ITACE QADDARATA CHAPTER 1

ITACE QADDARATA CHAPTER 1

BISMILLAHIR-RAHMANIRRAHEEM* *Dukkan yabo da godiya, suntabbata ga ubangijin talikai, ubangijin rana da wata, mai tsiro da tsirra akan ‘kasa, mai rayawa da kashewa adukkun sanda yaso* *Allah kai dad’in tsira da aminci abisa shugabanmu annabi Muhammad (S.A.W) da ahalinsa gidansa da sahabansa, da manzanninmu,* *Ya Allah kabamu ikon rubuta labarin nan, ka kuma bamu ikon kammalawa lafiya kuskuren dake ciki Allah kayafe mana, abinda yake dai-dai Allah kasa ya amfani al’umma amin*+ *Wannan novel ‘ka gaggen labarine, bamuyi shi dan wata kowaniba, idan abinda muka rubuta yayi dai-dai ga rayuwar ki/ka kuyi ha’kuri daga idea ne balaifin writers ciki* >>>>>>>><<<<<<<<<<<< Tafe muke nida Qurratul-ayn, tunaninmu yau kuma ina zamuje samo muku 'kaya taccen labari. Wani layine da muka, shiga yaja hankalinmu, domin tsarukan gidajen layin abin kallone, wucewar da zamuyi ta jikin wani gida da 'kofar gate d'in ke bud'e, Qurratul-ayn ce tata'boni tana fad'in "Zee Yabour kalla kigani, da alamu akwai labari agidannan" najuyo da sauri ina kallon 'kofar gate d'in, danni da nasaki baki da hanci da ido ina kallon wani gida, daya tafi da dukkan tunanina. Wata matashiyar yarinya ce nagani, kyakkyawa fara sol, da ba zata wuce shekaru goma sha shida da haihuwa ba, ri’ke da tiyo a hannunta, tana bawa flowers dake garden ruwa, Kayan jikinta duk sun yayyage sun tsufa daga gani sun ji jiki, Wa’ke-wa’kenta kawai take, kai kace babu abinda ke damunta arayuwarta. Zulum! Zulum!! Faqeer!!! Faqeer! taji muryar mahaifinta na kira. “Na’am Daddy” ta amsa cikin sanyin murya. “Kina ina? zo nan” mahaifin nata yafad’a. Tayi saurin yar da tiyon, dake hannunta jiki na rawa taje ta dur’kusa gabanshi, kanta sunkuye ‘kasa, tana kallon ‘kasa, bata ta’ba bari su hada ido, tun wata rana da by mistake suka hada ido ya Wanketa da mari yace shi sa’anta ne, da zata hada ido da shi, tun lokacin take tsoron had’a ido dashi. Dadyn nata Yace “kalleta sumi-sumi kamar ta Allah, ba kiran ki nayi kizo ki du’ka mun, kamar wata mai neman gafara ba, na kira ki ne na gaya miki ki had’a yan tsumukaranki yau, zaki bar gidan nan domin na d’aura miki aure da Alhaji Mamman!” Damm!!! gabanta yayi mummunar fad’uwa, yayin dataji Kanta yayi wani masifar sarawa, bata san lokacin da ta d’ago kai ba, charaf idonsu ya had’u, Kakkauran mari taji ya wanke fuskarta dashi, har sai da ta fad’i ‘kasa cikin kakkausar murya, yace “sau nawa zan gaya miki kada ki ri’ka hada ido dani, ‘yar jakar uba mai kashin tsiya” Yayi tsaki. Zafafan Hawaye ne ke kwaranya daga idanunta, cikin sanyin muryarta tayi ‘karfin halin fad’in “Dan Allah Daddy kayi ha’kuri, kar ka aura mun Alhaji Mamman tsoho ne, wallahi bana son shi Daddy, kayimin rai karufamin asiri, kabarni incigaba da zama anan” tafashe da wani matsanancin kuka, tare da kifa kanta akan ‘kafarsa. Daddy yajanye ‘kafarsa da ‘karfi, kanta yabugu da ‘kasa, zafin buguwar ya’kara sanyata kuka, cikin ‘bacin rai Daddy yacigaba da fad’in “Yi mun shiru! nan ko in tattaka ki, na gaji da ganinki cikin gidan nan, nafi son naga ba’kin kare akan ganinki a