NI DA PRINCE CHAPTER 2

NI DA PRINCE CHAPTER 2

Salmah kam suna tafiya gun ta tsugunna ta shiga maida numfashi ta dade ahaka kafin ta mike ganin mutane tai agun suna kallanta ta dauke idanta tare da kallan agoggon hannunta, gani saura 15 mins su shiga next lectures gashi ko sallah batai ba yasa tai saurin wucewa, tana dubawa ko zataga zee. + Salman yauma sai magrib yashigo gun mai martaba ya wuce, ya dade kafin sarki yabashi izinin shiga, cikin nutsuwa ya shiga mai martaba yakalli fadawan gun yace kubamu guri suka amsa tare da mikewa. Sarki ya kalli salman yace matso nan, cikin sanyin jiki salman ya matso kusa da sarki tare da sake gaidashi ya amsa fuska a d’aure, sannan ya cigaba haryanzu baka da aiki sai tsokanar mutane a makarantar ko? Salman yai kasa dakai Yace Ranka ya dade ba…….. Cikin b’acin rai sarki ya katseshi yace anfad’ama duk abinda kake a makarantar bana sani? Ka kasa maida hankali kai karatu sai bin kawayen banza da wulakanta mutanena, sannan kana kallo kaninka Nazir yai aure amma kai banda shegantaka bakada aikin yi😠. Salman kam idansa ya kad’a yai jaa batare da sarki yajira amsarsa ba yace wato yanzu rashin mutuncin ka ya kai wani mataki daka fara wulakanta mata ko? Salman yad’ago cikin mamaki sarki yace ina nan ishaq yazo yasanar dani ka cirewa wata hijab a makaranta ko karya aka ma? Gaban salman ne ya fad’I amma yadaure yace a’a, sarkj yace nagode salman kacigba da bakanta min rai. Salman yai shiru zuciyarshi na rayamai kabada hakuri, can wata zuciyar tace ka manta me suka ma? Jin bashi da niyar bada hakuri yasa sarki yace dama kai bakasaba yin laifi kabada hakuri, tashi Kaban guri, ga mamakin sarki gani yai salman na kokarin mekewa ranshi yakara b’aci yace kakuma tabbatar ka fito da matar aure nan da wata 1 dan bazan d’auki iskancin da kakeji dashi ba, salman yace Abba wata 1 ai……dasauri sarki ya katseshi yace wlh ka fita daga idona ka sani bana magana 2 dan haka ka kiyaye. Salman yai tsaye yakasa magana kuma ya kasa wucewa, wani bawa ne ya shigo yace ranka ya dade *Ishaq* na neman iso, sarki ya d’agamai kai alamar yashigo, dasuri ya juya, bai dade da fita ba ishaq ya shigo ganin salman yasa yasaki wani murmushi😏 tare da tsugunnawa ya gaida sarki, cikin sanyin murya ya amsa ishaq yace salman yanaganka a tsaye? Salman ya kalleshi sannan ya d’auke kai tare dacewa sarki nabarka lafiya, sarki bai amsaba salman kam da sauri yai waje. Ishaq yace Abba Allah yasa dai d’an kanin nan nawa ba laifi yama ba? Inkuwa laifi yai ina bada hakuri a maimakon shi, sarki yace kyale sokon yaro zanyi maganinsa, sannan kafad’ama fulani ta fara nemo yarinyar dazai aura dan in bai kawo wace zai auraba nan da wata 1 to ba shakka aure zan mai. Ishaq yace to ranka ya dade, sannan shima ya fita zuciyarshi fal farinciki lalai yau sunada karamin party. Salmah kam tagama aikin gida takoma d’aki ta d’auko littafinta kenan taji yaro na sallama sai dai kafin tafita goggo ta fita tace yaro ya akai? Yaron yace wai ana sallama da salmah inji Muftahu tace muftahu? Wanne kenan? Yace muftahu mai babban shagon can tace au toh nagane, je kace gatannan yanzu zata iso, yace to tare da yin waje. Goggo ta taho dasauri tana washe baki takaraso dakin salmah dake zaune duk taji abinda sukai da