MAKIRCI KO ASIRI CHAPTER 1

MAKIRCI KO ASIRI
CHAPTER 1

21 September
Birthdays are nature’s way of telling us to eat more cake. Birthdays are like boogers. The more you have the harder it is to breathe. Another year older, none the wiser. Birthdays are just finger posts on the road of getting old… I was born with a gift, the gift of awesomeness I’m not just a year older I’m also a year better and prettier. I know you’re jealous. I’d like to thank my mom and dad for making this miracle possible. ITS MY BIRTHDAY🎂🎉1
Boom! Yes, today is my birthday, Therefore I will be treated like a Queen👑💃
1
Wattpad @yar_ficika
Blog www.phirdauceejeebo.blogspot.com
Instagram: yar_ficika
Snapchat: phirdauceejeeb5
Twitter: Feedoh Deedoh
Skype: phirdaucee Jeeboh
Facebook: phirdaucee Jeeboh
®NWA
BABI NA D’AYA
    Shimfida
    Gidan Malam Bahaushe…
Idan akace gidan Malam Bahaushe gidane da kyar kasamu matar aure d’aya zaka iya samun sama da d’aya ga yara wasu zamansu lafiya da kishiyoyi wasu kuma zaka samu akasin haka…
    Zaune yake palour cikin lallausar kujera tagumi yayi gaba d’aya hankalinshi bai tare dashi, d’agowa tayi ta kalleshi girgiza kai tayi ta cigaba da shirya yaranta da zasu wuce islamiyya, tana gama shiryasu tabi kowaye ne da peck a kunci kallon babbar tayi tace
“Princess ki kula da k’annenki kinji ko?”
“To Ammi zan kula dasu”
“Kuje kar ku makara driver yana jiranku.”
   Tafiya suka yi suna
“Daddy mun tafi.”
Amma hankalinshi bai jikinshi.
   Mik’ewa tayi tsaye kayan dake jikinta sun bayyanar da cikar sura da zatin halittarta. Doguwa ce tana da d’an jiki sai dai ba sosai ba amma gabanta cike yake da dukiyar fulani bak’ace amma ba wulik ba idanuwanta farare ne gata da hips komai nata daidai ita.
   Matsawa tayi kusa dashi ta zauna, hannunshi ta janye daga tagumin da yayi d’agowa yayi ya kalleta tare da sakar mata murmushi kawar da kanta tayi gefe tace
“Tun yaushe nake binka ka gayaman damuwarka amma kak’i fad’aman shin ka mance matarka nake uwar yayanka ko kuma ban isa na san damuwarka ba?”
  Dasauri ya kalleta yace
“Ba haka bane ba bansan ya zaki d’auki abun bane ba”
  Tashi tayi taje gabanshi ta duk’a hannunshi ta kamo tace
“Ka fad’aman damuwarka kai tsaye ni kuma nayi alk’awarin zan baka goyon baya”2
   D’agota yayi ya zaunar da ita kan cinyarshi,
“RAMLAH”
  Ya kira sunanta jikinta sanyaye ta amsa da
“Naam”
“Kiyi hak’uri akan abinda za kiji daga bakina banyi haka dan in b’ata maki ba ko kuma kin rageni da wani abu tsawon shekarun da mukayi tare wallahi baki tab’ayi man laifi ba duk abinda na umurceki shi kikeman tabbas samun irinki a wannan zamanin sai an bincika.”
   Murmushi tayi tace
“Nagode kwarai da yabon ka a kaina mijina.”
“Ramlah”
D’agowa tayi ta kalleshi batare da ta amsa ba sai kuma ta saukar da kanta ganin yanayin daya shiga,
“Aure nakesan na k’ara. Da sauri ta d’ago
“AURE?”
“Eh aure.”
Ajiyar zuciya tayi ta saukar da kanta k’asa.
   Cikin kanta taji yana cewa
“Banyi niyar k’ara auren nan ba dan cin fuska ko kin rageni da wani abu ah ah kawai zan iya kiran wannan auren da auren k’addara dan Allah ki fahimci mi nake nufi.”
  Kallonshi tayi ta sakar mashi murmushi tace
“Yanzu dan zaka k’ara aure shine ka kasa gayaman, haba Imran kaifa mijina ne kuma ay Allah ya hallata maka k’arin aure, muddin zakayi adalci a tsakaninmu wallahi ni banda matsala fatana dai ka kasance mai adalci Allah yasa ta gari zaka auro Allah kuma ya had’a arzik’inmu.”
   Tun kafin ta k’are ya k’ank’ameta,
“Tabbas Ramlah ke Alheri ce (Biebee’n Feedoh) duk namijin daya sameki wallahi yayi sa’ar mata Allah ya saka da alheri ance Aljannar mace tana k’ark’ashin k’afar mijinta to nikam na d’aga maki k’afata.”
   Dariya tayi tare da sauka k’asa tace
“Nagode mijina. A ina k’anwar tawa take? Kuma miye sunanta?”
“Nan garin take a nan goruba road kuma sunanta Mufeedah”
  Murmushi tayi wanda ita kanta batasan na miye ba. Tashi yayi yace
“Zan fita”
Mik’ewa tayi tsaye tace
“Sai kadawo Allah ya kiyaye hanya”
Tana kaiwa nan ta wuce dan batasan ya gane halin da take ciki.12
     Tana shiga d’aki ta banko k’ofa fad’awa tayi kan gado ta fashe da kuka sai da tayi mai isarta taga ba maganin da zai mata ta mik’e ta nufi toilet  alwalla tayi ta fito tayi raka’a biyu tare da neman Allah ya bata juriya da dangana akan auren da mijinta zaiyi. Ta dad’e tana adua daga k’arshe ta shafa ta tashi ta nufi kitchen danyin girki kafin pikins d’inta su dawo.
