NI DA PRINCE CHAPTER 9

NI DA PRINCE CHAPTER 9

Kado ya hau ga mamakinsa duk b’acin ran dake damunsa ya tafi, ahankali yake satan kallanta tana duba wayar.+ Salma ta taso tazo kusa dashi ta tsaya tace kamar ba sim a ciki ko? Ya d’an dago tare da jingina a jikin gadon yamata alama da hannu ta zauna a kusa dashi, ahankali ta zauna tare da mikamai wayar, ya amsa yace ina ledar? Ta mike ta d’auko nan ya d’auko sim pack din yasa sim din sannan ya mika mata, ta kalleshi tace bakasamin numberka ba, ya amsa ya samata tare da kallan wayar so yake yaga mezatayi saving din sunan, ganin yana turo kai yasa salma tai dariya tare da rungume wayar, cikin zolaya tace me kake lekawa? Dasauri ya koma inda yake yace me kuwa? Tace me kakeso insa akan sunanka? Yace dama mutum ake tambaya me yakeso? Ta mike tare da dariya tace nama tuna, shima ya mike zaune yace me kika tuno🤔? Tace hmmm yama? Yace what? Tace to ai namanta☹ tafad’a cikin shagwaba, ya koma ya kwanta tarr da cewa bawani nan, tai murmushi tare da zama a shimfidarta azuciyarta tace mezansa? Rude? S?ahh me zansa? Tafad’a tare da rike haba, salman na kallanta yai murmushi tare da juyawa. Wata idea ce tazo mata kawai tai dialling number salman din, ganin waya ta shigomai kuma new number yasa ya d’ag da mamaki amma baiyi magana ba, salma tai kasa da murya tace hiii🙋🏻, jin muryar mace yasa yace waye? Salma tace is me😉 jin maganar kamar a d’akin yasa ya juyo tai murmushi tare da daga wayar ta jijiga, yace ahh what is this? Tace my no.😀 ya katse tare da sakin murmushi, tace kai saving. Ta taso a hankali tazo kusa dashi, salman daya kurawa number ido yana tunanin mai zai sa, jin motsin salma yasa ya rubuta Stubborn, salma ta fizgo wayar tace stubborn? Ni din😠 ya mike yace ba haka bane? Tace eh mana yace to yaya ne? Tace bandai sani ba amma banda wannan🤔 tafad’a tare da juya baya, hannu yasa a kugunta yaje juyo da ita ta taho gaba daya, ta fad’a jikinsa, ahankali ta d’ago nan fa suka shiga kallon juna, salman ganin tasa wayar a bayanta yasa yajawota ya rungume sannan yasa d’ayan hannun ya zare wayarsa, ya nuna mata sannan yace me kikeso insa? Tace inza’a sama mutum suna shi ake tambaya? Yai murmushi jin ta kwaikwayeshi, ta mike zata tashi ya rikota yace in baki fad’aba zan bashi a sunan d’azu, tace in kasa sunan d’azu nima zansa duk abinda yazomin arai, ka yarda?ya d’aga gira. Nan ta mike tare da kwanciya a kasa sai dai takasa bacci, sai juyi take, abubuwan daya faru tsakaninta da salman take tunowa, lumshe ido taja bargo…..ita kanta batasan meke faruwa da ita ba. Yau saturday hakan yasa salman ba inda zashi da safe bayan sun tashi, kawai yau tasamu kanta dacemai ina kwana? Mamaki ya kamashi a hankali ya amsa tare da cewa duk farin cikin ganin wayar ne? Ta rufe ido tace bafa haka bane☹ yace to naji, ki tashi mu shirya muje asibiti ko? Tace kasanar da sarki dalilin fitarmu ta jiya ne? Yace sai na sanar? Mamaki ya kamata tace kasan fa abinda yafaru jiya, yace to sai me? Zaki fasa zuwa duba mahaifinkine saboda wasu suna kai gulma? Tace ba abinda nake nufi kenan ba amma jiya anma fad’a yau…..yace ke akama? Tace a’a amm…yace ki tashi ki shirya in zaki, in bazaki ba kuma ki zauna, yana kainan yad’au kaya ya shiga toilet,salma ta rike kai tace yazanyi? Number Abba tasa ta kira, kamal ne ya d’aga tace yaya ya jikin Abba? Yace da sauki dan gashima a zaune nan ya mikama Abba suka gaisa, Abba yace basai kinzo ba yau kinga bai kamata daga aure kidinga yawo haka ba tace Abba amma ai yakamata inzo, yace na yafe zuwan, tadaure tace wannan ce numberta Abba kayi saving yace lalai ina murna tace na gode, nan ta kashe wayar. 