yaron, goggo tace tashi ‘yar nan alkairi yasamemu😁 salmah tace name fa? Goggo tace gidan ku kina nufi bakiji me mukai da yaron can ba😠? Salmah tace au nad’auka sa’a yake nema( kanwarta da akai aure wata 4 dasuka wuce). Goggo tace kaji min ‘yar rainin hankali sa’ar datai aure za’azo nema? Tace kin manta ne goggo kwanaki…..ta katseta rufemin baki yar iskar banza to ke ake nema kuma muftahu ne mai katan shagon can salma tad’an tabe baki tace goggo kinsan fa ni yaya kamal nakeso, goggo tace lalai dalla rufemin baki kamalo ba kamalu ba kinsan Allah salma😠 tashi kafin na fasa miki baki. Kasa tai dakanta tare da jan hijab dinta tai waje tana turo baki. Muftahu kam ansha shadda da hula ga motarsa Civic ya ajiyeta yana tsaye ya juya baya, yanajin motsin kofa ya juyo yana murmushi takalleshi tare da d’auke kai tace ina wuni? Yacw lafiya lau *Salmat*😊 tace salmat? Yace eh mana ni haka zan dinga kiranki ta juya kai tare da yin shiru, yace salmat plz nazo da magana mai girma hope zaki fahimceni? Ta juyo tare da kakaro murmushi tace am sorry muftahu nasan kasan inada Wanda zan aura. Muftahu yace salmat, kamal ba baida niyar auranki, inba haka ba shekararsa nawa acan? Kaf ‘yan layin nan gulmar abin suke mahaifinki yabarki kina jiran d’an uwansa bayan kila shi yamanta daku. Salma kam ranta yagama b’aci batare datace komai ba tai hanyar gida ta bude kofar tai dakin ta da sauri tafad’a kan gado ahankali hawaye yafara zubo mata. .Tanajin motsin umma a waje amma abin haushi ko tazo ta tambayeta meya faru, Abbanta nadawo wa tamike da sauri taje tagaidashi umma da goggo nazaune bayan ya amsa, goggo tace dazun korar muftahun kikai shima? Salma tai kasa dakai, Abba yace wai ke Basira meyasa bakyaji? Na dade da fad’a miki bana san kina takurama salmah, ko kin manta matar da kamal ce? Tace yahkuri Alhaji ganinai tanata zama a gida ba kamal ba labarinsa.+ Abba yace kada ki manta yanda muke da mahaifin kamal mu 2 ne a d’akin mu shine yayana kuma baki isa kisa zumuncin mu yai rauni ba, Goggo tace Allah yabaku hakuri, Alhaji nad’auka salma kamar ‘ya take a gurina tunda nina raineta, Allah bai bani ‘da ba….. Da sauri umma ta katseta tace Goggo kidaina wannan maganar, sannan takalli salma tace ke kuma tashi ki bamu guri, salma ta mike duk jikinta yai sanyi tai d’akinta. Umma takalli goggo tace kiyi hakuri hajiya, Alhaji bai kamata ka mata fad’a agaban wannan ‘yar ba, Alhaji yace ai basira ce na dade ina mata magana bata ji, amma yanzu abar maganar nan zan kira kamal inji menene ya tsayar dashi dan ni kaina nasan gaskiya basira take fad’a, yana kai nan yai waje, umma tashiga ba goggo hakuri. Yau salma na zaune a class suna d’aukan lectures hankalinta nakan karatun da akeyi har malamin yagama koyarwa ya fita zama tai a theater room din tana duba littafinta. Ganin mutum tai ya zauna a saman desk din datake ta d’ago cikin mamaki tare da matsawa, mamaki ne ya kamata ta zaro ido sannan gabanta ya fad’I ta mike zata wuce hannu yasa ya fizgota tare da maidata inda take yace ‘yar gidan Amadu ina zaki batare da uzinina ba? Tace izini? Yace eh ko kinfi karfi? Tai shiru tare da ture hannunshi tace wai menene dalilinka nasan shiga harkata? Yace I won’t leave you har sai kin janye maganarki na tausayi daga kaina, in