yanzu, Allah ya kawo mun hanyar rabuwa dake, cikin sau’ki dan haka ki tattara kayanki anjima nan da daddare za’a zo daukar ki”. “Lafiya dai nakeni jin kuka?” Mummy ce ta fito tana tambaya “ya aka yi ne Alhaji ina ta jin hayaniya”. Dady yakau da kai gefe, yana cewa “Wannan abar” ya nuna ta da yatsa “na aurarwa Alhaji Mamman, shine zatamin rashin kunya ta nunamin ita ‘yar zamani ce, zata nunamin tayi gadon ba’kin halin uwarta, waini zata kalla, tacemin batason za’bin danayi mata” yayi kwafa, tare da haurinta da ‘kafa. Momy tazaro ido tare da dafe ‘kirji, cikin kid’ima ta furta, “Aure fa kace Alhaji? wato yanzu ka fara son yarinyar nan, da har zaka aurar da ita ga mai kud’i, kuma yanxu idan ta tafi wa zai dinga yin aikace-aikacen gidan nan, bama wannan ba shi yace yana sonta ne?” Daddy yace “kinsan yanzu kud’i na sun ‘kare a caca, to bazan iya ha’kura da caca ba, da ita na dogara, ta hanyarta na zama abinda na zama yau, shiyasa na sata a caca da cewar duk wanda yaci cacar shi zai aureta, sai Allah yasa Alhaji Mamman yaci, anan take aka d’aura auren akan sadaki naira d’ari biyar(500) “. Mummy ta kyalkyale da dariya tace “hakan shine dai-dai shi yafi dacewa da ita, amma kayan d’aki fa, waye zaiyi?”. Daddy yace “kema Hajiya da maganar ban haushi kike, Wannan faqeer din zan wa kayan d’aki, wallahi ko sule na ba zai yi ciwon kai ba, yadda take matsiyaciyar ta haka za’a kai ta a tsiyar ta”. Mummy tayi dariya tace “yauwa Alhajiji na, zomuje daga ciki, nashirya maka dukkan abinda kakeso, manta da wannan kucakar”. suka shige ciki, suka barta nan, tana kuka kamar ranta zai fita, a fili tahau fad’in “Anya Daddy shi ya haife ni kuwa? ban ta’ba tunanin tsanar da yake mun har ta kai ya sani a caca ba, a daura aurena akan sadaki 500, wannan wacce irin tsana ce Uba kema yar’sa na rasa me na yiwa Daddy ya tsane ni haka, Wayyo Allah na! Mahaifiyata kina ina? Nasan ko’ina kike ina ranki, kuma ke baki tsane ni ba, kome zan aikata arayuwata…..!” Kukane yaci ‘karfinta sosai, amma babu mai lallashinta Zuciyarta nata tafarfasa kamar zata fito waje Sageer(kaninta) yazo wucewa ta ri’ko shi tana cewa “Dan Allah Sageer ka ro’kan mun, Daddy, kar ya aurar dani ga d’an caca tsoho”. Sageer Ya bige hannunta ya hankad’ata tafad’i ‘kasa Yana tad’in “Dallah ni sakeni, kin ta’bani da wannan kazamin hannunki naki, kar ki shafa mun tsiya, hakan ai shi yafi dacewa dake” ya tofa mata miyau ya wuce. Wani kukan ta sake fashewa dashi, ita ba miyau da ya tofa mata ya dameta ba, dan in wannan ne kad’an ne daka wulakancin da take fuskanta a gidan, rashin wanda zata kai kukanta gareshi shi ke mata ciwo. Ta tashi da ‘kyar ta nufi gate inda baba mai gadi ke zaune, domin shine kad’ai takejin dad’i agunsa, duk cikar gidan. Tana isa yaganta duk tafita hayyacinta, cikin rud’ewa Yace “lafiya Noor me ya sameki, me kuma aka miki yau?”