please baby help me wlh ina cikin yanayin da ba zai fassaruba,

Ta6e baki Amina tayi cikin ranta tace ji shi dan Allah babba da shi ammah yana shagwa6a mutumin da ya haifeni ammah…

Katseta yayi daga tunanin da take yace kinyi shuru baby please say something.

Hararar wayar tayi tace gaskiya Alh ba zan zo ba,

Why not? Please zan baki 500,000, kuma idan hajiya kikeji toh zan tambayar miki ita.

Nifa ba ita nakejiba kawai dai ban ra’ayine sai anjima.

Batajira jin abinda zai ce ba kawai takashe wayar.

Ta dad’e zaune tana juya wayar tana tunanin yadda zata rabu dashi cikin ruwan sanyi ba tare da ran kowa ya 6aciba.

Hajiya ce tafito daga bedroom tana murmushi tace har kun gama wayar?

Amina mik’a mata wayar tayi tace eh hajiya.

Bata jira jin abinda hajiya zata ce ba taficce daga d’akin.

Bata dad’e da fitaba yak’ara kiran wayar,  hajiya tad’auka tace yanzu rafita Alhaji bari akaimata.

Alhaji faruk yace a’a hajiya ba sai ankai mataba dake nakeso muyi magana.

Gyara zama hajiya tayi tace toh ina jinka.

Hajiya kinga ina son yarinyar nan sosai kuma ban k’asar yanzu dan Allah inaso insa ayi mata visa tabiyoni, nan da 2 weeks in naga abinda nake sai mudawo tare.

Shuru hajiya tayi na d’an lokaci sannan tace gaskiya Alhaji kayi hak’uri hakan ba zai yuwuba kayi la’akkari da nutsuwar. …

Katse mata magana yayi ba tare da ta gama ba yace hajiya zan baki dubu d’ari biyu idan kika shawo min kanta ta amince, kituro min account number d’inki zan turo miki 50,000 kifara ta6awa.

Hajiya rud’ewa tayi jin an amfaci wad’annan kud’ad’en tace Alhaji kaban lokaci zan shawo kanta.

Murmushi samun nasara Alh faruk yayi yace shikenan hajiya duk yadda kukayi da ita zamuyi waya,

Bai jira jin abinda zata ceba yakashe wayar yana dariya yace kud’i kenan inkana da su babu abinda zaka nema karasa….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page