RAMUWAR GAYYAH CHAPTER 1

RAMUWAR GAYYAH 
CHAPTER 1

_Da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai…._
~~~”Wannan shine abinda nake son kiyi kamar yadda nafada miki abaya, hakika ummulkhair nadade ina burin Allah ya bani ya mace domin wannan burin nawa ya cika amma Allah bai baniba sai yanzu, ina fata zaki dage ki zama silar cikar Burina kamar yadda nadade ina fata,+
Idan kikayi haka kin gama yimin komai kuma zanyi alfahari dake sannan koda na mutu to zan mutune da farin cikin abinda kika yimin, ina fata zaki mayar da hankali kan abinda natura ki sannan banda kula kawayen banza da samari barkatai idan kikayi haka to lallai ranki zai baci, Allah yayi miki albarka ya baki nasara”
Idonta fal da kwalla ta dago tana duban mahaifin nata wanda ke kishingide akan kujera fuskarsa cikeda walwala da annuri,
“Abba nayi maka alkawari zan zama silar cikar burinka kamar yadda ka dade kana fata sannan zanyi abinda ka turani batare da an samu kuskure ba”
Sai alokacin mahaifiyarta dake zaune agefe tayi magana itama idonta dauke da kwalla,
“Yanzu Alhaji abinda kayi ka kyauta kenan? Ka dauki yarinya karama yar shekara 22 katurata har nan da garin Kano kawai dan kanada buri acikin ranka kuma ka dage sai burin nan ya cika..”
Katseta yayi ta hanyar cewa “ya isa haka hajiya fati, ai dai ‘ya tawace ko? To ki barni na zabar mata abinda naga yafi cancanta da ita, tun shekaru 30 da suka wuce nake burin Allah ya mallaka min ya mace amma bai baniba sai yanzu, yayunta duk samarine maza d’ai d’ai har hudu, to yanzu tunda lokaci yazo dama ta samu ai sai ayi amfani da ita”
“Gaskiya Alhaji nidai ban goyi bayan ka tura min yarinya wata uwa duniya har kano ba kawai dan kana son cikar burinka”
“Mama kiyi hakuri babu komai insha Allah bazan yi abinda duniya zatayi Allah wadai dani ba, zan kare kimar gidan nan da mutuncinsa abinda abba ya tura ni shi zanyi bazan taba yin wani abuba sabanin haka” ummulkair ta fada tana share hawayen idonta,
“Allah yabada sa’a yayi miki albarka, maza ki tashi kije kar kuyi dare, Allah ya kiyaye hanya” mahaifinta yace da ita,
“Ummulkair Allah yabaki sa’a” mahaifiyarta tafada tana goge hawayen dake kwarara akan idonta,
Tashi tayi taja katuwar jakar kayanta (trolley) tafita tana share hawayen idonta,
Awaje ta iske yayanta wanda take bi yana jiranta, kayan ya karba ya saka acikin Mota ta shiga ta zauna suka lula,
Tunani take yi aranta domin wannan shine karo na farko da zataje garin kano kanon ma wai jami’ar bayero,
“Allah kabani sa’a” tafada acikin ranta tana kallon hanyar da zata fitarsu daga garin bauchi zuwa kanon dabo.
Tafiyar awa ukuce ta kaisu cikin kano lokacin karfe 3:30 na yamma atsakiyar makarantar kusa da hostel din da aka tanada domin mata yayanta ya ajiyeta yafara kokarin fito mata da kayayyakinta,
Tana ganinsa ya juya zai tafi take tasa kuka kamar yarinya ko saurarenta baiyi ba yayi tafiyarsa kasancewarsu sako da sako,
Kayanta tafara dauka tana kaiwa cikin hostel kofar dakin da aka bata, sai da tagama kwashewa tsaf sannan ta shigar da kayan cikin dakin wanda ya kasance nata ita daya domin bata son kazanta wannan dalilin ne yasa zata yi zamanta ita kadai,
Shisshirya kayan tayi ta mike akan gadonta ta kwanta ga wata irin yunwa da takeji gashi babu wanda tasani,
“Gaskiya bazan iya girki yanzu ba bari kawai naje na siyo abinci awaje” tafada acikin zuciyarta, mikewa tayi taja hijabinta tasa ta dauki yar karamar jakar hannunta ta fita,
Babu inda tasani dan haka taketa waige waige gashi ranar weekend ne makarantar babu dalibai da yawa,
Wani shago ta hango dan haka ta nufi can, wasu samari guda uku tagani suna zaune akofar shagon,
“Dan Allah me da me ake sayarwa anan?” Tafada tana kallonsu,
Shiru suka yi mata babu wanda ya tanka,
“Bayin Allah magana fa nake yi muku”
“Ke bar nan” wani saurayi acikinsu yafada fari dogo mai saje,
“Ba zaki bar nan ba sai nataso?” Yasake fada yana kallonta,
Da sauri tafara kokarin barin wurin har tana hadawa da gudu, dariya suka saka gaba dayansu tareda Tafawa,
“Sai 3 pointer” suka fada suna ihu,
Hostel takoma tana tunanin to shi wannan waye a makarantar? Itadai bakuwa ce bata da masaniyar ko waye shi, dambun naman da mamanta ta yi mata ta dauko tafara ci da biredi har ta koshi,
Zama tayi jugum tana jin hayaniyar mutane har dare yayi, atsorace ta kwanta adakin bayan ta kulle, baccine ya dauketa sakamakon gajiyar da tayi.
Tun asuba ta tashi tayi salla ta dauko alqur’aninta ta bude ta karanta har gari yayi haske,bucket ta dauka taje ta debo ruwa ta wuce bathroom tayi wanka ta zo ta shirya,
Ruwan zafi ta jona a heater ta hada tea ta saka kayanta riga da zani da katon hijab taja dakinta ta kulle ta fita,
Koda ta fita ganin makarantar tayi acike sabanin jiya da babu mutane da yawa,
“Yau ake yinta” tafada azuciyarta sakamakon bata san takamaimai wurin da zata samu yan ajinsu ba kuma babu wanda tasani aciki,
Wasu samari ta hango su hudu asaman wata mota daya daga cikinsu ya bata baya yana sanye da kananan kaya yana taje sumar kanshi da cumb,
“Ohh samarin jami’a kenan” tafada aranta tareda dosar wurin da samarin suke.
🅿herty novels
Ummi Shatu👌🏻
My wattpad Phertymerh1
[06/02, 11:10 a.m.] Pherty🎤👯: *RAMUWAR GAYYA…!*💘
_Love story 50,50_
_*UMMI A’ISHA*_
_with_
*_PHERTYMAH XARAH_*
*_2_*
~~~ Sallama ta yiwa samarin tareda cewa “dan Allah tamabaya nake, inane wurinda yan level 1 suke lectures?”
“Ke, yauma dawowa kikayi? Wai ke mu sa’anninki ne?” Wani saurayi ya fada sai da suka hada ido sannan ta gane ashe shine saurayin jiya,
“Kuyi hakuri” tafada atsorace zata juya ta tafi,
“Ina zakije? Zo nan” taji yafada da karfi,
Dawowa tayi ta tsaya, “wanne course kike karantawa?”
“Mathematics” ta bashi amsa,
“Ya sunanki?”
“Ummulkhairi” ta sake bashi amsa,
“Ungo jeki ki siyo min lemo, kuma indai baki kawo min ba kika gudu to zan nemoki duk inda kika shiga”
1000 ya zaro ya bata ta karba ta wuce,
Capteria ta nufa acan ta siyo masa lemon ta dawo duk hankalinta atashe yake domin bata san dalili ba kawai tsoronshi taji tana yi,gashi bata san cewa a jami’a kowa gashin kansa yake ci babu sawa babu hanawa ba, tayi zaton irin secondary school ne akwai seniority,
Wurin da suke ta karasa takai masa lemon,
“Ke wayasa ki siyo min fanta? Saboda ke villager ce ko? Karbi ki je ki canjo”
Hakuri tafara bashi “dan Allah kayi hakuri dan Allah”
Fashewa da dariya taji abokannshi sunyi sannan ga dalibai sun zagayesu suna yi mata dariya kun san jami’a komai abin kallo be kuma abin dariya ne, nutsewa ne kawai batayi ba dan kunya, kudin da lemon ta cilla masa ta juya idonta duk ya ciko da kwalla,
Wata tagani sanye da hijab nan budurwar ta kamo hannunta,
“Yar uwa me yakaiki wurinsu wadancan yaran marassa mutunci?”
Kwallar idonta ta goge tace “wallahi ban sansu ba daga zuwa tambayarsu wurin lecture dinmu shikenan fa harda aikena”
“Yi hakuri to share hawayenki, wanne department kike?”
“Mathematics”
“Level 1?”
Kai ta daga mata alamun ehh,
“Ayya department dinmu daya dake amma gaskiya naji dadi saboda dama ni kadai ce mace kullum atakure nake dama kuma ance mu biyune mata wadanda muka nemi course din”
Murmushi ummulkhairi tayi “kin san ai maths bashida farin jini majority din dalibai sun tsaneshi saboda akwai caja brain, nima fa da ban iyaba lokacin da ina primary school sai da naje secondary school sannan nadage na iya daga karshe har quiz nake zuwa na maths”
Dariya budurwar tayi “ah lallai ashe daya muke, wallahi nima yanzu bazan iya theory ba saboda tsananin sabon da nayi da lissafi”
“Koni gaskiya yanzu bazan iya theory ba nafi ganewa in zauna inyita Tarawa da debewa” ummulkhairi ta bata amsa,
“Allah Sarki ya sunanki?”
“Sunana ummulkhairi”
“Ayya nikuma sunana alawiyya”
“To inane wurin lectures din?” Ummulkhair ta tambayeta,
“Canne new side fa, ai abun namu muhimmi ne dan yau ma bamu da lecture sai 12”
Zaro ido ummulkhair tayi “kai amma akwai damuwa wallahi ni ai nayi tunanin tun 8 ake fara lectures din”
Hannunta alawiyya ta kama tana murmushi, “zo muje admin block kiga time table dinmu saboda nima bani dashi”
“Yawwa to muje”
Tafiya suke suna shan hirarsu tamkar dama can sun san juna ko kuma sun dade suna kawance, har suka karasa admin block din wurinda aka kafe time table na kowanne department,
Biro da dan karamin memo ummulkhair ta ciro ta fara kwafar musu time table din tana murmushi,
“Alawiyya wai wannan gayen na dazu wanene?”
“Meyasa kike son sanin waye shi?” Alawiyya ta tambayeta tana kallon fuskarta,
“Kawai ina son sanine domin inada wani buri akanshi” ummulkhair tace da ita tana rubutu ajikin memo dinta,
“Buri? Wanne irin buri ummulkhair? Ko dai kin kyasa ne?”
Murmushi ummulkhair tayi wanda har biro hannunta yana kokarin subucewa ya fadi kasa,
“Ko kadan bai yimin ba saboda na fuskanci dan rainin hankaline”
“Hmmm ummulkhair kenan ai duk makarantar nan kowa yasan three pointer saboda tsabagen kwakwalwarsa, yana ja fiyeda yadda bakya tunani shiyasa ma kika ga yana rashin mutuncinsa son ransa saboda yaga yanada ilimi, ni kaina yaron yana burgeni domin yasan abinda yake yi yana zama yayi karatu kuma bai taba samun carryover ba tun farawarsa har kawo yanzu, haka ake son mutum bawai yazama dan iskaba amma brain empty, shikam wannan gayen ya iya wulakanci amma kuma yasan me yake yi sannan yanda kika gansun nan shida friends dinshi to haka suke duk school dinnan kowa yasan basa kula yanmata.”
“Alawiyya kenan nifa duk wannan yabon da kika dage kina yi akanshi ba burgeni zaiyi ba”
“Dama nasan bazai taba burgeki ba ummulkhair tunda three pointer yasaki kuka, amma kisani ni ina fada miki ne abinda na sani agame dashi, sunanshi na asali *SAWWAM MUSTAPHA* ance shi kadai mahaifanshi suka haifa gidansu yana nan a unguwar sharada phase 2, kamar yanda na fada miki yaron nan yana ja domin baya wasa da karatu, shine president na makarantar nan domin lokacin da akayi zabe dalibai duk shi suka zaba”
“Yayi kyau” ummulkhair ta fada tana kokarin saka biro dinta da memo acikin jaka.
🅿herty novels📚
Duniyar makaranta👌🏻
[05/02, 3:24 p.m.] Baby aysha: *RAMUWAR GAYYA…*💘
_Love story 50,50_
*_UMMI A’ISHA_*
        _With_
_*PHERTYMAH XARAH*_
  *_3_*
    *H*annun ummulkhairi alawiyya ta kama suka fara kokarin barin admin block suka nufo cikin makaranta,
“To yanzu ina za muje?” Ummulkhairi tace da alawiyya,
“Muje kawai mu samu wuri mu zauna mu huta kafin lokacin shiga lecture yayi”
“Ok to muje”
Tafe suke suna hira cikeda annashuwa har suka je karkashin wata bishiyar mangoro wacce aka girka wata bakar doguwar kujerar karfe a wurin domin hutawa, zama suka yi bisa kujerar alawiyya ta fara koyawa ummulkhair abubuwan da aka danyi lokacin da bata nan, sun shafe fiye da mintuna goma sha biyar awurin suna tattaunawa sai ga wannan gayen na dazu shida wasu mutum biyu har shi na uku,
“Ke baki san nan wurin wajen da nake zama bane?? Dalla malamai ku tashi ku bawa mutane wuri..”
Ko kallonshi ummulkhair bata yi ba taci gaba da latsa wayar dake rike a hannunta,
“Ke tun ranar da nafara ganinki na lura kema fa yar rainin wayoce, agidanku ba akoya miki bawa babba girmansa bane?”
Nan dinma shiru tayi kuma da alama bata da niyyar tanka mishi kamar yadda ya zata,alawiyya ce ta fara harhada littattafanta tana sakawa acikin jaka,
“Ummulkhair tashi mu tafi”
Sai a lokacin ummulkhair din tayi magana,
“Ina zamu tafi? Shi har ya isa yazo ya tashe mu daga nan? Babu inda za muje har sai lokacin da muka yi niyya yayi sai dai idan shine zai yita tsayuwar jiranmu..”
“K’arya kike yarinya ke baki isa na tsaya ina jiranki ba God forbid”
Murmushi ummulkhair tayi “ehh ai da yake kujerar daga gidanku ka daukota ka kawo nan shiyasa zaka hana kowa zama awurin sai kai”,
“Ummulkhair dan Allah ki rabu dasu kizo mu tafi”
Alawiyya tace da ita bayan ta kama hannunta tana kokarin mikar da ita tsaye,
“Ke wallahi idan baki bar wurin nan sai kinyi nadamar yin haka..” Yafada yana huci,
“Idan har ni banyi nadama ba to kuwa kai zaka yi nadama, nonsense kawai..” Ummulkhair ta fada cikeda jin haushi domin ita haushi yake bata,
“Ke ni kika cewa nonsense? Ni kika zaga? Ke har kin isa ki zageni?” Ya fada cikin daga murya tareda zabura yayi kanta zai daketa,cikin zafin nama abokanshi suka rikeshi suna bashi hakuri,
“Dan Allah ku sakeni na koya mata hankali..”
“Ku sakeshi dan Allah in yaso naga abinda zai yimin, kai ka isa ka dakeni ka zauna lafiya? Wallahi baka isaba domin ni yanzu babu wanda ya isa ya dakeni sai ruwan sama…”
“Wai ku sakeni mana bakwa jin irin maganar da yarinyar nan take fada min?” Ya sake fada a zuciya,
Abokan nashi basu sakeshi ba sai hakuri da suke bashi ita kuma ummulkhair sai fama da ita alawiyya take yi akan ta tashi su tafi subar wurin domin mutane har sun fara taruwa amma fur ummulkhair taki tashi tace babu uban wanda ya isa ya tayar da ita daga wurin,
“Ke ni kike zagi..?”
“An zageka din kai dan gidan uban waye da ba za azageka ba?”
Wata kara ya saki take ya kwace daga rikon da abokan nashi suka yi masa ya nufi kanta gadan gadan, aguje suka sha gabansa suka tattareshi, ganin haka yasa alawiyya jan ummulkhair ta karfi suka bar wurin yayinda sawwam in banda huci babu abinda yake yi,
Lokaci kadan idonshi ya kada yayi jawur ranshi in yayi dubu to ya baci saboda zagin da ummulkhair tayi mishi agaban bainar jama’a,
“Wallahi sai na koyawa yarinyar nan hankali domin babu macen da ta taba zagina sai ita…”
Fusgewa yayi ransa a bace yabar wurin ya nufi wurinda motarsa ke ajiye,
Yana zuwa ya shiga ya yi mata key azuciye ya fita daga cikin makarantar bayan ya tayar da kura wacce kai in ba sani kayi ba zakace sansanin yakine,
Yanayin yanda yake tukin ma kana gani kasan ransa a bace yake, ji kake k’uuuuuuu ya taka wani wawan mahaukacin burki sakamakon tsayarsu da danja tayi,
Duk mutanen wurin sai da suka razana saboda sunyi zaton wani aka kade, shi kuwa gogan sai furzar da numfashi mai dumi yake yana shafa sumar kansa alamun ransa ya gama baci,
Kamar zai tashi sama haka yayi lokacin da danja ta basu hannu, da wannan gudun na masifa ya isa gidansu dake unguwar Sharada phase 2,
Wani tangamemen gida ya shiga bayan yayi horn mai gadi ya bude masa, yana yin packing ya fito a fusace ya shiga cikin gidan, falon mahaifiyarshi ya shiga kamar zai ci tuntube saboda bacin rai,
Zaune ya sameta itada wasu yanmata guda biyu kyawawa suna kallon Indian film awata tasha (zee world),
Tsallakesu yayi saboda bai sansu ba yawuce cikin bedroom dinta,tunda ganinshi mahaifiyarshi ta gane yana cikin bacin rai dan haka tayi gaggawar binshi cikin dakin,
A tsaye ta sameshi ya dunkule hannunshi sai naushin iska yake yi yana cewa “ohh my God…”
Saurin karasawa gareshi tayi ta rikeshi “sawwam me ya farune?” Mahaifiyarshi ta tambayeshi cukin kulawa,
“Mami wallahi a school ne aka bata min rai…”
Kama hannunshi tayi ta zaunar dashi a bakin gado itama ta zauna tana murmushi,
“Sawwam sau nawa zan fada maka cewar duk inda mutum ya tsinci kansa to dole sai yayi hakuri,kofa da wa zaka zauna dole sai kayi hakuri, kayita hakuri kaji…” Mami ta fada tana Shafa kanshi,
“Shikenan Mami naji kuma zanyi hakurin”
Mikewa yayi amma har lokacin ranshi a bace yake mutuka,
“Ga baki can a falo ‘yayan hajiya rahama ne ta turosu ka duba koda wacce zaka ga tayi maka acikinsu..”
Murmushin yake yayi domin idan har da sabo to ya saba kusan kowanne lokaci kawayen Mami sukan turo yaransu yanmata wai ya duba ko zai ga wacce tayi masa,
“Mami dan Allah nidai mubar wannan maganar..”
Kafin Mami tayi magana har ya fice daga cikin dakin, ko kallon yanmatan bai yi ba ya wuce abinshi, dakinsa ya shiga ya fada toilet ya sakarwa kanshi ruwa yayi wanka ya fito har lokacin bai daina hango fuskar ummulkhair tana zaginsa ba,
Kananan kaya yasa ya fita zuwa wurin mai gadinsu domin dama kusan kowanne lokaci idan yana gida can yake zuwa suyita hira,
Yau dinma zaman yayi suka fara hira baba dan tsoho yana bashi labari mai saka nishadi,
“Yawwa baba dan tsoho dama ina son tambayarka wai dan Allah me mata suka fi jin tsoro ne?”
Dariya baba dan tsoho yayi sannan yace,
“Ai sawwam babu abinda mata suka fi tsoro sama da kadangare komai kankantarsa kuwa, duk mace zaka sameta tana tsoron kadangare…”
🅿herty novels📚
Duniyar makaranta👌🏻
[06/02, 9:37 p.m.] Baby aysha: *RAMUWAR GAYYA…💘*
_Love story 50,50_
*FERTYMERH XARAH*
            _with_
*_UMMI A’ISHA_*
4
*W*ani irin malalacin murmushi ya saki marar fitar da sauti, ya shafi sumar kansa haďe da lumshe idanuwansa cikin farin ciki,
Baba ďan tsoho ya dubesa,
‘ya akayi ne sawwam meyasa kake tambaya?
Ya tashi yana faďin ba komai, aikin gida ne aka bamu a makaranta, kafin baba tsoho yayi mgn tuni ya fice cikin jin daďi,
San da ya koma cikin gidan ya sami har lokacin yan matan suna xaune a falo suna kallo, yaja qaramin tsaki…
Waďannan ko mayu ne yakamata su bar mana gida, yasa kai yayi shigewarsa ďakinsa batare da ya qara kallonsu ba….
_At hostel…._
Ummukhairi xaune da tulin takardu a hannunta tana dubawa, dogon tsaki taja xuciyarta a cunkushe hr lokacin tana cikin bacin rai,
Alawiyya ta juyo tana kallonta bayan ta xubo indomie a plate ta nufeta,
‘ke ummu Wlhy ki Kama kanki, Kada Kice xaki sanyawa xuciyarki taurin kai sawwam ba irin maxan da kike tunani bane, kowa anan Skul tsoronsa yake….
‘Mtseww idan kowa na tsoronsa ni bana tsoronsa, maganinsa xanyi..
‘Tace kiyi maganinsa kada ki tsaya kiyi karatu Abinda iyayenki suka turo ki kenan,
Tayi shiru data tuna alqawarinta da mahaifinta, bata qara mgn ba ta janye takardun gabanta ta matso suna cin indomie.
Washe gari bayan sun gama shirinsu suka nufi cikin Skul,
Tun a bakin gate suka tsinkayo sawwam da mutanensa suna tsaye shi yana kan mota Idanunsa sanye da baqin glass ta ciki ya xuba mata idanuwa yana kallonta sosai,
Alawiyya tace dan Allah khairi karki kulasu kibarsu kiyi sha’anin gabanki, kinga da alama fitina suke nema ke mace ce bai kamata ki biye masu ba,
Shikenan ta faďa a hankali ta ďauke kanta gefe batare da ta kalli inda suke xaune ba,
A hankali sawwam ya diro kan motarsa haďe da xare glass ďin idonsa yana kallonta da guntun murmushi alamar dani kike xancen…
Suna xuwa dab dasu suka kece da wata mahaukaciyar dariya suna nuna su da yatsa hakan yasa khairi ta soma kallon jikinta taga me suke ma dariya bata gane komai ba, Alawiyya Kuma tuni ta San halinsu shiyasa bata damu ba,
Ganin yanda khairi ke kallon jikinta duk ta tsargu yasanyasu kwashewa da wata dariya harda riqe ciki, banda sawwam Dake tsaye fuskarsa ba walwala yana kallonsu yaji daďin wannan wulaqancin da suka mata Dan tuni hankalin mutane ya dawo kansu….
Alawiyya taja hannunta tana fadin nace karki kulasu, Bafa Abinda suke ma dariya dan kawai kiji haushi ne….
Sosai taji haushi ta juya tana kallon sawwam, tsaki taja tana masa kallon cike da tsana kafin ta wuce…
A class suna xaune in group suna solving wani assignment da xasuyi submitting bada jimawa ba,
Su da yawa ne a hall ďin sai dai kowa da grup ďinsa kamar yanda lecturer ďin yayi dividing ďinsu,
Bata San yanda akayi ba sai jin tayi kamar abu na tafiya Saman hijab ďinta, dubawar da xatayi taga wani shirgegen qadangare qaton gaske kansa jawur, sauran matan dake gurin suka lura suka soma ihu suna watsewa,
ita kanta a tsorace take idanunta sun firfito ta saki qara sosai haďe da cire hijab ďin jikinta ta qanqame guri ďaya,
Hankalin mutanen dake hall ďin ya dawo kanta, harda hawayenta,
Tana sanye da Doguwar riga blue shape ďinta sosai ya fito sawwam na tsaye yana kallonta,
Alawiyya taje da sauri ta rufa mata hijab ďin, ta qanqameta tana kuka sosai,
Sawwam da mutanensa suka đauki dariya a hankali taji yana faďin _”ramuwar gayya,_ inbanda abinki yarinya wake shiga hurumina ya xauna lfy…..”
Shiru ummulkhair tayi tana kallonsa hawaye sai faman kwaranya suke yi acikin idonta gashi har lokacin jikinta in banda rawa babu abinda yake yi tamkar mazari,
Duk da halin da take ciki hakan bai hanata yi masa murmushin mugunta ba wato in kasan wata to baka san wata ba,
Mazan ajinsu ne suka taru suka dauki hijabin nata suka zazzageshi suka cire kadangaren suka fitar dashi, nan ta karba ta saka har lokacin a tsorace take, tana ganin sawwam ya dago mata hannu alamun bye bye sannan ya saka bakin glass dinsa ya juya yabar wurin fuskarsa dauke da murmushi,
Tattare littattafanta ta fara yi tana yi tana share hawayen fuskarta domin ba karamin kunya yau taji ba saboda idan akwai abinda tafi tsana a rayuwarta to shine namiji ya ganta babu hijab a jikinta amma yau gashi wannan sakaran gayen yasa maza masu yawa sun ga kirar jikinta ba tareda lullub’i ba……..
Ummi Shatu….
My wattpad Phertymerh1
[07/02, 8:41 p.m.] Baby aysha: *RAMUWAR GAYYA…*💘
_Love story 50,50_
*_UMMI A’ISHA_*
        _With_
_*PHERYMER XARAH*_
  *_5_*
*B*atare data sake magana ba ta dauki kayanta ta fice daga cikin hall din ta nufi hanyar hostel,
Sawwam ta gani atsaye ajikin wata bishiyar dogon yaro shida wasu dalibai sai faman murmusawa yake yi,
Bata sake duban inda yake ba ta wuce amma sai taji ya biyota yana mata magana,
“Dama na fada miki indai kikace zaki yi sa’insa da ni to wallahi ina mutukar tausaya miki saboda wuya zaki sha, ni dinnan da kika ganni bani da mutunci muddin aka shiga gonata, ko babu komai nasan yau kin fara gane halina da kuma ko ni waye,
Shawara daya Zan baki shine ki fita daga hanyata domin duk wanda ya taboni wallahi ya tabo gidan rina…”
Gabanta yasha dan haka babu shiri taja ta tsaya, glass din fuskarshi ya zare yana murmushi,
“Ke kadai ce macen da ta taba kokarin raina mini hankali duk cikin makarantar nan dan haka ina gargadinki and this is the last waning da zan baki karki sake garajen shiga hanyata, idan kunne yaji…”
Murmushi ya sake yi ya juya ya mayar da glass dinshi fuskarshi yayi tafiyarshi, juyawa tayi tabi bayanshi da kallo,
Ringing din da wayarta keyi ne ya dawo da ita cikin nutsuwarta, cikin gaggawa ta daga wayar saboda ganin sunan mahaifinta ajikin screen din wayar,
Gaisawa suka yi ya sake gargadinta akan ta dage ta aiwatar da abinda ya turata banda wasa, sun dan jima suna tattaunawa sannan suka yi sallama ta katse wayar ta tunkari hostel.
Tana shiga dakinta ta cire hijabinta tana karkadewa domin gani take kamar har yanzu kadangaren yana jiki gashi sai ta rinka jin kamar tafiyar kadangaren a jikinta,
Alawiyya ce ta biyota tana zaune sai gata ta shigo,
“Wai ummulkhair meyasa kike da taurin kaine..?”
“Da nayi me fa?” Ummulkhair ta tambayeta tana kallon fuskarta,
“Dama sai da na fada miki ki rabu da wannan gayen ba abokin fadan ki bane amma kika ki yarda to gashi yanzu kin gani tun ba aje ko inaba kin fara kwasar kashinki a hannu, nidai shawarar da zan baki itace tunda kin jarraba kinga ba zaki ci riba ba to ki sallama masa ki rabu dashi, ko me zai ce miki ki kyaleshi ki tura masa aniyarsa saboda idan fadan nan naku yaci gaba da faruwa to wallahi komai yana iya faruw…”
Ummulkhair ce tayi saurin katseta gamida mikewa tsaye hawaye na malala daga idanuwanta,
“Haba alawiyya, yanzu ni kika dorawa laifi? Shin bakiga abinda shi yayi min ba? Haba alawiyya ta yaya zaki tsammaci hakuri daga gareni,
Tayaya zaki zaci rashin mayar da martani daga gareni? Wallahi bazan kyaleshi ba sai dai idan shi ya gaji ya kyaleni, fada dani dashi yanzu muka fara so ki barmu muci gaba dayi har muzo gab’ar da marar juriya zai hakura ya sallamawa dan uwanshi..”
“Haba ummulkhair yanzu ashe bazan fada miki kiji ba? Karfa ki manta duk abinda yaje yazo daga karshe kece zaki ji kunya domin kece mace shi namiji ne kin san kuwa duk abinda namiji yayi shi ado ne agareshi..”
“Banda wannan karon, a wannan karon bazai taba zama ado agareshi ba…”
Ummulkhair ta mayarwa da alawiyya amsa har lokacin hawaye yana fita daga idanuwanta,
“Ummulkhair kiyi hakuri ki kyale yaron nan saboda a makarantar nan kowa sonshi yake, mutane da yawa suna girmama shi saboda kokarinshi wasu kuma suna girmama shi saboda tsabar kwarjininshi ke ko ma badan haka ba ana girmama shi saboda kyawunshi..”
“Ahakan? Mtswwwww” ummulkhair tace tareda jan wani dogon tsaki,
“Ke dama nasan tsananin gabar dake tsakaninku ba zata taba barinki kiga wadannan abubuwan da na lissafa miki ba amma ke kanki kin san yayi babu karya, ke dinma ina kyautata zaton soyayyar sa ce acikin zuciyarki shiyasa kiketa wannan…”
“Ubangiji Allah ya rufa asiri, wallahi babu abinda zanyi da wannan gajarabul din yaron..”
Dariya alawiyya ta fashe da ita wacce bata shirya ba,
“Duk abunki dai sawwam yafi karfin a kirashi da gaja, ko hasadun iza hasadi bazai kusheshi ba, kedai yanzu na gane tsakaninki dashi, sai anjima”
Jakarta ta saba ta fice tabar ummulkhair tsaye sororo tana kallonta.
  Yau cike da farin ciki sawwam yaja motarsa zuwa gida, tuki yake yana bin wakar da ya kunna ta larabci,
Horn yayi baba dan tsoho yazo ya bude masa,
“Barka da dawowa magaji…”
“Baba dan tsoho nace maka dan Allah ka daina kirana da sunan nan, wallahi gaba daya sunan nan baiyi min ba”
“Sawwam ai magajin da kaji ina ce maka saboda kaine magajin Alhaji, ehh kaine magajin masu gida…”
Murmushi sawwam yayi ya fito daga cikin motarsa bayan ya ajiyeta a muhallinta,
“To baba nidai kaci gaba da kirana da sawwam din abar magajin nan..”
“To, to, to uban gidana ai duk yanda kace haka za ayi..”
Naira Dubu daya sawwam ya ciro ya mika masa yawuce cikin gida cikeda farin cikin abinda yayiwa ummulkhair,
Yana shiga falo ya iske mami zaune gefenta kuma wata farar budurwa ce take mammatsa mata kafafunta,
“Mami mai yanmata yau kuma ko wa aka samo?” Ya fadi hakan acikin ransa saboda yasan duk yadda akayi shi aka kawowa yagani ko Allah zai sa ya kyasa….
Faty 1
Ummi Shatu
[09/02, 8:53 p.m.] Baby aysha: *RAMUWAR GAYYA…*💘
_love story 50,50_
*Fertymerh Xarah*
            &
*Ummy Aysher*
*6*
  Fuskarsa da murmushi ya shiga kasancewar yau cikin nishaďi yake jin kansa, ita kanta Mami ta fahimci haka lokacin da ya xauna kusa da ita yana qarewa yarinyar dake mata tausa kallo,
Hakan Kuwa ya Sanya Mami jin daďi a zatonta xaice yarinyar tayi masa ne,
Yau da alama kana cikin farin ciki sawwam ko miye dalili? Yayi murmushi a Karo na biyu,
‘ba komai, ina cikin farin ciki ne Mami, yau me xn samu a gidan, ya ďan yatsina fuska…
‘your favorite nasa Rukayya ta girka ma,
‘Wacece Rukayya? Ya tambaya fuskarsa a yatsine,
Rukayya yar gidan hajiya luba, nan da nan ya sauya fuskarsa haďe da maida madubinsa a idanuwansa,
Rukayya na xaune idanunta a kansa sosai ya tafi da imaninta yayi matuqar yi mata kwarjini, batare da ya tanka ba ya fice
Mami ta lura da yanayinsa bataji daďi ba, toilet ya nufa shower ya sakarwa kansa Idanunsa a lumshe, surarta yake gani a idanuwansa, baisan meyasa yarinyar ta tsaya masa a rai ba,
Ya gama shirinsa kenan sai ga Mami ta shigo fuskarta ba walwala,
Na rasa gane me kake nufi sawwam, Kada ka Bari fushina ya sauka akan ka,
Da akayi me Mami? Ya tambaya Idanunsa akanta cikin rashin fahimta,
Yarinyar dake xaune a falo, kada kace bakasan saboda kai ta xo ba,
‘Saboda ni ta xo, banfa Santa ba Mami…
‘ai nasan Baka Santa ba shiyasa nace taxo dan ku fahimci juna itace matar dana xaba ma ka aura ai kaganta kyakkyawa ce, ya ware Idanunsa sosai Akanta cikin mamaki,
‘Mami nifa namiji ne idan ita xa’a xaba mata mijin aure ni baxaa xaba min macen aure ba, gsky ni batamin ba ta fiye kallo da yawa, ko aurenta nayi haka xata xauna tayi ta kallon abokaina a falo, ni bana son ta Mami,
‘kada ka raina min wayo, da yaushe da yaushe take kallon ka Bari mahaifinka yaxo xan sanardashi, ai dole ta Kalle ka taga mijin da xata aura, ya soma kallon jikinsa ta madubi…
‘Mami ko makauniya tasan nayi, Kedai kibarta bana sonta, idan dole sai nayi aure ki canxa min da wata ko ki Bari na xabi wacce nakeso da kaina…
‘Tace kana nufin duk matan dana ke kawo ma ba wacce tayi ma? Ya gyada kansa, ta girgixa kanta kawai ta juya ta fice….
2 days~~
Sawwam tun daga ranar bai qara ganin ummulkhairi ba, baisan dalilin daya sa ya damu daya ganta ba,
Akwai lokacin da xuciyarsa ta takurasa da tunaninta shi kaďai a ďaki, idan ya rumtse ido surarta yake gani da kururuwarta a kunnensa lokacin da taji tsoro, meyiwuwa tayi fushine dashi, sai me ya furta da qarfi bayan ya xira hannayensa cikin sumar kanshi dake cike kamar xaka kitse ta saboda cika da tsawo,
At school…..
Yana Saman motarsa tare da abokansa, Idanunsa boye cikin baqin glass duk matan dake wucewa Idanunsa akansu, Alawiyya yakeson gani ya tambayeta khairi…
Mtseww wai me ke damuna ne ya faďa bayan ya cire glass ďin idonsa, ya diro daga Saman motarsa ,guys muje muci abinci….
Ummulkhairi da Alawiyya tsaye lokacin da taga su sawwam sun nufi gurin cin abinci,
‘Gashi can xaije kixo muje dan Allah,
‘khairi na xata kin bar mgnr nan ne tun bayan kwana biyu da suka wuce, kinga shima ya kyaleki kema ki barshi kiyi abinda ke gabanki,
‘Wlhy baxan barshi ba, idan na barshi yaci bulus kenan Ina tsoronsa,
‘karki manta Kefa Macece….
‘Mtseww kixo muje dan Allah,
Sun rigashi isa gurin saboda yanayin tafiyarsa ta izza, tuni ta dade da haďa masa plan rana kawai take jira Kuma gata,
Tana xuwa tayiwa Mai abincin mgn kafin ta sami guri ta xauna itakam Alawiyya jikinta sai kyarma yake bataso abu yana hadata da 3pointer saboda rashin mutuncinsa,
Suna xaune ya shigo, mutane suka soma tashi xasu bar gurin sanin halinsa,
Da hannu ya tsaidasu haďe da masu nuni da su xauna Su cigaba da cin abincin su, suka sami guri suka xauna ko kaďan baiga su khairi ba,
Suna kallo aka wuce da abincinsa kamar yanda ta umurta,
Ya cire glass ďinsa, with full confidence ba tunanin komai ya buďe plate ďin dake rufe, budewar keda wuya frog ya fira sai a fuskarsa, cike da tsoro ya saki ihu bayan ya tashi tsaye, frog ďin ya faďi qasa, mutanen dake gurin suka đauki dariya bama kamar abokansa da har kasa suka Kai gun dariya,
‘wannan plan ne aka haďa mashi, tor amma Waye? Gashi har ya jimasa ciwo a fuska, ya juya a fusace ya nufi inda Mai abinci anan Idanunsa sukayi toxali da ummulkhairi, suna haďa ido ta ďauki wata irin dariya taja hannun Alawiya ta gabansa suka wuce tana fadin,
‘qawata ashe haka kike da tsoro, na ďauka ba abinda xai tsorataki anan duniya, sai gashi qaramin kwaro yasanya kinyi ihun dana firgita mutane ya janyo hankalinsu akanki, gwanda ni Macece ansan mata da tsoron qadangare, maza fa? Cikin dauriya Alawiyya tace
‘qawata ba kowane namijine matsoraci ba, kinsan wani Iskanci a baki ne kawai, maxan ma suna suka tara wani abun kamar mace…. Suka sa kai suka fice suna dariya harda tafa hannaye,
Shi da abokansa kallonsu suke hr suka fice, bacin rai ne kwance a fuskarsa kallo ďaya xaka masa ka fahimci haka, ya juya yana kallon mutanen dake gurin shi ake kallo aga wane action xai ďauka, Ransa a bace ya juya yabi bayansu….*A*fusace ya juya yabi bayansu yana huci zuciyarsa na tafarfasa abinka da dogo taku kad’an yayi ya cimmusu,
Hijabinta ya fizgo afusace take hijabin ya yage daga wuya,
“Ke wai ke wacece? Me kike takama dashi da har zaki rinka shiga gonata…”
Abokanshi ne suka katseshi ta hanyar janyeshi daga wurin suna bashi hakuri,
“Haba 3 pointer kar ka biye mata mana, ai kai namiji ne me zai saka fada da mace, ai ba afada da mace…”
Har lokacin ummulkhair da alawiyya suna tsaye awurin hakama mutane duk sun jujjuyo suna kallonsu amma ko uffan ummulkhair bata ce ba in banda binsu sawwam da kallo babu abinda take gashi gabanta sai faman faduwa yake domin ba karamin tsorata da yanayinshi tayi ba ayanda fuskarshi ta nuna to yana iya dukanta a wannan lokacin sai dai Allah ya rufa mata asiri an ceceta bai samu damar dukanta ba,
Jan hannunta alawiyya tayi suka bar wurin domin har mutane sun fara cece kuce kowa yana fadin albarkacin bakinsa,
Wuyan hijabinta taja ta gyara domin duk yanzu yayi mata yawa sakamakon yagashin da sawwam yayi,
“Yanzu kin dai ga irin abinda naketa fada miki amma kika yi biris dani kika ki daukar shawarata,
Tun ba aje ko inaba kinga kin fara ganin abinda na jima ina guje miki, yanzu me amfanin haka agaban mutane ya yaga miki hijab dinki, kuma wallahi ma Allah ne yasoki da rahama da bai mammareki ba domin ya zuciya..”
Murmushi ummulkhair tayi,
“Ni kaina na tsorata dashi wallahi dan daga ganinsa kin san zaiyi zuciya sai dai fa amma naji dadi da ranshi ya baci dama ni burina shine yaji haushi sannan yaji kunya, to duk gashi hakan ta faru at the same time….”
“To nidai shawarata agareki akaro na karshe shine ki fita daga hanyarshi domin nasan shima ba hakura zaiyi da abinda kika yi masa ba, so idan ya rama ki rabu dashi shikenan kunyi 50,50..”
Sake murmushi ummulkhair tayi “insha Allah daga wannan karon zan rabu dashi bazan sake kulashi ba duk da nasan sai ya dau fansa akan abinda nayi masa..”
“Yawwa naji dadin wannan maganar taki, dan Allah kiyi kokarin kai zuciyarki nesa..”
“Insha Allah, bari naje hostel na canja hijab dinnan..”
Sakin hannun alawiyya tayi ta wuce zuwa hostel ta cire hijab dinta ta saka wani ta koma wurin alawiyya.
  Sawwam ba karamin haushin abinda ummulkhair tayi masa yaji ba gashi abokanshi sai faman tsokanarshi suke,
“Three pointer gashi nan a bayanka wooooohhhh”
Tun abin yana bashi takaici har ya dawo yana dariya, wuni suka yi acikin school din sai yamma sannan ya fita zuwa gida,
Yana shiga falon Mami ya isketa itada mahaifinshi akan dining table sai lokacin suke cin abincin rana,
Idonshi ya daga ya kalli agogon bangon dake sakale acikin falon, karfe 5 har da yan mintoci agogon ya nuna,
“Mami sai yanzu kuke cin abincin rana..?”
Karasawa yayi yaja kujera ya zauna akusa da dad dinshi,
“Dad barka da yamma”
Kallonshi mahaifin nashi yayi yana murmushi, farin ciki tsantsa bayyane akan fuskarsa gamida walwala domin yana mutukar kaunar tilon dan nashi,
“Sawwam barka dai, ya karatun?”
Sai da ya dan yamutsa fuskarshi sannan yace “alhamdulillah dad but akwai wahala gaskiya especially ma wannan semester din..”
Sai da dad din ya tura masa filet din abincin da yake ci gabanshi domin suci tare kasancewar koda wanne lokaci indai yana gida to tare suke cin abinci,
Hijabinta ya fizgo afusace take hijabin ya yage daga wuya,
“Ke wai ke wacece? Me kike takama dashi da har zaki rinka shiga gonata…”
Abokanshi ne suka katseshi ta hanyar janyeshi daga wurin suna bashi hakuri,
“Haba 3 pointer kar ka biye mata mana, ai kai namiji ne me zai saka fada da mace, ai ba afada da mace…”
Har lokacin ummulkhair da alawiyya suna tsaye awurin hakama mutane duk sun jujjuyo suna kallonsu amma ko uffan ummulkhair bata ce ba in banda binsu sawwam da kallo babu abinda take gashi gabanta sai faman faduwa yake domin ba karamin tsorata da yanayinshi tayi ba ayanda fuskarshi ta nuna to yana iya dukanta a wannan lokacin sai dai Allah ya rufa mata asiri an ceceta bai samu damar dukanta ba,
Jan hannunta alawiyya tayi suka bar wurin domin har mutane sun fara cece kuce kowa yana fadin albarkacin bakinsa,
Wuyan hijabinta taja ta gyara domin duk yanzu yayi mata yawa sakamakon yagashin da sawwam yayi,
“Yanzu kin dai ga irin abinda naketa fada miki amma kika yi biris dani kika ki daukar shawarata,
Tun ba aje ko inaba kinga kin fara ganin abinda na jima ina guje miki, yanzu me amfanin haka agaban mutane ya yaga miki hijab dinki, kuma wallahi ma Allah ne yasoki da rahama da bai mammareki ba domin ya zuciya..”
Murmushi ummulkhair tayi,
“Ni kaina na tsorata dashi wallahi dan daga ganinsa kin san zaiyi zuciya sai dai fa amma naji dadi da ranshi ya baci dama ni burina shine yaji haushi sannan yaji kunya, to duk gashi hakan ta faru at the same time….”
“To nidai shawarata agareki akaro na karshe shine ki fita daga hanyarshi domin nasan shima ba hakura zaiyi da abinda kika yi masa ba, so idan ya rama ki rabu dashi shikenan kunyi 50,50..”
Sake murmushi ummulkhair tayi “insha Allah daga wannan karon zan rabu dashi bazan sake kulashi ba duk da nasan sai ya dau fansa akan abinda nayi masa..”
“Yawwa naji dadin wannan maganar taki, dan Allah kiyi kokarin kai zuciyarki nesa..”
“Insha Allah, bari naje hostel na canja hijab dinnan..”
Sakin hannun alawiyya tayi ta wuce zuwa hostel ta cire hijab dinta ta saka wani ta koma wurin alawiyya.
  Sawwam ba karamin haushin abinda ummulkhair tayi masa yaji ba gashi abokanshi sai faman tsokanarshi suke,
“Three pointer gashi nan a bayanka wooooohhhh”
Tun abin yana bashi takaici har ya dawo yana dariya, wuni suka yi acikin school din sai yamma sannan ya fita zuwa gida,
Yana shiga falon Mami ya isketa itada mahaifinshi akan dining table sai lokacin suke cin abincin rana,
Idonshi ya daga ya kalli agogon bangon dake sakale acikin falon, karfe 5 har da yan mintoci agogon ya nuna,
“Mami sai yanzu kuke cin abincin rana..?”
Karasawa yayi yaja kujera ya zauna akusa da dad dinshi,
“Dad barka da yamma”
Kallonshi mahaifin nashi yayi yana murmushi, farin ciki tsantsa bayyane akan fuskarsa gamida walwala domin yana mutukar kaunar tilon dan nashi,
“Sawwam barka dai, ya karatun?”
Sai da ya dan yamutsa fuskarshi sannan yace “alhamdulillah dad but akwai wahala gaskiya especially ma wannan semester din..”
Sai da dad din ya tura masa filet din abincin da yake ci gabanshi domin suci tare kasancewar koda wanne lokaci indai yana gida to tare suke cin abinci,
‘saboda kai ne abokina, taji tsoro….. Suka kwashe da dariya harda tafawa dai dai lokacin ta xo ta gabansu, inda suke ma bata kalla ba kuma xuciyarta na bugawa dan tasan sarai ya gane ta tun daga lokacin da taga suna kallonta suna magana, Gashi ynxu sun yi mata dariyar dake qona mata rai….
Sawwam ya diro daga Saman Mota ya sha gabanta yana fadin,
‘Dan Allah sister kije hostel ki taimaka ki kiramin budurwata…
Bata tanka ba illah qoqarin kauce masa da takeyi, ta gane yana son raina mata hankali Kamar bai gane taba, ya dubi su Abdul cikin ďaga murya ya soma mgn,
‘Abokina taqi responding kodai yar shi’a ce?
‘Ga alama ka gani a jikinta baqin hijab baqin niqab, in kuma tayi gardama abokina ta buďe har ciki mugani idan ba baqaqen kaya ne a jikinta ba….
‘eh hakane kuma.. Sawwam ya faďa haďe da maido kallonsa gareta,
Xuciyarta tamkar ta faďo saboda baqin ciki ita suke dangantawa da shi’a Sannan har wai ta buďa masu jikinta Su gani, cikin bacin rai ta fisge niqab ďinta haďe da nuna sa da yatsa….
Ya xare ido haďe da bude bakinsa cikin tsananin mamaki ya juya yana kallon abokansa haďe da kashe masu ido ďaya,
Abdul ya tako yana faďin,
‘abokina ashe itace, taji tsoro,
Mtsewwwwww taja dogon tsaki haďe da janye hannunta, ta juya batare da tayi mgn ba ta fice hakan ya Sanya sawwam riqo hijabinta,
Abinda yayi matuqar bata mamaki da ďaure mata kai, ko suna mata kallon yar iska ne? idanun mutane akansu, ta juyo a fusace haďe da kai masa Mari a fuska kafin ta sauke hannunta ji kake tas.. tas.. ya ďauke ta da lafiyayyun Mari har guda biyu tayi baya kamar xata faďi sai da taga shuďewar wasu mintoci kafin ganinta ya dawo dai dai, nan da nan hawaye na soma ambaliya a fuskarta,
Yana tsaye yana huci kamar wani namijin xaki, a yanda yakeji komai xai iya faruwa a Wannan lokacin tunda yake a rayuwa baa taba Marin sa ba, Waďanda suka haifesa ma basu taba gwada hakan ba, abokansa mutuwar tsaye sukayi yayin da kallon mutane na dawo garesu maxa da mata,
Ta sunkuya ta đauki niqab ďinta dake qasa, har lokacin bata daina hawaye ba, suna haďa ido bakinta yayi motsi ga bacin rai kwance akan fuskarta,
‘Ban yafe ba, mugu axxalumi Allah xai sakamin, ta juya da sauri cikin yanayin tsoro tayi hanyar hostel,
Daga yanayin yanda take magana xaka karanci bitterness wato ďacin da Mgnr tayi mata Akan harshen ta, mgnr taso ta sanyashi dariya duk da yana cikin bacin rai…
‘3 pointer wannan yarinyar mu barta kawai Kada ta janyo mana raini wataran a skul ďinnan girman mu xai faďi…
Idan mun barta kenan munji tsoronta, yamin dai dai da ya Rama Marin, amma baabaa Marin fa ya shige ka da alama cos ga yatsunta biyu nan a kuncinka, sawwam ya shafi fuskarsa Idanunsa jawur yama xaije da wannan fuskar gida haka, idan an tambayesa shikenan sai yace mace ta mare sa kome? ai *Girma ya faďi (takori)*, ya dube su,
‘Son ta nake yi, if not because of the love sai na nuna mata ko waye sawwam a skul ďin nan, ban San Ina son ta ba sai ynxu dana kasa aiwatar da mummunan abu akan ta, xn iya raping ďin ta ba ruwana….
‘So fa kace sawwam….
‘of course ya faďa Kuma duk shegen dana ganta dashi a skul ďinnan sai ya raina kansa itama xn hana mata sukuni a skul ďinnan,
‘Abdul yace ni har xnce Ayi inviting ďinta ta shigo cikin mu muxama 4-pointers…
‘Nooooooo ya girgixa kansa,
Sai safa da marwa yake yi gurin, xuciyarsa a dagule take, suna gurin wasu mata biyu sun fito daga hostel sukaji suna faďin,
‘Kinsan abu a skul nan da nan kowa xaiji amma ni naji daďin da ta maresa Ummi, yaron ya fiye girman Kai da izza, wadda aka Kira da Ummi ta juya tana kallon dayar
‘Amma ance shima ya rama fa Pherty, ai wannan *ramuwar gayya* ce tunda har biyu yayi mata, ni naso naga wannan yarinyar tayi matuqar birgeni,
‘nima ta birgeni xnje in nemeta a hostel mu qulla qawance,
Sawwam ya rude kenan Mgnr ta biye ko ina mace ta maresa har ta birge mutane, ai Kuwa baxai barta ba, ya rasa dame xai jefi matan can biyu da suka wuce suna tsegumi sai ya ciro ďayan takalmin sa ya jefa masu sai akan keyar Ummi suka juyo da mamaki ganin ko Waye, ai Kuwa suna ganinsa suka falla da gudu….
A harxuqe ya shiga motarsa bai bi takan abokansa ba ya fita daga Skul ďin,
Driving yake kamar Wanda xai tashi sama, kwayar idanunta yake gani cike da hawaye da yanda bakinta yayi motsi a Wannan lokacin har xuwa Marin da tayi masa….. yayi firgigit kamar da gaske ďin Marin sa tayi abin Marin ya tsaya masa sosai a rai….
_Ban yafe ba, mugu axxalumi Allah xai sakamin._
Pherty…
     &
Shatu….
[12/02, 8:33 p.m.] Baby aysha: *RAMUWAR GAYYA..*💘
_Love story 50,50_
   *_UMMI A’ISHA_*
          _With_
_*PHERTYMERH XARAH*_
  *_9_*
*D*riving yaci gaba dayi zuciyarshi tana hasko masa hoton ummulkhair lokacin da ta mareshi,
“Lallai yarinyar nan..” Yafadi hakan acikin zuciyarsa,
“Wai yanzu ni ta mara? Idan na kyaleta shikenan ta mari banza kenan…? Kai impossible wallahi,dole sai na rama wannan rashin mutumcin da tayi min..” Yafadi yana shafa sumar kanshi,
Da tunaninta ya samu ya isa gida, koda yaje gidan kin shiga wurin Mami yayi yawuce dakinshi saboda baya son taga shatin yan yatsun ummulkhair dake zane akan kuncinsa,
Wuni yayi acikin daki har sai da yamma tayi sannan yafito lokacin shatin dake fuskarsa ya dan goge.
  Ummulkhair hostel ta wuce kai tsaye taje ta bude dakinta ta shiga ta kwanta nan ta fara kuka sosai, ta rasa meyasa sam bata da juriya akan wulakancin sawwam, gashi dai ita kanta fadan nasu ya soma isarta amma bata son ta kyaleshi yayi nasara akanta, tafi son suyi tayi har shi da kansa ya gaji ya sallama mata,
K’arar da wayarta keyi ne ya katse mata kukan nata, babu shiri ta tashi ta dauki wayar bayan ta hadiye kukan da take yi saboda ganin mahaifinta ne me kiran,
Sakin fuskarta tayi suka gaisa tamkar babu abinda ke damuta, sai da ya jaddada mata cewar ta dage tayi abinda ya turota sannan ya hadata da mamanta suka gaisa, kasancewar yayunta duk suna gida lokacin suma sai da suka gaggaisa sannan suka yi sallama,
Hakuri tayi ta daina kukan taci gaba da abinda ke gabanta,koda suka hadu da alawiyya ma bata yarda ta sanar da ita fadansu da sawwam na jiya ba,sannan tun daga lokacin bata sake sakashi acikin idonta ba har tsawon kwana biyu, gashi kullum hijabi take sawa har kasa da nikab ta rufe fuskarta,
Sai dai shi sawwam duk inda ya hangota yana ganeta haka kawai ya rasa dalilin da yasa daga ya ganta zai san itace.
Tafe yake shida abokansa sun nufi filin kwallo wanda ke cikin makarantar, yasha jar riga mai gajeren hannu da wando jeans blue, kasancewar yammaci ne yasa ko ina ka hanga dalibai kake gani kowa yana sha’anin gabanshi, wasu na hira wasu na karatu,
Zaune ya hangota a kan wata kujerar karfe dake girke a kasan wata bishiya, tana sanye da blue din hijabi har kasa da nikab a fuskarta hannunta rikeda lecture note da alama karatu take yi, tabbas ya gane itace sai dai ita Sam bata zaci cewar ya ganeta ba,
“Hello guys, ku bani 2 minutes kuyi gaba zan taho, bari naje neman fad’a…”
Bai jira amsarsu ba juya ya nufi wurinta,kanta yana sunkuye tana duba lecture note dinta ya karasa wurin,
“Mtswwwwww” yaja dogon tsaki yana kallon kafarta,ba karamin kyau kafar tata tayi mishi ba domin faratanta gaba daya sunsha jan kunshi,
Bata ko daga kanta ta kalleshi ba taci gaba da karatunta,
“Ke…! Zuwa nayi na sanar dake kan ki shirya karbar rashin mutuncina ako wanne lokaci domin wallahi kinyi kadan ki mareni na rabu dake, tunda nazo duniya babu wanda ya taba marina sai ke…, to wallahi sai na shuka miki gonar rashin mutunci so get ready” yana kaiwa nan ya juya ya wuce yana fito da bakinshi,
Bayanshi tabi da kallo tayi murmushi, “ko me kake ji dashi to a shirye nake domin nima ina ji dashi” ta fada ahankali.
  Kwana uku da faruwar wannan al’amari ummulkhair suka nufi wurin yin photocopy itada alawiyya, sawwam yana kallonsu kuma duk da cewar ta lullube fuskarta to ya ganeta,
Gaba daya hankalinsu ya tattara kan lissafin adadin lecture notes din da za ayi musu gefe kuma wasu yanmata ne wurin su biyar suma suna jira ayi musu, daya daga cikin yanmatan ne wayarta ta fadi ba tare data sani ba kuma akayi Sa,a babu wanda ya gani, sunkuyawa sawwam yayi ya dauki wayar ya wuce, a kusa da ummulkhair ya tsaya yana yiwa mai shagon magana, sam bata luraba ya jefa mata wannan wayar acikin jakarta,
Juyawa yayi ya koma gefe can nesa ya jingina ya tsaya yana kallonsu, yana kallo wannan budurwar ta fara neman wayarta amma bata samu ba nan aka soma dube dube, wata wayar ta karba ta kira layinta take wayar ta dau kara daga cikin jakar ummulkhair wacce sam ita bata ma san abinda yake faruwa ba,