kuwa ba haka ba I promise you sai kinyi dana sani mai karfi. Salma tai wani murmurshi😏 duk daba ganinta yake ba tace in naki fa?yace then mark my word😠, tace prince I am not afraid of u, yace u are not? Ta daga kai alamar yes yai murmushi yace then I will have to make you, yana kai nan yai waje. Wata doguwar ajiyar zuciya ta rike hannunta dake rawa murya taji cikin sanyin ance salmah kiyi hakuri ki kuma ba salman hakuri, tad’ago cikin mamaki Najib tagani tace mena mai? Yace bakiyi komai ba amma salman ba abinda yatsana irin yaji ance yana ba mutum tausayi, ya juya ya fita, ta bishi da kallo tare da runtse ido tace yazanyi yaya kamal? 😞 Batafi 1 hr ba zee tashigo dasauri tace salma me kikayi? Salma tace name fa? Tace an kafe sunan ki a notice board an baki suspension na 2 weeks na dasauri ta mike cikin kidema tace suspension? Ni *SALMAH AHMAD MOHD* ? Zee tace wlh sunan ki akasa tace menayi? Tafad’a hawaye na zubo wa daga idanta tace akan me? Zee tace kema kinsani ai, salma tace I have to go an ask dan salman yace a bani suspension dan ni ba ‘yar kowa bace sai abani? Zee tace ki rufa mana asiri kar kisa a koreki daga skul din gaba daga, hannu tasa akai tafara kuka zee ta dafata tana rarrashinta. Dakyar ta tsayar da hawayenta tare da d’aukar jakarta tace zee na wuce gida kuma plz karki fad’a a gida abinda yafaru tace to salmah. A hankali take sauka daga steps din gun zuciyarta nakan tunanin abinda ke faruwa har ta iso titi tana jiran mota. Motace tazo kusa da ita tai parking tad’ago jajjayen idanunta, ahankali aka zuge glass d’in bayan motar, tana kallan wanda ke ciki haushi da wata muguwar tsanarsa suka mata yawa tadan matsa daga gun ahankali motar takara matsowa gun salman yace sorry limamiya I really pity you☹yanzu what can we do🤔? Jitai kamar tasa ihu d’an bakin ciki kalamansa amma me? Daurewa tai tace u don’t have to pity me bawani abin bane dan anban suspension just take it as nasamu rest daga ganin mutanen dana tsani gani tana kainan ta matsa tafara tafiya da kafa. Salman yai kwafa haushin kalamanta suka kamashi yakalli driver dinsa yace dalla wuce mutafi yace to ranka ya dade. Salman na isa gida yana fitowa daga mota wanI bawa yazo yace sarki na nemanka, yace to tare dayin hanyar fadar sarki. Zaune suke su 2 sarki ya kalleshi yace ka kyauta da wulakantani dakai salman yace Abba bangane ba? Yace ai ni ka wulakanta tunda bakaji kunyar sawa abawa d’aliba suspension ba wlh salman sai kasan kayi kuskuren b’atamin suna dasauri ya d’ago yace Abba yarinyarce fa…….yace just keep silent ka kuma bani guri sanda ishaq ya fad’amin zancen nan I thought karya yakema amma yanzu na tabbatar dan haka mike kaban guri😠. Cikin sanyin jiki salman ya mike yana fita yai hanyar dakin ishaq sai dai yana tsaye daga waje yanajin shewar su ishaq da kannansa maza 4 suna murna kowa nacewa kai yarima ka birgeni, ishaq yace ai na dade da fad’a muku salman d’an karamin kwarone a gurina, ragowar sai jin jina mai suke ahankali ya juya yai bangarensa kansa na sarawa yana shiga d’aki ya zube ya shiga murkususu rike da kirji da kai dakyar yasha magani yashiga karanta *INA LILAHI WA INA ILAIHI RAJI’UN* ahankali yafara jin relief. Kuka sosai takeyi yi abinda ya kara tunzurata umma na zaune a waje tana