ITACE QADDARATA CHAPTER 8

ITACE QADDARATA CHAPTER 8

  “Khairat tai k’arfin halin cewa ba kuka ya kamata mu cigaba da yi ba,we should find a way out,a kira likita yazo ya dubashi maybe Suma ce yayi Hajiya tace wane suma,kina ganinshi cikin jini,ya riga ya kashe mun shi,Imran baka kyauta mun ba,laifin me ya maka ka kashe shi? ta sake fashewa da matsanancin kuka” “Batare da khairat ta sake cewa komai ba,ta fita taje sashen hajiya ta d’auki waya ta kira family doctor In few minutes time yazo,khairat taja shi xuwa sashen su Imran,Dr.Moha(DANGIN MAHAIFINA) shi kanshi ya tsorata da ganin halin da Yazeed yake ciki Ya d’an dafe kanshi yace Ya salam! Wa ya mishi wannan aikin ko yan fashi ne suka shigo gidan naku? Hajiya na sharar hawaye tace Imran Subhanallahi! Garin yaya Imran ya mishi haka,yana cikin hankalinshi kuwa ko ya fara shaye-shaye anyway ba lokacin tambaya bane,yanzu muyi k’ok’arin ceto ranshi,bari na kira a kawo ambulance a tafi dashi asibiti dan bazan iya treating d’inshi nan ba” “Ba b’ata lokaci,Ambulance tazo tare da wasu nurses,aka d’aukeshi,Hajiya,khairat,ihsan da iman suka shiga wata mota direba yaja su,Noor taso xuwa Hajiya tace bazata ba,waya sani ma ko itace silar dukan da Imran yama Yazeed,kuma ta sani idan ta gano itace sila toh wlh ta kuka da kanta,Furucin Hajiya ba k’aramin tada hankalin Noor yayi ba amma sai tayi tunanin Yazeed ko ya farfad’o bazai fad’a ba dan yasan bashi da gaskiya,Imran ma tasan bazai fad’a ba dan abun kunya ne” “Jiki a sanyaye,tana sharar k’walla,Fuskarta tayi jajir tsabar kuka abunka da farin mutum Ta koma sashen su Imran Ta murd’a k’ofar d’akinshi taji a rufe Tayi knocking taji shiru,Murya sanyaye can k’asan mak’oshi tace Imran dan Allah ka bud’e Noor ki tafi kawai bana son magana da kowa Dan Allah Imran ka bud’e ta fad’a cikin muryar kuka Jin muryarta kamar ta mai kuka yasa ya taso ya bud’e,ya koma ya zauna Ta shigo d’akin,ta zauna nesa dashi kanta sunkuye k’asa tace Imran me yasa zaka yi haka? Yai saurin dakatar da ita da hannu Tsaya idan maganar da kika zo yimun kenan tashi ki fita Ta marairaice murya tace Haba! Imran kai da na sanka da hak’uri,tausayi da sanyin hali but kana so kayi proving d’ina wrong Yai shiru bai ce mata komai ba Ta cigaba da cewa Imran,nasan abunda Yazeed yayi bai kyauta ba,he deserve to be punish but ka d’auki hukunci mai tsanani a kanshi,yanzu bamu da tabbacin ko zai rayu ko bazai rayu ba,idan ya rasa ranshi kai za’a ce ka kashe d’an uwanka,wanda hakan zai sa kai ta nadama har k’arshen rayuwarka A fusace yace ko kad’an bazan yi nadama ba,nafi so ya mutu akan inga abunda yayi niyyar aikata miki Kar kace haka Imran ,ka sassauta zuciyarka Dan Allah,Allah na son masu had’iye fushin su,kuma kar ka manta hadisin Manzo SAW da yake cewa La tagdab ma’ana kada kuyi fushi,Yazeed d’an uwanka ne jininka,hannunka baya rub’ewa ka cire ka yar,nasiha ya kamata ka mishi ka lurar dashi,ba ka mai mummunan rauni ba har ka kusa kashe shi,dukanshi da kayi bashi zaisa ya shiryu ba,watak’ila da ka zaunar dashi ka mishi nasiha yafi saurare,Duk kafircin fir’auna,Allah cewa Annabi Musa(AS) yayi: Yayi amfani da harshe mai sanyi wajen yi masa wa’azi,kaga kenan duka ko zagi bashi zai sa mutum ya shiryu ba,tattausan lafazi nasa zuciyar mutum ta karaya yayi nadamar abunda yayi Gaba d’aya jikin Imran yayi sanyi,duk