1 Salman na fitowa ta kalleshi tanaso tamai magana sai dai ganin ya d’aure fuska yasata tai shiru, mai yashafa yasa turare ya fita falo, tai tsuru a zaune can ta mike tai wanka ta fito falon, yana ganinta yad’an saki rai takaraso dinning ta zauna har suka ci abinci ba wanda yai magana suna gamawa ya shigo d’aki da niyyar d’aukan makuli, salma ta biyoshi,ta tsaya a bayanshi tace dan Allah kabari na tambaya inzamu fita, ya juyo cikin b’acin rai, harzai yi magana ko me ya tuna kawai taga ya fita da sauri, tabi bayanshi da kallo idanta taf da kwalla tace yazanyi😥? Salman na fita mota ya fad’a yazauna yana tunanin zata fito, salma kam ganin tsayuwar bazata mata amfani ba yasa ta jawo mayafi ta fito da sauri sai dai ba salman a falon ganin haka yasa ta zura takalmi tai waje bayinta suka biyota, da sauri ta bude kofar tsakar gidan zata fito dai_dai nan ishaq ya taho ai kuwa su kai gware baya tai da sauri tare da kallan wa ta bige? Ishaq ne ya d’ago cikin fad’a shima sai dai ganin fuskar daya dade yana bege yasa ya saki ajiyar zuciya, salma tai kasa dakai tace yahkuri yarima ban kula bane, murmushi yai yace are u alright? Tace eh kayi hakuri plz, yace indai bakiji ciwo ba is okay😉, ta d’ago da mamaki ta kalleshi yace yes that’s what I hope😊, kasa tai dakai tare da juyawa cikin gida ta turo kofar, hanne tace kinfasa fitar? Tace eh. Salman ganin ba alamar salma yasa yai waje da gudu ranshi a b’ace, dakin najib ya wuce, yana shiga ya fad’a gado, najib yace prince meya faru? Naga kamar kana kan fire😂. Salman yace banasan magana yau, najib zaiyi magana wayar salman tai kara ya kalli wayar stubborn ne yafito ajiki, ture wayar yai gefe, najib ya kalleshi yace waye stubborn? Salman yace ina ruwanka? Najib yace don’t tell me salma😂? Lalai taci sunnan itama naga ba kanwar lasa bace amma salman stubborn a waya? Lol so childish😜. 1 Salman yace ina ruwanka? Zan fita daga d’akin nan fa? Najib yace sorry amma kana kallo bazaka d’aga ba? Salman ya kalli wayar harta tsinke, salma takara kira, najib yace salman please, salman yace ba ruwanka malam bakasan metamin ba😠 najib yasa dariya yace har anfara love_ fight hahh lalai prince. 1 Cikin zafin rai salman ya mike yace love fight? Lalai kaci mutincina nida wa? Najib yace haba salman, cool down meye da zafin ran ko dai haka ne? Kakesan ka waske? Salman ya kwanta tare da juya baya, yanaji salma tai kira na 3, sai dai yaki d’auka itama batasake kira ba. Salma kam haka ta zauna sukuku a gidan sam batajin dadi gashi tasan duk kiran dazatama salman ba d’agawa zaiyi ba. + Salman kam da yamma yad’au najib sukaje suka dubo Abba yau kam kamal bayanan sai mahaifinsa, sun d’an dade kafin su taho, gidan najib ya koma, najib ya kalleshi yace prince wai meye hakan? Bazaka wuce gida ba? Salman yace malam ba ruwanka dani😠 najib yace amma salman ai hakan bai dace….ganin salman yayi ya mike tare da komawa gado ya kwanta, najib ya kalleshi sannan ya girgiza kai, salman sai juyi yake can kuma ya mike ya d’au makulli yai waje, najib ya bishi da kallo tare da murmushi yace tunda yazo yau hankalinshi baya nan amma yaje inda hankalinsa zai kwanta pride dinsa ya hana🤔 1 Salman