IN SO YAKI NE CHAPTER 8

IN SO YAKI NE CHAPTER 8

  K’iran sallar esha ne ya sa shi d’ago kai, da sauri ya dubi agogon shi sannan ya tada mota ya fice daga harabar Station d’in, bakin wani masallaci ya tsaya inda yayi alwala aka yi sallah sannan ya koma mota ya d’au hanyar gida……. Yana parking direct sashen sa ya nufa don ya duba bai ga motar Ameer ba, ya tabbata cewa basu dawo ba. Tsaye ya hango ta bakin stairs tana kallon shi har ya k’araso inda take “Suraj you scared me! Yanda ka fita d’azu……” bata k’arisa maganar ba ya sa yatsar sa guda kan labb’an ta yace “Shuush!…..i am sorry wani d’an emergency ne ya taso kuma it will be too late by then in har na tsaya yin bayani” hannun sa yasa ya shafa fuskar ta ya cigaba da cewa “Have you eaten?” kai ta jinjina da murmushi tace “No…. Jiran ka nake” Murmushi kawai yayi yace “ai da baki jira ni ba, actually bani da appetite, sam bana jin zan iya cin wani abinci yanzu” Wuce wa yayi zai haura stairs Meenah ta rik’o hannun shi, chak ya tsaya ya juyo yana kallon ta ido cikin ido. Hawaye take tana cewa “Suraj, idan soyayya ta tana takura maka or you feel any pressure because of me, ka sani cewa i am not forcing you to love me, just don’t push yourself hard, in dai kullum zan dinga ganin ka cikin farinciki hakan ma ya isheni, i am okay with that, in don saboda ni zaka k’i cin abinci please kar ka yi wa kanka horon yunwa, zan koma ciki ka je ka ci abincin ka i won’t complain i promise”. Sosai ta bashi tausayi jikin sa yayi sanyi ya san cewa Meenah tayi deserving soyayyar shi. Bai tsaya jin kalmar da zata furta a gaba ba ya fisgo ta jikin shi sannan ya had’e lips d’in shi da nata yana kissing, kasa tsayuwa tayi kan k’afafun ta tsabar yanda ya kashe mata jiki, sake ta yayi ya rik’e kafad’un ta idanuwan sa cikin nata yace “Ban tsane ki ba Meenah, ba kiyi offending d’ina ba ko kad’an kuma ba don ke na k’i cin abinci ba, kawai de bana jin yunwa ne.” jan hannun ta yayi har zuwa dining section, kujera ya ja mata ta zauna, sannan ya d’auko plate ya zuba abincin a ciki pasta ne da sauce k’amshi sai tashi yake ya saka fork a gefe sannan ya tura mata “Ki cinye wannan duk, i promise you in har kika cinye bazan ji yunwa ba don harda share na a ciki” sosai ya bata dariya tace “wannan ai wayau ne, besides abincin nan yayi min yawa sosai” dariya yayi ya shafa fuskar ta yace “Oya! Ki cinye duk, zan je in yi wanka in dawo, we can watch a movie.” cike da murna ta kad’a masa kai sai dariya take shi kuwa yana juyawa wasu zafafan hawaye ke gangaro masa yana tausaya wa halin da yake ciki domin shi a halin yanzu ko Meenah ma fuskar Laylah yake gani a fuskar ta, ga kuma tausaya wa Meenah da yake yi domin ta fad’a son maso wani, sam baya so yayi hurting d’in ta anymore amma in the process he always ends up hurting himself, ba k’aramin ciwo yake ji a ranshi ba duk lokacin da ya kusanci Meenah. Ita kuwa bin shi take da kallo sai murmushi take, affection d’in da Suraj ke nuna mata this days sabo ne a wajen ta, bazata iya banbance wa ko na gaskiya ne ba amma hakan ma ya ishe ta…. Tari ta fara kamar wasa ya k’i tsaya wa, tamkar wanda ta yi chocking, kasa controlling tayi ga wani ciwon kai, cikin y’an mintina da basu wuce biyu ba Meenah ta sauya duk plates da warmers dake kan table d’in saida