IN SO YAKI NE CHAPTER 9

IN SO YAKI NE CHAPTER 9

  horn tayi a wani d’an madaidaicin gida ba b’ata lokaci mai gadi ya lek’o, yana ganin ita ce ya washe hak’ora yana dariya har jiki na rawa ya bud’e k’ofar “Barka da zuwa Autar Hajiya barka da shigowa, ita ma Meenah murmushin tayi masa sannan tace “Yawwa sannu baba” nan suka gaisa sannan tayi parking motar ta shige cikin gidan, babu kowa a falo sai tv dake ta aiki, k’amshin abinci da ta jiyo ne yasa ta nufi kitchen da gudu.. Wak’ar ta take tana yankan alayyahu bata ankara ba taji an rungume ta, wuk’ar ta ajiye tace “YAA SALAAM!” Kukan Meenah da taji ne yasa ta sake tsorita da sauri ta zame daga rik’on da tayi mata sannan ta juyo tana kallon ta, kafad’un Meenah ta rik’e ta jijjiga ta tace “Ke! Miye hakan? Wani abun ne ya faru? Ina Suraj d’in? Me ya saka ki kuka? Ba yanzu muka rabu da ke ba a asibiti? Kodai ciwon naki ne ya tashi?” shiru Meenah tayi kai a k’asa bata bada amsa ba don haka matar ta juya ta kashe hotplate da take girki sannan ta ja hannun Meenah zuwa falo, da kyar Meenah ta kwashe labarin abunda ke faruwa ta sanar da ita sannan ta cigaba da cewa “Aunty fatima me yasa bazan d’aga hankali na ba after all Laylah yanzun haka ta dawo, in tak’aice miki ma har sun had’u ni ba wannan ne yafi damu na ba illa yanda Suraj ya dubi fuska na yace wai har yanzu yana k’aunar ta, why is he so selfish? In yana k’aunar ta ni kuma fa? What about me!”. Murmushi Aunt Fatima tayi sannan ta rik’e hannun Meenah tace “Suraj is not the one selfish Meenah you are….. A yanda kika labarta min yanzu ke ce kike son kanki da yawa, ina so karki manta matsayin da kike lokacin da Suraj ya aure ki, you are the one in love with him from the beginning, yabi umarnin Mahaifiyar shi ya aure ki, bai tab’a complaining ba, yau shekara uku kin yi iya k’ok’arin ki amma baki yi nasarar sace zuciyar shi ba se yanzu, ke da kanki d’azu da kika iske ni a asibiti farin cikin ki baya misaltuwa saboda kinga chanji daga wajen Suraj, don haka idan Suraj yace yana k’aunar Laylah ba yana nufin zata maye gurbin ki bane besides ke da kanki kin tabbatar cewa yanzu ita matar aure ce, zai je ya d’auke matar wani ne?” Kai Meenah ta girgiza sannan tace “Aunty believe me idan de Suraj ne zai iya d’auke ta d’in ma, domin kuwa he is the type that never gives up on something he loves, ni yanzu yaya zan yi Aunty?”.+ Aunty Fatima ta d’an yi shiru na wani lokaci kafin ta d’ago kai ta dubi Meenah tace “Kina sane cewa ba isasshen lafiya ne gareki ba, on top of that ga k’aramin ciki, kuma kin min alk’awarin zaki kula da kanki Meenah! Yanzu kukan da kike yi zai chanja komai ne? Na tabbata baki sanar da Suraj komai game da pregnancy d’in ki ba, ban san dalili ba amma kina kuka akan macen da bata da hurumin shiga rayuwar ki ko na Suraj a yanzu. Meenah pls kiyi hak’uri ki koma ki samu Suraj ki bashi hak’uri in kuma ba haka ba zan sanar da shi cutar da kike b’oye masa”. Zubewa Meenah tayi k’asa tana girgiza kai tana fad’in “No……No Aunty please kar ki sanar da shi, idan Suraj ya fahimci cewa ina d’auke da cutar CANCER, Na tabbata hankalin shi zai tashi sannan soyayyar da ya fara nuna min zata dawo tausayawa, bana son hakan ta faru, na sani cewa Ciwo na ya kusa kai wa last stage, ina so in k’arashe sauran lokacin da ya rage min a duniya tare da soyayyar Suraj ba tausaya wan shi ba, wannan cikin dake jiki nah ina so in haife shi ko da zan rasa raina in the process, idan kika sanar da Suraj ya fahimci illar da ajiye cikin yakeda a gareni na tabbata zai ce a zubar, Aunty you promised me bazaki fad’awa Suraj ba gameda