ya isa gida, salma tunda tai sallar isha’I tana zaune akan sallayar ta d’aura kanta akan gwiwarta tayi shiru tanajiran salman, ahaka batasan sanda bacci yafara d’aukanta ba, ahankali salman ya turo kofa sai dai ganin salma tana bacci yakara tunzura shi wato ita ko ajikinta ko? Shigowa yai ya d’au kaya ya wuce toilet yai shirin bacci, yana fitowa ya tsaya a jikin gado ya kurama salma ido, yarasa mai yake tunani, haka kawai yasamu kanshi da rashin san d’auke idanunta, a fili yace tanasan bacci a takure. 1 Salma dake bacci ahankali ta bude ido, idanun salman tai arba dasu, dasauri ya d’auke idanunsa, salma ta mike da sauri tazo kusa dashi tace yaushe ka dawo? Salman ya shareta, tace yanzu? Ya mata banza gado ya hau yasa earphones akunnensa ta zauna kusa dashi tace sannu da zuwa, salman yai kamar baya jinta, tace plz kace wani abun☹, tafad’a cikin shagwaba, salman kam wani gun ma yake kallo. Tarasa yazatai, hannu tasa tare da zare earphone na kunne daya ta Matso tasa a nata kunnen, wani sauti mai dadi ke tashi, dagaji piano ne,da mamaki salman ya kalleta, ta lumshe ido jin dadin sautin amma wannan kid’an bazai hana mutum jin magana ba wato yana jinta kenan, ido ta bude, sai dai salman tagani yana kallanta, tace sautin yamin dadi, sa hannu yai ya zare na kunnenta, ta hade rai tace dan Allah ni ka kulani, ko fad’ane kamin, amma ni bansan shirun nan. 2 Ganin bashida niyyar mata magana yama juya kansa d’aya gefen, itama komawa d’aya part din tai tasa hannu ta zare duk earphone din ta mike da sauri, salman ya kalleta yace bani abuna? Tace um um naki, tafad’a tare da noke kafad’a ta katasa wajen madubi, ya mike yafara tahowa inda take yacd bazaki bani ba? Tace naki sai ka tsaya munyi magana. Ya karaso inda take, dasauri ta boye a bayanta, ganin yana tahowa yasa sai sauri ta koma wajen gado, yakara tahowa yace bazaki bani ba? Tace naki, inkanaso kacemin ka hakura😉salman ya bita nan fa suka salma tasa gudu shima ya fara binta, ta gado ta haura ta zagayo shima ya bita ta ka ra zagayowa ta hau gado kenan yasa hannu ya kamo hannunta, itama ta fara ja a tare suka fad’a kan gadon, suka yi rigingine kowa na ajiyar numfashi. 1 Can salman ya d’ago ya matso daf da ita yace bani🤔? Yafad’a tare da mike hannu, itama ta d’ago tace ungu? Ya matso da hannun tace naki sai ka hakura, tafad’a tana kokarin tashi, jawota yai ya kwantar da ita ya matso daf da ita yanda kowa najin numfashin d’an uwanshi, yace kinsan me kika min? Yafad’a cikin wata murya mai rikitarwa ga sanyi, a hankali ta kalleshi zuciyarta sai bugawa take itama cikin sanyin murna tace sry I didn’t mean to hurt you, yace then? Tace narasa yanda zanyi ne😞 yace akan me? Tai shiru yace ba amsa? Ya fad’a tare da kokarin tashi da sauri tace banasan asake ma fad’a ne, tafad’a tare da runtse ido. Juyowa yai da sauri, baiyi tunanin amsar dazata bashiba kenan, yaji dadi har cikin ransa at least ta damu dashi, ganin yanda ta runtse ido yasa ya turo fuskarsa, zuciyarshi na haskomai bakinta, girgiza kai yai tare dasa hannu ya lakuce mata kumatu yace meyasa baki fad’amin ba? Ta bude ido sai dai ganinshi daf da ita yasa tai saurin murginawa d’aya bangaren tare da zama, tace um um to ba inasan ma maganaba ka fita tafad’a tare da turo baki, murmushi yai yace basai ki min text ba? Tace ince me? Yace abinda kikace yanzu, tai murmushi tare da rufe fuska. 