ta zubar su k’asa tana k’ok’arin janyo roban ruwa hannun ta guda ta rik’e wuyan ta, kasa janyo water bottle d’in tayi in the process ta zame daga kujerar ta fad’i k’asa, da sauri wasu masu aiki suka nufo ta “Madam lafiya kuwa?” duk sun rud’e, hannun ta na rawa ta nuna musu roban ruwa sannan da sauri suka mik’a mata ruwan ta sha tana maida numfashi kafin ta ankara hancin ta da baki duk jini ne ke fita tana b’oye wa ta ce “Kuyi sauri ku gyara wajen nan! And i am warning you kar wanda ya fad’a ma Miji na abunda ya faru, bana son hankalin shi ya tashi, kawai kware wa nayi ” kai suka girgiza da sauri suka hau tattare wajen ita kuwa Meenah da kyar ta ja jiki ta koma kan doguwar kujera ta kwanta saida ta d’an ji numfashin ta ya daidaita sannan ta mik’a hannu kan side table ta zaro wipes ta goge fuskar ta da shi tsaf duk jinin hancin ta goge shima, a nan babu jima wa barci yayi awon gaba da ita…….. Duk wannan abunda yake faruwa Suraj yana bathroom ya bud’e shower a kanshi yana tsaye shima ya shiga wata duniyar tunanin, saida ya gaji tukunna ya d’aura towel ya fito ko kaya bai tsaya sa wa ba ya sauk’o k’asa, kallon ta ya tsaya yi ganin tana barci hankali kwance, murmushi yai sannan ya d’auke ta chak zuwa bedroom ya kwantar sannan ya dawo falo domin ya kashe wutan se a lokacin yaga wipes d’in da tayi amfani da su, cike da mamaki a ranshi yace “Ciwo taji ne? If not me zai sa blood a jikin wipes?” Tab’e baki yayi yace “I will find out tomorrow in shaa Allah. Wipes d’in ya kwashe ya zubar a bin sannan ya kashe wuta ya koma bedroom. Duk ji yayi ya gaji don haka ya zira kayan barci sannan ya kashe wutan d’akin ya kwanta…..+ Yau weekend ne hakan yasa Suraj bai wani yunk’ura ba, tun bayan sallar asubah da ya kwanta bai tashi ba sai barcin sa yake hankali kwance. Da sauri ta fito daga wanka ko gama tsane gashin kanta bata yi ba a haka ta shafa hair oil ta taje kan, sannan sama sama ta shafe jikin ta da body moisturiser daga nan kuwa ko ta kan makeup kit nata bata bi ba, mik’e wa tayi ta nufi wardrobe blue atamfa ta d’auko d’inkin riga da plane zani ta kimtsa tsaf ta feshe jikin ta da turare, duk da babu makeup tayi charas da ita bak’in mayafi ta yafa sannan ta zari jakar ta da car keys ta fice da sauri bata bi ta kan Suraj ba ma ballantana ta sanar da shi inda ta nufa……. K’aran rufe k’ofa yaji, ba shiri yayi firgigit ya tashi zaune. Da kyar yake bud’e ido tsabar barcin bai ishe shi ba ya duba gefen sa bai ga Meenah ba, k’afafun sa ya sauk’e k’asan gado ya kifa fuskar shi cikin tafin hannuwan sa na y’an wasu dak’ik’ai sannan ya d’ago ya dubi lokaci, k’arfe tara ne ma, mik’ewa yayi yana mik’a ya nufi k’ofar da zata sada shi da terrace, wani iska mai dad’i ne ke busawa har saida Suraj ya lumshe ido ga yayyafan ruwan sama da ake yi, daf jikin k’arafunan ya tsaya ya rik’e k’arfen da hannun sa yana k’are wa harabar gidan kallo, da gudu Boboh ya fito rik’e da ball, khadijah na biye da shi tana k’ok’arin dawo da shi ciki don yayyafin bai tsaya ba gashi gari yayi sanyi, da gudu ya nufo sashen Suraj yana kuka, dariya Suraj yayi sannan ya juyada sauri ya nufi downstairs sannan ya bud’e k’ofa ai kuwa daman kamar jira yake bai tsaya ba ya ruga ta gefen Suraj yayi cikin gida da gudu. Kai ta sunkuyar tana dariya da taga Suraj, se