Girki take amma hankalinta bai tare da ita da haka harta gama, k’arfe shida da rabi yaranta suka dawo da gudu suka shigo
“Ammi mun dawo” abinda suke cewa kenan,
parlour suka had’u da ita gaba d’aya sukayi kanta suna dariya had’asu tayi gaba d’aya ta rungume, da sauri ta goge hawayen da suka gangaro daga fuskarta tayi….
    Sun kai kusan minti biyar a haka kana ta sakesu, kallonta babbar tayi tace
“Ammi kuka?”
Girgiza mata kai tayi
ba kuka nayi ba princess, murmushi tayi tace
“Ammi kuka kikayi mana ga idonki nan yayi ja”
jawota tayi jikinta tace
“nace maki ba kuka nayi ba abu ne ya fad’a man a ido kuma na cire.”
   Amm amma Ammi….
Haneefa jeki cire kayanki bansan yawan surutu
oya my pikins kuzo muje a cire kaya kafin a kira sallah, gaba d’aya suka rufama mata baya…4
   Suna shiga d’akin ta canja masu kaya, duk abinda takeyi idon Haneefa na kanta tana gama canja masu kaya tace
“Kuje kuyi alwalla”
Amsa mata sukayi da “to”
Sukabar d’akin….
Zama Haneefa tayi kusa da ita tace
“Ammi tunda muka dawo nagane kina cikin damuwa amma kin kasa fad’aman karki manta fa ni diyarki ce”
Kallonta tayi ta mata murmushi
“Karki damu princess na gaya maki abu ya fad’aman a ido kuma ayna cire karki damu kanki kinji”
d’aga mata kai tayi alamar
“To”
“Yauwa my baby tashi kije kema kiyi alwalla nima gani nan fitowa..”
   Saida sukayi isha kana suka hau dainning table dan cin abinci, da kanta tayi serving yaranta sai da taga sun k’oshi kana tace
“Kowa ya d’auko assignment d’inshi”
Tashi sukayi sukaje suka kawo, d’aya bayan d’aya ta masu inda ta masu assignment d’in nan sukayi bacci..
   Kwashe su tayi takai su d’aki ta masu ad’ua ta rufesu da blanket ta ja masu k’ofa…
  Tana shiga d’aki ta fad’a toilet, ta dad’e tana wanka daga baya ta fito gaban mirror ta tsaya tayi kwalliya tana  gamawa ta mulke jikinta da oil perfume ta d’auko kayan bacci masu kyau ta saka feshe jikinta tayi da turaren tom ford, tana gamawa ta koma parlour ta zauna ta kunna tv tana kallon mbc max..
   11:00pm daidai ya danna door bell a yangance ta tashi taje ta bud’e mashi, tana bud’ewa ya ware hannunwanshi da gudu ta ida isa wajenshi, k’ank’ameta yayi kamar wani zai kwace mashi sun kusa minti biyar a haka kana ya saketa murmushi ya sakar mata
“Angel kinga yanda kikayi kyau kuwa?”
“Bawani kyau hayatee”
Rufe mata bakinta yayi da hannuwanta yace
“Waya gaya maki baki kyau ba?”
“Ni ay nasan banyi kyau ba” tana magana tana zumb’ure baki..
“Ya salam”
Abinda ya fad’a kenan gaba d’aya duk ta hargitsa mashi lissafi
Kafin ta k’ara magana ya sunkuce ta baki d’aya ya shiga ciki da ita da k’afa ya tura k’ofan, bai ajeta ko ina ba sai saman 3seater..
   Zama yayi kusa da ita yana haki
“Haka kika k’ara nauyi? Wai mi kikeci idan na fita?”
Dariya tayi tace
“Nikam mizanci”
“Kedai fad’a gaskiya”
Allah bancin komi fa”
“To na yarda”
Kallonshi tayi
“Yanzu mi zaka farayi cin abinci ko wanka?”
“Duk abinda Angel tace inyi shi zanyi”
  Fari tayi da idanu tace
“To wanka zaka farayi”
“Your wish is my command..”
   Murmushi tayi tace
“Ina zuwa”
Binta yayi da ido tsananin tausanta ya kamashi shi kanshi yarasa dalilin da yasa yakesan k’ara mata kishiya dan Ramlat ba ta cancanci ay mata kishiya ba, bai gama tunaninshi ba yaji hannunta ciki sumarshi..
  D’agowa yayi yace
“Yadai?”
“Muje ga ruwan wanka can na had’a maka”
Tashi yayi yabi bayanta har suka isa d’akinshi suna shiga ta mik’a mashi towel karb’a yayi ya mata peck kana ya fad’a toilet…
   Kayan bacci ta fito mai dasu ta feshesu da turare kana ta aje mashi su kan gado…
  Fita tayi ta koma parlour dan had’a mashi abinci…11
Koda ya fito wanka bai ganta ba, shiryawa yayi cikin kayan da ta aje mashi yana gama shiryawa ya feshe jikinshi da turaren BOSS ORANGE. Parlour ya fito dam yasan can zai sameta, ta baya ya rufe mata idanuwa murmushi tayi
“Hayatee”
Dariya yayi yace
“Shine kika gudu kika barni?” Daidai yana juyo da ita…
“Abinci nazo na had’a maka fa”
“Kedai wayo kikaman kika gudo kika barni.”