. Fuskart fal hawaye ta dubi Baba mai gadi, murya adashe sabida tsabar kuka Tace “Baba dan Allah Daddy shine mahaifina na ainihi kuwa ?” Baba mai gadi yayi shiru, can yace”Eh shine mahaifinki *Noor* shi ya haifeki” “To in shi ya haifeni meyasa ya tsane ni haka, kuma ina mahaifiyata take, ba wanda ya ta’ba gaya mun inda mahaifiyata take, ko meyasa ta tafi ta barni, nasan ba zaka rasa sani ba, tunda ka dad’e a gidan nan” Baban mai gadi yayi ajiyar zuciya yace “Tabbas ina da amsoshin duka tambayoyin nan naki, dole ne infasa bara gurbin kwan daya dad’e ina lailayashi a hannuna, dole zanfad’a miki dukkan abunda ya faru…………………………..!” Baba mai gadi yagyara zama, batare data kalli Noor yasoma bata labarin asalinta. *ASALIN NOOR* “Alhaji Ibrahim Had’eja, asalin sa d’an garin had’eja ne dake jahar jigawa, Iyayensa sun rasu, tun yana ‘karami kuma shi kad’ai suka haifa, dan haka ri’konsa ya koma hannun kakarsa, bayan wasu shekaru kakarsa tasa ta rasu, hakan ne yasaka ya tashi sakaka a gidan ba mai kwa’barsa akan komai nasa, baisan dai-dai ba, bai kumasan ba dai-dai ba baya tan-tance fari da ba’ki a duk kan al’amuransa. Sabida bai yi ilimin addini da na boko ba, kwata-kwata, dan idan an turo shi makaranta yawonsa yake tafiya baya xuwa, A haka ya fad’a d’a sana’ar caca, ta hanyar wani abokinsa Anan cikin unguwar da suke yi idan kakansa ya bashi kud’in break, sai yaje ya sasu a caca. Tunda ya fara caca, ba’a ta’ba cin sa ba, ko da yaushe shi ke ci, dan haka ya fara samun kud’i sosai, kakansa yarasa ta inda yake samun kud’i, domin duk tambayar duniya bazaifad’i gaskiyaba, sabida hanashin da kakan yakeyi”. “Yana shekaru Ashirin da biyar, ya zama hamsha’kin mai kud’i millionaire, dan a lokacin cacar shi ta shahara, har ‘kasashen waje yake fita ya buga caca yasamo ma’kudan kud’i. Kakanshi yayi yayi ya hana shi, ya’ki bari, Da yaga kakan nashi, na neman takura masa ya had’a kayanshi ya bar garin, Ya koma Abuja inda ya kama hayar wani gida” “Bayan wani lokaci kuma, ya siyi wani ‘katon fili a Abuja cikin unguwar Garki II, yasa aka mai gina mai kyau, a lokacin kwata-kwata ba aure a tsarin shi a lokacin, amma yana da burin samun d’a namiji wanda zai gaje shi, ya tsani mace, a cewar shi mace bata da wani amfani, banda kai ta wahala da ita, ko aure tayi baka huta ba, shikuwa namiji zai girma ya nemi na kanshi, har kaima ka samu. A wajen filin dayake ginin gidan sa, akwai wasu buzaye dasuke zaune a wajen, irin buzayan nan masu zama, wato (uncompleted building) dake xuwa daga nijer, Anan yaga mahaifiyarki mai suna Zainab, Ya nuna yana sonta, ba musu ta amince dashi ,Da yan’uwanta take zaune iyayenta sun rasu ,Yan’uwanta suka amince da auren, ba ad’au lokaciba aka d’auransu, amarya ta tare a Sabon gidan daya gina. Bayan aure ya tare da amaryarsa Zainaba a had’ad’d’en Sabon gidanshi, yan’uwanta kuma ya basu ma’kudan kud’i, yace suje su nemi sana’a, daga lkcin suka tafi bata qara jin labarinsu ba. Ya nuna ma mahaifiyarki so,’kauna da kulawa sosai, ita bata san yana caca ba, kawai yace mata shi d’an kasuwa ne. A lokacin da ta samu ciki, Yace mata shi namiji yake so ta haifa, baya son mace kuma idan ta haifi d’a namiji zai mata babbar kyauta, zai bata jari mai yawa, ta ri’ka yin sana’a, amma idan mace ta haifa kuwa, sakinta zai yi kuma sai ya kashe ‘yar data haifa. Zainaba taji tsoron wannan furuci nashi, kuma tayi mamaki sosai meye da ‘ya mace da zai ce baya