DIYAM CHAPTER 7

DIYAM CHAPTER 7

Haka ya shige daki ya bar mu da budadden baki. Na kamo hannun Rumaisa muka fito da sauri.muna fitowa nace “what? Lallai ma mutumin nan” Rumaisa tana murmushi tace “ya hadu ko? Shi yasa nace miki kizo muje mu ganshi” nace “au wai kina nufin saboda mu ganshi kikajawo ni dakin nan? Meye abin kallo a gurinsa? Wai dan wulakanci nice bararoji” Rumaisa tayi dariya tace “au wai haushi kikaji? Ke baki san wasa ba? Wasa fa yake miki dallacan” na bata rai nace “it doesn’t look like wasa yake min, har cikin ransa abinda yake nufi kenan” Rumaisa ta bagarar da maganar tace “to ya kika ganshi? Ya hadu ko?” Na tabe baki nace “ko kusa da haduwa baije ba” tace “ko dai don idonki ya rufe, Sadauki ya tare gaba ya tare baya” nayi murmushi ina jin sanyi a raina nace “yanzu kika kamo hanya yar gari” ta bani hannu muka tafa. Rumaisa ita kadai ce wadda nake zama muyi hirar Sadauki sosai da ita, tasan komai akan yadda muke ji a zukatan mu. Muka samu guri muka zauna, na bata labarin tsarin da mukayi da sadauki na cewa zai ke zuwa zance gurina a matsayin saurayina. Ta rike baki tana zaro ido tace “Diyam? Ba kwajin tsoro? Ba kya jin tsoron a kama ku?” Nace “relax. Kinsan dai gidan nan akwai yammata da yawa ko? Kuma duk suna fita zance so babu wanda zai gane, he will be just one saurayi among others, kuma I will make sure duk wanda yasan fuskarsa bai ganshi ba, ballantana kadan ne a gidan nan suka sanshi”.+ Ranar da Sadauki ya fara zuwa gurina a ranar na bashi labarin encounter dina da hamma Saghir. Ya bata rai yace “kar ki sake shiga harkar sa, duk hanyar da kika san yana bi ma karki kara bi ta gurin ballantana ya sake gaya miki wata maganar banzan”. Duk sanda yazo zai gaya min next time da zai sake zuwa, dan haka ni nake fita da kaina in shigo dashi. A gefen dakin mai gadi muke zama, wanda yau da gobe sai muka zama very friendly dashi. Duk ranar da Sadauki yace min zaizo bai taba sabawa ba, koya wuce time din da yace zaizo to kuwa yan minutes kadai zai kara saboda traffic. A wannan lokacin na kara fahimtar cika alkawarin Sadauki, in dai yace zai yi abu to kuwa tabbas zaiyi din sai dai in wani abu ya faru beyond his ability. Tun ranar da hamma Saghir yace min bararoji bamu kuma haduwa ba, nabi shawarar Sadauki dan haka ko muryarsa naji a guri to bana shiga, inkuwa tsautsayi ya biyo dani ta hanyar da yake to zanyi saurin chanza hanya. Rumaisa ce mai nacin zuwa gurinsa wai burge ta yake yi. Sai ranar nan bayan nayi ten days a gidan, muna tafiya da Rumaisa zata rakani in shigo da Sadauki sai muka hango Saghir a can packing lot, yasha farin voile sai kyalli yake yi kuma daga inda muke muna jin kamshin turarensa sannan muna jin muryarsa yana ta sirfawa baba audu zagi akan wai bai wanke masa motar daya saka shi ba, dan tsohon Allah sai hakuri yake bayarwa kansa a kasa amma kamar kara zuga saghir yake yi “tsabar iskanci da rashin mutunci wajan awa guda kenan nace ka wanke min mota ta amma saboda ban isa ba shi yasa kaki wankewa ko?” Baba Audu yace “kayi hakuri yallabai, Alhaji ne ya saka ni in gyara masa gurin da yake shan iska yana so ya fito anjima” yace “dalla yi min shiru, wallahi in kayi wasa kafin in koma porthercout sai kabar gidan nan. Ka kiyaye ni wallahi” dan dattijo ya durkusa yana ta bada hakuri. Ban san lokacin da naja wani uban tsaki ba, Rumaisa tayi saurin toshe min baki ta jani bayan flowers “rufa ma kanki asiri Diyam. Tsaki? Hamma Saghir? Wallahi in yaji ki zai balla ki” nace “ai kuwa daya gane cewa shayi ma ruwa ne” ta girgiza kanta tace “Sadauki ne dai takamar ki ba wani ba, amma kiyi tunani, do you really want to get him involved with hamma Saghir?” Na juya ina kallonsa, tabbas Sadauki na is very brave and fearless, amma saghir is not his match dan at least ya bashi shekaru goma, ga kudi ga kuma gata. Dan haka hada shi rigima da Sadauki will be like putting Sadauki in trouble. Na ja bakina nayi shiru sannan muka zagaye ta bayan sa muka fita daga gidan. Sai three days to resumption date din mu sannan Baffa yazo da kansa ya daukeni zuwa gida. Matan gidan sun hada min goma ta arziki wai tsarabar boarding. Amma ni sai naji duk boarding din ta