Kanta yanmatan suka iyo, “sannu barauniya daga zuwa shine zaki dauke mana waya? To Allah ya toni asirinki…”
Wata daga cikin yanmatan tafada, cikin rashin fahimta ummulkhair ta jiyo tana kallonta,
“Meya faru?” Alawiyya ta tambaya,
“Wayarmu ta sace gata nan tana kara acikin jakarta…” Kafin alawiyya ta sake magana har sun fusge jakar sun ciro wayar, daga alawiyya har ummulkhair kasa magana suka yi nan yanmatan suka hau zagin ummulkhair suka yi mata tatas mutane na tsaye suna kallonsu,
Jakarta ta dauka tana hawaye ta nufi hanyar barin wurin,
“Hy barauniya, ashe dama ke barauniya ce?? Even though kin saba satar kayan mutane….”
Taji magana daga bayanta tana juyawa taga sawwam ne yana yi mata murmushi…
Ummi Shatu
Pherty..
[14/02, 9:03 p.m.] Baby aysha: *RAMUWAR GAYYA..*💘
   _Love story 50,50_
*_UMMI A’ISHA_*
         _With_
*_PHERTYMERH XARAH_*
  *_10_*
*Y*i tayi kamar bata san dashi ba awurin ta juya taci gaba da tafiyarta tana shasshekar kuka ta cikin nikab din dake daure a fuskarta, yan matan nan kuwa sai masifa suke yi suna cewa sai sun biyota sun yi mata duka alawiyya sai basu hakuri take domin ita tasan ba ummulkhair ce ta daukar musu wayaba tunda tare suke, to amma taya akayi wayar ta shiga cikin jakar ummulkhair din? Wannan itace amsar da take nema,
Cigaba da tafiya ummulkhair tayi yayinda sawwam yake biye da ita yana yi mata dariya,
“Hmmmmm, dama na fada miki yarinya wallahi duk wanda yaci tuwo dani to miya kawai yasha domin bana barin ta kwana, ke ni nan ma da kika ganni ban taba magana da wata mace acikin makarantar nan ba balle har ta nemi ta rena min hankali sai ke, ke kin isa ki mari kamata sannan kiyi tunanin zaki zauna lafiya? Wannan ma wasa ne, idan har muka ci gaba da irin wannan dake, to wallahi sai nayi miki abinda yafi wannan ciwo…”
Batayi niyyar tanka masa ba amma wannan maganar tashi ta karshe ita ta kular da ita har ta juya ta kulashi,
“Tabbas a wannan fagen kayi kokari kuma kayi nasara sakamakon daura min sharrin sata da kayi amma kasani fagen gaba bazai yi maka kyau ba domin ba zaka ji dadin shigarshi ba, kuma wallahi ba nice da jaje ba kaine da jaje, ni ban daukeka a matsayin namiji ba saboda namijin da ya amsa sunansa namiji baya sa’insa da mace…”
Wata uwar tsawa ya sakar mata wacce take taji mararta ta cika da fitsari yana shirin fara zuba,
“Control your tongue, idan ke marar kunya ce to wallahi daidai nake dake…”
Juyawa yayi ya wuce yabarta awurin, wani sabon kukan ta saka,
“Wallahi baka isa ka daura min sata kuma na rabu dakai ba, wallahi baka isaba mun rinka masifa kenan sai dai idan a koremu daga makarantar nida kai…”
Karasowar alawiyya ne ya katse mata maganar da take yi ita kadai,
“Khairi gaskiya nayi mamakin yadda akayi wannan wayar tashiga cikin jakarki..”
“Alawiyya babu abin mamaki aciki domin wannan kadan ne daga cikin sharrin sawwam,wallahi shine yayi min wannan abun”
“Oh my God, wai har yanzu baku daina wannan fadan ba? Khairi kinga ki rabu da wannan sawwam din domin na lura sharri yake nemanki dashi, ki fita a sabgarsa..”
“Ai babu wannan maganar alawiyya, ada dai nace miki bazan sake kulashi ba to amma banda yanzu, wallahi yanzu sai na mayar masa da martani, shi waye da zai hanani sakat a makarantar nan sai kace ubanshi ne ya gina…”
“Kenan kina nufin zaki cigaba da biyeshi kuna fadan?”
“Kwarai kuwa dan wallahi sai na rama..”
“Fine, tunda bazan fada miki kijiba shikenan kiyi abinda ranki keso..”
Alawiyya nagama fadin haka tayi gaba ta barta awurin, har lokacin ummulkhair kuka take saboda bata taba sha,awar daukar kayan wani ba amma gashi abanza wani ya daura mata sata.
Tunda haka ta faru ta rage fita karatu area class, tafi zama a hostel adakinta sai dai idan lecture zasuyi shine take fita wannan dalilin yasa suka kwana biyu basu hadu da sawwam ba amma ita ba hakura tayi da abinda yayi mata ba tana nan akan bakanta na sai ta rama abinda yayi mata,
Tana kwance tana karatu da tsakar rana a dakinta kamar wacce aka cewa ta tashi kawai sai ta mike ta dauki hijab dinta ta fita daga hostel, tana fita ta hango mutumin nata yana alwala zai tafi masallaci karamar wayarshi na ajiye gefe, tana kallonshi ya gama alwalar ya mike yawuce ya manta wayar awurin,tana ganinshi ya wuce yana gyara kwalar rigarshi abinku da dan gayu sai aikin karkade jikinshi yake, tana ganin ya kule tayi saurin zuwa inda wayar ke ajiye dauka tayi tana budewa taga ta bude domin babu password akai,
Sauri tayi ta shiga massage ta saka number dinta tayi sending din massage din ta ajiye wayar tana kallon hotonshi dake kan screen din wayar, yasha purple din shadda harda hula ya wani karkaceta gefe fuskarshi sanye cikin bakin glass ya saka hannuwanshi acikin aljihunan wandon yana tsaye a wani garden mai kyau,
Saurin buya tayi saboda jiyo maganganunsu shida abokanshi suna dosowa wurin,
“Na manta phone dina but inajin awurinda nayi alwala ne..”
Ta jiyo muryar sawwam yana yiwa friends dinshi magana, tana jinsu suka karaci maganganunsu ya dauki wayar suka shisshiga motarshi suka tafi,
Fitowa tayi tana dariya “sawwam kenan, kagama naka acting din nikuma gobe zan fara nawa..”
Hostel ta shige zuciyarta cikeda murna saboda gobe zata ciwa sawwam mutunci karshe kuma zata kunyata shi acikin friends dinshi da idon mutane.
Sawwam bai san abinda ke faruwa ba yana zuwa gida falon dad dinshi ya shiga ya cire rigarshi ya yar agafe ya kunna air condition ya hau doguwar kujera ya kwanta ya rufe idanuwanshi domin so yake yayi bacci kafin 3 tayi, hoton kafar ummulkhair ya fara gani acikin idonshi, juyi yayi ya koma rub da ciki yana mamakin wai meyasa ya kasa mantawa da ita? Gashi ya rasa koda me kafarta tafi ta sauran mata domin burgeshi take yi sosai kusan ma ko suna da yawa itada wasu matan idan suna tafiya to ta kafarta yake ganeta,hakama idan ta rufe fuskarta da nikab to ta kafa yake gane cewa itace,
“Wai ni wannan yarinyar zata cewa bata dauka a matsayin namiji ba, hmmm zan kuwa nuna mata ni cikakken namiji ne..”
Murmushi yayi sai kuma yaja tsaki ya sake juyawa ya rungume dan karamin pillow din kujerar, kasa baccin yayi ganin haka ya sashi tashi domin in banda tunaninta babu abinda yakeyi, rigarshi ya dauka ya fita ya nufi sashen mami,
Yana rike da rigarshi a hannu ya shiga falon Mami sai tsaki yakeyi, ganin mami da mufida zaune ya sake bata mishi rai domin yasan wurinshi mufidan tazo,
“A’a sawwam dama ka dawone?” Mami ta tambayeshi cikeda fara’a,
“Ban jima da dawowa ba..” Yabawa Mami amsa fuskarshi babu walwala,
“Ko baka da lafiya ne?” Mami ta sake tambayarshi cikeda kulawa,
“Kaina ke ciwo, bari naje na kwanta” yafadi tareda juyawa ya fice batare da yako kalli mufida ba, dakinsa yaje ya fada akan gado ya kwanta yana nan a kwance mufida ta shigo dauke da flasks din abinci akan wani farantin silver, ajiye kayan tayi ta je gefen gadon ta zauna, ko kala bai ce da itaba har tagama zamanta ta tashi ta fita, kwanciyar yaci gaba dayi har bacci yayi nasarar saceshi.
Washe gari wurin karfe 9 ummulkhair ta fito cikin shigar atamfa red colour, jan hijabi tasa ta daura nikab, awaje suka hadu da alawiyya dama basu da lecture sai 11 sannan zasu shiga, suna zaune suna hira tana kallon agogon hannunta,
Karfe tara da yan mintuna sawwam ya shiga cikin makarantar, yana shiga ya hadu da abokansa awurin da suka saba zama, saman motarshi ya dale yana sanye cikin blue din riga da bakin wando,fuskarshi tasha black face,
Sai da ta bashi minti biyar da zama sannan ta nufi wurinda suke zaune har lokacin bata bude fuskarta ba,
Sam hankalin sawwam ba agun yake ba dan haka bai ma san da zuwanta ba,
Jin wani kamshin turare nadaban da ya ziyarci hancinsa ya sanyashi jiyowa ayangance yana basarwa, kafarta ya fara kallo anan ya gane cewar ummulkhair ce,
“Assalamu alaikum, naga sakonka babu komai na hakura komai ya wuce kamar yadda ka nema..”
Kawar da kanshi yayi tamkar bai ganta ba,
“Three pointer dakai fa take..” Abdul yafada yana dariya kasa kasa,
“Ke dawa kike..?” Sawwam yace da ita bayan ya daure fuska,
“Dakai nake, ko ba kaine ka turo min da text kan cewa nayi hakuri da abinda kayi min ba..”
Tun kafin ta karasa ya diro daga kan motar afusace,nan ya doki bayan motar da karfi,
“Karya kike, ke kin isa na baki hakuri? Wallahi bakida wannan matsayin saboda duk duniya babu macen da ta isa nabata hakuri baya ga uwar data haifeni..”
Murumushi tayi ta dauko wayarta ta fara karanto sakon daga karshe ta karanto phone number dinsa,
“Ko wannan ba number dinka bane?,ya za ayi kayi min text kuma sannan kazo kana cewa wani kaza da kaza, ohh koda yake ba kason friends dinka su sani, da kasani tun farko sai kace min kar nayi maganar a gabansu….”
Tsura mata ido yayi cikin takaici, abdul ne ya karbi wayarta ya karanta sakon sannan ya mikawa sauran ma suka karanta, nan suka dau ihu,
“3 pointer kai dai kawai ka sauko tunda har ka bata hakuri” abdul yafada yana ihu wanda ya jawo hankulan mutane garesu, bakin ciki ne ya hana sawwam magana yayi shiru kawai yana kallonta amma yasan bashida hanyar karyatata tunda babu wanda zai yarda dashi kan cewar ba shine ya tura mata wannan sakon ba,
“Karka damu babu komai na hakura, sai anjima” ummulkhair tace bayan ta cire nikab din fuskarta tana yi masa mayaudarin murmushi wanda ya sake kularshi yana kallonta ta juya tabar wurin abokanshi sai dariya suke yi masa suna cewa,
“Lallai 3 pointer kaji tsoronta tunda har ka bata hakuri, babu shakka wannan tafi karfinka shiyasa ka sauko mu ai bamu zaci cewar akwai macen da zaka iya bawa hakuri ba”
Yana jinsu ya kasa furta koda kalma daya…..
Ummi Shatu
Pherty Xarah
[16/02, 8:30 a.m.] Serlymerh💞: *RAMUWAR GAYYA*💘
_Love story 50,50_
*Fertymerh Xarah*
              &
*Ummy Aysher*
       11
   Shiru yayi yana kallonta hannunsa sarqe a qirjinsa harta fice kansa a matuqar ďaure,
Baisan ya bata haquri ba, shi baima San inda xainemi numberta ba talk less of ya bata haquri, amma taya hakan ta faru? sai ya soma xargin abokansa da sune suka haďa masa wannan plan ďin…
Nan fa faďa na kauraye tsakanin su, kowa na musu da ďan uwansa da haka suka rabu kowane Ransa a matuqar bace…..
Ummulkhairi tana xuwa ta sami Alawiyya ta dawo hrta ďora masu girki, ta cillar da Jakarta kan katifa ta sami guri ta xauna hankalinta a kwance ba sauran damuwa a xuciyarta,
‘ya akayi ta sawwam hala yau baku haďu ba shiyasa naga kin shigo da fara’a, ta tabe bakinta
‘Wai ta sawwam, bakiji bakinki ya maki nauyin faďa ba, ni ko samari na rasa mexanyi da wannan yaron? Ke bakisan wani abu ba da Kinsan yanda nakejinsa a xuciyata da baki fadi Wannan Mgnr ba,
‘mai da wuqar hajiya, it seems like na bata maki rai am sorry ta juya Kan girkin da take….
‘khairi taja qaramin tsaki tana faďin,
‘ke bakima San wani abu ba, yaron ya bani haquri fa…..
Cikin rashin gamsuwa da Mgnr ta Alawiya ta juya tana kallonta,
‘Waye xai baki haquri, sawwam ko Waye?
‘shi ďin dai in kuma kinyi musu duba kigani, ta miqa mata wayar ta karba tana dubawa kafin ta kalli khairi,
‘lallai amma Waye ya bashi number ďinki,
‘Oho masa ni ba wannan ne damuwata ba, haquri ne anbani shikenan mgn ta wuce nidashi Kuma………
‘da dai yafi maku….
2 days~
Tun daga lokacin sawwam bai qara Kula ummulkhairi ba, bawai basu haďuwa bane suna haďuwa amma kallon inda take bayayi gani yake a ynxu ya cigaba da kulata rainin xaifi yawa bayan wanda abokansa suka siyamasa suka bata haquri,
Idan ya tuna abin Ransa baci yake, kenan Yanxu girma ya faďi….
Khairi Kuwa ko ajikinta, ynxu komai yayi mata sauqi ta maida hankalinta sosai a gurin karatunta bata da sauran damuwa a xuciyarta bayan aikin da mahaifinta ya turo ta yi, ko yaushe xata fara? Shine batasan lokaci ba, dan haka xata ďaura aniyar fara Abinda ya rabata daga gida ya kawota Skul ďin…..
Ta qara duba pic ďin da mahaifinta yabata tana naxari sosai kafin ta furxar da iska mai xafin gaske daga bakinta…
‘wannan guy ďin ya haďu fa, ta Ina xn soma inama xan ganshi?
ta lalubo wayarta ta Kira mahaifinta sun dade a waya suna tattauna Mgnr kafin ta Kira mahaifiyarta nan ma ta jima sosai suna waya…
Jin Motsin shigowar Alawiya ya sanyata boye pic ďin da sauri,
‘khairi ga qaramar wayarki, kamar an turo maki test baquwar number but ban buďa ba… Khairi ta Karbi saqon tana dubawa..
    _You may be out of my sight but never out of my mind. I miss you so much._
Number ce ba suna to waye ,ita wannan abin ya soma isarta haka jiya wani ya kirata Wai yana sonta, a ina ma suke samun numberta, tayi tsaki haďe da cillar da wayar gefe….
‘meya faru Kuma, Alawiya ta tambayeta,
‘ba komai ta soma haďa takardunta, idan kin shirya mutafi it’s olmost tym Kada muyi missing ďin lectures ďin,
A tare suka fito daga hostel…..
Fiye da kwana huďu bata qara ganin sawwam a idonta ba sai dai taga abokansa, bata damu ba kuma batason tasan halin dayake ciki dama wai batana son hulda dashi bane….
Bangaren sawwam Kuwa kusan kwanan sa huďu a kwance ba lfy, Mura ke damunsa da ciwon kai,
Koda yaushe su Abdul suka taso daga makaranta suna gidan tare dashi,
‘munga khairi yau Kuma bata tambayi abokin fadanta ba duk da tadaina ganin ka,
‘And so, Nima Kaga alamar na damu da itane kona taba tambayarka ita, nifa na riga Nafita batun yarinyar kudaina min mgnrta bana so kuna tuna min da Ita….
‘shi kenan mun daina, amma gobe xaka fita ko munga jikin da sauqi, ya tashi yana fadin
‘me xai hana, kai ni nama gaji da wannan Skul Yakamata muyi exam haka kowa yakama gabansa…
‘Wallahi kam.
Washe gari suna fitowa da Alawiya idanunta na sauka akansa yana sanye cikin qananan kaya yayi kyau sosai amma daga nesa xaka gane ya ďan yi rama,
Bai gantaba yana can yana sabgogin gabansa shida su Abdul sai tsokanar mutane suke suna dariya wannan yana daya ďaga cikin halayyarsu,
Abdul ya tabosa yana nuna masa su khairi, ko kaďan baiyi xaton itace Abdul ke nuna masa ba da baxai juyaba,
Yana juyawa Kuwa suka haďa ido ita dashi, kamar mai jira ta galla masa harara haďe da ďauke kanta, shima dogon tsaki yaja yana kallon Abdul fuskarsa ba walwala…….
Pherty
    &
Shatu
[18/02, 10:47 a.m.] Baby aysha: *RAMUWAR GAYYA…*💘
_Love story 50,50_
  *_UMMI A’ISHA_*
         _with_
_*PHERTYMERH XARAH*_
   *_12_*
   *K*allonsa Abdul yayi yana murmushi,
“Three pointer kai da waye kuma..?”
“Waccan marar kunyar yarinyar mana…”
“Ohhh budurwarka..?” Abdul ya fada cike da zolaya, wani naushi sawwam ya kai masa yayi saurin gocewa yana dariya, kallon inda su ummulkhairi suke yayi sai dai bai gansu ba domin har sun bar wurin itada alawiyya,
Sauka yayi daga saman motarshi suka tafi fatymah hall inda za agudanar musu da lecture.
Ummulkhair na shiga class taji wayarta na tsuwwa dubawar da zatayi kawai sai taga sako daga wannan number da ta saba ganin anturo mata da text,
   _You look so fine dear, kinyi kyau yau…_
Shine kawai abinda ta ga an rubuta, shiru tayi tana nazarin sakon domin ta kasa gane ko waye ke aiko mata da massage kullum gashi idan ta kira number din sai tajita arufe,
Kallon kanta tayi ajikin mudubun wayar babu laifi kam tayi kyau kamar yadda mai sakon yace, sharewa tayi taci gaba da sabgarta har suka kammala lecture sukayi sallama da alawiyya ta tafi ita kuma ta nufi hostel,
Tana bullowa kwanar da zata sadata da hostel din ta hango su sawwam suna alwala kasamcewar lokacin sallar azahar ya kawo jiki, daure fuska tayi saboda duk atunaninta zai tanka mata, har taje daf dashi tana kallonshi yayi dan rama tabe baki tayi ta kawar da kanta,
Yana shafar kai sai kawai ya hangota, kafarta ya fara kallo yaga dagaske ita dince, bashi da bukatar ya kalli fuskarta domin yasan ita ce din ba wata ba, cigaba da alwalarshi yayi ba tare da yako kalleta ba, yana jin abokanshi sai k’us k’us din gulmarsa sukeyi shida ita, bai kulasu ba ya mike yayi gaba domin gudun kada su bata masa rai.
  Washe gari kamar kullum ummulkhair ta shirya ta fita lecture domin alawiyya tuni har ta shigo makarantar, fita tayi tana tafiya tana waya da babban yayansu yaya bello, tana gama wayar taji karar shigowar massage,
  _Yau kin makara dear, kawarki tun da jimawa take jiranki baki fitoba_
Tsaki taja “wannan mutumin kodai aljanine sai haka” ta fadi hakan acikin zuciyarta domin komai nata mutumin nan yasani,da wannan tunanin ta karasa wurin alawiyya suka rankaya zuwa hall,
Zasu shiga hall din su kuma su sawwam sun fito, hada ido sukayi dashi nan ta harareshi, shi dinma harararta yayi yawuce,
“Kuna nan dai da halinku, kuna son junanku amma kun kasa bayyanawa junanku sirrin dake cikin zuciyoyinku..” Alawiyya tace da ummulkhair tana murmushi,
“Wa nake so??  Mtswww wallahi kin cuceni amma, na rasa wanda zan so sai wannan dan rainin hankalin…”
“To ya isa haka..” Alawiyya tayi saurin katse zancen tana dariya domin ita ta dade da fahimtarsu,
Koda suka fito daga lecture ma kogin tunani ta fada to meyasa wai alawiyya take cewa itada sawwam soyayya suke? Dama ana soyayya da fad’a ne? Wadannan tambayoyin sune suketa kai kawo acikin kwakwalwarta,
K’arar shigowar wani sabon sakon ne taji ya shigo cikin wayarta akasalance ta dauko wayar ta bude sakon,
  _kyakkyawar fuskarki bata kyau da rashin dariya, idan kina murmushi kinfi kyau, pls ki daina daure fuska domin baya yi miki kyau.._
Murmushi ta saki ita kadai tana kallon sakon, “koma wanene wannan to hakika ya gama sanin wacece ni” tafada tana murmushi,
“Lafiya?” Taji muryar alawiyya tana tambayarta,
“Lafiya lau, wani sakone yasani murmushi”
“Kodai sawwam din nakine ya turo…”
Hannu ummulkhair ta dagawa alawiyya “dan Allah ki daina yimin zancenshi ni wallahi bana so, ki taso muje hostel muci abinci nayi girki before na fito”
Alawiyya bata kara cewa komai ba ta mike suka nufi hanyar hostel, jinsu sawwam a bayansu yasata nutsuwa tana son ganin yanda ummulkhair da sawwam zasu dubi juna, ganinsu tayi kowa yana harare harare musamman ma ummulkhair, murmushi tayi ta dafa khairi,
“Taku salon soyayyar dabance data sauran wallahi kuna burgeni..”
Shiru ummulkhair tayi mata tawuce gaba ta barta a baya,
Hostel suka shiga suka ci abinci suka yi salla alawiyya ta fara yi mata kitso,
Kitson gaba tayi mata domin rabonta dashi tun tana karama, sake shiryawa tayi suka fita tare domin tana son yin karatu, sallama suka yi da alawiyya ta tafi gida ita kuma ta wuce inda ta saba zama domin gudanar da karatunta.
  Sanye take cikin jar atamfa da digon baki ajiki, jan mayafi ta yafa akaro nafarko domin tunda tazo makarantar bata taba saka mayafi ba sai dai hijab,
Sauri kawai take yi bata son ashiga lecture batare da ta karasa ba, tana zuwa ta iske yan ajinsu awaje kowa yana harkar gabansa ba ashiga ba,
“Washh alawiyya kinga saurin da nayi, duk tunanina anshiga…”
“Ba ashiga ba tukunna, kinyi kyau” alawiyya ta bata amsa, tun kafin ta sake yunkurin yin wata maganar taji karar shigowar sako, da hanzarinta ta duba,
  _Gaskiya kinyi kyau yanmata na amma kuma kin bar min gashin kanki awaje wasu mazan suna kalle min, kiyi hakuri ki koma ki saka hijab dan Allah, i love you…_
Murmushi tayi taja dan kwalinta ta gyara domin kitson da akayi mata jiya yaki rufuwa duk kokarinta na ganin ta rufe gashin dole sai da ya fito musamman ma taa gaba,suna nan atsaye itada alawiyya ta hango mutumin nata shida abokanshi yasha bakin glass duk inda suka wuce sai kiransa dalibai suke yi,
Ta cikin glass din ya kura mata ido yana kallonta taci kwalliya sosai cikin jar atamfa da mayafi gashi kitsonta siri siri tagaban goshinta ya rufe barin fuskarta daya, tabe baki yayi yaci gaba da kallonta dama amfanin bakin glass din da yake sawa kenan yayita kallonta bata san ita yake kalloba tunda bata ganin kwayar idonshi……
Ummi Shatu
Pherty Xarah
[19/02, 9:38 a.m.] Serlymerh💞: *RAMUWAR GAYYA*……💘
_Love story 50,50_
*Fertymerh Xarah*
              &
*Ummy Aysher*
             13
   Ta ďauke fuskarta daga garesa tana kallon Alawiyya,
Wasu maxane Dake gurin Waďanda nasan sawwam suka soma kiran sunansa,
‘3 pointer yane….., bai Kalle su ba ya ďaga masu hannu kawai ya fice da abokansa,
Basu jima da tsayuwa ba lecturer ďin yaxo, suka soma shiga hall ďin, xamanta keda wuya wayarta na đauki qarar shigowar txt,
   _kibi a hankali dear gurin shiga hall bana son wani ya rabi jikinki_.
Tayi murmushi, ta Kira number switch off, tana son sanin mai number nan yayi matuqar damuwa da lamarinta, she feels him tun bata ganshi ba ta yarda dashi….
Bayan sun fito lecture wata course mate ďinsu ke sanardasu birthday party ďin ta da xa’a yi anjima, she is inviting ol her course mate…..
‘wow wasu maza suka ďauki shewa, suna yi suna kwaso shoki yau akwai casu…
Bayan sun dawo hostel khairi tace gsky ni baxan jeba, bn taba xuwa wani party maxa da mata ba,
‘Allah sai Munje, wannan shine na farko agaremu kibari Ina shirya xn biyo maki muje muga ynda abin yake,
‘shikenan kawai ta faďa……
Da dare tana xaune da waya a hannunta, chatting take a facebook, qaramar wayarta ta ďauki qara tasan baxai wuce aljaninta bane tana dubawa Kuwa shine,
_idanuna nason ganin ki, ko xaki taimakamin ?_
  tayi murmushi dai dai lokacin da Alawiya ta shigo da sallama,
‘tashi muje khairi Gashi can Xaa fara, ko shiryawa bakiyi ba ashe,
‘shirin me xnyi qaton hijab ďina xan sanya, ta tashi tana gyara hijab ďinta, Alawiyya na qara gyara fuskarta, basu jima ba suka fito a tare,
So quiet kamar ba kowa a skul ďin, duk suna gurin party sai kiďa kakeji yana tashi, tayi waige waigenta ko xataga aljaninta Babu shi,
Suna xuwa gurin ya cakuďe maxa da mata, a filin Kuwa wasu maza biyu ne ke rawa, celebraty na xaune da saurayinta a gefe sunyi kyau sosai,
Suka sami guri suka xauna, wayarta na đauki qara,
_no makeup kinyi kyau, naji daďin da kika suturta min jikinki with hijab._
   Wannan Karon ma murmushi tayi tana waige waige ko Allah xai sa ta dace da mai turo saqon,
‘3 pointer…. 3 pointer, taji gurin ya ďauki sowa Sanda suka shigo,
Yayi kyau sosai cikin qananan kaya kamar bashi ba, su Abdul na bayansa, wannan Karon murmushi yake duk da idanuwansa a boye suke cikin baqin glass amma yana cikin farin cikin tarbar da aka masa,
Ya sami guri ya xauna,
ba su jima da xama ba, aka kawo masu qananan papers a dunqule mai ďauke da numbers a ciki, sawwam ya ďauki ďaya su Abdul basu ďauka ba,
Aka xo gurin mata suna ďauka banda su khairi,
Bayan an gama addua, akayi introducing mai birthday da taqaitaccen tarihinta kana suka soma game ďin numbers ďin da suka bayar…..
‘Number 1 suka kira……bai jima ba ya fito suka ďauki tafi kafin ace ya fiddo budurwarsa, dama tare suka xo kai tsaye ya nuna ta, ta fito tana murmushi, suka karanta mishi Abinda number tace ya cire abu biyar a jikinta,
Tsit akayi ana kallonsu, yayi murmushi ya matso gareta,
Ya cire gyalenta…… Suka ce one,
Ya cire takalminta….. Two
Ya cire awarwaronta….. Three,
Ya karbi wayarta….. Noo is not accepted sukaji muryar sawwam daga inda yake xaune, duk aka juya ana kallonsa,
‘bamu yarda da waya ba,
Yaron yace amma ai a hannunta take,
Sawwam yace Abinda ke jikinta akace ba Wanda ke hannunta ba, saurayin ya juya ya ciro sarqar wuyanta suka ce….. Four,  yayi shiru yana kallon mai xai ciro na qarshe kowa su ake kallo,+
Ya ciro ear rings ďinta ďaya….. Five aka ďauki sowa,
Aka kira number 2,3,har akaxo Kan na qarshe wanda sawwam ne kamar baxai fita ba sai Kuma ya fita ai Kuwa aka ďauki sowa, 3 pointer, Alawiyya ta dubeta
‘gafa naki can ya fito, inaji baisan kina nan gurin ba,
Khairi taja tsaki tana latsar wayarta,
‘sawwam your girlfriend Pls…. Yayi shiru kafin ya juya yana kallon su Abdul dan shi baida budurwa, matan dake gurin sai gyara mayafin su sukeyi, Abdul ya nuna masa wani gun da yatsa ya juya yana kallon gurin caraf idanunsu na sarqe dana juna, ya yatsina fuskarsa bayan ya ďauke idanuwansa
‘kai ake jira sawwam….
Da hannu ya nuna khairi sai da gabanta ya fadi ita kanta Alawiyya tayi mamaki,
Akace ta fito, ba musu Kuwa ta fito sai dai fuskarta ba walwala, matan dake gurin aka soma kus-kus,
Gabansa ta tsaya daga ita har shi bamai walwala kowa na cike da jin haushin ďan uwansa,
‘sawwam you are to kiss her for five minutes…..
Khairi ta xaro ido ta juya tana kallon mutanen gurin, duk idanu akansu can ta tsinkayo Alawiyya na dariya, a gefe daya ma su Abdul dariya suke ta juya tana kallon sawwam ga mamakinta ko a jikinsa, yaja Numfashi kafin ya xare glass ďin idonsa ya soka a gaban rigarsa, kallonta yake qasa qasa kafin ya matso gurinta,
da sauri ta matsa baya, shima ya matso, ta matsa, ya matso ta matsa cikin jin haushi sai abin ya bawa mutane dariya,
Ta rumtse idanuwanta dai dai lokacin da taji bugun numfashinsa a fuskarta….
‘wait sawwam an fanshe ta…. ya tsaya cak he mean it da sai yayi ba ruwansa ya juya yana kallon sa,
Wani gaye ne a tsaye gurin ya bada kuďi amatsayin belinta ne komiye Oho,
Sosai khairi taji daďi tabi saurayin da kallo,
Sawwam ya tabe bakinsa haďe da ďaga kafadarsa ko a jikinsa yayi nuni da a sanya masa music,
Da sauri khairi suka fito gurin wayarta na ďauki qara,
_ina sonki, ina matuqar kishin ki, shikuma Waye?_
tayi shiru xuciyarta na bugawa ta juya ko xataga wannan saurayin acan ta tsinkayo sawwam yana rawa sosai, ya birgeta ashe haka ya iya rawa…..*T*sayawa suka yi ta zuba masa ido tana kallon yanda yake rawa sai kace Michael Jackson domin rawar da yake yi yayi mutukar burge kowa dake wurin,
“Yan mata ai yau naso ace kinsha lab’b’a…” Muryar alawiyya ta dawo da ita cikin hayyacinta,
“Hmm ai wallahi kuwa da hakan ta faru to da sai yayi regrating..” Ummulkhair ta bata amsa tana tabe bakinta,
“Akan me? Saboda shine ya kawoki wurin ko yaya?”
“To dan bashi ya kawoni wurin ba meye dalilinshi na nuna ni a matsayin budurwarsa?”
Dariya alawiyya ta fashe da ita wadda har sai da ummulkhair ta kule mutuka,
“Ke yanzu in banda tsabar rainin hankali ni zaki kalla kiyiwa wannan maganar? Haba khairi ai kowa yasan wallahi soyayya kukeyi da sawwam kawai dai ban san meyasa ku taku soyayyar ta faro da haka ba”
Shiru tayi tana sauraren alawiyya har ta kammala maganarta,
“Idan kin gama sai da safe,amma kisani nikam tuni inada saurayina wanda yake sona ya damu dani yake kula da dukkan al,amurana ba wancan gajan gayen ba…”
Tana gama fadin haka ta yi gaba tabar alawiyya tana yi mata dariya,
Hostel ta wuce har lokacin a tsorace take kuma jikinta bai daina rawar da ya dauka ba lokacin da sawwam yake niyyar kissing dinta,
“Yau da na shiga uku da shikenan gayen nan yagama rainani” ta fadi hakan acikin zuciyarta,
Bude dakinta tayi ta shiga ta kwanta asaman katifarta tana jiran sakon masoyinta kamar yadda ta rada masa sunan domin yanzu tafara sonshi duk da bata taba haduwa dashi ba,
Kamar kuwa wanda yasan jiran nashi take yi sai taji karar wayarta kirrrr,
Dauka tayi ta bude sakon tafara karantawa,
  _Gareki yake wannan ma’abociyar kyawu da nutsuwa, hakika ban taba ganin macen da takaiki kyawu da kamala ba, nasan yanzu kin kwanta bacci to ina yi miki fatan wayar gari lafiya cikin aminci,masoyinki mai son farin cikinki…_
Murmushi tayi taci gaba da maimaita karanta sakon sai kace wacce aka bawa haddarshi, ji take kamar zata mayar mishi da amsa sai kuma ta fasa amma tana jin sonshi har cikin ranta gashi ko muryarshi bata taba jiba ahaka bacci ya sureta yayi gaba da ita.
  Su sawwam kuwa sai misalin karfe 11 da wani abu suka tashi daga wannan party din, abdul ne ya kamo hannunshi yana yi masa magana kasa kasa,
“Three pointer wallahi nafa kamu da son kanwar nan taka..”
Jiyowa sawwam yayi yana kallonsa “wacece kanwata kuma? Ni tunda muke daku kun taba ganin wata wai kanwata? Ni ai banida kowa banda kanwa banida yaya..”
“I know three pointer, i mean wannan yarinyar da kuke ta fada da ita..”
“Mtswwww, wai kana nufin wannan yarinyar ta dazu? Waye yace maka kanwata ce? Kaga malam wallahi baka isa ka saka yarinyar nan ta sake rainani ba dama sam na fuskanci bata ganin girmana..”
“Haba babban yaya…” Abdul yafadi cike da tsokana,
“Kaga ni kar ka bata min time idan tafiya zakayi kazo mu tafi idan kuma anan zaka kwana sai kayita zama..”
“Allah ya baka hakuri three pointer wai me yayi zafi? Daga maganar arziki?”
“Yes, me zakayi da wannan yarinyar yar kauye ko wayewa ma batayi ba kullum tana lullube cikin hijab, yanzu ka auri wannan kace ka auri wa?”
Murmushi abdul yayi daidai lokacin da suka karasa inda sawwam yayi packing din motarshi,
“You are right but nidai tayi min ahakan….”
“Wannan kuma ya rage gareka..” Sawwam ya fadi yana yatsina fuskarshi bayan ya ciro cingum daga cikin aljihun wandonshi,
Daga shi har abdul din babu wanda ya sake magana har ya kaishi gida yayi dropping dinshi shima ya wuce zuwa gidansu,
Driving yake yi yana sauraren wakar falguni wanda ya karade cikin motar, shi kadai ba tare da ya shirya ba kawai sai yaji ya fashe da dariya sakamakon tuno ummulkhair da yayi da yanayin da yaga ta shiga na tashin hankali lokacin da taji cewar zai yi kissing dinta,
“Yanmata ashe kina tsoro…” Yafada yana murmushi, jin yanayin garin ya sauya daga zafi zuwa kadawar iska ya sashi jin wani farin ciki yana ratsashi,
  A inda aka tanada domin ajiye motoci yaje yayi packing din motarshi bayan baba dan tsoho ya bude masa gate, fitowa yayi yana rike da rigarshi a hannu domin tun daga cikin motar ya cireta, sunkuyawa yayi yana duba tayar motarshi har baba dan tsoho yazo ya iskeshi awurin,
“Barka da dawowa uban gidana” baba dan tsoho yace dashi yana fara,a,
“Yawwa baba ya gida?” Sawwam ya bashi amsa bayan ya mike ya nufi cikin gida, yana kokarin shiga dakinshi suka yi kicibus da dad ya fito daga part din mami,
“Dan gidan daddy sai yanzu aka dawo? Dama kuwa ina nemanka domin nazo maka da albishir, insha Allahu acikin wannan satin zamu tafi umara domin visa dinmu ta samu..”
“Wow, am very happy dad”
“Anything for you my son, kai kadai na mallaka saboda haka you deserve more than this…”
“Thank you dad..”
Sawwam ya fadi yana murmushi daidai lokacin mami tazo ta iskesu,
“Ai Alhaji ba wannan kadai zaka sanar dashi ba sai ka fada masa cewar bayan kun dawo kuma zai fitar da matar aure idan kuma ya kasa to ni zan fitar masa…”
Zunbura baki sawwam yayi kamar wani karamin yaro, “haba mami sai kace wani…”
“Yiwa mutane shiru sai anyi magana kafara cewa kai kaza da kaza this and that..” Mami ta katseshi,
“Hajiya adai sake bashi dama mugani..” Inji dad,
“Wacce dama kuma zan bashi wacce da ban bashi ba..” Mami ta furta tare da wucewa ta barsu awurin, murmushi dad yayi ya wuce yabi bayanta, kada kai shima sawwam yayi ya fada cikin dakinshi yana korafin maganar da Mami ta fada domin shi har yanzu baiga matar da tayi masa ba a matsayin matar aure.
   Washe gari da misalin karfe 9 ya shiga makaranta yasha jar riga da bakin wando, yana tsaye ajikin motarshi da bakin glass a fuskarshi ummulkhair suka fito itada alawiyya tasha jan hijabi da bakin material,
“Kunyi anko keda sahibinki..” Alawiyya ta fadi cikeda tsokana,
“Wanne sahibi kuma..?” Ta fada tana kallon wurinda sawwam yake ai tana ganinshi da jar riga ta juya,
“Wallahi babu wani anko da zanyi dashi dan haka hostel ma zan koma na sake wasu kayan”
  Bata saurari kiran da alawiyya ke yimata ba ta nufi hostel da sauri taje ta cire kayan ta sako wata pink din shadda da farin hijabi ta fito,
Tun daga bakin gate din hostel dinsu sakon masoyinta ya shigo dan haka da murmushinta ta bude sakon,
  _Barka da fitowa, kuma yau Kinyi kyau my love.._
Murmushi tayi tana dan waige waige wai ko zata ganshi amma hakan bata faruba, wata harara ta aikawa da sawwam daidai lokacin da tazo wucewa ta gabansu, glass din fuskarshi ya cire shima ya harareta yaja dan karamin tsaki tareda dauke kanshi,
Ganin zata wuce yasa abdul yin tsalle ya diro daga saman mota ya nufeta yana kokarin tsayar da ita, jiyowa tayi tana kallonsa to ko dama wannan shine mutumin da yake yi mata wannan sakon? Wannan tambayar itace ta ziyarci kwakwalwarta damu masu rubutun.
Ummi Shatu
      &
Pherty Xarah
[21/02, 5:55 p.m.] Serlymerh💞: *RAMUWAR GAYYA*……💘
_love story 50,50_
*Fertymerh Xarah*
            &
*Ummy Aysher*
15
Kallon Ummy Aysher nayi dan son tabbatar da xargin da khairi keyi…… No answer,
‘qanwar mu…..ya faďa bayan ya shiga gabanta, kallonsa take tana nanata mgnr a xuciyarta wai qanwarmu
‘naga fuskarki da alamar mamaki, kinji wani iri banbarakwai wai namiji da suna hajara, ba komai ya janyo Hakan ba illah sonki nakeyi ummulkhairi….
Ta tsuke fuskarta xuciyarta na bugawa, Allah ya sa bashi bane ke tura mata wannan saqon dan baxata amince da shi baxata manta rashin mutuncin  da suka mata farkon xuwanta Skul ďin ba….
Sawwam a kishingide Kan motarsa Idanunsa cikin baqin glass sosai ya xuba mata ido yana kallonta yana son ganin re’action ďin ta akan Mgnr Abdul xata amince dashi ne ko Kuwa?
Xatayi mgn kenan saqo ya shigo a wayarta jikinta har rawa yake ta buďa ta gani,
    _’kin sani Ina matuqar kishin ki khairi……._
  Tayi ajiyar xuciya har a cikin ranta taji daďi kenan ba Abdul bane to waye wannan da bayason bayyana mata koshi Waye, she need to know him,ta juya tana waige waige bata ga kowa ba, ta dubi sawwam dake cire glass ďin sa taja tsaki shi Kuma yabita da harara atare suka ďauke kansu ga juna kowa cike da haushin ďan uwansa….
Abdul yace karki damu, shi wancan Yanxu ki kyalesa ba ruwanki dashi ko ranar da akayi party ďinnan Wanda ya fansheki hannunsa ni na turasa saboda ban yarda da abokina ba, Allah khairi I mean it sonki nakeyi, kallonsa tayi Qasa da Sama taja tsaki ta fice da sauri ganin take wani plan suke son haďa mata ta dan su cutar da Ita, ta Allah Kuwa bata su ba….
Raf…. Raf.. Raf… Sawwam ya ďauki tafi bayan ya diro daga Saman motarsa,
‘wow tayi matuqar birgeni kabani haushi, ai sai dana gayama girma kawai xaka xubar a Wannan yarinya dan Allah ynxu wa gari ya waya?
‘Abokina da gske nakeyi fa, ynxu birgeni takeyi xnyi qoqari mu fara soyayya da Ita,
Sawwam ya yatsina fuskarsa bayan ya tabe bakinsa,
‘is left for you, Allah yasa watarana ta mare ka acikin mutane,
‘And so, duk cikin so ne… Sawwam ya qara bata fuskarsa cikin son kawar da xancen baisan meyasa yakejin haushin Abdul dan yace yana son khairi ba….
‘muje hall Pls is olmost tym, suka fice a tare.
Khairi Kuwa da kyar ta gano inda Alawiyya take, anan ta labarta mata ynda sukayi da Abdul,
‘Hhhhhhhh to fa ke abokai biyu xaki haďa kiyi soyayya dasu kenan, gsky na xaba maki sawwam domin kunfi dacewa, tsiwarku da girman kanku yaxo ďaya……. Khairi taja tsaki
‘ke wannan ya dama, Wanda ya damu dani nakeso, Allah Alawiyya am eager naga wannan mutumin dake turomin text, xuciyata ta aminta dashi inajinsa a raina….
‘ke khairi Kinsan me kikeyi, bakisan mutum ba, bakisan kowa ye ba mutum ko aljan, Mai lfy ko musaki kawai kin amince kina sonsa….
‘yes koma shi waye inason abuna, inbaxaki min addua ba kiyi shiru ni ynxu nagane bakya sona tunda bakyason Abinda nake so,
‘nikam baxan so abinda bansan kowa ye ba, da dai sawwam ne dashi kuka fi dacewa, gashi ďan gayu ,kyakkyawa, ki dubi matan dake sonsa a skul ďinnan yana wulaqantasu kin ko San dame yake taqama? Khairi ta dubeta a fusace cikin bacin rai…
‘duk abinda yake taqama Ina taqama dashi ko da Kuwa *MULKI KO SARAUTA* ne ni miye ruwana da matan dake sonsa ni bakiji nace ina sonsa ba kuma baxan so sa ba……. Alawiyya ta tabe bakinta,
‘Allah ya kawo *RUWAN KASHE GOBARA* tsakanin ku……cikin tsiwa tace Amin ta fice cikin jin haushin Alawiyya a Wannan Karon ta nufi wata bishiya ta xauna kafin a shigar masu lectures,
Xaman ta keda wuya message na shigo wayarta, cikin xaquwa ta buďe,
    _’Har ynxu xuciyata tana min raďaďin ganin ki da wannan gayen, Ina kishinki sosai fiye da tunaninki, idan ya qara tunkararsa ki gayamasa *Ni da ke* mun dace, ina son Kare *Martabar ki* domin tawace….._
    Wannan Karon murmushi tayi har cikin xuciyarta taji daďin kalamansa, karo na farko data tsinci kanta dason maida masa martani tun sanda yake turo mata text,
      _kayi haquri……_
    Shine Abinda ta tura tana murmushi, cikin minti biyu taji shigowar wani text…
   _Na haqura amma ki tashi qarqashin wannan bishiyar saboda kare lfyrki daga Abinda ke cikinta_.
Xumbur ta tashi idan akwai abinda ta tsana cutar aljannu, ta soma waige waige tana ja da baya ko xataga aljaninta,
Bata ankaraba taji ta bigi mutum a baya, Kwallon dake hannunsa ta sumulyo akan qafarta,
Wash ta faďa tana kallonsa haďe da riqe qafar, sawwam ne ya bata rai…
‘Ajebo ita wannan Kwallon ake wa wani wash, kai mata akwai sharri a rayuwarsu ya faďa yana kallon Wanda suke tare Hafiz,
Hafiz yace wasu matan suka ma sharri sai kaji dama baka duniya, baabaa ka kyaleta muje field ana jiran mu Pls,
Sawwam ya cigaba da tafiya yana cilla Kwallon sama yana cafewa yace
‘wannan ma da gangan tayi dan ta taba jikina Kuma ta taba taji, ni daman nasan kiss ďin da ban mata ba tasha mafarki akansa, batasan wannan bakin ba gani nan bari nan……
Sukayi dariya a tare shida Hafiz suka fice yana tambayarsa
‘Au daman kasan tane, oh lallai shiyasa.
Sawwam yace tana cikin masu sona ne……..
Khairi na tsaye na kallonsu har suka fice ta gane yana son ta kulashi su koma yar gidan jiya, ita Kuwa baxata biye masa a ynxu musamman da take cikin farin ciki, ta tabe bakinta ta juya tana cigaba da latsar wayarta.
Pherty
     &
Ummy shatu
[22/02, 11:48 a.m.] Baby aysha: *RAMUWAR GAYYA…*💘
  _Love story 50,50_
*_UMMI A’ISHA_*
        _With_
_*PHERTYMERH XARAH*_
  16
*H*ar suka kule daga wurinda take tsaye bata sake kallon koda inda suke ba sai dai amma kuma maganarshi ta tsaya mata arai cewar wai dama so take yayi kissing dinta may be ma har mafarki tayi,
“Mtswwww,kai ka isa ma” tafadi bayan taja dogon tsaki, gyara tsayuwarta tayi tana jiran alawiyya wacce taga ta nufota,
“Yadai..?” Alawiyya tace da ita bayan tazo daf da ita,
“Wallahi wancan banzan gayen ne dan rainin hankali kuma wallahi sai na mayar masa da martani domin bai nemi zaman lafiya ba, har ni zai cewa wai sonshi nake..?” Ta fada cikin kunar rai,
“Hmmmm nidai babu abinda zance domin fadanku ne na masoya..”
Wani sabon haushi ne ya sake ziyartar ummulkhair domin bata kaunar taji ana hadata da sawwam a matsayin masoya, caraf ta hangoshi shida abokansa sun nufi motarshi suna kokarin shiga,
Kamar wata zakanya haka ta zubura ta nufi wurinsu, yana kokarin shiga gaban motarshi ta dakatar dashi,
“Kai sawwam kake ko kawwam ko me, har kaine zaka budi baki kace wai ina sonka? Mtswww Allah ya sawwake domin ni banga abin so a tattare dakai ba,sannan wannan kazamin bakin naka da ko brush may be baya samu shi zakace wai ina mafarki akanshi, mtswww amma kuwa Allah ya yaye min mutukar nayi mafarkin wannan kazamin bakin naka to na cancanci a jajanta min, bakin da Allah ne kadai yasan kazantar dake tattare dashi perhaps har na wasu arnan ma ya taba….”
Tana kaiwa nan ta juya ta wucesu yana tsaye sororo yana kallonta shi bai karasa shiga cikin motar ya zauna ba sannan shi bai fasaba,
“Tab….” Sawwam ya fadi acikin zuciyarshi, shi da ko mata acikin makarantar nan baya kulawa amma shi zata kalla tayi wa wannan maganar wai ya saba kissing din mata watakila ma harda arna aciki, duk makarantar nan kowa yasan yan group dinsu basa kula yanmata sannan basa shan komai sudai barsu da shakiyanci da tsokanar mutane,batare da yayi yunkurin yin komai ba ya shiga cikin motar ya tadata yana tsaki,
“Three pointer ko yarinyar nan sonka din takeyi da gaskene?” Yaji muryar hafiz yana tambayarshi,
“Oho mata…” Shine kawai abinda ya fada ya dauke kansa, yana jinsu Abdul sai shakiyanci suke yi masa suna dariya.
Alawiyya na tsaye tana kallonta har ta karaso wurinta tana murmushi,
“Ai sai yanzu naji dadi da naje na sanar dashi bai yimin ba balle har na soshi..” Kairi tace da alawiyya tana murmushi,
“Allah dai ya sassauta muku zuciyarku”
Alawiyya ta fadi tana kallonta, tun da wannan abun ya faru basa haduwa da sawwam,wannan abu ba karamin dadi yayi mata ba domin dama shine babbar matsalarta a makarantar nan, wani lokacin tana hangoshi daga nesa ko acikin abokanshi ko kuma a motarshi,
Yau dinma a motarshi ta hangoshi zaune amma yabar kofar motar a bude, bakin takalmi yasa da bakin wando sai blue din riga mai dogon hannu, kawai zaune yake domin baya ra’ayin shiga lecture yau dama wani lokacin zamanshi kawai yake yi yaki shiga lecture,
Ta gefenshi taje ta wuce tana ta yan harare hararenta, ta cikin glass din dake manne a idonshi yake kallonta sai wani daddauke kai take yi,
“Mtswww” yaja dogon tsaki tareda kawar da kanshi,
Murmushi tayi najin dadi domin dama burinta ta bakanta masa rai kuma gashi tayi nasara,
Sake juyawa yayi ya kalleta tana sanye da blue din leshi mai stones ajiki tasa bakin hijabi da bakin takalmi,
K’irr taji massage ya shigo, tana dubawa taga sahibinta ne,
  _Shigarki ta yau tafi ta kowacce rana kyau, da fatan dai kinci abinci domin bana son zamanki da yunwa_
“Hmmm Allah sarki masoyina” tafadi tana murmushi,
  _tnx dear, naci abinci ina fata kaima baka tareda yunwa.._
Ta mayar masa da reply bayan ta samu wata baranda ta zauna, dama yau alawiyya ba zata zoba ta danyi tafiya dan haka ita kadai ce, wani calculation ta fara yi saboda sunada text gobe, har yamma tayi tana zaune tanata karatunta ita kadai sai misalin karfe biyar sannan ta tashi zata shiga hostel anan yan department dinsu suke cemata da daddare tasamu ta fito domin zasuyi group discussion, kamar ba zata amsa musu ba sai kuma tace to, hostel ta shiga taje ta kwanta ta huta domin ta gama gajiya kasancewar ta wuni tana karatu.
  Misalin karfe 8 tafita tana zuwa ta iske yan ajinsu anan aka fara tattaunawa duk wanda yakeda wata tambaya ko wani abu wand ya shige masa duhu sai ya fada sai ayi masa bayani da hausa dalla dalla yanda zai gane gashi harda marker domin rubutu a bord,har 9:30 sunata tattaunawar sai wurin karfe goma saura sannan suka kammala, fitowa ummulkhair tayi zata koma hostel diffff taga an dauke wuta gashi tabar wayarta a hostel tana charge, nan ta fara lalube domin gurin ya gama gaurayewa da duhu dimm,
Sawwam dake class shi kadai yana karatu sai yaga diff yan wuta sun dauke, tsaki yayi ya tattara kayanshi ya fito dama shi haka yake yi da daddare karatunshi yake yi da rana kuma yayita biye friends dinshi suna shakiyanci,
“Mtswww ashe fa nabar wayar a mota..” Yafada ahankali bayan ya fito daga cikin class din, ahaka ya dauki hanya domin zuwa wurinda yayi packing din motarsa,
Ummulkhair tafiya kawai take yi tana laluben hanya cikin duhun taci tuntube da wani katon dutse wanda ke girke agun
Babu zato karaf sawwam yaji yaci karo da mutum ya fado jikinsa, ba ita ba shi kanshi ya tsorata,
“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…” Ummulkhair ta fada bakinta yana rawa,
K’amshin da yaji ne yasashi fahimtar cewar itace, gam ya riketa ajikinshi, jikinta ne yahau rawa,
“Nashiga uku, waye..?” Tafada da karfi tana kokarin kwacewa daga jikinshi,
“Sawwam ne…!” Ya fada cikin soft voice dinshi,
Ai tana jin haka ta bude baki zata yi masa rashin kunya,
“Mallam meye haka, dallah sakeni ni ba yar iska bace irinka..”
“Nine dan iska…?” Ya fada yana sake hadata da jikinsa,
“Me zanyi da wannan kazamin bakin naka wanda may be ma ko brush baya samu..” Maganar data fada masa rannan ta dawo cikin brain dinshi tafara circling,
Bai san lokacin da ya zubar da kayan hannunshi ba ya kankameta ajikinshi ya fara luluben bakinta acikin duhun,
“Wai meye haka…..” Ji tayi yakaiwa bakinta cafka,
“Yau na shiga uku na hadu da dan iska..” Tafadi acikin mind dinta,
“Yau kuwa zaki gane nidin dan iskane kamar yanda kika kirani da sunan…”
Kokarin kwatar kanta da bakinta take yi amma ta kasa, sawwam kuwa shi ba taba kula kowacce mace yake ba asalima bashida budurwa baima taba yin budurwa ba inba ta kuruciya ba lokacin da yana secondary school ita dinma bai wani damu da itaba, baima san yanda soyayyar take ba sai dai yana gani a finafinai kasancewar mayen kallon american films ne, shi dai kawai yana ganin suna hugging da kissing da sunan soyayya amma bai san abinda suke jiba,
Tun ummulkhair na kokarin kwatar kanta harta hakura ta kyaleshi amma sai tutture shi take yi,
“Dan iska kawai dama abinda yake ta so kenan rannan bai samuba shiyasa ya biyoni yau” haka taketa fada acikin zuciyarta,
Gaba daya kamshin jikinshi ya gama baibaye kowanne sassa nata, haka shi dinma kamshin jikinta duk ya cika kofofin hancinshi wannan dalilin ne yasashi kasa sakinta,
Dakyar ya iya sakinta yana maida numfashi ahankali, ai yana sakinta kairi tace kafa mai naci ban bakiba wanda har saida abin ya bashi dariya,
Sunkuyawa yayi ya tsince kayanshi dake yashe awurin ya nufi motarshi ya shiga yana murmushi,
Ummulkhair na shiga hostel aka kawo wuta, haki take yi sosai kamar wacce ta shekara tana gudu,
“Yau na shiga uku..ashe sawwam dan iskane ashe?” Ta fada har lokacin jikinta rawa yake yi,
Kirrrr sakon masoyinta ya shigo,
  _i love you dear_
Ko amsa bata mayar mishi ba saboda yau sawwam ya sata acikin wani hali, dakyar ta samu ta iya yin bacci domin da zarar ta rufe idonta numfashin sawwam take jiyowa acikin kunnenta lokacin da yake nuna mata halinsa.
   Da safe sukuku ta shirya ta fita misalin karfe 9 domin 9:30 zasu shiga test, tana fita ta hango sawwam atsakiyar abokanshi sunata hira sai dariya suke, kura mata ido yayi yana kallonta yana murmushi, ko wurinda yake bata kalla ba balle ta harareshi, wucesu tayi kanta akasa domin yanzu kuma kunyar hada ido take dashi,
“Yau babu fadanne..?” Abdul yafadi yana dariya,
Shiru sawwam yayi bai bashi amsa ba amma acikin zuciyarshi cewa yake “ai babu wannan maganar tunda jiya na koya mata hankali..”.