   Murmushi ta sakar mashi tace
“Am sorry”
Hancinta yaja yace
“Issokay”
   Hannunshi ta kama ta zaunar dashi
“Mizaka faraci?”
“Duk abinda Angel tabani”
  Murmushi ta zuba mashi tuwon shinkafa da miyar agushi, tura mashi plate d’in tayi, kallonta yayi yace
“Ya haka?”
“Kaci mana”
“Dama da kaina nake cin abinci?”
“Gara kasaba tun yanzu kasan nakusa samun k’anwa”
   Kallo ya tsareta dashi har saida taji kunyar yin maganar da tayi, jawota yayi jikinshi yace
“Aure na ba abinda zai rageki daga kula dani haka nima bai rageni daga kula dake da yarana ko kin manta kune rayuwata?”
Sunne kanta tayi cikin jikinshi tana share kwalla wanda bai san tana yinsu ba…
“Tashi kibani abinci inci” abinda taji yace kenan, ba musu ta tashi tafara bashi abinci yanaci suna fira har saida ta tabbatar da ya k’oshi, kayan ta kwashe takai kitchen saida ta wanke su kana tadawo parlour…
   Kallonta yayi yace
“Hajiya nifa bacci nakeji”
Dariya tayi tace
“Jeka kwanta saida safe”
“Aww inje in kwanta kikace ko?”
“Eh”
Bata ankaraba taji ya sungumeta niyar kwace kanta takeyi amma ta kasa haka ta hak’ura bai dire ta ko ina ba sai bisa gado, side lamp ya kashe masu yaja masu bargo ya rufe…..
            *********
    zaune suke biyar mata uku sai namiji biyu cikin d’akin shisha pot ce gabansu suna sha hankalinsu kwance ga wak’ar wizkid ta DADIYO na tashi…
“Yanzu Mufeedah dagaske aure zakiyi kibarni?”
Cewar wani saurayi dake zaune gefen ta..
   Hayakin shisha ta busar ta taso ta k’araso inda yake kanshi ta shafa tace
“Aure na ba abinda zai rageka dashi asalima kasan sanadiyar yin auren nawa so karka tada hankalinka baby nah”
Haka ta dinga kwantar mashi da hankali…
   A hankali ta zare jikinta, toilet ta fad’a tayi wanka tana fitowa ta tarda ya tashi murmushi ta sakar mashi shima murmushin ya sakar mata yace
“Shine kika tashi kika barni ko?” K’arasowa tayi inda yake tace
“Bansan na tasheka daga bacci ne shiyasa”
girgiza kai yayi ya mik’e ya fad’a toilet…
   Yana fitowa ta taimaka mashi ya shirya tsaf, hannunta yaja ya zaunar da ita bisa gado yace
“Ramlah inasan ki lissafaman duk abinda kike buk’ata na baki kudin cz next month ne bikin” murmshi tayi tace
“Ko nawa kaban bakomai Allah ya sa masu albarka kaida ke da hidima minene kuma sai kaman”
k’ura mata ido yayi kamar mai karantar wani abu. Ajiyan zuciya yayi ya kamo hannunta yace
“Hakk’in kine na maki dan haka karkiji komai kedai ki abinda nace”
murmshi ta mashi tace
“Shikenan in shaa Allah kafin kadawo nagama komai”.
Rungomata yayi
“Allah ya maki albarka yabani ikon faranta maki kamar yanda kike faranta man nima”
“Amin”
Tabashi amsa..
“Break fast is ready fa”
Kashe mata ido yayi yace
“Zokiji”
Dariya tayi ta ruga tace
“Naki wayon”
Girgiza kanshi yayi ya tashi ya bita yana jin k’ara san matarshi hannu ya d’aga ya nama Allah godia daya bashi Ramlah a matsayin mata…
    Parlour ya tarda ta tana had’a mashi abinci, hannunta yajawo
“Yanzu wana kama?”
Dariya tayi bata bashi amsa ba…
   Zaunar dashi tayi ta dinga bashi abinci kamar wani taro har sai da ya k’oshi kana ta kyaleshi….
   Jikarshi ta d’auko ta rik’o mashi hannu ta rakashi har gaban mota. Duk’awa tayi ta bashi jikar
“Allah ya kiyaye hanya ya kaika lafiya ya maidoka lafiya alkairin dake tattare da ranar nan Allah ya had’aka dashi sharrin dake cikinta kuma Allah ya nisanta kadashi ka kuma tabbata halak d’inka zaka kawo mana”
“Amin ya Allah”
Abinda yace kenan yana murmushi saboda irin aduar nan ta riga data zamar mashi jiki muddi zai fita saita mashi ita shiyasa yakejin duk duniya babu wanda yakaishi sa’ar mata..
   Kanta ya shafa yace “a kullum ina alfahari dake Allah ya bani abinda zan faranta maki”
Motar ta bud’e mashi peck ya mata kana ya shiga
“Kigaidaman yarana idan sun dawo yau na makara bamu gaisa ba har suka tafi makaranta”
   Murmshi tayi tace
“In shaa Allah zan gaya masu..”
Motar yama key ya fita d’aga mashi hannu takeyi har saida taga ya fita daga gate d’in gidan kana ta juya ta koma cikin gida…..
Kan kujera ta fad’a hawaye suka cigaba da sintiri kan fuskarta, dafa ta taji anyi da sauri ta d’ago fuskarta ganin waye ya dafata..