fara isata amma inaji inagani haka aka daukeni aka mayar dani. Sanda muka dawo next holiday shima ina zuwa na tarar da kaya na a ajiye, ban damu ba na shiga harkokina ina tunanin ai sharada ba nisa amma sai naga inna tana hada nasu kayan ita da Asma’u tace “Kollere zamu tafi, mun kwana biyu bamu je mun gaishe su ba musamman yan uwana da muke uba daya nan take naji bakin cikin duniya ya ishe ni amma haka Baffa ya debe mu a mota gabaki daya har su Ummah muka tafi, naji dama dama saboda ganin da Sadauki ne, amma bayan munje mun kwana daya a gidan Hardo da sabuwar matarsa sai naga su Baffa suna shirin komawa suna ta sallama da mutane, na bishi soro da gudu na rungume shi ina kuka nace “Baffa dan Allah zan biku mu koma tare” ya rike fuskata yace “kiyi hakuri uwata, ba tare daku zamu koma ba ku zaku zauna ku zagaya yan uwan innarku na gurin babanta” ai kuwa a take na kara wani kukan dan ni in akwai abinda bana so a lokacin to zama a Kollere ne. Suka tafi, Baffa da Ummah da Sadauki, suka barmu ni da Asma’u mun rike juna muna kuka, Inna ta tabe baki tace “sai suje ai suci uwar da zasu ci a gidan”. STORY CONTINUES BELOW Mune daga wannan gida mu koma wancan mu kwana anan mu tashi anan muna ta ziyarar yan uwa har sai da muka yi sati biyu, Asma’u ta dan ware amma niko alamar warewa banyi ba, ranar da muka cika sati biyu Baffa yazo daukarmu ashe wai yayi wa inna waya akan mu shirya zaizo mu tafi ita kuma taki. Yana zuwa ta lissafa masa sauran gidajen da bamu je ba shi kuma yace baisan magana ba, “Diyam makaranta zata koma nan da sati daya, kamata yayi taje gida ta huta tukunna” Inna tace “wanne hutu zatayi a gidan? Taje dai gida mayun gidan su cigaba da lasheta” Baffa ya gyada kai yace “in har mayun gidan basu cinyeta ba a tsahon wadannan shekarun, to kuwa ke a garin wannan yawon naku zaki kaita gurin mayun” nan take sai rigima, inna tace ai Baffa yace yan’uwanta mayu ne. Hardo ya goya mata baya yace “to in bata kaisu sunga yan’uwanta yanzu ba sai yaushe?” Wannan yasa Baffa ya shiga motarsa yayi tafiyar sa, yace duk sanda muka gama yawon ma taho a motar haya. Bamu koma ba sai two days to komawa ta makaranta, dan haka a gurguje na shirya shima kuma dan na samu Ummah ta fara harhada min wasu kayan kafin inzo. Dan haka wannan hutun ni da Sadauki sai gani da ido. A hutun second term ne Baffa ya buga kafarsa yace babu inda zanje hutu, shima yana so ya zauna dani. Nan take rikici ya balle a gidan mu, Inna ta fito da abinda yake zuciyarta na kiyayyar ta a dangane da dangantaka ta da Sadauki, tace “sai dai bayan raina wallahi, wannan yarinyar indai ni na haife ta ba zata auri wannan yaron ba” Baffa yace “saboda me? Menene dalilinki na cewa haka?” Tace “Saboda bana sonsa, na tsane shi tamkar yadda na tsani uwarsa kuma bazan taba yarda in hada jini na da nasu ba” Baffa yace “to shikenan dalilin naki? Kishi ne kawai dalilin naki? To kuma in Allah ya riga ya rubuta akwai aure a tsakanin su fa? Fada min ya zakiyi?” Tace “sai in sallama ta, in dai ta aure shi to babu ni babu ita har abada sai dai ta nemi wata uwar bani ba” na durkushe a gurin da nake ina kuka kamar raina zai fita. Ina da karancin shekaru a lokacin amma nasan muhimmancin Inna a gurina, nasan darajarta ta wuce in hada tada kowa a sauran mutane, amma kuma nasan irin zafin son da nakeyiwa Sadauki, nasan irin soyayyar da shima yake yi min da kuma irin kyawawan halayensa shida uwarsa. Menene laifinsa.1 Ta cikin hawayena na hangoshi ya shigo gidan da kayan da yake zuwa gareji dasu a jikinsa duk sunsha bakin mai. Ya tsaya yana kallon mu kawai, Ummah tayi masa alama da hannu cewa ya fita, sai ya ajiye kayan hannunsa ya juya har yakai bakin kofa sai kuma yajuyo yana kallona fuskarsa cike da concern. Wannan hutun sam ba ajin dadi nayi shiba dan sai dana gwammace ina ma wani gidan aka kaini dan sosai Inna ta mayar dani matar kulle, ko tsakar gida bata bari na in fito daga dakin mu sai palon ta, Baffa ma sai dai in ya shigo in ganshi in kaishe dashi. Yar islamiyyar da nake zuwa in nazo hutu itama ta hana ni zuwa. Asma’u ce kadai abokiyar hira ta duk da ita lokacin bata da hankalin fahimtar me yake faruwa sosai. Rannan ina kwance