1 Yamike yace kin b’atamin gun kwanciya ki tabbatar kin gyara kafin nasha ruwa😏 yanakai nan yai waje tace ahhhh wai wannan wani irin mutum ne?🤔 1 Mikewa tai tana gyara tana murmushi, shikanshi a falon zama yai yana murmushi. Salman zama yai afalon yai shiru tunaninsa shine meke sashi farin ciki bayan da ba haka yake ba? Idansa ya lumshe fuskar salma ya hango tana murmushi dasauri ya mike tsaya yafad’a a fili mai ke damuna🤔? 1 Salma kam kwanciya tai ganin salman bai dawoba yasa ta mike tayi hanyar falo, lokacin salman ya kashe wutar falon yai hanyar d’aki, salma data fito ganin duhu yasa tafara laluba bango ko zataji makunnar wutar gware sukai, salma ta saki wata kara, dasauri salman ya jawota ya rufe mata baki, yakai bakinshi kunnenta yace is me🙂 ajiyar zuciya tai ya rike ta tare da kunna wutar ta kalleshi tasa hannu tad’an bigi kirjinsa kad’an tace ka tsoratani wlh😰, salman ya rike hannun da ta dakeshi yace dakin d’auka meye? Ta turo baki cikin shagwaba tace tokai meyasa zaka zauna a duhu? Yace d’akin zan shigo shiyasa nakashe, tai ajiyar zuciya tace bakaji zuciyata ba wlh☹ yace kedai kawai kinfiya raki, ta kwace hannunta tare da juyawa,,ya kalleta yace me kika fito yi? Tace hmm…. yace don’t tell me fitowa nemana kikai?ta harareshi tace ni? Dalili? Ran salman ya soso yaso tace gunsa tazo, salma kuwa takarasa fridge tad’auko ruwa tace ruwa nazo sha, tawuce d’aki tabarshi agun. 1 Dakin shima ya shigo batare dayai magana ba ya fad’a gado, salma tuni tai bacci, sai dai salman sam yakasa barcin sai juyi yake, kallan salma yake wacce da alama tai nisa a bacci. Ganinai salman ya mike yazo kusa da salma a hankali ya d’agata yakaita kan gado ya kwantar da ita tare da lilibeta, yazauna kusa da ita yana kallanta, mamaki yake yanda sam baisan yadaina kallonta, yadade a haka kafin ya mike ya d’au pillow ya sauka kasa. 3 Ga mamakina gani nai ya kwanta a gunda salma ke kwanciya😳nace prince din?hmmmm… 2 Salma kam bacci yayi dadi gashi sai mafarkin saurayin nan take, suna zaune a bakin ruwa taga ya mike ya far gudu itama ta bishi, ganin yanda yake gudu da alama wani gurin zaije, ita kuma sam batasan ya tafi, gudu take sosai tanaso ta kamoshi sai dai gudun da saurayin yake yafi nata, ganin ya mata nisa sosai yasa ta zauna a kasa tahau kuka, yau ma bataga fuskarshi ba, a zabure ta mike, dai_dai nan salman ya fito daga toilet yayi alwala.1 Yace lafiya? Ga mamakinta hawaye taji a idanunta, salman ya zauna kusa da ita ya dafata cikin kid’ima yace menene?rungumeshi tai tsam batace komak ba, yace menene? Mafarki kikai? Ta d’aga kai yace mafarkin me? Tai shiru, ahankali ya d’agoda ita yace kidinga addu’a in kikai mafarkin da bashi da kyau, ta d’aga kai tare da kakaro murmushi, yace bari nai sallah tace to, ya juya ya fita. Binshi tai da kallo sannan takalli inda take, mamakine ya kamata, ya akai taganta a gado? Meya faru? Sam takasa tunano komai, mikewa tai tare da wucewa toilet. Salman kam da ciwo jiki yatashi, tun dayake ranar ce rana tafarko daya kwana a kasa duk jikinshi ciwo yake. Sai 6:30am salman ya shigo tana zaune tana karatu, tana kaiwa aya ta rufe qur’anin tareda mikewa taje gunsa, tace ina kwana? Salman ya amsa tace ya akai naganni anan?salman yai gyaran murya tace badai kaika maidani ba😬 ya hade rai yace jiyane naji bayana naciwo shi yasa na kwanta akasa, tai murmushi tace yanzu fa? Yadaina ciwo? Ya kalleta yace a’a, hannu tasa tace in bubuga ma? Ya