shi Suraj ne ya fara gaida ta yacigaba da cewa “Let him be sister in-law, he’s just a kid, they only do what they feel is right, and kin san Takwaran nawa da mulki, don’t spoil his mood this early morning, kyale ni da shi bazan bari yayi wasa a ruwa ba”. Murmushi kawai tayi ta juya zata koma bata ankare ba santsi ya ja ta zata zame k’asa Luckily Habeeb ya iso daf da ita yayi saurin rik’e ta “Subhanallah!” ya fad’a yaka k’ok’arin fad’uwa shima da kyar ya ja balance ya dubeta yace “Khadijah nayi warning d’inki several times ki daina saka wad’annan slippers d’in especially in waje akwai danshi! Duk ranar da kika sha k’asa kar kice ban fad’a miki ba” shidai Suraj kallon su yake da murmushi daga bisani ba juya wa yayi ya koma ciki sannan suka bi. bayan shi. Suna zaune suna hira ba’a jima ba Mubeenah da Ameer suka shigo d’auke da Iman, nan fa suka sake kafa wani sabon hira.. Wayar Habeeb ne tayi k’ara, da gaggawa ya d’aga ganin cewa secretary d’in shi ne kan layi. Tun da ya kafa wayar a kunne bai ce k’ala ba se ma kashe wayar yayi idanuwan shi kuwa ya kafe su kan Suraj, Ameer ma ya lura da kallon da Habeeb d’in ke yi wa Suraj don har shi kanshi Suraj ma ya tsargu da irin kallon. Rai a b’ace Habeeb yace “Suraj…….yaya zaka yi haka? Why? And you didn’t even bother to inform us?……” Suraj ya d’ago ya dubi Habeeb, sosai ya san inda maganar ta dosa amma sai ya basar kamar bai san me Habeeb ke nufi ba yace “What now? Me nayi kuma?” a fusace Habeeb ya mik’e ya juya masa baya yace “Mun yi agreeing cewa bazamu yi investing a partnership da Sufyan ba ballantana Muhseen Ali but yanzu secretary ya k’irani cewa jiya ka d’ebi legal documents d’in sannan ka had’u da Muhseen da Safwan me hakan yake nufi? What on earth does that mean? And you didn’t even bother to tell us! Besides kasan wad’annan mutanen are not trustworthy. I just hope you didn’t sign the contract?” Murmushi Suraj yayi yace “Relax Habeeb bro, me yasa kake neman mayar da such trivial matter into a big one? It’s true na had’u da su Muhseen, sannan mun tattauna a game da partnership but i did not sign a contract with either of them kuma bana jin nan da shekaru d’ari zan yi signing contract da su, documents d’in suna waje na i am not that stupid Habeeb, dalili daban ne ya kai ni, bai kuma shafi business ba, let’s say it’s more like na jefi tsuntsu biyu ne da dutse d’aya”. Yana kammala maganar ya saki wani killer smile ya cigaba da wasa da Boboh. Tuni Ameer ya gano inda maganar Suraj ta dosa da yake shi ma shu’umi ne ajin farko. Habeeb ne dai ya juyo ya ce “Me kake nufi?”. Ko d’ago wa Suraj bai yi ba yace “Na ga secret d’in da kuke b’oye min, kuma naga abunda ya kamata ku sanar da ni kuka kasa, na had’u da Laylah.” yana ida maganar yayi murmushi ya kalli idanuwan su ga mamaki k’arara a. fuskokin su, mik’e wa yayi ya kama hannun Boboh ya ja shi suka haura stairs yana tafe suna wasa. Daga Ameer har Habeeb babu wanda ya motsa har suraj ya shige. Cike da mamaki Mubeenah ta dubi khadijah sannan a tare suka saki tambaya d’aya “what secret is Suraj talking about?” Habeeb ya dube su duka yace “Zai yiwu sanin da kuka yi wa Suraj cikin y’an shekarun nan bai wuce cewa he is Rude, arrogant and hot tempered but a hak’ik’anin gaskiya he was just a victim of