IN SO YAKI NE CHAPTER 7

IN SO YAKI NE CHAPTER 7

  Yana komawa office yaga duk an watse, babu ma’aikata se y’an kad’an, se a lokacin ya tuna yau fa jumma’ah ne, da sauri ya d’auki jakar sa ya fice zuwa mota, direct ya nufi gida. Sashen shi ya nufa cikin sauri yana duba time already ya kusa yin latti, da sauri sauri yayi wanka, abinci ma bai tsaya ci ba ya fice,. Sea blue shadda ce sanye a jikin sa wanda aka mata d’inkin 3quater yayi matuk’ar fito da kyaun sa, hular shi ma a hannu ya rik’o sannan ya wuce sashen Habeeb. Meenah, Mubeenah da khadijah duk suna zaune a living room suna hirar su ya turo k’ofar da sallamar shi. Da gudu Boboh ya rungume shi yana fad’in “Daddy! Daddy!” Dariya Suraj yayi sannan ya d’aga shi chak yana mishi wasa kafin ya maida hankalin shi ga Mubeenah yace “Kude kam hirar ku bata k’arewa, Madam ina Habeeb?” ya tambayi Khadijah hankalin shi na kan Boboh. Murmushi Khadijah tayi sannan tace “Yana d’akin shi”.. Bai tsaya wata wata ba ya haura stairs zuwa d’akin Habeeb, Sallama yayi Habeeb ya amsa masa, da alamu shi ma Habeeb ya kammala shiri. Suraj ya kalla sannan yace “Ina ka shiga ne haka? I’ve been calling baka picking call” K’arasa wa cikin d’akin Suraj yayi sannan yace “na je wani waje ne mai muhimmanci, in an sauk’o daga masallaci zan sanar da kai but for now muyi sauri mu tafi kar mu rasa Sallah, nifa yau ina da sabgogi da dama anjima, ina so zan had’u da wani old friend d’ina yanzu shi inspector of police Victor jiya ya shigo gari, he was transferred to Abuja”. Kai Habeeb ya jinjina yace alright, come on….let’s go.. Tare suka fice da Suraj a motar Habeeb, cikin sauri Habeeb ke tuk’in saboda sun kusa latti…. ……AFTER FRIDAY PRAYERS…….. Wannan karon Suraj ne ke tuk’in motar Habeeb na gefe yana ta latsa wayar shi… “Suraj…..yanzu zaka je wajen inspector victor d’in ko se ka koma gida?” Kai Suraj ya jinjina yace “No, ba yanzu ba, dubi yanda ranan nan ta bud’e gaskiya se gari yayi sanyi don ni yanzu haka ma yunwa nake ji Allah-Allah nake mu isa gida in sa abinci a ciki na.” Murmushi Habeeb yayi yace “Ok toh, ni ka ajiye ni a gaba kad’an mun yi da Ameer zamu had’u a wanchan coffee shop d’in”. Dariya Suraj yayi yace “Coffee da wannan ranan haka? Habeeb in dai kai ne Habeeb d’in da na sani you are not actually a fan of coffee, ko dai akwai wani abun da kuke b’oye wa? Any secret?”… Zaro ido Habeeb yayi yana dariya kafin yace “Suraj my brother in zaka ajiye ni ka ajiye ni a nan kawai banda bincike, we will talk later”. Parking Suraj yayi sannan yace “Toh ranka shi dad’e! Se ka saik’a ga chan ma Ameer d’in zaune a motar sa. Kai Habeeb ya girgiza yana dariya ya bud’e motar ya fice shi kuwa Suraj ya d’au hanyar gida……… Da sauri yake bin bayan ta yana magiya ita kuwa ko sauraron shi bata yi ballantana ta tsaya. Ganin haka ne yasa Muhseen ya fisgo hannun ta ya manna ta da bango yace “Bebs please! Ya kike son ki yarfa ni a gaban mutane? Asibiti ne fa nan. Look……abunda ya faru i am really sorry na miki Alk’awari i will deal with Laylah in such a way that she will never forget! Amma in kika yi fushi da ni yaya zan yi? You know i will be doomed baby. You know i care about you, yanzu ki fad’a min me kike so? I will happily do anything you ask for. Dariya Feenah tayi ta kalleshi tace “Leave Laylah to me, i will personally deal with her” zaro idanuwa Muhseen yayi jin kalaman Feenah da yayi, se cewa yayi “Amma Feenah bana so matter d’in ya fito fili, sanin kanki ne i am a very respected and successful business man, kuma kowa yasan Laylah matata ce in kika yi wani wrong move yanzu y’an jarida zasu samu abun fad’a, please let me handle Laylah”. Kai Feenah ta girgiza tace “Ba zan yi abunda zai jawo maka press ba i promise but dole se na koya mata cewa ni haukar tawa me licence ce!”