a daki sai gata da takarda a bakin zanin ta ta miko min a hankali tace “inji Sadauki, yace kar Inna ta gani wai zata dake ki” na karba da sauri zuciyata tana muradin jin abinda yace, na bude na karanta, kalma uku ce kawai “how are you?” Naji hawaye ya taho min, shi concern dinsa akai nane, shi halin da nake ciki shine damuwarsa. Ranar nan muna gab da komawa makaranta Baffa yana palon Inna yana cin abinci ni kuma ina zaune kusa dashi na dora kaina a kafadarsa, a gurinshi ne kadai nake samun hope. Sallamar Sadauki muka ji a bakin kofa, nayi saurin kallon kofar amma sai naji Inna tace min “tashi ki shiga daki” kamar zanyi kuka na shiga dakin amma sai na makale a bayan labule. Ina kallonsa ya shigo ya durkusa a gaban Baffa ya ajiye wasu takardu yana yi masa bayani akan wata mota da suka siya zasu gyara su siyar. Amma ni ba abinda yake fada nake ji ba fuskarsa kawai nake kalla, sai naga ya kara kyau fuskar ta dan canza min, sannan na lura da abinda ya chanza, ya fara tara saje. Nayi murmushi na durkusa a gurin ina cigaba da kallon sa har ya gama maganar da yakeyi. Sannan ya juya side Inna ya gaishe ta duk da yasan ba amsawa zatayi ba. Bata amsa din ba har ya mike, sai daya je bakin kofa sannan ya juyo ya kalli kofar dakin mu, muka hada ido sai ya lumshe idonsa ya bude sannan yayi murmushi ya fita. Yana fita Baffa yace wa inna “Amina ni dai bazan gaji da gaya miki cewa ba kya kyautawa ba, kina dora kiyayya akan tushe marar dalili. Su yan uwan namu da suke kara zuga ki kike ganin kamar baki da masoya kamar su duk ranar da babu raina su zasu fara gudun ki keda yayanki, zasu fara ganinku kamar wasu responsibilities a gurin su. Ina ji miki tsoron wannan yaron da kike wulakantawa shine zai zama gatanki ke da yaranki watarana idan babu raina. Shi ɗa na kowa ne.” Sai da lokacin komawa ta makaranta yayi sai naji sam bana son tafiya, duk da cewa zaman gidan kamar zaman kurkuku nake jinsa amma haka nan naji bana son rabuwa da gidan. Kamar ko wanne term, wannan karon ma Baffa da Sadauki ne suka tafi dani. Sai bayan da muka dauki hanya sannan Baffa ya fara magana “Sadauki, Diyam ku bude kunne sosai kuji abinda zan gaya muku. Tun a gida naso yin magana daku amma saboda rigimar iyayen ku yasa na bar maganar nace mayi a hanya daga ni sai ku. Na farko, kun bani mamaki gaba dayan ku kuma kun bani kunya, yanzu har kunyi girman da har za ace an fara rigima akan auren ku? Yaushe aka haife ku gabaki dayan ku? Waye kuke tunanin zai yi muku aure yanzu? Ba dai ni ubanku ba. Musamman kai Sadauki kai da kake namiji, so nake kayi karatu mai zurfi kazama wani yadda wata rana zan kalle ka ince ‘yes, that’s my son’. Ke kuma Diyam, ko a ranki kada ki saka cewa zanyi miki aure yanzu. Sai kin gama makaranta kin shiga jami’a sannan in Allah ya kawo miji a lokacin sai inyi miki aure da sharadin zaki kammala karatun ki a gidansa, in kuma mijin bai samu basai kin kammala duk lokacin da Allah ya kawo shi sai ayi miki auren” yayi shiru muma duk mukayi shiru, sannan ya dora “in Allah ya kaimu lokacin, kun zama abinda nake fata zaku zama, kuma ya kasance har lokacin kuna son auren junan ku, to ni zan yi supporting dinku. Saboda dukkanin ku yaya nane, nasan halayenku kuma zanyi alfahari daku a matsayin surikai na. Kuma hausawa sunce da arziki a gidan wani gwara a gidan ka. Amma ku sani, daga ni sai Zainab ne zamu goyi bayan wannan hadin, ke Diyam a gabanki kinji kalaman da innarki ta fada, kuma da gaske take, kuma ni bazanyi miki fatan kiyi aure babu saka albarkar mahaifiyarki ba dan haka wannan shine challenge dinku ku tabbatar kafin lokacin dana fada muku kun yi kokari kuma kun dage da addu’ah kun juyo da hankalin ta ta amince.Tunda muka koma school nake lissafin kwanaki ina jiran zuwan Sadauki dan nasan wata daya yake yi yazo ya ganni, kuma nasan bashi da karya alkawari sam. Lissafi na yana cika kuwa na fara saka ran ganinsa. Ina zaune kuwa a class sai ga baba mai kiran alkhairi yazo kirana. Na tashi na bishi da sauri jidda tana tsokana ta dan tasan lissafin zuwan wanda nakeyi. Muna fita daga class din na tsaya na kara gyara fuskata ta glass din window, ina lura da yadda sabon kitson da na saka akayi