NI DA PRINCE CHAPTER 12

NI DA PRINCE CHAPTER 12

Suna isa farha ta dana kararawa, ba’afi 2min ba akazo aka bude, daga ganin wace ta bude mai aiki ce ta gaishesu tare da tambaya, salman yace hajiyar nanan? Tace a’a ta fita sai mami dasauri farha tace a’a yaya ma dawo wata ran, ya kalleta yace Baffan fa? Tace tare suka fita da hajiyar, ya kalli farha tace a’a yaya kasan halin mamin nan, muje kawai madawo daga baya. + Juyawa yai batare dayace komai ba, salma ta kallesu aranta tace mekenan? Itama dai batai maganar ba har suka isa mota, farha ta bude gaba zata shiga salma ta rike kofar tace kanwata kin manta? Farha ta mata wani kallo salma itama ta harare ta, tunani take wanda da kishiyarta ce yazatai?itama farha tunani take lalai inta auri salman sai ta gyarama salma zama, salman ne ya kallesu yace ke farha ki koma baya mana dolene sai kinzauna anan? Tace yaya ni nafisan zama kusa dakai☹salma tasa dariya tace me? Salman yai tsaki yace bansan iskanci ki wuce baya itaba matata bace? Farha ta bude baya tana turo baki, salma ta shiga tare da hade rai, salman yaja mota, sun dade suna tafiya a haka kafin salman yace kinga gari? Salma ta daure fuska tace hm yace ke kuma wannan cin maganin fa?ta kara hade rai yace jikin ne? Yafada tare dayin gefen titi, salma batai magana ba,parking yai tarr dasa hannunsa a goshinta, ya kalleta tare da hararar wasa yace ai bama zazzabin yanzu, ta kalleshi batare data ce komai ba, farha jitai kamar ta shake salma ganin sai wani hade rai take shikuma yana wani lallabata bayan ita akama abu amma bai kula ba😠. Yafara tuki takalleshi tace tunani nake yace name? Tace mun fito bamu tambaya ba kar yazama wani abun, salman yai tsaki yace ki daina damun kanki da wad’an nan abubuwan,ace mata da miji basu isa su fita ba sai sun tambaya? Har kasan ran salma taji dadin mata da mijin dayace amma a fili tace amma ai dokace☹ yace I don’t care about that, yafad’a tare da kallan titi, farha kamar tai kuka in ta kallesu. Sun isa gida suka fito dukansu, sai dai suna sauka ishaq ya karaso gun, cikin bacin rai ya kalli salman yace kaifa bakada mutunci, salman yai murmushi yace badai sai yanzu kasani ba😉 ishaq yace mu bar nan muje bangarenka dan yau bazan kyaleka ba, salman yai wani murmushi yace ahhh I hope bazaka canza kudirinka ba😏. STORY CONTINUES BELOW Sun isa bangaren su Farha ta kalli ishaq tace ya…..wata harara ya maka mata yace dalla fita daga nan, a zuciye ta juya tana kunkuni, ishaq ya kalli salman yace kaji asara wlh dazakasa baiwar Allah karya akan wata lalata dakake, salman yace ahh badai baiwar Allah daka fada tana nufin matata ba?salma da sauri tai hanyar kitchen, ishaq yace ita mana to wlh bazan…..salman ya katseshi yace matata? Ba matar ishaq ba ko? Nad’auka haa zancen yake? Ishaq yai shiru yana huci, salman yai murmushi yace yaya ina tausayin ka dasan shiga zancen ma’aurata😞 yazanyi in kaje kai baban laifi🙊? Ishaq yagama kuluwa jiyake kamar ya mutu, salma dake kitchen tai murmushi tace amma salman😀. A hankali salma ta fito dauke da ruwa da lemo, sannan ta kalli ishaq tace kazauna😊 wani sanyi ya kamashi nan yazauna yana kallanta kamar ya had’iyeta, salman ya kalli ishaq ganin yanda yake kallanta yasa yace yaya kasan me? Yace me😡? Yace akwai wani kare da ya takuramin, bayan nasai wani abu mai kyau sai na kua karan yasamin ido, burinshi yaga ya d’au abin nan, ishaq