cancer da nake da shi please keep your promise nima nayi miki alk’awari bazan tab’a gazawa ba wajen kyautata wa Suraj, da kuma nema mishi farin ciki ko da hakan yana nufin Laylah ce farin cikin nashi”. Guntun Hawayen da ya gangaro Aunty Fatima ta goge daga fuskar ta sannan ta d’ago Meenah ta zaunar da ita bisa kujera tace “That’s my beautiful sister, dole zaki min wani alk’awarin ma”. Kai Meenah ta d’ago tana kallon ta “Ki min alk’awari duk situation d’in da kika tsinci kanki kada ki yawaita b’ata ran ki domin hakan zai iya triggering ciwon ki at any moment, sannan a wannan lokacin Suraj zai iya gano matsalar ki, kuma maganin da na baki kar kiyi skipping ko da rana d’aya ne”. Kai Meenah ta jinjina tana murmushi tace “Aunty Yunwa nake ji ban ci komai ba tun safe, kai Fatima ta girgiza tace “Kar ki damu yanzun nan zan kammala girkin, i’m cooking your favourite” Da sauri Meenah ta d’ago kai tace “Potato porridge?” kai Aunty ta jinjina sannan ta nufi kitchen don k’arasa girkin ta……… 10:00pm…. Daga wanka ta fito d’aure da pink towel jik’akk’en gashin kanta a barbaje se d’igan ruwa yake. gado ta kalla taga Tasleem na barcin ta peacefully don haka ta bud’e k’ofa ta fita zuwa downstairs don haka kawai taji kwad’ayin tasha tea mai kauri, Tun da tasa k’afa ta d’auki step d’aya daga bene yake kallon ta, ko kyafta wa baya yi, har ta shige kitchen, bai ankara ba saida coffee mug d’in da ya rik’e ya karkace hot coffee ya zube masa a jiki, da sauri ya ajiye kofin yana tub’e rigar yayi wurgi da ita. Kitchen d’in ya nufa ya ajiye mug d’in. A d’an tsorace ta juyo ta kalleshi, ganin bashi da riga yasa tayi sauri ta d’auki kofin tea d’in ta juya ta bar masa kitchen d’in, tana tafe tana hard’e wa har ta kai k’ofar d’aki sannan ta juyo taga bai biyo ta ba don haka ta sauk’e nannauyan ajiyar zuciya ta shige ciki. Saida ta gama shan tea d’in ta ajiye cup sannan ta zira kayan barcin ta. Bata ankare ba taji ya bud’e k’ofa ya tsaya yana watsa mata wani miskilin kallo. Da sauri ta mik’e ta tsaya kallon shi har had’iye miyau take don ta san halin shi sarai. Dariya yayi har da chocking sound cike da isa ya k’araso daf da ita yana k’are mata kallo, tun tana kallon fuskar shi har ta sunnar da kai k’asa tana fiffigan rigar ta “seems like kwanakin nan you have been enjoying yourself, se wani k’ara kyau kike yi, miye sirrin ne? Look at the sparkle on your face! Mrs Muhseen…..answer me! Are you by any chance pregnant?……” Wani irin bugu k’irjin ta ya fara murya na sark’afe wa tace “What?….no…. Ni bani da wani ciki, it’s just yanayin garin.” Dariya ya sake yi ya dubi Tasleem dake kwance sannan ya kad’a kai ya juya ya fice, da gudu ta bi bayan shi ta gark’ame k’ofar da key sannan ta dafe kirji tana haki. ***** ****** ****** Yana kwance ta shigo d’akin, a tunanin ta barci yake yi don haka ta wuce bathroom, saida ta yi wanka sannan ta fito tana tsane jikin ta saida ta zauna gaban mirror ta fahimci idonsa biyu kallon ta yake, sauri ta juya suka had’a ido, tashi yayi daga gadon ya nufi bathroom ba tare da ya kula ta ba, da sauri ta mik’e tana kallon shi har ya shige, ai kuwa yana fito wa ta rungume shi ta baya tana kuka, “Suraj please kayi hak’uri abunda na maka d’azu i know i was wrong ban san dalilin da yasa na……. Bata k’arasa ba ya rik’e hannuwan ta ya juyo ya fuskance ta sannan yace “it’s alright Meenah, ya wuce besides kina da daman nuna b’acin ranki, but ina so ki sani no matter how much i need Laylah yanzu tayi min nisa so relax, ki sa kaya ki zo mu kwanta already dare yayi”. Ya k’are maganar yana k’irk’iro murmushi cikin zuciyar