min jiya ya kara fitowa wa da kyawun fuskata. A gefen staffroom na hango shi a kasan bishiyoyi kamar kullum in yazo. Sai dai amma dama matsa kusa sai naga kamar ba shiba, kamar Sadauki na baikai wannan girma da iya daukar wanka ba. Sai na tsaya daga dan nesa nayi sallama. Ya juyo kyakykyawar fuskarsa dauke da murmushinsa mai kyau, na rufe baki ina dariyar murnar ganinsa nace “ashe da gaske kaine, sai naga kamar ba kai ba” ya harde hannayensa a kirjinsa yana kallona yace “lallai Diyam girma yazo, yau ke ce da yi min sallama bayan da tahowa kike da gudu ki wuce kirjina?” Na dan jawo hijab dina na rufe fuskata ina jin kunyarsa, ya saka hannu ya bude fuskar yace “yanzu in taho gari ya gari dan inga fuskarki kuma sai kiyi min rowarta ki rufe? Kinyi min adalci kenan?” Na danyi murmushin jin kunya sannan na kalle shi daga sama zuwa kasa. Ya zama cikakken saurayi sosai, hatta sajen sa ma ya zama complete kuma yayi masa kyau sosai. Gani nake duk samarin duniya babu wanda ya kaishi kyau a lokacin.1 Sai kuma na rike baki nace “wai!! Sadauki ina zaka kai girma ne? Sai wani jin karfi kake kamar zaka dauki duniya” yace “ya kika ji sunan? Aliyu fa aka ce miki. Kin manta shi asalin mai sunan duniya kaf ta shaida karfinsa da jarumtakarsa? Sannan kuma akayi min lakani da Sadauki, kin san kuwa ko a cikin mayaka to duk wanda aka kira da Sadauki ina nufin jarumi ne shi a cikin jarumai. Ingarman namiji kenan” nayi dariya ina rufe baki, yace “what’s funny?” Nace “wai ingarma, sai kace wani doki” shima sai ya tayani dariyar. Na sunkuyar da idanuna ina wasa da fingers dina, mukayi shiru na wani lokaci sannan na dago kai na muka hada ido, na turo baki na buga kafa a kasa nace “ni ka daina kallona haka” yace “fada min menene shirrin, sai wani kara kyau kike yi kullum” na bata rai nace “bayan bana girma. Kuma wallahi ina cin abinci sosai” yayi dariya yace “girman zaizo ne Diyam. You won’t know sanda zaki girma kawai sai dai ki ganki kin zama katuwa” nace “ni tsoro nake ji?” Ya bata rai yace “tsoron me? Nace “kai gashi nan ka zama kato, gashi kuma zaka tafi jami’a, kar kaje kaga manyan yammata kace ka fasa dani” ya jingina da jikin bishiya yana kallona, yace “Diyam” na dago muka ido yace “you have no idea how much I love you, do you? Ke din fa zuciyata ce, sonki kuma jinin da zuciyata take bugawa ne yana zagaye ilahirin jikina. Ta yaya mutum zai iya rayuwa babu zuciyarsa. Idan kinga Sadauki ya daina sonki to numfashin sa ne ya bar jikinsa. Idan kinga na rabu dake Diyam to kirjina aka tsaga aka cire zuciyata daga ciki. Nine ya kamata in kasance cikin tsoron watarana zaki rabu dani, ina tsoron idan innarki ta ki amincewa dani Baffa zai hanani aurenki, ina tsoron in kin girma zaki samu wani wanda ya fini kudi wanda ya fini asali kice kin fasa dani” na girgiza kai na nace “never, ba dai Diyam ba, Diyam ai kai take so tun kafin ta san menene so, da kai ta saba da kai kuma za tayi rayuwa insha Allah. Rayuwa babu kai will not be only unbearable but also unimaginable. I can’t imagine Diyam without Sadauki” sai ido na ya kawo kwalla, yace “zaki fara kukan ko? I am here and I am going no where” Muka zauna akan bench ya fara bani labarin gida, ana yake gaya min Baffa ya siya masa fili, yace “filin fa babba ne sosai, wai ashe for years yana tara min kudin aikin da nakeyi masa a garage shine yakara akai yasiya min. Yace duk sanda natashi yi mana ginin gidan mu sai inyi akai. Sannan kuma ya fara bani salary a garage kamar sauran ma’aikata” nayi murmushi nace “inye, kaga masu albashi” ya daga gira yace “ya kika gani?” Nace “Baffa ya kyauta. Allah ya saka mishi” yace “ameen. Problem din da nake fuskanta daga Ummah ne, tun ba yau ba kinsan nake fama da ita akan ta kaini dangin babana taki, ni kuma yanzu ina ganin kamar har da rashin su a tare dani ne yake kara kiyayyata a zuciyar Inna, ina so su shiga rayuwata Inna ta gansu tun yanzu amma kullum Ummah tana ce min wai ba yanzu ba, wai lokaci bai yi ba. I just hope ba zai zama too late ba” nace “it won’t be, ni nasan Ummah kuma na tabbatar tana da dalilinta”. STORY CONTINUES BELOW Ya sunkuyar da kai yana kallon kafarsa fuskarsa da alamun damuwa, naji nima