wata zuciya da yake ji ta tafi,yaji ya k’ara son Noor matsayinta ya k’aru a zuciyarshi,Yayi nadamar dukan da yama Yazeed ba don komai ba,sai dan nasihar da Noor ta mishi,Amma bai daina jin haushin Yazeed ba( _idan ya tuna yadda ya ganshi akan noor_) A hankali ya furta nagode da shawararki Noor,Allah ya saka miki da alkhairi Tayi murmushi tace Ameen,ba komai yanxu sai ka shirya kaje asibiti Ya girgiza kai yace No i can’t do that Dan Allah Imran kaje Naji zanje And please one last favour Am listening Dan Allah kar ka gayawa su Hajiya abunda Yazeed yayi Da mamaki yake kallonta yace Why? Dole su sani,Hajiya ta daina ganin laifina akan hukuncin dana d’auka a kanshi,idan kuma suka sani zai ji kunya,yayi nadamar abunda ya aikata Noor tayi murmushin tak’aici tace ba’a san musulmi da tona ma d’an uwanshi musulmi asiri ba da yad’a laifinsa,ballatana Yazeed jininka ne idan ka rufa mai asiri kamar ka rufa ma kanka asiri ne,sannan idan ka rufa ma wani asiri kai ma Allah zai rufa ma,bai kamata ka fad’a musu ba,Ka mishi nasiha ka lurar dashi a matsayinka na babba Imran shiru kawai yayi yana kallon Noor gaba d’aya ta tafi da imaninshi ya kasa furta ko A,a ranshi yace ban tab’a sanin Noor na da kaifin tunani,ilimi da hankali sai yau,a gaskiya duk mijin da ya sameki a matsayin matar aure ya godewa Allah,Daddy bai dace dake ba,had’aki da Daddy da akayi an cuceki,banda aure ya haramta tsakanina dake da na aureki,na dad’e ina neman mace mai irin halayyarki gashi Allah ya had’ani dake sai dai Kash aure ya haramta tsakaninmu Ya kawar da kanshi gefe cike da takaici Noor tace baka ce komai ba,kamun alk’awari baza ka fad’a ba,zaka barshi sirri tsakananin ni kai Yazeed da Allah Kai kawai ya gyad’a mata ba tare da ya juyo ya kalleta ba Cike da murna tace nagode nagode Ta juya ta fita” …………………………… A asibiti likitoci sun ba Yazeed taimakon gaggawa,nan da aka shiga dashi emergency Hajiya dasu Ihsan sai faman zirga-zirga suke a passage d’in asibitin suna kuka+ Alhaji na can wajen buga caca, Iman ta kira shi ta gaya mai halin da ake ciki,ba shiri ya taso yazo asibitin,bai samu ganin Yazeed ba,amma sai jinjina al’amarin yake,me yama Imran ya mishi dukan da ya kusa kashe shi duk irin shak’uwar su da son juna Yayi ta kiran Imran yak’i picking,kashe wayar ma yayi gaba d’aya,Alhaji ya tsaya kawai yana cizon yatsa Dr.Moha ne ya fito yana zufa,Dukansu sukayi kanshi Hajiya tace”Ya dai doctor ” Dr.Moha ya goge zufan da ya k’eto masa yace “mun samu nasarar ceto rayuwarshi,amma har yanzu bai farfad’o ba sai nan da wasu awanni,sannan yana buk’atar jini da za’a mishi k’ari dan ya zubar da jini da yawa” Hajiya tai saurin cewa”muje a gwada nawa” “Abunda yafi kyau kuzo muje ku dukanku a gwada,wanda yayi dai-dai da nashi sai a d’iba” Dukkansu an gwada jininsu bai yi ba, Hajiya cike da damuwa tace “to yanzu ya za’ayi?” Kafin Dr ya bada amsa,Ihsan tace “Mum kin manta blood group d’insu d’aya da Ya Imran” Alhaji ne yace”tabbas hakane dan haka yi maza kuje ke da driver azo dashi” Tayi nodding kanta,ta juya tayi hanyar fita Tun fitar Noor,Imran na nan inda yake bai motsa ba,tunaninta kawai yake da maganganunta,yana jin wasu feelings game da ita wanda ya kasa gane na meye? A rud’e Ihsan ta shigo d’akin babu ko sallama “Yaya Dan Allah ka taso muje asibiti,a d’ibi jininka a sawa Ya yazeed,jinin kowa ba zaiyi