so, taga Allah ke bada haihuwa shi ke bada mace ko namiji, ba kai ke bawa kanka ba to dan me zaice baya son mace. Haka ta cigaba da addu’a Allah ya bata d’a namiji. Wataranar jumu’ah ce ta tashi da na’kuda Alhaji ya kaita asibiti yana ta murna yau za’a haifa masa d’a namiji. Nurses din da suka kar’bi haihuwar, suka fito daga d’akin haihuwar, cike da murna , Suke ce masa ta haihuwa lafiya, Yace mai aka samu? Suka ce ya’ mace Take ya murtuke fuska, ya zabga wata uwar ashar yace, “Durowan uwa, wato duk abunda na gayawa Zainaba bata ji ba, shine ta haifa mun mace wallahi sai ta gane kurenta, sai ta gwammace mutuwarta da u’kubar da zan gana mata, zata san ba’a karya mun doka, inyi me da ‘ya mace meye da ‘ya mace banda tsiya(abunku da jahili amfanin ilimin addini kenan dan da yana da ilimin addini ba zai fadi haka ba). Nurse d:in tace “ban gane ba Alhaji me kake fad’a haka? kar ka manta bafa ita taba kanta ba Allah ne ya bata” “Kinga likita kama mun bakinki, ko inyi k’asa-k’asa dake wallahi” Nurse ta ta’be baki tace “Allah ya huci zuciyarka” ta wuce abunta, tabarshi anan yana kumfar baki. Zainaba na rungume da yar’ta, kyakkyawa fara sol, ga gashi yala-yala tana kallonta tana kuka, Tana magana a fili “Yanzu Alhaji kashe ki zai yi, ni kuma ya sakeni, Ina sonki ya’ta, ina jinki a cikin jinin jikina, bana son rabuwa dake Ya Allah! Ka tsare mun ya’ta, kar kaba Alhaji ikon kashe mun ita, Ni yanzu idan ya sakeni ina zani bansan inda yan’uwana suka tafi ba, “Ya Allah dakai na dogara ka kawo mun agaji…….!” Garammm taji an turo ‘kofa’ da karfi Alhaji ne ya shigo fuska a murtuke, kamar wani bajimin zaki, ‘Yan hanjinta sai da suka kad’a, bata ta’ba ganinshi a irin wannan yanayin ba, Kanta yayo da Sauri, da ‘karfi, ya jawo dogon gashinta, Tana kuka tace “Dan Allah Alhaji kayi ha’kuri kayi mani rai, wallahi ba laifina bane Allah ya bani………!” Gummm ya kai mata naushi a baki ,sai jini baki ya bud’e Yace “yi mun shuri yar’iska, ni zaki ma iskanci, ki karya mun doka, nace miki kar ki haifa mun ya’ mace, shine zaki haifa mun, toh wallahi sai kin gane kuranki, sai na d’and’ana miki azabar da sai kin gwammace mutuwarki da ita, wannan shegiyar yar’ kuma” ya nuna ta da yatsa “kasheta zanyi”. Zainaba na kuka tace “Dan Allah kar ka kasheta, duk azabar da zaka mun kamun, amma kar ka kashe mun ‘ya….!” wani wawan mari ya wanke fuskarta dashi, tare da jan hannunta da ‘karfi, duk abinda take mata, tana rungumeta da yar’ta. Yace “wuce mu tafi gida”(bai ko jira an sallamesu ba), tana kuka yana jan’ta har suka kai mota, Ya hankad’ata, da ita da jaririyar cikin mota Ya figi mota sai gida……! Baba mai gadi yayi shiru, a lokacin daya kawo nan a labarin, saboda hawayen da suka cika idonshi, Noor kuka take sosaii tace “Baba cigaba da gaya mun, ya aka yi na rayu bai kasheni ba, mai yayimlwa Mahaifiyata kuma ina take yanxu???