Abdul bai fahimci komai ba, ya ďauke kansa yana kallon su Alawiyya har suka bacewa ganinsa,

Sawwam Kuwa ya maida hankalinsa ga kallon wata takarda dake hannunsa har acikin xuciyarsa idan ya tuna jiya yakanji wani iri Kuma abin ya basa dariya….
Khairi Kuwa tana isa hostel ta soma rage kayan jikinta kafin ta xauna ta ciro wayarta, noo mahaifinta ta Kira she is in need Akan aikin daya turo ta kai dan da alama tayi kusa cika burinsa a yanda take gani,
Basu jima akan wayar na ta tsinke, cornflakes ta haďa tasha dan ragewa kanta yunwar dake damunta kafin ta kwanta a mattress cikin tunanin aljaninta yau tajisa shiru, Allah yasa dai lfy,
Can wani bangare na xuciyarta ya halbo mata sawwam da yanda suka kasance jiya, nan da nan Kuwa ta bata ranta haďe da Jan tsaki,
Amma fa duk da haka ya cuceni Wlhy, sai Allah ya sakamin dama abinda yake nema bai samu ba ko yana xaton cewa ni yar iska ce idan Kuwa hakane Gobe sai na nuna masa iyakarsa….
Da Wannan qudurin tayi barci ta qagu safiya ta waye ta ganshi….
Washe garin Ranar ya fito cikin shirinsa na manyan kaya kasancewar yau Friday, da hularsa a hannu ya sami Mami a falo tana haďa breakfast,
‘Mrng Mami,
‘har ka fito kenan,
‘eh…… yaja kujera ya xauna dai dai lokacin da mahaifinsa ya fito shima cikin shirinsa na fita office, sawwam ya gaida sa,
Suna cikin ci ne yake sanardashi, Dad Mgnr xuwa Umrah ayimin uxuri har wani watan,
‘meyasa ya tambayesa yana kallonsa da mamaki,
‘Cos Muna gab da fara exam ynxu, I don’t want to lose it, idan mun gama exam ďin sai muje,
‘Allah ya bada Sa’a,
‘Amin ya tashi ya fice daga falon,
Yana shiga harabar Skul ďin ya tsinkayo su Hafiz, Abdul da Suhaib tsaye suna jiransa, inda suke yayi parking ya fito….
Hhhhhhhhhhhh suka ďauki dariya tare a lokacin da suke faďin yau harda hula three pointer… ya gyara xaman hular akansa yana faďin,
‘Dan na birge budurwata ne, Kunsan ni sabon shiga ne a Wannan fannin, kallonsa suke da mamaki,

‘ita kuma wacece acewar Suhaib, sawwam ya kalli Abdul,
‘Abdul yayi Saurin cewa karka kalleni malam bansan ko Wacece ba,
‘Hafiz yace inaji itace wannan yarinyar da muka haďu da ita ranar xamuje kwallo,
‘No ba Ita bace ya faďa yana yatsina fuskarsa koma Wacece idan lokaci yayi xaku ganta ku Santa Kuma……
Abdul yace kai ka sani, ni muje inaso na duba assignment ďina a laptop,
Sawwam yace ba inda xanje sai na ganta taga kwalliyata saboda ita nayi, bari ma kagani ka ďauki abin da wasa ne, ya haye Saman motarsa,
Abdul ya juya shida Hafiz suna dariya suka barshi da Suhaib gurin ,

A dai dai Wannan lokacin Alawiyya tuni ta fita class, test sukayi saboda suna gab da exam ake masu rushing akan test,
Fitowar ta kenan daga test ďin wayarta na đauki qarar shigowar test tana dubawa sahibintane,
   _’Mrng sahibata, my eyes need to see you_.

tayi murmushi ta sami guri ta xauna kafin Alawiyya ta fito, ta tura masa
    _da gaske, ina xan ganka…._

  Oh yau xata ganshi kenan, tana son sanin ko shi waye, how did he looks, tana wannan tunanin kuwa taji reply ďinsa..
     _’xaki ganni sanye da farar shadda ynxu ina tunkaroki_…

Cike da xaquwa ta ďago da sauri, caraf suka haďa ido dashi,
Wani babban mutum ne sanye cikin farar shaddarsa da hula akansa, mai kakkauran jiki, ta tashi tsaye daga inda take xaune xuciyarta na bugawa Kada dai shine wannan, no it can be him, wata xuciyar nace mata idan shine fa, accept him yana sonki ya damu da ke…
Ga mamakinta mutumin ya wuceta batare da ya mata mgn ba, nan da nan ta bata rai kenan yana nufin ni xn masa mgn….
    _’ban ganki ba….._

    taja tsaki a fili, taji haushin nuna ko in kula da yayi akanta, sai tayi fushi yama raina mata wayo bayan sun haďa ido xai ďauke kansa yayi ficewarsa, da sauri tabar gurin itama sai ta rama, ta cusa wayarta a jakarta tana tafiya taji dariyarsu sawwam da Suhaib akan Mota, ta juya tana kallonsu wayace suke kallo suke dariya ďagowar da sawwam xaiyi suka haďa ido, sai ta fashe da dariya cikin matuqar mamaki suka xuba mata ido suna kallonta,
Dariyarta yau sawwam acikin manyan kaya, farar shaddar tayi masa kyau, ita kanta tasan tanayin dariyar ne dan taci xarafinsa domin har nuna sa take da yatsa qasa da Sama,
Cikin tsarguwa yake kallon jikinsa, baiga wata miskila a tare dashi ba,
Suhaib yace ita wannan fa? Kai tsaye sawwam ya bashi amsa da,
‘mahaukaciya mana, kasan mahaukata suke irin Wannan dariyar ta babu gaira babu dalili,
Suhaib yace ita kuwa tana cikin yanayi cos haukarta bamai warkewa bace, suka taba hannayensu suna dariya sosai suma,
‘Kuma ai mahaukatan ne, Mtseww taja tsaki tana hararar sawwam,
‘wai dan ace yayi kyau, bakayi kyau ba, ni nasan dan ka birgeni kayi Kuma baka birgeba, Sam baka yimin ba👌🏻 akai kasuwa ummulkhairi bataso akai kasuwa ta fice tana dariya sosai,
Yayi shiru yana kallonta a qasan xuciyarsa yaji daďi, yasan yayi kyau ne take kushewa, ya diro daga Saman motar yana faďin,
‘muje Suhaib wannan ta bata min rai na fasa ganin sahibata😝,

Khairi Kuwa qin Kunna wayarta tayi she mean it fushi take da sahibinta tunda ya mata Wulaqanci, sai dai tana mamakin girman mutumin, black beauty ne, tana xaune Alawiyya ta shigo itama a gajiye.

Yau ya Kama weekend sai ta shirya ta nufi cikin gari saloon, saboda kanta ya cunkushe guri ďaya yana buqatar gyara,
Bayan ta gama ta fito tana tafe tana kallon yanayin garin, bata fiye fitowa ba sai idan tare da Alawiyya ne,
Wasa Wasa sai tafiya take takasa samun napep ga shi magrib ta kusanto,
Tayi tsaye bakin titi cike da jin haushi, tana gurin faďa ya kaure tsakanin wasu matasa uku, ga mamakinta kowa da makaminsa daka gansu Kaga yan ta’adda,
Da sauri ta tsallaka titi ta ďayan bangaren hankalinta a tashe, ganin mutane sai gudu ake kowa na ta kansa,
Tafiya take sauri sauri bata ko waiwayen bayanta kamar daga Sama taga Mota ta tsaya gabanta taja da sauri, batayi tunanin komai ba ta faďa motar cikin tashin hankali,
Ta sauke ajiyar xuciya tana kallon masu Faďan ta window kafin ta juyo dan ganin Waye ya taimaketa,
Sawwam ne, xuciyarta tayi wani irin bugawa kamar xata  faďo ta qirjinta,
Ko kallonta baiyiba fuskarsa a murtuqe, fitowarsa kenan daga wurin snooker ya ganta tana wannan uban Saurin ganin ana faďa, Unguwar ce kullum cikin faďace faďace suke shima ba koda yaushe yake xuwa gurin ba,
Ta maida kallonta ga titi bayan ta haďiye wani yawu da kyar, ba bakin mgn sai ma xuciyarta dake bugawa,
Har suka iso ba Wanda yayi mgn acikinsu, ta soma qoqarin bude motar, Kamar daga Sama taji muryarsa na faďin,
‘Kibi ahankali wannan Unguwar ba gurin xuwa bace….
Batayi mgn ba burinta taga ta fita daga motar, tana fitowa yaja motar da qarfi yabar gurin batare da ya waiwayetaba, tana tsaye a gurin tana kallonsa har ya fice.
Pherty xarah

        &

Ummy shatu

My wattpad Phertymerh1
[25/02, 7:28 a.m.] Baby aysha: *RAMUWAR GAYYA…*💘

  _Love story 50,50_

*_UMMI A’ISHA_*

          _With_

*_PHERTYMERH XARAH_*

   18

*N*annauyar ajiyar zuciya ta ajiye ta juya ta nufi hostel bayan ta daina hango motar sawwam din,

“Ikon Allah yau kuma sawwam ne ya taimakeni mutumin da idan banda fada babu abinda yake hadani dashi amma yau gashi shine harda taimakona..” Ta fadi hakan acikin zuciyarta,

Kasancewar tana fashin salla ya sanyata bin katifa ta kwanta tana nazarin masoyinta wanda ya shareta ya nuna halin ko in kula akanta bayan kuma tasan ya ganta,

“Hmmmmmm” taja ajiyar zuciya, k’arar shigowar sako cikin wayarta ne ya sanyata dan tashi daga kwancen da take,

  _kiyi hakuri bamu haduba,amma gaskiya naso ganin kyakkyawar fuskarki_

Kamar ba zata mayar masa da amsa ba domin fushi take dashi sai kuma wata zuciyar tace ta mayar masa da amsa,

_ai ni dear fushi nake dakai, bana nan ma dawowata kenan daga cikin gari._

Mintuna kadan taji shigowar wani sakon,

  _kiyi hakuri masoyiyata wallahi nima ba haka naso ba, me kikaje yi acikin gari?_

Murmushi tayi da alamar ta hakura kuma a yanda ta ganshi bata jin zata daina kulashi domin shima babu laifi kyakkyawa ne,

_gyaran gashi naje_

Ta mayar masa da amsa,

_wow, nasan dama kinada gashi ko ban ganiba i know yayi kyau.._

Murmushi tayi tana tunano kyakkyawar fuskarshi,

_kar kayi saurin yabona ni banida gashi karma ka sakani acikin sahun masu gashi kuma daga baya kaga bani dashi ka tsaneni.._

Mikewa tayi bayan ta tura masa sakon ta nufi flask din data adana abincinta, daukowa tayi ta zauna ta fara ci tanayi tana murmushi domin bata da burin da ya wuce na ta cikawa mahaifinta burinsa kamar yadda ta daukar masa alkawari,

K’irrrr taji sahibinta ya dawo mata da reply, cikin zakuwa ta bude sakon tana murmusawa,

_hmmm kece kike ganin haka, ai bazan taba tsanarki ba har karshen rayuwata, idan akwai abinda zanyi to bai wuce na kara sonki ba, ni ko kinada gashi ko baki dashi ina sonki domin ba gashinki nake so ba_

Dariya tayi batare data mayar masa da reply ba domin kudin wayarta ya kare, kamar ya sani sai kawai jin karar shigowar sako tayi tana dubawa taga recharge card ya turo mata na 2,000 through transfer,

Sakon godiya mai dauke da kalmomin soyayya masu sanyaya zuciya ta tura masa tayi shirin kwanciya ta kwanta tana tunanin sahibinta acikin zuciyarta.