shi kuwa raya mar take cewa komai wuya sai ya dawo da Laylar sa…… Murmushi tayi sannan ta nufi wardrobe ta d’auko kayan barcin ta ta zira sannan ta haye bisa gado.Tun around 7:30 na yamma bak’i suka fara isowa, kuma duk acikin su babu na yar wa domin kuwa they are Nigeria’s top enterpreneurs, kafin kace me har tafkeken Living room d’in ya cika da surutai, sai mata dake ta showoff ma junan su kowacce tana tunanin ita tayi fice, tuni aka fara serving drinks and snacks Habeeb da khadija ne suka shigo sannan Ameer da Mubeenah dukannin su sun sha kyau kam ba k’arya, kwata kwata couples takwas ne in total suka zo ya rage Safwan da kuma Muhseen da matan su. Shi kanshi gogan bai bayyana ba har yanzu sai su Habeeb dake ta chatting da bak’in ana ta raha. Ba jima wa Sufyan Khalil da matar shi Zarah suka k’araso (come see ado a gun zara ) nan ta shige cikin matan aka cigaba da bud’e chapters. Tun daga mota ya wani janyo ta jikin shi yana zuba mata uban warning Har suka shiga ciki, a bakin k’ofa suka had’e da Habeeb nan ya tarbe su yayi musu iso, kallon kallo Laylah suke da Habeeb har idanuwan ta sun cicciko, khadija ta lura da haka sai ta dafe k’afad’ar Habeeb tace “Honey please ko da sau d’aya talk to her, na tabbata tana son tayi magana da kai. a baya baka bata dama kun yi magana ba this is not right ko ka k’i ko ka so tunda ita d’iyar uncle Rasheed ce ta zama y’ar uwar ka tunda kamar yanda ka fad’a uncle Rasheed k’anin Abba ne (mahaifin Habeeb).” Shiru Habeeb yayi ba tare da ya ce k’ala ba ya cigaba da kallon Laylah wanda Muhseen ke jan ta tamkar rak’umi da akala kawar da kanshi yayi da murmushi ya bar wajen Khadijah ta bi shi da kallo.+ Zaune take bakin gado ta kafe shi da ido tana murmushi kamar zata had’iye shi, basar wa yayi duk da ya ganta daga madubi yacigaba da gyara necktie d’in shi. “Suraaj……” ta k’ira sunan shi cikin salon tambaya “Hmmm??” Ya amsa a tak’aice ba tare da ya juya ko barin abunda yake ba. Mik’e wa tayi tana fad’ad’a murmushin ta cikin sand’a ta rungume shi ta baya hannuwan ta a k’irjin shi tace “Did u remember shekaru uku a baya? No……. Sati biyu ma da suka wuce baka yanka min ticket d’in shiga d’akin ka ba, ko kasance wa kusa da kai talkless of being intimate with you…. A wancan lokacin ganin ka nake as rude and cruel, duk da ma dai i did not give up despite your attitude towards me, now i see the result kuma har in bar duniya bazan manta da wannan soyayyar ba da ka nuna min, i have no regret whatsoever just promise me you will always love me Suraj…. For the sake of our unborn baby……” Da sauri ya juyo fuskar shi d’auke da mamaki a shimfid’e yace “Baby? What baby?” Murmushi Meenah tayi sannan ta shafa kan tumbin ta tace “Yes Baby, our baby Suraj…….. We are going to have a baby” Wasu hawaye ne suke neman gangaro masa yayi saurin shanye su da sauri yayi hugging Meenah, duk da yana farin ciki amma sai yake tuna moment d’in da ya fara jin irin wannan albishir d’in shekaru bakwai da suka wuce, murya ciki ciki yace “thank you Meenah…..you have made me extremely happy today, kin min babban albishir, ki tambaye ni duk abunda kike buk’ata i will gladly give it to you” Murmushi tayi sannan tace “Ofcourse ina da abunda nake so daga gareka but kar ka manta watarana zan tambaye ka idan lokacin yayi keep that in mind for now Lets go downstairs i’m sure bak’in sun iso”. Kai ya jinjina ya kama hannun ta suka nufi downstairs. Tun da suka sa k’afa suka d’auki step na farko take kallon su. Hannun Meenah ta gani cikin na Suraj hakan yasa ba shiri ta mik’e k’irjin ta na dukan uku uku. Hannuwan ta har rawa suke suna karkarwa numfashin ta na neman d’auke wa. Bata ankara ba taji Muhseen ya chafko hannun ta ya ja ta zuwa inda Suraj ke tsaye da Meenah suna gaisa wa da Sufyan. Dariya Muhseen ya fara ya ware hannuwa suka yi hug da Suraj, se lokacin ne Meenah taji Suraj ya ce “Muhseen…..”