circumstances, shekaru kafin shekaru bakwai da suka shud’e ba haka yake ba. He was the loving, calm and welcoming kind of brother we have ever had, kamar yanda kuka sani mutane sukan sauya, sedai wasu basa duba dalilin chanja wan mutum ko halayen shi sai suyi judging d’in shi blindly based on character, labarin da zan baku labari ne da ya faru shekaru bakwai a baya….. Nan Habeeb ya kwashe labarin Laylah Y’AR MAKIYAYA da Suraj ya fad’a musu. Sosai jikin su yayi sanyi musamman Mubeenah wanda ta kasa d’auke kanta daga Ameer, hawayenta ta share sannan tace “You are right yaya Habeeb, mutane sukan chanja domin ko da zaka shekara dubu d’ari kana fad’a min Halin Abban Iman (Ameer) bazan tab’a yarda ba. Na gode Allah da ya bani kai as a changed person, yana da kyau idan d’an Adam ya gane laifin sa toh ya gyara kuma ya nemi yafiyar wanda ya cutar ko ya zalunta, i am so proud to call you my Husband. Abban Iman ka gode wa Allah domin you are one of the lucky few da suka kub’uta daga halaka. Murmushi Ameer yayi ya share hawayen shi yace “A hak’ik’anin gaskiya Suraj did me many favours wad’anda lissafa su zai yi wuya.” Khadijah ta dubi Habeeb tace “Amma duk tsawon lokacin nan Ina ita Laylah da kuma abun da ta Haifa?”. Dariyar takaici Habeeb yayi yace “Laylah!……. Khadijah you will be surprised in na fad’a miki cewa Yanzu haka Laylah tayi aure, she’s now a married woman. Kuma ma abunda zai k’ara baki mamaki shine wanda ta aura ya kasance mutum Na farko da Suraj yake k’i, d’an adawan sa ne a business MUHSEEN ALI. The same Muhseen Ali da Suraj yaje wajen sa kan maganar partnership jiya. To be frank khadijah dawowar Laylah cikin rayuwar Suraj tamkar tarwatsa farin cikin shi ne! Ba ma shi kad’ai ba Meenah…… What about her? Shekaru uku soyayyar Suraj, Finally ta samu attention nashi ya karkata zuwa gareta, Kina tunanin zata kyale wata ta Maye wannan gurbin ne all of a sudden? Dawowa Laylah cikin rayuwar Suraj zai yi ruining rayuwar Suraj, Meenah da ma ita kanta Laylah! Wannan shi yasa ni da Ameer muka b’oye al’amarin, duk da cewa MA Ameer bai so hakan ba da farko but it seems like Suraj ya riga ya gano Laylah, yanzu Tambaya a nan shine yaya zamu Yi handling situation d’in? Idan Suraj ya so abu nothing can stop him ni kaina tsoronsa nake yi domin kuwa he can go to any length to get it……… “+ Tun lokacin da ya fara maganar take tsaye har lokacin da ya dasa Aya. Hannuwan ta ba karkarwa tsabar yanda zuciyarta ke tafarfasa, wayar ya da jakar ta ne suka fad’i daga hannun ta hakan yasa duk suka juyo babu shiri. Ameer ya dubi Su Habeeb sannan suka sake maida dubansu ga Meenah wanda tayi sharkaf da hawaye, kafin su yi magana Meenah ta rufe kunnuwan ta da hannun ta sannan ta haura stairs a guje tana kuka, duk k’iran da suke mata bata bi ta kan su ba. Dafe Kai Ameer yayi yana fad’in “I guess haka Allah yaso, after all ko bamu fad’a Meenah ta ji ba in dai Laylah da Suraj sun had’u dole Meenah zata san wannan lamarin watarana, for now let’s leave them alone, my b’ari su yi solving problems d’in tsakanin su I am sure Meenah zata yi understanding Suraj da kuma halin da yake ciki. ” Kai Habeeb ya jinjina yace “I hope so “. Duk suka nemi waje suka zauna kowa na sak’e-sak’e a ranshi………. Ta dad’e tsaye a bakin k’ofar ta kasa bud’e wa hannuwanta