ba sai naka” Banza yayi da ita kamar bai ji ta ba Ta sake maimaitawa ya mata banza,sau uku tana fad’a yana mata banza Ta fashe da kuka “haba! Yaya kana ji na fah kayi shiru,kowane laifi Ya yazeed ya maka,ya kamata kaji tausayinshi yana can asibiti unconcious” A fusace yace”ba kowane laifi ba,laifin da yamun yafi k’arfin in yafe masa,zan iya yafe kowane laifi a duniya banda wannan,dan haka kije kice bazan bayar ba” Zata sake magana ya daka mata tsawa “I said get out” _Yana jin tausayin Yazeed,amma zafin abunda yayi niyyar yima Noor bazai barshi ya gane tausayinsa da yake ba_ Jiki na rawa ta fita tana hawaye,Taci karo da Noor ( _zata duba ta gani ya tafi asibitin ko yana nan_) Cike da damuwa tace “Ihsan me aka miki? Ya jikin Yazeed?” Ihsan ta galla mata harara tace “ban sani ba” “Please ki gaya mun Ihsan” “Idan baki kauce mun a hanya ba,zanyi k’asa k’asa dake wlh” Ta d’an matsa,ta wuce ta bar Noor sake da baki Falo taga mai wanki ya kawo kayansu Imran “Idi Dan Allah ko kasan me Ihsan ke ma kuka” “Imran ne yace bazai bada jininshi a sawa Yazee…..” Bata jira ya k’arasa magana ba,ta shiga d’akin Imran “Haba! Imran banyi tunanin haka daga gareka ba,ina tausayinka da imaninka suke? ko kasan idan ka ceci rai d’aya kamar ka ceci duka al’umma ne,haka idan ka kashe rai d’aya kamar ka kashe duka al’umma ne,D’an uwanka nacan kwance asibiti amma ba zaka iya taimakonshi ba, Cike da mamaki kawai yake kallon Noor a fusace yace “wacce irin zuciya ce dake Noor? Ke kika fi kowa tausayine a duniya? Duk abun nan da Yazeed ya miki but still kike tausayinsa,tun azabtar dake da yake har xuwa abunda ya miki yau” “Imran kenan Allah muke masa laifi ya yafe mana ballatana d’an adam,Ni wallahi na yafe ma Yazeed duniya da lahira” Imran a fusace yace “lallai Noor baki san ciwon kanki ba,bakya kishin kanki,ayi k’okarin miki fyad’e kuma ki yafe” Murmushin takaici tayi tace mutum yayi zina,yasha giya Allah ya yafe masa ballatana ni da k’okarin yimun yayi baimun ba mezai hana na yafe masa,dan haka Dan Allah Dan Annabi kaje ka bayar” “No i can’t Noor idan ke kin yafe masa,i can’t forgive him” Cike da mamaki take kallonsa tace “akan me bazaka yafe masa ba,ni yama laifin nan kuma na yafe masa,why not kaima bazaka hak’ura ba” Bai ce mata komai ba,a ranshi yace “ba zaki gane bane Noor,bakisan ya nake ji game dake ba,ni kaina na kasa ganewa,zuciyata zafi take tana tafarfasa idan na tuna yadda naga Yazeed kan ki”( _Ni Zee nace Imran ko dai kishi ne,taya zaka fara kishinta bayan ba so tsakaninku,Anya Imran baka fara sonta ba🤔,idan kuwa ka kuskura ka fara sonta zaka jefa kanka a rud’ani_) Kneeling tayi gabanshi,ta fashe da kuka “Dan Allah Imran kaje ka bayar” Har cikin ranshi yake jin kukanta,idan yana son mutuwarshi yana son kukanta Da sauri yace “tashi tashi Noor ki daina kuka,zanje” “kayi alk’awari” “Eh na miki alk’awari” “Nagode” “Ki daina mun godiya ba abunda bazan iya yi akan ki ba” _Ita kanta Noor tana mamakin yadda yake jin maganarta kuma baya son kukanta ko kad’an_ Ihsan ta koma asibiti sharb’e sharb’e da hawayenm,Hajiya ke tambayarta “Ina Imran d’in?” “Yace bazai zo ba,ba zai bayar da jininshi ba” Alhaji yace “haka Imran d’in yace?” “Eh” Hajiya tace “lallai Imran,anya yana cikin hankalinshi kuwa,gaskiya shima ya kamata a kawo shi asibitin nan a duba shi” Alhaji yace “ko shakka babu” “Dr