  Koda sawwam ya fita daga cikin school din gidansu ya hara yana tuki yana tsaki,

“Mtswww nima dai wallahi ban yiba, meyasa na taimaketa? Meyasa na tsaya har na dauketa acikin motata? Mtswww may be ma tayi tunanin ko sonta nake alhalil ni ba burgeni tayi ba…” Ya fadi haka cikeda jin haushin kansa saboda taimakon ummulkhairi da yayi,

“Hmm nan gaba ko me zai sameta sai dai ya sameta amma bazan sake taimakonta ba” yafadi bayan yaja dogon tsaki,

Cike da wannan haushin aranshi ya shiga gida, falon mami ya shiga bata falo dan haka ya bita cikin dakinta,tana zaune a bakin gado ita da yar aminiyarta Rukayya,

Tsuke fuska yayi yana ciccin magani,

“Mami ashe kina ciki?” Yafada fuskarsa babu annuri, ita mami yanzu abin nasa yafara bata tsoro domin indai kana son ganin fushinsa to akawo budurwa gidan nan za aga bacin ransa,

“Wallahi muna ciki Rukayya ce tazo yar gidan hajiya Amina..”

Ta kasan idonshi ya kalli fuskar yarinyar sannan ya dire kallonsa akan kafarta, shi bai taba ganin kafar da take yi masa kyau kamar ta ummulkhair ba sai dai yau yaga kafar tata tayi fari sol kamar ta baturiya may be menses take ya raya hakan acikin ranshi,

“Wai sawwam baka jine tana gaisheka..?”

Muryar mami ta dawo dashi cikin hayyacinsa, firgigit yayi yafara shafa sumar kanshi,

“Mami wallahi banji ba, umm lafiya lau” bayan ya juya ya kalli Rukayya wacce keta faman sussunkuyar da kai cikeda kunya, ita mami sai abin yayi mata dadi domin duk a tunaninta Rukayya tayi masa sai dai shi acikin zuciyarsa sam yarinyar bata yi masa ba,

Juyawa yayi ya fita yana cije lebenshi na kasa, dakinshi ya shiga ya zauna ya jawo katuwar laptop dinshi yafara danne danne.

  Dare ya raba yana kallon wani american film mai suna prison break, bashi ya kwanta bacci ba sai wurin karfe 3 nadare wannan dalilin ne yasa da safe ya makara domin sai karfe 11 ya iya tashi,

Ganin ya makara yasa ko makaranta bai shiga ba yayi zamansa agida ya shiga daki ya kulle kanshi ya kunna kallo.

  Ummulkhair yau sam bata ga sawwam ba abokin fadanta,kasa hakuri tayi har sai da ta fadawa alawiyya,

“Alawiyya yau fa banga mutuminki ba wannan dan rainin hankalin, ko kin san jiya bayan nadawo daga saloon shine y kawoni?”

Dariya alawiyya tayi ta dafa ummulkhair “kodai har kun daidaita kanku mu kuka mayar garori..”

“Allah ya sawwake, ni inada masoyina jiyama katin 2000 ya turo min, kuma in baki labari dazun nanma muka gama shan soyayyarmu…”

Dariya alawiyya tayi harda rike ciki, “kema dai wallahi baki da wayo, to kika sani ko sawwam dinne yake yimiki text massage?”

“Bashi bane ai indai sawwam ne to da kuwa sai nafasa wannan wayar tawa, nasanma ba shi bane domin ai shi inada number dinshi tun lokacin da yayi min massage ya bani hakuri..”

“Hmmm to shikenan..” Alawiyya tace da ita tana murmusawa,

“Ni kinga yanzu siyayya zan je, kayan kwalliyana sun kare gashi kuma kayan amfani na ma sun kare, jiya abba ya turo min da kudi..”

“Sai kin dawo” alawiyya tace da ita tawuce,

Juyawa ummulkhair tayi ta fita ta samu keke napep tace ya kaita store zatayi siyayya,

Wani babban store ya kaita ta shiga tabarshi awaje yana jiranta,

Sawwam yana daki yana bacci mami tazo ta tasheshi akan yazo yakai Rukayya shopping domin ita momy so take tayi amfani da wannan damar sawwam ya dan shaku da Rukayya din kafin tabar gidan,

Yana kunkuni yana komai ya shiga wanka ya fito duk ransa abace shi da yasan hakane ma da yayi tafiyarsa sch akan ya zauna yakai wannan yarinyar shopping,

Ransa abace ya shiga sashen mami yana sanye da blue din jeans da bakar riga, batare da yayi magana ba ya juya ya fita domin yasan sun ga shigowarsa,

“Tashi kibishi kinji, kiyi hakuri dashi kin san wani irin yarone sawwam sam baya son kula yanmata narasa dalili..”

Mami tace da Rukayya, tashi Rukayya tayi tabi bayanshi tasha kwalliya cikin leshi golden colour mai duwatsu ajiki tasa farin mayafi da farin takalmi sai kamshin turare takeyi,

Acikin mota ta sameshi ta shiga suka tafi, bakin glass yasa kamar yanda ya saba amma fuskarshi babu wlwala tamkar zai saka kuka haka yakeji,

Perfect store ya nufa da ita yana zuwa yayi packing ya fito itama ta fito suka shiga tare, layin kayan kwalliya suka bi Rukayya tana dan daddaukar abinda yayi mata, suna karyo kwana ya hango wata kamar kairi hannunta rikeda karamin basket ta cikashi da kaya,lokacin da sukaje kusa da ita ne yagane ashe ita dince, pad ta diba guda biyu tasaka acikin kwandon, kura mata ido yayi da abinda ta dauka,

“Tana off kenan ni dama nasan arina domin naga kafarta ta sake yin haske fiyeda ko yaushe…” Yafada yana kallon kafarta, barin Rukayya yayi abaya ya matsa wurin ummulkhair,

Kamar besan da ita ba yayi, tana jiyowa itama ta ganshi sai yan kalle kalle yake yi,

“Basai kin nunawa duniya kin fara menses ba idanma baki dauko wannan abun kin tallata ba mun san kin fara..”

Harararshi tayi aranta tana ganin kokarinshi na iya fada mata haka da yayi,

Banza tayi dashi saboda ta fuskanci shima kwallo ne idan ta biye masa hayaniya zasuyi awurin,

Wuceshi tayi ta nufi wurinda za a lissafa mata kayan, hakan da tayi yasa sawwam yin murmushi domin yafara samo lagonta, hanzartawa yayi yaje wurin da take tsaye,

Angama lissafi kenan an zuba mata kayan a leda,

“Barshi zan biya miki kinci darajar budurwata…” Ya nuna mata Rukayya da dan yatsanshi wacce ita rukayyan ma bata san abinda yake faruwa ba kasancewar tana can tana zabar turaruka, bude ido ummulkhair tayi ta kalli yarinyar da ya nuna mata a matsayin budurwarshi…..

aishaummi.blogspot.com

Ummi Shatu

Pherty Xarah

   19

   Ta tsaida idanuwanta sosai tana kallonta kafin ta juyo tana kallon sawwam suna haďa ido ya kanne mata ido ďaya cikin murmushi,
Ta ďauke fuskarta haďe da gyara tsayuwarta dai dai lokacin aka gama sanya kayan acikin Leda,
Ta karba batare da ta Kalle sa ba ta nufi inda Rukayya ke tsaye da turare a hannunta ta miqa mata ledar,
Kallon mamaki Rukayya ke mata alamar kayan menene, ke Wacece? Khairi ta tabe bakinta haďe da nuna sawwam dake kallonta da tsananin mamaki a fuskarsa,
‘haka yace inkawo maki, wai yana kunyar baki da hannunsa saboda pad ďin dake ciki,
Rukayya najin haka ta saki murmushi cikin jin daďi ta Karbi kayan a kunyace ta kasa haďa ido da sawwam ynxu kenan ya fara sonta,
Khairi ta juya ta fice sai da taxo dab dashi tayi masa wani kallon Baka isa ba kana tace,
‘Nafi qarfin naci albarkacin budurwarka, so budurwarka ka biyawa kuďi ba ni ba, Mtseww tasa kai ta fice,
Ya tabe bakinsa haďe da ďaga kafadunsa alamar ko ajikinsa ya dubi Rukayya dai dai lokacin da take duba kayan dake cikin ledar,
She don’t need them….. ta bata fuska, ai wannan provision ne, is not a gift da xai ce xai bata, did he mean gidansu ya ďauka basa shan tea da indomie ne or what bayan yasan ita ba xaman hostel takeyi ba, but ga pad, ta soma juya ledar a hannunta,
Sawwam ya miqa hannu ya karbi ledar ya juya batare da ya sake kallonta ba
ganin haka tabi bayansa tana faďin,

‘Baka biya Kuďin kayan dana ďauka ba….

Batare da ya Kalle taba yaje ya biya kudin suka nufi Mota, ta kasa haquri bayan ya tayar da motar sun nufi hanyar gida ta dubesa,
‘amma wannan kayan na waye?

‘wadda kika karba a hannunta meyasa baki tambayeta ba?
‘tace nawa ne daga gareka, but kayan dake ciki seems like not to be mine…
‘yeah kayan ta ne ta miki qarya and what else? Nan da nan ta bata fuskarta taji wani kishi ya taso mata har batasan sanda tayi subutal baki ba,
‘Ita kuma Wacece? ya ďan dubeta kafin ya maida hankalinsa ga tuqin da yake,
‘itace ummulkhairi, wadda nakeso xn aura…

‘Hmmm ta sauke naunanniyar ajiyar xuciya gabanta na faďuwa tsananin sonsa da kishinsa sun mamaye xuciyarta,
‘Ni kuma me kake nufi dani? Yayi mata wani irin kallo,
*’Ni da ke* mun taba mgnr so ne, inba yau da Mami ta tirsasani ba na taba tsayuwa dake ko mgn dake? ke a tunaninki kamata xa’a xabawa mace Kuma na amince, kibar umma ta gama neme nementa ta barni ba wacce nakeso daga cikin xabinta…… kamar xatayi kuka saboda takaici,
‘Amma Mami tana son muyi aure saboda tana tsinkayo *wani haske* a tattare da rayuwar auren mu,
‘A gareni babu shi, ki gayamata bn amince ba, yayi parking motar ya fito ya barta ciki ya nufi part ďinsa da kayan khairi a hannunsa, da kyar ta fito daga motar da kayanta a hannu ta nufi cikin gidan yanayinta ya Sanya Mami xargin wani abu,
‘me ya faru naganki wata sukuku haka ko sawwam ne,
‘A’a Mami…. ta nuna mata kayan Mami taji daďi sosai ganin Kuďin daya kashe mata,
‘Rukayya ta tashi tana fadin Bari naje gida kada hajiya taji shiru,
‘Ina sawwam yaxo ya kaiki gida,
‘A’a Mami kibarshi xn shiga napep,
‘baxaa yi haka ba kijirani, ta nufi sashensa,
‘yana ďaure da towel a qugunsa ta shigo,
‘wanka xakayi kenan to bari nace ta jiraka idan ka gama ka sauketa gida,
‘Wacece Kuma? ya tambayeta Idanunsa qasa qasa,
‘Rukayya mana, yaja guntun tsaki ya nufi hanyar toilet,
‘tayi tafiyarta Mami, ni ba inda xnje idan nayi wanka karatu xnyi, bai saurari amsarta ba yayi shigewarsa,
‘haka taje ta lalaba Rukayya ta tafi tana mamakin sawwam shi wannan da bayason son mace kodai aljana ke auren sane?

Koda ya fito wanka bayan ya shirya ya ciro kayan yana dubawa,
Duk kayan tea ne, sai macaroni da spaghetti, ya ciro pad ďin yana kallo yana juyata a hannunsa bakinsa a tabe,
‘lallai ma yarinyar nan, ganin tayi ta girma shiyasa take min rainin wayo, ya cillar da duka pad ďin gefe ya haďa mata sauran kayan a Leda da niyar gobe xai qara mata wasu akai ya kaimata….
Khairi Kuwa ko kaďan batayi Dana sanin bar masa kayan ba tunda da kudinsa ya biya sai dai gobe ta qudira akan xataje ta qara siyayyar,
Duk wani motsi da xatayi Rukayya take gani a idanuwanta batasan meyasa ta damu da yarinyar ba, Mtseww taja tsaki kafin ta kwanta,
Washe gari sun fito library da Alawiyya suna tsaye suna Mgnr exam ďinsu saurayin Alawiyya naxo, suka gaisa kana suka Tafi suka barta,
Duk yau bataji message ďin sahibin ta ba daga inda take tsaye ta tsinkayo sawwam shi kaďai tsaye a gurin motar sa batare da tunanin komai ba ta nufesa, suna haďa ido tayi far da idanunta
‘Abdul nake nema…. ya ďan dubeta cikin basarwa,
‘kodai ni abokin Abdul kike nema Kuma kinganni sai anjima, taja ta tsaya a kusa dashi haďe da sarqe hannuwanta a qirjinta,
‘daďina dakai kana so kana basarwa just send your request meyiwuwa  it will be accepted….. yayi mata wani kallo bayan shima ya jingina a motar kamar yanda tayi idan ka kallesu xakayi xaton wasu masoyane sabanin tunanin mutum,
‘sai ynxu nagane nufinki akaina, gwanda da kika fitomin da maitarki wato na turo request kiyi accepting and I will not request, bansan me xanso anan ba Abdul dayace yana so kijirasa ni ai kinga budurwata a jiya……
‘yes na ganta, ta juyo tana kallonsa shima ita yake kallo,
Xatayi mgn ya tsaidata ta hanyar bude motarsa ya ďauko mata kayanta ya miqa mata,
‘saqo ne daga matata Wai a maida maki ta gode mijinta xai iya siyamata fiye da Wannan, kamar baxata Karbi kayan ba ta karba tana dubawa ya qara kaya sosai a ciki sai dai ba pad ďinta Kuma baxata iya tambayarsa ba, ta tabe bakinta,
‘ka gayamata Nagode nima ta Jira nawa saqon ta juya ta fice…..
Pherty

   &

Ummy shatu

*RAMUWAR GAYYA…*💘

_Love story 50,50_

*_UMMI A’ISHA_*

          _with_

*_PHERTYMERH XARAH_*

   20

*D*akatar da ita sawwam yayi ta hanyar cewa,

“Wait yanmata…”

Tsayawa tayi cak batare da ta jiyo ba, ahankali ya taka zuwa inda take tsaye ta bashi baya,

“Basai kin biyo tanan zan san cewar kina sona ba, ni nasan babu wani abdul da kike nema ni kike nema kawai dai kin fake da neman abdul ne gudun kada ki ji kunya, sai dai kuma kin makaro domin ni bakya daga irin matan da nake son aura, amma may be zan iya karawa dake a matsayin ta biyu bayan na auri sarauniyar mata wacce kika gani jiya…..”+

Murmushi ta saki har lokacin bata jiyo ta kalleshi ba,

“Sawwam kenan, gaskiya zuciyarka ta zalunceka da har wai ta yaudareka da cewar ni ummulkhair ina sonka, hmmmm ikon Allah, wallahi kayi kuskure da kake zaton ina sonka, ni baka yimin ba abdul abokinka shine yayi min shi nake so….”

Dariya maganarta ta saka sawwam,

“Amma ke yarinya ce ke kina tsammanin abdul sonki yake?? Gaskiya kin yaudari kanki..”

Sai alokacin ta juyo ta kalleshi,

“Ko kuma kai ka yaudari kanka ba”

“To ya isa wuce kibar nan….” Yafadi bayan ya gintse fuskarsa,

“Kai har ka isa ka koreni daga nan? Ko ka dauka har yanzu tsoronka nake, to banyi niyyar tafiya ba har sai lokacin da nayi niyya..”

Matsawa yayi kusa da ita,

“Fine, ai kinga abinda nayi miki rannan da daddare ko? To wallahi yanzu ma indai baki bar wurin nan ba haka zanyi miki a idon jama,a and kinga kece zakiji kunya baniba ni hakanma wani suna zai sake saya min….”

Kamar ba zata tafiba sai kawai tayi gaba ba tare da tace dashi komai ba, hannuwanshi duka ya saka cikin aljihunshi yana murmushi,

“Ashe dai har yanzu din kina tsorona” ya daga murya yadda zata iya jiyoshi,

Ko saurarenshi batayi ba taci gaba da tafiyarta, ahanya suka haduda alawiyya wacce tun daga nesa take mata murmushi,

“Sai yanzu kuka gama soyewar?” Alawiyya tace da ita cikin tsokana,

“Hmm muje hostel kedai kiga kayan da ya kawo min, kullum kina cewa soyayya muke idan nace miki ba haka bane sai ki k’i yarda muyita musu dake to albishirinki?”

“Goro..” Alawiyya ta amsa mata,

“To wallahi jiya naga budurwarsa wacce zai aura kyakkyawa da ita yar gayu…”

“Shine yace miki budurwarshi ce…?” Alawiyya ta tambayeta,

“Ehhhh shine ya fada min mana wai harda wani cewa naci albarkacinta ya biya kudin kayan da na siya..”

Dariya alawiyya ta fara wadda har saida ummulkhair taji haushi,nan ta zallake gaba ta barta abaya tana cewa,

“Idan kin gama dariyar sai ki taho nidai nayi gaba…”

Har sukaje hostel suka shiga daki alawiyya bata daina dariya ba, dakyar ta dakatar da dariyar ta kalli kairi,

“Kairi kin san me nake yiwa dariya? Wallahi sawwam dinnan A ne, ayanda na fuskanta kece budurwar tasa ita kuma waccan nufinshi taci albarkacinki zai siya mata kaya, watakila ma awurin ya ganta ba tare suka zoba….”

“Hmmm sai kiyi kuma, ke dama bakya yarda da Abu acikin sauki sai anyita musu dake, keni ko tare suka zo koma awurin suka hadu duk su ta shafa ba kairi ba, fito da kayan kiga…”

Ummulkair ta fada tana cire hijab din jikinta,

Zama alawiyya tayi ta fara firfito da kayan, provision ne sosai su indomie,kifin gwangwani, kayan tea, cabin, cornflakes, dasu taliya zuwa macaroni, sannan ga wata leda daban mai kyalkyali da kayan kwalliya aciki irinsu powder, jan baki, jagira da turare,

“Ummmmm lallai sawwam ya iya siyayya, to yanzu in tambayeki pls, shi wadannan kayan da ya kawo miki su kuma a matsayin me suke? Ko suma duk acikin fadan ne?” Alawiyya ta tambayeta tana murmushi,

“Oho…..” Ummulkhair ta bata amsa bayan ta dauki wayarta domin yau kwata kwata bata ji mutuminta ba shiyasa zataji ko lafiya,

Text ta tura mishi domin tana son shima yasan ta damu dashi kamar yanda ya damu da ita,

_Farin cikin yau banjika ba ina fata kana lafiya aduk inda kake…_

Saida tayi sending din text massage din sannan ta mayar da hankalinta kan maganar da alawiyya keyi mata,

“Nidai kairi da ku yarda keda sawwam da karku yarda wallahi soyayya kuke yi, son junanku kuke yi, kina sonshi yana sonki kuma insha Allah sai kunyi aure kun haifi yara…”

Saurin toshe kunnuwanta ummulkhair tayi, “malama kar kiyi sabo domin ni inada abin kaunata wanda nake so..”

“Koma dai menene..”  Alawiyya tace da ita tana murmushi,

Tashi tayi taje ta fara kokarin dora girki tanayi tana jiran reply din sahibinta, kirrr taji ya turo, cikin azama ta ajiye tukunyar dake hannunta ta yi saurin daukar wayar tana duba sakon,

_Lafiya lau nake abar sona, ashe dama kin damu dani? Gaskiya nayi farin ciki sosai, i luv you…_

Ita kadai tafara dariya tana rubuta masa reply _I love you too_,

“Allah ya baki lafiya kairi” alawiyya dake kwance akan katifarta tace da ita,

“Amin amin, sahibina ne yace min i love you shine farin ciki ya kamani na mayar masa da reply…”

“Allah yasa sawwam ne…” Alawiyya tace,

“Ba amin ba..”

Kairi tace tareda ajiye wayar ta koma kan girkin da zata Dora.

  Sawwam yana tsaye har ummulkhair ta bace,

“Three pointer..” Ya jiyo muryar su abdul na kiranshi, juyawa yayi ya nufi kasan bishiyar da suka saba zama domin asalima nanne majalirsassu,

“Kaida wacce yarinya naganka atsaye ne three pointer?” Hafiz ya tambayeshi yana kiftawa su abdul ido,

“Wannan yarinyar ce wacce abdul yake so..” Yafada bayan yasha mur,

Dariya suka fashe da ita dukkaninsu,

“To kuma meye na bata ran daga tambaya?” Abdul ya fada yana kyakyata dariya,

“Kunga malamai sai anjimanku dama ni abinda nazo yi makarantar nan yau daban kuma nariga da na gama so sai kun fito kawai..”

Dira yayi daga kan motar da yake zaune ya wuce ya shiga motarsa yayi gaba yana jiyo su abdul suna yi masa dariya yana tafiya suka kafa zancensa shida kairi kan cewar son juna suke.

Lokacin da yaje gida ko sashen mami baije ba ya nufi dakinshi, kwanciya yayi yana tunanin dariyar da su abdul keyi masa, Kodai suna zaton son ummulkhair yake?

Girgiza kanshi yayi “wannan bazai taba faruwa ba…” Yafada yana mai cigaba da girgiza kansa,

Yana nan akwance yana kallon  wani American film a laptop dinshi mai suna bad boys, Mami ce ta shigo tana dauke da tiren abinci, daga shi sai gajeren wando da yar singileti ta maza,

“Sawwam yanzu dama ashe ka dawo shine baka shigo ka dauki abinci ba..?” Mami tace dashi bayan ta ajiye masa tiren abincin akan wani karamin stool,

“Mamina wallahi nagaji ne shiyasa..”

“To ai shikenan” Mami tace bayan ta juya zata fita, har takusa kaiwa kofa idonta ya sauka akan pad din da ya wurgar jiya, dawowa tayi da baya cikeda mamaki,

“Sawwam wannan fa…?” Mami ta tambayeshi cikeda mamaki,

Dagowa yayi ya kalleta sai kuma ya dauke idonshi domin yama rasa amsar da zai bata,

“Mami…. Mami na budurwata ne”

“To kuma sawwam in banda abinka ai sai kasata taji kunya idan kabata wannan abun, idan so kake ka yi mata kyauta ai kayan kwalliya zaka hada mata inyaso sai ka kara da wannan din aciki…”

“To Mami” ya amsa yana shafa kansa,

“A ina take?” Mami ta sake tambayarsa domin duk dadi ya isheta jin yanada budurwa,

“Mami a makarantarmu take amma yarinya ce dan yar level one cema”

Murmushi mami tayi “to ai hakanma babu laifi sawwam ni duk kasa ma nafara sonta tun kafin naganta, ya sunanta?”

“Mami sunanta Ummi, kinga hotonta” yace da mami bayan ya juyo mata da screen din laptop dinshi,

Gaban laptop din mami taje tana kallon hoton, wata kyakkyawar yarinya ta gani tana sanye da blue din material tayafa mayafi blue, gashinta ya zubo tagaba, fuskarta dauke da murmushi,

“Wai, wai, wai,zankadi amma sawwam ka iya zabe, wannan blarabiyar yarinyar fa? Tubarkalla wallahi kyakkyawa da ita, yaushe zaka kawo min ita?”

Murmushi yayi ya dauke kanshi cikeda kunya, “mami wannan din ba na fita kyau ba”

Dariya mami tayi “wallahi tafika kyau sawwam, ai ka zabo kyakkyawa..”

“To mami zata zo ta gaisheki amma ba yanzu ba”

“To ina jiranta sai tazo”

Juyawa mami tayi tafita cikeda farin ciki domin dama babban burinta taga sawwam yafara zancen aure.

    Washe gari da safe ummulkhair ta shirya kayanta ta tafi tasha domin tafiya bauchi kasancewar tun zuwanta bata taba zuwa gidaba gashi har semester ta dauko karewa,

Tun a mota tayiwa alawiyya text cewar tatafi gida sannan ta turawa sahibinta ma cewar yau tatafi bauchi, shiru shiru taji bai dawo da reply ba da alama baya kusa da wayar.

Karfe 2:30 na rana suka sauka agarin bauchi, cikeda farin ciki tahau napep zuwa gidansu, tun da tashiga gida ta ruga da gudu tana murna,

Dukka yayunta na falo suna kallon ball mamansu kuma na daki tana wanka shikuma abbansu yana sashensa,

Dagudu taje ta fada kan yayyenta tana dariya, “ko nemana bakwa yi?” Tafada idonta ya ciko da kwalla,

“Haba autar mama taya zamu ki nemanki” babban yayansu yace da ita yana bata hannu domin su tafa, alla alla take tayi tozali da mahaifinsu domin ta sanar dashi daddadan labari.

Da dare suka sami kebewa da mahaifinta, ta bashi lbrn komai da yanda abin yake xuwa a ynxu kan abinda ya turata,
Sosai yaji daďi ganin tayi kusa biya masa buqatarsa, ya kusa cimma burinsa akan qudirin daya ďauka a rayuwarsa,
Sai ya shiga sanya mata albarka tare da qara nuna mata yanda abin xai kasance, tana xaune tana saurarensa cikin ladabi har yagama faďa mata,
Wannan Karon taji daďin gida sosai sai nan nan ake da Ita tun daga iyayenta har yayyunta bama kamar mahaifinta, satin ta biyu ta soma shirye shiryen komawa Skul saboda sunyi waya da Alawiyya ta sanar da Ita exam is at the corner…..
Sahibinta Kuwa akai akai suna Kan charting, suna nunawa juna yanda sukayi tsananin missing ďin juna duk da ba wai haďuwa suke ba,
Sawwam Kuma 2days baiga mutuniyar ba sai da yaji lbr daga Alawiyya wai yaje gida tabe bakinsa kawai yayi amma har cikin ransa baiji daďi ba saboda ko sallama basuyi ba,
Tun daga lokacin shima bai qara shiga Skul ba baiga amfanin xuwansa mutuniyarsa bata ciki ba ganinta kawai farinciki yake sanyashi ballantana idan suna tare suna faďa yana kallon bakinta,
Su Suhaib sun xata bai lfy ne sukaje dubasa a gida ko lfy ya daina xuwa Skul,

‘haka kawai shine amsar da ya basu,
Kyalesa kawai sukayi cos sun san komai Abdul ya basu lbr, abin nasu mamaki yake basu shida khairi suna son juna sunqi su fito su nunawa juna sai dai suyita  noqe noqe suna basarwa suna harare hararen juna….
Sanda ta dawo ta shiga Skul itama bataga mutumin taba batasan yayiwa Skul ďin kaura ba sai ranar da ta dawo, ta tambayi Abdul ina sawwam

‘yana gida tunda kikaje gida ya daina fitowa shima,

Murmushi tayi Wanda batasan dalilin yinsa ba,
‘ka kirashi kace yaxo gani nadawo…
Abdul ya kirasa yace Fitowarsa wanka kenan amma gashi xuwa,
Fiye da minti talatin Kuwa sai ga motarsa ta shigo, tun cikin glass ya tsinkayota harda sauke ajiyar xuciya dai dai lokacin da yayi parking motarsa ya fito fuskarsa a ďaure sai wani basarwa yake yaqi su haďa ido da ita ya nufi inda Abdul,
Dariya ta soma yi tana kallonsa kafin ta maida kallonta ga Abdul,
‘Ana so ana kai kasuwa sai nayi mgn ace qaryane, saboda ni mutum ko skul ya daina shigowa Ashe dai ni ďin ta dabance,
Ya xare madubin idonsa yana kallonta yana kallon Abdul ya nuna ta da yatsa,
‘baabaa ita wannan da wa take, kagayamata inda ni take nafi qarfinta bnga abin so a tare da Ita ba,  bata isa ta hanani shigowa Skul ba sai rashin lfy….

‘gsky ne naga kayi rama sosai ta faďa tana murmushi,
Abdul dariya kawai yayi yasa kai ya fice, ta matso kusa garesa tana faďin,
‘daga ni sai kaine gayamin ynda kayi missing ďina,

‘yace ke kinyi missing ďina ne?

‘tace A’ah

‘yace tor nima banyi ba,

‘tace tor nayi

‘yace nifa banyi ba, bansan dalilin da xaisa nayi kewarki ba, ta tabe bakinta kawai,

‘Ina tsaraba, kinyi missing ďina Kuma shine baki siyamin komai ba,
‘ni banyi missing ďin ka Waďanda nayi missing sunayiwa tsaraba,
Ya tabe bakinsa alamar ko a jikinsa ya buďe motarsa ya ďauko wata baqar leda ya miqa mata,
‘ki karba inkinje xaki gani

da murmushi a fuskarta ta Karbi kayan, ta tabe bakinta batare da tayi godiya ba tayi masa wani kallo ta fice kawai.
Kallo ya bita da shi qasan xuciyarsa wani irin farin ciki yake ji kasancewarsa tare da khairi yau ba faďa,

Yanda yake ji kamar sun jima tare kamar su masoyane….
Itama khairi she don’t know why she feels happy today, ita kanta tana jin wani abu game da shi sai faman murmushi takeyi ita kaďai a ďaki ta xube kayan tana kallo exam success ne aciki har, wasu Kuma cards masu ďauke da test na love, ga biros masu kyau da tsada xasu kai goma, pencils, cleaner, sharpener, calculator da sauransu,
Ga wasu irin turarukka masu qamshi da tsada, harda sweet da chocolate, kaya gasu nan birjik sai kallo take tana mamaki,
Tana xaune taga saqon masoyinta,
  _My most brilliant achievement was my ability to be able to persuade my wife to marry me, will you marry me?_

Tayi shiru tana nanata karanta text ďin, how will she accepts to marry him, mutumin da basu taba xaunawa sun fahimci juna ba, batasan halayensa ba, sau ďaya rak ta taba ganinsa Kuma ya wulaqantata kamar baisan da Ita ba,
Ta tabe bakinta tana Mgnr xucci, if that is the case yaxo su fahimci juna, baxata gujesa ba mutumin dake sonka shine masoyinka a duniya, sai ta tura masa,
   _idan ba mun xauna mun fahimci juna ba, I will not marry you cos bansan halayanka ba_,

Tayi matuqar mamakin reply ďin sa har xuciyarta na bugawa,
  _kinfi kowa sanin halina, kamar yanda xn iya bada labarinki a jarida kema nasan xaki iya bada labarina a duniya, wace irin fahimta ce tsakanin mu bayan wacce mukayi a baya,_

Tayi Saurin kashe Wayar batare da ta tura masa reply ba, whatsapp ta hau cikin xaquwa tana so ta duba grups ďin taurarinta biyu ko an turo novels ďin da take matuqar so a yanxu, sabuwar number ta gani tayi mata text,
     _ina son ki khairi, kibani dama na nuna miki kalar kaunar dana ke maki._

Shi Kuma Wannan Waye ta faďa cikin tsananin mamaki, profile ďin sa ta duba cos taga photo akai, kafin yakai ga budewa tuni an cnxa dp xuwa wata jar flower mai ďauke da tambarin love,bataga ko Waye ba amma taji haushi sosai….
*

Sawwam Kuwa har ynxu pad din na ajiye a ďakinsa, idan ya kalleta xai tuna da khairi sai yayi dariya kawai ya girgixa kansa, shi kaďai yasan nufinsa na ajiye pad ďin……
Tun daga ranar sai suka xama friends ba faďa tsakaninsu sai dai tsokanar juna, olways xaka gansu tare cikin Skul suna yawo, yadaina xama dasu Abdul itama ta daina xama da Alawiyya,
Abincima tare suke xuwa suci, wani sa’in Kuma ita xatayi masa girki ta kawo masa yaci, har lokacin ta kasa yarda tana sonsa illah ta ďauke sa a matsayin friend ďin ta shi Kuma a xatonsa ta fara sonshi ne, har cikin gari xata bisa yaje yayi yawo da Ita su dawo,
Skul ďin kowa yasansu tare a ynxu, haka Mami tasan da xaman khairi a ynxu duk da bata taba ganinta ba amma tana adduar Allah ya sa ta gari ce. illah ta ďauke sa a matsayin friend ďin ta shi Kuma a xatonsa ta fara sonshi ne, har cikin gari xata bisa yaje yayi yawo da Ita su dawo,
Skul ďin kowa yasansu tare a ynxu, haka Mami tasan da xaman khairi a ynxu duk da bata taba ganinta ba amma tana adduar Allah ya sa ta gari ce.

Karatun exam ma tare sukeyi, da dare xai shigo da sunan karatu xasu yi idan sun haďu suyita faďa, in Kaga sunyi karatun nutsuwa to basu tare amma idan suna tare ba karatu sai faďa kowa da handout ďinsa a hannusa idan ya bata haushi tayi ta dukansa da Ita yana dariya ko ajikinsa,
Yau ma Faďan suke, kowane ya ďauki xafi,

‘karki qaramin magana,
‘kaima Karka qaramin magana,

Ya ďauki handout ďinsa ya koma gefe yana karatu ransa a bace ta bisa da kallo tana dariya kafin ta ciro wayarta tana daukarsa pic, sai ya qara tasowa yana faďin mugani yayi kyau,

‘kace karna qara ma mgn ina ruwanka dani,

‘ke meyasa xaki daukeni pic….. nan suka ďauki wata gardama ( Skul life is d best😂)
*Pherty xarah*

       &

*Ummy shatu*

*RAMUWAR GAYYA..*💘

_Love story 50,50_

_*UMMI A’ISHA*_

       _with_

_*PHERTYMERH XARAH*_

  22

Matsawa daga inda yake tayi tana harararsa,

“Wallahi zaka san ni ka yiwa haka akanma ka samu na daukeka a hoto da wayata shine zaka wani tsaya kana yimin…..” Shiru tayi bata karasa ba ta dauke kanta,

“Anyi miki din danme zaki daukeni ahoton, nasaki ne…?” Sawwam yace da ita shima yana harararta,

Mikashi wayarta tayi,

“Ungo karbi ka goge, ban son kayan tashin hankali…” Ta fada bayan ta murtuke fuskarta, shima kunu yasha ya karbi wayar sai kuma ya ajiye mata ya zauna akusa da ita,

“Haba kairu yanmata, yi murmushi muga, ki saki fuskarki mana, yi dariya nagani…”

“Malam nifa babu ruwana dakai dan Allah karka kara yimin magana..”

“Haka kikace?” Yafada yana kallon kafarta, lura da tayi da irin kallon kurullar da yake yiwa kafartata ne yasata janye kafar tata ta baza hijabinta ta lullube kafar,

Mikewa yayi batare da ya kara yimata magana ba ya koma can nesa da ita ya bude handout dinshi ya fara karantawa,kirrr yaji wayarshi ta soma kara kamar bazai dauka ba amma ganin Rukayya ce ke kiranshi yasashi dagawa,

“Hello baby, yakike…?”, cikin sauri ummulkhair ta daga kai ta kalleshi,

“Baby ina school karatu nake yi, kina son ganina ne? To da yaushe kike son ganin nawa, no kibari kawai sai anjima bayan sallar magrib sai nazo ki ganni, hakan yayi miki? Ok thank you baby, bye bye”

Ba ummulkhair ba hatta Rukayya sai da tayi mamakin jin wai sawwam ne yau yake amsa mata waya haka babu bata rai babu tsaki balle rashin yin magana, lallai yau ta taki Sa,a,

Ummulkhair har lokacin kallonshi take tana mamakin dama haka ya iya soyayya, kuma shine dan wulakanci ma agabanta zaiyi wayar,

“Nima bari na kira sahibina yaji…” Tafadi acikin zuciyarta amma koda ta kira sai taji wayar akashe, mikewa tayi cikeda takaici ta tattara takardunta zata tafi,

Cikin sauri yasha gabanta,

“Ina zakije? Wallahi yau bakiyi wani kwakkwaran karatu ba dan haka babu inda zakije sai kin sake kara awa biyu…”

Bata rai tayi ta kalleshi, “to ina ruwanka ko tare aka turo mu daga gida? Idanma naci zero ai b damuwarka bace…”

“Ehhh ba aturo mu tare ba amma yanzu muna zama tare so dole idan naga zakiyi ba daidai ba na hanaki…”

Sanin bazai barta ta tafiba yasata komawa ta zauna tana harararsa, shima wurinda yake zaune ya koma ya zauna yana karatu yana kallonta ta wani bata rai ko kallonshi taki yi ita ala dole tayi fushi saboda taji yana waya da budurwarshi to amma tambayar anan itace meye damuwarta da wayar da yayi da budurwarsa?

Wannan itace amsar data kasa bawa kanta,

Jin an fara kiran sallar la,asar ya sanya sawwam mikewa yana kallonta,

“Bari naje salla nadawo, dan Allah kije hostel ki dafa min indomie tunda ke nasan ba zakiyi salla ba…”

Wata harara ta watsa masa, “ehhh saboda ga kafura ba..”

“Am sorry, take it easy ni ba haka nake nufi ba..”

“To koma dai me kake nufi ni babu abinda zan dafo maka saboda babana ni kadai ya hadowa kaya batare da wani ba…”

Murmushi yayi ya tsaya yana kallonta, “malam daina kallona…” Tace dashi tana ciro takalmin kafarta, ganin bai daina kallonta ba yasata jefa masa abin tsautsayi sai akan fuskarshi, sunkuyawa kawai taga yayi ya dafe gwiwowinsa, kamar abin almara sai kawai taga jini yana fita daga hancinsa,

Dagudu ta tashi taje wurinsa,

“Sawwam habo kakeyi, na shiga uku….”

Jakarta ta dauka ta fita da sauri zuwa capteria, cikin rudewa ta debo ruwa masu sanyin gaske harda gudan kankara aciki, kudin kawai ta mikawa mai shagon ba tare da tasan ko nawa bane,

Kamar zata kifa dan sauri dahaka ta koma wurin sawwam har lokacin yana nan ayanda ta tafi tabarshi jinin ya taru awurin da yake diga,

Ruwan sanyin tafara kwarara masa akansa kwalla tana fita daga idonta,

“Sannu sawwam, sannu…” Shine kawai abinda bakinta keta furtawa, shi kuwa sawwam murmushi yake jin duk tabi ta rude tamkar wani wanda ya mutu,

Kansa ya daga sama ya zaro handkerchief daga aljihunsa ya goge fuskarsa, juyowar da zaiyi yaganta tana kuka,

“Meye nayin kuka kuma? Ashe kin damu dani amma shine harda yimin fushi yanzu yanzun nan, sorry stop crying…” Yace da ita yana murmushi,

“Dan Allah kayi hakuri wlh bada sanina bane…”

Murmushi ya sake yi ya zaro glass dinshi yasaka ya kura mata ido wanda har ita ajikinta saida ta fahimci wayo yayi mata kawai yana kare mata kallo,

“Sawwam wallahi ban yarda dakai ba dama nadade ina zargin cewa kana saka glass dinnan ne saboda kayita kallon mata….”

Ayanda tayi maganar sai abin ya bashi dariya, “sharri zaki yimin kuma?”

Zare glass din yayi ya mika mata, “karbi na baki…”

Karba tayi tasaka a fuskarta itama tana kallonsa,

“Kinga naje salla, amma ki fito min da abinci saboda yunwa nake ji….”

“To mai glass” tafada cikin tsokana tana dariya, shima dariyar ya fashe da ita ya wuce, kayanta da nashi ta tattara ta nufi hostel tana zuwa tayi wanka ta shirya tasake wasu kayan bayan tasha turare, indomie ta dafa musu taci sannan ta zubawa sawwam a karamin flask ta fita,

A inda suka saba karatu ta sameshi yana waya d abokanshi nan ta ajiye masa abincin da sauran kayan karatunshi takoma can baya dashi ta zauna,

Suna nan tare suna karatu har mangaruba tayi jin yanata cewa sauri yake yatafi gida saboda akwai wurinda zaije yasata tsarguwa da ko wurin wannan budurwar tashi zaije hakane ma yasata shirya masa plan ta yanda bazai tafi da wuri ba,

“Sawwam gaskiya bazaka tafiba sai ka koya min wannan calculation din gashi ko daya ban iyaba..”