zuciyata babu dadi sai nayi niyyar saka shi dariya nace “Sadauki kaga wani kwaro zai shigar maka ido rufe idonka inga ni” sai kuwa ya biye min ya rufe idonsa, sai kuma na shagalta da kallon fuskartasa. Fuskarsa bata cika tsaho ba kuma ba za’a kirata da zagayayyiya ba. Gashin girarsa mai cika ne da laushi kamar yadda gashin kansa yake, dogon hancinsa da kofofin suke budewa da sauri da sauri a yanzu alamun bugun zuciyarsa ya karu, madaidaicin bakinsa mai dauke da lips a slightly lighter than his dark skin color kuma suke zagaye da kyakykyawan sajensa mai laushi da kyalli, abinda yafi ɗaukan hankalina a fuskarsa sune zarazaran gashin idonsa da suka yi kama da irin wanda yammata suke sakawa a gidan kwalliya. Sai kuma nayi dariya, ya bude idonsa yana kallona yace “what? Ya fita?” Nace “wallahi gashin idonka irin na yammata ne” ya bata rai yace “Diyam kin raina ni Wallahi, dan kinga gurin kwana na ko?” Sanda aka zo min general visiting sai naga anxo har da Ummah wannan karon, abinda ba’a taba yi ba. Naji dadi sosai muka zauna mukayi ta hira, muka ci abinci har da Baffa. Da zasu tafi kawai sai na fara kuka, abinda na dade banyi ba. Baffa yace min “ki zama yarinyar kirki Diyam, ki rike addinin ki kuma ki dage da addu’a akan komai ya same ki. Allah yayi miki albarka” sai na rungume shi ina kuka, yana dariya yace “yau kuma shagwabar kaina tazo?” Ya cire hannu na daga jikinsa, Ummah tace “zo ni ki rungume ni tunda shi baya so” na sake shi kuwa na tafi na rungume ta, sannan na juya na rungume inna itama. Ina kallo suka shiga mota suka tafi, sai naki kamar wani part nawa ya tafi tare dasu. Kafin muyi hutu Sadauki ya sake dawowa. Wannan karon shida wani abokinsa suka zo kuma shine karo na farko da Sadauki ya fara introducing dina a gurin abokinsa, Ahmad Muhammad, na rike sunan ne saboda a ranar mun jima muna musu akan Ahmad da Muhammad duk suna daya ne. Sai kuma mukayi hirar carrier, shi Ahmad yace babu abinda yake so ya zama inya girma irin dan sanda, yace “duk ranar da na zama commissioner of police duk wadannan yan iskan da suke yawo a gari sai na rufe su” Sadauki kuma yace “ni kam whatever zan zama nan gaba a rayuwa will have to do with cars. Ni ina da wani passion sosai akan motoci” sai suka tambayeni ni kuma fa? Na girgiza kai na nace “I don’t know gaskiya” Ahmad yace “with time zaki yi finding your place in the society kema”. Tunda hutu ya kusa nake jin babu dadi kamar wadda zanyi rashin lafiya amma kuma ciwon yaki zuwa, haka nayi exams din duk babu dadi. Ko kitson hutu banyi ba. Ranar hutun kuwa sai jidda ce ta hada mana kayan mu ta kai mana bakin gate. Har ta dawo ina kwance akan gado kawai naki hawaye yana bin fuskata, tazo ta tsaya tana kallona tace “kuka kuma Halima? Wani abun ne yake miki ciwo?” Nace “zuciya ta ce babu dadi jidda, ji nake kamar bani da lafiya amma kuma lafiya ta kalau, gaba na sai faduwa yake yi jidda” tazo ta rike ni tace “to ai addu’a zaki ke yi, innalillahi wa inna ilaihir rajiun , ba wai kuka ba” na fara yi kuwa sai naji naji dadi. Muka fito tare akayi assembly aka sallame mu kowa yana murna bandani. A ka’ida duk ranar hutu kafin a bude gate su Baffa suke zuwa, amma yau sai naga an bude ana ta daukan sauran dalibai bandani. Na samu kofar wani class na zauna idona akan gate din makarantar amma ko motar da tayi kama da tamu ban gani ba. Har aka zo daukan jidda tazo tayi min sallama ta tafi. Har akayi sallar azahar shiru. A lokacin I was beyond crying kawai dai a zaune nake kamar mutum mutumi. Can sai ga wani malamin mu yazo inda nake yace “Halima? Ki zo anzo daukanki” na mike jiki ba kwari na bishi ina ta baza idon ganin Baffana ko Sadauki. Muna shiga staffroom sai naga Abba, baban su Rumaisa. Na tsaya kawai ina kallonsa yace “Diyam babu gaisuwa?” Sai na durkusa na gaishe shi malaman gurin suna ta kallona. Ya tashi da kansa ya zuba min kayana a motarsa sannan yace min inzo mu tafi, sai da muka shiga mota sannan nace “Abba ina Baffa yake?” Ya dauke kansa yace “sun taho motar su ta samu matsala, shine yayi min waya ni kuma na taho daga gumel yace dan Allah in biyo in taho dake” na gyada kaina kawai ina forcing zuciyata ta yarda da maganar