har karkarwa suke tana tunanin yanda zata yi facing d’in shi, a hankali ta tura k’ofar ta sa k’afa cikin d’akin shi kuwa daidai lokacin ya kwantar da Boboh kenan yana rufe shi da blancket, kallon sa kawai take a tsaye jiki ba laka wurya a dishashe tace “Why…..?” almost in a whispher tayi maganar hakan yasa ya d’ago yana kallon ta, ganin yanayin ta yasa yayi saurin mik’ewa ya taho daf da ita, hannu ya kai zai tab’a fuskar ta amma sai tasa hannu ta buge hannun nashi sannan ta kafe shi da ido tana sauk’e numfashi da kyar har labb’an ta na karkarwa, cike da mamaki ya sa hannu zai janyo ta jikin shi ,sai ta hankad’a shi yayi baya kad’an ya rage ya fad’i k’asa. Cikin tsawa tace “WHY??!! Why Suraj? Such big secret and you didn’t even bother to tell me? Yanzu na fahimci dalilin da yasa baka k’auna ta, i have realised that ni kad’ai nake hauka na, saboda ba nice cikin zuciyar ka ba, shekaru uku Suraj, 3 damn years na cinye na rayuwa ta ina muradin son ka, i couldn’t even win your heart, in da ace ka sanar da ni da bazan takura ma rayuwar ka ba because i don’t want to be the other woman in your life, ashe son maso wani nake….” Suraj idanuwan shi suka cicciko yana k’ok’arin pacifying Meenah amma sai ta janye jikin ta. Ganin Boboh na neman tashi daga barci yasa Suraj yayi sauri ya d’auke ta chak yayi waje da ita zuwa wani d’akin na daban duk da fisge fisgen da take, dire ta yayi a k’asa tana ta huci sannan yace “Meenah, ban san yanda aka yi kika ji wannan maganar ba kuma ko da baki ji ba daman i was about to tell you everything about my past, amma tunda kin riga kin gano hakan ma ba laifi bane, ina so ki sani abunda ya faru is all in the past, ko da ina k’aunar Laylah yanzu tayi min nisa, me zaisa ki dinga d’aga hankalin ki akan macen da ta riga da tayi aure? Ban san dalilin da yasa Laylah ta nemi saki ba daga gare ni because i am sure wannan ba yin ta bane tabbas akwai dalili, Meenah bazan b’oye miki ba i still love her to the core and i know she loves me too, wannan ce k’addarar mu kuma mun rungumi k’addara, Meenah na san ban kyauta miki ba and i am now rectifying for my mistakes please abunda ya wuce ya wuce lets just……” Bai k’arasa maganar ba tace “Humph!….. In da ace Laylah tana k’aunar ka da bata bar ka ba, she would have trusted you lokacin da kake neman yardar ta but instead she left you, You know Suraj da fari nayi zaton aure na ne baka so, sai yanzu na fahimci cewa akwai wata wanda ta hanaka cigaba da rayuwar ka! Now that she is back ni kuma miye matsayi na?” tana maganar muryar ta na k’ara dishe wa kafin Suraj ya ankara Hancin ta ya fara bleeding hakan kuma ya bashi tsoro da sauri ya kai hannu zai rik’o ta shima kukan yake sai ta ja da baya, ya bud’e baki zai yi magana sai ta toshe kunnuwan ta sannan ta juya ta fice daga d’akin, ganin haka yasa Suraj yabi bayan ta da sauri, har suka isa downstairs “Meenah stop! Please listen…Meenah!