………………..! Babah mai gadi yacigaba da fad’in “ina zaune bakin aiki, mahaifin yadawo tare da mahaifiyarki, yayi hon, natashi da sauri na bud’e mai gate, ko ‘karasa bud’ewa banyiba, yadanno kan motarsa cikin gidan, da sauri namatsa dan kad’an yarage yabugeni, natsorata sosai da ganinsa, yawuce parking space, Yana parking motar cikin harabar gidan, Ya fito tare da fizgota, ya jata zuwa cikin gida tana ta kuka, ya fizge jaririyar a hannunta, ya jefar da jaririyar kan gado. Ta tsandala ihu Zainaba a rud’e tayi kan jaririyar, cikin zafin nama ya fizgota, yahau dukanta da belt, yana cewa “ni zaki ma iskanci, na d’auko ki cikin rugga na rufa miki asiri, dan ki haifa mun d’a namiji, shine zaki haifa mun mace”. Ya cigaba da zabga mata belt, Jaririyar nata kuka, sai ta tashi zata je wurinta ya jawota ya cigaba da dukanta. Har jaririyar tai shiru ta daina numfashi Wata gigitacciyar ‘kara Zainaba ta saki, dashi kanshi sai da yaji tsoro, Tayi wajen jaririyar tana fad’in “shikenan ka kashemin ita…..” kafin ta ‘karasa ya fizgota, ya ajiye belt d’in, ya cigaba da marinta kota ina yana haurinta da ‘kafa. Ana cikin haka, Wayarshi tayi ringing, Ya d’auka ya kara a kunnansa. Akace ana nemanshi yazo yanzu zasu buga caca, mai mahimmanci wacce za’a cankaci ma’kudan kud’i, nan da nan yakashe wayar, ya juyo kanta, . Yayi k’wallo da ita, yace “bari inje in dawo, zaki ci ubanki kad’an na miki yanzu, kuma zan turo Baba mai gadi ya fitar mun da gawar tsiyar nan” ya nuna jaririyar, yaciga da fad’in ” abu na ‘karshe kuma kar kiga na fita, kice zaki gudu, wallahi kika gudu sai na nemo ki, duk inda kika shiga na kashe ki” yana kaiwa nan ya fice yana haki. Kan jaririyar tayi tana kuka, jikinta duk ya mutu, ga haihuwa ga duka, tata’ba jaririyar taji kwata-kwata bata numfashi, ta rungume jaririyar tana kuka, kamar ranta zai fita. A lokacin ni kuma na shiga, saboda Alhaji da yace nazo na fitar da gawar jaririyar. Halin da naga mahaifiyarki ta bani tausayi sosai na kar’bi jaririyar a hannunta,na kalleta sosai nace “Hajiya ki kwantar da hankalin, jaririyar nan kamar bata mutu ba,Kawo ruwan Zam-zam da dabino mu gani” Jiki na rawa, da ‘kyar take tafiya, taje ta d’auko ta kawomin. Na kar’ba na bude ruwan zam-zam d’in, nayi addu’o’i na yayyafa miki a fuska, na bud’e bakinki na zuba tare da dabino nan, cikin Ikon Allah kawai muka ga kina motsi. Zainaba ta kar’beki tana murna tana wa Allah godiya, Ganin jikinta rud’u-rud’u yayi jawur shatin duka yasa na tambayeta, mai yasameta, bata tsaya wani tunaniba, Tana kuka ta gaya mun komai, duk abunda ke faruwa, na tausaya mata sosai, kuma na lallasheta tare bata addu’o’in da zata ri’ka yi, tai mun godiya sosai na koma bakin gate, cike da tausayinta, dana rayuwarta dake. Alhaji na can wajan buga caca, cikin rashin sa’a aka cinye shi, Yana ganin haka hankalinshi ya tashi, zuciyarshi ta ‘kara harzu’ka yace “tunda yake ba’a ta’ba cin shi caca ba, amma sanadiyyar macen da aka haifa mai gashi an cinye shi caca, ya fara asarar dukiya tun ba’a je ko’ina”. A fusace yaja motarshi ya nufi gida, akan hanyarsane, A radio’n mota yake jin hukuncin kisan kai, duk wanda yai kisa a kashe shi, hakan ya tada mai hankali, dan shi bai ta’ba sanin hukuncin kisa ba,Yace “yanzu idan Zainaba ta fad’a ni na kashe jaririyar nan, kenan nima kasheni za’a yi, na shiga uku, dole inyi wani abu in hanata fad’a”. Ko da ya dawo gida, Zainaba har tayi