sa. Har muka shiga Kano bamu kara magana ba, na kwantar da kaina na rufe ido na kamar bacci nake yi amma ido na biyu. Na bude ido na kallon inda muke naga ba hanyar gida bane ba nace “Abba ba gida zamu tafi ba?” Yace “zan karbi wani sakona ne anan akth” na koma na kwanta. Ina ji muka shiga asibitin har mukayi packing, na daga kaina kadan ina kallon inda muka tsaya “Accidents and Emergencies” sai kuma ido na ya hango min wata kamar Aunty Fatima a tsaye a kofar gurin, sai na bude kofa na fita idanuna suna kara tabbatar min ita din ce amma zuciyata ta kasa yarda. Ina zuwa kusa da ita na lura kuka take yi, na bude baki zanyi mata magana sai na hango Inna a cikin hall din, Mama ta rike ta tana ta rusa kuka kamar ranta zai fita. Kamar mutum mutumi haka nake tafiya har nazo kusa dasu, sai naji muryar Ummah daga gefena tace “Diyam!!” Na juyo na zube idanuna a kanta, she looked old, ban taba ganinta a irin wannan yanayin ba amma kuma babu hawaye ko digo a idonta, “Diyam” ta sake fada sanda ta karaso kusa dani ta miko hannu da niyyar rungume ni amma sai ta sulale ta fadi kasa ta suma akan kafafuwana. Tsayawa nayi kawai ina kallonta yayinda jama’a da ma’aikatan asibitin sukayi kanta. “Addah” naji muryar Asma’u a bayana, na juyo lokacin data karaso da gudu ta rungume ni “addah mun shiga uku, Baffa da Sadauki sunyi accident kuma duk sun mutu”13 Na cire hannunta daga jikina na dan tura ta kadan ina kallon fuskartada take cike da hawaye, sai kuma naji wani abu yana fusgata zuwa wani daki da naga wani doctor ya fito daga ciki yanzu. Na tura kofar dakin ina kallon gadaje guda biyu da suke a cikin dakin, sannan na kalli wadanda suke kan gadajen. Gadon farko wanda yake kai an lullube shi har fuskarsa. Gado na biyu kuma an rufe shi zuwa kirjinsa. Sadauki. Daga inda nake ina iya hango jinin daya jika sumar kansa ya bata katifar da yake kai.Na dauke idona daga fuskarsa na mayar kan daya gadon da yake gaba na, sannan a hankali na taka na isa gaban gadon na saka hannu biyu na yaye sheet din da aka rufe mutumin. Idona ya sauka akan Baffa, kamar Sadauki shima gashinsa a jike da jini amma fuskarsa tas da ita babu emotions kamar mai bacci, na jima ina kallon sa dan ina jin ban taba yi masa cikakken kallo irin na yau ba. Kofa aka bude daga bayana wata nurse ta shigo da sauri tace “what .. ?” Sai kuma tayi shiru, ta karbe sheet din daga hannuna ta mayar ta rufe shi sannan ta kama hannuna ta jani kamar wata robot ta fita dani. Gurin su Inna ta kaini, wadda har yanzu take jikin Mama tana ta kuka, hannun ta daya rike da Asma’u. Nurse din tace “tare kuke da wannan yarinyar?” Inna ta kalle ni, da alama sai yanzu ta lura da zuwa na asibitin, tayi sauri ta jawo ni tana gyada wa nurse din kai tace “yata ce, yata ce” cikin kuka. Sai kuma ta rungume ni tana kara sautin kukanta. Mama tace “haba addah, ya zaki saka yara a gaba kiyi ta wannan kukan haka? Da wanne zasu ji. Dan Allah ki rage wannan kukan inba so kike kema ki yanke jiki ki fadi ba” ta jawo ni daga jikin Inna ta zaunar dani a kan benchi ta rike fuskata tace “kai kiyi kuka kinji Diyam? Kiyi ta karanta innalillahi wa inna ilaihir rajiun” na gyada mata kai ina kallonta. To ni kukan me zanyi ne bayan nasan mafarki nake yi? Yanzu zan farka amma bana so in farka din sai Baffa da Sadauki sun tashi. Wata nurse naga ta fito daga wani daki da sauri ta kira doctor sun koma tare, sai na samu kaina da mikewa na bisu amma ban shiga ba sai na tsaya a bakin kofar ina kallon ciki ta glass din jikin kofar. Ummah na hango akan gado, nurses biyu da likita daya a kanta suna ta kokarin bata taimako. Sai kuma ta fara convulsing, idanunta suka kakkafe doctor din yana ta kokarin reviving dinta amma sai jikinta ya saki. Ina kallo suka yi ta aaunata sannan doctor din ya kalli nurse din data dauko takarda da biro yace “time od death: 4:35” sannan ya bude kofa ya wuce ni jikinsa duk a sanyaye.3 “Death” na maimaita. “Ummah, Baffa, Sadauki” na fada a hankali ina jin kaina yana juyawa. Na bi bayansa a hankali naga ya tafi gurin su Inna yayi musu wata magana, sai naga Inna ta saki hannun Asma’u da sauri ta rufe bakinta ta durkushe a gurin, Mama tana ta salati ita ma su