yace a ina karen yake? Salman yai murmushi yace kanaji? Yace eh, salman yace kasan menama karen? yace a’a, yace zuwa nai nasashi a kejin daba mai budeshi har karshen rayuwa🙂 ishaq ya tabe baki yace ka kyauta, nifa karnuka basumin ba, salma dake tsaye tasan lalai magana salman yake dankarawa ishaq amma mamakimta shine badai ishaq ne karan ba ko? Salman ya saki murmushi ganin ishaq baisan mema yace ba, yace yaya inkaje ka tambayi fulani labarin karen ita tasani ai, ishaq yace to tare da kallan salma. Yana fita salman yai tsaki tare dayin d’aki dan yafarajin kansa na sarawa, dasauri ya had’iyi magani ya kwanta, salma ta shigo tare da zama kusa dashi tace labarin karen nan? Ya kalleta, tace badai dashi kake bako? Yai murmushi yace ashe kina gane maganar boye? Ta tabe baki tace me ka d’auken? Yace ummm bari muga….tasa hannu ta mintsineshi a ciki, hannun ya kama tare da jawota jikinsa yace umm ina tashi ramawa me kike tunani?ahankali tad’ago tace to ai kaid’in ne☹yace ni me? Tace wato bama kasan me ka d’aukeni ba🤔 habarta ya rike da hannu d’aya yafara juya fuskarta, yana cewa bari inga, ture hannun tai tare da mikewa, dasauri ya jawota, ta fad’a kanshi sunyi shiru na wani lokaci banda zuciyoyin biyu da suke bugawa, cikin wata irin murya salman yace haushi kikaji? A hankali itama tace um, wani sansanyan murmushi sukama juna yace bada wani abun na fad’aba, tace nasani yace then? Tace bantabaji kaba wani hakuri ba tunda nake, yace so?tace meyasa? Yace kawai, tace ummm nagane, yace bansan kid’inga zuwa inda kikasan ishaq na zuwa, in gurin fulanine kibari muje tare, tace y?yace kawai, ta tabe baki sannan tace to amma menene abu mekyau da kake magana d’azu? Yace u don’t have to know tace shikenan😞naji. Zaune suke akan dinning suna lunch, salma ta kalli salman tace bayan tafarnuwa meye bakaso?yace bangane ba? Aranta Tace banason wata tazo ta dinga nunamin tafini sanin mijina, tabude baki zatai magana taga salman na dariya, tace meye kuma😞 yace kedai zuba abinci, wato da farha kike ko? Tace mene? Yace wace zata nunamiki ta fiki sanina😉 dasauri ta rufe fuska dama yaji? Ahh kunya ya kamata,murmushi yai tare da matsowa kujerar kusa da ita, ahankali ya zare hannunta tai kasa dakai yace uhmm bari in tashi nama daina jin yunwar, dasauri ta rikeshi tace a’a muci dan Allah, yai murmushi tare da kallanta itama shita kalla, yamata alama da kai ta zubamai taI murmushi tare da jawo plate……… Ummmmm nikam nace tunda abin ba tayi bari nai nan🏃🏼🏃🏼Ishaq zaune a kusa da fulani ya bata labarin kare, ranta ya baci ta mike a fusace tace kai amma kazama babban shashasha kana zaune salman ya gane kanama salma wani kallo, ishaq yace to sai me? Tsoranshi nake? Tace to kasan waye karen?+ STORY CONTINUES BELOW Ishaq yace bayace kinsan karen ba? Haushi ya kamata a fusace tace to kaine karen dakai yake banza, tafad’a tare dayin d’aki, ishaq ya mike yace ni? Nine kare? 