Jin tace haka yasashi fasa tafiya, motarshi yaje ya dauko musu darduma da laptop dinshi ya kawo wurinda take,

Zama sukayi agabanta ya bude laptop din amma cikin sauri ya kare jikin screen din wai gudun kada taga hoton budurwarshi dake jiki,

“Wai me kaketa bobboyewa ne?? Idan bazaka koya min ba ka fada min natafi” tafada cikin tamke fuska,

“Hoton budurwata ne bana son kiga shiyasa na kare..” Ya bata amsa yana murmushi,

“Allah ya baka hakuri dadinta ma nidai ba mayya bace bare ace zan cinyeta kuma ni ba barauniya bace balle ace zan sace…”

“Ke barauniya ce mana, ko kin manta lokacin da aka samu waya a cikin jakarki sannan kuma nima ai kin taba satar min abuna….”

Katon text book din kusa dashi ta dauka takai masa duka tana cewa,

“Dama ka taba daura min sata yanzu ka fada min mai na satar maka…”

Littafin ya rike yana dariya harda kwarewa,

“Amma dai kinsan ba karya nayi miki ba ko….”

“Malam ban son ji ya isheni kawai, mai kallon mata kawai, kasa glass kayita kallon mata…”

“Dama maganar bata wuceba…” Yafada yana murmushi,

“Ehhhh” tabashi amsa, ahaka suka shantake batare da sunyi karatunba har 9 tayi sannan ta kyaleshi ya tafi domin ta tabbatar lokacin gida kawai zai nufa bazai iya zuwa wani wuriba.

Koda ya koma gidama bayan yayi wanka ya kwanta kiranta yayi awaya domin yabar mata laptop dinshi amma duk wurin da ya ajiye hotuna yasa security ta yanda bazata iya budewa ba,

“Kar ki kuskura kiyi min bincike a laptop dina…” Yace da ita cikin sigar jan fada,

“Ai wallahi baka da gaskiya tunda har kaki barin wurin hotuna abude…”

Dariya yayi sannan ya bata amsa, “gaskiyarce ta kawo haka akwai abinda bana son kigani ne…”

“Hmmm sawwam Kodai kaima kana kallon….” Shiru tayi ta kasa karasawa tana saurarensa,

“Wallahi karki yimin mummunan zato, ai nabar miki videos abude kiduba ki gani idan ina kallon shirme zaki gane idanma bana kallo zaki gane, shima hotunan akwai na budurwa tane ban son kigani..”

Tab’e baki tayi “Ku kuka sani dai, malam sai da safe karatu ni zanyi…” Ko jiran abinda zaice batayi ba ta katse wayar, shima ajiye tashi wayar yayi yana murmushi sakamakon tunota da yayi,

Ko Minti 20 ba ayiba ta kirashi,

“Gobe zaka kaini gyaran gashi…”

“Sai na kaiku tare keda budurwata itama tace zataje…”

“Toni nafasa…” Tabashi amsa,

“Yi hakuri ita nafasa kaita ke zan kai…”

Murmushi ta saki wanda har saida ya doki dodon kunnenshi….

aishaummi.blogspot.com

Ummi Shatu

Pherty Xarah

*RAMUWAR GAYYA…….*💘

_love story 50,50_

*Fertymerh Xarah*

            &

*Ummy Aysher*

      23

          ‘Murmushin me kika haka,

‘yaushe nayi murmushi, Mtseww saboda me xanyi ma tor?
‘ai naji sound ďin shine,

Ta tsinke Wayar da sauri tana dariya, can kuma sai taji alamar shigowar test bata duba ba cos tasan waye, ynxu she don’t have crush on him, idan ya matsu da Ita ya bayyana kansa gareta ta ganshi.
Washe gari bayan sun gama lectures koda suka fito da Alawiyya yana tsaye shida Suhaib suna jiranta,
Tun daga nesa suka sakarwa junansu murmushi, Alawiyya ta tabe bakinta tana fadin wonder shall never end, wai khairi da sawwam,
Sarai khairi taji ta sai dai bata kulata ba har suka qaraso gurinsu, handout ďinta gabaďaya ta ďora akansa tana tsaye a gabansa tana kallonsa shima kallonta yake,
‘ka ganni da tulin handout shine ko kaxo ka karbamin kayi tsaye kawai kana kallona,
Ya karbi handout din haďe da janye hannunta akansa,
‘Afuwan yayata,

Suka ďauki dariya,

Alawiyya ta soma tafiya tana faďin,

‘tafiya xanyi khairi nagaji Inaso nayi barci kafin nayi karatu,
Khairi ta jingina jikin motar kusa da sawwam tana faďin,
‘to qawata yau baxan rakaki ba,

‘ke kika sani ta fice, sawwam ya dubeta,
‘kije kici abinci kixo muje ko kin fasa ne,
‘oh yes harna manta but…. sai Kuma tayi shiru ta juya da sauri kawai xuwa hostel, sawwam yabita da kallo kafin ya maida kallonsa Ga Suhaib,
‘Su Abdul ina suka tsaya wai,
‘nima Yanxu can xnje Inaso na buga snooker, kai kuma nasan baxakaje yau ba saboda khairi,
‘kaje in nadawo xn sameku acan,

Suhaib ya fice yayinda sawwam ya shiga motar yana xaman jiranta,
Bata jima sosai ba ta fito daga hostel, tana qarasowa inda yake xaune ta yatsina fuskarta,
‘Ni nafasa xuwa saloon ďin ka tafiyarka,

Ya dubeta da kallon mamaki,
‘kin fasa baki gayamin ba tun ďaxu sai kika barni ina xaman jiranki,
Tayi masa shiru, Ransa a bace ya riqa murfin motarsa ya dubeta,
Matsa xn rufe motar, taqi ta matsa,
‘ki matsa mana,
Tayi masa banxa haďe da ďauke kanta gefe Kuma bata matsa ba,
Yayi shiru yana kallonta, sai Kuma ya tabe bakinsa haďe da maida qafafuwansa cikin motar ya Kunna music,
Murmushi tayi ta rufa masa motar kana ta xagaya ta shiga tana faďin muje ba dan halin ka ba,
‘yace a’a ni ba inda xanje ynxu kifita kawai daga nan sai gida,
‘nidai muje bana son qorafi nace ma baxan jeba sai ka tambayeni dalili amma kawani bata ranka,
Ganin ta bata rai ya sanyashi tada motar yana faďin ynxu na tambayeki gayamin dalili,
Ta fakaici idonsa tayi masa gwalo juyowar da xaiyi suka haďa ido, ta saki dariya sosai bada kai nakeyi ba,

baice komai ba har suka iso saloon ďin,
A tare suka shiga, bata sani mutane sosai aciki ba sai aka fara mata yana xaune a gefenta yana chatting binni binni yake kallonta yana mamakin kanta, baida tsawo sosai amma sai cika,
‘Ni kadaina kallo na haka,
Yaja tsaki haďe da juya mata,
‘kome xn kalla akanki ko gashin kirki bakida,
‘Naji dai amma a hakan kake kallo,
Mai saloon ďin murmushi kawai takeyi,
Bayan angama ya biya kuďi suka fito sai da ya biya da Ita tayi mata siyayya kana ya maidata hostel, kallonsa tayi,
‘ban gode ba,

Ya tabe bakinsa haďe da ďaga kafadunsa ko ajikinsa ya shiga motar sa yaja,
Haka suke kamar Farah da Assad
After a week aka sanya masu exam,

Ba Wasa kowa qoqarinsa to make it, sai suka daina haďuwa karatu makes them busy sai dai suyi waya,
Yau suka kammala exam ďin su, da yawa mutane yau xasu tafi gida wasu Kuma a gobe , khairi na cikin mutanen da xasu je gobe cos batason tafiyar marece,
Tunda ta fito exam take neman sawwam bata ganshi ba kuma bataga motarsa ba, tayi trying numbers baya shiga duk inda takesa ran ganin sa ta duba bayanan, so take ta sanardashi xuwan gidanta a gobe, da haka ta isa hostel ta soma parking na kayanta,
Alawiyya taxo tayi mata Sallama a ranar xata tafi, saduwar alheri Allah yasa munada rabon cin exam mudawo khairi,
Amin, Insha Allah ma xamu dawo,
Sukayi Sallama cike da kewar juna ta tafi,

Da dare bayan tagama haďa kayanta tana kwance da wayarta a hannu tana kiran number sawwam still bata shiga ko ina yaje, test ya shigo wayarta

    _’Gashi xaki tafi gida batare da kin gayamin matsayina a xuciyarki ba,_

Ta tura masa

   _idan baxaka damu ba Inaso na ganka._

Cikin qanqanin lokaci ya turo mata,
   _’kifito ina wajen hostel ďin ku ina jiranki._

Da sauri ta tashi ta sunkuci qaton hijab ďinta ta sanya yau xataga aljaninta Allah sa baxai mata Wulaqanci irin na ranar ba, tana tafe tana gwada number sawwam cikin Sa’a Kuwa ta shiga, harta gama ringing baa ďauka ba, taja tsaki dai dai lokacin da ta tsinkayota akan motarsa Idanunsa akan wayarsa, da sauri ta qarasa gurinsa tana faďin,
‘Ashe kana ganin kirana shine kaqi ďagawa ko, ya ďago yana kallonta,
‘saboda nasan xaki fito shiyasa bn ďaga ba, taja tsaki tana dube duben inda xata hango mutuminta,
‘me kike nema, kai tsaye ta bashi amsa da

‘wani nake nema Wlhy, ya dade yana min test a waya bansanshi ba bamu taba haduwa ba sai yau yace nafito yana wajen hostel ďin mu Kuma ni bn ganshiba,
‘ki kirasa mana,
‘nasha gwada kiran number baya shiga ai,
‘try and see….

Ba musu tayi dialing number Ga mamakinta sai taji Kukan wayar a hannun sawwam ta ďago tana kallonsa a hanxarce shima Idanunsa akanta,tsananin mamaki da kaďuwa sun hana mata magana, ya diro daga Saman motar ya tsaya gab da Ita kamar xai rungumeta har numfashinsu na bugun juna,
‘Am d one, nine sahibinki sunan da kika raďa min, lol

Ta haďe fuska sosai,
‘gwanda kisaki fuskarki, *Ni da ke* munjima muna son junanmu kawai girman Kai ya hana mu bayyanawa junan mu, so forget the past kada ma ki tuno komai ko qorafi duk abinda kikaga ina turo maki a test kinsan bamai iyawa sai ni cos nafi kusanci dake nasan komai akanki amma baki taba tunanin haka ba,
Ta sauke ajiyar xuciya tana tuna Alawiyya dake gayamata sawwam ne tana qaryatawa, no wonder duk sanda xai mata test ďin sai bayan sun rabu a skul ne ko kuma tana cikin Skul ďin yaga Abinda take, Ashe mutumin da tagani ranar bashi bane bayan ta qaraso daga wurin ta ganshi akan Mota har suka yi faďa amma bata taba kawo shi bane,
‘kinyi shiru, bana son ki tuna duk wani Faďan mu, forget ol d inconvenience ki tuna alherin dake tsakaninmu saboda *Alheri danqo ne*,

Ta tabe bakinta haďe da sarqe hannuwanta a qirjinta tana kallonsa, shima sai ya kwaikwayeta yayi yanda tayi hakan yabata dariya sosai bayan ta ďan matsa daga kusa dashi,
‘kigayamin kin yarda xakiyi soyayya dani, xaki aure ni?
Tayi far da ido tana kallonsa da murmushi, Hakan kaďai ya isa ya gane amsar tambayarsa koda bata bashi amsar ba……..
*pherty xarah*

       &

*ummy shatu*

[3/20, 21:58] Aysha~Humaira 😘: *RAMUWAR GAYYA..*💘

_Love story 50,50_

  *_UMMI A’ISHA_*

         _With_

_*PHERTYMERH XARAH*_
24

    _Masoyanmu muna ganin tarin sakonninku da kuma rokonku na mu kara yawan page din da mu keyi muku arana, kuyi hakuri hakika munso yin haka amma kuma saboda wani yanayi hakan bazai samuba da fatan zakuyi mana uzuri, muna godiya agareku bisa soyayyarku…_
  *W*ani kayataccen murmushi sawwam ya saki yana mai kallon fuskar ummulkhair,

“Banji kince komai ba, ina so kibani amsar tambayar da nayi miki, kina sona?”

Murmushi tayi ta kalleshi ta daga masa gira,

“Will you marry me?” Ya sake tambayarta, nan dinma girar ta daga masa kafin tasa tafukan hannunta ta rufe fuskarta,

“Kunyata kika fara ji tun yanzu..?” Yace da ita bayan ya zira hannayensa duka cikin wandonshi yana murmushi, babu shakka wannan ranar ta yau itace babbar rana agareshi bashida wacce tafita sai ko ranar aurensa da ummulkhair domin ya dade yana sonta tun ranar da ya fara ganinta,

“To yanzu kuma ya zakayi da auren Rukayya..” Ya jiyo ummulkhair ta jefa masa tambayar da bai shirya ba,

Juyo da kanshi yayi yana kallonta, shiru tayi tana kallon kasa tana jiran taji irin amsar da zai bata amma bataji yayi magana ba koda ta dago idonta ganinshi tayi ya zuba mata ido ko kiftawa bayayi,

“Am magana fa nayi maka ko bakaji bane?” Ta sake tambayarshi,

“Naji…” Yabata amsa yana wasa da agogon azurfar dake daure a hannunshi,

“To baka bani amsa ba ai..”

“To me kikeso nace miki? Nidai a iya sanina ke kadai nake so kamar yadda kike sona domin nasan kin dade dama kina sona amma kin kasa fada min saboda zurfin ciki..”

Murmushi tayi tana mai cigaba da kallonshi,

“Kaima ai kana sona amma baka fada ba sai yau…”

“Nafada mana ai nataba fada miki ke barauniya ce daga haduwa dake ranar farko kika tashi kika yimin gagarumar sata…”

Duka takai mishi, “me nasatar maka?, wallahi kadaina cemin barauniya..”

“Wallahi sai nafada ke barauniya ce..” Yasake maimaitawa yana dariya, takalmin kafarta tafara kokarin cirowa ganin haka yasashi matsawa zai gudu,binshi tayi suka fara zagaye motarshi dake ajiye awurin,

Ganin takasa cimmasa yasata yi masa dabara,

“Washhhh wayyo..” Tafada da karfi gamida tsugunnawa, cikin sauri ya dawo wurinda take,

“My lonely….. Meya sameki..”

Saurin rike rigarshi tayi tana murmushi,

“Gaskiya sahibi nafika wayo wallahi, yanzu kai dagaske yarda kayi wani abu ya sameni? Dama wayo nayi maka ai saboda in kamaka, yanzu fada min ta inda na zama thief, me nasatar maka..?”

“Zuciyata da tunanina duk kika hada kika sace a lokaci guda kinga kuwa ai babu satar da tafi wannan ko?” Yace da ita yana kallon fuskarta,

Shiru tayi ta tsaya tana kallonsa amma har lokacin tana rike da rigarshi,

“Oya sakeni to ko kuma in rungumeki…” Tun kafin ya karasa fadi ta sakeshi takoma jikin motarshi ta tsaya,

Tunani kawai take yi na rabuwar da zasuyi ita dashi gobe gashi tayi mutukar shakuwa dashi, tana tsananin sonshi wanda bata san da hakan ba har sai yanzu,

Gefenta yaje ya tsaya yana kallon wasu saurayi da budurwa dake zance acan gaba dasu kadan,

“My lonely nadade ina bawa Mami labarinki, kullum tana tambayata wai yaushe zan kaiki ku gaisa, gashi kuma zaki tafi gobe..”

Murmushi tayi tagyara wuyan hijabinta,

“Idan nadawo sai muje nagaidata, amma dan Allah kabani amsar tambayata ta dazu, ya zakayi da Rukayya?”

“Nifa Rukayya ba budurwata bace yar kawar mamice, da so suke su hadamu aure amma ni dama tun lokacin nacewa Mami inada wacce nake so, kuma da Mami taga hotonki shikenan sai ta bar maganar domin ke dinma kinfi kwanta mata arai, Allah Mami tana mutukar sonki…”

Ajiyar zuciya mai nauyi ta sauke domin tayi zaton ko dagaske itama Rukayyan budurwarshi ce,

“Hmmmmmm” tafada cikin ajiyar zuciya,

“Menene hmmmm, kina kishine?” Ya tambayeta yana kallon zoben dake makale a babban dan yatsanta,

“Ba dole ba nayi kishi,samun irinka ba abune mai sauki ba shiyasa bana son wata ta kwace min kai..”

“Babu mai kwace miki ni kamar yadda nima bazan bari wani ya kwace min keba, ina mutukar sonki ummulkhairi, ban san yanda zan kwatanta miki ba, i don’t know how to interpret it,but i know idan mukayi aure you will comprehend, because zan baki duk wata soyayya da kulawa…”

“Ya isa to..” Tayi saurin katseshi,

“Meye na katseni? Bakya son muyi auren ne?”

“A,a ba haka bane najine kafara kokarin wuce gona da iri..”

“Dannace zan baki kulawa shine zan wuce gona da iri? To wallahi ko kin k’i ko kin so sai nafada kuma sai kinji, zan baki kulawa sosai and kisani babu batun saka wannan hijabin ranar, awaje dai ban hanaki ba amma agida babu wannan maganar…”

Juya masa baya tayi ta kyaleshi bata tanka ba,

“Sannan Allah yasa kar akawo min ke kafarki tana fara dan nasan akwai matsala…”

“Sai kayi kuma” tace dashi bayan ta tura masa keya,

“Nadai ji dama ni idan za asamin ranar bikina farko farko za asamin”

Sai lokacin ta jiyo ta kalleshi,

“Nikuma nawa karshe…”

“Wallahi karya kike, karshe salon kizo min kafarki tana kyalli…”

Zubawa fuskarshi ido tayi tana kallonsa acikin zuciyarta tana mamakin yadda akayi wai sawwam yasan sirrinta haka, to wai tayaya yake ganeta ne?? Ita fa babu wanda yasan wannan sirrin nata sai ita sai mahaliccinta amma shi sawwam gashi yanzu yasani,

“Kasha kuruminka next semester da safa zan rinka yawo wallahi tunda ido kake saka min, eye dropper….”

“You can if you like, nidai tunda nariga da nagane shikenan ba zaki cuceni ba..”

“Kaga malam sai ka gayawa keya dan kwali yabaka ams…” Tun kafin ta karasa ya dungure mata keya,

“Keda ko gashin ma bakida shi…”

“Ehhh naji dai, ahaka kagani kake so…”

“Ai kuwa kisaka aranki ki ajiye komai dadewa zan auro miki kishiya mai gashi har baya…”

Juyowa tayi ta kalleshi, “Sawwam kabari, bana son irin wannan wasan, ban so kabari..”

“Wai kishina kike dan Allah?”

“Nidai nafada maka bana so..”

“To naji, nabari yi hakuri..” Yace da ita yana zaro cingum daga cikin aljihunsa, barewa yayi ya jefa a bakinshi,

“Nima bani…” Ta mika masa hannunta,

Na bakinshi ya ciro ya dora mata atafin hannunta,

“Wallahi babu wani ya kare, shikenan sauranshi…”

“Koma dai menene sai naci..” Tafada tareda jefashi cikin bakinta,

Kallonta ya tsaya yanayi yanda take taunar cingum din cikeda manyance,

“Ka aramin laptop dinka naje nayi kallon films tunda nagama exam”

Motarshi ya bude ya ciro laptop din ya mika mata,

“Gashi, zama ki iya tafiya da ita gida idan kina ra’ayi”

“A,a nidai bance ba, gobe zan baka kayarka kafin na tafi”

“Shikenan duk yanda kikace haka za ayi madam”

“Har nazama madam din?” Ta tambayeshi tana fara idonta,

“Ehh mana” yabata amsa yana duban agogon wayarshi, karfe 9 nadare agogon ya nuna, sam baya son tafiya yabar ummulkhair domin wannan lokacin yana cikin farin ciki,

“Sahibi katafi gida kaje ka huta” tafada bayan ta rungume laptop din a kirjinta,

“Zan tafi ai ko baki koreni ba, ina sone nagama kallon kyakkyawar fuskar matata”

Langabe kanta tayi gefe daya tana murmushi,

“Wannan fuskar kuwa dama ta sawwam ce shi kadai bayan shi duk wanda ya cika kallonta zan tsokale idonshi…”

Shima langabe kan nashi yayi kamar yadda tayi,

“Indai hakane kuwa to sawwam yayi alkawarin rike mamallakiyar fuskar nan bisa amana da kyautatawa, bazai taba rabuwa da ita ba sannan duk tsawon zamansu bazai sakata kukaba sai alokaci guda daya… Amma daga wannan lokacin zata dawwama cikin dariya”

Baki ta turo cikin shagwaba ta kalleshi,

“Wanne lokaci ne wannan?”

“Baki saniba? Nabaki assignment..” Yafadi yana murmushi,

“Wallahi a,a yanzu zaka fada min babu wani assignment da zaka bani, leave my brain to rest..”

Murmushi yayi “bafa zan fada ba, is an assignment kamar yadda nafada dafarko”

Kafada ta makale, “wallahi ban yarda ba”

Matsawa yayi kusa da ita,

“Ranar da aka kawo min ke a matsayin mata, nasan ranar da kuka zanzo nasameki kina kukan rabuwa da gida, dakyar zan iya lallashinki ki daina”

Lumshe idonta tayi har wani imagining din abun take acikin brain dinta,

“I love you sawwam” tafurta batare data sniba,

“I love you too my lonely..” Shima yafadi bayan ya sunkuyar da fuskarshi saitin tata,

“Sahibi bari naje nayi bacci, nagaji, kaima nasan ka gaji..”

“Kafin ki tafi ki bani wannan ring din na hannunki”

“Yayi maka kadan, nima dakyar idan zai fita daga hannuna saboda ya matseni..”

“Ai kuwa yau zoben nan a hannuna zai kwana” babu wata wata ya kamo hannunta yafara kokarin cire zoben,

“Sahibi bazai fita ba kabari kar ya yankeni” tafada tana runtse idonta,

“Yi hakuri…” Yace da ita tareda jan zoben da karfi nan yafita dakyar,

Hannunta tafara yarfewa tana kallonsa,

“Tunda ka rabani da nawa ai sai kabani naka”

“Gashi” yafadi tareda zare na hannunsa ya mika mata, karba tayi tasaka a babban dan yatsanta na tsakiya,

“Sahibi akwai wani saurayi da abbana ya bani hotonshi cewar in nemeshi muyi zumunci domin dan babban yayansu ne nikuma har yanzu ban ganshi ba sunanshi Faruk, bari kaga hotonshi, abbana yace tunda babansu ya rasu shikenan zumunci ya yanke tsakaninsu”

Wayarta ta bude ta mika mishi hoton ya karba yana gani,

“Wallahi nasanshi kuwa, bari ma naga kamar inada phone number dinshi…”

Wayarshi ya zaro ya fara laluben number din, saka mata yayi acikin wayarta ya bata,

“Yawwa naji dadi dama abba ya dade yana burin sake kulla zumunci dasu nasan yanzu zaiyi farin ciki”

Murmushi yayi “Allah yayi miki albarka”

“Amin sahibina, thank you, i love you, good night, have a nice sweet dream, bye” tace dashi bayan tafara tafiya da baya da baya tana daga mishi hannu,

Shima hannun yake daga mata batare da ya furta koda kalma daya ba,

Yana tsaye yana kallonta har ta bacewa ganinsa sannan ya shiga motarsa ya fita,

Hostel ta shiga ta zauna tafara neman layin faruk dakyar ta sameshi suka gaisa tayi masa bayanin ko ita wacece sannan sukayi sallama,

Kwanciya tayi rub da ciki ta bude laptop din sawwam take hotonta mai kyau ya mamaye kan screen din laptop din….

    Ta maida laptop ďin ta rufe haďe da ďora kanta akai, idanunta a lumshe tana tunanin sawwam,

da haka barci mai nauyin gaske ya ďauke ta tare da mafarkai iri iri a Wannan ranar,
Washe gari bayan tayi sallah ta soma haďa kayanta, tana fitowa wanka ta Kira sawwam dan shi xai kaita tashiga motar kasuwa,
Ta gama shirinta cikin koriyar atampha sosai tayi kyau duk da hijab ta sanya, ta janyo trolley ďinta ta fito hostel anan ta sameshi har yaxo da alama ko wanka baiyi ba dan kayan barcine ma ajikinsa,
Ya karbi trolley ďin ya Sanya a booth, ta koma hostel ta dauko laptop da sauran kayanta kana ta rufe ďakin tayiwa sauran qawayenta sallama ta fito,
‘sai kace wadda ake kora a gari, tunda safe haka khairi,

‘inaso na isa da wuri ne bana son tfyr dare, ta buďe motar ta shiga, ta ajiye masa laptop ďinsa a baya,

‘bnmayi kallon ba, barci ya ďauke ni,

‘ke har xaki iya barci kenan, ni tunanin rabuwarmu ya hana min barci, tayi murmushi har a xuciyarta taji sanya ta juya tana kallonsa,

‘sai kace wacce xatabar duniya gabaki ďaya, in banda abinka ai ga waya,

‘waya baxata gamsheni ba Kamar yanda xan gamsu idan muna tare, I will miss you,
‘miss you more kodan rigimarka,

Yayi dariya dai dai lokacin da suka qaraso tasha ya sami guri yayi parking, ya dubeta,

‘kijira bara na duba motar dake lodi ynxu, ta gyada kai tana kallonsa da murmushi har ya fice,
Bai jima ba ya dawo, ya buďe booth ďin ya ciro kayanta yakai motar, ya biya Kuďin kana ya dawo,

‘motar ma ta cika ke kaďai kika rage, ta buďe motar ta fito jikinta a sanyaye kamar karta barshi,

Tana fitowa yaja dogon hancinta yana murmushi ganin damuwa a tare da Ita,
‘ki Kula sosai kada kije daďin Mota ya bigeki kiyita barci har axo a wuce Bauchi,

Ta saki dariya tana kallonsa,

‘sai kace nice kai, da alama baka taba tafiya mai nisa ba, suka Jera tare suna tfy,

‘inda ma naje baki taba xuwa ba, ke daga Bauchi sai nan Skul, ta gyada kanta kawai tana tabe baki,

Sun jima suna Sallama kamar kada su rabu dole suka haqura da juna ta shiga motar, tana ďaga masa hannu yana ďaga mata, yana tsaye har suka fice kana ya shiga tashi motar ya fice cike da kewarta…..
Yana shigowa falon yaci Karo da Mami ta fito ďakin abbansa,
‘ina kafito da sassafe haka, ya ďan sosa kansa,

‘naje na kai khairi ta shiga motane yau xataje gida,

‘Ayya har ta tafi kenan baka kawo min ita naganta ba,

‘Mami inta dawo xn kawo maki ita ki ganta har sai kin gaji,

Tayi hanyar kitchen tana murmushi
‘Allah ya dawo da Ita lfy,
‘Amin yayi hanyar ďakinsa.

Khairi Kuwa tana isa gida ta kirasa a waya ta sanardashi,

Qannenta suka xagayeta cikin farin ciki kowa da irin labarin da yake bata iyakarta dariya,
Da dare ta sami mahaifinta tare da sanardashi abinda ke faruwa Wannan karon yafi wancan Karon farinciki ganin ganin burinsa na gab da cika, anan ma addua yayi mata haďe da sanya mata albarka,
Duk ba daďi takeji, she miss him alot, da’a Skul ne da Yanxu suna tare, shi kaďai take gani a xuciya,ruhi da kuma gangar jikinta,

Ta janyo wayarta tana qoqarin kiransa sai ga kiranshi, ta ďauka haďe da karata a kunnenta cikin murmushi,
‘guess where I’m? tayi shiru tana tunani,
‘inda Rukayya,
‘Nooo, bayan yaja guntun tsaki,
‘na baka gari,
‘gani Skul inda muke xama, yini ďaya kacal nayi kewarki,
‘nima kewarka nakeyi, tun ďaxu kai nake tunani sai naji gida ba daďi kamar naxama tsuntsuwa nadawo,
‘dana fi kowa farin ciki idan na ganki kusa dani a ynxu, so ya kika sami gida yasu Abba,

‘Gida Alhamdulillah, ya Mami,
‘Mami tana fushi dake kinxo baki mata Sallama ba,
‘Wayyo kabata haquri dana dawo xnxo naganta,
‘Allah yasa,
‘Amin

Nan suka cigaba da hirarsu cikin so da kewar juna.

Afuwan Pls masu qorafi, wannan ma ayi haquri dashi, inada test gobe next page xakujishi da yawa…..
Pherty xarah

      &

Ummy shatu
[3/20, 22:08] Aysha~Humaira 😘: *RAMUWAR GAYYA..*💘

_Love story 50,50_

*_UMMI A’ISHA_*

         _With_

*_PHERTYMERH XARAH_*
  26

*D*ukkaninsu suna dauke da kewar juna tamkar wadanda suka shekara da rabuwa,

Kwance take adakinta tana tunanin sawwam, duk hankalinta yatafi gareshi,

K’irrr taji wayarta na kara nan ta dauka a kasalance tana murmushi ganin sawwam ne,

“Sahibi…” Tafadi cikin siririyar muryarta me kamada ta yara,

“My lonely nayi missing dinki, amma kafin adawo school zanzo bauchi porpusely saboda ke…”

Zaune ta tashi daga kwancen da take,

“Are you serious??”

“Yes dear am serious but sai nadawo daga umarah, next week zamuje umara nida dad dina so idan nadawo zanzo gurinki..”

“Allah yadawo dakai lafiya sahibi, idan kaje dan Allah kayi min addu’a..”

Murmushi yayi yasake makale wayar a kunnenshi,

“Wacce irin addu’a kikeso nayi miki?”

“Kayi min addu’a Allah yasa ba zaka yimin kishiya ba har abada…”

Dariya yafara yi mata har saida yayi mai isarsa sannan yayi magana,

“Wai haka kike da tsoron kishiya? Ko bakiyi addu’a ba dama ni bazan yimiki kishiya ba my lonely…, you are the only one i love, ban taba son wata mace ba sai ke, only you i love,ki daina tada hsnkalinki akan sauran mata domin duk bana ganinsu idan ina tare dake, babu wacce zata hada miji dake indai nine mijin i promise you this…”

Zamanta tagyara ta tankwashe kafafunta tana murmushi,

“Kar kayi min alkawarin da bazaka iya cikawa ba sahibi”

“Wanne alkawarin ne bazan iya cikawa ba? Ni banida ra’ayin mata biyu ke kadai kin isheni rayuwata daga ni sai ke sai ‘yan yaranmu”

“Hmm kar dai sai lokacin yayi idan nace maka kayi min alkawari kace kai baka san maganar ba”

“Pls bar wannan maganar muyi wata, yara nawa kike so mu haifa? Tara ko goma?”

Dariya tayi kafin ta bashi amsa, “sai kace haihuwar babu wuya zaka wani ce goma, ai idan nayi biyar ma ka yaba min”

“Biyar? Gaskiya sunyi kadan ina laifin ma takwas” yafadi yana yimata dariya,

“Hmmm sawwam kenan kayi mana addu’a dai akan Allah ya bamu masu albarka”

“Insha Allah zanyi mana wannan addu,ar my lonely before kema kije kiyi da kanki ko?”

“Hmmm” kawai tace bayan tayi murmushi,

“Ina zuwa yunwa nakeji, bari naje wurin mami naci abinci”

“Ai baka son cin abinci sawwam inajin idan munyi aure dura zan runka yimaka..”

“Ehhhh dan Allah ki rinka yimin ina so indai kece zaki bani…”

Daidai lokacin ya isa falon mami tana tsaye a dining area tana shirya table domin tasan dady yana daf da zuwa cin abinci daga office,

“Idan banyi maka dura ba bazaka ciba kenan?” Yajiyo muryarta tana tambayarshi,

“Ehhh mana ni ke nake son ki rinka bani da kanki”

Dagowa mami tayi tana kallonsa daga shi sai boxer da body hug ja, girgiza kai Mami tayi tana murmushi,

“Sawwam baka da kunya ko?” Mami tace dashi tana zuba masa abinci acikin flate,

Kallon abincin yayi ya dan yatsina fuska,

“My lonely kin san wanne irin food zanci yanzu?”

“A’a wanne irine?”

“Sakwara da miyar kifi” yabata amsa bayan yaja kujera ya zauna,

“Ga mami zaku gaisa” tun kafin tayi magana ya mikawa mami wayar yana cewa,

“Mami ga in-law dinki zaku gaisa”

Karbar wayar mami tayi ita kuma ummulkhairi duk kunya ta lullubeta da ace tasan ma zai hadata da mami su gaisa da tun dazu tayi masa sallama,

Dad dinshi ne ya shigo fuskarsa dauke da murmushi, mika masa wayar mami tayi tafara yiwa abbanshi sannu da zuwa,

“Hello my lonely.. My dad done come back” yace da ita cikin rada,

“Wai yanzu da kai agaban mamin kake fada min wannan maganar dan rashin kunya? Ni wallahi kasani naji kunya tunda hakane munyi fada dakai…”

“No my lonely karki yi fushi dani please, am so sorry, ai ba wani abu nafada ba ko?, ko wani abu nace wanda zai saki kiji kunya?”

Mami ce ta yafuto dad da hannu ta nuna mishi sawwam,

“Yaronka fa yakusa ya girma dan ya samo matar aure yanzu ma ya hadani da ita muka gaisa kuma naga alamun yana sonta sosai..” Mami tace da dad ahankali,

Karasawa wurinshi dad yayi yana murmushi gamida dafa kafadarsay,

“Dan gidan dady a ina ka samo matar ne?”

Ummulkhair najin haka tayi saurin katse wayar amma  kuma rayuwar gidansu sawwam ba karamin burgeta yayiba saboda yanda suke tafiyar da rayuwarsu shida iyayenshi tamkar wasu abokai,

Dagowa sawwam yayi yana kallon dad cikeda kunya sai faman sosa keya yake,

“Dad a bauchi ne…”

“To Allah ya sanya alkairi yasa adace” dad yafada tareda jan kujerar kusa da sawwam ya zauna,

“Amin dady amma ai naga ita wannan din tayi masa” mami tace da dad tana zuba mishi abinci,

“Ai shiyasa nace miki dama ki rabu dashi zai nemo da kansa..”

“Ai kuwa dai gashi nan ya nemota kyakkyawar gaske”

Dariya dukkaninsu suka saka banda sawwam wanda yau duk kunyar iyayenshi suka rufeshi alla alla yake yagama cin abincin yaje dakinsa yasake kiran ummulkhair ya fada mata abinda mami tace,

Yana ganin mami da dad sun fita shima ya mike yayi Waje ya nufi dakinshi tun ahanya yake kiranta,

“Sahibi ya akayi?” Ta tambayeshi bayan ta kara wayar a kunnenta,

“Kinji me mami tacewa dad? Wai nazabo kyakkyawar gaske…”

Murmushi tayi, “nima ai nazabi kyakkyawan gaske danma dai danma dai lebenshi ja ne” tafadi cikin tsokana,

“Naji din, kema ai bakida gashi sai munyi aure sannan zan sanmiki…”

“Kaji shi”

“Wai dan Allah baki sani ba? Wallahi muna yin aure gashinki zai fito..”

“Naji to ya isa”

“Shikenan tunda bakya son ji sai anjima” tsinke wayar yayi yana murmushi, itama ummulkhair din murmushin take yi,ajiye wayar tayi tafita zuwa dakin mahaifiyarta.

Zaune ta taradda ita tana ninke kayan kannen ummulkhair wato yayan kanwarta wadanda suka zo mata hutu domin ita ummulkhair ce autar yarta,

Zama ummulkhair tayi akusa da ita tana kallon ta,

“Mama sannu da aiki..”

“Yawwa kairi..” Maman tabata amsa tana mai cigaba da ninke kayan,

“Mama dama dangane da maganar aikin nan da abba yasani ne to yanzu ina daf da kammala masa amma kuma zuciyata tana daf da shiga damuwa, wallahi mama zan iya rasa farin cikina asakamakon wannan abunda yake shirin faruwa..”

Barin ninkin kayan mama tayi ta maida hankalinta duka gaba daya ga ummulkhair,

“Babu komai ummulkhairi, kici gaba da addu,a amma tabbas nadade da sanin cewar mahaifinki yana da wannan burin zan iya cemiki ma tun lokacin da na aureshi nasanshi da wannan burin atattare dashi, amma nasan tunda yana sonki yana son farin cikinki to zai baki abinda kike so, amma shi faruk din ya nuna miki cewar yana sonki ne?”

Girgiza kai ummulkhair tayi, “mama nida banko taba ganinsa ba inba a hoto ba, nidai fatana daya kar abba yadage cewar sai ya hadani aure dashi domin wallahi inada wanda nake so..”

Murmushi mama tayi takama hannunta, “haba autar mama ai babu wanda zaiyi miki auran dole, sai wanda kikeso kika kawo mana zamu aura miki mu kaiki dakin mijinki shikenan kuma munyi sallama dake sai dai kizo mana da yawo kizo Ki gaishe mu gaisuwar samun lada”

Rufe fuskarta tayi da tafukan hannunta tana dariya nan kuma taji sawwam ya fado mata aranta, “sarkin azarbabi dama abinda yake so kenan”

Tafada acikin zuciyarta domin koda yaushe bashida zance sai dai yace “ranar da aka kawoki gidana”

Murmushi tayi ta debi kayan da mama take ninkewa tayi waje dasu zuwa dakinta ta zauna taci gaba da ninkewa, shikenan hirarsu da mama ta kare sai wani karon kuma.

Kullum suna manne ita da sawwam awaya suna hira har ya tafi umarah anan dinma wayar basu fasa ba sai dai ta dan ragu kasancewar tana son ta bashi dama ya gudanar da ibadarsa yadda ta kamata, satinshi uku suka dawo aranar da ya dawo kwana suka yi suna waya da ita, tsaraba kam akwati guda ya jibgo mata da dogayen riguna masu kyau da turarruka designers sai takalma masu dan karen kyau,

Kwananshi Biyar da dawowa ya shirya ya tafi bauchi ko fada mata baiyi ba kawai dai ya kirata awaya yace yabawa wani sako zai kawo mata,

Shagwaba tasaka masa harda kukanta saboda yace bashine zai zoba abokinsa ne zaizo yabashi tsarabarta ya taho mata da ita,

Tun yana zaton kukan nata nawasane har yagane dagaske take yi domin ga sautinsa nan tana rerashi yana jiyoshi acikin kunnensa, jin kukan nata yake kamar zubar wuta ajikin zuciyarshi, rarrashin duniya yayi mata taki ji daga karshe ma katse wayar tayi bayan ta tura masa da address din gidan nasu domin yace mata ta turo saboda yana son zai turawa abokin nashi,

Tunda ya kusa shiga garin bauchi yaketa kiran wayarta amma akashe murmushi yayi domin yasan fushi tayi shiyasa harda su kashe masa waya,

Karfe 2 narana ya shiga garin, wani hotel kayatacce yaje ya kama ya shiga ya huta yayi wanka ya sake sabon kaya,

Manyan kaya yasaka shadda ash colour harda hula, kasancewar bai saba da dogayen kayaba shiyasa duk yaji ya takura,

Motarshi ya shiga ya nufi kwatancen da tayi masa yana yi yana tambaya har Allah yasa yasamu unguwar bai wani sha wahala ba ya samo gidan nasu, cikin Sa,a lokacin da ya kira wayarta sai yaji ta shiga amma harta katse bata dauka ba nan yasake kira, tana kwance tana kallon wayar amma taki dauka har saida yayi mata miss called biyar ana shidane ta dauka ranta abace,

“My lonely kifita bakonki yazo yana waje zai baki sakon”

Ko amsashi batayi ba ta katse wayar ta dauki hijabinta har kasa pink colour tasaka, kafarta kawai ake iya gani sai hannunta data zira a hannun hijabin,

Fita tayi fuskarta kunshe da damuwa anata ganin sawwam bai damu da ita kamar yadda ta damu dashi ba domin yanzu fa satinsu shida basu ga junaba,

Har ta karasa gaban motar bata daga kanta ta kalli motarba balle tagane wanda ke ciki,

Tunda tafito yake kallonta ko kiftawa bayayi, kwalliyarta simple tayi amma ba karamin burgeshi tayiba,

Ajikin motar ta tsaya tana jiran fitowarsa, ahankali ya bude motar ya fito ya tsaya yana kallonta bayan ya dafe murfin kofar,

Wani sanyin kamshi taji ya doki hancinta irin na sahibinta domin bata manta kamshin nan tun ranar da yayi hugging dinta a makaranta da daddare,

“My lonely fushinne?” Taji muryar sawwam babu zato babu tsammani,

Cikin sauri ta jiyo ta kalleshi nan ta ganshi yayi mutukar kyau yana tsaye yana yi mata murmushi ya dan cije lebenshi na kasa da hakorinshi, tamkar ta rungumeshi haka taji dan tsananin farin ciki,

“Sahibi…” Tafada kwalla ta ciko idonta,

Girgiza mata kai yayi bayan yakai dan yatsanshi ya share kwallar dake shirin zuba a idonta,

“Don’t cry dear…. Tun dazu kike yimin asarar hawayenki”

Yace da ita yana murmushi,

“Dama zaka zo? Shine kuma kaki fada min?”