Aunty Fatima suna tayata. Da sauri Inna tazo ta wuce ni ta shiga dakin da Ummah take sai kuma ta sake fitowa da sauri ta hada kanta da bakin kofar tana kuka kamar ranta zai fita. Tunda nake a lokacin ban taba ganin Inna cikin tashin hankali irin na yau ba.1 Muryar yaya ladi na jiyo ta shigo gurin. “Innalillahi wa inna ilaihir rajiun. La haula wala quwata illah billah. Wayyo Usumanu wayyo Aliyu, yanzu aka kira ni akace sunyi hatsari an kawo su nan. Ya jikin nasu? Ya kuke ta kuka haka?” Kowa ya kalleta sai dai ya kara kukansa, ta rike kafada ta “Halima? Ina marasa lafiyan suke? Ina Zainabu kuma? Ya banganta anan ba?” Nurses ne su biyu suka zo suka kamata suka jata gefe, duk suma a diririce suke suna yi mata magana, bana jin me suke cewa amma can naji ta saka wani kuka mai ban tausayi sannan ta wuce mu da sauri ta shiga dakin da Ummah take. Alhaji Babba ne da kawu Isa suka shigo gurin, Alhaji Babba yana fada “menene hakan duk kun cika asibiti da koke koke? Kukan zai dawo dasu ne? Kun kuma san babu kyau yiwa mamaci kuka ko? Fatima ki riko yaran ke kuma Hafsa ki kamo Amina mu zamu taho da gawawwakin ayi musu wanka ayi musu suttura tun kafin magrib tayi”. Wannan maganar tasa ita ta dawo dani cikin hayyacina, lokaci daya naji reality din mutuwar ya doke ni. Na juya da sauri ina kallon kofar dakunan da gawawwakin suke. “Baffa!!” Na fada da iyakacin karfina “Sadauki!! Ummah” Aunty Fatima tayi saurin rufe min baki na da hannunta tace “kul Diyam, ba’a yiwa mamaci ihu”. Sai na mayar da kaina jikinta na kwanta na rufe ido ba tare da na sake cewa komai ba. Nasan dai mun shiga mota sannan mun fita, sai kuma naji mun shiga gida mun shiga daki an zaunar dani akan kujera. Sannan ne na bude ido ana ganni a palon Inna, Asma’u tana zaune kusa dani tasha kuka ta koshi, ina jiyo tashin sautin kukan Ummah sama sama amma ban juya ba ballantana in kalli inda take. STORY CONTINUES BELOW Muryar Alhaji Babba naji ya shigo gidan, ya daga labilen palon Inna yace “a dauke carpet din palonsa sai muyi masa wanka a can” na runtse idona ina so hawaye ya fito min amma babu. Muna nan zaune sai muka ji hayaniya kuma, muryar Alhaji Babba “ku fita da ita daga gidan nan, ai tun sanda ya aure ta mun gaya masa babu mu babu ita, dan haka yanzu ma babu mu babu ita” sai muryar yaya ladi tana kuka. Ji nayi kamar in tashi in shake shi, how dare he said that a ranar da Baffa ya bar duniya? A ranar da Ummah ta bar duniya?” Rigima sosai har makota suka fara taruwa, sai ga dattijon mutumin da har yau yaya ladi take gidan sa yazo yace “a gidan aurenta za’ayi mata suttura kamar kowacce matar aure, kai kuma baka isa ka hana ba in kuma zaka iya to ka dauko yan sanda” ganin mutane suna ta kallonsa accusingly ya saka Alhaji Babba ya ja baya ya bari aka shigo da gawar Ummah. Na tambayi kaina to ina Sadauki kuma?1 Tare akayi musu suttura, shi a palonsa ita a nata, sannan aka zo aka fita dasu ta gabanmu a tare. Na bi su a baya nayi musu rakiya har bakin gate sannan na tsaya ina kallo aja jera gawawwakin su akayi musu sallah a tare aka dauke su zuwa gidan su na karshe. Na koma gida ina tafi ina hada hanya. A tsakar gida na durkusa a cure a guri daya ina kara tambayar kaina ina Sadauki? Ji nake nima inama dai mala’ikan mutuwar zai zo ya hada dani. Mama ce tafito ta ganni a gurin, sai ta dauko tabarma ta shimfida mana muka zauna ta jani zuwa cinyarta na kwanta. Anan mukayi sallar magrib, sai ga yaya ladi ta fito tazo inda nake ta shafa kaina tace “sannu Halima, Allah yaji kansu yayi musu rahama, shi kuma Aliyu Allah ya bashi lafiya” na dago kai da sauri na ina kallonta sai naji tace wa Mama “zan koma asibiti inga halin da yake ciki” Mama tace “to Allah ya jishe mu alkhairi” nace da Mama “waye a abibitin?” Tace “Sadauki mana” naji wani abu mai nauyi daya tokare tun daga zuciyata zuwa makogwarona ya janye, numfashi na ya fara fita da sauri nace “Sadauki? Ba tare suka mutu ba? Na dauka ko an kai gawarsa wani gurin” ta rike hannuna tace “Sadauki bai mutu ba ya samu buguwa ne a kansa shi yasa doctors sukayi sedating dinsa. Baffanku kuma tun kafin a kawo su asibiti ya cika, Ummah kuma tashin hankali ne ya saka ta yanke jiki ta