😖😡 amma salman yagama cimin mutunci kuma wlh sai na hukuntashi sai yasan nidin kare mai cizo ne😡. Salman kwance a d’akin najib yayi rigingine tare da dora hannunsa a a goshi, najib ya kalleshi tare da girgiza kai yace prince dagaske bazamu fitan ba? Salman yai shiru, najib yace prince wai menene? Tun d’azu kazo kawai ka kwanta, salman ya mike da sauri yazauna akan gado yace najib, zo ka tab’ani kaji ko dai ina zazzabine? Najib ya matso tare da sa hannu a wuyansa, yace lafiyarka kalau🤔salman yace to meke nan? Najib yace wai me? Salman yace kai inaji gun likita na zani ina bukatar amsa, najib yace jikin ne? Salman yai tsaki yace haka kawai tunda nafito nake tunanin salma sannan daga na rufe ido sai indinga hangota, gashi in muna tare in tai wani abun sai inga kamar ita kad’ai nake gani a duniya, abinda yafi damuna in ta matso kusa dani ko na matsa sai injo zuciyata na bugawa, najib baka tunanin yakamata inga likita? Najib ya kwashe da dariya harda rike ciki, salman ya hade rai tare da mikewa yace wani sabon iskanci ne wannan kuma? Najib ya tsagaita yace salma dana d’auka kana masifar san farha me kenan? Salman yace insanta mana kamanta tare muka taso? Najib yace kundai shaku amma ba soyaya ba, salman yace bangane ba? najib yace prince yanzu kafara soyayya bada ba ai😂salman yace bansan iskanci meye hakan? Najib yace ayya prince salma ta gama da zuciyarka indai har ka kai wannan stage din😀gaskiya ina tayata murna da alama ya kamata in kirata muyi party😬 yafad’a yana d’aukan wayarsa, salman daya tsaya kamar sanda yana nanata kalaman najin, ganin najib yad’au waya yasa ya fizge wayar yace wani iskanci kake hakan? Najib yace abin murnane ai, salman yace ba wani soyaya so kake inka fad’amata tarainamin hankali😠najib yace kaifa matsalata dakai kenan, salman yace tashi mu fita, najib ya mike tare dacewa abokina ina tayaka murna😉, salman ya makamai harara yace kamanta, wannam d’in abun murnane kaifa bakada aikinyi😏. Salma na zaune a falo rike da littafinta,ganin mutum tai agabanta tasauke littafin tare da kallan wacce ke gurin, farha ce sanye da riga da wando, salma ta mata wani kallo tace na sallama? Farha tace ina yayana? salma tai wani murmushi tace menene? Farha tace meya dameki? Salma ta mike tare da d’aukan littafinta tace inkin fita ki rufe kofar ni nayi nan, farha tace kina nufin anan zaki barni😠? Salma tace naga ba guna kika zo ba kuma Wanda kike nema bayannan kinga sai kijira a falo inkin gaji sai ki tafi ko? Farha tafara muzurai salma takalleta tare da tura kofar d’akin. Tana shiga ta zauna akan gado ranta duk a bace tace what? Yayana😏? Tanaji farha ta fita tai tsaki tace yarinyar nan tama gama rainamin hankali. Falo ta fito dan ta bar wayarta acan, sai dai me? Muryar farha taji a waje da mamaki ta leka, salman taganj da farha akan kujerar gun suna hira, jitai kamar zata fashe dan kishi dakyar ta saisaita kanta ta fito wajen,salman tunda yaji motsi ya juya yaga salma ya zuba mata ido, yakasa d’aukewa, farha ta kalleshi tasa hannu ta taba hannunsa ya juyo tace yaya ina baka labarin skul, yace oh inaji, yafad’a tare da kallan gun da salma take, salma takaraso gun tace ashe kana nan? Salman yace eh yanzu na dawo, wani abun ne? Haushi yakama salma wai wani abun ne? Tahade rai tace ba wani abun🙄 tafad’a tare da juya,baisan sanda ya kama hannunta ba tad’an yi murmushin farin ciki sannan ta juyo, tace menene☹? salman daya rasa mai zaice yace umm dama ce miki zan kid’aukan earphone d’ina, salma ta kalleshi sannan ta kalli farha datasaki murmushi ganin kallan da salma tamai yasan taji haushin maganar, fizge hannunta tai wtare da juyawa, salman ya kalleta sannan ya kalli farha yace nashiga ciki tace yayana ba…..kasa karasawa tai ganin yayi gaba, haushi ya isheta ta mike tai d’aki a fusace. Salman na shiga d’aki yaga salma azaune