wanka, ta gasa jikinta, tama yar’ta wanka itama, tana rungume da ita a d’aki, tana aikin kuka abun duniya duk ya isheta. Alhaji ya bangazo kofar d’akin ya shigo, Zainaba ta zabura jiki na rawa, Ganin jaririyar da yayi a hannunta tana motsi, yasa shi yin ajiyar zuciya, a ranshi yace “ashe bata mutu ba, nima yanzu ba za’a kasheni ba, Yanzu da uwar da yar’ zan had’a, na gana musu azaba, amma haka zan cigaba da zama da tsiya a gidana, gashi daga haihuwarta anci ni a caca”, yaja tsaki. Yayi saurin kawar da tunanin Yace “keee, tashi yanzu bake ba hutu, kin zama yar aiki a gidan nan, daga yanxu d’akinki ya koma can kusa da na mai gadi, d’akin da ake ajiye kare da(before)”. Zainaba jiki na rawa tace “toh” ta mike(a ranta tana murna jin bai yi maganar yar’ta ba tana ro’kon Allah yasa ya fasa kasheta). Daga lokacin azaba da u’kuba ba irin wacce mahaifinki baya gana muku, tun kina jaririya Mahaifiyarki ta sa miki suna *Noor*(haske), ta kalleki tace In shaa Allahu sai kin zamo haske a rayuwar mahaifinki, sai ya dawo yana nadama, kuma sai yasan muhimmancin ‘ya mace a cikin al’umma, Mahaifinki da yaji sunan da take kiran ki *Noor* yaji kuma ma’anar Noor d’in, hakan yasa Yace “in ita haske ce a gurinta, to shi duhu ce a wurin shi, kuma tsiya ce, dan haka yake kiranki *Zulum* wato duhu ko *Faqeer* (tsiya), Kina wata tara a duniya ya sake aure, ya auro Hajiya Zulai(mummy) A lokacin mahaifiyarki taga tijara da wulakanci iri-iri ba irin cin mutunci da hajiya Zulai bata mata, Kina shekara d’aya tayi kucin-kucin tasaka Alhaji ya saki Zainaba, Yace “ta tafi ta bar mai gida, kuma ta tafi da yar’ta, ta manta ta ta’ba aurenshi balle tayi tunanin ta haihu dashi”. Mummy tace “a’ah kar ta tafi da yar’ta ta barta nan, shine hukuncinta, dan idan aka rabata da yar’ta sai tafi jin rad’ad’i akan abar ta da ita”. Alhaji ya amince da wannan shawara, duk da baya son ganinki a gidan. Mahaifiyarki ba irin ro’kon da bata mishi ba akan ya barta ta tafi dake, amma Ya’ki, dan mahaifiyarki najin tsoron halin dazaki shiga, daya gaji da magiyarta, jan ta ma yayi ya fitar da ita daga gidan, tana kuka tana ro’konshi, baiko saurare taba. Baba maigadi ya d’an yi shiru, yana share ‘kwalla, “yace kinji yadda aka yi, Alhaji bai kashe ki ba, kuma mahaifiyarki ta tafi ta barki”. Sannan ya cigaba “daga lokacin kika taso cikin rayuwar kunci, wahala da tsangawama Hajiya zulai kuma ta haifi ya’ya biyu maza, Sageer da Sameer Alhaji ya d’au son duniya ya d’aura musu su da uwarsu, ke kuma ya tsaneki, Har kannenki suka taso, suka ga irin tsanar da mahaifinki da mahaifiyarsu suke miki, suma suka d’au tsanar duniya suka d’aura miki, shine kike gani har girmanki. *BACK TO LABARI* Noor kuka take sosaii, kamar ranta zai fita, ta kasa cewa komai ,ji take kamar ta mutu ta huta da wannan tsanar da kowa yake mata, a gidansu, musamman tsanar da mahaifinta yake mata itace tajawo mata komai, kuma ya zata iya rayuwa da tsoho, wanda ya girmi mahaifinta, d’an caca a matsayin mijinta, ita meye laifinta, tunda ba ita tayo kanta ba da za’a ce ba’a sonta an tsane ta…………………..!?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page