    “Lafiya kike? Tunda na shigo nake sallama amma baki amsa ba sai ma kuka da kikeyi”
cewar wata mata dake tsaye
  Murmushi tayi ta share hawayenta
“Bakomai”
Zama matar tayi tare da murmushi wanda iya karshi labb’a
“Ba maganar ba komai gashi kina kuka sai dai in ban isa nasan damuwarki ba neba”..
Hawaye ta share
“Dama Imran ne zai k’ara aure”
Tashi tsaye matar tayi
“what?”
“Aure”
“Shi Imran d’inne zai k’ara aure?”..
     Kamo hannunta tayi ta zaunar da ita tace
“Eh aure zaiyi”
“Laifin mi kika mashi ne? Nidai iya sanina ban tab’ajin tsakaninku ba bare har  yace zai k’ara aure”
  Nisawa tayi tace
“Dama sai kama namiji laifi zai k’ara aure? Ai namiji duk sanda ya buk’aci k’ara aure to komi kake mashi sai ya k’ara sai dai fatan Allah ya sa wanda za’a auro ta gari ce..”
“To ke yanzu wane mataki kika d’auka?”
“Mataki kuma?”
“Eh kina nufin hakanan zaki zauna? Wallahi gara ki tashi tsaye kinsan wadda za’a kawo maki? Kinsan dami zata shigo gidanki? Gara kisan matakin da zaki d’auka ki shirya ina da wajen malamin da zan kaiki sha yanzu magani yanzu ke ina tabbatar maki ko auren baza’ayi ba..”
   D’agowa da sauri Ramlah tayi ta kalle ta
“Anya Zainab kina da lafiya kuwa? Kinsan mi kike fad’a wajen malami fa”
“Eh malami keni kin ganni nan wallahi mijina bai isa yace zai k’ara aure ba cz hannuna yake sai yanda nayi dashi..”
“Wa iya zubillah Allah kamana tsari da irinku Zainab da ina ganinki mai hankali ashe baki da hankali, to bari kiji wallahi ko da zan zama abun tausayi bazan iya zuwa wajen malami ba da sunan a hana mijina aure ba’a aure ni aka aure ni? Kuma miye hukuncin wanda ya haramta abinda Allah ya halasta? Allah ne yace suyi aure idan zasuyi adalci, Idan har bazan tashi da dare ba inkai ma Allah kuka na to kada Allah yaban ikon zuwa wajen wani malami Kuma idan kinsan saboda irin haka zaki dinga zuwa gidana karki k’ara zuwa nayi dana sanin k’awance dake amma ina neman maki shiriya Allah ya ganar dake”
Mik’ewa tsaye Zainab tayi tace
“Ko bakice ba ban k’ara zuwa kuma indai namiji ne gayacan ya gasaki sarkin biyayya”
tawani shek’e da dariya ta fita tabar gidan…
         **********
      Haneefa ce tare da k’annenta suka shigo da sallama yarinya yar kimanin shekara bakwai, k’arasowa sukayi inda take zaune, zare mata hannu tayi daga tagumin da tayi d’agowa tayi ta kallesu tana murmushi
“Har kun dawo? Banji shigowarku ba?”
   Murmushi tayi ta kalli k’anneta tace
“kuje d’aki ku cire kaya sai muyi wanka muzo muci abinci muyi shirin Islamiyya”
Ba musu suka nufi d’aki..1
   Zama tayi kusa da Ramlah tace
“Ammi akwai abinda ke damunki amma baki fad’aman”
Ita kanta tana mamakin irin wayon Haneefa da hankalinta
  Jawota tayi jikinta tace
” bakomai kinji my babe kedai ki rink’a man adua kinji ko”
“In shaa Allah Ammi”
“Allah ya maki albarka”
“Amin”
Mik’ewa tayi ta nufi d’akin dan itama ta cire kayanta…
   Binta tayi da kallo tana k’arajin k’aunar d’iyarta a ranta duk yanda take b’oye damuwa amma Haneefa tana ganewa..
    Suna fitowa suka wuce dainning dan cin abinci da kanta tayi serving yaranta suna gama ci suka wuce islamiyya..
2
    Da sallama ya shigo ga maigadi na ta shigowa da akwatina, bai ganta parlour ba yasan bata wuce d’aki.
    D’akinta ya lek’a zaune take bisa sallaya tana azkar, wuri ya samu ya zauna sai da tagama tsaf ta d’ago da murmushi ta kalleshi shima murmushin ya mayar mata
“Sannu da zuwa “
“Yauwa”
Ya amsa mata…
   Tashi tayi ta nufi toilet dan had’a mashi ruwan wanka, tana fitowa ta kalleshi tace
“Ga ruwan wanka can”
Mik’ewa yayi ya kamo hannunta suka nufi parlour baice mata komai ba..
    Zaunar da ita yayi ya kalleta yace
“Ga akwatina nan set biyu ki zab’i daya ki barma Amarya d’aya duk abinda ke nan akwai shi nan sai dai kayan kowane da kalarsu wad’an can kuma nasu Haneefa”
   Murmushi tayi tace
“Mungode Allah ya k’ara bud’i”
“Amin ya rabb”
Set guda ta d’auka ta duba komai na ciki ya mata tana cikin dubawa yace
“In akwai abinda bai maki ba saiki fad’a”
D’agowa tayi da murmushi tace komai yayi Allah ya k’ara rufa asiri…
“Amin”
Ya amsa tare da mik’ewa
“Gobe masu fenti zasuzo”
Yana fad’ar haka ya wuce d’aki dan yin wanka
“Allah ya kawosu lafiya”
Ta bashi amsa..