akasa tad’aura kanta a gado, jikinsa yai sanyi, yakarasa gunta shima ya zauna a gefenta yasa kansa a jikin gadon yana facing d’inta, kallansa tai idanunta taf kwalla,yace haushi kikaji? Tace haushin me? Yace shikenan amma miye na tahowa? Tace mezan muku agun? Yai shiru tace kagani ko? Nasani ai, yace me kika sani? Tasa hannu tashare kwallar data zubo mata tace shikenan, salman yasa hannunshi a kuncinta tare a shafa kanta yace bakisan komai ba, dan haka kiyi shiru, ta kalleshi sai dai yanda yake kallanta yasa takasa magana,shima kallanta yakeyi ahankali ya matso yakai bakinshi kan goshinta yai kissing, salma ta lumshe ido jitake zuciyarta kamar zata fashe, jawota yai ya rungumeta tsam ajikinsa tare da sakin wani nannauyan ajiyan zuciya, salma tai luf akirjin salman wata kwallar dadice ta zubo mata……. Fulani zaune a kilisarta bakar maganar da salman ya fad’a wa d’anta ta dameta dayawa wata baiwa tasa ta kira mata ishaq ganin yau sam bai shigoba da alama shima haushin abinda fulani ta fad’a yake.+ Salma ta shirya tsaf, dan salman ya fita makaranta kuma tafad’amai zataje gaida fulani, sun fito itada hanne, azahirin gaskiya gani take kamar bai kamata ace sai lokaci_lokaci take gaida fulani ba, ganin matan gidan kusan kullum sai sun gaidata, tana tsoron kar hakan yaja ma salman wani abun. Sun isa bangaren, wata baiwa tace kishiga tana kilisarta,tace duk bayin su fita amma ke ai ba matsala, salma tace tom tare dayin hanyar. Fulani zaune itada ishaq takalleshi tace wai haushi kaji? Yace umma ni narasa me kikeso inyi ki yabeni? Tace ina yabonka ishaq kawai banaso ne kadinga zama na karshe in aka had’aka da salman,ishaq yace nifa umma na tsani ganin yaron nan dan yana takuramin, daidai nan salma tazo shiga sai dai tasa hannu zatai knocking kofar taji fulani tace kodai musa amaidashi kasar waje? Ishaq yace ko? Tace eh mana ni kaina na tsani ganin salman gashi yai tamin kwarjini, inaji dai kawai musan yanda zamuyi yakoma can, dama acan yataso, salma da jikinta yashiga bari sai jitai ance in_law me kike anan? Salma ta juyo ad’an tsorace ta kalli farha, dakyar ta saisaita kanta ta kalli farha tace yanzu nazo tafad’a tare da kwankwasa kofar, fulani ta kalli kofar tace shigo? Salma ta d’aure murd’a kofar, farha ta kalleta tai tsaki tace da alama yau ranar ba sa’a tunda nafara karo da waccen. Salma jiki a sanyaye ta shiga tazauna tare da gaida fulani,ta amsa itama a sanyaye dan tana tsoron ko taji, ishaq kam ya zuba mata ido kawai yana kallo,fulani ta kalli salma tace ina d’an nawa? Salma tad’aure tasaki murmushi tace yana makaranta, fulani tace salma ki kulamin da d’ana kinji? Kinga maraya ne😊 salma aranta tace lalai akwai 2face dayawa a duniya amma afili tace insha Allahu, ishaq ya kalleta yace ni naza’amin magana ba🤔 tad’an dago ganin kallan dayake mata yasa tamaida idanta kasa tace ban kula kana nan ba tuba nake, sai a lokacin hankalin fulani ya kwanta, indai tajisu to aikuwa tasan ishaq nanan, ishaq yace au hakane? Wato jikinki bai……dasauri fulani ta katse maganar da cewa salma kingadai sarki natsananin san salman dan Allah ki taimakamai karya dinga abinda ransa zai b’aci tace to, tare da kallan ishaq, tana mamakin me yakesan cewa d’azu. Mikewa tai taredayi musu sallama, tana fitowa ta kalli kofar d’akin tace a waje kamar…….ta juya tai waje duk jikinta a sanyaye, tana shiga d’aki ta zauna