yanxu me ye abun yi?” Hajiya ta tambaya Yayi ajiyar zuciya ya d’an yi shiru na yan mintuna,zai yi magana kenan Iman tace “Ga Ya Imran” Duk suka juya suna kallonshi,yana tahowa har ya k’araso Ba wanda ya tanka cikinsu sai Dr “Dr muje a d’ibi jinin nawa” Hajiya tace “ai da baka zo ba, mara kunya,mara tausayi,da ka bari ya mutu” Alhaji yace “Imran me ke damunka? me ya shiga kankam me Yazeed ya maka ka mishi wannan mummunan rauni?” Ko uffan bai ce musu ba,sai likita da yace ma “Dr plss muje a d’iba ina da abun yi” Hajiya a fusace tace “Ai da baka zo ba,ka tsaya ka cigaba da abunda kake,mara tausayi kawai,baka damu ma ka tambayi ya jikin d’an uwan naka ba, zaka….” Dr.Moha ya katse ta”Hajiya kiyi hak’uri yanzu ba lokacin fad’a bane” Ana d’ibar jininshi,ko wajensu Hajiya bai koma ba,ya tafiyarshi Su hajiya tunani kawai suke wane laifi ne Yazeed ya mishi haka🤔 Su hajiya na zaune reception,Suna jiran lokacin da akace zasu iya ganin Yazeed yayi,dan ance bazasu iya ganinshi ba sai ya farfad’o Ana saura 30mins,Hajiya tace su Iman suje gida su had’o kayan tea Suna dawowa ana cewa su shiga Hajiya tayi kanshi tana kuka,duk idan Imran yaji mishi ciwo,ansa bandage an rufe,duk ya chanza kamanni,Daga gani yana jin jiki Dukansu suka had’a baki suka ce “Sannu Ya jiki?” Kai kad’ai ya gyad’a musu Alhaji bai yi tunanin raunin har ya kai haka ba,ganin irin raunukan ba k’aramin mamaki ya sake kamashi ba Hajiya ta had’a mai kakkauran tea,da k’yar yasha …………………………………………………. Imran daga asibiti gida ya koma,ya shiga d’aki ya rufe kanshi,yana ta tunani duk akan Noor,Tambayar da yake ma kanshi “me yasa nake jin haushin Yazeed sosai haka akn abunda yama Noor,me yasa zuciyata ke zafi idan na tuna yadda na ganshi a kanta why? why?”🤔 Ko tausayinta da nake yi ne? “NO wannan ba tausayi bane da tausayi ne da ba haka zanji ba,Toh menene?” _Readers ko zaku gayawa Imran me nene?_ Ta b’angaren Noor,Addu’ take Allah yasa Yazeed ya samu sauk’i,haka Imran na fad’o mata a rai akai-akai,duk sanda ta tuna shi sai tayi murmushi,sai ta rik’a ji tana son ganinshi Tambayar da take ma kanta itace “me yasa Imran ya damu kanshi sosai haka,ya d’auki zafi da yawa akn abnda Yazeed ya mata”🤔+ Da daddare aka sallami Yazeed,Dr yace “zasu iya tafiya gida,ba wani matsala,ciwonkan da yaji ne kawai kuma sannu a hankli zasu warke” Su Hajiya sun ma Dr godiya sosai Yazeed hankalinshi duk ya kasa kwanciya,fargaba kawai yake kar Imran ko Noor su fad’i abunda yayi Hajiya ta lura da yanayinshi dan haka ta tambayeshi “Me ke damunka ne Yazeed” Ya d’an k’ak’alo murmishi yace “ba komai mum me kika gani?” “Like something is bothering you” “Nothing mum ba abunda ke damuna” “Ok Allah yasa kuma Allah ya baka lafiya” “Ameen Mum” “Iman kira mun Imran da Noor” “Gaban yazeed ya fad’i da sauri yace “me zasu miki?” “Ka bari a kira su idan sunzo zaka gani” Zai sake magana Hajiya ta dakatar dashi da hannu “Iman yi sauri ki kira su” Zuciyar Yazeed kamar zata fito waje saboda tsoro da fargaba Dukkansu ana cewa Hajiya na kiransu,sun san tambaya zata yi laifin da Yazeed yama Imran? Noor ta fara shiga falon,Yazeed ya bita da kallo ji yake kamar ya tashi ya rungumeta ba abnda ya chnza game da yadda yake ji a kanta( _Ni Zee nace baka dandara ba kenan,kana so Imran ya kakkarya ka_😂),gabanshi nata fad’uwa Da durk’usa tace “mishi ya jiki?” Ba