goge kubewa amma ko ta tambayeta, ta dade tana kuka ganin ba mai lalasarta yasa ta mike tare da fitowa tad’au kwandam wanka tai toilet umma ta bita da kallo. + Qur’ani ta d’auko tashiga karantawa ahankali tafara jin sanyi na ziyarta zuciyarta, jin motsin Abba yasa ta fito da sauri takarasa tare da mai sannu da zuwa yai murmushi tare da cewa ‘yar Abba meya sami idanunki? Tai kasa dakai yakamo hannunta yace muje inji matsalar ‘yata tunda duk gidan ba mutanen da zasu tambayeki. A falo suka zauna yace menene salma? Tace Abba aran wayarka nakira yaya kamal yace to naji amma fad’amin menene? Tace bakomai Abba banajin dadi ne, yace ayya sannu ko muje asibiti? Tace A’a Abba naji sauki yace to sannu sannan yamika mata wayarsa ta amsa tare da mikewa tabar falon. D’aki tashiga tareda yima kamal flashing sau 6 tamai amma abin haushi bai biyoba, daga baya tai deciding ta kirashi sai dai shima no answer tadanyi tsaki tace kila yana wanI sabgar ne☹…..nace hmmm. Ishaq ne zaune gaban sarki, sarki ya kalleshi yace nasani ishaq kaimesan d’an uwankane, ishaq yai kasa dakai cikin sanyin murya yace Abba yazamuyi da matsalar yarinyar daya kora daga makaranta? Abin na damuna😞, gashi mutane an fara gulmar abin ina tsoron kar hakan yajama salman tsana daga mutane😕. Sarki yace ni kaina abin na damuna amma bari insa akira waziri inji yazamuyi, ishaq yai murmushi😏 ba b’ata lokaci sarki yasa akira waziri nan ishaq yafad’amai abinda ke faruwa. Waziri yai shiru can yace yarinyar ya take? Ishaq ya shiga yin bayani akan binciken dayasa ayi akan salma da kyawawan halin yarinyar, waziri ya nisa yace mezai hana muyi haka? Sarki yace me? Mu nunama mutane bawai korarta yasa akai ba dalili ba matar dazai aurace yakesan abata lokacin shirye shirye tahakan ne kowa zaisan salman ba mutum ne mara mutunci ba mai wulakanta mace, sarki yai shiru yana tunani. Ishaq kam baiso ba amma saboda san ya wulakanta salman jin yarinyar ‘yar talakace ba jinin sarauta ba ko ‘yar masu kudi yasa yace waziri ka kawo shawara Abba ya kagani? Sarki yace kasa a kara bincike akanta waziri banaso salman ya auri matar da bazata rufamai asiri ba waziri yace to ranka ya dade angama, ya mike yai waje. Salman kam yau weekend bacci yake sosai sai azahar yai wanka ya fito, al’adar gidan ne aje gaida duk matan gidan da ranar asabar hakan yasa salman ya fito bangaren hajiya karama(Amarya)yafara zuwa, bawani shiri sukeba gaisawa kawai sukai ya mike ya fita ta bishi da harara itakam gadarar yaron na bata haushi gashi ita d’anta namiji shekararashi 7😠. Bangaren Hajiya babba yaje(ta tsakiya) sun gaisa cikin sakin fuska sannan ya fito saidai yasani itama ba sanshi takeba. Yakarasa bangaren fulani itakam yasan halinta sarai amma ita gani take baisan komai ba cikin farinciki tasa aka damomai fura tace salman sha fura dan musamman saboda kai nasa aka dama yai murmushi yace nagode fulani tace sai kace wani bare? Kaifa d’ana ne yace haka ne😏. Bayan ya fito yakoma d’akinshi ya kwanta tare da runtse ido kaf ‘yan gidan yasani ‘yan uwansa mata 2 ne kesansa kuma sunyi aure sai yara dabasusan rayuwar gidan ba. Shima kuma kallan kowa yake tunda haryau bai manta abinda sukai mai ba yana yaro har sarkin kuwa☹.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page