     Fitowa yayi shirye cikin k’ana nan kaya, tana kallonshi tace
“Har kafara kyallin agonci”
Dariya yayi yace
“Zaki fara ko?”
Wuri yasamu ya zauna da taimakonta yaci abinci bayan ya gama ta kwashe kayan ta kai kitchen dawowa tayi ta
zauna k’asa tana matsa mashi k’afafuwa, kud’i ya zaro ya mik’a mata
1
“ga wannan dubu d’ari biyu ne idan akwai abinda zakiyi”
Murmushi tayi tace
“Wallahi ba abinda zanyi kaman komai dan haka ka barsu”
Tsura mata ido yayi yana kallonta, kanta ta saukar k’asa tana wasa da yan yatsunshi..
“Ramlah”
Ya kira sunanta d’agowa tayi ta kalleshi yace
“Nina baki wannan kud’in ko bazaki komai dasu ba ki aje wajenki”
    Hannu biyu tasa ta karb’a tace
“Nagode Allah yasaka da alkairi ya k’ara buri”
“Amin”
Ya amsa mata…
    Tashi tayi tace
“Ina zuwa”
Jim kad’an ta dawo da wata leda bud’ewa tayi ta fito da wata shedda getzner fara tasha dinki da babbar riga tace
“Ga tawa gudumuwar inasan mijina ya sata ranan d’aurin aure”
Karb’a yayi ya k’ura mata ido
“Ina kika sameta?”
Order ta nayi a YML fashion design sukace na tura mejoment d’inka na masu sending shine yau suka kawo man”
Ay tun kafin ta k’arasa ya rungumeta
“Tabbas samun mata kamarki sai an bincika a kullum ina godema Allah da yabanke a matsayin mata uwar yayana”
Dariya tayi tace
“Ganinka cikin farin ciki yafi man komai a rayuwa..”
  K’ank’ameta yayi yana k’ara jin san matarshi kwallan da suka gangaro mata ta share dan batasan ya gane halin da take ciki…
Ammi Ammi Ammi”
Haneefa ce ke kwalamata kira da sauri ta fito daga kitchen tace
“Haneefa lafiya?”
“Lafiya lau Ammi”
Ta bata amsa..
    B’ata fuska tayi tace
“Ji yanda kika d’agaman hankali da kira”
Dariya tayi tace
“Yi hak’uri”
“Inasu Haneef?”
Suna d’aki..
“Yauwa Ammi akwatina nagani d’akinki na waye?”
“Dama nasan wannan kiran da kike akwai wani abu”
Namune Daddynku ya kawo mana d’azu”
Ido ta zaro tace
“Namu ne muduka Ammi? Lallai Daddy naji damu”
Ta dinga tsalle tana murna, ita dai Ramlah binta tayi da ido tana girgiza kai.
“Amma Ammi miyasa ya siyo manasu?”
Kanta ta shafa tace
“Aunty zai kawo maku shine yamana d’inkin biki”
“Aunty?”
“Eh Aunty”
Ta bata amsa, bata k’ara cewa komai ba ta janye jikinta ta nufi d’akinsu, kallonta Ramlah tayi ta girgiza kai, ta koma kitchen…+
   Saida ta gama aikin da take kana ta nufi d’akin yaran, ganinsu tayi zaune sunyi tagumi kallonsu tayi tace
“My pikins ya kukayi tagumi?”
“Bakomai”
Haneef ya bata amsa
B’ata fuska tayi tace
“Akwai abinda ke damunku”
Numfasawa Haneefa tayi tace
“Ammi miyasa Daddy zai k’aro mana Aunty? Ina tsoro saboda gidansu Sadeeya kinga basu zaman kafiya kullum cikin dambe da fad’a kullum sai Sadeeya taban labarin irin fad’an da ake gidansu, Ammi ina tsoro kar itama ta dinga nemanki da fad’a”
Shiru Ramlah tayi
Yanzu kamar Haneefa tasan irin wannan matsalolin?”
Takowa tayi ta k’araso inda suke zaune ta sakar masu murmushi tace
“Haneefa ba kowane gida baneba basu zaman lafiya wani gidan idan kikaje zaki tunanin babu kishiya kisa aranki ta gari Daddy zai kawo kudai ku cigaba da adu’a kunji yarana..”
     D’aga mata kai sukayi sukace
“In shaa Allah Ammi zamu cigaba da adua”
D’aya bayan d’aya ta bisu ta masu peck tace
“Allah ya maku albarka”
“Amin”
Suka amsa…
             ************
  Gidan yau cike yake da mutane anata hidimar biki, duk wanda yaga Ramlah bai cewa itace za’ama kishiya ba, yanda take fara’a kowa sai mamakin irin halinta yakeyi…
   D’aki ta tardashi ya fito wanka tana ganinshi ta saki murmushi kaga
“Angon Mufeedah”
K’arasowa yayi inda take ya rungumeta yace
“Ramlah wace irin matace ke wai? Miyasa abu bai b’ata maki rai?”
   Kwalla ta share ta d’ago tace
“Bayan da zanyi da abinda Allah ya rubuta to kaga tada hankalin bashi da amfani nidai fatana dakai Allah ya baka ikon yin adalci..”
K’ara rungumeta yayi yace
“Ramlah ance Aljanar mace na k’ark’ashin k’afar mijinta ko?”