k’aramin mamaki yayi ba,da tmbayeshi jiki Yayi murmushi yace “Da sauk’i” “Allah ya k’ara sauk’i” “Ameen” Sai da aka d’au mintuna Imran ya shigo,Fuskar nan tashi babu annuri,Take bugun zuciyar Yazeed ya k’aru da sauri fat fat fat Ko saitin inda Yazeed yake bai kalla ba,ya samu wuri ya zauna Kowa ya bishi da kallo,Hajiya ta gyara murya tace “Imran ko zaka iya gaya mana dalilin dukan daka ma Yazeed” Yazeed yai saurin interrupting yace “No mum tsakaninmu ne laifi na mai,ya hukuntani so no need ai ta tashe tashe ya wuce” Hajiya ta galla mai wata harara tace ” na tambaye,kama mun bakin ka” Yazeed yaja bakinshi yayi shiru tare da had’iye miyau k’uttt Ta juya kan Imran “kai nake saurare” Imran ya d’an yi shiru na seconds sannan yace “Marin Noor yayi” Hajiya da Alhaji suka had’a baki sukace “WHAT” Alhaji yace “Dan ya mareta shine zaka mai dukan nan” Imran yai shiru bai ce komai ba Yazeed mamaki ne ya cika shi yadda Imran ya rufa mishi asiri Noor kuwa hakan dad’i ya mata da ya rufa mai asiri( _yaji maganarta kenan_) Hajiya ta nuna Noor da yatsa tace “Saboda wannan shegiyar ka ji mishi raunuka,har kake cewa ba zaka bashi jini ba” Ta juya kan Alhaji tace “duk kai ka kawo mana annoba jaraba cikin gida,tunda tazo gidan nan bamu huta ba,gashi ta fara had’a ya’yanka fad’a” Alhaji yayi shiru yana muzurai ji yake kamar yace ya saki Noor,amma ba dama “Kai koma Imran in dai akan Noor ne ka mishi haka,daga yau ba kai ba Noor,ka zab’a ko ni ko Noor” Furucin Hajiya ba k’aramin girgiza Imran yayi ba,A kid’ime ya kalli Hajiya Ya juya kan Noor yace “kiyi hak’uri Noor ki barni na fad’a” Tai saurin girgiza kai tace “No Imran pls kar kace komai” “I have to,ki barni kawai na fad’a” Su Hajiya binsu da kallo kawai suke da mamaki Yazeed kuwa duk ya tara gumi,ya gama tsorata “No Imran pls don’t say a word” ta fashe da kuka Ganin kukan da take ya sa shi yin shiru Yana jinjina ta yadda za’a raba shi da Noor _bayan ya riga ya saba da ita,ko kad’an baya son nisa da ita_ “Ka fad’a mana” cewar Hajiya “No mum lets forget” “Karyar iskanci kuke kai da ita,daga yau zaki fara yabawa aya zak’inta,dukan da kika sa aka mishi,wlh sai na rama shi a kanki” Hajiya ta mik’e tayi kanta Da sauri Yazeed ya taso ya tare hajiya yace “Please mum kiyi hak’uri kar ki mata komai” Hajiya sake da baki ta juyo tana kallon Yazeed tana mamaki Yau yazeed ne da tarewa kar a duki Noor kuma itace silar abnda aka mishi,ba hajiya kad’ai ba dukan falon kowa yayi mamaki( _hatta Imran da Noor sunyi mamaki,dan a tunaninsu dole ya rama abnda aka mishi a kanta tunda ya tsaneta_) “Yazeed kaine ke kare Noor” “Mum ni dai pls kiyi hak’uri ki k’yaleta,ai ba laifinta bane tunda ba ita ta dukeni ba” Hajiya komawa kawai tayi ta zauna kan kujera,dan ta zama speechless,jikinta duk yayi sanyi Yau Yazeed ne da kare Noor Imran a ranshi yace “lallai Yazeed nasan kayi hakane dan ka cimma mummunar manufarka akan Noor,toh wlh ba zaka tab’a samun nasara ba, idan ina numfashi a doran k’asa” Tsaki yayi ya mik’e ya bar falon Noor na durk’ushe a kasa ko k’wakk’waran motsi,gaba d’aya she is confused Yazeed kuwa ko kallonta baya son yi,dan duk sanda ya kalleta sai ya tsinci kansa a wani irin yanayi Alhaji ko uffan bai ce ba,ya tashi sumi-sumi ya bar falon,dan yaga abun yafi k’arfinshi …………………………………

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page