…” Kawai makullin mota ta d’auka da sauri ta nufi k’ofar fita Suraj ya bi bayanta, ko su Habeeb dake k’ok’arin bata baki babu wanda tace wa k’ala har saida ta kai wajen motar Suraj ta sa hannu zata bud’e, da sauri ya chafke hanun ta ga ruwan sama ya sake b’arke wa amma basu damu ba har su Habeeb na tsaye “Meenah please don’t make this harder for me, ina kuma zaki je? Duba kiga yanda ake ruwa, and …..” Bai k’arashe maganar ba ta janye hannun ta idanuwan ta cikin nashi tace “Don’t worry i will be fine, akwai maganin da zan k’arba a pharmacy sannan daga nan zan wuce gida na kwana biyu ban je ba, se dare zan dawo”. Tana kai nan ta shige motar ta tada yana tsaye ruwa na bugan shi daga shi har su Mubeenah babu wanda ya motsa. Juya wa yayi a hankali yana k’are musu kallo kafin kawai yayi murmushi ya nufi cikin gida, bai damu da yanda jikin shi ya jik’e ba ya zauna kan kujera ya lumshe idanuwan sa, ko da su Habeeb suka shigo tsayuwa suka yi suna kallon shi, shima yana bud’e ido ya aza kan Habeeb yace “Ya kuke tsaye haka?” Habeeb ya ce “Sorry Suraj bamu san Meenah tana tsaye ba lokac…….” Dakatar da shi Suraj yayi yace “Meenah ba don labarin da kuka bayar tayi behaving yanda tayi ba, akwai wani abun da take b’oye min ne, kar ku damu kan ku, ku taho muyi breakfast don ni yunwa nake ji” Habeeb ya sake cewa “Me kuma Meenah zata b’oye maka?” Suraj ba tare da ya d’ago kai ba yace. “she is seriously sick kawai de ta yi amfani da labarin Laylah ne ta tada bori domin kar na gane cewa bata da lafiya, i am sure, yau tun sassafe ta fita, jiya da dare ma naga ta yi amfani da wipes ta manta duk jiki blood, yau da safe ma i saw traces of blood a kan pillow d’in ta, d’azu ma kafin ta fito nayi noticing, muryar ta ya sauya sannan hancin ta na bleeding, Cikin y’an kwanakin nan ina ganin tana sauya wa. I think ya kamata nayi magana da Aunty Fatima, (yayar Meenah ) tunda ita ce wanda tafi kusa da Meenah and she is also a doctor am sure ta san wani abu”. Koma de menene i will definately find out”. Haka de suka kammala breakfast, lokacin ruwa ya tsaya don haka suka koma sashen su domin chanja kaya don duk a jik’e suke………. Da sauri Tasleem ta bud’e k’ofar motar ta shige haka ma Laylah yayinda driver ya gama loda jakankunan su cikin booth. Shima gogan motar ya shiga ya dake driver ya ja suka bar harabar Hotel d’in. Sun d’au lokaci suna tafiya kafin suka shigo wani tafkeken gida mai cike da k’awa. A daidai entrance driver yayi parking sannan ya bud’e musu k’ofa suka shiga yana bin su da akwatinan su, saida suka shigo tsakiyar falon Muhseen ya ce “Ga chan side naki, ke da y’ar ki, i don’t want to see you anywhere near my things, i hope its clear?”. Kai Laylah ta gyad’a ita ko Tasleem ta rik’e hannun Laylah gamgam don tsoro Muhseen ke bata, idan yana guri sam bata da sukuni. Laylah bata ma sake bi ta kanshi ba ta ja luggage d’in ta Tasleem ma ta ja nata suka haura side d’in benen da ya nuna mata, daga k’arshen benen wani tafkeken k’ofa ne saida tayi ajiyar zuci sannan ta tura k’ofar, falo ne mai girman gaske komai na ciki royal blue ne, sannan ga k’ofofin d’aki guda biyu daga wasu corridor mallam kud’i yaci ubansa a wannan flat d’in, wani sukuni Laylah taji a ranta domin yanzu ba sai tayi sharing d’aki da wancan monster d’in ba, mayafin jikinta ta cire ta jefa kan kujera sannan ta zube kai ta jingina da kujeran tana maida numfashi tamkar wanda tayi aikin noma, finally ta bar Hotel d’in chan kuma masifar Muhseen zai ragu domin ko da chan da suke newyork da yake d’akin su daban wasu lokutan ko ta kanta baya bi sai dai in rana ta b’aci……….”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page