Dan yatsanshi yakai kan lips dinta,

“Shhhhh ba fushi kike yi daniba….”

“Tayaya zanyi fushi da rabin raina…”

“Kinga” yace da ita, idonta ta daga ta kalleshi nan ya kashe mata idonshi daya,

Dagashi har ita murmushi suka saki mai dauke da soyayyar juna.

aishaummi.blogspot.com

Ummi Shatu

Pherty Xarah
[3/20, 22:13] Aysha~Humaira 😘: *RAMUWAR GAYYA…….. 💘*

     _love story 50,50_

   *Fertymerh Xarah*

               &

*Ummy Aysher*

          27

 
      Dagashi har ita murmushi suka saki mai ďauke da soyayyar juna, kafin ta juya tana faďin Ina xuwa ta nufi cikin gida,
Mama tayiwa bayanin xuwan baqonta sai tabata makullin falon babanta taje ta buďe masa kana ta fita har lokacin yana tsaye jingina da motarsa yana kallon yanayin unguwar ta madubinsa,
Yana ganinta ya saki wani murmushi itama murmushin tayi tana faďin bismillah,

Ya rufe motar kana yabi bayanta har falon mahaifinta, ya xauna yana kallon pics ďin dake falon,

Ta xauna tana kallonsa,
‘nifa kamar mafarki nakeyi, ya dubeta,

‘matso in mintsineki ko xaki gasgasta, tayi dariya tana kallonsa,

‘As I can see you miss me alot, nace baxan xo ba harda kuka ake min, ina ganin nafiki damuwa dake Ashe kin fini damuwa duk da dai nasan nafi sonki,

‘haka dai kace amma ba gsky bane, ta tashi tana faďin ,ina xuwa, yayi Saurin tsaidata,
‘Ni karki kawomin komai bana buqata ganinki ma ya wadatar, shiyasa naqi sanarda ke xuwa kada ki wahalarda kanki,

‘Au abinma yar hakane, ko ruwan gidanmu baxaka sha ba, ya gyada kansa yana kallonta,

‘Seriously am ok, bafa yau naxo ba, tun jiya a hotel na kwana kinga I need nothing, xo ki xauna nacigaba da kallonki, bakisan ynda nayi missing Naki ba dabaxaki tashi kibarni ba,
Tana dariya ta dawo ta xauna cikin jin kunya ya tashi ya dawo inda take xaune,

‘Ni ynxu naga sai wani guduna kikeyi, me kike nufi? ta dubesa bayan tayi far da ido,

‘akan me xn guji sahibina, Ina tsoron baba ya sameka a kusa dani,

‘is not bad, kinga xaice a matse nake inturo magabatana, tayi dariya sosai haďe da rufe fuskarta da tafin hannayenta,

Kallonta yake cikin so da qauna he Rilly miss her ji yake kamar ya rungumeta xuwa jikinsa,
Sun dade sosai suna hira kafin Abba ya dawo, ta gabatar da sawwam garesa,

Sun gaisa yayi masa tambayoyi, sawwam ya bashi amsa kuma ya gamsu,
Mama ma taxo sun gaisa da sawwam ta yaba da hankalinsa,

Sawwam ya tsinci kansa cikin farin ciki ganin bai sami matsala a gun iyayenta ba, sai ya sanya a xuciyarsa khairi tashi ce,

Qanninta haka suka xagaye sa kamar wani Wanda suka sani sai hira suke gwani sha’awa khairi na gefe xaune tana kallonsu da murmushi,
Sanda ya tashi tafiya ta ďauko rafar kuďi yabasu, sukayi godiya suka nufi cikin gida cike da murna,
A tare suka fito da khairi kamar kada su rabu haka kowa keji a xuciyarsa ya dubeta,

‘Yanxu kixo muje ki xagaya dani, inga garin Bauchi idan naje gida xnbawa Dad da Mami labari,

‘shikenan bari Nashiga gida na fito, yana tsaye harta shige cikin gidan kana ya shiga motar yana jiranta,
Bata jima ba sai gata ta fito Kuwa ďauke da wata Leda a hannunta tana shiga ta ajiyemasa a baya,

Mama tace a baka snacks ne tunda bakaci abinci ba idan kaje masauki kaci,

‘oh da alama mama na sona,kiyimin godiya sosai gareta,

‘olready nayi mata, tunda ta baka kamar ni tayiwa kyauta kaga kuwa dole inyi mata godiya,
Yayi murmushi har cikin ransa yaji daďi, kana ya tayarda motar yana faďin Ina Muka nufa kinsan bnsan gari ba inkuma xn baki motar ne kijamu kixo gata,

‘OK tor idan ka shirya xuwa lahira ynxu sai ka kawo nayi driving,
‘indai tare xamu je ai shikenan, bana so na mutu na barki ko ki mutu kibarni,

‘Insha Allah baxamu mutu ynxu ba sai munyi…. Sai Kuma tayi shiru,

Ya ďan dubeta,
‘sai munyi me… ta ďauke kanta gefe tana murmushi qasa qasa cikin jin kunyarsa,

‘kinyi shiru ki qarasa ko na tsayar da motar a fasa xuwa,
‘AURE ta bashi amsa fuskarta na gefe,

yayi murmushi bayan ya maida hankalinsa ga driving da yake,

‘wannan ta fini matsuwa da auren, da alama anyimin wani tanadi ne,

Ta juyo tana kallonsa,
‘wai an matsu ko kunyar faďi bakaji ba, in dan tani mutabbata a hakan Ina ruwana, ta faďa fuskarta ba walwala, ya tabe bakinsa haďe da kawar da mgnr ta hanyar faďin,

‘Ina Muka nufa ynxu, ta nuna masa hanya bakinta a tunxure ,yayi dariya ganin yanayinta yana son mace mai shagwaba,

Kin min kyau a haka, ta qara tunxurewa, sosai yake dariya……
Sun yi radius a ranar, ta kaishi gidan qawayenta ya gansu sun ganshi, he feels happy da xuwansa Bauchi kamar baxai koma ba yaji daďin kasancewa da khairi,

Sanda ya kawo ta gida ya bata tsarabar da yaxo mata da Ita, ta karba tana kallonsa da murmushi ya riqe hannunta,

‘I will miss you khairi kamar karnaje na barki,ta dubi hannunsa dake Kan nata tana murmushi,
‘Nima xnyi kewarka kamar kada ka tafi, yayi shiru kawai ya janye hannunsa daga nata…..

Sallama sukayi ta shiga motar ya fice itama tayi cikin gida jikinta a matuqar sanyaye she need him,

Kayan daya bata ta nunawa mama da Abba, dogayen rigunane  masu kyau da tsada samfurin India duk duwatsu ne ajikinsu, sai takalmi da gyaluluwa harda kayan barci aciki har kunya taji da tasan dasu da tacire tun kafin su Abba sugani, sai faman murmushi take ita kaďai
Da dare sun sha hira a waya Kamar kada su rabu, da kyar suka iyawa juna Sallama cike da kewar juna,

Washe gari yabar garin
Bauchi baya ya sanarda ita a waya ya wuce,
A ranar faruq yaxo gidansu Anyi Sa’a ya sami Abba har take gayamasa ai khairi ta kirasa a waya sanda tana Skul,
Abba yaji daďin ganinsa sun jima suna hira kafin ya nufi inda khairi,

A Wannan lokacin ya sanarda ita irin soyayyar da ya jima yanayi mata Kuma yana son iyaye su sani susan da Mgnr da tagama karatu ayi bikinsu,
Shiru tayi tana kallonsa da tsananin mamaki,
Bayan mutuncin dake tsakaninsu batasan komai ba, tasan waye faruq, he is simple bashi da hayaniya, halayarsa na birgeta duk da yake kyakkyawa amma batajin xata iya barin sawwam a halin da ake ciki ynxu,
Ta gyara tsayuwarta tana kallonsa,
Am sorry to say faruq, bawai naqi ka bane dan wani abu sai dan sawwam, ina sonsa shi xn aura,
Waye sawwam ya tambayeta Idanunsa akanta,

Tayi shiru tana kallon qasa kafin ta ďago tana kallonsa….
*pherty xarah*

      &

*ummy shatu*
[3/20, 22:17] Aysha~Humaira 😘: *RAMUWAR GAYYA..*💘

_Love story 50,50_

*_UMMI A’ISHA_*

       _With_

*_PHERTYMERH XARAH_*
28

*K*allonta yake sosai ko kiftawa baya yi yana jiran yaji amsar da zata bashi,

Murmushi tayi itama tana kallonsa,

“Sawwam shine mutumin da ya saukaka min hanyar nemanka domin asali ma shine yabani number wayarka…”

Kallonta ya sake yi cikeda mamaki,

“A ina ya sanni…?” Ya jefa mata wannan tambayar lokaci guda,

“Ni ban san a inda ya sanka ba but yadai cemin ya sanka, shima dan kanone…”

“Three pointer?” Ya tambayeta,

Daga mishi kai tayi alamun ehhhh,

Murmushi ya dan saki kadan yaci gaba da kallonta,

“Ok shi kike son aura kenan? Kinfi son bare akan dan uwanki,haba ummulkhair kiyi tunani mana, itafa rayuwa yanzu naka sai naka, kowacce mace tana kokarin samun wanda zai riketa bisa amana da gaskiya ne…”

Katseshi tayi domin da alama maganganun nashi sun fara kokarin sosa mata zuciyarta,

“Faruk kar muyi haka dakai, tun farko na fada maka sawwam nake so tsakanina dakai babu wata maganar soyayya sai dai ta zumunci so dan Allah kar kayi abinda zai jawo rashin fahimtar juna a tsakaninmu…”

Tana kaiwa nan ta mike zata wuce, cikin sauri faruk ya riko hannunta, fisgewa tayi tareda ja baya,

“Karka kara rike min hannu, ina ganin mutumcinka karka bari girmanka ya fadi a idona…”

Mikewa tsaye yayi yana kallonta,

“Alright, zan barki amma kafin nabarki din ya kamata ki zauna kiyi tunani sannan kiyi nazari..”

Juyawa yayi ya fita daga falon, duk sai taji ranta ya baci hankalinta ya tashi, juyawa tayi itama ta shiga dakinta ta zauna a bakin katifarta tana tunanin wannan al’amari na faruk,

Karar wayarta ne yadawo da ita cikin hayyacinta, dagawa tayi babu yabo babu fallasa atattare da ita saboda yanayin bacin rai wanda ta samu kanta,

“Sawwam…” Shine kawai abinda ta fada,

“My lonely ya akayi?” Sawwam yace da ita daga daya bangaren,

“Lafiya lau,yakake?”

Murmushi yayi kafin ya bata amsa,

“Ina cikin wani hali na rashinki akusa dani, ina ji kamar inama zan iya dawo da shekaran jiya tazama yau da nayi hakan domin ban gaji da kallonki akusa dani ba”

Duk da cewar ranta abace yake amma sai da tayi murmushi,

“Nikuma da za abani dama domin indawo da lokacin da nake so yafi burgeni to da kasan wanne lokaci zan dawo dashi?”

“No,fada min wanne” yabata amsa,

“Lokacin da muke fada a school, lokacin da muke soyayya a boye babu wanda yasani”

Murmushi yayi mai dan sauti,

“Dama ni soyayyarki bata buya ba agareni domin har friends dina sun gane ina sonki saboda duk Wanda yayi min maganarki haushinshi nake ji, lokacin da Abdul yace yana sonki ji nayi kamar na naushe shi wallahi…”

Dariya kairi tasa harda kwarewa, “to kuma da ace nima na amince da ya za kayi?”

“Ina jin da mutuwa zanyi my lonely, ranar fa wallahi kasa bacci nayi, ki godewa Allah domin ya jarrabeni da ciwon sonki mai tsanani, bazan iya jure rashinki ba”

“Nima haka sahibi, nima ina sonka and i can’t do without you, you are my life…”

“Dagaske kike Kodai kawai fada kika yi?”

“Dagaske nake mana” tafada bayan ta zame ta kwanta asaman katifarta,

“Nabawa mami da dad labarin irin karramawar da kika yimin, suma sunji dadi fiyeda yadda naji naganin na samu karbuwa sosai, amma zan baki hakurin abu guda daya”

“Hakurin me kuma?” Tayi saurin tambayarsa,

“Hakurin sai na gama school sannan zamuyi aure ina fata lokacin bai yimiki nisa dayawa ba…”

Murmushi tayi bayan ta sauke ajiyar zuciya,

“Indai akan wannan ne karka damu domin ba kai ya cancanta kabani hakuri ba nice nafi cacanta da in baka hakuri domin kafini dokin ganin ranar”

“Babu komai naji na yarda idanma nayi dokin ai nagirma ne shiyasa”

“To shikenan, kaji Anfara kiran salla bari nabarka haka”

“Kajita sai kace yi zatayi, kibari nida zanyi in fadi haka bake ba”

Shiru tayi masa ta kyaleshi bata bashi amsa ba,

“Bari naje salla nadawo, idan nadawo zan kiraki, i love you..”

“I love you too” ta furta ahankali.

Katse wayar tayi ta shiga duniyar tunani.

  Haka soyayyarsu taci gaba da gudana har aka fara shirye shiryen komawa makaranta,

Iyayenta sun hada mata kaya masu yawan gaske wanda zatayi amfani dasu a makaranta batare data nemi wani abu ta rasa ba,

Ranar lahadi ta shirya ta koma makaranta tana cike da kewar gida da kewar iyayenta, wannan tafiyar ma kamar ta farko da kuka ta tafi.

Karfe 3 na yamma ta sauka atasha,tana sauka sawwam na karasowa tashar,

Ganinta tana kuka abin yabashi dariya, abayan boot din motarshi ya sassaka mata kayanta tashiga suka tafi,

Tsokanarta yafara yi yana driving,

“Shiyasa ni ban san yanda zanyi ba ranar da aka kawoki domin nasan kwana zamuyi kina yimin kuka”

Hawayenta ta share idonta jajur ta kalleshi,

“Dole kace haka mana tunda kai kana kusa da mami da dad duk lokacin da ka so zakaje ka gansu nikuwa fa”

“Kema ai zaki ga su mama duk lokacin da kike so zan kaiki”

“Nidai ban yarda ba” tafada cikin shagwaba,

“Haba baby na, yi shiru kinji” yace da ita ganin har lokacin bata daina kuka ba,

Packing yayi agefen titi ya juya yana kallonta, hannuta ya kamo yana kallon fuskarta,

“My lonely yi shiru kinji, daina kuka dan Allah, ko kina so nima nayi kukan?”

Kai ta girgiza masa tana share hawayen fuskarta,

“To yi hakuri kiyi shiru, kina so nakaiki wurin mami yanzu?”

“Ehhh, amma kafara kaini naje na ajiye kayana a hostel”

“To sahibata yanda kikace ai haka za ayi”

Yace da ita cikeda tsokana, murmushi tayi ta zare hannunta daga cikin nashi cikin jin kunya,

Makaranta ya kaita ya fiffito mata da kayanta, daya bayan daya ta rinka dauka tana shigar dasu cikin hostel har ta kammala kwashewa,

Fitowa tayi ta iskeshi zaune acikin motarshi yana jiranta, ajikin motar ta jingina tana kallonsa, ita sai yanzu ma tasamu damar kallon irin shigar da yayi,

Bakar riga yasaka budy hug ajiki an rubuta you, da brown din wando,

“Kayi kyau” tace dashi tana kallonshi,

“Kema kinyi kyau gashi kinyi kumatu zo ki fada min me mama take baki kika yi kumatu haka?” Yafadi hakan yana kokarin fitowa daga cikin motar,ganin ya miko hannu zai kamo kumatunta yasata guduwa tana dariya,

“Kika gudu ko? Idan kika yi nauyi da yawa nakasa dagaki shikenan”

“Da taya zaka dagani? Sai kace wata baby?” Tace dashi tana dariya,

“Dagawa ma tamkar baby” yabata amsa bayan ya dora hannuwanshi asaman motar yana kallonta,

“Nafasa zuwa gidan mami sai gobe, yanzu zuwa zanyi nawanke dakina na shirya kayana”

“Shikenan to Allah ya kaimu, bari nabarki kije kiyi aikinki”

“Anjima da daddare fa kadawo, amma kataho min da shawarma ko abin dadi”

“To sai nadawo” yace da ita ya shiga cikin motarshi ya tafi, itama hostel ta koma ta shasshare dakinta tawanke ta shirya kayanta danma tayi Sa,a hostel din an daddawo babu laifi.

  Bayan sallar magrib sawwam ya dawo ya kirata, fitowarta daga wanka kenan, daya daga cikin dogayen rigunan da ya kawo mata tasaka tafesa turarruka masu kamshi ta fita,

Yana zaune yana jin music ta karasa,

Bangaren mai zaman banza ta bude ta shiga ta zauna tana kallonsa, shi dinma ya kara sake sabon wanka ya sauya kaya daga na dazu zuwa wasu kalar daban sai kamshi yake, har azuciyarta taji sawwam yayi mata dari bisa dari domin yana da tsananin tsafta da tsantseni gashi komai nashi sai kamshi yake,

Kallonta yayi yana leken kafarta, wayarshi ya kunna yahaska light yafara kokarin hasketa, cikin sauri tafara yunkurin kwace wayar,

“Wallahi ni kunshin kawai zanga ba wani abu ba”

Tabe baki tayi “ai da yake nasan kasaba saka min idone shiyasa”

“To yau ba sa idon zanyi ba..” Yafada yana murmushi, hannunshi ya mika sit din baya ya dauko wata leda mai kyalkyali ya mika mata,

“Ga abincin nakawo miki”

Hannu ta mika zata karba sai yafasa bata yana murmushi,

“Idan bazaka bani ba in tafi…”

Murmushi ya kara saki batare da yace da ita komai ba…

aishaummi.blogspot.com

Ummi shatu🏻

Pherty xarah
[3/20, 22:22] Aysha~Humaira 😘: *RAMUWAR GAYYA……. 💘*

_Love story 50,50_

29

*Fertymerh Xarah*

           &

*Ummy Aysher*

  Ta qara kallonsa,
‘kabani xnje gyaran ďaki na, ya miqa mata ledar yana kallon qafafunta,

‘Ina son wannan lallen sosai ya birgeni, ďago kafar ingani,

‘kajika da wani xance, ta Karbi ledar haďe da qara lullube qafafuwanta da hijab ďinta,
Ya ďauke kansa daga kallonta yana kallon wani gun alamar yayi fushi, tayi mgn yayi mata banxa sai tayi murmushi haďe da sunkuyowa,

‘Haba nawan, miye abin fushi akan abinka, yayi mata banxa,

‘ko in baka qafar ne ka cinye duka, ya juyo haďe da faďin,

‘da dai yafi, tayi murmushi haďe da lumshe idanuwanta,

‘duk na gaji sosai, kamar baxan iya gyaran ďakin ba,

‘sorry dear, ko inje in gyara maki ne,

Ta girgixa kanta tana kallonsa cikin dariya, ya kwantar da seat ďin da take xaune akai yana faďin bari nayi maki tausa it may help you,

Tayi saurin tayar da seat ďin tana faďin,
‘see you bana son haka, kan wane dalili xaka min tausa nace ma Ina buqatane,

Ya koma ya xauna yana faďin,
‘da dai kinbari nayi maki xaki ji daďina, ko banxa ma hannuna taushine dashi dan yafi naki,

‘ban yarda ba, nawa yafi naka,
‘to kawo a gwada, ta kwashe da dariya haďe da buďe motar,
‘naqi wayon salon ka taba min hannune, murmushi yayi yana kallonta bayan ya tayarda motar,

‘inma tabi ne da sauqi akan…..bari dai nayi shiru na tuna kefa yarinyace,

‘ta tabe bakinta cikin murmushi ta rufe motar ta sunkuya ta glass ďin tana faďin sai da safe dear,

‘idan kin gama aikin flash me I will call you back,

‘shikenan sahibina, a gaida Mami,

‘xataji Insha Allah, ya tayar da motar cikin murmushi, ta ďaga masa hannu ta fice,

Tana xuwa hostel tayi gyare gyarenta tayi wanka kana ta xauna cin shawarma, bayan ta gama ta kora da ruwan lemu kana ta Kira Alawiyya taji ko ta dawo,

‘gobe dai xn dawo, bngama kimtsawa bane amma gobe Ina hanya,

‘Allah ya kawo ki lfy,
‘Amin ta tsinke Wayar,

Sawwam ya kirata suka shiga waya…

*

Washe gari kasancewar Alawiyya abokiyar yawonta bata nan duk inda sawwam yake tana tare dashi, shima sai ya kyale su Abdul ya nacewa sahibarsa,

‘3 pointer fa ďan iskane, yaron dake cewa bai iya soyayya da waccan yarinya amma ynxu yafi jinta akan mu, cewar hafix

Abdul yace sanda nace ina sonta sai ka gani naushine kawai bai kaimin ba, wai na xubar da ajinmu mexanyi da waccan Ashe shegen sonta yakeyi,

‘itama ai sonsa takeyi baka ganinsu kamar xasu jinye junansu, sawwam an shiga kogin soyayya kaga ko xama damu ba’a yi ynxu sai an sami matsala ya dawo mana,  suka kwashe da dariya,
Ranar ya ďauki khairi yaje da Ita gidansu, tun da suka shigo harabar gidan take kallon yanayin gidan, lallai su sawwam masu kuďi ne,

Da kansa ya buďe mata motar yana murmushi, itama ta fito fuskarta da murmushi rataye da Jakarta,

Yana gaba tana biye dashi a baya har suka shigo falon,

‘ki xauna kina wani ďar ďar, ko kina xaton xn cutar dake ne?

Ta xauna har lokacin bata tankaba sai dai fuskarta taqi gushe murmushin dake kanta,

‘let me call mother, yayi hanyar ďakinta ta bisa da kallo kafin ta juyo tana kallon tsarin falon,

Ba qaramin birgeta yayi ba, falon baida hayaniyar kaya sai dai komai mai tsada ne, tana kallon hotunansa dana iyayensa ya dawo kusa da ita ya xauna yana faďin,
‘Mami tana xuwa, ta gyada kanta kawai, shi ya riqa janta da fira ganin taqi Sakin jikinta har Mami ta shigo,
Khairi ta russuna cikin girmamawa tana gaidata a kunyace, Mami tayi murmushi kafin ta amsa,

Yau naga ummulkhairi, na dade inajin labarinki a gun sawwam, bashi da mgn sai taki Ina roqonki da ki riqeshi amana domin yana sonki,

Khairi ta sunkuyarda kanta cikin jin kunya bayan ta dubi sawwam, Mami ta dubi sawwam,

‘na yaba da matar ďana, kaima ka riqe amana,
‘Mami ni baxanci amanartaba kinsani, bnda wadda nake so bayan ita, kice karta cutar dani tabarni taje ta sami wani,

Lokaci ďaya Mami da khairi suka yi dariya, suna xaune gurin masu aiki suka soma kawo mata abinci, sosai Mami ta tsareta sai taci duk a takure take musamman da sawwam yace tare xasuci kamar xata nutse qasa saboda kunya,

Kabarta son taci kada ka takurawa ya’ta,

‘au Mami har kin yayeni kin kama ta,

‘sosai ma kuwa,

Cikin barkwanci suke hirar su gwani sha’awa kamar ba surukai ba, sosai khairi ta saki jiki da Ita sukayi hira…

Sanda xataje, kayan kwalliya da sarqoqi ta bata masu kyau da tsada kana ta roqeta ta riqa xuwa nan ma ai gidane,

Jinjina kai kawai khairi tayi tana murmushi bayan tayi mata godiya,

Suna cikin Mota ta dubesa da murmushi,
‘Mami is simple batada hayaniya naji Ina sonta, murmushi yayi

‘nima karamcin da mama tayimin ya Sanya naji ina sonta, duk iyayenmu suna son mu, auren mu xaiyi albarka,

‘tayi murmushi xuciyarta cike da farin ciki tana kallon gefen hanya.
Pherty

     &

Ummy shatu

*RAMUWAR GAYYA…*💘
  _Love story 50,50_

*_UMMI A’ISHA_*

          _With_
_*PHERTYMERH XARAH*_

30

  *K*arkatar da kanshi yayi yana kallonta sannan kuma yana yin tuki,

“Ya kikayi shiru? Ko nadameki da surutu ne?”

Juyowa tayi ta kalleshi tana murmushi,

“A’a ba damuna kayi ba kawai dai ina tunanin irin yanda rayuwar aurenmu zata kasance ne bayan munyi aure…”

Burki ya taka sakamakon tsayar dasu da danja tayi,

“Yakamata ki tuna wannan ranar yanda ya kamata domin ki shirya mata, insha Allah zamuyi rayuwa mai dadi da burgewa musamman ma idan kika haifo yan tagwaye a haihuwarki ta farko”

Gefen mayafinta tasa ta kare fuskarta tana murmushi,

“Allah sawwam baka jin kunyata ko kadan, samari suna jin kunyar yan matansu amma kai banda kai…”

“Kunya? Gaskiya nidai ko zanji kunyar wasu to wallahi banda ke”

Murmushi tayi ta dan juya tana kallonsa lokaci daya kuma ta kawar da kanta,

Ganin ya dauki wani titin nadaban bana BUK ba yasata saurin kallonshi,

“Sahibi ina zamuje?” Ta tambayeshi bayan ta kafeshi da ido,

Kallonta yayi ya dauke idonsa ya dora bisa titi,

“Zanje na sayar da ke ne, kin san business dina kenan”

Murmushi tayi ta kalli window “woww ashe dan yankan kai zan aura”

“Ba dan yankan kai ba ne, mai sayar da kayuwan mutane ne” yabata amsa yana murmushi,itama murmushin take yi tana kallon yanayin garin domin bata taba doguwar tafiya hakaba iyakacinta cikin makaranta sai ko wajen makarantar in zataje siyayya ko saloon ko kuma gidansu alawiyya,

Wurin wasan yara ya kaita wato children parck,

“Wowww” tafada tana murmushi domin wurin ya hadu sosai gashi ba iya yara bane harda manya samari da yanmata masoya ko wadanne sai guje gujensu suke yi cikin so da kaunar juna,

Wurin wani lilo yajata suka nufa, gefen wurin ruwane yake kwaranya yana wucewa,

“Wowww sahibi kamar kasan ina son irin wadannan wuraren,

Wowww bari narigaka hawa lilon” tafadi bayan ta wuceshi tana murmushi, lilo taje ta hau tana kallon sauran mutanen dake harkokin gabansu wasu ma’aurata ne wasu kuma saurayi da budurwa ne,

Ji tayi an wullata sama da karfi,bata zataba bata nufaba,

“Woohhhhhhhhh, wayyo sawwam zan fad’o….” Tafada arude, ganin ta tsorata yasashi rike lilon tana ganin haka bata san sa’ilin da ta kamkameshi ba tana kallonsa,

“Ke matsoraciyace my lonely, idan bakya so sauko karki fado kiyi min asara”

“Karka kara turani dan Allah sawwam”

Murmushi yayi ya hau daya lilon na kusa da ita yana tura kansa ahankali yana kallonta,

“Ki rage tsoro khairi, ban san haka kike da tsoro ba sai yau”

Langabe kanta tayi tana kallonsa “ba kaine ka turani da karfi ba, ai laifinka ne kaine ka tsorata ni”

“To am sorry” yace da ita bayan yasaka dukkan hannuwansa ya rike kunnuwansa,

Kallonsa ta tsaya yi batare data bashi amsa ba, yayi mata kyau sosai yau dinnan domin blue din t shirt yasa mai gajeren hannu da bakin trouser, hatta takalmin kafarshi blue ne mai madauri,

Ganin ta zuba masa ido yasashi murza mata yan yatsunshi a saitin fuskarta,

“Tunanin me kike yi dear?” Ya tambayeta yana shillawa sama akan lilon,

“Tunaninka” tabashi amsa bayan ta dauke idonta daga kansa,

“Tunanina bayan muna tare dake? Kidai fadi gaskiya”

Murmushi tayi ta kalleshi,

“Haba sawwam ka yarda dani, akowanne lokaci cikin tunaninka nake ko muna tare ko sabanin haka”

Murmushi yayi cike da jin dadi, ahankali ya dora hannunshi akan nata, ganin haka yasata dabarar zarewa ta sauka daga kan lilon tana cewa,

“Bari kaima naturaka kaji irin yanda naji dazu”

Turashi tayi da karfi tayi saurin matsawa, nan yaci gaba da lilawarsa babu alamun tsoro atare dashi,

Sun jima awurin bayan sun hahhau kayan wasan dake harabar wurin,

Fitowa suka yi ya nufi makaranta da ita,

“Sahibi nagode madalla da wannan fitar tayau, sai yaushe zaka sake kaimu?”

“Duk lokacin da kika shirya” yabata amsa ya kallonta,

“To shikenan zan sake shiryawa sai muje”

“Yakamata kam”

Yabata amsa fuskarsa dauke da murmushi,

Makaranta ya shigar da ita nan dinma kafin ya tafi sai da ya tsaya suka sake wata hirar sannan yatafi,dukkaninsu suna dauke da kewar juna kamar kada su rabu.

  Al’amura sunci gaba da gudana,sun fara lectures sosai duk dai da har yanzu sch din bata dawo normal ba, alawiyya ma ta dawo domin harta fara shigowa lectures,

Kullum sawwam da ummulkhairi suna tare sai kace wasu yan biyu lectures ne kawai ke rabasu, yau kam wuni sukayi ma tare suna hira kasancewar yau basuyi lecture ko daya ba,

“My lonely bari natafi gida bacci nakeji wallahi” yace da ita yana yin hamma,

“Allah bana son katafi, dan Allah ka kwanta anan kayi”

Murmushi yayi ya kalli wurin “ai babu pillow”

“Sai inje hostel in dauko maka”

Kafada ya makale kamar wani karamin yaro, “sai dai inyi pillow din da kafarki”

“Ban isaba” tabashi amsa bayan ta tashi tsaye, bakin glass dinshi yasaka yana kallonta,

“Zaki isa dinne yarinya bari lokaci yayi wallahi bazan daga miki kafaba duk abinda bakiyi ba yanzu sai kinyisu lokacin”

“Naji,yanzu dai kaje kayi baccin sai kadawo, i love you,bye bye”

Mikewa yayi yana kallonta ya nufi motarsa, “i love you too, sai nadawo”

Tana tsaye tana kallonsa har yabar wurin, ganin tafiyarsa yasata barin wurin tatafi hostel.

   Aguje ya karasa gida sakamakon baccin da yakeji sosai, ko takan maganar da baba dan tsoho yake yi masa baibi ba ya wuce falon mami, bata ciki amma ya hangota ta labule a dining area tana aiki, akan center carpet din da yake tsakiyar falon ya kwanta bayan yaja pillow akan kujera, yana kwanciya bacci ya daukeshi, ita kanta mami bata san ya shigoba sai da tafito sannan tayi arba dashi yanata shakar bacci,kallonshi tayi cikeda tausayawa domin tunowa da tayi da gagarumin abinda yake shirin faruwa dashi wanda dole zai jawo su rabu dashi ba ason ransu ba.

  Karfe bakwai da rabi khairi na kwance adakinta tana browsing din wani assignment da aka basu wayarta tafara kara, nan taga sunan faruk ajiki, kamar ta shareshi sai kuma ta dauka da sallama,

Cemata yayi yana cikin sch dinsu ya rako wani abokinsa wurin budurwarsa, tafito su dan gaisa, badan tasoba haka ta tashi ta dauki hijab dunta tafita,

Awani dan fili ta sameshi zaune asaman motarshi yana jiranta, fuskarta babu yabo babu fallasa takarasa suka gaisa nan kuma ya shiga soko mata maganar sonta da yake yi har lokacin,

Sunanan tsaye yanata yimata zance tana amsa masa da uhm har sawwam yazo, sam ita bataga zuwansa ba amma shi Faruk din yaganshi ganin haka yasashi yin amfani da wannan damar yayita mata surutu idan tace zata tafi sai yakara kawo wani sabon topic din da haka har 9 tayi suna tsaye, shikuma sawwam yagama cika yayi fam bai taba sanin yana kishin ummulkhairi ba sai yau,

Dakyar tasamu ta yiwa faruk sallama ta wuce, harda wani kaimata kiss faruk yayi lokacin da zata wuce din, saurin gocewa tayi tana dariya domin ita yanzu faruk dariya yake bata,

Tana yin gaba taga sawwam tsaye, “a’a sahibi yaushe kazo?”

Tace masa tana kallonsa, “ban saniba idan ke baki ganni ba ai shi saurayin naki ya ganni”

Murmushi tayi “sawwam Faruk nefa, ko kamanta kaine ma ka bani number wayarshi?”

“Kinga banida lokacin ki yanzu, sai anjima”

Ganin zai shige cikin motarsa yasata saurin riko rigarshi ta baya,

“Dan Allah kayi hakuri”

“Bazanyi ba” yafada batare da ya jiyoba,

Sakinshi tayi tace “shikenan” tajuya tawuce, juyawa yayi yana kallonta cikin bacin rai, wato ma maimakon ta tsaya ta bashi hakuri shine zata tafi? Nan yaji ransa ya sake baci,

Motarshi ya shiga yatafi gida duk zuciyarsa a zafafe, texts yaga ta tutturo masa naban hakuri fiyeda guda Biyar amma har lokacin baiji sanyi acikin zuciyarsa ba.

  Washe gari koda suka hadu a sch dauke kanshi yayi yaki koda kallonta, kusa dashi taje ta tsaya,

“Sahibi dan Allah ka tsaya ka saurareni”

Shiru yayi yana jinta amma har lokacin bai daga idonshi ya kalleta ba.
aishaummi.blogspot.com

Ummi Shatu

Pherty Xarah

*RAMUWAR GAYYA…….. 💘*

_Love story 50,50_
*Fertymerh Xarah*

          &

*Ummy Aysher*
  31
Shiru yayi yana saurarenta amma har lokacin bai ďaga kanshi ya kalleta ba,
Jikinta yayi sanyi, she is not happy a yanda yake yi mata kamar xatayi kuka, ta qara marairaice murya,
‘kayi haquri idan na bata ma, wallahi faruq is nothing to me Kuma ni bansan da xuwanka ba da baxan tsaya gurinsa ba,
Ya tabe bakinsa haďe da ďaga kafadunsa ko ajikinsa, ya maida glass ďin sa ya rufe idonsa, ta ciki yake kallonta yaga duk ta damu, yaji daďin ganin yanda take bashi haquri tayi masa laifi, ya haqura amma yaqi ya nuna mata,
Alawiya ce ta qaraso da textbook a hannunta ta miqawa khairi,
‘ga book ďin ki gida xn tafi duk na tafi, khairi ta karba tana faďin,
‘anjima xaki shigo, kitso nake son kimin,
‘ban maki alqawari ba dan xn raka qawata biki amma idan mun dawo da wuri xn shigo,
‘shikenan sai Kindawo, Alawiyya ta dubi sawwam,
‘mutumin mu yau ba mgn ni naga yau sai wani daurewa kakeyi, yayi mata banxa, ta dubi khairi,
‘meke damunsa,
‘fushi yake dani,
‘shine ni Kuma abin ya shafeni, to kayi haquri ko menene ka sassautawa qawata haka,
Ya juya ga motarsa alamar xai shiga khairi taqi ta matsa, Alawiya ta fice tana dariya,
‘haquri nake ta Baka kake min shariya haka,
‘matsa xn shiga mota, ba musu ta matsa ta bashi guri ya shiga motar yaja ta a fusace tana tsaye tana kallonsa har ya fice daga Skul ďin,
Jiki a sanyaye ta nufi hostel,  baxata qara xubar da ajinta gurin bashi haquri ba har ya gaji da fushin ya sauko,
Sosai ta damu, ranar duk a kwance ta jini jikinta sukuku hankalinta da tunaninta duk yana kansa, ko ringing wayarta tayi da sauri take dubawa ko shine idan ba shi bane sai ta cillar da wayar tana tsaki, wayar kowa bata amsa ba ranar kamar yanda itama bataji muryar sahibinta ba,
Sawwam Kuwa har Ga Allah ya haqura, yayi mata Hakan ne dan ta gane laifinta sosai ta daina tsayuwa da wani, yana tsananin sonta da kishinsa baxai jure ganinta da wani ba, so a gobe xasu shirya ya nemi sulhu tunda yaga ta damu duk da itama yasan tayi fushi da shi tunda gashi bata nemesa ba, ba text ba Kira.

Washe gari da sauri tayi shirinta ta fita lectures kasancewar 8:00am suke da lectures,
Tana fita ta haďu da Alawiya xata shigo hostel sai suka wuce tare,
‘shine kika qi xuwa jiya ko, kinbar ni dakai duk ya cunkushe,
‘bamu dawo da wuri bane amma yau baxan je gida ba sai nayi maki,
‘kinxo min da assignment ďina kuwa?
‘yes yana jaka sai muyi submitting idan mun fito lectures,
‘shikenan,  suka shiga hall ďin,
10:00am suka fito lectures, bayan sun fito Alawiyya tayi gurin saurayinta, sai ta sami guri ta xauna cos xasu shiga wata lecture basu gama ba, kamar wacce aka ce ta ďago, tana ďagowa idanunta suka sauka akansa, yana tsaye jingine da motarsa hannuwansa sarqe a qirjinsa, wata budurwa ce a gabansa batasan ta ba yau ta soma ganinta,
Jikinta ya ďauki rawa sosai hankalinta ya tashi, kada sawwam ya barta ne ya sami wata da Kuwa ta shiga uku yanda take mutuwar sonsa a ynxu takejin ba abinda xai iya rabasu,
Suna haďa ido da sawwam tayi Saurin ďauke kanta, ta tattara kayanta ta tashi daga wurin ta shige hall inda sauran friends ďin ta,
Sawwam yayi murmushi yana kallonta,
‘kingane farida, Suhaib wani irin mutum ne mai wuyar al’amari, dole sai kina haquri dashi amma duk da haka bai kyauta ba xn mishi magana,
Tace Nagode sawwam, ina mutuniyarka yau duk ban ganku ba,
‘ita nake jira ma anan inaji bata fito lectures ba, tayi murmushi,

‘kuna birgeni dama haka Suhaib yake dana dace,
‘kinma dace abokina fa First Class ne matsalar shi ďaya Kuma xn mashi mgn xai gyara,
‘Nagode sosai ta juya ta fice, ya jingina yana jiran khairi yasan tayi fushi a ynda yaga fuskarta,
Wannan Karon lecture ďin da akayi komai bata fahimta ba duk hankalinta da tunaninta yana gurinsa gani take har ynxu yana tare da wannan budurwar,
Sun fito lectures Alawiya tace kije gani xuwa, man bai gaji da gani na ba,
Murmushi tayi kana tayi hostel fuskarta a ďaure ganinsa tsaye, inda yake ma bata kalla ba, ganin da gaske take yasha gabanta,
‘kin ganni fa shine kika wani fuske, tun ďaxu Ina jiranki ingayamiki na haqura shi kenan komai ya wuce, tabi ta gefensa xata wuce ya qara tare ta,
‘Ni ynxu Kuma menayi kike fushi dani,
Takaici na qara rufeta tambayarta yake meyayi bayan yasan abinda yayi, ta qara bata fuskarta taqi ma ta kallesa,
‘Ni ynxu koma menene kiyi haquri sulhu naxo muyi Kinsan banda wacce tafiki fa ya faďa cikin xolaya, harara tabisa da Ita kamar kwayar idonta xata faďi qasa,

‘ita wacce nagan ku tare fa?
‘au na manta… taja tsaki ta fice yayi saurin riqo hannunta,

*’Ramuwar gayya* ce da gangan nayi dan kiji yanda naji jiya dana ganki da wani, tunda kinji ynda naji shikenan, _50,50_ kiyi haquri,

Tayi shiru tana kallonsa, batare da ta tankaba,
‘budurwar Suhaib ce fa, mun fito lecture take gayamin abinda ya hadasu shine na jawota nan Muna mgn dan kigani, ni ynxu bama Wannan ba, abar mgnr, fushin ma kidaina nima na daina, Alawiya tayi maki kitson?