. Tana kai nan ta zame daga jikin bangon tayi ficewar ta daga asibitin. Dunk’ule hannu Muhseen yayi ya bugi bango sannan yace “LAYLAH! Look what you’ve done! I will deal with you today, sai na koya miki habkali..”+ 4:30pm……. K’aran doorbell taji, hakan yasa ta mik’e a daddafe ta je bud’e k’ofa, suna ido Hud’u da Feenah ta koma ciki zata rufe k’ofar. Fisgo hannun ta Feenah tayi sannan ta juya ta kalli gefen ta tace “Officer ita ce wannan” wani cikin police uniform ya matso suka fuskanci juna da Laylah yace “Madam…. You are under arrest for attempting to murder Miss Feenah, muna so ki bamu had’in kai muje chan station domin mu d’auki statement d’in ki ” Murmushi Laylah tayi se tace “Please just give me a minute zan je in kimtsa ba zai yiwu in fita a haka ba. ” Babu musu suka kyale ta domin sun san babu wani hanyar escaping, d’aki ta shiga ta d’auko wata abayar ta saka sannan ta yafa mayafin ta, waya ta d’auka tayi dialling waitress Habiba ta sanar da ita abunda ke faruwa tunda ita kad’ai ce ta sani a Hotel d’in sannan ta rok’e ta da ta taimaka ta kula mata da Tasleem…. Fitowar shi daga wanka kenan yaga wayar shi tana haske numban da aka k’ira shi ya duba yaga ai Habiba waitress ke k’iran shi, da sauri yayi dialing numbar yana ta sak’e-sak’e a ranshi “I hope Laylah is alright, in ba haka ba me zai sa Habiba ta k’ira ni so soon hakq?” “Hello Mr Suraj……tun d’azu nake k’ira baka d’aga waya” nan ta kwashe abunda ke faruwa ta sanar da shi. Wani bugu zuciyar shi ke yi ,bai ma tsaya sauraron sauran maganganun ba yayi wurgi da wayan kan gado sannan ya bud’e wardrobe, blue jeans ya d’auko da farar rigar shi long sleeve da sauri sauri ya zira ba tare da ya tsaya wani shafe-shafe ba ya sa agogon sa sannan ya kwashi wayar shi, wallet da kuma makullin mota ya fice jikin shi har b’ari yake. Meenah na masa magana amma sam ko ta kanta bai bi ba ya bud’e k’aramar motar shi ya shiga, a d’ari ya fice daga harabar gidan se lokacin ya d’auki wayar shi yayi dialing numbar inspector Victor daman sun yi a kan zasu had’u. “Hello victor!…gani nan i am on my way to the station please mu had’u a chan, wani abu ne ya taso very urgent i really need your help now”. Daga d’ayan b’angaren Inspector Victor yace “Alright se ka iso Suraj, daman i have been waiting for your call, ina ma office yanzu haka, se ka iso d’in” kowannen su ya ajiye waya Suraj yacigaba da tuk’i hankalin shi duk a tashe………. Direct cikin cell suka gark’ama Laylah se kuka take mara sauti ga uban ciwon ciki dake damun ta gaba d’aya ta tsorita ta rik’e k’arfen cell d’in da hannuwan ta tana hawaye. Kamar ance d’ago kanki ai kuwa tana d’agowa suka yi ido hud’u da Suraj, nan take wani sabon kuka yazo mata, sunan shi ta k’ira a firgice “Su..rra…jj..” sosai ta bashi tausayi, k’arasa wa inda take yayi ya rik’e k’arfen cell d’in shima idanuwan shi sun yi jajir murya na rawa yace “Who…..? Who is it ? Waye ya sa aka kawo ki nan? Duk da cewa sun san you were hurt and injured? Tell me what exactly happened? Me yasa suka yi arresting naki? Me kika aikata Laylah? Kuka ne ya kufce mata da kyar ta iya kwashe labarin abunda ya faru tsakanin ta da Feenah sannan tacigaba da Fad’in “she said i am such a pity, sannan tace i am helpless, i didn’t mean to hurt her i just wanted to teach her a lesson , i have no choice Suraj, in na kyale ta zata cigaba da d’auka na as helpless, trust me Suraj” Dunk’ule hannu Suraj yayi tuni idanuwan suka sake yin jajir da sauri ya juya ba tare da yace komai ba ya nufi office d’in inspector Victor. Zame wa tayi k’asa tana kuka tana tuna irin azabar da Muhseen ke ganar da ita da wulak’ancin da yake yi mata he is nothing compared to Suraj, yayinda Muhseen yake samun pleasure in ya ci zarafin ta Suraj kuma ko da kwarzane baya k’aunar gani a jikin ta, duk da cewa tayi masa Laifi shekaru bakwai a baya, ko kad’an baya