. Wani bomb taji ya fashe a k’ijin ta a lokacin ne ta d’ago suka yi ido hud’u da Laylah, nan Muhseen ya yi introducing Laylah wanda tuni idanuwan ta sun sauya launi, wutar da ke ruruwa a cikin jikin ta ne yake k’ara k’arfi, ji tayi babu abunda take gani a wajen se duhu da ya mamaye ko ina, da kyar ta iya daidaita kanta sannan ta saki murmushi wanda yafi kama da na dole sannan ta ce “Hi ” a tak’aice. Duk k’ok’arin Suraj na ganin ya had’a ido da ita ya ci tura, ji yake tamkar zuciyar shi zata fasa ribs d’in shi ta fice tsabar yanda take racing da beat d’in shi, da sauri Suraj ya dafe k’irjin shi, Murmushi Meenah tayi irin na helpless person ta kamo hannun nashi ta damk’e da kyar ya shanye emotions d’in shi ya dubi Meenah. Duk da Laylah kanta a k’asa hankalin ta a mugun tashe yake ganin yanda hannuwan su ke sark’afe da na juna. Suraj’s POV “Laylah…… We are in this mess because of you, you did’nt give me a chance to make things right instead you chose divorce, gashi yanzu ina tsaye a gabana wani daban yana rirrik’e ki, i know gani na da Meenah will make you feel just the way i am feeling, but this is all your fault! It’s all your bloody fault Laylah sannan bayan duk abunda ya faru i don’t know why i still love you even more than my life! Why did you leave me Laylah??” Laylah’s POV Daren yau ya kasance d’aya daga cikin dararrukan da nayi dana sanin kasancewa a raye ballantana na gan su, My only love is standing in front of me holding hands with another woman and loving her the way he is supposed to love me, yaya zan yi da raina? Why is it me that has to suffer all the pains? Firstly ka sake ni and now you are married, what about me Suraj? Yaya zan yi?…… Waiter ne ya taho d’auke da tray na drinks ya nufo inda suke, suraj ya dubi inda waiter ke tsaye kusa da Laylah sai ya saki murmushi a ranshi yace “Laylah we need to talk”. Da gangan ya sa hannu zai d’auki glass d’in juice sai ya buge tray d’in duk ya kwarara mata lemukan a jiki tsabar sanyi da taji yasa ta d’ago da sauri suka yi ido hud’u da Suraj, da sauri ta maida duban ta ga gown d’in nata taga irin mess d’in da ya tafka mata Shi kuma sai ya wayince yace “Oh no! Really sorry mrs Muhseen sorry about that! Please go upstairs and clean up this mess” Wani shu’umin murnushi Muhseen yayi wanda shi kad’ai ya san ma’anar hakan sannan ya saki hannun Laylah ta rik’e rigar tana kallon ta’asar da Suraj ya aikata sannan ta rab’a gefen shi ta wuce zuwa upstairs duk suka bi ta da kallo shi kuwa Suraj hankali kwance ya juya yana dariya. Habeeb ya ga duk abunda ya faru kuma bai nemi ya dakatar da Suraj ba domin ya san Halin d’an uwan nashi idan ya kafe a kan abu to mai hana shi sai ya dage tukunna……..Tana k’ure stairs ta sa gudu, wani d’aki ta bud’e ta shiga bata ma lura ba da d’akin ta bud’e k’ofar bathroom ta shige, numfashin ta sama sama yake fita tana k’ok’arin danne kukan da ya taso mata amma sai ta tsinci kanta da kasa wa don haka ta fitar da kukan mai d’auke da sauti, dafe basin d’in bathroom d’in tayi tana k’are wa kanta kallo a makeken madubin dake manne a bango, ita bata wanke stain d’in lemon ba sannan bata bar kukan ba…. Cikin taron dake wajen Suraj ya saci jiki ya nufi upstairs duk da Muhseen ya ganshi amma sai ya saki Murmushi ya zaro wayar shi daga aljihu ya fice daga party d’in ganin haka yasa Ameer ya bi bayan shi domin tun farko bai yarda da Muhseen ba…….