kalleta yace bansaki ba😏 ta hade rai itama tace dacema akai inaso inma? Ta juya, hannu yasa ya rikota yace serious jikina ciwo yake dannamin plz. 1 Kwanciya yai akan gado tashiga danna mai, ahankali yake lumshe ido bacci mai dadi ne yai gaba dashi, salma ganin yai bacci ta matso da fuskarta inda yake ta kalleshi, jitai zuciyarta na bugawa, sai ta hau shakuwa, dasauri tai falo ta bude fridge ta d’auko ruwa tasha. A kujerar dinning ta zauna tace menene hakan? tadade anan kafin ta dawo d’aki ta kwanta. Karfe 9 ta tashi dan yau zasu gaisuwa, matsawa tai takalli salman tare da murmushi, ga mamakinta shima murmushin yai cikin bacci, jitai zuciyarta yashiga bugawa dasauri takoma ta zauna,wayarta ce tai kara tad’aga tace waye?zee tace banza nice mara mutunci, salma tace duk ni kadai? Zee tace dazu naje gun Abba shiyaban number ki, tace ayya nan suka shiga hira, salma ganin zata tashi kamal yasa tafi to tai d’ayan d’akin, zee tace badai laulayi kike ba? Daga shiga? Salma tai tsaki tace kefa bakida mutunci, zee tace ah to meza’a jira? Salma tai shiru, zee tace badai haryanzu baki bada kaiba? Salma tace dalla nikimin shiru, dan Allah ni akwai abinda nakesan tambayar ki, zee tacw name? Salma tace watace intaga wani sai zuciyarta tad’inga bugawa shine ta tambayeni menene dalili, nikuma bansani ba nace bari na tambayeki. Zee ta kwashe da dariya tace ai kinji matsalar ke bakisan kowa ba sai kamal inafa zakisan karfin soyayya? Salma tace duk sanda nakema kamal? Zee tace oho dai amma kifad’ama mai tambayar ba shakka ta kamo da soyayya mai karfi tunda har zuciyarta take amsawa, cikin tsoro salma tace what? Soyayya? Bakisan me kike cewa ba🤔, zee tace oho sai dai inkim gaskiya zatai amma wannan shine gaskiya, dasauri salma ta kashe wayar tace ah hb? Ni? Ta ina?how? Tana komawa d’aki ta tadda salman bayannan da alama yana toilet, bayan ya fito takalleshi sai kuma ta girgiza kai ta wuce toilet dasauri, ya kalleta yace wannan kuma lafiya? Salma kam haka tai wanka sukuku, tasa kaya. Abinci kuwa ruwan zafi kawai tasha salman yace shikenan abinda zakicI? Tace nakoshi😞yace wasa ne, tace in muka dawo zanci to, yace naji amma meyasa tun d’azu bakya kallona?tace hmm bakomai, yace bazaki kallanba? A hankali tamai alama da bayin dake gun, hakan yasa yai shiru suka mike sukai cikin gida. Sunje bangaren hajiya karama da babba kafin suje gun fulani, ishaq na kalisarta tunda suka shigo yake kallan salma, itakam kasa tai da idanta dan sam batasan wannan kallon,sun gaida fulani nan tace salman rannan ka fita akaita fad’a nikam duk banji dadi ba nasan dai fitar dakai aI da dalili haka kawai bazaka fita ba😞salma takalleta, a iya saninta hanne tace fulani ce taita masifa kodai hannen bata fahimta bane? Muryar salman taji ya ce nasani ai kin damu dani, ishaq ya kalli salma yace salman amma matarnan taka bata magana ne? Salman ya kalleshi yaji haushin tambayar amma ya saki murmushi yace kai ya ishaq ko tana magana yaza’ai ta saki tai ta magana kana gun😏? Haushi ya kama ishaq yace nid’in meye?salman ya kalli fulani yace umma kodan abunda yakeyi zata sake jiki dashi? Yafad’a yana wani mugun murmushi, fulani ta kalleshi ta kalli ishaq bakin ciki ya isheta tace eh mana gaskiya ya fad’a. Salma ta d’ago ta kalli salman mamaki take yanda yake fad’ar bakar magana yana murmushi, wannan wani irin mutum ne?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page