“Eh”
“Toh na d’aga maki”
Murmushi tayi tace
“Nagode”
  Hannunshi taja tace
“Muje ka shirya kada ka makara….”2
    Da taimakon Ramlah Imran ya shirya tana shirya shi tana tsokanar shi
“Kaga yanda kayi kyau? Gaskiya baka tab’a kyau irin haka ba”
Murmshi yayi yace
“Nagode..”
   Tana gama shiryashi ta feshe shi da turaren BOSS ORANGE wani k’amshi ke tashi mai sanya zukatan masoya..
    Tana gamawa ta kalleshi tace
“Allah yabada sa’a Allah yasa abokiyar arzikinka ce zaka auro Allah ya had’a kanmu Allah ya baka ikon yi mana adalci.”
Tunda tafara maganar yake kallon bakinta tabbas yasan maganar nan har zuciyarta suke..
   Rungumeta yayi yace
“Nagode mata tagari ked’in daban ce acikin mata..”
   Hannunshi taja har gaban k’ofa kana ta kalleshi tace
“Allah ya kiyaye”
Juyawa tayi da sauri kar yagane halin da ta shiga, har yafita yadawo hugging d’inta yayi ta bayya yace
“Nasan yanda kikeji Allah ya maki albarka”
Murmushi tayi ta juyo tace
“Amin”
Peck ya manna mata a kunci ya fita..
   Yana fita ta fad’a kan gado ta saki kuka mai tsuma rai, saida tayi mai isarta kana ta tashi tayi wanka ta fita cikin mutane aka cigaba da hidima…2
              *********
   K’arfe shida aka shigo da amarya gud’a kake taji ta ko ina sai habaici ke tashi Maryam k’awar Ramlah zatayi magana Ramlah ta hanata, haka suka k’araci habaicinsu babu wanda ya tanka masu, babu wanda yayi tunanin ya kawo amarya wajen uwargida..
   Abin ya k’ona ran k’awayen Ramlah amma tahana suyi magana, wata daga cikinsu tace
“Gaskia Ramlah hak’urinki yayi yawa”
Murmushi tayi tace
“Hak’uri ay baya yawa”
Haka suka dinga mita amma bata biye masu ba…1
     K’arfe goma aka rako ango, bayan yan rakiya sun tafi ya tara matanshi dan ya masu nasiha…
    Nasiha ya masu mai ratsa jiki yace
“Mufeedah kece k’arama ya zama dole kibi Ramlah banda matsala da ita dan haka indai kina sona to dole kiso uwar yayana bazan so wani ya wulak’anta taba. Kema Ramlah ki kama girmanki ki bata girmanta na k’awarki nasan banda matsala dake..”
Murmushi Ramlah tayi tace
“In shaa Allah bazaka samu matsala dani ba”
“Allah ya maki albarka”
Ya fad’a..
Mufeeda tace
“Nima banda matsala sai dai ban d’aukar raini..”
Kallonta Imran yayi yace
“Indai dan Ramlah za’ayi fad’a to baza’ayi shi ba nasan halinta.”
Tab’e baki tayi, ita dai Ramlah ido ne nata…
  “Honey tashi muje mu kwanta kasan nagaji”
Murmushin yak’e yayi
Dariya Ramlah tayi tace
“Ya kamata kam kuje ku kwanta..”
Mik’ewa tsaye yayi yace
“Saida safe Hayatie”
“Allah ya kaimu..”
Ta amsa
  Juyawa sukayi suka fita, Mufeeda ce ta dawo da sauri ta kalli Ramlah tace
“Ke matar kirki ko? Ana wani yabonki ana kod’aki hmmm soon zan maki illa sai na rabaki da mijin da kike tak’ama dashi ke gidan ma zan rabaki dashi sai na tarwatsa kanku inga ta yabonki..”
  Tana kaiwa nan tayi tsoki ta juya ta tafi….
Hmmmm ana wata ga wata, anya Mufeedah zatayi galaba akan wannan ma’auratan da suke san junansu? Kudai biyo Phirdaucee Jeeboh danjin wannan badak’ala….
  Da kyar ta ja k’afanta ta nufi d’akinta, bisa gado ta fad’a rajab tagumi tayi wasu hawaye suka dinga sintiri kan fuskarta.
“Me matar nan take nufi da maganganunta mike shirin faruwa dani? Kodai na kira k’awata na shaida mata halin danake ciki ne?”
Wata zuciyar tace mata karki saki kifara fad’ama kowa damuwarki saboda wata k’awar tafi guba zata iya kaiki ga halaka kuma wannan ay sirrinki ne adu’a zaki dage dashi in shaa Allah bazata tab’a nasara akanki ba….
   Hannunta ta d’aga sama tace
“Allah kada kaba wannan baiwar taka yin galaba akanmu Allah ka kare man mijina da yarana da ni daga sharrinta” shafawa tayi tare da yin tagumi..
   Saurin mik’ewa tayi ta fad’a toilet Alwalla ta d’auro tazo ta kabbara sallah tana idarwa tahau adu’a neman kariya bata bar kan dadumarta ba sai da tayi sallar asuba kana ta koma kan gado ba jimawa bacci mai nauyi ya d’auketa…2
     K’arfe goma ta diro daga kan kado toilet ta fad’a saida tayi wanka kana tafito tana fitowa ta shirya cikin doguwar rigan atamfa purple d’inki yayi matuk’ar karb’anta a jikinta ba wata kwaliya tayi ba asalima ba kwalliya take ba turare ta fashe jikinta dashi kana ta nufi d’akin yaranta koda taje ta tarda sun tashi da gudu suka k’araso gurinta
“Good morning Ammi”
Murmushi tayi tace
“Morning my pikins hope kun tashi lafiya?”