+ Har zai wuce d’akin shi sai ya jiyo sheshek’ar kuka kasance war bata tura k’ofar bathroom d’in ba don haka kai tsaye ya bud’e d’akin ya kutsa kai, ya dad’e tsaye yana sauraron kukan nata wanda ke tsuma rai kafin ya shige washroom d’in ya d’auki k’aramin towel ya mik’a mata. A d’an tsorace ta juyo har saida ta rasa balance zata kai k’asa yayi saurin rik’o ta, jikin ta har rawa yake da taji k’ak’arfan rik’on da yayi mata, d’an ratan dake tsakanin k’irjin shi da nata yasa takan ji yanda zuciyar shi ke buga wa, numfashin su na gauraye wa , na wasu dak’ik’ai babu wanda ya motsa tsakanin shi da ita ,yanda ta kafe shi da ido haka shi ma ya kafe ta da ido, saida wayar shi tayi k’ara tukunna Laylah ta kyafta idanuwa da sauri ta fisge jikin ta tana gyara mayafin kan ta, murya a dishashe ta ce “Excuse me?” Shima hannuwan shi ya sauk’e yana kallon gefe trying to hide his tears “Sorry”. Ya fad’a murya ciki ciki sannan ya juya ya koma cikin d’akin ya tsaya, ruwa ya hango a glass da sauri ya d’auka ya kafa a baki saida ya shanye tas sannan ya ajiye glass d’in amma har lokacin jikin shi bai bar karkarwa ba, bakin gadon shi ya nema ya zauna yana bubbuga k’afa very anxiously lokaci zuwa lokaci yana furzar da isaka daga bakin shi Saida ta kammala goge stain d’in ta fito tana wasa da y’an yatsun ta, da sauri tana k’ok’arin fice wa daga d’akin shima da sauri ya mik’e ya tare ta “Laylah!” ya k’ira sunan ta, katse shi tayi ta hanyar cewa “Suraj bai dace ba, its inproper mu keb’e a nan, remember we both are married and we have nothing to discuss about, kar ka hanani fita please kafin matar ka ta gan mu tare i’m sure bazata ji dad’i ba.” bai tanka mata ba ya matsa ta wuce sai ya saki murmushi shima ya fice, da sauri take tafiya har k’afar ta yana sark’afe wa, yana tsaye bakin k’ofa yana kallon ta har saida ta kusa yin corner ya sa hannu ya danna switch d’in wuta ya kashe, bata ankara ba taji an fisgo ta ido ta k’ank’ame tsabar tsoro bata ma san inda aka yi da ita ba. Wani d’akin na daban ya kai ta sannan ya rufe k’ofar da key ya cusa cikin aljihun sa sai ya nemi bakin gado ya zauna yana kallon ta “zaki iya bud’e idanuwan ki Habibtyy” A tsorace ta bud’e idanuwan nata ta zaro su, ganin Suraj da tayi kishingid’e a bakin gado yana sakar mata wani shu’umin murmushi. Da sauri ta juya ta nufi k’ofa tana k’ok’arin bud’e wa amma ta kasa shi kuwa hankali kwance yana k’are mata kallo, juyo wa tayi tana kallon shi cike da mamaki sai lokacin yace “Na rufe k’ofar ai, look Laylah! Duk yanda kikayi k’ok’arin guduwa kina k’in gaskiya babu inda zai kai ki, na kawo ki nan coz ina da tambayoyi da dama da nake buk’atar amsar su kuma duk duniya babu inda zan samu amsar in ba a wurin ki ba so speak up! Tell me……me na rage ki da shi? Me nayi miki da har tsana ta zai sa ki nemi takardan saki daga gare ni? I have always loved you and all of a sudden kika sauya.” Tuni idanuwan ta suka kad’a ta d’ago tana kallon shi “ni na nemi ka sake ni Suraj? Ni? Shin ka san irin halin da na shiga lokacin da na fahimci cewa ka zab’i ka rabu da ni? Ka san tsawon lokacin da na d’iba ina jiran ka Suraj? A k’arshe de ka yanke hukuncin da kaga ya dace so yanzu me kake nema da ni? Ni ka barni na tafi My husband might be worried”. Wurgi Suraj yayi da wayar sa har saida Laylah ta durk’usa k’asa tsabar tsoro “MY HUSBAND! My Husband !My Husband!!