abakin gado, lalai yau ta yarda in mutum ya rasa uwa to fa yayi babban rashi, idanta ya ciko da kwalla tausayin salman ne ke ratsata, tace ko ya sani? Can tace da alama ganin yanda Yake musu. Bayan isha’I salman ya dawo tana zaune tana game a waya, tanajin motsin kofa ta mike da sauri tad’au turare ta kara fesawa ta gyara zama, salman ya shigo da sallama salma ta amsa tare da murza iso, yashigo yace wai bacci? Tad’an kalli agogo tace kadad’e harna fara bacci☹ yakaraso yace uhmm anya kuwa baccin ake? Tace eh mana🙄, yai murmushi tare da sa hancinsa a wuyanta yace amma kamar yanzu akasa turaren na? Sannan ya sa hannunshi a bayanta yace kamar kuma wayarnan amfani ake da ita? Ta mike da sauri tare da ware ido ta turo baki tace ahhh wai kai ba’a fooling d’inka☹? Yajawota jikinsa yace inafa bayan baki iya pretending d’in ba? Kawai dai kice so kike ind’inga dawowa da wuri ko ba haka akeso acemin ba? Yafad’a yana kallanta, dasauri tashige jikinshi jin wani shock yai daga kansa har zuwa ‘yan yatsun kafarsa, jiyai salma tace ni kad’ai d’in ne ba dadi☹ yai gyaran murya sanna yace insamomiki ‘yan tayin zama? Tace suwa? Yace inada kanne mata ai ga farh…..tureshi tai tare da zama akan gado, ya kalleta ba shakka wannan kishi salma takeyi, kenan itama tana sanshi? Zama yai kusa da ita yace in mutum baisan abu yafad’a kawai bawai yad’inga had’e rai ba🤔 salma tad’an matsa tare da harde hannayenta tace eh banaso, happy? Yai murmushi batai auni ba taga kan salman a cinyarta, ta runtse ido inama salman na santa? Da gani zatai tafi kowa farin ciki a duniya, a hankali ta bude idanta, salman na kwance idanunsa ta kalla, shima kallanta yake, dasauri tad’auke idanta jin gabanta na fad’uwa, salman ya kalleta tare dasa hannu yadawo da fuskarya kansa yace yau nagaji shiyasa zan d’an kwanta anan, an bani pass? Ta kalleshi tai murmushi tace kunsha yawo kenan da najib ya kankance ido yace ummm da alama matar nan tasa ana bina🤔 salma tai dariya fararrn hakoranta suka fito, tace sai an dubamin? Bayan nasan me kuke a skul d’in? Yace ahh ashe fa hakane. STORY CONTINUES BELOW Tace yaushe zaka fara karatu? Ya kalleta da mamaki yace da wasa nake? Tace nasani da saninka kake mika farar takarda, yace what? Mezai sani hakan inba rashin sanin amsa ba? Tace uhmm anya kuwa? No matter how much I think zuciyata ta kasa yarda da hakan,u are a smart person babu yanda za’ai kace ba ka fahimtar komai, salman ya juya kansa zuws cikinta yace mubar maganar, salma tasa hannu akansa tace why? Yace later, tai ajiyar zuciya tace to. Salman yayi shiru a jikin salma, zuciyarsa na kwadaitamai kusantarta, sai dai yayi alkawarin a rayuwarsa bazai tab’a kusantar macen dabata sanshi ba, yazama dole yatantance meke ran salma. Salma kam ta d’auka bacci yake tai shiru tana kallansa, maganar su fulani ce take dawo mata, shafa kan salman tai tausayinsa na ratsata. Salman ganin bazai iya bacci a haka ba yasa yai kamar yana bacci, yad’an mirgina, salma ta matso daf da fuskarsa tana kallansa a fili tace *Sweet one time, cold one time, rude one time, mean one time and romantic one time* Tai ajiyar zuciya tare da rufe ido, can ta mike tai shimfid’a ta kwanta. Salman ya bud’e ido ahankali ya maimaita kalaman data fad’a yai murmushi tare da kwanciya wani farinciki yakamashi da alama salma nasansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page