Kamar baxata tanka ba sai Kuma ta girgixa kanta,
‘muje saloon ayi maki acan bnga alamar ta iya kitso ba fa,

‘ta iya ita kemin ai, ynxu ma xataxo tana hanya, ya sauke ajiyar xuciya,
‘idan tayi ki dauki pic ďin ki turomin ta whatsapp

ingani inyayi kyau, dama ga gashin ba fasali,

Ta saki murmushi tana kallonsa,
‘Kuma a hakan wani ya gani yace yana so,
‘to ya xanyi tunda Ina son kayana, da haka suka bige da hira har Alawiya taxo itama tasa bakinta kana suka nufi hostel yayi gida.
*pherty xarah💞*

        &

*ummi shatu👌🏼*

*RAMUWAR GAYYA…*💘

  _Love story, 50,50_
*_UMMI A’ISHA_*

       _With_

*_PHERTYMAH XARAH_*

32

*T*un daga ranar suka shirya suka cigaba da gudanar da soyayyarsu cikin kaunar juna da kwanciyar hankali,

Koda wanne lokaci suna tare basa rabuwa, darene kawai ke rabasu da haka har semester tayi nisa, karatu kam suna yinsa babu kama hannun yaro musamman ma sawwam domin yanzu a final year yake kuma semester din karshe, khairi dai hankalinta yafara tashi da tunanin rabuwarsu da sawwam domin tasan idan yagama makaranta shikenan rabuwarsu tazo bazasu sake irin zaman da suka yi abaya ba, kullum cikin aikin rarrashinta yake yana nuna mata cewar koda ace yagama makaranta tofa basu rabuba, duk da hakan da yake fada mata dai hankalinta baya kwanciya yanda ya kamata,

Jin anfara kishin kishin din Cewar ankusa fitar da exam time table yasata shiga cikin wata damuwar,

Tana tsaye itada alawiyya sun fito daga lecture suna sallama domin alawiyyan gida zata tafi,

Sawwam ta hango yana zaune asaman motarsa idonshi sanye cikin bakin glass sai faman kallonta yake,

“Ohhh ni alawiyya ina ganin ikon Allah, anya kuwa ranar da aka daura muku aure da sawwam ba cinye junanku zakuyi ba…” Alawiyya tafadi tana dariya,

“Ehhh ai dayake kin san mu mayune”

“A,a karki yimin sharri malama ni bahaka nake nufi ba, gani dai nayi mutumin naki ya zauna ya kura miki ido ko kiftawa bayayi shiyasa”

Waiwayawa ummulkhairi tayi ta hangoshi zaune, murmushi tayi ta juya ga alawiyya tana cewa,

“Sannunki da sa ido in banda haka tayaya kika gane ni yake kallo bayan yasaka glass?”
“Uhm kinga tafiyata, kema ki hanzarta ki je wurin bita zaizai din naki kar yagaji da jiranki” tana kammala fadin haka tajuya tayi gaba,

Murmushi ummulkhairi tayi ta nufi wurin sawwam wanda har lokacin bai daina kallonta ba,

“Shine kaketa kallona gashi har kasa alawiyya tana tsokanata” tafadi cikin shagwaba bayan ta karasa kusa dashi tana kallonsa,

“Zo ki fada min abinda tace miki gobe idan tazo sai na rama miki”

Yace da ita yana murmushi, kafada ta makale tana kallonsa,

“Ba kaine kasa ta tsokaneni ba”

“Shine ai nace ki fada min sai na rama miki”

Zuba mishi ido tayi tana kallonsa, rigar jikinsa ja ce da fara aciki sai jan wando da jan takalmi,

“Kayi kyau” tace dashi ba tare data saniba,

“Dagaske?” Taji ya tambayeta,

Sake kallonshi tayi tana murmushi,

“Dagaske Mana, ina fata yan matan makarantar nan yau basu kalle min kaiba”

Murmushi yasaki yana sake kallonta ta cikin glass din idonshi,

“Babu wacce ta kalleni saboda duk sun san ni nakine ke daya…”

Murmushi tayi, “Allah yasa dagaske kake”

Tsalle yayi ya diro daga saman motar tashi ya bude mata gaban motar ta shiga ta zauna,

Shima budewa yayi yashiga ya zauna,

Hannunshi ya tura baya ya dauko project ya mika mata,

“Karbi kigani nagama project dina harma nayi submitting…”

Karba tayi tana gani sai dai tayi shiru kawai tana kallo, hawaye ya hango yana diga daga idanuwanta yana disa akan takardar project din,

Kanta ya dago ya juyo da fuskarta sai yaga hawaye fal,

Girgiza mata kai yashiga yi yana rikeda hannunta,

“Haba my lonely menene abin yin kuka kuma keda ya kamata kiyi murna nakusa gama karatu nafara aiki muyi aure mu zauna tare mu rayu tare har abada,

Kullum fa baccina marar dadine saboda rashinki akusa dani gashi dakin har tsoro yake bani domin yayi min girma ni daya, idan na makara babu mai tashina sai dai idan mami taga rana tafito ban fitoba ta taimaka min taje ta tadani,

Gashi kullum cikin….” Shiru yayi yana kallonta,

“In fada miki? Amma sirri nane..”

Dagowa tayi ta kalleshi bayan tadaga masa kai, “fada min..”

“To kullum cikin mafarkinki nake, gashi bana jin dadin baccin ko kadan saboda babu ke, amma kinga idan muka yi aure, tare zamu runka yin bacci dake, ajikina zan rinka kwantar dake,inyi miki pillow da kirjina, in tayi miki tausa har bacci ya daukeki kinga ai irin wannan baccin bama zamu san asuba tayiba…”

Dariya da kunyane suka ziyarceta a lokaci guda, daya hannunta tasa ta kare fuskarta tana murmushi,

“Gaskiya namiji bashida alkunya wallahi” tafada ahankali batare da tasan zaiji ba,

“Babu wani rashin kunya, abinda zai farune fa nake fada miki, ko ban fada miki yanzu ba ai idan lokacin yayi zaki ga hakan tafaru”

“To ni basai ka fada minba” tace dashi har lokacin fuskarta arufe take taki budewa,

“A’a gara dai in fada miki kiji, kar naje idan munyi auren kina rufe min kofa kina gudun daki, kin san da idan akayiwa yarinya aure guduwa take, to ban sani ba ko kema hakan zakiyi min”

Dariya tasaka tana kallonsa, “ai kuwa nima guduwar zanyi dama kakata ta bani labari”

Dariya yayi ya cire glass din fuskarshi ya ajiye tareda kwantar da kujerarsa baya kadan,

“Nima babar mami ce take bani labari wai lokacin da akayi aurenta tafi wata biyar tana wannan gudun sai daga baya sannan ta zauna tadaina guduwa, ke dai idan kika gudu wallahi binki zanyi ko inane”

Dariya ta sake yi “gidan mami ai zan gudu”

“Ta kwana gidan sauki indai gidan mamine wallahi zan iya binki, gidanku ne kawai zaki je na kyaleki ban biki ba saboda kar ace nayi rashin kunya”

Kallonsa tayi tana murmushi, “dama ai baka da ita”
Kallonta shima yayi yasaka murmushi, “sai kinji wani labari da baba dan tsoho yabani wai su a kauyensu idan an yiwa yarinya aure to sai an hadata da karamar yarinya kamar yar shekara takwas ko bakwai sun tafi gidan mijin tare, waima tare za akaisu..”

Kallonsa tayi cikeda tsokana tace, “muma haka al’adar garinmu take so be prepare dan nima da yar kanwata za akawo mu”

Dariya yayi kafin yajuya ya kalleta, “babu damuwa Ku taho tare inada extra room wanda zata rinka kwana nidai ba mai nisantani da matata dan wallahi bazan rinka kwana ni daya ba”

Dariya tasa harda kwalla dan tsabar dariya,

“Kiyi dariya da kyau, nidai ban hanaki zuwa da yar rakiya ba amma wallahi ko tazo sai dai ta rinka zama ita kadai danni wata daya zanyi agida ban leka ko inaba har sai nagama ganawa da matata”

Murmushi tayi ta ajiye masa project dinshi akujerar baya,

“Wasa nake maka ma, nasan abbanmu ma bazai bariba wallahi”

Dadi yaji ganin ya rabata da damuwar da take damunta gashi yanzu ta ware sunata hira kamar ba itace da tafara yi masa kuka ba,

“To idan ke kadaice idan aka kawoki da kwana biyu honey moon zamu tafi zamuje ki zazzaga gurare kiyi kallo”

“Hmmm sawwam kenan kaci buri akan wannan ranar, Allah dai ya nuna mana lokacin da alkairi”

“Kema nasan kina tason ranar tazo kawai kukan munafurci kike, amma aranki har addu’a kike Allah ya kawo ranar, nasanma ji kike kamar ki janyota da karfi ta dawo kusa..” Yafada cikin zolaya,

Murmushi tayi ta dan harareshi, “sai kace kai, ni barima natafi hostel yunwa nakeji”

“Muje nakaiki kici abinci a restaurant”
Kai ta girgiza masa, “wallahi indomie nake sha’awa, ita zanje na dafa yanzu”

Baki ya tabe ya girgiza mata kai, “Abin yazo kenan domin shima yana saku kwadayi”

Bude kofar motar tayi tafita batare data bashi amsaba domin sawwam sai kace maye yake duk lokacin da take cikin wannan yanayin sai ya ganeta tarasa tayaya yake fahimta,

“Ki shirya da yamma zanzo muje kigaida mami wallahi tun jiya take yimin magana akan na kaiki wai kwana biyu baku gaisa ba”

“To sai kazo”  ta bashi amsa gamida juyawa ta nufi hostel, shi dinma reverse yayi ya fita daga school din ya nufi gida.

  Kamar yadda yace da yamma zai dawo haka kuwa akayi sai gashi yadawo, waya yayi mata ta shirya tafita, irin dogayen rigunan da ya kawo mata tsaraba daga saudiyya aciki ta saka daya, blue din doguwar Arabian gown mai stones ajiki, tayi rolling da mayafin rigar tafita sai kamshi take zubawa,

Acikin mota ta iskeshi zaune yana jiranta amma fuskarsa ahade,

“Sahibi muje ko”

Motar kawai ya tada batare da ya kalleta ba,har saida suka fita daga makarantar sannan yayi magana,

“Kar nasake ganin kin fito haka, kinga yanda shape din jikinki ya fito acikin rigar nan? Duk yanda akayi ma wannan rigar rage mata fadi kikayi, ko kunya bakiji ba kika keto ta cikin maza kika fito ahaka ana kallonki, maimakon kisaka hijab shine kika dauko dan wannan mayafin”

Kallonshi tayi domin tagane abinda yake yiwa fushi yanzu,

“Amma naga dai ai kaine ka siyo min rigar ko? Danma dai banice na siya ba bare kaji dadin yimin fada”

Packing yayi agefen titi, to kuma danni na siyo miki sai ki rinka fitowa ahaka duk shape dunki awaje?”

“To yanzu me kakeso ayi? Kaga idan ba zaka kaini ba ka fada min na koma”

Shiru yayi mata yana kallon titi tunani yake dazu lokacin data fito wasu samari sun kai su shida azaune ganinta duk sai suka maida idonsu kanta harda waiwayenta yana kallonsu ta mirror din motarsa,

Bude kofar motar tayi zata fita, cikin zafin nama ya janyota yamaida kofar ya rufe,

“Bakida hankali? Titi zaki fita ahaka wasu su sake ganinki?”

Atsorace take kallonsa ganin yanda idanuwanshi suka sauya lokaci guda, kishine dankare aciki, ita sai taji ma tafara jin tsoransa,

“Kayi hakuri bazan sake ba”

Ajiyar zuciya yasaki ahankali ya kunna motar yana kallonta,

“Kairi saifa kinyi hakuri dani saboda wallahi bana son kowa ya kallar min yanda siffar jikinki take, nafi son ni kadai zan ga kayana a lokacin da mukayi aure”

Ajiyar zuciya itama ta ajiye tace dashi “baka son wani yaga jikina amma kasaka min kadangare ajikina har saida nacire hijabina acikin mutane?”

Murmushi yasaki babu shiri, “ai wannan duk acikin rashin sanine”

“Babu wani rashin sani kawai dai neman fada”

Dariya yayi yakama kunnensa daya “to am sorry, ai nabaki hakuri sai ki yafe min”

“Ni ban hakura ba” tace dashi,

“Sai yaushe zaki hakura?”

“Sai kace min i love you sau dari”

Dariya yayi yafara fada mata tana kirgawa da haka har sukaje gidan mami, suna shiga motar su hajiya Raliya mahaifiyar Rukayya na shigowa kamar tare suke,

Bude mata yayi ta fito yakama hannunta zuwa ciki hajiya raliya na kallonsu itada yarta Rukayya,

Afalo suka samu mami tana dudduba wasu hadaddun swiss lace wadanda aka kawo mata ta siya, ganinsu yasata ajiye kayan ta maida hankalinta garesu cikeda fara’a, daidai lokacin su Rukayya suka shigo ita da mahaifiyarta,

Wuri suka samu suka zazzauna Rukayya sai kallon sawwam take cikeda so shikuma duk hankalinsa naga abar sonshi kairi, zungurarta mahaifiyarta tayi,

“Wannan din wacece?” Ta tambayeta cikin rada,

“Momy inajin budurwarsa ce”
Zaro ido mahaifiyarta tayi, ai kuwa abinda bazai taba faruwaba kenan, lallai yazama dole su tashi atsaye tun kafin kwado yayi musu kafa,hajiya raliya mahaifiyar rukayya ta ayyana hakan acikin ranta…

aishaummi.blogspot.com

Ummi Shatu👌🏻

Pherty Xarah💞

*RAMUWAR GAYYA…*💘

  _Love story 50,50_

  *_UMMI A’ISHA_*

         _With_

*_PHERTYMAH XARAH_*

33
GWS my besty phertyma Xarah!

*J*ijjiga kai hajiya raliya tayi zuciyarta cunkushe da bacin rai gamida kunar zuciya, ido ta zubawa ummulkhairi wacce ke durkushe agaban mami mahaifiyar sawwam tana gaida ita,

Cikin sauri mami ta dago ummulkhairin ta rungumeta tana murmushi,

“Haba ummulkhairi wannan irin gaisuwa haka, gaisuwar ta isa haka maza zauna asaman kujera…”

“Mami kibarta tayita durkuson mana har kafarta sai ta tari jini” sawwam yafada cikin tsokana yana kallon khairi,

“Naki nabarta din, ni matsa kabani wuri ja’iri kawai” Mami tace dashi tana kokarin zaunar da ummulkhairi akan kujera,

“Ina yini?” Ummulkhairi ta katsewa hajiya raliya tunaninta ta hanyar gaisar da ita, sai da ta danyi firgigit kafin ta amsa da
“Lafiya lau yanmata” fuskarta adan sake amma kuma can kasan zuciyarta damuwace fal alla alla take su kebe da aminiyar tata tabaje mata abubuwan dake cikin ranta,

In banda kallon umkulkhair babu abinda take yi gashi babu laifi taganta kyakkyawa ce wacce bata da makusa,

Itama rukayyan duk hankalinta yana kansu sawwam da ummulkhair wanda suke zaune akujera daya, tayi tayi dashi ya tashi saboda su mami amma sam yaki yana zaune kusa da ita hannunshi rikeda remote yana canja channel,

“Um hajiya Raliya yi hakuri wallahi bakuwa nayi ne, sannu da zuwa, mukarasa ciki” mami tace da aminiyar tata fuskarta kumshe da murmushi,

“To Hajjaju mukarasa” hajiya raliya tace bayan ta mike dauke da jakarta,

Ummulkhair ce ta dubi sawwam wanda ya take mata kafarta daya da tashi,

“Sawwam wai menene haka? Dan kaga nazo gidanku shine zaka rinka yimin mugunta ko? Babu komai”

Murmushi yayi ya kalleta, kafin ya juya ya kalli baba lami daya daga cikin masu aikin gidan wacce taketa faman jajjera kayan marmari da kayan jika makoshi akan center table,

Sai da yabari baba lami tafita sannan ya juya ya kalleta,

“Kizo muje part dina kiga dakina”

Harararshi tayi ta koma jikin kujerar ta kishingida,

“Nikuma menene zai kaini dakinka yanzu? Tab Allah ya sawwake..”

Gyara zamanshi yayi yana kallonta,

“To me kike nufi? Tunani kike yi ko cutar dake zanyi ko?”

Murmushi ya sake yi ya sassauta muryarshi tayadda Rukayya bazata jiyosu ba domin yaga kamar kunnenta yana wurin,

“In banda abinki ana cutar da wadda watanta ya zagayo ne?”

Juya mishi baya tayi tana kallon Rukayya wacce fuskarta take adaure tamau sakamakon ganin ummulkhair da tayi domin bata manta lokacin da suka hadu a supermarket ba lokacin da sawwam yakaita shopping ashe dama budurwarsa ce yatsaya yana raina mata hankali sai dai amma tasha alwashin daukar fansa akansu.

  Hajiya raliya suna shiga dakin mami ta zauna abakin gado ranta abace,

“Mamin sawwam wacce yarinya Nagani ne tareda sawwam afalo?”

Murmushi mami tayi itama ta zauna tana mai fuskantar hajiya raliyan,

“Wallahi wai budurwarsa ce yace ita yake so zai aura”

Bata fuska hajiya raliya tayi,

“Haba haba mamin sawwam kuma yanzu ku sai kubarshi ya aureta?”

“To ya zamuyi tunda yana sonta tana sonshi, shi kansa dad dinsa yasan da maganar yarinyar”

Tabe baki hajiya raliya tayi, “tabdijan,amma kuwa wallahi mami kin bani mamaki, yanzu yarinyar da baku san asalinta ba ita zaku bari ya aura, kai duk ma ba wannan ba shin kunsan ko suwaye iyayenta? Hmmm sannan ina maganar alkawarinmu da mukayi na hadasu aure shida Rukayya?”

“Ai yaki amincewa hajiya raliya, wallahi babu yanda banyi dashi ba akan yayarda amma sam yaki yarda, da ace ya yarda ma ai da sai dai kiji labarin za azo ayi maganar bikin”

Tabe baki hajiya raliya tayi ta mike hannunta rike da jakarta,

“Shikenan tunda son ran danki zakibi, ni tawa yarma da take mace na iya tilastata ta amince sai danki ne zai bijire shida yake namiji? Ai shikenan, ni zan tafi sai wani lokacin kuma”

Bin bayanta mami tayi tana babbata hakuri kan cewar ba laifinta bane sawwam dinne bai aminceba,

Su sawwam na zaune afalo shida ummulkhair da Rukayya su mami suka fito, tashi Rukayya tayi suka fita ita da mahaifiyarta mami tana bayansu domin rakiya,

“Nima tafiya zanyi yanzu tunda dare yakusa yi” ummulkhair tace dashi idanunta yana kallon kasa,

“Allah ya kiyaye hanya danni na shigo gida kenan nida sake fita sai gobe”

“Tab ai wallahi baka isaba,yanda ka kawoni haka zaka mayar dani” tace dashi bayan takai masa duka,

Shigowar mami ce tahanashi bata amsa, nemar wuri mami tayi ta zauna tana fuskantarsu,

“Mami kinji wai tafiya zatayi bazata kwana ba”

Murmushi mami tayi tana kallonsu, “ai baka saniba ko wani uzurin zatayi idan ta koma”

“Wallahi mami babu abinda zatayi so take ta tafi da wuri saboda saurayinta zaizo, kar yazo bai sameta ba”

“Mami wallahi da wasa yake yi ni banida wani saurayi”

“Toma menene idan kina dashi ummulkhair ai dama ita mace yar hakace”

“Tab to wallahi mami banda wannan saboda ita ta banbanta da sauran mata” sawwam yafada cikin kishi,

Murmushi mami tayi ta mike ta shiga dakinta domin hadowa ummulkhair kayan kwalliya,

“Kibari ayi salla sai na mayar dake to”

Girgiza masa kai tayi, “kasan fa bana yi, bana son lokacin sallah yayi mami tace nazo nayi, ban san me zan ce mata ba”

“Bari tazo ni sai infada mata cewar bakya yi”

Bakinta ta rufe da hannunta bayan ta kwalalo ido “ka rufa min asiri dan Allah karka fada mata”

“To menene idan nafada? Karya nayi,kawai kin rigada kin girma yanmata”

“Baka da kunya sawwam, yanzu dan tsabar rashin kunya sai ka iya fadawa mami wannan maganar?”

“Tsaya wasa yarinya”

“Wallahi indai kafada nida kaine…”

Dariya yasa ya mike tsaye ya fita, tana zaune a inda suka barta mami ta fito dauke da katuwar leda mai dauke da kayan kwalliya masu tsada aciki harda turmin atamfa,

Mika mata mami tayi tana murmushi, “to gashi aje ayita yiwa yarona kwalliya Allah yabada Sa,ar karatu”

Cikeda kunya ummulkhair ta girgiza kai “a,a mami kibarshi wallahi nagode”

“Bawani nan sai kin karba dama jiya kike fada min kayan kwalliyarki sun kare da mami bata bayar bama da saina siyo, yanzu kuma anbaki ki tsaya kina fulako? Mami miko na rike mata angode madalla”

Tajiyo muryar sawwam yana fada daga bakin kofa, karbar kayan yayi yawuce, itama mikewa tayi tabi bayansa bayan tayiwa mami godiya, har bakin gate mami ta rakata sannan takoma gida ita kuma tawuce motar sawwam,

Zama tayi tana harararsa, “yaushe muka yi haka dakai?”

“Jiya” yabata amsa bayan ya tada motar,

“Jiya a ina?”

“A mafarki” yafada yana dariya, duka takai masa yayi saurin rike hannunta,

“Wai waye yafada miki ana dukan miji ne? Wallahi kibari tun kafin nafara ramawa”

“To waye yasaka ka fadawa mami haka”

Sakinta yayi yafara driving yana yimata gwalo, kyaleshi tayi sai murmushi kawai da fuskarta ke fitarwa.
***

Safa da marwa kawai takeyi a tangamemen falon nata, sai kaiwa da komowa take zuciyarta a bace,

“Lallai ya zama dole nasan irin matakin da zan dauka akan wannan al’amari, kuma wallahi indai muna raye to sawwam bashida matar da tawuce Rukayya, yama za ayi haka tafaru? Sai da nagama cin alwashi nagama buri akan wannan al’amari sannan wai azo ace min abun bazai faruba ba, wallahi karyane…”

Hajiya raliya tafada da karfi wanda har saida bangon dakin ya amsa ta hanyar daukar amon muryarta.

  _Masu karatu kuyi hakuri da wannan babu yawa, muna fatan kuna biye damu._

aishaummi.blogspot.com
Ummi Shatu👌🏻

Pherty Xarah💞

*RAMUWAR GAYYA……. 💘*
_love story 50,50_

*Fertymerh Xarah*

            &

*Ummy Aysher*
     34

   2 days later~

  Momin Rukayya taje gidan, sun jima suna hira da Mami Duk mgnrta dai akan irin son da rukkaya ke yiwa sawwam ne,
Mami tayi murmushi tana kallonta,
‘a ynxu sawwam bashida buri kamar khairi duk ynda kike tunani ba haka bane a ynxu domin sawwam baxaa mashi dole ba,
‘amma ai tun farko munyi niyar hadasu aure ne har kika amince da Rukayya taxo gidannan saboda shi, inaji har shopping yaje da Ita, ba mami taja numfashi,
Sawwam baya son rukkaya, khairi yake so, baxan tursasa mashi ba haka kuma baxanyi baqin ciki idan har yace Rukayya take so ba sai dai itama khairi abinso ce, fatana Allah ya bashi mace ta gari wadda xata riqesa da ya’yansa amana shine burina,
Maman Rukayya tayi shiru kafin tace Ina Swiss lace ďin da mukayi magana dake ki ďauko su naje dasu ko xa’a samu masu siye sai a saro wasu,
Shikenan mami ta faďa bayan ta tashi ta nufi dakinta da sauri maman Rukayya tayi kitchen inda Mai aikinsu, ta ciro magani Acikin Leda baqa ta bata,
‘Kan Mgnr da mukayi dake a waya gashi ki sanyawa sawwam a abinci Kuma ki tabbatar da yaci kada kibari a ganki, ga dubu goma idan aikin yayi xn qara maki wasu akai, Mai aikin ta karba jikinta na rawa,
Xamanta a falon yayi daidai da fitowar mami ďaki ďauke da kayan ta xube su a gabanta tana kallonta,

‘gasu guda goma ne, kinsan kuďin ni banason masu riqe bashi,
‘hakane ni ma banaso nasan Waďanda xn baiwa, ta soma haďa kayan…….
*

‘kibari anjima xn shigo, kinga ynxu Inaso nayi wanka, ga yunwa, ga barci…..
‘tor kabari nayima girki anan Pls sahibina, ni banaso ka tafi ne,
‘idan kinmin girki shi Kuma wanka fa? Ya faďa Idanunsa akanta, murmushi tayi,
‘kaje gida kayi mana, ya tayarda motar yana faďin,
‘shima abincin kibari naje gida naci, through out yau fa muna tare, bawai nagaji da ganinki bane is just that kamar banajin daďin jikina,
‘shikenan Allah ya kaika lfy ta juya xata fice ya riqo hannunta ta dubesa,
‘hope bakiyi fushi ba, ta gyada kanta,
‘smile… ta bata fuska,
‘Pls khairi….. taqi,
‘anjima xnxo I promise you, I will be with you, pls smile, tayi murmushi tana kallonsa,
‘kaxo min da irin Wannan cake ďin na jiya,
‘oh Mami tayishi fa, kinji daďin sa kenan, ta gyada Kai tana kallonsa da murmushi,
‘shikenan idan akwai sauran xn xo maki dashi, but remember me kafin naxo,
‘Tace shikenan safe trip,
‘yace bako kiss ko sau ďaya ne a kumatu,
‘lol kai kafiye shirme wani sa’in,
‘shikenan ni Kuma baxan xo ba, ya ďauke kansa daga kallonta, tayi dariya ta fice daga motar, ta rufe kana ta sunkuya ta glass ďin motar,
‘idan kaxo anjima xn yima, ya dubeta,
‘you promise….
ta gyada Kai tana murmushi,
‘idan kika qi fa?
‘baxan qi ba…. yayi murmushi yaja motar ya fice….,
Yana xuwa gida Kai tsaye dinning ya xauna yaci abinci sosai Mai aikin na labe tana kallonsa, bayan ya gama wanka yayi, bayan yayi sallah ya kwanta barci…..
Yinin ranar basuyi waya ba Kamar yanda suka saba, bata damu ba tunda ya gayamata barci xaiyi,
Da dare tayi kiran wayarsa tana ringing bai ďauka ba kuma bai kirata ba, sai ta shiga damuwa kada dai bai lfy ne….
Sawwam xaune a ďakinsa da robar ruwan swan yana kwararawa cikinsa, yana ganin kiran khairi yaqi ďauka haka kawai ya tsinci kansa cikin jin haushinta bai san meyasa ba, message ya shigo wayarsa yana dubawa khairi ce,
  _’Ina fatan ba jikin bane, idan shine Allah ya baka lfy, lonely without you….._

  Yaja tsaki ya cilla wayar aljihunsa, ya fice daga gidan, gidansu Rukayya ya nufa, daga ita har mamanta sunyi murna da xuwansu aikinsu yayi kyau kenan,
Sanda ta shiga motar ta xauna idanu kawai ya xuba mata yana kallonta, baisan dalilin dayasa xuciyarsa ta takuramasa da tunaninta ba bayan yasan ba itace a xuciyarsa ba,

‘Sannu da xuwa sawwam, nayi farin cikin ganinka, yaja Numfashi batare da ya tanka ba ya ďauke kansa daga kallonta,
‘baxaka shiga ciki ku gaisa da mama ba,
‘not now, shikadai  ya faďa batare da ya Kalle taba,
‘me xan kawo ma,
‘nothing,
‘uhm… uhm daman Abba ne yayi mgn kan auren mu, yaushe xaka turo ayi mgnr….
Ya juya yana kallon ta, sai Kuma ya tabe bakinsa,
‘xn wuce gida ko xaki iya fita, ba musu ta fice jikinta a sanyaye yaja motar ya fice, taje tayiwa mama bayani ynda sukayi,
‘kibarshi komai xai daidaita da kansa xaki ganshi yaxo neman aurenki,
Bayan fitarsa gidan kamar xaije Skul sai Kuma ya fasa har lokacin khairi na kiransa a waya daga qarshe ma kashe Wayar yayi gabaki ďaya,
A ranar khairi ta shiga damuwa, barci gagararta yayi tunani iri iri ba Wanda xuciyarta bata ayyana mata ba,

Washe garin ranar, daka ganta kasan bata cikin walwala gashi Alawiyya bata xoba ranar ballantana ta gayamata damuwarta, sukuku ta yini harta gama lectures ďin ta, koda ta fito babu sawwam bai jirataba kamar kullum alhali taga motarshi,
Xuciyarta na soma bugawa hankalinta ya tashi sosai, duk tunaninta ta kasa gano laifinta a jiya, tasan ba Mgnr kiss bane cos sun saba wannan rigimar dashi,
A waya ta kira Alawiyya take gayamata komai,
‘bana tunanin wani abune amma Kiyi addua may be akwai abinda ke damunsa gobe xn shigo,
Sai ga hawaye nabin kumatunta, so painful, tana jin sonsa har cikin xuciyarta, ta qara gwada kiran layinsa tana ringing ba’a ďauka ba daga qarshe ma aka kashe wayar, ta haďa kanta da gwiwarta tana kuka sosai, Ashe haka so yake?
Kwana biyu, yana tsaye bakin motarsa yana waya ta tunkaresa, yana haďa ido da ita sai da gabansa na faďi harda sauke numfashi sai dai fuskarsa ba walwala, ta matsa kaďan kusa dashi,
‘miye laifina da kake hukuntani haka, ko daman ka shigo rayuwatane dan ka yaudareni…. sai ga hawaye sharrrrr, yaji tausayinta sosai sai yaji kamar ya rungumeta yabata haquri, ya riqa hannunta suka shiga mota kana ya juyo da Ita suna fuskantar juna,
‘bansan meke damuna ba, kawai na tsinci kaina cikin jin haushinki, in short kamar bana son ganinki amma kina xuciyata,
Gabanta yayi mummunan faďuwa ta ware idanu sosai tana kallonsa jin kalamansa, baya son ganinta, meyasa, saboda wane dalili,
Ya soma share mata hawayen fuskarta,
‘I think komai xai daidai ta but just pray for me, ina sonki khairi… ga mamakinta sai ji tayi ya rungumeta sosai a jikinsa yana rarrashinta, da sauri ta xame jikinta daga nasa har lokacin idanunsa akanta, ta soma share hawayenta, gskyr Alawiya da tace ta tashi da addua meyiwuwa maqiya suka shiga alamarinsu gashi shima ya gayamata ta tayashi da addua, dole xata tashi tsaye akan xamantakewarsu,
Ta saqala hannunta cikin nasa, ya juyo yana kallonta har numfashinsa ke fita da sauri da sauri,
‘ba kiyi fushi ba, kin haqura,
‘ta gyada Kai tana kallonsa da murmushin yaqe, shima murmushin yayi cikin farin ciki.
Pherty💞

    &

Ummi shatu 👌🏼
Getting better, tnx 4 d Luv an care my fans…..

*RAMUWAR GAYYA…*💘

  _love story 50,50_
     *_UMMI A’ISHA_*

              _With_
     *_PHERTYMERH XARAH_*

35
“Tunda kin hakura yimin murmushi nagani”  sawwam yace da ita yana kallon kyakkyawar fuskarta har lokacin tana rike da yan yatsunshi cikin nata,

“Wanne murmushi kuma bayan wanda nake yi?”

Ta tambayeshi idanuwanta akasa,

“Dago da fuskarki kiga” yafada yana matse dan yatsanta daya,

“Me zan gani?” Ta tambayeshi gamida dago fuskarta,kyas taji karar camera da alama hoto ya dauketa,

Daya hannunta tasa ta kare fuskarta tana murmushi amma kuma acan kasan zuciyarta tausayinsu ne itada sawwam yake ratsata domin ganin sun fara fuskantar matsalar rayuwa tun kafin su kai ga cika burinsu nazama ma’aurata,

“Kalli kiga…” Ya mika mata wayar, karba tayi tana ganin hoton duk da ba ashirye akayi shi ba amma yayi kyau,

Murmushi tayi ta mika masa wayar “dama ai kasaba yimin hoto batare da sanina ba” tafada ashagwabance,

“Kuma wallahi duk wanda nayi sai yayi kyau, ko baki san nadauka ba”

Murmushi tayi tafara kokarin bude kofar motar,

“Tafiya zakiyi kibarni? Shikenan nima bari naje gida”

“Zaka dawo?” Ta tambayeshi idonta rau rau kamar zatayi hawaye,

“Zan dawo mana,zoma kiji..” Yace da ita amma kawai yafada ne saboda tasamu nutsuwa hankalinta ya kwanta amma magana ta gaskiya jinshi yake wani iri gashi dai yana mutukar son yaganta akusa dashi to amma kuma yanajin ranshi wani iri,

Batare data juya ba tace “me zanji?”

“To kijuyo mana indai kina son ji din”

Kanta ta sake daukewa, murmushi yayi ya matsa kusa da ita,

“Acuci maza kikayi ne?”

Hakan da yafurta ne yasata yin murmushi, “wa zan cuta?”

“Ni mana, nikuwa nasan baki da wani gashi sai bayan munyi aure sannan zakiyi”

“Sannunka, naga dai kaima ba gashin gareka ba”

“Kina sone nasake tarashi yafi wannan? Wallahi indai kina so to zan tara har yakamo naki a tsayi”

Dariya tayi ta juya tana kallonsa “har ka mutu gashinka bazai kamo nawa ba”

“Haka kikace?”

“Ehhh”

“Kalli bakinki na rashin kunya,zakiyi bayani ne”

“Ai kai yayane yi hakuri” tafada tana dariya, hannunta yasaki,”to sai anjima,kije hostel sai nadawo”

Fita tayi daga cikin motar tana yimasa bye bye har yabar wurin, hostel ta tasamma shiga amma acikin ranta ta daura niyyar taya sawwam da addu’a akan Allah ya yaye mishi abinda ke damusa.

  Sawwam gida ya wuce yana zuwa ya shiga falon mami tana zaune tana lissafin kudin wasu kaya da aka kawo mata,

Kan cinyarta sawwam ya dora kanshi,

“Mami ban san abinda yake damuna ba kwana biyu bana son ganin khairi, bana son koda jin muryarta gashi ina sonta ina kaunarta bana son rabuwa da ita..” Yana gama fadin haka sai ga hawaye nabin fuskarshi sharrrrrrr!

“Sawwam tun yaushe? Meya hadaku? Fada kukayi?” Girgiza mata kai yayi har lokacin hawaye ne yake fita daga idonsa,

“Yi shiru ka tashi kaje ka kira min baba dan tsoho”

Tashi yayi ya fita zuwa gate, baba dan tsoho na zaune yana sauraren rediyo sai dariya yake shi kadai,

“Baba dan tsoho hajiya tana Kira”

Yana fadin haka ya wuce yakoma cikin gida, ajiye rediyon baba dan tsoho yayi yabi bayan sawwam da sauri,

Cire takalmin kafarsa yayi ya shiga falon mami, tana zaune lullube da mayafi tayi tagumi, zama yayi suka gaisa ta sanar dashi duk abinda sawwam yafada mata dama sha’ani irin wannan tasaba fadawa baba dan tsoho kasancewar yana samar musu da mafita,

Gyara zama yayi ya kalli mami “babu komai insha Allah zanyi istihara kuma da yardar Allah koma menene zai warware”

“Allah yasa” mami tafada duk ranta ahargitse domin ji take kamar ta fashe da kuka.

Tun daga ranar baba dan tsoho ya dage da yiwa sawwam addu’a da rokon Allah, itama mami nayi hakama ummulkhair ba abarta abaya ba domin duk tafi kowa damuwa da halin da sawwam ya shiga, gashi soyayyarsu sai ja baya take ba kamar da ba,

Bayan kimanin sati biyu tana kwance adaki tayi shiru tana tunani sai taji karar wayarta, ganin sawwam ne yasata tashi zaune ta daga wayar,

“Bakya nema nane?” Taji yafada ahankali,

“Ni na isa, ina nemanka mana”

“To kizo gani awaje ina jiranki”

Kashe wayar tayi ta dauki gyalen doguwar rigar dake jikinta ta yafa tafita,

Yana zaune asaman motarshi yasha kananan kaya jeans & t shirt, yana hangota ya diro daga saman motar yana murmushi,

“My lonely barka da fitowa” dadine ya kamata domin rabonta da taji ya kirata da wannan sunan har ta fara mantawa,

Murmushi tayi tana wasa da hannun gyalenta,

“Say something mana my lonely..” Shiru tayi tana kallonsa amma kuma wani farin cikine ke ratsata,

“Kalli bayanki kigani..” Yace da ita yana dariya, tana juyawa taga wani katon kare yana nufota,

Cikin razana tawuce bayanshi ta rungumeshi, sosai ta kankameshi tareda boye fuskarta a bayanshi, in banda rawa babu abinda jikinta yake yi,

Dariya sawwam yake yi sosai yana jinta jikinta sai rawa yake, sannan ta rungumeshi ta baya kam kam,

“My lonely yatafi fa” yace da ita ahankali,

Dago kanta tayi ta lalleka bataga karen ba,

“Muje cikin mota, wallahi ni tsoron kare nake ji kar yazo ya cijeni”

Har yabude mata gaban motar tana rike dashi, zama tayi ya rufe yazagaya ya shiga yana mata dariya,

“Wai dama haka kike da tsoro ban saniba” yafada cikeda tsokana,

“Wallahi bana son kare, yatab’a biyoni ne lokacin ina yarinya, dakyar aka kwaceni da tuni ya cijeni tun daga lokacin nake tsoronsa”

“Ummulkhairi mai tsoron kare” yafada yana dariya, duka takai masa sai kuma tafasa tarike cikinta,

“Wallahi cikina ne yake ciwo washh”

Sunkuyawa yayi yana tambayarta “ciki? Me kika ci?”

“Babu komai..” Tabashi amsa har lokacin tana rikeda cikinta,

“Ciwon ciki kikace?”. Kai tadaga masa,hannunshi yasa acikin dan wani aljihu dake bayan kujerarsa ya dauko magani,

“Ga magani kisha indai ciwon cikine yanzu zai daina, idan kuma bashi bane ki fada min gaskiya…”

Dagowa tayi ta kalleshi batayi magana ba kuma bata karbi maganin ba,

“Idan kin san wata ne ya zagayo to kifada min gaskiya in Kuma ciwon cikine to ga magani”

Nan dinma shiru tayi masa tana kallonsa,

“Ciwon cikine ko ciwon mara?” Kai ta daga masa,

“Wanne aciki kike yi? Ciwon Mara? Ciwon ciki?”

Kai tasake daga masa,

“My lonely nidai ban gane wannan daga kan naki ba”

Fitilar motar ya kunna ya janyo kafarta daya yana kallo, kafar ta dan kumbura kuma tayi fari sosai, mayar mata kafarta yayi ya ajiye yana murmushi,

“Tun farko da sai kifada min gaskiya cewar watane ya zagayo amma kya wani tsaya kina kallona…, muje nakaiki chemist nasai miki magani”

Kwantar da kanta tayi ajikin kujera idanuwanta arufe, tana jinshi ya tashi motar, sai da suka fita daga cikin makarantar sannan ya juya yana kallonta,

“Dama can kina irin wannan ciwon ne?”

Girgiza masa kai tayi “sai dai ciwon kafa da tashin zuciya”

“Wannan kumburin da tayi dama na ciwonne?”

Daga masa kai tayi, “ciwo sosai ma, wani lokacin fa dakyar nake takawa”

“Ayya sorry my lonely insha Allahu kin kusa ki daina daga munyi aure shikenan zan baki magani, ai kina so ko?”

“Kai sawwam” tafada cikeda kunya,

“Babu wani kai” yafada yana dariya, wani sabon chemist sukaje wanda ke gaba kadan da makarantar, shiga yayi ya siyo mata magungunan yadawo, maidata makaranta yayi sai faman tsokanarta yake, ba karamin dadi tajiba ganin yanda ya koma mata sawwam dinta sak mai sonta, mai sake mata fuska,mai tsokanarta da sakata dariya akowanne lokaci wanda suke tare,

Ganin bata da lafiya yasashi yana ajiyeta yayi mata sallama yatafi,koda yakoma gidama yana kwanciya ya kirata lokacin ma ita har tayi bacci sakamakon maganin data sha, karar wayarne ya tasheta,

Hira sukayi sosai domin har wurin karfe 2 nadare suka kai suna hira, kamar karsu rabu haka suka daure suka yi sallama da juna.

***
  Baba lami na kitchen tana jajjera abinci akan faranti bayan ta kammala hadawa,

Dan wake ne tayiwa sawwam, ahankali take zaro kullin dake soke acikin zaninta,warwarewa tayi tafara diba kadan tana barbadawa aciki, sai da tagama barbadeshi tas sannan ta mayar ta soke a zaninta, rufe flasks din tayi ta kinkima zata fita, turus tayi sakamakon ganin mami atsaye tana kallonta,

“Ha…hajiya yanzu kika shigo?”