k’aunar yaga ta cutu Cikin kuka tace “Wannan wace irin k’addara ce? Ya Allah ka fitar da ni daga k’angin Muhseen….” Sun dad’e a ciki suna magana kafin inspector victor ya umarci a taho da Laylah zuwa office nashi. Shigowan ta kenan aka bata waje ta zauna tsabar kunya kasa had’a ido tayi da Suraj. “Mrs Muhseen, nayi magana da Suraj regarding your case, kuma ya sananar da ni duk abunda ya faru, Suraj was my childhood friend lokacin muna Egypt tare muka yi karatu, ya taimaka min kwarai da gaske ta fanni da dama, yau kuma na samu damar da zan rama masa alkairin da yayi min ya nemi Alfarma daga gare ni bazan k’i ba kuma a yanda na fahimci abun you are not at fault, i will grant you bail, but Mr Suraj dole se ka nemo legal papers daga court shine kad’ai alfarman da zan yi maka, gashi yanzu lokaci ya k’ure in kuma har ta wuce yau am afraid babu abunda zan iya a kai dole se on Monday sannan akwai wani takarda da zata saka hannu a kai cewa bazata sake getting involved da Feenah ba no matter what, this is a serious case! In har wani abu ya samu Feenah a gaba Am afraid Laylah zata kasance prime suspect so duk yanda zaki yi kiyi k’ok’ari kar ki yanke hukunci da kanki ki nemo security in babu akwai police”. Kai Laylah ta girgiza tana share hawayen ta. Mik’e wa Suraj yayi yace “I assure you Victor, zata kiyaye nothing of such will happen, yanzu zan je in yi preparing papers d’in duk da ma de lokaci ya k’ure amma bazai gagara ba, i will speak with my lawyer though zai d’auki lokaci please bear with me”. Kai Victor ya jinjina sannan yasa a maida Laylah sannan yayi ordern abinci mai rai da lafiya da ruwa aka kai mata…… Tun kusan k’arfe biyar da ya bar wajen har bayan maghrib bai dawo ba, duk da cewa Victor bai bari ta wahala ba duk Laylah ta jigata saboda daman ba isasshen lafiya gareta ba, a takure take zaune saman bench d’in ta had’a kai da gwiwa, takun k’afa da taji shine yasa tayi wuf ta mik’e da sauri ta koma tanan lek’a wa “Sura…..” Shiru tayi ba tare da ta k’arasa ambaton sunan Suraj d’in ba ganin cewa Muhseen ne tsaye hannuwan shi duk biyu cikin aljihu yana watso mata wani shu’umin murmushi. Daidai lokacin Suraj ma ya shigo, ganin Muhseen tsaye yasa shi yayi turus a bayan Muhseen yana kallon su. Wani sanyi taji a ranta da ta hango Suraj tsaye musamman ma da tagan shi da files ya rik’e. Dariya Muhseen yayi sannan ya k’arasa daf da cell d’in cike da tunk’aho bai san ma Suraj d’in na tsaye ba a bayan sa “Wow! Bayan duk actions d’in da kika yi d’azu da dramas d’in nan ne kenan k’arshen ki? Look at exactly where you have landed yourself because of your Middle class behaviour……… Yanzu idan wannan maganar ta fita kin news stations nawa ne zasu watsa labarin? Da hakan ta faru ko kin san irin mutumci na da zai zube? Amma kin san miye? Wollah you took me by Surprise sweetie, ashe haka kike kishi na? Then me ya hana ki kwantar da kai ki yi abunda nake so? Ina nufin try and learn from Feenah! So sexy, beautiful romantic, classy and wise she is just my type of girl! i hope kin fahimta?”. Kawar da kai Laylah tayi tana hawaye shi kuwa Suraj tsabar takaici hannu ya dunk’ule tamkar zai kai naushi. Muhseen ya cigaba da cewa “Now look what you have done! Me kike tsammanin zai faru in mutane suka ji labarin cewa matar famous industrialist Muhseen Ali was put behind bars on attempt to murder charges? You will ruin my reputation with your middle class behaviour. Jikin Suraj har karkarwa yake tsabar yanda yake jin kalaman Muhseen suna sukan shi, kai kace dashi yake. Da sauri ya juya ya bar wajen direct ya nufi office d’in inspector Victor, saida yayi controlling emotions nashi sannan ya bud’e k’ofar ya shiga+ ” Sorry na bar ka kanata jira, ga papers d’in na samo” mik’a papers d’in yayi ga Victor sannan ya nemi waje ya zauna “Very good! Ai babu