“Lafiya Lau”
Suka amsa mata
   Toilet ta shiga ta had’a masu ruwan wanka d’aya bayan d’aya tama yaranta wanka sai da ta gama da mazan kans tace ma Haneefa taje tayi itama ta shiryasu tsaf kana tace
“Muje parlour”
Suna isa parlour ta kunna masu cartoon ta nufi kitchen dan shirya breakfast…
                      ******
   Zaune yake kan gado yayi tagumi shidai yasan ba cikakkiyar mace ya sami Mufeedah ba amma kuma yakasa tsanarta, k’ofar toilet aka bud’e fitowa tayi da wani shu’umin murmushi yana ganinta yafara dariya ya ware mata hannu da gudu ta k’arasa wajenshi ya rungumeta kamar wani zai kwace mashi ita..
    K’arfe shad’aya suka fito daga d’aki ganin su Ramlah parlour yasa Mufeedah k’ara shige mashi, shiko kunya duk ta kamashi saboda yanda Haneefa ke kallonsu, k’arasowa yayi wajensu ya kalli Ramlah yace
“Morning Angel”
Murmushi tayi tace
“Ango kun tashi lafiya?”
Had’a hannuwanta yayi yace
“Lafiya lau”
Juyowa yayi ya kalli yaranshi gaba d’aya sukace
“Morning Daddy”
Murmushi ya sakar masu ya rungumesu tare da yima kowa peck …
   Duk abinda akeyi Mufeedah na tsaye tsanar Ramlah da yaranta ta k’araji a zuciyanta
“Soon zan tarwatsa wannan family”
Abinda tace a zuciyarta kenan
    Imrah yace
“Bakiga Angel ba? Banga kin gaidata ba”
Wani takaici ya kamata tace
“Hmm zanyi maganinku”
A zahiri kuma tace
“Naga kuna magana shiyasa”
   Bai k’ara magana ba ta zube k’asa tace
“Anty ina kwana?”
Da far’anta ta amsa
“Da lafiya lau antashi lafiya ya kwanan bak’unta?”
“Lafiya lau ta amsa”
   Juyawa tayi kan yaran kafin tayi magana sun gaidata, banda Haneefa data cika ta batse
   A hankali Ramlah tace
“Princess baki gaida Mammy ba?”
Da kyar ta bud’e baki ta gaidata
“Zakici ubanki yarinya”
A zahiri ta amsa cikin sakin fuska tace
“Babyn tawa miskilace”
Hameef yayi sauri yace
“Haka take Mammy batasan yin magana”
Kafin su k’ara magana Ramlah ta kallesu tace
“Breakfast  is ready”
Gaba d’ayansu suka nufi dainning danyin kalaci..5
    Abinci sukeci suna fira banda Haneefa wanda ta had’e rai abincin ma da kyar take taunashi..
   “Yarinyar nan zatayi taurin kai amma zan gyara mata zama”
A zahiri kuma tace
“Babynah yana ga baki cin abincin?”
Banza tayi da ita ta kyale sanin halinta da Ramlah tayi bazata tanka ba tace
“Haneefa bakijin Mammy na magana?”
  D’agowa tayi da runanun idanuwanta tace
“Banjin dad’ine”
   Nanfa Imran ya rud’e dan duk duniya bai had’a yaranshi da kowa ba
“Babyna mike damunki gayaman kinji”
Dariya tayi tace
“Calm down Daddy ciwon kai ne kuma yayi sauk’i”
Ajiyar zuciya yayi yace
“Har naji sanyi “
Tab’e baki Ramlah tayi dan dama tasan k’arya Haneefa takeyi dan tasan lafiyarta lau. Murmshin takaici Mufeeda tayi a ranta tace
“Wannan rawan kan da yakeyi kanku nan bada jimawa ba zai tsaneku tsanar da ko hanya yaganku bazai nuna ya sanku ba…
    Haka suka k’arasa cin abincin suka dawo parlour….2
     Imaran yace
“Mufeedah ga yara na nan wannan sunanta Haneefa shekaranta gona tana primary 5 shikuma mai bita shekaranshi bakwai yana primary 3 nd sai d’an Auta Mukhtar shekaranshi hud’u yana primary 1 duka suna school a Hope intenational school i hope zaki rik’esu kamar yaranki..”
    “Mufeda?”
Ni zai kira da Mufeeda gabana yake kiran shegiyar matarshi Angel amma ni Mufeeda zakuyi danasani ku duka..
    Zahiri kuma tace
“Allah ya masu albarka in shaa Allah zan rik’esu kamar yarana”
Murmushi yayi yace
“Nagode”
Ya juyo kan yaran yace
“Mufeeda kece babba dan haka ga Mammy nan kamar yanda naji Amminku tace ku kirata kuyi mata biyayya kamar yanda zakuyima Ammi kece babba duk abinda kikayi shi k’annenki zasuyi thou banda matsala daku I trust you yarana nasan zaku mata biyayya..”
    Itadai Haneefa batace komai ba haka kuma bata d’aga kai ta kallesu ba dan gaskia tun da taga Mufeedah taji ta tsaneta bata kwanta mata ba….