Mika mata hannu mami tayi,

“Bani abinda kika boye a zaninki”

“Hajiya babu koma..”

“Kibani nace” mami ta daka Mata tsawa, cikin rawar jiki tafito da kullin garin maganin ta mika mata ta tsugunna tana neman gafara,

“Ina so ki fada min wanda yasaki”

Shiru baba lami tayi domin dama hajiya raliya sai da ta gargadeta da cewar kada ta kuskura tafadi cewar itace tasata idan ankamata,

Tambayar duniya mami tayi mata amma taki amsawa, ganin haka yasa mami dauko mata kudinta wato albashinta datake biyanta tabata tace tabar mata gida domin duk wanda yayi maka wannan to za a iya hada baki dashi akasheka,haka baba lami ta tattara komatsanta tayi gaba to sai muce Allah ya raka taki gona.

  Ahalin yanzu kam soyayyar sawwam da khairi tadawo normal, kullum suna tare basa nisa da juna, Rukayya kuwa yama manta da ita dama can bata gabansa,

Ganin ankafe time table din exam yasa ummulkhairi shiryawa domin zuwa gida weekend, lokacin da ta sanarwa sawwam sai yabata rai saboda baya son ta tafi amma ganin tunda tazo bataje ba yasashi hakura yarakata tasha ta tafi, amma duk da haka koda yaushe suna makale awaya minti kadan zai kirata ko abinci zaici sai yafada mata,

Yanzun ma tashinsa daga bacci kenan zai shiga wanka ya kirata, tana tsakar gida tana gyarawa mama alayyahu ganin kiransa yasata sadadawa daki ta kwanta akan katifarta ta daga wayar,

“Sahibina har katashi daga baccin?”

Wata hamma yayi sannan yayi mik’a,

“Yanzun nan natashi, baccin ai babu dadi saboda babu ke..”

Murmushi tayi “me kakeci nabaka na zuba, idan munyi auren har gajiya da ganina zakayi watarana ka korani dakina kace hutawa zaka yi..”

Murmushi yayi ya tashi zaune ya ziro kafafunshi daga saman gado zuwa kasa,

“Tab kar Allah ya kawo wannan ranar, ranar dai da zan gaji dake bana fatan ganin wannan ranar,nida nake son irinka ganin ki akusa dani saboda nasan zan samu kulawa, kinga yanzu wanka nake son yi amma duk jin jikina nake a mace, da ace munyi aure kinga da kece zaki yimin ki shiryani tsaf…”

“Hoohhh sawwam ya isa” tafada cikin jin kunya,

“Au bazaki ringa yimin wankan ba idan munyi aure?”

“Zanyi maka, shikenan?”

“Ba shikenan ba” yabata amsa,

“To koma dai me kakeso zanyi maka idan lokacin yayi”

Murmushi yayi yashafa sumarshi,

“Lokacin fa yakusa, wallahi ina gama service ko ban fara aiki ba aure zamuyi, kinga yanzu nanda next year munyi aure may be ma kina da ciki….”

Kit ta kashe wayar tana dariya, “sawwam rashin kunya,duk maganar da taxi bakinka fada min kake” tafada acikin zuciyarta,

Tashi tayi tafita tsakar gida domin karasa aikin data fara, mama tagani zaune tana yi,

“Mama da kanki?”

“Ehh mana tunda ke kin tafi waya, wannan saurayi naki komai zaiyi sai yafada miki ne? Allah ya kaimu lokacin da zamu aurar daku mu huta kuje can gidanku ku karata”

“Haba mama nida bana so narabu dake”

“Tashi kibani wuri ja’ira”

Mikewa ummulkhairi tayi tana dariya ta fada kitchen, satinta biyu tadawo makaranta, lokacin su sawwam har sun fara exam sunyi rabi ma saura kiris su kammala,

Kasa banbance yanayin da take ciki tayi domin wani bangare na zuciyarta yana murna saboda kammala karatun da sawwam zaiyi domin tasan yana gamawa za afara maganar bikinsu dan haka baza ajima ba za adaura musu aure suje sawwam yabata daddadar rayuwar da kullum yake fada mata zai bata, yayinda wani sashe na zuciyarta yake bakin cikin rabuwar da zasuyi da sawwam musamman ma idan aka turashi service gari mai nisa, kullum cikin wannan tunanin take,

Tana tsaye ta rungume hannuwanta a kirjinta shikuma sawwam yana jingine ajikin motarsa shima yayi yanda tayi, ita kanta tsaiwar tasu yanda sukayi abin burgewa ce domin duk wanda ya wuce sai ya kallesu,

“Sawwam bana son katafi nesa a service dinka..”

“Saboda baki yarda daniba? Tsoron me kikeji? Uhm”

Murmushi tayi “ba rashin yarda bane nidai bana son kayi nisane”

“Ki fadi gaskiyarki dai, kina tsoron kar naje kudu nazama dan bariki ko” yafada yana dariya,

“Ni bahaka bane”

“Hakane mana, ai nasan abinda kike jin tsoro kenan”

Matsawa yayi kusa da ita kamar wanda zai rungumeta,

“Ki kwantar da hankalinki sawwam nakine ke kadai babu da wacce zaku rabashi.. Ke kadai zaki mallaki kayanki kiyi yadda kike so dashi”.
aishaummi.blogspot.com

Ummi Shatu🏻

Pherty Xarah

*RAMUWAR GAYYA……. 💘*

_Love story 50,50_

    *Fertymerh Xarah*

              &

    *Ummy Aysher*

     36

   Murmushi tayi tana kallonsa har cikin xuciyarta taji daďi,

Shima murmushin yayi yana kallonta,

‘xan tafi na barki da faruq, I know xaku kasance tare, ta bata fuska harda harararsa,

‘saboda Baka yarda dani bane kome, I told you ba komai tsakanina dashi idan ma da akwai a gurinshi to ni kaine xabina Kai nakeso,

‘I trust you nasan you can’t cheat on me, bama faruq kaďai ba Duk Wanda kika tsaya dashi I will know,
tayi far da ido tana kallonsa,

‘taya xaka sani, Suhaib, Hafiz and Abdul ma duk xaku tafi to Waye xai gayama,

Ya tabe bakinsa,
‘baxaki san kowaye ba amma ki gwada kigani, ko kin ďauka suka ďai ne frnds ďina, I have many, a class ďin ku ma akwai,

Itama tabe bakin kawai tayi,
tace nima duk ka tsaya da wata budurwa xn sani Kuma xa’a gayamin,

Dariya yayi sosai yana kallonta,
‘Waye xai gayamiki, wa kika sani, su Abdul ne Kuma ba guri ďaya xamu je ba idan ma an hadamu ai baxasu gayamiki ba,
Ta tunxuro bakinta,

‘shikenan Allah yana ganinka,ya mintsini bakinta,

‘Allah baxai kamani da laifin komai ba cos baxanci amanarki ba, I so much love you dear,
tayi murmushi tana kallon wani gu,

‘kinga baxan iya haqura har kigama Skul kafin muyi aure ba dana dawo xa’a fara mgnr aure, kin qarasa a gidana,

‘ban yarda ba, Nima sai nagama karatuna kamar yanda kagama,

‘Wasa kike yarinya, kibari kigani……
Posting ďin su ya fito, sawwam a Lagos shida Suhaib, Hafiz Kuma a Niger, sai Abdul dake kusa yana kaduna,

Abdul yaji daďi sosai sai dariya yakewa friends ďinsa, sawwam yaji dama shine aka ajiye a kaduna, yasan da xai bada kuďi xa’a cnxa mishi komai hanyane amma kuma yana son xuwa Lagos ďin,
Ranar da xai tafi kamar kada su rabu, harda hawayenta shima namijin qoqarine kawai yayi, da kyar ya samu ya lallabata ta haqura,

Yaja hancinta yana murmushi,
‘sai kace idan nadawo baxamu tabbata a tare ba, indai nine sai kingaji dani,

ta hararesa da jajjayen idanuwanta haďe da turo bakinta tana kallon wani gu,

‘gayamin me kikeso na siyo maki,
‘komai banaso,
‘harda ni bakyaso? ta gyada kanta tana kallonsa,
‘shikenan ma baxan dawo ba xn sami wata inyamura acan na aura… ta kaimasa duka ya goce yana dariya….. da dabaru yasamu ya rabu da Ita sukayi Sallama yabar garin cike da kewar sahibarsa haka ma ita ďin…..

Tunda ya tafi kullum suna waya dare da rana, watansa uku yaxo garin Kuma tunda ya koma bai sake dawowa ba, they are missing each other.
*

Kwana asarar mai rai, Alhamdulillah sawwam ya kammala karatunsa,

Lokacin khairi itama saura shekara ďaya ta kammala nata karatun,

Sawwam yayi wani Haske ya qara kyau kamar bashi ba da alama Lagos ta karbesa sosai har wata qiba yayi,

Sanda ya dawo mami kamar xata haďiye sa dan murna, harda Rukayya ďa mamanta ma taxo tarbarsa, ganin ynda sawwam ya koma hankalin Rukayya ta tashi tunda suka koma gida kuka takewa mamanta akan sawwam, baxata iya auren kowa ba idan ba sawwam ba,

Dole su San abinyi…

Mami Kuwa ta rasa inda xata sanya tilon ďanta, cimma iri iri ta haďa masa amma hankalinsa na gun khairi,

A gurguje ya gama cin abincin yayi wanka ya shirya ya fito,

Mami tace sai Ina haka Wannan Saurin da kake daga dawowarka baxama ka tsaya ingankaba,

‘inda in-law xnje mami kema nasan kina so naje,

Murmushi kawai tayi tana kallonsa har ya fice,

Tun da yagamata yaxo ta kasa nutsuwa a hanxarce ta gama shirinta ta fito, burinta kawai tasanyashi a ido,

Kamar su rungume junansu haka sukaji, sunyi matuqar kewar juna har wani kunyar juna suke domin su kasa mgn sai dai su kalli juna suyi murmushi,

Ta ganshi ya sauya yayi kyau abinsa baida wata damuwa lallai sawwam,

Anashi bangaren Kuma sai yaga duk ta faďa, sai wani Haske da tayi sosai idanunta sun xurma, ya rankwafo dai dai kunnenta,

‘dear ko kin fara bleaching ne? ta ďan dubesa,

‘kafara ko, kaima ai bleaching ďin kake yi,

‘Ni naga kinyi haske kin rame, ramar ta mecece idan nine gani na dawo sai kin cinyeni, ya juyo kacokan yana kallonta sai taga ya mata girma sosai a gabanta,

‘tor ka matsa min,
‘baxan matsa ba, ni naga kamar bakiyi missing ďina ba yanda nayi, tayi murmushi tana kallonsa,

‘Ni Nafi kowa missing ďin ka….

Haka suka cigaba da hirarsu kamar xasu cinye junansu,
Sawwam yayi Mgnr yana so ya tura iyayensa neman aurenta, sai ta Kira gidansu ta gayawa Abbanta,

Abba ya amince suje gun qaninsa Alhaji mukhtar su nemi aurenta cos shi baya gari,
Sunyi murna har sawwam ya qagu aje neman auren,

Shida Dad dinsa, da uncles ďinsa sukaje neman auren a gombe,

Sun sami tarba, karamci da mutunci a gidan Dad yaji daďi sosai domin mutanen sunsan darajar ďan Adam,

Batare da bata lokaci ba suka gabatar da kansu, kuma aka amince an bashi ummulkhairi,

Sunyi murna Kuma sunyi godiya sosai bama kamar sawwam har ya Kira mami ya sanarda ita,

Taji daďi sosai, kuma tayi masa addua,

Basu bar garin ba sai da suka biya Kuďin komai har sadaki ma,

Suna dawowa gida ya kirata,

‘you are mine khairi….
‘Tace da gaske,
‘Allah sun bani ummulkhairi, tayi murmushi batare da tayi mgn ba xuciyarta na bugawa sosai, batasan a wane yanayi take ciki ba farin ciki ko sabanin haka,

‘why silent dear, are you not happy?
‘am happy, is just…. sai Kuma tayi shiru,
‘tell me, Kada ki boyemin komai,
‘bafa komai kawai najini somehow, naji inajin nauyinka and I feel so happy,

Murmushi yayi yana faďin,

‘tun ynxu lallai da sauran rina a gaba, itama dariya tayi,

‘xaka shigo anjima,
‘kina so na shigo ne,
‘yes am missing you,
‘shikenan xn shigo, yayi mata kiss ya tsinke Wayar, sai da taji wani yarrrr,

Ta kwanta a ďakin cikin farin ciki, anbawa sawwam ita, ta Kira Alawiyya tana gayamata cikin farin ciki……

*_PHERTYMERH XARAH_*
37
   *Z*ama ummulkhairi tayi sukuku hankalinta ya dan tashi zuciyarta sai harbawa take yi,
“Oh Allah gani gareka, ya Allah kai kadai kasan abinda kake nufi da haka….” Tafada ahankali sai kuma hawaye ya hau tsiyaya daga idonta, kuka tayi sosai wanda ita kanta bata san ko na menene ba,
Ta dade tana risgar kuka wanda anan take kanta yafara ciwo, dolenta ta nemi wuri ta kwanta sakamakon ciwon da kanta ke yi,
Bacci ne ya samu damar daukarta wanda tajima tana yi daga karshe ta tashi afirgice sakamakon wani mummunan mafarki da tayi da sawwam,
“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un, allahuma inni a’uzubika min sharri fi manami an yadurruni fi dini wa duniyaya…” Tafada atsorace tana dube duben gefenta da kusa da ita,
Wayarta ta dauka takira number din sawwam, akasalance ya daga wayar sakamakon shima barcin yake yi,
“Hello matata…” Yafada cikin muryar bacci,
“Sawwam lafiya kake? Babu abinda ya sameka?” Ta tambayeshi jikinta har rawa yake,
“Lafiyata lau bacci nake yi amma yanzu tunda natashi wanka zanyi nataho wurinki”
“Dagaske babu abinda ya sameka?”
Murmushi yayi “meya farune? Ance miki wani abu ya sameni ne?”
Kai ta girgiza masa kamar yana ganinta,
“A,a kawai dai wani mafarki nayine wanda ya razana ni, nikuma wallahi na tsorata gashi bana son wani abu ya sameka” yanda tayi maganar kamar zata saka kuka,
“Ashe kina sona da yawa haka, wohhhh ashe nima dan gatane ana sona sosai ba ason wani abu ya sameni”
“Kayi hakuri na katse maka baccinka, am sorry”
“Babu komai my lonely, naji dadi ai da naji muryarki awannan time din”
“To sai ka shigo”
Murmushi yayi yafara kokarin tashi, “kiyi min kwalliya fa”
Bata bashi amsa ba ta katse wayar tana zazzare idanu domin tayi mutukar tsorata da mafarkin da tayi, fatanta dai guda dayane na Allah yasa ba wani abu neba yake shirin samun sawwam.
   Daurewa tayi ta cire damuwar dake ranta tayi wanka ta shirya tayi kwalliya, riga da skirt tasaka na atamfa ta saka farin hijab ta fita Inda sawwam ke tsaye yana jiranta,
“Kinyi kyau” taji yafada lokacin da ta karasa gabansa,
“Kaima haka”
“Nidin kyau nayi?” Ya tambayeta cikin tsokana,
Murmushi tayi ta matsa jikin motarshi ta jingina,
“Yau ina cike da farin ciki saboda yanzu nasan kin kusa zama mallaki na”
Kallonsa tayi tana jin faduwar gaba atare da ita “wai kai da kafara neman aure baka fara aikiba waye zai rinka ciyar damu?”
Dariya yayi yana kallonta, “Allah ne zai ciyar damu amma ta silar dad, ke nifa wallahi idan nakara wata biyar nan gaba ba ayi min aure ba to sai an kwantar dani agadon asibiti…”
“Allah yabaka lafiya, kana nufin kenan yanzu nan da wata nawane bikin?”
Kallonta yayi ya harde hannuwansa a kirjinsa duka,
“Ai samun lafiyata kawai a aura min ke wallahi, biki kuma nan da wata biyu insha Allah zaki zama amarya”
Murmushi tasaki tajuya ta fuskanceshi,
“Sannu fa, nan da wata biyu fa kace? sai kace wani a film aure nanda wata biyu?”
Dariya yayi sannan yabata amsa, “to shikenan ki zauna kigani, wallahi bikinmu bazai wuce hakafa kuma zakice nafada miki, sannan da kike wani zancen kamar a film to ba a film zaki ganiba afili zaki gani filin ma kuma akanki”
Kallonsa kawai take tana yin murmushi amma bata gasgata shi ba saboda atunaninta koda za ayi bikin to kila sai kamar nanda wata biyar ko shida domin yanzu suna dab da shiga level 4,
“Ke kinfi sone ayi bikin bayan kin gama karatu?”
Kai tadaga masa, “ehh wlh”
“Tab ai kuwa hakan bazai yiyuba garama ki ware” yafada yana tabe baki,
“Shikenan Allah ya tabbatar da alkairi” tafada cikin sigar kalar tausayi,
“Amin, da tun farko ma hakan kika fada da yafi miki”
Zuba masa ido tayi kawai tana kallonsa ko kiftawa batayi, ba karamin sake haduwa yayi ba, yayi kyau sosai fiyeda lokacin da yana dalibi,
Matsawa yayi kusa da ita yana kallon fuskarta,
“Gaskiya wannan ramar da kikayi ki mayar da ita kafin lokacin aurenmu”
Murmushi kawai tayi batace dashi komai ba domin ita dai tun lokacin dataji angama maganar aurensu sai ta nemi nutsuwarta ta rasa gashi duk jikinta yayi sanyi hankalinta ya tashi,
“Wai ke duk fargabar auren ce haka?” Yace da ita yana dariya,
“Hmmm dama ai kai dariya zakayi nasani”
“Wallahi kamar kin sani kuwa, kina kuka ranar nikuma ina dariya…”
“Wallahi dan baka san yanda nakeji bane, zuciyata har wani harbawa take yanda kasan gobe ne auren”
Dariya yasaka yana kallonta, haka yasata agaba yanata yi mata dariya, sun dade suna hirarsu sannan yayi mata sallama yatafi,tunda yatafi kuma kullum yana hanyar zuwa wurinta koda yaushe suna tare gashi takusa fara exam.
Gidansu sawwam kam dagaske shirin aure suke yi sosai domin mami harta fara hada lefen sawwam, kaya kam masu mutukar tsada ta siyo, kullum cikin yin waya take tana bada sautin kaya asiyo mata daga dubai, kasancewar bata san abinda hajiya raliya mahaifiyar rukayya tayi mata ba yasa take bata sautin kayan kusanma fin rabin kayan hajiya raliyan ce ta sissiyo,
  Tashinsa daga bacci kenan bayan yagama waya da ummulkhairi ya nufi part din mami,samunta yayi acikin bedroom dinta tana dudduba wasu kaya wanda zata saka acikin lefen, zama yayi akan gadon mami yana kallon kayan,
“Mami wai har yanzu ba agama hada kayan bane?”
“Ankusa agama ai, nanda sati biyu masu zuwa zamu kaimusu asaka maka date din biki”
“To mami Allah ya kaimu”
“Yawwa amma fa ba asaka inner wears ba, menene size dinta?”
Sosa keya yayi sannan ya kalli mami,
“Mami wallahi ni ban saniba amma tunda yanzu zanje wurinta sai na tambayeta”
“To shikenan amma karfa ka manta saboda nafi so komai ya zama ready”
“To mami, barima natashi naje”
Mikewa yayi da niyyar fita sai kuma yaga dad dinshi ya shigo cikin dakin cikin shirinsa na zuwa office,
“Dan gidan dady ka shirya fa ranar Monday zaka fara fita aiki domin har an fitar da offer dinka”
Cikeda farin ciki sawwam ya isa gaban dad ya rungumeshi,
“Thank you dad, thank you dad, thank you…”
Murna mami tafara yi tana addu’ar Allah ya sanya alkairi, zuciyarta jinta take tayi mata sanyi domin ganin danta datafi so tafi kauna yakusa zama cikakken mutum ga aiki ga aure,
“To duk da nidai ba asaka ni acikin maganar ba amma zanyi magana, naga wariyar launi ake nuna min, awanne ministry zai fara zuwa aikin?”
Mami tafada cikeda zolaya,
“Ba wariya bace maganar ce iya dan gidan dady dani ta Shafa, a code of conduct bureau ne kin san abinda ya karanta bangaren statistics ne dan haka dole sai a irin wadannan wuraren zaiyi aiki, suna da headquarter a abuja amma nace shi abarshi anan kusa dake..”
Murmushi mami tayi cikin barkwanci tace, “to ai nima nakusa sallama dashi tunda ya kusa aure kaga shikenan”
Sum sum sawwam yasa kai yafice daga dakin ya nufi nashi, wanka yayi yana wankan yana tunanin irin zaman da iyayensa suke yi wanda tun tasowarshi bai taba ganin suna kace nace da junaba idanma suna yi to basu taba yi agaban idonsa ba,kullum cikin barkwanci suke gashi sai kace wasu kakanninsa wannan ya tsokaneshi tacan wannan ya tsokaneshi tacan fata yake aransa shima Allah yasa irin wannan zaman zasuyi da lonely dinshi.
  Shiryawa yayi sosai cikin kananan kaya gashi ba karamin kyau suka yi masa ba,
Makarantar su ummulkhairi ya nufa, fitowarta kenan daga lecture sai gashi aguje tagabanta kamar zai kadeta, cikin razani ta kankame alawiyya, burki yataka yana dariya ya koma baya, bude idonta tayi tana kallonsa,
“Alawiyya kinji yanda na tsorata, tab lallai sawwam wallahi zaka sani bari nazo”
Dariya alawiyya tasa ta juya tafara tafiya tana cewa “kunfi kusa nidai kinga nayi nan sai gobe idan kuma nasamu nashigo karatu da yamma shikenan”
Wurin sawwam ta nufa yana cikin mota yana waya dasu Abdul yana fada musu cewar yasamu aiki yanzu ma haka ranar monday zai fara fita office, nan Abdul yake fada masa shima yaje yayi interview awani ministry suma su suhaib duk sun halarci interview din”
Murmushi sawwam yayi ya daki sitiyarin motarshi,
“Hohhhhh! Lucky guys, kace mun kusa fara amsar salary…..”
Ganin ummulkhairi tsaye tana jiransa yasashi yiwa Abdul sallama ya kashe wayar ya fita wurinta,
“Meye naga kinbi kin wani bata rai”
Harararsa tayi ta juyar da kanta, “to meyasa zaka wani zo ka tsoratani daka kadeni fa?”
Murmushi yayi yana kallonta, “koda ace na kadeki ai ba fasa aurenki zanyi ba, ke matsoraciya ce wallahi”
“Nayarda” tafada har lokacin bata kalleshi ba,
“To nidai ba fada nazo ba yau, mami ce ta aikoni in tambayeki size dinki,nasan na takalmi dai 38 ne shi harma an sissiyo, yanzu na inner wears nake so”
Shiru tayi takasa magana domin kunyar fada masa take, dakyar ta bude bakinta,
“36”
“36 fa? Tab” yace da ita yana dariya,
“Sai kayi kuma” tafada tana harararshi,
“Kin san me? Kinata cewa wai idan munyi aure waye zai ciyar damu to nasamu aiki ranar monday ma zan fara fita office”
Juyowa tayi gaba daya ma tamanta da cewar tana jin kunyarshi, tsalle tayi ta rungumeshi, tana fadin,
“Congratulations dear…..”
Sai kuma tayi saurin sakinshi ta rufe fuskarta,
“Au, wallahi duk tsananin murna ce”
Dariya yayi ya kalleta,
“Bawani murna kedai kawai kinyi missing dina kina so kiji farin ciki”
Dariyar itama tayi, “koma me zakace dai nayarda, nidai yau ina cike da farin ciki”
Hira sukayi mai cike da kaunar juna lokacin, sai bayan isha sannan yatafi,
Ranar monday yafara fita aiki, duk kuma sai ummulkhair taji babu dadi saboda rashin ganinshi wuni guda domin da dane da tare zasu wuni duk kuwa da cewar suna yi suna fada amma dole haka zasu zauna tare,
Shima a bangaren sawwam din yayi missing dinta sosai dan haka yana tashi daga office wurinta ya wuce,
Lokacin da tafito ganinshi tayi agajiye yana tsaye yasha farar shadda riga da wando ita sai abinma yabata dariya domin duk yayi mata kalar tausayi, baifi minti goma ba yatafi gida, tun daga lokacin haduwar tasu tazama sai dare sai ko a weekend domin kullum yana office,
Salary dinshi nafarko gida uku ya raba yabawa maminshi kashi daya ya dauki daya sannan ya kai daya kason cikin daya account dinshi yafara tarawa  ummulkhair, duk da haka sai da ya cira acikin kudinsa ya siyo mata turaruka da kayan kwalliya.
38
  Lokaci babu wuya har su ummulkhair sun kammala exam dinsu, ranar da suka gama ranar ta tafi gida dayake jarabawar safe sukayi, kwananta biyu da tafiya aka kawo lefenta aka yanke date din biki karshen wata mai zuwa, murna awurin yan gidansu ba a magana, sawwam kuma yafi kowa farin ciki ganin ansaka masa ranar kamar yadda ya nema, ita dai ummulkhair tana cikin wani hali gaba daya jinta take sukuku gashi tanata jin tausayinsu ita da sawwam,
Satinta biyu agida sai gashi ya jemata,da murna ta tareshi tana fara’a,
“Kai yarinyar nan kiba zakiyi, ji fa tun yanzu har kinyi kumatu daga dawowa”
Murmushi tayi ta zauna bayan ta gabatar masa da kayan motsa baki wadanda ta tanadar masa,
“Kin fara zama yar lukuta wallahi idan kikayi nauyi dayawa bazan rinka daukarki ba…”
“Kai sawwam dan Allah” tafada cikin jin kunya, kwaikwayon maganarta shima yayi yace,
“Kai khairi dan Allah” dariya suka saka daga shi har ita.
Hira sukayi sosai lokacin da yatashi tafiya yajata motarshi ya dauko mata wata katuwar leda,
“Mami tace akawo miki wannan”
Karba tayi tana leka cikin ledar tana dubawa taga kayane kayan gyara irin na amare, “lallai mami tana son danta” tafada acikin zuciyarta,
Hannunta taji ya dan buga, “wai kayan menene? Nifa mami nagane yanzu tafi sonki akaina”
Murmushi tayi, “wallahi mami tana sonka kaima”
Gyada kai yayi “naji wannan, fita zan tafi”
“Haba sawwam meye abin fushi? Harda korata…”
“Na koreki din”
Murmushi tayi ta kalleshi “nima fa ban san menene ba sai naje ciki zan duba”
“Tace ai akwai takarda anrubuta komai ajiki, mantawa ma nayi da ban dauka na karanta ba”
Hannu ya mika zai kwace ledar tayi saurin kankameta ajikinta, yanaja tana ja, ganin ledar zata yage yasashi sakar mata ya tabe bakinshi,
“Idan tayi tsami zamuji”
Dariya tayi aranta tana cewa “mami ai kai take yiwa gata”
Amma afili sai tace masa “bama zatayi ba”
Sallama yayi mata suka rabu cikeda kaunar juna, lokacin dataje gida ta nunawa mama kayan ba karamin mamaki mama tayiba saboda ganin irin soyayyar da maman sawwam ke yiwa ummulkhair,
Nan itama mama tadage wurin gyara yarta, amma kullum ita ummulkhair cikin kuka take shikuma sawwam sai zumudi yake domin bikin yazo, shida abokansa koda yaushe cikin shirin bikin suke,
Itama ummulkhair ita da kawayenta sai tsare tsaren yanda bikin zai kasance suke,
Sawwam kullum cikin yimata waya yake yana zolayarta gashi tsabar zumudi kullum agidansu wanda zasu zauna da ita yake kwana,
Yauma yana gidan akwance shi kadai ya kirata yana tsokanarta,
“Wai kana inane?” Ta tambayeshi,
“Ina gidanki, a dakinki”
“Gidana kuma? Saboda kaine gandoki”
Murmushi yayi, “wallahi dagaske fa ina cikin dakinki, acan zan kwana”
Katse wayar tayi tana cewa “ohh sawwam zumudinka yayi yawa”
Wayarta ta latsa ta kira alawiyya tafada mata biki yakusa saura sati biyu, sai dai alawiyyan bazata samu damar zuwaba domin itama sunada bikin cousin dinta amma tayi musu addu’ar samun zaman lafiya.
Angama dukkan shirye shirye ranar alhamis za ayi kamu, aranar aka yiwa ummulkhair kunshi na jan lalle da baki kuma aka yimata gyaran gashi nan tafito a amarya sak tayi kyau sosai,
Misalin karfe biyar akayi kamun awani hall dake harabar hotel din nishadi hotel babu karya kamun ya kayatu kuma ya hadu sosai, aranar shima sawwam suka taho dasu Abdul duk cikinsu shi kadai ne zaiyi aure domin su koma shiri basu fara yiba,dan haka sai tsokanarshi suke suna cewa zai rigasu tsufa,
Karfe 6 aka gama kamun suka koma gida lokacin suma su sawwam sun sauka suna hotel suna hutawa,wayarta yakira sai daf da zata katse sannan ta dauka gabanta yanata faduwa,
“Sawwam..”
“Kun dawo daga wurin kamun?”
“Ehhh” tafada a takaice domin ita yanzu sam bata son ganinshi bata son jin muryarshi asalima tsoronshi taji tanaji,
“Bakya nemana ne?
Yasake tambayarta”
“Uhm” tabashi amsa,
“Kikace uhm? Dagaske bakya nemana? Nito ina nemanki kuma zanzo yanzu”
“To” tace dashi tareda katse wayar tana turo baki tamkar yana ganinta.
Karfe takwas suka je gidansu kairin, ko ina yan uwane duk sun tattaru sun cika gidan, dakyar ta samu ta fita ko kayan da tasaka taje wurin kamu bata cireba, mayafi kawai tayafa ta fita,
Suna cikin mota shida abdul ta tsaya daga waje suka gaisa, kallonta kawai sawwam yake yi ganin yanda tayi kyau tasha kwalliya a fuskarta ga kunshi yazanu radau ahannunta da kafarta,
Gaisawa sukayi da abdul yanata tsokanarta, kallon sawwam tayi,
“Kaina ciwo yake bari nakoma ciki”
“To kafin ki tafi kiyi kissing dina”
“A’a wallahi….”
Hannunta ya riko yajata da karfi kawai sai jinta tayi tafada kan jikinsa, kunyace duk ta kamata ganin abdul yana wurin, shikuwa Abdul naganin haka yafita daga cikin motar yabasu wuri,
Rungumeta sawwam yayi yana kallon fuskarta
“Da haka zaki barni natafi babu kiss babu hugging?”
“Dan Allah kayi hakuri”
“Kiss me…” Yace da ita yana sake matseta ajikinsa,
“Kayi hakuri”
“Ok bakya son kije ki huta din kenan”
Dagowa tayi da niyyar yi masa magana taji lips dinshi kan nata……..
Ummi Shatu👌🏻
Pherty Xarah💞
*RAMUWAR GAYYA…… 💘*
_Love story 50,50_
*Fertymerh Xarah*
          &
*Ummy Aysher*
39
    Da sauri ta turesa, ta matsa baya haďe da tunxuro bakinta yayi dariya yana kallonta qasa qasa,
A fakaice ta juya tana kallon Abdul sai taga kwata kwata hankalinsa baya gunsu, ta maida kallonta ga sawwam,
‘tor sai anjima,
‘korata ma kike yi, lallai ma yarinyar nan, to jibi sai kihanani abinda naso ko ki korani daga gidan,
Ta juya tana murmushi tayi hanyar gida shima murmushin yayi yana kallonta,
‘bako sallama ,ta juyo tana kallonsa,
‘gobe da wuri xaka shigo ko, banaso ka bata lokaci,
‘baxan ma bata ba dear, Inaso dinner ta qayatar…
‘Allah yasa,
‘yace Amin, sukayi Sallama da juna.
Washe garin Ranar ta Kama dinner, 
Amarya khairi tayi matuqar kyau sai kyalli take tamkar wata sarauniya, kalar fatar jikinta Mai kyau da sheqi, tayi kyau sosai cikin wata gown doguwa pink, an yane kanta da wani qaramin net shima , komai in pink daga cikinta hr waje, tayi matuqar kyau sosai,
Yayin da ango ke sanye cikin wani lallausan yadi Mai shara shara fari sol, yayi matuqar kyau sosai
Kallo ďaya xakayi wa sawwam ka sake marmarin kallonsa saboda haske da kwarjininsa ya dushe hasken Duk wani matashi Mai ji da kansa dake harabar hotel ďin,
Su Abdul ma ba’a barsu baya ba, cikin nasu anko sai waige waige suke Acikin abokan amarya ko xa’a dace….
Dinner tayi kyau ta qayatu anci ansha anyi raye raye harda amarya da ango,
Sanda aka tashi dinner ango yaja amaryarsa motarsa da kansa ya kawota gida, yana xaune a motarsa har ta shige gida kana yabar gurin, yana son khairi sosai ya qagu safiya tayi ta xama mallakinsa.
Daren ranar sun jima a waya, sun sha soyayya sosai baxasu manta wannan ranar a tarihin rayuwarsu ba domin sun amayarda irin qaunar da suke wa junansu,
Washe gari ta kama asabar ranar ďaurin aure,
Acan gidan alhaji mukhtar xa’a ďaura auren, shiyasa suka dunguma acan,
Ango yasha manyan kaya cikin farar shadda harda babbar riga da hula, anko sukayi da Dad,
Mami ta dube su da murmushi,
‘kunyi kyau, Allah ya kaiku lfy ya dawo daku lfy, suka amsa da Amin, sawwam ya sumbaceta yana faďin,
‘khairi will be part of us mami K……
‘karka tsaya gurin surutu lokaci na tafiya ga dad ďin ka harya fice,ya fita da sauri yana dariya,
Sun iso gombe kai tsaye gidan baba mukhtar suka nufa, yayi ta kiran wayar khairi tana ringing bata ďauka ba, xai sanarda ita xuwansu ne, daga qarshe ma sai yaji wayar switch off,
Bai kawo komai a ransa ba yacigaba da amsar wayar friends ďinsa masu taya sa murna, yana tare da dad yan uwansa suka fara isowa,
Suma su Abdul tuni sun iso da tasu gayyar, yauma anko suka sha abokan 3 pointers,
Wuri ya taru, jama’a sai son barka, mutane kamar da bakin kwarya sun hallaro bikin sawwam da khairi, kowa na gurin bnda mahaifin amarya, sai suka tsaya jiran isowarsa,
Mutane sun soma damuwa ďaurin aure nason xama lalura Abinda ya kamata ayi tun ďaxu Gashi kusan awa ďaya da xuwa baa daura auren ba kuma har lokacin Abba bai xo ba,
Kowa gurin ya damu bama kamar sawwam, hankalinsa ya soma tashi Allah yasa lfy Gashi ya Kira Wayar har lokacin switch off.
*
Khairi xaune hannuwanta da suka sha qunshin baqin lalle da surkin ja akan fuskarta,
Kuka take sosai gwani tausayi, kuka take Kamar ranta xai fice daga jikinta, a halin da take ynxu gwanda mutuwarta  da rayuwarta dan baxata iya rayuwa batare da sawwam ba,
Mama ma cikin damuwa da halin da yar’ta take ciki ta dubi Abba,
‘wannan hukunci Sam baiyi ba alhaji, bai kamata ka hukuntar da ummu ta wannan sigar ba, amma meyasa baxaka haqura kabarsu ba tunda suna son junansu,
‘saboda *Ramuwar gayya* nayi wannan so bnga dalilin ki na sanyo bakinki acikiba, kinfi kowa sanin meke faruwa Kuma kinfi kowa sanin dalilina nayin haka,
‘ummulkhairi baxata auri sawwam ba, faruq xata aura kuma dole xata min biyayya ynxu xnje can a gudanar da komai,
Jin kalaman sa ya Sanya khairi fashewa da wani irin kuka, idanunta sunyi jawur sosai ta dawo gabansa ta tsugunna haďe da riqe qafafuwansa,
‘Dan girman Allah Abba kayi haquri ka tausayawa rayuwata, na kasance mai biyayya agareka Abba, na cika ma burinka nayima biyayya kabarni da Wanda nake so, shi kaďai nake so Abba baxan iya rayuwa da wani namiji idan ba sawwam ba, bana son faruq Abba ka tausayamin,
Ya janye qafarsa a hankali yana kallonta,
‘Kinsan ina son ki ummulkhairi, kinsan baxanyi Abinda xai cutar dake a rayuwarki ba, kin kasance mai biyayya agareni shiyasa xn xaba maki miji dai dai rayuwarki, faruq shi kaďai xai iya riqeki amana yana son ki khairi kema ki koyi sonsa domin shine uban Ya’yan ki,
‘Abba sawwam ma yana sona xai iya riqeni amana, wlhy baxai cutar dani ba, maminsa ma tana qaunata Abba, karka raba soyayyar mu Abba, ka cika min burina na kasancewa da sawwam kamar yanda na cika maka naka burin,
‘idan na kasance mai laifi a gareki ummulkhairi to Kiyi haquri amma baxaki auri sawwam ba yasa kai ya fice da sauri, ta durqushe gurin tana kuka Kamar ranta, mama ma tausayinta take,
Mutane sun soma gajiya wasu har sun fara qorafi da yawa suna da abinyi gurin, wasu Kuma nesa suke, wasu Kuma suna da wani ďaurin auren shiyasa suka qagu, barin ma kamar dad daxai bar qasar gabaki ďaya ya dubi baba mukhtar,
‘Alhaji ai gurinka Muka xo neman aure Kuma kai kabamu yarinya, kaine waliyinta kai Yakamata ka ďaura mata aure tunda mahaifinta baya kusa kowa nan gurin ya qagu wani ba’a San uxurinsa ba,
‘hakane, tor bara a ďaura……
Nan take aka daura auren sawwam da khairi, dai dai lokacin Abba ya iso gurin, da sauri ya fito cikin motar ya soma kutsawa cikin dimbin mutanen dake gurin,
Suna haďa ido da alhaji mukhtar abinda ya tambaya,
‘Kada dai an ďaura auren ne? Sawwam kaďai ya lura da xuwansa dad nacan na gaisawa da mutanen sai dai yanayin da ya ganshi ya tabbatar masa ba lfy,+
‘eh an ďaura yaya saboda mutane sun gaji da…. ya katsesa a fusace Wanda ya janyo hankalin jama’a harda dad xuwa garesa,
‘amma meyasa xakamin haka, nikeda haqqin auradda ita, dole ya sakarmin yarinya ynxu,
Xuciyar sawwam ta buga ya xare ido yana kallonsa kome ya faru yayinda gurin yayi tsit,
‘dad ya dubi sawwam,
‘Kada dai wannan ne mahaifiyar yarinyar da kake aure sawwam? Jikin sawwam ya ďauki rawa yana kallonsa ya gyada kansa,
‘baxai yiwu ba, ai tun farko danasan shine mahaifinta baxaka neme ta ba, wannan auren Kuwa xa’a warwareshi ynxu,
Sawwam ya tashi tsaye idanunsa sun sauya Kala,
‘why dad? wai meke faruwa ne?
‘you must divorce her sawwam,
‘I can’t dad, Ina sonta and you know it…… Bai qarasaba ya ďauke sa da Mari,
Mutane suka shiga ruďani abin ya ďaure masu kai, su Abdul suka matso jikinsu a sanyaye suka riqe sawwam dake dafe da kuncinsa yana kallon yanda faďa ya qaure tsakanin mahaifinsa da mahaifinta, miye tsakaninsu Ina suka San juna?
Sabon al’amari ne Wannan ga dimbin mutanen dana xo ďaurin aure gurin, musamman ganin mahaifin ango da mahaifin amarya suna faďa Kamar xasu cinye junansu,
Sawwam ya fita gefe ya Kira mami yana sanarda ita, kuka yake sosai yana roqonta ta taimaka masa baxai iya rabuwa da khairi ba…….
Sosai hankalinta ya tashi to meke faruwa meya janyo fitinar, ta tsinke Wayar da sauri dan baxata jure jin kukan sawwam ba, ta soma qoqarin nema layin dad da jin meke faruwa,
Yana ganin kiranta baxai iya ďaga wayar ba kasancewar hankalinsa baya jikinsa, kallo ďaya xaka yiwa Iyayen biyu ka gane suna cikin bacin rai sosai na tsawon wasu shekaru da suka shuďe a baya,
Manyansu tsofaffi suka sanya baki,
‘yace lallai sai an sakar masa yarinya,
‘dole ma xai sake ta saboda muma bamu buqata,
‘ya saketa ynxu xa’a ďaura mata aure da Wanda ya dace faruq,
Dad ya dubi sawwam,
‘ka saketa ynxu xn ďaura ma aure da wacce ta dace Rukayya,
Hankalin sawwam ya tashi Cak numfashinsa na ďauke ya xube gurin a sume….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page