fadi, jininta yayi mugun hawan da cikin yan mintina ta mutu” naji wani abu yana sauka daga kai na zuwa kafafuwana. Sadauki is alive. Then there is hope for me.2 A daren ranar banyi bacci ba, muna kwance ina rungume da Asma’u da take ta jera ajjiyar zuciya saboda kukan da tasha, sai da naga ta samu bacci mai nauyi sannan na zame jikina na fita palo, Inna na gani zaune akan sallaya ta rufe fuskarta da hannayenta tana kuka a hankali, sai na wuce ta na shiga toilet nayo alwala nafito nima na tayar da Sallah, yau shine daren Baffa da Ummah na farko a kabarinsu kuma nasan suna bukatar adduoin mu sosai. Har na idar da sallolina Inna tana kuka, sai na kwanta akan sallayar na dora kaina akan cinyoyinta sannan nima na samu kuka yazo min. Washegari yan Kollere suka zo, gida ya cika taf ana ta karbar yan gaisuwa amma babu wanda naji ya kuma maganar halin da Sadauki yake ciki, yaya ladi ma kuma ban kuma ganinta ba duk kuwa da cewa jama’ar Ummah suna ta zuwa gaisuwa suma. Inna dai kam tayi kuka kamar idonta zai fita kowa yashigo gidan sai ya tausaya “uwargidan sace kuma uwar yayansa”. Sai dare na ajiye tsorona na tambayi Inna “Inna ya jikin Sadauki kuwa?” Ta kalle ni ta dauke kai, “ban sani ba” ta fada tare da cigaba da jan carbin ta. Ranar da akayi sadakar uku ranar munga mutane, dan ko ranar mutuwar gidan baiyi wannan cikar ba, ranar yaya ladi tazo akayi adduoi da ita, sai da aka gama ta tashi zata tafi na bita a baya nace “yaya ladi ya jikin Sadauki?” Ta juyo ta kalleni tace “da sauki Halima, jikinsa da sauki” sai ta juya tayi tafiyarta. Alhaji Babba ya shigo bayan an gaishe shi yace “Amina zamu saka a gyara muku guri a can gidana, idan anyi bakwai sai ku koma can ku zauna ke da yara saboda nan din ba zaku ji dadin zama ba ku kadai. Allah ya ji kansa” akace ameen sannan akayi masa godiya ya tashi ya tafi. Zuwa yamma I have taken all I can, ji nake nima kamar nawa jinin zai hau irin na ummah nima in mutu, an gama adduoin kuma an mayar da gidan kamar gidan biki sai ciye ciye ake da hira da dariya. Na shiga dakin inna na bude jakar ta na dauki kudi na saka hijab dina na fixe ba tare da kowa ya lura ba. Adaidai na hau direct na tafi asibitin malam, naje har emergency room nayi sa’a kuma visiting hours ne dan haka na tambayi nurses Aliyu Usman Kollere nake nema sai suka ce inje aminity room 3. Da sauri na na tafi, zuciya ta tana jin kamar zata kara sauri tayi gaba ta riga ni shiga dakin. A kwance na same shi da drip a hannunsa daga alamar har yanzu allurar baccin akeyi masa, fuskarsa da dan fada kuma tayi haske, kansa a nade da bandage. Babu kowa a dakin sai shi kadai. Na karasa ciki inajin wani irin tausayinsa yana saukar min, na zauna a gefen gadon na kamo hannunsa nayi intertwining fingers din mu. Ya dan bata rai sai kuma yayi blinking ya bude jajayen idonsa yana kallona, ya kakalo murmushi mai nuna yana jin ciwon yinsa yace “you are here” na gyada kai nace “am here” yace “waye ya dauko ki daga school?” nace “Abban su Rumaisa” yace “good” mukayi shiru kuma can sai yace “ya jikin Baffa?” Gabana naji ya fadi na zuba masa ido, wato bai ma san abinda yake faruwa ba? Ya sake cewa “yaya ladi tace min ya samu karaya ne shine aka kai shi asibitin kashi. Shine kuma duk kuka tafi gurinsa ko?” Ya sake kirkiro murmushi “dama nasan Ummah tafi son Baffa akaina shine ta tafi jinyarsa ta barni, in kin koma ki gaya mata nayi fushi, nima tawa matar tazo ta ganni” na cije lebena ina danne kukan da yake so ya kwace min, sai yace “don’t cry please, everything will be alright”1 Na gyada kaina nace “yes Sadauki, everything will be alright. Ka koma kayi baccinka” ya lumshe ido yana kara rike fingers dina a cikin nasa. Mun jima a haka ina kallon fuskarsa ina jin wani irin yanayi yana kara shiga ta a kansa, nayi kokarin zare hannuna daga nasa sai ya kara rikewa a hankali cikin bacci yace “don’t leave me please, stay with me please” sai ya dora hannayenmu akan kirjinsa sannan ya dora daya hannun ya sake rike wa.1 A haka yaya ladi ta shigo ta same mu, ta tsaya tana kallon mu sannan ta girgiza kanta tace “an mutu an bar muku gadon wahala”.4

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page