   A hankali ta d’ago tace
“In shaa Allah Daddy zamu kwatanta”
“Allah ya maku albarka”
Suka amsa da
“AMIN”…Kallonshi Mufeedah tayi tace
“Honey muje mud’an huta ko?”
Dariya yayi yana sosa kai yana kallon Ramlah murmushi tayi tamashi alama da ido alamun sutafi…
   Kyam idon Mufeedah akansu, wani malalacin murmushi ta saki ta k’ara narke murya
“Honey pls tashi muje wallahi nagaji kasan jiya kaban wahala”
Dum yaji abu har cikin ranshi
“Wannan wace irin mata ce haka? Shin bata ganin yaranshi take wannan maganana”
Amma a zahiri murmushi yayi ya mik’e tun kafin ta k’ara sako wata maganar…
Ita dai Ramlah bata ce komai ba sai ma murmushi da ta sakar masu..2
    Har sun kai bakin k’ofa ta juyo ta masu wani kallon kun kusa zama abun tausai kana ta shige d’aki…
    Hankalinta Ramlah ta maido kan yaranta tace
“Kuje d’aki ku kunna tv amma ke Haneefa ki tsaya zanyi magana dake..”
   Ba musu suka mik’e suka nufi d’akinsu, sai data ga sun shige kana ta maido hankalinta wajen Haneefa..
“Miyasa kikamata haka? Shin tarbiyar da muka baki kenan?”
Cikin rashin fahimta Haneefa tace
“Wake nan?”
Murmushi Ramlah tayi dan tasani sarai ta gane watake magana amma tasan miskilancin ta bazai bari ta nuna ta gane ba..
“Mammy nake magana miyasa zaki mata haka? Itamafa mamarkice saboda Babanki ya auro ta kingako ay tazama Uwa wajenku..”
D’agowa Haneefa tayi tace
“Ammi baki lura da yanayin matar ba? Nikam gaskia bataman ba”
Bige bakinta tayi tace
“Karna sake ji kince bata maki ba kimata biyayya kamar yanda zakiman kinajina?”
D’aga kai tayi murya sanyaye tace
“Naji Ammi”
Allah ya maki albarka tashi kije kiyi muraji’a kafin lokacin Islamiyya yayi. Tashi tayi ta nufi d’aki a ranta tana sak’a yanda zata ma matar nan dan muddin bata bari taci zarafin Amminta kuma da alamu matar zatayi rashin mutunci…
                     ******
   “Gaskia banji dad’i yanda kike maganganu gabansu Haneefa ba yara nefa mikike so su d’auka?”
Imran ne kema Mufeedah magana..
   Turo baki tayi tace
“Minayi? Ina cewa da mijina nake magana”
Tana magana tana cika tana batsewa, ganin tana fushi yasa duk ya daburce ya shiga lallashinta da kyar ya samu ta sauko..
  Ajiyan zuciya yayi yace
“Nagode”
Murmushi tayi ta fara shafoshi ganin abinda take shirinyi yasa ya mik’e yace
“Bari naje naga abokina”
Bai jira mi zata ce ba yayi waje..
   Kitchen ya sameta da sand’a ya shiga idonta ya rufe kamshin turarenshi yasa ta saki murmushi tace
“Hayatee”
Kwantar da kanshi yayi a bayanta ya kai minti 5 a haka baice komai ba.
“Yadai?”
Abinda tace kenan, ajiyan zuciya yayi yace
“Nothing”
Juyowa tayi ta suna kallon juna murmushi ta sakar mashi tace
“Ina baccin?”
Hancinta yaja yace
“Zanga Ahmad ne”
“Ok”
Hugging d’inta yayi tare da mata peck a kunci yace
“Saina dawo”
“Allah ya dawo dakai lafiya “
Ta bashi amsa, kai yasa ya fita a bakin kitchen yaci karo da Mufeedah murmushi ta sakar mashi sosa kai yayi yace
“Ya akai kika fito?”
Dariya tayi tace
“Nazo taya Anty aiki ne”
Dad’i yaji ya mata peck yasa kai ya fita, cikin kitchen d’in ta k’arasa
“Ke k’aramar karuwa”
Da sauri Ramlah ta juyo tana kallonta
“Eh dake nake ubanmi ya had’aki da mijina? Ai kinsan daga nan har tsawon kwana bakwai yana tare dani amma shine dan munafunci saida kikasan yanda kikayi kika jawoshi jikinki wallahi zaki gane kurenki saina dasa mashi tsanarki dagake har shaggun yaran da kike tak’ama dasu….”
   Tun da take magana Ramlah bata ce mata komai ba har tagama, juyawar da zatayi taga Haneefa tsaye tana mata kallon tsana
“How dare you zaki dinga kiran Mahaifiyata da munanan kalamai haka? Miki keji dashi ne kodan kinga tana hak’uri kwana d’aya da zuwanki kina neman tarwatsa mana gida mikike tak’am……”
  Tsawar da Ramlah ta matane yasa tayi shiru da bakinta..
    “Dake take? Ko kuwa sa’arkice ita?”
Duk’a ki bata hak’uri, turo baki Mufeedah tayi tace
“Kiyi hak’uri”
Murmushi tayi ta dafa kanta tace
“Karki damu yantama da sannu zan maidaku abun tausai dake da uwartaki..”
Tana fad’ar haka tayi d’akinta..
   K’arasowa Haneefa tayi cikin kitchen tace
“Ammi saikin aje hak’urin ki indai baso kike matar nan tayi galaba akanki ba..”
Tana fad’ar haka ta juya tayi d’akinsu cike da takaici….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page