…… Listen carefully Laylah idan ina magana da ke kar ki sake yi min zancen wancan mahaukacin if not i will……..” kasa k’arashe maganar yayi ganin duk ta bi ta rud’e ta kafe shi da idanuwa, ya koma bakin gado ya zauna ya rik’e kai yana sauk’e numfashi ba tare da ya d’ago ba yace “Tell me the truth Laylah me ya faru da kika tafi? Me yasa kika zab’i ki rabu da ni?”. A gadarance ta juya kai gefe tana cewa “you can kill me if you wish but i will not tell you anything besides kai ne ka zab’i ka rabu da ni, zab’in ka ne saboda haka i don’t care. Kuma babu abunda zaka iya yi a kai”… Dariya yayi har yana shid’e wa ya dube ta yace “Akwai abunda zan iya yi Laylah”…. A tsorace ta d’ago har tana k’ink’ina tace “W….wa….what will you do??” Mik’ewa Suraj yayi yana tunkarar ta ita kuma ganin haka yasa ta fara ja da baya bata ankare ba tayi ta bugu da k’ofa gashi ya iso daf da ita sannan ya sa hannuwan sa ya tokare duk gefe da gefen sannan ya saki Miskilin Murmushi cikin sassanyar Murya yace “Here’s what i am going to do, kinga de babu kowa a d’akin nan daga ni sai ke and there is no other way to escape so idan baki fad’a min amsar tambaya ta ba i will…….” K’ank’ame ido tayi tana jiran taji k’arshen statement d’in nashi shi kuwa sai yayi shiru hakan yasa ta bud’e manyan idanuwanta ta ajiye su kan fuskar shi murya ciki ciki tace “What will you do?” Murmushi yayi sannan yace “idan baki fad’a ba i will……Rape you!!” Ihu ta saka wanda ya sa saida Suraj ya rufe ido yana ta dariya saboda sosai ta bashi dariya, Ja yayi da baya yana kashe mata ido hannun shi d’aya kuma yana cire bottons d’in rigar shi, nan da nan Laylah ta sake kid’ime wa ta sa ihu “Scream all you want baby! Babu wanda zai ji ki!!…kina da option, tell my why you chose to leave me ko kuma in yi abunda nace zan aikata a kan ki, and remember d’akin nan ko zaki shekara d’ari kina ihu babu wanda zai ji”. Jin haka ya k’ara tsorita Laylah tace “ni na fad’a maka Suraj i loved you more than my life bazan tab’a yunk’urin rabuwa da kai ba, Abba na shi ya kawo min takardan saki kuma Lawyers sun shaida kai kayi signing da kan ka, did you know how shattered i was? Na farko na haihu baka ko kallon d’iyar ka baka yi ba, we have waited for you Suraj har yanzu Tasleem bata san menene dad’in mahaifi ba, you have done a grave injustice to your own daughter and wife” Hawaye ne ke gangaro masa yana kallon Laylah yace “My daughter? ….. Cike da mamaki Laylah tace “Ya dai? Ya kake acting as if kana mamaki? Why are you behaving as if Abbah na bai sanar da kai cewa na haihu ba? Or are you surprised that we managed to survive without you?”. Kai Suraj ya girgiza yace “Idan Abban ki ya sanar da ni me zai hana ni zuwa? Sau nawa nake k’iran ki? Sau nawa Laylah? Daga bisani ma layin naki daina tafiya yayi, just with a blink of an eye! Na rasa komai nawa! Duniya tayi min zafi sannan speaking of divorce ni bani ne na buk’aci saki ba Abban ki ne ya turo Lawyers cewa in ban rabu da ke ba zaki yi sue d’in mu a court wanne option nake da shi Laylah? Cewa nayi tunda saki kika zab’a i am sure shine mafi alkhairi bazan takura miki ba with your decision”. Zame wa k’asa tayi tana kuka shima ya zauna ya jingina da bango yana kuka sai kuma ya mik’e ya nufi k’ofar ya bud’e nan ya fice ya barta a wajen tana ta fama, saida kukan ya ishe ta sannan ta bud’e bathroom d’in d’akin ta wanke fuskar ta, makeup tayi applying sannan ta fito ta nufi downstairs inda har an zagaye luxurious dining table za’a fara cin abinci baka jin komai se k’aran silver spoons da glasses se kuma chatting d’in bak’i k’asa k’asa. Muhseen baya wajen don haka ta ja kujera ta zauna tana k’irk’iro murmushi……….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page