komai, jinkirin yayi amfani tunda luckily ka samo papers d’in. Barin duba se ayi processing bail d’in” kai Suraj ya jinjina yana cewa “One more thing inspector, please bana son Muhseen ya san cewa nine nayi bailing Laylah, Victor kasan cewa Laylah was my wife and now my ex-wife nasan zaka fahimci cewa the reason is personal, bana son ta fuskanci wasu matsaloli saboda ni, buk’ata na ta gane cewa i care for her kuma Alhamdulillah ta fahimci hakan, wannan ma kad’ai ya ishe ni”. Murmushi Victor yayi sannan ya yi ajiyar zuci yace “You still love her don’t you?” Murmushi shima Suraj yayi sannan ya mik’e tsaye yana mai cewa “I will take my leave Victor, tambayar da kamin nasan kafi kowa sanin amsar ta, kawai de kai ma kayi tambayar ne just to kill time. Yanzu babu wani abu tsakani na da Laylah! She’s married and have already moved on, ko da ace ina k’aunar ta ma babu yanda na iya, it’s high time i learn to accept reality” Nan yayi wa Victor godiya sannan suka fita tare Victor ya taka masa har wajen motar sa sannan ya koma office. Yana tsaye jikin motar shi ya kafa wa entrance d’in station d’in ido, hango ta yayi tafe tana d’ingishi Muhseen na biye da ita tare da Inspector Victor, duk da cewa Muhseen ya tambayi wanda ya nemi bail d’in Laylah bai samu kwakwaran amsa ba, hannu suka yi shaking da Muhseen sannan ya fisgo hannun Laylah zuwa inda motar shi ke ajiye. Kallon su kawai Suraj ke yi yana tausaya wa Laylah sannan yana mamakin wanne irin namiji ne Muhseen mara tausayi mara imani, duk da cewa Laylah a jigace take bai wani damu ba sabida kawai baya son mutumcin shi ya tab’u sekace ita ba mutum ce ba….. Kai ya girgiza kawai ya bud’e motar sa zai shige, Muhseen na hango shi ya wani janyo Laylah ya matse a jikin shi kamar zai had’e da ita yana murmushi sannan ya k’ira sunan Suraj. Ba k’aramin mamaki Suraj yayi ba ganin change of attitude d’in Muhseen cikin y’an dak’ik’ai. Tsabar takaici da kyar ya k’ak’alo Murmushi yace “Mr and Mrs Muhseen Ali! What a coincidence! Barka da yamma” Murmushin shima Muhseen yayi sannan yace “Mr Maleek barka da yamma, nayi mamakin ganin ka a nan a wannan lokacin hope all is well?” Chocking smile Suraj yayi yace “The inspector here is My friend, tsawon lokaci bamu had’u ba, jiya yayi reporting ya dawo branch d’in nan so na zo mu gaisa ne”. Kai Muhseen ya kad’a yace “Nice! Zumunci ko? Thats good! Ka kyauta kam.” Tab’e baki Suraj yayi ya dubi Laylah kanta a k’asa yace “Hi Mrs Muhseen, yaya gida? D’azu i was in a hurry bamu gaisa a nutse ba, you look sick and pale! Ina fatan de lafiya??” Kasa magana tayi saboda wani kuka da ya taho mata se kad’a kai tayi ta d’an saki murmushin dole. Ganin yanda Muhseen ke matse ta a jikin shi, Suraj ya had’e rai yace “Let her go!” har jikin shi na karkarwa. Cike da mamaki Muhseen ya dubi Laylah sannan ya dubi Suraj yace “What??” Tuni Suraj ya yi controlling emotions d’in shi yayi murmushi yace ” abunda nake nufi shine…. In dai zaka cigaba da rik’e ta haka am sure zaku kwana haka a nan, it seems Mrs Muhseen bata da lafiya you better hurry home coz da alama ruwa zai sauk’o at any moment i am sure bazaka so beautiful wife d’in ka ta jik’e cikin ruwa ba” Suraj ya k’ark’are maganar da dariyan takaici. Dariyar shima Muhseen yayi cikin dariyar ya nuna Suraj da d’an yatsa yace “You are funny! I like your sense of humour, Suraj listen, idan iska ya chanja hakan ba yana nufin ruwan sama zai sauk’o ba, anyways daman tafiya zamu yi, se mun zo dinner d’in on Sunday seems like we are destined to meet these days”. Murmushi Suraj yayi ya bi su da kallo hannuwan shi nad’e a k’irjin shi har suka shige mota suka bar harabar station d’in. Motar shi ya shiga ya had’e kai da sitiyarin mota yana ta tunanin halin Muhseen na d’an maciji……..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page